The document is a 3-part story titled "MAKWABTAKA" about a woman named Umaimah who takes a trip to Malaysia. In the first part:
- Umaimah visits a busy shopping district in Kuala Lumpur, Malaysia.
- She observes the different styles of dress worn by local women, including traditional and modern clothing.
- Umaimah interacts with some Malaysian women and learns about their customs and religion.
The document is a 3-part story titled "MAKWABTAKA" about a woman named Umaimah who takes a trip to Malaysia. In the first part:
- Umaimah visits a busy shopping district in Kuala Lumpur, Malaysia.
- She observes the different styles of dress worn by local women, including traditional and modern clothing.
- Umaimah interacts with some Malaysian women and learns about their customs and religion.
The document is a 3-part story titled "MAKWABTAKA" about a woman named Umaimah who takes a trip to Malaysia. In the first part:
- Umaimah visits a busy shopping district in Kuala Lumpur, Malaysia.
- She observes the different styles of dress worn by local women, including traditional and modern clothing.
- Umaimah interacts with some Malaysian women and learns about their customs and religion.
The document is a 3-part story titled "MAKWABTAKA" about a woman named Umaimah who takes a trip to Malaysia. In the first part:
- Umaimah visits a busy shopping district in Kuala Lumpur, Malaysia.
- She observes the different styles of dress worn by local women, including traditional and modern clothing.
- Umaimah interacts with some Malaysian women and learns about their customs and religion.
Download as TXT, PDF, TXT or read online from Scribd
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 373
MAKWABTAKA
Na Jamila Umar Tank
Ebook publish by - http://hausaebooks.cf PART 1 A cikin jerin dogayen gininnikan da suke kan titin Maharjalele, Kaula Lumpur babban birnim Malaysia. Da misalin karfe takwas na safiyar litinin, ga sanyin safiya, ga sanyi daga gandun dajin da yake gefen gidajensu yana kadowa. Iskar da ke kadawa ta yi dai-dai da yanayin garin saboda zafi-zafin da ake yi. Nan da nan sai mazauna garin suka sami nishadi da walwala a wannan safiyar. Motoci na gani na fada ne suke ta giftawa a wannan titin, yayin da wasu jama'a da yawa suke ta wurwucewa da kafafuwansu. Halittar Ubangiji kala-kala, Allah daya gari bam-bam, kowacce kasa da nata yanayin haka da irin kalar halittunta. Matansu sanye suke da riga da siket na yadi (material) mai kama da atamfa, sai dan guntun hijabi iyaka kirji, wasu kuwa riga da wando suke sakawa (jeans da blause), sai su saka hijabi ko dankwali babba. *Yan mata *yan gayu kuwa gajeren wando suke sakawa iya cinyarsu da *yar shimi. Mazansu kuwa sukan daura zani da riga ko riga da wando da hula mai kama da Pakistan launin bakake ko wasu kalolin. *Yan gajeru ne yawancinsu, farare tas-tas masu gajeran hanci da luhu luhun idanuwa, suna da gashi mai tsayi da tsanani laushi da baki. Kusan gaba dayansu musulmai ne kadan ne suke yin wani addinin. Amma duk da haka ba sa shari,ar musulunci, kowa yana holewarsa yadda yake so. Akwai bakaken indiyawa wadanda asalinsu bayi ne aka kawo su suma yanzu sun zama *yan kasar suna addinin Hindu. Sunan kudinsu Riggit, yana da daraja sosai idan aka hada shi da Naira dan har ya fi Saudi Riyad daraja. Umaimah Bello tsaleliyar budurwa matashiya wacce shekarunta basu wuce ashirin da biyar ba. Bakar fatace *yar Africa amma tafi wasu fararen fatar kyau nesa ba kusaba. Fara ce sosai idan ta shiga cikin fararen ba dukka ba ne zasu nuna mata fari ba, haka hanci, idanuwa masu kyau, baki dan madaidaici gani da gashi mai tsawo da laushi. Kirar jikinta kuwa ba kowacce mace ba ce ta sami irin wannan kirar. Umaimah doguwa ce ba tsawo tsololo ba, marar kiba amma ba bushashshiya ba. Tsaye take akan barandar gidanta, bene hawa na goma sha tara, tana kallon kasa tana shakar daddadan yanayin garin. Daga gani babu tambaya ta sami nishadi saboda annurin da yake kwaranya a fuskarta. Matsatstsan lemon zaki ne ta matse a kofin tangaran (fresh orange juice) a hannunta. Idan ta leka ta kalli titi, sai ta kurbi lemon nan mai sanyi. Kallon kowannensu take daya bayan daya, ta ga suna tafe a nutse cikin nishsdi. Sabanin tadda *yan kasarta suke Nigeria, kowa yana tafe a zabure kai ka ce koro shi aka yi, wasu suna tafe suna lissafin kudin cefane saboda masifa da suka sha mana kai. Sai tausayi ya rufeta har kwalla ta cika mata ido, musamman da ta tuno danginta na karkara Fulani masu kiwon shanu. Ta fada a bayyane, ''Allah Ka kawowa kasata Nigeria agaji, mu ma mu samu ci gaba kamar *yan kasar Malaysia. Tana daga ido ta kalli ginin gidajen da suke fuskantar gidanta, sai ta yi arba da mutumin nan mai nacin kallonta shi ma a tsaye yake a barandarsa. Daman ta ji ajikinta ana kallonta kamar yadda ya saba. Ta galla masa harara, ta ja dogon tsaki ta shige gida cike da tsananin takaici, musamman yanda ya ganta daga ita sai *yar yaloluwar rigar bacci koriya iya gwiwarta, kanta babu dankwali. Ya yi murmushi yana shirin ya gaishe ta sai ta koma cikin gida da sauri. Tana shiga falonta sai ta daga labule ta leka barandar ta ga baya nan, daga nan ta tabbatar daman don ita yake fitowa ya tsaya da ta koma shi ma ya bar wajen. Ta kuduri niyyar shirya masa rashin mutunci muddin ya ci gaba da takura mata da hana ta sakewa a farfajiyar gidanta. Bakar fata ne, amma daga ganinsa ba dan Nigeria ba ne. Koma dai dan wacce kasa ne yana da kyau da kyawun sura, dogo ne sosai mai dan kiba kadan, fari ne sol, mai hanci da gwarza-gwarzan idanuwa, mai yawan fara,a gami da fararen hakora a jere reras a cikin bakinsa madaidaici. Daga ganinsa yana da tsafta dan dan gayu ne na karshen zamani. Tun daga gashin kansa zuwa gemunsa zaka gane tsaftarsa koda yaushe zaka ga suna sheki, kamshin turarensa kuwa tun daga benenta take fara jiyowa. Ta daga ido ta kalli agogo, karfe takwas saura kwata. Tana da darasi (lecture) karfe tara don haka sai ta hanzarta fadawa wanka, kan ka ce kwabo ya gama shiryawa ta fito tsaf sanye da riga me dogon hannu launin ruwan hoda (pink blause), wando (jeans) baki da takalmi (cover shoe pink) sai dan hijabinta baki iya kirji irin na *yan kasar Malaysia. *Yar karamar jakar (computer laptop) ta ratayo a kafadarta ta rufo gidanta, ta fito. Ta hadu da jama,a da yawa a lift (*yan Malaysia, Chinese, Indian) da sauransu, amma ba su ishe ta kallo ba balle ta yi musu murmushi saboda bata sha,awar ta saba da MAKWABTANTA. Tana isa kasa ta fito daga lift ta kama gabanta sannan ta nufo get din fita. Abun mamaki sai ta ci karo da mutumin na mai nacin kallonta, wanda gidansa yake saitin gidanta shima a hawa na goma sha tara yake, amma gininsu daban sai dai get dinsu daya saboda duk gida daya ne. Nan danan ta sake tsuke fuska ta kara daga kafa tana sauri, domin taga ya fara mata wannan murmushin nasa. Yana da niyyar ya gaisheta, ita kuma bata bukatar hakan. Saurin da take ya wuce misali, don haka nan da nan ta bace masa, sai da ta waiga ta ga ba ta hango shi ba, sannan ta rage tafiya ta ci gaba da tafiyarta a nutse. Tana hawan matattakala zata tsallaka gada zuwa daya hannun kasancewar kasashen da aka ci gaba ba,a tsallaka titin mota sai dai su bi ta gada. Hawan matattakala da wuya sai ta ji ta gaji likis, kasancewar hawan da yawa. Kwatsam ta ji wata lallausar murya a gefenta cikin harshen turanci ana yi mata sannu da aiki. Ta waiga da sauri, sai ta ga mutuminta, makwabcinta. Ta yi mamaki da ganinsa saboda ta dade da tsere masa, sai dai idan ta lunguna ya biyo ba ta titi ba, don ta waiwaya ba ta ga kowa na biye da ita ba. Cikin harshen turanci yake magana, sai da ya jero mata tambayoyi har guda uku ba ta amsa masa ko guda daya ba, harya fara tunanin ko ba ta jin turanci ne? Sai ya shiga yi mata maganar gwarawa ya fara kacaccala Turancin yadda ko dan koyo zai gane. Ya ce, ''Are you from Sudan? Libya? Egypt? Ethopia? Or Mali?'' Sai ta harare shi ta kawar da kai ta ci gaba da tafiya. Hat yanzu dai yana biye da ita yadda ta ke sauri haka shi ma yake yi. ''What is your name? Yasan dai dole tasan wannan kalmar, sai ya sake ganin wata sabuwar harara daga gare ta, ta kalle shi sama da kasa , cikin takaici ta ce, ''MAYE kawai, sai nacin tsiya !'' Ta yi murmushi ya ce, ''Your name is Maye? Wow nice name. A zatonsa ta ce sunanta maye. Ya bita yana ta bayani cukin harshen Turanci, duk magana daya sai ya ambbaci sunan nan ''MAYE. Sai takaici ya sake karuwa a zuciyar Umaimah ta rasa yadda zatayi dashi, kalmar karshe da ya fada mata ita ce. ''My name is Abdul-Sabur'' Da ya ga da gaske ta kufula sai ya kyale ta, ta wuce ta nufi hanyar makarantarsu ko tantama babu a FTMS GLOBAL COLLEGE ta ke yi, don ya ga ta nufi hanyar makarantar. Idan kuwa *yar jami,ace ya za a yi ta ce ba ta jin Turanci? Sai dai idan idan ba ta da niyyar amsa masa ne, wannan hujjar mai karbuwace. Tunda ta sunkuyar da kanta kasa tana tafiya ba ta kara dagowaba balle ta waiwayo bayanta. Ba ta tsaya a ko'ina ba sai a cikin ajinsu, a inda ta sami kujera ta zauna. Zamanta ke da wuya sai Malami ya shigo ajin ya fara yi musu darasi akan abin da ta ke karantawa, wato soft ware engineering. **************************************** Washe gari misalin karfe goma na safe Umaimah ta sake fitowa ta nufi makaranta sanye ta ke da bakar abaya, sauri ta ke saboda tana da test karfe goma sha daya. Yau ma a bakin get ta ci karo da mutumin nata Abdul-Sabur, shi ma zai fita. Sanye yake da wata nakar (suit). Sai da ta yi da gaske ta gane shi, don ya sauya taga ya kara kyau. Ya yi mata murmushi sannan ya yi mata sallama gami da dorawa da ambaton sunan nan da yake zaton sunanta ne, wato, ''MAYE''. Nan da nan ta ji ya bata mata rai, ta harare shi ta wuce ba tare da ta amsa masa ba. Sai ya shiga mamakin yadda *yar musulma ta ke da bakar zuciya haka ko sallama ba ta amsawa. Ba shi kadai ta ke yiwa haka ba,daga dukkan alamu harda sauran MAKWABTAN, don ya ga yadda ta ke tafiya a fusace ba ta ko kallon inda suke. Tunda yaga Dr, Faduwa ta wuce ba su gaisa ba ya san tabbas abin ya fi karfin Dr. Faduwa, watakila ta gwada sau daya ta ga babu riba, dole ta kyale ta don ba don haka ba ya san yadda ta ke da matukar son mutane, gata da fara,a ko ka ganta ko ba ka ganta ba zata yi maka magana. Ya tsaya suka gaisa da Dr. Faduwa, sannan suka dunguma su uku suka yi bakin titi. Umaima na gabansu su biyu suna baya suna ta hirarsu cikin harshen Nasara (English). Dr. Faduwa balarabiyar Egypt ce. Allah Ya yi halittarsa anan saboda ko a larabawan ma kafin ka sami mai kyauwu irin na Faduwa sai ka bincika. Bata da tsayi kuma tana da *yar kiba amma a dire take, hanci dogo, ga manyan idanuwa, da lallausan gashi har yana taba cinyarta dan ma koda yaushe tana cikin yanke shi. Gata *yar gayun gaske ce tana shiga suturunta na larabawa a mutunce, kallo daya zaka yi mata ka tabbatar likita ce dan sana,ar ta dace da surarta. >>>>>>>>> MAKWABTAKA <<<<<<<<< PART 1 A cikin jerin dogayen gininnikan da suke kan titin Maharjalele, Kaula Lumpur babban birnim Malaysia. Da misalin karfe takwas na safiyar litinin, ga sanyin safiya, ga sanyi daga gandun dajin da yake gefen gidajensu yana kadowa. Iskar da ke kadawa ta yi dai-dai da yanayin garin saboda zafi-zafin da ake yi. Nan da nan sai mazauna garin suka sami nishadi da walwala a wannan safiyar. Motoci na gani na fada ne suke ta giftawa a wannan titin, yayin da wasu jama'a da yawa suke ta wurwucewa da kafafuwansu. Halittar Ubangiji kala-kala, Allah daya gari bam-bam, kowacce kasa da nata yanayin haka da irin kalar halittunta. Matansu sanye suke da riga da siket na yadi (material) mai kama da atamfa, sai dan guntun hijabi iyaka kirji, wasu kuwa riga da wando suke sakawa (jeans da blause), sai su saka hijabi ko dankwali babba. *Yan mata *yan gayu kuwa gajeren wando suke sakawa iya cinyarsu da *yar shimi. Mazansu kuwa sukan daura zani da riga ko riga da wando da hula mai kama da Pakistan launin bakake ko wasu kalolin. *Yan gajeru ne yawancinsu, farare tas-tas masu gajeran hanci da luhu luhun idanuwa, suna da gashi mai tsayi da tsanani laushi da baki. Kusan gaba dayansu musulmai ne kadan ne suke yin wani addinin. Amma duk da haka ba sa shari,ar musulunci, kowa yana holewarsa yadda yake so. Akwai bakaken indiyawa wadanda asalinsu bayi ne aka kawo su suma yanzu sun zama *yan kasar suna addinin Hindu. Sunan kudinsu Riggit, yana da daraja sosai idan aka hada shi da Naira dan har ya fi Saudi Riyad daraja. Umaimah Bello tsaleliyar budurwa matashiya wacce shekarunta basu wuce ashirin da biyar ba. Bakar fatace *yar Africa amma tafi wasu fararen fatar kyau nesa ba kusaba. Fara ce sosai idan ta shiga cikin fararen ba dukka ba ne zasu nuna mata fari ba, haka hanci, idanuwa masu kyau, baki dan madaidaici gani da gashi mai tsawo da laushi. Kirar jikinta kuwa ba kowacce mace ba ce ta sami irin wannan kirar. Umaimah doguwa ce ba tsawo tsololo ba, marar kiba amma ba bushashshiya ba. Tsaye take akan barandar gidanta, bene hawa na goma sha tara, tana kallon kasa tana shakar daddadan yanayin garin. Daga gani babu tambaya ta sami nishadi saboda annurin da yake kwaranya a fuskarta. Matsatstsan lemon zaki ne ta matse a kofin tangaran (fresh orange juice) a hannunta. Idan ta leka ta kalli titi, sai ta kurbi lemon nan mai sanyi. Kallon kowannensu take daya bayan daya, ta ga suna tafe a nutse cikin nishsdi. Sabanin tadda *yan kasarta suke Nigeria, kowa yana tafe a zabure kai ka ce koro shi aka yi, wasu suna tafe suna lissafin kudin cefane saboda masifa da suka sha mana kai. Sai tausayi ya rufeta har kwalla ta cika mata ido, musamman da ta tuno danginta na karkara Fulani masu kiwon shanu. Ta fada a bayyane, ''Allah Ka kawowa kasata Nigeria agaji, mu ma mu samu ci gaba kamar *yan kasar Malaysia. Tana daga ido ta kalli ginin gidajen da suke fuskantar gidanta, sai ta yi arba da mutumin nan mai nacin kallonta shi ma a tsaye yake a barandarsa. Daman ta ji ajikinta ana kallonta kamar yadda ya saba. Ta galla masa harara, ta ja dogon tsaki ta shige gida cike da tsananin takaici, musamman yanda ya ganta daga ita sai *yar yaloluwar rigar bacci koriya iya gwiwarta, kanta babu dankwali. Ya yi murmushi yana shirin ya gaishe ta sai ta koma cikin gida da sauri. Tana shiga falonta sai ta daga labule ta leka barandar ta ga baya nan, daga nan ta tabbatar daman don ita yake fitowa ya tsaya da ta koma shi ma ya bar wajen. Ta kuduri niyyar shirya masa rashin mutunci muddin ya ci gaba da takura mata da hana ta sakewa a farfajiyar gidanta. Bakar fata ne, amma daga ganinsa ba dan Nigeria ba ne. Koma dai dan wacce kasa ne yana da kyau da kyawun sura, dogo ne sosai mai dan kiba kadan, fari ne sol, mai hanci da gwarza-gwarzan idanuwa, mai yawan fara,a gami da fararen hakora a jere reras a cikin bakinsa madaidaici. Daga ganinsa yana da tsafta dan dan gayu ne na karshen zamani. Tun daga gashin kansa zuwa gemunsa zaka gane tsaftarsa koda yaushe zaka ga suna sheki, kamshin turarensa kuwa tun daga benenta take fara jiyowa. Ta daga ido ta kalli agogo, karfe takwas saura kwata. Tana da darasi (lecture) karfe tara don haka sai ta hanzarta fadawa wanka, kan ka ce kwabo ya gama shiryawa ta fito tsaf sanye da riga me dogon hannu launin ruwan hoda (pink blause), wando (jeans) baki da takalmi (cover shoe pink) sai dan hijabinta baki iya kirji irin na *yan kasar Malaysia. *Yar karamar jakar (computer laptop) ta ratayo a kafadarta ta rufo gidanta, ta fito. Ta hadu da jama,a da yawa a lift (*yan Malaysia, Chinese, Indian) da sauransu, amma ba su ishe ta kallo ba balle ta yi musu murmushi saboda bata sha,awar ta saba da MAKWABTANTA. Tana isa kasa ta fito daga lift ta kama gabanta sannan ta nufo get din fita. Abun mamaki sai ta ci karo da mutumin na mai nacin kallonta, wanda gidansa yake saitin gidanta shima a hawa na goma sha tara yake, amma gininsu daban sai dai get dinsu daya saboda duk gida daya ne. Nan danan ta sake tsuke fuska ta kara daga kafa tana sauri, domin taga ya fara mata wannan murmushin nasa. Yana da niyyar ya gaisheta, ita kuma bata bukatar hakan. Saurin da take ya wuce misali, don haka nan da nan ta bace masa, sai da ta waiga ta ga ba ta hango shi ba, sannan ta rage tafiya ta ci gaba da tafiyarta a nutse. Tana hawan matattakala zata tsallaka gada zuwa daya hannun kasancewar kasashen da aka ci gaba ba,a tsallaka titin mota sai dai su bi ta gada. Hawan matattakala da wuya sai ta ji ta gaji likis, kasancewar hawan da yawa. Kwatsam ta ji wata lallausar murya a gefenta cikin harshen turanci ana yi mata sannu da aiki. Ta waiga da sauri, sai ta ga mutuminta, makwabcinta. Ta yi mamaki da ganinsa saboda ta dade da tsere masa, sai dai idan ta lunguna ya biyo ba ta titi ba, don ta waiwaya ba ta ga kowa na biye da ita ba. Cikin harshen turanci yake magana, sai da ya jero mata tambayoyi har guda uku ba ta amsa masa ko guda daya ba, harya fara tunanin ko ba ta jin turanci ne? Sai ya shiga yi mata maganar gwarawa ya fara kacaccala Turancin yadda ko dan koyo zai gane. Ya ce, ''Are you from Sudan? Libya? Egypt? Ethopia? Or Mali?'' Sai ta harare shi ta kawar da kai ta ci gaba da tafiya. Hat yanzu dai yana biye da ita yadda ta ke sauri haka shi ma yake yi. ''What is your name? Yasan dai dole tasan wannan kalmar, sai ya sake ganin wata sabuwar harara daga gare ta, ta kalle shi sama da kasa , cikin takaici ta ce, ''MAYE kawai, sai nacin tsiya !'' Ta yi murmushi ya ce, ''Your name is Maye? Wow nice name. A zatonsa ta ce sunanta maye. Ya bita yana ta bayani cukin harshen Turanci, duk magana daya sai ya ambbaci sunan nan ''MAYE. Sai takaici ya sake karuwa a zuciyar Umaimah ta rasa yadda zatayi dashi, kalmar karshe da ya fada mata ita ce. ''My name is Abdul-Sabur'' Da ya ga da gaske ta kufula sai ya kyale ta, ta wuce ta nufi hanyar makarantarsu ko tantama babu a FTMS GLOBAL COLLEGE ta ke yi, don ya ga ta nufi hanyar makarantar. Idan kuwa *yar jami,ace ya za a yi ta ce ba ta jin Turanci? Sai dai idan idan ba ta da niyyar amsa masa ne, wannan hujjar mai karbuwace. Tunda ta sunkuyar da kanta kasa tana tafiya ba ta kara dagowaba balle ta waiwayo bayanta. Ba ta tsaya a ko'ina ba sai a cikin ajinsu, a inda ta sami kujera ta zauna. Zamanta ke da wuya sai Malami ya shigo ajin ya fara yi musu darasi akan abin da ta ke karantawa, wato soft ware engineering. **************************************** Washe gari misalin karfe goma na safe Umaimah ta sake fitowa ta nufi makaranta sanye ta ke da bakar abaya, sauri ta ke saboda tana da test karfe goma sha daya. Yau ma a bakin get ta ci karo da mutumin nata Abdul-Sabur, shi ma zai fita. Sanye yake da wata nakar (suit). Sai da ta yi da gaske ta gane shi, don ya sauya taga ya kara kyau. Ya yi mata murmushi sannan ya yi mata sallama gami da dorawa da ambaton sunan nan da yake zaton sunanta ne, wato, ''MAYE''. Nan da nan ta ji ya bata mata rai, ta harare shi ta wuce ba tare da ta amsa masa ba. Sai ya shiga mamakin yadda *yar musulma ta ke da bakar zuciya haka ko sallama ba ta amsawa. Ba shi kadai ta ke yiwa haka ba,daga dukkan alamu harda sauran MAKWABTAN, don ya ga yadda ta ke tafiya a fusace ba ta ko kallon inda suke. Tunda yaga Dr, Faduwa ta wuce ba su gaisa ba ya san tabbas abin ya fi karfin Dr. Faduwa, watakila ta gwada sau daya ta ga babu riba, dole ta kyale ta don ba don haka ba ya san yadda ta ke da matukar son mutane, gata da fara,a ko ka ganta ko ba ka ganta ba zata yi maka magana. Ya tsaya suka gaisa da Dr. Faduwa, sannan suka dunguma su uku suka yi bakin titi. Umaima na gabansu su biyu suna baya suna ta hirarsu cikin harshen Nasara (English). Dr. Faduwa balarabiyar Egypt ce. Allah Ya yi halittarsa anan saboda ko a larabawan ma kafin ka sami mai kyauwu irin na Faduwa sai ka bincika. Bata da tsayi kuma tana da *yar kiba amma a dire take, hanci dogo, ga manyan idanuwa, da lallausan gashi har yana taba cinyarta dan ma koda yaushe tana cikin yanke shi. Gata *yar gayun gaske ce tana shiga suturunta na larabawa a mutunce, kallo daya zaka yi mata ka tabbatar likita ce dan sana,ar ta dace da surarta. MAKWABTAKA 3 Manyan ledoji biyu ta cika makil da kaya, don haka ta fara tunanin hawa tasi wacce zata kai ta har kofar gida zai fi yi mata sauki don idan ta ce zata bi jirgi zata sha wuyar hawa da sauka benaye. Don haka saita tsaya a titi ta tsayar da tasi ba tare da bata lokaci ba, ta shige ita da kayanta dukka. Ta sanar masa inda zata je, ya danna meter suka nausa. Da suka isa unguwar sai ta dinga nuna masa hanya har bakin get din gidan su. Ta biyashi Riggit 10 ne cif-cif, sannan ta jido ledojinta ta fito mai tasi yaja motarsa ya tafi abinsa. Kamar daga sama ta ji wata murya wacce ta ke kokarin gusar mata da farin cikin da ta kunso daga BB Plaza. Kalmar ''MAYE'' ta ji ya ambata, Ta waiwayo a fusace Abdul-Sabur ne ya nufo ta da farin cikin sa. Ta ji kamar ta kifa masa mari, sai tayi tsaki ta juya da sauri yayin da nauyin ledojin hannunta suke rinjayarta. Cikin harshen Turanci ya ce, ''Maye, taimakonki da leda daya, saboda naga kayan sun yi miki nauyi. Ba ta amsa masa ba, sai ta ci gaba da tafiya, ya kai hannu zai karba ta daka masa tsawa. Cikin harshen Hausa yau ma ta yi masa magana. Kai ! Ka kyale ni, dole ne? Duk da ba ya jin yarenta ya ga alamar fushi a fuskarta, ya san fada take yi masa. Don haka sai ya sakar mata ledarta ya tsaya cak yana kallonta har ta haye branda, ta ci gaba da jan Ledojinta sannan ta shige lift ta haye sama. Masu suna daga zaune suna kallonsa daga dukkan alamu suna tausaya masa saboda kacaccalawar da ta yi masa. Ya wuce gidansa ransa ba dadi, babu abin da bai saka ba a ransa game da Umaimah, ya kudira har karshen rayuwarsa ya daina kula ta. Tunda Umaimah ta shiga gida ta rufe dukkan wundunanta da kofofinta ta kashe fitulun dakunan falo da korido, kicin dinta ne kawai da fitila. Ac da talabijin ce kawai a kukkunne. Wanka, Salla, cin abinci, karatu bacci da kallo kawai ta ke yi acikin gidannan ita kadai, sai da ta shafe sati guda cur ba ta leka wundo ba ma balle ta fito baranda ko ta fito waje. Tana ta kallon yanda ake ta bukukuwan kirsimeti a talabijin, ba ta damu ta ga kowa ba kamar yadda ba ta so itama aganta. Dama a ce ba sai ta fita makaranta ba za,a dinga turo mata darasin da za a koya mata ta computer, ba dan dole ba ba zata sake lekowa waje ba, don ita wannan rayuwar ta ita kadai ta fiye mata dadi. A ranar ne da daddare misalin karfe goma na dare, ta ji ana buga mata kofa. Mamaki marar misaltuwa ne ya rufo mata, don tunda ta ke a gidan nan ba ta taba yin baki ba, ba ta da kowa a kasar nan. *Yar karamar shimi ce a jikinta da gajeran wando nan danan ta yayimi zubulelen hijabinta ta saka tana sanda ta zo ta leka ta hudar da ke jikin kofa. Sai ta ga wata mace duk da batasan sunanta ba, tasan MAKWABCIYARTA ce, sun sha haduwa a lift ko a bakin get amma basa magana. Kawar Abdul-Sabur ce, don tana yawan ganin su tare, wato Dr.Faduwa. Sai taki budewa, kuma har yanzu Dr. Faduwa ba ta daina buga kofar ba gami da danna kararrawa ba kakkautawa. Umaimah tana jikin kofar tana kallonta ta ki ta bude, fiye da mintina goma. Daga karshe Dr. Faduwa ta zaro wayarta ta kira Abdul-Sabur cikin harshen turanci ta ke shaida masa tana ta bugawa ba,a bude ba, da alama dai babu kowa a gidan. Ba ta ji amsar da ya bata ba, sai taga ta kashe wayar ta ci gaba da kai-kawo a koridon. Ba jimawa sai ga AbdulSabur ya bayyana, sanye yake da doguwar riga jallabiyya fara da carbi a hannunsa, daga dukkan alamudai daga masallaci ya ke. Ya hau bugun kofa da karfi, yana danna kararrawa shi ma kamar yadda Dr. Faduwa ta yi ta gaji ta bari. Umaimah na labe tana kallonsu ko kwakwkwaran numfashi ba ta yi balle ta yi tari. Banda haushin su ba abin da ta ke ji, ta rasa dalilin shishshigin da suke yi mata, sun takurawa rayuwarta. Saboda takura ta baro kasarta ta zo inda ba,a taba saninta ba. To saboda me za su saka mata ido, dole ne a yi mutuncin? Ta ci gaba da saka yadda zata bullowa Abdul-Sabur ya kyale ta, ta yi rayuwarta ita kadai, yadda ta tsarawa kanta. Nan dai ta ga su Abdul Sabur suna tsaye suna shawarar yadda za su yi. Sun yi shawara kala-kala, sun yi shawarar kiran jami,an su zo su balla kofar su gani, ko suje makaranta su fada, ko kuma su sanarwa masu gadin gidan (security). Shawarar da suka tsaya mafi sauki, ita ce su fara sanarwa masu gadi. Nan da nan taga sun juya sun nufi lift ta tabbatar bakin get suka tafi. Ta ruga daki da gudu ta je ta saka kayanta, wata doguwar rigar leshi ce (gown) ta saka da dan karamin hijabi ta dawo bakin kofar ta tsaya tana jiran wanda Allah Zai kawo. Ba jimawa sai ga security guda biyu a bakin kofarta, hannayensu cike da makullai suna kokarin soka makulli a jikin kofar gidanta, sai ta yi wuf ta bude ta bayyana a gabansu cike da mamaki a fuskarta. Cikin harshen Turanci ta tambaye su, ''Lafiya me yake faruwa ne? Sai suka yi cirko-cirko suna kallonta amsa daya ta gagare su. Da kyar dayan ya bude baki ya ce. ''Makwabtanki ne suka lura sati guda ba sa jin motsinki, kuma ba,aga fitarki ba, sun buga ba ki bude ba, shine suka sanar mana za mu bude gidan mu ba ko lafiya? Ta hade rai tare da yamutsa fuska, ta ce, ''Ina nan, lafiyata kalau. Sai dai inaso ku jawa wadannan makwabtan nawa biyu kunne, mace da namiji su fita daga harkata, musamman namijin yana takurawa rayuwata. Ku fada masa ba shi ba ni, ya rabu da ni tunda ba zamansa nake yi ba. Suka amsa mata da, ''To zamu sanar musu... Basu rufe bakinsu ba, sai ga Abdul-Sabur da Dr. Faduwa sun taho da sauri hankalinsu a tashe suka nufo su. Kafin su karaso Umaimah ta ce da ma'aikatan ''Good night. Ta shige gida ta banko kofa ta datse ta ci gaba da lekensu ta jikin hudar kofar. Dr. Faduwa ta tambaya a dimauce, ''Kun bude gidan, tana nan lafiya? Sai suka shaida musu duk abin da ya faru, kuma suka dora da sanar da su sakon da ta bayar a fada musu. Dr. Faduwa ta dubi Abdul-Sabur shima ya dube ta, sai ya sunkuyar da kai kasa cikin jin kunya ya rasa abin da zai ce. Ma'aikatan suka wuce suka barsu a nan a tsaye suna ta kallon kofar gidan Umaima. Can Dr. Faduwa ta nisa cikin kufula. ta ce, ''Abdul tsayuwar me muke yi anan? Mu koma gidajen mu mana, ai maganinmu kenan da shiga shirgin da babu ruwanmu. Kai duk ka jawomin harna fara baccina mai dadi ka ishe ni da waya in zo in duba ta. Ashe duk bugun nan da muke tana jinmu don tsabar rainin hankali ta kyalemu saboda tsabar tsana. To ma ye ya yi zafi zamu zauna muna wulakanta kanmu, muna yar da girman mu akan *yar yarinya karama kamar wannan? Allah Ya gani mun fita hakkin MAKWABTAKA. Abdul-Sabur ya gyada kai ya ce, ''Kin fadi gaskiya Faduwa, ki yi hakuri da na jawo miki, insha Allah bazan kara jawo miki irin wannan ba. Sai suka juya suka tafi, yayin da Umaimah ta jingina ajikin kofar ta dade a tsaye, ita kanta ta rasa dalilin da yasa ta ji aranta ba dadi. Ta san tabbas bata kyauta musu ba, ai wanda ya kulaka ya damu da hakin da kake ciki mai kaunarka ne. Amma ba laifin ta ba ne, zuciyarta ne batason makwabtaka. Ba ta so adinga bada hakkin KAKWABTAKAR. **************************************** Gaba dayansu jarabawa suke yi, don haka kowannensu ba ya zama a gida, gari na wayewa sai su fice makaranta, sai da magaruba kuma. Wasu lokutan Umaima tana rigasu dawowa, tana daga kan barandarta ta ke hango dawowar su, sai tayi sauri ta koma cikin gida, don kada ma Abdul-Sabur ya hau sama ya bude barandarsa ko wundo ya ganta. Shi ma ya sha hangenta tana tafiya, ko tana dawowa daga makaranta, amma bai sake marmarin saukowa su hadu ba. Ya cika da mamakin dalilin da yasa ta ke wannan muguwar zuciya kamar ba musulma ba, harya fara tunanin kilama ba musulma ba ce, hijabin dai kawai take sakawa don ta saje da *yan kasar kamar yadda wasu baragurbi ke yi idan suna son su cimma wasu manufofi nasu. A haka suka ci gaba da zama har suka gama jarrabawar semester, aka rufe makarantu. Da yawa daga dalibai suna ta shirin tafiya gida hutu, saboda yana da yawa yayin da wasu irin su Umaimah suka mike kafa ba in da za su je. Abdul-Sabur ya yanki tikitin jirgin sama na komawa kasarsu Ghana don yin dogon hutun nan. Haka Dr. Faduwa ita ma a satin zata tafi kasarsu Egypt. Don ta shekara ba ta je ba. Ranar da Abdul-Sabur xai tafi harya saka kayansa a tasi sai ya garzaya gidan Umaima ya sakale wata farar takarda a jikin kofarta, ya juya da sauri ya tafi. Jirginsa na dare ne dan haka kwana da yini suka yi a hanya ya isa Accra babban birnin Ghana. Sai bayan tafiyar Abdul-Sabur da kwana uku Umaima ta fito zata je Bukit bin tang za ta yi cefane, sai ta razana da ganin doguwar wasika a jikin kofarta, alhali bata da kowa, kuma ba ta san kowa ba a kasar. Ta dade tana tofa addu'o'i kafin ta taba takardar, sannan ta dangwala hannu a kikin takardar, ta yi sauri ta cire hannunta alamun tsoro, kai ka ce wuta ce ta done ta. Ta sake mika hannu a karo na uku kamar mai tsantsani, kamar wacce zata taba kashi ta zaro takardar ta bude a tsorace. MAKWABTAKA 4 Ba komai ba ne a cikinta illa zankadeden rubutu cikin wani kayataccen turanci. Ta fara karanta saman, sallama ce cikakkiya aka yi mata. Ko waye mai wasikar nan cikakken musulmi ne, don haka ta sami kanta da kosawa ta karanta abin da ya ke cikin takardar. Cikin nutsuwa ta hanzarta karanta cikakken sunan marubucin wasikar Abdul-Sabur Abdul-Rashsid, wannan ne ya sa ta yi kokwanton ko ba ita aka yi wa takardar ba, kuskure ne aka samu don ba ta jin ta taba cin karo da mai irin wannan sunan. Ta manta a lokacin da mutumin nata mai kiranta da MAYE ya fada mata sunansa. Ko da ta fara karanta layi na biyu daga cikin wasikar sai ta ga kalmar 'MAYE' ta bayyana, don haka ta tabbatar ta tabbatar wasikar ta ta ce, daga makwabcinta ta ke. Sai ta ji ranta ya baci, ta yi kwafa ta gyada kai saboda takaici. Ta yamutse fuska ta fara karantawa a shelake. Ta gyara tsayuwarta, ta gyara gilashin idonta sosai ta ci gaba da karantawa, nan da nan taji kafarta kamar ba zata iya daukarta ba, saboda sagewa hade da tashin hankali. Sai ta ji ba zata iya fita ba kuma, ta koma cikin gida ta zauna a gefen gadonta tana karantawa. Ta na sake maimaitawa, yayin da taji kanta ya yi mata nauyi, zuciyarta tana ta bugawa kamar zata fashe. Ta jji ta shiga damuwa marar adadi, ta ji kamar an zare mata lakka. Wai shin me yake faruwa? Me Abdul-Sabur ya rubuta mata ne da ya ta ba zuciyarta haka Oho? Allah Shi Ya barwa kanSa sani. Har ta kwanta cikin dare ta ji maganarsa tana yi mata yawo a kwakwalwarta, sai ta laleba fitilar da ke gefen idonta ta kunna ta sake jawo wasikar a karkashin filonta ta karanta, ta sake maimaitawa. Hakika maganganun gaskiya ne, amma tana ganin ba zata iya bin gaskiyar nan ba, don zata takura. Daman masu magana suna cewa, gaskiya daci ne da ita. Abin da ya rubuta kuwa ba wani abu ba ne illa aya ce guda ya dauko sukutum don ya wa,azantar da ita, don yana tunanin jahilci ne yake damunta. Da Turanci ne amma ga fassarar kamar haka:Assalamu alaikum warahamatullahi wa barkatuhu. Ya *yar uwata musulma 'MAYE' ina matukar jin ciwon halayenki a matsayinki na musulma. Shin ko kin san MAKWABCI a musulunci? A'a ba ki sani ba, don da kin sani da kin dinga amsa sallamar MAKWABTANKI. Idan ni namiji ne kina zargin zan cutar da ke. Dr. Faduwa fa? Ki yi tunani ki gyara halayenki. A cikin arba,una hadis, hadisi na goma sha biyar Manzon Allah (S.A.W) ya ce, ''Duk wanda ya zama ya bada gaskiya da Allah da ranar lahira, to ya kyautatawa makwabcinsa. Ki sani makwabci ba karamin hakki gare shi akan makwabcinsa ba. Daga karshe ina yi miki sallama na tafi kasata Ghana. Allah ya kaddara saduwarmu, amin. Daga Abdul-Sabur Abdul-Rashid. **************************************** Dr. Faduwa ma ta tafi kasarta Egypt, bayan tafiyar AbdulSabur da kwanaki uku. Sun tafi sun barwa Umaima gidan sai ta yi ta leke-lekenta ita kadai babu mai kulata bare ya takura mata. Tama yawan tsayawa baranda ta yi ta kallon titi, idan ta gaji da tsayuwa akan baranda, sai ta jawo doguwar kujera (stool) ta zauna, idan ta fara gyangyadi sannan ta tashi ta shiga cikin gida, ta kwanta akan doguwar kujerar falonta, ko kuma ta wuce daki kan gadonta. Ba ta cika yin girki ba, sai dai tayi ta shan shayi da biskit, ko lemo (juice) da biskit abincinta ke nan. Sai jifa-jifa take dafa abinci, shima ba wani kayatacce ba ne, shinkafa da wake da mai da yaji ne saboda ba ta da walwalar da zata nutsu ta shiryawa kanta abinci mai dadi. Tana sallah ta yi addu,a sosai, haka kuma ta ke ware lokacin da take shirgar kuka, kusan kullum sai tayi wannan kukan saboda tuna baya. Tabbas kawai rayuwa ta ke amma ba ta jin dadin rayuwarta, tana iya kwana biyar bata furta kalma daya ba, banda karatun sallah bata magana. To idan ta yi maganar ma da wa za ta yi? Daman da tana da waya ne ta amsa waya ta kira ko a kira ta, to ba ta da waya don bata bukatar asan tana raye. Anya kuwa rayuwa zata yiwu a haka? Ace mutum shi kadai zaiyi rayuwa a duniya, babu dangim babu MAKWABTA, babu abokai? Kai abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, inji masu iya magana. Umaimah dai haka ta zabarwa kanta, sai ta dade tana kallon barandar Abdul-Sabur, ta ga kamar zata ganshi amma sai taga wayam! Idan iska ta kada wundon kabule ya kada, sai ta bude ido tana kallo, sai ta zaci motsinsa ne sannan taga ba shi ba ne. Ashe dai ko ya ya mutum yake dadi ne dashi? Tabbas tana jin ba dadi da ta zamo babu wanda ya san da ita. Ga shi anyi hutun makarantu balle ta je makaranta duk da ba hira ta ke da kawaye da abokai ba, amma dai tana dan jin sanyi a ranta, kuma tana rage lokaci akan dogon zaman da ta ke yi da ta ke yi agida ita kadai. Dare ya ki yi da wuri, idan da daddare ne ta ga gari ya ki wayewa da wuri. Dogon hutu ne aka basu na tsawon watanni uku, gashi ko wata daya ba ta cika ba, zaman duk ya gallabe ta. Tana ta sassaka abubuwa aranta. Ta yi shawarar ko ta tafi Negeria, amma garin da ba a taba saninta ba ta je ta gama hutunta ta dawo? Ko kuma ta tafi dubai ta shakata ko zata ga abubuwan da za su nishadantar da ita, ta ga jama,u kala-kala daga kasashe daban-daban? Amma tana fatan kada Allah Ya sa ta hadu da *yan kasarta *yan garinsu wadanda suka taba saninta a rayuwa. Domim dubai ta zama matattara, kuma cibiyar cinikayya mutane daga kowacce kasa a duniya zuwa suke. Sai ta ga da taje Dubai me zai hana ta tafi Saudia don tayi umara ta fadawa Allah bukatunta duk da tasan duk inda bawa yake ya yi addu,a Allah Yana ganinsa, kuma Mai amsawa ne. Yadda rayuwa ta kuntata a gare ta ina ita ina maganar nishadi? Ai gara ta je Saudia, ta kaura Ka,aba da Shabbaki, tunda ita a ranta ta fi kaunar mutuwa da ace ta ci gaba da rayuwa a haka. Sai ta surno da hawaye zafafa a lokacin da take binciko Passport dinta, tana tunanin yadda rayuwa ta cunkushe ta cakude mata cikin dan kankanin lokaci tana karamarta. Ta fada a bayyane yayin da ta saka gefen hannunta ta sharce hawaye. ''Alhamdu lillah alah kulli halin''. Ta fada a bayyane. Yadda taga dare haka ta ga rana, tana ta sake-sake iri-iri a ranta. Kafin gari ya waye zuciyarta ta tsayar mata da shawarar gwara ta tafi Saudia. Gari na wayewa laraba ce, misalin karfe goma sha daya na safe Umaima ta fito a shirye tsaf cikin kyakykyawar shigarta, dogon hijabi ne har kasa. Babu abin da ake iya gani a fuskarta sai tafukan hannayenta. Ta ratayo jakarta mai dauke da Passport dinta da kudi masu yawa. Sannan ta hado da ATM Card dinta, don idan kudi bai isa ba ta fitar da wani. Tana fitowa titi, sai ta tsayar da tasi tana zama ta ce ya kai ta, 'JALAN AMPANG' unguwar da ofisoshin Embassy suke. Ta shaida masa Embassy Saudi Arabia ta ke so ta je. Ba tare da bata lokaci ba suka tafi, Riggit goma sha tara ne dai-dai, ta bashi ashirin ta wuce ba tare da ta karbi canjin ba. Shigarta ke da wuya sai ta ga ma'aikata na girmamata, sun karbeta cike da fara,a saboda shigarta da ta burge su. Ta koro musu bayanin cewar Visa ta ke nema zuwa Saudiyya har tsawon wata guda saboda tana so taga likita a can. Nan danan aka yi ta dogon Turanci da cike-ciken takardu aka ce ta dawo bayan kwana biyu, bayan sun karbi Passport dinta Sai ta tsinci kanta tana mai farin ciki tun bata tabbatar za su ba ta ko ba zasu ba ta ba. Tana komawa gida ta kama harhada kayan tafiya ta zuba a akwati. Kirga awanni kawai ta ke yi don ta kagu kwana biyu ta cika taje ta karbo Visa, tikiti kawai zata yanka ta hau jirgi ta isa kasa mai tsarki. SAUDI ARABIA Haka kuwa aka yi, kafin sati ya zagayo Umaimah har ta hada komai ta isa gari mai albarka, Madina. Satinta biyu a Madina ta kaura kacokan Shabbaku, bacci ne kawai ya ke dawowa da ita dakinta na Hotel. Addu'a kawai ta ke akan dimbun bukatunta da kuma fatan cikawa da imani. Sannan ta dawo Makka a inda ta ci gaba da gudanar da ibadunta. Kwana take a harami tana dawafi, da nafilfili. Addu'a ta ke, amma fa kuka ta ke da hawaye tana fadawa mai kowa mai komai abin da yake addabarta. Takan saki nikaf dinta ta rufe fuskarta idan ta hangi *yan uwanta bakar fata, musamman idan ta ga *yan Nigeria ne Hausa/Fulani, saboda ba ta so dai-dai da rana daya ta hadu da fuskar da ta sani. A ranar da ta cika wata guda cur a ranar kuma zata koma gida Malaysia, da daddare misalin karfe tara tana cikin dawafin bankwana sai ta yi kicibus da wani abu daya firgita ta, ya ba ta mamaki, ga shi cikin rashin sa,a ba ta saka nikafinta ba. Fuskarta a bude take tarr ! A fili ga hasken lantarki tamkar da rana. Kamar yadda ta hadu da mummunan faduwar gaba mai dauke da dimbin mamaki a bayyane a fuskarta haka ta ga ya faru da su su ma. Ta tsaya cak tana kallonsu yayin da suma suka kame suna dogon kallonta. Abdul-Sabur Abdul-Rashid na hannunsa na sakale a kafadar wata mata daga dukkan alamu dai matarsa ce, wacce yake matukar so da kulawa. Sai Matar ta yi mamaki da razanar da Umaimah da Abdul-Sabur suka yi da suka ga junansu. Nan aka hau kallon-kallo tsakaninsu su dukka ukun ba tare da wani daga cikinsu ya iya furta kalma daya ba. Umaimah ce ta fara gaggauta barin wajen, ta kutsa cikin jama,a tun suna hango ta har ta bace musu. MAKWABTAKA 5 Umaimah ta sauka a kasarta Malaysia a cikin gidanta. Tabbas addu,a ba ta faduwa kasa, Allah Ya na amsa addu'ar bayinSa a duk sanda suka rokeShi. Ta riki Allah Ya yaye mata kunci da damuwa nan da ta addabi zuciyarta. Haka kuwa ta sami saukin damuwar nan da ta dankare mata a zuciya. Ita kaidai agidanta amma tana ta nishadi. Wannan muguwar faduwar gaba da mugayen tunani na tuna abubuwan da suka faru da ita a baya duk suka ragu. Haka Allah Ya amsa addu'arta Ya rage mata tunanin matattun da ta rasa a cikin danginta, ta sami tawakkali a ranta cewar sun tafi ba zasu dawo ba. Ta yi tawakkali da *yan uwanta jinin jikinta, masoyanta na hakika da ta rabu da su karfi da yaji. Ta tattara tunaninta, rayuwarta da lamuranta ga mahaliccinta. Shi kadai ne gatanta, kuma Shi ne mai taimakonta. Ta sami nutsuwa nan ta jawo takardun karatunta ta yi ta karatun abin da za su yi nan gaba tun ma kafin a koya musu. Don haka daga dukkan alamu zata fi *yan ajinsu ganewa. Karatu ne ake yinsa cikin sauki babu neman wani biro da littafi ana dogon rubutu (note), a computer (internet) za ka yi ta dubawa, kowa yana da printer sai dai ka yi ta fitarwa a cikin takardu kana karantawa. Bayan nan ta mallaki manyan littafan karatu (text books) wadanda suke bayani filla-filla game da abin da ta ke karanta, su ma suna taimaka mata wajen ganewa sosai da sosai. Da hutu ya kare sai ta ci gaba da zuwa makaranta tana daukar darasi. Kullum ba ta fashi asabar da lahadi ne kawai take zama a gida ta yini tana bacci safe da rana, da yamma kuma ta tsaya akan baranda tana kallon titi. Idan dare ya yi sai tayi karatun boko ko kur'ani, sai ta yi dan kallo ta tashi ta fara salloli (kiyamullaili), abubuwan da take gudanarwa a rayuwarta kenan a kasar nan. Har yanzu Dr. Faduwa da Engr. Abdul-Sabur ba su dawo ba, ba wai ta damu su dawo ba, amma koda yaushe suna fado mata a rai. Har ma ta fi kaunar kada su dawo balle su fara shiga rayuwarta. Ba ta ki ace da suka tafin nan ba sun tafi ke nan har abada, zai fiye mata sauki don ba ta son a dinga gaisawa kamar yadda suka bukaci haka daga gare ta. Tasan sun fi ta gaskiya, kuma ba ta kyauta musu ba. Maimakon ta yi ta rashin kyautawar ai gara ace ba sa nan, ba ta gansu ba, basa ganta ba. Don ba zata iya yi musu abin da suke bukata daga gare ta ba wannan alkawari ne ta yiwa zuciyarta babu ita babu wani MAKWABCINTA har abada. **************************************** A yammacin ranar lahadi misalin karfe biyar na yamma, Umaimah na zaune a babban wajen shakatawa na sun way Lagoom tana bangaren da aka killace namun daji (zoo). Tana zaune a gefen wani dutse wanda ke bulbulowa da ruwa, tana hango namun daji da dandazon Turawan da suke ta layin kallo da daukar hotuna. Iska mai sanyi ce ta ke ta kadawa har cikin kanta ta ke jiyo sanyin iskar duk da dan karamin hijabin da ta saka. Riga da siket ne a jikinta *yan kanti masu launin fari da baki, sannan ta saka takalmi fari mai tsananin tsini da jakarsa fara. Turawa biyu ne mace da namiji daban-daban sukazo suka roke ta ta yarda su dauki hoto da ita saboda ta yi kyau sosai. Sai ta tsinci kanta tana duban jama,a tana murmushi ita ma kamar yadda suke yi mata murmushi da zarar sun hada ido da ita. ''Assalamu alaikum''. Kalmar da ta jito kenan cikin kamilalliyar murya a saitin kunnenta na dama. Nan da nan ta wurga ido ta dubi inda muryar ta fito. Kafin ta gama waiwayowa kamshin turarensa ya daki hudojin hancinta, ko ba a fada mata ba tasan kanshin wannan disigner ne (Dolce Gabbana) ya fesa. Ta daga ido da sauri ta dubi kyakykyawar surar jikinsa, har zuwa zukekiyar fuskarsa. Yayin da idanuwanta suka tsaya cak tana kallon wasu fararen hakoransa yana yi mata dariya. Ta yi matukar mamaki da ganinsa a wannan waje kuma a dai dai wannan lokaci. Ba ta amsa masa ba, sai ta dukar da kanta kasa. Abdul-Sabur ya sake matsowa gare ta cikin harshen Nassara ya ce, ''Kin yi min izinin na zauna tare da ke? Ta girgiza kai alamar a'a Sai ya yi murmushin karfin hali ya ce, ''Ni ne Abdul-Sabur makwabcinki, yau satina guda da dawowa. Wannan kalmar ta makwabci ita ta sake saka mata tsanar ya kasance a kusa da ita, don haka tun bai rufe bakinsa ba, ta yi cimak ta mike tsaye da sauri ko waiwayowa shi ba ta yi ba, ta nufi get din fita. Kira ya ke, ''Maye! Maye!! Ta ki waiwayowa a inda kalmar 'maye ta sake hassalata. Ba ta yi wata-wata ba ta tsayar da tasi ta shige ta tafi gida. Ta nemi nishadin zuciyarta ta rasa, sai takaici da ya taru ya yi mata dankar. Ta yi da na sanin zama a gidan nan saboda takurawar da Abdul-Sabur yake yi mata. Tabbas dole ta tashi daga gidannan da zarar kudin hayarta na shekara ya kare gara ta nemi inda babu bakar fata ko daya balle ya yi tunanin yi mata magana. Tana fitowa daga tasi ta ci karo da Dr. Faduwa ita da kawayenta sun fito daga cikin get daga dukkan alamu rako su tayi za su shiga tasi su tafi gida. Don haka ta yi saurin tsayar da ya kawo Umaimah, ta yi ta kallon Umaimah tana so su hada ido ta yi mata magana, yayin da Umaima ta ki kallon inda suke balle su gaisa. Ta zaro kudin mota ta biya ta saba jakarta, ta kawar da kanta gefe ta kara gaba. Dr. Faduwa ta bi ta da kallo kawai tana girgiza kai da alama tana mamakin hali irin na Umainah. **************************************** Jiki da jini, dare daya Allah Ya ke sauke ciwo sauki kuwa sai ahankali. Kwana daya da yini guda cur ta yi tana ciwon ciki mai tsanani, tun tana kan gado tana murkususu har ciwo ya tsananta ta fado kasa. Juyi kawai ta ke a tsakar daki babu abin da ta ke ambato sai, ''Wayyo Allah, wayyo Allah cikina, Allah Ka taimake ni. Idan ciwon ya dan lafa kadan sai ta rufe ido ta fara dan bacci, can sai ciwo ya dawo ya turniketa, ta sake kwalla kiran sunan Allah, tana neman agajinSa. Allahu Akbar, Shi kadai ne mai yaye ciwo a duk sanda Ya so. Addu'a ta ke, kuka ta ke, murkususu ta ke yi ita kadai, amma ciwon bai dauke ba ga shi ta kasa tashi zaune ma balle ta tashi tsaye tayi tafiya. Tun cikin dare Abdul-Sabur yake ta kasa kunne yana sake saurarawa shi dai kamar daga dakin yarinyar nan yana jin ihu ana kiran Allah-Allah. Don haka a zaune ya kwana, idan aka jima sai ya tashi ya bude wundo ya yi ta leken gidanta bai ga kowa ba, kuma bai daina jiyo karar ba. Ya bude baramda ya fito ya tsaya yana ta sauraro, tabbas ihun mace ne, kuma daga saitin dakin yake fitowa. Tabbas yau ba lafiya akwai matsala! To amma ya za'a yi ya sani? Ta ina zai iya taimakonta? Abin da ya kwana ya yini ke nan yana zulumi. Ya saukko ya hau benensu kofar gidanta ya tsaya. Ya tabbatar ta ciki aka datse. Ihun take yi kuma sosai yana jiyo ta, sai yai kamar zai buga mata kofa sai ya tuno sakon jan kunnen da ta bayar a bashi, don haka sai ya fasa. Ya juya zai koma gida sai ya ji ba zai iyaba, ya sauko gidan Dr. Faduwa da yake kasan na Umaimah a hawa na goma sha takwas ta ke. Ya ci sa,a ma kofarta a bude don ita mace ce mai jama,a ta yi baki, wasu mata ne guda biyu *yan Indiya suna ta hira. A yadda ta gan shi ta san ba ta jin dadi, saboda ba ya walwala, sai ta shiga tambayarsa ko lafiya? Ya yi murmushin karfin hali ya gaishe ta da kawayenta, sai ya roki Dr. Faduwa ta fito waje suyi magana. Ta biyo shi a gigice, yayin da zuciyarta ta ke ta kadawa don fargabar abin da zai fada mata. Cikin zumudi ta ke tambayarsa, ''Lafiya?'' Ya girgiza kai, magana ya ke cikin marairaciyar murya. Ya ce, ''Faduwa, ki yi hakuri, ki taimaka min ki taimakawa addininki, ki yi don bin sunnar Manzon Allah (S.A.W) ki yi don hakkin MAKWABTAKA'' Sai ta dafe kiriji ta fara hawaye nan da nan ta rikice daman rikirkitacciyar ce, ma,ana tana da saurin gigicewa. Nan da nan Larabci ya hautsine bakinta ta manta ma Abdul-Sabur ba ya jin larabci. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Abdul-Sabur ishfi? Ya girgiza kai ya fada cikin harshen Turanci, ''Ki yi mini turanci don na fahimce ki. Ki kwantar da hankalinki, ba wani abu bane illa matsala ce ta faru ga makociyarmu. Waccan yarinyar ta hawa goma sha tara. Ina ga kwana ta yi a kwance ba ta da lafiya, ina jin ta kasa ta shi ta bude kofa. Ina tsoron ka da ta mutu a cikin gida ita kadai don ba ta da lafiya sosai. Dr. Faduwa ta murtike fuska, tare da aika masa harara, ta tabe baki yayin da ta yi saurin goge hawayen da ya cika mata ido. Ta murje idanuwan radau ta dube shi. Ta ce, ''Tunda nake a rayuwata ban taba ganin mutum mai laushi da rashin zuciya irinka ba. Haka tunda nake ban taba ganin mutum mai taurin da bakar zuciya ba irin na wancan yarinyar, fitsararriya ce marar kunya, wacce ba ta son mutane, mai bakar aniya. Ko a cikin satin nan na hadu da ita a bakin get ta harare ni da *yan uwana ta wuce. To ni kuwa me zan yi da ita? Shawara ta karshe da zan ba ka Abdul-Sabur shine, ka koma gidanka ka shige ka rufe, abin da babu ruwanka dadin kallo gare shi. Idan ta mutu tarube ta yi wari masu gadi za su gaji da warin su balla gidan su dauke ta su binne. Idan da *yan uwanta anan a sanar musu, ballantana ma ba ta da *yan uwa ko kawa, balle saurayi saboda bakin halinta. Ni dai kaga shiga ta gida, ina da abun yi, ba zan kare a wannan yarinyar ba. Ta juya a fusace zata shige. Dan Aunty. MAKWABTAKA 6 Ya yi sauri ya tari gabanta yana magiya cikin wata marainiyar murya mai tafe da tsananin damuwa, magiya da tausasa lafazai. Ya ce, ''Faduwa, ki yi taimako don Allah ba don niba, ba don ita ba, ba don halinta ba. Ki yi don cika hakkin MAKWABTAKA, kina da ilimi, kin san yadda Ubangiji Allah (S.W.A) Ya yi magana a alkur'ani mai girma akan hakkin makwabci akan makwabcinsa. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, a lokacin da Mala'ika Jibrilu ya ke isar masa da wahayi akan hakkin makwabci akan makwabcinsa ya ce, ya zaci za'a ce makwabci zai iya gadar makwabcinsa. Abdul-Sabur ya surnano da hawaye mai yawa. Ya ce, ''Allah Shi ne Sabur, ma,ana Mahakurci, na kasance Abdul-Sabur bawan Allah mai yawan hakuri. Bana rama tsiya da tsiya, sai da alkhairi. Haka bana fushi sabida darajar sunana. Faduwa yarinyar nan tana da hakki a kanmu a matsayinta na musulma, kuma makwabciyarmu. Mu cika hakkin daya rataya a kanmu ko da ita ta ki, zai yuwu jahilci ne ke damunta, rashin sani ko kuma wani dalili nata na daban saboda shirmen yarinta da yake damunta. Tana cikin halin wuya, ciwo mai tsanani tun cikin dare ba ta runtsa ba, ina jiyo rakinta. Dr. Faduwa ta yi kasake tana dubansa, domin ya daure ta da jijiyoyin jikinta. Ya fada cikin sassanyar murya, ta ce, ''Kana so na taimake ta ko? To ta ya ya zan iya taimakon yarinyar da ta kulle gidanta, kuma ta ce a ja mana kunne kada mu sake shiga harkarta? Abdul-Sabur ya marairaice, ya ce, ''Wajen masu gadi za mu je, mu sanar musu su debo mukullai su bude ta ta baya a ga halin da ta ke ciki. Sannan a matsayinki na likita kije da akwatinki na taimakon gaggawa (first aid box) ki taimaka mata kafin a kaita asibiti. Dr. Faduwa ta ce, ''Kaje ka sanar musu idan an bude gidan an tabbatar ba ta da lafiyar da gaske, kuma ta amince na zo sai ka kirani a waya na taho da akwatina. Abdul-Sabur ya dukar da kai kasa, ya yi godiya ya hanzarta sauka kasa wajen masu gadi, don ya sanar musu. Yayin da Dr. Faduwa ta shiga gida ta fara korowa kawayenta labarin abin da ya ke wakana tsakaninsu da Umaimah. Sun fusata dajin haka suna masu roko, magiya da ba wa Dr. Faduwa shawarar cewa ko Umaimah zata mutu kada ta taimaka mata. Ya yin da haushin Abdul-Sabur ya rufe su, suka yi ta Allah wadai da irin wannan rashin zuciya tasa. Bayan mintuna goma wayar Faduwa tayi kara, ta na dubawa ta ga sunan Abdul-Sabur ne, sai ta dubi kawayenta ta yi murmushi. Ta ce, ''Ga shi nan inajin zancen zai yi min. Suka ce ''Kada ki amsa, ki kyale su can su karata. Faduwa ta ki amsawa, sai kira yake yana sake maimaitawa amma ta ki dagawa. Kwatsam suka gan shi a gabansu, yayin da ya dubi Faduwa ya dubi wayar da ke kan cinyarta tana ruri, ma'ana amsawa ne kawai ba zata yi ba. Ya girgiza kai cikin rashin jin dadi, ya ce, ''Ashe Faduwa ba ki aminta da ayar da na kawo miki ba, game da hakkin makwabci akan makwabcinsa? A cikin suratul Nisa'i Aya ta 36 Allah Ya yi magana akan makwabta. ''Kuma ku bautawa Allah, kada ku tara shi da kowanne abu.Ga mahaifa a kyautata musu kuma ga ma,abocin zumunci da marayu da matalauta da makwabci ma,abocin kusanci da makwabci manisanci da abokin gefe da hanya da abubuwanda hannuwanku na dama suka mallaka. Lallaine Allah baya son wanda ya kasance mai takama mai yawan alfahari. Sadakallahul azim. Faduwa ta dubi kawayenta, ta ce, ''Kunji yadda yake daure ni da jijoyoyin jikina ko? Ai dole na je na duba yarinyar nan. Kawayenta suka hautsine da hayaniya suna cewa, kada ta je. Abdul-Sabur ya dube su a nazarce, ya sake tabbatarwa ba musulmai ba ne, kana ganinsu zuryan ka ga Hindu. Ya juya ya dubi Faduwa cike da takaici, ya ce, ''Har zaki tsaya kina sauraron Ahlul-kitabi, wadanda ba musulmai ba, ana miki maganar Allah da Manzon Sa, maganarsu har tafi maganar mahaliccinki? Haba Faduwa kada fa ki bata a sanadiyyar wannan abu ki rasa imaninki. Abu kalilan sai ya kai bawa aljanna, haka abu kankani sai yakai mutum wuta. A sanadiyyar taimakon yarinyar nan da zaki yi, ki ceto ranta za ki iya samun rahamar Ubangiji...'' Bai rufe bakinsa ba Faduwa ta yi cimak ta mike tsaye ta shiga daki ta dauko akwatinta, suka fice yayin da kawayenta suka bisu da harara babu abinda suke ji sai haushin Abdul-Sabur da ita da Faduwar da ta biye masa. Lallai Umaimah ta galabaita, bakinta ya bushe ko makwarwar ruwa babu a makoshinta. Ta tuje gashin kanta, haka rigar barcin da ke jikinta duk ta kanannade saboda burgima. A karkashin gado ma aka zakulota saboda burgima,, ta wahala har karfinta ya kare, don haka ko yatsanta bata iya dagawa balle ta bude ido ta kalli wanda ke kanta. Daga ta bude ido sai ta rufe luuu kamar sumammiya. Nan da nan tausayinta ya lullube zuciyoyin duk bil'adaman da yake gurin, scurity uku, Faduwa da AbdulSabur. A gigice Faduwa ta bude akwatinta ta dauko allurai da magunguna ta fara aiwatar da ayyuka irin na kwararriyar likita. Abdul-Sabur ya ruga kicin ya bude firij ya dauko ruwan sanyi ya kawo ya mikawa Dr. Faduwa. Ta ce, ''A,a kada a ba ta ruwan sanyi sai dai abu mai dumi kanar shayi ko Coka oat. Don haka Abdul-Sabur ya sake garzayawa kicin ya jona ruwan zafi a butar lantarki (kettle), ya bude lokokin kicin din sai ga komai a jere reras wajen kayan abinci daban, kayan shayi daban kwanuka,kofuna,cokula. Kicin dinta a tsare ya ke ga tsafta ko ina. Ya dauko kofi da cokali ya sake daurayewa sannan ya zuba sukari kadan, milo da madara, sannan ya zuga tafasasshen ruwan zafi akai, ya jujjuya ya dauko ya kawo. Dr. Faduwa ta karbi kofin ta dago kan Umaimah akan cinyarta ta dinga tarfa mata da cokali, sai sha take sabida tsananin yunwa da kishirwar da ta ke addabarta. Dr. Faduwa ta dubi security ta ce, ''tana bukatar karin ruwa da gwaje-gwaje a gano kan ciwon, dole a kaita asibiti. Sai suka gaggauta kiran wayar asibiti suka bukaci da su turo da motarsu (ambulance) za,a dauki mara lafiya. Abdul-Sabur ya bude durowar kayanta yana dubawa, ba tare da ya san wanda zai daukar mata ba. Kaya ne a goge a linke sanka-sanka, sai kamshi suke yi, daga baya ya riguna da bangarensu, siket, abayoyi, mayafai da dai sauransu. Ya jawo wata doguwar riga ja (abaya) da dan kwalin ya hada ya mikawa Faduwa, ya ce ta saka mata. Ya roki masu gadi da su fita falo su bari mace ta shityata. A falo ne ya isa kan teburin cin abinci a in da ta dora laptop dinta da takardunta, ya shiga babbankadawa, a nan ne ya ke ganin sunanta ajikin takardun, ta rubuta UMAIMA BELLO, a she ba sunanta MAYE ba? To me kalmar MAYE take nufi? Ya karanta a baiyane, ya sake maimaitawa, sai yau yasan sunanta. Ya ci gaba da bankada durorwoyinta da suke falon, takardu ne kala-kala duk na makaranta. A jikin durowar Talabijin stand ya ga wata *yar karamar jaka ya bude ya ga himilin hotunanta ne. Ya fara budewa cikin sauri yana dubawa, ya ganta ita da danginta mata da maza, yara da manya, da kuma tsofaffi. Wato iyayenta da kakanninta. Ya cika da mamaki da ya ga wasu hotunan, gashi babu wanda zai iya tambaya a yi masa bayani. Bai gama kallo ba ya ji jiniyar mota (zmbulance), kan kace kwabo sun hayo da gadonsu, suka shiga dakinta cikin gaggawa, suka dorata akan gadon mai taya suka turota a shassheme kamar gawa sai numfashi ta ke yi sama-sama. Abdul-Sabur ya shiga dakinta da sauri ya bude jakarta ya fara bincikawa yana neman I,D card dinta bai gani ba, sai dai yaga passport dinta. Ya yi sauri ya bude ya duba, ya ga hotonta da sunanta radau, sai yau yasan kasarta ashe yar Nigeria ce? Ya zakulo *yar karamar jaka (wallet). A cikin jakar ya bude anan ne ya ga I.D card dinta na makaranta wato FTMS, da wasu kuma na wasu makarantunta na can Nigeria. Ya hada ya mikawa malaman asibitin. Shi da masu gadin gidan ne suka kukkulle mata ko ina a gidan, sannan suka watse. Dr. Faduwa ta koma gidanta, security suna rike da makullin gidan suka koma dan dakinsu a bakin get, yayin da Abdul-Sabur ya koma gidansa. Umaima kuwa na can akan gadon asibitin ana ceto rayuwarta don ta galabaita, bata ciki hayyacinta. Daga asibitin aka yi wa makarantarta waya suka tura malamai mata guda biyu, su ne za su dinga zama da ita. Ya kasa zaune, ya kasa tsaye, balle ya kwanta, babu ma maganar cin abinci a wajen Abdul-Sabur, ya shiga damuwa sosai, saboda tausayin rai. Babban abun tausayin ma shine rashin hakikan *yan uwanta a kusa ga babu waya balle a buga a sanar musu. Ko saboda hakin mutuwa. Addu,a yake, Allah Ya sa ta rayu kada ta mutu, ba ya son ta mutu duk da ta tsane shi, ba ta ki ta ga ba ya doron kasa ba. A daddafe ya bari gari ya waye, da sassafe ya shirya ya fito wajen masu gadi, da suka gaisa sai ya tambaye su adireshin asibitin da aka kai Umainah. A rubuce suka bashi kamar haka:- Sime Darby Medical Center Subang Jaya Jalan SS12/1A 47500 Selangor Darul Ehsan, Malaysia. Babu wata matsala yasan ma asibitin, ba shi da nisa da makarantarsu. Sai ya yi musu godiya ya nufi asibitin. Yana hanya yana fargaba guda biyu. Na farko yana fargabar yadda zaiga jikinta, sauki ko tsanani. Sannan na biyu yana fargabar yadda za ta yi idan ta ganshi, farin ciki ko takaici? MAKWABTAKA 7 Ko ba a fada masa ba, yasan ta tsane shi, ba mamaki idan ta ganshi ta disga shi. Shi dai koma mai zai faru ya ji ya gani sai ya je ya saka a ransa duk abin da yake yi yana yi ne saboda Allah, kuma a wajenSa yake neman sakayya. Ya isa asibiti a reception, ya yi musu bayanin suna da yanayin ciwonta, na da nan suka fada masa hawa na uku ta ke, da lambar dakin da ta ke. Ya yi godiya ya nufi dakin, yayin da fargabar da yake ciki ta sake tsananta. Yana ta addu'a dai har ya isa kofar dakin, ya kwankwasa a nutse gami da yin sallama, sai yaji muryar wasu mata sun amsa masa sannan ya tura kofar ya shiga. Aka hau kallon-kallo tsakaninsa da matan biyu, daya *yar Malaysia ce, daya kuwa India ce. Yayin da Umaimah ta ke sheme akan gado ana mata karin ruwa, idanuwanta a rufe alama dai baccci ta ke yi. Ya karaso jikin gadon ya gaishe su, sannan ya gabatar da kansa cewar shi makocinta ne, sannan suka saki ransu don da sun yi masa kallon rashin fahimta. Ya tambayesu yaya me jikim? Suka yi ta koro masa bayanin abubuwan da suka faru da ita a jiya, cewar ciwon cikin ya tsananta, amma yau da safe ta sami sauki sosai, har ta sami bacci. A cikin bayanansu ya gane cewar ma,aikatan makarantarta ne, sai ya ji hankalinsa ya kwanta tun da ga masu kula da ita Allah Ya kawo. Ya je kanta ya tsaya ya yi ta tofa mata addu,o,i na neman sauki, afuwa, rangwame daga Rabbul-Samawati. Ya ce da su, ''Idan ta tashi a ce Abdul-Sabur yana yi mata sannu. Ya yi musu sallama ya tafi sai yanzu yaji hankalinsa ya kwanta, da ya ga jikin da sauki. Da yammacin ranar Dr. Faduwa zata tafi unguwa ta biyo ta gidansa ta iske shi a zaune a falo ya yi tagumi. Kallo daya ta yi masa ta san bayajin dadin rayuwarsa. Ta sami kujera ta zauna ta gaishe shi, sannan ta tambaye shi. Shin yana da labarin halin da marar lafiyar nan ta ke? Ya amsa mata da, ''eh ta sami sauki sosai, na je na duba ta ma dazu. Sai ta yi kasake tana kallonsa, da alama tana so ta ji yadda suka karke. Ta tambaya da sauri ''Ta ganka? Kun gaisa? Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''gaskiya bata ma san na je ba, saboda tana bacci. Dr. Faduwa ta yi ajiyar zuciya ta ce, ''Barkanka, na taya ka murna da ba ka sameta idon ta biyu ba. Ya yi mamaki dajin kalamanta, sai ya tambaya, ''Me yasa kika ce haka?'' Ta tabe baki ta ce, ''Da ba zata amsa maka ba, saboda yadda nasan tsanar da ta yi mana. Ya kyalkyale da dariya, ya ce, ''Kai Faduwa, ai abun bai kai haka ba. Ni dai uzirin da nake bata shine, na san tana da wani dalilinta na daban, aka bibiya laifin wasu ne ya shafemu. Ina yi mata addu'a Allah Ya sa ta gane. Faduwa ta ce, ''Ai ba don kai ba yarinyar nan ko zata mutu ba zanje kanta ba. Kai ne dai da naci ka kasa rabuwa da ita, na rasa dalili. Koda yake na fahimce ka, kana son yarinyar nan sosai, kuma har cikin zuciyarka. Abdul-Sabur ya gyra zama ya zazzare ido don mamaki, sai ya girgiza kai. Ya ce, ''Babu ko daya, da za ki yarda da ni yi miki rantsuwa, wallahi babu maganar so a tsakanina da wannan yarinyar. Haba Faduwa kamar ba ki san halina ba, shekararmu biyu da ke agidan nan, ya kamata ki fahimce ni ki kuma fahimci irin macen da take burge ni. Na daya, kin sanni da son macen da ta mallaki hankalinta, ta san rayuwar duniya sosai, ba *yan matan nan da suke rawar kai ba, wai su *yan boko. Umaimah yarinya ce karama ba sa,ar soyayyata ba ce. Na biyu halayenta kwata-kwata ba su yi min ba don ba ta da tarbiyya, fitsararriya ce, ba ta burge ni ba don ina son mace mai kunya da sanin darajar na gaba da ita. Na uku, musulma ce amma ba ta da ilimin aiwatar da addinin don ba ta bin abin da Allah ya ce, ba ta kyautatawa makwabtanta ba, bata bayar da hakkin MAKWABTAKA. Inajin tausayinta ne kawai kasancewarta mace, kuma yarinya karama a kasar da babu iyayenta, ba dangi ba kawayenta. Ina so na nusantar da ita tasan hakkin makwabci akan makwabcinsa, ko don gaba ma tasan yadda zata zauna da makwabtanta ko bayan ta yi aure. Na dauketa kamar karamar kanwata mai neman shawarata. Yanzu da na biye mata shirmen nan da ta ke na babu ruwanta da mu, da ta yaya za,a yi a san tana cikin gidan nan a kwance babu lafiya? Ai ko mutuwa ta yi ba za,a sani ba, sai dai idan ta mutun ta kwana uku ta rube wari ya ishi jama,ar gidan a balla kofa a ganta. Ina amfanin irin wannan alhalin mu dukka musulmai ne? Faduwa, ina tausayin mace, musamman wacce ba ta gaban iyayenta, ko hannun mijinta. Duk inda na ga matashiyar mace sai na ji ina sonta, saboda ina da kanwa wacce na fi sonta a duniya fiye da kowa da kuma komai da na mallaka. Dr. Faduwa ta yi murmushi, ta ce. ''Nasan da haka Abdul amma fa yarinyar can ba *yar mutunci ba ce. Duk inda ka kai ga nuna mata hanyar Allah ba zata saurare ka ba. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Wanda yake abu saboda Allah baya cewa ya gaji kuma baya fushi ya ce ya daina. Ina yi mata addu'ar Allah Ya ganar da ita, yanzu a matsayinki na likita idan kika duba yarinyar nan (psychologycally) za ki ga tana da matsala a rayuwarta. Zai yiwu an guma mata wani abu ne na takaici ta yi hijira ta dawo nan, amma ya za,ayi ace mace ita kadai ko kawa ba ta yi, balle saurayi ko miji, kuma ko wayar hannu ba ta da ita (handset). Wannan fa abin dubawa ne Faduwa. Dr. Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Na lura tana cikin damuwa, amma duk damuwarta ai ba ta fi ni ba, amma na ke daurewa na ke shiga jama,a na ke gaisawa da kowa lafiya. Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ka ji ta, wai ba ta kai ki ba ni me yiwuwa duk na fi ku damuwa, amma nake daurewa. Kowanne mutum da kika gani a duniyar nan yana da tasa matsalar, kuma tasa kadai ya sani, sai ya yi ta ganin kamar ya fi kowa matsala. Dr. Faduwa ta ce, ''Haka ne, Allah Ya yaye mana. Zo ka raka ni 'KL Sentral zan je na ga wata kawata ta haihu. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''yi hakuri wallahi bazan iya zuwa ba. Bana jin dadi saboda bana iya cin abinci, ba na bacci kwana biyu ke nan. Dr. Faduwa ta mike tsaye ta yi dariya, ta ce, ''Lallai kai kafi kowa ma tausayi, akan ciwon yarinyar ne ka kasa bacci da cin abinci? Ai kuwa gara ma ka cire ciwon nan a ranka, kaci gaba da harkokinka idan dai wannan ce ina nan da kai tana warkewa zata ce ba ta san mu ba. Abdul ya yi dariya ya ce, ''Ke ma na ga alama kin kasa fahimta ta, amma ina fatan ki fahimce ni nan gana. Faduwa ta fice ba tare da ta sake cewa komai ba, ta bar Abdul-Sabur a nan a zaune yana tunani. Bayan kwanaki hudu, sannan aka sallamo Umaimah daga asibiti, sai da matan nan biyu suka raka ta har cikin falonta. Bayan sun roke ta ta dawo gidansu ta zauna har jikinta ya yi kwari saboda ba dadi zaman ita kadai ta ki amincewa, ta ce su barta zata iya zama ita kadai. Suka ba ta magunguna suka fita suka tafi a motar da suka zo. Fitarsu da kamar mintina goma, Umaimah na zaune har yanzu akan kujera tana tunanin tashi ta rufe kofa sannan ta shiga ta yi wanka, sai taji ana danna kararrawa a bakin kofar gidanta. Ta yi mamaki marar misaltuwa, ta taso da sauri ta daga labule don kofar a bude ta ke. Abdul-Sabur ta gani cikin kyakykyawar shigarsa ta wando baki (jeans) da riga fara (Shirt). Kamshin nan nasa na turaren (Dolce Gabbana) shi ne ya daki hancinta, kamshin nan ba karamin tuno mata baya ya yi ba. Ta yi mamak da jin yau ya ambaci sunanta 'Umaimah' maimakon 'Maye' da yake kiranta a baya. Sai ta ji saukin tsanar da tayi masa a baya. Ba ta amsa masa ba, ta ci gaba da sauraron abin da zai ce don ta matsu ya fada ya wuce, ba ta kaunar ya dade a bakin kofarta. Ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Ya ya jikinki? Ina fatan kin sami sauki sosai? Allah Ya baki lafiya. Ta saki labulen ta labe ba tare da ta amsa masa ba. Ya ci gaba da jiran amsar da zata ba shi, ya ji ta yi shuru. Sai ya gyara tsayuwa. Ya ce, ''Umaima, ba na binki da wata manufa illa alkhairi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, kada ka kwana ka koshi makocinka ya kwanta da yunwa. Haka ka dubashi idan bashi da lafiya. Idan har makwabci bai amince da makwabcinsa ba yana gudun zai cuce shi ta hanyar fada masa bakar magana, zagi ko duka, ko kuma neman halaka shi, to wannan makwabci ba shi da rabo a lahira. A kwai kissar wata mata da ta rasu bayan kuma an shaide ta da yawan sallah, azumi, kyauta sadaka. Amma aka ganta a wuta. Da Annabi (S.A.W) Ya binciki abubuwan da ta aikata a rayuwarta ta duniya sai aka shaide ta ta cika komai banda abu daya, shine ba ta kyautatawa makwabtanta. Tana musguna musu, ba ta zauna lafiya da su ba, wannan dalili shi kadai ne ya kaita wuta (Wa'iyazubillah). Don haka ya ke kanwata Umaimah ki yi hakuri ki zauna da MAKWABTANKI lafiya, ki ba ni ba ko don nan gaba. Na barki lafiya, duba ki na zo yi ina fatan Allah Ya baki lafiya, bissalam. Ya juya ya tafi gidansa. Sai ya wuce ya bar ta a nane da jikin labule ta kasa motsawa, daga dukkan alamu wa'azin fa ya shige ta, dan ta tsorata, tabbas ta san gaskiya ya fada mata tsagwaronta. Amma ba ta jin zata iya aiwatar da nasihohinsa, saboda dalilinta da yawa akan cuta da musgunawar da MAKWABTANTA suka dade suna yi mata a doron kasa. Ta girgiza kai ta fada a bayyane, ''Zam iya amincewa da kowa a duniya, amma ban da makwabtana, saboda sun zalunce ni.'' UHM to ai da sauki tunda ni ba makwabci bane, da fatan zaki aminta dani Umaimah MAKWABTAKA 8 Ta jawo kofarta a fusace ta datse, yayin da ta hau faman huci, ranta ya duguzuma ya baci. Ta tabbatar muddin ba ta bi nasihar Abdul-Sabur ba tana cikin halaka. Duk abin da ya fada gaskiya ya fada mata, amma kuma ya tuno mata da kasurgumin bacin ran da ya faru da ita a baya tsakaninta da MAKWABTA. Ta dade a zaune a falo tana tunanin yadda aka yi MAKWABTANTA suka san ba ta da lafiya, sai ta shiga mamakin yadda ma aka shigo gidan akasan bata da lafiya alhali kofarta a kulle. Ta tashi a hankali ta shiga dakin, ta tsaya tana kallon inda ta kwanta, ta shiga dauki ba dadi da kwakwalwarta tana kokarin tuno abubuwan da suka faru da ita kafin ta fara ciwon ciki. Abin da zata iya tunawa shi ne, ta saka rigar bacci ta kwanta akan gado, yayin da ta fara jin ciwon ciki mai tsanani ya turnike ta. Tun tana juyi harta fado kasa abin da zata iya tunawa kenan. Ta tsuguna kasa a hankali ta dauko rigarta a tsakar daki ta dudduba, sai ta shiga dogon tunanin yadda aka yi aka sauya mata rigar jikinta. To yaya ma aka yi aka san bata da lafiya? Shine abin da yake damunta. Tabbas ishara ce Allah Ya nuna mata, saboda mutum dadi ne da shi. Duk in da ka kai da kin mutane ka kwanta kai ka dai a cikin gida ka mutu dole mutane za su bude su dauke gawar, su bunneka, don haka dole mutum ya yi mu'amala da mutane. Ta dade a zaune tana tunani, har da koke-koke, dom ita ma ba haka ta so ta kasance tare da jama,aba, dole ce ta saka ta ko ta fito da niyyar gaisawa da jama,a tana ganinsu sai ranta ya baci ta fasa. Ta jima a zaune a gefen gado tana kuka, sannan ta tashi ta shiga wanka. Bayan ta yi wanka ta yi sallah, sannan ta lallaba ta shiga kicin don dafa abin da zata ci, saboda yunwar da ta ke addabarta. Ciwo ne yake samun mutum a lokaci guda, sauki kuwa sai a hankali. Babu ciwon cikin dai a yanzu amma ba ta jin karfin jikinta da dadin bakinta. Tana kuma shan magungunanta, don haka gaba daya satin Umaimah ta kasance a gida ba ta fita makaranta ba. Sai da ta tabbatar ta warware sosai, sannan ta shirya ta fito zuwa makaranta, ranar litinin da safe da misalin karfe tara kenan. A cikin lift Umaima ta hadu da Dr.Faduwa, mai hali ba ya fasa halinsa, ba ta yarda ta hada ido da Dr.Faduwa ba, balle ta yi mata sallama. Kasancewar su takwas ne a cikin lift din, sai ta sami lungu ta labe daga bayan Faduwa har suka iso kasa inda kowa ya firfito. Jefa kafarsu ke da wuya akan baranda suka yi kicibus da Abdul-Sabur daga dukkan alamu Faduwa yake jira. Daga yadda ya ga Umaimah ta zabura ya san ta yi mamakin ganinsa dai-dai wannan lokacin, kuma a wannan waje. ''Zo ki wuce''. Inji Abdul-Sabur ya ce da Umaimah gami da matsawa ya bata hanya. Ta sunkuyar da kanta kasa ta wuce abinta ba tare da ta gaishe shi ba kamar yadda ya ke sa ran samun gaisuwarta ko don wa,azin da yayi mata. Faduwa ta dube shi ta juya ta dubi Umaimah, ta girgiza kai ta ce da shi. ''Ka ga abin da nake fada maka ko? Ai mai hali ba ya fasa halinsa. Tafiya suke zuwa get din fita, yayin da Umaimah ke gabansu, sauri kawai ta ke yi, don kada ma ta jera da su. Amma duk da haka takan jiwo wasu abubuwan da suke fada a kanta. Faduwa fada ta ke yi da karfi kan rashin tarbiyyar Umaimah, yayin da Abdul-Sabur yake nemar mata uziri cewar, akwai dalilinta na yin haka kada tayi saurin yanke mata hukunci. Umaimah ta tabe baki ta ce a ranta, ''Koma dai me zaku ce matsalarku ce, ku ta shafa dan ba kwa gabana, da zaku rabu da ni, da na fi jin dadi. Ta kara daga kafa tana sauri, ta haye saman bene a inda zata haye gada zuwa makarantarta. Daga nan ba ta waiwayo su ba, bata san inda suka bulle ba kuma. Tana kyautata zaton tasi suka tsayar suka shiga. **************************************** Zangon karatu na karshen 2nd semester ya zo karshe, har an fara jarabawa a wasu makarantun, yayin da makarantar su Umaimah har sun yi nisa da farawa. Ta yi karatu cikin dare, ta yi da safe, ta yi da maraice, yayin da ta ji kwakwalwarta ta yi kamar zata buga don takura. Harta daina fahimtar abin da ta ke karantawa don haka sai ta harhada ta rufe. Ta fito baranda ta tsaya tana kallon titi, motoci da mutanen da suke giftawa. Iska mai sanyi ta yamma ce ta ke fifitawa, ta sake gyra tsayuwarta tana kallonsu, sai ta ji ta fara washewa daga damuwa da gajiyar karatu. Sallama ta ji an yi mata babu bata lokaci ta kalli inda muryar ta fito, ko ba a fada mata ba ta san AbdulSabur ne dan daga saitin gidansa muryar ta fito. Ta dube shi ta ga yana tsaye a barandarsa yana yi mata murmushi. Ya yi matukar mamaki da ya ji ta amsa da ''Wa'alaikassalam. ''Ya ya karatu? Ya yi karfin halin tambayarta. Wannan karon dai bashi da amsa, don haka ya ja fatar bakin ya kame, bai sake yi mata magana ba. A zatonsa zata koma cikin gida kamar yadda ta saba idan ta ganshi, sai ya ga ba ta tafi ba, amma ba ta sake daga ta dube shi ba. Ya dade a tsaye yana kallonta, sai ya koma ciki ya rabu da ita. Sai da ta ji ana kiran sallar magaruba ta koma cikin gida daga nan bai sake ganinta ba, sai da yammar washegari tana dawowa daga makaranta da alama dai jarabawa ta je ta zana ta dawo. **************************************** A lokacin da gaba daya makarantun jami'o'in suka gama jarabawa suka yi hutu, dalibai suka fara yayewa, yayin da Umaimah ta ji a ranta, daman zata iya tafiya kasarta hutu itama don ta gaji da zaman kadaici, sai dai kash! Ba zata iya tafiya ba don ba ta so a san tana raye. Jifa-jifa ta ke hango Faduwa da Abdul-Sabur da alama su ma wannan hutun ba zasu tafi gida ba. Suna nan, don haka sai ta dan ji sanyi a ranata, ta ji ashe ba ita kadai ba ce wacce zata zauna. Duk da ba ta tunanin za su dauke mata kewar komai. Idan taji kamar zuciyarta zata fashe don tunani, sai ta shirya ta fita wuraren shan iska, inda zata ga jama'a daban-daban da abubuwa masu ban sha,awa. Malaysia kasa ce wacce babu abinda suka saka a gaba irin shakatawa musamman daga yamma zuwa dare. Idan ka shiga cikin KL inda tulin malls suke babu abin da zaka dinga jiyowa sai sautin kida. A gefen tituna kuwa jama,a ne da'ira-da'ira sun zage abubuwan kallo kamar masu wasa da maciji, masu kada giraya (giter), masu rufa ido. Kida kuwa duk kusurwar da ka zo giftawa da irin sautinsa, kasancewar baki musamman Turawa suna shigowa sosai don shakatawa. A yau Umaimah yawon nata ne ya motsa don ba ta san takamaimai inda zata nufa ba, zaman gidan ne ya ishe ta niyyarta tunda yamma idan ta fita sai dayan dare zata shigo gida. Don kwanaki biyu ta yi tana bacci ta gaji da kwanciya. Da ta je sayan tikitin jirgin kasa sai ta tamabayesu, ina ne tasha ta karshe idan aka tafi daga nan? Matar mai sayr da tikiti ta zayyano mata cewar. ''Yanzu jirgi zai zo daga KL Centaral, ya shigo ta 'Tunsamban Than' ya zo nan 'Maharjalela', sai ku tafi 'Hangtuah', sai 'Imbi' sannan 'Bukit bin tang, Umaimah ta ce, ''Idan ya wuce Bukit bin tang, sai ya tafi ina? Matar ta ce, ''Zai tafi 'Raja Chuland', 'Bukit nenas' 'Dang Wangi', 'Medantuanku', 'Chow kit' sai ya tsaya a 'Titi Wangsa' sannan ya juyo...'' Umaimah ta yi murmushi, saboda ta ji yawon da akalla zata kai sha biyun dare a hanya. Sai ta tambaya nawa ne kudinta daga Maharjalela zuwa Titi wangsa? Matar ta ce, ''Riggit goma sha uku''. Ta zaro ta biya ta wuce, zuciyarta cike da annuri. Ana ta turmutsitsin shiga jirgi mutumin da ke gabanta ya yi sa'ar samun kujera ya zauna. Ita kuwa a tsaye ta ke ta rike karfe. Bayan ya zauna ya juto ya dubi mutanen da suke tsaye a kansa. Abdul-Sabur ne sai yayi ido hudu da Umaimah itama sai yanzu taga fuskarsa, sai ya yi zuruf ya mike tsaye kai ka ce bawa ne ya ga ubangidansa. Yayin da ita kuma take kokarin kawar da kai gefe har da matsawa da da hanya ma cikin mutane zata kutsa ta bace masa. Cikin harshen Turanci yake magana, don haka duk jama'a na jin abin da yake fada kuma sun zuba musu ido. Ya ce, ''Zo ki zauna, ki zauna ga kujera. Umaimah zo ki zauna. Har sau uku, don babu yadda zata yi ido ya yi mata yawa ta lallabo ta zauna cikin sanda kanta a sunkuye a kasa. Ranta a bace don bata so hadu da wanda ta sani a yammacin nan, saboda ta fito da niyyar yawatawa ta ga gari, gari ya ganta. Ba ta son wani mahaluki ya dame ta kuma. Jirgi dai sai tafiya yake yana tsayawa a tasoshisa dabandaban, ya sauke wasu ya kwashi wasu. Sai ta ga AbdulSabur ba shi da niyyar sauka ta dago ta dube shi, shima ya dube ta sai ya yi mata murmushi, Ya ce, ''Ai ba'a zo Bukit bin tang ba na san a nan za ki sauka, ni ma haka can zan je. Ta tabe baki ta sunkuyar da kai kasa cikin rashin kulawa da zancensa. Ba jimawa aka sanar, 'Bukit bin tang', ya juyo ya kalle ta, sai ta rataya jakarta ta yunkura ta tashi, ta bi bayansa su da dandazon jama,a. Yayin da ta tabbatar ya wuce gaba, sai ta noke ta ki fita ta kutsa lungu cikin mutane ta sami kujera ta yi zamanta a wani bangaren. Ba ta dago da kanta ba sai da ta tabbatar an rufe jirgi yadda bazai iya dawowa ba. Ai kuwa ta hango shi yana ta waiwaye-waiwaye yana nemanta, har ya so ya ba ta tausayi, amma kuma taji sakayau kamar an cire mata kaya da ya sauka. MAKWABTAKA 9 Duk ta karaci yawonta da bata lokacinta a karfe goma ta hawo jirgi ta juyo gida. Da suka zo tashar 'Bukit bin tang' sai suka sauke fasinjoji suka dibi wasu. Kwatsam sai ta ga AbdulSabur ya nufo ta kai tsaye, idanuwansa a kanta suke. A ranta ta ce, ''Ga mayen nan, kamar aljani, duk inda na sa kafata sai na ganshi ko da kuwa kasar na bari. Anya kuwa wannan mutum ne? Ta hada girar sama da kasaa, don tasan ta yi masa laifi kada ma ya ga fuskar tambayarta wani abu. Sai ta cika da mamaki a lokacin da ta ga fara,arsa yadda ka san ba ta taba saba masa ba. Ya yi mata sallama gami da yi mata sannu da dawowa. Ta gyada kai kawai ba ta amsa masa ba, suka ci gaba da tafiya babu abin da yake yi illa kakkare ta da yake, don kada a matseta a lungu saboda karatan da suka cunkushe cikin jirgin. Jirgi ya cika makil saboda kowa ya na so ya koma gida, don dare ya yi. Har yanzu su duk a tsaitsaye suke sun rike igiya babu kujerar zama. Motsi kadan ta yi sai ya juyo ya kalle ta cikin tattausar murya yake yi mata sannu. Sai ta ji kamar ta kurma ihu don takaicin ya shiga harkarta. A haka dai har suka karasa 'Maharjalela'. Babu yadda ta iya, dole ta fito dan niyyarta ta ki fita a wuce da ita wata unguwar, sannan ta dawo idan ya tafi. Kamar yasan haka ta ke nufi, sai da ya tabbatar ya saka ta a gaba suka fito tare. Tafiya kawai take kanta a sunkuye a kasa, tambaya kala-kala da labaru ya ke rero mata, wadanda basu shafe ta ba, ba su shafi tsarin rayuwarta ba. 'Yes ko 'No kawai ta ke jero masa. Har suka sauko daga tashar jirgin suka nufo gida. Tambayrta yake, ya ya kwarin jikinta, cikin ya daina ciwo ko? Ta dago kai ta dube shi a fusace ta galla masa harara ta girgiza kai don takaici gami da dorawa da dan siririn tsaki. Cikin harshen turanci suke magana ta ce, ''Kai.... Kai Abdul-Sabaur, bazan boye maka ba, a gaskiya kana takurawa rayuwata da yawa. Ka sani na baro garinmu, kasarmu na zo kasar da ba a taba sanina ba, ni ma bansan kowa ba, saboda gudun takura. Me yasa zaka nemi saika sanni dole? Bana son damuwa, don Allah ka yi hakuri ka daina shigar min harka, na fi jin dadin rayuwata ni kadai. Murmushi ya yi mata, ya ce, ''Allah Sarki yarinta. Umaimah ki yi hakuri, ki kara hakuri, ko ba ki fada min da baki ba, na san kin takura a yanayinki da nake gani, na san na dame ki. Amma ita rayuwar duniya da kike gani kowa hakuri yake da ita, kuma kowa yana da matsala, wata matsalar ma har ta fi ta ki. A matsayinki na musulma ai ba wannan hukuncin za ki yanke ba na tahowa inda ba asanki ba, kuma ki ki yarda ki saba da kowa idan kika yi haka kamar kinyi fushi ne da kaddarar da Allah Ya dora miki. Musulmi na gari yana fara,a yana mai godiya ga Allah a lokacin da yake cikin tsanani. Ba ki taba jin kissar nan ta wani mutum ba? Wanda bakin cikin duniya ya dame shi, ya je Ka'aba yana dawafi, yana cikin damuwa, yana ta addu'a. Sai ya hadu da wata mata, wacce suke zagaye tare. Fara'a matar ta ke ti fuskarta cike da annuri, gata kyakyktawar gaske. Sai ta burge shi ta bashi sha'awa ya ji dama shine ya sami irin farin cikin da take ciki. Tun yana fada aransa, har ya fito ya tambayeta. Ya ce, 'Yah ke wannan mata, ke kuwa wanne irin farin ciki kike yi haka ne? Daga ganinki ba ki da matsala a duniya. Sai matar ta sake yin murmushi, ta ce, 'bawan Allah ni ce kuwa nake da damuwa, saboda mai gidana ne ya tafi kiwo tunda safe bai dawoba har dare ya yi, ashe mutuwa ya yi a can, sai na aika babban dana ya je ya nemo shi daya tafi shima maciji ya sare shi ya mutu, ma kaji shiru na fita neman su na bar karamin jariri kafin in dawo gida na zo na tarar kura ta cinye shi. Na dawo bani da kowa yanzu a duniya Allah Ya karbe abunSa. Godiyar Allah ce kawai da wadatar zuci yasa kaga ina dariya. Tun daga wannan lokaci mutumin ya daina damuwa da matsalarsa ya ji ashe shi tashi matsalar shafar mai ce. To haka akeso musulmi na gari ya kasance. Umaimah ta dubeshi yayin da jikinta ya yi sanyi, ba ta kara magana ba har suka shiga bakin get. Ta kama hanyar gidanta shima ya nufi bangarensa. Kalmar karshe da ya furta a gare ta, ita ce, ''Bissalam. Ta amsa da ''Ma'assalam. Ta wuce gida yana mai tsananin mamaki da irin kwakwalwa da dadadan kalamai masu tausasawa irin na Abdul-Sabur. Mutum ko shaidan ne sai jikinsa ya yi sanyi idan ya fara yi maka nasiha. Tabbas Abdul-Sabur mutum ne mai rikon addini da iya xama da jama. Amma ita duk da haka bata tunanin taci gaba da zama a gidan nan, don ta ga sannu a hankali AbdulSabur zai sa ta saba da MAKWABTA, ita kuwa ba ta son su saba sam. Sai yau Abdul-Sabur ya fara jin sanyi a ransa a game da Umaimah, yau ce rana ta farko da ta fara bude bakinta ta yi masa doguwar magana, har da ya yi tunanin ko batajin turanci ne sosai shi yasa ba ta son magana. Sai ya ji ta iya Turanci sosai, sai ka ce a kasar Turawa ta yi karatun tubalinta (Primary da secondary). Daga dukkan alamu zaici galaba a kanta, ya fara rusa mata bakar akidar nan da ta saka a ranta, ta kin gaisawa da makwabtanta. Asuba ta gari Abdumaimah !!! *************** *************** A lokacin da Dr. Faduwa ta ga Umaimah a tsaye a kofar falonta sai da ta razana, a lokacin data bude kofa tana shara da sanyin safiyar lahadi. Dr. Faduwa cike da mamaki ta tsurawa Umaimah ido tana kallo, don tana kokonton ko ba ita ba ce, ko kuma mafarki ta ke yi? Umaimah ta lura da hakan, don haka sai ta yi murmushi ta gaisheta. Dr. Faduwa ta tambaya, *Yan mata kuwa, daga ina? Umamimah ta yi mamaki da jin wannan tambayar, don haka sai ta kasa amsa mata. Ta ce, ''Tabbas za ki yi mamakin ganina a gidanki a yau, kuma a dai-dai wannan lokaci, amma kada ki yi mamaki alkhairi ne ya kawo ni. Ko ba ki san sunana ba na san kin san fuskata, ni makwabciyarki ce, sunana Umaimah Bello. Dr. Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Na gane ki Umaimah, zo ki zauna. Suka dungumaa suka isa cikin falo suka zauna. Yayin da Umaimah ta sunkuyar da kai kasa ba tare da ta san ta inda zata fara ba. ''Ina sauraronki *yan mata''. Inji Faduwa. Umaimah ta dago a hankali ta dube ta, ta yi murmushi. Ta ce, ''Na zo na gaishe da ke, kuma na ba ki hakuri, sannan na yi miki sallama zan tashi daga gidan nan yau, shi ne na ga ya dace na yi muku sallama. Don Allah ki taya ni fadawa abokinki Abdul-Sabur. Dr. Faduwa ta dade tana dubanta ba tare da ta san abin da zata fada mata ba, saboda mamaki da takaici. Can ta yi murmushin karfin hali, ta ce, ''Daman kin shekara ne a gidan ko ba kudin shekara kika biya ba? Umaimah ta sunkuyar da kai kasa ta yi dan murmushi. Ta ce, ''A,a kudin shekara na biya, yanzu watannina tara ina dai so na tashi ne kawai. ''Saboda kin tsani MAKWABTANki ko? Faduwa ta fada cikin gatsali. Sai tambayar ta yi wa kwakwalwar Umaimah nauyi, cike da mamaki ta dago da sauri ta dubi Faduwa tana tuhumarta da idanu. Dr. Faduwa ta sake zaro ido ta dubeta duba irin na ido cikin ido, ta ce, ''Kwarai kuwa zaki tashi saboda kin tsani makwabtanki, suna takura miki da gaisuwa. Sun ishe ki da yi miki sallama a duk sanda ku ka hadu a bakin get a matsayinku na musulmai ku dukka. Babu wannan kaunar ta musulmi da yake yi wa dan uwansa musulmi a zuciyarki. Sai hawaye ya cikawa Umaimah ido ta girgiza kai, ta ce, ''Ba haka ba ne, ina dai so na tashi ne kawai don ra'ayin kaina. Faduwa ta gyada kai, ta ce ''Bazan hana ki yim abin da kike so kiyi ba, haka ba zan sauya miki ra'ayinki ba, kuma ba zan daina yi miki addu'a ba, da fatan alkhairi a rayuwarki ko ba kya tare da mu. Sai dai ina so ki sani kuma ki saka a ranki, kin yi asarar makwabci na gari, mai mutunci da tausayi da sanin ya kamata, wato Abdul-Sabur. Kin tsane shi har tsanarsa ta shafe ni, to ki cire ni ma a ciki don ni tuni na cire shafinki a rayuwata, tunda ba kya so a bawa juna hakkin makwantaka na rabu da ke. Abdul-Sabur ne ba zai iya ba, du ba ki ga duk irin wulakancin da kike yi masa amma bai damu ba, kuma bai daina ba. Kar ki dauka don ke mace ce, kuma mai kyau, a,a ko maza ne haka yake kula da MAKWABTA, don shi cikakken musulmi ne, mai rikon addini duk wata sunnah Manzon Allah (S.A.W) yana rike da ita. Bari na baki wani labarin da ba ki sani ba, ba don Abdul-Sabur ba, da babu wanda zai san kina cikin gidanki kin kwana kina ciwo. Ke ko mutuwa kika yi babu wanda zai sani, don babu wanda ya damu da rayuwarki. Shi ne ya damu da ke, ya ke lura da shige da ficenki, ya ke lura da motsinki a lokacin da kike cikin gidanki. Har ya gano ba ki da lafiya, kamar wancan lokacin da ya sani na zo na duba ko lafiya ya yi sati baiji motsinki ba, kika tula masa kasa a ido, kika ce mu fita harkarki. Ni daman tun daga ranar nai alkawari na rabu da ke. Amma da ya zo min da maganar ciwo in daure in zo in taimake ki a matsayina na likita, dole na je na duba ki saboda zuciyar musulunci da tsabagen magiya da wa,azin da ya saka ni a gaba yana yi. Don haka ki kula da duniya, kuma kisan darajar mutum, ki tabbata za ki mutu halinki na gari shi zai bi ki, kuma shaidar mutane itace shaidar lahira. Umaima ta doka uban tagumi tana mai surnano da hawaye. Ta dade ba ta iya furta kalma daya ba, tana dubam Faduwa tana sauraron labarin da ta ke ba ta na Abdul-Sabur tun daga farko har karshe. Umaimah ta matse hawaye ta dubi Faduwa ta fara magana cikin sassanyar murya a sanadiyyar sanyin da jikinta ya yi. Ta ce, ''Duk abinda kika fada min gaskiya ne kuma nasan duk kuskuren da nake yi, in takaice miki ko a mafarkina Allah Ya nuna min gaskiya. Domin ina yawan mafarki akan makwabtana, sai na ga na shiga hali na tsoro ko na halaka, sai na ga Abdul-Sabur ya zo ya fitar da ni. Na san Ubangijina Yana nuna min darajar makwabtana. Ko a daren jiya na ga na fada rami AbdulSabur ya zo ya fito da ni, wasu lokutan shi kadai, wasu lokuta har da ke. To ashe ke nan Allah Ya na nuna min cewar, kuskure nake yi ke nan da bana kula ku? Nasan ina cikin halaka saboda rashin kyautatawa MAKWABTA, bana so wannan dalili ya sa na halaka shi ne na yanke hukuncin na tashi kawai. Dr. Faduwa ta tambaye ta cike da mamaki, ta ce, ''Kin gwammace gara ki tashi daga gidan ki sauya hakinki na zauna da makwabtanki lafiya? Umaimah ta sunkuyar da kanta kasa can ta dago ta dubi Faduwa ta gyada kai. Ta ce, ''Tabbas ina da dalilina da suka sa ba zan sauya ra'ayina ba akan MAKWABTA. Faduwa ta shiga jinjina kai ba tare da ta sake cewa komai ba. Tsabar mamaki Umaimah ta ke ba ta, ga ta *yar yarinya sai taurin zuciya. A hankali Faduwa ta mika hannu kan teburin da ke gabansu ta dauko wayarta ba ta yi wata-wata ba, ta danno lambar Abdul-Sabur. Ba jimawa ya amsa cikin harshen Turanci suke magana. Faduwa ta fada cike da zolaya, ''Kai da Allah tashi daga baccin nan mu mata ma mun tashi tun asuba balle kai namiji. Ya sake yin juyi ya yi mika, ya ce, ''Ki kyale ni, yau ba ni da wurin zuwa. Ta ce, ''Ko baka da wurin zuwa a da, yanzu ka sami wajen zuwa. Ka zo gidana za ku yi sallama da makwabciyarka, mai shirin tashi daga gidan nan da sanyin safiyar nan. Sai ya mutsike ido ya ce, ''Ban fahimce ki ba Faduwa, wa kenan? Ta yi dariya, ta ce makwabciyarka wacce gidanka ke kallon nata. Ya shiga jero mata yambayoyin da ba ta san amsarsu ba. ''Me yasa zata tashi? Me akayi mata? Kewa ya fada miki zata tashi? Inji Abdul-Sabur. ''Ni ma ban sani ba, ga ta a gidana ka zo kawai ku yi sallama. Tana gama fadar haka ta kashe wayar. Ya dade a zaune bai iya tashi tsaye ba, don yana tunanin mafarki yake yi. Can dai ya katse tunanin da yake yi, ya mike tsaye. Kai tsaye ban daki ya shiga ya yi wanka. Fiye da minti ashirin bai fito ba, Faduwa ta sake rangada masa waya, ya ce ga shi nan zuwa. Aka shafe mintuna biyar bai bayyana ba, har Umaimah ta fara kosawa zata tafi, Faduwa na lallashinta ta yi hakuri ya zo. A karo na uku Faduwa ta kira shi, sai ya tabbatar mata ba zai zo ba ya san karya ta ke yi shi har ya koma ya sake kwantawa. Sai da ya ji ta yi magana cikin fushi, sannan ya shiga bata hakuri gami da yi mata alkawari ga shi nan zuwa. Bai wuce mintuna biyar ba ya bayyana a falon Faduwa, sai da ya ga Umaimah ya gasgata maganar Faduwa, don har ya taho bai yarda ba. Mamaki mabaiyyani ya fito daga fuskarsa, ya dubi Umaimah ya dubi Faduwa, can dai ya zauna, sannan ya sake yi musu sallama suka amsa a lokaci guda. Har zuwa wasu *ya dakikai babu wanda ya yi magana a cikinsu, sannan Faduwa ta dubi Umaimah. Ta ce, ''Ga shi ya zo kuma kinyi shiru. Umaimah ta sake dukar da kai kasa ta ce, ''Ko bai zo ba na ce ki yi masa sallama zan tashi yau daga gidan nan. Ina muku godiya da fatan alkhairi. Abdul-Sabur ya gyara zama ya dubi Umaimah ya ce ''Yarinya, me ya sa za ki tashi ke da ko shekara ba ki yo ba a gidan nan? Sannan ga makarantarku a kusa da gidan ko mota ba kya hawa? Ina kike so ki koma? Umaimah ta dago a hankali ta dube shi, ta ce, ''Damansara zan koma. ''Damansara? Inji Abdul-Sabur da Faduwa suka tambaya a lokaci guda. Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Eh, Damansara. ''Damansara ta yi nisa da makarantarku, kin san da cewa sai kin shiga mota ko? Sabanin nan da kike zuwa makaranta da kafa. In ji Abdul-Sabur. Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Eh na sani. Abdul-Sabur ya cika da mamaki, ya ce, ''Me yasa kike so ki tashi? Anyi miki laifi ne na ga ko shekara ba ki yi ba? Ta gyada kai, ta ce, ''Eh Faduwa ta yi ajiyar zuciya, ta ce, ''Babu irin tambayoyin da ban yi mata ba da nasihohi amma ta ki ji don haka ka kyale ta ka yi mata fatan alheri, don idan ka takurata da tambaya ma kuka zata yi. Abdul-Sabur ya yi shiru yana tunani, can ya dubi Umaimah. Ya ce, ''Akwai wata matsala ne da ta sa dole za ki bar gidan nan? Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ba komai. Ya juya ya dubi Faduwa ya ce, ''Ke ma ba ta fada miki dalilanta ba? Faduwa ta tabe baki, ta ce, ''Ni a su wa da zata fadamin? Amsar da ta ke baka ita ta bani. Abdul-Sabur ya shafa dan siririn gemun da ya zagaye bakinsa, ya ce, ''Nasan dalilinki Umaimah, mu ne matsalarki, musamman ma ni da kike ganin ina takura miki. Ki yi min alfarma ki zauna har zuwa lokacin da za ki cika shekara, nan da watanni uku ni zan tashi na bar gidan. Ki ci gana da zama a nan saboda ya fi kusa da makarantarku, tunda makarantarmu tana Subang Jaya, ni zan koma can kusa da makarantarmu. Faduwa ba ta da matsala ita ba zata takura miki ba, daman ni nake takurawa ta je wajenki. Umaimah ta sake dunkufar da kai kasa saboda nauyin maganar da Abdul-Sabur yake yi. Can ta bude baki zata yi magana sai ya dakatar da ita. Ya ce, ''Kar ki damu, alfarma kawai na ce ki yi min, na san akwai takura, amma don Allah ki daure kar ki tashi, ki zauna. Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ina so na tashi ne kawai ba don ku ba, har ma na sami gida a can na biya na wata uku. Abdul-Sabur ya ce, ''Wannan ba matsala ba ce, kina iya cewa kin fasa tunda ba ki shiga ba, kuma ba ki bata musu lokaci ba, za su dawo miki da kudinki. Faduwa dai ta dade tana dubansu ta cika da al'ajabi. Can ta ce, ''Ai kin fada dazu kin ce saboda mu zaki tashi saboda kin san ba kya kyautatawa makwabtanki. Allah Ya ke nuna miki a mafarki shi yasa kike so ki tashi ba kya so ki halaka, don ba za ki iya sauyawa ba. Abdul-Sabur ya sake lankwashe kafa daya akan daya yana girgizawa, kallon Umaimah kawai yake yi yana so ya ji amsar da zata bayar, sai ta sunkuyar da kanta kasa don ba zata iya dubansa ba. Ya ambaci sunanta cikin wata sanyayyiyar murya, ya kara da cewa. Umaimah, me ye matsalarki ne a gaba daya rayuwarki? Ta dago a hankali ta dube shi da luhu-luhun idanuwanta da suka cika da hawaye. Sai ta girgiza kai alamar babu komai. Ya ce, ''Ko ba ki fada ba, duba daya za a yi miki a san kina da matsala. Kin baro kasarki Nigeria kin zo Malaysia da zummar yin karatu kamata ya yi ki kasance cikin walwala, ko ba a ganki da kowa ba, ya kamata a ganki da kawaye *yar kasarku, amma babu kowa ke kadai kike rayuwarki. Babu ko daya da na taba ganin ku tare. Babban abin da ya ba ni mamaki shi ne, na lura ko wayar hannu ba ki da shi, ba kya kiran *yan gida su ma ba sa kiranki. Ta yaya za,a yi ace iyayenki su turo ki wannan kasa mai nisa su manta da ke ko a waya ba satuntubarki. Umaimah ta fara kuka wiwi, kan ka ce kwabo hankalin Faduwa da Abdul-Sabur ya yi mummunan tashi. Faduwa ta zaro toilet paper ta mika mata don ta share hawayenta. Sai suka shiga lallashinta suna ba ta hakuri. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''yi hakuri ki daina kuka, ba ke kadai ba ce mai matsala, mu dukkanmu nan da kika gani muna da matsaloli manyamanya, wadanda da zamu bude miki mai yiyuwa ma ki ji taki shafar mai ce akan tamu. Amma kinga mun ci gaba da rayuwa, muna gaisawa da mutane, muna da kawaye, muna dariya ba ma jin haushin kowa saboda munyi tawakkali, mun dogara da Allah Shi Ya dora mana, Shi zai yaye mana. Haka ake so duk wani musulmi ya kasance, akwai irinmu da yawa a duniya masu matsaloli da suka linka naki sun yi hakuri suna ratuwarsu cikin walwala idan kin gansu ma ba za ki taba zaton sun taba yin kuka ba a duniya, amma suna bude baki suna fada miki matsalarsu sai kin yi musu hawaye. Umaimah ina mai baki shawara ki cire damuwa a ranki, a matsayinki na musulma duk abin da ta dame ki, ki roki Allah Ya yaye miki, idan wani abu kika rasa ki yi addu'a Allah Ya musnya miki da mafificin alkhairi. Kada kuma laifin wani ya shafi wani kamar yadda kika hada mu gaba dayan mu kika tsana, ba a yin haka, kin ji kanwata. Ina fatan zaki dauki shawarata ki fasa tashi, ki kawo mim rasitin na biyan kudin da kika yi na sabon gidan, zan je na yi musu magana za su dawo miki da kudinki In shaa Allah idan har ba kya son zaman a gidan ni zan tashi nan da watanni uku, sai ki ci gaba da zuwa makaranta hankalinki a kwance. Daga karshe ina yi miki addu,a Allah Ya yaye miki damuwar da ke damunki, Ya ba ki hakuri, Ya sauko miki da walwala a cikin zuciyarki. Ya kare ki daga sharrin masu sharri. Ya ba ki sa,ar jarabawa. Umaimai tana sharce hawaye tama amsa masa da ''Amin.'' ,,, ,,, ,,, ,,, sai an kara kaimi wajen commnt kafin mu kara yawan rubutu... MAKWABTAKA 11 Ta yunkura zata mike gami da yi musu godiya da sallama, sai Faduwa ta mike ta jawo hannunta ta zaunar. Ta ce, ''ba zaki tafi ba, sai mun ci abinci safe (break fast)'' Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''na koshi, na gode. Abdul-Sabur da Faduwa suka hada baki. ''A'a sai kin ci. Yaushe garin ya waye da har kika karya kumallo? Faduwa ta shiga kicin da sauri ta jona ruwan zafi a buta (kettle). Ta jona toaster a inda ta shiga gasa musu biredi da wainar kwai, wato (sandwich). Minti goma sha biyar ya yi yawa komai ya hadu akan dinning table. Ta umarce su da su karaso kan tebur su ci abinci. Umaimah da Aabdul-Sabur da suka dade a zaune suna kallom Talabijin ba tare da dayansu ya sake yin tari ba tun bayan shigan Faduwa kicin, sai yanzu suka motsa suka karaso kan dinning table suka zauna inda kowa ya shiga hada shayi a cikin kofin da yake gabansu. Faduwa sarkin surutu ta dubi Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Allah Sarki *yar yarinya mai kyau, kina da kyau ga ki fara kamar *yan kasarmu Misira kamar ba *yan Nigeria ba. Sai Umaimah da Abdul-Sabur suka kalli juna suka yi murmushi. Abdul-Sabur ya ce, ''An ce miki babu farare kyawawa a Nigeria? *Yan kasarku ne farare kawai? ''Ina ne garinku a Nigeria? Faduwa ta tambayi Umaimah. Yayin da Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Gombe''. Abdul-Sabur ya ce, ''Yauwa ma san ke bafillatana ce ina ganinki na gane haka. Mamaki marar misaltuwa ka ke gani a idon Umaimah, ta ke tambayar kanta da kanta a inda ya san Gombe har yasan Fulani ne a garin. Da ya lura da hakan sai ya dubeta ya yi murmushi, ya ce, ''Kina mamaki yanda na san YARENKI ko? To kibar mamaki, mu dukka nan da kika gani *yan asalin Nigeria ne, kuma Hausa/Fulani. Umaimah ta daina juya shayin ta zuba musu ido tana kallon fuskokin kowannensu. Babu alamar *yan Nigeria a tattare da su musamman ma Faduwa. Ta ina za,a hada Faduwa Balarabiya sak gashinta har tsantsarta mai laushi, farinta tas babu digon baki a jikinta, hanci har baka irin na Larabawan asali amma ace mata *yar Nigeria? Lallai wannan ma so yake ya raina mata hankali. Har ta ji ta tsane shi, tana tunanin rusa duk nasihohin da ya yi mata. Don a zatonta mai tsoron Allah ne a she makaryaci ne? Inji zuciyar Umaimah. Faduwa da Abdul-Sabur sai dariya suke ta yi, saboda kallon karyatawar da suka ga Umaimah na yo musu barobaro. Faduwa ta tambayi Umaimah, ''Kina mamaki ne? Ba ki yarda ba ko? Umaimah ta gyada kai, ta ce ''Eh, ban yarda ba gaskiya. Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''To Faduwa kiyi mata Hausa sai ta yarda. Nan ma dai Umaimah ta sake zaro ido da taji an ambaci yarenta na Hausa. Ta sake cika da mamakin yadda yasan Nigeria har ya san kabilun kasar. Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Umaimah ni da ke kasarmu daya, YARENMU daya Hausa/Fulani, ADDININMU daya musulunci. Da girmana na je Ghana amma ni dan asalin Nigeria ne. Faduwa ma *yar Nigeria ce saboda mahaifinta bakar fata ne, bahaushe dan asalin garin Sokoto, mahaifiyarta ce *yar Egypt, amma a wajen mahaifiyarta ta girma ita ta rike ta, duk da haka ta iya Hausa. Umaimah ta cika da mamaki, yayin da wasu gumaguman farin ciki suka dinga dirgowa a kahon zuciyarta saboda ta ba *yan gidata dafe haba da hannu tana jinjina kai, fadi ta ke, ''Ikon Allah, ashe ku duk *yan Nigeria ne? Abdul-Sabur ya ce, ''Kwarai kuwa, kuma muna yawan zuwa idan ta kama. Ta juya ya dubi Faduwa ya yi dariya, ya ce da ita, ''Bismillah, fara yara mata Hausa don ta yarda, na ga har yanzu tana kokonto. Faduwa ta yi dariya ta kurbi shayi, ta du bi Umaimah har yanzu dai cikin harshen Turanci suke magana. Ta ce, ''Kanwata wai da gaske har yanzu kina kokonto mu ba *yan kasarki ba ne? Umaimah ta yi murmushi ta gyada kai ta ce, ''gaskiya ina dan tantama. Abdul-Sabur ya furta kalmar Hausa, ya ce ''Da gaske muke yi, mu Hausawa ne, har wasu lokutan ni da Faduwa mu kanyi yaren Hausa, idan muna so mu yi maganar da ba ma so a ji a cikin mutane. Umaimah ta sankare a zaune, saboda ta san ashe ya gama jin duk zagin da ta ke yi masa a baya. Ashe yana sane yake kiranta da ''MAYE'' ramawa yake yi kenan? Faduwa ta kaikaice cikin harshen Hausa ta ke magana, duk da Hausar ba ta fita radau, amma ana ganewa tar! LABARIN FADUWA. Ta ce, ''Sunana Faduwa, sunan mahaifina Ahmad Sokoto. Mahaifina bakar fata ne bakikirin kuwa, dan asalin garin Sokoto ne gaba da baya. Mahaifiyata mai suna Zainab kuwa *ya asalin kasar Egypt ce, *yar cikin garin Cairo babban birnin. Ita dai ruwa biyu ce, mahaifinta ne dan Egypt, mahaifiyarta *yar kasar Saudia ce, don haka ina da *yan uwa a Saudia sosai. Karatu ya kai mahaifina Egypt, tun yana dan matashin saurayi shi da kannensa guda biyu Mansur da Adamu. Sun dade a Egypt har bayan sun kammala karatun ba su koma kasarsu ba, suna kasuwanci harma da aikin gwamnati, kasancewar mahaifinsu mai arziki ne, yana yawan zuwa Egypt shi ma ya zauna yana Hada-Hadar kasuwanci. Allah Ya hada soyayya tsakanin mahaifana, aure ya kankama a tsakanin fara da baki, duk da surutai da kyamar abin da dangin mahaifiyata ke nunawa a sanadiyyar auren nan Zainab kuwa idonta ya rufe, saboda soyayya ta ce ta ji ta gani zata aureshi haaka. Daman a lokacin marainiya ce, a hannun dangin mahaifinta ta ke, iyayenta duk sun rasu su duka biyun tun ma tana karamarta. Aure ya tabbata tsakanin Ahmad da Zainab da sharadin ba zai koma Nigeria ba, a Cairo zai bar ta. Zama na rufin asiri, saboda ya na da hali. Allah Ya albarkace su da samun haihuwa *ya*ya biyu, yayana Ibrahim da ni Faduwa. Ina da shekara uku yayana yana da shekaru biyar kakana ya rasu wanda ya haifi mahaifina, bayan rasuwarsa ne aka takurawa mahaifina da kannensa su dawo gida, tun da ba ran mahaifinsu don su ci gaba da kula da kasuwanci da iyayensu mata da kananan kannensu mata da maza. Nan fa rigima sabuwa ta fara don mahaifiyata ta ce ba zata biyo shi Nigeria ba, danginta kuma suka ce ba zai tafi ya bar ta da aurensa ba, sai dai idan ya sake ta. Yayi-yayi ta yi hakuri su koma Nigeria ko a ci gaba da auren yana zuwa yana dawowa, suka ce bazai yuwu ba, sai dai su rabu. Dole ya sake ta, sannan aka shiga rigimar daukar yara, ya ce sai ya tafi da mu, ita kuma ta ce ko da daya ba zata ba shi ba. Kamar daiza,a tafi kotu aka samu tsofaffi suka shiga aka yi sulhu, shi na mijin aka ba shi, macen aka barni a wajenta, da sharadin zai dinga kawo Ibrahim yana ganinta. Ta yi ta kukan rabuwa da danta tana ji tana gani aka tafi da danta, ni ma ina ji ina gani mahaifina mai sona, wanda muka shaku da shi ya tafi ya bar ni. Gidan da muke ciki kato ne sosai, ina yarinya sosai. A hankali har na soma mantawa da su, mahaifiyata da danginta kadai na sani, don su na budi ido na ga ina rayuwa da su. Aka saka ni a makaranta mai kyau, tun daga Nursiry har zuwa sakandire. Sai da na shiga aji uku na sakandire sannan Yayana Ibrahim ya zo Egypt, kanin babanmu uncle Mansur ne ya kawo shi, a lokacin ya gama sakandire. Kukan dadi Mamana ta yi data gan shi, don dama kullum addu,arta ke nan ta ga danta, sai ta shirya zata je Nigeria sai danginta su hana ta. Mahaifinmu tunda ya tapi gida ya manta da mu, ya auri mata biyu suna ta zazzago masa haihuwa, arziki ya kara bukasa. Sai a lokacin na san Yayana Ibrahim, ashe kamarmu daya da shi, dukka mahaifiyarmu muka biyo. Fari ne sol sak balarabe sai dai ki ji Hausa a bakinsa rangadadai irin ta Sakkotawa amma babu digo daya a jikinsa da ya yi kama bakar fata. Babu alamar wahala a jikinsa kasancewar a can a cikin daula suke, babu talauci har sun fimu jin dadi saboda Egypt ba kudi, ba albashin kirki a ma'aikata, babu kasuwanci da zai kawo kudi irin a Nigeria. Na zaci ma ya kauro kenan da na ga Baffanmu da ya kawo shi ya koma ya barshi. Da Ibrahim ya yi watanni hudu ya yi waya da *yan gida suka ce masa sakamakon jarabawarsa ya fito sai ya ce Nigeria zai koma ya yi jami,a. Babu yadda mamanmu ba ta yi ba kada ya tafi. Ya ce ya fi son ya tafi, saboda da can ya fi sabawa. Amma ya yi alkawarin duk shekara zai dinga zuwa hutu tunda ya ga hanya yanzu. Tabbas ya tausaya mana da ya ga muna ta kame- kame babu wadata shi ma ba kudin ne da shi ba, tikitin zuwa da komawa ya ba shi, sai *yan canji a aljihunsa. Mun shaku dashi sosai a wannan watannin hudu da ya yi damu. Munsha hira kala-kala, baya gajiya da jerin gwanon tambayoyin da na dinga jero masa game da mahaifinmu da kasarmu da kuma kannena na can. Allah Ya taimaka Mahaifina da kannensa sun koya larabci don haka da Larabci don haka da larabci muke magana, idan ta kakare ya juya Turanci. Ni kuma na fara koyon Hausa a wajensa kadan-kadan. Dalilina na yi masa tambayoyi akan kasata Nigeria shi ne, na karada cikin kawayena da cewa. Ni *yar Nigeria ce, amma ban san komai ba akan kasar, har suke karyata ni. Amma da Ibrahim ya yi min dalla-dalla na rubuta shikenan za su sha labari a makaranta. Bayan tafiyarsa ya sami damar shiga jami,ar Ahmadu Bello Zaria, yana karantar Engneering. A lokacin wayar land-line ta wadata babu wayar hannu, koda yaushe yana bugo mana waya mu yi ta hira, amma dai dai da rana daya Mahaifina bai taba cewa a ba shi ni ko Mamana mu gaisa ba. .. Muna farrin ciki da ganinsa har ma yana taho mana da tsaraba kamar su atamfofi, leshina dinkakku sai kukar kadi, garin masara, garin dawa, kubewa bushasshiya, harda daddawa. Da yake Mamana ta iya dafa abincin hausawa, zaman da ta yi da Babanmu ya koya mata, yana sawa ta dafa masa. Ni ma inajin dadin cin tuwo sosai, don haka na dage na koya. A lokacin da Ibrahim yake daf da gama jami,a ni kuma na gama sakandire da sakamako mai kyan gaske. Kai tsaye jami,a na wuce suka bani medicine. Kwakwalwa gareni, duk da ina da yawan surutu da son wasa, amma a aji idan aka sami na daya, to ni ce ta biyu. Ibrahim ya yi farin ciki da samun labarin ina karantar likita, ya kara min karfin gwiwa in dage in kammala. Sai a lokacin ne ma na taba jin muryar Mahaifina, Ibrahim ya bani shi a waya muka gaisa ya yi min addu'ar fatn alkhari. Sai na yi wa Mahaifina tambayar da ta girgiza shi jikinsa yayi sanyi. Na ce, 'Baba, au daman kasan kana da *ya ta cikinka a Egypt? Ka manta da ni dai-dai da rana daya baka taba zuwa ka ganni ba, ko ka neme ni a waya ko ka aiko da tikiti ka ce inzo in ganka, kuma inga sauran *yan uwana? Sai ya yi kasake ya kasa bani amsa, Mahaifiyata ta fusata ta kwace kan wayar ta ajiye ta hau ni da bambamin fada. Wai akan me zan ce ya aiko datikiti in je Nigeria? Sai dai in bayan ranta zan je Nigeria. Wai ina so in je nima su shanye ni kamar yadda suka shanye Ibrahim, ya kasa baro wajensu. Sai na yi ta kuka ina ta takaicin irin wannan kwamacalar aure da rabe-rabe tsakanin Mahaifana. Da Ibrahim ya kammala karatu ya yi bautar kasa, sai ya taho Cairo ya zauna tare da mu da takardunsa. Nan da nan kuwa ya sami aiki a wani kamfani Albashinsa mai kyau ne, idan aka hada da yadda ake biyan *yan kasa shi ya sami kari saboda suna daraja abin da ya karanta, kuma sun ga a Nigeria ya yi, Sai a lokacin na fara fuskantar matsaloli da goregore, saboda na isa aure ina da samari da yawa, idan maganar aure ta taso ranga-ranga sai iyayen mazan su bijire su ce ba a san ubana ba. Ko kuma idan suka bincika aka san ni ba shegiya ba ce, sai su ji cewa uban bakar fatane, ya gudu ya bar mu sai a ce ba za,ayi ba. Dan haka ni ba matar da zasu iya aura ba ce, dan zan iya sulalewa watarana na gudu kamar yadda Mahaifina ya yi. An yi haka ya fi sau uku, babu abin da nake yi sai kuka, Mamana da Ibrahim suna ta ba ni baki. Na shirya zan tafi Nigeria wajen Mahaifina ya fi a kirga, Mahaifiyata sai ta tubure ta ce bazan je ba. Shi ma kansa Ibrahim tunda ya zo ya fara aiki ta hanashi zuwa Sokoto shima kuma Mahaifinmu yana nuna halin ko'in-kula da mu, da zuwanmu da rashinsa duk daya ne a wajensa, saboda matansa na can sun dauke masa hankali akan mu, sun fi so su manta yana da *ya*ya a Cairo, *ya*yansu ne kadai *ya*yansa. To haka dai ake ta fama ni ina a asibiti ina samun kudi har na sayi mota, haka Ibrahim ma yana aikinsa da motarsa. Mahaifiyarmu ta fara jim dadin rayuwarta babu abin da ba ma ajiye mata. Mun tashi daga dan karamin gida mun sayi babba soasai da kayan alatu, matsalarmu daya ita ce a wajen maganar aure. Ibrahim ma ya sha neman aure ana hana shi saboda ba'asan Mahaifinsa ba, idan kuma an san akwai shi, to ana tsoron kada ya sulale watarana shima ya gudu kamar yadda ubansa ya yi. Babbar matsalata na fara girma, don na bawa shekaru talatin baya a lokacin, duk kawayena duk sunyi aure suna haihuwa, ni haryanzu abu ya ki yiwuwa. Idan na zauna ina kuka sai Mahaifiyata ta yi ta ba ni hakuri wai a hankali mijina zaizo wanda ba zai damu da bincike na ba. Ta ce in ma cire raina da cewar zanje Nigeria, saboda tana tsoron wadannen mutane ba su da kirki, za su iya salwantar min da rayuwata. Sai na tambayeta ''ta ya ya za su cuce ni bayan ni jininsu ce, me yasa ta aure shi tunda ta san ba su da kirki? Ya akayi ita ba,a cutar da ita ba har ta zauna da shi suka haife mu? Da yake tana da fada sai ta rufe ni da masifa ina ji ina gani laifi ya dawo kaina na koma ina ta ba ta hakuri. Da naga kabilancin *yan Cairo ya yi yawa a kaina wajen aure sai na yanke hukuncin na auri baki muzauna Egypt *yan Nigeria da yake akwai su da yawa, ko kuma a cikin bakaken da suke zuwa Nigeria ganin likita a asibitinmu. Duk inda na ga dan Nigeria sai na ji ina sonsa, musamman Bahaushe, ko ba ya so sai na tsokano shi da hira dan na sanar masa nima *yar uwarsa ce har ma in yara masa YARENA na Hausa, tunda na koya wajen Ibrahim, Mamana ma tana ji kadan-kadan. Ta haka sai na yi abokai da kawaye masu dumbin yawa, ko sun koma Nigeria suna da lambata sai mu yi ta waya da su ina cika bakin watarana za su ganni a Nigeria.Duk wani dan Nigeria da ya ke zuwa Cairo, musamman asibiti idan ku ka tambaye su Dr. Faduwa Ahmad sun sanni. Ina son mutane saboda ina da yawan hira a sanadiyyar hakan sai na hadu da manyan *yan Nigeria ma su kudi da mulki, kamar ambassadors, ministoci, kwamishinoni, *yan kasuwa manya-manyan masu kudi. Wasu suna sona da son fasikanci, wasu kuwa da aure suke sona. Bana boye-boye, baro-baro nake fadawa fasikan nan ni ba *yar iska ba ce, kada su sake shiga harkata. Masu sona da aure kuwa suna cewa idan sun aureni zasu tafi da ni Nigeria ba za su barni a Cairo ba, sai na rusa maganar dan na san ma bazai yiwu ba don mahaifiyarta ba zata yarda ba. Ni ma kuma bana son abin da zan jawowa *ya*yana raberabe kamar yadda na tsinci kaina. Da na ga abin ba kararre ba ne, aure ya ki yiwuwa saina yankewa kaina shawarar ko aikin nawa ne sai na bari na auri dan Nigeria na bi shi can mu zauna. Har na taba tunkarar mahaifiyata da maganar aurena da Alh. Murtala wani Bakano ne, dan kasuwa, yana da mata uku ni ce ta hudu, amma duk ban damu ba. Yana matukar so na, yana da kirki ga dukiya mai yawa, saboda son da yake min bai ki ya raba dukiyarsa gida biyu ya bani rabi ba. Kuka yake yi da idanunsa akan na daure na aure shi, gidana daban ba zai hada ni da iyalansa ba. Kuma zai dinga kawo ni akai-akai ina ganin iyayena. Koda na fadawa mahaifiyata wannan labari, sai ya dora hannu aka ta yi min kukan mutuwa. Ta yi ta kiran lambar *yan uwanta wai su yi maza su zo ga Faduwa zata kashe ta. Nan da nan kowa ya zargayo a gigice suka tarar ba kisan hannu zan yi mata ba, kisan zuciya zan yi mata. Nan da nan suka taru suka hada baki babu wanda ya amince min. Ibrahim ne kadai ya ke bani goyon baya, shi ma ba a tashi daga taron ba sai da aka tsige shi tas. Aka ce ba shi da hankali, ya za a yi ya bawa kanwarsa wannan muguwar shawara na auren namiji mai mata uku, kuma dan Nigeria narasa rike aure, wadan da ba su san muhimmancin haihuwa ba. Dole na yiwa Alh. Murtala sallama muka rabu, ba shi kadai ba ma akwai wani babba mai mulki shi ma daga Abuja yake, ya kawo Mahaifinsa asibitin da nake ciki muka saba, har soayyaya ta shiga. Matarsa daya da *ya*ya biyar shi ma da na fada a gida aka hana ni. Sai na hakura da maganar aure gaba daya, tunda na rasa miji a Egypt, an hana ni auren *yan Nigeria. Sagir dan asalin Cairo ne, sannan dan sanda ne. Shine tsohon saurayina da muka hadu da shi tun bayan da na kammala sakandire, tashin farko daman mahaifiyarsa ta ce ba ta yarda ba, ba zai aure ni ba. Dan bani da sali, *yar uwarsa zai aura mai cikakken asali ba ruwa biyu ba. Yana sona sosai ya kasa rabuwa da ni, duk da yasan aurenmu ba zai yiwu ba, yana ganin kamar wata rana zata iya yarje masa ya aure ni. Ashe ita ba ta san ma muna tare ba har tsawon shekaru da yawa, sannan ya sake gabatar mata da ni a matsayin wacce zai aura. A take ta nuna mishi sai dai idan bata raye, ba zai aureni ba. Ina kuka, yana kuka ya ce shi bazai rabu da ni ba, kullum yana gidanmu, idan ina gida idan kuwa bana gida ina asibitin da nake aiki, to zaka anshi a kusa da ni, sai dai idan nasa aikin ne ya hanashi zuwa. Mahaifiyarsa tana kiransa sama da sau goma kafin yabar wajena, kai ka ce duba ta ke yi. Muddin ya zo sai ta gane sai ta yi ta kiransa. Ka ji tana magana cikin fushi, kasaita da daga murya. ''Sagir, kana ina? Cikin fushi da takaici yake amsa mata. ''Mama ya kike tambayata kamar karamin yaro da zai bata a Cairo? Sai ta ce, ''Kana tare da wannan tsinanniyar Faduwar ko? To ka dawo gida yanzun nan, nan da awa guda mazamaza ka karaso. Sai ta kashe waya a fusace bayan kamar mintuna biyar sai ta kirashi kuma. Ta ce, ''Ka taho ne? Sai ya ce, ''Zan dai taho yanzu. Idan ta ji shuru bai iso ba, sai ta sake kira. Ta ce ''Ya banji karar motoci ba, bayan ka ce min kuma kana hanya? Aikin kenan sai raina ya baci na ce ya tashi ya tafi. Ana nan-ana nan ni da shi kullum muna ta shawarwari yadda zanu bullowa wannan matsalolin. Mun shirya duk yadda zamu yi rayuwar aurenmu cikin farin ciki. Tsalelen gida ya gina ya zuba kayan alatu. Ya nuna min bangarena da bangarensa da kuma bangaren *y *yanmu idan mun haifa, tunda ko yaushe muna hasashen zamuyi aure har ma mu hayayyafa.. A gidan muka yi liyafar cikarmu shekara goma sha biyu da haduwarmu (12 anniversary). Muka gayyaci kawaye da abokai, muka yanka kek, aka yi mana hotuna. Kowa ya tausaya mana ya yi mana addu,ar Allah Ya sa wannan aure ya tabbata, saboda yadda aka lura muna kaunar junanmu matuka. .. .. .. ..MAKWABTAKA 12 Tunda mahaifiyarsa taji labarin wannan liyafar da muka yi, ta ga hotuna sai hankalinta ya sake tashi, ta kirani ta zazzage ni, wai nabar mata danta kada na cinye shi. Na ga santalelen saurayi, kyakkyawa na makale masa, to bari ta fada min, ban isa na aure shi ba duk nacina kuwa. Wai tasan duk hanyoyin da na bi na mallake mata da, sihiri ne ita ma zata bi ta karbo danta daga mugun hannu. Na kame a zaune ina ta sauraronta, na ji tashin hankalin da ban taba ji ba a duniya. Na tsani wannan kalmar, 'SIHIRI'. Dana fadawa Mamana abun da matar nan ta yi min sai ta girgiza kai ta ce, ''Ki yi hakuri Faduwa, sannan ki yi addu'a sosai. Ban fadawa Sagir cewa mahaifiyarsa ta zazzageni ba, a can ya jiyo da hawayensa ya yi ta bani hakuri, ya ce, yafi kaunar mutuwarsa da irin wannan kuncin da mahaifiyarsa ta ke so ta cusa shi a ciki. Na ba shi hakuri na fada masa nasihar da mahaiyata ta fada min cewar, na yi hakuri, sannan na yi addu,a sosai, babu abin da ya gagari addu,a. Tsafi ya kan ci mai shi, sihiri gaskiya ne, ana yinsa idan Allah Ya nufa sai ya kama wanda aka yiwa. Ta fada da bakinta kuma ta aikata, saboda yadda naga Sagir ya sauya nan da nan. Idan ya zo wajena muna hirarmu ta masoya cikin farin ciki da annashuwa da zarar ta kirashi, sai ka ga jikinsa ya dau karkarwa, muryarsa na rawa. Idan ta ce masa. ''Kana ina? To duk inda kake ka taho gida yanzun nan, na baka minitina goma idan ba hakaba ranka zai baci. Tana kashe waya zai mike tsaye ya ce ''Mamana tana kira, na tafi, sai wani lokacin. Ina masa magana baya saurarona a guje zai je ya shige mota ya tafi ko waiwayena baya yi. Sabanin da sai ya gama hirarsa zai tafi ko zata yi waya sau dari. Ashe duk wannan somin tabi ne, abin takaici na gaba. Sai ma ta hanashi zuwa gidanmu, ga shi kirikiri munyi waya da shi ya ce min ya kamo hanyar gidanmu. In caba ado in zauna ina jiransa, sai ya yi min waya ya ce, ya koma gida mahaifiyarsa ta ce ya dawo. Hakafa ya ke sanar min ba tare da sakayawa ba, i dan ba dan furucinta da tayi min ba da sai na ce yanason kyauyaya mu'amalarsa da mahaifansa sosai, to amma furucin da tayi ya kauda komai. Tun ana haka har ya daina tarkar tahowa wajena, wayar ma jifa-jifa. Idan son sa ya yi min yawa sai na dauki motata na je na ganshi a gidansa ko a wajen aikinsa. Sai ta ji labari ina zuwa, sai ta sa shi ya fara kora ta. Wai ni Faduwa ni na zama abin kora a wajen Sagir, bayan a da babu wadda yake son kasancewa tare da ita kama ta. Sagir ba ya son ganina, har ta kai ta kawo ya fada min baro-baro da bakinsa. ''Faduwa ki rabu da ni, mu hakura da juna, saboda kina jawomin sabani tsakani na da mahaifiyata. Ni kuwa ba na son duk wani abu da ba ta so, koda kuwa shine zabin raina. Sai na ji jiri ya kwashe ni ina zaune na ji na kwanta can na dago na dube shi, sai na ga bana ganinsa sai duhu. Daga dukkan alamu suma ce na yi a ofis dinsa ne, sai ganinsa na yi da abokansa sun zagaye ni suna shafamin ruwan sanyi a fuskata. Da na warware sai na ga idanunsa sharkaf da hawaye, wanda har yau ba ya kafewa muddin na tuna Sagir ko na ji mai sunan sa, kuma ina tuna korar karen da ya yi min daga rayuwarsa. Da kyar na dauko jakata da makullin motata na fito daga ofishin na bar shi da abokansa suna tambayarsa me yake faruwa, don shima kukan yake yi. Tun daga ranar har rana irin ta yau ban sake ganin Sagir ba ko na jiyo muryarsa a dodon kunnena. Na hakura da shi koda kuwa sonsa shine ajalina. Faduwa ta rushe da kuka mai tsanani yayin da tausayinta ya cika zuciyoyin Umaimah da Abdul-Sabur, suma kwalla ta cika musu ido. Lokaci mai tsawo babu wanda ya yi magana a cikinsu, sai shasshekar kukan Faduwa ne ka tashi. Umaimah ta dinga shafa kafadarta tana jijjiga ta tamkar tana lallashin dan jariri, kalmar ''Sorry..... Sorry. Suke ta ambatowa Faduwa. Abdul-Sabur ya ce , ''Yaya rayuwarki ta kasance ke da mahaifanki? Faduwa ta sharce hawaye ta ce. ''Wannan shi ne mataki na farko da na fara takawa na tashin hankali a rayuwata. Daga nan abubuwa marasa dadi suka yi ta biyo ni daya bayan daya. Kusan kowanne dan Adam bisa kan mizanin kaddararsa ya ke, to haka nima na yi ta hawa kaddarorin rayuwata. Yayana Ibrahin ya kamu da ciwo, wanda aka rasa kansa. Abu kamar wasa tun yana iya fita ya je aiki har ya kasa fita. Tun yana kwance a bangarensa har Mamana ta dauke shi ta dawo da shi dakinta tana kula da shi, dom komai sai an yi masa. Gwaje-gwaje kala-kala an kasa gano kan ciwon sa. Kuma a cikinsa ya ke, ya shekara uku a kwance babu abin da ake sai kashe kudi, sai da komai namu ya kare, daman shi sun sallame shi a wajen aiki, sun ba shi kudin sallamarsa ya kare a magani (Wannan banzar dabi,ace da ke faruwa a kowacce kasa, wai adan ma,aika ci ba shi da lafiya, maimakon a taimake shi a dauki nauyin maganin ciwonsa, wata kilama a sanadin kulawar wajen aiki ya samu sauki, amma sai a yi biris da shi karshe ma a yi masa tagonashi da takardar sallama da dan kudin da ba zasu kashe masa kwarnafi ba). Duk albashina a magani yake tafiya, ta kai ta kawo sai da na siyar da motata na biya masa wani kudin gwaji (test) mai tsada. Daman shi tasa motar tuni an siyar, haka mahaifiyata ta sayar da komai nata abin da ya rage mana kwangwarmin gidan da muke ciki kadai. Faduwa ta sake fasa kuka mai cike da ban tausayi. Umaimah ta girgiza kai don tausayawa, ta ce, ''Allahu Akbar! Ba ku yi waya Nigeria kun sanarwa da mahaifinku ba? Faduwa ta matse hawayen da ke gurbin idonta, cike da takaici ta ce. ''Waya sau nawa kuwa, na yi waya har na gaji. Duk lambobin da Ibrahim ya ba ni na kira daya bayan daya. Daga ta gidanmu, danginmu da abokansa. Na sanar musu halin da Ibrahim ya ke ciki, kuma tunda sauran lafiyarsa ya buga waya ya fadawa Babanmu. Ashe boye mana ake yi shima a kwance yake irin ciwonsu iri daya (cancer) ce a hunhunsu, shi ma can duk kudinsa ya kare a neman magani. Sai su yi ta min hanya-hanya wai za,a turo daya daga Baffannina ya zo ya duba shi. Na gaji dai na fito barobaro na shaida musu kudi ne babu, ko ba zasu zo ba suturo mana da kudin asibiti. Sai alkawuran karya, ko sisinsu ban gani ba. Allah Ya karbi ran abinsa, yayana Ibrahim ya rasu ranar wata litinin a asibiti. Kuka mai tsanani Faduwa ta ke, yayin da Umaimah ta dafe kirji, ta ce. ''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Abdul-Sabur ya dafe kai, ya girgiza don tausayawa, amma bai iya cewa komai ba, sai girgiza kan da yake cikin tsananin jimantawa. Cikin kuka Faduwa ta ci gaba da magana. ''Allah Ya sa mutuwa hutu ce, din da wata cutar gara mutuwa, tsananin wahala babu irin wacce bai sha ba, ko ruwa ba ya tsayawa a cikinsa, sai ya amayo da shi, ya rame ya yi baki, gashin kansa ya kade. Ba magana sai kaga hawaye na zuba daga idanunsa idan masifar tayi masifa. Sai ni sai Mahifiyata muka rage ga talauci saboda albashin ma ba ya isa ta, dumbin bashin da yake kanmu nake biya duk wata, wanda muka ranta aka biya kudin asibiti. Duk da kokarin da nakeyi ina ta biya ban daina fuskantar cin mutunci daga wadanda suke bina bashi ba, suna ganin cinye musu zan yi. Hakika ni da ita ba ma jin dadin rayuwarmu. Saboda rashin Ibrahim ga babban tabon da ya tafi ya barmu da shi, mun kasa mance tsananin wahalar da ya sha a sanadiyyar ciwon. Mun yi waya Nigeria mun shaida musu mutuwar Ibrahim, wasu da yawa sun kira suna yi mana gaisuwa. A lokacin ne ma aka ba wa mahaifina kan waya ya yi min magana, muryarsa na rawa yake bani hakuri akan abin da ya yi mana, ya shaida min shima a kwance yake bashi da lafiya sai an kwantar an tayar. Tsananin tsanar da na yi masa sai ta ragu son da na kullace shi sosai, na yi da-na-sanin da ya zama mahaifina tunda ba ya kaunarmu, ba ya kula da mu. Amma a lokacin da yayimin wannan bayanin sai na janye tsanar. Na yi masa fatan Allah Ya ba shi lafiya, daga yadda na suffanta ciwon na gane irin ciwon Ibrahim ne, don haka na cire rai da shi a rayuwa. Tun daga wannan lokaci hankalina ya yi Nigeria, na ji ina so na zo na gana da mahaifina tunda ransa. Saboda ban san shi ba sai a hoto, ga babu dan uwana Ibrahim shi ne daman ya san su, wanda ko ba ran mahaifinmu zai iya kawo ni na ga dangin ubana ko da kuwa aurena ne ya zo. Mahaifiyata ta dage ta ce ba zan je ba, don ba son mu suke yi ba. Tana tsoro kada ma na zo su cuceni, ko su hada baki su hallakar da ni, tunda ta ji labari su *yan Nigeria suna da hadamar gado, kuma za su iya yin komai a kan gado . Kuma ta fuskanci matansa ba sa son mu, da akwai yadda za su yi da sun soke sunanmu daga cikin *ya*yansa, *ya*yansu ne *ya*ya. Na ji ba dadi don na sawa raina ina son zuwan, to amma babban dalilin da yasa na hakura ba ni da kudin jirgi. Muna nan haka rayuwa ba dadi, rana daya ba zato ba tsammani zuciyar mahaifiyata ta buga, sai dai kawai ta fadi aka dauki gawarta. Tsakaninta da yayana shekara guda dai-dai. Nima mutuwa ce kawai ban yi ba, saboda na girgiza, na dimauce zan iya cewa dai na zautu tamkar kwakwalwata ta tabu. Ta fashe da kuka mai tsanani. Ya yin da Umaima da Abdul-sabur suka razana har suna hada baki ''Mama ce ta mutu? Faduwa ta gyada kai ta ce, ''Mamana ta rasu, ta tafi ta bar ni, ni kadai a duniya. Tun daga wannan Lokaci na daina zuwa aiki kwata-kwata. Faduwa ta gyada kai ta ce, ''Mamana ta rasu, ta tafi ta bar ni, ni kadai a duniya. Tun daga lokacin nan na daina zuwa aiki kwata-kwata don ko naje shirme zan yi, yanayin aiki na kuwa sai da nutsuwa. Babu yadda dangin mahaifiyata ba su yi ba na je aikina nayi hakuri na maida komai ba komai ba. Na fada musu baro-baro, ba zan je ba, tun *yan ofishinmu na ba ni dama suna daga min kafa har suka fara turomin da doguwar wasikar gargadi (warning letter) cewar, ko na dawo aiki, ko a kore ni. Daga karshe dai naga wasikar kora daga aiki, ban damu ba daman haka nake so. Na hada *yan abubuwan da aka ba ni na daga cikin dan abin da Mahaifiyata ta bar min na gado, na sayi tikiti na kaura Saudiya wajen danginta na can na zauna da su a 'Tayif. Bayan mutuwar Mahaifiyata na kira lambar gidanmu ta Nigeria ina so na shaidawa Mahaifina rasuwarta, sai matarsa ta dauka, na ce ta bashi muyi magana, ta ce min ba ya kusa. Na shaida mata sakon da zata fada masa, a shelake ta amsa min gami da ajiye waya tun ban gama magana ba. Sai na kira Baffana daya daga cikin su wanda yake zaune a Kano Baffa Mansur na shaida masa abubuwan da yake wakana, ya yi min alkawarin zai sanar da shi idan ya je duba shi, don shi ma jikin ya tsananta. Na yi kuka, kullum cikinsa nake yi har yau saboda bani da kowa, ba ni da komai, daman dai na san Allah (S.W.T) ne kadai gatana. Rayuwata ta tsananta a 'Tayif' ba na ganin dai-dai duk inda na je sai naga kaman ana min kora da hali, sun kosa da ni. Duk da masu arziki ne abinci da sutura ba sa wuya sai na ga suna yi min habaici game da mijinsu suna gudun kada mazansu su ce suna sona saboda Allah Ya yi min fara'a, hira da saurin sabo da mutane. Duk na tsargu na fara zama mujiya a cikin jama,a. Dole na tarkato na dawo Cairo don na tantance cewar na wuce zama a gaban wasu. Na zo na bude gidana na zauna, ina cin dan abin da na samo, daya kare sai na fara shiga garari. Egypt ba kudi ba kamar Saudiya ba komai a wadace, a Egypt ma'aikaci mai daukar albashi kukan babu yake yi, albashin bashi da yawa balle ni da bana aiki. Bayan shekara ne na ga ya dace na kira na ji jikin mahaifina tunda kozai mutu babu mai kirana ya ji hakin da nake ciki, ina kira gidanmu, wani kanina mai suna Salahuddin ne ya dauk wayar, sai yake shaidamin ai mahaifinmu ya shekara da mutuwa... Faduwa ta girgiza kai ta yi murmushin takaici, yayin da Abdul-Sabur da Umaimah suka zazzare ido don tashin hankali. ''Ya rasu amma ba su fada miki ba? Im ji Abdul-Sabur. Faduwa ta fashe da kuka, ta ce, ''Ba su fada min ba, saboda bana cikin lissafin *ya *yansa. Raina ya yi matukar baci, na yi ta fada, a lokacin na kira Baffanaina daya bayan daya na wanke su tas da bakaken maganganu, na ce yanzu har Mahaifina ya shekara ya shekara da rasuwa a kasa fada min. Sai suka hau kame-kame wai saboda suna gudun kada zuciyata ta buga abubuwan su yi min yawa, ga mutuwar dan uwana da mahaifiyata, ya za a yi a fada min mutuwar mahaifina, daman so suke a kwana biyu tukunna. Babu abin da na ce musu, sai na kashe waya, na fi sati ina kuka a daki ni kadai, sai da kanwar mahaifiyata ta zo ta tambaye ni ko lafiya? Na shaida mata duk abin da ya faru. Nan da nan ta hado taron gaggawa, kowa sai da ransa ya baci da ya ji abin da aka yi min, suka ce ai ba za a zura musu ido aci gaba da cutata ba, dole a kwatarmin hakkina tunda sun nuna ba su san mutunci ba, sai an raba abin da ya bari da ni. Suka ba ni waya na kira gidan a gabansu na bude magana(speaker). Cikin harshen Hausa na yi magana dasu a waya dangina basu ji abin da muka ce ba, amma na fassara musu daga baya abin da aka ce. Matan Babana na tambaya me da me Mahaifina ya bari? Suka hau kame-kame wai bai bar komai ba, duk sun kare a asibiti. Ko gidan ma da suke ciki na aro ne. Sai na katse waya na bugawa Baffa Adamu waya, shi yana jin larabci na tambaye shi gadon Mahaifina, sai ya ce fili ya bari guda daya. Da na kira Baffa Mansur kuwa shi ma a cikin harshen Larabci mukayi magana, kowa yana ji. Sai ya ce baibar komai ba sai shaguna guda uku a kasuwa da mota biyu tirela. Daga jin haka mun san ba su da gaskiya, don haka aka ce na shirya kawai na tafi Nigeria, na je na shigar da kara na karbi hakkina. Suka hadamin kudin jirgi, amma sai da na sami wanda ya ke da tabbas ya san gidanmu na sokoto amma a Abuja yake a zaune. Don haka Abuja na nufa gidan da matarsa su ma sakkwatawa ne, unguwarsu daya da mahaifina ni kuma a asibitinmu na sansu sun kawo dansu wata shekarar muke waya da su har bayan sun tafi. Hira ta kawo hira suka gane mahaifina... Umaimah ta gyara zama ta ce,''Ya aka yi kika je?'' Abdul-Sabur ya ja doguawar ajiyar zuciya, ya gyada kai. Ya ce, ''Ikon Allah, rayuwa kenan. Yaya ta kasance tsakaninki da su?'' Faduwa ta tabe baki ta ce, ''Inda ranka a duniya za ka sha kallo. Wasu mutane gani suke kamar ba zasu mutu ba, sun kauro duniya ke nan, ba sa tsoron Allah. Sun manta inda wancan ya je su ma za su je ne ko ba jima ko ba dade. Da na isa Nigeria garin Abuja aka kai ni garinmu Sokoto cikin gidan Babana. Sai ga ni a zaune a falonsa, ga ni ga hotunansa a kusa da ni, amma baya nan. Allah Ya yanke haduwarmu har abada. Na ga kannene rututu, dangi kamar tururuwa kowa ya taho ya ga Faduwa, suna murna ina murna, yayin da aka dinga jeremin kwanukan abinci da kyaututtuka iri-iri kamar Muhutai, atamfofi, leshina, kwarya da dai sauransu. Kowa so yake ya yi hira da ni, kai ka ce suna sona. Wasu daga cikinsu kauyawa ne futik babu boko, wasu kuwa *yan gayu ne masu kudi. Su ka ce ma idan na huta zasu kai ni Kano, Kaduna da Abuja wajen *yan uwa (cousins) da suke auren manyan masu kudi a can. An ba ni su a waya mun gaggaisa na ce musu idanna na gama da sokoto za,a kawo ni sun yi murna da jin haka. Wasu turanci muke yi da su, wasu Larabci, wasu kuwa hausa kawai suka iya sai mu yara. Sai da na shafe kwanaki goma cur babu wanda ya yi min maganar gadona, sai dai a gaisa, a yi hira wasa da dariyaa, a tulo min abinci da kayan marmari a gyaramin gado na kwanta in yi bacci washe gari in tashi a ci gaba da haka. Sai na nemi a taro min kannen Mahaifina da manyan kannena da iyayensu mata, duk muka hadu a babban falon gidan. Na bude baki na yi magana cikin harshen Hausa yadda kowannensu zai gane. Na ce, na zo ne na karbi gadon mahaifina don na kasa ganewa duk wanda na tambaya me ya bari, abin da zai fadamin daban ne. Me ya bari, kuma ina nawa kason? Sai aka hau kallon-kallo, wata matarsa wacce ita tafi tsana ta ta dinga bayani irin na rashin gaskiya, wai gidan nan kawai ya bari duk asibiti ya cinye kudin, an siyar da kadarorinsa gaba daya. Gidan ma ba dukka ba dole sai an siyar da rabi an biya masa bashin da ake binsa. Ni kuma abin da na gida dai an gama raba shi, don naga kowa ya kama nasa bangaren an yi toshe-toshe da likelike. Baffa Adamu ya ce na yi hakuri na koma kasarmu idan komai ya daidaita za a turomin da kashina. Na fusata na ce da shi, ina fili da ka fada min yana da shi? Na juya na dubi Baffa Mansur, da ya ce min yana da shaguna a kasuwa, na tambayeshi. Na ce, ''Ina shagunan da ka fada min ya bari a kasuwa da motoci? Duk ba ni da kaso a ciki ke nan? Na yi kuka sosai don takaici na dube su dukkansu na ce, ''To na gane abin da dukka kuke nufi, kun cire ni daga cikin *ya*yan gidan nan, kun rabe gadon ku banda ni. A wajen Allah ina da hakki ku ka danne, to duk wanda ya ci kashina ko da kwayar zarra ce ban yafe ba, zai biya ni a ranar da bashi da abin da zai ba ni sai ladansa. In da Mutumin daya tara dukiyar da ku ka cinye ya je dukkanmu nan zamu je, kuma ba kowa ya jawo min wannan wulakancin ba sai shi da kansa Mahaifina da ya nuna muku ni ba komai ba ce, kuma bai damu da ni ba. Sai suka hau timin tsawa da fada, wai kada na yi musu rashin kunya. Kannena har da masu cewa, za su dake ni idan na sake yiwa iyayensu rashin kunya. Da yake zuciyata ta kekashe ban yi shiru ba ni ma fadan na ke na ce su zo su dake ni idan sun so ma su kashe ni. Aka shiga tsakani aka kai ni bangaren masaukina. Cikin dare Baffa Adamu ya aiko na zo gidansa yana nemana. Da farko na ki zuwa sai da ya aiko matarsa ta zo, ta tafi da ni ya dauke ni a mota ya kai ni gidan wani dattijo, a she shine alakalin daya raba gadon. Aka daukomin takardun da aka yi rabon gadon. Ga sunayen magada nan, amma babu sunana, sannan ga dumbin dukiyar da ya bari, shagunan kasuwa, filaye da tireloli, amma babu nawa duk an rabe musu. Wanda da ace an raba da ni da na yi sallama da talauci. Baffa Adamu ya dube ni fuskarsa cike da nadama. Ya ce da ni, ''Faduwa ina tsoron ranar da zan mutu Allah Ya tuhume ni da laifin ban fada miki gaskiya ba. Saboda ni dai banci gadon ki ba ko sisi. Allah ba zai tuhume ni da wannan ba, amma zai tuhume ni da nasan komai na boye miki. Na yi ta kuka na ci gaba da yi musu bayanin halin da nake ciki a can Egypt ba ni da komai, ba ni da kowa. Alkali ya ce, ''Shawara biyu zan ba ki, ki zabi wacce ta fi miki sauki. Ta farko ko kiyi hakuri ki bar wa Allah cutar da akayi miki, ko kuma ki nemo kudi ki dauki lauyoyi su tsaya miki ki karbi hakkinki. Amma ki sani za a iya shekara goma ana ta shari'ar nan ba tare da ta kare ba. Allah ya raba mu da son zucia. MAKWABTAKA 13 Na tashi na fice don takaici, Baffa l Adamu ya dawo dani gida babu abin da yake sai ba ni hakuri yana neman gafarata. Yana sake ba ne labarin mugun hali irin na matan babana cewar, karfi da yaji suka hana mahaifina maganarmu, don da koda yaushe yana maganar zaije ya dauko Faduwa ta dawo wajensa ko ya je ya ganki, ya ba ki wani abu daga cikin dukiyoyinsa, wanda zan ci gaba da karatu. Sai su ce bazai je ba ni me yasa ban taba zuwa ba? Kuma duk *ya*yan da yake da su sama da ashirin ba su ishe shi ba sai ya je neman wata. Dole ya hakura ya janye wannan zance na zuwa Egypt don ba yadda zai yi. Na ce da shi, ''Don kansu, kowa ya yi na gari zai gani. Nawa rayuwar duniyar ta ke ne? Washegari da sassafe na hada kayana na ce, tafiya Abuja zan yi, daman ta Abuja na zo. Baffa Adamu ya hada ni da babban dansa ya kai ni har Abuja gidan *yarsa Ummul Kursim na zauna na gama kwanakina don daman wata guda ne booking din tikitina, na komawa Egypt. Gidan Ummulkursi ne tamkar aljannar duniya tana auren Sanata, komai gashinan a wadace kamar ba a Nigeria nake ba. Ta zazzagaya da ni garin Abuja na ga gidaje, sai a lokacin nasan ashe Nigeria tana da kyau da arziki haka. Sai a lokacin na ji zuciyata ta fara warwarewa daga kuncin da nake ciki, ta ba ni hakuri bisa abubuwan da *yan uwana suka yi min. Ta yi min alkawari idan har zan iya zama a kasar nan ita kuwa zata yi wa mijinta magana ya samar min aiki a asibiti mai kyau inda za a biyani da kyau, na kama gidan haya nayi zamana har Allah Ya fito min da miji. Na yi sha,awar shawarar nan da ta ba ni, amma na ce mata zan koma Cairo tukunna na sanarwa dangina, na kuma yi musu sallama. Kafin na tahi sai da ta kai ni Kaduna wajen daya *yar uwar tamu, ita take auren Manajan wani babban banki, kudi kam ba,a magana. Muka dungumo muka je Kano wajen Hajiya Lami itama kakarmu daya, ita ma ta kafu a gidan, mijinta hamshakin dan kasuwa ne, su dukka sun yi min kyautar kudi da kaya. Da muka koma Abuja a ranar da zan tafi Sanata ya yi min yayyafin dallar, har sai da na tsorata don yawa. Allah Mai jinkan bawanSa, Ya hana ni a can Ya bude min anan. Na yi kukan farin ciki, gami da godiya mai dumbin yawa. Duk da haka Ummul Kursim ba ta barni haka ba sai da ta ba ni shaddoji da leshina dinkakku ta ce na dinga sakawa a can, ta kara bani daloli da yawa. Lallai ba dukka aka taru aka zama daya ba, wani mai kirki, wani bashi da kirki, wani mai kyauta wani marowaci. Wani mai tausayi, wani kuwa mugu ne, haka mutanen suke ciki. Suka kaini filin jirgi suka saka ni a jirgi na taho Cairo. Da na ba wa dangina labari sai suka yi takaici, suka tayani da addu ar Allah Ya saka min. Shawarar Ummul Kursim kuwa tuni suka yi facali da ita, suka ce bazan koma Nigeria ba, gara na hakura na yi zamana a cikinsu. To ba ni da zabi saboda na sallama rayuwar ma gaba daya ba ta min dadi. Ina zaune ina canja dalolina a hankali ina ci, talauci ya daina nukurkusata. Na dade ina cikin rufin asiri ina kashe dalolin nan, amma da suka dauko karewa sai hankalina ya tashi na tabbatar zan koma gidan jiya na kashewa zai gagare ni, don haka na koma neman aiki. A asibitin da na yi aiki na fara zuwa na roke su, su mayar da ni sai suka ki. Babu ta kan babban da ban bi ina roko, durkuso har kasa kuka da hawaye suka cemin sun cike gurbina da wata, ba su da inda za su saka ni. Na bazama gari duk wani asibiti da kuka sani a Cairo sai da na mika takarduna na neman aiki, kai har ma wasu asibitoci na wasu jihohin sai da na tuttuta wasu na je da kaina, wasu na aika ta internate ko na ba wa wani sako ya kai min. Amma babu wanda ya kira ni interview, don haka babu aiki. Ina cikin hali na rashi da wahala da fargabar neman aiki, sai dai a *yan uwana wanda ya dubi Allah ya ba ni dan kudi, wasu sai na roka ko su ba ni ko su hana. Babu irin wulakancin da bana gani, ga shi ba ni da saurayi ko daya balle so na ya sa ya tallafe ni ya kwantarmin da hankali. Ana cikin wannan hali sai na hadu da Gaddafi, a makarantar lafiya ajinmu daya a jami,a. Ban yi mamakin ganinsa ba, don shima likita ne, amma tunda muka gama karatu ban san inda yake ba. Yana ganina ya rungume ni cikin farin ciki muka gaisa. Hakika na ga sauyi a fatarsa da kayan da yake sanye a jikinsa, domin tsadaddu ne, kudi ya zauna masa matuka. Ya tambaye ni ''ina maigida? Ina yara? Ya kuma wajen aiki? Sai ya ga alamar damuwa nan da nan a fuskata, jikina ya yi sanyi don na rasa amsar da zan ba shi. ''Faduwa lapia kika sauya nan da nan? Ya tambaye ni yana kallona cikin yanayin tuhuma. Cikin hawaye na amsa masa dukkan tambayar da ya yi min, amsar ita ce babu. Ba ni da uwa, ba uba babu dan uwa, babu aiki balle *ya*ya. 'Subhanallah! Subhanallah!! Kalmar da yake ambato ke nan. Ya ja hannuna zuwa ga kyakkyawar motarsa muka zauna, ya roki na share hawayena na yi masa bayanin matsalolina. Tunda na fara magana ya fara girgiza kai don tausayina. Hawaye ya kasa tsayawa a idona, har na sa shima yana zubarwa. 'Faduwa kwantar da hankalinki, zan taimaka iya karfina. Kalmar da ya fara fada min kenan har tasa na tsagaita da kukan. Ya fara ba ni labarin yadda rayuwa ta yi masa kyau. Ya ce, da muka gama karatu sai ya tafi Malaysia karatu akan likita ya karanci kwarewa akan fannin tiyata ya zama Sugical Doctor Consultant. Yana gama karatu sai ya sami aiki a wani babban asibiti anan cikin babban birnin Kaula Lumpur ana biyansa albashi mai kyau. An bashi gida mai kyawun gaske, ana cirewa a albashinsa har ya zama nasa. Ya dawo gida ya yi aure ya tafi da matarsa suna zaune a can lafiya kalau cikin so da kaunar juna yanzu yaransu guda biyu mace da namiji su ma har sunyi nisa a makaranta. Ya ce washe gari zai koma Malaysia, zai karbi lambata da photocopy din takardu da E-mail address dina ya tafi da su, zai fadamin halin da ake ciki game da neman aiki. Wai amma na je na fara tuntubar dangina sun yarda sannan zai zo ya karbi takardun a ranar da daddare, saboda washegari zai wuce. Na ce, kada ma ya damu, babu abin da dangina za su ce ko su yarda ko kada su yarda ni dai zan tafi saboda yanzu da na rasa babu wanda ya dauki nauyina, babu wanda ya ke tayani yawon neman aiki, don haka yanzu na gane zan bi duk wata hanya wacce rayuwa zata yi min dadi idan dai ba hanyar sabon Ubangiji ba ce. Na ba shi adireshin gidanmu da lambar wayata, na ce don Allah da daddare ya zo ya karba zan hada masa su. Ya ce, ba don ma bai gama harhada takardun da ya zo nema ba da mun tafi ya ga gidan a lokacin, na ce masa, ba komai ya zo da daddaren. Sai na fasa shiga neman aikin na koma gida na shiga tsara takarduna, yadda suna gani zasu dauke ni. Na dukufa ina addu,a ina kuka, ina rokon Allah Ya tabbatar min da tafiyar nan, kuma Ya sa alkhairi a cikinta. Har karfe goma na dare banga Gaddafi ba, na yi ta kiran wayarsa bai amsa ba, sai na shiga zargin karya ya zukala min, nan da nan murna ta koma ciki. Sai na ji wayata tana ruri, ina dubawa na ga sunansa ne, a guje na amsa. Ya ce, 'Ga ni a kofar gidanki, ki fito. Na ce, ya shigo babu damuwa. Bayan ya shigo falona na dinga jere masa abinci da lemo da na yini ina shirya masa, don ya ji dadi ni ma ya taimake ni. Ya ji dadi da ganin abincin nan saboda yunwar da ta ke addabarsa yini guda bai ci abinci ba, yana ta yawon harhado kan takardunsa. Ya ci ya sha ya mike kafa muka yi ta hira muna kallo talabijin har karfe daya saura, sai da ya fara gyangyadi ya tashi ya yi haramar tafiya bayan na zuba masa takardun da duk ya bukata a ambulan na bashi. Ya kara ba ni hakuri a bisa bakar rayuwar da nake ciki. Ya ba ni tabbacin zai taimake ni insha Allahu. Allah Sarki, abokina kudi mai yawa ya bani da lambobin wayarsa ta gida da ta ofis na can Malaysia. Na yi masa godiaya ya tafi, yana isa Malaysia ya kira ya fada min ya isa bayan kwanaki biyu ya sake shaida min cewar ya fara nema min aiki. Abu kamar wasa an shafe watanni uku babu aiki, hankalina ya yi matukar tashi, na dameshi da waya safe da rana, ina rokonsa ya taimake ni. Har matarsa ta fara kishi da ni, tana cewa wai na rabu da mijinta kada na sake kiransa. Duk bayanin da bayanin da ya yi mata cewar ni kawarsa ce, karatu muka yi tare, amma ba ta yarda ba, kasan mata da kishi. Ban damu ba duk yana daya daga jarrabawa daga Allah. Daga karshe Gaddafi ya fitomin da sakamakon karshe cewar ba zan iya samun aiki a Malaysia ba, sai dai idan zan dawo karatu. Sai dai in zabi bangare daya na karanta har tsawon shekaru biyu ina gamawa sai su ba ni aiki ba tare da wani Cuku-cuku ba. Na ce masa duk wannan ba matsala ba ce, amma ina zan sami kudin da zan dawo Malaysia na yi karatu? Ina zan sami kudin abinci da na hayar gida? Gaddafi ya ce min, duk ba matsala ba ce, zai fada min hanyar da zan bi na sami tallafi daga Gamnatin tarayya. Ya turomin forms ta internate duk na cike na yi ta kaiwa. Kafin lokaci ya yi Gamnati ta yarda zata ba ni tallafin karatu har sai na gama. Kudin makaranta, abinci, kudin hayar gida duk sun biya min wadataccen kudi. Sai da komai ya kankama na shapawa dangina labari, kadanne suka yarjemin, duk ba su bani goyon baya ba. Na nuna musu ba neman shawararsu nake yi ba ina dai yi musu sallama ne tafiya kamar da kasa inji mai ciwon ido. Gaddafi ya taimaka min na sami gida, muka je makaranta ya ya taimaka min nayi registration ina karantar bangaren mata (Gynea). Sai na tsinci kaina cikin sabuwar rayuwa a Malaysia tare da sababbin mutane ba wadanda na sani a da ba. Na yi kokarin na zubar da bakin cikin da yake damuna a baya, na nemo farin ciki na sakawa zuciyata ba don komai ba, sai don kawai na taimaki kaina duniya da lahira. Na yi hakuri, nayi tawakalli na yarda Allah Yana sane da ni, duk yadda Ya tsaro min rayuwata dole haka za a yi. Na yarda da kaddara, yanzu ina shekara ta biyu a karatuna, ina gamawa ina da kujerar aikina a Subang Jaya Hospital idan har na ci jarabawata, wacce ba na fargabar zan fadi. Umaimah da Abdul-Sabur sun buga tagumi suna kallon Faduwa. Tausayinta ya cika musu zuciya, baiwar Allah sai murmushi ta ke don tawakkali. Nan da nan sabon tunani ya kutso zuciyar Umaimah ta tabbatar ashe ba ita kadai ce ta ke da matsala ba a rayuwa. Sai ta ji Faduwa ta burgeta ta da mayar da komai ba komai ba ta ci gaba da rayuwarta cikin kawaye da abokai tana walwala tamkar ba ta da matsalar rayuwa. Amma ita sam ta kasa yin hakan. ''ina ma zuciyata ta sami juriya da tawakkali irin na Faduwa? Umaimah ke fada a zuciyarta. Faduwa ce ta katse tunaninta data ambaci sunanta. Ta ce ''Umaimah, kalle ni nan ki gani. Kinga alamar damuwa ko fushi a fuskata? To haka kowa ya ke dannewa ya manta da komai. Shekaruna talatin da takwas a duniya amma banyi auren fari ba, nan da *yan shekaru zan shiga layin tsofaffi wadanda haihuwa zata dauke musu kuma ban haifi ko daya ba. Har yanzu Allah Bai kawo min miji ba, ga shi ina son aure. Ya ya na iya, sai in daina dariya ko kuma sai na tsani mutanen da babu ruwansu, su suka doramin? Allah ne Yake jarraba ni ya ga yaya zanyi idan Ya doramin masifa. Insha Allah Zai yaye min ko ban samuba a duniya Zai yaye min a lahira. Na yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau. Sai ta kyalkyale da dariya saboda yadda ta ga sun tsura mata ido suna kallonta kai kace talabijin suka saka a gaba. Su dukka suka yi murmushi, gami da jan doguwar ajjiyar zuciya. Abdul-Sabur ya ce, ''Ni har na rasa ma abin da zance da ke, saboda tsabagen tausayi. Sannu Faduwa, sannu da kokarin hakuri gami da juriya. Allah Ya jikan nahaifanki da dan uwanki, ke kuma Allah Ya warware miki. Wallahi ni dai ina ganinki amma ban taba tunanin a cikin wannan halin ki ke cika ba, don ba mu taba zama munyi yi hira irin hakaba. Na ga dai alamar dai ba ki da miji, sai na yi tunanin ko mutuwa ya yi ko rabuwa kuka yi yaranki na can kasarku. Faduwa ta girgiza kai ta ce, ''Babu ko daya, haka nake ni kadai, ba ni da kowa. Umaimah ta ce, ''Allah Sarki, Allah Ya jikansu, mu kuma Ya kyautata namu zuwan. Faduwa ta share hawaye ta ce, ''Ameen, na gode.'' Su dukka sun kasa cin sandwich din, ruwan shayin ne suka kukkurba suka ajiye, don tashin hankalin abubuwan da suke fitowa daga bakin Faduwa. Suka dunguma zuwa kan kujerun da suke falon, suka fara kallon wani film da ake yi a MBC Action mai suna NIKITA Faduwa ta dubi Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Umamah, zan so naji tarihinki. Kina karamarki me yasa kika shiga damuwa haka? Naga shekarunki ba suyi nisan da zaki damu ba don ba ki yi aure ba. Meye matsalarki? Yayin da Abdul-Sabur ya ware ido da kunnuwa yana kallo, yana kuma saurarenta don ya kagu ya ji ko ita wace ce. Sai kunya ta rufe Umaimah, ta yi murmushi ta sunkuyar da kai gami da sosa goshi. Ba ta san ta inda zata fara amsa wannan tambayoyi da Faduwa ta jero mata ba, tana da nauyi amsawa sosai. Abdul-Sabur ya gyara zama ya ce, ''Mu da ke mun zama *yan uwa masu kaunar juna da tausayawa. Kamar faduwa yaune na farajin labarinta, na ji na sake shakuwa da ita, kuma zanyi tattalinta wajen kula da walwalarta da taimakonta da shawarwari. To haka musulmai ya kamata su kasance musamman na MAKWABTA. Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Haka ya ke, ka ba ni labarinka tukunna sai in bada nawa. Abdul-Sabur da Faduwa suka kwashe da dariya ya ce, ''Labarina kike so ki ji kafin ki bani naki? To ki gyara zama ki karkade kunnenki kisha labari. Ni da Faduwa za,a sami wanda rayuwarsa ta fi abin tausayi. Faduwa da Umaimah suka gyara zama suka zuba masa na mujiya suna kallo, suka baza na zomo suna saurarensa, dan sun kagu ya fara fada. LABARIN ABDUL-SABUR Ya ce, ''Sunana Abdul-Sabur, sunan mahaifina AbdulRashid, Mahifiyata kuwa Habiba. Mahaifina mutumin kasar Ghana ne a cikin garin Accra, duk da asalinsa Bakano ne mahaifansa zama ya kai su Accra aka haife shi a can. Mahaifiyata kuwa mutumiyar Kano ce, wani gari da ake kira Gwarzo. Kasuwanci tsakanin Accra zuwa Lagos, zuwa Kano shine sana,ar da mahaifina yake yi, shi da *yan uwansa da abokansa a dalilin haka ne ya zo Kano harya hadu da Mahaifiyata. Aka yi rufa-rufa aka hada baki da tsohon da ya ke yi musu masauki a Kano mai suna Malam Barau, ya ce shi ne mahaifinsa, aka ba shi auren mahaifiyata Habibah ba tare da danginta sun san gaskiyar magana ba. Bayan anyi biki suka zauna a unguwar kofar Nassarawa kusa da gidan Sarki, gida daya suke zaune da Malam Barau. Don haka Mahaifiyata ta zaci Malam Barau shi ne surukinta, wanda ya haifi mijinta, ko kuma yaya ga mahaifinsa uwa daya uba daya. Suna zaune zama na girmama juna da martaba juna, har Allah Ya albarkace su da samun haihuwa, aka haifi ni Abdul-Sabur sunana, Malam Barau ya zaba ya saka min, banci sunan kowa ba. Shekaruna hudu a duniya aka haifi kanwata aka saka mata suna Khausar. Ni da Khausar muka taso cikin kuncin rayuwa, shi kan shi gidan Malam Barau din dan karami ne, matansa biyu da *ya*ya kwatsam. A cikin gidan aka yanki daki daya kacal aka zagaye mana babu kicin sai dai muyi a kofar daki, ban daki kuwa sai dai mu dauki buta mu zagaya gidan Malam Barau mu bi dogon layin shiga bandaki. Babu maganar makarantar boko ma a nan a zube muke tare da yaran unguwa, sai dai muna zuwa makarantar allo safe da yamma. Mahaifina matafiyi ne, bai cika zama a gida ba saboda yanayin kasuwancinsa tsakanin kano da Lagos, zuwa Accra bai daina ba, kuma ya fi dadewa Accra ashe can ne garinsu, can ya fi sabawa a can ya fi zama. Mu sai ya shafe watanni shida baizo ba. Kayan abinci ya kare babu kudi, sai mu yi ta fama, bara ce kawai ba ma yi. Allah Sarki uwa, Mahaifiyarmu Umma Habiba muke kiranta ta sha wahala da mu. Saboda tsabar surfe da daka har zannuwanta yayyagewa suke yi, ba ma a maganar hannayenta duk sunyi kanta, don kawai ta ba mu abinci muci. Allah sarki rayuwa kowa da kalar tasa jarabawan. Allah ya yayewa kowa kunci na rayuwar sa yasa mu haye jarabawar rayuwar dunia. Aameen. Babu irin sana'ar da ba ta yi ba, har da irin sana'ar nan da mata suke yi a kasuwar rimi ta siyar da tsofaffin kayan sakawa. Ba zan manta ba aka ba ta dillancin wasu kaya atamfofi da leshina akan ta je ta siyar za a bata lada ashe kayan sata ne, sai mai kaya ta kama kayanta a wajen siyarwa da aka bi diddigi aka gane mahaifiyata ce ta siyar, aka taho da *yan sanda aka kama ta har gida. Kwanan Ummana Habiba biyar a daure a ofishin *yan sanda, hankalina ya yi matukar tashi. Daga lokacin na kuduri niyyar neman sana'ar yi kowacce iri ce, idan dai halak ce, don na hana mahaifiyata irin wannan wahala. Malam Barau ne ya dinga kai kawo da kyar aka fito da ita da sharadin sai ta biya mutane kudinsu, ita kuwa ba ita ba ce ta kashe kudi, lada aka bata wanda bai kai ya kawo ba. Data yiwa matar data sato kayan ta bata talla maganar cewar ta kawo wadannan kudi su mayar, sai ta ce ita tuni ta kashe kudi. Tsohuwar fankar mu, tsohon gadon mu mai rumfa na karfe su muka fitar muka siyar muka biya bashi muka koma bacci akan tsofaffin tabarmi da tsummokaan kayanmu., don ko tsohuwar katifa bamu da ita.... Abdul-Sabur ya cije lebe yayin da hawaye mai zafi ya yi ta kwaranyowa masa. Ya kasa ci gaba da magana saboda tsananin kunar da zuciyarsa ke yi masa. Faduwa ma ta matse hawaye ta girgiza kai ta ce, Allah Sarki ka sake tuna min da uwata ita kadai na sani a duniya ta tafi ta bar ni. Umaimah ta runtse ido sai hawaye ya bulbulo daga idanuwanta masu radadin fita, tabbas itama ta tuna da tata tsuhuwar. Abdul-Sabur ya sa hannu a aljihu ya zaro hankici ya sharbe ido da hanci ya ci gaba da cewa. ''Duk abin nan da ake wai sunan mahaifina yana raye a duniya ya yi tafiyarsa ya bar mu. Abinci da yake bari da kudin cefane bai fi na wata guda ba, sai ya je ya yi watanni shida kuma sannan ya zo ya yi wata daya ya koma. Sutura sai da sallah zai yi mana guda daya-daya su ma ba na kirki ba kafin shekara ta zagayo sun kece. Mahaifiyata ta so ta dinga rike hannun Khausar suna zuwa bara, na hana su, na ce su zauna a gida ni zan fita nema. Shekaruna goma sha daya na saba da dako a kasuwar *yan rodi da ke kofar ruwa, nan cikin jihar Kano. Tokar itace ce muke daukowa aka mu ke kaiwa masu karafe, su bamu naira biyu ko uku, a yini dai baifi na sami naira biyar ba. Ba zan manta ba akwai wata rana da na dauko toka aka cikin wani katon daro ashe akwai garwashi a ciki ban sani ba, tururin zafinne ya cinye kwalin da na dora a kaina ya soma cinye gashin kaina, sai da ya fara kona fatar kaina sannan na ji zafi na yi wurgi da daron, sai ga gashina kamar anyi gobara. Ranar babu kudi saboda na zubar da toka ga ciwo a kaina ba zan iya zuwa na nemo wata ba. Da kafa na taho gida ga nisa, ga yunwa, ga ciwo. Ina zuwa gida na iske taron jama,a aka shaidamin daga Accra aka aiko da wasikar cewar, mahaifina ya rasu. Na gigice, na tambaya ina gawar aka ce an binnne shi a can. Sai na yi mamaki me yasa ba a kawo shi ba wajen mahaifinsa da *yan uwansa ba an binne shi? Mun yi kuka sosai, musamman mahaifiyata, ashe ita tasan tashin hankalin da zata shiga nan gaba. Muna nan dai a haka har ta gama takaba, ni nake fita inayin dako na kawo muci garau-garau mu kwanta. Sai naga Malam Barau da abokan mahaifana su uku suma *yan Ghana ne sun shigo bangarenmu suka kira Mahaifiyata suka zazzauna. Sai aka koremu waje ni da kanwata suka ce za su yi magana. Na kama hannun kanwata muka fice, na zaunar da ita a kofar gida, sai na dawo na labe ina so na ji abin da yake faruwa. Kamar yadda Umma Habibah ta girgiza ta razana da jin bayanansu, haka nima na dimauce, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Abdul-Sabur ya yi shiru ya dafe kai ya kasa ci gaba da magana. ''Me ya ke faruwa?'' Umaimah ta tambata a gigice. AbdulSabur ya dago da jajayen idanuwansa ya dube su. Ya ce, ''Allah Ya yi mana maganin masifa, kada Allah Ya maimaita mana bala,i. Wato gaskiya ce aka fede ta daga wuya har bindi. Malam Barau ya fadi duk kulla-kullar da aka harhada wajen auren Umma Habibah aka ce shi ne mahaifinsa alhali shi bai san shi ba, sai a sanadiyyar kasuwanci. Malam Barau ya kara da cewa shi ya ke basu masauki idan sun kawo kaya daga Ghana. Ashe zaman nan da muke yi agidan Malam Barau haya ce muke yi, duk shekara mahaifina yana biya. Don haka babu hadin mahaifina da Kano, danginsa dukka suna Accra. Wadannan da suke tare da Malam Barau sune abokansa daga Accra su ma suke zuwa tare da mahaifina, su ne ma suka kawowa Malam Barau labarin rasuwarsa. Sun shaida cewar iyaye da kakannin mahaifina *yan Accra ne. Mahaifinsa ya rasu Mahaifiyarsa na nan a raye wato kakarmu. Kuma yana da *yan uwa da yawa wadanda suke uwa daya uba daya, da wadan da suke uba daya kawai. Sannan yana da mata biyu a can da *ya*ya takwas. Bai fada musu ya yi aure a Kano ba har ya haifi *ya*ya biyu ba, sai bayan rasuwarsa aka fada musu sun ce babu ruwansu tunda bai fada musu da bakinsa ba. Suka rabe gadonsu duk da hotunanmu da aka nuna musu a cikin kayansa. Kenan mu mun tashi a tutar babu, ba mu da gado a can, a she a nan ma ba gidanmu ba ne. ''Allah Ya isa tsakanina da ku da shi da ya mutu, kun ci amanata.'' Kalmar da Ummana Habibah ta dinga fada ke nan, ta tashi da gudu ta shiga daki tana kuka. Subhanallahi! Sai na sulale na tsuguna na rike kai, har su Malam Barau suka fito suka iske ni a inda na labe. Sai suka tausaya min. Baba Mukhtar daya daga cikin abokan Babana ne ya jawo hannuna ya rike ya ce, ''Yi hakuri Abdul-Sabur ka zama jarumin namiji ka taimaki mahaifiyarka da kanwarka. Gata daya zaka yiwa kanka a duniya shi ne ka yi karatu, ka shiga makaranta ka dage ka yo karatu duk runtsi, sannan rayuwarka zata yi haske. Ya damko kudi daga aljihunsa ya mika min, sauran abokansa ma suka bani kudi mai auki kuwa, suna tafiya ban shiga gida ba, sai na je na kama hannun kanwata. Na ce da ita, ''Zo muje nu shiga makarantar boko. Da rana tsaka head master makarantar gwamnati ta unguwarmu ya ganni a cikin ofishinsa. Na yi masa bayani ya fahimce ni amma bai gamsu ba har sai ya ga manya na, ya ce na je na taho da wani babba. Na je na sami Malam Barau na shaida masa, sai ya yi dariya ya ce, kada na bata lokacina wajen yin boko, na tafi kasuwa kawai. Na fito na je na sami mahaifiyata na ce, ta zo ana nemanta a makarantar boko. Sai ta yi mamaki da jin haka, ta hau rawar jiki ta dafe kirji ta tambaye ni ko lafiya. Na shaida mata lafiya kalau, Khausar ma na can a ofishin shugaban makaranta shi ya ce na kira babba. Sai ta gigice ta dauka laifi ta yi, ta hau karkarwar jiki muka dunguma muka je. Da muka isa sai ta tambaye shi ko lafiya, me muka yi? Sai shugaban makarantar ya yi mamaki da jin kalaman mahaifiyata, amma sai ya yi mata bayanin abin da na zo da shi. Ta girgiza kai ta ce, ''Ba ni na turo su ba, ba ni da kudin da zan iya saka su a makarantar boko. Shugaban makarantar ya ce, ''Ah babu abinda za ki biya makarantar gwamnati ce, sai kayan makaranta da litattafai, wasu littattafan ma ana basu a makarantar. Ta ce, ''Ba ni da kudin siyen kayan makarantar ma, idan ma ya fara zuwa makarantar waye zai je ya yi dako ya samo mana abin da zamu ci? Ai shi ne mai fita nema dan haka ba ma son karatun. Na fito da kudi daga aljihuna na ce, ''Ina da kudi, Baba Mukhtar ne ya ba ni suka ce na shiga makarantar boko shi ne kadai zan yi wa kaina gata. Shugaban makarantar ya yi farin ciki dajin haka. Ya ce, ''Wannan haka yake yaro, ka daure ka yi karatu. Hajiya ki barshi ya yi karatu don inganta rayuwarku gaba daya''. Ba ta da ta cewa, sai ta yi min addu'ar Allah Ya sa albarka a karatun da zanyi, sai dai Khausar ce ake ta shawara a kanta, na ce a saka mu a aji daya. Daga makarantar kasuwa muka wuce da Ummanmu Habibah ta yankar mana yadin makaranta, aka kawo wajen tela ta dinka mana, muka fara zuwa makaranta. A aji daya aka sakamu, *yan ajin namu duk yara ne dai-dai Khausar, na fi duk *yan ajin girma a haka dai nake zuwa duk da tsokanar da nake sha a wajen yara wai gardi a cikin yara da dai shauransu. Ban damu ba haka nake zuwa makaranta idan na dawo na tafi kasuwa neman kudi, sana,a kala-kala babu irin wacce bana yi ta karfi. In samo kudi na zo muyi tuwon masara miyar kuka, kullum shine abincin mu. Malam Barau ya yi mana mutunci bama biyan haya a kyauta muke zaune, ya ga babu yadda zamu yi. Nine monita a ajinmu na fi kowa kokari daga ni sai kanwata Khausar ta iya karatu radau a baki, nan da nan ta fara iya rubutu itama kai ka ce daman an taba koya mana a gida. Muna aji uku na firamare Malam Barau ya rasu, ko wata daya bai yi ba iyalansa suka ba mu lokaci mu tashi daga gidansu. Tashin hankali ya same mu, ba mu da mafita sai dai mu koma Gwarzo wajen danginta, duk da bata da uwa da uba tana da *yan uwanta da dakinta na gado duk da na kasa ne. Can muka kaura muka zauna, sai na samu aka yimin cuku-cuku na shiga sakandiren maza ta kwana, na bar Khausar a gida suna ta sana'ar cura fura ita da Ummarmu. Ba laifi talauci ya ragu saboda rayuwar kauye ta fi ta birni sauki, duk inda kaa samu rogo da gyada ka ci na naira biyar sai ka yini kana shan ruwa. Mahaifiyata ta yi wani auren a cikin Gwarzo ta tafi da Khausar ni aka bari a cikin gida wajen dangi yau na kwana a nan gidan, idan an min gori na koma wani gidan. Har na fi so na koma makaranta idan mun yi hutu dan na fi jin dadin makarantar, saboda ina tare da abokaina *ya*yan masu hali dakikai, ni nake ba su amsa su kuma su bani kudi ko biskit da madara. Allah ba Ya hadawa mutum daya komai, ni ya bani kokari Ya hanani dukiya, su Ya yaye musu talauci, Ya dauke kwakwalwar. Mahaifiyata ta haifi *yan biyu a gidan sabon mijinta mace da namiji, Hassan da hussaina. Da ta sami ciki na biyu kuma a garin haihuwa ta sami matsala har ta rasu a garin haihuwa, ta mutu ba ta haifi cikin ba. Muka zamo babu uwa babu uba.... 'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Faduwa da Umaimah suka hada baki suka fada. ''Allah Sarki, Allah Ya jikanta. Inji Umaimah. Faduwa ta rushe da kuka, daga dukkan alamu ta tuna ranar da ta rasa ta ta mahaifiyar ta rasu. Abdul-Sabur ya goge hawaye ya ci gaba da cewa. ''Dangin Baban Hassan da Usaina suka dauke su, ni da kanwata ce abun tausayi. Ina makaranta ina tunanin Khausar saboda na san babu mai kula da ita. Sannan idan na dawo ba jin dadin halin da nake zuwa na iske ba nake ji, abinci a wulakance ake ba ta, haka babu mai kulawa da lafiyarta da tarbiyarta. Ba zan manta ba, muka yi fada da wani dan yayar Ummarmu mai suna Gali, ya yi min gori wai shegu wadanda ba'a san asalin Babansu ba. Tun daga lokacin na kuduri aniyar sai na nemo dangin Mahaifina. Ina aji hudu a sakandire na daina zuwa makaranta na shiga aikin gona sosai, muka sami amfanin gona a gonar Mahaifiyata data bar mana gado, na siyar da abinci buhubuhu na kunshe kudina na boye. Na dawo Kano na sami Yaya Bala babban dan Malam Barau na ce ya kai ni wajen da su Baba Mukhtar suke sauka, abokan Babana. Na ci sa'a kuwa sun zo gari a lokacin, ya kai ni har masaukinsu. Sai suka yi mamaki da ganina, bayan mun gaisa sannan na shaida musu Ummana Habibah ta rasu, sun girgiza da jin haka sun tausayamin gami da yi mata addu'a Allah Ya jikanta da rahama. Na ce musu so nake su kaini wajen dangin Mahaifina a Accra. Sai suka hau kame-kame da alama basa so su kai ni, na ce ni dai ina so na je na gansu. Yadda na fuskanta gudun wahala suke, sun dauki ba ni da kudin mota. Da na nuna musu kudina sai nan da nan suka yarda zan bi Baba Mukhtar dan shine zai tafi kwanakin. Muka ci gaba da hira na shaida masa cewar zan tafi da kanwata Khausar. Ya ce, a,a na ja dai ni kadai tukunna, na ce a'a nafi so naje da kanwata tunda Kakarmu na nan mu zauna tare da ita saboda bamu da kowa a nan. Muka shirya ranar tafiya ya ce na je mu shiryo mu zo mu tafi wani satin. Na ke na sanarwa Khausar, ya amince, sannan muka je muka yi wa dangin Mahaifiyata sallama na ce zan bi wani dan uwan Babana Accra za mu ga dangin Mahaifinmu. Wasu sun amince, wasu basu amince ba, daman ba amincewar su muke nema ba, don babu wanda ya ke tsninana mana komai. Zumuncin yanzu ya zama kamar shuka gyada a bakin kurege. Kawu mai kudi ne Yaya ne ga Umma Habibah Babansu daya ya dage ba zamu ta fi ba saboda ba'a san wanda zamu bi ba yadda duniyar nan ta zama abar tsoro. Sai na je na kirawo Baba Mukhtar ya je har Gwarzo ya yi musu bayani. Sun gamsu ya san Mahaifinmu amma dole aka ce sai an hada mu da wani Babba ya raka mu. Da aka yi shawara sai aka ce Shehune zai raka mu shine mai bin Ummana Habibah a dakinsu, muka dungumo muka taho tare zuwa Kano tashar Unguwa uku, muka wuce kai tsaye, muka hau doguwar motar nan zuwa Lagos da magruba. Ba mu isa Lagos ba sai da sassafe, sallah kadai muka yi muka sayi gayan biredi da ruwa muka ci muka sake shiga wata mota wacce zata kaimu har Accra. Tafiya yankin azaba, mun gaji likis ga yunwa, saboda wahala ta yi ta amai saboda rashin sabon shiga mota da ba ta yi. Ledoji aka yi ta bata tana cikawa ana jefawa ta wundo. Da muka zo bodar Abijan, Immigration suka tsayar da mu suka sa kowa ya firfito suka ce kowa ya fito da passport dinsa. Masu shi suka fito da su, irin su Baba Mukhtar. Mu da ba mu da shi sai hankalinmu ya tashi. Baba Mukhtar ya ce, na kwantar da hankalina dan kudi kawai zamu rike a hannu maimakon Passport sai mu sunna musu cin hanci, sai zance ya wuce. Haka kuwa aka yi, na rike naira hamsin na bawa Khausar da Kawu Shehu suma suka rike, da aka zo kanmu sai muka mika musu kudi, suka karbe aka ce mu koma cikin mota mu zauna, aka ci gaba da tafiya (cin hanci ruwan dare). Haka da muka zo bodar Togo ma immigration suka tsayar da nu irin na bodar Abijan aka yi, naira hamsin ta raba mu da su muka wuce daga nan har cikin Accra babu matsala kuma. GHANA, ACCRA Mun isa Accra daf da magruba muka sauka a tashar Aflawu, daga nan muka dauki tasi muka nufi 'Lagon New town' a in da gidan Kakarmu ya ke. Sunanta Husaina suna kiranta da Ummana Fuse. Da yake ta san labarinmu daga wajen Baba Mukhtar, tana ganin Baba Mukhtar da yara biyi jikinta ya bata mu ne, sai ta fashe da kuka ta rungume mu. Mahaifina kamarsu daya sak da mahaifiyarsa, haka Khausar tayi kama da su sak, bakake ne sannan ba su da tsayi sosai masu dogon hanci. Ni kuwa da mahaifiyata nayi kama, don ita farar bafillatana ce, doguwa ga ido da hanci. Ghana kasa ce da take dauke da kabilu daban-daban, arna sunfi yawa duk inda kaga musulmi Bahaushe, to zuwa ya yi kamar daga Niger ko Nigeria. Manyan yaren kasar guda biyu ne, Ankara da Asanti. *Yan yaren Asanti su ne asalin *yan Ghana sun fitone daga Kumasi, akasarinsu gajeru ne bakake. Ankarawa kuwa farare ne masu bille sunfi *yan kabilar Asanti kyau. Su ma ana tunanin zuwa suka yi shekaru aru-aru da suka wauce. Sunan kudinsu CEDIS wanda ko rabin darajar Naira bai kai ba, idan ka ji ance Cedis 1000 tabbata bai wuce naira 10 ba. Washegari kakarmu Ummana Fuse ta aika aka hado mata *ya*ya da jikokinta ta gabatar damu. Babu tantama kowa ya shaida mu ma *ya*yansa ne, daman can suna da labarinmu. Da bakinsa ya shaida musu cewar ya yi aure a Nigeria har yana da *ya*ya biyu, amma fa sai daf da zai mutu ya fada. Mu ne dai bai fada mana ba yana da wasu matan da yara a can. Gado dai an rabe, daman ba wani abin kirki ya bari ba. Sai suka yi ta zukewa kowa yana gudun wahala aka rasa mai rike mu. Ummana Fuse itace dolenmu don haka wajenta muka zauna. Gida ne a gine ginin sumunti daki biyu da tsakar gida, *ya*yanta suka gina mata a unguwa mai kyau. Bayan wannan kuwa babu wani abu da suke ajiye mata, komai ita ta ke nema ta yiwa kanta. Sana'ar kera tukwane na kasa take yi kuma ba wani kudin kirki ta ke samu a yini. Ta shaida mana cewa a garin nan babu mai zaman banza, kowa fita yake ya nemi abinda zai ci,tun daga safe zuwa dare. Idan ka zauna a gida babu mai baka, haka mata da maza, yara da manya suke yi. Ga su da nuna kabilanci, Hausawa koma na ce Musulmi ba su da karfi a kasar wajen yin mulki ko samun aikin gwamnati. Babu karatu babu aikin gwamnati don haka sana'ar karfice ta wajaba akansu. Ummana Fuse ta sa aka samo min aikin jiran shago a wani kantin dan uwanta da yake kasuwar Art Traditional Tourism inda suke siyar da kayan gargajiya, kamar takalman fata, abin wuya na dutsuna, gangam hula dara, kayan kinta (yadi) da dai sauransu. A nanne zaka ga Turawa daga kasashe daban-daban suna zuwa suna kallo, kuma suna siya. Abinka da Nasara asarar duniya, sun fi sha'awar irin wadannan abubuwan na gargajiya. Ciniki ake yi sosaikullum nake zuwa tun daga safe har zuwa magruba. Cedis dubu biyar yake ba ni kwatankwacin naira dari kudin Nigeria, kasancewar kudin Ghana ba shi da daraja kamar yadda na fada a baya. Cedis dubu biyar din nan abinci kadai nake iya ci na rana da dare, shi ma kuma ba don na koshi ba, kuma babu nama. Dukunu da Tankwa nake ci kullum, shi zai fi kosar da ni, don ya fi arha. Umaimah ta dubo shi, ya ce, ''Meye dukunu da tankwa kuma? Abdul-Sabur ya yi murmushi ya ce, ''Abincin *yan Ghana ke nan. Dukunu shi ne kamar tuwo, tankwa kuwa ita ce miyar da ake ci da shi. Idan aka jika masara ta kwama sai aje a markado sai a dan dafa ya yi kauri shi ke nan sai a ci da tankwa. Tankwa kuwa kayan miya ne da attaruhu, albasa da tumatir ake murjewa a asanka. Kanwata Khausar kuwa a kasuwar Agulgoshi aka kai ta nan ce kasuwar da ake siyar da danyen kaya buhu-buhu, ana saukewa daga mota-mota. Shagon wata mata mai suna Hajiya Momi tana sayr da bainci, Khausar ta ke taya ta dafawa da siyarwa. Suna siyar da shinkafa da miya, Dukunu, muri da Algilma, su yi miyar gyada ko miyar kwakwa. Idan kuna neman muguwar mata aka samu Hajiya Momi to aja layi a tsaya, saboda bata da tausayi ta wahalar da kanwata Khausar, ba kudi ta ke ba ta ba, abincin rana da na dare ne kawai ta ke ci ta koshi. Sai shegen fada da duka kullun ta ke yi mata bayan aikin da ya fi karfinta, da ta ke jifga mata. Idan ku kaga daron da ta ke dauka a kanta ta kai markadem kayan miya da markaden masarar yin Dukunu sai kun tausaya mata duk da dai ba wani nisa ne ke da akwai ba tsakanin inda suke kasuwancin da gurin kai markaden. Gashin tsakiyar kanta har saisayewa ya ke yi saboda daukar kaya. Idan abinci ya yi kwantai akai zata dora mata ta yi zagayawa gari sai ta siyar. MAKWABTAKA 15 Khausar kullum tana kuka da zarar gari ya waye saboda fargabar wahalar da zata je ta tarar a kasuwa. Ni da kakata abin nan ya fara isarmu ita ba kudi ta ke kawo mana ba, don ba ta biyanta komai. Da kakata ta yiwa Hajiya Momi magana akan ta rangwanta mata wahala, ta kuma dinga biynata kudi, sai ta ce sai dai idan ta daina aikin saboda abincin da ta ke ci ma ai na kudi ne, mai yawa. Dole muka bar Khausar ta ci gaba da yi don idan ba ta yi ba wa zai ba ta abinci ta ci, kowa yana ta kansa? Ana cikin wannan hali ne sai Allah Ya kawo wani kawunmu Hamza koma in ce Kakanmu don shine auta a dakin su Ummana Fuse. Ya fi shekara ashirin a England, ya auri baturiya ya haifi yaransa Turawa guda uku, Babban namijin ne zaiyi sa'ana sauran kuma dukka mata, sai a lokacin ya fara kawo su kasarsa. Da Uncle Hamza ya zo gidan Ummana Fuse ya ganmu sai ya tambaye ta mu su waye? Sai ta zauna ta bashi tarihinmu kakaf. Sai ya tausaya mana daman ya ji labarin rasuwar Babanmu ta waya. Ya tambaya yanzu me muke yi karatu ko aiki? Ummana Fuse ta fada masa cewar ni ina tsare kanti, Khausar tana siyarwa wata abinci a kasuwa. Ya tambaye ni nawa ake biyanmu, na koro masa bayanin cewa babu abin da muke samu banda abinci, sai ya girgiza kai. Ya ce, ''A'a wannan ba sana'a ba ce, gara mu koma makaranta. Kamar yadda na fada muku a baya ana nunawa Hausawa, Musulmai kabilanci. Ba a bari suyi karatu, idan sun kutsa sunyi karatun ma babu aikin gwamnati. Ya ce kafin ya tafi zai samo min makarantar sakandire ta kudi na karasa karatuna, tunda har na kai aji na hudu a can, kuma ya fuskanci ina da kokari, ina magana da Turanci sosai. Ita kuma Khausar tunda ba ta yi nisa a karatu ba zai samar mata makarantar koyon sana,a ta koyo ta dinga yi. Sai Ummana Fuse ta ce a saka ta a makarantar koyon rinin kamfala, amma babu makarantar anan kusa sai a Abrkan ake yi. Sai dai idan ta koma gidan kanwarta Umma Aisha da ta ke unguwar Dukuma ya fi kusa da Abekan. Shikenan sai aka tsayar da wannan shawara kafin ya koma England sai da ya tabbatar na fara zuwa makaranta, Khausar ta khaura gidan Ummna Aisha da ke Dakuma da zama, tana zuwa Abekan koyon kamfala. Ya yi mana alkawarin zai dinga aiko mana da kudin makaranta (school fees), da kudin motar zuwa da dawowa har mu gama. Abu daya ne ba mu ji dadi ba, shi ne da aka raba mu ni da Khausar domin tunda muke a rayuwarmu ba mu taba rabuwa ba. Ta yi ta kuka kullum ana ba ta hakuri haka ni ma idan na shiga bacci, sai na yi ta kuka ni kadai don tausayinta, bata da kowa sai ni na rage mata, haka ni ma ita ta rage min. Koda yake muna ganin kakarmu mai tausayinmu muna jin dadi, sai kadan daga cikin dangi masu kula mu kamar su Uncle Hamza da ya zo ya taimake mu. Duk wanda ya taimaki wani Allah Zai taimake shi...'' Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta ce, ''Ya ya aka yi kuma? Abdul-Sabur ya yi dan murmushi, ya ce, ''Suna kiran motar hayarsu Bus da suna Toro-toro, kullum sai na hau toro-toro na tafi makaranta idan an taso na hau na dawo gida. Na ga bambanci tsakanin karatun Kano da na Accra, a Kano na fi *yan ajinmu kokari, tunda na shiga makaranta daga firamare har zuwa sakandire ni ne monita dan kokarina, amma a Accra ni nake zuwa na karshe a ajinmu har ana tunanin a mayar da ni ajin baya. Allah Ya taikama Malamin ajinmu ya ce a kyale ni ya ga alamar ina da kwazo da saurin koyo, watakila idan na dage na saba da *yan ajin zan yi kokari. Turancin su daban da namu, domin su suna kwaikwayon irin na turawa ne sosai ba kamar anan Nigeria ba da kowa yake yin yadda ya ke so. Hausawa suna turanci kamar da Hausa suke magana, Yarbawa suna yi kamar da Yarbanci, haka Igbo da sauran kabilu (broken English). Idan ka ji dan Ghana yana Turanci sai ka rantse a Turai ya girma, saboda kowacce kalma suna furta ta dai-dai da yadda Turawan suke furtawa. Tabbas yadda Malamin ajinmu ya fada haka ne, rashin sabo, fargaba da gane turancinsu ne ya sa na zama komabaya a ajinmu ba wai rashin kokarin ba ne. Amma da shekara ta zagayo sai warware gaba daya na rikide, ni da *yan ajin ake damawa. Da muka gama aji hudu muka wuce aji na biyar nan ne na gagari maza, ba ma matan ajin ba. Mu uku ne muke gumurzu akan karbar na daya. Idan na tashi daga makaranta da yamma sai na tafi 'Zarbarma Land' sunan unguwar ke nan, akasarin *yan unguwar Zabarmawa ne, ma'ana daga kasar Niger suke. Suna sana'ar canjin kudi, wasu na siyar da albasa, leda da fina-finan Hausa ko pure water. Ko na je unguwar Zango nan kuma *yan Nigeria ne, a nan ne za ku ga masu bara kutare, makafi da guragu. Nan na ke samun abin yi irin su dako, ko jiran shago ko tallata kaya a cikin kasuwa na je na zazzagaya na yi ciniki na kawo a sallame ni da dan kudi kalilan na ci abinci, na rago sauran na ba wa kakata ko na boye na ci abinci a makaranta idan an fito break.... Faduwa ta girgiza kai alamar tausayi, ta ce, Allah Sarki, ina kanwarka Khausar, a wanne hali ta ke ciki a can unguwa mai nisa Dukuma?'' Abdul-Sabur ya yi murmushin karfin hali ya ce, ''Tana can tunda ta je sai da ta shekara ba ta zo unguwarmu ba, ni ne dai duk sanda na bushi iska nake zuwa na ganta, haka kakarmu tana kokarin zuwa. Idan ta samo kwancen atamfofi sai ta zuba a leda ta je ta kai mata. Rayuwar Khausar abin tausayi ce a can, gida ne da yake cike da *yan mata, *ya*ya da jikoki na Ummana Aisha. Wasu *yan makaranta, wasu babu karatun, wasu ustazai wasu kuwa *yan iska. *Yan mata sunfi goma don haka sai rigingimu da tsegungumi, sun tsani Khausar, sharrace-sharrece kalakala idan an rasa wani abu ace ita ta dauka ayi ta zaginta ana dungureta. Sai daga baya aga abin ko a kama wacce ta sace a cikinsu Haka kowacce ta ke ciyar da kanta, don haka dole Khausar ta fita nema. Kudin motar zuwa da dawowa Abekan ba ya da matsala Uncle Hamza ya turowa Ummana Aisha tana ba ta, sai na siyen abinci ne da na zirga-zirga don daga makarantar wani lokaci suna hawa toro-toro su je wasu unguwannin koyon aiki kamar unguwar Nima, Guinea kwanakir ko Mamubi. Suna yini acan tun daga safe har marece. Ina iyakacin kokarina wajen kawo mata agaji da *yan kudade, biredi ko fanke da zata dinga yaga tana ci a duk lokacin da ta ji alamar yunwa zata yi mata illa. Rayuwa kenan, komai mai wucewa ne, dadi ko wahala.... Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Haka ne, babu abin da yake dauwamamme a duniya. Ya ce, ''Khausa ta rame saboda kewa ta, ga tsangwama da rashin wadataccen abinci. Sai na bata shawara ta dinga zuwa kasuwa tana rini ranar asabar da lahadi sai ta dan adana kudin da ta samo ta dinga cin abinci a makaranta. Da kai na na kai ta wata karamar kasuwa da ake kira Malata, anfi siyar da gwanjo a kasuwar, anan na samar mata aiki a shagon wata mata mai suna Mrs. Ibrahim don bana so na kai ta shagon maza saboda lalata. Ghana ba kamar Nigeria ba ne, inda ADDINI da AL'ADA suka saka kunyaa idon mutane, sukan rike mace a bainal nasi ba komai ba ne. Don haka zinace-zinace ya yi yawa, saboda arna sun fi yawa. Da farko Mrs. Ibrahim ta ki yarda ta dauke ta aiki data ji an ce sai asabar da lahadi kadai zata dinga zuwa, ta fi son wacce zata dinga zuwa kullum. Na dinga rokar ta har da durkusawa a kasa ina zubar da hawaye ina cewa ta taimaka mana mu marayu ne kuma baki ne a kasar dan bamu da inda zamu je mu sami wani aikin in ba a wajenta ba. Nan danan ta ji zuciyarta ta karaya sai ta tausaya mana ta amince. Sai na ji hankalina ya kwanta dan naga hankalin Kausar ya kwanta, ta kuwa ci sa'a ta hadu da uwar daki mai kyauta da tausayi. Tana bata lada fiye da kudin aikin yadda ta dauke ta. Allahu Akbar! Rayuwa kenan Allah Yana bayan wanda Ya dogara da Shi. Shekara biyu ne daman ake yi a makarantar koyar kamfala, Allah cikin ikonSa Khausar ta kammala, aka bata satifiket dan haka Ummana Fuse ta daukota, ta dawo da ita gidanta sai farin ciki ya kama mu. A waya na shaidawa Uncle Hamza cewar Khausar ta kammala makaranta tana neman jari za ta dinga yin rinin a gida. Ummana Fuse ta karbi waya ta sake yi masa bayani ta roke shi daya sake jurewa ya ci gaba da taimakon mu, dan mu marayu ne Allah zai taimakesa shima. Ya ce babu matsala, Khausar ta rubuta abubuwan da take bukata da yawan kudaden dan ya turo mata da kudin. Akwai wani bangare a gidanmu tsohon waje ne, bangarensa na gado ya ce ya bata aro ta dauka sai ta dinga yin rinin a ciki. Daya turo mata da kudin sai muka dauko masana suka tona mata ramukan, muka je kasuwa muka hado duk abubuwan da ake bukata a wajen rinin. Ni da Ummana Fuse sai muke dan taya ta duk da bamu san yadda ake yi ba amma muna taya ta da miko wannan, zubo wancan kamo wadancan. Idan tayi rina ta buga kamfalu kamar turmi goma ko ashirin sai ta kai kasuwa ta sararwa masu shagunan da suke sayar da atamfofi, shaddoji da kamfalu. Khausar ta zamo ita take bani kudin abinci idan zan tafi makaranta a lokacin ina ajin karshe ina shirin fita. Muka zamo ba'a sauke tukunya a gidan Ummana Fuse abincin safe, rana da na dare duk muna dafawa saboda cinikin kamfalar da Khausar take samu. Hankali a kwance nake ta karatu yadda ya kamata dan haka na ci jarabawa sosai fiye da tunanin mutane. Daga cikin darussa guda tara da muke yi na ci A1 shida, B1 biyu C1, kuma sciences na yi. Koda na fadawa Uncle Hamza abunda na ci a jarabawa sai ya yi farin ciki ya kuma yi min alkawari zai nemar min makaranta a jami'a mai kyau a Ingila sai in karanci Medicine ko Engineering. Farin ciki ya lullubemu, Ummana Fuse ta ce nayi shuru da bakina kada na fadawa *yan uba da sauran *yan uwa masu hassada sai dai kawai suji tafiya. Na ja bakina na yi shuru inajin *yan hassada kuwa suna ta surutai wai mu ne tsintacciyar mage an ci jarabawa an rasa kudin shiga jami'a. Da aka fada maka Hamza zai iya biya maka kudin jami'a ne? Wanan me shegiyar rowar? Ummana Fuse ta ce in yi musu shuru kada in ce komai. Allah cikin ikonSa shekara na zagayowa Uncle Hamza ya yi waya ya ce in hada takarduna in kai gidan abokinsa zai kai masa Ingila, ina rawar jiki na hada na kaiwa abokin. Bayan tafiyar abokinsa da watanni uku sai ya turo min da komai na tafiya kamar tikiti da biza aka tabbatar min na sami shiga jami'ar Cambridge da take cikin Ingila. Na yi sallama da kakata da kanwata ina kuka suna kuka, makiya suka sha takaici a lokacin da na zaga dangi ina mai musu sallama tafiya ta tabbata. Na tafi Ingila karatu cikin kwanciyar hankali, sai dai matsalolin da ba'a rasa ba daga matarsa da *ya*yansa ba sa so na, saboda tsabar ba su saba ganin bako a gidansu bakar fata ba, da kuma yahudancin da yake cikin ransu. Ko kudi ko kaya zai ba ni, sai dai da dubara kuma a boye, saboda matar sai ta hana shi baro-baro a gabana. Kun san Nasara bai iya boye-boye ba da gulma, gar da gar suke abubuwansu. Ban damu ba saboda na saba da irin wadannan tsangame-tsangwame a baya. Karatuna na saka a gaba don shi zau fishshe ni. Da zaman ya gagara ma sai na shawarci Uncle Hamza nace ina so na koma zama a cikin makaranta a rukunin gidajen dalibai da yake cikin makaranta. Ina so mu zauna gida daya da abokina Usman shima dan Accra ne. Uncle Hamza ya yarda ya biyamin duk abin da na bukata na kudin haya, kayan abinci da dai sauransu. Lokacin wayar hannu ba ta wadata ba sosai a Accra, sai dai na kira wani gida a kusa da gidan su Ummana Fuse na ce a kira su, bayan mintuna ashirin sai na sake kira mu yi magana da su. Kullum suna cemin ba su da wata matsala kasancewar aikin rinin kamfala ya karbi Khausar, an fara saninta ana ta kawo mata aiki, suna samun na cefane. Amma duk da haka idan na sami mai tafiya ko kuma transfer ta banki sai na kundige rabin kudin da Uncle Hamza ya ke ba ni na tura musu, don su sake jin dadin rayuwarsu. Kasancewar akwai ayyukan yi a England da na gane gari, sai na dinga fita ina yin ayyuka irin na awannin nan a biya ni. Kamar ba da abinci a hotel, goge-goge da share-share a ofisoshi, duk ranar da ba ni da darasi. Alhamdulillahi na samu kudi mai yawa a wannan harkar, saboda na iya aikin karfi, kuma ba ni da girman kai. Sabanin abokaina *ya*yan masu hali, wadanda iyayensu ne suke turo su karatu sun kuma jifgo musu dukiya mai yawa saboda gata, kada ma *yan Nigeria su ji labari sun fi kowa irin wannan wadaka da kudi. Ina turawa su Khausar kudi masu yawa da kayan sakawa daga English wears har atamfofin super Hollanda yayin da mahassada suka shiga aikinsu na hassada da yada labarun karya. Wai sai dai idan ba karatu na je ba, damfara nake ina turo musu da kaya da kudi haka. Idan su Khausar suka fada min sai na yi dariya na ce su rabu da su, kuma su toshe kunnuwansu ko sun ji su ki ji. Abinka da Babba sai Ummana Fuse ta shiga yimin nasihohi tana cewa, kada na yarda na biyewa abokan banza na fada harkar banza. Kada na sake na yi sata ko damfara dan na turo musu da kudi, su rinin kamfalar nan ma ya ishe su, su ci abinci. Na yi mata rantsuwa bana banayin wannan harkar inda ina yi da Uncle Hamza ya sani tuntuni, kuma da zai sanar da ita koma ya koro ni gida. Kuma can kasa ce mai tsaro kana yi za,a kama ka, na'urorin daukar hotuna a ko'ina. Khausar daman a bayana ta ke, tasan halina don haka ba ta damu da sharci-fadin mutane ba, ita ce mai hana Ummana Fuse zato. A waya suke fara fada min cewar, Khausar ta sami saurayi yana so ya aure ta, sunansa Isah. A Accra yake zaune yana sana'ar siyar da gwanjo, amma dan asalin garin Kita ne dan Yaren Aibe. Umaimah ta ce ''duk kasar Ghana ne? Ya ce ''Ai garin Kita nan ne ma asalin Ghana dan dai yanzu garin duk babu mutane sosai ruwa ya cinye su, saboda suna da katon teku wanda ya ke fita har kasashen turawa. Akwai gidajen tarihi da suke wajen idan ku ka je zaku ga jinin bayin da turawa suka kashe, idan bayin suka yi gardama ko rashin lafiya, ko idan suka yiwa mace baiwa ciki sai su harbe ta anan dan basa son su haihu da su. Ban bawa Khausar goyon baya ba, don ban cika son auren Accra ba, dama zata sami dan Kano mana ta aura ta dawo gida don ni har yanzu ban fitar da ran zan kaura gida ba, don tarbiyar Ghana ba ta yi min ba, ga su da nuna kabilanci. Da na ji maganar aure tana kara kankama sai na fito baro-baro na fada musu ra'ayina cewar, bana so a yi auren nan, na fi so ta auri Bakano. Haba sai Ummana na Fuse ta hauni da fada, ta zage ni tas har da koke-koke a waya, wai dama har yanzu ba na kaunarsu, su dangin mahaifina, na fi son dangin mahaifiyata duk wahalar nan da ta yi da mu dama niyyarmu mu gudu mu bar ta wata rana? Kun san tsoho da rikicewa, yanzu ya lauya maka magna. Hankalina ya tashi na shiga lallashi ina gyara lafazina. Da kyar dai ma samu ta huce da ni, don da ta daina zuwa ta dauki wayar ma idan na bugo sai dai Khausar ta zo. Daga baya ma na hada musu wayar a gidan (land line) suka huta zirga-zirgar daukar waya gidan mutane kullum.... ''Ya yi dariya. Umaimah ta yi murmushi ta girgiza kai, ta ce ''Kai! Me yasa ba ka so kamwarka ta yi aure alhali ta yi shekara ashirin koma fiye da haka tunda ba karatu take yi ba ai gara auren. Abdul-Sabur ya gyara zama ya yi dariya, ya ce ''Haka ne, na gode da wannan tambaya taki. Ina da dalilaina masu yawa. Kinga macen Ghana dole ta fita nema don idan ma baki da sana'a ko aiki babu mai auranki. Na tabbata yaron da yake son Khausar ya zo wajenta ne a dalilin ya ga tana da sana'a, tana samun kudi, kuma ga ni Yayanta a turai, ina turo musu da dukiya. Da ace ba ta da komai ba ma zai zo ba. Haka idan an yi auren raba dai-dai za a dinga yi ta yi wani aikin ciyarwar, ya yi wani shima. A lokacin ne ma zata fi zagewa tana yin rini tun karfi don takai masa wadataccen kudi. Na biyu, tarbiyar yaran da zata haifa ba zata yi kyau ba, saboda al'adunsu kamar babu musulunci a ciki. Na uku, bana so na tafi na bar ta ita kadai a kasar, na santa da mako, tuni zata gigice ta rame da koke-koke don ba ni da ra'ayin sake zama a Accra kuma, idan bana turai to ina Nigeria, Abuja da Kano.'' Faduwa ta yi murmushi ta ce, ''Ashe ba ka auri *yar Ghana ba?'' Ya tuntsire da dariya, ya girgiza kai, ya ce, ''Ban auri *yar Ghana ba. Ina can suka fadamin an saka rana, don haka suna bukatar kudi masu yawa saboda shagalin bikin da ake a can ya baci. Bidi'a ce zallah. Umaimah ta ce, ''Ai daman ko a Nigeria al'adar auren Hausawa gidan mata suna shan wuya, bayan kayan daki da gara. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, can mata ba sa kai kayan gara, duk miji ne zai yi. A inda suke kashe kudi a wajen shagalin biki ne sai a fi sati mata suna daukar girki ba na wasa ba, kuma mai dadi da nama cusu-cusu. A biki dole ne ka yanka sa ko shanu, rago ko raguna, bayan kaji. Saboda bikin ne mata suke hada kungiya (meeting) suna taro duk karshen wata suna tara kudi ana ajiyewa don idan biki ya kama wata a cikin kudin da aka tara za a siya mata abubuwa don ta rage nauyi. Suna fara aiki ranar juma'a da daddare a yi kunshi nan ma taro ne za a yi mata tuli a kan kujeru a kofar gida, abinci kala-kala, iyayen amarya dole su sayiwa *yarsu leshi mai tsadar gaske ta saka a wannan rana. Washe gari asabar sai a yi Ashadi shima amarya sai ta canza kaya tsadaddu kamar kala uku ko biyar. Duk sai da na kundige wadannan kudade na aiko musu suka sha shagalinsu, na bita da addu'ar fatan fatan alkhairi. Da na kammala karatun degree dina da kaina na biya na wuce na yi masters dina. A lokacin na mallaki gidan haya babba ni kadai, da motar hawa. Sai dai naje ofishin Uncle Hamza na gaishe shi a can dan kiyayyara tayi tsamari tsakanina da iyalansa har babban dansa ya ja min kunne kada in sake zuwa gidansu, idan ya sake ganina sai ya harbe ni. Don haka sai na fadawa Uncle Hamza sai dai na dinga ganinsa a ofis ko kan titi. To yawanci ma sai ya zo ya same ni a makaranta ko a gidana mu yo maganar da zamuyi, don so yake idan na gama karatu ya gutsuro wasu daga cikin dukiyarsa ya fara aikena Indonesia da Swizerland ina saro masa shaddoji, leshina na mata da huluna sana'arsa ke nan. Amma ya lura *ya*yansa da matarsa suna kacaccala masa dukiya sai ya je kasuwa ya tarar sun je sun karbe ciniki bada izininsa ba. Haka kuwa akayi, ina gama karatu ya hadani da wani Ishaya babban yaronsa dan Nigeria ne shi ma, muka je kasashe uku ya nunamin wuraren sa suke saro kaya. MAKWABTAKA 16 Zuwana cikin shagon sai na ruguza cutar da suke yi masa wajen lissafin bogi, na saka musu ido don ba su isa su yi min wayo ba, na fi su ilimi. Sabanin Uncle Hamza wanda bai yi makaranta ba. Bakin jini na yi sosai a wajen ma'aikatan dan suna ganin ba karamin tauye musu rayuwa nayi ba, sun daina samun kudin cuta. Da akwai yadda zasu yi da sun kawar da ni daga doron kasa. Ganin wannan riba mai yawa da Uncle Hamza ya yi sai ya sake yarjewa da ni ya fi so na kasance tare da dukiyarsa. Ya sa na zo muka zauna muka tattauna abin da za a yi kowa ya ji dadi tsakanin ni da shi. Ya ce, kada na damu da sai na yi aiki, duk tafiya daya idan aka saro kaya sai a bari a siyar sannan a raba gida hudu. Shi kashi biyu, ma'aikatan kashi daya, ni kashi daya. Na yi murna da jin haka, don kudin da zan dinga samu ya fi albashina na watanni shida ma. Na amince na yi godiya muka ci gaba da yin haka. Sai a lokacin da na karbi ribata ta farko na shirya na taho Accra ganin gida, shekaruna shidda rabona da gida. Na ga Ummana Fuse ta kara tsufa yayin da Khausar ta yamutse saboda wahala, ba ta jin dadin auren, azzalumin miji ta samu yana yi mata wayo tana nemowa yana karbewa. Duk sun yi mamaki da ganina, na girma na yi kyau, na yi fari kal, ga wata kasumba da na tara. Ina isowa na tari sabuwar motar da na auno tun ban zoba na turo, a ita na ke yawo gidan *yan uwa da abokai. Sai kallo na ake ana sha'awar ni'imar da Allah Ya yi min a rayuwa, mahassada suna ta surutai, babu abin da ba su ce ba. Sane nake yi, damfara, yankan aljihu da dai sauransu haka suke cewa. Ban damu ba, don ko sauraron su bana yi. Uncle Hamza ya yi bakin jini a wajen dangi makusantansa, wadanda suka fini kusanci da shi. Wai har ya dauko bare ya saka shi a harkar arziki su bai dauki *ya*yansu ba. Nan fa kowacce ta fara buga masa waya tana balokoko da magiya ita ma ya turo ya kai danta England. Dogon turanci yake musu, bayanai ne kawai da lallashi, a cikin bayanan nasa kuwa ba zai yiwu ba ne kawai su yi hakuri. Kaina da kafata na yi ta taimakon dangi mabukata, suna ta godiya, masu kushewa suna karba sai dai idan na tafi su zaga. Na canja fasalin gidan kakata, na canjawa Kanwata ita ma duk abubuwan da ta ke da bukata. Na kara mata jari, na kuma bata hakuri gami da yi mata nasihohi akan ta yi hakuri ta ci gaba da biyayyar aure. Na kira mijinta muka gaisa, na yi masa kyauta mai tsoka, sannan na yi masa wa'azi cikin siyasa akan ya sani mace kiwo ce Allah Ya ba shi, Allah zai tambaye shi yadda ya yi da ababan kiwon nan da aka ba shi a ranar tsayuwa. Ya fahimci abin da nake nufi, shi ne ya rage sosai zaluncin da yake yi mata, daman dai ba su taba haihuwa ba, saukinta kenan. Na koma England harka ta sake budewa, na samu Uncle Hamza yana samu, ina murna yana murna haka muka yi da bawan Allah nan har tsawon shekaru biyar. A lokacin ne hassadar iyalansa ta fito baro-baro *ya*yansa suka zo har ofishina suka cakume ni suka fito da ni, wai na bar musu dukiyar mahaifinsu ya tsufa yanzu zasu ci gaba da kula da ita. Babu yadda zai yi a gabansa na harhada na fice yana hawaye, ina hawaye. Ya san kawai rusa shi zasu yi, tunda duk *yan shaye-shaye ne su da uwarsu. Uncle Hamza ya koma gida ya zauna ya zuba musu ido sai abin da suka kawo masa yake karba, sai lokacin ya ga illar auren Ahlul-kitabi, nasara asarar duniya. Oho, sunyi ta banza don ni duk ribata da ake ba ni suna boye a banki, kuma na riga na san hanya nasan mutanen kamfanin su ma sun san ni. Da jarin na je na kawo kayan na canja gari na bude shagona a can. A hankali aka gane ni, nima na sami masu siya. A hankali na sami ma'aikata da teloli. Amma kafin na fara sai da na je na shawarci Uncle Hamza ya ce ya ba ni izini na yi, ya yi min fatan alkhairi. Sai a lokacin na sami nutsuwa nake zuwa Accra akai-kai, wani zuwa dana yi na iske auren Khausar dai ya ki yiwuwa, sai da suka rabu ta dawo gida suka zauna da Ummana Fuse. Na ma fi jin dadi da aka yi haka, ga shi ba haihuwa suke yi ba, sai rigima kullum, har dukanta yake yi. Na ba ta shawara ta koma makaranta ta yi yaki da jahilci, ta kudi ce ana koyar da kowanne darasi da Turanci tsabarsa kuma ka sami kwali mai daraja kamar kowacce sakandire. Ta yarda ta shiga ta fara daga aji daya na sakandire, don ta iya aikin firamare. Ina can dai a Ingila, na sami labarin daga Khausar cewar ta yi hutun makaranta, sai na yi musu biza ita da Ummana Fuse, na turo musu kudi suka sayi tikiti suka zo suka same ni a Ingila. Wata guda suka shafe tare da ni ina ta yawatawa da su, duk wani wajen shakatawa sai da na kaisu. Kwanakin su biyu a gidan Uncle Hamza, sannan suka dawo gidana. To a wannan zuwanne abokina Shamsu dan Nigeria garinsu Minna, Niger State banufe ne. Ya ga Khausar kanwata ya ce yana sonta, shima tare muka yi karatu yana aiki a Abuja, amma yana zuwa Ingila akaiakai. Sai na ce, a,a ba zai yuwuba, shi da ya ke saurayi bai yi auren fari ba, ita kuwa bazawara ce duk da ma ba ta taba haihuwa ba. Ya girme ni nesa ba kusa ba, ba yaro ba ne, don alokacin ya yi shekara arba'in. Ita kuwa ba ta wuce talatin ba. Ya ce, shi dai yana sonta, zai aureta kuma. Sai na ga ita ma ta karkata da sonsa. Ban hana ta ba, na fi kowa farin ciki idan har za a yi auren saboda nasan Shamsu na san halinsa, yana da kirki ga rikom addini. Uwa-uba dan Nigeria ne a can zai zauna da ita, wanda shi ne ra'ayina daman tuntuni. Da ta ji na ce Nigeria zamu wuce daga nan ni da su Khausar, sai ya yi murna don kawai za'ayi ta, ta kare, ma,ana idan ya biyo mu Nigeria sai ya kai ta iyayensa su ganta a tsayar da maganar aure ko ma a daura kawai tunda gani ga Ummana Fuse, ga dangin mu a can. Mun riga shi iso Nigeria san nan ya biyo mu daga baya. A waya ya sanar da ni ya iso Mina, na ba shi adireshin inda zai same mu. A gwarzo muka sauka, sun sha mamaki da ganinmu, don sun zata ma ba ma raye. Tun sanda Baba Mukhtar ya kai mu ya dawo babu wanda yasan halin da muke ciki. Sai muka zama tamkar taurari abin haskawa a kauyen nan. Aka dinga tururuwar zuwa ganin mu ana kawo mana abinci kala-kala. Kannena Hassana da Usaina su na fi damuwa da na gani, Alhamdulillah suna cikin rayuwar rufin asiri kasancewar mahaifinsu tsayayye ne me neman na kansa ne. Na siya musu kayan sakawa da kayan kwalliya kai ka ce lefe ne suma aka hada musu. Ummana Fuse ta yi mamaki da ganin yadda dangin mahaifiyarmu ke da yawa kuma akwai masu rufin asiri. Har ta bude baki ta yar musu da magana, ta ce, ''ashe kuna son su amma ku ka tankada keyarsu Ghana? Sai kuka yi wuki-wuki, mu ma kunya ta rufe mu, ni da Khausar. Da Shamsuddin ya ta shi zuwa, sai ya taho tare da danginsa maza hade da kudin aurensu, har sadaki. Sai muka karba aka tsayar da maganar aure. Bayan wata guda har ya hada lefe mata suka kawo, aka daura uare gami da *yar kwarya-kwaryar liyafa. Muka rakata har katafaren gidanta na Mina. Bayan danginsa sun gan mu sai muka dungumo Accra tare da su ango da amarya nan ma aka gabatar da angon Khausar da dangin Babanmu. Na sha zagi dai ba adadi saboda na kai Nigeria dangin uwata sun daura mata aure. Ban damu da surutansu ba saboda na san ni da kakata ne kadai muka raine ta babu wanda ya san cinta da shanta a cikinsu. Khausar ta yiwa Accra sallama ta biyo mijinta mai sonta zuwa Abuja, a nan suke da zama din-din-din. Yanzu haka *ya*yansu uku, haihuwarta biyu na farkon tagwayene, mace da namiji Habiba da Abdul-Sabur, sai na biyu mace ce aka saka mata sunan Ummana Fuse, wato Usaina. Nima a Gwarzo na sayi fili na yi mana katafaren gini inda idan muka je mu dinga sauka a unguwar iyayen Mahaifiyata. A Kano kuma a kusa da dangin Malam Barau na yi gini don a nan na saba duk da ya rasu ina taimakawa iyalansa a koda yaushe. WANNAN SHI NE LABARINA. Umaimah da Faduwa har lumshe ido suke yi saboda dadin labarin da Abdul-Sabur yake ba su sun fi jin dadin labarin da aka zo gurin ci gaban rayuwarsa sai suka ji tamkar almara saboda komai yana tafiya yadda ya kamata. Umaimah ta yi murmushi ta dubi Abdul-Sabur ta ce, 'To a ina ka yi karatun kur'ani, ka sami ilimin addini haka? Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce, 'Duk inda na je kuma ko me nake yi ina samun makarantar islamiyya na shiga. Kinga da farko daman na fada muku da girmana na shiga makarantar boko kinga tun tashina a makarantar allo nake, anan na koyi baki na iya rubutu a allo na da kaina. Sai da nayi nisa sosai muka tashi daga Kano muka koma Gwarzo a can ma na shiga allo ko sanda na shiga sakandire ta kwana idan anyi hutu ina ci gaba da zuwa. Da muka dawo Ghana Ummana Fuse ta saka mu a islamiyya a nan na koyi Fikhu da Hadisai. Da na dawo Ingila duk ranar asabar da lahadi muna zuwa gidan wani Balarabe mutumin Syria ne yana koyar da mu Kur'ani da Hadidai. Da na fara zuwa Indonesia sarinn kaya ina zuwa wajen malamai daban-daban ina neman ilimi, ina samun karuwa da tasu baiwar. Na yi saukar kur'ani mai tsarki fiye da sau goma, yanzu haka na haddace shi ina sake maimaitawa. Umaimah da Faduwa suka jinjina kai, Faduwa ta ce kaji dadi, ni ma dai na yi sauka tun ina yarinya kafin na gama sakandire, daga baya boko ya hana ni ci gaba. Amma ina da burin ci gaba da karatun addini a kasar nan idan na nutsu na ga akwai makarantun matan aure na islamiyya. Abdul-Sabur ya ce, ''Yana da kyau a nemi ilimin gaskiya. Ke fa Umaimah ba kya sha'awar shiga islamiyya? Ta yi murmushi, ta ce, ''Ina da niyya idan Allah Ya so zan shiga nima. ''Kin yi nisa ne a kur'ani? Abdul-Sabur ya tambaye ta cike da zumudi. Ta yi dariya ta gyada kai ta ce, ''Alhamdulillah, ni ma dai na sauke kur'ani tun ina matashiyam bayan na girma na ci gaba da karatun har na fara hadda. Abdul-sabur ya ji dadi da jin haka, da ya zaci Umaimah jahila ce da yaga yadda take danne hakkin MAKWABTAKA. Ya yi murmushi ya ce, ''Alhamdulillah, mu dukka mu godewa Allah da Ya ba mu ilimin saninSa. Allah Ya ba mu ikon yin amfani da shi. Su dukka suka ce ''Amin. Faduwa ta gyara zama ta ce, ''Abdul-Sabur ba ka gama labarinka ba. Ban ji ka yi maganar matarka da *ya*yanka ba. *Yar ina ka aura, Ghana, Najeria. Ingila ko *yar Indonesia? Abdul-Sabur ya kwashe da dariya, ya ce, ''Kai Faduwa ta yaya za ki jero min wadannan kasashe Ingila da Indonesia daga zuwa ci-rani sai na hau yin aure? Ai ba zan yi wannan kuskuren ba, na auren matar da ta ke wata kasa wacce ba kasata ba. Ashe zan maimaita kuskuren da iyayena suka tafka, suka haife mu muka shiga garari a duniya ba tare da mun san dangin da zamu bi ba, duk a rarrabe?. Faduwa ta ce, ''Yar Accra ko Kano ka aura? Ya sake yin dariya ya girgiza kai, ya ce,, ''Babu ko daya wallahi. Faduwa ta harare shi, ta ce, ''Ban fahimce ka ba kana nufin ba ka taba yin aure ba ne? Ko dai kun rabu ko ta mutu? Umaimah ta dube shi ita ma cike da rashin yarda ta ce, ''Me kake so ka ce mana, ba ka da mata? Matar da na ganka tare fa a Saudia kuna dawafi ka dafa ta? Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Af har ma kin taba ganinsu ko? Da har zai boye mana. Ai na san kana da mata, tunda baka dadewa sai ka je gida ka gan ta sannan ka dawo. *Ya*yanka nawa? Har yanzu Abdul-Sabur dariya yake yi musu ya kasa amsa jerin tambayoyin da suke jeho masa. Can ya yi ajitar zuciya ya gyara zama ya dube su, ya ce, ''Babu maganar boye-boye a tsakaninmu, ku kannena ne tamkar na jinina mun zama daya. Ban yi aure ba har yanzu balle na sami *ya*ya, ga shi kuwa wannan shekarar zan cika shekaru arba'in a duniya. Na zama tuzuru nima kamar Faduwa. Su dukka ukun suka kyalkyale da dariya. Faduwa ta ce, ''Kai ai namiji ne, kai zaka nemi aure kuma duk irin wacce ka nema zata so ka saboda kana da kudi, kyau da ilimi. Watakila dai zabe kake yi har yanzu kana ruwan ido. Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya ya ce, ''Haka ne, amma dai yadda kike tunani ba haka nake ba. Ni dai kawai ba ni da ra'ayin auren ne saboda a tsorace nake da matan, kuma mata suna sona su yi ta bibiyata ina zukewa. Tunda nake a rayuwata ma sau daya na taba yin budurwa wacce na ji ina sonta har na taka gidansu da sunan hira, sunanta Aminat a Ingila muka hadu, asalinta *yar Bauci ce. Ta so ni sosai, ta so na aure ta na ki saboda wasu dalilaina. Yanzu ta yi aurenta har ta hayayyafa a garin Manchester gidanta ya ke. Yanzu dai a takaice Allah ne bai kawo lokacin yin auren ba, da zarar ya zo sai ku ga Allah Ya hada ni da matar, sai mu yi aure mu hayayyafa. Ko ba haka bane *yan mata? Umaimah wannan matar da kika ganni tare da ita a Saudia ba wata ba ce, kanwata ce Khausar. Tana son zuwa Umra duk shekara mijinta kuma ba shi da lokaci koda yaushe to da naje Najeriya a cikin hutu sai ta ce na yi mata namijin biza mu je muyi umarar kwana biyar, shi ne kika gan mu tare. Ita ma haka ta tutsiye ni da tamabaya wai ina na sanki, ko dai ke budurwata ce. Sai na fada mata ke makwabciyata ca a Malaysia, da farko ta ki yarda amma da nayi mata rantsuwa sai ta yarda daga baya, don dai ta san bana yin budurwa. Su dukka ukun suka yi dariya a lokaci guda. Abdul-Sabur ya dubi Faduwa ya juya ya dubi Umaimah, ya ce, ''To *yanmata kunji tarihin AbdulSabur daga farko har tsakiya, Allah ne kadai Ya san karshen abin da zai faru. Idan akwai mai tambaya ta tambaye ni akan abin da ba ta gane ba, ko wanda na manta ban fada ba. Suka yi dariya, Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Babu tambaya, ni dai a nawa bangaren. Allah Ya jikan wadanda suka rasu, mu kuma Allah Ya kyautata namu zuwan. Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Amin, na gode kanwata. Faduwa ta ce, ''Allah Sarki Abdul abokina, dan uwana, maraya kuma tuzuru. Allah Ya jikan iyayenmu, Ya bamu abokan zama na gari. Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya ya ce, ''Faduwa kin cika abin dariya, koda yake addu'a ce mai kyau. Amin Ya Rabbu''. Abdul-Sabur ya juya ya dubi Umaimah wacce ta yunkura tana shirin tashi ta tafi. Ya ce, ''Kin ji tarihinmu, yanzu kin san mu, kin san asalinmu. Ko zamu iya saninki ke ma?. Ta mike tsaye gaba daya tana murmushi, ta ce, ''Eh, za ku san ni, amma sai nan gaba. Yanzu zan tafi gida, ina da *yan aikace-aikacen da zan yi. Ai muna tare, komai daren dadewa tunda kun hana ni tashi daga gidan nan, za ku san ni. Faduwa ta jawo hannun Umaimah ta zaunar da ita, ta ce, ''Babu inda zaki je, yau a nan zamu yini har la'asar. Sai kin bamu tarihinki kamar yadda kika ji namu.'' Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce ''A,a kada ki takuta mata Faduwa, ki bari a hankali wata rana sai ta bamu. Faduwa ta ce, ''Wannan yarinyar, lallai ba ka san halinta ba, yanzu idan ta shige gida ba zamu kara ganinta ba, ko mun buga ba zata bude ba''. Suka tuntsire da dariya su dukka, Umamah ta ce, ''Ai da ne, yanzu ba haka ba ne, za ku ganni mana. Faduwa ta ce, ''Ni dai ban yarda ba, yanzu nake so a bani labari na ji. Umaimah ta ce, ''To zan bayar, amma ki bari na je gida na yi sallar walha tukunna, sai na dawo. Kina ganin har goma da rabi ta yi''. Faduwa ta ce, ''To muje na kai ki ban daki sai ki yi sallar a nan, ni fa har yanzu tsoronki nake''. Umaimah ta yi murmushi kawai ba ta ce komai ba, tana biye da ita har katafaren dakinta a inda kayataccen ban dakinta yake ciki. Gidajen iri daya ne har kayan ciki, yadda na Umaimah yake haka sak na Faduwa ma. Gida ne mai dauke da dakuna biyu babban daki da bandakinsa a ciki, sai wani karamin daki, bandakin kuma a waje (coridor). Kowanne daki da gado, madubi da durowar kaya da labulaye na alfarma kalar kore (lemon green), sai katafaren falo mai dauke da dinning area duk an zuba kujeru da dinnin table da labulaye koraye. Kicin ma babu abin da ba'a saka ba, kama daga injin wanki, gas cooker, firij da duk wani abun da ake bukata a kiicin kamar tukwane, farantai, cokula. Kofuna da dai sauransu. Duk kasan gidan tiles ne launin kore da fari, haka kofofin gidan farare ne sun kayata. Faduwa sarkin kwalliya, ta kayata bandakinta da kyalkyali, komai ruwan hoda ne (pinc color). Umaimah ta yi sha'awar bandakin nan tas-tas kamar mutum ya kwanta ya yi bacci. Da ta idar da alwallar sai ta fito ta iske Faduwa har ta yi mata shimfida da sallaya da tsaftataccen hijabi. Umaimah ta yi godiya yayin da ta shiga saka hijabi ta fara haramar yin sallah. Faduwa ta fito daga daki ta iske Abdul-Sabur ya fito daga daya bandakin ya dauro alwala shi ma. Ta yi sauri ta shimfida masa abin sallah a falo ya tayar da ikama. Faduwa ta yi murmushi ta ce, ''Wato ku dukka sallar walha ku ke yi ashe, ni kadai ce bana yi? Gaskiya da sake, na daina yarda kuyi min wayo, ni ma zan yi wa kaina fada na fara yi. Tana gama magana ita kadai, har ta shiga kicin a inda ta bude firij ta dauko dankwaleliyar kaza a gidan kankara ta shiga wankewa, ta bankare ta ta zuba mata kayan hadi, yayin da ta turmutsa ta a cikin oven don gasawa. Kan ka ce kwabo kamshi mai dadi ya gauraye gidan, ta fara tururi. Yayin da ta dora shinkafa fara amma fa irin dahuwarsu ta *yan Egypt. Farar shinkafa ce ake dafawa kafin ta dahu sai a saka gishiri, maggi, koren wake (green beans da peans), karas sannan a yayyafa dan man kuli. Ba sai an yi miya ba, sai a ci hade da gashasshiyar kaza. Kafin su idar su hallara a falo har Faduwa ta fara jera musu abubuwa akan dinnin table. Kamar ruwa, lemon (juice) ayaba, lemo, abarba, kayan shayi da dai saauransu. ''Abincin mai zamu ci kuma yanzu bayan mun yi karin kumallo? Umaimah ta tambayi Faduwa a lokacin da ta ke duban ta tana dariya. Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Abincin hantsi zaku ci. Na ga duk ba mu ci abincin ba dazu saboda tashin hankalin labarina, duk muna kuka, ruwan shayi kadai muka kukkurba. Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ruwan shayi ma ai abinci ne, ni ba don ku bama da ba zan karya ba, don ni bana yin karin kumallo ma kwata-kwata. Ai shi yasa kike ta sake dunkulewa kina yin kiba kin cika ci. Suka kwashe da dariya su dukka, Faduwa ta ce ''Au tsiya kakemin a gaban kanwata? To zan rama''. Umaimah ta ce, ''Mu je kicin din na taya ki aiki, ko nima na koyi irin abincinku na Larabawa. Na ji kamshi sai fitowa yake yi. Faduwa ta wuce gaba, Umaimah na biye da ita har kicin a inda Faduwa ta shiga yi mata bayanin abincin da ta ke dafawa da yadda ake yi. Tabbas Umaimah ta karu don ba ta taba sanin irin wannan launin girkin ba, don ba irin namu ba ne na Hausawa. Suka karasa yi tare suka zo suka jere akan dinnin table, kamshi ne ke tashi tururu. Da suka gama shiryawa sai suka gayyaci Dan Aunty zuwa kan tebur. Lolx.. Kowa ya maida yawun sa ni kadai aka gayyata banda gayyar sodi. Gani ga... Alhamdulillahi. En uwa ina godia a gareku na nuna kulawa da soyayya da kuka taimaka mana da Addu'oi daga bakunan ku masu Albarka. Alhamdulillahi. Masu jiki da sauki sosai dan daya yayan nawa an sallame shi saura kanin namu. Allah yasaka muku da Alkhair. Ina mai kara godia a gare ku baki daya. Allah yabar xumunci. MAKWABTAKA 17 Da suka gama shiryawa sai suka gayyaci Abdul-Sabur zuwa kan tebur. Tun kafin ya karaso ya hango abincin gwanin ban sha'awa, kai ka ce a hadadden hotel suke. Gwanin sha'awa idan ka kalla, haka kamshinsa abin so ne balle ka kai baki ka ji dandanonsa. Cokula (forks da spoons) da faranti (plates) aka ajiyewa kowannensu a gabansa, ga kufuna da robobin lemuna (juice) kala-kala, shinkafa da kaza suna manyan farantai. Faduwa ta shiga daddatsa dankwaleliyar kazar nan gashasshiya gunduwa-gunduwa. Kowa ya shiga zuba daidai cikinsa da kansa. Yayin da sanyin A.C ya fara ratsa hudojin jikinsu, sanyin lemon ya dinga kwaranya a cikin hanjin jikinsu. Sannan dadin abincin ya daki harshensu zuwa tumbinsu. Nan da nan kowannansu ya tsinci kansa yana cikin farin ciki da annashuwa a fuskokinsu. Abdul-Sabur ya hadiye lomar abincin da yake tauna a bakinsa, ya kora da lemo mai sanyi (apple juice) ya dubi Umaimah ya yi murmushi. Ya ce ''Muna sauraronki Umaimah, layi ya zo kanki''. Faduwa ma ta kura mata ido kallo ko kyaftawa ba ta yi, daga dukkan alamu ita ma ta kagu ta ji abinda Umaimah zata fada. Cikin jin kunya Umaimah ta yi murmushi, ta sunkuyar da kai kasa. Can ta dago ta dube su daya bayan daya, sai ta yi fari da ido. Ta ce, ''Yau dai kun rantse sai kunji labarina ko? To babu damuwa ku bude kunnuwanku da kyau ku ji tarihina mai taken MAKWABTAKA''. Ai kuwa sai taga suna gyara zama, gami da sake miko hankalinsu gaba daya a kanta. LABARIN UMAIMAH. ''Sunana Umaimah Muhammad Bello, muna kiran mahaifinmu da suna Baffa, mahaifiyata kuwa sunanta Mariya ita ma muna kiranta da Yafindo. Iyayena dukka biyun fulani ne, sun fito daga riga daya, sunan rigarmu Dugge a karkashin karamar hukumar Dukku jahar Gombe, a kasar Nigeria. Mahaifiyata ita ce mace ta uku a wajen Baffa Bello, ta same shi yana da mata biyu, Nene da Inna, kusan su dukkansu sun haife ta ma. Sai dai ba su taba haihuwa ba a gidan, sai a kanta ya fara samun haihuwa. Aka haifi Yayata mai suna Nasiba. Nasiba ta girme min da shekaru biyar, sannan aka haife ni, bayan shekaru biyu aka haifi kanina Sabitu. Rayuwa ce ta kauye daga kiwo, sai noma, surfe da casa, shi kenan sana'armu. A gidan kasa dakin yumbu da rufin ciyawa, sai katangar zana, ba mu da komai bayan wannan. Yaren Fulatanci kadai na tashi na ji ana yi a gidanmu, don yaren Hausa ma sai daga baya na koya a birni. Muna zuwa makarantar allo kadai ita ma makarantar da fulatanci muke karatun, bayan Fatiha babu wani abun da malaman suka iya. Ita kadai na san na koya, duk sauran karatu rawawu fulani ne shirme ne kawai, don haka ilimi ya yi mana karanci a Dugge. Babu abin da *yan mata da yara kanana suke yi mata da maza sai wake a dandali da yamma. Ko kuma a yi wasan shadi idan bukunkuna sun taso, mu taru muna kallo, shi ne babban nishadin *yan kauyen. Abdul-Sabur da Faduwa har lumshe ido suke yi saboda zazzakar muryar Umaimah da daddadan labarinta. Har yanzu harshenta bai warware daga illar lauyewar da Fulatanci ya yi masa ba. Kana jin Hausar ka ji ta Fulani, amma sai hakan ya sake dadada yaren suka ji tamkar ba yaren da suka iya ba ne. Hausa ta fi dadi a bakin Umaimah fiye da a bakunansu. Don Abdul-Sabur Hausar *yan Ghana ce fal a bakinsa, yayin da Faduwa kuwa ta larabawa ce wasu kalaman dai sai dai ta soka da Larabci. Umaimah Bello ta yi murmushi, yayin da fararen hakoranta suka sake haskaka, sai kyawunta ya sake bayyana. Ta ci gaba da cewa. ''Ba kamar ni ma ina son wasan gada, raye-raye da wake-wake, da son kallon shadi da garaya. Idan aka zo dandali kika fito kina waka kawayenki sai su yi miki amshi su wake miki saurayinki. Da yake tun muna *yan shekaru biyar-shida kowacce za a lakaba mata saurayin dandali, wasu su zarce har su girma ya kai su ga yin aure, wasu kuwa na yarinta ne su zubar da samartakan a dandali. Sunan saurayina Isma'il, ana kiransa da Ilah makwabcinmu ne, katangar gidanmu daya, daga hannun dama. Ilah ya girme min sosai, sa'an yayata ne Nasiba tare aka yi goyonsu, babu wanda ta hadamu samartaka a dandali, shi ne daman ya ke matukar sona tun ina goye a baya. Duk da ni ban san so ba amma na tashi na budi ido da shi yana yawan kyautatamun a rayuwata. Kullum sai ya siyo min rake, mangwaro, ko ya tatsomin nono da madara kullum ne wannan, saboda mahaifiyarsa tallar nono ta ke yi kasuwa-kasuwa. Mahaifinsa na da garkunan shanu guda biyu suna kiwo. Ilah shi ne karami a gidan, kuma su dukkan yayyansa maza ne guda hudu ba su da *ya mace ko daya a gidan, kuma mahaifiyarsu ita kadai ce mata a gidan, ba ta da kishiya. Muna kallonsu a matsayin masu arzikin Rugarmu. MAKWABTANMU daga hannun hagu kuwa gidan Baffa Modibbo ne, suna da *ya Zahra'u. Zahra'u kawata ce sosai, tare aka yi goyonmu ma, kamar yadda muka tashi muka tarar da Innarta da Yafindona suna kawance mu ma sai muka jone. Kowa yasan tauraruwar nan da ta fi sauran taurari haske, wato 'ZAHRA' da ake cewa matar wata ce saboda a koda yaushe tana kusa da wata. To itama kawata Zahra'u ana kiranta da 'Matawata', babu ma wanda yake kiranta da Zahra'u a garin, kowa da Matawata ya san ta. Ni da Matawata koda yaushe muna tare kanmu daya, farinmu daya, yanayin jikinmu daya, har ma ake cewa mun juye kamarmu daya kamar wasu tagwaye. Allah Ya dora min tsananin sonta kamar yadda nake son Sabitu da Nasiba, komai a bani a gida ko a waje sai na boye na rago mata, haka ita ma ta ke yi. Tun iyayenmu suna dungure mu su yi mana fada har suka fara kashi da mu. Don haka a gidansu ina da kasona, haka itama a gidanmu idan dai Yafindo ce ta yi rabo zata raba da Matawata. Dan haka hasken Zahra ya haskakamin fuskata zuwa zuciyata ita ce kadai wacce na fi so a cikin kawayena na Dugge da kewaye. Ita ma tana da saurayi a dandali mai suna Lawwali, kusan sa'anmu ne ko ya girmemu da kadan. Muna ta ji dadin rayuwarmu a haka, don mu ba mu san akwai wani jin dadin rayuwa ba a duniya wanda ya wuce haka. Duk ranar asabar kasuwar garinmu ta ke ci, mu dunkule *yan nairorinmu nu je mu yi siyayya kamar Aya, Rogo, Gyada, Magarya, Kurna, Kuli-kuli, mu yi kallon Garaya da Shadi ko kalankuwa mu dawo gida. A kasuwar muke haduwa da fulanin wasu garuruwan kusa da garinmu kamar *yan Konare, Nzagala da Shuwe. Mu ma ranar kasuwarsu muna zuwa mu saya mu sayar. Idan muka je rafi dauko ruwa sai mu shiga mu yi ta wanka har sai an turo babba ya koro mu, don ba zamu kawo ruwan da wuri ba, idan tukunya ce ta tuwo aka dora har sai an sauke saboda ba mu kawo ruwan girkin ba. Daman ba mu tashi mun ga ruwan famfo ba balle wutar lantarki, fitilar kwai ce mai lagwani da kalanzir, ko aci-bal-bal fitilar kwalba a zuba kalanzir da tsumma a kyasta ashana ya dinga ci a hankali..... Faduwa ta zazzare ido, ta ce, ''Kuna iya rayuwa babu firij ba fanka?'' Umaimah ta yi dariya, ta ce, ''Ba mu san shi ba balle mu saba da su. Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Wannan ita ce rayuwar *yan Africa ziryan. Ci gaba da labarinki Umaimah don ina jin dadin sauraronki. Da ace Turawa za su ga garinku da sunyi fim da *yan garin don su irin wannan rayuwar suka fi so. Umaimah ta yi murmushin takaici tare da ciza lebenta, ta ce gaba da cewa. ''Muna da Sarkinmu, wato Dagacin garinmu da *yan fadarsa irin su mahaifina dattijan gari, shi ne mai fada a ji, su ne masu yin shari'a idan rigimar gado ta taso, ko rigima akan shanu, ko rigimar manoma da makiyaya da rigingimun cikin gida tsakanin kishiya da kishiya ko mata da mijinta, duk dai wata rigima. Ana tsoron hukuma don haka kowa yake ta kiyayewa ana zaune lafiya sumul babu tashin hankali. Cikin gidanmu rigimar da sauki, saboda mahaifinmu a tsaye yake akan iyalansa dai-dai karfinsa yana ba wa kowacce mata hakkinta. Daman dai bai wuce ranar girkinki ba ya bude rumbu ya auno miki dawa ko Gero kwarya daya, sai ya dora miki da *yar Murtala (naira Ashirin) kudin cefane. A ciki zaki sayi abin kadi ki yi tuwo da miyar kuka ko kubewa ba nama, sai dai ki watsa wake a ciki idan da hali. Daman wannan a aje yake, ke zaki zuba a turmi ki surfa, ki bakace ki dake har sai ya zama gari. Daga baya ne ma injin tahuna na surfe da nika ya shigo garinmu mata suka huta da dakan hannu ko nikan dutse. Idan mun gaji da cin tuwo sai a matso nono a sha da fura, ko kuma a yi mana dawa da wake, dambu, fatefate, ko gero da wake. Ko kuma wasa-wasa. Shinkafa kuwa daman sai ranar sallah kowanne gida ake yin tuwonta, ita din ma dai *yar Hausa. Nama kuwa sai a layya wasu gidajen kalilan ne suke iya yanka Akuya ko Bunsuru. Shanu da Raguna kuwa na kiwo ne ba na ci ba, ban ki ba dai idan Sa ya kasa dole ne a yanka a kai kasuwa a siyar a cika a sayo wani, a ci kadan daga cikin naman. Don haka dukkanmu muke tafiya a kemare saboda babu abincin da zai gina mana jiki. Duk wannan labarin da nake baku dukka shekaruna ba su wuce takwas ba a lokacin. Bikin nadin sarauta ya tashi a Gombe, aka gayyaci Dagatan kauyukan da jama'arsu don su je taya murna hade da duk wani dan wasa da za,a nishandantar da bikin. Dagacinmu ya zazzabi *yan matan garinsa wadanda suka kware da iya wakoki da rawar Fulani za a kai su wajen taron. Nasiba yayata tana daya daga cikin *yanmatan da aka zaba zuwa birni. Ita ce ma zabiyar da zata bada waka,, sauran su yi mata amshi, saboda Allah Ya yi mata kyau da zazzakar murya. Fara ce sol tamkar Balarabiya ga kyawun kirar jiki, don haka samarin kauyen suke ta shan dambe a kanta saboda kowa yana so. Mu kanana ne ba a zabe mu ba, don kada muje mu bata a cikin taro. *Yan mata goma sha biyu aka zaba, *yan samari biyar sune masu kada musu ganga da garaya da kuma yi musu goge. Abin gwanin ban sha'awa aka koyar da su duk irin rawa da wakokin da zasu yi a wajen. Ranar taron aka ba su sababbin atamfofi suka saka iri daya aka zuba su a mota suka tafi, yayin da sha'awarsu ta lullube duk wanda ba a tafi da su ba. Na sawa a raina zan dage da iya rawa da rera waka kafin na girma don ni ma a tafi da ni nan gaba. Ilah saurayina ya ci sa'a an tafi da shi, ya yi min alkawari zai siyo min *yar tsana da kifi a birni. Suka kyalkyale da dariya su dukka ukun. Faduwa ta ce, ''Gaskiya ina jin dadin labarin nan naki, kamar tatsuniya. Mahaifiyata ce ta ke ba ni shigen irin wannan labarin da ina yarinya a matsayin tatsuniya ashe dai irin hakan na faruwa? Umaimah ta nisa ta dago ta dube su daya bayan daya ta yi murmushi, ta tauna naman da yake cike da bakinta ta hadiye. Ta ce, ''Kamar yadda yake faruwa yau Umaimah ta na zama a irin wannan muhalli ba? Gaba daya suka sake yin dariya, sannan Umaimah ta ci gaba da cewa. ''Ba *yan garinmu kadai ba duk Kauyukan da suke karkashin karamar hukumar Dukku suma an gayyace su kamar: *yan garin Birni, Gombe Abba, Konare, Nzagala, Zange da dai sauransu a cikin garin Dukku suka taru a unguwar Se'ngo, daga nan aka debe su zuwa cikin garin Gombe kofar fada. A ranar yini muka yi a karkashin bishiyoyi mu ka ki shiga gida muna jiran dawowarsu. Tun daga safe har zuwa bayan magruba ba mu shiga gida ba sai da suka dawo. Muna ganin dogayen bus guda biyu muka rugo da gudu muna murna. Dagacinmu da jama'arsa ne suka firfito daga daya bus din, yayin da su Nasiba suka fito daga dayar. Su dukka fuskokinsu cike da annuri hannayensu cike da ledoji da alama sun samo kyaututtuka. Nan fa aka hau murna da ife-ife. Wajen Ilah na ruga na ce, ''Ina alkawarinmu?'' Ya miko min *yar tsana da kifina, sai na hau tsalle ni da kawata Matawata. Yayin da bakin ciki ya rufe sauran kawayenmu wadanda ba su da *yar tsana kuma suna tunanin bazan basu aro ba, ba ma wasa tare da su. Ledojin Nasiba sun fi na kowa yawa, da muka shiga gida ta zazzage sai kowa ya shiga mamaki, har da mahaifina, da yake yana gida bai bi tawagar Dagaci ba. ''Waye ya ba ki duk wadannan kayan? Baffa ne ya tambayi Nasiba. Ta ce, ''Wasu daga cikin kayan a can aka rabawa kowannen mu, wadannan kuwa ni kadai wani mutum ya ba ni. Amma ka tambayi mai martaba ya san mutumin da ya bani kayan, na ga sun kebe suna magana. Baffa ya jinjina kai ya bude ya sake bubbudewa, atamfofi ne manya guda biyu, leshina masu tsada guda biyu, shaddoji guda uku turare da kudi mai yawa. Yayin da ka ga kishi da hassada a wajen Nene da Inna, kishiyoyin Yafindo. Suka fara cewa, kada a karbi kayan nan a mayarwa Dagaci ya ajiye ya mayar musu, saboda ba a san ko dan yankan kai bane, ko dan iska ne ya yi asirin da zata yi ta binsa. Surutai dai barkatai na rashin ilimi da hassada muraran. Baffa ya zugu matuka, ya dura kaya a jaka ya tafi fada. Yafindo ba ta ce musu komai ba, don so suke ta ce a'a a yi fada, sun hade kai suna ta musguna mata, to ita kuma sai Allah Ya yi ta mace ce mai kawaici, sam ba ta nuna damuwarta akan irin wannan lamarin, wai a zartar da hukunci a kan nata ta nuna ta damu? A'a ba ta da haka. Mu ma ba mu tsira ba, sun tsane mu, daga zagi sai dunguri, komai muka yi ba dai-dai ba. Dagaci yana ganin Baffanmu sai ya ce, ''Yauwa daman yanzu zan aika a kira ka. Nasiba ta yi miji a birni, yaro dan boko mai ilimin addini da na zamani. Kyakkyawan bafullatani dan asalin, dan sarauta, ya ganta a wajen taro ya dasa, har ya fadawa mahaifinsa shi ne suka sa aka kira ni aka tambayi mahaifinta, na ce bai zo ba. Aka ce na isar da wannan sako nasu cewar suna neman iri a wajen ka na neman auren yarinyar nan. Ba ka kusa sai na ga idan na zartar da hukunci akan yarinyar nan ba zaka ce komai ba, don haka na amsa musu da cewar, babu damuwa an ba su ita. Mahaifina ya yi murna, ya duka ya yi godiya, ya ce duk abin da Dagaci ya zartar shi ne dai-dai. Gaba daya magana ya bari a hannunsa har a gama Hada-Hadar auren. Ya bar wadannan kaya gaba daya a hannun Dagaci. Baffa ya dawo gida ya sanar mana da yadda suka yi, sai gida ya hargitse mu da mahaifiyarmu muka dau kokekoke, musamman Nasiba ihu ta ke ta yi, har da yada zani wai ba ta so, saurayinta Kamilu ta fi so. Baffa ma ya dinga kuka yana bamu hakuri, ya ce, babu yadda zai yi ne yana jin nauyin Dagaci. Yayin da kishiyoyin Yafindo suka hau shewa da habaicehabaice wai kuda wajen kwadayi ya kan mutu, da aka ga kaya an bude ana murna, ashe za'a je a siyarwa da mai kudi *ya. Wa ya sani ma ko dan yankan kai ne ana yin auren ya kashe ta ya gudu ba a san asalinsa ba. Idan suka fadi haka, sai Yafindo ta sake tsorata ta rusa kuka, nima ina yi Nasiba tana yi, kaninmu Sabitu yana yi. Gida ya hargitse har makwabta suka shigo suna tambaya ko lafiya? Aka fara yamudidi da maganar a cikin garin, maganar ba ta bugu ba sosai sai asabar din da angon ya zo da iyayensa maza, a cikin wata dankareriyar mota baka. Abunka da Ruga ba a saba ganin mota mai kyau ba, sai aka hau guje-guje, wasu suka haye bishiya, wasu suka labe a bayan Zana, wai ga yan yankan kai nan.....'' Suka kyalkyale da dariya su dukka. Ba kamar Faduwa ma har da hawaye ta ke yi dan dariya. Abdul-Sabur ya ce, ''Ikon Allah ashe da gaske ana irin wannan rayuwa a kasarmu. Yaya aka yi kuma da suka zo? Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Mu dai muna daga gabagaba muna kallon *yan birni. Sunan saurayin da yake son auren Nasiba Abdul-Basi, ya hadu karshe inji samari. Dan Fulani, dogo, kyakkyawan gaske dan boko. A lokacin yana hada digiri dinsa a jami'ar Ahmadu Bello (A.B.U Zaria) bai gama ba. Mahaifinsa ma mai arziki ne da sarauta a Gombe, tare da shi suka zo da *yan uwan mahaifin. Aka yiwa Nasiba kwalliya da daya daga cikin leshinan da ya bata aka sa kawayenta biyu suka rako ta fada ta gaishe su. Duk da hawayen da yake zuba daga idanuwanta, amma ta yi kyau. Abdul-Basi kallonta kawai yake yi, na so da kauna. Mahaifina yana kusa da Dagaci aka gama magana sun nema kuma aka yi musu alkawari an ba su. Sai suka yi musu yayyafin naira, wacce sai da su kansu su Dagaci suka tsorata suka tafi suka bar *yan gari da yamadidi da zance. Watan Nasiba ya kama a garinmu, duk lungu da sako hirar kawai ake yi, yayin da Nasiba ta kaura daki ta dunkule a lungu ta bude shafin kuka. Hakuri kadai iyayenmu suke ba ta, da fatan alkhairi a cikin wannan lamari mai ban mamaki.... Faduwa ta kurbi lemo ta dubi Umaimah, ta ce ''Yaya ta kasance kuma? Umaimah ta ce, ''A takaice dai an yi auren amma ba yadda iyayensa suka so a yi da wurwuri ba. Abdul-Basi mai ilimi ne, ya ce su bari a shekara tukunna shi da ita su gama fahimtar juna, kada a yi tana kokekoke tana jin tsoronsa, shi ma a sannan ya kammala karatunsa. Da motar haya yake zuwa garinmu, dan acaba ya shiga da shi har kofar gidanmu. Ya shigo zaurenmu ya zauna akan tabarmar kaba a kira masa ita. Ta kudundune a lungu ta ki magana, sai dai ya yi hira da kawayenta. Inda ya burgeni sai ya daina cusa mata kudi sai dai ya yi mata kyaututtuka kadan-kadan ya fi so ya sami soyayyarta ba don kudinsa ba. Haka yake zuwa dandali ya zauna idan ana gada yana sauraron dadadar wakokinmu na gargajiya. Ranar kasuwa ma sai dai kawai mu gan shi tsakiyarmu idan muna Hada-Hadar cin kasuwarmu. Ni ce *yar gaban goshinsa daman na cika rawar kai, sai na yi tsalle na dane shi, ya ba ni kudi na siyo mana gyafa, magarya, kantu, mu shimfida tabarma mu zauna mu ci. Ita kuwa Nasiba ko tana walwala da ta gan shi sai ta bata rai, ta hau murgude-murguden baki, kawayenta suna ta shakiyanci suna sake tura ta. Sai su yi ta ce mata, ''Ka ga amarya, dan ta ga angonta har wani fari ta ke yi da ido. Shi ma ya shiga a yi ta zolayarta, dole ta yi dariya. Wasawasa har ta saki jiki da shi suke hirarsu rangadadai. Kafin ayi auren sai da ya sa su Baffa suka je gidansu suka gani, Nasiba ma da ni da kawayenta mun taba zuwa gidansu muka gaishe da mahaifiyarsa. Gida ne mai get na bulo da bulo a cikin garin Gombe. Hajiyarsa ta yi murna da ganinmu, ta yi mana kyauta ta girma. Ita ma tana son Nasiba sosai, ta roke ta data auri danta su zauna lafiya dan babu abinda ta fi so a duniya wanda ya wuce abunda *ya*yanta su ke so musamman ma Abdul-Basi, tafi sonsa gashi ba dan fari ba kuma ba auta ba. Aka zo muka sha biki a kauyenmu, irin wanda ba a taba yin irinsa ba. A lokacin an tura shi bautar kasa a Kaduna, a can aka wuce da amaryar. Muka je muka ga gida kamar ba a kasar nan ba, kuma gidan bene ne. Shi ma benen ba mu taba hawa ba, ya zama abin kwatance a wajenmu. Amarya tana son angonta kamar yadda yake matukar sonta, suka yi zamansu lafiya a can Kaduna. Sai da ya dade bai kawo ta ba, amma sanda ya kawo ta sai suka ganta da ciki. A lokacin duka-duka shekarunta ba su wu ce goma sha hudu ba a duniya. **************************** Ni da saurayina Ilah muna ta ci gaba da shakuwa don a lokacin ba zancen soyayya ba ne. Ta kai ta kawo duk garin an san shakuwarmu. Ko kiwo ni nake rako shi ni da kawata Matawata. Wata rana wasu baki manyan Alarammomi suka zo garinmu gidan Dagaci suka yi wa'azi suka bada shawara akan ya kamata a tura yara makarantar allo. Wato yawon almajiranci don a sami Malamai a garin, su ma nan gaba su koyar da na bayanmu. Sun yi gaskiya don gaskiya kam babu ilimi a garin, haka muke kara zube yara da manyanmu. 'Dirga da dirge' haka ne karatun da ake koya mana ba Fikhu, ba Tauhid, ba Hadis. Sallah kuwa duk yadda muka ga dama muke ta dungurawa. Da Dagaci ya yi yekuwa (sanarwa) aka hada dattawan gari ya sanar da shawarar wadannan malamai sai iyayen yara da yawa suka ki yarda, kalilan ne suka amince. Mahaifin Ilah ne yayarda zai tura yaransa biyu kananan wato Ilah da yayansa Sule. Mahaifina ya yarda zai tura dansa kwaya daya dan karami Sabitu kanina. Sai wasu kalilan da iyayensu suka amince. Muka yi ta kuka da zasu tafi yawon almajirancin nan da tabarma da akwatunan su aka. Ni abin ma ya yimin yawa, ga saurayina zai tafi ga dan karamin kanina da nake so zai tafi ya bar ni. Har kofar gari na dinga bin su da gudu ina kuka, Matawata ta ruko ni, ita ma da Ilah kukan suke yi. Ina ji ina gani suka tafi suka barni, garin Kaltingo aka kai Ilah karatu, yayin da Sabitu aka kai shi Numan. Sauran yara aka kai wasu Mubi, Jalingo da Adamawa da dai sauransu. Na dawo bana jin dadin garin a sanadiyyar rashin Ilah, babu mai siya min Rake, Kifi Mangwaro, in ci. Babu mai taya ni hira, saboda haka kullum ni da Matawata ba mu da hira sai tasa, tana matukar tausayamin, musamman idan ta ga na zauna ina ta kuka. Har waka na yi masa da YARENMU na Fulatanci ina bayyana yadda na yi rashinsa a tare da ni.... Tana zuwa nan ta kyalkyale da dariya. Abdul-Sabur ya ce, ''Gaskiya sai kin rera mana mun ji, don nima din da kika gan ni ina jin Fulatanci kadankadan. Faduwa ma ta yi dariya ta ce, ''Ki rera mana ko kadan ne mu ji. Umaima ta sake tuntsurewa da dariya, ta ce, ''Yau dai kun saka ni a lungu bayan labari har waka zaku sani na yi? To bari na rera muku kadan ku ji. ''Baba warnanu Inna warnanu Udilli uwartai Sayinde in gartatai Wure in imirintima Mi huidi a warti'' Ma'ana ''Baba ka zo Inna ki zo Ya tafi bai dawo ba Yaushe zaka dawo? Ka zo ina jiranka Na yi mafarki ka dawo. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Allah Sarki sabo, dan na san a lokacin ba ki san soyayya ba, don shekarunki ba su wuce tara ba a duniya zuwa goma. Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Haka ne, ban kai shekaru goma ba a lokacin. Babu yadda iyayenmu ba su yi ba a kawo Nasiba gida ta haihu, Abdul-Basi ya ki yarda ya ce, tana zuwa asibiti awo, kuma can zata haihu likitoci za su fi kula da ita. Ai da ta haihu ya sa kaninsa Ja'afar ya zo ya fada, ya ce a zabo masu zuwa suna kamar mata goma, za a aiko da mota a dauke su ana gobe suna. Mahaifiyarmu ba ta je ba, saboda alkunya *yar farinta ce, sai dai ta hada duk kayan da ta tanada kamar su yajin daddawa, rigunan jarirai, atamfofi masu arha, kwallin jarirai da guru da layoyi irin namu na Fulani dai da ake daurawa yara a wuya da hannaye. ( kafin ilimi ya shigo mu musan babu kyau ) Ta hada su cikin ledoji ta ce akai mata. Kishiyoyinta ne suka shirya su da sauran matan dangi da ni muka tafi. Inna zata dawo Nene ce zata zauna da ita, har sai anyi arba'in a haka aka shawarta. Muka je muka iske ta gida cike da mutane, bayan mai aikinta Talatuwa, ga kanwar baban Abdul-Basi a gidan tana kula da ita. Dakuna biyu ne kacal a gidan, sai falo da bandaki daya da kicin. Saboda taro dole ya koma gidan abokansa yake kwana. Nasiba ta saba da MAKWABTANTA masu kirki, girke-girke kala-kala suke yi mana su kawo mana. Gidaje takwas ne a farfajiyar get din, an zagaye da katanga doguwa. Sama da kasa ne flat guda hudu kenan, daga dukkan alamu gidajen haya ne a unguwar Rimi, Kaduna. Na tsinci kaina ina walwala a cikin birni, na harhada labarun abubuwan da na gani a birni zan ba wa Matawata idan na koma garinmu da Ilah idan ya zo da sallah, don an ce za su zo sallah. Sai naga duk mun zama *yan kauye a ranar suna, saboda kwalliyar *yan birni ba irin tamu ba ce. Bayan shudiyar atamfa da muka saka irin ta Fulani da jagira da dige-digen baki dabe-dabe a fuska, ga wata damara da na ci duk a dole gayu ne na yi na kure adaka, ni da iyayen nawa mu dukka, don ma Nasiba tana hanamu wani abun da ba karamin kwaba fuskarmu zamu yi ba da baki.. Suka kwashe da dariya su dukka ukun. Nima na kashe da daria.. Sai na tuna lokacin da Mal. Habu Imamu yakai Hannah Makarantar F.G.G.C Kazaure... Haka itama taci Uban damara kamar zataje dandali... Sai kuma Gobe idan Allah yakai mu. Sai kuma kumin apuwa na rashin jina jiya saka makon rashin wutan nepa.MAKWABTAKA 18 Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai gefe muka koma muna kallon makadan zamani irin nasu na Kaduna. Mun dai dauki hotuna wanda idan na gan su yanzu sai na yi ta dariya, mun yi wani wuki-wuki kamar ace kulle mu arce. Allah Ya raba mu da duhun kai da talauci. Amin. Su Faduwa suka hada baki su dukka suka amsa mata da, ''Amin''. Abdul-Sabur ya ce, ''Kinga birni daga dukkan alamu ya birge ki. Kin yarda kin koma Ruga kuwa? Umaimah ta harare shi kadan, ta yi gatsine ta ce, ''Cabdi! Ban koma ba, kamar ka sani zama na na yi ni da Nene har sai da aka yi arba'in. ''Ya sunan jaririn ko jaririyar da aka haifa? Umaimah ta ce, ''Namiji ne, sunan Mahaifin Abdul-Basi aka saka masa Salisu, amma Babangida ake kiransa. Da suka yi arba'in Nene ta ce, na shirya za mu koma gida, sai na ki saboda har na shiga islamiyya ni da yaran makwabta. Ga wuta, ruwa, kallon talabijin, bayan ruwan sanyi na firij da lemuna kala-kala (juice) da fanka da A,c, ana dauke wuta sai a tayar da Generator. Abinci mai rai da lafiya kala-kala, shinkafa kullum wanda a Ruga sai da sallah kadai, nama, taliya, makaroni da dai sauransu. A Central bank Abdul-Basi yake bautar kasa suna biyansa ba laifi, amma mutum ne mai kokarin ciyarwa. Sai a lokacin ne ma na fara koyon Hausa don bayan Fullancin ba ma yin Hausa sai kadan-kadan. Nasiba ta ce a bar ni a wajenta, bayan ta yi shawara da maigidanta ya amince a sallami Talatuwa mai aiki, ni na ci gaba da taya ta raino da aikin gida. Farin ciki ya rufe ni na ci gaba da zamana, Nene kadai aka mayar Dugge a motar da Baban Abdul-Basi ya aiko a dauke ta, bayan an hada mata goma ta arziki, da nata da na iyayenmu... Faduwa ta ce, ''An daurawa jaririn guru da layun? Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Mun daura masa mana, Babansa ne ya ciccisge ya zubar ya yi mana fada, ya ce ba ya so a sake daura masa irin wannan. Nan birni ne ba sa yin irin wadannan abubuwan. Abdul-Sabur ya ce, ''Sai suka saka ki a makarantar boko? Umaimah ta ce, ''An saka ni a makarantar boko, nima da girmana na shiga makaranta ajin *yan Nursery duk na fi su girma. To ban iya komai ba, duk sa'annina a aji uku suke na firamare, ban damu ba ina jin dadin sabuwar makarantata da kuma sabuwar rayuwata. Yaya Abdul-Basi ya ga da gaske na kasa koyon ABCD sai ya dage duk ranar asabar da lahadi da safe ko a ranakun aiki da daddare yana koyamin har da duka da bulala idan yaga ina noke-noke bana so na koya. Dole na tsaya na dinga koyo, har haushi Nasiba ta ke ji wataran idan ta ga ya dake ni, tana ganin ya takurawa rayuwata. Ya kan ce mana nan gaba za ku san gata nake yi muku ba zalunci ba ne. Ita ma dai suna nasu karatun idan ya gama da ni, ita ma dai da kadan ta wuce ABCD. Islamiyyar matan aure ya saka ta tana zuwa ranar asabar da lahadi daga takwas na safe zuwa karfe goma sha biyu. Sai na rike mata danta ta je ta dawo. Rayuwa ta fara yi mana kyau, can ma a Ruga wadata ta fara iske su, don kansa da kafarsa Yaya Abdul-Basi yana kai musu kayan abinci buhu-buhu, haka ma Babansa da yake mai arziki ne kuma mai yawan kyauta yana aika musu. Sai da na shekara ba mu je gida ba, da muka tashi zuwa sai muka je a gogenmu, lokacin birni ya fara ratsa jininmu. Sai muka zama abin sha'awa a wajen *yan garin Dugge, suna addu'ar dama su ne mu. Na iske Ilah ya zo gida ganin gida, sai farin ciki ya lullube mu. Na gan shi ya yi baki ya rame, amma fa akwai karatu. Ni da dan guntun abin da na koya zan kureshi, sai na ga ashe ya min nisa fintinkau. Ya iya rubutawa ya karanta kur'ani, ni da shi da kawata Matawata ne muke zama muyi ta ba wa juna labari, kowa ya bada labarin garin da yake da abubuwan da suka faru. Na ke ta basu labarin Kaduna da irin hadaddun da nake tare da su a gida da makaranta. Na dinga nuna musu yadda ake rubutun boko, da irin kayan dadin da ake ci a birni, ga wuta ga ruwa da kayan more rayuwa. Matawata ta yi ta bamu labarin dandali da sababbin wakokin da aka fitar wadanda ba mu iya ba, saboda ba ma nan. Ilah ya ba mu labarin Kaltingo da irin duka, bara da aikin da suke tika a makarantarsu ta almajirai. Yana cikin ba mu labari na fashe da kuka saboda tausayinsa shi da dan kanina Sabitu. Sai shi ma Ilah ya fara kuka, Matawata tana bamu hakuri. Na riga shi komawa Kaduna a garin na bar shi, nan ma sai da muka yi kukan rabuwa ni da Ilah har da Matawata ma ta sha kuka. Allah Sarki, sabo turken wawa. Abdul-Sabur da Faduwa sai jinjina kai suke yi saboda tausayawa. Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Muka dawo Kaduna muka ci gaba da rayuwarmu, mu hudu a gida. Ni da Babangida a dakinmu daya, Nasiba da mijinta a daki daya. Bankin Yaya Abdul-Basi ya yi bautar kasa ne suka rike shi ya fara aiki a wajen, suna biyansa kuwa albashi mai kyau. Ya sauya mota, ya sauya mana kayan gida gaba daya (furniture). Da a risho muke girki ya siyo mana gas cooker ya ga Nasiba ta sake hankali da wayewa zata iya amfani da gas don ada tsoro yake ji karta tashi gobara. Kowa ya kalli Nasiba da danta ya san suna cikin jin dadi da kwanciyar hankali, kyakkyawan yaro, lafiyayye, dan gata mai kama da mahaifiyarsa. Duk wani abu na sakawa, ci, sha ko na wasanni irin na yara Yaya Abdul-Basi ya siyowa dansa, saboda tsananin son da yake yi masa. Haka Nasiba ita ma duk wani abu na kwalliya da ya gani a wajen makwabta ko matan abokansa zai siyo ya kawo mata. Ni ma haka, duk abin da nake bukata ba ya kyashi yana siya min... Abdul-Sabur ya ce, ''Allah Sarki, Allah Ya sakawa AbdulBasi da alkhairi. Umaimah ta yi murmushi, tare da jinjina kai, ta ce, ''Amin. Nan da nan rayuwa ta sauya mana, duhu ya kauce, haske ya zo. Mun sami ilimi a maimakon jahilci, mun samu rufin asiri a maimakon talauci. Yaya Abdul-Basi yana farin ciki da ni, saboda ina kula da dansa sosai, kai ka ce ni na haife shi, saboda yadda yake sona har fiye da mahaifiyarsa. Allah dai Ya sakawa wannan mijin yayar tawa da alkhairi, don ya koyar da ni abubuwa da dama. Wadanda ko a makaranta ban koya ba. Mutum ne mai tausayi da kulawa, tattali da sanin darajar dan Adam. Idan ya so akwai sakin fuska a yi ta wasa da dariya, idan ya ki sai ya sha mur don ba ya son raini, daga ni har matar tasa sai mu nutsu idan muka ga irin yanayin. Ina gama Nursery sai kwakwalwata ta bude sai aka cilla ni gaba, daga aji daya sai na tafi aji uku, daga uku sai na yi biyar. Gaskiya ne na cancanci a tsallake min aji, don Yaya Abdul-Basi ya koyar da ni tsaf a gida. Dai-dai lokacin na fara girma, shekaruna sun kai goma sha uku a duniya. Haka idan na je garinmu sai na nutsu na daina baragada, saboda na ga yadda kowacce mace ta ke kama kanta. A lokacin Ilah ya dawo gida don ya yi sauka, ya zama kato har da gemu. Sai muka shiga gaisuwa ta mutunci da girmama juna gami da jin kunyar juna. Sai a lokacin na tabbatar har yanzu Ilah yana raina bai sauya ba. Ina sonsa matuka, ina jin dadin hira da shi. Matawata ta sha mamaki da ta ga har a lokacin ban daina kula Ilah ba, ta zaci na yi samari a birni, na manta da shi, ba ta san a birni ni kwaila ba ce, duk da ina samun samarin bana kula su Ilah ne kadai a raina. Ilah ya zama malam kowa sai ya durkusa yake gaishe shi, yara da manya da tsofaffi mata da maza. Ya bude makarantar Tsangaya, ma'ana makarantar allo a kofar gidansu shi da *yan uwansa kolawa ne suke koyar da karatu sosai irin su Alifun, Ba,un, an daina karatun dadirga da dirge. Yakan shiga gidajen iyayenmu mata ya koya musu. Na ji dadi da ganin wannan sauyi a Rugarmu. Kanina Sabitu shi bai dawo ba, don bai karasa sauka ba. Amma an ce ya kusa saukewa, wata shekarar zai dawo gida. Tunda ya tafi ba mu hadu ba shekara da shekaru, ko zai zo hutu ni bana nan. Idan na zo shi kuma sai ace ya tafi. Ina so na gan shi don ance ya girma har ya fini girma. Ni ma dai ina ta yakar jahilcin da ya mamaye iyayena mata da maza. Ina ta kokarin koya musu sallah don dai duk tsawon shekarun nan ba sallar suke yi ba, dungure ne kawai. Baffana da Yafindo ne kadai suka yarda suke gyarawa, Inna da Nene ki suka yi suka ce ba ni da kunya, yaushe aka haife ni da zan koya musu sallah? Haihuwa ta tsayawa Nasiba ita da mijinta, sai suka shiga damuwa suna ta yawo a asibitoci ganin likita. Babangida ya girma har ya shiga pree-nusery. Ni kuma na shiga sakandire mai kyau mai tsada, Federal Girls college da take unguwar Malali, ina zuwa ta jeka-ka-dawo. Ina aji biyu na sakandire na je garinmu Dugge hutu, ni kadai ce ma na je a lokacin ban da Nasiba. A lokacin mummunan labari ya zo mana an kashe samarin garinmu su biyar a hanya gaba dayansu abokan Ilah ne, har da yayansa daya Abashe. Ashe *yan fashi ne duk dare suke fita su tare hanya da mugayen makamai su kashe su kwace dukiya. Ilah ya yi kuka sosai ya razana matuka, yake ba ni labari bayan an yi sadakar bakwai. Ya ce, sun sha cewa ya zo su yi sana'ar da za su sami kudi ya bar maluntar nan, sai ya ki binsu, bai san me suke ba, amma yasan jahilai ne ba abin kirki suke yi ba. Shi kuwa da darajarsa a gari kowa yana gaishe shi, malam sama malam kasa ina shi ina biyewa zauna-gari banza? Ya ce, ko ranar da za a kashe su ma tare suke kwance su shida a daki daya suka farka cikin dare suka ce ya zo su je wani waje, sai ya ki zuwa suka fice suka barshi, sai gawarsu ya gani da safe. Allahu Akbar! Allah Ya shiryi zuriyarmu gaba daya.... Abdul-Sabur da Faduwa sai girgiza kai suke don babu dadi abin. Umaimah ta langwabar da kai cikin sanyin murya, ta ce, ''Sai na ji Ilah ya kara burge ni, na ji na sake sonsa. Ya tambaye ni yaushe nake so mu yi aure don mahaifinsa ya ce ya kamata ya fitar da mata ya yi aure, duk sa'anninsa sun hayayyafa. Yana gama fada min haka sai na ji kunyarsa ta lullube ni, na rufe ido na tashi da sauri na shiga gida. Na ji dadi da jin batunsa, duk da bana son kauye, amma idan dai zan auri Ilah na yarda na dawo Ruga mu zauna tare. Na kira kawata Matawata na bata labarin yadda muka yi da Ilah na ce ta je ta bashi amsar tambayar da ya yi min don na kasa fada masa amsa saboda kunya. Na ce ta ce masa ya tura Babansa ya je ya sami Baffana su yi maganar na san Baffana zai kira ni ya tambaye ni ko ina sonsa. Ni kuma sai na ce eh, shikenan sai a cire ni daga makaranta mu yi aure. Matawata ta ce, ''to shikenan, bari in je in same shi gashi can a tsaye a kofar gidansu. Ta tafi wajensa ina lungu a labe ina lekensu, a gabana ta isa wajen Ilah suka kebe suna magana, daga nesa nake bana jiyo abin da suke fada. Sai na ga Ilah yana fada yana wurga hannu, sannan ya juya ya shiga gida a fusace. Hankalina ya tashi na je da gudu na tambayi Matawata me ya ce? Sai ta tabe baki ta ce, ''Ya ce shi ai bai ce zai aure ki ba, bayan kin je birni samarin birni sun lalata ki me zai yi da saura? Sai na sankare a tsaye hawaye ya cika min ido, na daure na shiga gida ba tare da na bari an san halin da nake ciki ba, kwana da kwanaki. Kullum Matawata na gefena tana zuga ni wai na rabu da Ilah fa dan iska ne, ba malamin kirki ba ne, kawai yana labewa da guzuma ne yana harbin karsana. Ko wannan fashin da abokansa suke yi tare suke zuwa, shi da yake malami ne sai ya tauna layar zana ya bata. Wani lokacin naki yarda da maganarta, wani lokaci kuma na yarda dom ina ganin ma a wanne dalili zata min karya ni da aminiyata kuma MAKWABCIYATA? Idan muka hadu da Ilah sai ya harare ni, nima na rama ya wuce, na wuce alhali muna tsananin son juna. Sai na ji garin ya fita a raina ma gaba daya, gara na koma Kaduna. Na shirya na tafi ba tare da hutu ya kare ba... Abdul-Sabur ya yi shuru yana kallonta, can ya ce, ''Amma me ta ce masa? Anya kuwa ba hadaku ta yi ba? Umaimah ta ce, ''Hadamu ta yi mana, ba abin da na fada mata ta je ta fada masa ba. Ashe ce masa ta yi na ce ya fita harka ta, ni yanzu ba ajinsa ba ce, sai dan boko. Wai na ce me zanyi da almajiri, gardi mai bara? Faduwa ta ce, ''Subhanallahi. Ita kuwa a wanne dalili ta yi miki haka? Kafin Umaimah ta yi magana, Abdul-Sabur ya ce, ''Hassada don ita ba ta da saurayi? Umaimah ta runtse ido ta zubo da hawaye mai zafi ta ce, ''Ashe ita ma sonsa ta ke. Yadda ta ke zuga ni haka a can bangaren ta ke ta binsa tana min kazafi kala-kala, har da cewa, an zubar min da ciki a birni. Har sai da ya ji babu abin da zai yi da ni sannan ta yi kokarin cusa kanta wajensa, ba shi da zabi don babu yadda zai yi, amma zancen so ni ce kadai macen da yake so a duniya. In ba rashin wayewa ba me yasa ba zai kira ni ya zaunar da ni ya tambaye ni ba, ko ya aiko mahaifansa su bincika? Ni kuma da yarinta sai nayi ta boyewa Yafindona ko ta tambaye ni idan taga ina damuwa sai in ki fada. Shekara ba ta dawo ba aka zo min da labarin anyi auren Matawata da Ilahna. Suma ne kawai ban yi ba, amma na gigice, sai da Nasiba ta rike ni dan da faduwa zan yi. Kuka muke ta yi ni da Nasiba tun Yaya Abdul-Basi yana ba mu hakuri, har ya ji haushi ya kwakkwayemu, ya ce, ni da nake karatu ina ni ina maganar saurayi a kauye, almajiri dan Ruga? Ina ma auren zai yiwu? Ni da zuciyata ne kadai muka san halin da muke ciki, wannan bakauyen almajirin ya fi min samarin Birni sai dubu, don shine farin cikina. Duk tsananin bacin ran da nake ciki idan na ga Ilah sai na ji sanyi, don zai lallashe ni ya ba ni labaru masu dadi. Wannan shi ne cin amana da musgunawar da MAKWABTANA suka fara yi min a rayuwa.... Umaimah ta sa gefen hannunta ta sharce hawaye mai radadi. ''Yi shiru daina kuka. Inji Abdul-Sabur da Faduwa, Su ma tausayinta ya rufe su. Ta ce, ''Ban koma garinmu ba, har sai da na shiga aji hudu na sakandire shi ma ba zuwan dadi ba ne, kawai Yaya Abdul-Basi ya ce mu zo gida ana nemanmu, ashe Yafindonmu ce ta rasu. ''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Inji Faduwa da AbdulSabur, yayin da kuka ya barkewa Umaimah. Ta dade tana yi kafin su lallashe ta, ta ci gaba da labarin. Ta girgiza kai ta ce. ''Da aka yi sadakan bakwai dole muka shirya zamu koma Kaduna, saboda watan haihuwar Nasiba ne, ta samu ciki da kyar ya zauna mata. Ilah ya zo ya yi min gaisuwa a tsaitsaye, amma Matawata ga ni ga-ta, a jikin zanar gidan su Ilah ta ki yi min magana. Ciki ne ma da ita a lokacin, har wata rangwada ta ke yi tana shafa cikin. Wai har na zama abar zolaya a wajen Matawata duk amincin da ke tsakanina da ita. Zuciyata sai ta yi ta tafasa idan na jiyo masoyina Ilah da aminiyata Matawata suna hira a gidansu. Tunda a gidan iyayensa aka ba su daki, mu kuma katangar gidan mu daya don haka ana jiyo hirarrakin da ake yi a tsakanin gidajen biyu. Muka koma Kaduna muka yi jugum-jugum cikin damuwa, mu dukkanmu. Bayan sati uku dai-dai da rasuwar Yafindo sai haihuwa ta tasowa Nasiba aka kaita asibiti. Allahu Akbar haihuwar ta zo da matsala, likitoci suka yi iya kokarinsu wajen ceto uwar da *yar abu ya ci tura.. Sai kuka ya hana Umaimah ta ci gaba da magana. Faduwa ta zabura ta ce, 'Ba dai ta rasu ba? Umaimah ta gyada kai cikin kuka mai tsanani. Ta ce, ''Yayata Nasiba ta rasu ita da *yar cikin dukka. Sai Faduwa ta rungume ta ita ma kukan ta ke taya ta don tausayi. Abdul-Sabur ya yi ta girgiza kai kalmar ''Sorry-sorry. Kadai ya ke ambato. Umaimah ta matse hawaye ta gyara zama ta ci gaba da cewa, ''Na yi kuka, har yau ina kan yin kuka amma ba zasu dawo ba, sun tafi, sun tafi kenan. Na damu matuka, amma sai Yaya Abdul-Basi ya fi ni damuwa, har na fi shi tawakkali, shi har sai da aka yi ta rike shi don ya rike makara ya ki ya saki, da za a saka ta a kushewarta. Ta sha addu'a kuwa a wajensa, ya ce, ''Nasiba, ke ce matar da na taba so, nake so, kuma zan dauwama ina so a duniya. Ki sani GANGAR JIKINMU ce kawai zata rabu, amma ruhin mu yana tare..'' Hawaye ya yi ta kwaranyowa daga idanuwan su dukka ukun. Har zuwa lokaci mai tsawo kowannensu yana matsar hawaye, sannan Umaimah ta ci gaba da magana. ''Aka kai Babangida Gombe wajen kakarsa wato Hajiyan Abdul-Basi, ni kuma da kayana kacokan aka dawo da ni Dugge, sai kunci ya karu. Na dawo gidanmu dakin Yafindo bata duniya, sannan babu kawata abokiyar hirata Matawata, babu masoyina mai saka ni farin ciki, wato, Ilah. Allah Ya sa Sabitu ya zo a lokacin, da shi kadai nake hira na dan ji dadi, don shi kadai ya rage min a duniya, daga shi sai Baffana. Baffa kuwa ya tsufa, ciwociwo kala-kala. Kishiyoyin Yafindo Inna da Nene suka saka ni a gaba suna ta yi min habaici wai karya ta kare dan birni ya dawo kauye. Kullum sai su yi ta zafuta ta da dungure kai, dole sai na fito daga daki na taya su surfe da girki. Na ga tashin hankali don na manta yadda ake surfe da cin gabza. Yaya na iya, dole na yi ta cusawa cikina duk abin da na samu, don kada yunwa ta kashe ni. Matawata ta haihu, yawanci ma a gidanmu aka yi girkegirke da taron *yan suna, sai na yi mamaki da na ji sunan jaririyar, wai MARIYA, sunan Yafindona ne don dai nasan danginsa kakaf da nata babu Mariya. Ba su gayyace ni ba suna haka tashin hankali ya hana ni fitowa daga daki, sai kuka nake yi yadda ku ka san na tsaga kasa na shige ta rufe ni na huta don tashin hankali. Hakika na ji haushin cin amanar da aka yi min, na shiga zargin ni ce ban sani ba watakila tuntuni ma suna son junansu. Kamshin suyar naman rago da dan Akuya har cikin dakina, amma ko hanji ba a san min ba, raina ya yi ta biyawa. Babban tashin hankalina ma shi ne gulmata da aka dasa kungiya-kungiya ana ta yi, wai na ki auren bakauye na koma birni, ga shi na rasa dan birni na dawo kauyen, Ilah ya yi aurensa yanzu bakin ciki zai kashe ni na ma kasa fitowa cikin jama'a. Su Nene ne masu kara zuga magulmatan, koma dai mene ne na fauwalawa Allah komai, Shi ne mai sakayya. Ba'a yi watanni shida ba kuwa Allah Mai komai da kowa sai da Ya yi min sakayya a bisa abubuwan da duk aka yi min... Faduwa ta dafa kirji tare da yin ajiyar zuciya, ta ce, ''Me ya faru da su? Umaimah ta yi nata takaitaccen murmushin, ta ce, ''Uhum, Allah ba azzalumin bawanSa ba ne. Ashe tunda Ilah ya auri Matawata ba ya jin dadin zama da ita, bayan rashin son da yake yi mata ta cika makirci da hada husuma. Ta hada shi da *yan uwansa saboda fada da take yi da matansu, ta raba shi da abokansa ta dawo tana hada iyayensa fada. Kullum ba ta shiri da surukarta rashin kunya ta ke yi mata sosai, shi kuma Baffansa yana bin bayan Matawata don haka sai a yi ta rigima, Ilah mai hakuri ne yana zaune ba ya magana duk abin da zata yi ba ya iya tsawatar mata. Mahaifiyarsa har kuka ta ke tana cewa, ta yi asarar haihuwa, idan har danta zai auro macen da zata yi mata rashin kunya a gabansa ya kasa magana. Allah kada Ka tsayar da ni ranar shaida, an ce bokaye ta ke bi ta shanye shi, ba ya ganin laifinta sam! Amma Allah Ya fi ta, sai kuwa aka kama ta da laifin kwartanci ita da tsohon saurayinta lawwali. Gari gaba daya sun shaida, har aka rakota gida da waka ana ga kwartuwa. A take Ilah ya yi mata saki uku, ina daga dakina nake jiyo komai. Ban fito ba ma balle ace tsegumi sai na ji a raina ban ji dadin wannan bakin al'amarin ba. Domin dukkan musulmi dan uwan musulmi ne, Allah Ya rufa mana asiri, Ya sa mu gama da duniya lafiya, Ya sa mu fi karfin zuciyarmu. Abdul-Sabur da Faduwa suka amsa da ''Amin''. Umaimah ta kurbi ruwan sanyi ta dago da ido ta dube su, ta yi murmushi don ta ga sun kammala hankalinsu kacokam a kanta, ita suke kallo. Ta ci gaba da cewa, ''Ai ba'a yi wata ba sai na ji an ce ga Ilah can da Baffana a wajen Baffana suna maganata a aure, Ilah har yana kuka yana bada hakuri. Na ji zuciyata ta fusata na kudiri niyyar duk wanda ya kira ni akan maganar sai na fadi ba dadi, kuma ba zan yarda ba, don a lokacin ko ganinsa bana son yi. Ina cikin tunani ne na ji Baffana ya kwallamin kira, na saka hijabina na fito na same su a zaure. Na durkushe a gefe na gaishe su, sai Baffana ya fara bayanin. Ya ce, ''Ga Ilah ya dawo daman makircin Matawata ne ya raba ku. Na girgiza kai na ce, ''Baffa ka yi min afuwa ka bar maganar nan, don maganar nan ba mai yiwuwa ba ce. Na hakura da Ilah tuntuni, ya je ya auri wata. Wato sai da ya rasa Matawata zai tuno da ni? Ai ba a 6ari a kwashe dukka. Nan fa Baffana, Ilah da Baffansa suka hau dogon fillanci, ni wata kalmar hakurin ma sai a ranar na taba jinta a fullanci. Suka yi ta magiya Ilah yana sake fada min duk abubuwan da ya faru tun farko. Wai ashe sanda na aike ta wajensa sakon da ta fada masa daban ne ba wanda na fada mata ba ne, cewa ta yi na ce na fi karfinsa yanzu, ya cire ma maganar aure a tsakaninmu. Sai ya ce tace min ya gode tunda wulakancin da zan yi masa kenan. Sai ni kuma ta dawo ta ce min, ya ce, me zai yi da ni na je birni na zama *yar iska ragowar maza? Sai a lokacin ya fadi duk abubuwan da ta fada masa a kaina, ni ma na fada muka gane Matawata ce munafuka, sai zuciyata ta yi sanyi na amince zan aure shi. Muka watse daga zauren kowannenmu cike da farin ciki. Dare, Safe, da yamma Ilah yana wajena, koda yaushe sai ya zo zance, hade da hidimomin da ya saba yi min tuntuni. Kamar: atamfa ce, mangoro, rake, kaji da dai sauransu. Ita ma Matawata tana jiyo hirarmu da shewarmu daga zaurensu, don gidanmu ne a tsakiyar nasu. Bakin ciki ya rufe ta, ta rasa inda zata saka kanta. Rannan har da fitowa tana zage-zage tamkar mahaukaciya, yara kuwa suka hau yi mata wakar kwartuwa. Idan aka yi sata ko kwartanci a kauye ka shiga uku, gara ma ka bar garin zai fiye maka sauki. Muna ta shirye-shiryen aurenmu Ilah ya siyo siminti ya ce zai sumulce bangon dakina sannan ya yi dabe a kasa, saboda na saba da gidajen birni. Muka shiryawa kanmu rayuwar jin dadi ta aure, irin tamu ta talakawa dai, har yake cewa yana so ya koma Kaltingo da zama wani Alhaji da ya zauna a gidansa ya ce zai bude shago ya dinga jire masa. Muna tunanin nan da wata uku a yi aurenmu. Allah Mai yadda Ya so da bawanSa, ashe dai Ilah ba mijina ba ne har abada. Faduwa da Abdul-Sabur suka zabura suka ce, ''Shi ma ya rasu? Umaimah ta matse hawaye ta ce, ''Ilah bai rasu ba, har yanzu yana nan a raye, koda yake yanzu ban san halin da suke ciki ba. ''To me ya faru? Abdul-Sabur ya tambaya cike da zumudi. Ta yi shuru kanta a sunkuye a kasa, da alama dai tana jin ciwon tuna abubuwan da suka faru da ita ne a baya. Faduwa ta shafa kafadarta tana jijjigawa, kamar me lallashin jariri. Kalmar, ''Ma'alesh, ma'alesh''. Ta ke ta ambatowa, ma'ana 'yi hakuri'. Umaimah ta dago da jajayan idanuwanta ta dube su, ta ce, ''Kun san me ya faru? Baban Abdul-Basi ne ya dawo wajen Dagacin garinmu aka kira Baffana aka yi shawara, wai na maye gurbin Yayata marigayiya. Ma'ana na auri Yaya Abdul-Basi, babu wanda bai amince ba a cikinsu. Kwatsam ni da Ilah muna zaune wannan bakin labarin ya zo mana muka gigice nan da nan sai kuka ya barke mana. Mun yi tunanin guduwa ma dai muka fasa, Ilah ya yi min nasiha ya ba ni hakuri, na yi iya kokarina a fasa auren nan aka fi karfina. Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ba kya ganin auren Abdul-Basi ya fi miki Ilah, tunda Abdul-Basin kin san shi, kin san halinsa, yana da kirki? Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ba maganar kirki muke ba kadai, maganar so da shakuwa shi ne aure. Faduwa ta ce, ''Haka so yake ba ruwansa da kudi ko birni''. Umaimah ta ce, ''Son da nake yi wa Yaya Abdul-Basi na *yan uwantaka ne ba na aure ba, Ilah kuwa shi ne farin cikina, shi ne abinda nake tunawa na ji dadi a zuciyata. Daga dukkan alamu Yaya Abdul-Basi ma ba ya son hadin nan, an fi karfinsa ne, babu yadda zai yi. Amma shi ma ya kasa cire Nasiba a ransa. Aka tarka ta mu aka yi auren aka dawo da ni gidan nan dai na Nasiba, ba a dawo da Babangida ba wajena, saboda Abdul-Basi ya mayar da ni makarantar boko, aji biyar. Yana kai ni da safe na dawo a motar haya idan an ta shi, sai dare yake dawowa. Bai taba kusanta ta ba, wata da watanni ina dakina yana dakinsa. Ina tunanin Ilahna yana tunanin Nasibarsa. Ya fada min baro-baro cewar shi fa Nasiba yake so har yanzu, da zata dawo su zauna da ya fi masa. Ni ma na fada masa da zai sake ni na koma wajen Ilahna na zauna da ya fi min zama a gidansa. Bai damu ba nima ban damu ba da maganar da muka fadawa juna saboda kowa gaskiyar abin da yake ransa ya fada ke nan. Ba ya damuwa da girkina, balle kwalliyata, haka ni ma ba na damuwa da na yi masa komai. 'Zo na kai ki makaranta, ungo kudin makaranta, karbi kudin cefane. Shikenan maganar da ta ke hadamu. Hakan ya fiye min dadi a rai ni kuwa. Daga baya ya fara warewa yake yawan shiga harka ta, yawan jana da hira da kai ni unguwanni wuraren shakatawa. Ya mayar da ni islamiyya, ranar asabar da lahadi yake kai ni ya dauko ni, ya dawo da yi min home work da dai sauran kulawa. Ni ce nake ta baudewa don ban fitar da ran komawa wajen masoyina ba Ilah. Da ya dau hutu ya kai ni gidansu Gombe, muka ga Babangida, ya girma yana zuwa makaranta. Daga nan na roke shi ya karasa da ni Dugge, kai tsaye ya ce 'a'a idan dai su Baffa ne zai je ya gano su ba sai na je ba' wai shi nan da tsiya kishi yake, ya san Ilah nake so na je na gani. Na yi ta kuka da ihu har sai da surukata ta ce, ya tashi ya kai ni garinmu na kwana biyu sannan ya koma ya dawo da ni. Ya dinga harbamin harara da ya ga ina murna a mota saboda tsananin kishi. Ai kuwa mun kai musu goma ta arziki, kayan abinci, ya diddika da atamfofi, gidanmu da gidan Dagaci. Da aka gama gaggaisawa sai Abdul-Basi ya tafi ya barni. Kudi mai yawa na kunso na kawowa tsohona a dunkule a boye na ba shi, ya yi ta mamaki yana tambaya ta ina na samo kudin nan? Na shaida masa kudin makaranta ne da ragowar kudin cefane nake tarawa. Ya yi godiya ya shi min albarka ya yiwa mahaifiyata da yayata addu'a Allah Ya sada su da rahama. Na gyara zama na tambaye shi Ilah, sai na ga ya girgiza kai ya tabe baki, ya ce, 'Ilah sai addu'a Allah Ya hadashi da jarababbiyar mata!. Ina jin haka gabana ya yanke ya fadi, na ce, 'Lafiya? Baffana ya yi shiru can ya dago ya dube ni, ya ga yadda na dimauce. Ya ce, 'Ki rike mijinki, ki rabu da Ilah ba mijin da zaki yi tunanin za ki aura ba ne. Sai na sulale kamar zan kwanta na sume don fargaba. Baffa ya ce, ''Yarinyar nan Matawata auren kisan wuta ta yi na sati uku ta fito ta yi idda ta dawo wajen Ilah, yanzu haka suna tare tana gidan na ji ance ma wani cikin ne da ita. Don haka ki je ki kama mijinki ki manta da Ilah a rayuwarki. Na matse hawaye na ce, ''Idan Allah Ya so Baffa na hakura da Ilah a rayuwata. Na koma daki a sanyaye sai na ji dama Yaya Abdul-Basi bai tafi ba na bishi mu koma, don bana son garin ko kadan. Matawata ta ji labari na zo, washegari da sassafe ta shigo gidan ta same ni har kofar dakina ta zazzage min habaici iri-iri. Wai Ilah nata ne duk naci da sihirce-sihircena dole na hakura na bar mata shi. Ban rama ba ta yi ta gaji ta tafi. Wasika doguwa da ajami Ilah ya aiko ,in da daddare yana mai ba ni hakuri da yi min fatan alkhairi, ya kuma roke ni da na taya shi da addu'a, rayuwarsa tana cikin kunci don bai yi sa'ar abokiyar zama ta gari ba. Ban gama karantawa ba ma na yayyaga na zubar a shara. Ban yarda na hadu da shi ba har na yi mako a garin, sannan Yaya Abdul-Basi ya zo ya dauke ni muka tafi. Tun a hanya ya ga alamu ina cikin damuwa, da ya dame ni da tambaya sai na rushe da kuka. Na shaida masa Ilah ya sake mayar da Matawata a dakinsa. Wani dogon tsaki na ji ya ja, sannan ya watso min wata hargitsattsiyar harara. Ya ce, 'Idan bai mayar da ita ba ke zai saka a dakin? Wallahi Umaimah ki rufawa kanki asiri, ki sani fa kina kona kanki ne, da auren wani a kanki amma kike tunanin wani katon banza, har kina kishi akan ya maida tsohuwar matarsa. To ina ruwanki? Ya shiga yi min nasihohi masu ratsa jiki ya ce, gara ni da shi dukka mu yi wa kanmu fada mu manta da Nasiba da Ilah mu fuskanci sabuwar rayuwa, Allah ne kadai Ya san dalilin da Ya raba mu da wadanda muka fi so, Ya hada junanmu. MAKWABTAKA 19 Tun lokacin na yiwa kaina fada, na nutsu na fara kokarin cusawa raina zama da AbdulBasi a matsayin miji na, shi ma haka. Sai bayan ma da na gama sakandire sannan muka budewa kanmu sabuwar rayuwar jin dadi da son juna. Abdul-Basi ya dawo yana sona tamkar Nasiba, don na juye ta sak! Da na yi kiba, ni ma na cire Ilah a raina, na daukeshi a matsayin munafiki na barshi da Matawata can su karata da bakin munafincinsu... Abdul-Sabur ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Ya aka yi kika zo nan kasar kika baro masoyinki Abdul-Basi a can? Sai ta yi murmushi karfin hali, ta ce, ''Kai ma tun da ka ganni a nan kasar alhali ina da aure a can kasan sai dai idan da wata matsala ne. Kuma ai da sauran kuka wai anci gumba an hana maye, me aka yi a hawa bishiyar bare a tsinko reshenta? Sai Abdul-Sabur da Faduwa suka hada idanu. Sannan Faduwa ta dafe kirji, ta ce, ''Me ya hada ku? Umaimah ta tabe baki ta ce, ''MAKWABTANA ne suka hada mu, MAKWABTAKA! ''Kamar yaya? AbdulSabur ya tambaya cike da fargaba. Umaimah ta yi shuru kanta a sunkuye a kasa, kamar me tunani. Can ta dago ta dube su, idanuwanta a cike da kwallah. Ta ce, 'Na kasance mai saurin yarda da amincewa mutane, na saba da Makwabtana da *ya*yansu tun lokacin marigayiya don haka nake jinsu tamkar dangina. Kamar yadda na fada a baya gidaje takwas ne a farfajiyar, sama da kasa guda hudu. Mu muna sama kasanmu kuma wata mata ce mai suna Hajiya Ladidi, *yan garin Minna ne aiki ya kawo mijinta Kaduna, suna yaren Nufe da *ya*yanta hudu ta girme ni harta kusan haifata ma. Sai gidaje biyu da suke fuskantar namu wata beyarabiya ce amma musulmace mai suna Zulaiha Senegal. Tana zuwa Senegal tana dinko kayan mata da maza shaddoji da yadiddika tana siyarwa *yan siyasa da matan masu kudi. Tana ji da gayu da rawar kai tana abu kamar wata budurwa alhali ta ajiye karatan *ya*ya guda uku. Samari maza guda biyu har daya ya gama sakandire ya shiga jami'a, daya ya na daf da gama sakandire, sai mace ita ce a sakandire aji uku. Ta rabu da baban yaran tun suna kanana ta zo ta kama haya ta ke kasuwanci, ta ke kula da *ya*yanta. Ba laifi matar tana da kirki da yawan fara'a da jan mutane a jikinta, bakinta rairai-rai saboda iya magana, don haka gidanta kullum a cike da mutane yake, mata da maza, kawayenta da kawayen *ya*yanta, *yan uwanta da *yan uwan tsohon mijinta zuwa suke yi tana maraba da kowa. Ta ja ni a jiki sosai muka saba tun lokacin Nasiba, shakuwarmu ta fi yawa a lokacin da na dawo ni kadai, ba ni da abokiyar shawara sai ita. Gidaje hudun kuwa da suke gefenmu, gidan wasu kabilu ne ba musulmai ba ne, wa da kani, daya sama daya a kasa da matansu, ko na ce dadironsu, wadannan ba ma harka da su. Sai dayan ginin Hajiya Bishra a kasa, mijinta ya mutu ya bar ta da yara, amma fa duk ta aurar da *ya*yanta. *Yan mata biyu ne suka rage mata sa'annina ne, Nana da Wahida, suna neman gurbin karatu a Kaduna Polytechnic. Sai saman su wata amarya ce ba su dade da tarewa ba, mai suna Bara'atu ta riga ni aure har ta haifi *yan biyu. Ita ma kawance muke yi na hakika kamar yadda mai gidanta Kamal da maigidana suke yi saboda su dukka banki daya suke aiki. Duk wani sirrina, na gidanmu can Dugge dama tsakani na da mijjina da kawata Bara'atu nake tattaunawa saboda na yarda da ita. Mijina sai ya yi ta jiyo maganarsa ya rasa daga inda magana ta ke fitowa. Ban tashi ganewa ba har sai da abu ya kwabe, a lokacin da bazan iya gyarawa ba... Kamar yaya? Abdul-Sabur ya tambaye ta cike da rashin fahimta. Cikin jimami Umaimah ta ce, ''Matsalata da Bara'atu ke nan, sai ni da Zulaiha Senegal. Auntyna nake kiranta koda yaushe sai na dauki kayan abinci kamar idan zanyi wainar shinkafa ko alala, to ban iya sosai ba, ita take koya min. Ko ta shigo da kanta har gidana ta koya min, ta koya min yadda zanyi magana da miji, da yadda ake tafiya da kissa gami da kisisina. Na dauke ta tamkar *yar uwata Nasiba, saboda yadda ta ke nuna min, sai na zaci tana sona. Abdul-Basi ya fara min fada akan na dinga ja da baya da Makwabtana, dan ya ga na bawa Makwabta gaskiya fiye da shi mijina. Ni kuwa a wajena dole ne na shiga makwabta saboda zaman gidan ya yi min yawa ni kadai, ga yawan dauke wuta haka ga mijina baya dawowa sai karfe takwas ko tara na dare tun karfe bakwai na safe. Idan ma na zauna ni kadai tunani ne ya ke addabata na yi ta kuka. Da jimamin rashin mahaifiyata ko *yar uwata zan ji ko kuma da takaicin cin amanar da Matawata ta yi min ta raba ni da wanda nake so? Makwabta nake shiga in sha hira, suma su shigo min, amma a ce a raba wannan karfaffan zumunci ba zai yiwu ba. Don haka ban ji maganar Abdul-Basi ba, na ci gaba da huldata da su. Muna nan a haka na samu ciki, na haifi dana santalele, mai kama da mahaifinsa, aka saka masa suna Bilal. Abdul-Sabur da Faduwa suka bude baki don tsananin mamaki. Tambayarta suke yi, ''Au ashe kin taba haihuwa? Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Ina da dana yana can a gidansu. Abdul-Sabur ya ce ''Ke kuwa me ya raba ki da mijinki da danki kika taho kika bar su? Umaimah ta ce ''Kaddara ce wacce ta riga fata, kaddara ta sanadin amincewa MAKWABTAKA da na yo. Kafin na yaye Bilal sai na sami wani cikin, ni dai tun daga wannan lokacin na rasa kan mijina, sai na ga kamar ya daina sona, ya tsane ni. Ya daina shiga harkata, kullum sai ya dawo gida a koshe ya ce ya ci abinci a waje. Ashe ni ce ban sani ba Zulayha Senegal ta kwace min mijina, tun baya biye ta har ya fara. Ashe tunda magruba ya ke dawowa sai ya shige gidanta a can zai ci abinci, ya yi kallo, ni kuwa ina cikin duhu idan babu wuta ina jiransa ya dawo ya tayar min da janareto don ba zan iya tayar da shi ba, ya yi min tauri. Ban san wainar da ake toyawa ba MAKWABTA duk sun sani babu wacce ta fada min, sai dai suna gefe suna tausayamin, idan suka ganni a gidanta, ko suka ganta a gidana. Ni ma dai na ga a lokacin ta fiye bugun cikina ta ji irin zaman da nake yi da mijina, ban boye mata ba na fada mata irin canjin da na ga ni daga wajensa, sai ta yi murmushin mugunta. Ta-kai-ta-kawo sai in zo in ganta a kicin dina tana min barbaden magani a cikin kwanukan abincina. Rannan kuma na kama ta ta budamin gas cooker wajen da ake ajiye silinda ta jefa min wani abu, ashe laya ce. Matattakalata duk ruwan rubutu ne idan na fito nake gani, sai na yi ta mamaki, amma kuma ko kusa zuciyata ba ta taba yi miin zargin tana bi na da sharri ba. Kuma ban daina kula ta ba. Wata ranar asabar da safe cikina ya tsufa ina son na je na nemo mai aiki a unguwar Dosa, wata Hajiya Balaraba babar kawata ce ta ke samowa, ta yi min waya ta ce an kawo masu aiki da yawa na zo na dauka. Kasancewar watan haihuwata ne gani da karamin da bai fi shekara daya da rabi ba, ba ya tafiya ma a lokacin sosai, ga shi daf da watan azumi za,a fara aiki zai yi min yawa dole na sami mataimakiya. Na dade da fada masa zan nemi mai aiki, ya kuma yarda, sai na sanar masa a safiyar ya zo ya kai ni na dauko mai aikin. Ya daka min tsawa ya ce, ba zai kai ni ba. Na shiga yi masa bayani cikin ladabi duk da haka ya ce, ba zai je ba sai dai ni na je. Na ce ya ba ni kudin tasi drop na je na dawo, ya ce ba zai bayar ba. Na duba jakata na ga kudin dari biyu ne kawai, ba zasu ishe ni daukar tasi zuwa da dawowa ba. Sai na kuduri niyyar hawan acaba na yi sauri na je na dawo, in yaso Haj. Balaraba sai ta ba ni na dawowar. Na ce to ya rike min dana na je yanzu na dawo. Abin mamaki sai ya daka min tsawa. Ya ce, ''dauki danki ki tafi da shi, ba zan rike ba nima ina da wajen zuwa. Kuma ki tafi da makullanki don bazan jire miki gida ba. Na dauki dana na tafi jikina a sanyaye ina ta hawaye ina jin bakin cikin wulakancin da ya tarki yi min, da kyar nake tafiya ga ciki ga goyo, nauyi jikit. Na fara jin alamun nakuda dan lokacin haihuwar ya cika. Na wuce gidan Zulayha Senegal na iske ta tana ta caba ado sai na ga ta yi min kallon banza. Na gaishe ta, na shaida mata na kawo mata Bilal ta rike min zan je unguwar Dosa yanzu zan dawo, zan dauko mai aiki.... Ban rufe bakina ba ta ce, ''dauki danki ki tafi da shi, nima unguwa zan je. Na fice a sanyaye na nufi titi na tare dan acaba na hau. Banda kuka babu abin da nake yi. A gaban mai babur aka saka Bilal duk da ya yi kankanta a zaunar da shi a nan babu yadda zan yi, tsinin cikina bazai bari na zaunar da shi a gaba na ba, haka ba zan iya yin goyo ba. A lokacin ana taron siyasa a garin, kowanne titi a garin Kaduna motoci ne (go slow). Don haka sai muyi mintuna talatin akan titi daya kafin mu matsa gaba. Kwatsam ina kan babur a cikin rana ni da dana, da mai acaba mun galabaita. Juyawar nan da zan yi, sai na ga galleliyar motar Zulayha a gefena, koda na sake wurga ido itace a gefe namiji ne yake tukawa. Sun yi luf a cikin AC babu ruwansu da kura, zafi, balle hayakin *yan acaba, dariya suke yi suna hira da shewa, har da tafawa da hannu. Ko da na dubi mai tukawar sai na ga AbdulBasi ne. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Na dinga fada a bayyane, yayin da dan acaban ya gigice, ya fara tambayata ko lafiya? Na barke da kuka, yayin da jikina ya dau karkarwa cewa nake, ''Ga miji na can da MAKWABCIYATA suna cin amanata. Zulayha ce ta fara ganina, muka hada ido, sai ta zunguro Abdul-Basi ta nuna ni ga mu nan a kusa da su, muna daf da su. Sai jikinsu ya yi sanyi suka kasa hada ido da ni. Mun jima kafin a bada hannu, su ka ja da gudu suka tafi suka bar mu a baya muna gurgurwa. Na ga masifa a ranar, na ji kamar na hadiyi zuciya na mutu. Dan acaban ya yi ta yimin nasiha yana bani hakuri, suna gabana ina hango motarsu, hanyar kawo suka yi da alama garin ma zasu bari gaba daya. Gudu muke yi kawai a hanya, to ni dai ban san me ya faru ba, sai na ji mu gijif! Mun watse a titi, mun yi karo da wani babur din mun fadi. Na fadi a kan cikin nawa, yayin da dana Bilal aka cilla shi a gefen titi ya fadi. Ya kurje a fuska da kafafuwa, ni ma fuskata, gwiwoyin hannu da kafafuwana duk jini. Dan acabar ya karye, ya yin da daya mai acabar ya suma. Nan dai na mike tsaye wuriwuri ban damu da ciwon da yake jikina ba, dana kawai na ke nema. A can gefe aka tsinto min shi, jini gaje-gaje na rushe da kuka na rungumeshi.... Umaimah ta fashe da kuka, yayin da tausayinta ya lullube zuciyoyin wadanda ta ke ba wa labarin. Faduwa ta ce, ''Sannu *yar uwata, ashe kin sha wuya ke ma? Umaimah ta nisa ta sa toilet paper ta share hawaye, ta ci gaba da cewa. ''Alhamdu lillah a kowanne hali nake, sai aka fasa tafiyar unguwar Dosa, aka kawo motar asibiti (ambulance) aka zuba mu a ciki, an sace min jakata, waya ta na hango akan titi har wani ya dauke na karbi abuna. Wayar Abdul-Basi nake ta yiwa flashing don ba ni da kudi a wayar, amma ya ki kira na. Na yi flashin fiye da sau goma ina so na sanar masa mun yi hatsari, muna asibiti ya ki kira na, da na dame shi ma ya kashe wayarsa. Su Bara'atu na yiwa flashing suka kira ni na sanar musu halin da nake ciki, na fada musu sunan asibitin. Suka gigice ba jimawa kuwa sai gata da Haj. Bishra sun zo, ni dai ta dana nake yi, ban damu da kaina ba. Babu dinki a raunin sai dai aka wanke ciwukan aka saka mana auduga da iodine. Mun sha zafi, aka ba mu allurai da magunguna duk kyauta. Sai aka zo maganar dan cikina suka ce ya bugu, amma na koma asibitin da nake awo na ga likita ya yi sauri a fitar da jaririn. Bara'atu da Haj. Bishra na sa su tsayar mana da me tasi, muka hau muka kama hanyar gida. Fadi suke, ''Umaimah ma tafi gida kuwa ba asibitin da kike awo ba zamu je? Saboda maganar dan cikin nan naki. Ki kira mai gidan ki fada masa halin da kike ciki mana. Sai suka ga na barke da kuka, suka gigice ainun, suna tambaya ta, da kyar na iya fada musu abin da idanuwana suka hango min, wato Zulayhat Senegal da mijina Abdul-Basi a mota suna tafe suna hira da shewa. Sai na ga sun hada ido sun sunkuyar da kai kasa, da alama dai sun san komai, don na ga ba su yi mamaki ba. Bara'atu ta fara magana, sai Aunty Bishra ta dinga zungurarta, wai ta yi shiru. Na ce, ''Au daman har da abin da zaku iya boyemin? Me kuwa za ku boye min bayan na gani da idona? Sai Bara'atu ta gyara zama ta dinga ba ni labarin abubuwan da suke faruwa wanda ban san da su ba. Tun ina fahimtarta har na gigice na fita daga hayyacina, na dora hannu aka na mimmike a cikin tasi kamar wacce zata sume. Ga ciwo a fuskata, ga kuka ina yi, ga dana yana nasa kukan saboda azabar ciwo... Faduwa ta ce, ''Me suka fada miki? Umaimah ta goge hawaye, ta ce, ''Labarin dawowar da yake yi da wuri ya shige gidanta ya ci abinci, ko ya dauketa suje restaurant su ci. Da yadda ta ke zuwa ofis dinsa daga dukkan alamu kuma suna neman juna. Yanzu haka wannan fitar da suka yi garin su Zulay zasu je Zariya maganar aurensu, ni ban sani ba,,,,, Abdul-Sabur ya ce ''Allah Sarki, da kin yi hakuri kin zauna da ita. Me ye kishiya? Ko wacce ta zauna da halinta. Umaimah ta tabe baki ta ce, ''Ban ki zama da ita ba ita ta fitar da ni dole, Ya zan yi tunda an kore ni? Faduwa ta ce, ''Ya aka yi da cikin a ranar? Umaimah ta sake goge hawaye, ta ce, ''Ba muje asibitin ba, gida na je na kwanta ni da dana, MAKWABTA suna jinyarmu. Su AbdulBasi ba su dawo ba sai karfe goma sha daya na dare. Ya shigo yana bata rai don kada ma na yi masa maganar dazu. Sai ya tsorata da yaga ciwon jikinmu, ya shiga karkarwa. Ban iya yi masa magana ba sai Bara'atu ce ta ba shi labari. Ya fito da makulli ya kinkimi Bilal ya ce, ta kamo ni mu je asibiti a sake bincikarmu musamman ma dan cikin. Haushinsa kawai na ke ji, muka duru a mota har da Bara'atu muka je. Muna isa saiga Zulayha ita ma ta biyo mu a motarta, ban san wanda ya fada mata ba ma. A gigice ta hau kissa da kisisina, wai ita tausayi. Likita yayi scanning a cikina ya ce, ''Baby ta mutu a ciki, za su ba ni gado zuwa gobe a yi tiyata. Cikin dare nakuda ta taso da kaina na haifi *ya ta fara jawur mai kyan gaske, amma ba ta da rai. Kwanana uku a asibiti a kwance, abin takaici Zulayha ce a kaina ita ya barwa kudin komai, tunda shi yana ofis sai dare yake zuwa su tafi gida tare, sun daina boyemin komai ma a gabana ake hirar soyayya, wasa da dariya. Abincinta nake ci, haka dana a hannunta yake kacokan ita ke kula da shi. Na yi kuka, na sha takaici, ba yadda zan yi sai kallo da ido. Bara'atu na sake dora min da wasu bayanan ma da ban sani ba, ashe an dade ana cin amanata. Su ma MAKWABTAn abin da suke takaici ta girme shi, ya fi ta kyau, ya fi ta ilimi ba ajinsa ba ce. Me zai yi da tsohuwar *yar duniya? Kanta har da farar fufura, shi da yake da mata kamar ni fara, yarinya mai kyau da ilimi? Amsar ita ce ta fini iya duniyanci, bariki zalla, wayo, iya tattali da rashin kunya, sai kuma asirai da ta dogara da shi, ta haka ya fara sonta. Aka sallamo ni na dawo gida zan karbi dana sai ta hana ni, wai na bari sai na gama jego tukun na ita zata kular min da shi. Tsabar kissa ce da son jan ra'ayin Abdul-Basi ba don Allah ba ne, na hakura na bar sa. Ta goya shi ta sauke, ta yi masa rawa, ta kai shi kantina siyayya kalakala. Uban kuma sai ya yi ta jin dadi. Wata asabar suka shirya a motarta shi da ita suka tafi Gombe wajen mahaifansa, zai gabatar da ita a matsayin amaryar da zai aura. Kudin cefane kawai ya wurgo min kan cinyata, ya ce mu mun tafi Gombe sai goben za mu dawo. Na san da ita za su tafi, na daure ban tambaye shi ba balle na yi korafi, ya samu damar yi min rashin mutunci. Ya kada kai ya fice da jakar kayansa. Na tafi wundo da gudu ina lekensa, na ga ya shige gidanta fiye da mintuna ashirin, sannan suka fito a tare, ashe shaddar jikinsu iri daya ce. Ita ta dinko musu daga Senegal sun yi kyau, sai kamshi suke yi. Ina saka ran za su miko min dana kafin su wuce, sai na ga har da shi da kayansa suka shige mota, an yi masa kwalliya shi ma. Na manta rabon da na ga dariyar Abdul-Basi amma tunda suka shiga mota suka fara hira da dariya, har da kyakyatawa. Na sake bin daya wundon da gudu don na ga fatarsu daga get, to ko na gani ma ba komai zai kara min ba banda tsabagen takaici da kunar zuci. Suna tafiya na sulale na zauna na dora hannu aka na surnano da wasu zazzafan hawaye mai radadin fita. Kafin hawayen ya diro kasa sai na ga Haj. Bishra a tsaye a gabana, na yi sauri na goge hawayena ina kokarin wayancewa. Sai ta ce, ''Kada ma ki bata hawayenki *yata, ki kwantar da hankalinki, ki saka musu ido kawai, komai ya yi farko zai yi karshe. Da yarinta jikinki shi yasa kike amincewa kowa alhali ana cutar da ke. Ba Zulayha kadai ba, duk wasu da kike mu'amala da su a gidan nan sai kin yi takatsan-tsan, kuma kin rufe bakinki, kin boye sirrinki. Ba ta fada min ba dai baro-baro saboda gudun haddasa husuma a matsayinta na babba, amma tabbas na san akwai wata magana a kasa. Sai ta tashe ni tsaye ta zaunar da ni akan kujera ta ci gaba da yi min nasihohi masu kwantar da hankali, sai na ji dan sanyi a raina. Na yi mata godiya ta tafi na kasa cin abinci, shi ya sa ban dafa ba. Daga lemo da biskit sai ruwa na yi ta sha, a lokacin ina da kiba tunda na yi wannan ramar har yau ban mayar da jikina ba. Da na tuna da son da Alhaji surukina ya ke yi min, sai ban damu ba nasan da kyar zai amince ya bar Abdul-Basi ya yi wannan auren. Mahaifiyarsa ce dai na ke zaton zata amince, don duk abin da *ya*yanta suke so shi ta ke so, ba ta hana su. Na dukufa ina ta addu'a ina kuka akan Allah Ya dawo da hankalin mijina kaina, don na ga ba ya sona yanzu. Bara'atu kawata, makwabciyata ta shigo gidan da yamma da sababbin gulma, ita ba kwantar min da hankali ta zo ta yi ba, irin na Haj. Bishra, sai ma tayar min da hankali ta sake yi. Mijinta ne yake sanar mata da komai, duk hirar da suke yi da Abdul-Basi akan Zulayha. Wai shi Zulayha ta fiye masa ni, gara ya auri babba mai hankali wacce ta san tattalin miji ba irina ba, raino kadai yake yi. Ni ma na saki baki na yi ta fada mata irin wulakancin da yake yi min, Allah Sarki! Kuruciya dangin hauka. Ba su dawo ba sai washegari lahadi, da daddare ya dawo gida bai yi min bayanin komai ba ya shige dakinsa ya kwanta kamar yadda ya saba, ya raba daki da ni yanzu. Da sassafe ya fice wajen aiki ko kudin cefane bai bani ba, ina sallah na ji fitarsa. Misalin karfe goma da rabi na safe na ci kuka na gaji, na fito barandar waje na tsaya ina mai kallon gidan Zulayha, sai kawai na yi ido hudu da Babangida dan gidan Yayata a zaune akan kujera, dana Bilal akan cinyarsa. Yana ganina ya zabura ya ce, ''Aunty Umaimah''. Bilal ma ya hau tsalle da murna da ganina. Na yi matukar razana da ganin Babangida, na dafe kirji na ce, ''Lah yaushe ka zo? Ya ce, ''Ni da Abba muka zo jiya, ai na dawo Kano gaba daya za'a saka ni a makaranta a nan. Anti Zulayha ta ce min ba kya nan ni daman a wajenki zan zauna'' Sai ya mike da sauri ya ajiye Bilal yana shirin ya zagayo wajena. Sai na ce, ''Ka taho da Bilal shi ma. Ya dauko shi suka taho, a falo na jiyo muryarta ta ce, ya koma ya zauna babu inda za su je. Sai na ji shiru ba su zagayo ba. Na fusata ainun na kwalla kiran sunansa, amma kiri-kiri matar nan ta hana shi amsawa. Ban dauki gyalena ba sai na fita na shiga gidan haka nan. Na iske su a zaune a gabanta sun yi tsuru-tsuru, kana ganinsu kasan a takure suke. Ita kadai ce a gidan yaranta duk sun tafi makaranta. Na yi sallama sam ba ta amsa min ba, na wuce kai tsaye na dauki Bilal na kama hannun Babangida na ja, ai kuwa sai ta rike shi ta ja. Ta ce, ''Ki tafi da danki, wannan dai ba ke kika haifa ba, kuma ba ke kika ba ni ba, Kakarsa ce ta ba ni da ubansa, don haka sai a bar min dana. Na auna mata harara, na ce, ''Kin manta wace ce ta haife shi? Idan kin manta ki tuna, dana ne, dan yayata ne uwa daya uba daya, don haka ni na fi cancanta na rike shi ba ke ba. Sai ta sake shi ta gyada kai, ta ce, ''dauke su ki tafi da su, na ji *ya*yanki ne amma ki sani daukar *ya*yan nan da kika yi daga wajena zai zai janyo miki bacin ran da za ki dauwama da shi bai gushe ba. Ni Haj. Zulayha ba a ja da ni, yaro bai san wuta ba sai ya dafa ta. Idan kin san wata ba ki san wata ba, da sannu za ki banbance zuma da madaci. Na sake auna mata harara na ce, ''Allah Ya fi ki ai, duk abin da ya same ni daga Allah ne ba dai mutum ba. Ta rike baki tana mamaki, sai ta gyada kai, ta ce, ''Au har kin yi baki? Kin yi wayon yi min rashin kunya? Tabbas sai na zame miki duhu a cikin rayuwarki, sai kin yi dana-sani da ba ki zage ni ba. Na ja wani dogon tsaki ba tare da na tanka mata ba, na fice da *ya*yana muka shiga gidana. Sai na ji sanyin kasurgumin bacin ran da nake ciki da na ganni da yarana suna taya ni hira. Amma ina mai tsananin mamaki da takaicin kawo Babangida a dalilin Zulayha ba a dalilina ba. Babu irin magiyar da ban yiwa Abdul-Basi ba tun farkon aurenmu ya dawo da Babangida wajena, amma fur! Ya ki sai ga shi yanzu ya dauko shi tun kafin ma ya aure ta ya damka mata shi. Na san halin kissa da kisisinar Zulayha ta yi musu dadin baki ne shi yasa suke ganin ita zata iya rike su alhalin nan gaba wahalar da su zata yi. Na san zata fadawa Abdul-Basi zai yi fushi da ni amma ban zaci har zai yanke min irin wannan hukuncin ba.... Sai ta dafe kai ta surnano da hawaye. Faduwa ta dafe kirji, ta ce, ''Ba dai dukanki ya yi ba akan haka? Kafin ta amsa Abdul-Sabur ya amshe da cewa. ''Ba dai saki ya baki ba? Umaimah ta sharce hawaye mai hade da majina, ''Ina fita tayi masa waya wajen azahar sai ga shi a gida. Na yi mamaki da ganinsa daidai wannan lokacin. A fusace ya fado mana cikin falon, muna cin abinci. A gigice muka mike don tsorata, ya daka min tsawa ya tambaye ni. ''Me ya kai ki gidan Zulayha kika zage ta? Na ce, ''Ban zage ta ba, ni karya ta ke yi min'' Ya dakamin tsawa, ya fada cike da fusata, ''Ita ta ke yi miki karya? Sa'ar ki ce? Daman ta ce kin zama fitsararriya, don haka ki kwashi yaran nan ki mayar da su, amma ki durkusa ki ba ta hakuri kada ki sake shiga gidanta. Na tambaye shi har Bilal din ma a wajenta zai zauna? Ba saboda rashin lafiya ba ne aka ba ta ba, yanzu kuwa ai na warke ni zan rike dana. Sai na ji ya kwashe ni da mari dau! Na durkushe na rike kunci. Ya fada cikin kakkausar murya. ''Daga yau idan ina magana kina yi sai na saba miki. Banza! Ballagaza, saunar mata. Yaushe aka gama rainonki da zaki iya rainon wasu? Yaushe kika gama sanin ciwon kanki balle ki san ciwon wani? To tunda bakyajin maganata ki shirya kayanki gobe na saki a mota ki koma Dugge can ki zauna a gidanku, sai ki yi musu fitsarar a kauye, ba a nan ba. Dama tsiyar bakauye ke nan, ya zo birni ya sha jar miya ya nuna maka ya fi ka iya tafiya a kan tiles. Na ji kamar almara, na kasa kuka, na kasa magana. Ya ja hannun yaran suna ta tsala kuka, har da ihu ya kai su wajen Zulayha, sannan ya shiga motarsa ya koma ofis. Sai a lokacin na fara rusa kuka ni kadai a daki, amma na tsorata da maganar kora ta da ya yi, na san tonan asirina ya zo idan ya sake ni na koma Ruga da zama. Har dare jikina rawa ya ke yi, ina ta addu'ar Allah Ya huci zuciyarsa kada ya dawo da fushi ya sake ni. Ya dawo tunda magruba, na ga tsayuwar motarsa amma ba gidana ya shigo ba, gidan Zulayha ya shiga inda ya ci lafiyayyen abincin da ta dafa masa. Ni kuwa da yake bai bar min kudin abinci ba, sai na dafa shinkafa da wake da mai da yaji, dan na ga yana sonsa. Na kakkalato kudi na aika aka siyo min salad da tumatir da *yar albasa na yayyanka masa don na burge shi. Bai shigo gidan ba sai sha dayan dare. Na durkusa na gaishe shi ya yi banza da ni kamar bai san da wanzuwata a gurin ba, na yunkura zan je na dauko abinci, sai ya ce dawo nan, bana son abincinki munafuka. Na tsorata da jin wannan kalma da ta fito daga bakinsa. Na dawo na durkusa, sai ya fara zayyano min maganganu kalakala na tsakani na da shi, amma ya ji maganar nan a waje a ofis ma aka fada masa. Sai jikina ya hau rawa na ce, ''Ni ban fadawa kowa ba. Ya daka min tsawa ya ce, ''Ki fada min da wacce ku ke hira a gidan nan idan bani nan, ko kuma yanzu na yi kasa-kasa da ke, bakar makira kina tafiya a sum-sumke, amma sai tsabar bakin munafurci da tozarci. Can na tuno aminiyata Bara'atu ce kadai nake irin wannan hirar da ita. Sai na ce, ''Na san dai mu kan yi hira da Bara'atu. Ya ce, ''To zamana da ke ya kare tunda ba kya iya boyemin sirrina. Bara'atu kike fadawa ita kuma ta ke kwashewa ta fadawa mijinta, shi kuma ya je ofis yana yadawa ga abokan aikinmu. Na yi ta ba shi hakuri, na ce, ''Ba zan kara ba. Ya yi banza da ni, ya shiga daki sai ya fito min da farar takarda mai kunshe da bakin sako. Na bude na karanta tun a gabansa, saki daya ya rubuta min, wanda tunda nake a rayuwata ban taba jin tashin hankali ba sai irin na ranar. Allah Ya sa ban manta ambaton innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ba. Na yi ta fada ina mai-maitawa kamar yadda malamin islamiyyarmu ya ce mu dinga yi da zarar mun hadu da bala'i. Ya damke gashina ya kai ni dakina ya ce, na fara hada kayana gobe da safe zai saka ni a mota na tafi garinmu. Ina makyarkyata ina hada kayana a lokacin na nemi hawaye na rasa, saboda masifa ta yi masifa, tashin hankalina rabuwa da karamin dana Bilal ga Babamgida da aka dauko shi daga gidan tarbiyya, wajen rufin asiri aka kawo shi wajen wahala, inda za a iya gurbata masa tarbiyya, shi ma zan fi so da an bar shi a Gombe ya fi komai a gare ni. Yana ta zagina ta uwa ta uba, yana ambaton albasa ba ta yi halin ruwa ba, ban yi halin Nasiba ba, ba don albarkacin Nasiba ba ai da tuni ya sake ni. Alhali na fi yi masa biyayya ma akan Nasiba, na fi ta wayewa da sanin tattalin miji... Abdul-Sabur ya kumbura ya yi suntum kai ka ce Abdul-Basi ne a gabansa, ko Zulayha sai harare-harare yake zuciyar nan na ta tafasa don takaici. Faduwa kuwa sai girgiza kai ta ke, kira ta ke, ''Lahaula wala kuwwata illah billah. Umaimah ta zubo da hawayen takaici, ta ce, ''Na kwana ban runtsa ba a zaune, ina ta sake-saken inda zan nufa don ba zan iya zama a tsakiyar Matawata da Ilah ba, ga gulmar gari, ga tsangwamar matan uba, ga talauci da rashin lafiyar mahaifina babu kudin magani. Daman Abdul-Basi ne mai siya ya aika masa, ni ma na tara dan kudi na kunshe idan na je na ba shi, yanzu duk babu mai ba mu. Gari ya waye na tashi na yi wanka na yi sallah tun da asubah. Sai da na jima da kimtsawa sannan na ji Abdul-Basi ya shiga wanka, misalin karfe shida da rabi, bakar abaya na saka a jikina sai na zindimo bakin hijabi na fice da sauri na nufi gidan Bara'atu zuciyata tana ta tafasa. Ba su bude gida ba ma ni na kwankwasa, na san sun tashi tunda mijinta ma Ma'aikacin Banki ne. Ta yi mamaki da ganina, gami da hawaye face-face a idona. ''Lafiya Umaimah? Ta tambaye ni a dan duburce Na ce, ''Na zo ne na yi miki sallama na kuma yi miki godiya. Na ji abin da duk kika fadawa mijinki shi kuma ya je ya yada a ofis har Abdul-Basi ya zo ya sake ni a dalilin haka. Amma wallahi Bara'atu kin ba ni mamaki, ban taba tunanin MAKWABTAKA takan iya komawa cuta ba. Yanzu duk yadda na dauke ki a gurina ki rasa abin da zaki saka min da shi, sai ki kwashe duk maganar da muka yi da ke ki fadawa mijinki, shi kuma don rashin lissafi kamar shi namiji wai ya buge da kwasar maganar mata yana kaiwa gurin aiki. Sai ta hau fada da daga murya don mijinta ya ji ya fito. Ta na cewa, ''Kamar yaya, me kike nufi? Ni da mijina munafukai ne ke nan? To mun fada din ke dai kawai kishi ne ya dame ki za a auro miki wayayyiya *yar birni, kin tsorata za ki gudu, amma mu ina ruwanmu? Idan ma na fada ni na gayyatoki kizo ki fada min? Surutai dai da cin mutunci ya yi ta fitowa daga bakin Bara'atu, na yi kasake ina kallonta cike da tsananin mamaki, makwabciyar da na amincewa ce yau ta ke min wannan tonan sililin.MAKWABTAKA 20 Na tuno cin amanar da Matawata ma ta yi min na hado da cin amanar da Zulayha ta yi min, sai na ji a raina na tsani duk wani MAKWABCINA. Na kudira a raina har abada ko gaisuwa babu tsakanina da MAKWABTANA, haka na dai na ba da hakkin MAKWABTAKA.. Umaimah ta fashe da kuka mai cin rai. Abdul-Sabur ya yi doguwar ajiyar zuciya, ya gyara zama ya ce, ''Ke wanne sirrinsa ne kika barbaza a waje wanda ya ba shi haushi haka har da saki? Kin san fa maza ba sa son kananan maganganu irin na mata, amma shi ma ai duk wannan bai kai ga saki ba. Umaimah ta ci gaba da kuka, abin da kuwa ba ta sani ba, kukanta yana tayar da hankali ga duk mai raunin zuciya. Sai suka shiga rarrashinta suna mika mata toilet paper tana ta sharcewa. Sai can ta nisa ta ci gaba da magana, ''Allah Sarki kuruciya mai dadi, rashin sani ya fi dare duhu. Ba wani abu na fada ba wanda ya wuce hirar da nake ba ku yanzu. Hirar garinmu na ba ta, ta kuruciyarmu da waken dandali. Da hirar yanda Abdul-Basi ya hadu da yayata Nasiba har aka yi aure, dawowata wajensu da zamana a wajensu, da shiga makaranta. Don ita bata san Nasiba ba a lokacin ba a yi mata aure ba, ba sa gidan, wadan da suka zauna da Nasiba sun bar gidan. Kuma da bakinta ta tambaye ni wai wacece Nasiba da ta ke jin su Haj. Bishra suna ta maganarta, wai an ce yayata ce? Shi ne na bata labari, na hada mata da labarina da Ilah da Matawata sai kuma labarinsa da Zulayha a lokacin da maganar cin amanar da ake yi min ban sani ba. Ita ma Bara'atun ta ke karamin da abubuwan da idanuwanta suka gani, ko wanda mijinta ya jiyo a ofis ya fada mata. To amma ka san magana idan ta zamana ta koma ta gulma, to yadda za'a jujjuya ta sai ka ji ba iri daya ba ce da yadda ta ke tun fil'azal. Yadda Kamal mijim Bara'atu ya je yake fada a ofis cewa ya yi, Abdul-Basi dan birni ne, dan masu kudi da sarauta a Gombe, amma saboda neman kyau ya shiga Ruga ya auro mai tallar nono Nasiba Yayata ke nan, wai don ta haifa masa kyawawan *ya*ya. Da ta rasu ya koma nacewa kanwar bayan shi ya rike ta ya ce sai ya aure ta, ba ta sonsa, tana ta wulakanta shi ya yi ta cusa kudi aka raba ta da saurayinta da ta ke matukar so mai suna Ilah, ta zo gidan ba ta sonsa. To burinsa ya cika ya sami fararen *ya*ya, amma fa duk maza ne ya fi son *ya mace don ta kawo masa jari. Kun ji yadda aka juya zancen, kuma dai shi ma ya tsane ni ya fasa zama da ni akan Zulayha shi ne ya sa ya yi saki, amma ba don maganar nan kadai ba. Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Tabbas haka ne, nima abin da zan fada kenan kika riga ni. Abdul-sabur ya kurbi lemo ya ce, ''Haka ya ke yanzu na fuskanci maganar. Ya dai so ya sake ki ne ya rasa dalili, kuma ba ya so ace ya sake ki a dalilin zai yi aure. Umaimah ta langwabe kai gefe, ta ce, ''Sai na ji Kamal yana magana da Abdul-Basi a waya, wai ya zo gidansa ya fitar da ni ga shi nan na zo gidansa ina ta takalar matarsa da fada. To shi ba ya son tashin hankali, ya za a yi na zo gidansa na tayar musu da hankali da sassafen nan? Sai na ji muryar Abdul-Basi yana kwalla min kira a bakin matattakalar gidan. Na fito da sauri jikina yana rawa. Bayanai nake yi masa cewar ni ba fada na zo na yi da ita ba, sallama zan yi mata. Ai kuwa ban rufe bakina ba na ji ya rufe ni da duka ta ko'ina, yana zagi yana jana ya wurga ni a cikin mota. Da gudu MAKWABTA suka kawo min agaji, amma ina! Har ya kulle ni a mota. Haj. Bishra har da hawayenta ta shiga yi masa fada tana cewa, ''Haba AbdulBasi kashe yarinyar na kake so ka yi bayan cin amana da cin mutuncin da Zulayha take mata a gidan nan tana hakuri, kuma har da duka da zagi? Sai ya balbale ta da rashin kunya, wai babu ruwanta da iyalansa. Ina daga cikin mota na bude mata takardar sakin da ke kunshe a cikin rigata. Ta gilas ta karanta, sai ta fashe da kuka ta shiga gida. Kalmar karshe da ta fada kafin ta tafi ita ce, ''Ki yi hakuri Allah Zai musanya miki da miji mafi aikhairi. ''Insha Allah''. Inji Abdul-Sabur. Faduwa ta ce, ''Kayanki fa, ya bari kin koma kin dauko? Ta ce, ''Eh, gidan amaryarsa ya shiga ko in ce farkarsa don ba a yi auren ba suke holewarsu. Ta lalata shi, salihin mutum ne Abdul-Basi, ban taba jinsa da neman mata ba, amma sai ga shi kowa ya san abin da suke aikatawa da Zulayha Senegal. Yana shiga na bude kofar da gudu na hau samana Allah Ya sa bai kulle ba na jawo katuwar akwatina da na shirya ta tun cikin dare na ratayo jakata mai dauke da tarkacen kayan kwalliyata na fito, har nazo matattakala zan sauka na tuna takarduna na firamare da sakandire, da na diploma da na yi akan na'ura mai kwakwalwa (computer) suna cikin akwatin da yake ajiye muhimman takardunsa na garzaya da gudu na dauko a cikin ambulan na cusa su a cikin riga don idan ya gani zai kwace tunda ya yi niyyar yin mugunta, baya son ci gabana. Ina saukowa sai na ji an ambaci sunana, wata *yar karamar murya daga kan barandar Zulayha. Na daga kai da sauri sai na ga Bilal dina ne ya tashi daga barci daga shi sai pampers. Yana murna yana tsalle yana fadin, ''Ga Umma'' Sai Babangida ya fito da gudu ya ce, ''Aunty Umaimah ina za ki je na ga kin dauko akwati? Kar ki tafi ki bar mu, ni ma zan bi ki Gomben. Sai ta fashe da kuka cikin rurin kukan ta ci gaba da magana, ta ce, ''Sai na daga ido na dube su na yi musu addu'a, na ce ''Allah Ya kare ku, Ya raya ku na ba wa Allah amanarku. Na ja akwatina da sauri na tafi, suna ganin na tafi sai suka fashe da kuka suna kiran sunana. Na tsugunna a bakin motar Abdul-Basi na toshe kunnuwana da hannayena biyu saboda sautin kukansu tamkar darmar wuta ake caka min a dodon kunnena.... Kuka ya ci karfinta sosai, yayin da ta kifa kai akan dinning table din da ta ke ta yi ta rusawa. Hawaye mai yawa ya yi ta zubowa daga idanunwan Abdul-Sabur da Faduwa su ma saboda tausayi. Lokaci mai tsawo suka dauka kowa ya kasa magana. Umaimah ta dago da kanta ta sa toilet peper ta goge hawayen da ya bata mata fuska, yayin da idanuwanta suka yi jajawur ta ci gaba da cewa. ''Har yanzu wani lokacin sai na ji kamar kukansu ne a cikin kunnuwana, sai na yi ta tunanin ko a wanne hali suke ciki? Na san Allah ba zai bari su wulakanta ba insha Allah. Ya fito a fusace na yi sauri na mike tsaye kada ya sake dukana, ya harari akwatina ya bude bayan mota ya wuce ya shiga mota ya kunna. Sai na kinkimi akwatina na saka a cikin bayan motar na mayar na rufe. Na sake daga ido na dubi su Bilal har yanzu ba su gushe daga wajen ba, ba su daina kallona ba suna kuka suna kiran sunana ba. Na sake daga kai na dubi wundon kicin sai ga Zulayha a labe ita da *yarta suna nuna ni suna dariyar mugunta. Na yi sauri na bude gidan baya na zauna don na san gidan gaba ya haramta a gare ni yanzu a wajensa. A fusace ya fisgi motar sauran MAKWABTA sun fito sun jeru suna daga min hannu suna nuna min jimami a gare ni, har da kabilun mazan nan da suke zaune a gidan su ma sun tausaya min har da yi min hawaye. Ya kai ni tasha ya fito ya bude bayan mota ya kira masu lodi ya ce su saka kayan a motar Gombe, daga Gombe zai biya direba ya wuce da ni Dugge, ya kai ni har gida ya damka ni a hannun mahaifana. Da suka ji ciniki sai suka rugo suka kira direban ya garzayo da kansa don ya caski kudi. Nan da nan ya amince da bukatun Abdul-Basi, kudi mai yawa ya ba shi ya juya ya tafi ya bar ni da dirobobi a tsaye. Bai ma sake waigowa ba balle ya ga na shiga ko ban shiga ba. Ko sisi bai ba ni ba, bayan kuma ya san ba ni da ko sisi a jakata. Na yi ta rusa kuka a motar ana kallona, wasu na ba ni hakuri, wasu na tambayar me aka yi min. Har mota ta tashi muka tafi ban daina kuka ba, idanuwana kamar za su zazzago su fado don zafi da kumburi ga ja da suka yi, sai na yi tawakkali na zaro carbi na yi ta jan ''Lahaula wala kuwwata illa billahil alaihil azim. Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan minha''. Ba adadi har muka isa Gombe. Na yi kamar na ki wucewa garinmu na tafi gidan iyayensa na sanar musu ko za su sa ya mayar da ni, sai na ga gara na hakura da shi tunda ya daina sona, so yake ya rabu da ni ta kowanne hali. Direba ya kai ni Dugge da misalin karfe biyar na yamma, sai yara suka hau murna da ihu sun zaci na taho musu da tsaraba kamar yadda na saba zo musu da su alewa, biskit, cingam, biredi, lemo, ayaba. Har na tafi kullum sai na rabawa yara alewa kwali-kwali nake saya. Wannan karon babu komai, nima makoshina a bushe yake ba ci ba sha a hanya, pure water guda daya wata mata da ta zauna a kusa da ni ta ba ni na sha, bayan shi ban ci komai ba ina ji ina gani, ina jin yunwa ba ni da kudin siya, duk *yan mota suna ta ciye-ciye. Abdul-Sabur ya ce, ''Allah Sarki, abu bai yi dadi ba. Daman shi aure a karkashin bishiyar dabino ake daura shi, a raba shi a karkashin bishiyar aduwa, ko darbejiya. Ma'ana bishiyar dabino zaki, bishiyar aduwa kaya, ko darbejiya daci. Allah Ya kyauta, Ya kare mu daga sakin aure, ai ni bana son na ji anyi sakin aure. Bana burin na auri macen da zan iya saki da bakina sai dai mutuwa ta raba mu. Faduwa ta ce, ''Ai ko ba ka fada ba kai ai mai laushi ne, macen da ta aure ka sai dai ta nemo rigima da kanta, amma kai ba ka da matsala. Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta ci gaba da cewa, ''Ilah da almajirinsa da Sabitu kanina sai suka zuba min ido suna yi min kallon rashin fahimta da suka ga na fito daga mota jikina sanyi kalau, ido ya yi min jawur alamar kuka da na sha. Sun san ba lafiya ba, kuma ba su taba ganin na zo ni kadai ba babu Abdul-Basi, kuma a motar haya. Direba ya sauko min da akwatina, yara suka kinkima suka kai min ciki. Na sunkuyar da kai na shige cikin gida. A zaure na ga Baffa jin sunana da ya yi yasa ya tashi zaune. Kira ya ke, ''Ina Bilal zo nan ja'iri. Sai na girgiza kai na ce, ''Baffa ni kadai na zo, na baro shi a Kaduna. Ya ce, ''Af ke da Basi'un ne? Na sunkuyar da kai ina shirin fasa kuka, sai na daure na ce, ''Shi ma bai zo ba. Sai ya yi jigum can ya nisa ya ce, ''Zuwan lafiya kuwa kika yi ko ce miki aka yi na mutu ne? Na fara kuka, na ce, ''A'a babu wanda ya ce ka mutu. A nan ya fara fuskantar wani abu ba lafiya ba, shi ma ba ya so yara su ji ko matansa, sai ya yi sauri. Ya ce, ''Je ki ciki ki huta kin sha hanya. Na shiga na gaishe da su Nene sun yi carko-carko a tsakar gida suna jiran labari marar dadi. Na shige dakin Yafindo wanda ya zama dakin Sabitu. Na yi sallah na jira abincin dare, tuwon dawa ne miyar kuka lami shatab a haka na cuccusa saboda yunwa. Sabitu ya shigo ya zauna kusa da ni ya gaishe ni ya shiga tambayata. Cikin rada na ba shi labari, amma na ce kada ya fadawa kowa sai ya dafe kai ya yi shiru da alama hankalinshi ya tashi matuka. Ya ce da ni, ''Ai ko kada ki fadawa Baffa, kada jininsa ya hau. Ki shirya ki je Gombe ki sanarwa iyayensa za su mayar da auren tunda *yan mutumci ne. Na ce, ''Ai ba ni da kudin mota'' Ya ce, ''Zan ba ki idan kin tashi tafiya. Da safe Baffa ya tambaye ni lafiya? Sai na shirga masa karya na ce, umara ya tafi ya ce na dawo gidansu Gombe na zauna, ni kuma na ce gara na zo gida. Ya ce, ''Ban da abinki me ye abin zuwa nan ki zauna Allah Ya rufa miki asiri kina zaman birni, me yasa za ki waiwayi baya? Na ce, ''Ai zan dinga zuwa Gombe ina dawowa'' Sai ya yi addu'a Allah Ya dawo da shi lafiya, na ce, ''Amin. Duk da ban fada ba matan Babana dai suna ta zarge-zarge anya kuwa ba karya na ke yi ba, aurena ne ya mutu irin wannan katuwar akwati dana ciko da kaya? Matawata ma yara suke fadamin ta kirasu tana tambayarsu ko sakina aka yi, na dawo gida? Sai suka ce mata, a'a mijina ne ya tafi Makka na dawo gida, Ta ce, ''Allah Ya sa a sake ta ma. Ilah ma ya tambayi Sabitu anya kuwa lafiya ya ga na zo a jejjeme? Sabitu ya ce, ''Lafiya kalau mijin ne ya yi tafiya shi ne ta zo Gombe daga nan ta karaso gida. Bayan kwana biyu na shirya na dauki kayana kala biyu a *yar jakata na kira Sabitu ya ba ni isasshen kudin motar Gombe zuwa da dawowa. Na kama hanya. Na isa da rana na iske Hajiyar Abdul-Basi, ta kalle ni ta watsar, don ba haka ta saba yi min ba, sai na tsorata na zube na gaishe ta. Idan na yi mata Fulatanci sai ta amsamin da Hausa, sai na rasa wannan dalili. Na fara yi mata bayani sai ta katse ni, ta ce, ta ji duk abubuwan da na shuka, ai ba a kaina aka fara yin kishiya ba da zan dagawa danta hankali don zai yi aure. Na shiga yi mata bayani dalla-dalla sai ta dinga amsawa a shelake, ban yi mamaki ba don irin dinkakkun kayan Senegal wanda Zulayha ta ke siyarwa ta kawo mata, saboda a lokacin ma irinsu ne a jikinta. Don haka Zulayha ta fi ni kirki, don ta fi ni kudi tunda ni bana dinko mata kaya na kawo. Daman mahaifinsa ne ke son mu ita ta fi son ya auri *yar mai kudi, *yan birni don dai rabon Babangida da Bilal ne, babu yadda ta iya. Sai na fashe mata da kuka na durkushe a gaban matar nan ko rarrashina ba ta yi ba, na yi ta yi har na gaji na daina. Na tambaye ta ina Alhaji, sai ta ce da ni, ''Me za ki yi masa? Na ce ''Zan fada masa cewar Yaya Abdul-Basi ya sake ni''. Sai ta ce, ''Wa yace miki bai sani ba? Shi zai hana a sake ki ko shi yake zaune da ku? Zulayha ta kira ni a waya a dai-dai lokacin da kika gama min zagi, wai kin kwace Babangida ke za ki rike tunda dan yayarki ne. Ban da munafunci nima da na hana ki rike shi yanzu na dauka na ba ta saboda na ga gidan maiko ko? To duk na ji zagin da kika yi min. Abdul-Basi ma ya bugo ya tabbatar min kin yi har kin shiga gidan kin kwaso *ya*yan kina masa rashin kunya don kin koshi, kinsha jar miya, kin taka matsayin da ba ki isa ki taka ba, saboda samun guri. Sannan kika yada sirrinmu a makwabta har ofis ake gulmarsa, to me zai yi da ke dan ba son kai da rashin kunya irin ta mutanen kauye ba? Hannu na dora aka ina salati ina kuka, ina kuma rantserantsen ban fadi haka ba, sharri ne kawai aka kulla min. Da Halamu Littafin nan ya fara isan ku. In bakwaso kuyi magana sai a canxa wani. MAKWABTAKA 21 sai ganin fitowar Ja'afar nagani. Ya fito a fusace ya daka min tsawa, ya ce, ''Ke Umaimah ki rufe mana baki, kin ishe mu da kuka tun dazu. Sai na nutsu na rufe bakina na hau makyarkyata kada ya yi min duka, don gidansu na tako na zo. Hajiyarsu ta ce, ''Yauwa gara ka fada mata, kukanta ba zai amfane ta da komai ba, domin mun gano bakin munafunci da kwantingwilarta. Ya karaso ya zauna ya dade kansa a sunkuye a kasa kamar mai tunani, sai can ya dago ya dube mu, ya girgiza kai don takaici. Ya ce, ''Har yanzu daman ana zama na zalunci da jahilci, gami da makirci a duniya? Haba wannan abu da me ya yi kama? Hajiya ta ce, ''Fada mata dai ta ji, an gano ta yanzu, da dai an dauka mai tarbiyya ce, ashe kallon kitse ake yiwa rogo. An dai ji kunya wai kura da satar tsumma. Ya ce, ''Ke dai za a fadawa Hajiya ba Umaimah ba. Kin yi kuskure da kika ba wa danki damar auren karuwa, ya rabu da matarsa ta arziki. Sai dadi ya sa na yi ajiyar zuciya. Ta kuwa fusata da jin batunsa, ta hau zaginsa. Tana cewa, ''Au dama da ni kake, da ka ke cewa ana zalunci, jahilci da makirci? Ya girgiza kai, ya ce, ''Ya ya zan ce miki haka? Da azzalumar karuwar nan nake da shi yaya Abdul-Basin da suka sami yarinya karama marainiya suna wahalarwa. Ta daka masa tsawa, ta ce, ''Ku tashi daga gabana bana son ganinku. Muka mike sadaf-sadaf muka fice, yayin da muke ta jiyo bambamin fadanta. Da muka fito waje sai na ce da shi, ''Ina Alhaji? Ya ce, ''Ya tafi umarar maulid shi da Sarki''. Na ce, ''Ja'afar ya ya zan yi? Ka taya ni fada masa idan ya yi waya, halin da nake ciki''. Ya ce, ''Ki yi shuru, ki daina kuka, ki bari Alhaji ya dawo a tsanake zan same shi na fada masa, zancen bana waya ba ne. Saura kwana uku ya dawo sai na zo mu yi maganar, yanzu dai bari na kai ki tasha ki koma. Na ce, ''To Allah Ya kaimu. Ya dauko mukullin motarsa ya fito da motar, na bude gidan baya na takure yana ta ba ni baki, yaro mai hankalin manya duk da ya girme ni ma. Ya fara wucewa da ni wajen cin abinci (restaurant) ya siya min shinkafa da miya da kaji, ina ji ina gani kamshin tururu amma na kasa ci. Yana rokona da kyar na ci rabi muka fito muka tafi. Harya kama hanyar tasha zai saka ni a motar garinmu, sai na ce ya kai ni gidan kawata Lamijo dake unguwar Checheniya, tare muka yi firamare a Kaduna, ta dawo Gombe tai sakandire daman *yan Gombe ne aiki ya kaisu Kaduna a lokacin. Ta yi aure a nan cikin garin Gombe, ta auri wani hamshakin mai kudi da mulki. Duk zuwan da muke yi ni da Abdul-Basi sai ya kai ni gidan na yini, ita ma idan ta je Kaduna da yake da yayarta da ta yi aure, sai ta zo gidana ta yiyi ko ta kwana. Da farko Ja'afar ya ki amincewa ya kai ni, sai da na yi masa bayanin cewar, so nake na jira Alhaji a gidan ba sai na sha wahalar komawa da dawowa ba. Ya ce ''Kina ganin za ki zauna a gidan har kwana uku ba matsala? Na ce, ''Ba matsala tana da wadataccen dakuna a gidanta. Ya amince ya kai ni har cikin get din gidan, ta hango ni ta wundo ta fito da gudu ta tare ni da murna, muka yi sallama da Ja'afar. Ya ce, zai kira ni idan Alhaji ya dawo, sai ya zo ya dauke ni muje wajensa. Bayan ta hada min goma ta arziki muka fara hira, sai na fara kuka ina ba ta labarin matsalata. Tabbas ta tausaya min, ta ba ni goyon baya na zauna a gidanta har Alhaji ya dawo, sannan ta yi min addu'a Allah Ya sa na koma dakina. Da daddare dan mijinta ya shigo wani matashi yaro, a shekarar ya gama sakandire, sunansa Hanif. Da takardunsa a hannu ya zo neman Babansa... Faduwa ta ce, ''Dan mijinta kamar ya ya? Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Ke fa Hausa ba ta ishe ki ba. Ana nufin mijin yana da wata matar da kuma gidajensu daban-daban. Kuma girkin amaryar ne shi ne dansa ya zo nemansa. Ko ba haka kike nufi ba Umaimah? Ta yi murmushi, ta ce, ''Haka nake nufi kuwa. Alh. Rabi'u Damuna sunan mijin kawata, matansa biyu ne, ita ce ta uku, kowacce kuma gidanta daban, saboda mai kudi ne. Ina zaune Lamijo da Hanif suna hirar tafiya karatu Malaysia tun bana fahimta har na fara fahimta, tun ban damu ba har na tsoma baki ina jero musu tambayoyi. Ya ce, ai ba Babansa ba ne zai biya ba, gwamnati ce ta yi alkawarin duk *yan asalin garin wanda ya gama sakandire ya keda credit tara za a biya masa. Sai na ga ai ni ma na cancanci shiga cikin wadanda ake neman nan. Sai na fara fadawa kawata to ko nima na dauko takarduna, mijinta ya taimakamin? Ta ce, a,a ya ya za'a yi haka alhali ga shawarar da aka yi za a zartar? Sai Hanif ya shiga ba ni kwarin gwiwa yana murna ya sami *yar uwa, ya ce, sai mu tafi tare. Ya tafi akan zan hada takarduna da nasa a ba wa babansa ya nemar mana tallafi daga gwamnati (schoolership), tunda ana damawa da shi a gwamnati, shi ma kusa ne. Lamido ta shiga yimin nasiha gara auren shi ne mutuncina da na je kasar waje karatu ace na zama *ya iska. Na gyara zama na sake bude mata cikina ta ji duk halin da nake ciki a Kaduna, Gombe da can Dugge garinmu. Na tabbatar mata Abdul-Basi ba ya sona, ba zai mayar da ni ba, ko na koma Zulayha ba zata bar ni mu zauna lafiya ba. Ga mahaifiyarsa ta tarko tsana ko ita ba zata bari ya mayar da ni ba. Idan na zauna a garinmu gori da wuya ne za su gallabe ni. Sai ta yi saranda ta yi amanna na bar kasar. Amma ta shawarce ni na jira zuwa kwana ukun surukina ya dawo a ji abin da zai ce. Na dukufa ina ta addu'ar neman zabin Allah mafi alkhairi tsakanin zuwana karatu Malaysia da komawata gidan mijina. Na yi ta yin wannan addu'ar istihara da Manzon Allah (S.W.A) ya ce mu dinga yi zamu ji abin da ya fi alkhairi ya fi kwanciya a ran mai yinta.. Faduwa ta ce, ''Ya ya addu'ar ta ke? Umaimah ta ce, ''Sallah raka'a biyu ce a karanta Fatiha da kowacce surah, sannan a karanta wannan addu'ar:Allahumma inni astihiruka bi ilmika, wa astakdiruka bi kudaratika, wa as'aluka min fadlukal azim, fa'innaka takdiru wala akdaru, wa ta'alamu wala a'alam, wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta ta'amu an hazal amru kairan li fi dini, wa ma'ashiyi, wa akibati amri au kala ajili amri, wa'ajilihi, fakdurhuli, wa yassarhuli, summa barakli fihi, wa in kunta ta'alamul annahazal amra, sharranlifi dini wa ma'a shiyi, wa akibati amri, au kala fi ajili amri, wa'ajilihi, fasrifhu anna wasrifni anhu, wa kudirli kaira haisu kana summa Ardinibihi.'' A ranar da Ja'afar ya ce Alhaji zai dawo na ji shiru bai neme ni a waya ba. Sai na kira shi bai dauka ba. Na ce, to ko shigowar dare ya yi, bari na bari sai gobe na sake kira. Washegari har yamma Ja'afar bai kira ni ba, na kira bai dauka ba. Hankalinmu ya tashi ni da kawata babu abin da ba mu saka a ranmu ba. Na tabbatar mata sai dai idan Hajiyarsa ce ta hana shi fadawa Alhaji shi yasa bai dauki wayata ba. Sai Lamijo ta kira da layinta ya dauka da ta fara yi masa maganata sai ya katse wayar, da muka sake kira sai muka jita a kashe murus. Na yi ta kuka Lamijo na ba ni hakuri, ta shawarce ni na je na debo takarduna ta yi min alkawari zata tsaya min har sai na sami tafiya, domin mijinta yana ji da ita. Sai abin da ta ce kasancewar ba ta haihu ba har yanzu da ita ake cin amarcin, kasa-kasa da ita yake zuwa. Ta bani kudin mota na garzaya Dugge takarduna kadai na kwaso na ajiye wadancan kayan na dauko wasu kala uku, na kunso a jaka. Na sake barkawa Baffa karya, amma Sabitu na fada masa komai. Da farko ya tsorata ya ce, kada na je kasar Turawa su kashe ni. Na yi dariya kawai, na san rashin wayewa yake damunsa. Na jaddada masa insha Allah ba matsala zan je lafiya na dawo lafiya, sai ya yi min addu'a Allah Ya ba ni sa'a. Na dawo Gombe a ranar, na kawowa Lamijo takarduna, daman ta gama fadawa mijinta ya san da zancen. Da ya duba sai ya gyada kai ya ce, na cancanta a ba ni tallafi in je karatu dan na cinye jarabawata dukka. Sannan ya ce na yi photocopy na ba shi na ajiye original a wajena. Ta sake ba ni tabbaci na je na kwantar da hankalina komai zai dai-daita nan da watanni biyu zuwa uku komai zai kammala, za'a yi tafiyar. Sai a lokacin hankalina ya tashi yadda zan zauna har tsawon watanni uku a garinmu, wai! Abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Dama ya lafiyar Kura bare kuma ta yi hauka? Ni kam na san tawa ta kare, asirin da bana son ya tonu ne a kauyenmu shi zai tonu. Da muka kebe da Lamijo na shaida mata ni fa bana so na zauna da yawa a garinmu, don ban ce musu aurena ya mutu ba, ta ce, to na zo mu zauna a gidanta mana. Na ce, a'a ba zai yiwu ba, sai dai ta samo min aikin wanke-wanke da shara na yi, don na sami gidan zama har lokacin tafiya ya yi. Ta girgiza kai ta ce, ''Allah Ya sauwake na barki ki yi wanke-wanke da shara. A karshe dai muka tsayar da shawarar na zauna da mahaifiyarta, daman ba ta da karamar yarinya a gabanta, Lamijo ce *yar autarta tare suke zama, gashi ta yi aure ta bar ta ita kadai. Umma mahaifiyar Lamijo ba ta ki ni ba da muka je, sai ta amince na zauna tare da ita, unguwar Herwagana gidan ya ke. Ai kuwa ba ta yi da-na-sanin zuwana ba, na zame mata abar alfahari, bacci ne kadai bana yi mata, amma ko tsinke bana barinta ta dauke. Bayan zuwana da sati biyu na ga ya dace na je gida na sanarwa Sabitu kada ya ji shiru ban dawo ba ya dauka Turawa sun sace ni ya fito da maganar. Na shirya na tafi Dugge, na zaunar da shi na ba shi labarin halin da ake ciki. Ya ji dadi da ganina, don gaskiya har ya tashi hankalinsa. Baffa kuwa karya dai na sake shimfida masa, na ce AbdulBasi ya dawo zan koma Kaduna, kuma ina tunanin zamu kaura wata kasar nan da *yan watanni, zan zo na yi masa sallama idan dai tafiyar ta tabbata. Ya ce, 'To Allah Ya kaiku lafiya. Na zabgawa *yan gida karya na kwashi kayana dukka na nufi birni na ci gaba da zama da Umman Lamijo. Tafiya kamar zata yiwu kamar ba zata yiwu ba, sai da aka zarce watanni hudu ma, abinka da gwamnati kuma sai masu hanya. Na takaice muku ma dai sai tafiya ta fara shiriricewa kamar an fasa. Hankalina ya tashi na gigice, ga shi an ce lokacin karatu ya karato, idan ba mu je akan lokaci ba sai dai mu bari sai wata shekarar. Na sankare a kwance ina kuka, ina tunanin yadda zan koma garinmu na ci gaba da rayuwa. Na rame kai ka ce ban taba cin lomar tuwo bakina ba, rama da koke-koke ma sai sanda MAKWABTANA a nan Gombe suka sake banka min wata kullalliyar. 'kamar ya ya, a nan Gomben kika yi MAKWABTA har suka kulla miki kullalliya? Abdul-Sabur ne ya tambaye ta cike da takaici. Umaimah ta yi murmushin karfin hali, sannan ta zubo da hawaye ta yi sauri ta sa hannunta ta goge, ta ci gaba da cewa. 'Ina zaune da Ummar Lamijo lafiya cikin jin dadin juna ba tsangwama ta lura dai ina cikin damuwa don idan na zauna sai ta ga na yi tagumi. Cikin dare idan ta farka sai ta gan ni a zaune, kwanciya ta gagara sai shesshekar kuka. Ta dinga yi min nasihohi, ta ce na yi tawakkali na yi hakuri komai mai wucewa ne. Ta yi ta shawarta ta na dinga shiga gidan Salame makwabciyarsu ita ma dai duk sa'armu ce, kawar Lamijo ce sosai kafin ta yi aure, kullum tana shiga tana hira, sai na cewa Ummar Lamijo a'a zan dinga zama a gida ni kadai. Ita kuwa Salame tun farkon zuwana ta ke ta nacin na dinga shigowa gidanta idan ta shigo gidan. Ko ta yi ta aiko *ya*yanta wai na zo zata yi min wata magana, hankalina ya tashi na suri gyale a gigice na je, sai na iske daman ba komai zata fada min ba, hira kawai ta ke so mu yi. Sai na dan zauna mata kadan sannan na tashi na shigo gida. Kamar da hantsi idan mijinta ya tafi aiki yaranta suka tafi makaranta, Umma ta shiga daki baccin hantsin da ta saba, da yake ta manyanta tana shan magungunan ciwuka kala-kala. Sai na dauki gyalena na shiga gidan Salame mu yi ta hira, hirar ma ta Lamijo ce kawai don babu wani wanda muka sani tare, bayan Lamijo. Sai na ga tana ta bugun cikina tana so ta ji ni budurwa ce ko bazawara, ni *yar uwarsu ce ko kawa ce, na kauro Gombe gaba daya da zama ko zan koma garinmu? Bana ba ta amsa sosai, don haka ba ta san komai nawa ba, idan taga kamar bana so sai ta canza hira, mu koma hirar makaranta. Na fara sakin jiki da Salame, dimbun damuwar da nake ciki ta ragu saboda tana dauke min kewa. Daga na shiga gidanta sai ka ga ta tare ni da murna, ta yi ta kawo min kayan ciye-ciye, yadda, yadda ku kasan ta ba ni babu. Na ji dadi da zama da Salame, na yi farin ciki da Allah Ya bani madadin Matawata kawata, kuma makwabciyata mai sona. Duk sanda zan je gidan Lamijo tare da Salame muke zuwa, ta sa mijinta ya kaimu, ina baya suna gaba ana ta hira. Umar sunansa, mutum mai yawan fara'a da son hira, har Lamijo ta ke zolayarmu wai kada fa mu didare mu barta da zagayen baranda, ma'ana kada dukka kawayenta ne a dalilinta muka san juna, kada mu hade kai mu ware ta, don ta ga shakuwar ta kai shakuwa. Wata rana da daddare muna kwance a tsakar gida ni da Umma, sai muke ta jiyo hayaniya a tsakanin Salame da mijinta Umar su ma a tsakar gidansu, da yake katangarmu daya da su. Hayaniya sai karuwa ta ke yi, har yana cewa sai ya sake ta. Na dafe kirji na tashi zaune, Umma ma ta zauna muka shiga fargaba. Ta ce, kafarta ke ciwo naje na ba su hakuri, na je na ce inji ta ta ce su daina. Na saka gyalena jikina yana rawa har naje bakin kofa na juyo, na zo na durkusa a gaban Umma. Na ce, 'Umma ki daure ki zo mu shiga tunda babu nisa, ki yi musu magana da kanki za su fi ji tunda ke babba ce, na ga kamar fadan ba karami ba ne, tunda na ji dukkansu ransu a bace yake, kada ayi batacciya. Ta ce, 'To dauko min gyale na a daki. Na shiga da sauri na dauko mata ina rike da hannunta muna doddogarawa har muka isa cikin gidansu. Muka iske su kaca-kaca kowa ido yayi masa jajawur, baki yana kumfa da alama sun kai kololuwar bacin rai. Yaransu suna ta kuka ga wayoyinsu a kasa duk sun farfasa. Umma tayi musu tsawa cikin ba cin rai ta shiga yi musu fada tana nuna musu ba su kyauta ba. Budar bakin Umar ke da wuya, sai ya ce 'Yauwa ga Umaimar ki maimata abin da kika ce a kanta, ni kuma na shiga daki na dauko kur'ani mu yi alwala mu dukka ukun mu dafa, Allah Ya wargaza mai karya.MAKWABTAKA 22 Sai na ji wata gagarumar fargaba yadda ku ka san zuciyata zata fito waje. Na dafe kirji cikin rawar jiki da rawar murya na tambaye su, ''Lafiya, me na yi? Sai Salame ta aiko min harara sama da kasa, ta murguda baki ta sake gyara damarar da ta yi ta shirin dambe. Ta ce, ''Kai da ita dukka munafikai ne, bakinku daya, ko me zaku fada min ba zan yarda ba, amanata kuke ci. 'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Allahumma ajirni fi masibatin wa akhlif ni khairan minha. Addu'ar da na fara fada ke nan a bayyane, yayin da na dafe kirji da hannu daya na rike kai da hannu daya. Kan ka ce kwabo na rikice da kuka, yayin da Umar ma ya fara hawaye don haushin kazafin da ta yi mana. Umma ma ta fusata ta ce, ''Duk ku yi min shuru, Salame wacce hujja gare ki ta cewa suna cin amanarki? Salame ta rike kugu tana girgiza idanunta mursisi babu ko digon kunya, ta dube ni ta juya ta dube shi. Ta ce ''Ga su nan da ran Allah ba zan musu karya ba, ko a gabana ko a bayan idona ba su da buri irin su ga junansu su yu hira. Bini-bini sai ta shigo in ta ga yana nan haka sai ta tarki cewa zata je gidan Lamijo, shi kuma sai ya ce ku shirya in kai ku. Ta madubi ma lekenta yake sai kuma ga lambarta a wayarsa daga ta yi flashin sai ya kira, ya fice kofar gida ya yi mata waya. Kila ma suna haduwa a wani wajen... Ba ta rufe bakinta ba sai na rusa kuka na ce, ''Tsakanina da ke Salame sai Allah ya isa, kin yi mana kazafi don ni ban taba sanin kalar lambar Umar ba, ba mu taba waya da shi ba...'' Umar ya dube ta cike da takaici, ya ce, ''Salame, ki ji tsoron Allah, ke makira ce, kuma idan ba ki nemi gafarar wannan baiwar Allah ba baza ki gama da duniya lafiya ba. Zato kike yi kawai saboda shaidan ya yi miki huduba a zuciyarki. Waya kuwa da kika ji ina yi ba da wata nake ba illa kanwar abokina da aka turo bautar kasa a nan Gombe daga Kano, ba tasan kowa ba a nan na hada ta da wata mata ma'aikaciyarmu ta samo mata gidan haya ta zauna. Sunanta Aisha babu abin da ya hada sunan Umaimah da nata. Sai Salame ta sake rikicewa wai ita za mu mayar *yar iska, marar wayo shi yasa kwana biyu idan zata dauki wayata sai ta ga bana so, don kada ta ga lambarsa ne. Takaici ya sa na fice ina sharbar kuka, na bar Umma da sulhu. Ina shiga daki na fada kan katifa ina rusa kuka, wayata ce ta yi kara, sai na ga lambar Lamijo. Gabana ya sake faduwa, na san labari ya isa gare ta. Na danna a sanyaye ina sauraron abin da zata fada min, zagi ko kuwa rarrashi? Na ji ta cike da fara'a sai ta ce min, ''Albishir! Albishir!! Albishir!!! Har sau uku. Na tashi na goge hawaye na dafe kirji na kagu na ji abin da zata fada min. Ta ce, ''Tafiyarku ta tabbata, an gama komai. Ki shirya gobe ke da Hanif inji Alhaji mijina zai kai ku Abuja ku yi passport da takardunku na ainihi (original) za ku kai federal ministry of education da autentication. Sai na yi ajiyar zuciya mai dadi, na kumshe ido, na zabura na ce, ''Da gaske kike? Alhamdu lillah ke da mijinki Allah Ya saka muku da gidan aljanna. Na gode, na gode. Godiya nake yi mata har ta gaji da amsawa ta kashe wayar, sai na ji zuciyata ta dan yi sanyi daga tafasar da ta ke yi. Na tashi zumbur na fara hada *yar jakata ta tafiya, duk da ba ta fada min kwanaki nawa zamu yi ba, na san dai dole zamu kwana don haka kaya kala biyu na dauka, da katuwar ambulan da na saka takarduna na makarantun da na yi (original certificate). Umma na shigowa na tare ta da farin ciki, na fara shaida mata abin da Lamijo ta fada min yanzu. Sai ta tabe baki ta harare ni. Ta ce, ''Ni ba a zaman munafunci da ni da cin amana, biri ya yi kama da mutum, kwana biyu sai na jiyo ki a daki kina ta waya wanda a da ba kya yi. To ni lafiya nake zaune da MAKWABTANA ba zaki zo ki raba ni da su ba. Idan kin san irin haka zaki yi ta yi, to ki hada kayanki ki yi gaba, shegen kwashekwashe ne da yarda irin na Lamijo ta kwaso ki daga cewa wata daya an shude watanni uku.. Ba ta rufe bakinta ba, sai na ji jiri ya kwashe ni don tashin hankali. Na laluba bango na jingina na zauna na rike kai da hannayena biyu na takure ina ta addu'a Allah Ya yi min agaji, dan na shiga garari, na shiga masifa. Ba ni da mafita sai Allah ne kadai zai fitar da ni. Na kasa magana don ba ni da bakin da zan yi mata bayanin komai ta yarda da ni. Ba ni da masaniya a bisa wayar dare da ta ce ina yi, bayan Lamijo babu mai kirana a duniya, ni ma ita kadai nake kira. Sabon layi ne na siya saboda MAKWABTANA da kawayena na Kaduna suna ta kirana suna yi min maganar Abdul-Basi, wacce ta ke tayar min da hankali, don haka na karya layin na watsar.... Umaimah ta ci gaba da sharce hawaye. Abdul-Sabur ya sake luntsomowa cikin tausayinta, kallonta kawai ya tsaya yana yi, yayin da zuciyarsa ta ke suya tana konewa. Yayin da Faduwa ce mai karfin halin yin magana. Fadi ta ke, ''Allahu Akbar! Sannu yarinya, kin sha takaicin rayuwa ashe. Umaimah ta cije lebe ta kasa ci gaba da magana, har sai da ta dauki lokaci mai tsawo ta yi ajiyar zuciya, ta ci gaba da cewa. ''Rayuwa ke nan tana da wahala, fatanmu dai mu gama da duniya lafiya. Yaro ya ji dadi idan na tuna sanda nake karama ban san bakin ciki ba. Ga uwa ga uba, ga *yar uwa, ga dan uwa, ga kawa ga saurayina. Ba ni da aiki sai rawa da waka, walwala da nishadi kullum amma dubi lokaci guda Allah Ya kwace duk wannan farin cikin ya koma kadaici, ku san kowa nawa ya kare, ba ni da komai, ku san kowa ya tsane ni. Allah mai yadda Ya so da bayinSa. Na gode maSa a kowanne hali Ya bar ni a ciki. Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Kinyi gaskiya yarinya, Allah Yana jarrabar bayinSa ta kowacce hanya. Ki ci gaba da tawakkali Allah Zai yaye miki komai da izininSa, Ya hada ki da madadinsu, Ya dawo miki da wasu daga cikin farin cikin da kika rasa. Umaimah ta gyada kai cikin gamsuwa, ta ce, ''Haka ne, na gode. Faduwa ta ce, ''Yaya na ga kuna kokarin kammala labari alhalin ba ki gama ba mu karshen labarin ba. Yadda aka yi kika zo Malaysia da rabuwarku da su. Umaimah ta ce, ''Ai kawai na fuskanci Ummar Lamijo ta gaji da zamana so ta ke ta kore ni, *yar ce take tausarta kullum. Na shiga daki na kwanta babu barci, sai tunani da kuka har asuba. Na tashi na shirya da sassafe ina jiran isowar Hanif da Babansa. Karfe bakwai da rabi a cikin gidan ta yi musu, suka iske Umma a zaune a tsakar gida, ni kuma na gama shara ke nen. Muka gaisa da su na dauko jakata na rataya na durkusa na yiwa Umma sallama ta amsamin da kyar. Sai ta dinga fada tana sake nanatawa 'a yi dai a hankali, kuma ko me mutum zai yi yayi bisa amana. Da alama dai surukinta bai fahimce ta ba, amma ni na fahimci abin da ta ke nufi, tunda na zama maci amana zan kwacewa Lamijo miji ke nan. Shi kuwa bawan Allah hidima yake yi min saboda dansa da matarsa da yake matukar son abin da su ke so. Muka tafi hanyar Abuja cikin hadaddiyar mota CRB ruwan zuma, sabuwa ce Gar! A ledarta, sai kamshi da sanyin AC ke tashi. Hanif da mahaifinsa suna ta farin ciki annuri fal a fuskarsu, ina baya ina yake da kyar nake kakalo hira da dariya, amma fa hawaye na ke sharcewa a boye. Ba mu karasa Abuja ba sai Lamijo ta kira shi, ta dinga zazzaga magana cikin daga murya, sai na ga ya kalle ni ta madubi yayin da ya ce bari zai kirata idan mun isa, yana tuki ne. Ya yi sauri ya katse wayar, tun daga lokacin na ji ya daina magana, da alama ransa ya baci, jikinsa ya yi sanyi, sai na shiga fargaba kada fa zuga Lamijo suka yi ta shiga zargina. Kai tsaye muka wuce Federal ministry of education daga shigarmu Abuja, ba mu bi layi ba muka bibbiya aka buga mana tambari a jikin takardunmu (stamp) shaidar zamu yi karatu a kasar waje. Sannan muka wuce Ministry of forin affairs suma kai tsaye ya wuce da mu kasancewar yasan wasu daga cikin ma'aikatan don ya yi aiki sosai a wurare daban-daban a nan Abuja. Kafin la'asar har mun gama ya wuce da mu gidansa, da yake unguwar Asokoro. Gida ne babba da get ga wajen ajiye motoci, manyan faluka biyu da wajen cin abinci (dinning area), dakuna hudu kowanne da bandakinsa sai katon kicin guda daya. Mai aikinsa inyamuri da matarsa a boy's kuarters, su ne masu share gidan. An share tsaf an goge, an yi mana girki an jera akan tebur dan sun san da zuwanmu. Muna shiga Alhaji ya nunawa kowannenmu daki daya nasa da bandakai a ciki, kowannenmu ya shiga don ya kimtsa kamar wanka da sallah. Da muka idar muka fito dinnin table don cin abinci saboda muna jin yunwa. Kunyar Alhaji da ladabi ya hana na zauna akan teburi daya mu ci abinci, suka yi ta rokona na ki hawa mu ci, sai Alhaji ya ce, Hanif ya zuba min ya kai min dakina. Na shiga daki na ci abinci yayin da nake jiyo hirarsu a falo. Can na ji Alhaji yana Magana a waya yana cewa. ''Lamijo me yake faruwa ne, wai Umaimah ba kawarki ba ce? Waye ya zuga ki? To ni gaskiya bana son haka, kuma tafiyar nan kamar ta tafi ta gama tunda an gama yi mata komai. Idan kinga ba ta tafi ba to Hanif ma ba zai je ba ke nan. Haba me yasa ku mata ba ku da tunani ne? Tunda abun naki har da zargi to bari na bar gidan na je hotel na kwana. Na bar ta da Hanif su kwana, gobe zamu dawo da sassafe har mun gama abin da zamu yi''. Inji Alhaji yake karadi a waya shi da matarsa, kawata, aminiyata Lamijo, a kokacin da take tuhumarsa, ta ke zargin kada ya ce yana sona ko mu ci amanarta a Abuja. Sai na dafe kirji na mike tsaye yayin da na ji tamkar ba a raye nake ba, dama na hadiyi zuciya na mutu mana na huta. Anya kuwa lafiya irin wadannan bala'ai suke ta rufto min? Duk mutumin da na amincewa sai ya ci amanata. Na tambayi kaina da kaina, yayin da nake magana a bayyane. 'Me yasa kowa ya tsane ni yanzu alhali kuwa ada kowa yana sona? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Na durkusa ina fada yayin da kuka ya hana ni sakat, na kasa ci gaba da cin abincin, ga yunwa ina matukar ji ko abincin safe ban ci ba, sai dan lemo da Alhaji ya siya mana a hanya. Hanif ne ya yi ta kallonsa a falo yana ta nishadinsa, amma ni kadai a dakina ina ta juyi babu barci saboda gagarumar fargaba da kunar zuci. Yadda na ga dare haka na ga safiya na tashi da wuri na yi wanka na takure a lungu gado. Hanif ne da sassafe yake buga min kofa, wai na fito na zo mu karya kumallo, Babansa ya yi waya ya ce mu shirya da wuri ga shi nan zai zo mu wuce Gomben. An shirya mana abin karin kumallo na gani na fada an jera akan dinnin table. Tura abincin nan kawai nake yi a cikina ba don ina jin dadin ci ba, sai saboda kada yunwa ta kashe ni ko kada Hanif ya gane ina cikin halin damuwa. Hira kawai yake yi min cikin farin ciki da dokin zamu je Malaysia, sai ya ce da ni ya ga kamar yanzu ban damu ba alhali a da har na fi shi dokin tafiya. 'Eh ko 'a'a kawai nake ta binsa da shi har muka kammala, sai muka ji tsayuwar motar Alhaji ya iso. Ya aiko ya ce ace mu fito ba zai shigo ba. Muka debo kayanmu muka fito muka iske shi a zaune a cikin mota, gaba daya ya daina wannan fara'ar tasa. Cikin sanyin jiki na gaishe shi ya amsa min cikin sanyayyiyar murya, muka shiga mota muka tafi. Hanif ne kadai mai walwala da surutu ni da Babansa dai to ga mu nan ne dai kawai babu mai son yin magana. La'asar sakaliya suka sauke ni a kofar gidan Umma na yi musu godiya da sallama na shiga gida su kuma suka wuce. Na yi mata sallama, fuskarta babu fara'a ta amsa min, na shaida mata mun iso, ko ta kalle ni ma ta dauke kai. Sumi-sumi na shiga dakina sai na firgita da na ga an hada min dukkan kayayyakina da na baza a gidan a lungu daya. Kamar takalmana, sosona daga bandaki da dai sauransu. Katifar da na lallaye da zanin gado an jingineta a tsaye. Daga nan jikina ya ba ni zamana ya zo karshe a gidan nan, don haka na shiga tunanin inda zan nufa, Abu na farko da na fara yi shi ne, na ware kayan da na fi so kamar kala biyar na bar sauran don ban san yadda zan iya kinkimar rusheshiyar akwatin nan na shiga gari ba. Na zuba a karamar jaka, soso, brush da makilin gami da takalma kala biyu. Saura na dura su a cikin babbar akwatin na rufe na jingineta a gefe. Na shimfida katifar na hau na zauna a hankali. Ina cikin fargaba musamman da na ji tahowar Umma. Tana shigowa sai ta harare ni ta harari katifarta da na shimfida ta tabe baki ta ce, ''Umaimah, yanzu dare ya yi idan Allah Ya kaimu gobe ki shirya da sassafe ki koma garinku ki jira fitowar tafiyarku a can. Bana son zamanki a gidan nan tunda kin fara jawo min fitina, ina tsoron rayuwa, musamman *yar autata da nake son dorewar zamanta a gidan mijinta. Ta zaci zan razana da maganganunta sai taga ko kadan ban rude ba. Na ce mata, ''To Umma Allah Ya nuna mana goben lafiya, na gode ma da karamcin da aka yi min, Allah Ya saka da alkhairi''. Ta fice a fusace, tana fita hannuna yana karkarwa sai na kira Lamijo don na sanar mata gobe zan koma gida. Na yi mata godiya da sallama na roketa idan tafiyarmu ta zo ta sanarmin ta waya. Don na ga akwai waya a Dukku zan dinga fitowa ina kiran ta kullum ina jin labarin tafiya. Sai taki amsa wayar, har ta fara katsewa (rejecting), ina kira sai ta katse. Muka dinga haka fiye da sau goma, mamaki cike da zuciyata. Daga karshe sai na tura mata rubutaccen sako na yi mata duk wadannan bayanai. Har gari ya waye ba ta ba ni amsa ba. Na daina kuka saboda masifar ta yi masifa, addu'a kawai nake yi ina neman mafita, ina so Allah Ya musanya min da muhallin da ya fi irin wanda nake ciki daraja da kwanciyar hankali. Na shirya na fito rataye da karamar jakata na bar babbar a dakin. Na durkusa a gaban Umma na gaisheta.. Na ce, ''Zan tafi Sai ta hararenim ta ce, ''Ban ganki da kaya ba? Na yi murmushin takaici, na ce, ''Zan je na samo mai tasi ne yanzu zan dawo. Ta tabe baki ta ce, ''Kina da kudin motarko? Na yi murmushi na ce, Eh Ban sani ba ko idan na ce ba ni da shi zata ba ni ne ko ba banin zataiba, oho. Ba ni da kudin kirki a jakata, *yan canji ne kawai wanda bai wuce ya kai ni tasha ba.MAKWABTAKA 23 Ina fitowa na ci karo da Salame da mijnta Umar, har yau inajin haushin kallon banzar da ta yi min, ta yi tsaki da tsartar da yawu ta bude gaban motar mijinta ta zauna, ta daka masa tsawa. Ta ce, ''Ja mu je mana, wa kake jira? Ya fisgi mota ya tafi suka bar ni, sai a lokacin na fara kuka. Ina tsaye a kofar gida na dubi gabas da yamma, kudu da arewa ban san inda zan nufa ba. Na yi ta tafiya da kafa na nufi hanyar tashar garinmu da nisa sosai, amma da kafa na je. Sannan na tuna ba ni da kudin da zai kai ni garinmu. A bakin tasha a kofar shagon wata tsohuwar mata mai siyar da abinci da ma'aikatanta da yawa, na zauna na huta. Sannan na karasa gabanta na durkusa a gaban Hajiyar na gaishe ta ina hawaye, na sanar mata ina so na dinga tayata aiki, na ce amma ba ni da wajen zama. Da farko ta ki amincewa, amma da kawarta ta ce, ''ki dauki kyakkyawar yarinyar nan ko don saboda ita ma za ki sami samu masu saya kin san mazan nan suna da son kyawawa. Ai wannan yarinyar kadara ce kar ki bari ta kubuce miki. Sai na ji zuciyata ta harba, na kasa gane abin da matar nan ta ke nufi. Nan da nan Hajiya babba ta yarda ta umarce ni da na shiga cikin shagon da kayana, sai da magriba suke tashi sai mu dunguma mu tafi gida. Na shiga shagon kujeru ne da tebura yayin da duk masu dafa abincin sun yi kama da karuwai, suka hau yi min kallon banza saboda hassada. Dana ajiye jakar kayana a loko sai na koma bakin baranda na hau kan benci na zauna, jikina sanyi kalau. Daya daga cikin ma'aikatan ce ta yi min tsawa wai na zo na karbi abinci na mika ciki, ina ganin masu siya suna ta shiga ciki na sami waje na zauna. Sai na tashi jikina yana rawa na karbi farantin abincin na shiga ciki ba tare da na san wanda zan ba wa ba, maza ne dankar a ciki. Kallona suke sama da kasa, duk da na yafa gyale. Amma sai duk na tsargu. Nan da nan na juya waje na koma wajen matar da ta aiko ni na ce wa zan ba wa? Ta harare ni ta ce, ''Ki ce ina Ali Ali mai mangyada? Sai na koma ciki muryata na karkarwa na tambaya, sai ya yi dariya ya ce, ''Zo nan *yar shila, ga ni nan. Zagayo nan. Na je na ajiye a gabansa sai na ga ya kawowa hannuna cafka, na yi sauri na zame, sai suka kwashe da dariya shi da abokansa. Su ka ce, ''Wannan sabuwar zuwa ce dai ko? Shi yasa ba ta san dawan garin ba. Ali Ali ya ce, ''Haka ne, bakuwa ce dan ko jiya ma na zo ba ta nan. Ke yarinya ki saki jikinki da mu, mune masu yi muku ciniki, gara ma ki saba da mu don a jikinmu zaki sami abin duniya, don shi kika fito nema. Idan kuwa kina bukatar manda sai ki bayar da gishiri. Yana maganar yana kanne min ido kamar tsohon maye. Na shiga zargin anya kuwa ban fada mugun hannu ba? Anya ba a cikin karuwai nake ba? Ai kuwa sai na tsinkayo maza suna kaiwa mata cafka, duk wacce ta zo ajiye abinci sai na ga maza suna wawurarta. Da aka ce na zo na kai abinci a karo na biyu sai na sake lullube jikina na dauki farantin abincin na mikawa wani Alhaji mai katon ciki da gemu, ga shan taba. Yana ganina sai ya zabura ya ce, ''Wai Allah! Wannan halittar fa daga ina? Lallai Hajiya ta yi tsintuwa mai kyau. Ta zo mu yi magana ko nawa ne zan biya don na samu wannan yarinya. Ya dinga dagamin gira alamar iskanci tsantsa a kansa. Rana ta yi aka ce na je na zubo abinci da zai ishe ni na zo na ci akan baranda. Ina kusa da Hajiya babba ta shiga yi min nasiha da lallashin cewar, na kwantar da hankalina na saki jiki da abokan cinikayyarmu. Na kasa gane me ta ke nufi, in bari maza su ringa taba ni yadda suke tattaba sauran ko me...? Abdul-Sabur ya girgiza kai yayin da takaici ya hana shi magana, sai cika yake yana batsewa kai ka ce shirin dambe yake yi. Faduwa kuwa salati ta ke yi tana zabura tana dafe kirji. Umaimah ta langwabar da kai, ta ce, ''Da na idar da sallar la'asar sai na rataya jakata na zo na durkusa a gaban Hajiya babba. Na ce, ''Ki ba ni kwatancen gidanki zan je na sanarwa uwar dakina cewar na sami aiki a wajenki'' Ta girgiza kai ta ce, ''Mai zai hana ki bari sai gobe ki je da wuri zai fi sauki. Na girgiza kai na ce, ''To, bari na yi sauri na je na dawo kafin ku tashi a nan kusa ne unguwar. Ta ce, ''To ajiye jakarki mana, tunda yanzu za ki je ki dawo. Na rasa wannan wayo na matar nan, ko da yake bai kamata na yi mamakin gogewarta akan hikimomi irin haka ba, tunda ta manyanta, kuma gashi idanunta a bude suke tas! Na ce, ''Ai kayanta ne zan mayar mata na debo nawa, ban zaci zan sami aikin ba zuwa dai na yi na tambaya, yanzu da na samu shi ne zan je na sanar mata. Ta ce, to na je na dawo da wuri, na sauke ajiyar zuciya da na ji ta ambaci haka, na tashi jikina yana bari kai ka ce cafko ni za a yi, sai sauri nake yi kamar zan kifa ina yi ina waiwayen baya. Na haye acaba don ina tunanin kudin jakata zai ishe ni na biya shi. ''ina za ki je? Inji Faduwa. Umaimah ta ja fasali, ta ce, ''Wallahi ban sani ba, sai da mai acaba ya fara tafiya yana tambayata ina zai kaini? Fiye da sau uku sannan na fara tunanin inda zan je. Can na ce, ''Ka kai ni ma'aikatar ilimi (ministry of education). Koda ya tambaye ni wacce unguwa ban sani ba. Sai ya ce, ''Koda yake ita ce dai guda daya, bari na kai ki can... Abdul-Sabur ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Me zaki yi a ministry of education? Tambayarsu zancen tafiya zaki yi? Ta girgiza kai, ta ce, ''Na san mijin Lamijo a can yake aiki, sannan ne ina fadar sunansa za su san shi, wajensa zan je na tambaye shi ranar tafiya. A bakin get dan acaba ya ajiye ni na biya shi na shiga ciki a tsorace, ina tsoron kada a koro ni ko ace min ba nan yake ba. Har kasa na durkusa na gaishe da masu gadi, daga dukkan alamu sunji dadin gaisuwar da na yi musu, suka amsa cike da fara'a. Na tambaye su shi da cikakken sunansa Alhaji Nasir Nafada. Sai suka ce ''yana ciki ga motarsa ma bai tashi daga aiki ba. Na ce, ''Ina ne ofisshinsa? Suka fara kwatanta min da hannu, sai suka fuskanci ban gane ba, daya ya taso da sauri ya ce na biyo shi a baya zai kai ni can. Akan bene yake can ciki, ya kai ni har cikin ofishin gami da sanar masa, ''Alhaji ka yi bakuwa. Yana dago ido sai ya ga ni ce, don haka sai na ga ya dan firgita kuma ya cika da mamaki. Ya ambaci sunana, sannan ya ce na shigo ga kujera na zauna. Na yi wa maigadi godiya ya fita ya rufo mana kofa. Maimakon na zauna sai na durkushe a gabansa na barke da kuka mai tsanani ina magana, amma kuka ya hana ni ya fahimce ni. Ya tausaya min matuka, hankalinsa ya tashi, har kwalla ta cika masa ido. Rokona yake na tashi na zauna, na daina kukan na nutsu.. Da kyar na tsagaita da kukan na tashi na zauna, shi ma ya zauna a tasa kujerar yana ta ba ni hakuri cikin Fulatanci muke magana, shi ma bafillace ne. Da kansa ya ce, ''Duk na san halin da kike ciki Umaimah, wannan abu da ya faru da ke kulalliya ce aka hada miki, kawarki Lamijo zuga ta aka yi amma ita ai mai sonki ce. Na sharce hawaye na ce, ''Ummarta ma ta kore ni daga gidanta shi ne na zo na shaida maka bana gari zan koma Rugarmu Dugge, ga shi babu waya balle na ji ranar tafiyarmu. Ko zaka fada min takamaimai ranar da zamu tafi na dawo, ko kuma na karbi lambarka idan har ba zai zama matsala ba na dinga fitowa daga Dugge na zo Dukku na dinga kiranka ina jin labarin tafiya? Sai ya girgiza kai don tausayi, ya yi shiru yana kallona, har tsawon wani lokaci mai tsawo. Can ya dauko wayarsa ya buga, sai na ji ya ambaci, ''Ranka ya dade permanent sectery na kira ne game da maganar tafiya karatun yaran nan Malaysia. Ka ce a cikin satin nan ne wacce ce takamaimiyar ranar tafiyar? Saboda akwai yarinya daya a nan *yar Dugge ce, zata koma Ruga ba su da waya balle ta sani ta fito. Sai ya ce, ''Rana ita yau ne tafiya, talata, amma ranar ake so su hallara a Gombe za a dibe su a mota a kai su Abuja su kwana litinin a sake tantance su a can, sannan talata su wuce. Da ya gama wayar ya yi min duk wadannan bayanai, sai naji sanyi a zuciyata, kamar zanyi tsalle. Sai a lokacin ya ga fara'ata shi ma da alama ya ji sanyi a ransa. Ya miko min lemo da ruwa ya ce, na sha ya shiga tambayata me ye takamaiman tarihin rayuwata? Na langwabe kai na ba shi tarihina kakaf da inda na hadu da matarsa har zuwa rana irin ta yau da muka rabu da ita, wanda bansan dalilin rabuwarmu ba. Sai ya girgiza kai ya ce, ''Na tausaya miki Umaimah, ki yi hakuri Allah Yana bayan mai gaskiya. Ki yi min alkawarin idan kin je wannan kasar zaki kama kanki, ki rike mutuncinki, ki yi abin da ya kai ki, ki dawo gida lafiya. Idan kika yi haka insha Allah sai kin fita daban da *yan rugarku. Sai kin zama abar kwatance a garinku, zaki zama abar alfahari ga gwamnatin garinmu. Idan kika yi min wannan alkawari zan ji dadi, kuma zan taimake ki kamar yadda dolena na taimaki dana na cikina Hanif. Sai na sulalo na durkusa a gabansa. Na ce, ''Allah Shine shaidata, idan na tafi can ba ka ganina Allah Yana ganina, na yi alkawarin zan kama mutumcina, abin da naje yi shi zan yi insha Allah Baba ba zan ba ka kunya ba. Sai ya ji dadi ya yi murmushi, ya ce na tashi na zauna. Na mike tsaye na duka na ce, ''Dare ya fara yi zan tafi garinmu don ba ni da inda zan kwana a nan. Ya ciro bandir din kudi mai yawa ya miko min, sai hannuna ya hau karkarwa don razana da yawan kyautar. Na yi godiya na fito akan ranar lahadi in fito da wuri na zarto gidan gwamna a nan zamu taru a yi mana jawabin karshe. Da na fito daga ofishin na duba kudin *yan naira dari-dari ne dubu goma ke nan. Tasi na hau ban kula masu acaba ba, na nufi Dukku daga Dukku na hau motar garinmu. Daga bakin garin acaba ne dole zai shiga da kai cikin rigagenmu. Ban isa Dugge ba sai bayan sallar isha'i, sai *yan gida suka yi mamaki da ganina a dai-dai wannan lokaci. Ba su firgita ba don sun ganni a nutse na, cikin farin ciki da tsarabata kala-kala. Sai da garin Allah Ya waye sannan labari ya kai ko'ina aka ce na iso. Masu zuwa sannu da zuwa suka yi ta shigo min, ina ta rabon lemon bawo da biredi, yara kuwa suna ta karbar alewa. Na zauna na korawa Baffa da matansa bayanan karyar cewar, an tura mijina AbdulBasi aiki kasar Turawa da ni zai tafi, wani satin ne tafiyar. Dama idan kun tuna can baya na fada masa zamu kaura daga kasar nan. Baffa ya yi murna ya yi mana addu'ar fatan alkhairi, yayin da matansa suka nuna hassadarsu kiri-kiri a fuska ba haka suka so ba. Labari ya cika gari cewar Umaimah da mijinta za su kaura Turai da zama, har zuwa kallona suke yi har da masu shafa jikina wai suma su kwashi albarka. Allah Ya sa suma wataran su je. Bakin ciki ya rufe Matawata, kawayenmu suka dinga fada min irin mugayen fatan da ta ke yi min, wai dama ace mijina ya sake ni ya fasa tafiya Turai da ni na dawo rugar nan na zauna na ganta da Ilah bakin ciki ya kashe ni. Na sake godewa Allah da Ya sa na rufe bakina ban fadi aurena ya mutu ba, masu jin dadin suna da yawa. Sabitu ne da ni a cikin dakinmu mun saka fitilar kwai a gaba da littafi kai ka ce karatu muke biyawa, nan kuwa hira muke yi ta sirri. Na ba shi labarin zamana a Gombe tas da duk yadda aka yi. Na ba shi labarin tafiyata nan da *yan kwanaki. Sai ya fara hawaye ya tausaya min akan kunci da na shiga da kazafi da aka yi min. Sai ya nuna fargabarsa akan wannan tafiya da zan yi kasar da ban san kowa ba, kuma ba ni da kowa. Yana tsoro kada na je na fada hannun muyagu su cutar da ni, ko halin mutuwa a rasa *yan uwana. Na roke shi da ya kwantar da hankalinsa insha Allah zan je lafiya na dawo lafiya. Ina so ya rufamin asiri, kada ya fadawa kowa gaskiyar magana, saboda idan Baffa ya ji ni kadai na tafi hankalinsa zai tashi, ga shi da hawan jini. Ranar lahadi da sassafe na shirya tafiya na fito na fara sallama da *yan cikin gida, sannan na lelleka MAKWABTA har wajen mahaifiyar Ilah na shiga da yake har goben tana sona. Ta rungume ni ta fashe da kuka. Matawata ta kama kugu tana ta girgiza ta cika taf don fushi kamar zata fashe wai don na shigo gidan. Tun zuwana sai a ranar na ga Ilah, sai dai na jiyo muryarsa daga cikin gidanmu. Ya kalle ni sau daya nima na kalle shi mu dukkanmu sai muka sunkuyar da kai kasa, tsoron matarsa ya hana ya yi min magana. Na fice na bar ta a nan ni kyankyami ma ta ba ni, duk ta kazance da wani kodadden zani daurin kirji, ba riga. Kanta buyaya ba dankwali ba kitso, gashin nan duk ya kakkarye, bututu jikinta da jar kasa don babu sumunti, haihuwa kawai ta ke yi ciki da goyo. A lokacin ma tsohon ciki ne da ita. Baffa da Sabitu ne suka rako ni har kofar fita daga gari, idan Sabitu ya kalle ni sai idanuwansa ya cika da kwalla. Ya ce da ni, ''Adda Umaimah za ki je lafiya ki dawo lafiya ki same mu lafiya a cikin izinin Ubangiji. Kada ki manta kin tafi kin bar ni ba ni da kowa sai tsohon nan, ba Yafindo, ba Nasiba yanzu ke ma babu ke.... Muka rushe da kuka mu dukka har Baffa. Can Baffa ya ce, ''Umaimah fatana a gare ki shi ne ki je ki dawo lafiya, Allah Ya kare ki daga sharrin makiya, idan kin dawo kin same ni a raye to Alhamdulillah, amma idan kin dawo kin iske na mutu to ki yi min addu'a, Allah Ya jikaina. Tsufa ya zo min, lafiya ta yi karanci a gare ni, don haka ina daf da tafiya. Na yafe miki duk abin da kika yi min a duniya. Allah Ya tsare ki Ya ba ku zaman lafiya ke da mijinki da zuri'a ta gari. Sai muka sake fashewa da kuka, na kankame Baffa na ji kamar na fasa tafiyar. Da kyar na sake shi na juya na fara tafiya zuwa bishiyar da masu acaba suke tsayawa. Ina waiwayensu suna tsaye a inda na bar su, kowannensu yana sharce hawaye yana daga min hannu.. Umaimah ta rushe da kuka yayin da ta kasa ci gaba da labarin. Hawaye ya cika idanun Abdul-Sabur da Faduwa su ma. Ta ci gaba da cewa, ''Na hau acaba ina ta rusa kuka, ban daina ba har na isa garin Dukku na shiga motar Gombe. Na isa gidan gwamna a kurarren lokaci har an yi nisa a taro da kyar aka bar ni na kutsa cikin masu tafiya. MAKWABTAKA 24 Mai girma gwamna ya yi mana jawabai masu dadi gami da nasihohi masu ratsa jiki cewar mu yi karatu sosai mu ci jarabawa, babu ruwanmu da shiga kungiyar *yan iska, mu kama kanmu mu rike mutuncin garinmu da kasarmu. Sannan ya yi mana yayyafin albishir cewa kowanne dalibi daga cikinmu mu dari daya cur maza tamanin mata ashirin ya biya mana zunzurutun kudin makaranta har na tsawon shekaru ukun da zamu yi mu kammala karatun digiri dinmu. Sannan an budewa kowannenmu account a banki duk karshen wata za a dinga turo mana da kudin abinci da gidan haya, har dalla dari biyar. Sannan aka raba mana na'ura mai kwakwalwa (laptop) kowa daidaiya kauta. Iyayen yara suka yi jawabin godiya, yayin da aka yi addu'a aka tashi kowa ya je ya yi sallama da iyaye da *yan uwansa, yayin da ni da Hanif muka yi wajen Babansa. Ya ji dadi sosai da isowata, amma ya tambaye ni ina akwatin kayana, sai na nuna masa jakata a rataye a kafadata na ce, ba ni da jaka sai wannan kaya kala uku ne a ciki, sai tarkacen kayan kwalliyata da hotunana da takardun makaranta. Sai ya tausaya min, ya ce ni idan muka isa Abuja zai fadawa abokinsa wanda su ne jami'an Gwamnatin da za su raka mu har can Malaysia zai ba shi kudi ya sissiya min akwati mai taya karama, wacce ake ja da suturu na tsukewa wadanda ba atamfofi ba, don kada na fita daban. Sannan ya kara da cewa, 'iyaye sun karawa *ya*yansu kudi da zasu dinga kashewa, don haka zan baki kudi daidai da yadda zan ba wa Hanif ku dinga kashewa har shekara. Ku bude account a banki daban ku turo min da account number zan sakawa kowannenku naira miliyan daidaiya, zan canja muku zuwa dallar. Sai na durkushe a gabansa ina kuka ina ta godiya Hanif ma sai ya durkusa ya yi godiya. Abdul-Sabur ya buda baki don mamaki, ya ce, ''Allah Sarki bayin Allah ba sa karewa a duniya. Faduwa ta ce, ''Lamijo matarsa kuwa ta sani? Umaimah ta goge hawaye ta ce, ''Ba ta sani ba, don tun lokacin da ta fara nuna kishi da zargi ya nuna ya cire hannunsa daga kaina, ya nuna mata Hanif ne kawai zai tafi. Ya gargadi Hanif kada ya fada mata da ni za a tafi. Alhaji. Rabi'u ya hadamu da abokinsa Alh. Sani ya dinga kula da mu, daga Abuja har Malaysia. Ya ba shi kudi mai yawa ya rike muma ya ba mu dallar dari bibbiyu mu rike a hannunmu kafin mu gane gari mu fara kashewa. Muka dunguma cikin birnin tarayya a cikin zungurazunguran mota (bus) mai sanyin A.C ta gidan gwamnati. A hadadden hotel aka sauke mu a Abuja, mata dakunansu daban mu uku-uku, maza ma dakunansu daban. Washe gari aka kai mu Embassy inda aka sake tantance mu kowa da takardunsa (original) a wajensa, da takardunmu da aka turawa kowa daga makarantarsa a Malaysia (admission letter), babu wanda ya sami matsala, aka mayar da mu hotel muka sake kwana. ''Kin yi kawaye amma daga cikin *yan matan nan dai ko, kuna hira? Faduwa ta tambayi Umaimah. Murmushi Umaimah ta yi, ta ce ''Ai tuni na sawa raina babu ni babu duk wani bil'adama a duniya, mace ko namiji, yaro ko babba. Abdul-Sabur ya tuntsire da dariya ya ce, ''Ba ke babu bil'adama sai jinnu? Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai gara na hadu da jinnu da na hadu da bil'adama don sun wahalar da ni. Don haka ba na kula kowacce kawa, na girmi wasu, wasu sun girme ni, wasu shekarunmu daya. Sun shisshige min sun ga babu fuska har sun rabu da ni. Mai girman kai suka dauke ni, *yar wulakanci, suna tunanin ni *yar wani hamshakin mai kudi ne, musamman da suka ga Alhaji Sani yana ta kula da ni da Hanif. A Abuja Alhaji Sani ya yi min siyayyar kaya kamar riga da siket kala biyu, riga da wando (jeans) kala biyu, abaya kala biyu, *yan kananan gyaleluwa, takalma da jaka kala biyu. Ya zuba a cikin dandatsetsiyar akwati *yar madaidaiciya dai dai ta shiga jirgi ya kawo min. Ai tuni na yi wurgi da zannuwana kala daya na dauko wata super holland sabuwar riga da zani, kacokan na bawa wata miskina sadakar kayan da jakar. Abu kamar wasa ranar litinin da daddare sai gamu a jirgi Egypt air ne, da ya kwashe mu daga Abuja sai birnin Cairo. Wannan shi ne karo na farko da na taba hawa jirgin sama a rayuwata, don haka maganar kauyanci ma an san dole ne na yi shi. Faduwa ta hau tafa hannu tana murna ta ji an hau jirgin kasarsu, an sauka a garinsu. Ta ce, ''Ya ya kika ga Cairo? Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Airport ya yi, kuma an dibe mu a mota an kai mu wani hotel a cikin gari mai suna Novotel aka bamu daki mutum bibbiyu, ga abincin safe da na rana, sai yadda ka ga dama zaka diba. Awannai goma sha biyu muka yi daga shida na safe zuwa shida na yamma. Tun karfe biyar aka dawo da mu filin jirgi muka shiga muka fara lulawa doguwar tafiya daga Egypt zuwa Bounkok awa goma sha daya, daga Bonkok (Thailanda) zuwa Malaysia awa biyu. Abdul-Sabur ya ce, ''Au sai da kuka tsaya a Bonkok sannan kuka taho? Umaimah ta ce, ''Eh, mun yi transit na awa biyu an sauke fasinja kuma an debi wasu fasinjoji zuwa Malaysia. Mun iso Malaysia daf da magruba, ba mu sha wahalar binciken immigration ba saboda a tawagar gwamnati muka taho ga jami'an gwamnati wadanda suka san gari ga takardun kowa tsaf-tsaf. Kai tsaye cikin Kaula Lumfur (KL) aka shigo da mu wani babban hotel ni har yau na ban san wanne ne ba muka kwana. Washe gari aka hau rarraba mu, ashe ba mu dukka ba ne a makaranta daya, makarantu biyar ne za a rarraba mu ashirin-ashirin a kowacce makaranta. Ya danganta ashe da course din da ka zaba ka cike. A makarantarmu FTMS mu ashirin ne mata biyar maza goma sha biyar. Sai Intii Nilai su ma garin Nilai za su zauna su ashirin maza sha takwas mata biyu, sai su Hanif da suke 'Legenda, sannan wasu aka kai su 'Help Uneversity wasu kuwa 'Putra Jaya' aka kaisu, a 'Apiit University' kowa course mai kyau ya zaba kamar ni da nake karantar Software Engineering wasu medicine, wasu Computer Engineering da dai sauransu. Aka rarraba *yan rakiya kowannensu ya dauki tasa tawagar ashirin-ashirin zuwa garin da makarantar ta ke. A lokacin muka yi sallama da Hanif har ya yi kamar zai yi kuka, ni kuwa sai da na yi kukan ma. Ya tafi 'Legenda' kauye ne mu kuwa a cikin 'KL ne, na ci sa'a kuwa Alhaji Sani shine jami'inmu. Kai tsaye cikin makarantarmu FTMS mu muka nufa ba mu tsaya wata-wata ba aka nuna mana katon gidan haya a kusa da makaranta mata mu biyar bangarenmu daban, amma mutum bibbiyu a daki daya, daya dakin kuwa su uku ne. Ni da Aisha bingyal aka hada mu ita ma mai ji da kai ce kamata, don haka kowa ya juyawa kowa baya, tunda kowa da gadonsa. Washegari babu abin da muka yi sai cuku-cukun registration da cike-ciken forms. Da muka gama sai aka daddanka mana account number mu da ATM aka nuna mana bankin da zamu dinga zuwa daukar kudi. Bayan wannan sai Alhaji Sani ya ja ni zuwa banki daban ya bude min sabon account wanda Alhaji Rabi'u ya ce a bude min na musamman zai sako min naira miliyan daya. Alhaji Sani ya yi waya da jami'in da yake Lagenda ya umarce shi da ya budewa Hanif ma, ya turo masa da account number, haka kuwa aka yi aka budewa Hanif shi ma. Sai na ga duk sun sayi layuka ana ta musanya lamba, sai ni naki siya fur. Alhaji Sani ya ba ni waya na yi magana da Alhaji Rabi'u ya jajjada min zai sako wannan kudi da ya yi mana alkawari, na yi ta godiya. Tun kafin Alhaji Sani ya bar Malaysia ya tabbatar min an sako kudin nan muka je banki aka duba min dallar dubu takwas tabbas nasan na yi sallama da talauci a duniya. Ban san da yaren da zan yiwa bawan Allah nan godiya ba. Alhaji Sani ya sake kira min Alhaji Rabi'u a waya na fada masa da bakina na ga kudin sannan na sake yin godiya, ya sake yi min nasihohi da na yi karatu, kuma na kama kaina ban da bin samari da lalatattun kawaye. Wannan shine labarina. Umaimah ta dube su tana murmushi. Suka yi ajiyar zuciya a lokaci guda, Abdul-Sabur ya gyada kai. Ya ce, ''Wannan labari ya kayatar da ni kamar kada ya kare. To amma ya aka yi kika baro can Hostel kika dawo nan gidajen? Umaimah ta yi murmushi ta ce, ''Da na yi wata guda na gane gari, ina ta hira da malamai ina tambayarsu dokoki da tsarin karbar hayar gidajensu, sai na ji da sauki babu tsada ai zan iya kama gida ni kadai. Suka tabbatar min akwai gidajen haya kusa da makarantar nan wanda ba sai na hau mota ba zan iso. Ba ni da matsalar kudi, don haka na ba wa wani malami dan kasa ne cigiya, ba tare da bata lokaci ba ya samo min nan, na tarkato na dawo. Daman ba dadi nake ji da dukka daliban ba musamman Aisha Bingyal da muke daki daya, na kasa sakin jikina da ita, na kasa yin ko hira da ita balle mu saba. Dan Allah ta yi hakuri ta yafe min, wallahi ba halina ba ne tsoro nake ji saboda abubuwan da aka yi min a baya. Har yau haushina suke ji, na ware ni kadai, a ji kawai nake shiga a gama lecture na fito na dawo gida. Sai ta dauro dole a yi magana sannan nake magana da su. Kamar misali idan an ba mu group assignmen ko practical a lab. Ba ni da waya balle na kira Hanif ya ji labarina, ba ni da waya balle mu dinga gaisawa da Alhaji Rabi'u da Alhaji Sani, ban kira kowa ba balle a san ina raye ban ki ba dai ko Hanif yana da lambar wasu daga cikin *yan makarantarmu ya tambaye ni ace masa ina nan bana kula kowa. Ni kuwa bakin hali da kyaliya ba halina ba ne, saka ni aka yi dole na zama haka saboda duk wanda na amincewa sai ya zalunce ni. Ta sunkuyar da kai ta dafe ta yi shiru, tana mai takaicin abubuwan da ta tuna a baya. Abdul-Sabur da Faduwa kuwa suka zuba mata ido kawai suna kallonta, suna masu tsananin tausayinta. Can ya yi gyaran murya ya fara magana cikin rarrashi da nasiha. ''Umaimah, na san MAKWABTAKA da kawaye sunyi miki ba dai-dai ba, amma kada wannan yasa ki zaci duk wasu MAKWABTA da zaki yi nan gaba su ma halinsu daya, ki dauka su daban mu daban. Ki dauke ni a matsayin babban yayanki Faduwa kuwa idan ba ki dauke ta uwa ba, to ki dauke ta a matsayin kanwar uwa (Aunty) saboda ke yarinya ce karama a cikinmu, babu zancen yi miki gulma, kazafi, cin amana da dai sauran tarkace. Rashin ilimi ne su ma can da kuruciya yasa suka yi miki haka. Umaimah, rayuwa ba zata yiwu a haka ba, babu yadda za a yi ki ware ki ce kin daina gaisawa da kowa a duniya musamman MAKWABTA. Ina kara baki hakuri da ki cire duk wannan ra'ayi naki ki kyautatawa MAKWABTA da duk wanda Allah Ya hadaku zama tare.... Faduwa ta ci gaba da cewa, ''Da kika ba mu tarihin rayuwarki sai na ji na fara sonki da na ji dalilinki, don a da haushinki nake ji, saboda nuna mana tsana kirikiri da kike yi. Yanzu mun zama daya, ke ma kanki idan kina shigowa cikinmu rayuwa a Malaysia zata fi yi miki dadi akan rayuwar kuncin da kike ciki ke kadai. Ki shigo cikinmu mu zauna tare, mu yi hira, mu zaga gari tare mu ba wa juna shawara. Allah Ya hada mu da babban Yaya Abdul-Sabur mai kaifin hankali, hakuri da hangen nesa, shi yake ba ni shawara koda yaushe. Ki dinga sauraron abubuwan da yake fada miki idan kika bi ba zaki yi nadama ba. Dadin kalaman Faduwa sai ya yi mata kama da na Matawata koda yaushe tana ce mata. ''Umaimah mu hada kanmu, kada mu yi fada kawaye su yi mana dariya, don haushin kawancenmu ake ji a garin nan, an kasa kunne ana so aji wata baraka a tsakaninmu. Amma a karshe ita ta fara cin amanata a duniya. Ta dago ta dubi Abdul-Sabur murmushi kadai ya yi mata yana yi mata kallo na tausayi da tsan-tsar kulawa. Sai ta gan shi sak Ilah haka yake yi mata, karshe ya ci amanarta. Sai ta ji da kyar idan zata amincewa da wadannan mutane kamar yadda suke tunanin zata yi. Ta yi zumbur ta mike tsaye ta wawuri mukullin gidanta babu abin da ta fi so irin ta ganta a gidanta ita kadai. Faduwa ta ce, ''Ki bari mu yi sallar azahar a jam,i, Abdul ya ja mu sai mu yi addu'a Allah Ya yayewa kowa damuwarsa, Ya biya mana bukatunmu, Ya kare mu daga sharrin makiya, Ya ba mu zaman lafiya a tsakaninmu. Umaimah har ta kai bakin kofa ta fara tafiya don ta gaji da dadin bakin Faduwa, har ta fara ganin kamar cutarta ta ke shirin yi. Faduwa ta mike da sauri cikin wasa zata je ta kamo hannunta ta dawo da ita, sai ta ga Umaimah ta zabura ta ja da baya a firgice. Abdul-Sabur ya dagawa Faduwa hannu alamar ta dawo ta zauna ta rabu da ita ta tafi. Umaimah ta juya da sauri ta fice daga cikin gidan, sai ta ji ta tamkar wacce ta fito daga kurkuku don ta takura da yawa zaman da ta yi a cikinsu na tsawon awoyi. Wai me me ya kai ta wannan katobarar a gurin mutane? Me yasa ta manta aminci ne duk ya jawo mata matsala a rayuwa? Ta shige lift ta haye sama ta isa gidanta, hannunta na rawa ta bude gidanta ta shige ta mayar da kofa ta kulle ta je ta haye kan kujera ta takure tana huci don an taso mata da dumbin takaici da abubuwan bakin cikin da aka guma mata a baya. Abdul-Sabur ya dubi Faduwa ya ce, ''Kin ga abin da nake fada miki ko? Daman na ce ki yiwa yarinyar nan uziri tana da dalilinta na yin haka, ashe an sha ta, ta warke shi yasa ta shiga tsoronmu. Ki bari a hankali zata gane mu su waye, kuma da wacce manufa muke bin ta. Ta sha wuya ne a rayuwa, ta rasa kowa, ta rasa komai tana karamarta. Umaimah ta cancanci a tausaya mata, a rarrashe ta, a daina damuwa da duk wasu halaye mararsa dadi da zata nuna. Ita a ganinta idan ta yi haka shi ne zata sami sauki a rayuwarta. Faduwa ta ce, ''Ai dole ta tsorata da mutane, sun ci amanarta, to Allah Ya sa mu dace. Abdul-Sabur ya ce, ''Amin Yayin da ya mike gami da yin mika da hamma. Ya dubi Faduwa ya ce, ''Yau kin hana mu baccin safe, daman ke baki iya ba. Da tuni sai yanzu zan tashi na yi sallah sannan na karya kumallo, amma yanzu cin abinci biyu kika sa mu. Daman ke yini kike kina dora tukunya, kullum bakinki yana ciye-ciye. Suka kwashe da dariya su dukka. Faduwa ta ce, ''Au kana nufin ban sami ladanka ba, na zaunar da yarinyar da ka dade kana so ta amsa gaisuwarka ma balle ta zauna da kai ku ci abinci a teburi guda ku yi hira. Ai na yi jihadi ba don ni ba wallahi har abada ba zata amsa maka ba. MAKWABATAKA 25 Ya juya ya tafi yayin da Faduwa ta tura kofarta ta rufe. Sallah ta yi ta kwanta, ta dade bacci bai dauketa ba tana tuna labarin Umaimah shi ya fi sosa mata zuciya. Abdul-Sabur ma haka da ya yi sallah a masallaci sai ya koma gida ya kwanta, labarin Umaimah shi ne yake yi masa reto a zuciya yana tausayinta yana tunanin hanyoyin da zai bi ya kawar mata da damuwar da ta addabe ta. Yayin da Umaimah ma bayan ta yi sallah ta kwanta bacci ya gagari idanuwanta, labarin Faduwa da Abdul-Sabur ne ya ke yi mata kewaye a zuciyarta. Hakika ashe ba ita kadai ba ce ta fuskanci matsalar rayuwa a duniya, a she su marayune, ba su da aure ba *ya*ya. Gara ita ma da ta taba auren har ta haifi da, ko ba ta sake aure a duniya ba nan gaba babu damuwa, ko mutuwa ta yi ta bar wanda za a kalla a tuna da ita a yi mata addu'a. Ba kamar Faduwa ma ita mace ta fi ba ta tausayi ta girma har ta manyanta babu aure, tabbas ta cancanci a tausaya mata. Ta shiga jero addu'oi Allah Ya fitowa da Faduwa miji na gari ta yi aure ko sau daya ne ta samu ta haihu. Asuba ta gari Abdul-fadu-maimah!!! ********************** Faduwa da Abdul-Sabur ne suke zaune a gidan cin abinci na Golden Folk da yake cikin KL. Faduwa ta kurbi lemo ta dubi abokinta Abdul-Sabur ta tabe baki cikin harshen Hausa suke magana kamar yadda suka yiwa juna alkawari sun daina yiwa juna Turanci sai Hausa. Ta ce, ''Mai hali baya fasa halinsa, da Umaimah nake, ka ga yau kwana hudu ke nan rabuwarmu ba mu sake jin motsinta ba balle mu ganta. Abdul-Sabur ya ce, ''Ta daina ma fitowa baranda, amma dazu ta fito da safe ta tsaya. Ta iske ni a tsaye a baranda kallo daya ta yi min ta sunkuyar da kai ba ta gaishe ni ba. Sai na ki yi mata sallama don idan na yi mata zata ji na takura mata, dole sai ta amsa tunda a musulunce ne. Faduwa ta gyara zama ta kai lomar salad a bakinta, ta ce, ''Yaya kuka yi daga karshe? Abdul-Sabur ya ce, ''Tsayawa na yi ina kallonta kawai, sai ta bata rai ta turo baki ta dube ni, ta ce, ina kwana? Irin na takura mata din nan. Sai na yi murmushi na ce mata, assalamu alaikum. Ta juya ta shige gida ta rufe kofa. Suka kwashe da dariya su dukka. Faduwa ta ce, ''Har yanzu fa ba son zamanta ta ke da mu ba, gani ta ke mun takure ta. Abdul-Sabur ya ce, ''Za ta ware nan gaba mu rage shisshige mata, idan ada bata san mu ko su waye ba yanzu ta sani. *Yan uwanta musulmai, Hausawa, duk inda ta je zata dawo ta neme mu. Yarinyar tana burge ni ne haka kawai, ban san dalili ba. Ba wai nace tana kyautatawa ba amma sai ta kalle ka ta harare ka kuma sai ta ji kunyar ka ta sunkuyar da kai, ta kasa hada ido da kai. Faduwa ta ce, ''Ba ka karsa ba, ba ka ce ga ta da kyau, fara mai gashi, ga dirin jiki dai-dai kauna ba. Abdul-Sabur ya harare ta, ya ce, ''Ni fa bana son ki dinaga kawo maganar so idan ana maganar zumunci. Faduwa ta ce, ''Ni dai na yi maka kamu, zan zauna da ita na isar da wannan sako naka. Kafin ta dago da kai ta tsinkayo Abdul-Sabur ya kai bakin kofa zai fice, ta wawuro jakarta ta biyo shi da sauri. Daman ya biya kudin abincin ko rabi ba su ci ba, ya tashi ya bar abincin. Wai shi nan fushi ya yi. Ta yi ta bin sa tana yi masa magana ya kyaleta har sai da ta sauko, ta shiga ba shi hakuri. Ta ce, ta fasa ba zata fadawa Umaimah ba, daman wasa take yi masa, sannan ya fara amsa mata. Su ka shiga jirgin kasa suka koma gida. Ranar lahadi da sanyin safiya misalin karfe tara, sai ga Faduwa a tsaye a kofar gidan Umaimah tana ta danna kararrawa. Yayin da tsoro, fargaba, gami da dimaucewa suka ruftowa Umaimah. Tayi figigit ta fito daga cikin bargonta ta diro daga kan gado ba shiri ta ruga da gudu zuwa bakin kofa, ta leka ta jikin *yar huda dan taga me buga mata kofa. Sai kuwa ta hango Faduwa dan haka mamakin sai ya ragu. Ta bude mata da sauri gami da yi mata murmushi da sannu da zuwa. Faduwa ta ji dadi da taga ta karbe ta da farin ciki, itama sai ta sake samun kwarin gwiwa ta shigo da fara'ar ta. Umaimah na gaba Faduwa tana biye da ita har kan kujerun falo suka zauna suka sake gaisawa. Zata je ta dauko mata shayi da lemo Faduwa ta tsayar da ita ta ce ta bar shi a koshe take daman ta zo ne dan ta sanar mata yau ranar haihuwar Abdul-Sabur ta zagayo (birhday) suna gaiyatar walima da yamma. Umaimah tayi dim! Kadan sannan tayi gyaran murya ta gyara zama zata yi magana, Faduwa ta daga mata hannu ta katse ta. Ta ce ''Kada ki ba mu wani uziri ki ce ba za ki sami damar zuwa ba dole ki je. Ki shirya da yamma ki fito ni da ke da Abdul ne kadai. Sai Umaimah ta yi murmushi ta langwabe kai ta ce ''to Allah Ya kaimu anjiman din zan je. Faduwa ta yi dariya ta mike da sauri ta dafa kafadarta ta ce, ''Yauwa Baby na zan biyo miki anjima sai mu tafi. Umaimah ta raka ta har bakin kofa suka yi sallama kowannensu cike da fara'a. Ta tafi sannan Umaimah ta dawo ta zauna tana ta fargaba da sake-saken yadda zata bijire taki zuwa dan bata son zuwan kwata-kwata. Tana idar da sallar la'asar sai ta sake fesa wanka ta tsala ado da wasu sababbin kayanta wanda bata taba sakawa ba, riga fara me layi-layi baki da bakin dogon wando (jeans) sai ta sami dan yalolon gyale ta nade kanta da shi kalar fari da baki ne, sannan ta saka takalmi coge mai tsini sosai da bakar jaka mai kyawun gaske. Ta dora da farin gilashi a fuskarta mai hasken gilashi. Tana gama shiryawa tana tsaye a gaban madubi tana sake saka hoda da jagira sai ta ji kararrawar kofar gidanta tana kara ko kokonto bata yi ta san Faduwa ce. Sai ta fito da sauri bata bata lokacin ta ba na lekawa sai ta bude kofar ta fito gaba daya. Faduwar ce kuwa itama ta dandasa ado ku san kwalli iri daya suka yi a tare. ''Kin yi kyau kanwata. ''Faduwa ta fada a lokacin da take kallon Umamai sama da kasa. Kin fi ni kyau Antina. Itama ta fada a lokacin da take kokarin kulle kofar gidanta. Sai suka yi dariya su dukka suka dinguma zuwa cikin Lifter dan sauka kasa. Suka nufi get din fita daga farfajiyar gidan kamar Umaimah ta tambaye ta Abdul-Sabur sai ta fasa. Su na fita sai taga Faduwa ta nufi wajen wata tsaleliyar mota mai kyawun gaske, kalar baka mai farin gilashi tar! Har shekin kyau take dan sabunta, ko ba'a fada ba ka san sabuwa ce fil! Daga ledarta. Cikin sauri Faduwa ta budewa Umaimah gidan baya, ta shiga tana sanda gami da yiwa mutumin data iske a cikin motar sallama. Ya amsa mata cike da fara'a gami da juyowa a tsanake ya dube ta. Abdul-Sabur Abdul-Rashid ta gani sai ta cika da mamaki tana tunanin inda ya samo aron mota dan bata taba ganinsa da mota ba. Faduwa ta bude gidan gaba ta zauna, ya tashi mota suka hau kan titi suka fara tafiya. Umaimah ta leka fuskarsa ta ce ''happy birhday''. Ya yi murmushi ya ce Na gode. Yayin da Faduwa ta hau magana ba kakkautawa dan ita bata gajiya da magana. 'Eh ko A,a ko ya ce rufemin baki kin fiye surutu' Abdul ya fada mata, yayin da Umaimah ta kunshe baki tana dariya dan ita dariya suke bata kamar wasu *yan tagwaye. Ita Faduwa ta cika magana, ta fuskanci tana damun Abdul-Sabur bashi da surutu. Suka isa wajen da ake ajiye motoci suka sami waje suka tsaya yayin da suka firfito zuwa cikin KL plaza. Suka nufi babban wajen cin abinci, babu abinda babu na ci abinci kasashe kala-kala sai wanda kake so zaka zaba. Suna zama aka kawo musu takarda mai rubuce da duk launin abincin da suke sayarwa a wajen. Sai kowa ya shiga cankar abinda ya fi so ya ci, shinkafa da salad sai *yar miyar gargajiya kaji kadai Umaimah ta zaba. Sai Abdul-Sabur ya ce a'a yayi mata kadan sai ta kara da wasu abinciccikan dan shi so yake a cika kan teburin dankar da abinci da abin makulashe. Ta yi murmushi ''ta ce to a kawo komai ma duk sai a hadu a ci. Ma'aikata sun ga ciniki sai suka hau rawar jiki suka garzaya a rude suka hau harhadowa, ma'aikata a layi suke ta zuwa suna ajiye farantai da kofuna a cike da kayan alatu. Faduwa ta zabura ta mike zata je kicin. Abdul-Sabur ya dakatar da ita da sauri. Ya ce, ''Kin fiye rawar kai, wa kika ga yana shiga kicin, kowa ba'a zaune yake ba su suke zasu kawo komai ba? Faduwa ta mike gami da tabe baki ta ce, ''Ka ga tafiyata, kai ma ka san babu yadda za'ayi in zo waje in zauna dam sai na motsa. Umaimah ta tuntsire da dariya ta bi Faduwa da kallo tana mamakin irin wannan hali nata. Abdul-Sabur ya yi dariya ya dubi Umaimah ya ce ''Kin fara ganin halin makwabciyarki ko? Haka take bata iya zama shiru. Umaimah ta sake tuntsirewa da dariya ta gyara zama ta dube shi ta ce ''Ina son halinta, tana burge ni dan tana da kirki sosai. Dama ka aure ta, da zan so haka wallahi. Ya yi firgigit ta dago da sauri ya dube ta cike da dinbun mamakin yadda aka yi wadannan kalamai suka fito daga bakinta a daidai wannan lokaci. Sai ya dan yatsune fuska ya tambaye ta me ta ce, dan yana tunanin kunnuwansa basu jiyo masa dai-dai ba. Data maimaita sai ya ji abun da ta fada dazu shi ta maimata. Ya gyara zama ya ce ''Me yasa kika yi wannan tunanin? Ta yi murmushi ta ce, ''Kamar yadda na fada dazu tana da kirki kuma ina tausayinta har yanzu bata taba yin auren fari ba. Sai ya sankare a zaune ya kasa amsa mata wannan tambaya. Faduwa ce ta taho dauke da babban faranti dauke da katan kek da wukar yankawa ta zo ta ajiye a gaban AbdulSabur. Ya yi murmushi ya ce, ''Ke ni fa ba wani kek da zan yanka. Faduwa ta yi dariya ta ce ''Sai ka yanka yanzu kuwa. Umaimah ta mike ta nufi kicin yayin da Abdul-Sabur ya ce, ''Au kema kicin din zaki shigar musu irin na Yayarki? Umaimah ta yi dariya ta kada kai ta tafi ba tare data ba shi amsa ba. Sai Faduwa ce ta amsa masa ta ce ''Kada fa ka takurawa kanwata ka bar mu yau mu wataya muna murna da zagayowar haihuwar dan uwanmu. Ya ce ''Allah Ya huci zuciyarku ban hana ku watayawa ba ai. Faduwa ta ciro kyamarar daukar hoto ta ce, ''Bari Umaimah ta zo sai mu fara daukar hoto, kuma ka yanka kek dinka. Yayana me zai hana mu bi yarinyar nan a hankali har ta saki jiki damu sannan mu bayyana mata manufarmu? Abdul-Sabur ya zabura ya dubi Faduwa a gigice ya tamabaya, ''Wacce manufa muke da ita a game da ita? Ta yi dariya ta gyara zama sannan ta kanne ido ta ce ''Ah maganar ka da ita mana, ni fa da gaske nake na maka sha'awarta. Kai ka fi cancanta ka auri yarinyar nan dan ina tausayawa rayuwarta, ta sha wahala gata marainiya. Na yarda dakai, zaka iya rike ta amana. Sai ya sulale ya mimmike a zaune akan kujerar da yake zaune, ya daga kai sama saboda tsabar tashin hankali, dimuwa, mamaki da firgici. Ya ji ko ya tsansa ba zai iya dagawa ba saboda sanyin jiki. Ya hau tambayr kansa da kansa. Wai shin me yake faruwa da ni ne a yau? Yau me yake shirin fado min cikin rayuwata ne haka? Me yasa Umaimah ta yi min sha,awar in auri Faduwa itama Faduwa ta yi min sha'awar ta yi min sha'awar in auri Umaimah? Shin mafarki nake yi ne ko idanuwana biyu? Anya kuwa ba hade min kai suka yi ba suke shirin su waina ni ba? Kai haba ya ma za'ayi a ce sun hada baki, yaushe suka san juna ma? Ya zanyi kuma menene ya kamata in yi? KARKSHEN LITTAFI NA 2.. _________(3)_____ Umaimah ta fito dauke da *yan gwangwanayen fulawar roba a hannayenta ta zo ta jera akan tebur, yadda teburin zai sake kayatuwa. Faduwa ta shiga tarwatun kiran jama'ar da suke zazzaune suna cin abinci, wai su zo su taya su yanka kek din birhday. Masu hali irin nata na rawar kai da son wasa suka ta so yuya guda har da wasu daga cikin ma'aikata, ana tafi ana fadin. ''Happy birhday Abdul'' kamar yadda suka ji Faduwa tana fada suma ita suke ta fada. Takaici ya hana Abdul-Sabur sakat ya ji dama bai zo wajen nan ba, a dole aka kewaye shi ana kirga daya har zuwa goma sannan ya yanka kek, aka hau tafawa kamar wani yaro karami. Sai Faduwa ta shiga daddatsa kek kowa yana caka da colali yana ci. Hotuna iri-iri Faduwa ta dinga yiwa Abdul-Sabur da Umaimah a kusa da shi, babu abinda Umaimah take sai murmushi dan tabbas ta shaki farin ciki a wannan fita. Bayan nan sai Faduwa ta yiwa jama'a godiya game da yi musu tayin su zauna su ci abinci tare da su, da yake kusan kowa an riga an kawo masa nasa abincin kan teburinsa sai suka ki zama suka koma in da suka fito suka zauna suka ci gaba da cin abincinsu. Suma su Faduwa suka zauna suka fara cin jifgin abincin da yake jere akan teburin gabansu, daga gani abincin nan ya fi karfin hanjinsu saboda yawa gashi kaloli dabandaban. Duk wanda ya shigo kafin ya zauna sai Faduwa ta kirashi tebur dinsu, ta yi masa ta yi in akwai abinda ya ke so a ciki ya zauna ya ci ba sai ya saya ba sun saya da yawa saboda bikin birhday da suke yi. Abinci kadan Abdul-Sabur ya ci sai ya daina ci yana daga zaune ya dubi Faduwa, ya juya ya dubi Umaimah, sai ya yi sauri ya sunkuyar da kai, yayin da kwalla ta cika masa ido yana tausayin kansu su dukka ukun. Kasancewarsu gaba dayansu marayu ne, kuma baki a kasar da babu danginsu. Haka su dukka ukun bagware ne, ba su da mai kula da su, kowannensu shi kadai a cikin gidansa kamar maye. Ya fi tausayin matan ma akan kansa, rayuwar mace a gurgunce ta ke muddin ta kai munzalin aure, kuma ba ta yi ba. Sai zuciyarsa ta shiga saka masa hanyoyi daban-daban da zai bi don magance wadannan matsalolin da suka addabe su. Faduwa ta dubi Umaimah ita ma ta dubeta, gaba daya suka tsurawa Abdul-Sabur idanu, tabbas sun ga ya sauya yanayinsa, ya shiga halin tunani a dai-dai lokacin da suke hayaniyarsu su kadai. Babu wacce ta tambaye shi me yasa saboda kowacce ta san dalilinsa na yin haka, sai dai dalilin kowacce daban, ya sha ban-bam da na dayar. Faduwa tasan tayi masa maganar ya auri Umaimah ta san maganar ce ta ke yi masa zillo a zuciyarsa, ita ma Umaimah ta san maganar data yi masa kan ya auri Faduwa ita ce ta toshe masa a kahon zuci. Abin da ba su sani ba shi ne, farin ciki maganarsu ta saka masa a rai, ko kuwa damuwa, ya amince ko kuwa bai amince ba? Shawarar da yayanke shine ya auri Faduwa Umaima kuma ya aurawa Dan Aunty..lolx.. Ehemm. Ko ya kukagani en uwa.? MAKWABTAKA 26 Kallon da suke yi masa shiyasa ya hanzarta farfadowa daga duniyar tunani ya karkato hankalinsa gare su, ya biye musu aka yi ta hayaniya da ciye-ciye. Karfe tara na dare suka baro 'KL plaza, kai tsaye suka wuce da motar wajen ajiye motocin da yake cikin gidansu. Yayin da suka firfito kowannensu cikin fara'a suke yiwa juna sallama da fatan Allah Ya tashe su lafiya. Faduwa da Umaimah suka nufi bangarensu, yayin da Abdul-Sabur ya nufi na sa bangaren. A cikin lift Faduwa da Umaimah hirarsu kawai suke yi cikin harshensu, wato Hausa. Wasa da dariya gami da dimbin nishadi ne ya tabbata a zukatansu. Kaunar juna, gami da rashin jin dadin rabuwa suke ji a cikin kalbinsu. Faduwa ce ta ba Umaimah hannu suka gaisa gami da rungume ta, ta sumbaci gefen kumatunta irin gaisuwarsu ta Larabawa, a lokacin da aka zo hawa na goma sha takwas wato gidanta. Lokacin rabuwarsu ta zo kenan amma fa a yau. Kalmar karshe da ta fadawa Umaimah ita ce 'Bissalam. Ta fice daga cikin lift yayin da kofar lift ta rufe kanta, umaimah da sauran jama'a suka karayin sama, a hawa na goma sha tara Umaimah ta fice ta nufi gidanta fuskarta cike da annuri, har waka take rerawa a hankali cikin harshenta na fulatanci. Wakar nan da suke yi a dandali ita da kawarta Matawata, wacce suke kiran junansu kawata, masoyiyata kuma makwabciyata. Abun tambaya a nan shine Faduwa ce ta maye gurbin Matawata, ko kuwa Abdul-Sabur ne? Asuba ta gari Fadu-maimah-sabur!!! Shigar kowannensu gida ba tare da bata lokaci ba ya yi wanka da kuma sallar isha'i, bayan saka rigunan baccinsu, sai suka haye gado yayin da kowannensu ya shiga tunanin dan uwansa suna masu tunano abubuwan da suka faru da su a dazun nan. Haduwarsu ta zame musu tamkar a mafarki, suna mamakin yadda haka ta kasance. Matsananciyar shakuwa da kaunar juna nan da nan ta wanzu a ransu. Bacci mai dadi ya kwashe su a lokaci daya, saboda sun gaji ya hadu da mafarkai kusan iri daya, abubuwan da suka faru dazun suke maimaita gani a mafarki. Umaimah ta yi firgigit ta bude ido tana mai murmushi a fuskarta sai ta ga ashe fa a mafarki ne, Abdul-Sabur ta yi mafarki yana yi mata magana. Ya ce da ita, ''Umaimah kinga abin da nake fada miki ko? Annabi (S.A.W) ya yi gaskiya da ya ce, ''dukkan musulmi dan uwan musulmi ne'' Ta yi firgigit ta tashi zaune ta dafe kirji gami da jinjina kai tana mai gasgata wannan maganar da ta ji a mafarki. Sai ta yi cimak ta sauko daga kan gado ta je jikin tagar dakinta ta daga labule ta leka gidan Abdul-Sabur. A tsaye ta gan shi a jikin tagarsa aka yi katari yana kallonta, sai ta sake firgita ta saki labulen tagar da sauri tana ambaton. ''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Anya wannan mutum ne? Ta dade a tsaye a tsakar daki ta rike baki tana mamaki, can ta suri filo ta fito falo kan doguwar kujera ta zauna, bacci ya gagare ta, don haka ta tashi ta shiga kicin ta tsaya, ta dade a tsaye sannan ta tuna kishirwa ta ke ji, kasancewar an ci maiko dazu. Ta bude firij ta dauko robar ruwa ta tsiyaya a kofi ta kurba. Sai ta jiyo magana a waje kan baranda kamar muryar Abdul-Sabur. Cikin sanda ta bude kofar da zata kai barandar waje, tana budewa sai ga Abdul-Sabur muraran shi ma atsaye akan barandarsa ta kicin yana mai dubanta yana murmushi. Ya na magana amma a waya cikin wani yare wanda ba nata ba. Dan haka ba ta gane me yake cewa ba, sai ta yi sauri ta tura kofar ta rufe ta gaggauta kashe fitulun gidan gaba daya tana mai tottofa addo'o'i a kowacce kusurwa ta cikin gidan. Ta shige daki ta haye kan gado can cikin lungu ta kudundune a cikin bargo tana ta makyarkyata saboda tsoron daya kamata. Tana tunanin anya kuwa AbdulSabur mutum ne, ko kuwa aljani ne yake shigarsa don ya tsorata ta? Da kyar ta yi bacci bayan da ta daina jiyo maganarsa da kuma motsin shige da fitar da yake yi a cikin gidansa. Ko bayan da ta yi baccin ma mafarkinsa ta ci gaba da yi har yanzu dai nasihohin yake yi mata a mafarki, wannan karon kuma babin mace ta yiwa mijinta biyayya yake bayani. TIkon Allah, wannan shi ake kira boyayyen al'amari, ko mene ne ma'anar hakan? Allah Shi Ya barwa kanSa sani. Asuba ta gari Fadumaimasabur. *************** Dif Umaimah ta bace kwana biyar ma ba su sake ganinta ba, haka ba sa jin motsinta a gidan, a makaranta ta ke yini idan ta taso sai ta wuce Bukit bing tang ta ci abinci a restaurant bayan ta zazzagaya malls sannan ta dawo gida da daddare ta kwanta, ko fitila ba ta kunnawa balle a san tana ciki. Amma koda yaushe MAKWABTAnta suna cikin ranta, kuma ba ta da mummunan zato a kansu, saboda ta saba da zaman kadaici, shi yasa ba ta damu ta neme su ba. Ranar juma'a bayan masallci tana cikin tunaninsu, sai kuwa ta ji bugun kofa gami da jiyo muryoyinsu, babu tantama tasan su ne sai ta rasa dalilin jin farin ciki a cikin zuciyarta. Da sauri ta bude musu kofa bayan ta zumbula dogon hijab. Yadda ta ke murna da ganinsu har sun fita murna, saboda dariyar da ta ga suna bangalawa. Ta yi musu iso zuwa cikin falonta suka shigo suka zauna akan doguwar kujera su biyu a jere. Ta zauna a kujerar da ta ke fuskantarsu cike da ladabi ta duka ta gaishe su, sannan ta koma ta gyara zama ta dube su ta yi dariya, ta furta kalmar da gaba dayansu suka dimauce, aka hau kallon-kallo. Cewa ta yi, ''Kun ba ni sha'awa da na ganku a tare, Allah Ya tabbatar da alkhairi, mafarkina ya zamo gaskiya. Musamman Faduwa ta fi Abdul-Sabur rashin fahimtar abin da Umaimah ta ke nufi, ga rashin wadatacciyar Hausa, ga rashin sanin ainihin kan maganar, saboda ba ta san maganar da Umaimah ta fadawa Abdul-Sabur ba a kanta. Ita ma kuma yanzun nan ta sake furtawa AbdulSabur sabuwar maganarsa da Umaimah shi ne ma dalilin da yasa ta taso shi a gaba don su zo su ganta duk da ita ma tana tsoron furatawa Umaimah wannan batu. Tana gudun kada ta ki amincewa kuma ta shiga gudunsu, don tasan halinta. Duk da Abdul-Sabur bai bata goyon baya ba akan aniyarta ta hada shi da soyayya da Umaimah ba, har ya kan yi fushin gan-gan idan tayi masa maganar, amma ta san nokewa yake yana so yana kaiwa kasuwa. Shi ma kuma ya kasa fada mata abin da yake zuciyar Umaimah na yunkurin hada aure da ta ke yi. Faduwa ce ta takurawa Umaimah da tambayoyi akan ta yi mata FASHIN-BAKI akan maganar da ta yi dazun. Hausa cikin Hausa Umaimah ta sake rikita mata kwakwalwa, sai Faduwa ta dawo turanci dan ta ji Hausar ta gagare ta, duk da haka Umaimah ta goce ba ta bari ta fahimci abin da ta ke nufi ba. Abdul-Sabur ya gane, dariya kawai yake kyakyata musu daga karshe dai ya kawar da hirar ya shigo musu da wata hirar wacce ta shafi kowannensu, wato hirar makaranta da shirin fara jarabawa. Umaimah ta mike cikin nutsuwa ta ke tafiya ta nufi kicin dinta, ba jimawa ta fito hannayenta dauke da kwalin lemo da kuma kofuna guda uku, ta kawo tsakiyar kujeru (center table) ta shiga tsaiyaya musu, ta durkusa ta mikawa kowannensu sannan ta sake tashi ta shiga kicin. Faduwa ta dubi Abdul-Sabur ta yi murmushi, magana ta ke yi masa cikin rada. Ta ce ''Ka ga abin da nake fada maka ko? Yarinyar nan ta dace da rayuwarka, nutsattsiya ce ga ladabi. Sai ya harareta ta kawai ya sunkuyar da kai, sai ta kyalkyale da dariya. Umaimah ce ta fito dauke da farantin tangaran da 'cake' da biskit a cikinsa ta kawo ta ajiye a gabansu, ta koma ta zauna suka ci gaba da hira da kallon talabijin. Faduwa ta kurbi lemo, ta gyara zama ta ce, ''Umaimah ba ruwanki da neman MAKWABTANki ko za ki shekara ba ki gansu ba ko? Umaimah ta yi sauri ta dubi Abdul-Sabur, yayin da ya yi saurin kawar da kansa gefe tamkar bai san abin da suke cewa ba. Kunyarsa ta ke ji saboda nasihohin da ya dade yana yi mata akan ta sauya wannan mugun halin na kin mutane. Ta yi saurin sauya hira, amma sai Faduwa ta sake jeho mata wata tambayar. Ta ce, ''Ba kya neman mutane a waya ko ba ki zo inda muke ba, sai mu dinga gaisawa a waya, koda yake ko lambobinmu ma ba ki karba ba. Wannan karon ma Umaimah Abdul-Sabur ta sake kallo, yayin da yaki yarda su hada idanu, ya ci gaba da matsa remote yana sauya tasha a talabijin. Faduwa ta ce, ''Ba ni lambarki, ga tawa. Ta dauko wayarta tana jiran Umaimah ta karanto mata lambobin. Takaicin tonar asirin da Faduwa ke kokarin yi mata ta toshe zuciyarta, ba ta so aka yi wannan hira agaban Abdul-Sabur ba, saboda kada ya zaci ba ta sauya ra'ayinta ba har yanzu. Cikin sanyin murya ta ke ba wa Faduwa amsa ''Ai ba ni da waya. Don firgita Faduwa har da dafe kirji, ta dauki dogon salati kai ka ce mutuwa aka yi. Ta ce ''Kamar ya ya baki da waya? Ta bata ne ko ba ki taba yin waya ba daman can a rayuwarki? Umaimah ta yi dan murmushin karfin hali, ta ce ''Ban taba yin waya ba daman can a rayuwata. Kallo daya Abdul-Sabur ya yi musu ya juyar da kansa ya ci gaba da kallon talabijin. Faduwa ta zungure shi, ta ce ''Aboki, ka ji ikon Allah, wai Umaimah ba ta da waya, a rayuwarta ma bata yi waya ba, ko ta zaci a ruga take har yanzu? Su dukka ukun suka kyalkyale da dariya. Abdul-Sabur ya ce, ''Matsalata da ke ke nan, kin cika kwakwazo, meye abun mamaki don bata da waya? Kowa fa da ra'ayinsa. Faduwa ta ce, ''Da mamaki mana yadda duniyar nan ta ci gaba, almajirai a cikin kauye ma rike waya suke yi balle ita da ta ke birni. Birnin ma irin Malaysia, a Malaysia ma a babban birnin Kaula Lumfur, kuma a jami'a. Haba Umaimah me yasa haka, ya ya kike da *yan gidanku, samarinki, da kawayenki? Abdul-Sabur ya tsurawa Umaimah ido yana jira ya ji amsar da zata bayar, sai ta ki magama ta sunkuyar da kanta kasa, murmushi kadai ta ke yi. Faduwa dai ba ta daina mamaki ba, haka ba ta daina yi mata tsiya ba, har sai da Abdul-Sabur ya mike tsaye ya ce zai tafi masallaci, ya ji ana kiran sallar la'asar. Faduwa ta tashi ta bi shi suka fice. Umaimah ta raka su har kofar bakin lift suka yiwa juna godiya, sallama, gami da fatan alkhairi suka shige lift suka tafi, ita kuma ta p dawo gida tana maijin sanyi a ranta, kasancewar a halin yanzu tana samun baki a gidanta, ta sami wadanda suka san da ita suka damu da lafiyarta, wadanda zata yi hira da su har su saka ta dariya. Bayan kwanaki biyu da zuwan su Faduwa gidanta, ranar lahadi da yamma Umaimah ta shirya ta rufo gidanta ta shiga gidan Faduwa don ta gaishe ta. Faduwa ta yi matukar mamaki gami da farin cikin ganinta. Ta mike da sauri ta rungume Umaimah ta kamo hannunta ta zaunar da ita akan kujera. Sai a lokacin Umaimah ta dubi mata biyu da suke zaune a kan sauran kujerun. Ashe baki gare ta, daya inyamura, daya *yar Malaysia. Uhum! Faduwa mai mutane, kawayenta kala-kala daga kowacce kusurwa ta duniya tana da kawaye mata da maza. Umaimah ta daga musu hannu ta gaishe su, gaisuwar dai ta hello da hi ce, don ba ta ga alamar musulunci a tattare da su balle ta yi musu sallama. Suka amsa mata cikin fara'a su ma yayin da Faduwa ta gabatarwa kawayenta Umaimah, sannan ta gabatar da su ga Umaimah. Sun jima suna hira bayan sun ci, sun sha, Umaimah ta yi musu sallama kasancewar magruba ta kusa. Su ma lambar wayar Umaimah suke tambaya. Faduwa ta yi sauri ta ce, ''Ina da ita, zan baku anjima. Saboda ta ga Umaimah ta rasa amsar da zata ba su. Bayan tafiyar Umaimah sun dade suna yiwa Faduwa zancenta cewar, tana da kirki ga hankali. Sannan ta ba su sha'awa yarinya kyakkyawar gaske kamar ba *yar Africa ba. Faduwa ta yi musu alkawarin zata kawo musu Umaimah har gidajensu wata rana. Misalin karfe goma na safiyar wata litinin Umaimah ta bude barandar kiicin dinta don shanya hankicin da ta gama goge-gogen gidanta. A tsaye ta iske Abdul-Sabur shi ma akan barandarsa yana shan iska, sun kwana biyu ba su hadu ba ko akan hanya. Ta dan razana da ganinsa, ta yi kamar zata koma ciki, sai ta daure, ta dake, kasancewar ta daure kanta da dankwali duk da riga da wandon bacci ne a jikinta, amma dogaye ne ba kanana ba. Suna hada ido sai suka yiwa juna murmushi, ta duka ta gaishe shi. ''Umaimah daman kina nan? Kwana biyu kin buya. Abdul ya tambaye ta. Cikin kadabi ta ba shi amsa. ''Ina nan, lafiya kalau. Ta ci gaba da shanya, ya gyara tsayuwa ya ce, ''Ba a ganinki sosai, ko makaranta ce? Koda yake masu ganinki suna ganinki, Faduwa ta ce kusan kullum sai kun hadu, idan ba ta je gidanki ba, ke kina zuwa. Har ma kun je unguwa jiya tare. Umaimah ta yi murmushi, ta gyada kai ta ce, ''Haka ne. Ya gyada kai, ya ce ''Yana da kyau, kuma na ji dadi da samun wannan canjin. Ki ci gaba da yin hakan, saboda zaman kadaici ba dadi. Ta yi dariya ta ce, ''Insha Allah zan ci gaba da yin haka. Ya ce, ''To na gode idan ba zaki damu ba da yamma mu hadu a gidan Faduwa ina son magana da ke. Sai ta ji zuciyarta ta harba nan da nan ta ji hankalinta ya tashi, ta shiga mamakin dalilin neman ta da yake yi. Mamaki cike a fuskarta a bayyane ta dube shi cikin sanyayyiyar murya ta tambaye shi, ''Lafiya? Ya yi murmushi ya gyada kai, ya ce, ''Kar ki damu, ba wata matsala ba ce face alkhairi. Ta gyada kai a sanyaye ta ce, ''Allah Ya kaimu yammar. Ta juta ta shiga gida. Ta dade a zaune akan kujera tana sake-sake a zuciyarta tana ayyano mata abubuwa daban-daban da ya sa yake nemanta anjima a gidan Faduwa. Ko dai maganar nan da ta yi masa za'a tayar, wacce ta yi masa na ya auri Faduwa, yake so ta maimata a gaban Faduwa? Idan dai haka ne ai ta kwana gidan sauki, sai ta maimaita ba wani abu ba ne, alkhairi ta ke so ta hada. Daga karshe ta mike cimak ta je ta yi wanka, ta shirya ta fito zuwa makaranta tana da darasi da karfe goma sha biyu. Dai-dai get din gidansu ta ci karo da Abdul-Sabur da Faduwa a cikin tsaleliyar motarsa za su fita da alama makaranta za su tafi. Sai da suka rage gilashin motar ta hango su, sannan ta gane su ne, suka yi mata izini ta shigo su tafi. Zata yi gardama Abdul ya ce ta shigo su tafi ba ya bukatar wani bayaninta. Ta bude gidan baya ta zauna, ya ja mota suka fara tafiya. MAKWABTAKA 27 Daga dukkan alamu dalibai da malamai a yau sun cika da mamaki da suka ga Umaimah tana magana da wasu bil'adama har ma da shiga motarsu. Sai kowa ya yi ta kallon Abdul-Sabur da Faduwa suna ta yi musu jinjina bisa namijin kokarin da suka yi har Umaimah ta aminta da su. Musamman kawayenta *yan Nigeria kuma *yan garinsu suka yi tsuru-tsuru suna kallonta suna kallon mutanen da suke cikin mota, da alama dai sun san ba *yan uwanta ba ne, amma kuma ga shi ta saba da su. Abdul-Sabur ya dubi Umaimah, ya ce, ''Karfe nawa za ki tashi in zo in dauke ki? Ta girgiza kai, ta ce, ''Kar ka damu, zan dawo da kaina, ai ba dadewa zan yi ba yau. Faduwa ta ce, ''To mu zauna ki shiga ki yi lecture ki fito mu ma sai ki raka mu tamu makarantar da yamma sai mu dawo tare. Umaimah ta kyalkyale da dariya ta ce, ''Haba Aunty Faduwa, ya za'a yi ku zauna ku jira ni kamar wata Sarki? Ku je makarantarku. Kada ku jira ni, ni ai ba ni da nisa, na gode Allah Ya saka muku da alkhairi. Faduwa da Abdul-Sabur ma suka yi mata fatan alkhairi, ya ja motarsa suka tafi, yayin da Umaimah ta juya ta dubi dumbin idanuwan da suke kallonta. Ta shiga karanto kula'uzai a zuciyarta don kada baki ya kamata. Tabbas an saka mata ido a makarantar nan hakan ya samo asali ne ta sanadiyyar rashin kula su da ta ke yi, kuma jama'a da dama suna son shiga harkarta. ************************* Umaimah ba ta baro gidanta ba sai bayan da ta idar da sallar magruba. Ta ci sa'a kuwa tana shigowa gidan Faduwa ko zama ba ta yi ba, Abdul-Sabur ma ya shigo, Umaimah ta dube su ta yi murmushi. Ta ce, ''Ku yi min afuwa na makara ban zo da yamma ba kamar yadda na yi alkawarin zan zo, na yi bacci ne ban tashi ba sai bayan la'asar sosai, shine ya sa na bari sai da na yi sallar magruba sannan na shigo. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce ''Ba damuwa, tunda yamma na zo muke ta jiranki ga shi na samu na je masallaci na yi sallah nima, na dawo a dai dai ke ma kin zo. Ta yi tsuru-tsuru tana jiran abin da zai ce mata, ta ji shiru bai yi magana ba, Faduwa ce kawai ke ta zuba kamar bushasshiyar kanya. Labarinta ta ke ta ba su tun tana firamare yadda ta yi kin ji. Suka sha dariyarsu har da kyakyatawa. Abdul-Sabur ya gyara zama ya dubi Umaimah ya ambaci sunan, sai ta ji wani abu ya tsargo daga kirjinta don fargaba. Cikin lallausar murya ta amsa masa gami da tsura masa ido tana son ta ji abin da yake shirin fada. ''Kina da lambar wayar *yan gidanku? Ya tambaye ta. Nan da nan ta cika da mamakin irin wannan tambaya da ta fito daga bakinsa. Sai ta rasa amsar da zata ba shi. Ya lura da hakan sai ya yi murmushi ya mika hannu kan teburin da ya ke gabansu ya dauko wani dan madaidaicin kwali ya hau budewa. Ya zaro wata tsaleliyar waya kirar Nokia E5 ya mika mata, ya sake zaro layin waya ya mika mata, ta karba a sanyaye kuma cike da mamaki, tambaya ce a cike da bakinta ta gagara furtawa. Faduwa ta ce, ''Wayarki ce yayanmu ya siyo mana iri daya, nima kinga tawa can a caji. Umaimah ta dubi Abdul-Sabur da sauri shi ma ya dube ta, sai ta sunkuyar da kai kasa ta yi dan murmushi. Ta ce, ''Na gode Yayanmu, amma ka yi hakuri bana so in saka ka asara in karbi wayar in ajiye ta don ba zan yi amfani da ita ba. Abdul-Sabur ya tsuke fuska, ya ce, ''Ni dai na baki, idan kin so za ki iya jefarwa a bola. Daga dukkan alamu Umaimah ba ta ji dadin wannan kalmar da ta fito daga bakin Abdul-Sabur ba, nan da nan sai ta ji hawayen takaici ya fara kwaranya daga idanuwanta. Faduwa ta zabura ta je ta rike ta tana mai lallashinta tana ba ta hakuri. Ta juyo ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ka sa ta kuka fa saboda kalmar da ka fada mata. Kasan fa ita *yar a lallaba ce. Ya yi ajiyar zuciya ya daga gira, ya ci gaba da kallon talabijin bai ce da su komai ba. Umaimah ta hasala ta ajiye wayar akan tebur ta zabura ta mike tsaye zata fice, Faduwa ta rike ta tana ba ta baki. Cikin kuka Umaimah ta ke magana, ta ce, ''Anti ki kyale ni in tafi gida, shi ya fi min sauki. Ni bana son waya, bana bukatar in rike waya a rayuwata. Faduwa ta ce, 'Duk da haka tunda ya siyo miki sai ki karba ki yi godiya, bai kamata a gabansa ki ce ba kya so ba. Yana da dalilinsa da yasa ya ce ki rike waya. Ki dauka ki sakata a caji ta kwana, sannan ki saka layinki in an kira ki dauka daman ba a ce sai kin kira kowa ba. Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''Ba zan tafi da ita ba da gaske nake, bana so in rike waya. A fusace ta warci mukulllin gidanta ta fice, Faduwa zata bi ta Abdul-Sabur ya dakatar da ita da hannu alamar ta tsaya kada ta bi ta. Faduwa ta dawo ta zauna a sanyaye. Ta ce, ''Haba Abdul kai da kasan lallabata ake yi ya zaka yi mata gatse-gatse alhali kasan halinta baudaddiyar yarinya ce. Ya yi murmushi, ya ce, ''Ina sane na yi mata haka, akwai dalili. Faduwa ta gyara zama ta tambaya, ''Me ye dalilin? Ya yi murmushi ya ce, ''Za ki ji nan gaba. Faduwa ta ce, ''Koma dai maye dalilinka ka jawo mana yanzu, tunda ranta ya baci sai mun yi rabin shekara muna bin kanta kafin ta fara kula mu. Ai ka fi kowa sanin wahalar da muka sha kafin ma ta fara amsa gaisuwarmu. Mun samu ta fara karkatowa kuma ka dagula mana lamuranmu. Yanzu ga shi soyayyar da nake shiri ginawa a tsakaninku ka rusa min. Ya harare ta, ya ce, ''Waye zai yi soyayyar da karamar yarinyar da har yanzu ba ta mallaki hankalin kanta ba? Ni ai ba haka nake ba. Faduwa ta bude baki don mamaki tana duban AbdulSabur, ta ce, ''Yau kuma da bakinka kake fadar haka? Nasan kana sonta. Wai me yake faruwa ne a tsakaninku, ta yi maka laifi ne? Abdul-Sabur ya yunkura ya mike ya ce, ''Ki saka mata wayar a caji ta kwana da safe ki saka mata layi ki kai mata. Faduwa ta amsa masa da ''to'' cike da ladabi. Ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, ya nufi gidansa. Da alama dai babu walwala a tattare da shi yau. Faduwa ta kamu da mamakin halin fushi da Abdul-Sabur ya shiga yau wanda ba ta taba gani ba. Alhali tunda safe suke tare ba ta ga bacin rai tattare da shi ba, sai yanzu. Ta aiwatar da abin da ya umarce ta da ta yi. Gari na wayewa karfe takwas na safe a kofar gidan Umaimah ta yi mata. Ta danna kararrawa. Umaimah ta yi mamaki da jin ana danna mata kofa, amma mamakin ba shi da yawa tasan dayan biyun, idan ba Faduwa ba ce, Abdul-Sabur ne, kuma zancen dai na waya ne. Daman idanunta biyu tana zaune a falo tana kallon wani film baccin safe ta gagari idanunta na daren ma kadan ta yi, ta rasa dalilinta na shiga wannan damuwa, saboda sun sami dan sabani da Abdul-Sabur. Ta tashi da sauri ta je ta bude kofar, tabbas tunaninta ya zama gaskiya, Faduwa ta gani tsaye a bakin kofarta fuskarta cike da murmushi. Ita ma ta yi mata murmushi gami da yi mata izini ta shigo. Suka shiga suka zauna Faduwa ta zaro waya ta mika mata Umaimah ta langwabar da kai gefe tana shirin bude shafin wani sabon kukan. Cikin shesshekar kuka ta ce, ''Bana son na rike waya a rayuwata shi ne kadai dalilina na kin hada waya. Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Umaimah, kada ki zama mace mai yawan taurin kai, ma'ana mai gardama, kasancewarki mace wacce zata yi aure ta zauna a karkashin wani bai dace ace haka halinki yake ba. Maza ba sa son mace mai gardama, musamman Yayana AbdulSabur mutum ne mai saukin kai, ba ya shiri da mai gardama. Tunda ya siyo ya baki ya kamata ki karba ki yi godiya. Yanzu ma shi ya aiko ni ya ce na kawo miki, ki karba ki rike ba dadi mayar da hannun kyauta baya. Umaimah ta mika hannu a hankali ta karba ta ajiye a gefenta a sanyaye, sannan Faduwa ta ji dadi a ranta. Faduwa ta zaro wayarta ta kira lambar Umaimah nan da nan ta hau ruri. Umaimah ta tsurawa wayar ido da kallo. Faduwa ta ce, ''Ita ce lambata, ki yi saving Umaimah ta gyada kai ba tare da ta ce komai ba. Faduwa ta mike ta nufi hanyar fita yayin da Umaimah ta ke yi mata rakiya har bakin kofa. Faduwa ba ta daina yi mata nasihohi ba, akan ta cire damuwa, ba a kanta aka fara samun matsalar rayuwa ba, haka ba a kanta za a kare ba. Don haka ta saki jikinta ta yi walwalarta ta saba da sababbin mutanen da ba su santa a baya ba. Bayan Faduwa ta tafi Umaimah ta dawo ta zauna a kusa da wayar ta buga tagumi tana tunani da sakesaken yadda zata salwantar da wannan waya kada ma ta jawo mata matsala da tone-tone. Don ita ta buya a duniyar da babu wanda ya santa, ba ta so a tono ta. Wayarta ce ta hau ruri abinka da rashin sabo, sai ta daka tsalle ta mike tsaye, ta tsorata tana shirin ta zura da gudu. Sannan hankalinta ya kawo kan wayar ta tuna ashe waya ta yi sam ta manta. Ta dawo ta zauna tana ajiyar zuciya, yayin da ta jawo wayar tana ta kallo har ta katse ba ta amsa ba. Daga dukkan alamu ta gane lambar irin ta dazu ce, ta Faduwa ce. Ba ta gama kallon lambar ba aka sake kira, ta amsa a sanyaye ta yi mata sallama. Faduwa ce ke magana cikin walwala, ta ce, ''Yauwa, ita ce lambar tawa na kira in shaida miki na iso gida lafiya. Kuma ga cajar wayarki a gidana duk sanda kike son caji ki zo ki dauka. Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''To na gode Antina, Allah huta gajiya, Allah Ya bar zumunci. Suka kashe wayar a tare. Umaimah ta hau gunguni tana magana ita kadai, ''kawai ta takura min da kira, shiyasa ma suka hada min wayar dan su hanani sukuni. ***************** Tunda Umaimah ta ajiye wayar a daki a karkashin filo fiye da kwanaki uku ba ta sake waiwayarta ba. Babu irin kiran da Faduwa ba ta yi mata ba shiru babu amsa, haka idan ta fice zuwa makaranta tunda safe har yamma likis ba ta dawowa gida. Shin darasi ne yake hana ta ta shi da wuri ko kuwa saboda wayar da aka hada mata ne, ta zame mata tamkar dodo a gidan shi yasa take guduwa? Oho! AbdulSabur ya lura da hakan cewar ba ta dawowa da wuri, tunda aka bata waya don haka bai taba garajen kiranta ba ma kada ta zaci manufar hada wayar ke nan. Yana tsaye akan barandar gidansa tun daga can kololuwar nesa ya hango tana dawowa daga makaranta a yammacin wannan rana. Yana daga sama ya zuba mata ido yana kallo, tafiya ta ke kanta a sunkuye a kasa, ba ta kallon kowa, sai ya shiga mamaki irin wannan hali nata na ko in kula da mutane. Kafin ta hau sama sai ya yi saurin barin barandar don kada ma su hadu. Ya lura a kufele ta ke da shi saboda ya yi mata mummunan laifi da ya fitar da kudinsa ya sai mata waya, kuma ya tilasta mata ta karba dole. Tana shiga dakinta wayarta ta dau ruri karkashin filo, da farko sai ta razana har da dafe kirji taji kara a karkashin filonta. Can ta tuna ashe waya ce, ta mika hannu da sauri ta dauka, ta ga Dr. Faduwa ce. Kafin ta amsa waya ta katse, missed call 49 ta gani duk na Dr. Faduwa har cajin waya ya kusa karewa. Sai ta yi tagumi tana tunani, ita kanta ta san ba ta kyautatawa Faduwa ba, nauyi da kunyarta suka addabe ta. Faduwa mai kaunarta ce, bai kamata ta dinga share ta ba tabbas. Faduwa ce ta ke kira har yanzu, kunya ya hana ta dauka, don haka ta yanke hukuncin tashi ta tafi gidan Faduwa a wannan lokaci, wannan ita ce hanya kadai da Faduwa zata goge wannan abin da ta saka a rai cewar wulakanci ne ya hana ta daukar waya. Ta ci sa'a ta iske Faduwa a gida, tana ganin Umaimah sai ta yi farin ciki gami da ja mata kunne ta murde a hankali. Ta ce, ''Kin cika taurin kunne Umaima, kin jefar da wayar ko? Umaimah ta yi murmushi ta fito da wayar daga aljihun wandonta (jeans) ta nuna mata. Ta ce, ''Ban yar ba, a gida nake manta ta idan zanje makaranta. Faduwa ta kwashe da dariya, ta ce, ''Au wayar ta ki ma kike mantawa a gida? Lallai a gaishe ki, tsabar wayar ba ta gabanki ke nan. Anya Umaimah rayuwa zata yiwu a haka? Ya kamata ki sauya ra'ayinki. Nawa kike a shekaru, rayuwar ma yanzu kika fara da har zaki zama haka. Umaimah ta zauna a sanyaye ta yi ajiyar zuciya, ta yi tagumi tana duban Faduwa, ita dai ba ta gajiya da yi mata nasiha. Ta karbi wayar ta dudduba sai ta kyalkyale ta yi dariya. Ta ce, ''Ban da ni babu wanda yake yi miki waya? Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Babu wanda ya taba kirana. Faduwa ta ce, ''Abdul-Sabur bai taba kiranki ba? Ai yana da lambarki tunda shi ya siyo mana sim card din. Kafin Faduwa ta rufe bakinta sai taji kaurin abincin data dora yana shirin kamawa nan da nan ta arta da gudu zuwa kicin. Shigarta kicin ke da wuya sai AbdulSabur ya yi sallama gami da daga labulen kofar falon ya shigo cikin nutsuwa. Nan da nan Umaimah ta daga kai da sauri ta dubi mai shigowa, sannan ta amsa sallamar ita ma cikin nutsuwa. Sai ta yi sauri ta sunkuyar da kanta kasa don kunya da nauyin abin da ta yi masa. Kan ka ce kwabo ta sulalo daga kan kujera ta gaishe shi cikin harshen Hausa. Ya fada cike da fara'a ''ta shi ki zauna ba sai kin sauko daga kan kujera ba in za ki gaishe ni. Ina Faduwa? Ta nuna kicin da yatsanta ta fada cikin girmamawa, ''Tana kicin yanzu ta shiga. Ya kwallawa Faduwa kira ta fito da sauri tana mai maraba da zuwan MAKWABCINTA kuma abokinta. Su dukka ukun a zaune suke akan kujeru, Faduwa ce ke ta labari, tunda Umaimah ta sunkuyar da kanta kasa ta tattakure ba ta sake dagowa ta dube su ba. Wayar Umaimah akan tebur (center table) ta fara ruri, ma'ana tana nunawa caji ya kusa karewa wato (battery low), su dukka ukun suka kalli junansu. Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Ga cajarki can a wajen soket, ki saka wayar a caji ga ta nan har zata mutu kamar a kasarmu Nigeria inda ake rashin wuta har caji ya kare waya ta mutu. Daga Abdul-Sabur har Umaimah babu wanda ya yi magana. Umaimah ta mike a sanyaye ta dauki wayar, ta je ta saka ta a caji, daga nan ta dubi kofar fita, ta juyo a hankali ta dube su ta yi dan murmushi, ta yi musu sallama ta ce zata tafi gida. Faduwa ta zabura ta ce, ''Me yasa zaki tafi gida alhali muna zaune muna hira har an dora mana abinci ya kusa dahuwa. Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''Alhamdulillah ai a koshe nake, ban dade da cin abinci ba. Faduwa ta yatsune fuska ta ce, 'Ko ba zaki ci abinci ba, ai sai ki zauna ayi hira in kin je gidan ma ke kadai ce me za ki yi? naku akulun IB MAKWABTAKA 28 Umaimah ta kara kutsa kai kofar fita, ta ce, ''Ai ina da ayyukan yi ne a gidan, kuma ina so na yi karatu. Faduwa ta juya ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ka taya ni rokonta ta ki zama. Ya dubi Faduwa ya juya ya dubi Umaimah sai ya juya ya ci gaba da kallon talabijin bai ce da su komai ba. Faduwa ta yi ajiyar zuciya ta tabe baki, ta mike tsaye kafin ta daga kai har Umaimah ta bace daga bakin kofar, ba ita babu ko inuwarta. Faduwa ta wawuro wayar Umaimah da cajar da sauri ta biyo ta waje tana kwalla kiran sunanta. Umaimah da Faduwa sun dade a tsaye a bakin lift suna magana, Faduwa tana nuna rashin kyautawa da Umaimah ta ke yi wajen rashin sakin jiki su saba har yanzu. Ita kuma Umaimah tana amfani da wasu hujjojinta wajen kare kanta. Daga karshe ta karbi wayarta suka yi sallama ta tafi gidanta. Faduwa ma ta dawo gida, ta iske Abdul-Sabur a zaune a inda ta bar shi. Babu yadda Faduwa ba ta yi da Abdul-Sabur ba akan ya ce wani abu game da al'amarin Umaimah, ya ki magana. Faduwa ta shiga zulumi akan wannan sauyin al'amari da yake gudana tsakanin Abdul da Umaimah Bello. Ta fara tambayar kanta, ''Shin Abdul-Sabur ya yi fushi ne da Umaimah ko kuwa da ni yake fushi ni da na kawo maganar so ya ji ya tsani daga ni har Umaimah? Don Faduwa ta fuskanci baya son maganar soyayya ballantana maganar aure a rayuwarsa. Ko kuwa wata *yar aljana ce ta aure shi ya ke gudun bil'adama? Allah Shi Ya barwa kansa sani. Ta bi Abdul-Sabur da kallo a lokacin da ya yi cimak ya mike har ya fice da alama babu walwala a fuskarsa, babu annuri sam a tare da shi. Faduwa ta yi tagumi tana tunani, Umaimah ta dagulawa yayanta lissafi, ya fara shiga halin da bata saba ganinshi a ciki ba. Ita dai a da wasa da dariya suke yi a koda yaushe baya fushi. Ta jiyo kauri a kicin, abincinta ya fara konewa, ta zabura da gudu ta shiga kicin tana magana ita kadai a lokacin da ta ke kashe wutar. Ta ce, ''Uhm, ina can ina tunani abincina zai kone a banza saboda son hada soyayyar da ba mai yiwuwa ba. Allah Ya yi mana jagora Ya zaba mana abin da ya fi alkhairi. *********************** Abdul-Sabur ne ya fito daga get din gidansu cikin tsaleliyar motarsa da sanyin safiyar laraba da alama dai sauri yake zai tafi makaranta. Dai-dai lokacin Umaimah ma ta fito kamar ta ci da kai don sauri. Ita ma rataye da jakar na'ura mai kwakwalwa a kafada (laptop). Tana hada ido da shi sai ta yi turus da alama ta dan razana, taso a ce akwai lungu da zata shige ta buya da ta labe idan ya tafi sai ta fito. Ya gangara gefe ya tsaya yana jiranta ta karaso tana tafe tana sanda dole dai ta iso gare shi dai-dai saitin tagar da yake zaune. Sai yayi sauri ya sauke gilashi ya leko da kai ya dube ta ya yi murmushi, sannan ya ambaci sunanta. Ta yi dan murmushi ta duka ta gaishe shi. Ya ce, ''Ina za ki je ne? Ta ce, ''Makaranta, ina da jarabawa. Ya gyada kai, ya ce, ''Af ku ma kun fara jarabawar, ni ma jarabawar zan yi. Ki shigo in fara sauke ki sai na wuce. Ta girgiza kai, ta ce, ''A'a ka tafi kawai zan karasa ai da sauran awa daya kafin mu shiga har zan karasa ma ba a fara ba, kada ka makara. Ya girgiza kai gami da yunkurawa ya bude mata kofar gaba ya ce, ''Ki shigo in kai ki ba damuwa ai. Nauyi, kunya da fargaba ne suka rufto mata a cikin zuciyarta. Nauyinsa ta ke ji, saboda ba su saba ba, ba ta san wacce irin hirar zata yi masa ba, ga shi daga ita sai shi yau babu Faduwa sarkin hira. Kunyarsa ta ke ji saboda abubuwan da ta yi masa a baya da kuma rashin kyautawar da ta yi masa akan tsaleliyar wayar da ya fitar da zunzurutun kudinsa ya saya mata ta ce bata so. Sannan fargaba ta ke kada jama'ar makarantarsu su ganta da shi kamar yadda rannan aka jeru ana kallonta da su. Dadinta ma wancan lokacin akwai Faduwa a zaune a gidan gaba, yau kuwa daga ita sai shi. Shin wanne irin kallo da fassara mutane za su yi mata game da wannan canjin da suka gani? Hannayenta da kafafuwanta har karkarwa suke da ta zo shiga motar ta zauna a hankali ta rufo kofar motar, ya ja suka fara tafiya. Duk da makarantar babu nisa daga gidansu, amma ta kagu su karasa ya sauke ta ya tafi ya bar ta. Tunda ta sunkuyar da kanta kasa ta damki jakarta kai ka ce in an ce kulle zata ce cas ta arta da gudu. Kallo daya ya yi mata, sai ya dauke kai ya lura da halin da ta shiga, don haka ya fasa jero mata dimbum tambayoyin da suke cikin ransa. Ya kunna CD yayin da wani kida mai dadi ya fara tashi gami da wata zazzakar waka tana fitowa, wakar ba da Hausa aka yi ta ba, haka ba da Turanci ba ce. Ta dago da kai a hankali ta dube shi, kauyanci ya hana ta jero masa tambayoyi game da wakar. Ko ba ta fada ba tabbas ya san tana so ta tambaye shi wannan wanne yare ne? Da suka hada ido sai ta yi sauri ta sunkuyar da kai kasa, ya yi murmushi ya dube ta. Ya ce, ''Kina da tambaya ne? Ta ce, ''A'a. Ya ce ''To ni ina da tambaya. Kin san sunan mawakin kuma da sunan yaren da ya ke wakar? Ta yi murmushi, ta ce, ''ba zan sani ba, saboda yaren Hausa, Fulatanci da Turanci kadai nake ji, shi kuwa ba irin su ya ke yi ba. Ya gyada kai, ya ce, ''Haka ne, amma ai ya kamata ki tambaye ni saboda ki karu, kin san tambaya tana kara ilimi, haka duk yaron da zai yi kokari a rayuwarsa za ki ga yana da yawan tambaya. Ko ba haka ba? Umaimah ta yi murmushi ta gyada kai ba tare da ta dube shi ba, kuma ba ta yi magana ba. Ya ce ''Wannan mawakin sunansa 'Akuri Afomsa' dan kasar Ghana ne, da yaren 'Asanti' yake wakar. Ya na magana akan soyayya yana fadar zafin rabuwar da ya ji a lokacin da ya rasa budurwarsa. Umaimah ta dago da sauri ta dube shi, sai ya yi mamakin kallon da ta yi masa tamkar tana tuhumarsa da wani laifi game da furucinsa. Ya dan yatsune fuska, ya ce, ''Lafiya ko na yi laifi ne da na fada miki fassarar wakar? Ko dai kina ganin kamar ina tsokanarki ne dan kin baro Ilah ko Abdul-Basi? Ta girgiza kai ba tare da ta yi murmushi ba ko magana. Daga nan Abdul-Sabur ya ja bakinsa ya yi shiru, don ya fuskanci duk nacinsa Umaimah ba zata saba da shi ba, ba ta da niyyar yin hakan. Sabuwar waka ce ya sake sakawa, ita ma dai mawakin Ghana ne mai suna 'Kwabula-Kwabula, shima da yaren Asanti ya ke rerowa, Umaimah ta tambaya. ''Ita kuma wannan akan me ya ke yinta? Abdul-Sabur ya yi mamaki da jin wannan tambayar ta Umaimah, sai ya ji farin ciki a ransa. Ya ce, ''Ya na waka ne akan mutuwa da ta raba shi da wadanda ya fi so a duniya, wato mahaifansa, da kuma masoyiyarsa. Umaimah ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa tana dagowa sai ya ga kwalla ta cika mata idanu. ''Lafiya kike hawaye? Abdul-Sabur ya tambaya cikin gigicewa mai tsanani. Ta yi sauri ta sharce hawaye da gefen gyalenta. Ta girgiza kai ta ce, ''Wani abu na tuna shine ya sani kuka. Abdul-Sabur ya ce, ''Yafindo ko? Yi hakuri ba ke kadai ba ce marainiya. Ki tuna fa ni da Faduwa babu uwa babu uba, gara ke da sauki tunda Baffa yana nan. Fatanmu Allah Ya gafarta musu, Ya saka su a aljanna, Allah Ya kai mu inda suka je a sa'a. Babu wanda zai yi saura a duniya. Ta sake surnano da hawaye mai radadi, ta ce, Amin. Shi wannan mawaki bai yi waka akan yara kanana da suka rasa uwarsu ba alhali bata mutu ba? Abdul-Sabur ta ji hankalinsa ya tashi da wannan tambayar tata, ya fahimci da *ya*yanta da ta baro ta ke. Sai ya girgiza kai, ya ce, ''Bai yi waka a kansu ba. Amma ai yaro don ya rabu da mahaifiyarsa alhali tana raye a duniya bai zama maraya ba, za su hadu wata rana. Dai-dai lokacin da ya zo makarantar ya sami waje ya tsaya sannan ya yi mata fatan samun nasarar jarabawa. Ta amsa da, ''Na gode, sai anjima. Ta yunkura zata fice, sai ta ji ya kira sunanta. Ta juyo da jajayen idanunta da suka jike sharkaf da hawaye, ta dube shi. Ya ce, ''Ina wayarki? Ta yi saurin sunkuyar da kai kasa, amsa ta gagare ta. Ya yi ajiyar zuciya ya ce, ''Kin baro ta a gida ko? To abin da nake bukata a wajenki shi ne, ki yi min alfarma ki nemo min lambar wayar Hanif a wajen abokanku, na san suna waya a junansu, ke ce dai ba kya waya da su. Ki karbo min lambar ina so in yi amfani da ita. Yau nake so kada ki ce min kuma kin manta. Ta gyada kai da alama dai ta cika da mamaki amma bata iya tambayarsa meyasa ba. Ta fita daga motar, tana shirin rufowa ta sake ji ya ambaci sunanta, sai ta fasa rufe kofar ta amsa masa cikin ladabi. Ya ce, ''Karfe nawa zaki tashi ne yau? Ta ce, ''Karfe sha biyu. Ya ce, ''Ni sha daya zan tashi zan biyo miki mu koma gida, sai in karbi lambar Hanif din, kada ki manta ki karbar min. ''Me zaka yi da lambar Hanif? Ta tambaya cike da damuwa. Ya fada cike da gadara, ''Me ake yi da lambar waya bayan kira? Zan kira shi ne kawai, kada ki damu bawai zan tona ki ba ne daga inda kika buya. Insha Allahu sai alkhairi. Ta dan yi jugum can ta gyada kai, ta ce, ''Zan tambayo maka lambar amma sai da yamma zan dawo gida, kada ka damu ba sai ka zo daukana ba. Ya gyada kai, ya ce, ''Ba damuwa, sai kin dawo din, Allah Ya bada sa'ar jarabawa. Ta amsa masa da, ''Amin na gode. Ta gaggauta rufo masa kofar mota ta yi saurin barin wajen. Ta kuwa yi sa'a babu jama'a a farfajiyar makarantar sosai, kasancewar sassafe ne. Abdul-Sabur ya dade a zaune a cikin mota kamar ba shi ne mai saurin nan ba, ya kasa tukawa ya tafi kasancewar damuwa, tausayi gami da jimamin hawayen da ya gani ya zubo daga idanuwan Umaimah. Tabbas Umaimah ta kasance abar tausayi, kuma abar tausayawa. Ta kasance marainiya, kuma ta bar danta ko *ya*yanta tamkar marayu. Zafafan hawaye ya dinga digowa daga cikin idanuwansa, har ya isa makaranta. Ya tuno da mahaifansa musamman mahaifiyarsa da ta sha fama da su suna kanana. Mutuwa ta dauke ta ga shi yanzu sun kawo karfin da za su iya taimakonta, amma ba ta nan. Tabbas duk mutumin da ya yi kokarin raba uwa da danta imaninsa ragagge ne, saboda tsananin soyayyar da uwa ta ke yiwa danta. Allah ne kadai isasshe, Shi ne mai rayawa, kuma mai kashewa, bayan Shi babu wanda zai raba soyayyar nan. ***************** Abdul-Sabur bai sake haduwa da Umaima ba sai bayan kwanaki uku, wato ranar asabar da yamma. Tabbas ya san gudunsa ta ke yi shi yasa ba ta yarda ta hadu da shi ba. Yana kwance akan doguwar kujerar falonsa ya hangota a tsaye akan baranda tana shakar daddadar iskar da ta ke busowa a yammacin wannan rana bayan da ruwan saman da aka yini ana yi ya dauke dif! Ya yi wuf ya mike ya fito barandarsa sai gasu kiri- kiri suna kallon juna. Ya yi mata murmushi gami da yi mata cikakkiyar sallama. Ta amsa masa ita ma gami da gaishe shi. Ya amsa mata cike da fara'a, ya ce ''Ya ya jarabawar? Karatun ne ya sa kika buya? To Allah Ya taimaka. Ta ce, ''Amin. Ga sakonka ma na karbo ba mu hadu ba shi yasa ban baka ba. Ya ji dadi da jin haka, sai ya yi dariya, ya ce, ''Yauwa na gode, amma ki ajiye min zuwa gobe da safe misalin karfe goma na safe mu hadu a gidan Faduwa. A ciki-ciki ta amsa masa, daga dukkan alamu ya fara takurawa rayuwarta fa. Tana jin nauyinsa ba zata iya yi masa musu ba. Abdul-Sabur ya lura da canji daga fuskarta, amma sai ya yi kamar bai san ta yi fushi ba, ya ci gaba da yi mata tambayoyi game da jarabawa, eh ko a'a kadai ta ke ambato yayin da ta shiga tunanin yadda zata shige gida ta rabu da shi. Da ya gane sai ya yi mata sallama ya shige abunsa ya barta a tsaye tana hararar kofarsa. Asuba ta gari Umaimah Bello!! **************** Washe gari ranar Lahadi kenan ta dade tana sake-sake a ranta ta ji kamar ta je gidan Faduwa su hadu ko kada ta je. Karfe goma har ta wuce da minti goma Umaimah na zaune a falonta bayan ta shirya tsaf ta kasa tashi ta fito. A bayyane ta ke mita, ''Wai shi wannan mutumin ba zai daina shiga harka ta ba? Lallai-lallai sai ya yi min katsalandan a cikin al'amurana? Ni daman tunda na ga ya siyo min waya na san akwai abin da yake shiryawa. Ina ruwansa da lambar Hanif? Wayarta ce ta dau kara, ta zabura ta dauko ta duba, lambar Faduwa ce ta shigo. Sai bayan da ta gama hararar wayar gami da siraran tsaki guda uku a jejjere, sannan ta dannan wayar ta kunbura kumatu ta rada sallama kamar dole. Baiwar Allah, Faduwa ba ta san abin da ake yi mata ba a nan, ita sai fara'arta ta ke tana kyakyata dariya. Ta ce, ''Umaimah kin tashi kuwa? Ga mu nan a nan mun hadu muna jiranki. ''Kun hadu kuna jirana ke da su wa? Umaimah ta tambaya cike da kidimewa. Faduwa ta sake kyalkyalewa da dariya ta ce, ''Matsoraciya, mai gudun mutane. To mu biyu ne ni da Abdul. Ta murguda baki sau biyu, sannan ta ce ''Na fito ina hanyar zuwa gidanki ma. ''Sai kin karaso''. Inji faduwa. Sannan suka kashe wayar su dukka biyun. Bayan ajiye wayarsu da kimanin mintina biyar, Umaimah Bello ta bayyana a gaban Abdul-Sabur da Faduwa. Zuciyarta babu dadi, amma tana karfin hali tana ta yin murmushi da ba ta shirya ba. Da ta duka ta gaishe su sai ta sami kujera a gefen su ta zauna tana mai tsananin fargabar abin da zai ce mata. Abdul-Sabur ya gyara zama ya karkata gaba dayansa yana dubanta, ya ambaci sunanta sannan ya dora da bayanai. ''Umaimah, dalilin da yasa na ce ki nemo min lambar Hanif ba wani abu ba ne illa ina so ki kira shi da layinki ku gaisa, ba wai in kun gaisa yau shikenan ba, a'a ku ci gaba da gaisawa har ma ku dinga ziyartar juna tamkar ke da kaninki Sabitu. Dalilina shi ne, ko za ki ki kula kowa a Malaysia bai kamata ki ki kula Hanif ba, saboda dalilan da kika fi ni saninsu. Hanif mai kaunarki ne, haka mahaifinsa ya yi miki halaccin da bai kamata ki yarda su ba. Umaimah ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, ji ta ke tamkar ta kurma ihu saboda dabaibayin da yake shirin lauya mata. Tabbas gaskiya yake fada mata, kuma ta yarda da hakan, amma fa ba karamin aiki yake shirin ya ballo mata ba a safiyar wannan rana. Ta fada a ranta, ''Me ya kawo ni wannan gida da zama da har na hadu da mutum mai naci da shisshigi? Na yi da sanin saninka Abdul-Sabur. Gaskia dole na tada Umaimah ta koma wani anguwar daban. Wannan takuran da mai yayi kama.. MAKWABTAKA 29 Ba ta gama tunaninta ba ya katse ta, ya ce, ''Ina lambar tasa? A sanyaye ta mika masa karamar takarda wacce ke dauke da sunan Hanif da lambar wayar daga kasan sunan. Ya karba ya duba ya tabbatar lambar ingatacciya ce, sai ya dago ya dube ta. Ta yi kicin-kicin da fuska tabbas ba za a dauki lokaci mai tsawo ba zata fashe da kuka. Don haka sai ya murtike fuska ya fuskanci ana fara lallashinta zata rushe da kuka, koma ta sami damar yin fushi ta fice. Ya fada cikin kasaitacciyar murya, ''Ba ni wayarki. Ta mika masa nan da nan. Ya tambaye ta, ''Akwai kudi? Ta girgiza kai, ta ce, ''Ban san ko akwai kudi a ciki ba. Ya shiga duba wayar ya ga ko sau daya ba ta kira wani ba balle a kira ta bayan Faduwa babu wanda ya taba kiran wayar. Ya yi ajiyar zuciya ya girgiza kai saboda takaici. Akwai kudi a ciikin wayar saboda layin da aka siya da kudi a ciki. Faduwa ta tsura musu ido tana kallon ikon Allah, tabbas ba don Abdul-Sabur ya gargade ta da kada ta yi magana ba, da tuni ta tunzura Umaimah da magana. Ya saka lambobin ya yi sabin sunan Hanif, sannan ya kira shi. Bugu daya ya dauka, Abdul-Sabur ya yi masa sallama, sannan ya gabatar da kansa. Ya ce, ''Sunana Abdul-Sabur, daga Kaula Lumpur, dan uwan Umaimah ne. Ina fatan ka san Umaimah Bello ko? Daga dukkan alamu Hanif ya cika da mamaki. Ya amsa cikin sauri. Kwarai na san Umaimah. Lafiya, me ya faru da ita? Abdul-Sabur ya ce, ''Lafiya kalau, wannan ma lambarta ce sai yanzu ta hada waya, shi ne zata yi maka magana. Abdul-Sabur ya mikawa Umaimah waya ta karba a sanyaye. Sai da Hanif ya ji muryarta ya saki jikinsa ya tabbatar ita din ce. Ya tambaye ta tambayoyi masu yawa, sai ta kasa amsawa nan da nan hawaye ya fara kwaranya. Ya ce, ''Anti Umaimah, me na miki ba kya nemana? Na kira Samir dan ajinku rannan na ce ya ba ki waya in gaishe ki ya ce ba kya yi masa magana, ba zai kai miki waya ba. Na kira Aisha Bingyal ita ma ta ce ba kwa magana ba zata kai miki waya ba. Na shigo garin naku ranar wata lahadi na ziyarci gidajen dukka *yan garinmu, na rasa mutum daya da ya san gidanki balle a rako ni. Haba Umaimah meye duniya? Me yasa kike gudun *yan kasarku, *yan uwanki don kin zo kasar fararen fata.... Ta katse shi cikin kuka, ta fara magana, ''Hanif, ba haka ba ne, ba gudunku nake yi ba wallahi wasu dalilaina suka sa na ware kaina daga gare ku. Ka yi hakuri Hanif, ka cewa Baba ma ya yafe min don Allah. Sai dukka biyun suka fashe da kuka, kuka ya ci karfin Umaimah har ta cire wayar daga kunnenta ta kifa kai akan gwiwarta. Abdul-Sabur ya yi sauri ya karba ya ci gaba da magana da Hanif. Hanif ya matse hawaye, ya ce, ''Na dade ba ni da lafiya watannin baya, ke ce ta farko wacce Babana ya tambaya saboda yana ganin ke ce tamkar *yar uwata makusanciyata, ke ya kamata ki zo kaina don har na fita hayyacina. Ya yi mamaki da aka ce ba a san inda kike ba, kuma tun ranar da muka iso rabona da ke kenan. Ya yi takaicin barina da kika yi, har yau yana tambaya ta ke. Na shaida masa kina nan lafiya, kuma kina Makaranta abokaina *yan makarantarku suna ganinki. Ko sanda ya turo mana da kudi watanni biyu da suka wuce ya ce in je in neme ki, in tambayeki ki kin sami kudin da ya turo miki? Shine lokacin da nake ta yiwa su Samir waya ba su nemo min ke ba, na zo da kaina ban ganki ba na hakura na koma, sannan na shaidawa Baba ban ganki ba. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Hanif kada ka damu, yanzu ga ka ga Umaimah, ga lambarta nan ka dauka. Kuma ka turomin da lambar Babanka ta wannan layin yanzu zata kira shi. Hanif ya sake matse hawaye ya ce' ''To, zan turo maka yanzu. Suka yi sallama suka kashe waya. Ba jimawa sako ya shigo Abdul-Sabur ya duba ya ga Hanif ne ya turo lambar Babansa. Ya dago ya dubi Umaimah har yanzu ba ta dago da kanta ba, tun sanda ta kifa kai akan cinya ba ta daina kuka ba. Ya ambaci sunanta, ta dago a hankali da jajayen idanuwanta ta dube shi. Ya ce ''Goge hawayenki ga lambar Baban Hanif zan kira ku yi magana. Hanif ya ce Babansa ya turo muku kudin da ya saba turo muku duk shekara. In ban manta ba kin ce miliyan dai-dai yake ba ku ko? Yana tambaya wai kin sami kudin a account dinki? Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Eh kudin ya shigo. Abdul-Sabur ya zazzare ido don mamaki ya kurawa Umaimah ido sai ta sunkuyar da kai kasa ya juya ya dubi Faduwa ta buga tagumi tana kallonsu. Ya sake juyowa ya kalli Umaimah sannan ya tambaye ta. ''Da kika sami kudin kin kira Baban Hanif kin yi masa godiya? Ta girgiza kai ta ce, ''Ba ni da lambarsa shi yasa ban kira ba. Ya yi shiru har zuwa lokaci mai tsawo, ya kasa magana. Can ya dago ya dubi Umaimah wacce har yanzu ta ke sharce hawaye da hankicin da Faduwa ta miko mata. Ya ce, ''A ganinki kin kyauta da ba ki yiwa mutumin da ya aiko miki da wadannan makudan kudi godiya ba Ta yi shiru ba ta amsa masa ba. Ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Allah Ya kyauta. Don ya fuskanci al'amarin Umaimah ya girma har yana so ya fi karfin tunaninsa. Sannan ya matsa lambar Baban Hanif. Ta yi ta ringin har ta katse bai amsa ba, yayin da Abdul-Sabur ya ci gaba da kira ba kakkautawa. Hankalin Umaimah ya tashi matuka zuciyarta ta hau dukan uku-uku tana fargabar abu biyu. Na farko, yadda Alh. Nasir zai karbe ta don dole zai yi fushi da ita saboda gaskiya ta tapka masa laifi. Na biyu, tana fargabar kada a kira shi a gaban Lamijo kawarta kishi ya kamata alhali sun boye mata zuwanta Malaysia. Ta yi zumbur ta mike tsaye kamar wacce aka mintsina. Ta ce, ''Kada ka yi masa maganata, sai ka tabbatar ba a gida yake ba saboda labarin da na baku game da yadda muka yi da matarsa Lamijo. Kafin Abdul-Sabur ya ce wani abu Alh. Nasir ya kira lambar da yaga Missed call rututu. Kafin ya amsa Abdul-Sabur ya ce da ita ta kwantar da hankalinta ta koma ta zauna ya san abin da zai ce masa. Ya dannan da sauri ya amsa, ''Hanif dan albarka, ya naga ka canja layi kuma, ko ka yarda wayar taka ne? In ji Baban Hanif. Abdul-Sabur ya dukar da kai kasa, ya ce, ''Alhaji ina wuni. Ba Hanif ba ne, yanzu dai Hanif din ya turo min da lambarka. Sunana Abdul-Sabur Abdul-Rashid, ni ma dan kasarku ne Nigeria. Kana hanya ne ko kana gida? Ina so na yi magana da kai. Alh. Nasir ya ji hankalinsa ya tashi matuka sai ya zaci wata matsala ce ta sami dansa, musamman da ya sha rashin lafiya kwanaki. Yana fargaba ko ciwon ne ya tashi. Nan da nan jikinsa ya dau bari, muryarsa ta yi ta makyarkyata ya tashi zaune daga kwanciyar da yake. Don alokacin da Malaysia suke karfe goma sha daya na safe, a Nigeria kuma karfe shida ne na yamma banbancin awanni bakwai ne a tsakani. Alh. Nasir ya ce, ''A'a, ai na fito kofar gida muna shirin yin sallar magruba. Lafiya, me yake faruwa ne? Abdul-Sabur ya ce, ''Lafiya kalau Alhaji kada ka damu, tunda sallah za ku yi idan ka idar ko gobe da safe za muyi maganar. Alh, nasir ya girgiza kai, yayin da ya yi wuf ya mike tsaye. Ya ce, ''Ba damuwa, ina ma Abuja ni kadai ne, ba'a kira sallar ba. Abdul-Sabur ya yi mumushi, ya ce, ''To ba damuwa ranka ya dade, a nan ina tare da *yarka kuma kawar matarka Umaimah. ''Umaima Bello! Umaimah!! Alh. Nasir ya tambaya ya sake nanata sunan. Abdul-Sabur ya ce, ''Sai yanzu ta hada waya tun zuwanta ba ta da waya. Muka kira Hanif ya turo mana lambar wayarka. Alh. Nasir ya ce, ''Wannnan wacce irin rayuwa ce? Me muka yi mata da ta ke gudunmu? Haba Malam kai ma ka san Umaimah ba ta kyauta min ba. Taimako da nake mata ba zan fasa ba saboda don Allah nake yi, a wajenSa nake neman lada. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Ka yi hakuri Alhaji, ba yanzu zaka fahimce ta ba, ni zan yi maka bayanin dalilinta. Kamar yadda ka sani Umaimah tana da matsaloli da tashin hankalin rashin uwa, *yar uwa, miji da kuma danta da dan *yar uwarta. Alh. Nasir ya gyada kai, ya ce, ''Haka yake, ta ba ni labari. To amma ai duk ya wuce, Allah Ya masanya mata rayuwa mafi alkhairi. A tunanina ta warware ta fitar da waccan matsalolin da suka addabi rayuwarta. To ashe in dai damuwa zata saka a ranta ba ta iya yin karatun ma daya kai ta kenan kudi ake kashewa a banza. Abdul-Sabur ya duka ya ce, ''Ranka ya dade tana karatu sosai ma kuwa, ba ta da matsala. Ga ta ku fara gaisawa tukunna. Umaimah ta dafe kirji tun sanda Abdul ya fara waya da Baban Hanif, saboda tashin hankali. Hawaye ne kawai yake zubowa face-face tana jiyo duk abin da suke cewa. Ta yi sallama cikin girmamawa da shesshekar kuka, sannan ta duka ta gaishe shi cikin harshen fulatanci. Ya amsa gami da tambayarta lafiyarta da kuma karatunta. Ya dora da nuna mata rashin kyautawarta da rashin tunani akan hukuncin da ta yankewa kanta na fita daga harkar kawaye da *yan uwa. Ba ta neman kowa ta yi dif! Kamar wacce ba ta duniyar. A matsayinsa na uba ya dade yana yi mata fada, nasiha da jan kunne busa kuskuren da ta tafka cikin harsunan nan uku, Hausa, Turanci da Fulatanci yarensu. Kalmar, ''I am sorry sir, Alhaji yi hakuri, Baba mutubi'am. Amsar da ta ke ta ba shi ke nan har ya yi mata sallama ya kashe waya. Da alama Baban Hanif ya yi fushi da Umaimah, amma hawayen nadama, tuban da ta ke yi da hakurin da ta dinga ba shi ya sanyaya masa zuciya matuka. Har ya dora mata doguwar addu'a kafin ya ajiye wayar. Wannan karon kukan dadi da samun sauki daga kullutun da ya dankare mata a zuciya ta ke fitarwa. Hakika yau Umaimah ta dan ji sanyi daga tsantsar damuwar da ta dade tana addabarta. Abdul-Sabur ya dauko wayarsa ya dauki lambar Hanif da ta babansa sannan ya mika mata wayarta. Kalmar da ya fada mata ta karshe wacce daga ita ya mike tsaye ya fice ita ce, ''Umaimah ki yi hakuri ki daina kuka, don ba zai yi miki maganin matsalarki ba. Ki yi addu'a sannan ki yi hakuri sai kuma ke da kanki ki gyara lamuranki da jama'a. Idan kika yi haka za ki inganta rayuwarki, kuma ki ji dadinta duniya da lahira. Sai anjimanku. Ya fice ya bar su a zaune, Umaimah ba ta daina kuka ba, sabon shafi ma ta bude na kuka. Yayin da Faduwa ta rungume ta tana lallashi tamkar wata *yar jaririyar goye. Umaimah ta kasa tafiya gida a gidan Faduwa ta yini, suka dafa abincin rana suka ci, suka yi sallar azahar da la'asar, suka yi kallon talabijin suka yi ta hira. Hakika Faduwa ta zauna ta bawa Umaimah shawara game da yadda zata yi mu'amala da jama'a. Ta gargade ta da ta canja halayenta, domin shi mutum rahma ne. Dole ta canja wannan ra'ayin nata na kin kula mutane da gudun danginta da *yan kasarta. Ya zama dole ta bi Abdul-Sabur a hankali har ya samar mata mafita. Amma ko da wasa Faduwa ba ta sako mata maganar soyayyar da ta ke shirin kullawa a tsakaninta da Abdul-Sabur ba, saboda kada Umaimah ta zaci da wata manufar yake kula da ita. Kuma tana gudun bacin ran Abdul-Sabur kada ta furta wata kalma da zai yi fushi da ita. Umaimah ta fara saduda, a yau ta fuskanci rashin kyautawarta barobaro a zahiri, wacce ta yiwa Alh. Nasir da dansa Hanif. ''Tabbas na san Abdul-Sabur mutum ne mai fadar gaskiya komai dacinta, haka yana kokarin kwatantawa. Ba ya fushi, kuma bai damu da duk bakar maganar da za a fada masa ba. Umaimah take fada a ranta. Umaimah ta sake yiwa Faduwa sha'awarsa don tabbas zata yi dace da miji na gari idan har hakan ta kasance. ******************* Tsakar dare misalin karfe uku Umaimah na zaune a tsakiyar gadonta, ta mike kafa don bacci ya kauracewa kwayar idanunta. Ta fuskanci kuka ma ba zai yi mata wannan magani ba, sai addu'a. Tana ta jan carbi tana karanto 'hailala da istigfari, sannan lahaula wala kuwwata illa billahil azim. Fitilar dakin Abdul-Sabur ce aka kunna nan da nan taga hasken ya hasko mata daki, don haka sai ta tsurawa dakin ido. Da alama ya tashi daga barci, shi yasa ya kunna fitilar. Ta tashi a hankali ta je jikin windo ta daga labule tana duban inuwarsa yana ta kai kawo a cikin dakinsa. Ba ta ankara ba sai ganinshi ta yi a jikin windonsa yana kallon windon dakinta, sai ta yi sauri ta durkusa tana kyautata zaton ya ganta. Sai ta ga ya gyara labule ya sake rufewa, ya koma ciki da alama magana yake yi a waya. Ya wuce zuwa falonsa sai ta ji motsi ya bude kofar kicin ya shiga. Tana jin karar bude firij ya zuba lemo a kofi ya sha, ya bude kofar barandar waje ya fito baranda duk tana sanda tana hango shi. A halin yanzu in ta yi sa'a zata iya jiyo abin da yake cewa, saboda dare ne kuma harshen Hausa ya ke magana. Tana tsaye a cikin kicin a makale a jikin kofa, sai dai kash, ba zata iya bude kofar baranda ta fito ba, saboda zai ganta. Babu tantama ta ji ya ambaci sunana Baban Hanif daga dukkan alamu da Alh. Nasir yake waya. Kwatsam sai ta ji ya ambaci sunanta baro-baro. Ya ce, ''Alh Umaimah tana da hankali, amma tana neman taimako wajen kula da ita don kada ta shiga wani hali na bakin cikin rayuwa, Allah ma dai Ya kiyaye. Ta yi wuki-wuki ta rasa yadda zata yi ta jiyo sauran abin da ya ke fada, don ya koma cikin gida ya rufo kofar. Tana hango inuwarsa a zaune akan dinning table yana hada shayi har yanzu wayar na sakale a kunnensa yana magana. Tabbas sun shafe fiye da awa guda cur suna maganarta. Ta jawo wayarta ta duba tsaf, babu lambar Abdul-Sabur a cikin lambobin da ta ke da su, lambobin mutane uku ne kacal a ciki, daga ta Faduwa, Hanif sai ta Babansa. Ta ji duk ta damu kanta, sai ta ji abin da suke fada amma kuma babu hanyar da zata ji don haka ta cirewa kanta damuwa, tasan koma me za su fada alkhairi ne. Duk laifin da ta yiwa Alh. Nasir tasan Abdul-Sabur yana da wayon da zai kare ta. Dole ma Alh. Nasir ya ji sanyi a ransa in dai Abdul-Sabur ya jawo masa hadisai da ayoyin alkur'ani. Jikinta ya yi sanyi ta tashi ta dauro alwala ta hau nafilfili har aka kira assalatu, ta yi sallah ta sha ragargazo addo'i akan Allah Ya yaye mata duk wani abu da yake damunta na kunci a rayuwarta. MAKWABTAKA 30 Washe gari litinin ce amma ita ba ta da jarabawa, don haka ba zata je makaranta yau ba. Ta fito ta tsaya akan baranda tana shakar sanyayyiyar iskar da ta ke kadawa. Abdul-Sabur ne ya hango ta, ya yi kamar zai fito su gaisa sai ya fasa ya fuskanci ba ta son a cika shisshege mata. Ya shirya tsaf cikin bakar riga da wando na suit ya fice kasa. Tana daga sama ta hango giftawarsa ya sauko, sai ya wuce zuwa gareji ya dauko motarsa. Bai dago da kansa ba balle tasan ya ganta a tunaninta bai san tana tsaye akan baranda tana kallonsa ba alhali ya sani. Tana tsaye tana leke har ya fita daga get din ya figi motar ya hau titi, daga dukkan alamu sauri yake yi yana da jarabawa da sassafen nan. ''Tabbas ka yi dace da hali na gari, Allah Ya ba ka mace ta gari Abdul-Sabur. Umaimah ta fada a cikin zuciyarta, yayin da hamma ta hana ta sakat saboda baccin da ta ke ji, ta kwana idonta biyu. Sai yanzu baccin ya zo. Hawaye ne yake kwararowa daga idanunta da zarar ta yi hamma, sai yinta take ba kakkautawa, mafita daya ce ta je ta kwanta ta yi bacci, amma sai ta cika tumbinta zata yi bacci daga dukkan alamu tabahuwa zata iya hana ta baccin. Kan ka ce kwabo ta shige kicin ta jona butar ruwan zafi (kettle), nan da nan ta tafasa ta hada shayi ta sha da biskit. Daman yawancin abincinta ke nan, ba ta cika cin abinci mai nauyi ba, shi yasa har yanzu kiba ta gagare ta. Da kyar ta ke takawa ta shiga daki, da rarrafe ta hau gado saboda tsananin baccin da ya yi mata nauyi a ido. Abu na farko da ta fara tunawa shine: ''Shin ko yaya Abdul-Sabur ya ke ji shima da ya kwana yana yawo yana waya bai runtsa ba? Da safe bai yi bacci ba ya fita zuwa makaranta. Ta fada a bayyane ''Ka ga bayin Allah masu kaunar *yan uwa musulmai, matsalar wani ta zama matsalarsu. Allah Ya saka masa da alkhairi. Daga nan ta rufe ido bacci mai dadin gaske ya rufeta, sai ta dora da mafarkai masu dadi. Umaimah ta yi mafarki Alh. Nasir ya zo yana fara'a yana ambaton sunanta har ya ce da ita tare muke da kawarki Lamijo zo mu je inda ta ke ku gaisa. Umaimah ta hau murna a cikin mafarkin tana fadin, ''Alhamdulillah da Lamijo ta fahimce ni ta bar zargina. Sai taga Abdul-Sabur ma a mafarkin ya yi murmushi ya gyada kai, ya ce, ''Dauki takalmanki sababbi ki saka ki je ku gaisa da kawarki. Ta yi zumbur ta bude ido, sai ta ga ashe mafarki ta ke yi. Hakika mafarkin nan ya bata mamaki matuka. Sai ta tofa addu'a Gabas da Yamma, Kudu da Arewa ta canja yanayin kwanciyarta ta ci gaba da barci. Mafarkai makamantan wadannan dai ta ci gaba da yi. Bacci ya yi bacci abu kamar wasa, har karfe uku saura mintina na rana sannan Umaimah ta farka daga baccin nan da ta ka yi, shi ma a sanadiyyar wayar da Hanif ya rangado mata ne ya tashe ta, ba don baccin ya ishe ta ba. Ta yi sauri ta mika hannu ta wawuro wayar ta duba sai ta ga sunan Hanif ne, nan da nan ta amsa. Hanif ya gaishe ta cikin ladabi, ''Anti fal bakinsa haka yake kiranta kamar yadda ya ke kiran Lamijo matar Babansa. ''Anti ya makaranta? Ya ya karatun jarabawar, koda yake fa Anti ba kwa tsoron jarabawa na ji labari irin pionts din da kike ja. Ance 4pointer ce ana kyautata zaton da first class za ki fita. Ashe ba'a banza ba da ba kya kula mutane boko ne kadai a gabanki. Ta tuntsure da dariya da bata shirya ba, sai ta nemi baccin da ya ke idanuwanta ta rasa. Ta ce da shi, ''Kai Hanif wa ya fada maka haka? Kai ne dai ka kirkiro hakan don ka tsokane ni. Ya ce, ''Wallahi an fada min, ba daga bakin mutum daya na ji haka ba, *yan ajinku ma sun fada min. Ke ki rantse in ba haka ba ne kamar yadda na rantse. Umaimah ta kyalkyale da dariya, ta ce, ''To meye abun rantse-rantse tunda ka ce haka ne, to abarshi a hakan. Hanif ya ce, ''Kin san haka ne ke ma. Amma ai abun alfahari ne ma a wajenki, ni da zan sami haka ai da na dinga dagawa ina alfahari a kasar nan da ma Nigeria gaba daya. Tanadi na musamman fa gwamna ya yiwa wanda ya fito da first class a cikinmu, kuma ya yi alkawarin zai biyawa wanda ya fita da first class kudin karatun master da PhD a kowacce kasa ya ke so yayi a duniya. Bayan babban aiki da za a bashi a gwamnatin garinmu. Ina ga ku biyu ne za ku sami wannan garabasar ke da wani Abba Ahmad dan makarantarmu. Umaimah ta yi murmushin farin ciki, ta lumshe ido ta ce, ''Alhamdu lillahi, kai ma fa idan ka dage zaka iya kamo mu ka fito da first class. Hanif ya kyalkyale da dariya, ya ce, ''A yaushe kuma bayan saura shekara daya da kadan mu gama, an cinye rabin karatu ina zan iya kamo ku? Mu dai ki barmu a second calass upper ko lower ma ai kwakwalwar ma ba iri daya ba ce. Baba ya ce kun kira shi jiya, ya yi farin ciki sosai, ya ce idan an yi hutu in dinga ziyartarki muna gaisawa. Kuma idan an yi hutu in tambayeki in kina so ki zo ki ga gida zai aiko mana da kudin tikiti. Sai ta ji kamar ya daba mata wuka a kirji, ta dafe kirji ta yi firgigit ta tashi ta zauna. Ta ce, ''A'a bazan je gida ba, sai na gama sai dai ka tafi kai kadai. Hanif ya ce, ''Ba ga irinta ba, mu ne masu yin nisa da littafi ku masu kokarin nan ba kwa yin nisa da littafinku, boko ya hana. Suka yi dariya su dukkansu, daga karshe suka yiwa juna fatan alkahairi da sallama suka kashe waya. Umaimah ta ji dadin hira da Hanif, yaro mai kirki da ladabi, sai ta ji sanyi a ranta tamkar ta ji muryar dan uwanta rabin jiki Sabitu. Tana duba agogo ta ga lokaci ya ja azahar har ta gota, sai ta yi wuf! Ta diro daga kan gado tana fadin, ''Astagfirullah! A'uzu billah, na makara azahar ta wuce ban yi sallah ba. Gaskiyarki Umaimah, sallah ita ce gaba da komai. Allah Yana hukunta masu aikata tarikul salat. Allah Ya mana jagora, Ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, amin!!! ************** Faduwa ce a tsaye a gaban kofar gidan Umaimah da yammacin ranar juma'a, Umaimah na bude kofa sai ta ga bakuwarta. Farin ciki ne ya duro mata mabayyani a fuskarta. Ta yi sauri ta rungume ta gami da ruko hannunta suka zo suka zauna a cikin falo akan kujerun nan nata na alfarma. Faduwa ta dube ta ta yi murmushi, ta ce, ''Ya na ga kin rame ko jarrabawa ce? Umaimah ta taba kashin wuyanta, ta ce, ''Jarabawa ce Anti, bana iya cin abincin kirki kullum. Faduwa ta ce, ''Bayan jarabawar fa, meye yake ramar da ke? Sai Umaimah ta yi kasake tana kallonta ta kasa amsa wannan tambayar. Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Kin saka damuwa a ranki da yawan tunani, ga kuka kullum. Ki daina, babu kyau ko don lafiyarki ma, mu likitoci ba ma son haka. Nan da nan idanuwanta suka ciko da kwalla da alama da wani kukan zata fashe. Faduwa ta ce, ''Au tuno miki ma na yi? Shi ne za ki bude min sabon shafin kuka? A'a kada ki tayar min da hankalina, na zo mu yi hira wasa da dariya kuma zaki fashe da kuka? Umaimah ta yi sauri ta goge idanunta, ta yi murmushin karfin hali, ta ce, ''To na goge hawayen na daina kukan, mu yi hirar. Faduwa ta shafi kuncinta ta ce, ''Yauwa kanwata, ko ke fa rayuwa ma yanzu za ki fara. Nawa kike da zaki nemi kashe zuciyarki? Ki sakawa ranki damuwa. Abdul-Sabur ya aiko ni wajenki, ya ce in ce ki ba shi lambar Abdul-Basi... Faduwa ba ta rufe bakinta ba Umaimah ta zabura ta mike tsaye gami da dafe kirji. Ta ce, ''Subhanallahi, ina zan sami lambar Abdul-Basi? In ina da ita ma me zai yi da ita da yake nema? Me ye hadina da Abdul-Basi? Me Abdul-Sabur yake nufi da yake neman in ba shi lambar Abdul-Basi? Kada ya sake ya ce zai dai-daita ni da shi don in koma gidansa a matsayin matarsa, da in yi haka gara a dauki gawata a kai masa. Faduwa ta mike tsaye cike da damuwa, da kuma mamaki, ta dafa kafadar Umaimah. Ta ce, ''Ya naga hankalinki ya dugunzuma daga kiran sunan Abdul-Basi? Mijinki ne fa uban danki ya aka yi kika zamar da shi makiyi? Umaimah ki fahimci Abdul-Sabur shi mutum ne mai son shirya alkhairi, me son ya ga hankalin kowanne musulmi a kwance, musamman mu mata da muke kasar da babu dangin iya babu na Baba. Ki bada lambar tasa ki zuba masa ido ki ga wacce hikima zai bullo da ita... Umaimah ta katse ta kafin ta rufe bakinta, ta dakatar da ita da hannu sannan ta zame kafadarta daga hannun Faduwa, hawaye ya yi mata face-face a fuska. Ta fada cikin kakkausar murya. ''Anti Faduwa, ba zan boye miki ba Abdul-Sabur yana yawan takura min a rayuwa yana saka ni a cikin wani hali, yana saka ni aikata abubuwan da ba na ra'ayi. Wannan karon dai sai dai ya yi hakuri bazan aiwatar da abin da yake so na yi ba. Sai dai in a kashe ni amma ba zan yi magana da Abdul-Basi ba. Kada Abdul-Sabur ya ga na yarda na gaisa da Hanif da Babansa ya zaci zan yarda in yi magana da abdul-Basi. Faduwa ta yi dan murmushi, ta ce, ''Abdul-Sabur ne ya aiko ni ya ce in kin ki bani inyi masa waya ya zo da kansa. Umaimah ta ce, ''Ko ya zo da kansa ba zan iya ba shi lambarsa ba balle ma ban san lambarsa ba.. Ba ta rufe baki ba sai ga Abdul-Sabur a gabanta. Nan da nan ta zabura ta yi wuki-wuki da ido kamar ba ita ba ce take fiffikala ba yanzun nan. Ya zura mata ido yana kallo, sai ta yi sauri ta sunkuyar da kanta kasa. Daga dukkan alamu daman a kusa da kofar ya ke, ya ji dun abin da ta fada. A sanyaye ta sami kujera ta zauna ta rike kai, yayin da hawaye zazzafa ya dinga digowa daga idanunta. Zuciyarta ta yi ta tafasa, wani sabon tashin hankalin matsalar rayuwa ne suka zubo mata. Malaysia ta yi mata zafi, ta ji dama ba ta zo unguwar nan ba balle tasan Abdul-Sabur. Ta ji ta tsane shi tsanar da ba ta yi masa irin ta ba a baya. Tabbas yana yawan shigar mata hanci da kudundune amma a yau ta shirya tsaf zata fyeto shi. Ta kuduri niyyar tashi daga gidan nan a cikin satin nan, kuma har abada ba zai taba sanin inda zata koma ba, balle ya takura mata. Ina ruwansa da rayuwarta da zai saka mata ido ya damu da sai ta shirya da mutanen da ba ta bata da su a baya? A mutanen har da Abdul-Basi mutumin da ya shayar da ita ruwan madaci, ya wahalar da ita, ya ci amanarta, ya rabata da abin kaunarta a duniya *ya*yanta. Tana cikin wannan tunani da murkusun takaici, kanta a sunkuye a kasa yayin da hawayen takaici ya ci gaba da bulbulowa daga matse-matsin yatsunta na hannu data dafe fuskarta da su. Ya rasa kalmar da zai fara furta mata, saboda bai zaci har wannan abun da ya nema ba zai sakata a cikin wannan tashin hankali ba. Ya yi ajiyar zuciya mai karfi, ya sunkuyar da kansa kasa ya dauki lokaci mai dan tsawo a tsaye a kanta, sannan ya zaro wayarsa ya nanika mata a cikin hannayenta. Ta zabura ta dago da jajayen idanunta ta dube shi, duba irin na rashin fahimta da takaici. Ya fada cikin sororuwar murya mai cike da tausayawa gami da lallashi, 'Saka min lamabar Abdul-Basi a wayata na ce, ba a wayarki ba. Kuma ni bance zan kira shi don ku yi magana ba, haka bance zan sasantaku ba don ku koma. Na miki alkawari babu wani abu da zan yi don in jawo ranki ya baci, ko hankalinki ya tashi. Tsakani na da ku sai fata na gari da dimbin alkhairi. Ta dube shi, ta juya ta dubi Faduwa wacce ke gefe sai kifta mata ido ta ke, tana yi mata nuni da hannu alamar ta rubuta masa lambar wayar. Umaimah ta zamo tamkar wacce kwakwalwarta ta zare, kamar ba ta da wata dubara ko tunanin kanta sai yadda suka yi da ita. Ta karbi wayar ta zurawa wayar Abdul-Sabur ido tana jujjuyawa. Ta ci gaba da zubo da wani sabon baiti na hawaye mai radadi wannan karon hawayen tuno da takaicin da Abdul-Basi ya guma mata a rayuwa ta ke yi. Ta shiga danno lambarsa a hankali, yayin da zuciyarta ta ke rababbaka, bata taba zaton akwai ranar da zata zo da har zata danno lambar wayar Abdul-Basi ba. Abdul-Sabur ya cuci rayuwarta da ya tursasa mata take yin abn da ba ta so, amma yau komai zai kare saboda a bisa sharadin barin gidan nan ta ba shi lambar shi ne dai bai sani ba. Ta mika masa wayarsa ya kurawa lambobin ido, da alama dai kirgawa yake yi sai da ya tabbatar sun cika. Sai ya matsa code number Nageria ya kira lambar, yana dannawa ta shiga ya tabbatar tana aiki ko ba ta yi. Yayin da numfashin Umaimah ya ke kokarin daukewa saboda tashin hankali, amma ta kuduri niyyar ko me Abdul-Sabur zai mata yau ba zata yi magana da AbdulBasi ba. Ta ci gaba da addu'a Allah Ya sa ya canja layi a kasa samunsa, kuma daman layinsa daya na MTN din nan. Abdul-Sabur ya yi murmushi ya gyada kai, da alama dai ya ci nasara lambar ta shiga sai ya katse. Ya dubi Umaimah, duba na tausayi ya girgiza kai, ya juya ya dubi Faduwa. Ya ce, ''Ki lallashe ta ta daina kuka, ki fadakar da ita manufata. Ya juya da sauri ya fice bai sake waiwayowaba. Faduwa ta karaso kujerar da Umaimah ta ke zaune, sai ta zauna a hannun kujerar ta rungume ta. Ta ce, ''Yi shiru kanwata, na san zaki tsane mu yanzu, amma nan gaba zaki yabe mu. Mu masu sonki ne, kuma masu son inganta rayuwarki ne. Zo mu je gidana mu yini saboda ki sami saukin bacin ran. Umaimah ta fizge jikinta tana magana cikin shasshekar kuka ta ce, ''Kaina ne yake ciwo magani zan sha na kwanta. Faduwa ta ce, ''Allah Ya sauwake, mu je gidana in ba ki magani in kisha ki kwanta. Umaimah ta sake turo baki gaba don takaici, ta ce ''Ina da magani a daki. Faduwa ta ce, ''To ki je ki sha ki kwanta. Bari in tafi in barki, ki huta sai mun hadu gobe. Faduwa ta tashi ta fice fuskarta har yanzu cike da murmushi, don ita ba ta fushi. Yayin da Umaimah ta bita da harara don tsana. Fitar Faduwa ba jimawa Umaimah ta tashi a fusace ta banko kofar gidan ta ta datse da mukulli gami da karawa da sakata. Ba don jarabawa ta ke zanawa ba da sai ta shafe sati guda a cikin gida bata fita ba, kuma ba zata kunna fitila ba balle a san tana ciki. Tsananin takaicin da take ji bata ki a wayi gari a ganta a mace ba don ta huta. Kalmar 'La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin. Ta yi ta karantowa a ranta, sannan ta fara jin sa'ida a zuciyarta. Don ma bacin rai ba ya hana ta yin karatu da a yau ba zata yi karatuba. To daga anzo maganar karatu tana iya jingine damuwa ta lura da littafinta har sai ta gane. Allah Ya yi mana maganin duk wata masifa, Aamiin!!MAKWABTAKA 31 Sati ya zagayo Umaimah ta kammala jarabawarta babu abin da ya yi mata saura sai shirin tashi daga gidan nan. Har ta fara cigiyar gidajen haya a unguwa mai nisan gaske yadda su Abdul-Sabur ba zasu sake ganinta ba. Amma fa ta fara jin dadin wayarta saboda Hanif kullum sai ya yi mata waya sun sha hira. Haka jifajifa babansa yana kiranta su gaisa ya tambayi lafiyarta da karatunta. Ita ma in aka kwana biyu sai ta yi masa flashin in dai ba ya aiki, ko baya tare da Lamijo sai kaga ya kira ta su gaisa. Don ba ta son ta kira shi lokacin da yake tare da iyalinsa, kada su zarge shi da wani abu. musamman Lamijo da tuni ta zarga. Lambobin mutane tara gare ta a wayarta, a kalla a kowacce rana mutane biyar suna kiranta su jima suna hira. Mutanen kuwa sune Hanif, Baban Hanif, Faduwa, Aisha Bingyal, Binta Hamisu, Tahir Aliyu duk *yan Gombe ne *yan ajinsu. Sai kuma sauran ukun kuwa malamanta ne na makaranta matan nan biyu da suka yi zaman jinyarta a asibiti *yar India da *yar Malaysia Mrs. Sonia, da Mrs. Rabi'at, sai lambar Mr. Cheu HOD department dinsu. Wasu daman tana da lambobinsu a rubuce rashin waya ne ya sa ba ta kira su ba, kamar Malamanta. Dalibai *yan uwanta kuwa da suka ga waya a hannunta sai suka karbi lambarta, idan ta dawo gida sai ta ji suna kiranta sai ta yi saved number masu hankali cikinsu. Tabbas Umaimah ta fara ganin canji a rayuwarta don a yanzu daga safe zuwa lokacin da rana zata fadi zata yi hira da bil'adama ta yi murmushi, ta yi dariya har ta kyakyace, musamman idan Hanif ya kira ta baya gajiya da magana, baya kuma jin tsoron katin waya don yana da ishasshen kudi. Kawayenta suna kiranta su fada mata halin da makaranta ta ke ciki, duk ranar da bata fito da wuri ba haka malamanta tana kira ta tambaye su abubuwan da ta ke bida ta ji na game da sakamakon jarabawar da suka gama jarabawa. Ta ji shin an gama dubawa (making) ko ba a gama ba, da dai suaransu. Ta fara jinta ta dawo cikin duniya tsundum don a da tana ganin kamar ba a raye ta ke ba, ita kadai sai ta yi kwana uku ba ta yi ko tari ba a cikin gida, komai ba ya mata dadi, ko abinci ta dafa sai ta kasa ci. Allah Ya kauta. ******************* Ranar litinin ce da misalin karfe goma na safe da yake ba makaranta zata je ba, don haka ko wanka ba ta yi ba, tana sanye da rigar baccinta. Shayi da lifton ne kawai ta ke kurba, ko madara babu yayin da ta mike kafa a tsakiyar falo akan kafet tana kallon talabijin tashar MBC 4 suna shirin 'The Doctors'. Tana jin dadin yadda ake jero abincin da masu kiba zasu ringa ci don su rage kiba. Ita da ta kekashe ba kibar ta kudiri niyyar shi zata dinga ci don ta yi kiba, sai dai kash ! Ko ta sissiyo ma ba iya ci zata yi ba, saboda rashin kwanciyar hankali. Ta yi ajiyar zuciya mai karfi ta fada a bayyane. ''Allah kai ne jagorana ka kawo min agaji a bisa al'amurana. Ka musanya min damuwar nan ta koma farin ciki a rayuwata. Sai ta girgiza kai ta zubo da kwalla. Kwankwasa kofar da ta ji ana yi ita ce ta ba ta mamaki a dai-dai wannan lokaci. Mamaki bai tsawaita ba saboda tana kyautata zaton Faduwa ce. Ana ta kwankwasawa kofa gami da danna kararrawa duk lokaci guda. Ta taso a hankali ta leka ta jikin hudar kofa. Faduwa ta gani, don haka ba ta damu da neman hijabi ko dankwali ba, amma fa sai da ta yi dan siririn tsaki, sannan ta bude kofar a sanyaye. Faduwa ta yi sallama ta shigo sai ta rada mata cewar su biyu ne da Abdul-Sabur, ta je ta sako hijabi. Umaimah ta arta cikin daki da gudu don kada ya sako kai ya ganta a haka. Har yanzu Abdul-Sabur yana tsaye daga waje bai shigo ba sai da Faduwa ta sake lekowa ta yi masa iso ya shigo. Sun jima a zaune akan kujera, Umaimah ta ki fitowa bayan ta saka dogon hijab ta daura zani, sai ta yi zamanta a gefen gado ta cika ta yi fam! Kamar zata fashe. Da zata iya datse kofar dakinta zata yi ta ki fitowa in sun gaji sa tashi su tafi. Tana ganin girmansu har yanzu haka kuma wulakanta mutum babu dadi shiyasa ba zata yi hakan ba. Ta fito falo yayin da ta dan kirkiro wani bushasshen murmushi tana yi, ta duka ta gaishe su ta koma gefe ta sami kujera ta zauna tana sauraron abin da za su fada. Ko ba ta fada ba sun san ba ta farin ciki da zuwansu. Abdul-Sabur ya jawo wayarsa ya matsa wata lamba ya kara a kunne, ba jimawa sai ya taso da sauri ya mikawa Umaimah, nan da nan ta ji kirjinta ya buga ta kura masa ido, kallo irin na tsana ta ke yi masa. Ya yi dan murmushi, ya ce, ''Karbi waya Umaimah, kada ki damu amsawa kawai za ki yi. Huci kawai ta ke yi tamkar zuciyarta zata fice, nan da nan hannayenta suka dau karkarwa ta karba ta dora wayar a kunnenta ba tare da ta yi magana ba. Kamar a mafarki, kamar daga sama ta ke jiyo muryar wanda ba ta taba zato zata sake ji a duniya ba. Ta dafe kirji ta lumshe ido, yayin da ta rushe da kukan dadi amma fa dariya take yi. Ta tashi da gudu ta shiga daki ta fada akan gado, har yanzu wayar na makale a kunnenta. Faduwa ta dubi Abdul-Sabur ta cika da mamaki, ta ga ya sami kujera ya zauna babu abin da yake sai murmushi yake yi kasa-kasa. Faduwa ta matso kusa da shi ta zauna ta zungure shi, ta ce, ''Da wa ka hadata a waya ta fashe da kuka daga jin muryarsa, Abdul-Basi ne? Abdul-Sabur ya ce, ''A'a, danta ne Bilal da dan yayarta Babangida. Sai da na roki Abdul-Basi kada ya ce zai yi magana da ita ya hada ta da yaran kawai. Na sami Abdul-Basi a lokacin da yake tsakiyar cigiyar Umaimah, gari-gari, gida-gida yake zuwa nemanta. Ya rasa ta a ko'ina wanda daga karshe ya sami labarin Umaimah tana daya daga cikin daliban da suka sami zuwa Malaysia, amma ya yi iyakacin bincike ya rasa lambarta ta nan. Allah cikin ikonSa sai ya ji na kira shi kuma har na ambata masa ina tare da ita anan. Da farko ya tsorata yana tunanin ni mijinta ne, ko kuma saurayinta na shaida masa ni malaminta ne, kuma yayanta, dan uwanta a musulunci, me niyyar taimakonta ta fita daga kunci. Ya roke ni alfarma da yawa wasu na masa alkawari zan iya, wasu ban yi masa alkawarin zan yi ba. Wani abun kuma na ce kada ya yi garaje, ya yi addu'a, Allah Zai iya mana. Na ce ba zan ba shi lambarta ba har sai ta yi min izinin yin hakan sannan ba zan hada su a waya su yi magana ba har sai ta yarda da kanta. Alfarma daya na roke shi ya dinga hada ta da *ya*yanta a waya suna gaisawa ba sai ya ji muryarta ba. Nan da nan ya amince min da haka, don ya yi nadama yana tsakiyar yin dana sanin abubuwan da ya yi mata a baya. Faduwa ta ce ''Ina matar da ya aura Zulayha Senegal? Abdul-Sabur ya ce ''Ban tambaye shi wannan ba, don ba layina ba ne. Fatana kawai ta ji muryar *ya*yanta don ta sami nutsuwa. Je ki kiji ko ta gama wayar ki dauko min wayata idan tana son lambar ta dauka ta saka a wayarta ta dinga kira suna gaisawa. Idan ta ki karbar lambar kada ki dame ta ki kyale ta kawai. Don ba lambar da ta ba ni ba ce wannan. Ina jin lambar mamar Abdul-Sasi ce, don shi ya ba ni lambar ya ce in kira za a ba ni yaran suna Gombe. Faduwa ta tashi ta shiga dakin Umaimah akan gado ta iske ta tayi sharkaf da hawaye, tana ta hira da yaranta a waya. Kukan ya yi kama da kukan farin ciki don tana kuka tana dariya. Babu abin da ta ke ambata sai sunan Bilal da Babangida. ''Ka sanni kuwa Bilal? Ni ce mama da ka santa a da can. Shi kuma yana ta tsalle yana mata gwaranci. Babangida ne bai mance da ita ba, sunanta yake kira, ''Aunty Umaimah yaushe za ki dawo? Jiya mun ga hotonki, Bilal bai manta ki ba sai ya ce ga anti. Umaimah ta dafe kai hawaye ya kasa kafewa daga idanunta. Fadwa ta dafa kafadarta, ta ce, ''Ya kamata ace a yau kin yi sallama da kuka, kusan duk wadanda kika rasa a baya sun dawo. Ki godewa Allah Umaimah tunda Allah Ya sa *ya*yanki suna raye suna cikin koshin lafiya. Umaimah ta katse waya ta rungume Faduwa tana kuka, ta ce, ''Anti Faduwa na ji muryar Babangida, na ji muryar Bilal ya fara magana bai manta ni ba. Faduwa ta ce, ''To Alhamdu lillah, ai shi ke nan tunda kinji lafiyarsu ki daina kuka. Ki dauki lambarsu ki saka a wayarki koda yaushe sai ki dinga kira kuna gaisawa. Tunda an ce suna Gombe ba lambar Abdul-Basi ba ce. Umaimah ta dauki wayar Abdul-Sabur ta duba lambar da ta yi magana yanzu an rubuta Gombe, amma ba lambar Abdul-Basi ba ce, sai ta ji sanyi a ranta ta dauko wayarta ta dauki lambar ta saka a wayarta. Ta mikawa Faduwa wayar Abdul-Sabur ta sharce hawaye ta ce, ''Na gode ki ce ina masa godiya shi ma. Faduwa ta yi dariyar jin dadi, ta ce, ''Fito mu je falo ki yi masa godiya ya ji da kunnensa. Umaimah ta yi murmushi kadan ta girgiza kai alamar a'a, ta koma ta kwanta akan gado. Ta sake matso lambar *ya*yanta, Babangida ya dauka. Ya ce, ''Anti Umaimah yanzu muke cewa Hajiya ta saka kudi a wayar mu kirawo ki. Sai aka hau kokawa shi da Bilal shi ma yana so ya karbi waya ya yi magana da mahaifiyarsa. Da da uwa sai Allah, zai yiwu bai tuna ta ba saboda yana yaro sosai suka rabu sai dai ana yawan nuna masa ita a hoto amma wannan soyayyar da Allah (S.W.T) Ya saka a zuciyar uwa da danta tana nan. Shiyasa yana jin muryarta ya ji yana sonta, yana jin dadin hira da ita. Umaimah ta ce, ''Babangida kai fa yaya ne, ba wa kaninka wayar mu gaisa, kada ya yi kuka. Sannan ya ba shi wayar, tana jin muryarsa yana kiran Antina, sai ta ji hawayen dadi ya surnano mata. Faduwa ta dade a tsaye a kanta tana kallonta yayin da tausayinsu ya rufe ta babu abin da ta tuna sai soyayyar da mahaifiyarta ta nuna mata a lokacin tana raye, ta tuna dan uwanta Ibrahim. Hawaye ne ita ma ya surnano mata ta yi sauri ta fice daga dakin tana mai gaggawar gogewa don kada AbduSabur ya gane ita ma ta yi kuka. Ta mikawa Abdul-Sabur wayarsa, sannan ya tashi suka dunguma suka fito daga gidan. Labarin abin da ya faru a daki ta ke ba shi gami da isar da sakon da Umaimah ta bata zuwa gare shi na godiya. Daga dukkan alamu Abdul-Sabur ya ji dadi da jin sakon Umaimah, hankalinsa ya kwanta, da ya ga na Umaimah ya kwanta. Sun dade a tsaye a farfajiyar gidan suna ta tattaunawa game da matsalolin Umaimah, sannan daga karshe suka yi sallama ya nufi hanyar gidansa, Faduwa tai sama ita ma ta shiga gidanta. Yayin da Umaimah ta dade tana waya da *ya*yanta har sai da katinta ya kare. Aiki ya sami Umaimah ta yi firgigit ta tashi ta shiga wanka, ta saka doguwar riga abaya ta fita neman katin waya, don hirar ba ta ishe ta da su ba. Umaimah ta sami abun yi ita kadai a cikin gida, koda yaushe tana waya da jama'ar da ta ke da lambobinsu a wayarta, musamman ma *ya*yanta na Gombe. Duk wannan hirar da ta ke yi da su Babangida bata taba jin muryar wani babba da daga cikin *yan gidan. Ita dai in ta buga Babangida ne yake dauka, haka idan ba ya kusa sai ta ji ba a dauka ba idan aka jima sai ta sake kira, in yana kusa sai ya dauka su yi hira ya kira mata Bilal shi ma ya zo ya yi mata gwarancinsa. Labaru kala-kala Babangida yake yi mata, wani abun idan ya fada sai tayi mamaki, musamman da ta ji radau yana bata labarin Zulayha Senegal matar Babansa irin fadan da suka yi ita da Babansa, kuma daga karshe suka rabu ya dawo da su Gombe shi yana Kaduna har yanzu. Ta tambaye shi an taba kai su Dugge? Ya ce, ba a taba kai su ba, su ma *yan Dugge ba sa zuwa. Sai ta ji ba ta ji dadi ba da aka ki nunawa *ya*yanta danginta. Idan suna hira sai ta ji tausayinsu har wani lokaci su sakata kuka, ko su saka ta dariya har da kyakayatawa. Allah Sarki, haka rayuwa ta ke. ******************** A satin ne Hanif ya shaida mata zai je gida Najeriya hutu, ta rokeshi da kafin ya wuce ya zo ya karbi sako ya kai mata rugarsu Dugge. Ya yi mata alkawari zai zo, amma ita fargaba ta ke, kada ya manta ya wuce bai zo ba, don haka wayar safe daban, ta rana daban ta ke yi masa tana sake nanata masa. Duk da haka ta ji ta matsu ta damkawa Hanif sakonnin nan da ta shiryawa *yan gidansu. Ta zuba kayanta kala biyu a jaka. Ta yi wanka tsaf ta ci ado da wata riga da siket blue gyalenta baki da takalmi baki ta rataya jakarta baka a kafadarta, ta rufo gidanta ta fito. A gidan Faduwa ta tsaya ta iske gidan a datse daga dukkan alamu ta fita unguwa, makaranta ko asibitin da ta fara cuku-cukun neman aiki, ko kuwa gidan kawayenta don tana da kawaye rututu iri-iri mata da maza. Ta dade a tsaye a bakin kofar ta rasa wanda zata ba wa sako a fadawa Faduwa cewar zata yi tafiya zuwa garin 'Mantin' makarantar su Hanif wato Legenda zata kwana daya ko biyu a can. Sai can ta tuna ashe fa yanzu tana da waya babu sakon da waya ba ta isarwa cikin sauki da gaggawa. Nan da nan ta zaro wayarta ta nemo sunan Faduwa ta kira ta. Ta yi mamaki da ganin kiran Umaimah, ta amsa cike da fara'a sannan Umaimah ta shaida mata ga ta a kofar gidanta, amma ba ta nan daman sallama zata yi mata zata Mantin makarantar Legenda wajen Hanif da sauran kawayenta mata *yan Gombe. Faduwa ta yi farin ciki da jin haka, ta kuma yi mata fatan Allah Ya kiyaye hanya. Daga karshe ta tambaye ta, ''Kin yiwa Abdul-Sabur sallama kuwa? Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ai ba ni da lambarsa. Faduwa ta ce, ''Amma ai yana gida ki shiga ki yi masa sallama. Umamai ta ce, ''Ban san ta inda zan bi in je gidansa ba, kasancewar ban taba hawa block dinsu ba, sai dai ki turomin da lambarsa. Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Kuna gida iri daya ki ce ba ki san yadda za ki hau samansa ba? Ai kina ma yin kokari a hakan kin fi da. To bari na turo miki lambarsa. Umaimah ta sauka kasa tana daf da zata fita daga get sakon Faduwa ya shigo wayarta. Tana dubawa ta ga lambar Abdul-Sabur ce. Nan da nan ta kira duk da sai da ta ji faduwar gaba kafin ya dauka. Ba ta sani ba ko ba ya so ta kira shi shiyasa bai karbi lambarta ba bai taba kiranta ba. Ina fatan nacika Alkawari.? Sai kuma Gobe idan Allah yakai mu da rai da lafiya... Marbass Dan Aunty.MAKWABTAKA 32 yana daga wayar ta ya gyara zama ya ce, ''da wa nake magana ne? Wannan karon mamaki ne ya kama ta, don a zatonta yana da lambarta kira ne bai taba yi ba. Ta yi ajiyar zuciya, ta ce, ''Sunana Umaimah Bello Gombe. Sai ya bude ido da baki don mamaki, amma bai fallasa mamakinsa a fili ba. Ya ce, ''Barkanki da safiya Umaimah. Kina lafiya? Ta amsa, ''Lafiya kalau. Yayin da ta fara gaggauta fadar sakon da zata fada. ''Zan je Mantin makarantar Legenda wajen Hanif, zai je Nigeria a cikin satin nan, zan ba shi sako ya kai Dugge shine zan kai masa. Zan kwana daya ko biyu a can saboda akwai kawayena su Zainab a makarantar, sai in zauna a wajensu. Shi ne na kira in yi maka sallama, na yiwa Anti Faduwa ma, ita ce ta turo min lambarka. Sai ya yi mamaki da wannan sauyi, ya kuma ji dadi sosai. Ya yi murmushin dadi ya ce, ''Lallai kin yi tunani, kuma kin yi dubara kin kuma kyauta. Yanzu har kin shirya kin sauko ne? Kina waje ko? Don na ji karar motoci. Ta ce, ''Na fita, har na kusa isa bakin titi. Ya ce, kin san inda za ki je ki hau mota zuwa Mantin daga can ki hau mota zuwa Legenda? Ta ce, ''A'a, yanzu in mun gama wayar nan zan kira Hanif ya kwatanta min inda zan je da inda zan jira idan na isa Legenda ya je ya dauke ni. Abdul-Sabur ya ce, ''Ki tsallaka gada sai ki jira ni zan zo in kai ki har Mantin. Ta ce, ''A'a, ka bar shi kawai, zan iya zuwa da kaina,,, Ba ta rufe bakinta ba ya kashe waya, sai ta ji kamar ta fasa zuwa Legenda saboda Abdul-Sabur ya ce zai bi ta. Ba ta so a dinga ganinta da shi, saboda ba al'adarmu ba ce, a yawaita ganin mace da namiji tare alhali ba mijinta ba ne kuma ba dan uwanta ba, ai sai ayi musu wata fassarar. Nan da nan ta ji hankalinta ya tashi, ta fara tafiya cikin sauri, burinta ta yi sauri ta bace masa ya zo ya rasa ta. Ta tuna ai yana da lambar wayarta zai kira ta kuma ba dadi ta kashe wayarta bayan yanzu suka gama yin waya. Tana matukar ganin girmansa yanzu ba zata iya yi masa musu ba. Ta kula yana yi musu komai saboda Allah, don Allah Ya halicce shi mutum mai tausayi, kulawa da kuma son kyautatawa kowa bata ga wata alama ba bayan haka. Bayan ta tsallaka gada sai ta tsaya a inda ya umarce ta da jira shi, ba jimawa sai ta ga ya bayyana a kusa da ita cikin tsaleliyar motar nan ttasa. Ya tsaya a gefenta ta bude ta shiga gidan gaba ta zauna. Ta dube shi ta yi murmushi, shi ma ya yi mata murmushi. Ya ce, ''Kina so ki bata ne a kasar mutane? Ke da kike kamar kifin rijiya, babu inda kika sani daga gida sai makaranta idan kin yi nisa ne ma kike zuwa Bukit bing tang. Sai ta yi dariya, ta ce, ''Ka kai ni tashar da zan hau motar Mantin sai in hau in je da kaina ba sai ka wahalar da kanka ba. Ya ci gaba da kallon titi yana tuki, yayi dan murmushi, ya ce, ''Kada ki damu, ba zan kai ki inda za a ganmu tare ba. Sai in kai ki makarantarsu tunda a hostel suke gidajen dalibai ba nisa da cikin makarantar sai su zo su dauke ki ni kuma sai in tafi kafin su karaso. Ta ji sanyi a ranta, sai ta gyara zama ta saki jikinta. Ya isa bakin wani banki ya sami waje ya tsaya, ya juya ya dube ta, ya ce. ''Ki min hakuri mintina kadan zan shiga banki na fito. Ta gyada kai, ta yi murmushi ta ce, ''Ba damuwa sai ka fito. Ya fice da sauri ya bar mata A.c da CD a kunne tana ji. Ta bude gidan da yake ajiyer CDs ta shiga duddubawa can ta hango wakar da ta ke nema ta saka don wakar rannan ta yi mata dadi wato ta 'Akuri Afomsa. Ya dan dade amma ba da yawa ba ya fito, bayan ya yi mata sallama sannan ya shigo motar ya zauna. Ta dukar da kai ta yi masa sannu da zuwa. Ya yi murmushi ya amsa, sannan ya fara tuki. Sai bayan da suka yi nisa ya kula ta canja wakar ba ta da ba ce da yake ji. Wato wakar Rihanna' mai taken 'Te amo' sai ya ji ana Yaren 'Asanti' maimakon 'Turanci' ya kurawa rediyon ido ya juya ya dube ta, ita ma ta tsaya tana kallonsa tana sauraron abin da zai ce mata, don daga dukkan alamu ta ga yana shirin yin magana. Sai ya fasa maganar ya ci gaba da duban gabansa. Ta ji ta fara zargin kanta ko ya fi son waccan wakar ta canja masa? Nan da nan ta dauko wancan CD na farko ta mika hannu ta danna wajen fitarwa, sai ya sa hannu ya tare ya hana CD fitowa ya sake tura shi ciki, ya ce gaba da yi. Ta kalle shi, sai ta sunkuyar da kanta kasa ta ajiye CD da yake hannunta suka ci gaba da tafiya ba tare da wani ya sake magana a cikinsu ba. Sai sanyin AC mai hade da kamshin daddadan turaren mota, gami da sautin kida da zazzakar muryar da yake rera wakarne kadai yake tashi. Nan da nan sai suka ga tafiyar ta yi musu sauri, kan ka ce kwabo suka isa Mantin suka gangara zuwa cikin Legenda makarantar su Hanif. Ya sami waje ya tsaya sannan ya juyo ya dube ta. Ya ce, ''Yaushe Hanif din zai tafi Najeriyar? Ta ce, ''Cikin satin nan ne. Ya ce, ''Me yasa ke ba zaki bishi ba, ku je ki ga *yan gida, kin fi so ki ba shi sako? Ta sunkuyar da kanta kasa da alama ba shi da amsar wannan tambaya. Ya ce ''Me da me kike so ki aikawa *yan gidan? Ta shafa jakarta, ta ce, ''Wata ambulan ce na rubuta wasika doguwa zuwa ga Baffa da Sabitu, ina shaida musu ina nan lafiya su kwantar da hankalinsu. Idan na gama karatu zan zo na gan su. Sannan na ce su taimaka su je Gombe gidan iyayen Abdul-Basi su duba Babangida da Bilal. Sannan na siyo musu wayoyi guda biyu daya ta Sabitu daya ta Baffa, don ina kyautata zaton an kai musu service din waya garin ko kusa da garin. Sannan na dauki kudi na je na canja Riggit ya zama Dallar dubu biyu, zan ba shi idan ya je Najeriya ya canja ya zama naira dubu dari uku da ashirin da wani abu, ya kaiwa su Baffa da Sabitu su yi jari, sai kuma hotunana dana dauka a nan kasar guda goma na wanke na hada musu don su ganni ina cikin koshin lafiya. Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Kin yi dai-dai, gaskiya kinyi tunani, ya yi kyau hakan da kika yi. Na ji dadi da kika yi wannan tunanin, kuma daman haka ya kama ta ki yi gara su ji motsinki akan shirun nan da kika yi kamar ba kya raye. Yanzu za su ji dadi, kuma hankalinsu zai kwanta. Sun san bakya tare da Abdul-Basi kuwa? Ta yi shiru kamar mai tunani, can ta dago a hankali ta dube shi, ta ce, ''Ina kyautata zaton sun sani, saboda daman Sabitu ya sani ban boye masa komai ba, ban sani ba ko dalili zai sa ya fada musu. Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Zancen gaskiya sun san ba kwa tare, saboda Abdul-Basi har garinku ya je nemanki, kuma ya yi musu bayanin cewar kina cikin wadanda ku ka tafi karatu Malaysia, shima kuma daga baya ya bincika a gari ya ji labari, kaninsa ne ya kai shi gidan Lamijo nemanki ta ce ba ta san inda kike ba yanzu, sai Baban Hanif ya fada musu gaskiyar magana. Alh. Nasir dinma ya fada min haka Abdul- Basi ma ya fada min, don haka kada ki boyewa Baffa komai ki sanar da shi ba ki da aure, amma kina kama kanki, kina tsare mutuncin kanki ya taya ki addu'a. Hawaye ya cika mata ido taf! Ta sharce da gefen gyalenta ta ce, ''Yanzu Lamijo ta ji labarin tahowata alhalin tana zargina da mijinta? Abdul-Sabur ya ce, ''Ah! To meye dan ta ji ai ta fi kowa sanin zaki taho daman kuma me ye abun mamaki don ta ji kina nan? Mijinta kuwa ai ba da shi kika taho ba, kin bar mata abinta a can. Kuma babu wanda ya fada mata makudan kudin da Alh. Nasir yake baki ke da Hanif, ko nima ya so ya boye min, sai da ya ga dai na sani sannan ya sake fada min, ya ce kuma bayan Hanif da ke da Alh. Sani da ya fara aikowa ya baku bai taba fadawa kowa ba. Kuma ya gargadi Hanif kada ya fadawa kowa hatta mahaifiyarsa, saboda yana da *ya*ya da yawa, duk uwarsu daban abun zai iya zama rigima idan wata mata ta ji ita bai bawa danta ba. Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta sake goge hawayen idonta da alama ta ji sanyi a ranta. Ya dube ta ya yi murmushi, ya ce, ''Babu matsala. Na gode sosai, sai na dawo. Ta yunkura zata bude kofar mota ta fice sai ta ji ya ambaci sunanta, sai ta waiwayo da sauri ta dube shi. Ya zaro kudi daga aljihunsa Dallar dari biyar ce ya mika mata, ya ce. ''Ga shi ki hadawa su Baffa na canjo musu yanzu, na zaci ba za ki hada musu da kudi ba, sai ki rike nawa idan kuma kina ganin dukka za ki aika musu ya yi dai-dai. Za ta ki karba ya bata rai, kuma ya ja mata kunne ba ya so duk abin da ya yi niyyar yi mata ta ce ya bar shi. Tayi godiya ta karba. Ya ce, ''Yaushe za ki dawo gida? Ta ce, ''Gobe ko jibi Ya ce, ''Magana daya za ki fada don zan dawo in dauke ki a dai-dai nan wajen inda na ajiye ki? Ta yi shiru can ta ce, ''Jibi zan dawo. Ya ce, ''To ba damuwa, kuma ga waya ma zamu yi, ki gaida su Hanif. Akwai wanda nake so na gani a cikin garinnan, amma sauri nake yi idan na dawo jibin zan gan shi. Zan je na dauko Faduwa a Putra jaya mun yi da ita karfe goma sha biyu za ta gama. Umaimah ta yi murmushi gami da lumshe ido, ta ce, ''To shi ke nan, ka gaida gida. Ta bude kofar mota ta fice, yana daga mata hannu tana daga masa. Ya ja mota a guje ya fice daga farfajiyar makarantar. Ta dade a tsaye tana mamakin irin wannan kirki da kulawa na Abdul- Sabur. Ta ji dadi data ji yayi zancen Faduwa don daga dukkan alamu ya yarda da shawararta, ya amince zai so Faduwa kuma ya aure ta. ''Amma fa na taya Faduwa murna da samun miji kamili. Ina fatan ni ma Allah Ya ba ni miji na gari mai halinsa. Inji Umaimah ta fada a zuciyarta. Yayin da ta ke kokarin zakulo wayarta daga aljihun jakarta zata bugawa Hanif ta shaida masa ta iso makarantarsu ya zo ya dauke ta. Tun da Umaimah ta tafi Legenda ba ta kira Abdul ba, shima bai kirata ba har ta cika kwanaki biyunta da la'asar tana shirin kiransa sai ta ji ya kira ta. Ya shaida mata ya shigo garin, amma ya wuce gidan abokinsa da zai gani don haka ta shirya bayan sallar magruba zai zo ya dauke ta. Ya tambaye ta inda zai same ta a gidan su Hanif ko a makaranta inda ya ajiye ta? Ta ce, zata fito ta jira shi a inda ya aje ta. Suka yi sallama suka kashe waya. Yana idar da sallar magruba kuwa ya zo ya tsaya a inda suka yi ya dauke ta, ya iske ba ta karaso ba, don haka ya yi zaton ko tana kan hanya don haka bai damu da ya dame ta da kira ba. Ya shefe fiye da awa babu ita babu kiranta. Da ya ji shirun yayi yawa sai ya kira ta, tana ta ruri ba ta amsa ba. A masallacin Makarantar ya yi sallar isha'i ya dawo cikin mota ya ci gaba da jira bata zo ba sai ya sake kiranta. Tun wayar tana shiga har ya ji an kashe ta mudik. Sai ya shiga mamaki marar misaltuwa, gami da fargaba ko ba lafiya. Yana nan a wajen har karfe goma sha dayan dare. Ya yanke shawarar neman gidan Hanif ya je ya gani ko lafiya? Sai ya fasa zuwa saboda ya fuskanci ba ta so a dinga ganinta da namiji. Ya zama ba shi da wata shawara ko dubara kuma. Ya shiga tunani anya kuwa mai ilimi da wayewa zata yi haka? Fatansa dai ace tana nan lafiya, kuma cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali. Ya shiga tunanin ko kara kwana ta ke so ta yi, ko kuwa motar haya ta hau ta koma gida? Sai wata dabara ta fado masa ya yanke shawarar ya kira Faduwa ya tambaya ko Umaimah tana gida. Yana kiran Faduwa bugu daya wayar ta shiga, ta dauka. Ya tambaye ta tana ina? Sai ta yi mamaki da tambayar da ya yi mata alhali da yamma nan ma sun hadu tana gida. Ta tambaye shi, ''Lafiya? Ya ce, ''Idan kina gida ki duba min gidan Umaimah tana nan? Faduwa dai ba ta daina ambaton lafiya ba. Ya ce, ''Lafiya mana, ko kinji alamar rashin lafiya a tare da ni? Ta yi dariya ta ce, ''Ai tambayoyin ne na ji ba irin wadanda ka saba yi min ba ne. Ya ce, ''Dubo min ita za ki yi kawai ki fada min ko ta dawo daga Mantin? Faduwa ta ce, ''To kashe wayar bari na gani, zan kira ka. Ta kira wayar Umaimah a kashe, don haka dole ta katse baccinta ta tashi ta dauki mayafi ta hau sama gidanta. Ta danna kararrawa sau daya kacal sai ga Umaimah a bakin kofa, ta bude kofar da sauri tana kokarin cewa Faduwa ta shigo ta zauna. Faduwa ta ce, ''Bacci na ke ji zuwa na yi in duba in ga ko kin dawo? Na ji wayarki a kashe kuma. Bayanin Faduwa ya ba ta mamaki, tabbas ta san akwai dalili. Sai ta yi kasake abunka da marar gaskiya, can ta dago ta dubi Faduwa ta ce, ''Ina Abdul-Sabur? Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Shi ya taso ni ya ce in duba ko kin dawo gida lafiya. Wai me yake faruwa ne? Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Babu komai. Kamar yadda na fada miki shi ma na fada masa yau zan dawo, to kuma waya ta a kashe ban yi caji ba shiyasa ban fada masa na dawo ba. Faduwa ta ce, ''Kiyi caji ki kunna ki fada masa kin dawo. Umaimah ta ce, ''Yana gidansa ne? Faduwa ta ce, ''Ina ma na san inda yake, a waya dai ya kirani yanzu. Bari na kira na fada masa kin dawo. Rufe gidan ki kwanta, ni ma zan je in kwanta. Ta juya ta tafi, ta danno lambar Abdul-Sabur tana tafe tana magana da shi yayin da Umaimah ta sankare a tsaye saboda tasan ba ta kyauta masa ba. ''Yanzu ina mafita? Ya ya zan yi in wanke kaina daga wannan rashin ladabin da na tafka? Umaimah ta ke wasu-wasi a zuciyarta. Abdul-Sabur bai shigo gidansa ba sai karfe daya da rabi na dare, yayin da Umaimah ke tsaye a dakinta tana kai kawo, ta kasa sukuni har sai da ta ji motsinsa a cikin gidansa. Tana hango hasken fitilun da ya kukkunna yana ya kai kawo a cikin gidansa. Bai kwanta ba sai karfe biyu da kwata sannan ita ma ta samu ta kwanta, hakarkarinta. Da kyar ta yi bacci tana sake-saken yadda zata tunkare shi da bayanin da zai gamsu da ita, kuma da idanuwan da zata kalle shi. Tabbas ta tabbatar ba ta kyauta masa ba. *************** Washe gari da misalin karfe goma sha daya da minti goma sha daya Abdul-Sabur ya ji wayarsa ta dauki ruri. Yana zaune a falonsa yana kallon labaran CNN. Yana dubawa sai ya ga Umaimah ce don haka sai ya gyara zama don ya ji abin da zata fada masa, sannan ya danna wayar gami da yi mata sallama. Shima maganin sa. Yabi ya takura mata sosai.MAKWABTAKA 33 Ya ji tana magana da kyar yayin da muryarta ke karkarwa. Bayan ta gaishe shi, sai ta fara da ba shi hakuri, sannan ta dora da bayanai barkatai.. Da ya hada dogayen bayananta a waje daya ya dunkule ya fuskanci tana magana ne akan da ta tashi tahowa Hanif da kawayenta ne suka cika mota guda suka ce za su kawo ta har gida, ita kuma ta kasa fada musu akwai wanda ya ke jiranta. Sanda yake kiranta a waya tana tare da su a mota ba zata iya amsa masa ba a gabansu, don haka ta kashe wayar. Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Kada ki damu Umaimah na fahimce ki sosai, kuma na yi miki uziri. Hakan da kika yi kin yi dai-dai da ba ki bari wani ya zarge ki ba balle aje Gombe ana yadawa nasan halin mutanenmu. Ki shirya da yamma ke da Faduwa za mu fita mu dan kewaya gari. Farin ciki ya rufe ta da Allah Ya sa ya fahimce ta. Nan da nan ta amsa masa da, ''To, Allah Ya kaimu anjimar, na gode. Karfe biyar saura kwata a motar Abdul-Sabur suka hallara shi yake tukawa, Faduwa na gefensa a gidan gaba yayin da Umaimah ta ke zaune a kujerar baya. Babu abin da yake tashi a motar sai sautin kida wakar larabawa ce Faduwa ta saka ta 'Nancy' mai taken 'Yatabtab. Tana daga zaune ta ke rawa tana bin wakar. Abdul-Sabur ya kashe, ta sake kunnawa idan ya rage sai ta sake karawa, Umaimah na zaune ba ta da aiki sai dariya da kyalkyalawa. Waje-waje na shakatawa suka dinga zuwa kama daga wajen cin abincim shan ice-cream, gidan zoo da kuma malls inda ya ce kowacce ta dauki abin da ta ke so ko nawa ne zai biya, su ka jidi kaya kuwa. Ba su shigo gidajensu ba sai karfe daya na dare daman sun riga da sun yi sallolinsu a masallacin 'BB Plaza' don haka kowannensu wanka ya yi ya kwanta. Washe gari da ya yamma sai ga Faduwa a gidan Umaimah dauke da wasu takardu a hannunta, tana shigowa ko zama bata yi ba sai ta mika mata. Ta ce, ''Ga form, ki cike inji Abdul-Sabur na makarantar koyon tukin mota ne, kullum da safe ko da yamma ake zuwa. Ke da ba ki taba iya tukin mota ba watanni uku zaki yi. Kina gamawa in kin ci jarabawa za'a baki 'driving liences'. Ni kuma da yake tsohuwar direba ce wata daya kacal zan yi a ba ni nima nawa idan na ci jarabawa. Umaimah ta cika da mamaki ta ce, ''Me yasa zan shiga Makarantar koyon tuki alhali ba ni da mota, kuma ba inda nake zuwa Makarantarmu ga ta a kusa da ni? Faduwa ta ce, ''Haka dai ya ga ya dace mu shiga kasancewar dogon hutu ne, idan ma kika zauna a gidan me zaki yi kuma shi tuki ai yana da amfani idan ka iya din, saboda ko a kasarku nan gaba zai amfane ki sai ki dinga tukinki ba sai kinyi ta neman direba ba. Umaimah ta ce, ''Haka ne, na gode. Ta karbi forms din ta cike ta mikawa Faduwa. Yayin da Faduwa ta ce, ''Ai tashi zaki yi mu je koyontukin yau za'a fara, ga Abdul din can ma a mota yana jiranmu. Umaimah ta dafe kirji ta zabura ta ce, ''Wai! Tukin yau zan fara? Gaskiya Anti Faduwa tsoron mota nake ji. Faduwa ta kyalkyale da dariya, ta ce ''Ke *yar kauye ce har yanzu. Meye abun tsoro kuma a tukin mota? Ki zo mu je kada mu bata masa lokaci. Daman Umaimah a shirye ta ke tsaf, don haka gyalenta kadai ta jawo da wayarta ta rufo gidan suka sauko, suna shiga motar Umaimah ta gaishe shi sannan ta yi masa godiya bisa kulawar da yake yi musu. Faduwa ta fara ba shi labarin yadda suka yi da umaimah a sama da ta ce ita tsoron tukin mota ta ke yi. Suka sha kyalkyala dariya su dukka ukun. Abdul-Sabur ya shiga yi mata bayani akan ta kwantar da hankalinta ba wuya, shi tuki nutsuwa ya ke so da kuma cire tsoro. ''Na samar muku makarantar da ba ta da nisa ko bana nan sai ku dinga takawa da kafa ko ku hau tasi, Riggit uku ma zai kai ku. Inji Abdul. Su dukka suka amsa masa da godiya gami da fatan alkhairi. Ashe dai makarantar koyon tuki makaranta ce sosai, har da ajujuwa da takardun rubutu da karatu. A koya musu a rubuce sannan a fita ayi gwaji a zahiri. A ranar Abdul-Sabur ya jira su a mota har suka gama suka fito daga ajujuwansu suka dawo gida tare. Amma sun yi shawara su dinga zuwa da safe ba da yamma ba, karfe tara zuwa karfe goma sha biyu na rana. Don haka kullum Umaimah ce ta ke saukowa, sai ta bi ta gidan Faduwa sannan su dunguma su tafi a motar haya, ko a kafa ko kuma Abdul Sabur ya kai su, ko ya dauko su idan ya ga fitarsu. Ku san kullum da yamma ka'ida ne sai sun fita wuraren shakatawa iri-iri, don haka kowannensu ya daina girki abinci kala-kala suke ci a waje, kuma har su tafi da wasu gida. Gaskiya Umaimah ta ji dadin hutun nan, ba ta taba jin dadin Malaysia irin wannan karon ba, har kiba ta fara yi babu kashin nan rankwal-rankwal na rama. Babu sauran hawaye a idanunta, kullum suna tare su uku, wasa da dariya kadai ne a tsakaninsu. Sai ta ji ta saba da su sosai ta cire jin kunya, nauyi da tsanar ganinsu da take ji ada da. Sai ga ta gidanta ba ya rabo da mutane ku san kullum sai ta yi baki *yan makarantarsu, kuma *yan garinsu suma suna zuwa. Su Aisha Bingyal sukan yi kungiya su ziyarce ta, ita ma da su AbdulSabur suna biyawa ta gidajensu. A wannan sabuwar makarantar ma ta koyon tuki sai ga ta ta yi kawaye mata wasu sa'anninta, wasu kuma sun girmeta sosai, su ma har gidanta suke ziyartarta. Wasu kuwa kawayen Faduwa ne idan suka zo gidan Faduwa sai ta shigo da su gidan Umaimah. A hadu a yi ta hira ana ciye-ciye ana shewa. Idan dare ya yi kuma sai ta yi zaman kiran wayar *yan gida Nigeria, garin Gombe wato *ya*yanta, Babangida da Bilal. Wannan dole ne kullum da daddare sai sun yi waya, kuma su dade suna yi. Ta fuskanci dai-dai lokacin da suke gida sun dawo daga makarantar islamiyya da ta boko kuma ba su yi bacci ba. Sai yau Hajiyar Abdul-Basi ta karbi wayar suka gaisa faram-faram. Alhamdulillah, mutum rahma ne'' inji Umaimah dai-dai lokacin da ta tsinci kanta ta amsa wayoyi har sau shida a jejjere. Hanif ne ya kira ta daga Najeriya ya bata hakuri saboda bai kai sakonta da wuri ba, ya tabbatar mata kuma gobe ne insha Allah ya shirya zuwa 'Dugge' neman gidansu zai kai mata wadannan sakonnin. Farin ciki ya rufe ta, ta yi masa godiya gami da yi masa magiya kada kuma ya sake shiga wasu safgoginsa wadanda ya saba yi, ga shi har ya shafe wata guda cur a Najeriya bai je ya kai sakonta ba. Wannan karon dai ya tabbatar mata gaske yake zai je. Allah cikin ikonSa kuwa ya cika mata alkawari, ya nemi gidansu a Dugge, ya kai mata sakon hannu da hannun Baffanta da Sabitu ya damka. Misalin karfe goma sha biyun rana a agogon Najeriya wanda yayi dai dai da karfe bakwai na dare a agogon Malaysia, wayar Hanif ta shigo wayar Umaimah, shigowarta gida kenan daga gidan Faduwa tana shirin dauro alwallar magruba. Data dauki wayar maimakon ta ji muryar Hanif tunda lambarsa ce sai ta ji yaren fulatanci ne maimakon Hausar da suka saba yi. Muryar tsohonta ta ji, Baffa yana ambaton sunanta cike da farin ciki marar misaltuwa. Ta daka tsalle don murna ta fashe da kukan dadi. Fadi ta ke, ''Baffa ka yafe min. Alhamdulillah da Allah Ya sa kana raye. Shi ma kukan dadi yake yana hamdala da Allah ya sa tana raye tana cikin koshin lafiya. Ya shaida mata cewar ya kasance cikin dumbin damuwa a lokacin da Abdu-Basi ya zo ya shaida musu ba ya tare da ita. Sabitu ma ya karbi wayar ya gaishe ta sannan ya shaida mata sun karbi sakon da ta aiko musu sun ji dadin sakon kudin nan sosai don ta aiko musu a lokacin da suke tsananin bukatarsu saboda al'amura sun tsananta a gare su, abincin ci ya yi musu wahala, wataran a ci, watarana a rasa a kwana da yunwa. Sai ta fashe da kuka don tausayinsu, sai ta sake godewa Allah da ya hore mata har ta kai matsayin da zata taimaka musu. Hanif ya shaida mata gari 'Dukku' suka taho don su yi waya babu service a 'Dugge' har yanzu, ko wutar lantarki ba su da shi balle ayi cajin waya. Sai ta roki Hanif ya siya musu layin waya ya saka musu a cikin wayoyin ya saka musu a caji ya kuma kunna ya saka musu lambarta, sannan ya koyawa Sabitu yadda a ke yin wayar. Lokaci lokaci sai su dinga zuwa Dukku suna kiranta suna yin magana. Ta sake rokar Hanif ya karanta musu wasikar da ta rubuto musu. Hanif ya aiwatar da duk abinda ta bukata. Ya sake kiranta da layin Baffa da na Sabitu suka yi magana da wayoyin dukka biyu. Suka sake daukar lokaci suna hira, ta sake yi musu bayani yadda za su dinga yi da wayar suna samunta duk lokacin da suke bukatar yin magana da ita. Sun gamsu da bayananta sosai, sannan ta ce su adana kudin da ta aiko musu, su nutsu su ga irin sana'ar data kamata su yi dan kudin ya yaukaka ya zama babban jari, su sami na cin abinci a saukake a cikin riba ba tare da uwar kudin ta wargaje ba. Ta sha addu'ar fatan alkhairi, da shi albarka daga wajen Baffa da Sabitu. Daga karshe ta yi masa godiya suka kashe waya. Saboda dadi Umaimah ta durkusa gwiwoyinta dukka biyu a kasa ta daga hannayenta biyu sama tana yi wa Allah godiya da ya fara warware mata matsalolinta. Ta yiwa Abdul-Sabur addu'a da fatan alkhairi da fatan Allah Ya saka masa da gidan aljanna shi da yayi mata sanadiyyar nemo iyayenta da *ya*yanta dan ba dan shi ba da wannan tunanin ba zai taba kawowa a kwakwalwarta ba. Farin ciki ya hana ta daurewa, nan da nan sai ta bugawa Abdul-Sabur waya kafin ta yi masa bayani ma ya fuskanci tana cikin nishadi. Ta shaida masa dimbun farin cikin da ya same ta yanzu a sanadiyyar jin muryar Baffanta da kaninta Sabitu. Sai ya ji dadi shi ma a ransa, ya taya ta murna ya kuma sake mata nasihohi masu ratsa jiki game da yadda Musulmi ya kamata ya zauna da Musulmi dan uwansa. Ya sake gargadinta da ta zauna da kowa lafiya a duk inda take ta rike mutum da daraja ko yaya matsayinsa yake a rayuwa, don mutum yana da daraja a wajen mahaliccinsa, ba abin wulakantawa ba ne. Umaimah ta yi masa alkawari zata bi duk nasihohin da ya yi mata, kuma zata ci gaba da saka shi a cikin addu'arta bisa kokarin da ya yi mata wajen ceto rayuwarta daga kunci zuwa farin ciki. Daga dukkan alamu Abdul-Sabur ya fi ta jin dadi, fadi ya ke, ''Alhamdu lillah, nima na gode miki. Tana godiya yana godiya har suka katse waya. Allah Akbar! Allah mai musanya duk abin da Ya so Ya canzu. ******************** Tuni Faduwa ta kammala makarantar koyon tukin mota a cikin wata daya da sati daya, aka buga mata 'driving licence' dinta aka ba ta. Har ta zamto tana tuka motar Abdul-Sabur tana kai Umaimah Makaranta ta dauko ta, da yamma kuma ta tuka su fita yawo. Da farko tsoro ne ya hana Umaimah kwarewa a tuki, amma gori da tsokanar da Abdul-Sabur da Faduwa suke yi mata itace ta sanya zuciyarta ta dake ta kuduri niyyar dagewa ta koya. Tabbas tana kokari matuka don Abdul-Sabur ya kan fito ya tsaya ta barandar baya ya ga wucewarta a cikin motar Makarantar ita da Malamin da yake koya mata, har sun fara hawa manyan titina. Allah cikin ikonSa a satin da zasu koma makaranta a satin Umaimah ta ci jarabawarta ta makarantar koyon tuki, aka bata satifiket da 'driving licence. Tana ta tsalle da murna a lokacin da ta karbo, don taya bera-bari har hotuna Faduwa ta dinga yi mata dauke da satifiket din a hannunta. Ta sha yiwa Umaimah hotuna ita kadai, sannan suka yi da Faduwa, Abdul-Sabur ne ya dauke su, sanan aka yiwa Umaimah da Abdul-Sabur, Faduwa ta dauke su. A halin yanzu duk inda za su je Umaimah ce take tuka su. Tabbas hannu ya fada sosai ma, ta san dokokin tuki ko'ina tana kai kanta har wani gari. Don ita ta tuka su suka je har 'Mantin' Garin su Hanif, da yake hutu ya kare ya dawo daga Najeriya. Ta je ta karbo hotunan da su Baffa suka aiko mata. Hotuna ne da yawa, bayan na Baffa da ba Sabitu har da na *yan garinsu kamar na matan Babanta Nene da Inna, ga na kawayenta da *ya*yansu. Ta cika da mamaki taf a lokacin data ga hotunan Matawata da Ilah, sai ta zabura ta wurgar don firgici. ''Lafiya? Faduwa, Abdul-Sabur da Hanif suka tambaye ta. Ta girgiza kai, hawaye mai radadi ya sirnano mata. Ta yi murmushin karfin hali. Ta ce, ''Hoton Ilah da Matawata suma suka aiko min shine yasa na firgita. Faduwa da Abdul-Sabur saka hau rige-rigen daukowa su gani. Tabbas mutanen ruga ne sosai, babu digon birni a jikinsu. Faduwa ta yi dariya, ta ce, ''Allah na tuba, Umaimah ina ke ina aure da wannan bawan Allah 'Ilah? Ina ke ina kishi da wannan 'Matawata? Ai ko ada ma ba ajinki ba ne balle yanzu. Idan kika ga Allah Ya yi ikonSa Ya hana bawansa abunda kake so to ka rungimi kaddara kawai kayi hakuri, Allah Shi Ya san me yake nufi, kuma me zai faru, dan abun nan da kake so ba alkhairi ba ne a wajenka. Da Ya hana ki auren Ilah, alkhairi ne don Ya yi niyyar daukaka ki fiye da su. Ki yi fatan auren mijin da ya dace da rayuwarki kawai, tsakaninki da su sai taimako na musulunci. Abdul-Sabur ya ce da Faduwa, ''Ke rufe mana baki, an fada miki akwai maganar kudi, wayewa ko kyau a soyayya ne? Ai shi so ba ruwansa da bakauye ko dan birni. Suka kyalkyale da dariya su dukka aka ci gaba da kallon hotuna. A wata ambulan daban Umaimah ta buda, nan kuma hotunan *yan Gombe ne wato na Bilal da Babangida kowannensu an yi masa shi kadai, sannan da wanda aka yi musu a tare su biyu. Sun girma sosai, kuma da kyan kamarsu tamkar a gaban mahaifansu su ke. Kamarsu daya sak tamkar uwa daya uba daya. Umaimah ta dafe kirji ta rushe da kukan dadi, sai ta sumbaci hotunan gami da daga ido sama ta godewa Allah da Ya raya mata *ya*anta, basu tagayyaraba bayan tahowarta. Su Abdul-Sabur ma suka karbi hotunan suka kalla tabbas sun taya ta murna, yaran sun ba su sha'awa, kyawawan *ya*ya gaba daya sun juye kamannin Umaimah. Faduwa mai son yara sai ta hau rungume hoton tana sunbatar hotunan. Dukkan godiya ta tabbata ga ubangijin talikai, mai kowa mai komai. **************** Da sati ya zagayo ranar Alhamis da yamma Umaimah tana daura alala a kicin dinta, saboda Faduwa ma ta tarki yin Alalar don Faduwa tana son alala sosai, amma ba ta iya yi ba. Tana ta sauri ta gama ta zuba ta kai mata ita da Abdul-Sabur.MAKWABTAKA 34 Ta ji ana bugun kofar gidanta da karfi ana kada kararrawa ba adadi. Da sauri ta fito daga kicin a gigice tana zaton ko ba lafiya ba. Ta fara lekawa ta huda kafin ta bude don ta ga ko waye, Faduwa ta gani duk a gigce ta ke, amma tana fara'a daga dukkan alamu alkhairi ne ya kawo ta. Cikin gaggawa ta bude kofa, kafin ta ce wani abu Faduwa ta yi caraf ta rungume ta tana tsalle. Umaimah dai dariya ta ke taya ta gami da tambayar ta, ''Lafiya? Me ya faru? '' Albishirinki? Inji Faduwa. Umaimah ta ce ''Goro fari tas-tas. Faduwa ta ce, ''Sai kin ba ni goro zan fada miki. Umaimah ta yi-ta yi Faduwa ta fara fada mata inyaso ta dauko mata goron. Faduwa ta ce, gaskiya sai an ba ta goro zata fada, don albishir din babba ne. Umaimah ta cika da mamaki matuka, ta ce, ''To, bari na je daki na dauko miki goron sai ki fada min. Ta shiga dakinta ta yi diri-diri ta rasa ma me zata dauko mata. Ta rasa mene wannan abu da Faduwa ta ke ja mata rai kafin ta fada mata. A zuciyarta ta ke magana, ''To ko Abdul-Sabur ne ya amince zai aure ta, shi yasa ta ke murna? Haka ne ma labarin, ina jin ya fada mata ni na ce ya dace ya aure ta shi yasa zata yi min albishir. Ta jawo jakarta ta bude ta dauko kudi Riggit dari biyu, wanda ya yi dai-dai da naira dubu tara, ta kawo mata. Faduwa ta karba, sannan ta cewa Umaimah ta rufe idanunta. Tunda ta kagu ta ji sai ta yi sauri ta rufe idanunta. Faduwa ta ce, ta miko hannayenta duka biyu. Umaimah ta yi yadda ta umarce ta. Da faduwa ta saka mata abu guda biyu kowanne hannu guda daya sai ta umarci Umaimah ta bude idanunta ta gani. Da ta bude ta duba sai ta kasa fahimtar abin da Faduwa ta ke nufi. Mukulli ne guda biyu a kowanne hannunta. Ta tambayi Faduwa cike da rashin fahimta, ''Mukullan me ye wannan? Faduwa ta ce, ''Mukullan motocinmu ne ni da ke kowa daya. Umaimah ta turo baki ta ajiye mukullan akan tebur ta ce, ''Anti Faduwa, wallahi kin cika son wasa. Wacce irin mota kuma, ya za a yi ki ce mukullin motata? Na dora abinci akan wuta bari na je na duba kada ya kama. Ta shiga kicin da gudu ta ci gaba da daura alala tana jefawa a cikin ruwan zafin da yake a kan wuta. Faduwa ce ta sake debo mukullai ta biyo ta kicin ta ce, ''Wallahi da gaske nake mukullan motarmu ne. Umaimah ta tsaya tana kallonta tana mamakin irin wannan son wasa da tsokana na Faduwa. Faduwa ta ce, ''Na ga alamar har yanzu ba ki yarda da ni ba, to gama daura alalar ki zo mu sauka kasa sai ki ga zahiri. Umaimah ta gama sannan ta dauko gyalenta ta biyo Faduwa kasa. Kai tsaye Faduwa ta shige wajen da aka tanada don ajiyar motoci. Ta je ta bude wasu motoci guda biyu iri daya, sai dai bambancin fenti. Saboda mamaki sai Umaimah ta kame a tsaye tana kallon Faduwa da motocin da aka fi hawan irinsu a Malaysia 'persona' Har yanzu da ragowar kokonto a cikin zuciyarta, tana ganin kamar wasa Faduwa ta ke yi mata. ''Me yasa Abdul-Sabur zai yi tunaninya saya mana motoci? A wanne dalili? Umaimah ta ke fada a cikin zuciyarta. Faduwa ta ce, ''Zabi daya wacce kala kika fi so, baka ko ruwan tokar? Cikin rawar jiki Umaimah ta ce, ''Duk wacce kika zabar min. Faduwa ta ce, ''Ki dauki ruwan tokar tunda na fiki haske, sai in dauki bakar. Ta mikawa Umaimah mukullin motarta a hannu yayin da Umaimah ta ji tamkar a mafarki, wai yau ita ce a kasar waje, har ta mallaki mota wanda tunda take a rayuwa ta ke matukar sha'awar duk macen data ga tana tuki. Bata taba saka ran zata yi mota ba a rayuwarta. Duk da dan Adam ba ya fitar da rai da samun rahamar Ubangiji. Allah Yana iya mallakawa bawanSa mulki, dukiya, lafiya ga wanda Ya so, kuma Ya hana idan Ya so. Umaimah ta yi tsalle ta kankame Faduwa suka hadu suka sha tsalle-tsalle suna murna su biyu. Yayin da tsurarun jama'ar da suke wajen suka jeru suna kallonsu, su ma fuskokinsu cike da murna sun fuskanci abun alkhairi ne ya same su. Da yake Faduwa duk ta sansu sai ta dinga jawo su tana sanar musu yau aka yi musu kyautar su. Ba ta fadi wanda ya saya musu ba, amma dai ta ce su zo gidanta gobe da yamma zata yi gagarumar liyafa. Faduwa da Umaimah ne suke tsaye a kofar gidan Abdul-Sabur suna kwankwasawa. Da alama ba ya zaune a falo saboda sai da ya jima kafin ta bude. Daga dukkan alamu ma daga wanka ya fito saboda jikinsa a jike da ruwa yake, yana sanye da doguwar riga jallabiya. Yaune karo na farko da Umaimah ta tako bangarensa (block) ballantana ta shigo gidansa. Ya yi matukar mamaki da ganinta, kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da hakan. Ya yi musu iso suka shiga suka zazzauna a falo, yayin da ya nemi izininsu sannan ya shiga daki ya saka kayansa riga da wando (jeans & T.Shirt) ya fito ya zauna tare da su. Suka gaishe shi sannan Faduwa ta fara bayani. Ta ce, ''Abdul ka fadawa Umaimah da bakinka ko zata yarda saboda na ga alama har yanzu ba ta gama yarda cewar wadannan motocinmu ne ba, kai ka sayo mana. Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya, ya ce, ''Umaimah, me ye abin mamaki? Ai tunda ku ka daure ku ka koyi mota, mallakar motar ba wahala ba ce tunda basu da tsada a Malaysia. Ni na ga ya dace in ba wa kowaccenku ku huta da hawa motar haya, tafiyar kafa ko hawa jirgin kasa. Umaimah ta silalo daga kan kujera ta durkusa ta yi masa godiya, gami da dogayen addu'o'i na fatan alkhairi. Yayin da Faduwa ma ta silmiyo daga kan kujera ta durkusa itama a gabansa ta rangada godiya. Abdul-Sabur ya ce, ''Haba-haba meye haka? Ya za ku durkusa min kamar wanda na ba ku duniya? Allah na tuba nawa motocin nan suke da har za ku dinga irin wannan doguwar godiya? Ku tashi ku zazzauna. Fatana Allah Ya kiyaye tsautsayi da asara. Suka amsa da, ''Amin''. Suka koma suka zazzauna. Faduwa ta ce, ''Ina gayyatarka liyafa (lauching) din bude motocin gobe a gidana da yamma. Zaka iya gayyato abokanka guda biyu ku zo tare. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''A'a Faduwa ba na son bidi'a. Me abun hada liyafa don kin yi mota? Kin ga abin da yasa wataran ba ma shiri ko, kin cika rawar kai. Umaimah me ya kamata ku yi? Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''Godiya ga Allah. Abdul-Sabur ya ce, ''Yauwa, haka ya kamata a yi ba holewa ba. Faduwa ta zabura ta ce, ''To liyafa ba ciyar da Musulmai ba ce a sami lada? Abdul-Sabur ya ce, ''Party za ki hada sosai da kek, da kunna disko na san sai kin cashe. Bayan haduwa da mata da maza a waje daya wadanda ba muharramanku ba. Ni dai ganina tunda mu dukka ukun nan mun sauke alkur'ani, mu kwana a daren yau muna karatu har sai mun sauke kur'ani. Mun ci sa'a kuwa yau alhamis ce daren juma'a, mu godewa Allah da Ya ba mu lafiya, arziki da zaman lafiya. Sannan mu yi wa iyayenmu da *yan uwanmu musulmi da suka mutu fatan neman gafara da aljanna ya kuma kai mu a sa'a idan tamu mutuwar ta zo. Mu yi fatan Allah Ya raba mu da sharrin karfe lafiya, Allah Ya sa a tuka su lafiya, a rabu lafiya. Sai kuma mu yiwa kasarmu ta gado addu'a, wato Nageria fatan zaman lafiya da yalwal arziki da wadata, mu yiwa sauran kasashenmu addu'a kamar su Ghana, Cairo da Malaysia kasashen musulunci Allah Ya kare Musulmi da addininSa Musulunci. A ganina haka ne kadai hanyar da zamu bi mu godewa Allah ba tare da mun saba maSa ba. Sannan kafin ku fara hawa motar kowaccenku ta dafa saman motarta ta yi wannan addu'a ''Allahumma inni as'aluka min khariha wa khaira ma fiha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa'uzu bika min sharrinha wa sharri ma fiha wa sharri ma jabaltaha alaihi. ''Ya Allah ina neman alkhairinta (mota) da alkhairi da yake tare da ita da alkhairin da Ka halicceta akai kuma ina neman tsarinKa daga sharrin ta da sharrin da yake tare da ita da sharrin da Ka halicce ta akai. Su dukka suka yi amanna da maganarsa, suka gasgata shi. Umaimah ta mike tsaye ta ce, ''To karfe nawa za'a fara saukar kur'anin kuma a ina zamu hadu? Don zan je duba tukunya na dora abinci. Faduwa ta ce, ''A gidanki za'a taru bayan sallar isha'i na ga kina da kur'anai da yawa, idan mun ci alala sai mu fara karatun. Abdul kada ka ci abincin dare yau ka zo gidan Umaimah ka ci alala daga gani zata yi dadi, saboda ta sha hanta da kwai ga albasa da attaruhu. Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Ban cika son alala ba da dai danwake ne. Umaimah ta yi caraf ta ce, ''Zan yi maka danwaken yanzun nan kuwa, ka zo ka ci. Ya yi murmushi, ya ce, ''Na kuwa gode. Bari na je masallaci na yi sallar magruba da isha'i daga nan sai na yi sallama da gida don karatun zai kai mu har asuba kun ga daga can sai mu yi jam'i mu yi sallar asuba. Sannan kowa ya tafi gida yayi bacci da safe. Ina fatan dai babu wanda ya ke da lecture ko test da sassafe gobe a Makaranta? Su dukka suka ce ba su da lecture balle jarabawa. Umaimah da Faduwa suka fito daga gidan Abdul-Sabur suka nufi gidajensu yayin da shi kuma ya shiga bandaki ya dauro alwala dan Almuru (Magaruba) ta kawo kai, ya rufo gidansa ya nufi masallaci. Karfe takwas da rabi bayan sallar Isha'i Abdul-Sabur ya biya ta gidan Faduwa ko zama bai yi ba, ya iske ta a shirye tsaf sanye da hijabinta ta idar da sallar isha'i dan haka sai ta rufo gidanta ita ma suka dungumo zuwa gidan Umaimah. Bugu daya suka yiwa kofar sai ta zo ta bude musu. Babu shakka sun yi farinciki da ganin Umaimah, domin yadda ta karbe su da farin ciki. Ta tsaftace gidanta kal-kal-kal ko kwayar tsinke babu a kasa. Kai ka ce harshe aka saka aka sude tiles din gidan. Kamshin turaren wuta tururu daga shigowarsu kamshin ya daki hancinsu. Umaimah sanye ta ke da riga da siket na material, sannan ta saka dogon hijabi daga dukkan alamu daga sallah ta idar da carbi a hannunta. Kan dinning table kai tsaye ta wuce da su inda ta tsara shi ta kawata da food flask da jugs na alfarma, ga farantai da cokulla a gefe. Daman su dukka ukun tsananin yunwa suke ji, sai suka zauna gaba dayansu kowa ya jawo farantinsa da cokali. Umaimah ta bubbude kowanne flask sai kamshi tururu ya daki hancinsu. Alala ce a flask daya, dan wake a daya flask din, yayin da daya flask din hadaddiyar shinkafa ce 'fried rice' tasha curry, hanta, peas da karas. Yayin da flask din karshe farfesun kaza ne mai romo da yawa an dafa da dankalin turawa sun hadu sun dahu luguf sai kamshi suje yi. Dogon kofi (Jug) daya, kunun aya ne sannan daya kofin markadaddiyar kwakwa ce da abarba aka tace aka zuba (coconut da pineaple) aka zuba dan sukari a ciki. Tabbas Yau Umamaimah ta yi musu komai, saboda ta dafa musu abun da suke so. Sai ga Faduwa da ta ke son alala kawai ta buge da cin shinkafa da danwake. Haka Abdul-Sabur da yake son dan wake ya hau cin alala da shinkafa gami da farfesu da dankalin da aka jejjefa a cikin romo. Suka ci suka sha gami da yiwa Umaimah doguwar godiya da jinjina bisa iya dafa zazzakan girki. To meye matsalar da zaisa abinci ya ki yin dadi? Da suka gama ci Umaimah ta kwashe kwanuka ta kai kicin ta wanke, sannan ta dawo suka matsar da tebur din da yake tsakiya (center table) suka zazzauna akan kafet suka buda kur'anai. Izufi ashirin-ashirin suka rarraba, Umaimah zata fara daga kasa, Faduwa daga sama, yayin da AbdulSabur ya dauki tsakiya. Faduwa ta yi hamma gami da yin doguwar mika ta dubi Abdul-Sabur da Umaimah, ta ce, ''Anya kuwa ba zamu bar saukar nan ba sai gobe da safe ba, da na ci abincin nan sai jikina ya mutu bacci kawai nake ji. Abdul-Sabur ya ce, ''Ba ki isa ba, sai kin yi karatunan, kina gyangyadi ruwan sanyi zan watsa miki. Kina so ki bari shaidan ya yi miki huduba, idan abun Allah ne sai ki dinga rauni, amma da party ne ko za a kwana ba kya gajiya. Faduwa ta dauki dogon salati, ta ce, ''Har haka na zama? Irin wannan shaidar zaka yi min? A'uzubillahi minal shaidanir rajim, mu fara karatu na kori shaidan. Umaimah ta sha tuntsira dariya, suka yi salati goma gafiyayyen halitta (S.A.W) sannan suka fara karatu babu wanda ya sake yin magana a cikinsu . Ayar Allah kawai suke ta ragargazowa. Ba su sauke ba har sai da suka kai asuba. Allah Ya amsa mana addu'o'inmu, Ya biya mana bukatunmu na alkhairi, amin!! *************** Ranar lahadi da yamma Abdul-Sabur Faduwa da Umaimah suna zaune a wajen shakatawa na jenting high land, wani gari ne mai nisa 51km daga KL. Wajen yin wasanni ne iri-iri da shakatawa, wajen akan tsauni yake babu abinda kake hangowa daga sama sai fulawowi da ruwan teku. Ga liluka wasu akan tsauni wasu a can kasa. Yawancin mutanen da suka fi yawa a wajen turawa ne masu zuwa kasar musamman dan shakatawa. Su Umaimah na zaune akan kujeru da tebur shake da kayan ciye-ciye kamar; gasassun kaji, meatpie, cake, gogguru, lemuka kala-kala. Tun daga karin kumallo na safe babu wanda ya kara cin abinci a cikinsu, saboda haka yunwa ce take ta addabarsu, suna zuwa sai suka hau yin maganinta. Abdul-Sabur ba ya kiwar kashe kudi komai ya tashi saya sai ya jifgo da yawa, yadda zai ishe su, su ci har su bari. Don haka har nauyi da kunyarsa suke ji wani lokaci su yi kokarin fitar da kudi za su biya sai ya hana su. Ransa yana baci da duk wacce ta aikata hakan daga cikinsu, don haka ma suka daina damuwa da sai sun dauko jakar kudi don babu abin da zai bari su saya da kansu. Sannan ya gargade su da su daina yi masa godiya duk abin da ya yi musu yana yi musu ne saboda Allah. Wai! Wai! Wa ya ga garabasa? Tabbas cikin *yan watannin nan Umaimah da Faduwa sun yi kiba sun kara jawur saboda ciye-ciye da kwanciyar hankalin da suka samu. Abdul-Sabur din ma a dalilinsu yana samu ya ci abinci sosai sabanin da da yake ci shi kadai ba ya iya ci da yawa. Mutum rahma ne inji masu iya magana, hira suke yi sosai ta shakuwa. Umaimah ta dubi Faduwa ta juya ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Wani lokaci ma sai in ji farin ciki ya yi min yawa, saboda na duba, na hanga a halin yanzu babu abin da yake damuna na kuncin rayuwa ko akwai abin da na rasa ma kadan ne, shima ban daukesa a matsayin damuwa ba. Allah Shine abin godiya, shi kadai Ya cancanci a godewa a koda yaushe. KU DAN HUTA ANAN SAI ZUWA GOBE DA YARDAR ALLAH A KWAI CI GABA INA GAYYATAR KU XUWA SHAFINA NA FACEBOOK DOMIN SADA XUMUN TA DA FADAKAR DA JUNAMAKWABTAKA 35 Faduwa da Abdul-Sabur suka yi murmushi, Faduwa ta ce, ''Gaskiya ne kanwata babu abin da yake damuna ni ma yanzu a duniya. Iyayenmu da suka rigamu gidan gaskiya muna yi musu addu'a Allah Ya kai rahma kabarinsu, amma na cire damuwa da bakin ciki daga cikin zuciyata. Son Sagir da talauci da yake addabata a baya sun gushe. Saura watanni uku in kammala karatuna, a take ina da upper ta aiki. Albashi mai tsoka, gida da motar hawa duk kyauta za a ba ni. Miji kuwa na hakura da nemansa, idan Allah Ya yi zan yi aure, in lokaci ya yi zan yi, idan kuwa ba ni da rabon aure a duniya ina addu'a Allah Ya tayani tsare kaina da kama mutuncina har karshen rayuwa. Tausayinta ya rufe Abdul-Sabur da Umaimah. Ya girgiza kai ya ce, ''Ki ma daina irin wannan magana za ki yi aure insha Allah ki hayayyafa, fatana ace kafin ma ki karbi takardar aikin naki a hannu ki sami mijinki a hannu kin ga dai-dai ke nan. Faduwa da Umaimah suka amsa da, ''Amin, amin Ya rabbi. Abdul-sabur ya gyara zama ya yi murmushi ya dubi Faduwa, ya ce, ''Ai ni da ina so ki ba ni adireshin Sagir idan na je Cairo in neme shi mu zauna inji yadda za'a yi a yi komai in dai zai yiwu. Faduwa ta harare shi, ta ce, ''Ka ji shi da tsokana ko, shekaru nawa da rabuwarmu ya taba nemana? Ai in mahaifiyarsa na raye auren nan da kyar zai yuwu, sai dai ikon Allah. Nasan ma ya yi aurensa ya manta da ni. Don ni ma gaskiya da kyar zan iya zama da Sagir yanzu, saboda na sake wayewa nasan daraja da martabar kaina yanzu, ba wai na fi karfinsa ba ne, a'a na ga yadda ake kula da tarairayar mace, bana tunanin Sagir zai iya yi min irin wannan tarairayar dana gani. Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya, ya ce, ''A ina kika ga tarairayar mace? Ai matan Malaysia su suke fita su nemo abincinsu, yaransu da manyansu kowa aiki yake yi dan ya ciyar da kansa. Kin manta sai kiga mata da miji da *ya*yansu sun je cin abinci restaurant kowa ya ci ya biya nasa? Faduwa ta ce, ''Na san da wannan amma ni yanzu na ga inda namiji yake tarairayar matarsa, sai ya burge ni haka nake fata in auri irinsa. Abdul-Sabur ya tabe baki ya ce, ''Ke kike leke-lekenki har kika hango wannan daman shegen yawo gare ki, gidajen kawaye iri-iri. ''Eh anyi yawon, Faduwa ta fada a fusace. Umaimah ta kyalkyale da dariya, daman ita ba ta da aiki sai dariya idan ta ji sun fara irin wannan fadan nasu. Abdul-Sabur ne ya katse dariyar da take kyakyatawa, nan da nan dariyar ta koma fushi. Da ya ce, ''Ke kuma Umaimah idan na je Nigeria zan je har Kaduna mu zauna da Abdul- Basi idan kuma Ilah kika fi so zan je Dugge mu gana. Kada ki ji tsoron Matawata, zan yi mata nasiha ku zauna lafiya. Faduwa ta kyalkyale da dariya, har da tsugunawa yayin da Umaimah ta ji wani kululun takaici ya dira a cikin zuciyarta, kuma ba ta sha'awar auren Ilah ko kadan balle Abdul-Basi. Sabuwar rayuwa ce ta bude don haka ba ta so ta waiwayi baya. Takaici ne sabo fil ya ke dirgo mata a kahon zuci har ta tuna dacin da suka dandana mata a rayuwarta ta baya su dukka biyun. Abdul-Sabur ma ya yi ta dariya daga karshe ya shiga lallashinta yana ba ta hakuri, don yaga da gaske take ta yi fushi, har ta daina cin abincin. Dariyar da Faduwa ta ke kyakyata mata ita tafi tunzura ta sai da Abdul-Sabur ya roki Faduwa ta daina yi mata dariya kada ta sa ta kuka. Da faduwa ta ki dainawa sai ya ce, ''Zan je Nigeria in hada ki da Alhajin Birni. Nan dai aka rincabe da Faduwa da Abdul-Sabur suka hau zolayar juna. Umaimah ta sami abin dariya, tana ta kyakyatawa. Abdul-Sabur ya saka hannu a aljihun wandonsa ya ciro wasu kananan katina guda biyu masu kyawu da kyalkyali kai ka ce da ruwan gwal aka yi rubutun. Ya mikawa Faduwa daya, Umaimah ma guda daya. Sai suka yi sauri suka karba suka karanta, daga dukkan alamu ba su fahimci ko katin mene ne ba. Ba na gayyatar aure ba ne, haka ba na liyafa ba ne. Abin da za su iya gani shi ne 'Graduation Ceremoney. Abdul-Sabur ya yi dariya ya gyada kai a lokacin da ya ga duk sun zuba masa ido suna neman karin bayani daga gare shi. Ya ce ''Me ye ba ku gane ba? Katin gayyata ne na bikin yaye mu mun gama karatun PhD za a bamu satifiket. Lokaci ga shi nan an rubuta karfe goma na safe, waje ga adireshin nan da sunan hotel din 'J.W MaRRIOTT HOTEL'. A bukit Bing Tang. Sai kun nuna katin nan za a barku ku shiga, shi ne ya sa na karbo muku. Ku yi kokari ku fito da wuri gobe, tara da rabi ta yi muku a can. Tafiyarmu ba zata zama daya ba saboda ni a cikin makarant zan kwana, tun karfe bakwai na safe zamu shiga taro (meeting), sannan a raba mana riguna da huluna (graduation gown) a zuba mu a doguwar motar makaranta a kawo mu can. *Yan uwa da abokan arziki za su zo daga kasashe daban-daban, ni dai ku ne *yan uwana kuma dangina, in kuka makara ba ku zo ba shikenan na zama ba ni da kowa, babu mai daukana a hoto a lokacin da ake mika min satifiket. Faduwa da Umaimah suka zabura suka hada baki, ''Ah haba zamu zo mana. Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce, ''Tsokanarku nake, na san zaku zo, ai na yarda da ku kannena. Na so ace Ummana Fuse ta zo itama, amma sai na kyale ta ban gayyace ta ba saboda nisa, Malaysia ta yiwa tsoho nisa tun daga Ghana zuwa Malaysia, zata sha wahalar zuwa. Amma kanwata Kausar da maigidanta sun ce min za su zo ban dai tabbatar da zuwan nasu ba, don nasan shiriritarsu. Jiya dai da muka yi waya suna London sun ce min za su taho nasan ko za su iso sai yau da tsakar dare. Na kira su dazu na ji wayarsu a kashe, ban sani ba ko suna hanya in sun iso na san za su kira ni, ga dai katinsu a hannuna in sun zo in ba su su shiga. Faduwa da Umaimah suka yiwa su Khausar fatan Allah Ya kawo su lafiya. Sai da suka yi sallar isha'i sannan suka sha hawan lilo da tsalle-tsalle, sannan suka fara haramar tafiya. A motar Umaimah aka zo ita ake tukawa. Abdul-Sabur ya so ya karbi tukin saboda garin da nisa, kuma ga dare ya yi, Umaimah ta ce ya bari zata tuka, ya shiga gidan baya ya zauna Faduwa da Umaimah a gaba suka tafi. A 'Sabang Jaya' ya ce su sauke shi cikin makarantarsu da suka sauke shi sai suka yi masa sallama akan sai goben idan sun hadu a can. Umaimah ta fisgi mota sai unguwarsu wato 'MAHARJALELA' Allah Ya ba mu alheri!! **************** Tsabagen kwalliya mai suna kwalliya an caba ta a wannan rana da kaya na karya, sai a wajen ma su Umaimah suka taba ganin wata suturar. Gwala-gwalai da lu'u-lu'u a wuyan wasu matan, abun sai a rike baki. Hausawa, Inyamurai, Yarbawa, Larabawa da Turawa duk sun hallara a wannan katafaren hotel da ake ji da shi a Malaysia, wato 'J.W Marriott', kowa sai ya nuna kati za'a bar shi ya shiga, yana shiga sai ya sami waje ya zauna a cikin katafaren dakin taron da yake cikin hotel din. Babu abin da yake tashi a wajen sai sautin kida a hankali gami da sanyin A.C da kamshi na alfarma. Kowanne tubur an zagaye da kujeru hudu, abubuwan sha ne kalakala a gaban kowa. Faduwa, Umaimah da wasu Turawan Spain mata da miji ne suka zauna a teburi daya. Kan ka ce kwabo Faduwa ta saba da su suna ta hira, suka shaida musu su ma sun zo jiya daga Spain wajen dan uwansu. Umaimah da Faduwa suka shaida musu su a nan kasar suke zaune suna karatu, amma asalinsu *yan Africa ne suma dan uwansu suka zowa. Su umaimah sun yi kwalliya, amma ba su zaci irin wannan caba adon za a yi ba, yadda suke hango dakakkun leshina da dakakkun riguna (English wears) a jikin mata sai suka raina shigarsu. Sun saka wando jeans, da riga mai dogon hannu, gami da kananan hijabai da takalma masu tsini da jakunkuna ratayawa masu tsada. Hannayensu a jere da zobuna English gold. To me ye laifin shigarsu? Ba ta yi muni ba, kuma sun fi wasu kyau duk da su ma da yawa sun fi su. Har yanzu dai ana jiran isowar manyan kasar da manyan furofososhin makarantar da kuma dalibai masu fita wato su Abdul-Sabur. Har yanzu dai shigowa ake ta yi hall dai sai hadidiyar mutane yake yi, kowa ya shigo ba ya rasa wajen zama, saboda girman wajen da kujeru rututu. Karfe goma saura minti goma sha biyar aka sanar da shigowar dalibai da malamansu. A bun gwanin ban sha'awa sai ga su Abdul-Sabur nan a jere a layi suna shigowa sun yi anko da riguna da huluna iri daya (Graduation gown). Abdul-Sabur yana daga baya-baya kasancewar mata ne gajeru daga gaba, shi da yake dogo ne sosai a mazan ma yana daga kusan karshe. Umaimah da Faduwa sai zare ido suke suna hange ba su ga nasu ba alhali yawanci kowa ya ga dan uwansa yana murna, yana dauka a hotuna. Can suka hango gogan nasu ya zuba kyau kuwa a cikin kayan fiye da fararen fatar ma. Nan da nan kowaccensu ta tashi da kyamararta a hannu suna daukarsa a lokacin da yake tafiya a cikin ayari. A lokacin da suke daukarsa a hotuna sun fahimci wata mata da mijinta su ma sun ta so da sauri suna daukarsa a hoto. Ko tantama babu kanwarsa ce Kausar tare da mijinta, sai suka hau kallon-kallo tsakanin su Kausar da su Umaimah. Da yake Umaimah ta taba ganin Kausar a Makka sai nan da nan ta shaida ta. Ba su yiwa juna magana ba har kowa ya koma mazauninsa ya zauna, yayin da su Abdul-Sabur suka isa bangaren da aka tanadar musu na musamman suka zazzauna daga gaba. Bayan kowa ya zauna ne aka fara bayanai cikin harshen Nasara (turanci). Daga karshe aka fara kiran sunayen dalibai guda goma da suka fi kowa cin jarabawa, ana ba su satifiket dinsu a hannu. Ihu, tafi da murna marar misaltuwa *yan uwan wadannan bayin Allah suke yi. Allah cikin ikonSa kwatsam aka kira sunan Abdul-Sabur shi ne na hudu, nan da nan Faduwa da Umaimah, Kausar da mijinta suka dau murna da tafi raf-raf-raf, hotuna kuwa sun kyasa masa ba adadi. Sarkin rawar kai har kan stage ta haye tana daukarsa a hoto, kai ka ce ita ce zata mika masa satifiket din, wato Faduwa. Banda dariyar farin ciki sai dagawa jama'a hannu da Abdul-Sabur yake yi. Dalibai suna da yawa don haka an kai karfe daya da rabi ana abu daya. Abinci kala-kala masu dadin gaske ake ta jerewa akan teburan kowa. Suka ci suka sha suka gyatse ba tare da ko sisinsu ba. Da aka gama rufe taro da jawabi sai taro ya fara watsewa. A lokacin ne su Abdul- Sabur suka sami damar tunkaro inda *yan uwansu suke dauke da kwalinsu a hannu. Ana ta rungumar juna ana murna. . Allahu Akbar, sai ya karaso inda su Umaimah suke cike da murna, Kausar da mijinta suka taho suma aka taru waje daya. Bai ankara ba yana juyawa sai ga Uncle Hamza a bayansa shi da babban yaron da ya ke mai aiki a shago na London wato Emeka. Hade da El-Abdullahi dan Indonosia ne daya daga cikin shugaban kamfanin da suke saro kaya a wajensu, takanas ya zo taya shi murna. Nan dai murna ta hautsine yayin da Abdul-Sabur ya shiga gabatar da kowa da kowa. Yawanci sun san junansu, Umaimah da Faduwa ne basu sani ba. Ya gabatar da su matsayin MAKWABTANsa, kuma aminansa, sannan ya juya ya gabatar da *yan uwansa ga su Umaimah. Aka gaggaisa aka dinga daukar hotuna daban-daban. Faduwa da Umaimah suka yi musu bankwana suka kama hanyar gida yayin da Abdul-Sabur ya tafi ya raka su Uncle Hamza da tawagarsa masaukinsu. Kausar da mijinta kuwa su ma hotel dinsu ba shi da nisa da kafa ma suka karasa anan cikin Bukit Bing Tang. Abdul-Sabur ya yiwa su Kausar alkawarin daga ya raka su Uncle Hamza zai zo hotel dinsu ya samesu. Faduwa ce ke tuka motarta Umaimah na zaune a gefenta babu abin da suke sai hirar kayan jikin Kausar, leshine tsadadden gaske kuma ya yi kyau, ruwan dorawa da fulawar ruwan bula (blue), dinkin riga da siket matsattse ga lu'u- lu'u yana ta kyalli a wuyanta. Shaddar da ke jikin mijinta ta hadu sosai fara sol. Tabbas kudi ya zauna musu ko ba'a fada ba, Allah Ya yarda da su Ya amince su yi arziki. Haka ai rayuwa ta ke, babu abin da yake dauwamamme, talauci ko wadata. Sun jinjina tsohon nan da ya yi kara ya yi zumunci ya zo, wato Uncle Hamza, shima ya sha babbar riga da hula da wani hadadden filted, bai bar al'adarsa ba bawan Allah. 'Allah Ya azurtamu duniya da lahira da alfarmar Annabinmu (S.A.W). In ji Faduwa yayin da Umaimah ta cafke salatin suka dire tare. Taro ya yi taro, haduwa takai haduwa yadda baki ba zai iya lissafa wasu abubuwan ba sai dai ayi kurum! Farin ciki da nishadi babu irin wanda ba su shaka ba a yau. Haka babu wani abun dadi da ba su ci ba a yau. Don haka sai hamdala ga uwa uba wanda suka je dominsa ya burge, ya fito da sakamako mafi daraja. Da yamma Abdul-Sabur ya iso gidan Faduwa shi da Kausar suka ci sa'ar iske Umaimah a gidan, don haka aka hadu a kasha hira. Babu abin da Kausar ke yi sai lura da Yayanta da *yan matan nan ta ke yi idan suna hira, tana so ta tantance wace ce budurwar a ciki. Don ta kula Yayanta yana ji da su alhali bata taba ganin in da ya saba da mata haka ba, har yake shiga cikinsu yana musu hira haka. Ta kasa tantancewa wani sa'in sai ta ga kamar yana shisshigewa Umaimah idan aka jima sai ta ga ya fi kula Faduwa. Ta shiga gaggawar su kebe ita da shi ta jero masa tambayoyi game da matan nan. Sai da aka kira sallar magruba suka watse, Umaimah ta koma gidanta, Abdul-Sabur da Kausar suka tafi gidansa. Da ya bude mata kofar gidan ta shiga, sai ya sauko ya tafi masallaci. Daga masallaci ya je ya dauko mijin kanwarsa daga hotel ya ce su kauro gidansa dakuna biyu ne. Kafin su iso Umaimah da Faduwa duk sun kawowa Kausar abinci kala-kala. Da Abdul-Sabur ya dawo Kausar ta nuna masa abin arzikin da kawayensa suka kawo mata, ya ji dadi kwarai. Sai suka jere akan dinnin table suka zauna cin dadadan abinci, aka bude shafin hira. Kausar ta dubi Yayanta tayi dariya ta ce, 'To wai a cikinsu wacece Yayar tawa don nasan dai akwai guda daya da aka yarda da ita. Abbdul-Sabur ya harareta ya bata rai, don baya so ta dinga masa shisshigi game da maganar aure. A'a ka ga ka daina hararar min mata, ai gaskiya ne, ka fada mana kawai, in ita kanwarka ce ba zaka bata amsa ba, ni ai abokinka, ne, kuma yayanka idan aka bi ta shekaru. Malam ka fada mana kawai. Inji mijin Kausar. SAI GOBE INSHA ALLAH TA'ALA INA GODIYA A GAREKU DA ADDU'OIN KU A GARE NI. Dan Aunty.MAKWABTAKA 36 Suka kyalkyale da dariya su duka ukun. Abdul ya kai lomar abinci, ya ce, ''Idan na fada muku wani abu za ku yarda? Babu guda daya a cikinsu da muke soyayya. Sun dauke ni tamkar yayansu, na dauke su tamkar kannena na jini. Su duka rayuwarsu abar tausayi ce, marayu ne kuma ba su da miji a kasar da ba su da dangi. Ina jin tausayinsu matuka shi yasa na yi kokari mu hada kai mu zauna lafiya. Kuma kun san wani abin mamaki? Gaba dayansu *yan asalin Nigeria ne har Faduwa Balarabiya, mahaifinta mutumin Sokoto ne, Umaimah kuma bafilatanar Gombe ce, *yar asalin wani kauye Dugge. Kausar ta yi dariya ta gyada kai ta ce, ''Lallai wannan hadin ya yi kyau. Amma Yaya ya kamata ka zabi daya naga duk suna da kirki, kuma ga su masu ilimi, kyawawa. Amma ni na fi yi maka sha'awar babbar, wato Faduwa. Abdul-Sabur ya katse hammar da yake yi, ya ajiye cokali ya dade yana kallon Khausar don mamaki, can ya daure ya yi magana. Ya ce, ''Me yasa kika ce haka? Ta ce, ''Za ku fi daidaitawa saboda ta manyanta zata fi sanin rayuwa da hakurin zaman aure, ga ta da fara'a da sakin fuska. Ita ma karamar ba laifi tana da kirki, amma wani lokacin kamar tana da jan aji da ji da kai. Wai shin ba ita ba ce muka hadu da ita a Ka'aba ba, ta harare mu ta tafi? Shamsuddin Ya girgiza kai, ''Ai gara ya auri karamar za su fi dacewa, saboda Faduwa zata ga kamar sa'anta ne ba zata yi biyayyar aure ba. Amma karamar, yarinya ce karama budurwa za su fi daidaitawa. Abdul-Sabur ya yi murmushi kawai ba tare da ya sake cewa komai ba, har suka yi surutun su suka bari. Kwanakin su Kausar biyar a Malaysia, Abdul-Sabur na dawainiyar kai su wuraren shakatawa kalakala. Idan suka fita tunda safe sai tsakar dare suke dawowa. Yawanci da Faduwa ake tafiya kasancewar Umaimah na zuwa makaranta kullum. Sau daya ne suka je 'Langkawi Beach' da Umaimah shi ma don bata taba zuwa ba tana so ta je ta gani, idan ba ta bi su ba yanzu zuwan zai yi mata wuya nan gaba, musamman idan lecture ta kankama. 'Langkawi Beach' teku ne babban gaske wanda aka kawata shi fiye da sauran tekunan da suke kasar. Garin yana da nisa sosai a mota, don haka wasu suke hawa jirgin sama. Abdul-Sabur ne ya saya musu tikitin jirgin sama su dukka biyar din, suka isa garin ranar alhamis da rana. Ba su baro wajen ba sai karfe goma na dare, su dukka sun kunshi nishadi marar adadi. Ranar da Kausar da mijinta zasu tafi Abdul-Sabur ya rako su gidan Faduwa suka yi mata sallama, sannan suka dunguma gidan Umaimah ita ma suka yi mata sallama. Umaimah ta rako su har bakin lift suka tafi, tayi musu fatan alkhairi da fatan Allah Ya kaisu gida lafiya sannan ta koma gida ta ci gaba da karatu. Kasancewar wannan semester bata samu ta zauna ta yi bita ba sosai, tana ta biyewa su Abdul-Sabur suna yawon shakatawa don haka ta yiwa kanta fada ta zauna a gida tayi karatu. Faduwa kuwa da ita aka yi rakiya har filin jirgi. Kafin su Kausar su wuce zuwa wajen screening sai ta jawo hannun Abdul-Sabur gefe suka kebe, a zatonsa wata magana zata fada masa mai muhimmanaci. Sai ya ji ta ce, ''Zan fadawa Faduwa kana sonta zaka aure ta in ka kasa fada. Don gaskiya ta damu dakai fiye da Umaimah, ba ka ganin Umaimah ko rako mu bata yi ba, Faduwa ce ta katse baccinta da tsakar daren nan ta taso ta zo. Ya ji tamkar ya kifa mata don takaici, ya harare ta ya yi tsaki. Ya ce, ''Wai ke me yake damunki ne? Kada ki kuskura ki fadawa Faduwa wata magana, naga kin karbi lambarta wallahi idan na ji wata magana sai na bata miki rai. Babu ruwanki da wannan maganar. Kausar ta tabe baki, ta ce, ''Allah Ya huci zuciyarka ba ruwana, daga yau ma na daina yi maka maganar aure ma balle na yi laifi. Ya ce, ''Da kin hutawa kanki kuwa. Haka suka yi sallama baram-baram ba ta walwala. Har mijinta da Faduwa suka fuskanci hakan, amma ba a shiga tsakanin dan uwa da dan uwa, babu wanda ya tambaye su me ya faru. Sai karfe biyu na dare Abdul-Sabur da Faduwa suka dawo gida. Suka yiwa juna sallama kowa ya shiga gida. Asuba ta gari Abdufaduwa. * Sai bayan tafiyar su Kausar ne Abdul-Sabur ya samu yake yin isasshen bacci kwana biyu, amma da su Uncle Hamza suka dawo Malaysia daga Singapore sai aiki ya dawo masa sabo fil. Saboda yana tashi da safe yake zuwa ya same su a hotel, daga nan su nausa cikin kasuwa. Daman dai Uncle Hamza dan kasuwa ne don haka duk kasar da ya je sai ya nemi abin da zai sara, wani ya aika shagonsa na London, wani kuma ya tura shagunansa na Ghana. Ba dare ba rana Abdul-Sabur yana tare da Uncle Hamaza har sai da suka shafe kwanaki goma a haka, sannan ya kai su filin jirgi shi da Emeke suka koma London. Don haka Abdul da su Faduwa ma ba a haduwa ko a waya ba sa samunsa. Bayan tafiyar bakinsa da ya dawo gida ma sai da yai kwanaki uku bai kunna waya ba, bacci kawai yake yi, sai dai ya tashi ya yi sallah ya koma bacci, bai cika fita masallaci ba ma abinci ma jifa jifa yake ci. To me zai yi tunda ya gama karatu? Sai da ya tabbatar ya huta sosai ya kunna wayarsa missed call ya fi guda dari ya tarar daga kasashe daban-daban. Missed calls din Faduwa guda ashirin da biyu. Na Umaimah guda biyar sai na Kausar guda talatin da uku, ta damu tana ta kiransa a tunaninta saboda ita ya kashe waya, don ta bata masa rai ta yi masa maganar Faduwa, don haka duk ta bi ta damu. Ya dinga bin su daya bayan daya yana kira yana yi musu bayanin yana nan lafiya kalau, baccin gajiya ne kawai. Ya cewa Umaimah da Faduwa in ba sa komai ranar asabar da yamma su hadu a wajen shakatawa na 'Sunway Pyramid' su yi hira, dukkansu suka ce ba damuwa za su je. Ranar asabar misalin karfe biyar da rabi suka gama hallaruwa a cikin *yar rumfar da suka saba haduwa, kowanne daban-daban ya zo. Ba daga gida suke ba, Umaimah daga makaranta ta ke gidan su Aisha Bingyal. Faduwa daga Hotel din wasu kawayenta da suka zo daga Cairo, Abdul-Sabur ne ya fito daga gida. A jere suka jera motocinsu a wajen da aka tanada don yin 'parking'. Ka'ida ne daga ka zauna a cikin rumfunan ma'aikata su kawo maka littafin abinci da abin shan da ake siyarwa, ka zaba ka saya, don haka sai kowa ya zabi abin da ya ke so. Faduwa da Umaimah a koshe suke dam! Kasancewar sun ci abinci a wajen kawayensu. Lemo kadai suka zaba. Abdul ne yake jin yunwa sosai don ko karyawa bai yi ba shi ya zabi shinkafa da kaza. Suna shan lemo suna hira, wasa da dariya Abdul-Sabur ya kammala cin abinci ya goge baki da hankici, ya juya ya kalle su ya yi murmushi. Ya ce, ''Na tara ku anan don mu yi zaman karshe, kuma hirar karshe. Sai duka suka zura masa ido suna yi masa duban rashin fahimta. Yayin da mummunar faduwar gaba ta addabi zukatansu. ''Wacce irin magana kake yi Abdul? Idan ka ce hirar karshe zaman karshe, ai sai mu yi zaton mutuwa zaka yi. Inji Faduwa. Umaimah ta ja dogon numfashi ta dire bata iya cewa komai ba. Abdul-Sabur ya yi shiru kansa a kasa kamar mai tunani, sannan ya dago ya dube su ya yi murmushin karfin hali. Ya ce, ''Kin yi gaskiya Faduwa, banda Allah babu wanda Ya san abin da zai faru a gaba amma Allah Ya kadarto rabuwarmu wanda ba na tunanin zan sake waiwayar Malaysia kuma idan na tafi. Sai suka ji tamkar an dire aradu a kahon zuciyoyinsu, suka zazzare ido suna dubansa. Ya ci gaba da cewa, ''Na kammala karatuna, na so in dan zauna da ku saboda sabo, amma Uncle Hamza ya ce in tattara in koma gida. Don haka zan tafi gobe har na cike takardar sakin gidana sun dawo min da ragowar kudina don ban cika shekara ba. Yana rufe bakinsa sai Faduwa ta dora hannu aka, Umaimah ta cije yatsa suka kame tamkar wasu gumaka, idanuwansu a sunkuye a kasa. Da ya ambaci sunayensu suka dago suka dube shi, sai yaga hawaye sharkaf na zubowa daga idanuwansu. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un? Suke karantowa su duka ukun a bayyane. Faduwa ta sharce hawaye ta ce, ''Amma Abdul zaka tafi ka ki yi mana sallama da wuri, sai da ya rage saura awanni? Ya girgiza kai, ya ce, ''Ku yi hakuri na san zafin da zaku ji na rabuwarmu, bana so in tayar muku da hankali da wuri. Ku yi hakuri don Allah ba boye muku na yi ba. Ku yafe min idan na bata muku rai, ko na kuskure muku ban sani ba, kun san mutum ajizi ne. Ni ma na yafe muku idan kun yi min laifi a fili ko a boye, balle ni babu wacce ta yi min laifi a cikinku. Ku yi min alkawari za ku ci gaba da zumunci a junanku ko ba na nan, ku ci gaba da mutunta kanku da kare mutumcinku a kasar nan har ku kammala karatunku. Umaimah ina rokonki da zarar kin kammala karatu ki koma gida ki zauna kusa da iyayenki ko a cikin garin Gombe ki kama aiki har Allah Ya ba ki wani mijin ki yi aure, saboda kin yi kankanta ace kin zauna a wata kasar ba a gaban iyayenki ba. Ki manta komai da ya faru da ke a baya, ki bude sabuwar rayuwa Allah zai taimake ki. Kuka ya ci karfin Umaimah, sai ta gyada kai don ba zata iya magana ba. Hawaye mai zafi ne ya fara zubowa daga idanunsa shi ma kasancewar ya ga halin da suka shiga na kuka. Bai zaci zasu ji radadin rabuwa da shi haka ba. Ya goge hawaye ya juya ya dubi Faduwa, ta kifa kai akan tebur tana kuka ta ki dagowa har sai da ya ambaci sunanta ba adadi, sannan ta dago ta dube shi idanunta sun yi jawur. Ya ce, ''Faduwa ki yi hakuri da duk yanayin da kika tsinci kanki, Allah Yana tare da ke, zai yaye miki damuwarki insha Allah, ki rike aikinki ki dinga ziyartar *yan uwnaki na Cairo da Nigeria. Kada ki yanke zumunci da su don Allah ba Ya bada rahama ga mai yanke zumunci, haka zumunci yana kai bawa aljanna. Faduwa ta gyada kai cikin shesshekar kuka, ta ce, ''Na ji zan yi amfani da shawararka insha Allah. Umaimah ta goge hawayenta ta tashi tsaye cimak ta dube su, ta ce, ''Zan koma makaranta, dama group assignment muke yi a gidan Aisha Bingyal na taho zan koma mu karasa. Abdul-Sabur ina maka fatan Allah Ya kai ka gida lafiya, kuma Allah Ya saka maka da alkhairi a bisa dawainiya da kulawar da ka yi mana. A da rayuwata tana cikin kunci har sai da ka bi duk yadda zaka yi na sami sauki. A da farin ciki ya kaurace min, kai ka taimaka ya dawo. Ina gudun mutane ka sa na shigo cikin mutane. Ina cikin kuskure na dawo hanyar Allah madaidaiciya. Yanzu na san tawakkali na nemi wadanda na kauracewa a baya. Da jikinka da dukiyarka babu abin da baka yi mana ba, tsakaninmu da kai sai addu'ar Allah Ya kaddara saduwarmu ko ba a duniya ba ranar gobe kiyama, Allah Ya hada mu a aljanna.. Kuka ne ya hana ta karasa maganarta, sai ta juya da sauri ta tafi. Ta ki dawowa duk kwalla kiran sunanta da Faduwa ke yi. A guje ta shiga wajen da ta ajiye motarta ta bude ta zauna ta dora kai a sitiyari ta sharbi kukanta har ta godewa Allah. Ita kanta ta rasa dalilin yin wannan kukan saboda Abdul-Sabur din nan a kasar nan ta san shi kwanan nan, to me don ya ce zai tafi zata damu kanta? ''Mutumin da na ki jini a da na tsana, na tsani in hadu da shi a hanya? Ya aka yi ya zama abokina har na ke jin ciwon rabuwa da shi? Sabo turken wawa in ji masu iya magna. Abdul yana da kirki, yana da kyautatawa, kuma zuciya tana son mai kyautata mata wannan ita ce kadai amsar. Inji zuciyar Umaimah. Tana tuki tana tafe tana tunani, hawaye kuwa ya ki kafewa sai shatata ya ke. Faduwa ta zabura ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ya na ga ka saka kafa ka shure maganar da muka yi da kai? Ya fada cikin sanyin jiki, ''Wacce ke nan? Faduwa ta sharce hawaye ta ce, ''Maganarka da Umaimah ta aure. Abdul-Sabur ya yi murmushin karfin hali ya gyara zama, ya ce, ''Daman na amince, na yi miki alkawari zan aure ta ne? Ai ban taba amsa miki ba ke kadai kike maganarki. Abinda kika kasa fahimta shi ne, babu maganar soyayya tsakanina da Umaimah, yadda nake mutumci da ke haka nake yi da ita.. Faduwa ta katse shi cikin kuka ta ke magana, ta ce, ''Amma ni naga kun dace na hada ku, ka ce kana tausayinta, maganin tausayi sai ka aure ta. Kai ma ka san zaku dai-daita da ita don ba ta tsane ka ba, ta saba da kai, ta shaku da kai, ga ta da ladabi da kunya da tarbiyya.. Abdul-Sabur ya dafe kai, ji yake tamkar tana daka tabarya a kwakwalwarsa.. Ya daga hannu da sauri ya dakatar da ita. Ya ce, ''Ya isa haka Faduwa, ba ki fahimce ni ba, ba za ki taba fahimtata ba kuma. Ni kadai na san halin da nake ciki yanzu, zuwan da Uncle Hamza ya yi, ya zo min da magana kuma ba zan iya ketare ta ba, ya ce in zo in auri *yarsa.. Bai rufe baki ba Faduwa ta dafe kirji don fargaba da tashin hankali. Ta ce, ''Shi yasa kake yi mana sallama irin wacce har abada ba zaka sake waiwayarmu ba? Ta girgiza kai yayin da hawaye ya ci gaba da surnanowa daga idanunta. Ta ji ba zata iya ci gaba da zama tare da shi ba, saboda zuciyarta kamar zata burme. Nan da nan ta mike, ta suri mukullin motarta. Ta ce, ''Abdul Allah Ya kiyaye hanya, Allah Ya kaddara saduwarmu. Ni ma zan tafi ana jirana Putra Jaya'. Ta tafi da sauri hawaye yana zuba. ''Faduwa, Faduwa zo ki ji. Inji Abdul. Ta ki waiwayowa ma balle ta dawo, ta dade a zaune a mota tana kuka, sannan ta tuka ta tafi, don kada ma ta kwana a gidan ta ga tafiyarsa sai ta wuce garin 'Putra Jaya' zata kwana a gidan kawarta. Umaimah ma ma a gidan kawarta Aisha ta yi niyyar kwana. Karfe dayan dare kowa yana bacci yayin da Faduwa da Umaimah suke murkususu a cikin duhu saboda damuwa. Abdul-Sabur ya damu kwarai da ya je gidajensu ya iske ba sa gidajensu, ke nan babu me yi masa rakiya. Yana filin jirgi ya kira Faduwa ya sake yi mata sallama ya tabbatar mata yana filin jirgi zai tafi, ta rushe da kuka, ta yi masa fatan alkhairi da fatan Allah Ya kiyaye hanya. Ya tambaye ta laifin me ya yi suka gudu daga gidajensu suka ki raka shi filin jirgi. Ta ce bai yi musu komai ba, saboda tashin hankali ba zasu iya ganinsa zai tafi ba. Irin wanna tambayar ya yiwa Umaimah da ya kira ta a waya, irin amsar da Faduwa ta ba shi ita Umaimah ta bayar, sai ya shaida mata yana filin jirgi nan da awa guda za su tashi.MAKWABTAKA 37 ya shaida mata yana filin jirgi nan da awa guda za su tashi. Ta tambaye shi ina zai je? Ya amsa mata Ghana zai je. Ta yi masa tambayar data ba shi mamaki, irin tambayar da Faduwa ta yi masa dazu. Umaimah ta ce, ''Yayana ba ka ji shawarar da na baka ba ko wacce na ce ka auri Dr. Faduwa? Idan ka duba maganata baku da matsala saboda kun shaku, ka san halinta ta san naka, mace me fara'a da son mutane. Me zai hana ka share mata hawayenta ka aure ta? Sai ya ji kansa ya yi masa gingirim ya ji tamkar zai fasa ihu. Wai shin me yake shirin faruwa da shi ne a rayuwa? Tabbas ya gasgata ba bakinsu daya ba da sai ya ce hada baki suka yi don su gwada shi. Ya fuskanci kowacce magana take yi masa tsakani da Allah. Lallai suna kaunar junansu, kuma kowacce na tausayin *yar uwarta. Umaimah ta ji shirun yayi yawa, sai ta zaci wayar ta katse fadi ta ke, ''Hello! Hello kana jina? Ya yi ajiyar zuciya mai karfi, ya yi gyaran murya ya ce ''Umaimah, ban ki shawararki ba, amma ina so ki gane wani abu guda daya. Babu soyayya tsakanina da Faduwa ko kusa a matsayin kanwa ko kawa na dauke ta, kamar yadda na dauke ki. Sannan Uncle Hamza ya zo min da maganar auren *yarsa wanda ba zan iya bujire masa ba. Umaimah ta dafe kirji ta runtse ido yayin da hawayen takaici ya surnano mata. Sai ta yi masa fatan alkhairi da fatan Allah Ya ba su zaman lafiya da zuri'a dayyiba. Ya amsa mata da ''Amin, na gode. Suka kashe wayar babu wanda ba ya hawaye a cikin su ukun. Da ya shiga jirgi ma ya zauna sai da ya kikkirawo su ya shaida musu ya shiga jirgi ya zauna, nan da *yan mintuna za su tashi don haka zai kashe wayarsa. Suka sake yin bankwana da fatan Allah Ya kai shi gida lafiya. Jirgi ya lula da Abdul-Sabur, ya bar Umaimah da Faduwa cikin gagarumar damuwa da kewarsa. Allah Ya kiyaye hanya!!! * Faduwa da Umaimah su kan hadu jifa-jifa, amma ba koda yaushe ba, tabbas Abdul-Sabur shi ne ginshikin hada wannan shakuwa tasu. Babu wacce take jin dadin zaman gidanta a cikinsu, kullum da sassafe Umaimah sai ta fito kan baranda ta tsaya babu abin da ta ke gani a idanuwanta kamar inuwar Abdul-Sabur a lokacin da yake tsayawa yana kallonta yana yi mata murmushin nan na sa. Nan da nan sai ta ji hawaye ya surnano mata, sai ta jawo doguwar kujerarta ta zauna don kada jiri ya kwashe ta ta fadi. Ta duba dukka wundunan gidansa, ta ji kamar za ta ji motsinsa, amma ta ga wayam. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ta ke ta karantawa a bayyane. Ta tashi ta shiga gida ta kudundune akan kujera ta dora filo a kanta babu abin da ta ke hange sai Abdul-Sabur. ''Me yake shirin faruwa da ni ne? Inji Umaimah ta ke tambayar zuciyarta. Wayarta ce ta yi ruri nan da nan ta tashi ta suri wayar addu'a ta ke, fata ta ke Allah Ya sa AbdulSabur ne. Amma kash! Sai ta ga sunan Faduwa. Ta amsa a sanyaye. Bayan sun gaisa Faduwa ta ce, ''Abdul-Sabur kuwa ya kiraki bayan tafiyarsa? Umaimah ta ce, ''Bai kira ni ba. Faduwa taja dogon tsaki, ta ce, ''Ni ma bai kira ni ba, kinga duk lambobinsa na London da Ghana da nake da su na kira a rufe. Umaimah ta ce, ''Baki da lambarsa ta Nigeria? Ina jin can ya tafi. Faduwa ta ce, ''Bai taba kirana da lambar Najeriya ba. Suka yi sallama suka kashe waya, yayin da kowacce ta shiga mamakin damuwar da dayar ta shiga a sanadiyyar rashin Abdul-Sabur. Kwana da kwanaki Abdu-Sabur bai kira kowaccensu ba, har suka fara irga satittika, har ya tafi wata guda shiru. A daddafe kowacce ta ke gurgurawa ta tafi makaranta, a dole suke daurewa suke yin karatu don babu yadda zasu yi, abin da ya kawo su kasar kenan, amma tabbas rashin Abdul- Sabur ba karamin gibi ba ne a rayuwarsu ta Malaysia ba. Sai su yi sati ba su hadu ba, haka sai su kwana uku ba su yiwa juna waya ba. Wani sa'in sai dai su hadu a titi, kowacce a cikin motarta su yiwa juna fitila su daga hannu. Shin ko shi wanda suke yi dominsa ya san suna yi? Watakila ma yana can ya mike kafa ya bude sabuwar rayuwarsa ya manta da ya taba saninsu a duniya. Ko kuwa har ya fi su shiga halin damuwa, saboda kewarsu? Oho! Allah ne kadai Ya sani. * Umaima ce ta ke juyi akan gadonta cikin dare tana tambayar kanta da kanta, wai shin me yake damunta ne ta damu haka da yawa don Abdul- Sabur ya tafi? A wanne dalili ta ke kasa cin abinci, barci da kuka mai hawaye? Ta fada a bayyane, yayin da ta yi zumbur ta tashi zaune, ta sauko daga kan gado da sauri ta shiga ban daki ta dauro alwalla ta zo ta fara sallah tana addu'a kada Allah Ya dasa mata son mutumin da ba zata taba samu ba a rayuwarta. Faduwa ce a zaune a falonta da sassafe, barcin safe ya kauracewa idanunta, yayin da shara ta gagari hannayenta saboda sanyin jiki. Babu abin da ta ke fata da bege irin ta gani sai Abdul-Sabur ko a waya ne. Ta shiga tantance sakamakon da zuciyarta ta ba ta. Hakika zuciyarta tana matukar kaunar Abdul-Sabur, son ba na wasa ba. ''To ashe na so in tafka kuskure da nake kokarin kakaba masa Umaimah, ni nake sonsa, NI NA FI CANCANTA da shi ba ita ba? Uncle Hamza ka cuce ni da ka kakaba masa *yarka kace ya aura, da ace ba shi da kowa tabbas Abdul-Sabur zai so ni kamar yadda na ke sonsa, don mun shaku. Ta jawo wayarta a sanyaye ta kira lambar Umaimah bugu daya ta bude ido daga baccin da ta dan fara yi. Fatanta ace Abdul-Sabur ne, sai ta ga Faduwa, murna ta koma ciki. Ta amsa dukkanninsu magana suke yi cikin rashin kuzari. ''Abdul-Sabur bai kira ki ba har yanzu Faduwa ta tambayi Umaimah. Ta ce ''Bai kira ni ba Anti Faduwa. Allah Ya sa dai lafiya. Faduwa ta ce, ''Insha Allah lafiya kalau Umaimah. Zai kira, mu kwantar da hankalinmu. Bayan sun ajiye waya sai kowannensu ya shiga tunanin ba dai abin da yake addabarsa na so shi yake addabar dan uwansa ba. Caf! Idan haka ta kasance a kwai matsala ke nan. Ko da yake wacce matsala ma, mutumin da babu wacce yake so a cikinsu ya riga ya sami matar da zai aura baturiya, aka bibiya ma ya manta da su. Haka su dukka suke tattaunawa a cikin zuciyoyinsu. Faduwa dai ta damu ta tantance wannan zargi da zuciyarta ta ke yi mata reto kulum. Ta yanke hukuncin gara ta sami Umaimah gar-da-gar su ji ra'ayin juna. Saboda ita yanzu saura wata guda kacal ta kammala karatunta don haka tana so a cikin satin nan ta kaura cikin makarantar kacokan don ta zana jarabawar karshe. Zai fi mata sauki ta kaura cikin makaranta ta daina ma hango gidan Abdul-Sabur, balle ta yi zaton zata hango shi. Tuni ita ma ta cike takardar tashi daga gidan har ta yi musu cikon kudinsu na haya don ta zarta shekara da watanni biyu. Ta ji tausayin Umaimah ga shi su dukka zasu watse su bar ta tasan ba zata ji dadin zama ba. Ita ma ta shiga jin nauyin fadawa Umaimah za ta tashi don kada ta shiga damuwa irin yadda Abdul-Sabur ya dinga larurar fada musu da zai tashi. Faduwa ce a kofar gidan Umaimah tana bugawa, a rashin sa'a ba ta same ta ba, don haka sai ta kira wayarta, Umaimah ta shaida mata tana makaranta sai karfe hudu zata dawo. Faduwa ta ce, idan ta taso ta zarce 'Sunway pyramid' inda suka saba zama da Abdul- Sabur. Umaimah ba ta tambaye ta me ysa ba, ta amsa mata da, ''to, zan je insha Allahu. Karfe biyar da rabi suka hadu a can Umaimah har ta riga Faduwa isowa dan a tasi ma ta je, ta kai motar wajen wankewa. Su ka rungumi juna don murna, saboda sun dade ba su haduba. Suna zama sai ma'aikata suka jero musu sunayen abinci da abin sha kala-kala. Faduwa a koshe ta ke saboda daga gida ta ke, Umaimah ce ta ke jin bakar yunwa. Don haka ta zabi abinci har kala biyu, shinkafa da rabin kaza sai jalof din taliya, kowanne ya zabi kalar lemon da yake so. Bayan an jere musu a kan tebur sai aka ajiye musu risitin kudi. Babu wacce ba ta tuno da AbdulSabur ba, me biya musu kudin duk abin da suka ci, sai yau suka san ashe abincin da suke ci mai tsada ne. Aka hau rigaye-rigayen biyan kudin a junansu daga karshe Faduwa ta yi sauri ta mikawa ma'aikacin kudi. Ta ce ''Nice babba, na karbi girman da Abdul-Sabir ya dauka a baya. Idan ina waje duk abin da kika ci ni zan biya miki, kanwata. Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''To na gode Antina. Umaimah tana cin abinci suna hira har ta koshi ta ajiye sauran sannan Faduwa ta gyara zama ta zare farin gilashin da yake fuskarta, ta dubi Umaimah. Ta ce, ''Umaimah, kin rame sosai, ba ki cika walwala ba, me yake damunki. Umaimah ta girgiza kai, ta ce,''Karatu ne saboda darasi ya kankama yanzu a makaranta, babu hutu sosai. Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Bayan wannan akwai kewar Abdul-Sabur ko? Umaimah ta dan yi murmushi ta ce, ''Hmm, ya za a yi? Haka sabo ya ke. Faduwa ta ce, ''Kun taba yin wata magana da Abdul-Sabur game da ni? Umaimah ta firgita da jin wannan tambaya, yayin da kanta ya juye. ''Ban fahimce ki ba? Umaimah ta fada a gigice. Faduwa ta ce, ''Mun yi maganarki da shi na zaci ya furta miki Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Bai furtamin komai ba, me ku ka ce? Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Tunda bai fada miki ba, bai dauki maganar da muhimmanci ba. Umaimah ta ce, ''Ni ma na yi maganarki da shi, ko ya taba fada miki? Faduwa ta gyara zama, ta ce, ''Don Allah fada min abin da ku ka ce, bai taba fadamin ba wallahi. Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''A'a, ba sai na fada miki ba. Da dai kin fada min naki ne sai in fadi nawa. Suka kwashe da dariya su dukkansu. Faduwa ta ce, ''Irin na yara ke nan, ki fara fada min sai in fada miki. Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta ce, ''Ce masa na yi ya aure ki, kun dace. Faduwa ta zabura ta dafe kirji ta ce, ''Ya aka yi tunaninmu ya zamto iri daya? Ni ma shawara na ba shi na ce ya aure ki. Umaimah ta rike baki don mamaki. Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Bai ba ni amsa ba har sai ranar da ya yi mana bankwana ya shaida min Uncle Hamza ya ba shi *yarsa ita zai aura. Umaimah ta yi shuru kamar mai takaici, can ta gyada kai, ta ce, ''Tabbas ni ma irin wannan amsar ya ba ni da na sake tuntubarsa da maganar a lokacin da ya rage saura awa guda jirginsu ya tashi. Suka yi tagumi su dukka biyun suna tunani da alamar damuwa a fuskokinsu. Har zuwa lokaci mai tsawo babu mai magana a cikinsu. Faduwa ta nisa sannan ta dago ido sama tana kallon silin rumfar da suke zaune a ciki. Tayi murmushi ta ce ''Ada ban sani ba sai yanzu na tantance ashe ni nake son Abdul- Sabur. Ashe ni da kaina, ni nafi son Abdul-Sabur, rashin sani yafi dare duhu, gashi ashe kema kin yi min sha'awarsa har nake kokarin turaki ni in koma baya. Umaimah tayi murmushi ta ce, ''Ina kyautata zaton abunda ya faru da ke shiya faru da ni. Na so in hada soyayyarku ashe ni ce mai sonsa sai yanzu nima zuciyata ta gama tantance min. Faduwa ta kura mata ido tana kallonta, itama Umaimah ta zuba mata ido suka dade suna kallon juna. Faduwa ta yi murmushi ta ce ''Ashe matsalarmu iri daya ce kenan? Yanzu ina mafita? Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai magana ta wuce Anti Faduwa, tunda Abdul-Sabur ya tafi bai sake waiwayar daya daga cikin mu ba, sannan ya riga ya zabi wacce yake so bai zabi daya daga cikinmu ba. Faduwa ta ce, ''Misali da ace zai dawo ya ce zai aure mu, mu dukka biyun zaki yarda mu zauna tare? Wannan magana ta Faduwa ta gigita Umaimah sannan ta bata mamaki matuka. Dan haka sai ta gagari bada amsa. Faduwa tayi *yar siririyar dariya ta ce, ''Ina tausayinki fiye da kaina duk da nasan nima abar a tausayawa ce shiyasa na hakura da son Abdul-Sabur ina ganin ba zan samu ba dan na yi masa girma. Na ga ke da shi zaku fi dacewa musamman yadda na ga ya damu da shiga harkarki. Na so in hada wannan soyayyar cikin rashin sani ashe kema kin min irin wanna sha'awar hakan ya jawo rudewar tunanin Abdul-Sabur ya yanke shawarar ya bar mu kawai mu dukka saboda baya so ya batawa kowannenmu rai. Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Nima na fara tunanin shine dalilinsa na tafiya ba waya. Anti Faduwa ina sonki, ina son ki sami miji na gari kamar Abdul-Sabur. Daga sanda muka hada miji daya daga lokacin zamu fara kishin junanmu komai na rashin dadi zai iya faruwa. Ina da kishi sosai musamman ma yanzu dana mallaki hankalin kaina kuma na sami zabin zuciyata Abdul-Sabur, ba kamar Abdul- Basi ba wanda aka hada ni da shi. Na san irin zafin kishin dana dandana a lokacin da naga Abdul-Basi da Zulayha suna son junansu, da kuma sanda naga Matawata da Ilah suna son junansu. Barci da abinci sai da ya gagare ni ci. Ba zan iya jera kishi da ke ba saboda duk Malaysia ba ni da tamkar ku. Ina nan akan baka ta ina son Abdul-Sabur amma ba zan iya aurensa ba saboda ke, na bar miki ki aure shi. Idan Abdul ya aureki kin yi dace da miji na gari, kuma in dai muna raye na yi miki alkawarin zan yi miki yaki har sai kin same shi da izinin Ubangiji. Faduwa ta yi murmushi yayin da idanunta suka cika da kwalla. Ta ce, ''Umaimah, ta yaya zaki taya ni yakin neman soyayyar Abdul alhali ya sami wacce zai aura, *yar uwarsa, gata baturiya? Umaimah tayi murmushi ta ce, ''Allah Ya halaktawa maza su auri mata biyu, uku ko hudu dan haka koya auri waccan zai iya aurenki. Faduwa ta matse dan guntun hawayen daya fara tsattsafowa daga idanuwanta. Ta ce ''Ko kina so ki taimaka in sami Abdul-Sabur ai sai mun gan shi a gabanmu amma kuma yanzu baya nan ya tafi baya ko waiwayarmu. Umaimah ta nisa ta ce, ''Na ji a jikina Abdul-Sabur zai dawo. Kuma duk inda muka kai ga yin kewarsa na tabbata ya fi mu kewar rashinmu saboda nasan halinsa na yawan jin tausayi da damuwa da mutane, sannan yana mayar da matsalar wani ta zama matsalarsa. Faduwa ta ce ''Lallai kin san halayen Abdul-Sabur kema, kamar yadda na san shi nima. Bari in fada miki abunda ba ki sani ba tun daga kan Sagir ban taba son wani da namiji a duniya ba sai yanzu dana hadu da Abdul shiyasa abun yake bani tsoro. Yanzu a rayuwa duk wanda nake so ya bi bayan Abdul-Sabur, shi ma kuma ya zo ya tafi kamar yadda Sagir ya tafi. A rayuwata ba zan taba samun abinda nake so ba kenan? Sai ta rushe da kuka mai tsanani. Kwalla ta cikawa Umaimah ido tana tausayin kanta amma ta fi jin tausayin Faduwa, ta shiga tunanin hanyar da zata bi ta share mata wannan hawayen da ya ke ta shatata.MAKWABTAKA 38 Sai ta dafa kafadar Faduwa tana girgizawa kamar me lallashin yaro karami. Ta ce, "Share hawayenki yayata, aure lokaci ne insha Allahu zaki yi aure kuma sai kin auri wanda kike so. Faduwa ta yi dariya ta sharce hawaye ta ce, "Haka ne Umaimah amma baza ki gane halin da nake ciki ba ne, kin ga ke kin taba yin aure har kin haifi da gashi har yanzu ke yarinya ce da kuruciyarki ko nan da shekaru goma kika kai baki yi aure ba, babu matsala sosai da sauran ki. Ni kuwa fa shekaruna suna ta tafiya babu aure, babu haihuwa, babu takamaimai mai sona. Astagfirullah, ba wai ina korafi ba ne akan nuna gajiyawaba, a'a nasan Allah Ya na sane da ni kuma na gode maSa a duk halin dana tsinci kaina. Faduwa da Umaimah suka surnano da hawaye masu radadi a lokaci guda saboda tsananin kunar da zuciyoyinsu suke yi, daga nan babu wanda ya sake cewa komai suka yunkura suka mike tsaye a lokaci guda, suka taka da kafa inda ake ajiye motoci suka shiga, Umaimah ce ke tuka motar Faduwa suka nufi gida. Faduwa ta dubi Umaimah ta ce, "Na dade ina son inyi miki sallama saboda bansan yadda zaki ji ba ne idan na fada miki da wuri kafin lokacin ya zo. Yanzu abin ya zo daf da faruwa dole in sanar miki. Irin yadda Abdul-Sabur yayi mana har nake ganin laifinsa da bai yi mana sallama da wuri ba, ashe abu ne mai nauyin fada dan zai bata zuciyar masoyi. Umaimah ta kalle ta duba na rashin fahimta. Faduwa ta yi dariya ta ce, "Saura wata daya mu kammala karatunmu, zamu fara jarabawar karshe shiyasa gobe nake son in kaura Hostel din cikin makaranta in yi jarabawa a nutse zai fi min kwanciyar hankali saboda rashin Abdul-Sabur ba kara min taba ni yayi ba har naji bana son zaman gida. Umaimah ta girgiza kai kawai ba tare da tasan abunda zata ce mata ba, abubuwa biyu ne suka soki zuciyarta. Na farko: tsananin son Abdul-Sabur amma ya zama haramiyarta ko ta gan shi ba yadda zata yi ta same shi. Na biyu: takaicin rashin Faduwa daga gidansu, zata zama ta rasa kowa, ma'ana ungulu zata koma gidanta na tsamiya. Irin rayuwar kadaicin data sha fama a baya. Hawaye mai zafi ya sirnano daga idanuwan Umaimah ta ce, "Allah Ya baki sa'ar cin jarabawa. Ya kaddara saduwarmu. Amin Da suka isa wajen ajiye motocin dake gidan sai suka yiwa juna sallama akan sai gobe da safe in Faduwa zata tafi zata shigo ta yi mata sallama. Umaimah ta shiga gidanta, Faduwa ma haka su dukka suna dandana kuna da zugin ciwon son Abdul-Sabur da ciwon rabuwa da juna. Haka kuwa aka yi, washegari da safe Faduwa da kawayenta da suka zo tafiya da ita sai suka shigo gidan Umaimah zata yi mata sallama, tana ganinsu ta rushe da kuka sai tausayinta ya kama su. Faduwa ma kuka take dan ta san tsananin kunar zucin da Umaimah zata ji a sanadiyyar zaman kadaicin da zata yi, suka taru suna lallashin Umaimah suna bata baki. Faduwa ta ce, "Ai gari daya muke, zamu dinga haduwa akai-akai, kina da mota ina da mota duk sanda muka yi niyyar ganin juna sai mu ziyarci juna. Kuma zamu hadu a ranar Graduation din mu. Umaimah ta sharce hawaye ta ce, ''Insha Allah zan zo, Allah Ya kaimu. Umaimah ta jawo mayafinta zata yi musu rakiya sai suka ce ta yi zamanta sun gama cika kaya a motoci, tafiya kawai za su yi har sun fitar da motocin kofar gida. Umaimah ta koma ta zauna akan kujera a sanyaye har yanzu bata daina zubar da hawaye ba, tana ji tana gani Faduwa ta tafi ta barta. Ta bude wundo tana leken su Faduwa har suka shude sannan ta sulale ta tsuguna a gaban wundo, sabon kuka ya kece mata. Babu abin da ta tuna sai sanda Abdul-Sabur ya nace a dole sai sun saba da ita, ya daure da duk irin wulakancin data dinga yi musu a jejjere. Allah Sarki! Suka ci gaba da lallashinta suna ta bin ta har sai da ta yarda ta saba dasu amma yau ga rabuwa ta raba dukka sun watse sun barta ita kadai kamar mayya a gidan, yanzu sai ta ci abinda zata ci. Tayi kuka harta godewa Allah sai da ta gaji da kanta ta daina ta hakura saboda babu mai lallashinta. Kwayar idanuwannan farare sol sai da suka yi jajawur kai ka ce garwashi ne aka rura, yayin da kanta ya daure da ciwo kamar zai tsage. Ta rarrafa ta sulale ta kwanta akan doguwar kujera sai shesshekar kuka take da ajiyar zuciya kamar yarinya *yar goye. Barci ya dauketa mai nauyi ta yini tana yi. * A daddafe take daurewa tana ci gaba da rayuwa tabbas ba karamin kokari take yi ba data ci gaba da zama a gidan, ji take tamkar ta tashi tabar gidan sai ta tuna ashe ba zaman gidan ba ne matsalarta wadanda ta saba da su ne ta rasa, su ne damuwarta ko ina ta koma ba ganinsu zata yi ba. "Me yasa na yarda na saba da su alhali sun san tafiya zasu yi su barni. Umaimah take fada a bayyane. Kusan kullum suna yin waya da Faduwa shi ne ma yasa take samun saukin damuwar da take ciki, amma da karatu ya yi karatu ko ta kira wayar Faduwa sai ta jita a kashe. Musamman da suka fara jarabawa Faduwa sai ta yi sati guda ba ta kunna wayarta ba. Umaimah ta rungumi kaddara a dole take sabawa da kanta zaman kadaici. Kullum sai ta kira *ya*yanta a waya su yi ta hira, shi ne kadai samun saukin kuncin da take ciki. Sannan kuma tsohonta da kaninta idan suka fita birni sai su kirata, idan ta ji muryasu suna cikin kosjin lafiya sai ta ji sanyi a ranta nan ma. "Haka Allah Ya so yi da ni, haka Ya ke son Ya ganni. Umaimah ta fada a lokacin da ta saka abinci a gaba ta kasa ci saboda kewar Abdul- Sabur. Hawaye mai zafi ya sirnano daga idanuwanta ta girgiza kai. Ta ce ''Raba zuciyata da son Abdul-Sabur ba karamin tashin hankali ba ne. Hakika ban taba son wani da namiji ba a duniya irin yadda naji son Abdul-Sabur. Allah Ya yayemin sonsa dan ya zama cuta a gare ni, ya tafi ya bar ni da ciwo kuma ko ya dawo ma kwalelena dan na yiwa Faduwa alkawari zan bar mata shi. Tabbas zan dauwama cikin kunci muddin zuciyata ta rasa Abdul-Sabur. Meye ma ya kai ni furta masa ya zo ya auri Faduwa, gashi nan mun yi biyu babu mu dukka. Dama ace sanda Faduwa ta fada masa cewar ya aure ni, ta fada min halin da ake cik da ba zan yi garajen yi masa maganar ya auri Faduwa ba. Na san shine kadai dalilin da yasa ya bar mu, mu dukka. * A lokacin da Umaimah take shirin fara jarabawar 2nd semester wanda ita ce zasu gama level two, shekara me zagayowa war haka zata gama karatunta na digiri gaba daya itama. Faduwa ce ta kirata a waya take sanar mata cewar bikin yaye su (Graduation ceremony) ranar litinin karfe goma na safe a 'Nilai Spring Hotel. Umamai ta taya ta murna game da yi mata alkawari zata ji insha Allah, amma ta tanadar mata Katina biyu zata zo da kawarta Aisha. A ranar litinin da misalin karfe tara da rabi na safe Umaimah Bello da kawarta Aisha Bingyal suka bayyana a kofar 'Spring Hotel' ba su shiga ba. A bakin Hotel din suka tsaya suna jiranta, dan Umaimah ta yi mata waya ta ce tana hanya. Ba'a dade ba sai gata nan a cikin motarta ta shigo farfajiyar Hotel din, ta wuce kai tsaye wajen da aka tanada dan ajiye motoci. Ta fito sanye da riga da hula wato graduation gown. Tayi kyau kuwa a cikin kayan, da saurinta wajen Umaimah ta nufa sai ta rungume ta cikin dumbin farin ciki. Sannan Umaimah ta gabatar da kawarta ga Faduwa wato Aisha Bingyal, sai suka gaisa. Faduwa ta mika musu Katina guda biyu kowa daidaya. Ashe duk yawanci jama'ar da suke tsaye bakin kofar Hotel din jama'ar Faduwa ne, tabbas jama'arta har sun fi karfin katinan da suke hannunta. Ta dinga bi tana gaggaisawa da bakinta daya bayan daya tana ta mimmika musu Katina, da Katinan hannunta suka kare sai ta ciro wayarta ta kira kawayenta ta roke su da su zo su sammata Katinansu na ta sun kare, ga sauran jama'a da yawa basu samu ba. Babu wanda yayi mamaki ko yaji haushi a cikin jama'ar da suka rasa kati, kowa ya san halinta na jama'a da yawa. Kawayenta suka shaida mata gasu nan zuwa suna kan hanya sun kusa karasowa zasu zo mata da katinansu da suka yi saura. Anan bakin kofar shiga Hotel su Umaimah suke tsaye har yanzu basu shigs ba duk da sun samu katinansu a hannu. Jama'a dai na ta duruwa shiga cikin hotel yayin da Umaimah take kyasawa Faduwa hotuna iri-iri. Wata murya ce ta kwalla kiran sunan Faduwa, nan danan sai kowa ya juya ya dubi in da kiran ya fito, wani tsalelen saurayi ne ya fito daga cikin tasi ya tunkaro in da suke tsaitsaye. Nan da nan suka ga Faduwa ta cika da dumbin mamaki marar misaltuwa, ta bude baki, ta dafe kirji da hannayenta biyu, sannan ta kame a tsaye, ba ta iya motsawa ba. Yana mai tsananin murna da fara'a cike a fuskarsa. Yana karasowa inda take sai ya mika mata hannu yana so su gaisa, sai tayi wuf ta kauce yayin da zazzafan hawaye ya fara kwaranyowa daga idanuwanta, nan da nan larabci ya barke daga bakunansu, su dukka biyun. Faduwa ta yi fushi fuskarta a murtike sai ta balbale shi da fada, tana masa nuni da hannu ya tafi bata son ganinsa, yayin da shi kuma yake bata hakuri kamar zai yi kuka. Daga karshe sai ya durkusa kasa gwiwoyinsa dukka biyu a durkushe a kasa, ya barke da kuka yana fadin. "Ma'alesh, Afuwan yah Faduwa. Hankalin kowa ya tashi a wurin musamman da suka ga kato yana kuka, kuma gashi a durkushe a kasa yana neman gafara. Umaimah ta rike Faduwa tana tambayarta a gigice cikin harshen Hausa "Me yake faruwa ne Anti Faduwa? Faduwa ta sharce hawaye magana take yi cikin kakkausar murya, amma cikin harshen turanci take bawa Umaimah amsa yadda kowa zaiji. Ta ce, "Umaimah wannan shine mutumin da ya fara jefa rayuwata cikin kunci da musiba. Shine wanda ya tozarta ni a lokacin da nake neman mafaka. Shi ne wanda yayi min tsirara a lokacin da nake neman sutura, yaki share min hawaye a lokacin da nake kwararar da hawaye "Waye kenan? Umaimah ta tambaya Faduwa ta matse hawaye ta nuna shi da hannu. Ta ce, "Wannan shine Sagir wanda nake baku labarinsa. Da yake jama'a da dama sun san labarinta da Sagir, bata iya boye zafi da radadin kunar da ta yi masa a baya kuma ya rabu da ita ya guje ta. Sagir ma ya dawo yana magana cikin harshen turanci dan kowa ya fahince shi kuma ya tausaya masa. Ya ce, "Ku taya ni rokar Faduwa ta saurare ni, ta ji abun da nake tafe dashi. Abun da ya faru a baya ta yafe min ba laifi na ba ne, takanas daga Cairo na zo wajenta dan na samu labarin yau ne ranar Graduation din ta, da magana mai muhimmanci na zo mata da ita. Faduwa, ban yaudare ki ba a baya, yanzu ma ban zo da niyyar yaudararki ba, kin fi kowa sanin abunda ya raba mu a baya. Bayan rabuwarmu dai-dai da sakon daya ban taba mantawa dake ba, ban taba yini guda ban tuna da ke ba. Ki ji tausayina Faduwa, ke ce farin cikin rayuwata.. Bai rufe baki ba sai kuka ya kece masa, jama'a da dama sai da suka yiwa Sagir da Faduwa hawaye saboda irin ruwan hawayen da yake shatata daga idanuwansu, musamman ma Umaimah wacce ta rushe da kuka daman kiris take jira daman ciwon rabuwa da nata masoyin ya addabe ta. Ahmad dan asalin kasar Malaysia ne, daya daga cikin abokan Faduwa shi ne yaje ya kama hannun Sagir, ya tasheshi tsaye gami da karkade masa kurar daya kwasa a jikinsa, yana mai yi masa albishir da ya kwantar da hankalinsa za su taya shi rokar Faduwa har sai ta saurare shi. Aka zagaye Faduwa ana bata hakuri, daga ta dubi Sagir sai ta sake barkewa da kuka daga dukkan alamu tana tuna tsiyar daya kulla mata a baya. A lokacin ne kawayenta da zasu kawo mata kati suka karaso da saurinsu kuma a gigice, sun zaci ba lafiya ba. Suna tambayar me yake faruwa, bayan an kora musu bayani sai suma suka shiga bawa Faduwa baki akan ta yi hakuri ta yafewa Sagir. Daga karshe dai aka rarrabawa kowa katinsa a hannu har da Sagir, sannan suka shiga ciki aka zazzauna aka fara gudanar da bikin yaye dalibai. Tabbas suma na su yayi kyau matuka amma bai kai na su Abdul-Sabur haduwa ba. Anci, an sha, an gyatse, aka yi ta hotuna ba adadi a lokacin da dalibai suke ta karbar satifiket din shaidar kammala karatunsu a hannu. Bayan karbar satifiket din Faduwa da kwana biyu sai ta kaura rikunin gidajen da aka tanada dan ma'aikatan asibitin, a nan sabon babban birnin Malaysia wato Putra Jaya Dankareren gida mai dauke da dakuna har guda uku da faluka biyu gami da bandakai guda hudu, aljannar duniya sunan gidan nan dan ya kayatu da kayana alatu. Kamar su gadaje na alfarma, kujeru, dinnin table, kafet, gass cooker, firij, injin wanki da dai sauransu. Duk abunda ake bukata a gida na amfani an zuba ko cukali bata shiga da shi ba daga ita sai akwatinan kayan sakawarta. Dadin-da-dawa aka hada mata da tsaleliyar mota dan haka waccan sai ta barwa wata kawarta kyauta. Aka zo aka shato mata makudan kudi duk wata za'a dinga bata a matsayin albashinta. Tabbas Faduwa ta zama babbar likitan mata (gyanae consultant) wacce aka ji da ita a wannan gari, shi yasa aka wadata mata kayan more rayuwa wanda zata samu nutsuwa wajen aiwatar da aiyukanta yadda ya kamata. Sai Faduwa ta ji kamar a mafarki ba a ido biyu ba saboda canjin rayuwa da ta samu nan da nan. Allahu akbar Allah mai iko, sarki mai kyauta a duniya. Dr. Faduwa Ahmad ke zaune a cikin katafaren ofishinta da yake cikin babban asibitin Putra Jaya. Ta jawo wayarta ta kira aminiyarta Umaimah Bello. Bugu daya Umaimah ta dauka cike da farin ciki ko gaisawa basu yi ba. Faduwa ta ce "Umaimah yaushe zaki zo Putra Jaya? Ki zo kiga yadda Allah Ya canjawa Dr. Faduwa rayuwarta a cikin lokaci kankani. Umaimah ta gyara zama dan ta ji dadin labarin sosai gami da jawo remote din talabijin ta rage maganar data cika mata kunne. Saboda tabbas labarin da Faduwa take bata ya sanya ta nishadi tana kuma taya ta murna. Faduwa ta lumshe ido ta ci gaba da cewa. "Ni Faduwa yanzu ni ce nake da katon gida, mota mai tsada, albashi mai tsoka, mai gadi, mai aiki a cikin gida da direba mai tuka ni. Haka nake da *yan hidimata daban a cikin ofishina na asibiti, kananan likitoci, manyan nurses, masu gadi duk sai sun duka suke gaishe ni. Addu'ar da Abdul-Sabur yayi min Allah Ya amsa daya ce insha Allah kafin ma na karbi satifiket dina a hannu zan sami nijin aure. ALHAMAKWABTAKA 39 Kinga kuwa haka Allah Ya yi ikonSa ya jeho min da sagir ba zato ba tsammani. Ya zo nema na ido rufe, maganar aure ya zo min da ita. Umaimah ta lumshe ido don farin ciki ta shafa kirji ta ce "Alhamdulillah, na taya ki murna Dr. Faduwa. Allah Ya tabbatar muku da alkhairi, Sagir din yana nan ko ya koma Cairo? Dr.Faduwa ta yi dariya ta ce, "Satinsa biyu a garin nan sannan ya tafi, ya sha koke-koke da magiya da tuba, dakyar na fara sauraransa na fuskanci abun da yake tafe da shi maganar aure ya zo min da ita kuma a cikin dan kankanin lokaci yake son ayi. Na ce masa ya je zan yi shawara ko zan iya aurensa koma ba zan iya ba. Umaimah ta zabura ta rike haba ta ce, "Dan Allah, da gaske? Ina mahaifiyarsa ko ta mutu? Faduwa ta girgiza kai ta ce, "Bata mutu ba tana nan a raye Allah ne Ya nuna mata ishara. Tana raye tana ji tana gani za ayi, da wuya ta yi wuya ma dakanta ta ce ya nemo ni ta amince ya aure ni. "Ikon Allah" Umaimah take ta fada tana maimaitawa cike da mamaki yayin da take jin dadin sauraran wannan labarai masu abun alajabi. Dr. Faduwa ta yi fari da ido ta kyalkyale da dariya ta ce, "Ai bala'i kala-kala ne ya saukar mata tun bayan data hanashi aure nan Allah ya dinga nuna mata ishara har ta gwammace da tun farko ni ta bari ya aura. Umaimah ta ce, "Tunda ki ka rabu bai yi aure ba? Faduwa ta ce, "Yayi aure-aure ma tunda mata uku ya aura daban daban suna rabuwa, a sanadiyyar rashin son su da yake da kuma azabtar da mahaifiyarsa da matan suke yi. Mata daya ce ta haifa masa *ya daya aka saka sunan mahaifiyarsa. In takaice miki har da wacce take zuwa gabanta suyi zage-zage. Dayar barauniya ce ta je ta sacewa mahaifiyarsa gwala-gwalanta tatas masu yawan gaske wadanda ta ke da su tun na gadon mahaifiyarta data rasu ta bar mata, dana aurenta, da wadanda danta ya dinga saya mata da yayi kudi, shi kuma ta yashe masa kudinsa kaf daya ajiye a gida ta gudu daman ba sonsa take yi ba, abun da ya kawota kenan. Jinin mahaifiyarsa yahau sosai dan takaici ta fadi rabin jiki ya shanye. Dakyar dai aka dinga yi mata magani sannan ta fara warkewa ta fara takawa da sanda. Da kanta ta tambaye shi wai a ina nake yanzu? Ya ce ina Malaysia banyi aure ba, ta ce ta amince ya zo ya aure ni. Umaimah, nasan basu kyauta min a baya ba amma ina son Sagir so na hakika kuma na tsakani da Allah, tun bani da komai shima bashi da komai muke son juna, ki duba ki ga tsawon shekarun da muka yi tare. Kuma ko alokacin da ya rabu da ni na san ba ra'ayinsa bane tilasta masa akayi. A rashin Sagir ne nake jin son wani amma da zan same shi babu zancen in so wani ma. Umaimah ta fada a cikin zuciyarta ta ce, "Ashe ni ce nake son Abdul-Sabur ba Faduwa ba, rashin Sagir ne yasa take son Abdul-Sabur daman. Ashe ma da ya aure ta idan Sagir ya dawo zata iya rabuwa da shi ta koma wajen Sagir. Ni kuwa yadda nake son Abdul-Sabur, Abdul-Basi da Ilah baza su sa in rabu da son sa ba. Faduwa ce ta katse tunanin da Umaimah ta ke yi ta ce, "Yanzu dai hira a waya ba zata yiwu dukka ba. Yaushe za ku yi hutu in dauke ki? Ki zo gidana kiyi sati biyu mu dade muna hira. Allah Ya sa lokacin bikinmu a cikin hutunku ne ki zo mu je Cairo ki ga yanda larabawa suke kashe kudi idan suna shagalin biki. Bikina ya zo dai dai da kudi ya zo, Sagir ma ya samu mukami babba a aikin dan sanda, yanzu haka baya tafiya shi kadai sai da *yan rakiya a bayansa yake yawo don haka yanzu kudi ya zauna masa. Yaya kika ga cashewa da rakashewa a wajen bikinmu? Kai! Inama Abdul- Sabur zai kira in gayyace shi bikin nan, na san idan na fada masa zai zo har Cairo. Umaimah ina miki addu'a da fatan ke ma Allah Ya fito miki da miji na gari kuma wanda zuciyarki ta ke so wato Abdul-Sabur. Umaimah ta yi murmushin karfin hali yayin da ta ji kamar ta barke da kuka ta dai daure ta amsawa Faduwa da amin sannan ta yi mata alkawarin zata je gidanta idan suka yi hutu. Su ka yiwa juna sallama da fatan alkhairi. Suna ajiye waya Umaimah ta fashe da kuka ta sulale ta kwanta tana fadin "wayyo Abdul-Sabur ina ma ka zo a lokacin da bana zaton zuwanka, da maganar aure kamar yadda Sagir ya zowa Faduwa. Ina sonka, na kasa daina sonka. Allah Ka agaje ni, Ka taimake ni in samu abunda zuciyata take so. * Haka kuwa aka yi da su Umaimah suka yi hutu Faduwa ta turo direbanta ya zo ya dauke ta da *yar akwatin kayanta ta yi shirin yin sati guda. Tabbas bata zaci daukakar da Faduwa ta ke fada ta kai haka ba, ta sha mamaki da ganin wannan daula ta gidan Faduwa. Suka hadu suka dinga murna da alama Faduwa ta fara koya mata wannan halayyarta ta hayaniya. Faduwa da me aikinta ce suke ta layin jerawa Umaimah abinci da abubuwan sha iri-iri a gabanta wanda suka dafa musamman dan ita a matsayin karrama babbar bakuwa. Umaimah ta ji dadi da ganin irin wannan karramawa ta yi godiya ta ci, ta sha har ta barshi. Daki na musamman Faduwa ta mallaka mata da bandakinsa ita kadai ta baje har ta gama kwanakin da zata yi ba tare da takurawa ba. Idan Faduwa ta tafi aiki da sassafe Umaimah sai ta ci gaba da mimmikewa tana shirgar baccinta babu abin da ya dame ta, sai ta yi ya isheta sanna ta farka. Wanka kawai take yi da kanta sannan ta fito falo ta iske mai aiki ta shirya mata abin karya kumallo iri-iri sai wanda take so ta ke ci tabar wanda bata so. Da daddare Faduwa take dawowa gida sannan su zauna zaman hira har zuwa karfe dayan dare koma fiye da haka. Umaimah tana kirgawa a iya wanda ta gani ban da wadanda bata nan, Sagir yakan kira Faduwa sama da sau ashirin a rana, bayan turo sakonni a jejjere duk bayan mintuna saboda so da kauna. Samun waje wai *yar caca da yado in ji masu iya magana. Faduwa sai share shi take tana ja masa aji tana cewa ya rage kiran nan saboda tana da aikin yi. Wani lokaci yana bawa mahaifiyarsa waya su gaisa da Faduwa, tsohuwa sai rawar jiki take har tana kiran Faduwa da ''Yah Faduwa Yah Habbitti. Ma'ana masoyiyarta. Tabbas ashe kiyayya tana iya komawa soyayya!!! Sagir da mahaifiyarsa sun fi so ayi bikin nan da watanni biyu, Faduwa ce ta ki amincewa dan ta san ba za'a bata hutu a cikin wannan kankanin lokaci ba a wajen aiki saboda bata dade da farawa ba amma akalla bayan watanni shida za'a bata hutu. Sai ta je Cairo ta shafe wata biyu ayi hidimomin biki a tsanake. Har Sagir ya bi dukka danginta ya gaggaishe su ya shaida musu sun gama daidaitawa da Faduwa zasu yi aure. Kowa ya yi murna da jin haka. Kwatsam sai dai Faduwa ta ji tsofaffi sun kira ta a waya suna surfa mata zagi wai ta gama shirya aurenta bata fada musu ba dan ba su suka haife ta ba. Ta yi musu bayani tana bada hakuri wasu su gamsu wasu su ki yarda sunyi fushi kenan. Kullum tana gargadin Sagir ya daina yadawa har sai zance ya kankama amma ina doki ya hana shi dainawa. A dole Faduwa ta shiga fadawa *yan uwa da kawayenta cewar zata yi aure. Da Umaimah ta lissafa lokacin da Faduwa ta ke so ta dauki hutu ayi bikin a lokacin sungama jarabawar 1st semester a level 3 dan haka ta kudiri niyyar zuwa biki har Cairo. Kudin jirgi ba matsala ba ne zata biyawa kanta ko Faduwa bata biya mata ba. Balle ma ta ji Faduwa ta jerowa Sagir sunayen kawayenta guda goma da zai dauki nauyin siyan tikitin zuwansu Cairo daga Malaysia, da sunan Umaimah a ciki. Umaimah da ta zo da shirin sati daya a gidan Faduwa sai gata ta zarce tayi sati biyu saboda zaman gidan Faduwa ya yi dadi, duk da haka ma dakyar Faduwa ta bar da zata tafi wai sai ta gama hutunta dukka a gidan, hutun kuwa har na tsawon watanni biyu ne. Umaimah taki saboda tana so ta dawo gidanta zata fi samun nutsuwa yin tilawar karatu. Gashi zasu shiga shekarar karshe dan haka karatu ya karu dole sai ta sake zagewa. Duk sanda Umaimah ta ji Faduwa da Sagir suna waya suna hirar so da kauna sai taji jikinta yayi sanyi saboda sai ta tuno nata masoyin wato Abdul-Sabur. Allah Sarki soyayya gamon jini ce!!! ** Rana bata karya sai dai uwar *ya taji kunya' inji masu iya magana. Watanni shida kamar kwana shida ne a wajen Allah, sai ga bikin Faduwa ya rage saura sati uku. A lokacin Faduwa da kawayenta suka shirya tafiya biki Cairo. Sai dai kash a lokacin Umaimah bata gama jarabawa ba saura sati guda ta gama, dan haka ba zata yiwu tare ba. Sai Faduwa ta damka mata tikitinta a hannu da zarar ta gama jarabawa sai ta hau jirgi ta je. Kullum akwai Egypt air wanda yake tasowa daga Malaysia kai tsaye zuwa Cairo. Bayan su Faduwa sun tafi da kwanaki goma sannan Umaimah ta yi shirinta a nutse, ta kira waya ta yiwa Hanif, Babansa, Baffanta, Kaninta da kwayenta su Aisha Bingyal sallama ta shaida musu cewar zata je Cairo bikin aminiyarta Faduwa, dukkansu sun yi amanna ta je saboda sun san yadda ta ke da Faduwa. Suka yi mata fatan alkhairi da fatan ta ji lafiya ta dawo lafiya. Bata dauki wasu kaya masu yawa ba sai dai ta dauki kudi masu yawa saboda ta sayi kaya a can, dan ta ji Faduwa tana cewa in ta zo har Dubai zasu shiga su yi kwanaki suyi siyayyar auren. Kudi masu gidan rana. Allah Ya bamu na halak. Sanda Umaimah zata baro Malaysia sai ta kira Faduwa a waya ta shaida mata gata nan a filin jirgi zasu taso, tafiyar awanni goma sha hudu ce a jirgi daga Malaysia zuwa Egypt, dan haka Umaimah ta zaunu har taji babu dadi duk da daman ta taba dandana nisan tafiyar shekaru biyu da rabi da suka shude, a lokacin da suka zo. Faduwa tana kirga awanni dan haka daidai sanda jirgin su Umaimah ya sauka a filin jirgin Cairo, Faduwa da angonta Sagir sun baiyana suna jiranta. Tana fitowa daga ciki sai ta gansu sai suka hautsine da murna suka rungume juna, suka ja jakarta zuwa inda suka ajiye motarsu. Umaimah ta iske Faduwa a cikin babban gida inda danginta kakaf suke, bangare-bangare, iyaye da kakanni, mata da maza, yara da *yan mata. Kyawawan gaske jajur-jajur da su, larabawan asali, tabbas da dangin Mahaifiyarta Faduwa tayi kama, basa jin wani yare a duniya wanda ya wuce larabci sai dan kadan da suka yi makaranta suke jin turanci. Umaimah ta ji tamkar a wata duniyar take ba'a wacce take ciki ba ada. Da ta tuno da danginta na ruga inda ta taso sai ta tabbatar da da kuma yanzu ba daya bane. Tabbas ta sami ci gaba a rayuwarta, Larabawan da take gani a hoto ko a talabijin yau ga su a gabanta tana cikinsu tsundum suna ta gaggaisawa. Ashe ba Faduwa ba ce kadai mai son mutane da fara'a duk danginta haka suke, lallai sun yi dace da hali na gari hade da shaida mai kyau. Hakika sunyi farin ciki da ganin Umaimah gata dukka ilahirin wadanda suka zo bikin nan ita kadaice bakar fata, sai itama ta saki jiki dasu kamar yadda taga sauran bakin da suka taho daga Malaysia sun ware sun zama *yan gida kuma *yan gari. Ana ta yawatawa da su Umaimah waje-waje na tarihin Egypt kasancewar Misra tana daya daga cikin manyan kasashe da suke da asali da dimbun kayan tarihi. A nan ne kasar da Annabi Musa (AS) ya yi rayuwarsa shida fir'auna. An kai su sun ga gawar fir'auna, gawar matansa da *yan fadarsa. Sun ga gawawwakin sarakuna daban daban da suka mulki Egypt shekaru dubunnai a baya. Sun ga kayayyakin da suka yi amfani da su kamar su: dutsen nika, duwatsu da aka fafe aka yi tukwane da su, sun je wannan tsaunin da ake kira Pyramid da dai sauransu. Sanda bikin ya rage kwanaki takwas Faduwa, Umaimah da kawayenta guda uku suka yi visar Dubai domin sake yin sayayyar da amarya da kawayenta suke bukata. Umaimah ta damu da taga wannan kasa da take yawan jin labarinta a cikin duniya 'United Arab Emarate' wato Dubai. Ta kagu da taga wannan kasa me dumbin arziki da yalwar kasuwanci wanda ta ji labarinta a cikin wani littafi mai farin jin wato' ADON DAWA'' Hakika taga Dubai sosai ta je Daira, ta ga Bur Dubai, ta tsallaka ruwan har take hange-hange ko Allah Zai sa taga gidan Kaltum da Mambela. Kwanansu hudu a Dubai suka sha yin siyayya iri-iri, Umaimah ta samu atamfofi super holland, shaddoji da materials kala-kala ta bayar a dinka mata, dinkin surfani masu kyawun gaske riga da zani, dogayen riguna da dan kwalayensu, ta sayi gayaleluwa, takalma da jakunkuna wadanda suka shiga da kayan. Suka koma Cairo inda aka fara gudanar da harkokin biki sai da aka shafe sati guda cur a na ta shagulgula. Party na zamani a manyan hotel na cikin garin Cairo aka dinga yi kala-kala sannan aka yi na gargajiya a wasu wuraren tarihi na kasar. Abun ya bawa su Umaimah sha'awa sosai, makadan larabawa kala-kala aka gayyato suka wake amarya da ango aka sha raye-raye. Kaya na alfarma amarya da ango suke ta canzawa masu kyalkyalin gaske, Umaimah da sauran kawayen amarya shigar kayan larabawa suka dinga yi kala-kala, irin dogayen rigunan nan masu dan kwali sannan aka jera wasu sulalla masu kyalli suna kara kacau-kacau, haka ake daura sulillikan a kugu da kafafuwa, an sha hotuna da bidiyo ba adadi. Tunda Allah Ya halicci Umaimah bata taba ganin bikin da ya kayatar da ita ba irin na Faduwa, ta shaki farin ciki irin wanda bazai misaltu ba. Har ta yi katarin haduwa da santalelen saurayi mai suna Kamal daya daga cikin abokan ango, ya ce yana sonta. Ya ji duk duniya bashi da matar da ya ji yana so ya aura sai Umaimah. Hidindimu iri-iri yake ta yi mata yana ta kashe mata makudan kudi daman kuma akwaisu dan har ya fi Sagir kudi, hamshakin dan kasuwa ne kuma dan gidan dan kasuwa, a wajen mahaifinsa ya gada. Ita dai baya gabanta so take ta gama biki ta juya kasar da ta fito wato Malaysia. Aka kai amarya wannan katafaren gidan na Sagir wanda ya gina da sunan Faduwa. Zamani ya canja dan haka ya rushe fiye da rabin gidan ya sake yi masa sabon fasali, ya zuba kaya irin na zamani a ciki. Al'adar larabawa mace daga ita sai kayan jikinta zata shiga gidan miji shine zai yi mata kayan gida gaba daya da kayan sakawa. Sauran tazurai SAI GOBE DA YARDAR ALLAH ZA KU JINI DA CI GABA. Dan AuntyMAKWABTAKA 41 Ranar talata za'ayi na makarantar su Umaimah a Hotel din da su Abdul-Sabur suka yi na su. Wato 'J.W Marriotte. Dan haka tun ranar lahadi iyayen yara da jami'an gwamnati suka iso birnin Malaysia suka sauka a manyan Hotels anan cikin 'Bukit bing tanga. Shirye-shirye su Umaimah suke yi tun kafin ranar ta zo bana wasa ba. Abubuwa sunyi mata yawa har bata samu ta je ta gaishe da Baban Hanif ba a inda ya sauka sai dai Hanif ya hadasu a waya sun gaisa. Ta shaida masa ita ce aka dorawa nauyin yin jawabi a wajen shiyasa take ta zuwa gwaji kullum a makaranta ta ke yini. Yayi farin ciki dajin haka kuma ya ce kada ta damu ta ci gaba da yin abun da yake gabanta. Ranar talata Daliban nan dukka guda dari, iyayen wadanda suka zo, da wakilan gwamna guda ashirin sune reras a zaune a gaba. Sai ka rantse a Nigeria suke kuma a Gombe yadda yaren fulatanci da Hausa suke tashi a wajen. Saboda a kungiyance suka shigo babu zancen sai su Umaimah sun raba musu katin gayyata. Wadannan *yan Nigeria na bangaren Gombe kadai, akwai *yan Nigeria daga garuruwa daban daban wadanda suma gwamnatinsu ta biya musu ko iyayensu. Wasu daga arewa, kudu yamma da gabancin Nigeria. Suma da iyayensu, sauran kuma fararen fata ne. Taro yayi taro, an cika sosai har ya fi na su Abdul-Sabur cika saboda daliban da suke digiri sun fi masu Master da PHD yawa. Sai da kowa ya hallara sannan aka bayar da sanarwar shigowar dalibai wadanda suka taru domin su wato su Umaimah Bello. Tana daga gaba-gaba sanye suke da riga da hular Graduation. Suka shigo a layi yayin da aka dinga daukarsu a hotuna, ana ta tafawa, har suka zo suka zazzauna a inda aka tanadar dominsu. Jawabai daga bakunan shugabannin kasar da shugannin makaranta, sai caraf aka kira sunan Umaimah Bello wacce zata zo tayi jawabin maraba da zuwan baki sannan tayi bayani game da wani cos data iya shi sosai fiye da sauran dalibai, shekaru biyar da suka shude ba'a taba samun dalibin daya ci A1 a kos din ba sai Umaimah. Bayan mai gabatarwa ya wasa ta, ya kodata, ya yaba da kwazonta, sai ya bukaci data fito ita da wani dan Indiya mai suna Muhammad Parwez, suka fito tare suka hau kan stage. Ihu da tafi kawai ake tayi yayin da ake daukar su a hotuna tamkar hasken walkiya, kai ka ce ruwan sama za'ayi hadari ne ya hado walkiya take ta haskawa. Ba bakake kadai ba ne suke daukarsu a hoto ba har da fararen fatar ma suna ta daukarsu. Babu wanda Umaimah take ganewa a wajen saboda idanuwa sun yi mata yawa amma hakan bai sa ta rude ba, saboda zama da Faduwa yasa ta goge wajen iya magana a gaban kowa. Tabbas Umaimah da Parwez sun burge kowa a wajen yadda suke turanci da kuma bayanai akan Computer Project Management' kai ka ce su suka kirkiro Computer soft were. Lallai sai yanzu ta tabbar da Faduwa ta iso wajen nan data ganta a gabanta, ta hau har kan stage tana daukarta a hotuna. Da suka kare sai suka koma suka zauna ana ta tafa musu. Baban Hanif ya ji dadi sosai, ya ji Umaima tamkar *yarsa ta cikinsa. Ya godewa Allah daya bashi damar taimakonta har ta sami ilimi, yarinya ashe mai hazaka ce a kunshe a cikin Rugage, da a haka rayuwarta zata kare a banza. Bai yi nadamar makudan kudin daya kashe mata ba. Sannan aka fara kiran dalibai da suka fito da sakamako mafi kyawu, da aka kira dalibi na farko Umaimah Bello ce ta biyu wacce ta fito da 1st class yayin da aka hautsine da murna ana ta tafawa, daukar hotuna har ya fi na dazu. Allahu Akbar sai Umaimah ta fashe da kukan dadi bayan data karbi sakamakonta a hannu, ta juyo ta kalli dubban jama'ar da suke taya ta murna, sai ta daga musu kwalin sama ta nuna musu. Ta tabbatar banda Allah babu wanda zai zabi talaka likis, *yar gidan talakawa, bakauyiya Ya bata wannan matsayi da daukaka. Banda Allah babu wanda zai zabe ta ita kadai daga cikin *yan kasarta ya ce ta fi kowa. Ta tuna Baffanta, Sabitunta, marigayiya Yafindonta da marigayiya Nasibarta yadda suka yi rayuwarsu a baya. Tabbas Allah Ya so ta da rahamarsa shiyasa ya raya ta dan Ya bata babbar kyauta, ko a mafarki bata taba zaton zata taka wannan matsayi ba. Babu abinda take fadi a fili da kuma a boye sai kiran ''Alhamdulillah'' Sai a lokacin ta kalli jama'ar da suke tururuwar daukanta a hotuna, ta gane Faduwa, ta gane Hanif, sannan da ta sake wurga ido gefenta sai ta hango wani mutum wanda ko a mafarki ta ganshi tabbas bacci zai katse saboda razana. Nan da nan tayi sauri ta kawar da idanuwanta daya gefen don bata son ta sake ganinsa, sai ta yi kicibus da wata fuska wacce take tunanin ko idanuwanta ne suka fara yi mata gezau. Taji zuciyarta ta harba bom! Kai kace tayar mota ce zata fashe. Ta sake bude ido ta dube su sosai cikin firgici da mamaki marar misaltuwa, su dinne dai mace da namiji wadanda bata taba zaton zata gansu a wannan waje ba kuma bata addu'a ta gansu din, dan basu rufa mata asiri ba a lokacin da take neman sutura, suma a hotuna suke daukarta basu daina ba har ta koma kujerarta ta zauna suma sannan suka koma suka zazzauna. Sun ga alamar ta razana da ganinsu kuma ba tayi farin ciki da ganinsu ba saboda tana ganinsu yanayinta ya canja, duk da kuka take yi daman amma tana dariya a cikin kukan, ganinsu yasa ta fashe da kukan takaici hade da fushi. Babu abunda yake yi mata zillo a zuciyarta sai sunayensu ta dinga fada tana maimaitawa. ''Abdul-Basi, Lamijo. Me ya kawo ku wajena? Me yasa zaku zo inda na ke? Me yasa zaku dawo cikin rayuwata, alhali rashin ku ne ya sa na tarki tafiya na rabu na bar *yan uwana da *ya*yana? Sai abubuwan da suka yi mata a baya na rashin kyautatawa suka yi ta dawo mata a jejjere, hawaye ya gagara tsayawa daga idanunta. Ana kiran dalibai suna tasowa a layi suna karbar takardar sakamakonsu. Aisha Bingyal ma ta karbo nata, dukkansu sun karba suna tsalle suna murna saboda kowa yayi kokari dan babu wanda bai fito da sakamako mai kyau ba daga cikin *yan garinsu. Sai dai Umaimah ce kadai baqa data sami 1st slass a wannan shekarar a makarantarsu. Tunda Umaimah ta ga Lamijo da Abdul-Basi bata sake fahimtar abubuwan da ake cewa ba a wajen. Hankalinta ya kada can yayi hanyar waje babu abunda ta fi so irin tabar wajen kada ma su sake haduwa. Ai kuwa babu damar fita dole sai angama sannan kowa zai tashi, ta kagu ma a gama dogayen jawaban nan da ake ta faman yi a tashi. Ta kasa kurbar ko ruwa balle ta figi naman kaji da abinci iri-iri da aka yi ta jerawa kowa a gabansa. An ci, an sha, kamar yadda aka yi a na su AbdulSabur. Da aka kammala taro sai kowa ya tashi ya nufi wajen *yan uwansa, tafiya Umaimah take tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki bata son ta karasa wajen *yan uwanta, badan mutuncin Baban Hanif ba da arcewa zata yi a neme ta a rasa sai dai su hadu a filin jirgi ranar da zasu tafi. Ta ci sa'a Faduwa ta zo ta figo hannunta daga cikin yuyar mutanen da suka baibaye ta suna tambayarta adireshinta da lambar wayarta. Ta cika da mamakin dalilin da yasa mutane suke tambayarta adireshi da lambar wayarta alhali duk fararen fata ne turawa, Indiyawa da kuma *yan Maley. Tabbas haka ake yi a turai wanda Allah Ya bawa wata baiwa ta daukaka zasu dinga tururuwar son yin mu'amala da shi. Abun burgewa ne a gansu da shi sun yi hoto ko ya rubuta sunansa a cikin wani abu nasu hankicin ko dan littafi. Da Faduwa ta figo hannun Umaimah bata dire ta a ko ina ba sai tsakiyar *yan Nigeria a gaban Hanif da Babansa, sai ta durkushe ta gaishe da Baban Hanif. Ya yi mata addu'a mai kyau ya yabe ta sosai kuma ya jinjina mata ya ce ta burge shi yana alfahari da ita. Lamijo ce a gefensa mowarsa kenan, da ita ya zo. Sai kallon Umaimah take kasa-kasa amma bata yi mata magana ba. Darajar mijinta ya sa Umaimah ta ambaci sunanta sannan ta gaishe ta, gami da tambayarta lafiyar Ummarta. ''Lafiya kalau''. Kawai Lamijo ke cewa. Umaimah ta san dai ba dan ita Lamijo ta zo ba saboda Hanif ta zo bata zaci zata ganta ba dan tana yi mata kallo irin na takaici da bakin ciki. Umaimah ta gaggauta barin wajen iyayen kawayenta da wakilan gwamna. Zubewa a kasa kawai take yi tana kwasar gaisuwa cikin ladabi da biyayya. Amsawa suke yi cikin kulawa da kaunarta game da jero mata addu'oin alkhairi. Daga karshe aka jeru aka dinga yin hotuna iri-iri ita da su. Abun mamaki sai ta nemi Abdul-Basi ta rasa a wurin, bata san inda ya kutsa ba, haka bata damu da ta gan shi ba daman. Da suka fito daga ciki sai aka taru a waje daya aka tsayar da shawarar kowa ya koma masaukinsa sai bayan kwanaki uku za'a hadu a 'Royal Bingtang Hotel' da karfe goma na safe in da makarantar su Hanif wato 'Legenda' za su gudanar da nasu bikin suma. Faduwa an sami abunda ake so, dan ita babban burinta shine ta ganta cikin *yan uwanta *yan Nigeria ta shiga cikinsu tayi ta yaren Hausa suna mamaki, sai ta hau basu labarin cewa itama *yar Nigeria ce Babanta dan Sokoto ne. Ta dinga hira da su kamar wacce ta shekara da saninsu, kowa ya ji yana sonta ya na so ya saba da ita har da musayar lambar waya suka dinga yi. Umaimah ta kagu su tafi ta san halin surutun Faduwa bata ki a kwana ana yi ba, dakyar ta jawo ta suka tafi. Umaimah ta bi Faduwa a motarta suka tafi dan bada motarta ta zo ba a motocin makaranta aka kawo su, Faduwa tana tuki ta juya ta dubi Umaimah wacce taga alamar damuwa a tattare da ita sai ta zungureta ta tambayeta. ''Lafiya? Yau ranar farin cikinki, kowacce zata yi fatan ta zama ke. Me yasa kika shiga damuwa? Na ga alamar bayan kukan murna kina cikin damuwa kuma. Umaimah ta sake barkewa da kuka, cikin shesshekar kuka take magana. Ta ce, ''Abdul-Basi da Lamijo na gani a wajen. Shine na ji duk raina ya baci, tunanin abubuwan da suka yi min a baya ya dawo min. Faduwa ta zabura ta ce, ''Haba dan Allah? Ai abun farin ciki ne ke a wajenki, ba shikenan ba sai ku shirya da aminiyarki, ta daina zarginki da mijinta ba. Ga mijinki uban danki shima ya dawo kuje a daura muku sabon aure ku yi zamanku. Umaimah ta girgiza kai ta ce ''Ba saboda ni Lamijo ta zo ba kuma na san bata zaci zata ganni ba anan, ko ma dai menene ya kawo ta bata yi min magana ba, albarkacin mijinta ni na gaishe ta. Abdul-Basi kuwa zai yiwu shi dan ni ya zo amma bana jin bayan gaisuwa zai ga fuskar yi min wata maganar. Babu zancen kome a tsakaninmu, dan ni ba zan iya zama da shi ba kwata-kwata, shima haka yanzu zai sha wahala idan ya ce zai zauna da ni. Saboda zaman da muka yi ada zama ne da yake yi mana mulki, son nuna isa, takama da son girma. Ya kira mu kauyawa, ya daka mana tsawa, duk abunda yake so dole shi za mu yi, ba mu da zabin kanmu. Haka yayi mana ni da Nasiba musamman ma ni da ba zabinsa ba kuma ya ganni yarinta sosai. Zamansa da Zulayha Senegal kuwa ita take sonsa, take binsa, take kashe masa kudinta, daga lokacin da ta gama gulmar ta daina yi masa biyayyar, bayan ta samu ta aure shi kenan, na san daga lokacin masifa ta kunnu. Ya fito mata da halinsa na rashin mutunci itama daman ta fi shi iyawa suka babe. Dr. Faduwa ba zan iya auren kowa ba yanzu a duniya in ba mai irin halin Abdul-Sabur ba. Halayensa sune: Hakuri, kulawa, damuwa da halin da mutum ya ke ciki, tattali, karamci, kyauta, tausayi, nasihohi masu taushi, ga lallausan lafazi, wasa da dariya, iya hira, amfani da hankalinsa baya taba damunka idan kana cikin fushi ya san yadda zai zauna da kai a duk yanayin da kake ciki. Faduwa ta dade tana kallonta sai ta kasa yin magana, can tayi ajiyar zuciya. Ta ce ''Ni yanzu ba gashi na hakura nayi aurena ba tunda nasan ba zan same shi ba. Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta ce ''Amma kina son Sagir sosai, kuma a rashinsa ne ma har Abdul-Sabur ya burgeki. Ni kuwa bana son Abdul-Basi tun farko ma, Abdul-Sabur na fara so a duniya, ban tantance ba har sai da na rasa shi, sannan na tabbatar duk duniya babu mai yimin kulawar da yake min alhali ada na tsane shi akan ya damu da ni. Faduwa ta ce, ''Gara ki auri wanda yake hannunki Umaimah, kada ki yi biyu babu. Umaimah ta yi *yar siririyar dariya ta ce, ''Anti Faduwa, daman sauri ne aure? Bana sauri ko yanzu da babu Abdul-Sabur babu dalilinsa, na tabbatar na rasa shi ba zan same shi ba, ba zan koma wajen Abdul-basi ba dan bashi da kirki. Ya kore ni a lokacin da nake tsananin son zama dashi, a lokacin da babu in da zan zauna inji sanyi sai gidansa. Sai yanzu da na zama mutum, nake da yadda zan yi sannan zai dawo min. Ba Abdul-Sabur nake jira ba amma ba zan auri Abdul-Basi ba. Zan ci gaba da yin addu'a Allah Ya turo min da miji na gari. Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Allah Ya turo miki Kamal kika ki shi, kullum ni da Sagir yake damu ya ce yana ta kiranki bakya amsawa. Ashe Umaimah ba za kiyiwa kanki fada ba ki auri dan larabawa ba, ga kyau ga kudi. Zai kula da ke sosai dan mazanmu suna da rikon aure. Umaimah ta yi dan murmushi ta ce, "Yi hakuri Antina, ba zan iya auren shi ba, kema kinsan dalili. Daidai lokacin Faduwa ta ja ta tsaya a kofar gidan Umaimah ta ce, "Kin san nayi nauyi yanzu bana yawo, saboda ke ne ma na fito yau. Ba zan iya hawa sama ba yanzu, zan je gidan kawata in jira direbana ya zo ya mayar da ni 'Putra Jaya' dan ba zan iya dogon tuki ba. Umaimah ta ce, ''Allah Ya sa ki haihu a cikin satin nan kafin na tafi in ga babyn ki. Faduwa tayi dariya ta ce, "Amin Umaimah, hakan zai iya faruwa saboda watan haihuwana ya kama. Umaimah ta bude kofar mota ta fito, ta yi mata godiya gami da yi mata fatan sauka lafiya. Tunda Umaimah ta shiga gidanta bata sake fitowa ba sai bayan kwanaki uku wato sai ranar bikin yaye su Hanif, Umaimah ta shirya tsaf, ta ce kwalliya ba ta kadan ba saboda ta ga yadda ake tsala ado idan za'aje bikin Graduation. Tana Allah.. Allah yasa taga dan Aunty a wajen ko xataji sanyi a xuciyar ta.. hmm. To Alhamdulillah. Allah yayi na cika alkawari.sai kuma gobe da yardar Allah xaku jini da cigaban kayattaccen, kasai taccen wannan littafin na Mashahuriyar marubucia wato Jamila Umar Tanko.. Naku a kullun mai kaunar nishadin ku. Abbas Abdulkadir Hada Hada (Marbass Dan Aunty). See translationMAKWABTAKA 42 Umaimah ta shirya tsaf, ta ce kwalliya ba ta kadan ba saboda ta ga yadda ake tsala ado idan za'aje bikin Graduation. Ta saka daya daga cikin tsala-tsalan shaddojinta data dinko daga Dubai. Ta dauki wayarta da mukullin motarta sai digital camera data rataya a wuyanta, ta nufi 'Royal bingtang Hotel' a cikin motarta, tana tafe tana sauraron wakarnan da take so ta mutumin Ghana 'Akuri Afomsa' wacce yake yi cikin yaren 'Asanti, wacce Abdul-Sabur ya bata. Babu abinda take tunawa sai Abdul-Sabur dinta ta tuna ranar da ya kaita Mantin wakar suka yi ta ji yana fassara mata. Ta ci karo da su Aysha Bingyal a bakin Hotel din, tana isowa kawayenta mata da maza suka yo kanta caa! Su na ta yabawa da tsananin kyawun da ta yi har suka ce basu gane ta ba da farko sai da tayi magana suka gane. Anya kuwa wannan kwalliya da Umaimah ta yi ba kwalele take yiwa Abdul-Basi ba? OHO! Wato a lokacin da ta nufo cikin Hotel din a cikin motarta sai da kowa ya zuba mata ido yana kallon halittar Ubangiji, sai kowa ya kagu da ya tantance ko wacece wannan, ashe Umaima Bello ce sai da ta fito aka shaidata. Umaimah ta dade a tsaye tana hira da kawayenta sai daga baya ta gane ashe Abdul- Basi ne a tsaye a gefensu shi da abokinsa Tanimu Wada. To ai ba dan ita su ka zo Malaysia ba saboda kanin Tanimu Wada suka zo wato Bashir Wada, ajinsu daya da Hanif. Tanimu ya karaso inda Umaimah take a tsaye ita da kawayenta cike da fara'arsa, yayin da itama ta juyo ta kalleshi tayi murmushi sai suka gaisa. "Shin ba ki gane mu ba ne? Tanimu ya tambaye ta. Sai ta cika da mamakin wannan tambaya tasa. Itama ta tambaye shin kamar yaya? "Naga da kika shigo kin kalle mu sanna kika watsar. Ta tabe baki ta kawar da kai dan taga alamar rai yake so ya bata mata. Ya nisa ya ce, "Ki zo ki gaishe shi mana. Ta dube shi duba irin na takaici ta kasa bashi amsa, har ya gaji da surutu ya yi mata sallama ya koma in da ya fito. Yana ta mamaki a zuciyarsa dan ya zaci Umaimar daya sani a da ce, da take zuwa ta durkushe a gaban abokan mijinta, ta kudindine a cikin hijabi ta shige lungu, ko me zata mika musu sai ta durkusa har kasa. Yanzu ya tantance ya gane akwai banbanci, dan shima Abdul- Basin daga dukkan alamu ya zaci irin ta da ce shiyasa yake daddakewa. Sai da ta juya taga Tanimu ya bace, acan ta hango shi yana bawa Abdul-Basi labarin abin da ya faru. Tanimu ya ce da abokinsa Abdul-Basi "Umaimar daka sani ada ba irin ta ba ce yanzu, akwai bambanci sosai. In har kana tunanin Umaimah zata zo ta gaishe ka yanzu to ba zata zo ba. Tunda biko ka zo to ka zo mu je kayi *yar murya ko Allah Zai sa ta amince maka dan na lura bata marmarin son zama da kai kuma. Abdul-Basi ya girgiza kai ya ce, "Haba nawa Umaimah take da za'a ce ni zan je in gaishe ta. Ai tana kallona bata zo ta gaishe ni ba tayaya ni zan je wajenta? Za ta kawo kanta ka kyale ta, guguwar digiri ne yake kwasar ta sai ta sake ta sannan, kasan *yan jami'a da ji da kai. Tanimu ya ce "a'a abokina ka cire girman kai ka zo mu gwada, ka san halin mace da jan aji balle ace ita aka yiwa laifi, kai ne fa me nema. Kai kake tsananin son ta dawo, kai kake kasa bacci dominta, kai kake hana ni sakat da hirarta, gara ka zo mu je tunda wuri. Abdul-Basi ya ce ba zai je ba sai dai ta zo ta gaishe shi. Girman kai rawanin tsiya ne! Su Umaimah ne suka fara shigowa ciki, suka sami waje mai kyau suka zauna daga gaba dan suga komai radau. Su Abdul-Basi ma suka shigo amma daga baya suka sami waje suka zauna suna hango su Umaimah da kwayenta, da lama babu abin da ya dameta, harkarta da kawayenta kadai take yi, suna ta wasa da dariya suna ta daukar junansu a hotuna. Da su Hanif suka shigo, sai aka hau tafi ana ta dasa musu hotuna kala-kala. Umaimah tabi Hanif tana dauka a hoto har saida ya zauna sannan ta dawo ta zauna itama. Babu abinda Lamijo da AbdulBasi suke yi sai mamakin Umaimah, suna kallon irin wannan kyau da tayi, da wayewa. Tabbas yanzu Umaimah tayi musu zarra tafi su komai, dan haka ta girmi wulakancinsu. Abunda ya fi tsayawa Lamijo a rai shine yadda taga Umaimah a Malaysia har tukin mota, ko ma dai menene a ransu basa gaban Umaimah ko kallon inda suke bata yi ba bayan farin ciki bata da wani abun yi. Taro yayi kyau, an rabawa su Hanif sakamakon jarabawarsu a hannu, sannan aka yi ta dogayen jawabi, aka ci, aka sha, sai aka watse. Sai kuma gobe war haka wani sabon bikin za'a yi na wadanda suka fita daga jami'ar 'Intii Nilai' su kuma a 'Radius International Hotel' za'ayi, tabbas gobe za'a sake wata sabuwar haduwar. Cancadi! Za'a kece raini da suturu da gwala-gwalai. Washe gari ma haka Umaimah Bello ta caba ado kai kace tarwada ce wacce take sheki, santsi, sulbi, yadda take karairaya idan tana takawa. Ta zama tamkar tauraruwa mafi haske a cikin *yan iwanta taurari wato 'Zahra'. To ko ita zata maye sunan kawarta wato 'MATAWATA? OHO! Ta hadu da Abdul-Basi da Lamijo a sanda ta je ta gaida Baban Hanif, basu yi mata magana ba dan sunga haduwar data yi ta wuce tunaninsu, da suka ganta sai suka kawar da kai gefe, sai ita ta je gare su ta duka ta gaishe su. Dan ta tuna kadan daga cikin irin halayyar Abdul-Sabur, idan ka gan shi ka share sai kaga shi ya zo yayi maka sallaman bawan Allah kenan me koyi da halin Manzon Allah (S.A.W). Ta gaggauta kaucewa daga bangarensu ta ta fi wajen masu kaunarta. Aka gudanar da biki yadda ya kamata kowa yana murna, da aka gama kowa ya watse. Daga nan ba'a sake yin bikin yaye dalibai ba sai da aka shafe kwanaki biyar, baki suka dinga cika dogayen motoci aka yi ta zagaye gari da su, suna kallon wuraren shakatawa iri-iri. Umaimah bata bi su ba saboda Lamijo da Abdul-Basi, babu yadda kawarta bata yi da ita ba akan ta zo su je su dinga raka su, ta ce ba zata je ba a gida zata zauna. Bata fito daga gida ba sai a ranar bikin yaye dalibai na jami'ar 'Subang Jaya' shi kuma a Capitol Kaula Lumpur Hotel ake yi. Me za'a fasa mutuwa ko tonar kabari? Inji masu iya magana. Ado ne dai Umaimah bata daina caba shi ba, kuma a dole sai ta zuba kyau, idan ta fito fili sai kowa ya kalle ta kuma sai ta burge, suturu ne Allah Ya hore mata kala-kala. Saura makaranta daya ce ta rage basu yi ba, su ba yanzu zasu yi ba saura wata guda, dan haka aka bawa dalibai hakuri dan ba zai yiwu a jira su ba saboda ba dole bane yin bikin. Abu mai muhimmanci dai shine karbar sakamako kuma za'a kawo musu har gida Nigeria idan ya kammala. Daliban makarantar basu ji dadi ba dai amma dole tasa suka hakura suka tarkato dan a taho gaba daya a tare. Dole ne a tafi sabida viser sati bibbiyu ce kacal aka bawa su Baban Hanif. **** gobe su Umaimah zasu tafi, tunda sanyin safiya ta dinga bin duk jama'ar data sani tana yi musu sallama, daga nan ta wuce gidan Faduwa a cikin motarta a inda zata yi mata sallama sannan kuma za'a sayi motarta, wata kawar Faduwa mai suna Salma ita ma *yar Egypt ce tana so zata saya. Bayan da aka gama cinikin mota, salma ta biya ta kudinta cif a hannu, da Dallar ta biya ta kamar yadda Umamai ta bukata dan ta canja gaba daya kudinta ya zama Dallar, saboda ta fi saukin canzuwa a nan gida Najeriya. Umaimah tana ji tana gani Salma ta haye motarta ta tafi, tana tsananin son motarta dole ce tasa ta rabu da ita. Faduwa ce ta hana ta tafiya da wuri, acan suka yini har zuwa yamma, Sagir ma ya zo daukar matarsa zai tafi da ita Cairo acan zata haihu koma a ce kacokan zata kaura ta bar Malaysia, har ta yi sallama da wajen aikinta suma saura kwanaki uku su tafi. Da Umaimah ta tashi tafiya direban Faduwa ne zai mayar da ita gida sai Faduwa da Sagir suka yi mata rakiya har bakin mota suka mika mata babbar leda a cike da alawowi iri-iri masu tsadar gaske suka ce ta kaiwa yaranta tsaraba, . Umaimah ta karba ta yi godiya sai kuma ta rushe da kuka ta rungume Faduwa itama tuni daman Faduwa ta fara kuka. Suka yi ta rusa kuka ba na wasa ba. Sagir ne ya dinga lallashinsu dakyar kukan ya tsagaita. Umaimah ta sharce hawaye ta ce, ''Ada na tsani MAKWABTAna, bana sonsu, nayi zaton dukka MAKWABTA haka suke basa bada hakkin MAKWABTAKA ashe ba haka ba ne. Anti Faduwa, daga kanki ke da Abdul-Sabur na fara son MAKWABTAna kuma daga yanzu duk inda zama ya hada ni da mutane zan zauna da MAKWABTAna lafiya. Kun yi jahadi da ku ka fahimtar da ni na san hakkin MAKWABTAKA. Allah Ya saka muku da gidan aljanna, ba zan manta da ku ba har abada. Faduwa ta sharce hawaye ta ce ''Ada na tsani *yan Najeriya saboda yadda *yan uwana suka musguna min, amma zamana da ke yasa na fahimci ashe wasunku kuna da kirki. Ke ce *yar Nijeriyar dana fara sani mai kamun kai, hankali, kunya da ladabi. Ke ce wacce kika sadaukar min da abunda kike so kika hakura da shi dan in samu. Ina jin ki a zuciyata tamkar kanwata uwa daya uba daya, saboda bani da kanwa ko daya a duniya.... Kuka ne ya ci karfin Faduwa ta kasa karasa bayananta suka sake kankame juna, ji suke kamar kar su rabu. Faduwa ta sake sharce hawaye ta juya ta dubi Sagir wanda shima sun saka shi hawaye dan tausayi duk da ba Hausa yake ji ba amma ya san kalaman rabuwa suke yi. Ta yi magana da turanci ta ce, ''Sagir ka taya ni cikawa Umaimah alkawarin da zan daukar mata idan na haifi mace zan saka mata suna Umaimah, saboda kauna da zaman amanar da muka yi. Sagir ya gyada kai ya ce, ''Na amince miki Yah Habitti. Umaimah ta fashe da kukam farin ciki ta ce ''Na gode muku, nima insha Allah kafin in bar duniya inda rabon nayi aure na haihu zan saka sunanki. Zasu sake kankame juna su sake bude wani sabon shafin kukan sai Sagir ya janya Faduwa ya ce Umaimah ta shiga mota ta tafi, kukan ya isa haka zasu sakawa kansu ciwon kai. Basu daina dagawa juna hannu ba har sai da suka yi nisa suka daina hango juna. Allah Sarki sabo, turken wawa. Ko da rabon a sake haduwa ko kuwa rabuwar ce har abada? Allah ne kadai Ya sani. Amma dai sun yiwa juna alkawari zasu ziyarci juna Egypt da Nigeria ba nisa sosai. *** Ba Umaimah kadai ce me himilin kaya ba dalibai da dama sun lodi kaya da yawa musamman ma matan. Ai kuwa ansha dogon turanci a tsakanin wakilan Gwamna da ma'aikatan Egypt air saboda himilin kayan da dalibai suka loda yayi yawa ainun. Duk da alafarma da rangwamen da suka yarda suka yi amma sai da aka biya makudan kudin awo. Su Umaimah suna gefe kamar ba akan kayansu ake hayaniya ba, suka yi lukus a gefe. Ka ga *yan gatan gwamnati, sai da aka gama komai aka miko musu 'tag label' din kayansu, suka wuce abinsu zuwa cikin jirgi, daga su sai *yar jakarsu ta ratayawa da jakar Laptop dinsu. Umaimah Bello da kawarta Aisha Bingyal ne suka shigo cikin jirgi sanye da riga da wando (jeans) sai suka dora bakar abaya akai, zo kaga farar fata a cikin bakin kaya yadda suka haska. Kananan hijabai ruwan madara masu kwalliyar fulawa baka suka dora akansu, suka saka takalmi masu tsini da kalarsa ruwan madara, suka dora farin gilasai a idanuwansu. Rigiji-gafji! Wani kaya sai amale. Kowa sai da ya dago ido ya dube su, dan su ne suka shigo daga karshe kasancewar sun bata lokaci a wajen awo aka dade ana ta hayaniya akan kayansu, sun yi kyau sosai, sai suka zama tamkar *yan tagwaye masu kama daya, kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sunyi kama da masu digiri digirgir. Su na tafe suna hirarsu suna ta tuntsira dariya har suka shigo ciki, suka fara duba inda lambar kujerarsu take kamar yadda take a rubuce a jikin 'Bording pass' din kowanne fasinja. Dama tsakiyar jirgin lambarsu take dan haka suka wurwuce mutane da yawa kafin su isa mazauninsu. Tunda suka shigo suke aikin gaishe da iyayen kawayensu irin su Baban Hanif dan su tuni sun shisshigo. Tana juyawa gefenta Abdul-Basi da Tanimu ta gani suna zazzaune, sai ta duka ta gaishe su cikin girmamawa, nan da nan suka yi caraf suka amsa abunka da daman jira suke. Ta gaggauta wuce zuwa can baya inda kujerunsa suke tana tafe tana mamakin irin wannan isa da girman kai na AbdulBasi, ta shiga addu'a kada Allah Ya sa *ya*yanta su biyo halinsa. Sai yanzu ta sake curewa da jinjinawa Abdul-Sabur, sai da ya shekara yana bin ta yana yi mata magana tana share shi bai taba gajiya ba ya daina. ''Na yi rashin masoyi Abdul-Sabur. Ta fada a zuciyarta. Gaba daya *yan tawagar su Umaimah su dari biyu ne, jirgi kuwa mai cin mutane dari biyar ne dan haka aka batse da farar fata masu zuwa Cairo su dari uku. Bayan kowa ya zauna, sai aka kwararo addu'ar nan ta tafiya. Jirgi ya zabura ya tashi sama ya luma cikin gajimare yayin da Umaimah ta runtse idanuwanta, babu wanda take hangowa daga Abdul-Sabur sai Faduwa, hawaye mai zafi ya kwararo mata. Ta sake tunowa da kawayenta *yan Malaysia da *yan India, da malamanta da suka saba sun rabu da wuya su sake ganin juna kuma har abada. Ta dade tana ta kuka bata daina ba duk da lallashin da Aisha ta dinga yi mata dakyar ta daina. Tana cike da farin ciki dan zata je taga Baffanta, *ya*yanta da *yan uwanta amma ta san yanzu zata hadu da ce-ce-ku-ce da kananan maganganu, da masu shiga sharo ba shanu, masu fada ba'a tambayesu ba. Africa kenan sabanin nan da ba ruwan wani da wani. Sai wata rana Malaysia!!! CAIRO Tafiyar kwanaki biyu zasu yi sai da suka shafe awanni goma sha hudu a sama sannan suka isa Cairo da misalin karfe shida na asuba agogon Cairo, sannan aka kwashe su a motoci aka rarraba su a Hotels. Saboda yawansu ma a Hotel daban-daban aka rarrabasu, dan sai sun shafe awanni goma sha biyu sannan zasu taho Nigeria. Duk daki daya mutane biyu aka rarraba, Umaimah da kawarta Aisha dakinsu daya, bata ga Abdul-Basi ba daman ba nemansa take ba. Bata ga Lamijo da mijinta ba amma taga Hanif shi da abokinsa Bashir Wada, a kusa da dakinsu ma suke. Burinta kawai ta shiga dakin ta kwanta saboda gajiya da bacci, sai bayan data yi bacci ya ishe ta sannan suka yi wanka da salloli suka sauko suka ci abinci. Saida yamma karfe biyar aka kawo motoci aka kwashe su zuwa jirgi da karfe shida na yamma jirgi ya tashi zuwa Abuja, tafiyar ba nisa sosai awanni uku da rabi ne kacal, suka isa Abuja da karfe goma na dare a birni tarayya ta yi musu. . Plz in barar addu,ar ku bani da lapy Ngd MAKWABTAKA 43 ABUJA, NIGERIA Suka ci sa'a kuwa suka sauka da kayansu gaba daya kafin su iso dogayen motocin gidan gwamnatin garinsu sun zo sun jeru reras suna jiransu a filin jirgi, suna fitowa sai suka duru a ciki su da kayansu a ka zarce dasu katafaren Hotel. Aka rarraba su mata dakunansu daban, maza ma dakunansu daban, mutane uku-uku. Daliban ne kadai aka kai wannan Hotel din sauran kowa ya tafi ya kama nasa da kudinsa masu gidan *yan uwa ko abokai suka tafi can. Ta san Abdul-Basi gidan Yayansa ya tafi wato Abdul-Badi. Washi gari da sanyin safiya suka shirya suka shiga motocin suka nufi garinsu Gombe, nan danan suka isa, abinka da motoci masu lafiya. GOMBE, NIGERIA Suna shiga garin sai suka gan shi kamar anyi gobara haka mutanen garin duk sun yi baki-kirin, amma ba baki suka yi ba haka garin ba ayi gobara ba, illa sun saba ganin jajayen fata da dogayen gininnika kamar gidajen tangaran. Gidan Gwamna aka zarce da su sai suka iske gidan a cike da masu taryarsu, Umaimah bata damu da duba nata *yan uwan ba ta san babu mai zuwa mata duk da dai su Baffa sun san tana tafe amma ba suyi da ita za su zo ba. Gagarumar liyafa aka shirya musu a gidan Gwamna, aka yi dafe-dafe iri-iri aka zazzauna akan kujeru da suke babban dakin taron da yake gidan gwamnati, tare da mai girma Gwamna aka ci. Da aka ci, aka sha, sai ya yi musu jawabin maraba gami da yaba musu bisa kokarin cin jarabawa da kowannensu yayi sannan ya gode musu da cika masa alkawarin da suka yi suka je can basu yi wani abu na rashin da'a ba. Dalibai uku maza biyu, mace daya suka tashi suka yiwa mai girma gwamna godiya bisa dawainiyar da ya sha yi da su har suka kammala karatunsu na tsawon shekara uku bai taba gajiyawa ba. Daga karshe aka umarci kowannensu ya dauki kayansa ya tafi gida, za'a neme su nan da wata daya da rabi zasu tafi bautar kasa. Abuja za su yi bautar kasarsu dan haka acan zasu karbo takardunsu wato 'Call up letter. Umaimah Bello ce ke tsaye a farfajiyar gidan gwamnati tana kallon kawayenta da abokananta suna ta tururuwar shiga cikin tsala-tsalan motocin iyayensu. Allah Sarki, ita kuwa bata da kowa da ya zo daukar ta a mota, ta na tsaye tana ta zulumin yadda zata yi. Shawara take ko dai ta fita ta je ta samo tasi ta zo ta kwashi kayan akaita har Dugge, amma anya kuwa jami'an tsaro zasu bar dan tasi ya shigo wannan gida? Gashi kayan kuma ba zasu dauku ba da sai ta kinkima zuwa bakin titi ta hau mota amma saboda yawansu da nauyinsu ba zata iya ba. Tana cikin wannan tunani sai ta ga Hanif a gabanta. Ya ce "Ke muke neme tun dazu, Baba ya ce ki zo ki shiga mota mu tafi gidanmu ki kwana gobe sai a kai ki gida. Sai ta ji gabanta ya fadi nan da nan muryarta ta dauki rawa dan ba zata iya zuwa gidan Lamijo ta kwana ba har abada. Ta ce, "A'a na gode, yanzu nake so in tafi gida, Hanif ka taya ni yiwa Baba bayani dan ya fahimce ni, ba kin bin ku nayi ba. Hanif ya ce, "To ina motar da zata kai ki gida? Umaimah ta ce, "Yanzu nake tunanin ko bakin titi zan fita in nemo tasi? Ko kuma kayan zan baka ka tafi min da shi ni kuma sai in tafi tasha in dauko mota in zo gidanku in dauka amma gidanku ba gidan Lamijo ba zaka kai min dan gidanku ya fi kusa da tasha. Hanif ya ce, ''Nifa bana so in ji kina maganar motar haya, ke fa babbar yarinya ce. Kina da mota a Malaysia taki ta kanki a kasar ku a ganki a motar haya. Ki zo mu je gidanmu kawai ki kwana gobe da wuri zan tashi in kai ki Dugge da kaina. Umaimah, ta girgiza kai alamar bata amince ba, wani takaici ya rufe ta data ji wannan bayanai na Hanif, kai da jin bayanan Hanif ka san da sauran kuruciya a kansa, da kuma gata da yayi masa yawa bai san wahala ba, shi dai magiya yake yi mata. Tabbas tun yanzu Umaimah ta san ta fara tozarta a kasarsu. Kamar daga sama ta ji wata murya ta kira sunanta, muryar ta yi mata kama da muryar data sani tana kuma matukar kewar mai muryar, amma bata zaton bayyannar mai muryar a halin yanzu kuma adaidai wannan lokaci. Ta waiga da sauri ta dubi inda sautin yake fitowa tabbas mai muryar da take tunani ne. Baffanta ta gani a tsaye, Sabitu da kuma Ilah cikin yagulallun rigunansu, kai kace daga bakin kura aka kwato kayan jikinsu, basu yage ba amma sun kode sunyi yaushi. Daman ta san za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya, duk da ta aiko musu da makudan kudi ta san ba zasu saki jiki su ci ba, boyewa zasu yi su cigaba da wahala daman ita suka saba yi. Ta ji hankalinta yayi matukar tashi data gansu cikin wannan hali dan ma wai sun yi wanka sun caba ado zasu shigo birni taryar babbar bakuwa daga kasar waje. Cike da mamaki gami da farin ciki mabayyani ta ruga da sauri kai tsaye wajen Baffanta ta nufa ta kankame shi su dukka suna kukan murna, ta rike hannun Sabitu shima hawayen murna yake, sannan ta juya ta kalli Ilah duk ya tsufa saboda talauci ga *ya*ya, ga masifar Matawata. A sanyaye ta ambaci sunansa ''Hamma Ilah, ina wuni. Ya yi murmushin dadi, yayi caraf cike da murnar ganin amaryarsa ya ce, ''Lafiya Umaimah, sannu da dawowa. Sai suka ji ana ta matsa 'horn' din mota a bayansu nan da nan suka waiwaya, mota dankareriya kirar BENZA suka sake tabbatarwa da su mai motar yake, amma ba su gane ko waye ba saboda gilashin motar a rufe kuma bakin-kirin basa ganin cikin motar. Ko daya sauke gilashin motar, ya zare bakin gilashin da yake fuskarsa sai suka shaida shi. Abdul-Basi ne ya bayyana muraran a gaban su. Ta dukar da kai kasa ya ce, ''Baffa, ina wuni. Ku shigo mota in kai ku gida. Baffa, Sabitu da Ilah sai suka zubawa Umaimah ido suna jiran su ji abunda zata ce. Ta kuwa sha kunu tana harararsa zuciyarta cike da tsantsar tsanarsa, ta cije baki ta juya ta dubi Baffa ta girgiza kai. Ta ce ''Kada ku shiga motarsa tunda ba shi ya kawo ku ba. Aka yi carko-carko na kallon-kallo tsakanin Umaima da Abdul-Basi daga dukkan alamu yana mamaki yadda Umaimah ta waye har ta fara yi masa musu. Sai ya sauke gilashin kujerun bayan motarsa, sai ga Babangida da Bilal sun bayyana. Su ma aka hau kallon-kallo da su da su Umaimah, da farko yaran basu shaida ta ba. Sai ta ji wani farin ciki ya lullubeta, ta runtse ido dan ta tabbatar ba'a mafarki take ganinsu ba sannan ta bude ido ta tabbata zahiri take ba'a mafarki ba, ta yi murmushi ta ambaci sunayen yaran. ''Baku gane Anti Umaimah ta Malaysia, ba na fada muku a waya nace zan zo ba? Sai suka gasgata ita ce suka fara tafa hannu da ihu suna tsalle, yayin da suka yunkura zasu bude kofa su rugo wajenta, Babansu ya dakatar da su. Ya ce ''Ku koma ku zauna zata zo. Yana so ya nuna mata idan ta isa da Baffanta shima ya isa da *ya*yansa. Aka jima ana kallonkallon, har yanzu su Umaimah na tsaye a inda suke haka Abdul-Basi da *ya*yanta suna zaune a cikin mota. Sai fullanci ya hargitse tsakanin Baffa da Sabitu suna rokarta data manta da abubuwan da yayi mata a baya ta dubi albarkacin yara ta yafe masa. Wanne miji take da shi yanzu a duniya wanda ya wuce shi, mutumin da ya rike ta tun tana karama, ya dauki nauyin karatunta har ta zama mutum. Ba dan tubalin karatu (firamare da sakandire) daya bata ba ada a ina za ta sami ilimin da har zata sami damar tafiya kasar waje ta yi karatu? Ita kuma tana fada musu irin wulakanci da korar karen da yayi mata a lokacin daya tabbatar bata da kowa din sai shi. Baffa yana hawaye a zuciye ya jawo hannunta ya tura ta cikin mota kusa da *ya*yanta ta rushe da kuka ta rungume su. Baffa ya shiga kusa da Umaimah ya zauna, Sabitu ya zauna kusa da Baffa, dukkansu a gidan baya, yayin da Ilah ya ja burki ya tsaya cak. Baffa ya leko ta windo ya ce da Ilah ya shiga gaban mota ya zauna. Ilah ya ce su tafi kawai ba zai shiga motar ba zai taho a motar haya. Da alama dai kishi ne ya ke zakularsa, wannan shi ake kira da 'ta leko ta koma kenan' har da ya fara murna Umaimarsa ta rabu da Abdu-Basi zasu daidaita gashi ya dawo, har su Baffa sun fara goyon bayansa. Aka hau galle-gallan harara a tsakanin Ilah da Abdul-Basi yayin da Umaimah ke tsakiya tana kallon ikon Allah da mamaki marar adadi. Kishi kumallom maza!!! Baffa dai har yanzu magiya yake yiwa Ilah don ya shigo motar, ya ce in dai ka dauke ni uba kamar yadda ka dauki Jani to ka shiga mu tafi. Umaimah ta ce, ''Hamma Ilah, yi hakuri ka shiga mu tafi kada ka damu. Nan da nan ya ji sanyi a ransa. Sai yayi amanna da maganarsu, har da tafiyar takama yake yi saboda ko a yanzu Umaimah ta gwada wanda ta fi so a cikinsu shi ta zaba, ya zo ya bude gidan gaba ya zauna basu daina gallawa juna harara ba har yanzu. ''A ina kayanki suke? Abdul-Basi ya tambayi Umaimah a gadarance ba tare da ya juyo ya kalle ta ba. Ta turo baki tayi masa nuni da hannu ba tare da tayi masa magana ba, ya ja mota ya tafi kusa da kayan. Da yake babbar mota ce tana da katon but yana daga zaune bai fita ba sai ya bude but ya kira wasu kartai ma'aikatan gidan gwamna masu jidar kaya a cikin but. Nan da nan suka dinga cicciba suna sakawa har suka gama, ya zaro naira dubu ya basu. Abdul-Basi ya yi addu'ar tafiya, ya zaro bakin gilashi daga aljihunsa ya saka, ya daga gilashin windunan mota sama, ya kunna Ac gami da sautin kida a hankali, ya fisgi mota ya kama hanyar Dugge. Gudu yake ba kakkautawa, bai sake magana ba kuma babu mai yin magana a cikin motar, sai muryar Babangida da Bilal ne ke tashi, suna ta yiwa Umaimah hira kala-kala, tana biye musu suna hira amma gaba daya hankalinta a tashe yake. Ganin Abdul-Basi da tayi ya ruguza mata lissafi gaba daya amma ta ji dadi ya kawo mata *ya*yanta, tun daga cikin mota ta fara zakulo musu tsarabarsu ta alawoyi masu dadi da tsada sai suka ji sun kara sonta dan suna kaular alewa sosai. Suna shiga Dugge sai Umaimah taga yara da samarin garin kacokan sun firfito waje suna daga mata hannu daga dukkan alamu taryarta kowa ya fito yi sai farin ciki ya rufe ta, tausayinsu ya kamata saboda ta gansu har yanzu a gidan jiya babu wani ci gaba a tare da su. Sai taga garinsu ya zama tamkar wanda aka cisu a da yaki, bututu da su a cikin yashi. Amma bada yaki aka ci garin ba tsabar talauci ne daman can ma haka suke, dan ta saba ganin titina dodar da kwalta, fitulu da dogayen gininnika, a garin fararen fata garau-garau. Ta dinga addu'a a zuciyarta Allah Ya taimaki Africa da garinsu Dugge, su sami ci gaba suma su ji yadda a ke ji a kasashen da suka ci gaba. Amin. Ta sauke gilashin kasa ta leko da kanta tana ta daga musu hannu, sai yanzu suka hangota dan da duhun gilas yasa basa ganin komai suna ganinta sai murna ta karu. Yara suka biyo motar a guje har kofar gidansu suna fadin ''ga Umaimah daga turai'' tana fitowa daga mota sai suka ganta ta juye jar fata ta zama tamkar balarabiya jajawur a cikin bakar abaya, ta yi kyau, ta yi kiba, sai kamshin turare take. A haka ta dinga rungumar yara kaca-kaca da su, duk wacce ta ci sa'a Umaimah ta taba ta sai ta ji tamkar an yi mata gafara dan ta sami babban rabo a duniya, sai ka ji suna cewa kamshinta ya shafe ni, su dinga shinshina kayan su. Mata suka dinga leke ta saman katangu ko zana suna kallon Umaimah, sai rike baki ake saboda mamakin wannan canjawa da ta yi. Har sai da ta gaji da gaisawa da jama'a ta shiga gida, yuu! Kungiya guda aka bita ciki. Nene da Inna da murna suka fito suka rungume Umaimah tabbas yau sun san ba karamar daukaka Allah Ya yi musu ba da Ya sa suka auri Baffa wanda ya haifi wannan galleleliyar yarinya Umaimah, ba karamin abun alfahari ba ne a ga Umaiman ta wuce kowanne gida ta shigo gidan da suke. Subhan Allah, sai Umaimah taga gidansu tamkar turken shanu, dakinta tamkar kejin kaji wai dan ma saboda zuwanta Baffa yasa an yabe shi da jar kasa, an share, an shinfida sabuwar leda da sabuwar katifa karama, ga sabon labule. Su Sabitu suka dinga jidar manyan jakunkunanta suna saka mata a daki. Babangida da Bilal suka rirrike Umaimah wai ba za su shiga dakin nan ba itama ba zata shiga ba sai dai ta zo su tafi gidansu, dadi ya rufe Abdul-Basi yadda zata ji zuciyarta ta karaya saboda yara ta koma gidansa. Nene tana rawar jiki ta yiwa Baffa da Abdul-Basi shimfidar tabarmar kaba a zaure, ta kawo musu dakwalkwalin ruwan sha a kwanan sha, ko ba'a fada ba Abdul-Basi ba zai iya shan wannan ruwa ba da ruwansa na roba a mota. Umaimah ta dinga lallashinsu yaran dakyar suka shiga dakin a bisa sharadin ana jimawa zasu fito su tafi da ita. Mata, yara da manya kowacce ta wanko kafa ta zo yiwa gimbiya Umaimah sannu da zuwa har da masu guzurin abinci, wasu dafaffiyar kaza, wasu fura da nono aka jere mata a gabanta, sai godiya take tana ta gaisawa da mutane har sai da ta ji ba dadi, kanta ya fara ciwo saboda ta dade rabon data ji rin wannan hayaniya, gida ya cika dankar kai ka ce gidan biki ne. Kowacce mace a dangi da MAKWABTAN Umaimah sun hallara a gidan amma banda Matawata, ta kulle kanta a daki ita da *ya*yanta ta hana su fitowa, sai cizon yatsa take tana kai kawo daga wannan bango zuwa wancan bango, zama balle kwanciya sun gagare ta saboda bakin cikin dawowar Umaimah musamman Ilah ya shirya ya je har Gombe taryar ta. Daman ta san da wanan maganar har yanzu yana son Umaimah, ya fada da bakinsa ba zai daina sonta ba har abada. Ko bayan ransa yana fatan Allah Ya hada su a aljanna su zauna tare. Duk da ta rufe kanta a daki babu abinda bata jiyowa daga gidan su Umaimah, shewa kawai ake yi ana yiwa Umaimah kirari ana yabawa da kyawun da ta tsatso a can, har ma ana kwatantata da ta zama tsoka daya a miya dan ita ce *yan asalin garin ta farko data taba yin karatu mai zurfi kuma ma ba akasar nan ba a kasar waje. Rashin sani yafi dare duhu bata san kuncin da Ilah yake ciki ba a yau har ya fi nata saboda yaga alamar Abdul-Basi da gaske biko yake nema. Ya kasa zaman gida ya kaura gaba daya bakin rafi ya zauna yana lazimi. Hehehehe.. Duk naku wasa ne kallon ku kawai nake naga iya gudun ruwan ku. Dan Umaimah ta dan Aunty ce..MAKWABTAKA 44 A lokacin da Umaimah take fama da baki a cikin gida, Abdul-Basi ya tara dattijai masu fada aji a gari cikin zauran gidan, yana yi musu bayanai da basu hujjoji da zasu yarda dashi a tilastawa Umaimah ta koma gidansa. Daga duk alamu ba alfarma ya ke nema ba illa shi ne zai yi musu alfarma saboda ya na ganin su kidahumai babu boko, ba wayewa, ga talauci, na masara da dawa kawai suke nema. Baffa da Sabitu suna gefe ba su ce komai ba daga dukkan alamu ba su yi amanna da bukatunsa ba. Abdul-Basi ya kula da haka sai ya tuno wata hanya wacce zai bi ba sai ya bi ta wajen Baffa ba kuma ita ce hanya mafi sauki da zai cimma burinsa, daman ta inda a hau tanan ake sauka ba da Baffa suka yi magana ba, da Dagaci suka yi magana tun a lokacin auren Nasiba dan haka da ya gama dandankawa dattijai na goro sai ya dunkulo kudi mai dan yawa ya ajiye a gaban Baffa da Sabitu ya mike tsaye ya ce zai je ya gaida Dagaci. Da kafa ya tafi ya bar bar motarsa a kofar gidan, yana fita Baffa ya juya ya kalli *yan uwa da abokansa na zaune a wannan zauren ya ce, ''Kada ku yi gaggawar amsawa Abdul-basi, yanzu ba ra'ayinmu za'a bi ba ra'ayin yarinya za'a bi tunda ita ce ta zauna da shi ita ya wulakanta kuma ya wahalar, ita ce kuma nan gaba zata zauna da shi dan haka sai abun da ta zaba za'a yi. Wasu daga cikinsu suka gasgata da maganarsa, wasu kuwa suka ce ba zai yiwu ba, ba za'a bi ra'ayin yarinya ba, dan ba ita ce ta haife su ba su suka haifeta. Ko dan tayi ilimi tayi kudi shine zata gagari manya? To in shi ba zai iya tsawatar mata ba saboda ta aiko masa da makudan kudi yayi jari su zasu iya tsawatar mata. Surutai dai barkatai suka dinyi suna fada harda kumfar baki. Sabitu ya kufula ya bude baki zai yi magana, Baffa ya hana shi. Haka aka tashi daga taro barambaram Baffa da Sabitu ne kawai suka rage a zaune a zauren. Baffa ya ce Sabitu ya shiga gida ya kira masa Umaimah, shigar Sabitu gida ba dadewa sai ga shi da Umaimah sun bayyana a gaban Baffa. A gigice ta fito yayin da zuciyarta ta dinga dukan uku-uku ta san maganar dai ta Abdul-Basi ce. Fargabar da take yi ita ce wanne hukunci Baffa ya yanke akan maganar, tafi kyautata zaton Baffa yana goyon bayan Abdul-Basi yin hakan kuwa da Baffa zai yi ba karamar matsala zai tayar mata ba, dan ba zata bi ra'ayinsu ba. *Ya*yanta suna makale da ita suka zazzauna. ''Baffa lafiya na ganku a cikin damuwa? Umaimah ta tambaye shi cike da rikicewa. Ya dago a hankali ya dube ta tabbas har yanzu babu annuri a fuskarsa. Ya gyada kai ya ce, "Umaimah na shiga matsanciyar damuwa akan maganarki da Abdul-Basi, yana son ki koma gidansa, dangina da abokaina suna son ki koma. Yaya kike gani? Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''Baffa, ka tuna a sanda Abdul-Basi ya kore ni, kunya nake ji wani ma ya ji abunda yayi min. Kai kanka ma kasa fada maka nayi ina ta rufewa ina ganin kamar zai zo ya mayar dani. Ya juya min baya bai sake waiwayata ba balle yasan wanne hali nake ciki. Alokacin koda na fito da maganar wadannan mutanen nan da kake kiransu *yan uwanka, abokanka babu mutum daya da zai iya tashi ya je ya cewa Abdul-Basi bai kyauta ba, ya zo ya mayar dani. Daga masu murna da surutu, suna yada zance, sai wadanda za suyi dariya suce Allah Ya kara, babu wanda yasan wahalar da na sha, na dinga garari a garin Gombe har hannun karuwai na kusa fadawa, Allah ne Ya kiyaye ni ka tambayi Sabitu duk na bashi labarin yadda aka yi. Baffa zamani ya canja, kan mage ya waye, ka rabu da ra'ayin mutane ka yi abunda ya dace da kai. Maganar gaskiya ita ce Abdul-Basi yayi sha'aninsa in yi nawa ba zan iya aurensa ba, dan zamanmu a yanzu ba zai yiwu ba. Baffa ya nisa ya ce, "Bakya tausayin yaran nan da suka shaku dake, ki duba kiga yadda suka rirrikeki basa so ku rabu. Umaimah ta dubesu ta sirnano da hawaye mai radadi ta ce, ''Rayuwarsu, cinsu, shansu da kariya duk yana hannun mahaliccinsu. Shi Ya rayasu a lokacin da suna kanana basu ma kai haka ba na tafi na bar su, ina kuka suna kuka Abdul-Basi ya rabamu. Duk inda suke ina yi musu addu'a kuma zata isa gare su, duk daren dadewa za su zo inda nake. Baffa ya girgiza kai ya ce, ''Bakya ganin zan zama abin tsana a wajen Dagaci da sauran jama'ar gari idan na bi bayanki? Yanzu ma an yi min gori wai dan kin yi ilimi, kin yi kudi, kin aiko min da jari shiyasa bana iya tsawatar miki. Umaimah ta ce, "Abun da na gama fada maka fa kenan, ka bi ra'ayinka ka rabu da mutane dan mutane ba'a iya musu. Su je suyi magana har su gaji su daina babu abinda zai shafe mu. Duhu ya gushe haske ya zo, kai yanzu ya waye, talauci ya tafi. Babu abinda yanzu wani zai iya yi maka wanda bazan iya yi maka shi ba, daga Abdul-Basi har Dagaci balle abokanka. Ka toshe kunnuwanka, ka rufe idanuwanka, ka zamo baka ji baka gani su je su ce duk abunda zasu ce. Sabitu ya kyalkyale da dariya ya yi tafi ya ce, ''Yayi daidai Adda Umaiman, maganarki haka take. Baffa ya girgiza kai ya ce ''haka za ki ci gaba da zama a cikin Rugar nan ba aure, ko birni zaki je ki kama gida ba aure ki zauna? Ai sai a zage mu. Umaimah ta gyara zama yayin da ciwon da kanta ke yi ya sake tsananta ta ce, "Ba'a kaina mace take zama a gidansu ba idan aurenta ya mutu ba, har zuwa ranar da Allah Zai aiko da wani mijin ayi aure. Me zai hana ni zama a gidan nan tunda anan Allah Ya rubuto min, anan aka haife ni harna girma, anan zan zauna inci gaba da rayuwata irin ta da. Ba zan koma birni da zama ba duk da cewa ya kamata in fara aiki sai in hakura da aikin, nima nasan bai kamata a ce ina zaman kaina ba a can. Ni dai zan hakura da duk wani jin dadi da zan samu in dai sai na koma gidan Abdul-Basi. Baffa ya ce, ''A tsakanin Rugagen nan wanne namiji kike gani zai iya tunkararki da maganar aure? Kowa gudunki zai yi saboda kinfi karfinsu babu mai iya aurenki. Idan Ilah kike so har yanzu shima yana sonki, amma kinsan halin Matawata, kin kuma san irin tashin hankalin da aka yi a baya. Umaimah ta yi murmushin takaici ta dubin yaran da suke kwance a jikinta ta yi magana cikin harshe turanci ta ce su tashi su shiga gida zata shigo itama yanzu. Yara masu hankali da jin magana suka tashi cimak suka shiga gida. Ta dubi Baffa ta juya ta dubi Sabitu ta ce, ''A yanzu ba ni da wanda nake so a duniya irin AbdulSabur, shine kadai namiji daya da halayyarsa suka yi min, kuma wanda zan iya zama da shi in yi masa biyayyar aure. ''Waye Abdul-Sabur? Baffa da Sabitu suka hada baki suka tambaye ta. Ta yi mumushi kuma hawaye ya cika mata ido ta gyara zama ta fara basu labarin Abdul-Sabur. Ta fara da fayyace musu asali, yare, da kuma kasar da ya fito, ta fada musu a inda suka hadu da yadda akayi suka hadu, yadda aka yi suka saba da dalilin da ya sa ta fara sonsa da yadda kyawawan halayensa suka saka take marmarin aurensa sannan ta fada musu yadda suka rabu. Sai suka tausaya mata saboda suma sun san ta rasa Abdul-Sabur din data ke so. Baffa ya ce, "Zaki ki auren mutumin da kike da shi a hannu saboda mutumin da baki da tabbacin ko zaki sake ganinsa a rayuwarki ba? Kuma har ya fada miki da bakinsa ya tafi ya auri *yar uwarsa. Dadin dadawa kuma bai ma san kina nan kina sonsa ba, dan haka ko yana sonki ba zai yi garajen nemanki ba. Ta sharce hawaye ta gyada kai ta ce, "Wannan haka yake, ko ban same shi ba na tabbata shi nake so kuma zan sami wani makamancinsa amma ba Abdul-Basi ba. Kafin ta rufe bakinta suka ji sallama suka daga kai gaba daya suka kalli me shigowa, Musa ne daya daga cikin fadawan Dagaci, ya duka ya gaishe da Baffa ya shaida masa ana kira a fada. Baffa da Umaimah suka zurawa juna ido can Umaimah ta juya ta dubi Musa Ta ce "Malam Musa, ka je ka ce gashi nan zuwa Ya fice da sauri da sauri, ta dubi Sabitu ta ce ''Ka raka shi dan ka karfafa masa gwiwa ka da ya ga idon Dagaci ya ji nauyinsa ya amsa musu abinda suke so ni kuma in cutu. Baffa ya dakatar da ita da hannu ya ce "Yi shiru shiga gida ki bar ni da su ni na san amsar da zan basu. Ya tashi da sauri ya fice Sabitu ma ya bi shi a baya, sai ta daskare a zaune tana kallon ikon Allah, mulkin mallaka kiri-kiri ake yi musu tuntuni ashe rashin ilim ya hana su ganewa. Ta dade a zaune sannan ta tashi ta shiga gida, ta iske *ya*yanta a tsugune a tsakar gida sunki yarda su shiga daki. Su Nene da sauran baki sun yi fillancin duniyarnan akan su zo su zauna suka ki. Umaimah tana shigowa suka taso da gudu suka runguma ta, ta ja hannayensu suka shiga daki. Cikin lungu ta shige ta dinga shirgar kuka amma a wayence bata son yaran su gane. Allah Yayi dare gari ya waye ta dawo kasarta har matsaloli sun sake dawo mata. Idan ta dubi yaran sai su bata tausayi su ne kadai suka saka take ragawa Abdul-Basi tana gudun kada ayi baram-baram ya hana ta ganin yaran ma gaba daya, dan kadan daga cikin aikinsa. A haka ta daure take dan cin abincin nan dakyar take hadiyewa, saboda babu kamshin curry, bana spies, sai karni take ji a hancinta yayin da harshenta ya gauraye da zakin kafi zabuwa babu magi, nan da nan ta ji zuciyarta ta fara tashi kamar zata yi amai. Su kuwa su Babangida da yake yara ne sai suka ji dadin abinci miya mai zaki cakwai. Duk da gajiya, barci da ciwon kan da yake damunta bata so ta fara bude akwatinan tsaraba yanzu ba amma ya zama dole ta bude taci biskit da butter tunda ta kasa cin abinci kuma ta dauko tsarabar da ta siyowa yaranta su tafi da ita taga alama yau ita da Abdul-Basi zasu rabu baram- baram, idan aka yi haka kuwa ba zai sake kawo mata su ba. Jaka guda ta cika musu da kayan sakawa, takalma da alewowi da a wata shida ma ba baza su iya shanyewa ba duk shan da zasu yi, bayan wacce suka sha suka gaji a gidan. Duk wanda zata tafi sai Umaimah ta zabo abin da ya dace da ita ta bata. Tabbas haka ne duk abinda ta siyo, anan suna ganin darajarsa, tunda ba su taba ganin irinsa ba sai taga sun barke da murna da zarar ta mika musu. Godiya da shi albarka abun baya kirguwa suke tayi mata. Baffa kuwa ana can ana ta fafatawa a fadar Dagaci shi da Abdul-Basi. Yayin da Abdul-Basi ya cika da mamaki a lokacin da yaga Baffa ya fara yi masa musu, alhali a da duk abin daya fada sai ya zauna yayi daidai. Baffa ya murje ido bai ji nauyin Dagaci ba haka bai ji shakkar Abdul-Basi ba ya ce ba shi da magana da Abdul-Basi sai dai da manyansa. Nan fa gizo yake saka dan mahaifin Abdul-Basi ba zai zo Dugge ba da niyyar biko saboda sun boye masa a lokacin da suka kori Umaimah san sun san idan yaji zai ce a dawo da ita ko ya hana auran Zulayha. Sai da ta sami fiye da shekara sannan ya ji a gari cewar Umaimah basa tare da Abdul-Basi. Dan haka har yau ya ki maganar zuwa bikonta, yayi fushi ainun, don sun zubar masa da mutunci. Abdul-Basi ya san ba zai iya tarar Alhaji yayi masa maganar bikon Umaimah ba dan haka sai ya nemi su sulhunta a tsakaninsu shi da Baffa, amma Baffa ya kekasa kasa ya ce sai Alhaji ya zo, ko bayan ya zo din ma sai an kira Umaimahh ta fadi ra'ayinta. Tabbas Baffa shi zai kawowa Abdul-Basi cikas, dan haka sai hankalinsa yayi matukar tashi ya fuskanci ba tunanin Baffa ba ne wannan mai ilimi ce ta karanta masa abunda xai ce. Dagaci yayi amanna da bayanan Baffa cewar ya turo magabatansa. A haka aka tashi daga taron. Cikin fushi Abdul-Basi ya shiga mota ya zauna ya aika cikin gidan ya ce Babangida da Bilal su fito su tafi. Sai suka ki fitowa wai su sai tare da Umaimah. Ta ji hankalinta ya tashi ta shiga lallashinsu tana yi musu dubara iri-iri tace itama gobe zata hado kayanta ta biyo su. Suka ki amincewa, sai da karfin tsiya ta ce Sabitu ya dauke su saboda sai danna horn din mota Abdul-Basi yake yi a fusace. Suna kuka kamar ransu zai fita aka banbare su daga jikinta suna kiranta suna cewa "Mu a wajen Aunty Umaimah zamu zauna. ''Su da jakar tsarabarsu a ka jifge a baya. Yayin da Abdul-Basi ya daka musu tsawa guda daya ta wadatar suka yi kulas a lungu, amma basu fasa kukan zuci ba. Ya ja mota ya tafi a fusace ko sallama bai yiwa Baffa ba. Umaimah tana zaune a cikin dakinta ko rakiya kasa yi musu tayi, ta rike kai ta rushe da kuka na takaicin rabuwa da yaranta, lallai tana cikin wani hali idan ta kwallafa son yaran nan saboda ita ta yankewa kanta ba zata sake zama da Abdul-Basi ba shi ma kuma ba zai bata yaranta ba. Magruba ta yi, da ta kewaya bandaki zata kama ruwa sai ta kasa tsugunawa saboda cakwalin kasa mrtik da bawali babu siminti, *yar zana ce aka kewaye. To wannan idan ta tashi yin wanka ya za ayi kenan? ''mishkila" inji Larabawa Haka da daddare ta ji sauro yana gantsara mata cizo sai hankalinta ya tashi. Ta kuduri niyyar tafiya Dukku da sassafe ta siyo shaltos da gidan sauro, ruwan swan, kayan shayi, risho food flask da duk kayan abinci. Sai dai jama'ar Ruga su zage ta amma ba zata zauna yunwa da wahala su kashe ta ba alhali tana dashi. Haka kuwa akayi washe gari da safe ita da Sabitu suka tafi birni suka yi siyayya, kaya cikin bayan mota 'a kori-kura aka zo aka jifge himilin kaya a dakin Umaimah. Ai kuwa tasha zimde da yafice a wajen su Nene kan ka ce kwabo magana ta yadu a gari Umaimah ta siyo kayan abinci irin na turawa ba zata iya cin tuwo ba. Haka tasa aka yi mata siminti a bandaki daidai inda zata dinga hawa tana yin wanka. Tabbas gayunta ya tabbata, dan ma tana daurewa tana hakura da wasu abubuwan da kada maganar ta yi yawa. Da generator zata siyo ta dauko me alsawa ya hada mata ta dinga yini tana kwana a cikin fanka, dole ta hakura da wutar lantarki. A daddafe ta shafe wata guda cur sai ta ce da Baffa zata je Gombe ta ji yadda ake ciki da zancen tafiyarsu bautar kasa. Sabitu ne ya rakata da kayansu kala biyu suka zuba a cikin jaka. Tana shiga birni Gombe ta sayi layi ta kunna wayarta, Hanif ta fara kira, ya ji dadi dajin wayarta dan har ada ya fara tunanin muddin bata zo a cikin satin nan ba sai ya je Dugge da kansa ya sanar mata maganar tafiyarsu bautar har sun yi taro sau biyu a gidan gwamnati, saura sati biyu su tafi Abuja. akwai Post anjima in kuna so.?MAKWABTAKA 45 Da kansa ya sanar mata maganar tafiyarsu bautar har ma sun yi taro sau biyu a gidan gwamnati, saura sati biyu su tafi Abuja Tana gama waya da Hanif sai ta kira kawarta Aisha Bingyal, da farko Aisha bata gane mai magana ba kasancewar sabon layi ne yanzun nan Umaimah ta saya sai daga baya ta shaida muryar, Umaimah Bello ce aminiyarta. "Gani a garinku, kwatanta min gidanku" Umaimah ta fada cike da fara'a. Farin ciki ya rufe Aisha ta ce "Fada min inda kike bari na zo kawai in dauke ki. Ko da mota kika zo? Umaimah ta ce "Da motar haya muka zo ni da kanina Sabitu gamu nan a bakin tashar Dukku, ki zo ki dauke mu. "Gani nan zuwa yanzu, daman a shirye nake tsaf. Inji Aisha. Su Umaimah suna ta tsayuwar jiran Aisha a bakin titi, sun dade suna jira kasancewar akwai tafiya daga unguwarsu pantami zuwa tashar Dukku. Mota kirar discoussion continious ce baka me bakin gilashi ta zo ta tsaya a gaban su Umaimah. Sai suka tsurawa motar ido dan basa ganin cikin motar saboda duhun gilashin bata zaci Aisha ce a cikin motar ba har sai da ta sauke gilashin motar ta leko da kai. Ta ce "Umaimah Bello, ku shigo mu tafi Umaimah ta yi mamaki da ganin Aisha cikin wannan daula, bata zaci *yar gidan masu kudi ba ce haka. Umaimah ta shiga gaba Sabitu ya zauna a baya suka tafi, bayan sun gama gaggaisawa sannan hira ta rincabe. Aisha ta gyara farin gilashin da yake fuskarta ta dubi Umaimah tayi murmushi. Ta ce "Kin gudu garinku ba waya kin bar ni a nan jama'arki sun hana ni sakat wai sai na kai su gidanku. Cike da rashin fahimta Umaimah ta tambaya "Su waye kuma jama'ata? Aisha ta ce "Na san baki san su ba amma dai idan nayi miki bayani zaki gane su, wallahi jama'a da yawa da suka je graduation dinmu Malaysia suka gan ki suka ce suna sonki. Yanzu dai su biyu ne suka zo suka same ni daban-daban kowanne yana son in bashi adireshi da lambar wayarki. Na ce musu ban sani ba amma su zo ranar da zamu tafi Abuja karbo 'call up letter' mu ta bautar kasa za su ganki. Umaimah ta yi ajiyar zuciya jikinta a sanyaye ta juya ta dubi kaninta ta ce "Malam Sabitu ka ji wata sabuwa kuma. Yayi dariya ya ce "Alhamdulillah, haka ake so Allah Ya zabar miki duk wanda ya fi alkhairi a cikinsu. Umaimah ta dafe kai ta ce "Ai zai yi wuya in so ko dayan ne ma daga cikinsu saboda ni tuni na dankawa Abdul-Sabur zuciyata. Sabitu da Aisha suka dau salati a lokaci daya dan mamaki kasancewar su dukka suna da labarin Abdul-Sabur, da yadda suka rabu. Aisha ta fada cike da gatsali ta ce "Au anga Abdul-Sabur din ne daga in da ya bace din? Umaimah ta harare ta ta ce "Daman bata yayi? Aisha ta yi dariya ta ce "Kin cika abun haushi ana miki maganar mutanen da suke sonki a zahiri kina maganar mutumin da ya tafi zai auri wacce yake so. Umaimah, wadannan mutane manyan mutane ne, kusoshin gwamnati ne wadanda ake damawa da su a kasa, masu kudi, masu fada aji, kuma ba yara ba ne. Idan kika gansu za ki shaida su daya ma kawun Khadija Jauro ne wannan yarinya fara doguwa wacce suke tare da Zainab *yan Legenda makarantar su Hanif tai graduation dinta kuma kasashen waje yake zuwa yana shigowa da kaya. Ita ta rako shi ma gidan nan nemanki. Sunan sa Alh. Bilyaminu, da naga motar da ya zo da ita sai da na tsorata saboda kyan motar, matarsa daya *ya*yansa hudu, gashi matashi ga kyau ga kudi. Daya mutumin ban san yadda aka yi ya sami lambata ba, kwatsam na ji ya kira ni ya kwatanta min kansa sannan na gane shi. Kin tuna wani mutumin da ya dinga magana da masu awon kayanmu a filin jirgi, wanda ya saka koriyar shadda. Umaimah ta yi shiru kamar mai tunani can ta ce "Na tuno shi dogo, mai kiba, wanda suke kiransa yallabai. Aisha ta zabura ta ce "Eh shi, shima ya ganki ya dasa. Kusan kullum sai yayi min waya ya tambaya ko kin zo. Sai in ce masa zaki zo dai baki zo ba yanzu. Umaimah ta girgiza kai ta ce "Gaskiya suyi hakuri ba zan iya kula su ba. Me yasa sai ni, duk a cikin dalibai mata ga kyawawa ace sai ni kadai suka sani za su dama. Aisha ta kyalkyale da dariya ta ce "Ai kin fimu kyau, gayu, iya tafiya da iya magana da turanci shi yasa ya rude. Suka sa dariya su dukkansu Aisha ta ci gaba da cewa nima na hadu da guda daya tun acan daman ya karbi lambata sunansa Mujahid. Shima wajen kaninsa ya je Aliyu wanda yayi Inti Nilai. Amma ni kin san ba irin ki ba ce me tsattsauran ra'ayi, ni ina son shi, magana har ta yi nisa, ya zo gidanmu yafi a kirga. Umaimah ta yi dariya ta ce, "Allah Ya taimaka, Ya barku tare, mu zo musha biki bayan mun gama bautar kasa. Aisha ta ce "Ai kin kai ni da nisa, kafin mu gama za'ayi ma insha Allahu. Ina Hanif kaninki kuwa? Wannan yaron ya cika surutu har da cewa zai dinga zuwa muna gaisawa, ban sake ganinsa ba. Umaimah ta zabura ta ja wayarta ta ce, "Har kin ma tuna min, na shigo gari ban kira Baban Hanif na gaishe shi ba. Daman da lambar wayarsa a cikin wayar sai ta nemo sunansa ta kira. Da farko bai amsaba kasancewar bai san lambar ba amma data ci gaba da kira ba adadi sai ya dauka. Bayan sun gaisa sai ta gabatar da kanta nan da nan ya gane ta, yayi farin ciki da jinta a waya, ta shaida masa ta shigo gari dazun. Yana kokarin ya ce ta zo gidan sa ta sauka a wajen kawarta Lamijo sai tayi sauri ta shaida masa tana gidan kawarta Aisha Bingyal amma wani lokaci idan ta shigo zata je. Baban Hanif ya yi gyaran murya ya ce "Lamabarki ce wannan? Umaimah ta ce "Eh ita ce Baba. Ya ce "To zan ajiye lambar, kina da labarin saura sati biyu ku tafi Abuja bautar kasa? Umaimah ta ce "Eh an fada min, mun yi waya da Hanif ma dazu. Suka dan jima suna hira sannan suka yi sallama kafin su kashe waya kwatsam ta ji Baban Hanif ya furta mata wata kalma wacce ko a mafarki ba ta zaci maganar nan zata fito daga bakinsa ba. Nan da nan ta gigice ta dafe kirji tana ta salati a cikin zuciyarta, hakika maganarsa ta firgitata kuma ta daga mata hankali. Bata da mafita dan haka sai ta amsa da "To Baba, na amince Allah Ya tabbatar mana da alkhairi. Saboda ba ta isa ya nemi alfarma a wajenta ta ki yi masa ba, muddin dai bai sabawa addininta ba, ya yi mata halaccin da babu wanda ya taba yi mata irinsa a rayuwarta ba. Daga karshe suka sake yin sallama ta ajiye waya a sanyaye kai ka ce laka ce aka zare mata. Ta dafe kai da hannaye guda biyu tana ta karanta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Aisha tambaya take, Sabitu ma tambaya yake "Lafiya? Me ya ce miki? Ta dade kanta a kife sai can ta dago ta dubi kawarta cike da damuwa. Ta ce "Aisha ina zan saka kaina? Yaya zan yi da taron mazan nan da suka addabe ni? Aisha ta zabura ta dafa kafadarta ta ce "Baban Hanif ma cewa yayi yana sonki ko? Daman ni nasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Sabitu ya ce "Wannan shi ake kira ga akuya ga kura. Ya ya za'a yi da Lamijo kenan? Umaimah ta ce "Kai, ka rufe mana baki maganar manya ce wannan, kawata idan muka isa gida zan baki labari. Sabitu ya kyalkyale da dariya ya ce "Au haka ne ma abun? Ina cikin zamana zaki zo ki saka ni a cikin maganar. Daidai lokacin suka iso katafaren get din gidan su Aisha, me gadi ya taso da sauri ya wangale get sika kutsa da motar cikin gidan. Makeken gida bangare-bangare ya kawatu da fulawowi an kewaye gidan kai ka ce Hotel ne ba gida ba. Umaimah ta ce "Bari mu gaisa da su Mama sai in yiwa Hanif waya ya zo ya tafi da Sabitu gidansu tunda shi namiji ne. Aisha Bingyal ta ce "A'a akwai bangaren baki maza ko sun kai guda nawa zasu zauna ba tare da wani ya takurawa wani ba. Umaimah, ku saki jikinku wannan gidanku ne babu mai gajiya da ku, muna son baki. Kin san nice *yar auta a gidanmu dukka yayuna mata ne guda hudu duk sun yi aure. Umaimah da Sabitu dai sai kallon gida suke suna masu annuri dan yau za su yi kwanan dadi ga fanka ga Ac ba sauro balle kwari irin na Dugge. Cikin katafaren falo suka fara shiga ta yi musu izini su zauna tana zuwa, ta wuce zuwa kicin ta bawa mai aiki izinin ta kawowa baki ruwa da lemo sannan ta fito ta wuce zuwa bangaren Mamarta, dan ta sanar da mata cewar bakin sun karaso. Sabitu ya dubi Umaimah ya yi dariya ya ce "Adda Umaimah, Allah Ya baki kudi da ikon gina mana gida irin wanna a birni. Ko kuma Allah Ya baki miji mai arziki mu zo mu huta. Umaimah ta yi dariya ta dafe kirji dan jin dadin kalaman Sabitu. Ta ce ''Allah Ya biyewa bakinka dan kanina. Suka dinga shan lemuna kala-kala ko ruwa ba su kalla ba, suka sami kek da meat pie suka dinga ci. Sai da suka dan jima a zaune sannan Aisha da Mamarta suka fito, Umaimah da kaninta suka silalo daga kan kujerun da suke zaune suka kwashi gaisuwa. Ta umarcesu da su koma su zauna akan kujera, amma suka ki zama suka ci gaba da zama akan kafet saboda kunya da girmamawa irin ta Fulani. Mama tana zaune, Aisha na zaune a kusa da ita. Aisha ta ce "Mama ita ce Umaimah *yar makarantarmu da nake baki labarinta, ita ce babbar aminiyata mai sona nima ina sonta. Suka yi dariya su dukkansu. Mama ta ce "Ai kuwa ina shan labarin Umaimah tun daga can ai mun taba gaisawa ma a waya, sai yau Allah Ya nuna min Umaimah *yar mutanen Dugge. To sannunku da zuwa kawar Aisha. Ke da Yayanki ne ko? Umaimah ta dago da sauri ta dubi Sabitu ta yi dariya ta ce "Kanina ne Mama. Mama ta ce "Na ganshi ne kamar babba da yake namiji ne ya fi ku girma, amma kamarku daya. Aisha ta ce "Sabitu mu je in kai ka dakinka sai ka dan huta. Sabitu ya tashi yana biye da Aisha, Umaimah ma ta bi su suka fice zuwa wani bangare a can waje, falo, daki daya da bandaki, babu abinda babu tamkar dakin wata amarya. Umaimah ta bude jaka ta ware masa kayansa kala biyu ya zuba a durowa sannan ta tafi da jakar kayanta a ciki bayan sun nunnuna masa duk yadda zai yi amfani da kayan ciki. Dakin Aisha suka wuce akan bene sai da Umaimah ta jinjimawa dakin saboda ya kayatu ga girma, kai kace filin kwallo ne. Katafaren gado da kujerunsa, ga kayan kallo duk daki daya, kayataccen bandaki mai kyau kai ka ce na tangaren ne kamar ka kwanta ka yi bacci a ciki. Wanka Umaimah ta fara yi sannan aka aje mata abinci kala-kala ita da kawarta suna ci suna ta hira har suka koshi, tabbas ta tuna Malaysia a yau musamman da sanyin Ac ya ratsa ta. Bayan ci sai kwanciya, Umaimah ta kwanta hakarkarinta akan lallausar katifa saboda gajiya, sai ta tsinci kanta tana mai aiyanowa a ranta dama ace gidanta ne nan ita da abun kaunarta Abdul-Sabur sai ta ji kwalla ta cika mata ido. Nan da nan ta tuno da Faduwa sai ta jawo wayarta a sanyaye ta dubo sunan Faduwa ta kira ta. Bugu daya Faduwa ta amsa tun kafin ma Umaimah ta yi magana Faduwa ta ambaci sunanta. Cike da mamaki Umaimah ta tambaye ta "Ya aka yi kika san ni ce tun ma ban yi magana ba? Faduwa ta ce "Dare da rana ina jiran in ji kiranki daga Nigeria, dan haka ina ganin lambar Nigeria sai na san kece duk da yanzu *yan uwana suna yawan kirana daga Sokoto. Umaimah ta ce "Kira nayi in ji yadda kike ciki. Kin haihu lafiya ko? Faduwa ta ce "Ai na yi fushi tunda baki neme ni ba tuntuni, sai yanzu. Umaimah ta ce "Allah Sarki Antina kin san Rugarmu ba mu da waya, yanzun nan na fito birni, na sayi layi. Faduwa ta ce "Na haifi *ya mace gata nan kamarta daya da ni sak, na saka mata suna Umaimah. Sai Umaimah ta daka tsalle ta diro daga kan gado dan murna har da hawayen dadi ne yake kwarara Ta ce "Anti Faduwa, da gaske Umaimah sunanta? Ai kuwa zanzo har Cairo wata rana musamman dan in ga takwarata. Amma na ji dadi na gode, Allah Ya raya ta, Ya yi mata albarka. Faduwa ta ce "Amin, ga Sagir ku gaisa shima yana tambayar ki, zai sake fada miki sunan baby ki ji. Ai shi zaki fi yarda da maganarsa. Faduwa ta mikawa maigidanta waya cikin harshen turanci suka gaisa da Umaimah ya sake shaida mata sunanta aka saka. Ta yi masa godiya da taya shi murna, gami da yiwa jaririya doguwar addu'a. Daga karshe ta yi sallama da su suka kashe waya. Daidai lokacin Aisha Bingyal ta idar da sallah ta dubi Umaimah ta ce "Aminiyarki ce Faduwa ta haihu? Ai da kin bani ita mun gaisa, dan tana da kirki. Umaimah ta ce "Tana da kirki sosai ma kuwa, har sunana ta sakawa *yar jaririyar data haifa, shiyasa kika ji ina ta tsalle. Zan baki lambarta sai ki kira ta ku gaisa, ta sanki sosai, kiyi mata barka. Faduwa da Abdul-Sabur ai aminaina ne na hakika, na ji dadin zama da su, ba zan taba mantawa da su ba kuma ba zan daina kaunarsu a raina ba har abada. Aisha ta yi dariya ta ce "Musamman ma Abdul-Sabur din, shi so na musamma kike yi masa bayan na MAKWABTAKA. Suka yi dariya su dukkansu. Aisha ta tashi daga kan abin sallah ta cire hijabinta ta linke ta zo ta zauna akan gado kusa da Umaimah. Ta ce "Yauwa, har kin tuna min ma da maganar Baban Hanif, kin ce zaki fada min abunda ya ce miki. Umaimah ta kalle ta tayi murmushi ta jawo filo ta ringisa. Ta ce ''Uhum, ashe baki manta ba kema? Ni ma wallahi tun dazu maganarsa ta tsaye min a rai, har na fara tunanin da ace akwai inda zan kaura da garin nan zan bari in tafi inda ba'a taba sanina ba, zai fi min sauki. Aisha ta harare ta, ta ce "Irin yadda kika yi mana a Malaysia za ki sake yi musu a garin da zaki kaura? Ai duk in da kika je dole ki sami wadanda zasu saba da ke, sai sun sanki dole, kamar yadda kika saba da Faduwa da Abdul-Sabur. Umaimah ta ce "Haka ne, dan gaskiya ko a mafarki ban zaci akwai ranar da zan saba da makwabtana ba su Faduwa, sai gashi daga baya bani da tamkarsu har ban so muka rabu ba. Baban Hanif yayi min wata magana wacce a wajena ba mai yiwuwa ba ce, kuma idan ban amince ba tabbas ba zai ji dadi ba kuma ban kyauta masa ba. Aisha ta ce "Me ya ce miki, cewa ya yi yana sonki zai aureki? ............ Eh cewa yayi xai aure ni, nikuma a duniya banga wanda nake so da kauna ba irin Dan Aunty... Kuma shi xan aura...lols. Ehem yan uba kunji dai da bakin Umaimah wanda tace xata aura dan nima bayin kaina bane a dole xan aure ta... Marbass Dan Aunty. See translationMAKWABTAKA 46 Aisha ta ce "Me yace miki, cewa ya yi yana sonki zai aure ki? Umaimah ta ce "Cewa yayi daya daga cikin abokan aikinsu ne ya ganni ya ce yana sona, ya biyo ta wajensa. Hmm, Baban Hanif ya na sake maimaita min cewar Alh. Nura ogansa ne yana jin nauyinsa sosai. Ina jin yasan halina yana tsoron kada in wulakanta masa oga. Ya dami Baban Hanif wai ya nemo masa lambar wayata, wai idan na amince zai ba shi lambar yanzu. Nauyinsa nake ji ba zan iya cewa kada ya ba shi lambata ba, sai na ce ba damuwa ya bashi lambar, sannan ba zan iya wulakanta mutumin da ya kawo min ba ko da a bayan idonsa ne, sannan ba zan iya aurensa ba saboda AbdulSabur nake so. Yaya kika ga za'ayi yanzu? Tabbas ina cikin wani hali Aisha. Umaimah ta sulale ta kwanta saboda tashin hankali. Aisha ta dade a zaune tana kallon Umaimah daga dukkan alamu tana jin tausayinta, sai can ta matso kusa da ita ta dafa kanta. Ta ce "Gaskiya sai yanzu na fara fahimtar matsalarki kawata, ba wai dan kina son Abdul-Sabur ba ne yasa na fara jin tausayinki ba, ni na fi so ma ki cire shi a lissafinki. Naga alama cunkushewar maneman ne da suka fara yi miki yawa, zai yi wuya ki tantance wanda ya fi a cikinsu. Yanxu haka na turawa Bilyaminu lambarki dazun nan da muke cin abinci, ya ce zai kiraki dan ni na fi yi miki sha'awarsa fiye da yallabai saboda shi Bilyamin matashi ne, me mata daya da *ya*ya kadan ba kamar yallabai ba matansa biyu, sannan da tulin *ya*ya sai dai akwai tulin kudi. Ga na bangaren Baban Hanif daga gani shima me kudi ne, dubi duk kudin Baban Hanif ya ce wancan ogansa ne ya fishi kudi kenan, lallai akwai Naira. Ko baki aure shi ba zaki sami kudi a wajensa. Umaimah, wannan fa ba abin damuwa ba ne, ana hada samari biyar ko goma har mai rabo ya samu ya aura, ba abin damuwa bane. Za ki iya kula su dukka, ba dai gaisawa ba ne a waya ko kuma suzo ki fita ku yi hira shikenan fa. Umaimah ta ce gaba da karanta "Lahaula wala kuwwata illa billahil aliyyil azim. Dan ta shiga garari. Wayar Umaimah ce ta dau kara bata yi mamaki ba dan ta kikkira mutane da yawa ta san yanzu an fara sanin lambarta. Ta mika hannu a sanyaye zata dauka sai Aisha ta yi sauri ta sura ta duba lambar, kallo daya ta yiwa lambar ta shaida lambar Bilyaminu ce. Sai ta yi dariya ta ce "dan halak Bilyaminu ne da gaske fa yake kawata, dan Allah kada kiyi masa wulakanci. Ta danna da sauri ta karawa Umaimah a kunne, cike da takaici Umaimah ta ke magana. Yayi farin ciki da jin muryarta sai ya rikice gaba daya ya hau rawar jiki, cewa yake wai zai baro Kaduna a yau ya zo dan ya ganta a gidan su Aisha da daddare. "Allah Ya kawo ka lafiya. In ji Umaimah ta kashe waya a fusace. Kafin Aisha ta yi magana sai wayar Umaimah ta sake yin kara alamar kira ake yi, ta zaci Bilyaminu ne sai taga wata lamba ce daban, bata yi mamaki ba dan zai yiwu yana da layika da yawa, ta danna ba tare da walwala a fuskarta ba. Wannan karon salon maganar da muryar ba irin ta dazu ba ce. Dan haka sai Umaimah ta yi kasake tana sauraron abunda zai ce, har yanzu magana yake yi cikin kasaita. "Ko bada Umaimah nake magna ba ne? Ya tambaya "Ita ce" in ji Umaimah Ya ce "Kina magana da Justice Nura, ni ne wanda Alh Nasir ya yi miki maganata, yanzu ya turo min lambarki. Sai Umaimah ta zabura ta tashi zaune dan fargaba yayin da Aisha ma ta zare ido tana kallon ta. Aisha ta shiga yi mata rada tana tambayarta "Lafiya, me yake ce miki. Umaimah ta daga mata hannu alamar ta tsaya tana zuwa. Umaimah ta gaishe shi cikin girmamawa. Ya ce "An ce kin shigo gari, zaki kwana biyu ko? Yana kokarin ya ce zai zo wajenta ya ganta su gaisa. Sai ta yi sauri ta ce ai a yau zata koma Dugge sai dai idan ta sake shigowa. Ya ce "Ba matsala zan saka direbana ya kawo miki sako ya dauke ki ya kai ki Dugge sai ya gano min gidanku saboda gaba idan zan je ya kai ni. Umaima ta ce ai bata gida yanzu haka tana cikin tasha har ta hau mota zata koma amma wani lokaci idan ta dawo sai su je direban ya ga gidan. Ya ji ba dadi amma ya yi mata uziri. Yana tantamar bata san ko shi waye ba shiyasa take yi masa wargi yana saka ran daga sanda ta gan shi, ta san matsayinsa zata shiga hankalinta. Suka yi sallama suka kashe waya. Umaimah ta dora hannu a kai ta mike tsaye ta ce "Aisha wannan ba Bilyaminu ba ne, wanda Baban Hanif ya fada min ne shine ya kira shima maganar zuwa yake yi min. Aisha yau zan koma Rugarmu na fasa kwana a nan. Umaimah ta shiga linke kaya tana zubawa a jaka, a gigice take. Hankalin Aisha ya tashi ta shiga lallashin Umaimah amma kamar zuga ta take yi, har da rantsuwa Umaimah take yi ba zata kwana ba tafiya zata yi. Umaimah ta juya ta dubi Aisha wacce ta yi kasake a gefe tana kallon ikon Allah dan ta rasa me ma zata fada mata ta yarda da ita. Ta girgiza kai ta ce "Yi hakuri ba laifina ba ne dole ce ta sa zan tafi, ki kira Bilyaminun ki ce ya fasa zuwa ba zan kwana a Gombe ba. Za ki iya ce masa daga gida aka ce in koma yanzu. Kafin Umaimah ta rufe bakinta wayar Aisha ce ta dau ruri sai su dukka suka zurawa wayar ido a tsorace. Aisha ta dau ki wayar a hankali ta duba, sai ta dago ta kallo Umaimah ta zazzare ido. Ta ce "Dayan ne shima yake kira, Yallabai ne, na san ma maganar lambar wayarki zai yi min. Umaimah ta zabura ta ce "Kada ki bashi lambata, Aisha ki rufamin asiri dan Allah. Aisha ta dannan waya da sauri, bayan sun gaisa kamar kullum ya tambaye ta lambar abar kaunarsa Umaimah. Sai Aisha ta saka wayar a 'speaker' yadda Umaimah zata ji da kunnuwanta abunda yake tambaya. Aisha ta ce "Ranka ya dade, idan ta zo da kaina zan kira ka ku gaisa ka karbi lambarta. Ya ji dadi da bayanan Aisha yayi mata godiya suka yi sallama suka kashe waya. Umaimah ta gyada kai ta ce cafdijam! Zaman birni yafi karfina. Ina zan kai wadannan mazan? Gara in koma Ruga in yi zamana ba waya balle wani ya kira ni, kada ma ki dinga fada musu sunan garin mu dan akwai wanda zai iya shiga garin ya nemo ni. Aisha ta ce "Ai na san matsalarki son Abdul-Sabur ne ya hana ki son kowa, amma meye laifinsu da zaki dinga gudun su dan suna sonki. Umaimah ta ce "In bana son kowa sai Abdul-Sabur a duniya ai ba laipina ba ne Aisha. Dole Aisha ta jawo gyalenta ta biyo bayan Umaimah wacce tuni har ta rataya jakarta ta fara saukowa daga matattakalar bene da sauri kai ka ce da karfi za'a kamata a aurar. Suka shiga dakin Mama , Umaimah ta durkusa a gabanta tayi mata sallama. Mama ta cika da mamaki da ta ji Umaimah ta ce zata tafi yanzu alhali ance kwana biyu zasu yi. To me yasa zasu tafi? Aisha ta ce "Mama, waya aka yi daga gidansu aka ce su dawo sun yi baki daga nesa. Mama ta dauko kudi da turare ta bata sannan ta dauko yadin maza ta ce a bawa Sabitu. Umaimah ta yi godiya suka fito zuwa bangaren Sabitu. A mimmike suka tarar da shi yayi dai-dai akan kujera a falo yana kallon talabijin, ga fanka gami da Ac dukkansu ya kure, falon sanyi garau. "Samun waje wai *yar caca da yado. In ji masu iya magana. Umaimah bata san sanda murmushi ya kubce mata ba ganin yanayi na hutu da walawa da ta ga Sabitu ya shiga duk da tasan yau ba zata kyauta masa ba idan ta ce ya taso su koma Dugge. Ya zabura ya tambaye ta "Lafiya? Ta ce "Lafiya kalau. Har yanzu dai a zaune yake cike da rashin fahimta yana kallon Umaimah da Aisha cike da damuwa. Aisha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kai ma ka tambaye ta Sabitu haka kawai kamar wata me aljanu ta tashi ta zuba kaya a jaka ta ce zata tafi, saboda kawai wadannan masu son nata sun ce zasu zo da daddare. Sabitu ya yi ajiyar zuciya saboda ya sami saukin fargabar da ya shiga, dan har ya fara tunanin ko waya aka yi mata gida ba lapia ba. Ya girgiza kai cike da takaici ya ce "Haba Adda Umaimah, me yasa ki ke haka ne? Meye abun tafiya kamar wata wacce za'a kama ki dole a ce za'a aurar ki, abubuwan da muka zo yi duk bamu yi ba. Ta yi sauri ta katse shi ta ce, ''Ni wallahi yanzu zan tafi sai dai kai ka kara kwana. Abunda na zo yi na yi tunda na san takamaimiyar ranar da zan dawo dan tafiya bautar kasa, sai zuwa gidan su Babangida shi kuma na hakura daman ina fargabar zuwa kasancewar karshen sati ne (week end) ina ga AbdulBasi yana gari. Daman niyyata mu bari sai ranar litinin da safe in zamu wuce mu biya, sannan ina tunanin yadda za mu yi arangama da mahaifiyarsa saboda guduna ta ke yi ko a waya bata so mu hadu saboda kunyar abunda tayi min. Alhajinsa kuwa bana so mu hadu dan kada ya yi min magiya in auri dansa ni kuma ba zan iya ba gashi ina ganin mutuncinsa sosai. Dan haka gara kawai mu hakura da zuwa gidan, abubuwan dana siyo musu mu koma da su gida ko in bawa Aisha takai musu idan ta kai mu tasha tana dawowa da yake duk hanya daya ce, sai in nuna mata gidan. Rai a bace Sabitu ya tashi ya debo kayansa ya karbi jaka a hannun Umaimah ya zuba a ciki ya fito suka tafi, babu mai walwala a cikin su ukun. Dan haka gum! Suka yi babu mai yin hira har suka isa tasha daidai inda motocin Dukku suke lodi manya da kanana, Aisha ta ja ta tsaya Umaimah ta juyo ta dubeta, ta yi dan murmushi. Ta ce "Yi hakuri kawata, ki yafe min na san na yi miki ba daidai ba amma ba yin kaina ba ne. Aisha ta girgiza kai ta ce "Kin ga kamar na damu ne? Ba damuwa na yi ba, na fahimce ki kuma zan taya ki da addu'a duk mai kaunarki zai yi miki fatan ki sami abunda kikeso. Umaimah ta gyada kai ta ce "Na gode da kika fahimce ni, ga sakon su Baban gida idan ba zaki damu ba ki mika musu idan kika zo giftawa ta gidan, ai na nuna miki gidan bakin titi zaki gane ko. Aisha ta ce "Kawo sakon sai in kai musu ba damuwa. Umaimah ta juya bayan mota ta dubi Sabitu ta ce "Ciro ledar nan ka bata. Ya mikawa Aisha leda cike da alawowi, biskit da wasu kananan turarruka na yara masu kamshi guda hudu. Aisha ta dunkulo kudi masu yawa ta mikawa Sabitu shi da Umaimah suka tirje, wai ba za'a karba ba. Sai da Aisha ta matsa sannan Umaimah ta ce ya karba. Suka yi mata godiya suka fito daga mota suka nufi motocin hayar da suke lodi, suka zabi karama (Golf) mai kyau suka shiga. Mutane uku ne ya kamata su zauna a kujerun baya, Umaimah ta ce a barsu su biyu zata biya kudin mutum dayan dan kada a matse su. Hmmm kudi masu gidan rana Umaimah Bello Allah Ya yarda, har yanzu dalolin data rago suna nan dankar tana canjawa a hankali. Tabbas Dr. Faduwa ta koya mata dubara. Tunda suka zauna Sabitu ya lura Umaimah kukan zuci take yi hawaye yana cika mata ido sai ta yi sauri ta sharce ta shiga damuwa da tunani mai tsanani. Ya tausaya mata matuka dan bashi da maganin ciwon da yake damunta daya je ya nemo mata ko a ina maganin yake. Ya fada cikin rada "Adda Umaimah, ki daina kuka maganin damuwarki ita ce addu'a. Ki yawaita karanta wannan addu'a sau uku yayin da kika tsinci kanki cikin musiba da bacin rai. Allah zai yaye miki cikin gaggawa. "Walahaula wala kuwwata illa billahil aliyyil azim. Nan da nan Umaimah ta cafki addu'ar tana sake maimaitawa, cikin ikon Allah basu yi mintina talatin ba sai ya fuskanci ta fara warwarewa daga dinbun damuwar da take ciki. Ya gyara zama ya ce da ita "Me zai hana ki zaba daya daga cikin wadannan sababbin mutanen ki aura idan ma ba zaki koma gidan Abdul-Basi ba. Saboda zamanki a haka babu aure ba zai yiwu ba kin ga mu ba a birni muke ba in da aka waye, ga arziki da wadata. Yanzu kamar a gidan su kawar nan taki Aisha babu wanda zai damu da sai ta yi aure da wuri saboda ga dakuna ma sun yi masa yawa har neman wanda zai taya su zama suke, amma a Ruga kowa zai so ki matsa dan dakuna sun yi kadan. Da-san-samu ne ma kiyi aure kafin ki gama bautar kasa sai kiyi a gidan mijinki. Dan yanzu ko ba a Abuja zaki bautar kasa, a cikin Gombe za kiyi kuma bazai yiwu ace kullum ki je Dugge washe gari ki dawo Gombe ba. Ki zabi wanda Baban Hanif ya zabar miki tunda na san ba zai zabar miki wanda ya san ba na gari ba ne, dan ki dadada masa. Umaimah ta tsurawa Malam Sabitu ido tana kallonsa yayin da take jin maganarsa tamkar dabaibayi yake yi mata tabbas ta san shawara mai kayau yake bata kuma abinda zai yiwu shi za'ayi amma lallai ta sami tawaya a rayuwarta dan zata kasance ta rasa walwala har abada, dan ta san ba zata taba son namijin da zata aura ba in dai ba Abdul-Sabur ba ne. Ta gyada kai alamar ta gamsu da shawararsa daga nan babu wanda ya sake yin magana a cikinsu har suka isa Dukku. Kafin su hau motar Rigarsu sai da suka shiga kasuwa dan siyo kayan abinci kamar yadda yanzu ita ta dauki nauyin ciyar da gaba daya gidan, kuma abinci mai kyau ga kifi da nama. Tuwon dawa ko na gero sai dai su Nene suna so su ci amarmace su auno su surfa su ci, amma shinkafa ta dafawa, fara ta yin tuwo, makaroni, taliya, kifin gwangwani da kayan shayi duk Umaimah ta jifge a dakin Baffa. Ba ta ma kai dakinta ba kada ace kanta ta siyowa. Da suka gama sayayyar kayan abincin sai suka loda a motar da zata kaisu gida su kadai da kayansu har kofar gida. Bayan an lode kaya a dakin Baffa sai ya dinga kwararowa Umaimah fatan alkhairi da fatan ta gama da duniya lafiya, hawayen dadi ne ya sirnano daga idanuwan Umaimah ta durkusa a gabansa ta shaida masa cewar tafiyarsu bautar kasa saura sati biyu. Ya yi mata addu'ar fatan alkhairi ta je a sa'a ta dawo gida a sa'a. Shima nasihohin da Sabitu ya yi ma ta shima irinsu ya yi ma ta cewar ta daure ta fitar da miji ta yi aure zai fi musu kwanciyar hankali su dukka. Tabbas ta shiga tsaka mai wuya, domin duka maneman nata babu wanda ta gani da idanuwanta a cikin su, babu wanda ta zauna da shi ta ga yadda halinsa yake balle ta rufe ido ta zabi daya. Sai ta dukufa ba dare ba rana tana ta addu'a Allah Ya kawo mata mafita mafi alkhairi a rayuwarta. Allah Ya bata miji na gari mai sonta su zauna lafiya. Ta ji a ranta ina ma bata dawo daga Malaysia ba data yi zamanta acan ko ma dai bata hadu da Abdul-Sabur ba tana ganin gidansa daya zauna zata fi jin dan sanyi. Idan ta fara tuno irin zaman da suka yi da Abdul-Sabur a baya sai tayi ta kuka ita kadai, ta yi nadamar wulakancin da ta yi masa a baya, ta jinjinawa hakuri da juriyar da ya yi ya ci gaba da bin ta, ta yaba matuka da kyautatawar da yayi mata a baya da yadda ya jajirce har sai da ya nemo mata gaba daya danginta da kawayenta ta daina zama ita kadai. Ya cusa mata ra'ayin kaunar makwabta wanda a baya ta kudiri niyyar cusgunawa duk wani makwabcinta. Allahu Akbar! Ta duba ta hanga, ta ga babu namijin da zata samu wanda zai yi mata so da kulawar da Abdul-Sabur ya yi mata. Sai dai ta yi aure saboda kawai dan ta raya sunna, ta bi miji dan Allah ne Ya ce mace ta bi amma ba dan hankalinta zai kwanta ba. ** Ranar da sati biyu ta cika ranar lahadi da sassafe Umaimah ta tashi ta yi wanka daman ta shirya kayanta a karamar akwati tun jiya. Bayan ta yiwa Dagaci, danginta da Makwabtanta sallama ta ce Gwamna yana nemansu a Gombe. Ba ta shaida musu daga Gombe ma Abuja zasu wuce ba duk da haka sai da ta ji gulmammaki ana ta yada zance wai kullum tana hanyar birni, kanta ya waye bata iya zaman Ruga. Shiyasa ta fi so duk in da zata je ta tafi da muharraminta Sabitu tana samun saukin zargin idan aka ga sun tafi su biyu akan a ga ita kadai ta ci kwalliya ta tafi birni. Dan ita ko kayan da take sakawa a tsakar gida ma masu kyaune da tsada balle ace na kwalliyarta data ware. SAI MUN HADU ZUWA GOBE INSHA ALLAH. Dan Aunty.MAKWABTAKA 47 Wani cancadeden leshi Umaimah ta saka baki mai fulawa koriya, aka dinka mata riga da siket da dan kwali, ta hada da takalmi mai tsini da gyale kore da bakar jaka. Sai kamshin turare da mayukan data shafa ya daki hancin *yan gida da makwabta daga fitowarta daga daki. Takaici ya kama Matawata a lokacin da ta jiyo muryar Umaimah da kaninta suna yiwa *yan gidansu sallama zasu tafi birni sai bayan sati uku zasu dawo. Matawata ta tabe baki ta harari maigidanta Ilah wanda yake zaune akan abun sallarsa yana lazinzumi. Ta ce ga *yar iskan birni can Umaimah za'a tafi birni yin sana'ar. A fusace Ilah ya juyo ya dube ta duba irin na tsana da fusata. Ya ce " Ba lallai ba ne dan mace ta yi karatu, ta waye, Allah Ya daukaka ta ganin Gwamna baya yi mata wahala sai a ce ta zama *yar iska. Wata macen a Ruga take zaune ba kudi, ba wayewa, ba illimin arabi babu na boko, da aurenta ma sai ta yi kwartanci a kama ta da mijin da ba nata ba. Baki da labari jahilci babban ciwo ne? Ai mai ilimi yana gudun ya sabawa Allah. Tabbas Matawata ta san dukka wannan mugayen halaye ita ya suffanta kuma da ita yake. Yana rufe bakinsa sai ta yi kukan kura ta shake shi yana zaune. Dakyar ya yunkura ya tashi zaune, dambe ya barke. Ya dake ta, ya sake daka san ransa daman ta ishe shi da rashin mutunci kala- kala tunda Umaimah ta dawo, yayin da ta dinga ihu tana yago fuskarsa da farata. Unguwa gaba daya ta cika da ihun Matawata, kasancewar sassafe ne ita kadai ake jiyowa. Hankalin kowa ya tashi musamman sirikan Matawata da iyayenta da kuma *ya*yanta da suka dinga tayata da ihun suma. Sai hankalin Umaimah ya fi na kowa tashi musamman data ji akanta aka barke da danbe. Ta ji kwata-kwata ta washi zaman garin nan, ta kudiri niyyar idan ta tafi yanzu ba zata dawo ba har sai ta gama bautar kasarta na tsawon shekara guda kuma Abuja zata zaba tayi zamanta acan duk abunda mutane zasu ce su ce. Kwatsam! Umaimah ta jiyo muryar Ilah ya furtawa Matawata saki daya, ai da saki uku ma zai yi aka dafe bakinsa manya suka hana shi. Bakin Matawata baya shiru bata daina kiran sunan Umaimah ba tana dirka mata zagi ba, tana fada tana sake maimaitawa Umaimah karuwa, shi kuma bai daina bi yana tafka mata duka ba muddin bata daina zagar masa abar kaunarsa ba. Babu wanda bai fito rabiya ba, mata da mazan unguwa harsu Baffa, Sabitu da su Nene amma Matawata bata ji nauyinsu ta daina dankarawa Umaimah zagi ba. Kofar gida ya cika dankar sai hayaniya ake yi babu wanda yabi bayan Matawata har iyayenta laifinta ita suka bawa laifi. Umaimah ta rushe da kuka ta koma daki ta zauna ta kudundine a lungu ta rasa me yake yi mata dadi. Baffa yana kuka ya shigo dakin Umaimah bayan da rigima ta lafa, dan an tura Ilah gidansa yayin da Matawata ma aka turata gidansu. Ya dubi Umaimah ya ce "Tashi ku tafi kada ki damu Allah Yana bayan mai gaskiya, shaidar duniya ita ce ta kiyama, duk wajen nan babu wanda baiyi miki shaidar arziki ba kowa yasan ita ce watsattsiya tunda mijinta ma ya fada kwartuwa ce, ke meye abin damuwa. Ki daure dai kiyi aure sai ki cire kage da zargi a zuciyar makiya. Umaimah ta gyada kai ta ce "Amin Baffa insha Allahu zanyi aure. Sabitu ya dora akwatinan kayansu aka, Baffa ya raka su har kofar gari, suka yi sallama, su dukka ukun kuka suke yi. A cikin mota ma Umaimah bata daina kwararar da hawayen bakin ciki da damuwa ba yayin da Sabitu bai fasa kwararo mata nasihohi da wa'azi ba har sai da zuciyarta ta yi sanyi kafin su isa birni. Sabitu ya ishe ta da Magiya akan ta daure ta shafa hoda da kwalli a fuskarta dan kada jama'a su gane ta yi kuka kasancewar idanuwanta duk sun kumbura sun yi jajawur. Kafin su sauka daga mota Umaimah ta goge fuskarta ta shafa hoda da kwalli kamar yanda dan'uwanta ya bata shawara, suka fito daga tasha zuwa bakin titi inda zasu hau tasi zuwa gidan Gwamnati. Karfe tara da rabi a kofar gidan gwamna ta yi musu, yayin da suka iske taro yayi taro kowa ya hallara, ga dogayen motoci da zasu kwashe su zuwa Abuja. Bayan anyi musu *yan muhimman jawabai takaitattu sai aka basu umarni su je su shiga motoci akai su Abuja. Ana fitowa sai ta ci karo da Baban Hanif a kusa da shi wani mutum ne dogo baki suna tsaitsaye a kusa da dogayen bus, ta durkusa ta gaishe su cikin ladabi. Bayan sun gaisa sai Baban Hanif ya juya ya dubi abokinsa ya yi murmushi. Ya ce "Ranka ya dade, gata ma ashe ta iso. Sai yanzu Umaimah ta gane shine Alh. Nura dan haka sai ta sadu da mummunar faduwar gaba, Alh Nura ya yi dariya. Ya ce "Na gane ta ai, na santa tun a Malaysia ita ce dai bata waye da ni ba. Umaimah ya kokari, za'a tafi bautar kasa ko? To Allah Ya yi jagora. Ta duka ta ce "Amin na gode. Sabitu ma ya duka ya gaishe su, sai Baban Hanif ya tambayi Umaimah "Shima wannan acan ku ka yi karatun amma ban taba ganin shi ba? Umaimah ta girgiza kai ta ce, "Bada shi muka je ba, kanina ne sunansa Sabitu. Su dukka suka hada baki "Malam Sabitu ya gari? Dadi ya rufe Sabitu ya ga manyan mutane suna gaishe shi, sai ya duka ya ce "Gari lafiya kalau. Aisha Bingyal ce ta taho a gigice tana neman Umaimah can ta hangota, ta karaso inda suke bata kula da wadanda Umaimah take tare ba ta jawo hannunta. Ta ce "Zo muje tun dazu Bilyaminu ya zo ya ce in nemo ki. Umaimah ta ji tamkar ta nutse a kasa dan kunya, ta fisge hannunta daga hannun Aisha ta fada a sanyaye. "Ki bari mu gama gaisawa da Baban Hanif. Sannan Aisha ta lura da wadanda suke tare nan da nan ta zube a kasa ta kwashi gaisuwa. Alh. Nura ya yi gyaran murya ya ce "Zaku tafi ko? Gara ku yi sauri ku kama hanya kada ku yi yamma dan ku samu ku fara 'registration' yau kuma za ku yi kwanan 'camp' Umaimah ta durkusa ta yi musu sallama cike da ladabi Aisha ma haka suka juya suka fara tafiya Sabitu yana biye da su a baya sai Alh Nura ya kira shi zuwa wajen motarsa bandir din kudi ya zakulo ya mikawa Sabitu *yan dari biya- biyar sababbi naira dubu hamsin kenan ya ce ya kaiwa Umaimah shi kuma ya zaro bandir din *yan dari-dari dubu goma kenan ya ce na sa ne. Farin ciki ya rufe Sabitu yana ta godiya har suka rabu. Umaimah ta sami jikin daya daga cikin dogayen motocin nan ta tsaya ta ki bin Aisha wajen Bilyaminu duk da magiyar da Aisha take yi mata bata amince ba. Sai dai Aisha ce ta je ta kira shi ya iso ga Umaimah ta kirkiro murmushi ta duka ta gaishe shi sai ta birge shi data durkusa masa ya tabbatar yarinya ce mai hankali ba irin *yan matan zamanin nan ba ne masu rawar kai. Ya shiga yi mata bayanai barkatai wadanda bata cika gane me yake cewa ba duk da yaren fulatanci yake magana. Ta kagu ya gama ya matsa ko zata sami saukin nauyin da kwakwalwarta ke faman yi mata. Sabitu ya kara so inda Umaimah take dan ya dade yana nemanta sai ya yi kasake yana kallon Bilyaminu tabbas yasan dole Umaimah ta shiga rigima, dan gaba daya masu sonta manyan mutane ne babu wanda ya zo da maganar wasa duk aurenta suke so suyi. Sabitu ya gaishe shi sannan ya gabatar masa da kansa duk da ba'a tambaye shi ba. Sai Alh. Bilyaminu ya saki jiki ya sake gaisawa da Sabitu. Ya dauko naira dubu ashirin daga aljihunsa ya mikawa Umaimah sai taki karba, sai ya mikawa Sabitu ya ce ya rike mata, ya bawa Sabitu dubu biyar, ya mikawa Aisha Naira dubu goma. Suka yi masa godiya ya yi musu fatan Allah ya kiyaye hanya. Ya ce Umaimah ta daure ta kunna wayarta zai kira ya ji idan sun isa lafiya, sanna ya juya ya tafi. Aisha Bingyal ma ta tafi tayiwa Babanta sallama dan shi ya kawo ta. Umaimah da Sabitu ne suka kebe a gefe suna maganar sirri, ya dauko himilin kudin Alh Nura ya bata da wanda ya bashi sannan ya dauko kudin da Alh Bilyaminu ya bayar, da ya hada kudinta dukka Naira dubu saba'in ne, nasa kuma dubu goma sha biyar. Umaimah ta saka gefen gyalenta ta matse hawaye. Ta ce "Sabitu yaya zanyi da raina? Ina zan kai wadannan mutane? Gashi kowa ka karbar masa kudinsa. Sabitu ya shiga damuwa sosai sai ya hau bata hauri yana bata shawara cewar komai ta fawwalawa Allah, Shi zai zabar mata abinda ya fi alkhairi. Umaimah ta gyada kai yayin da hawaye ya ki tsayawa daga idanuwanta. Ta ce "Yaya kake ganin zamu yi tafiyar nan? Ba yadda za'ayi mu tafi Abuja tare, ko ka bi ni Abuja ba yadda za'ayi mu zauna waje daya tunda mu sojoji ne zasu tsaremu a NYSC Camp ba zasu bari ka shiga ba sannan baka san Abuja ba balle in ce ka zauna a cikin gari ka jira ni. Kunyar Aisha nake balle in ce ka zauna a gidansu har mu je mu dawo sannan kuma bana so ka koma Dugge su ga an yi sati uku ban dawo ba Sabitu ya ce "Sai in kama hayar daki anan garin in zauna har ku dawo tun da ga kudi mun samu da yawa. Umaimah ta ce "Kana ganin babu matsala ba zaka takura ba, ka san garin nan ba zaka bata ba? Ya yi dariya ya ce "Adda Umaimah, mu ne fa garin nan, na san garin nan tun ina yawon almajiranci. Ta karbi Naira dubu ashirin ta saka a jakarta. Ta ce ya rike sauran ya kama daki ya dinga cin abinci amma ya yi hankali da kudin kada ya kashe dukka. Farin ciki ya lullube zuciyar Sabitu ya fada a bayyane "Na godewa Allah da Ya yi mu ni da ke a ciki daya, ke alkhairi ce a tare da ni shiyasa Allah Ya bar min ke. Rayuwata ba irin ta da ba ce, ta canza yanzu, Ada sai an rage jagwalgwalallan tuwo sannan a bani yanzu kuwa ki gani dubu sittin da biyar a hannuna. Sai ya surnano da wani zazzafan hawaye yayin dana Umaimah ta fi nasa fitowa. Ta ce "Idan muka yi sati ukun za'a tura mu wuraren da zamu shekara muna aiki naji ana cewa matan za'a dawo da mu cikin Gombe, maza ne zasu zauna suyi aiki a Abuja. Ka ga zamana a garin Gombe ma ni kadai matsala ne dan haka nake so idan na dawo zamu kama gida a garin nan sai ka auro Aliya Budurwar da kake so ka dawo birni, sai ku bani daki daya mu zauna tare har in gama bautar kasar idan ka sami cikakkiyar sana'a kaga zaka ci gaba da zama a Gombe to sai ku zauna, idan babu sana'a sai mu koma Dugge mu zauna idan kuma na sami aiki mai kyau da zai sa na ciyar da kaina da iyalinka sai mu zauna. Sabitu ya ji tamkar ta yi mishi albishir da gidan aljanna sai ya washe baki ya ce "Allah ma zai hore mana mu ci gaba da zama har mu gina gidanmu mu kwaso su Baffa su dawo birni. Me za'ayi da zaman cikin daji? Ke ma Allah Ya duba ki ya kawo miki wanda kike so Abdul-Sabur. Ta ji sanyi a ranta daya ambato mata sunan abinda tafi so a rayuwarta, bayan iyayenta da dan uwanta sai Abdul-Sabur. Ta sharce wani zazzafan hawaye. Ta ce "Ina jin rayuwata ta kusa karewa Sabitu, saboda ba zan sami Abdul-Sabur ba gashi ba zan iya son duk wadannan ba. Anya kuwa daga Abuja zan dawo garin ba tafiya zan yi a rasa ni ba? Hankali Sabitu ya tashi ya zabura ya ce "Kar kiyi haka Adda Umaimah, zamanki a kusa da mu shine arzikinmu, idan baki dawo dan ni da *ya*yanki ba zaki dawo dan Baffa saboda ya tsufa. Allah ne gatanmu ke ce gatanmu. Kina karamarki Allah Ya dora miki girma. Kin zamto kece uwa kece uba. Ta yi kasake tana mai gasgata maganar sa, tabbas bai yi karya ba idan ta tafi dukka mutanen nan da ya karanto rayuwarsu zata tawaya. Ta dago zata yi masa magana sai taga ya kurawa wani abu ido daga bayanta, da alama wani abu yake hange wanda ya bashi mamaki ko ya firgita shi. Nan da nan ta ji hankalinta ya tashi yayin data shiga fargabar waiwayawa kada ta hangowa kanta a binda ya fi karfinta. Sabitu menene, lafiya? Bai amsa mata ba yayin data juya da kanta a hankali ta dubi inda yake kallo sai kuwa ta firgice da taga ashe abun da yake kallo yana daf da ita, a tsaye a bayanta. Tayi sauri ta ja da baya ta labe a bayan Sabitu yayin da mamakin da Sabitu yake yi ya zama tamkar shafar mai ne akan wanda ta shiga. Bakinta ta dafe da hannayenta biyu saboda fatar bakin ta ki rufuwa, ta ji kamar ba'a wannan duniya take ba, mafarki take yi. Ta mika hannu a hankali ta mintsini Sabitu dan ta tabbatar ba mafarki take yi ba, sai ta ga ya zabura ya sosa wajen sannan ta tabbatar a raye suke. Ta sake shakar numfashi ta dire tabbas kamshin turaren nan 'Dolce Gabbana' ne yake dukan hancinta. Sai ta sake bude ido ta duba ta sake dubawa gaskiya ne abunda take gani ba gizau idanunta suke yi mata ba. "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai mai kowa mai komai. Haka ta fada a bayyane. Hawayen farin ciki ne ya fara kwararowa wannan karon, masu sanyi ne hawayen daga dukkan alamu Allah Ya amshi addu'arta. Jama'a ku taya ni canka wa taga ni ne haka? Allah mai amsa addu'ar bawanSa a lokacin da Ya so. Abdul-Sabur Abdul-Rashid ta gani a gabanta cikin kyakkyawar shiga farar shadda ce sol gami da yanayi na farin ciki a fuskarsa. Ta ji kamar ta daka tsalle ta rike shi sai ta saka gyalenta ta rufe ido ta yi magana cikin rada ta ce "Sabitu gashi nan. Sabitu ya tambayeta cike da mamaki "Waye shi? Abdul-Sabur ya yi murmushi ya karaso daf da su ya mikawa Sabitu hannu suka gaisa. Ya ce "Sunana Abdul-Sabur Abdul-Rashid. Nan da nan Sabitu ya gigice da murya ya yi kabbara gami da hamdala. Ya ce "Ka cika dan halak yanzunnan maganarka muke yi... Bai rufe bakinsa ba Umaimah ta zungure shi wai yayi shiru. Abdul-Sabur ya dubi Umaimah ya yi dariya. Ya ce "Kada ma ki hana shi fada na gama jin duk abunda kuke fada tun dazu nake tsaye a bayan motar nan da kuke jingine babu abinda ban ji ba. Yanzu da ki ka ganni maimakon ki zo wajena kuma sai kika koma gefen Sabitu ki ka labe. Ko in koma bakya farin ciki da ganina? Umaimah ta matso kusa da shi tana mai fara'a da dariya amma fa kukan dadi take yi hawaye faceface a idonta ta gaishe shi cikin muryar kuka. Ya girgiza kai sannan ya zaro hankici fari kal mai kamshi daga aljihunsa ya mika mata. Ya ce "Ba zan amsa miki ba kina kuka, goge hawayen ki Umaimah ki daina kuka, ina mai shaida miki daga yau kin daina zubar da hawaye muddin ina raye sai dai bayan raina in Allah Ya yarda. Farin ciki ya lullube Umaimah da kaninta a bayyane. Abdul-Sabur ya ce bamu da isasshen lokacin da zamu yi doguwar magana ina nan tare da Sabitu har ki je ki dawo. Umaimah da kaninta suka tsaya suna kallonsa duba irin na rashin fahimta, sai ya yi murmushi. Ya ce "Na ce kada ki damu ki je camp dinki ki fito zaki same ni tare da Sabitu anan zan zauna in jira ki. Ki je ki shiga mota ku tafi ga su Hanif can na hango suna ta shiga motoci da kayansu. Sabitu ya ta da jakar kayanta ya kai mata mota. Umaimah ta zama tamkar an zare mata laka kallon Abdul-Sabur kawai ta ke yi har yanzu da sauran kokonto a cikin zuciyarta tana ganin kamar mafarki take yi ta kasa yarda gaskiya ne. Tafiya ta ke a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tana tafe tana waiwayensa yayin daya tsaya cak yana kallonta shima, amma murmushi kawai yake yi ya san abun da yake damunta. Sabitu har but din motar da zata shiga ya kai mata akwatinta sannan ya shiga cikin motar har kujerar da ta zauna, ya yi mata sallama, ya yi mata rada bata san me yake cewa ba kasancewar hankalinta baya jikinta tana can tana kallon Abdul-Sabur. Motoci sun cika taf da dalibai kowa ya zauna yayin da motocin suka fara tafiya a layi. Idon Umaimah akan Sabitu da Abdul suke, tana kallonsu kawai yayin da su ke daga mata hannu, dariya kawai suke kyalkyatawa saboda sun ga ta susuce gaba daya ta zama kamar doluwa wacce bata gane komai. Alhali kuma ba doluwa ta zama ba ta kamu da mamaki mai tsanani ne. Ikon Allah Ya wuce da haka Umaimah Bello. Allah Ya kiyaye hanya !!! AI KAWAI SAI RANA ITA YAU ZAN CI GABA... Abdul-Sabur ya dawo ga Umaimah . Dole na sheke shi kawai... Dan Aunty.MAKWABTAKA 48 Har su Umaimah suka fita daga garin Gombe hankalinta bai dawo jikinta ba, tunani take kawai mai rikitarwa game da abunda idanuwanta suka gane mata. Aisha ta zungureta ta ce "Lafiyarki kalau kuwa, tunanin me kike yi haka? Kada fa ki damu kan ki akan wadannan mutane ki zaba ki darje a cikinsu babu na yarwa, gaba daya suna da abunyi kuma suna sonki. Amma ni nafi so a auri kawunmu Bilyaminu. Ko ba haka ba Khadija Jauro? Khadija da take zaune a kujerar gabansu ta waiwayo tana dariya. Ta ce "Gaskiya mu dai muna kamun kafa ayi mana kara a auri kawunmu, dan ya mutu a sonki kuma da gaske yake. Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta matse hawaye ta ce "Abdul-Sabur na gani ya zo. Aisha ta tsaya tana yi mata kallo irin na rashin fahimta har ta fara tunanin ko ta fara zautuwa ne. Umaimah ta dubi Aisha tayi dariya ta gyada kai ta ce "Da gaske nake na san abunda na ke fada a haiyacina nake. Ba ki ganshi ba a tsaye shi da Sabitu suna dagamin hannu? Aisha ta ja doguwar ajiyar zuciya ta ce "Na ga wani mutum fari, dogo, tare da Sabitu. Da gaske shine? Umaimah ta yi fari da ido ta dafe kirji ta ce "Yau kamar an jefa ni a aljanna nake ji, Allah abin godiya Ya amsamin addu'ata ya kawo min Abdul-Sabur. Ta kankame Aisha tana ta murna. Daga dukkan alamu itama ta taya ta murna duk da ta shiga tunanin yadda zata dubi idon Alh. Bilyaminu ta fada masa Umaimah ta sami mai sonta ba. Khadija ta waiwayo da sauri ta dube su, ta ce "Me nake ji kuna cewa, kawun nawa aka yiwa kishiya? Aisha ta kalli Umaimah itama ta kalle ta suka juyo gaba daya suka kalli Khadija a firgice ba tare da sun san me zasu ce mata ba, dan maganar tana da nauyi da kuma kunyar fada. Umaimah ta yi murmushi ta fara magana cikin tausayawa ta ce "Banki kawunki ba Khadija, amma wanda nake maganar sa shine wanda muka yi alkawarin aure da shi shekaru biyu da suka wuce. Khadija ta yi murmushin karfin hali ta gyada kai ta ce "Shikenan ba damuwa Aisha zamu san yadda zamu fadawa Kawu zai fahimce mu. Umaimah zamu so ki auri wanda kike so kema dan mu ma nan da kika ganmu duk wadanda muke so muka zaba mu aura. Aisha ta ce "Gaskiya ne Khadija, kowa yana so ya auri wanda yake so. Umaimah ta ji dadi da suka fahimce ta sai ta yi dariya ta yi musu godiya. Sannan kowaccensu ta juya ta ci gaba da karanta littafi da take karantawa (novel). Umaimah ta zaro wayarta ta kunna yayin da sakonnin suka dinga shigowa rututu wasu daga Faduwa na gaisuwa ne, wasu na Alh Bilyaminu na so da kauna ne, wasu daga Alh Nura tambayarta yake yi yaushe zata shigo gari. Sai wasu sakonni da yawa da wata lambar MTN. Ta cika da mamaki a lokacin data fara karanta sakonnin da aka turo mata da sabuwar lambar, sai daga karshe ta gane mai sakon daya rubuta sunansa Abdul-Sabur. Masha Allah!!! Ta cika da murna da ta sami lambar Abdul-Sabur amma ta shiga mamakin yadda aka yi ya sami lambarta. Bata gama dubawa ba ta ji an kira ta da lambar, sai ta tabbatar rabin ranta ne ya kira ta. Sai kuwa ta yi sauri ta amsa muryarsa kadai ta ji yana yi mata sallama sai ta lumshe ido dan dadi. Abdul-Sabur ya ce "Gani nan da kanina Sabitu muna maraici kin tafi kin barmu. Umaimah ta yi murmushi ta girgiza kai ta ce "Allah Sarki, ai zan dawo kwanannan. Ina ka sami lambata naga sakonninka yanzu dana kunna wayar? Ya yi dariya ya ce "Ni dana damu da ke ai duk motsinki na sani, haka a Malaysia ba ke kadai ki ke rayuwa ba ina biye da ke har ranar da kuka tafi filin jirgi za ku taho Nigeria. Ta dafe kirji ta bude baki tana mamaki ta fada da karfi, har su Aisha suka dago ido suna kallonta Ta ce "Da gaske? Me yasa kayi mana haka? Meye hujjarka da kayi hakan? Ya yi dariya ya ce "Ina da hujjoji masu yawa sai mun hadu zan fada miki dalilina na yin haka. Yanzu zamu tafi da Sabitu 'Emerald Royal Hill Hotel' acan na ke daman mu ci gaba da zama, dan satina biyu a garin nan yanzu. Mamaki ya sake lullube Umaimah har ta ji ta fara tsorata da al'amuran Abdul-Sabur. Ya yi mata fatan Allah Ya kiyaye hanya, suka kashe waya. Hotel suka nufa a cikin tsaleliyar motarsa 'ACURA' dakin Sabitu na kusa da dakin Abdul-Sabur. Dadin duniya dai Sabitu yana ji a wannan yanayi na zaman Hotel duk da sai da Abdul- Sabur ya yi kwana biyu yana gadinsa yana nuna masa yadda zai yi amfani da kayan ciki. Famfon ruwan sanyi dana zafi bandaki, kunna Ac karawa da ragewa, kunna talabijin da kashewa. Amma daya koya masa ya gane sosai sai yake cin gashin kansa shi kadai a dakinsa. Abdul-Sabur ya cika masa firij da yake dakin kayan dadi kala-kala, sai da azahar suke fitowa suyi sallar azahar a masallacin kusa da Hotel din, sannan su shiga mota su shiga gari. Manyan gidajen cin abincin garin ba wanda basa zuwa, haka duk wani wajen shakatawa na garin sun je sun huta kamar 'Kanawa Forest' da Zamfarawa, dan haka tun Sabitu baya iya shan ice cream da su shawarma sai da ya koya zama da Abdul-Sabur. Idan Sabitu ya ci ya koshi baya sanin sanda yake yage baki yayi ta bawa Abdul-Sabur labarin abunda ya faru game da rayuwar Umaimah. Tabbas Abdul-Sabur ya gamsu, ya daina tantama Umaimah tana sonsa ko bata sonsa kamar yadda Faduwa ta bashi labari. Ya kudiri niyyar aurenta dan bashi da matar data fi dacewa da rayuwarsa irinta don ita ce kadai macen daya taba ji yana so a rayuwarsa. "Sabitu meye abun yi, daga ina zan fara neman auren Umaimah? Tunda daman ni da ita mungama fahimtar juna ni take jira. So nake in bata mamaki kafin ta dawo an gama shirya magana komai. "Abdul-Sabur ya tambayi shawara. Ya yi gyaran murya gami da gyara zama dan ya ji tambayar babba ce. Ya ce "Gaskiya babu abinda Baffa ya fi so irin ta yi aure a cikin *yan kwanakin nan kuma ta yarda ta zabi wanda take so ta aura ko wanene. Ta bamu labarinka tatas ni da Baffa dan haka ya sanka. Yanzu mu je ka gaishe da Baffa, Dagacin garinmu da sauran tsofaffin garin. Tabbas jama'ar garinmu ba zasu karbe ka ba zasu kushe ka, zasu ce kai bare ne ba'asan asalinka ba. Duk da daman cewa zamu yi kai dan Gwarzo ne ba zamu ce kai dan Ghana ba ne. Amma kada ka damu in dai Baffa ya yarda da kai Dagaci zai yarda da kai musamman idan aka aika masa kyautar Shaddoji da Yadina, sauran mutanen duk su gama surutunsu sai mu toshe kunnuwanmu. Abdul-Sabur ya yi dariyar jin dadi ya lumshe ido. Ya ce "In dai dan wannan ne an gama, ba damuwa gobe sai mu kama hanyar Dugge. Haka kuwa aka yi washe gari da safe, babbar kasuwar suka nufa a inda suka yi ta jidar shaddoji, yadiddika da atamfofi masu yawan gaske suka cike but da kujerun bayan motan, sannan ya sayi lemuna (juice) katan-katan har sai da Sabitu ya dinga hanashi saboda sayayyar ta cika yawa. Suka dinguma suka shiga Dugge da hantsin ranar lahadi a lokacin satin Umaimah biyu da tafiya. Daman motar na shiga garin, *yan garin suka tabbatar Umaimah Bello ce, ai kuwa a kofar gidan motar ta tsaya. Sai aka tsaitsaya ana jiran aga fitowarta daga mota da irin shigar da ta yi a yau, sai suka ga wayam! Babu Umaimah daga Sabitu sai tsalelen bako daga gani babu tambaya kudi ya ratsa shi. Baffa ya fito cike da dimbun mamaki amma ya cika da fargaba da bai ga *yarsa ba, fadi yake yana sake maimaitawa "Ina Umaimah, ya banga Umaimah ba? Da fatan tana nan lafiya? Sabitu ya yi sauri ya amsa masa dan ya ga tsoho ya shiga damuwa da yawa. Ya ce "Umaimah tana nan lafiya kuma cikin koshin lafiya da dinbun farin ciki da kwanciyar hankali. Sai Baffa ya yi ajiyar zuciyar jin dadi sannan ya juya ya dubi Abdul-Sabur ya yi masa fara'a da sannnu da zuwa, kallo irin na rashin fahimta Baffa yake yiwa Abdul-Sabur. Da sauri Sabitu ya shiga cikin gida dan ya daukowa bakonsa tabarma dan ya zauna, dan yaga Baffa da su Nene sun bi layi suna kallonsa kallo irin na kauyanci. Inna ce ta bi Sabitu tana tambayarsa, suna neman labari su ji waye shi daga ina ya zo kuma me ya zo yi? Sannan a ina suka baro Umaimah? Sabitu bai bata cikakkiyar amsa ba cewa ya yi "Idan tayi tsami zaki ji Inna, me kike ci na baka na zuba. Ke da bako ya sauka a gidanki. A zauren kofar gida aka yiwa Abdul Sabur shimfida suka zauna tare da Baffa, Sabitu na zaune a gefensu. Baffa yayi-yayi da Sabitu ya daukowa bako ruwa. Sabitu ya ce "A koshe yake. "Ya aka yi ka san a koshe yake? Inji Baffa. Sabitu ya ce "Ko ni dana rabe shi a koshe nake, yanzu ba zan iya shan wannan bakin ruwan na garinku ba balle shi. Su dukka suka kyalkyale da dariya. Bayan Abdul-Sabur ya gaishe da Baffa sai ya tambaye shi lafiyar mutanen gida, sunayen su Nene fal a bakinsa. Sai Baffa ya sake cika da mamaki ya san ko waye wannan ya yi musu farin sani amma abun daure kai shine bai taba ganinsa ba a rayuwa. Sabitu kadai zai warware wannan dabaibayi, ya gyara zama ya fara yiwa Baffa bayanin ko waye Abdul-Sabur da kuma abunda yake tafe da shi. Tabbas daga gani babu tambaya Baffa ya yi farin ciki matuka kuma yayi amanna da wannan magana, baya kokonto saboda yasan Umaimah shi take bege kuma take jira. Ya yi musu fatan alkhairi da fatan ayi biki lafiya. Babu abinda Abdul-Sabur yake yi sai washe baki da godiya, ji yake yau kamar an bashi mukullin aljanna. Ya gyara zama ya dubi Baffa akunyace, sai ya sunkuyar da kai kasa ya sosa keya. Ya ce "Baffa inaso ayi bikin nan da wata uku ko biyu. Amma yaya ka gani? Sabitu ya ce "Nan da wata guda ma mu a shirye muke. Baffa ya ce "Eh to ban ki ta taku ba, amma a bari dai Umaimah ta dawo sai mu ji sanda take ganin zata gama shirinta, ni yanzu ai ba nine da magana ba tunda babu abinda zan yi mata. Abdul-Sabur ya gyara zama ya ce "Baffa ai ina ganin babu wata siyayya da Umaimah zata yi daga kayan sakawa, kayan daki, ko abincin *yan biki duk ni zan yi. Baffa ya ji hawayen dadi ya rikito masa babu shiri ya barke da kuka. Musamman da Sabitu ya fara jido masa Yadiddika da Shaddoji da katan-katan din lemuna (juice) yana jifgewa a gabansa sai da zauren nan ya cika makil. Baffa sai fadi yake yana sake maimaitawa "Menene wanan? Na maye wannan? Ina zan kai duk wadannan kaya? Abdul-Sabur ya ce "Baffa duk naka ne ka diba ka dibarwa *yan uwa da abokan arziki. Baffa ya girgiza kai ya ce "Abdul-Sabur wannan ya yi yawa ai sai a zage ni a gari ace naga wanda yafi Abdul-Basi kudi shiyasa na bashi *yata. Sabitu ya zabura ya ce "Baffa ina ruwanka da jama'a? Ka rabu da mutum ka kama Allah babu abinda bil'adama zai yi maka banda ya kai ka ya baro ka, ya dawo yana yi maka dariya idan ta kwabe. "Kirawo su Nene suzo su gaisa da surukinsu. "Baffa ya aiki Sabitu. Sabitu ya kira su daman a shirye suke da gyaleluwansu a yafe a jikinsu, sai suka yi zuruf suka biyo shi. Suka zo suka zube a gabansa, nan da nan Abdul-Sabur ya tsuguna ya gaishe su. Baffa ya nuna musu Abdul-Sabur ya ce shi zai auri Umaimah, ai kuwa kowacce sai da ta zabura suka hau kallonkallo cike da rashin fahimta. Baffa ya sake nunnuna musu wadannan himilin kayan da ya kawo musu sai suka hau murna suka calla buda. Suka taya Sabitu jidar kaya suka yi ta lodawa a dakin Baffa har ya zamanto babu inda mutum zai sa kafa. Baffa, Sabitu da Abdul-Sabur ne suka tafi gidan Dagaci, bayan Baffa ya aika a kirawo duk wani shahikinsa, da abokinsa ya zo gidan Dagaci zasu gaisa da bako. Ba'a dauki lokaci mai tsawo ba aka taru. A sanda aka fara bayani zuciyar Abdul-Sabur ce take ta harbawa dan fargaba kada a sami wadanda zasu hana a bashi farin cikin rayuwarsa Umaimah. Sai ya shiga karanto musu addu'a. Baffa ya gabatar da Abdul-Sabur sai kowa ya zura masa ido yana kallo, a kunya ce ya duka ya sake gaishesu irin ta girmamawa duk da wasu basa iya jin Hausar sosai sai fillanci. Koda ya fara fadar abunda yake tafe da Abdul-Sabur sai waje ya rude da hayaniya. Wasu harda fada da kumfar baki wai ina za'akai maganar Abdul-Basi? Amsar da Baffa ya basu shine Umaimah ta ce bata son ta sake zama da Abdul-Basi saboda wulakancin da yayi mata abaya. Dagaci ya ce abari yarinya ta dawo a tambaye ta wanda tafi so shi za a bata. Sabitu ya zabura ya ce "Ga wanda Umaimah tafi so dan ita ta bada izini ya kawo sadakinta yanzu. Aka hau kallon-kallo a tsakaninsu dan sun ji magana ta nutsa ba ma kudin na gani ina so ba ko kudin gaisuwar uwa da uba kudin sadaki gaba daya Sabitu ya ambata. Dagaci ya ce "Ba za a karbi kudi a hannunsa shi kadai ba sai ya kawo magabatansa sannan a binciki asalinsa. "Ba damuwa, wannan mai sauki ne, haka kuma ya kamata. Iyayena zasu zo kuma za'a zabi wasunku a je garinmu a gani. "In ji Abdul-Sabur. Sai ya fara musu yayyafin Naira suka fara washe baki. Sabitu ya ce "Ai godiya tana gaba idan na je na dauko muku himilin kayan daya kawo muku ku da matanku. Baffa ya ce, Sabitu ya je ya dauko musu ya bar kadan. Babu wanda bai sami yadi da atamfar matarsa ba kala dai-dai, na Dagaci kuwa daban ne sunfi tsada sun fi yawa. Sai ka ji bakin masu zakewa dazu yayi lukus babu abinda yake tashi a wajen sai kalmar albarka da ake jerowa AbdulSabur. "Ina Umaimah? Kowa sai ya tambayi Sabitu. "Tana wajen bautar kasa. Inji Sabitu "Au kasar ma bauta mata ake yi? An bar Musulunci kenan. In ji wadanda basu fahimci abunda ake nufi ba. Sabitu da Abdul-Sabur suka sha dariya har suka godewa Allah. Karkara kenan!!! Abdul-Sabur ya yi sallama zai koma Baffa ya ce sai Sabitu ya zauna ba zai bishi ba. Zo ka ga tashin hankali a idanuwan Sabitu, a yaren Hausa da fulatanci babu kalmar da bai furta ba dan yiwa Baffa bayanin da zai gamsu cewar zamansa a birni shi yafi masa alkhairi, kai har da guntayen turanci daya koya a wajen Abdul-Sabur da Umaimah a dan zaman da suka yi saida ya yara. Abdul-Sabur ma ya taya shi bawa Baffa baki, sannan ya hakura ya bar shi suka tafi tare. Banda dariya babu abinda suke yi a hanya, musamman Abdul-Sabur ya sha dariya. Kafin su fita daga garin sai da Sabitu ya roki Abdul-Sabur ya tsaya akofar gidan rabin ransa Aliya. Ta fito suka gaisa da masoyinta wanda Allah Ya yiwa lidifi ya sha kwana nan da nan, babu kamarsa duk a samarin garin. Abdul-Sabur yayi mata kyautar bajinta yayin da Sabitu ya shiga cikin gidan ya gauraye iyayen da kannenta da ruwan Naira. A take mahaifinta ya sanar masa shi kadai suke jira ya fito a daura aure. Sabitu ya tabbatar musu da zarar Umaimah ta dawo za'ayi komai, watakila ma a hada bikinta da nasu ayi tare nan da wata biyu. Murna wajen Aliya da iyayenta bata misaltuwa, suka yi musu rakiya har bakin kofar mota suka ga tafiyarsu. Abdul-Sabur ya kara tausayawa rayuwar Umaimah, ko a labarin data basu bai zaci haka Rugar take ba kauyen kayayau, basu san ma anci gaba ba a duniya rayuwarsu kawai suke yi a cikin daji. Sai ya shiga mamaki ace anan aka haifesu iyaye da kakanninsu. Ya kudiri niyyar aurenta da taimaka musu, su ma suji dadin da *yan birni suke ji. Bayan tafiyarsu da kwana biyu sai ga iyayen AbdulSabur maza a cikin mota bus sun iso garin Gombe daga Gwarzo. Tuni harya musu waya ya sa sun shirya tahowa, aka kawo su a cikin daya daga cikin motocinsu na haya daya rabawa *yan uwansa marasa aikin yi suna jigila suna samun na cefane. . NADAWO YAN UWA INA MAI BAKU HAKURI NARASHIN JINA KWANA2 SAKAMAKON WASU DALILAI AMMAN YANXU INSHA ALLAH NADAWO ZANCI GABADA SUBURBUDO MAKU LABARIN MAKWABTA INSHA ALLAH NINE DAI NAKUMAKWABTAKA 49 Kafin su karaso ya riga ya tanadar musu dakunan da zasu sauka a Hotel din da suke, dan su huta, suna isowa suka ci abincin da suke so. Washe gari aka dunguma su dukkansu tare da Sabitu da Abdul-Sabur suka tafi Dugge. A gaban Dagaci aka dire komai gami da kudinsa na aure, sun karbi kudin amma a bisa sharadin sai an bisu garinsu Gwarzo an gani, dan haka aka zabi zakakuran maza guda biyar harda mahaifin Ilah Baba Jani aka tafi da su. A ranar aka wuce Gwarzo kasancewar dare bai yi ba. Abdul-Sabur bai bi su ba shi da Sabitu suka ci gaba da zaman jiran Umaimah a Gombe. Kwana biyu su Baba Jani suka yi a Gwarzo suka dawo Gombe wajen Abdul-Sabur cike da farin ciki saboda an karbe su sosai sun ji dadin zama da Kanawa. Da suka je Dugge suka korawa Baffa bayani sai kowa yayi amanna da wannnan aure. Gari gaba daya ya dauka Umaimah zata auri Bakano, masu kushewa nayi saboda hassada irin su Matawata, masu yabawa nayi irin su Ilah, gashi dai yana matukar takaicin rabuwa da wacce yake so, amma ya san ya rasa ta har abada dan haka tsakaninsa da ita sai addu'a da fatan alkhairi. Asuba ta gari Ilamaima!! *** Ranar da su Umaimah suka cika sati uku cif a NYSC Camp da yake kuwa, ranar ne zasu fito daga camp za'a bawa kowa takardar da zai kai in da zai yi aikin bautar kasa. Yawanci dai duk inda ka cike takarda nan za'a kai ka kamar yadda su Umaimah suka cike Gombe can din dai aka basu. Amma ba'a fara raba musu takardun ba sai da suka gudanar da fareti ga FCT Minister. Taro yayi taro kusoshin Nigeria sun hallara a safiyar wannan rana ta litinin. Umaimah Bello ce a gaba dauke da tutar Nigeria a hannunta a lokacin da ake gudanar da faretin, su dari biyu aka zaba masu yin fareti daga cikin dubban *yan bautar kasa. Bayan Umaimah an zabi Aisha Bingyal, Hanif da wasu maza guda biyu sune daga Gombe. Umaimah bata ankara ba sai ta tsinci Abdul-Sabur a gabanta yana daukarta a hoto, tabbas ya bata mamaki dan ko a ranar sun yi waya amma bai fada mata ya zo gari ba. Ta hango Sabitu ma a gefe ko shima sunyi magana a waya a safiyar nan amma bai fada mata suna Abuja ba, dan Abdul-Sabur ya saya masa waya yanzu, ashe ma a lokacin suna Abuja dan ta san anan suka kwana, ba zai yiwu ace ranar suka zo ba. Da aka gama fareti sai FCT Minister ya fara bayanai yana basu shawara da nasihu akan su zama *yan kasa na gari masu rikon amana dan su ne manyan gobe da zasu zama shugabannin kasar nan. Aka dauki lokaci mai tsawo, da ya gama jawaban su Umaimah suka raka su shi da *yan rakiya har mota da fareti. Hakika faretin bana ya yi kyau sosai an tsara shi, kuma kayan NYSC ya yiwa Umaimah kyau sosai, Sabitu da Abdul-Sabur sun yi farin ciki da ganinta a cikin wannan fareti abun alfaharinsu ne. Bayan tafiyar shugabannin sai kowa ya nufo inda dan uwansa yake. A lokacim da su Aisha Bingyal suka nufi wajen wakilan Gwamnan garinsu da aka turo, ita kuwa Umaimah sai ta nufi wajen rabin ranta da dan uwanta, sai suka hautsine da murna. Matan dukka Gombe aka dawo da su mazan ne zasu yi a Abuja, dan haka a dunkule aka basu takardarsu zasu tafi da ita can za'a rarraba su in sunje. Abdul-Sabur ya tambayeta in da take so a kaita, ta ce makarantar sakandire ta garin Dukku take so ta je ta yi koyarwa amma ta ji ana cewa duk wacce tayi computer banki za'a kai ta. Sai yayi murmushi ya ce aransa "Waye zai bar ki, ki wahalar da kan ki kiyi aiki a banki? Babu yadda za'ayi ta bi su Abdul-Sabur a motarsu saboda dukka za'a dunguma a koma kamar yadda aka zo. Dakyar ta bawa Abdul-Sabur hakuri ya hakura ya kyale ta dan cewa yayi ba zata shiga bus ba sai dai su tafi tare da ita a motarsa. Sun jima suna hira sannan ta tafi ba dan taso ba sai dan kowa ya shiga mota da kayansa, ita kadai ake jira. Haka ma Abdul-Sabur bai so ya rabu da Umaimarsa ba amma ya dangana ya san anjima zasu hadu, a Gombe. Sai ga su Abdul-Sabur sun rigasu karasawa da yamma likis, nan ma haka sai da aka sha jawabai a sakateriya sannan aka sallame su bayan an bawa kowa takarda ta cike inda take so tayi aiki, suka tafi akan su dawo gobe su ga inda aka kaisu sai su fara registration. Da aka fito daga sakateriya sai ta hadu da su Abdul-Sabur, yake tambayarta yadda take so ayi. Ita kanta bata san yadda zata tsara rayuwarta ba saboda dai zamanta a Gombe ita kadai ba zai yiwu ba. Ta san dai yau a gidan su Aisha Bingyal zata kwana washe gari zasu je in da zasu kai takarda sauran zaman kuma bata san yadda zata yi ba. Abdul-Sabur ya bata shawara kada ta damu kanta wannan mai sauki ne shi yasan yadda zai tsara mata, ta yarda da hikimarsa dan haka bata damu da sai ta ji abunda yake shirin tsarawa ba, tasan zai yi mata yadda take so. Shi ya dauke su a motarsa ita da kawarta ya kai su gida, suka tsayar da shawara gobe zai dawo ya kai ta sakateriya da bankin da zata kai takarda. Abdul-Sabur da Sabitu suka koma Hotel din da suke yayin da Umaimah da kawarta suka shiga cikin gida bayan sunyi wanka, salla da cin abinci. Dan dare ya yi, sai suka kwanta amma bacci ya gagara babu abinda suke sai sabon babi da suka bude na hirar Abdul-Sabur. Aisha ta kalli kawarta Umaimah ta yi murmushi ta ce "Naga alama angon nan naki yana ji dake fiye da yadda kike ji da shi. Dadi ya lullube Umaimah ta yi dariya ta ce "Allah ko? Ashe kin lura da haka abinda nake fada miki kenan ada kika kasa fahimta ta. Abdul-Sabur daban ne da sauran maza, yana da tausayi matuka da kulawa ba'a cika samun namijin da zai iya dawainiya da matarsa ba irin yadda yake yi, halinsa ne kuma a cikin jininsa. Aisha ta harare ta, ta ce "Daman na san yanzu zan ji bakinki radai kina bayani, in dai akan AbdulSabur ne kin fi kowa iya bayani. Yanzu mu duk kin watsar da namu mazan da muka kawo miki, da kika sami Abdul-Sabur ko? Ya zaki yi da Baban Hanif da ya kawo miki abokinsa kika ki aurarsa? Umaimah ta ce "Wannan ai mai sauki ne tuni ma aikin gama ya gama, mun yi waya da shi na masa bayanin komai kuma ya gamsu da ni. Shi mai ilimi ne kuma mai ganewa, yayi min addu'a gami da fatan alkhairi. Ya ce in bari ya san yadda zai fadawa Alh. Nura yadda ba zai damu ba. Kin san Baban Hanif ya san Abdul-Sabur sosai a waya ashe a ranar ma Hanif ya kai Abdul-Sabur sun gaisa da Babansa. Kinga tunda shi ba yaro ba ne ai zai gane akwai soyayya a tsakaninmu tunda ya biyo ni har Nigeria. Aisha ta yi tagumi tana kallon bakin Umaimah a lokacin da take zuba bayanai. Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yanzu shi Abdul-Sabur din da maganar aure ya zo, ya fada miki zai aure ki? Umaimah ta ji zuciyarta ta harba da ta ji wannan tambaya ta yi shiru can ta girgiza kai ta ce "Muna waya kullum amma bai ce min komai ba haka Sabitu ma bai ce min komai ba. Aisha ta ce "Ta yaya kikasan zai aure ki bai auri wancan baturiyar ba da aka bashi? Umaimah ta yi shiru can ta sulale ta kwanta ba tare da ta sake yin magana ba haka ba bacci ba ne ya dauke ta ba tsabar jujjuya maganar Aisha take yi a cikin kwakwalwarta. Tana jiyo munsharin Aisha tuni bacci ya dauke ta, ita kuwa fargaba ta hana ta. Amma ta kan tuna abunda Abdul-Sabur ya fada mata aranar da zasu tafi Abuja a bakin mota, ya ce ta daina kuka in dai yana raye karshen hawayenta ya zo. Tana mai tsananin fargaba kada dai ace Abdul-Sabur ba da aure ya zo mata ba. Wa zata aura, a ina zata saka ranta da zaman garinsu? Asuba ta gari Umaimasabur!! *** Washe gari karfe goma na safe a kofar gidan su Aisha Bingyal ta yiwa Abdul-Sabur da Sabitu daman sun yi waya ta shirya dan haka suna fada mata sun iso sai ta fito a shirye tsaf cikin kayanta na NYSC. Kayan nan sun yi matukar yi mata kyau, kamar dan ita aka yi. Ta shiga gidan baya ta zauna ta gaishe su sannan ta fadi inda za'a fara zuwa, sun zama *yan gari sai taga sun kutsa ta hanyoyin da bata taba sani ba. Ko ina aka zo wucewa sai ta ji Sabitu ya ce "Ga inda muka zo ran nan cin kifi, kaza ko shan askirim. Tabbas ta gastata Sabitu ba karamar hutawa ya yi ba a cikin sati ukun nan tana iya ganin shaida a jikinsa. Fatarsa ta yi luwai-luwai, ya goge wajen saka suturu sababbi, ga wayewa wajen iya magana har dan turanci yake jefawa. Tabbas Abdul-Sabur alkhairi ne a rayuwarta, saboda ta dubi yadda ake tarairayar dan uwanta balle ita. Sabanin Abdul-Basi wanda ko doguwar hira baya yi da ita balle kaninta, ta san da Abdul-Sabur ne ba zai yadda akai Sabitu yawon Almajiranci ba a wancan lokacin ba. A makarantar boko zai saka shi. Kafin azahar Abdul-Sabur ya gama taya Umaimah yin komai, amma ya kirkiro wasu dalilai da dole sai an yarda da shi, aka bata hutun sati biyu kafin ta fara zuwa aiki, GT bank aka kaita. Abdul-Sabur ya ce da ita idan tana so ta tafi Dugge yanzu ta dauko kayanta su tafi idan kuma tana so ta kara hutawa su bari gobe da sassafe sai su tafi. Har ta ce gara su tafi ayau, sai Sabitu ya ishe ta da magiya akan ta bari ta sake hutawa sai su tafi gobe. Ta san abunda yake nufi kauyen ne baya so ya koma, zaman birni yake so sai ta tausaya masa ta bari sai goben. Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce mata "Ke ce *yar kauye, an rufe ku har tsawon sati uku a daji daga ku sai sojoji, bari a zagaya gari da ke ayi miki sayayya ki dan sha Ice cream. Ko Sabitu? Umaimah ta kyalkyale da dariya ta ce "Ba zan ci amanar kawata ba in je in sha ni kadai in barta, mu biya mu dauko ta ita ta ma fini sha'awar shan Ice cream. Abdul-Sabur ya ce "Kira ta awaya mu ji in da take sai mu je mu dauko ta. Da Umaimah ta kirata a waya sai ta shaida musu tana sakateriya, ta kare abunda take tana jiran direba ya zo ya mayar da ita gida. Umaimah ta ce "To gamu nan zamu zo daukar ki, ki hana direban zuwa. Bata dade tana jiransu ba suka bayyana a gabanta, ta shiga mota suka tafi. Aranar babu abin da basu ci sun bari ba haka kuma suka ciko ledoji da himilin siyayya, kama daga kayan kwalliya zuwa kayan ciye-ciye. Umaimah sayayyar wata guda ya yi mata, duk wani abu da zata nema ya saya mata har da kayan abinci, sai da but din motarsa ya cika taf! Da kyar yake rufuwa dashi zasu tafi Dugge gobe. A take Aisha ta gasgata cewar Abdul-Sabur ya bambanta da sauran mazan Africa, ba dukka ba ne suke da irin wannan. Ta yi amanna kawarta ta aure shi, dan shi ya fi cancanta ta aura duk a cikin mazajen da suka fito nemam aurenta. Daman dai shi take so idan ma bashi ta aura ba ba zata sami nutsuwa ba. Ba su dawo gida ba sai da magaruba Aisha ta jidi ledojinta cike da kaya tana ta godiya suka shiga gida, Umaimah bata dauki komai ba banda ledar Yogot da lemuna sai snakc wanda zasu ci a cikin dare amma sauran sai a Dugge. Bakin Sabitu kadai take kallo yayi jage-jage da naman kaza, Ice cream kuwa robar kawai yake kafawa a baki yayi mata shan koko, a take yake wurgar da dan tsinken da ake hadowa a cikin robar Ice Cream din, dan ba zai bata lokacinsa ba wajen cakula. Hararar duniyar nan da kifta ido Umaimah ta yi masa dan ya fahimta ya ja aji amma ina! Abu ya ci tura. Ba Abdul-Sabur take ji ba, Aisha ta fi ji ana harkar yanga shi kuma yana kwafsawa. Ta kudiri niyyar mayar dashi makaranta ko ta yaki da jahilci ce ba zai ci gaba da zama da duhun kai ba. Ta fuskanci Abdul-Sabur yana san Sabitu sosai, yana bashi dariya yana kyakyatawa, shi yake zuga shi ma yake sake tuburewa. Da su Umaimah suka shiga gida da kawarta suka sami abun yi wato hirar Abdul-Sabur, suna yaba irin kirkinsa. Haka ma Abdul-Sabur da Sabitu babu abin da suke yi sai hirar Umaimah suna yaba nutsuwa, hankali da mutuncinta. Asuba ta gari. *** Karfe tara na safe suka fito garin Gombe suka kama hanyar Dukku tafiya suke cikin lafiyayyiyar mota mai sanyin AC, gami da sautin kida mai dadi, wakarta ya saka mata ta 'Akuri Afomsa' bayan ya bata wancan CD ashe yana da wasu. Ta yi dariya ta ce "Bayan na kwace maka wancan ya aka yi ka sami wani? Ya yi dariya ya ce "Saboda ke na samo wani nakeji kullum, kin sa nima yanzu ina son wakar nan. Haka dai suka yi ta hira nan da nan suka ga sun isa Dugge, babu gajiyar tafiya a tare da su. Sai su Umaimah kwatsam a Dugge yayin da yara suka baibaye bakin mota suna tsalle, sun ga Umaimah mai basu alewa ta zo. Suka taya Sabitu jidar kayan aka kai cikin gida, dakin Baffa. Zo kaga washe baki da murna a wajen su Nene, yanzu kam suna son Umaimah dan ta zama mutum, basa kyararta. Muryar Matawata Umaimah take jiyowa ta jikin zana tana gidan iyayenta, tana ta zage-zage tana habaice-habaice. Wai duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba tasa ko dumi ba zata yi ba. Tunda Umaimah ta hanata zama a gidan mijinta itama kuwa idan tana raye ba zata barta ta yi aure ba sai dai idan babu bokaye a gari. Hankalin Umaimah ya tashi ranta ya baci sai ta fara kuka, su Nene suka kaita daki suna lallashi, suka ce kada ta kula ta. Matawata ta zautu bata da cikakken hankali, Ilah ya ki mayar da ita ya ce har abada baya sonta shine ta zama kamar me tabin hankali. Baffa da Abdul-Sabur ma suka shigo tsakar gida suka ji da kunnensu abunda take cewa sai suka shiga har dakin Umaimah suna bata hakuri. Allah Sarki yarinya ta zo da farin cikinta amma har an bata mata rai, ta shiga fargabar yadda zata kasance da ci gaba da zama da Matawata a matsayin Makwabciyarta ta din-din-din. Abdul-Sabur ma ya ji hankalinsa ya tashi, dan ada jita-jita yake ji bai san abun har ya kai haka ba. Da suka koma zaure suka kebe Baffa ya bashi labarin abunda ya faru tatas a ranar da Umaimah zata tafi, Sabitu yana karin bayani. Abdul-Sabur ya gyara zama ya shawarci Baffa, ya ce "Gara a yi sauri ayi bikin nan daga nan zuwa wata guda saboda kada ma zamansu tare ya tsawaita ta ci gaba da bata mata rai. Baffa ya ce "Zan yi farin ciki da hakan amma dai zan tuntubi Umaimah da maganar tukunna. Da Abdul-Sabur zai tafi sai ya damko kudi mai yawa ya bawa Sabitu da Baffa ya sake ambalowa ya bawa Sabitu ya ce ya bawa Umaimah, ya mikiwa Nene da Inna kudin da tunda suke a rayuwarsu basu taba mallakar irinsu ba, sannan ya yi ta rabawa mata da suka zo yiwa Umaimah sannu da zuwa. Sabitu ya kira Umaimah dan su yi sallama da Abdul- Sabur zai tafi, bai ji dadin yadda zasu rabu ba idanuwanta sharkaf da hawaye. Yana zaune a cikin mota yayin da ta kama kofar motar ta tsaya babu walwala a fuskokinsu su dukka. Abdul-Sabur ya nisa sannan ya girgiza kai ya ce "Na san yadda kike ji, babu dadi, akwai takura, amma ki ci gaba da yin hakuri komai mai wucewa ne, watarana za ki ga kamar ba'ayi ba. Zan tafi yanzu kuma gashi ban san yadda zamu sake haduwa ba tunda ba ku da waya balle in kira. Na daukar miki hutun sati biyu a wajen da za kiyi aikin bautar kasa, idan ya cika kije kisa hannu (signing) kawai, ba sai kin kwana ba ki dawo gida yanzu. Dan zan je can in ga manajan bankin mu daidaita ba sai kin je ba har tsawon wata guda, kafin a tsayar da shawara a ga yadda za kiyi zaman, dan gaskiya zamanki a gidan su Aisha bai dace ba. Hankalin Umaimah ya tashi matuka musamman da ta ji ya ce zai tafi bai san sanda zasu sake haduwa ba. Sai hawaye ya barke mata ba tsayawa, nan da nan ta gigice har sai da shima ya razana. Ta tambaye shi, "Ghana zaka tafi ko Ingila? Ya yi dariya dan ya fuskanci bata san abunda ya ke faruwa ba. Ya ce "Yanzu dai Gwarzo da Kano zan koma, ina kasar zuwa wani dan lokaci. Ta cire rai da shi ta ga alama ba da niyyar aurenta ya zo ba, dan duk abun nan da ake bai taba yi mata maganar aure ba. Tabbas zata iya rasa rayuwarta sanadiyyar bugun zuciya muddin ya tafi ya bar ta bai aure ta ba. Fargaba ta hanata tambayarsa, ya auri baturiya ko bai aura ba, ga takurawa kuwa basa yarda ayi musu kishiya. Dan Aunty..MAKWABTAKA 51 Abdul-Basi ya harare su sama da kasa ya ja dogon tsaki ya shiga motarsa a fusace ya fisga da gudu ya tayar da kura, ya tafi. Umaimah ta juya a fusace ta fara tafiya har ta gifta sai ta dawo da baya ta zo gaban Matawata da mahaifiyarta suna tsaye ta dube ta sama da kasa. Ta ce "Matawata, gari ya waye tunda safiya ta yi, haske ya bayyana yayin da duhu ya kauce. Ina fatan kin fahimce ni dan da yaren fulatanci na ke miki magana ba da Hausa ba ko turanci. Kada ma ki wahalar da kan ki wajen zuwa gaban Dagaci dan yi mana sulhu idan kina so kada ki fasa daukar matakin da kika yi niyya. Ki sani shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne, na yi hakuri a baya bana nufin hakurina ya kare amma ina mai tabbatar miki nan gaba ba zan kara daukar abin da na dauka a baya ba. Na fuskanci sai na nuna miki rashin kunyar baki iya ba. Na bar miki Ilah tuntuni babu hadina da shi Allah Ya musanya min Ya kawo mijin da ya fi kowa a wajena shine Abdul-Sabur. Kada ki sake shiga harkata, bana nufin ina gaba da ke amma zagi da habaici ba zan sake dauka ba. Umaimah ta gyada kai ta wuce ta bar Matawata a tsaye tana kallonta tamkar an zare mata laka. Kowa ya fara fadar albarkacin bakinsa yana fadin tabbas Umaimah ta yi gaskiya ta yi hakuri da wulakanci da cin amanar da Matawata ta yi mata. Aliya budurwar Sabitu da kawayenta su ne suke yiwa Matawata habaici suna fada mata Umaimah ta fi karfinta ba sa'ar yin ta ba ce. Da Matawata ta hau zaginsu sai suka zamar da ita shiri-shiri su da yara suka hau rero mata wakar da aka rere mata a lokacin da ta yi kwartanci, har kofar gida aka rako ta dan ma iyayenta suna duka suna rarraka yara gida a guje. Abdul-Sabur ya koma cikin motarsa ya zauna yayi shiru yana tunani ransa ya sosu a yau musamman da ya ga fushin Umaimah har ta fara zaton yana cin amanarta. Bayan da Sabitu, da su Baffa sun raka Dagaci fada ya zauna sai Sabitu ya dawo da sauri wajen Abdul-Sabur ya iske shi har yanzu a cikin mota, ba kowa a wajen duk *yan kallon kwakwaf sun watse. Ya bude gaban mota ya shiga ya zauna ya dubi Abdul-Sabur Ya ce "Yayana kada fa ka damu, idan ka ga aure anyi shi babu rigima babu kananan surutu ma bai cika karko ba. Abdul-Sabur ya girgiza kai ya yi ajiyar zuciya ya ce "Sabitu gobe zan bar Gombe zan koma garinmu. Lafiya? Me yasa? Ka fasa aurenta ne saboda Abdul-sabur? Sabitu ya tambaya a gigice. Abdul-Sabur ya ce "Haba Sabitu ko raina aka ce zan rasa ai bazan fasa auren ta ba. Ina jin baka da labarin irin yaki da wahalar dana sha wajen nemo Umaimah. Sabitu ya ce "Kada ka damu Umaimah ta fahimce ka, mu je kuyi sallama. Abdul-Sabur ya kunna mota suka nufi kofar gidan su Umaimah, a zaune a zaure suka hangota ta tare da Baffa daga dukkan alamu nasiha yake yi mata, kanta a sunkuye a kasa tana hawaye. Karar tsayuwar motar ne yasa suka dago suka kalle su. Sabitu ya bude ya fito yayin da Abdul-Sabur ya ci gaba da zama a cikin mota ya kura mata ido yana kallo cike da damuwa da tausayawar da yake yi mata. Sabitu da Baffa suka dade suna yi mata magiya sannan ta yarda ta fito bayan Sabitu ya shiga cikin dakinta ya dauko mata gyale da takalminta. Tafiya take yi cikin sanda har ta karaso gare shi kanta a sunkuye a kasa, ya sha magiya akan ta shigo cikin mota ta zauna zai yi mata wata magana amma ta ki yarda ta shiga ta zauna, sai da yayi ta rokarta kamar zai yi kuka ta tuna ashe ta daina gudun maganar abunda *yan garinsu zasu fadi alhali kanta take takurawa kuma duk da haka bata fita. Sai ta zagayo ta shiga ta zauna, bayan ta zauna sai Abdul-Sabur ya dubeta ya sunkuyar da kai kasa ya yi shiru zuwa wasu lokuta masu tsawo, sannan ya dago ya dube ta ya ambaci sunanta har sau uku. Magana yake cikin sassanyar murya mai cike da damuwa. Ya ce "Ni mutum ne mai kaifi daya marar boye-boye, ina iya jurewa in yi hakuri da abunda nake so in har abun nan ba zai zame min kwanciyar hankali ba, abunda nake nufi anan shine a lokacin da zan bar Malaysia na hadu da wani abu mai suna tsananin kaunar Umaimah ya zo ya hade min da Faduwa tana tsananin kaunata ni kuma ina tsananin tausayinta da ganin mutuncinta. Ba wai na rasa yadda zan yi da ku ba ne ya sa na gudu na bar ku ba ku dukka, a'a kamar yadda na fada miki dazu ni mutum ne mai son tacewa da rairayewa in ga abunda zan yi ya zame min farin ciki. Maganar *yar gidan Uncle Hamza dana fada muku gaskiya ne, na je Ingila na hadu da ita da mamarta da wanta wato babban dan Uncle Hamza, a lokacin Uncle Hamza baya kasar. Mun zauna da su munyi magana tabbas sun nuna min su dukka suna son abun amma ni na sani ba dan Allah su ke sona ba, shi kansa Uncle Hamza na kula bai fahimce su ba. Manufarsu ta aure ni ta kwashe dukiyata dan suna cewa a jikin mahaifinsu na samu, in ya so bayan sun kwashe sai a rabu koma su kashe ni magana ta wuce. Na gama sauraron dadin bakinsu sai nima na shirya musu nawa sharuddan da gangan dan na san ba za su iya bi ba. Abunda na fada musu kuwa shine duk matar da zan aura sai ta kasance cikakkiyar musulma mai shiga irin ta musulunci, sannan dole ta tsaya a matsayinta na mace bata da cikakkiyar *yancin da zata dinga fita tana yawo gari-gari ko kasa-kasa tana yin abunda ta ga dama. Sannan ina da damar zabar mata kasar da zata zauna, kasar nan da zan zaba dole ta kasance kuwa kasar Musulunci ce kamar Nigeria ko Indonesia ko Malaysia na cire Ingila ma a ciki. Daga nan taro ya watse muka tashi baram-baram ta ce ta fasa ba zata iya ba, daman na san ba zata iya ba yarinyar da take yawo da dan siket ko dan wando iya cinya tana shaye-shaye ina zata iya kulle da saka hijabi. Daman ita da uwarta suka kintsa maganarsu suka sami Uncle Hamza suka kintsa masa da kanta ta koma ta ce ta fasa, ya same ni ya sanar min har da bani hakuri kada in ga ya yi magana ya canja. Na ce masa ba komai. Umaimah ta gyara zama daga dukkan alamu ta fara jin dadin sauraron labarinsa. Ya ci gaba da cewa "Dana gama da wannan matsalar sai na wuce Cairo daman ina da lambar wayar wasu daga cikin *yan uwan Faduwa maza, na sami daya daga cikin kannenta da suka hada kakanni daya mai suna Habib. Ya zo har Hotel din dana sauka muka zauna daman tun a waya na shaida masa ni aminin Faduwa ne daga Malaysia tare muke karatu a can. Na fara da tambayarsa labarin Sagir tsohon saurayinta, ya bani labarinsa kakaf da halin da yake ciki. Ya ce min bayan ya rabu da Faduwa sai ya shiga wani hali na damuwa har ya fara shaye-shaye har sai da aka dakatar da shi a wajen aiki, da kyar mahaifiyarsa ta lallashe shi ya auri wata *yar uwarta amma zaman bai yiwu ba suka rabu ya sake auren wata suka rabu. Na ce ko zai bani lambarsa? Habib ya ce ba shi da lambarsa sai dai ya san gidansa kuma yasan ofishinsa. Sai na ce ya kai ni wajen aikin na sa, da farko da aka yi min iso cikin ofishinsa da ya ji an ce daga Malaysia kuma abokin Faduwa ne sai ya fara harara ta yana tunanin mijinta ne amma dana yi masa bayanin abunda yake tafe da ni sai ya yi kamar zai kwanta min saboda rawar jiki da girmamawa. Abunda na ce masa shine Faduwa ta bani labarinka kakaf amma bata taba zaton ma zan zo Cairo ba balle in neme shi ba, ni naga ya dace in zo in gan shi mu gaisa. Ya nuna min yana cikin damuwa da tashin hankali a rayuwarsa tunda ya rabu da Faduwa haka yake, yanzu nemanta yake kamar ruwa a jallo mahaifiyarsa ma ta yarje masa ya neme ta ya aure ta, ta yafe masa. Ni na masa alkawari zan hada shi da Faduwa na shirya masa lokacin daya kamata ya je ya sameta a Malaysia. Na san za kiyi mamaki idan na ce tare da shi muka je Malaysia ranar Graduation dinta na hango ku a tsaye a bakin Hotel din, sanda Sagir ya je ya durkusa a gabanku. Ina labe a lungu ina gano ku ban fito ba dan kada ku ganni kuma na fadawa Sagir kada ya bari ku sani. Na ji dadi da Faduwa ta yarda aka yi aure duk muna waya da Sagir har sai bayan data haihu naje Cairo kwatsam Faduwa ta ganni a gidanta. Na ji dadi da aka sakawa yarinyar sunan ki kuma nayi mata godiya na basu abun arziki bana kadan ba saboda albarkacin sunanki. Sai a lokacin Sagir ya fayyace mata komai ta sha dariya da mamaki. Faduwa ta sanar da ni duk abubuwan da suka faru bayan tafiyata, cewar kina sona har ki ka kasa sauraron Abdul-Basi. Na ce kada ta fada miki komai har sai na gama bincikena, a wajenta na sami lambar wayar ki ta Nigeria. Umaimah ta tsura masa ido tana kallonsa tana sauraron hirarsa tamkar almara dan ita bata taba ganin mutum mai daukar matsalar wani ta zamo tasa ba irinsa. Ya ci gaba da cewa "A lokacin da na gama da Sagir, Abdul-Basi ma muna waya da shi saboda ina da lambar wayarsa na tambaye shi ra'ayinsa akan ki, ya shaida min bashi da mata yanzu kuma ya kasa kara auren kowacce sai ke yake so. Amma na fuskanci yana da girman kai yawanci duk hanyoyin dana fada masa ya bi yaki bi. Misali na fada masa ya tura miki sako na bada hakuri gami da daddadan kalamai yadda zaki huce amma ya ki, ya ce min idan kin dawo zaku hadu yasan idan yayi magana da su Baffa zasu tilasta miki ki koma gidansa. Da nazo Nigeria muka hadu a Kaduna mun zauna na nuna masa mace bata son ji da kai dole su mata a bi su da tattausan lafazi da kyautatawa, har a lokacin na bashi labarin zaman da muka yi da ke da yadda na yi ta bin kanki har ki ka yarda ki ka saba damu. Daga karshe na fayyace masa gaskiya na ce ina sonki kina sona amma na buya bana so ki san ma ina sonki dan na fi so ya aure ki ko dan saboda *ya*yanku. Sai a lokacin ya amince zai je graduation dinku idan kun hadu acan zaku daidaita. Bayan ya tafi nima naje Malaysia na labe na ga duk yadda ku ke yiwa juna babu maganar daidaituwa dan haka saina fito fili na bayyana kika ganni bayan na shaidawa dangina gaba daya labarinki cewar ke zan aura. Ni da Sabitu mun boye miki maganar kai kudin aure da aka yi saboda muna so mu baki mamaki ki ji kwatsam! Ta sama dan ki gigice dan dadi to mu shigo da farin ciki Matawata ta batawa kowa rai na je na sami Dagaci na ce a shiga tsakaninku ina fitowa zan tafi kuma Abdul-Basi ya tare ni yana nemana da bala'i. To kin ji abubuwan da suke faruwa Umaimah bana boye miki komai. Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta yi murmushi gami da yin fari da ido ta ce "Tabbas nayi mamaki sannan na yi farin ciki a lokacin dana ji yadda maganar ta ke. Amma fa kayi kasada, to da ace a rashinka na hakura na yarda na amsawa Abdul-Basi yaya zaka yi alhali na ji a baya kayi magana kan cewa tsananin so kake yiwa Umaimah. Su dukka suka kwashe da dariya ya jinjina kai. Ya ce "Allah ne kadai Ya san yadda zai yi da ni amma tabbas na san zan shiga damuwa amma na yarda da kaddara me dadi da marar dadi. Gashi na girma idan ban yi aure yanzu ba ban san sanda zan yi ba kuma nasan halina game da soyayya ba na iya samun wacce zan ji ina sonta daman daga kan ki na fara jin son da yanzu na rasa ki kwanciya zan yi in ce su Khausar su yi min auren dole kawai tunda sun dame ni da maganar aure. Suka kyalkyale da dariya su dukka. Umaimah ta ce "Allah Ya rufa mana asiri, Ya zaba mana abunda ya fi alkhairi. Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce "Allah ma Ya zaba mana addu'ar da zamu yi nan gaba ita ce Allah Ya bamu zaman lafiya da *ya*ya masu tarin yawa da albarka.. Sai Umaimah ta ji ta tamkar a mafarki yau Allah Ya cika mata burinta a rayuwa ta sami wanda take so zata aura daga dukkan alamu mijinta ya fi na kowacce mace a duniya haka take ji a zuciyarta. Abdul-Sabur ya ci gaba da cewa "Zan koma Kano yau, jibi zan tafi Ingila sai in turowa Khausar kayan lefenki Abuja zai in wuce Ghana in sanarwa da dangina cewar zan yi aure sai kuma in dauko Ummana Fuse mu taho Gwarzo sai a hada da su Khausar da sauran mata, nan da sati biyu a kawo lefe. Sai mu hadu dake da Sabitu a Gombe a ranar amma ku je da shirin yin kwanaki uku yadda zaki ji dadin rabon katin biki dan zan taho miki da su. Umaimah ta rike baki dan mamaki ta ce "Abun ya zo ashe, yaya na ga kamar kana gaggawa? Amma daurin aure kadai za'yi ko ban da tariya? Abdul-Sabur ya ce "Daurin aure da biki dukka meye kuma tariya? Ta yi dariya ta ce "Haba dai ai ni ban shirya ba. Ya harare ta ya ce, "Wanne shiri kike tunani za kiyi alhali gani a raye, ai idan ina nan ko ba ni za ki aura ba kin san kin daina wahala ko tunanin yadda za kiyi. Na san bai wuce kiyi maganar gado da katifa ba wanda bana bukatar wannan. Na zaci ma zaki tambaye ni a inda zamu zauna tun da ni Allah Ya halicce ni rayuwata a kasashe daban-daban. Umaimah ta yi murmushi ta ce "Tambayar nan tana raina sai dai na daure na danne ta dan kada kaga gaggawata. To a ina zamu zauna? Abdul-Sabur yayi murmushi ya ce "A ina kike so mu zauna? Ta sa gyale ta rufe fuskarta alamar jin dadi da kuma kunya. Ta ce "Wallahi ban sani ba na baka zabi. Ya ce "To shikenan tunda kin bani zabi zan zaba mana, na fi son mu zauna a Nigeria a garin Abuja, ina da gida a Gwarumfa sama da kasa ga bangare daban in da nake so in saka Ummana Fuse ku zauna tare amma kowa da bangarensa ga Khausar ma a Abuja baku da nisa. Idan Sallah ko biki ya taso a dangina sai mu zo Gwarzo ko Kano mu bude gidanmu mu shiga duk ina da gidaje. Sai mu dinga zuwa Ghana da Ingila ziyara lokaci-lokaci, babu abinda zai ragu a kasuwancina ina da yara masu kular min daman ba ni nake zama ba, sai dai idan kaya sun kare ni nake tafiya Indonesia, China, America in auno. Kin ga sai in bude ofishina a Abuja in baki matsayin Manajata sai mu fara turo kaya zuwa Nigeria, a bude babban shago na san zai karbu, Sabitu ma sai a samar masa abunyi ya yi aurensa. Hawayen dadi ya rufowa Umaimah ta sharce hawaye ta ce "Abdul-Sabur ina jin dadin maganarka tamkar a mafarki ban san kalmar da zan yi maka godiya ba idan kayi min wata kyautar, lallai Allah Ya amsamin addu'ata ya hada ni da miji na gari. Na so in tura Sabitu makaranta ya samo ilimin zamani dan na san ko kasuwanci zai yi sai da ilimin saboda lissafi shi kuwa bai iya ba a boko. Abdul-Sabur ya ce "Wannan ai mai sauki ne mun yi magana da shi ya nuna min cewar yana so ya je Madina ya karo ilimin kur'ani amma kafin ya tafi za'a iya samo masa malamin da zai koya masa karatu da rubutu na boko a shekara daya ko biyu zai iya koya idan ya so sai ya tafi jami'ar Makka ko Madina ya yi digiri dinsa. Ko yaya kika gani? Umaimah ta gyada kai ta ce "Haka ya yi daidai ranka ya dade, sai dai in sake neman wata alfarmar dan Allah. Abdul-Sabur ya gyada kai ya ce "Fadi duk abinda kike so Umaimah kina tare da mijinki, a shirye nake na zama bawa a gare ki. Ta ce "Ina matukar jin tausayin Ilah, ci gaba da zamansa a kusa da Matawata ba karamin ciwon zuciya zai jawo masa ba, ga talauci da yara. Ka taimaka ka hada shi da Sabitu dukka abunda ka yiwa Sabitu ka yi masa dan shima tare suka je yawon almajiranci. Mu yi masa aure idan ya tashi yi a hada su da matansu su tafi Madina suyi karatu bayan sun yi yaki da jahilci sun koyi karatun boko. Abdul-Sabur ya ce "Kin yi dai dai haka ya nuna min kina bada hakkin MAKWABTAKA. Na ji ra'ayinki akan su Sabitu, Baffa da matansa fa, yaya za'ayi da su? Ko kina so su ci gaba da dawwama a Ruga har karshen rayuwarsu? Umaimah ta girgiza kai ta ce "Abun sai yayi maka yawa, Baffa yana nan a inda yake bana jin zai yarda ya baro Rugar nan daya saba. Sai dai mu dinga kawo masa duk wani taimako yana daga nan. Abdul-Sabur ya ce a'a dole Baffa ya dawo birni ya zauna idan ma ba zai yi nisa ba ya tsaya a cikin garin Gombe. Babu yadda za'ayi muna birni muna shan wutar lantarki, ga Ac, ga wayar sadarwa, su suna cikin duhu. Dole a hankali in gina gidaje a jere har guda hudu masu dauke da dakuna uku, daya Baffa da matansa, daya Sabitu da matarsa daya Ilah da matarsa idan yayi wani auren amma ba Matawata ba, daya kuma Umaimah da Abdul-Sabur idan sun zo su dinga sauka a ciki. HMM___ wayyo ni Matawata ta, kowa ya tsaneta haka kawai, mace kyakkyawa da ita. Amma ba komai zan turata Malaysia ita ma, ko ya kuka ce? Kuna tare da ni a ko yaushe. A.A Hada HadaMAKWABTAKA 52 daya kuma Umaimah da Abdul-Sabur idan sun zo su dinga sauka a ciki. Umaimah ta rushe da kukan dadi ta ce "Na ji dadi da Allah Ya halicce ni Ya raya ni, Ya kaini Malaysia na hadu da kai, babu abinda zance maka sai Allah Ya biya ka Ya jikan mahaifanka. Abdul-Sabur ya ce "Amin na gode. Amma kin san halina tun ada bana son in yi kyauta a yi ta godiya balle har a barke min da kuka bana jin dafin haka. Ki dauka duk abinda nayi miki aikinane daman, kuma dole in yi. Kamar yadda dole in rike iyayena dole in rike su Baffa, haka kamar yadda ya zama dole in kula da kaina ya zama dole in kula da ke da duk wani naki. Mu yi fatan Allah Ya raya mu Ya bamu tsawon kwana masu amfani. Umaimah ta goge hawaye ta ce "Amin. Ya ce "Yauwa, ko ke fa, goge hawayenki ki daina kuka. Yanzu zan tafi ki taya ni da addu'a in je lafiya in dawo lafiya in same ku lafiya. Sai nan da sati biyun in mun hadu a Gombe, ki sanarwa Baffa *yan uwana mata za su zo kawo lefe nan da sati biyu. Umaimah ta ce "Zan fada masa daga na shiga gida yanzu, Allah Ya kawo su lafiya. Ina yi maka fatan ka je lafiya ka dawo lafiya. Ta bude kofar mota ta fita ba tare da zuciyoyinsu suna so ba, basa so su rabu da junansu sai dole. Ji yake tamkar ya hadiye ta dan so da kauna haka itama take ji a ranta tamkar su dauwama suna tare suna hira. Ya tafi yana daga mata hannu tana daga masa itama har ya bace. Ta shiga gida da sauri ta iske Baffa da Sabitu a dakin Baffa sai ta daka tsalle ta shiga tsakiyarsu ta zauna tana ta dariya da shesshekar jin dadi ta rasa daga inda zata fara zano musu irin wadan nan abubuwan alkhairi, sun kagu su ji sun tattara hankulansu gaba daya gare ta suna ta jero mata tambayoyi. Ta gyara zama ta fara zayyano musu abubuwan alkahairi sanka-sanka daga Abdul-Sabur zuwa gare su sai Sabitu ya sulale ya kwanta wai shi dadi ne ya sumar da shi, yayin da Baffa yake faman daga hannu sama yana ta hamdala ga mahaliccinsa. Umaimah ta sami sukuni a zamanta na Dugge, Matawata ta tsorata bata kara jiyo habaicinta ba balle zagi, haka su Nene da mutanen gari kowa girmanta yake gani, tun kafin ta ce ayi abu ake yi balle kuma ta ce ayi din. *** _____ Tun bayan tafiyar Abdul-Sabur Umaimah bata kwanta ba aka hau gyaran gida ana ta yi masa kwaskwarima yadda *yan kawo lefe da *yan biki zasu sami dan wajen zama mai kyau. Ta hada ku san kudinta kakaf wajen sumulce bangon gidan da tsakar gidan aka cire duk inda zana take aka dora bulo din kasa aka sumulce da zumunti, aka buga runfunan kwano yadda za'a zazzauna a sami inuwa, bayan data katange bandaki da bulo da simunti aka saka kyaure. Tabarmi manya-manya masu yawa ta aika Sabitu ya siyo mata a birni. Sannan ta zauna ta rubuta yawan abinciccikan da za'a shiryawa baki, ana gobe zasu zo *yan matan garim irin su Aliya da take kama kafa da Umaimah suka zo suka taya ta soye-soye, bata bari su Nene sun saka mata hannu ba dan ta san basu iya girkin zamani ba. Haka a ranar da za'a kawo lefe ma tunda asuba su Umaimah suka tashi aka dora abinci kala-kala kamar Fried rice, cincin, miet pie, kek, sakwara da dai sauransu. Aka siyo mata kankara da kuloli aka saka lemuna iri- iri. Sai da ta shirya komai sannan ta yi wanka ta shirya kayanta kala uku ita da Sabitu suka nufi Gombe da misalin karfe goma sha daya da rabi suka isa. Kai tsaye ofishinsu da take bautar kasa ta fara zuwa, ta saka hannu aka tabbatar mata an kara mata hutun sati biyu Abdul-Sabur ya nemar mata wannan alfarma. Tana fitowa ta kira shi a waya ya tabbatar mata a Gombe ya kwana amma su Khausar sun taho sun kusa karasowa Gombe da kayan lefe in ya so sai Sabitu ya raka su Dugge su kai. Ya ce su jira shi a bakin banki zai fito daga Hotel din daya sauka ya zo ya same su. Bai dade ba ya bayyana a gabansu wannan karon ba a irin motar da ya zo da ita ada ba ce, wannan ta fi kyau da tsada. Umaimah a gidan gaba Sabitu a zaune a baya, bayan sun gaisa sai ya shaida mata zai kai ta gidan su Aisha Bingyal ta zauna sai Aisha ta rarraka ta su fara rabon kati. Ya zaro wasu lafiyayyun Katina kala-kala ya mika mata masu yawan gaske. Ta yi caraf ta karba ta fara karantawa ta ji idanuwanta sun dauki karkarwa saboda tsabar gani take kamar almara. Wasu na daurin aure ne, wasu na yini, wasu kuma na Dinner party ne da za'ayi a hadadden Hotel din nan na Emerald Royal Hild. Yin ranar juma'a a Dugge, daurin aure ranar asabar a gidan Dagacin Dugge, daga nan sai a dunguma a taho Gombe dan yin dinner duk a ranar din. Lahadi kuma kai amarya kuma daga Gombe zuwa Abuja. Allah Ya ba su ikon halarta, a iso lafiya amin. Sabitu ba'a iya karatu ba sai dai ya karba ya jujjuya katinan sai da Umaimah ta karanto masa, sannan ya hau murna. Su dukka ukun murna suke suna kyakyata dariya har suka isa kofar gidan su Aisha, sun kuwa ci sa'a suka ci karo da ita tana dawowa itama daga wajen aiki zata shiga da motarta cikin gidan data ga su Umaimah bakin get sai ta fasa shiga ta fito daga motarta ta iske su a cikin motarsu, suka gaisa. Abdul-Sabur ya shaida mata ya kawo mata matarsa ta rike masa ita zuwa kwana biyu, kada ta bari ko kuda ya taba ta. Aisha ta yi dariya ta ce "Ba matsala ranka ya dade na rike amana. Suka yi sallama su Abdul-Sabur suka tafi yayin da Umaimah da kawarta suka shiga cikin gida. Bayan sun shiga bangaren Mama Umaimah ta gaisheta sai suka wuce bangaren Aisha anan aka baje labari da katunan biki, Aisha ta sha mamaki a lokacin da Umaimah ta fito da katunan biki ta nuna mata sai ta za ci gezau idanuwanta suke yi mata. Ta taya Umaimah murna sosai, bayan da suka huta su ka ci abinci suka yi sallar azahar sai su ka bazama suka shiga gari suka fara rabon katuna na biki. Duk bayan *yan mintuna Abdul-Sabur sai ya kira ya ji lafiyar sahibarsa Umaimah, tabbas mafarkinta ya zama gaskiya abunda taga Sagir yana yiwa Faduwa ya burge ta ita ma yau gashi Allah Ya nuna mata ana yi mata irinsa. Ya tabbatar mata da cewar baki sun iso har zai kai su Hotel su ci abinci Sabitu ya hana ya ce an yi musu dafe-dafe a can. Abdul-Sabur ya tuhumi Umaimah da laifin akan me yasa ta wahalar da kanta ta dafa musu abinci, alhali so yayi su je a koshe suna mikawa su juyo. Umaimah ta ce kada ya zarge ta dan ta girmama bakinta abunda ake yi kenan a ko'ina dan me yasa su zasu ki yi. Ya yi godiya itama ta yi masa suka kashe waya. Babu abinda Aisha ke yi sai kallon Umaimah tana sha'awar kyautar da Allah Ya yi mata tana fata da buri itama ta sami miji kwatankwacin na Umaimah. Masha Allah Tabarakallah. Sai ga Umaimah a gidan Lamijo kwatsam ta gansu a falonta tabbas ta firgita a fili take a bayyane sai da kowa ya gane ta, sai jikinta ya dau rawa musamman kafin ta ji dalilin zuwansu. Jikinta sanyi kalau ta tare su tana yake daga gani bai kai zuci ba. Bayan data basu izini suka zauna sai suka gaisa ba tare da bata lokaci ba Umaimah ta mika mata katunan nan kowanne sai da ta bata daya. Na daurin aure ta ce ta bawa Baban Hanif, Yini da Dinner kuma nata ne. Sai Lamijo ta kasa dago ido ta kalli Umaimah dan kunya. Ta tambaya "Waye mijin, dan Malaysia ne ko Abdul-Basi ne ya koma Abdul-Sabur? Aisha ta yi caraf ta ce "Eh a Malaysia suka hadu amma Bakanone sai dai mazaunin Ingila ne amma a Abuja zata zauna, gashi saurayi babu ruwanta da kishiyoyi. Bakar magana Aisha ta fada mata, suka mike suka ce zasu tafi sauri suke yi, har tana kokarin cewa mai aikinta ta kawo musu lemo suka ce ta bar shi. Ta rako su har bakin get ta yi arba da tsaleliyar motar Aisha amma Umaimah ce take tukawa a zaton ta ma ta Umaimah ce, har da cewa Umaimah ta bata lambar wayarta dan idan suka tashi zuwa Dugge biki su kira su ji, Umaimah ta bata itama ta karbi ta ta. Gidan mahaifiyar Lamijo suka wuce Umma, itama dai haka ta kasa hada ido da Umaimah saboda nauyi da kunyar wulakancin da suka yi mata a baya. Umma ta tambaya "Mijin dan ina ne? Aisha ta bata irin amsar da ta bawa Lamijo dazu. Suka fito daga gidan sai suka shiga gidan Makwabciyar Umma wato Salma wacce ta yiwa Umaimah kazafi, itama ta yi mamaki da ganin Umaimah a gidanta, bayan sun bata katin Dinner guda biyu ita da mijinta sai suka juya zasu tafi. Sai Umaimah ta ji Salma ta dafa kafadarta tana juyowa sai taga hawaye yana surnanowa daga idanuwan Salma. Umaimah da Aisha suka kidime suna tambayarta lafiya take kuka? Sai ta sake fashewa da kuka. Ta ce "Na zalunci kaina Umaimah da gangan na yi miki kazafi, saboda kawai ina so ki daina shigowa gidana na ga kin fini kyau da tsari ina tsoron kada ki burge mijina ya ji yana sonki. Gashi yanzu kin yi ilimi, kin yi kudi, kin sami mijin da yafi nawa. Ki yi hakuri Umaimah ki yafe min. Umaima ta yi murmushin karfin hali hawaye zazzafa ya surnano mata, ta sa hannu ta goge wa Salma hawayen fuskarta. Ta ce "Ki daina kuka na yafe miki daman tuntuni shiyasa kika ganni a gidanki ban kullace ki ba ko kadan, Allah Ubangiji ya yafe mana. Salma ta yi musu alkawarin za su je ita da mijinta in Allah Ya yarda. Suka ci gaba da rabon katuna har sai da dare yayi sosai suka koma gida akan gobe zasu karasa rabon. Suna shiga gida Abdul-Sabur ya kira ya tambayi in da suke, ta ce sun dawo gida. Ya tabbatar mata masu lefe sun kai sun dawo har ya kai su masaukin su a Hotel din da yake ya kama musu dakuna da yawa suna can sun kwanta. Ya ce yana so ta shirya gobe da safe su wuce ita da Aisha su zo su gaisa suma dan suma su ganta musamman Khausar. Umaimah ta ce "To, babu matsala za mu zo goben in Allah Ya kaimu. Ya ce "Su Khausar suna ta godiya sun ce an yi musu dafe-dafe, kuma an karbe su hannu bibbiyu. Umaimah taji dadi da jin haka dan haka sai ta godewa Allah da suka fita kunya. Washe gari su Umaimah suka tashi da wuri suka shirya suka caba ado kai ka ce gidan biki zasu je, su ka nufi Hotel din data fada musu, a hanya Umaimah ta tsaya a wani kanti ta sayi alewowi cikin leda masu tsada ta tafi musu da shi. Suna isa bakin get din Hotel ta kira shi a waya, ya sauko ya shiga da su ciki. *Yan uwan Abdul-Sabur sun sha mamaki da suka ga zukekiyar amaryarsu Umaimah, dan basu zaci zasu ganta hadaddiya kuma wayyiya haka ba. Har da sun fara *yan gulmammaki suna cewa shi kuwa Abdul-Sabur me yayi masa zafi ya shigo Rugar nan neman aure ya tsallake duk matan duniyar nan? Duk da Khausar ta san Umaimah amma bata zaci a Ruga take ba kuma sai ta ga Umaimah ta sake yin kyau fiye da yadda ta ganta a Malaysia. Ta gasgata lallai dole Yayanta ya makale ya nace anan dan tana da kyau ga hankali. Bayan su Umaimah sun gaisa da su suka dade suna hira, abokan wasansa suka dinga yiwa Umaimah tsiya, ashe da gaske ne dangin mahaifiyarsa Fulani ne kawai masu jin fillanci dan haka sai suka sha yarawa da Umaimah. Da suka fito zasu tafi Umaimah ta basu alewowin nan cikin leda ta ce su kaiwa yara, suna godiya har suka shiga hadaddun motocin da suka zo suka tafi, Khausar ta karbi lambar Umaimah itama ta karbi ta ta. Umaimah da Aisha suka yiwa Abdul-Sabur sallama suka ce zasu tafi su ci gaba da rabon kati yayin da Abdul-Sabur da Sabitu suma suka nausa gari yawo kamar yadda suka saba. A yau dai Umaimah ta karade duk inda take so ta kai kati kowa ta bashi daga cikin maza da matan da suka yi karatu a Malaysia babu wanda basu je gidansu ba. Kowa yayi alkawari zai je komai da komai da za'ayi har da rakiyar amarya Abuja. A ranar ne kuma da daddare Aisha da Sabitu suka raka ango da amarya gidan daukar hoto, hotuna masu yawan gaske aka yi musu kala-kala aka wanke da yawa. Ya dibi wasu Umaimah ta dauki wasu dan su rabawa masu bukatar da zasu buga musu wani abu, duk da ba sai ya jira wani ya buga masa memo da kalandu ba shi zaisa a buga kuma masu inganci. Bayan sun dawo gida ne Sabitu ya samu lungu ya labe yadda Abdul-Sabur ba zai jiyo shi ba, ya kira Umaimah a waya ya fara kyasa mata kayan da aka zuba mata a lefe, kaya masu yawan gaske da tsananin kyau da tsada. Akwatu na dukan akwatuna har guda takwas, bayan manyan gwalagwalai har seti uku. Mamaki gami da farin ciki ya lullube ta, ta yiwa Allah godiya ta yiwa Abdul-Sabur godiya. Washe gari da safe Umaimah da kawarta Aisha su ka shirya, Abdul-Sabur ma suka shiraya suka kama hanyar zuwa Dugge dan su ga kayan lefe kuma Aisha ta taya ta zabar wadanda zata kai dinkunan fitar biki. Masha Allah! Su Umaimah sun sha mamaki da suka ga jifgin kayan nan, kai kace kanti za'a bude, duk yadda za'a baka labari ba zaka taba gane yadda lefen yake ba har sai ka gani da idanuwanka. Gaba daya garin Dugge da Rugagen da suke MAKWABTAKA da su sai da labarin lefen Umaimah ya karade, dan basu taba cin karo da lefe makamancin wannan ba. Aka sha bata labarin halin da Matawata ta shiga a lokacin da ta ji labarin yadda lefen yake, aka ce sai data fadi kasa dan bacin rai da tsananin bakin ciki. Yaya ta iya da ikon Allah ai sai kallo. Allah ba Ya son masu hassada da bakin ciki, Allah Ya hana yin hassada. Allah Ya raba mu da aikata ta amin. A ranar suka juyo Gombe bayan sun ciko akwati guda da kayan da ta zaba zata diddinka. Bayan kudin da suka sako akan lefe a matsayin kudin dinki, Abdul-Sabur ya hana ta biya kudin gaba daya shiya biya mata kudin dinkuna, dinkuna kuwa masu tsada da kyau. Haka ya yiwa Aisha yayyafin Naira ya ce itama ta yi dinkunan da zata fito tayi kyau a matsayinta na babbar kawar amaryarsa. A Gombe ya bar Umaimah a gidan su Aisha, Sabitu kuma a Hotel, amma a bisa sharadin direban gidan su Aisha ne zai mayar da su Dugge idan an gama dinkunan, dan bai yarda ta hau motar haya ba. Allah Sarki kauna! Bayan jiran dinki ma har da jiran gyaran jiki ne ya tsayar da Umaimah, mata masu yin dilka da alewa ne su ka sha suntirin zuwa har gida suka kalkale ta tatas kai kace fatar dan jarari ce. Har da Aisha aka shirya tafiya Dugge a lokaci da biki ya rage saura kwanaki takwas. Da ta yini a Dugge sai ta koma Gombe a bisa sharadin zata dawo idan biki ya rage saura kwanaki biyu, idan ta zo ba zata koma gida ba har sai an kai amarya Abuja. Jama'ar gari suna ta kaffa-kaffa da Umaimah kowa yana mata ladabi idan aka ga abunda bata So da gudu ake kaucewa wanda take so ne ake yi mata tun kan ta ce balle kuma ta ce ayi, ai babu bata lokaci ake yi. Labarin auren Umaimah ake ta yi a kowacce kusurwa ka zo giftawa ba a Rugarsu kadai ba har da rugagen da suka yi MAKWABTAKA kowa ya kagu ya zo wajen bikin nan ko da ba'a gayyace shi ba, dan ganewa idanuwansa kuma su cika tumbinsu. Washe gari Umaimah ta shiga rabon goro da alewa dan su a nan babu ruwansu da kati, babu gidan da bata shiga ta kai ba a garin ita da *yar rakiyarta *yan mata har ma da matan aure burjik ana ta take mata baya ana mata fadanci. Gida na karshe data shiga shine gidan su Matawata, ba Mawata kadai ba duk mai rai da yake gidan nan babba da yaro sai da jikinsa ya yi sanyi da suka ga Umaimah. Ta yi musu sallama, sannan ta duka ta gaishe da Mahaifan Matawata, ta basu daurin goro da alewa har leda uku. Ta ce daya na Matawata sauran biyun na uwar da uban. Sai Matawata ta sunkuyar da kanta kasa bata iya dagowa ta hada ido da ita ba. Innar Matawata ta rushe da kuka ta nuna Matawata da yatsa ta cewa Umaimah "Kin ga yadda kawarki Matawata ta zama ko? Saboda tashin hankali ta fita hayyacinta ta zama tamkar tababbiya. Tunda ta auri Ilah bata taba samun kwanciyar hankali ba muma namu bai kwanta ba, na san hakkinki ne yake biye da ita. Umaimah idan baki yafe mata ba, a haka zata dauwama. Sai kuma rana ita yau xaku jini da ci gaban shirin..MAKWABTAKA 53 Tunda ta auri Ilah bata taba samun kwanciyar hankali ba muma namu bai kwanta ba, na san hakkinki ne yake biye da ita. Umaimah idan baki yafe mata ba, a haka zata dauwama. Umaimah ta dafa kafadar Inna ta ce "Ki daina fadin haka Inna, ni fata na ma ace Ilah ya huce su koma su rike *ya*yansu. Babu abinda ta yi min, idan ma ta yi min na yafe mata ko ba komai ni makwabciyar ta ce, ina kare hakkin MAKWABTAKA. Ina girmama duk wani makwabcina ina kare hakkinsa domin makwabci yana da hakki akan makwabcinsa. Matawata ta dago a hankali ta dubi Umaimah ta mayar da kai kasa ta sunkuyar. Umaimah da tawagarta suka fice yayin da kowa ya dinga yaba hakuri da afuwa irin ta Umaimah. Allah Ya kyauta! Da daddare Umaimah tana zaune a kan abun sallarta a dakinta tana jero addu'o'in godiya ga Allah da Ya bata miji na gari, bayan ta idar da sallar isha'i. Sai ta ji yara sun shigo suna cewa ana sallama da Umaimah a kofar gida. Sai abun ya bata matukar mamaki ta fito tsakar gida a gigice ta na tambayarsu "Waye yake nema na? Suka ce "Ilah ne. Ta dan yi kasake kamar ba zata je ba sai su Nene suka dinga yi mata magiya suka ce ta je. Ta fita a zaure ta hango shi a rabe a tsugune a lungu, itama ta zo ta durkusa duk sun juyawa juna baya. A haka suka gaisa sannan ta ci gaba da sauraron abunda zai fada mata. Ilah ya yi ajiyar zuciya ya ce "Umaimah, na zo ne dan in yi miki murna in kuma yi miki fatan alkhairi bisa wannan abun arziki daya same mu gaba daya, dan abunda ya yi ki shi ya yi ni. Ina jin ki tamkar *yar uwata ta jini ba zan manta da ke ba har abada kuma ba zan sami kamar ki ba, ni na san da haka. Ba wai ina dawo da maganar data wuce a baya ba amma kaddara ce ta gifto mana ta raba mu wanda komai rubutacce ne a wajen Mahaliccinmu. Kin yi hakuri, kin jure da duk abubuwan da aka dinga yi miki a kaina daga karshe Allah Ya dinga saka miki da wadanda suka fini alkhairi. Allah bai rubuto ki daga cikin wahalallu ba irinmu shiyasa ma ya raba ki da ni. Daga karshe ina baki shawara da ki bi mijinki sau da kafa wannan daman halinki ne biyayyar aure. Allah Ya baku zaman lafiya. Sai ya surnano da hawaye mai zafi. Umaimah ta sharce hawaye itama ta ce "Ba komai Hamma Ilah, nima ba zan daina ganin girmanka ba haka ba zan yanke zumunci da ku ba, ba zan iya daina maka kaunar nan ta *yan uwantaka ba har abada. Ina rokar ka da ka zama mai tausayi da rangwame a bisa zamanka da Matawata. Allah Ya jarrabe ka da mace mai wuyar sha'ani idan akwai rabon ci gaba da zama kada ka ki mayar da ita zan ci gaba da taya ta addu'a Allah Ya shirye ta. Ilah ya girgiza kai ya ce "Ki taya ni da addu'a Allah Ya daidaita ni da Furera kawar Aliya ita nake shirin aure har magana ta yi nisa, gara Furera ita yarinya ce karama zata fiye min alkhairi amma ba zan iya ci gaba da zama da Matawata ba. Tunda muka yi aure bamu taba yin sati guda ba, ba tare da mun bata ba, na gaji. Umaimah ta yi masa addu'ar alkhairi shima yayi mata suka yi sallama kowa ya juya ya tafi. Tana shiga gida sai gashi ya aiko yaro dauke da wani littafi karami, yaron ya mika mata. Ya ce "In ji Ilah gudunmawarsa ce. Sai ta karba cike da tausayi, da sauri ta bude ta fara karantawa, ta ga addu'oi na zaman lafiya da kara soyayya tsakaninta da mijinta da kuma addu'oin tsari daga makiya, ya zauna ya rubuta mata da larabci. A tsakiyar littafin kuma kudi ne har Naira dubu uku. Sai tausayinsa ya kamata ta san yafi wata guda yana tara wadannan kudi. Ta kuduri niyyar taimaka masa nan gaba fiye da tunaninsa. Biki yana ta karatowa ya rage saura kwana uku aka tashi Umaimah da sassafe tana bacci wai ta zo ga sako daga Kano. Bata gama fuskantar ma me ake nufi har sai data fito kofar gida, taga katuwar mota a cike da kayan abinci da abun sha har ma da katuwar Saniya da raguna biyu, ga katon jannareto dan a kunna ayi biki a cikin haske, ga katon firij dan asha ruwa da lemo mai sanyi, ga babbar rediyo mai safiku dan *yan biki suji sauti, manyamanyan kwalaye har guda uku a cike da kalandu da memo mai dauke da hotunan amarya da ango dan arabawa mahalatta bikin duk daga Abdul-Sabur. Sai ta ji ta rasa kalma daya da zata furta ta godiya sai ta koma cikin gida da sauri ta kira Baffa da Sabitu suka fito cike da murna, aka hada da kartan gari aka dinga sauke buhunhunan abinci da za'a ci a biki, bayan nan sai ga makudan kudi sun biyo baya su kuma na cefane bayan Kwando-kwandon kayan miya da aka hado. Tabbas wadata ce duk ta kawo haka bayan so da kaunar da yake yi mata, *yan Dugge suna kallon harkar arziki wanda basu taba ganin irin ta ba. Bayan an bawa direbobin abinci sun ci sai aka ba su tukuicin kudi mai yawa wanda babu wanda bai yi dariya a cikinsu ba, suna godiya su Umaimah suna godiya suka tafi. Ta rubuta doguwar wasika ta basu su kaiwa Abdul-Sabur, kalamai masu taushi da tausasa zuciya ta rubuta masa tana nuna godiya a bisa hidimomin da yake yi mata. *** BIKI! BIDIRI!! BIREDE!!! Rana bata karta sai dai uwar *ya ta ji kunya, saura kwana daya a fara biki sai ga garin Dugge ya fara samun manyan baki ba daga kasar nan ba ma har daga wata kasa. Aisha Bingyal da Faduwa ne suka iso tare ranar alhamis. Zo ka ga tsalle da murna a wajen Umaimah, da gudu ta rugu ta dane Faduwa, ta dauki takwararta *yar jaririyar Faduwa wato Umaimat. Umaimah Sagir ta fara tambayar Faduwa ta ce yana Kano tare da Abdul-Sabur sai gobe zasu taho Gombe. *Yan Dugge kuwa sai aka bi layi ana kallon Faduwa ana nuna ta suna fadin ga balarabiya. Dan basu taba ganin irinta ba a garin. Gidan su Umaimah ne guda daya tak mai hasken lantarki a garin sai dai sun samwa makwabtansu na hagu da dama hasken saboda sanin hakkin MAKWABTAKA. Ku san dukka *yan mata da samarin garin sun hallara a kofar gidan da daddare, babu abinda yake tashi sai kidan kalangu, samari suna ta shadi amarya tana yi musu liki. Faduwa kuwa ta sami abin kallo tana yi tana mamakin yadda suke tikar junansu da sanda. Fargaba daya Umaimah ta dinga yi yadda Faduwa da *yarta zasu iya bacci a dan tsukururun dakinta amma ta ga sun baje suna baccinsu babu abinda ya dame su. To menene babu a dakin? An shimfida kafet, ga injin janareto ya kwana yana yi, ga fanka, an fesa Shaltos duk an saka net a bakin wundo da kofar shiga sauro ba zai iya shigowa ba. Sannan ga firij da ruwan sanyi duk Sabitu ya je birin ya taho da ma'aikacin Nepa ya zo ya hada mata komai. Ranar juma'a ake yin biki, kawayenta daga Gombe mata kakaf sun hallara kowacce ta ci ado, sai ga Lamijo, Umma da makwabciyarsu Salma, Hanif ne ya kawo su a motarsa. Taro ya yi taro dan wasu da yawa ma amarya bata sansu ba suka taho cin arziki, abinci dai mai suna abinci kowa sai da ya ci ya bar shi. Amarya ta yi ta shigar kaya kala-kala ta na canjawa kai ba zaka ce amaryar nan daga Rugar nan ta fito ba saboda ta iya tsara ado. Ma su daukar hotuna da bidiyo ma sun zo suna ta daukar amarya da jama'arta, Matawata ta kasa shigowa saboda kunya. Makada daga Rugage daban-daban suka zo suka hau wasa ba tare da an gayyace su ba. Sun sha liki daga wajen Umaimah da kawayenta. Da yamma baki suka zo daga Gombe irin su Lamijo suka fara haramar komawa gida, idan zaka tafi da himilin kayan biki za'a hadoka da leda-leda a ciki akwai memo, kalanda kofuna, farantai duk masu dauke da hotunan ango da amarya kawayenta su Aisha sun yi kokarinyi mata duk wadannan. Da yawa daga cikin kawayenta sun zo da shirin kwana, kadan ne suka tafi. Da daddare aka yi ta sa wasanni iri-iri har zuwa sha biyun dare sannan aka tashi sai kuma gobe. ____ RANAR DAURIN AURE Washe gari asabar ita ce ranar daurin aure za'a daura da karfe goma sha daya na safe. Karfe takwas saura mintina yara suka shigo gidan su Umaimah kace-kace suka iske ta a cikin masu girki suna ta faman hadawa bakinta shayi, dankali, doya da wainar kwai, su ka ce ta zo in ji wani mutum mai mota yana kofar gida. Babu wanda ta kawo a ranta sai angonta Abdul-Sabur, ta yi mamaki yadda suka iso da wuri. Nan da nan ta daka tsalle ta shiga daki ta canja kaya masu kyau ta fito, tana fitowa kofar gida sai ta ga ba Abdul-Sabur ba ne maimakonsa Abdul-Basi ta gani dan haka ta ki ta karaso in da yake kuma ta bata fuska babu ko annuri a fuskarta. Ya bude kofar mota ya fito cike da murmushi ya tunkaro ta sai ta koma cikin zaure ta tsaya, shima ya shigo gami da yi mata sallama. Amma magana yake yi cikin nadama har da hawaye a idanuwansa. Ya ce "Yanzu Umaimah kin yarda ki rabu da ni ki auri wani bare wanda ba'a san asalinsa ba? Kin yarda ki rabu da ni har abada ni da *ya*yanki? Cike da gatsali ta ke amsa masa da "Eh Ya ce "Na roke ki kada ki yarda a daura miki aure da shi ki ce ni kike so a daura da ni, na yarda na yi miki laifi a baya yanzu na canja. Umaimah ta yi murmushin takaici ta ce "Ina ga kamanta bada Umaimar daka sani ada ba ce kake magana, a da ne duk yadda ka tsara min nake bi bana iya yi maka musu, a lokacin dana dauke ka miji, uwa, uba kuma yayana sai dai kash ka nuna min duk ba haka ba ne, ashe na kai ka matsayin da baka cancanta ba, domin Uwa da uba ba zasu kori dan su ba. Kana magana akan abunda kai kanka ka san ba mai yiwuwa ba ne, ina ga kamar kana bata bakinka, ai ka makara. Yarana kuma Allah Ya raya min su. Ta fashe da kuka ta yi wuf ta fada cikin gida ta bar shi anan a durkushe ya rike kai yana fitar da zazzafan hawaye na nadama. Dakyar ya mike a hankali ya nufi motarsa dan yaga yara sun fara zagaye shi suna kallo dan su abun kallo baya yi musu wuya a kauye. Gidan Dagaci ya nufa anan ya iske Baffa da Sabitu da sauran jama'a ana ta share- share ana shinfidawa baki tabarmi da kilisai ana shirin daurin aure, kowa ya tsorata da ganinsa saboda mummunan lafazinsa da yayi a baya. Amma sun saki jikinsu da suka ga bai shigo da suffar fada ba ko tashin hankali. Ya je ya durkusa a gaban Dagaci sai ya kece da kuka na nadama. Ya ce "Yanzu haka zaku yi min ku hana ni auren matata ku bawa wani bare? Alhali ina sonta, *ya*yanta suna neman kulawarta. Dagaci ya girgiza kai ya ce, "Ni da Baffan Umaimah bamu da yadda za muyi da kai sai dai mu yi maka fatan Allah Ya baka wata amma baka bi hanyar da za'a dawo maka da matarka ba. Ka zo ka sake bata magana kwanakin baya, zaginmu ne kadai ba ka yi ba. Takaici ma ya hana Baffa da Sabitu yin magana. Babu abinda Abdul-Basi ya ke sai kallon tsala- tsalan shaddojin da suke jikin Baffa, Sabitu da Dagaci , kana ganin dinkunan nan kasan ba'a kasar aka yi su ba dan dinkunan ma abin kallo ne, ya san duk Abdul-Sabur ne ya dinko musu. Ya kasa tashi ya tafi sai yake ji tamkar zasu ji tausayinsa su fasa daurawa da Abdul-Sabur a daura da shi. Amma ina sai ya ji ana cewa ga ango ya iso shi da tawagarsa, nan fa aka dinga shigowa da darukan naman kaji, kek, da su meat pie, bayan lemuna masu sanyi a cikin kankara kula-kula duk ango ne yayi oda daga Hotel har da ma'aikatan da zasu dinga rabawa su bawa kowa. Tabbas wannan daurin auren ya fita daban da na sauran daurin auren da aka taba yi a garin. A lokacin da Angon Umaimah ya shigo farfajiyar gidan Dagaci babu abinda kake hangowa sai walkiya kai kace yau aka ciro shi daga leda ya sha fararen kaya dinkin babbar riga ta sha surfani, ko ka ki kallonsa da idanuwanka hancinka zai jiyo maka daddadan kamshinsa. Yana gaisawa da jama'a domin waje ya cika makil har wani baya iya ganin wani, bayan hayaniyar jama'a, karar gangar makada sai tashi take. Daga gidan Gwamnati ma su Baban Hanif motoci da yawa suka ciko haka abokan Umaimah maza su Hanif kenan suma sun hallara, kusan kowa da motarsa ya zo. Jami'an tsaro wato *yan sanda motoci biyu aka kawo daga Dukku don su tabbatar da zaman lafiya saboda furucin da Abdul-Basi ya yi. Sai ga Abdul-Basi a gaban Abdul-Sabur suna kallon-kallo, mamaki ya hana Abdul-Sabur rufe bakinsa har sai da Abdul-Basi ya taso ya zo ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya ji sanyi a ransa, ya tabbatar ba yaki ba ne ya kawo shi sulhu ne. Tabbas Abdul-Sabur ya ji tausayinsa sai dai ya fi jin tausayin kansa dan ya fi shi son Umaimah, ba zai iya hakura ya bar masa ita ba. Aka daura aure a bisa Sadaki mafi kankanta yadda Allah Ya ce suna neman albarka a aurensu. Idan ka tona zuciyar Abdul-Basi a yau gawayi ya fita haske baki kirin da ita saboda bakin ciki, haka idan da za'a bude zuciyar Abdul-Sabur a yau tafi nono fari saboda farin ciki. Bakin ango ya kasa rufuwa dan murna, da ka gama daurawa aka ci aka sha. Sai ango ya aika aka kira amarya da kawayenta suka firfito kowacce da katon gyale saboda maza. Umaimah ta yi ta gaisawa da baki aka dinga daukar ango da amarya da jama'a a hotuna. Umaimah ta je ta durkusa a gaban Baban Hanif ta gaishe shi gami da yi masa godiya daya samu ya zo, ya yi mata fatan alkhairi gami da addu'ar Allah Ya basu zaman lafiya gami da yi mata nasihu akan ta bi mijinta su zauna lafiya. Daga karshe ya zaro katuwar ambulan ya mika mata ya ce ayi hakuri ga gudunmawarsa babu yawa, ta karba ta yi masa godiya sosai. Uhumm lallai kuwa babu yawa Naira na dukan Naira har Naira dubu dari biyu ce a cikin ambulan din. Ango da amarya suka kebe suna tattaunawa, ya dube ta duba na tsananin kauna ya yi dariya. Ya ce "Kin yi kyau amaryata. Ta kyalkyale da dariya ta ce "Ka fini kyau angona. Su ka yi ta tuntsura dariya jama'a suna ta sha'awarsu. Ya shaida mata tare suka taho da mata su Khausar kenan itama da kawayenta *yan Abuja, Ummana Fuse da tawagarta daga Ghana, *yan Gwarzo ma zokar da su, ya baro su a Gombe Hotel guda ya kama musu. Ya shiga maganar yadda za'a shirya daukar mutane masu tafiya Gombe wajen Dinner amma banda tsofaffi da yara. Su tsofaffi mata sai gobe za'a aiko da motoci a dibi masu zuwa rakiyar amarya Abuja dan haka yau ma su Nene sabon yini zasu aiwatar a junansu. Saboda yawan masu son zuwa Umaimah ta ce a kawo manyan bus ayi ta kwasa kawai har yadda motocin zasu kare. Haka kuwa aka yi aka turo motoci da yawa, kafin a tafi Umaimah ta je ta yiwa Baffa sallama gami da neman gafararsa, yana kuka tana kuka ya yi mata nasiha masu ratsa jiki, suka tuno da Yafindo da Nasiba sai kukan ya sake karuwa. Daga nan ta nufi gidan Dagaci shima ta yi masa sallama yayi mata fada akan ta bi mijinta gami da addu'a Allah Ya ba su zaman lafiya. Umaimah da jama'ar da suke da amfani a wajenta ne sune suka shiga tsala-tsalan motoci, *yan gayyar sodi na jiki sune suka sami shiga bus saura kuwa dole sai dai su yi hakuri saboda motocin sun cika. Har an tayar da motoci za'a tafi sai Matawata ta fito da gudu ta zo jikin motar da Umaimah take ciki tana kwankwasa gilashin, kuka take yi wiwi tana ambaton sunan Umaimah. Hankalin Umaimah ya tashi ta ce direba ya tsaya, ta bude kofa ta fito da sauri ta rike Matawata tana tambayar ta "Lafiya? Matawata ta sake rusa kuka ta ce "Umaimah, ki yafe ni kiyi hakuri na san na zalunce ki a rayuwa, na dade ina miki zalunci ba ki taba daga kai kin tanka min ba. Daga karshe dubi yadda rayuwarki ta daukakawa ni kuma dubi yadda na kaskanta. Ki taya ni bawa Ilah hakuri shima na cuce shi dana raba shi da wacce yake so. Umaimah, ke Ilah yake so ba zai daina sonki ba kuma, ni na sani dan Allah ku yafe min ni na raba soyayyarku. Umaimah ta matse hawaye ta ce "Daina kuka Matawata, na ya fe miki tuntuni kuma na yi miki alkawari ina tare da ke zan dinga taimakonki ta kowacce hanya. Kar ki damu zo ki shiga mota mu tafi Gombe zan baki wasu kayan ki saka acan. Kayan jikinta duk sun kode tamkar almajira sai tsamin dauda take aka saka ta agidan gaba, da Aliya ce a zaune a wajen Umaimah ta roketa ta koma wata motar. Faduwa da Aisha suka dinga kallon ikon Allah. Sannan suka kama hanyar Gombe. Dan Aunty.MAKWABTAKA 54 Da suka isa Gombe a gidan su Aisha, Umaimah da tawagarta suka sauka sai da karfe takwas na dare za'a fara gudanar da bikin. Da yamma bayan sun idar da sallar la'asar Umaimah da kawarta Aisha suka sulale kowacce sanye da katon hijabi kamar masu lekawa kofar gida ba tare da kowa ya san inda suka tafi ba, suka shiga motar Aisha suka fice Umaimah ce me tukawa. Ba su tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan iyayen AbdulBasi. Mamaki marar musaltuwa kake gani a fuskokin *yan gidan, daga shigowar Umaimah sai suka yi carko-carko manyansu da yaransu suna kallonta, gashi gaba daya gidan kowa ya hallara kamar wadanda suke meetin. Alhaji shi ma yana nan, Hajiya ma tana nan, ga Abdul-Basi zaune akan kujera ya rike kai dan takaici yayin da idanuwansa suka yi jawur saboda kuka. Daga dukkan alamu haduwar nan da akayi gaba daya hakuri aka taru ana bashi kuma ana yi masa nasihar maganar. Shigowar Umaimah ya sa kowa ya shiga zargi kala-kala amma abunda kowannensu ya fi zargi shine Umaimah ta fasa auren wancan ta dawo wajen Abdul-Basi. Ya mike tsaye a zabure yana mai fara'a gami da zuba mata ido yana saurare. Sun yi musu sallama tafi a kirga aka rasa mai amsawa saboda kowa ya fita hayyacinsa. Umaimah ta zo ta durkusa a gaban sirikinta ta gaishe shi ta juya ta gaishe da Hajiya, Aisha ma haka ta gaishe su suka amsa cike da fara'a da sakin fuska. Sannan suka gyara zama, Umaimah ta fara da cewa. "Alhaji, jiya aka daura min aure. Alhaji ya gyada kai ya ce "Alhamdulillah, na taya ki murna Allah Ya bada zaman lafiya. Abdul-Basi na tsaye akansu sai ya sake matsowa kusa, kalma daya ya ke so ya ji ta furta ita ce ta ce "Bana son wancan na dawo wajen danka Abdul-Basi, maimakon haka sai ya ji ta ce. "Yau ne za'ayi Dinner da daddare anan garin, gobe lahadi za'a kai ni Abuja can ma za'ayi wani bikin, shine nake so a taimaka a bani yara suma su zo wajen bikin ayi hotuna da su saboda tarihi. Sai kowa ya yi juyi na takaici, musamman Abdul-Basi wani dogon tsaki ya ja. Har zai yi magana, a fusace Alhaji yayi masa tsawa ya ce ya rufe masa baki babu ruwansa da wannan maganar, ba'a raba uwa da *ya*yanta ba dan ma a gidan wani zata je da kyauta zai bata *ya*yan in har zata iya rikewa, rikon da sai Uwarsa. Daga dukkan alamu Hajiya ma magana take so ta yi amma tsoro ya hanata dan ta san itama tsawar zai yi mata a gabansu, dan ransa a bace yake. Umaimah tana ta murna sai godiya take yi masa, ya nuna mata dakinsu ya ce ta shiga ta dauko su da kayansu su je asha biki lafiya. Su Umaimah suka tashi suka shiga dakin tana daga labule tayi sallama suka gane muryarta zo kaga tsalle, ihu, da danewa. Ta shaida musu ta zo daukarsu zasu je biki dan haka su dauko akwati su zuba sababbin kayansu ta taya su zabe aka cika akwati suka fito tayi musu sallama suka fice sai harara amma babu wanda ya isa ya ce su dawo, ga Alhaji a zaune, ya kasa, ya tsare, ya raka. Da daddare aka fara gudanar da bikin Dinner, waje yayi kyau, abinci ya wadata masu dadi kalakala, jama'a sun hallara har su Lamijo. Bangaren *yan uwan ango daban, bangaren abokan ango daban, na *yan uwan amarya daban, haka amarya da ango bangarensu daban wato 'high table. Amarya da ango sun caba ado sun yi kyau sosai kuma sun dace da juna, kowa yayi sha'awarsu, *ya*yanta sune aka saka a gaban ango da amarya yayin shigowarsu, kayansu iri daya kuma sun rike fulawa. Ba'a tashi daga shagali ba sai karfe goma sha dayan dare ana ta rakashewa. Hotel din garin nan daidai ne Abdul-Sabur bai kama ya zuba bakinsa ba. Aka tsayar da shawara washe gari lahadi da sassafe kowa ya shirya ya fito za a kama hanyar tafiya Abuja kai amarya. Haka kuwa aka yi da sassafe aka turo motoci Dugge aka debo su Nene da jama'arsu a zo aka hadu aka kama hanya, motoci sun yi guda dari kowacce ka samu kaduru kawai. Haka motar amarya da kawayenta daban ta ango ma da abokansa daban. A jere aka tafi ana ta nishadi a hanya sai tafiyat bata yi musu nisa ba. Allah cikin ikonsa aka isa da wuri. ABUJA Ashe anan ma Abujar lafiyayyiyar liyafa aka hada musu makeken wajen yin bikin nan mai tsadar gaske wato 'M and B Gardern'. Shamsuddin mijin Khausar ne ya hada musu wannan. Manyan gidaje aka tanada na saukar baki, gidan maza daban na mata daban anan kowa ya baje yana hutawa ba'a je gidan amarya ba tukunna sai bayan an dawo daga Dinner da daddare. Kafin su iso an tanadar musu abinci kala-kala, kowa ya ci amma ya rage waje a tunbinsa in da zai dura abincin da za'a ci a wajen Dinner anjima. Umaimah ta dankawa Aisha amanar *ya*yanta ta ce ta dinga kula da su a wajen bikin daga nan har zuwa Gombe bayan biki ta mayar da su gidansu amma ta ci gaba da ziyartarsu tana tambayarsu abubuwan da suke so, sai ta kira Umaimah a waya ta fada mata ita kuma zata turo mata ko meye ta kai musu. Aisha ta yarda ta karbi amana dan tana da son yara kasancewar bata da kanne. Kafin taga yadda hali yayi tana da burin ta daukosu ta rike su nan gaba kamar yadda Alhaji ya bata zabi ta san Abdul-Sabur bawan Allah ba zai ki ba. Wajen bikin ma (Hall) abun kallo ne haka duk inda ka waiga fararen fata ne suke haskawa wato turawa abokan Abdul-Sabur ne suka zo daga Ingila, Indonosiya da Malaysia. Sai ga babban bako ya shigo wajen aka gabatar dashi sai kowa ya mike tsaye saboda girmamawa wato Uncle Hamaza. Wannan ne karo na farko dalili ya yi dalili ya taba zuwa Najeriya, a dalilin Abdul- Sabur. Su ba'a wahalar da su wajen kai su Gombe ba aka hada musu ta su liyafar anan. Ba kowa aka bari yaje ba sai wayayyu hadaddu. Zabgi amarya ta zuba kyau dan ba a gida aka yi mata kwalliya ba, a kanti aka yi mata kuma baturiya ce ake biya take shirya amare dan haka idan har baka san Umaimah ba sosai, sai ka ce an canja ta, ba ita ba ce. Dan gaba daya ta sake saboda kyau, kayan jikinta ma abun kallo ne. Da zarar Abdul-Sabur ya dube ta sai ya fara godiya ga Allah da Ya bashi Umaimah. Daga wajen Dinner aka dauko amarya sai aka nufi gidanta, Allah mai halitta ita kanta amarya bude baki ta yi tana kallon kayan alatu da ginin gidan kansa. Wasu abubuwan ma basu taba ganinsa ba duk zaman da suka yi a Malaysia. Ya dankara gida ya zuba kayan alfarma faluka kala-kala kowanne da kalar kujerunsa da labulayensa haka dakuna daban-daban gadaje iri-iri *yan kamfani. Haka bangaren Ummana Fuse itama ya hadu kai ka ce itama amaryar ce, katon falo, dinning area da dakuna guda biyu kowanne da bandakinsa a ciki, a ranar ta tare da kayanta ita da danginta na Ghana. Khausar kuma ta tafi da danginsu na gwarzo gidanta suka sauka acan. Babu abinda Umaimah take yi sai kukam dadi, ana ta lallashi gami da yi mata murna da addu'oin Allah Ya dauwamar da ita a gidanta ya basu zuriya ta gari. Kowacce ta ga kyakkyawan gida sai ta makale ta ce anan zata kwana, manya suka ce ba za'a batawa amarya da ango gidansu ba kowa ya fito ya tafi masaukin da aka ajiye su dazu ga motoci can a kofar gida suna jira. Dakyar amarya ta roka aka barta da kawayenta guda uku su taya ta kwana, Aisha, Faduwa da Khadija sai kuma *ya*yanta su Babangida. Abdul-Sabur ma a wajen abokansa ya kwana a hadadden Hotel din nan Nicon, amma fa su dukkansu amarya da angon a zaune suka kwana bacci ya gagare su dan murna da begen junansu suka hana masu taya su kwana bacci sai hira ta barke. Washe gari bayan kowa ya yi wanka daman Abdul-Sabur yayi magana abin karin kumallo da masu Hotel, sai suka shiryowa baki abinci kala-kala sai abunda kake so zaka zuba kowanne gida an mika na su. Bayan kowa ya ci sannan aka sake haduwa a gidan amarya, aka dinga hayaniya ana raye-raye aka sake kallon abun da ba'a karewa kallo jiya ba, sannan aka yi ta daukar hotuna ba adadi. Daga karshe aka dinga jifgowa amarya gudunmawa da yawa daga bangarori daban-daban. Kudi mai sunan kudi kuwa baya kirguwa, a take ta zama miloniya saboda manyan attajirai abokan Abdul-Sabur turawa basa harka da Naira daga Pounds sal Dallars haka suka dinga zarowa suna mika mata. Kawayenta da *yan Uwan ango sun yi kokari sun hada mata kudi da yawa. Haka Hanif ma ya aiko mata katuwar ambulan da kudi Naira dubu dari ya ce shi da sauran abokansa maza suka hada mata. Faduwa da Sagir ma kudinsu mai yawa a ambulam suma kuma Dalla ce suka bata. Ga babba da kansa Uncle Hamza ya yi musu yayyafin Pounds, gudunmawarsa ta fi ta kowa yawa. "Shin mafarki nake yi ko idanuwana biyu? Umaimah take tambayar zuciyarta. Dan ta rasa da bakin da zata yi wa jama'a godiya. Sai kuka kawai take yi da alama ana yin kukan dadi dan ita ta rabu da kukan bakin ciki kuma a rayuwarta. "Talauci a sauka lafiya, marhaban da zuwan arziki" Inji zuciyar Sabitu a lokacin da yake hango kudi yana ta ambaliya a hannun *yar Uwarsa. "Samun naku shine namu. In ji almajiri Sabitu. "Allah Ya bada zaman lafiya, mu mun tafi Umaimah sai watarana. Haka kowannensu yake ta fada a lokacin da suka shiga motocinsu zasu tafi. Dakyar aka banbare Babangida da Bilal daga jikin Umaimah, sai hankalin ta ya sake tashi matuka. Umaimah bata daina rusa kuka ba, wannan karon kukan na bakin cikin rabuwa da *yan uwa da kuma gida ne, dan kowa yabar gida, gida ya bar shi. Tana ji tana gani kowa ya tafi ya bar ta, Aisha da Umaimah suka rungume juna suka yi ta kuka ba adadi har sai da suka saka jama'a da dama kuka. Saboda tausayi, tabas sabo turken wawa ne. Faduwa da Sagir dinta kuwa ba su yi sallama gaba daya ba zasu tafi su dawo dan ba yanzu zasu koma Cairo ba sai ta zaga dangi ta nuna mijinta da *yarta. Bayan ta zagaya gidan danginta na Abuja, Kaduna da Zariya zasu wuce su gaisa da dangi. Sai ta wuce Kano nan ma akwai su daga nan sai su wuce Sokoto mai dungurungum in da cibiyar take, daga dukkan alamu zata dade a kasar. Abdul-Sabur ne ya dauki nauyin basu mota da direban da zai kewaya ko ina dasu. *** Kowa ya yoye babu kowa kuma gida ya rage daga amarya sai angonta sai kuma so da kauna sa suke tsakani. Dan Ummana Fuse ma da mai aikin da aka daukar mata duk gidan Khausar suka gudu, da taro ya watse sai ta ji zaman babu dadi, suka tafi can zasu yi kwanaki sannan su dawo. Dakyar Abdul-Sabur ya lallasheta ta shigo gidan daga bakin get, ya dauko nankici daga aljihunsa mai kamshin gaske ya mika mata, ta karba a sanyaye ta goge hawaye. Cikin tattausan lafazi yake magana. Ya ce "Yanzu Umaimah har kuka kike yi dan *yan uwanki sun kawo ki wajena sun tafi sun bar ki? A tunanina ni ne kadai mutum daya tak da zaki so ki dauwama tare da ni. Ta gyada kai ta ce "Haka ne. Ya ce "To meyasa kike kuka alhali kin gama kukan rabuwa da Baffa tun acan? Idan baki manta ba na taba fada miki cewar kin daina zubar da hawaye daga ranar da kika hadu da ni. Ki yi shiru ki daina kuka Umaimah Allah ne gatanki, Abdul-Sabur ne gatanki. Kin rabu da maraici daga yau, kin rabu da takaicin da namiji, kin rabu da cin amanar makwabtanki kuma kin rabu da babu insha Allah. Farin ciki ya rufe Umaimah ta yi sauri ta durkusa a gabansa ta yi masa godiya, ya girgiza kai ya mika hannu ya tashe ta tsaye. Ya ce "Ki daina yi min godiya, ke dolena ce babu abinda ba zan iya yi miki shi ba aduniya. Ta yi murmushi ta lumshe ido ta ce "Ko baka fada ba na san da haka, na yarda da tarbiyarka, ka cika dan halak. Na maka alkawarin nima zan zama baiwarka babu abinda ba zan iya yi ba in har zan kyautata maka. Ya yi ajiyar zuciya ya yi murmushi ya ce "Na yarda da tarbiyyarki nima kuma na yarda da son da kike yi min na tsakani da Allah. Mu je daki mu yi alwalla mu yi sallah raka'a biyu mu godewa Allah, mu kuma roke Shi Ya kare mu daga duk wata fitina da ke cikin aurenmu. Umaimah ta bishi suka shiga daya daga cikin maka-makan dakunan da suka jere a saman bene. Babu abinda yake tashi a cikin dakin daga sanyi Ac sai kamshi na alfarma. Tabbas idan kana cikin dakin nan ba zaka san yanayin da gari yake ciki ba, dare ko rana, zafi ko sanyi, guguwa ko ruwan sama. Dan haka ango da amarya suka yi lif a cikin ni'ima basu sake tunawa da hayaniyar waje ba, sai ka rantse babu bil adama a cikin gidan nan. Asuba ta gari Abduumimah. Abdul-Sabur yana jin dadin zama da amaryarsa sosai ya same ta mace mai ladabi da biyayya da godiya. Ba ta da kwadayi haka bata karya da dogon buri irin na *yan matan zamani, duk abunda ya bata sai ta karba da murna ta yi godiya. Ga ta mace mai kunya da tsoron Allah dan akwaita da ibada, ya yarda da ita ya san ko baya nan ba zata ci amanarsa ba. Tana masa biyayya matuka dan bai taba hana ta abu ta yi ba, haka bai taba saka ta abu tayi masa musu ba. Abunda ya kara masa sonta shine tana kula sosai da tsohuwar kakarsa wato Ummana Fuse. Ita ce mai yanken farcenta, ta tsefe ta wanke, ta kitse mata gashinta. Haka kawai sai Umaimah ta shiga kasuwa ta siyo mata atamfofi ta kai mata dinki, ta kawo ba tare da kowa ya sani ba kuma da kudinta. Sai dai Ummana Fuse ta fada musu shiyasa Khausar ma take matukar son Umaimah har take fadawa Abdul-Sabur cewar ashe ta so tayi kuskure da ta so hana shi auren Umaimah a Malaysia. Rayuwa kenan duk wanda yayi zalunci tun daga duniya zai fara ganin ba dai-dai ba. Sai ga Faduwa ta dawo daga Sokoto wurjanjan a gidan Umaimah hankalinta a tashe. Har hankalin su Abdul-Sabur ya tashi da suka ganta a haka, kafin ta basu labari. Ta fayyace musu irin abubuwan da ta gani a Sokoto shine ya tayar mata da hankali. Suka gyara zama suka tambaye ta me ta gani? Ta zauna ta basu labarin komai ta ce "A sakamakon hanata gadon Mahaifinta da suka yi sun hadu da bala'ai kala-kala gidan gaba daya babu wanda ya ci gaba. Talauci ya ruftowa, matan Babanta da *ya*yansu haka ma kawunnanta komai ya kare. Gaba daya kuka suke suna neman gafararta wai sunsan sun zalunce ta, yanzu abincin da zasu ci ma ya gaggaresu. Sai ita ta dinga taimaka musu duk da *yan kudin da suka rage ya kare a can. Yanzu ma akwai alkawuran da ta yi zata aiko musu da kudi idan ta koma Cairo. Har da masu rokarta a cikin kannenta wai zasu biyo ta Cairo ta samar musu aiki koda share-share ne saboda talaucin ya ishe su, ta ce a'a ba sai sun biyo ta ba zata dinga yi musu aike. Abdul-Sabur ma yayi alkawari idan ya tashi bayar da taimako zai dinga kai musu agaji. Sati guda cur Faduwa da Sagir suka sake yi a gidan su Umaimah sunji dadin karramawar dasu Umaimah suka yi musu sun ji dadin zama a Abuja dan an kewaya da su ko ina, suna ta sha'awar ango da amarya yadda suke zaune lafiya cikin tsantsar so da kauna. Ba'a son ransu suka rabu ba, sai suke ji kamar su ci gaba da zaman kamar yadda suka zauna a Malaysia. Idan suka zauna sai su raba dare suna hira, har sai da Sagir ya fara koyon Hausa sabida tsabar Hausa da yake ji idan suka hautsine da hira. Kyautar girma su Abdul-Sabur suka yi musu, suka kaisu filin jirgi suka hau suka tafi Abdul-Sabur yayi musu alkawari zasu zo Cairo suma su kwana biyu Asuba ta gari Abdulmaimah! ** Allah cikin ikonSa ya cikawa Abdul-Sabur gaba daya burinsa daya kudira na taimako, gaba daya alkawuran daya dauka sai da ya cika su, tun kafin shekara ta zagayo. Shi yayi komai a auren Sabitu da Aliya, haka Ilah da Furera, amma Baffa ya hana su tarewa a Gombe ya ce su ci gaba da zama a Dugge anan suka saba iyaye da kakanni. Gidajen sumunti Abdul-Sabur ya giggina musu a garin masu kyawun gaske, haka gidan Baffa gaba daya aka sauke na kasa aka kafa na siminti, sannan ya ginewa Dagaci nasa shima na siminti, sai suka haskaka garin. Ya gina katafaren gida a cikin Gombe a unguwar masu kudi, na Umaimah ne idan sun zo gari suke sauka. Dan zamanta a Gombe ya so ya fi na Abuja yawa saboda tana da abubuwan yi a garin dole sai tana nan zai yiwu. Abdul-Sabur ya fahimce ta, bashi da matsala ga saukin kai idan ta taho sai ya biyo ta su zauna. Umaimah bata manta da mutanen garinsu ba. Abubuwan da garin zai ci gaba take yi musu hanya a gwamnati, ana saka su a cikin lissafi yanzu. Rubutu take yi a jaridu da mujallu akan a dinga tunawa da Rugage ana tallafa musu da abubuwan more rayuwa kamar irin na burni. Dan suma mutane ne, *yan kasa, kuma *yan jiha. Dan suna jefa kuri'a idan lokacin zabe ya zo, saboda haka suna da alhaki akan gwamnati. Nan da nan ake sauraron kiranta dan su Hanif sun sami aiki a cikin gwamnati sune a gaba-gaba ana damawa da su a siyasa da mulki. A kowacce ma'aikata Umaimah sai ta ga kawarta ko abokinta ne da suka yi karatu a Malaysia masu rike da wajen dan haka nan da nan takardarta take isa gaban gwamna, kuma su saka baki ayi mata abunda take so. An kai ruwan fanfo garin Dugge, wutar lamtarki, service din waya, anyi titina, da uwa uba Makarantar boko da malamai kwararru. Da kanta ta zo ta tara iyayen yara ta yi musu nasihu na wayar da kai akan su saka yaransu a makarantu dan su yi ilimi kamar yadda ta yi, suma su inganta rayuwarsu. Tabbas Umaimah ita ce babbar musali, ita ce abar da zasu yi kwaikwayo da ita, nan da nan suka yi amanna da wannan kira nata su saka *yan*yansu a makarantu. Makarantun Islamiyya ta bude da kanta ta dauko malamai kwararru ta zuba suke koyarwa har da Sabitu da Ilah, tana biyanzu albashi duk wata.... Shafin karshe a shafe yake ma'ana rubutun ya ba ce don haka na ke sanar da ku cewa mun yi Bankwana da MAKWABTAKA ayau. Kuma nima nayi bankwana daku ayau. Alhamdulillahi. Ina godewa Allah da yardarSa da Amince war Sa daya nuna mana wannan lokacin na ranan karshe a littafin Makwabtaka. Ina mai godiya a gare ku en uwa da addu'oin ku da fatan alkhairi a gare ni. Nagode.. Nagode.. Nagode sosai Allah yabar xumunci. Ina kuma mai nemon afuwa da yafiya ga duk wanda na batawa ko wani maganar da baiji dadi ba ko wajen jinkirin post ko wajen kuskeren rubutu da sauran su. Na yafewa kowa tsakani na da ku baki daya. Allah ya yafe mana kura-kuren mu baki daya manya da kanana. Aamiin. Sannan ina mai nemon addu'r ku Auntyna bata jin dadin jikin ta kwana biyu kuma nima mun koma makaranta dukka muna baran addu'o'i daga bakunan ku masu Albarka. Allah yabiyawa kowa bukatun sa na Alkhairi... Aamiin. Sai wata rana... Wa'assalam.. Abbas Abdulkadir Hada Ebooks dinnan ya zo maku ne daga shafin http://hausaebooks.cf Ku ziyarci shafinmu don daukio wasu ebook din akan wannan adireshi http://hausaebooks.cf