Content-Length: 144836 | pFad | https://ha.wikipedia.org/wiki/Bakan_gizo

Bakan gizo - Wikipedia Jump to content

Bakan gizo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
bakan gizo
phenomenon (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na photometeor (en) Fassara
Bakan gizo, Coronel Fabriciano, Brazil
Bakan Gizo.
Bakan gizo
Bakan gizo
Bakar gizo

Bakan-gizo(( القوس - المطر)) Rainbow wani muhimmin haske ne da yake bayyana a cikin giza-gizai a sararin samaniya wanda zaka ga ya yi lanƙwasa kamar misalin baka ya dangana daga kusurwa zuwa kusurwa. A turance ana kiransa Rainbow. Shi dai wannan abu yana ɗauke da kaloli daban-daban har kusan guda bakwai, mafi akasari yana bayyana ne lokacin da hadari ya taso, cikin ikon Allah da zarar bakan gizo ya bayyana, nan take zaka ga hadarin ya lafa ma'ana zai washe zuwa wani dan lokaci daga nan kuma sai Ruwa ya kece. Amma mafi akasari wani lokacin sam baza ma ayi ruwan ba.

Wannan dalilin ne yasa Hausawa tun kaka da kakanni suke bayyana shi a matsayin cewa shi bakan gizo wai yana fitowa ne daga tsohuwar rijiya domin ya shanye ruwan dake cikin giza gizai, da zarar kuma ya sha ya koshi to sai ya amayar da ruwan daya sha, shi ne zai zubo a matsayin ruwan sama.

Wannan dai tun kaka da kakanni haka ake cewa kafin masana ilimin kimiyya su shiga lamarin.

BAKAN GIZO A KIMIYYANCE

[gyara sashe | gyara masomin]

Masana ilimin kimiyya na duniya sun yi ruwa sunyi tsaki domin binciko menene hakikanin bakan gizo, kuma daga ina yake, kuma me yasa yake bayyana, sannan kuma ta yaya yake bayyana.

Binciken masana ilimin kimiyya dai ya tabbatar da cewa bakan gizo hasken rana ne da yake bayyana a sararin samaniya a wasu lokuta idan hasken rana ya ratsa ta cikin giza gizai masu dauke da feshin ruwa wanda ya haɗe da iska mai zafi.

Wato hasken rana da muke gani kamar fari ba fari ne kaɗai ba, yana ɗauke da kaloli har bakwai ko takwas to amma idanuwanmu bazasu iya ganin dukkanin kalolin ba. Sai dai yayin da hasken rana ya ratsa ta cikin feshin ruwa ko wani gilashi sa'an nan sai mu iya ganin  dukkan kalolin sun bayyana.

Wannan shi ne abinda yake faruwa yayinda bakan gizo ya bayyana a sama, wato idan hasken rana ya ratsa ta cikin iska mai zafi ko giza-gizai masu ɗauke da feshin ruwa wanda ake kira "water droplet" a turance, to sai muga bakan gizo ya bayyana.

Kasani cewa zaka iya ganin bakan gizo ne kaɗai yayin da ka baiwa rana baya, shi yasa idan bakan gizo zai bayyana da safe to sai dai kaga ya fito a yamma, idan kuma da yamma zai bayyana to sai dai ya fito ta gabas, kaga kenan sai yayinda mai kallo ya juyawa rana baya kenan kaɗai idanuwansa zasu iya ganin bakan gizo.

Bayan haka bakan gizo kamar sha-tale-tale siffarsa take wato "circle" amma mai gani ba zai iya ganinsa duka ba saboda ana iya hangensa ne daga nesa, idanuwanmu kuma ba zasu iya kaiwa muga dukkan sashin kewayensa ba, shi yasa muke ganinsa kamar baka.

GWAJI CIKIN SAUKI

[gyara sashe | gyara masomin]

Idan kana so ka gwada fitar da bakan gizo zaka iya da kanka ba tare da amfani da na'ura ba:

1.Abu na farko da zaka tanada shi ne ruwa sai ka gumtsa a bakinka sai ka fita cikin hasken rana sai ka fesa ruwan, kana fesawa kana kallon cikin feshin nan take zaka ga launuka daban-daban sun bayyana.

2.Ko kuma ka sami madubi sai kaba abokinka ko wani ya tsaya a haske rana sai ya walwala hasken dake cikin madubin zuwa cikin daki kodai wani lungu mai dan duhu sai ka fesa ruwa a cikin hasken nan take zaka ga kaloli sun bayyana har da lankwasa kamar dai misalin yadda yake bayyana a sama.

IRE-IREN BAKAN GIZO

[gyara sashe | gyara masomin]

1. Wani lokaci guda ɗaya ne yake bayyana wato gwauron bakan gizo kenan kamar yadda wasu ke cewa.

Nau,oin Bakan gizo

.

2. A wani lokacin kuma guda biyu ne suke bayyana a lokaci ɗaya, irin waɗannan su wasu kewa laƙabi da tagwaye.









ApplySandwichStrip

pFad - (p)hone/(F)rame/(a)nonymizer/(d)eclutterfier!      Saves Data!


--- a PPN by Garber Painting Akron. With Image Size Reduction included!

Fetched URL: https://ha.wikipedia.org/wiki/Bakan_gizo

Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy