Lesson Tips
Lesson Tips
Assalamu Alaikum
Sunana @MohiddeenAhmad, ni ne zan gabatar muku da darasin Digital Marketing a wannan gida wanda
makarantar yanar gizo Flowdiary Academy da kungiyar Zo Mu Gina Kamfani Initiative suna dauki nauyi.
Da farko na shiga harkar Digital Marketing akalla shekaru 6-7 da suka gabata muna gwagwarmaya a
cikinta. A cikin wannan darasin zan koyar da abun da na sani tare da kafa hujja da littatafai da batutuwan
kwararru.
i. Kamar yadda wannan ajin ya kasance kyauta, za mu yi shi ne sau uku kacal: Day 1, Day 2 da kuma Day
3.
ii. Duk karshen darasi zan yi kokari na turo wasu littatafai da za su mana amfani
iii. Bayan an kamala shikenan kowa zai iya fita, amma ba mu yarda da kowanne irin talla a ajin ba
iv. Ba a rufe kofar yin magana ba, don haka kowa zai iya yi amma ka bari sai bayan an kamala darasi kafin
ka yi tambayarka
v. Kada ka turo wani abu da bai dace ba, idan za ka yi tambaya to ka yi rubutu ba voice note ko video ba
vi. Ga abubuwan da za mu tattauna a kansu a kasa.
Table of Contents
1. Menene Digital Marketing
2. Amfanin Digital Marketing
3. Matakan Digital Marketing da Bambancinsa da Traditional Marketing
4. Amfani da Website ko Blog
5. Bayani da Amfanin “SEO”, “SMM”, da “SEM”
6. Bayani da Amfanin Email Marketing, Affiliate Marketing,
7. Content Writing and Marketing
8. Digital Assets
9. Digital Advertising
10. E-Commerce Management
Wato kasuwancin yanar gizo kamar yadda muka sani yana da ma’anoni daban-daban. Don haka wasu
sukan cire rai a yin amfani da shi wajen fadada kasuwancinsu na zahiri ko kuma fara wani sabo. To amma
magana gaskiya shi ne yana da sauki matuka. Matukar dai za aka jure da kalubalen da za ka iya fuskanta
ko wata wahalar da za ka sha, in Allah Ya yarda kai ne da riba.
Sannan akwai wani abu da ba mu sani ba shine hada hannu a kasuwanci na da matukar fa’ida ta yadda
dukkanin masu hannu a kasuwancin za su kasance masu morarsa har ma wadanda ba sa ciki. Wannan
dalilin ya sa muka samar da tafiyar #ZoMuGinaKamfani , don karfafa wa mutane gwiwwa su hada hannu
su yi abu na kansu.
Cikin sauki kuma a takaice, Digital Marketing shi ne kasuwancin yanar gizo, walau saye-da-sayarwa, aikin
kwadago ko kuma kamasho –wadannan su ne bangarorin Digital Marketing. Bugu da kari, duk wani aiki
da mutum zai yi to yana karkashinsu ne.
Zuwan fasahar yanar gizo ne ya ba wa ‘yan kasuwa da matasa damar shiga harkar kasuwanci a yanar gizo,
don samun na kashewa da kuma fadada karkokinsu na kasuwanci na yau da kullum.
i. Awareness: wannan shi ne campaign da za ka fara yi don gayyato mutane zuwa ga kasuwancinka. Sai
dai a wannan matakin ne mafi yawan lokuta ake samun kuskure.
a. kada don ka bude shagon sayar da textile ka bude group ka saka mutane a ciki kana musu talla
b. kada ka rinka tura wa mutane tallace-tallace ta inbox
c. abun da ya kamata ka yi shi ne jan ra’ayin mutane zuwa ga kasuwacinka ta hanyar amfani da dabaru.
Misali:
i. Kada ka boye kanka, sunanka, hotonka, garinku, address dinka ko lambar wayarka ko email matukar ka
shirya yin Digital Marketing. Sannan kada ka yi hulda da duk wanda ya boye wadannan bayanan.
ii. Ka tanadi suna, logo, banner, phone number, email address na kasuwancinka ko kamfaninka
iii. Da farko idan za ka fara jan hankalin mutane game da kasuwancinka, sai ka yi posting a social media a
takaice game da kasuwancinka da yadda zai kawo canji a wannan zamanin, da fa’idar sayan kaya a
wajenka da kuma saukin da za a samu idan aka yi hulda da kai.
iv. Dole za ka yi sauki –wato discount don fara bayyana kasuwancinka da yadda zai dore
v. Yanzu sai ka tsaya ka ga me mutane suke cewa game da hakan, shin an karanta post din, wane result
aka samu?
ii. Engagement: wannan shi ne matakin da za ka gina mu'amala da mutanen da ke son kasuwanci da kai.
Ta nan za ka fuskanci shin suna son yin kasuwanci da kai ko kuma ba sa so, sannan su din kansu su
wanene?
Wannan shi ake kira tsarin attracting din 'audience' din da suka dace. Kamar dai yadda na yi bayani a
littafina Zo Mu Gina Kamfani cewa kowacce business tana nasara ne da inda ta fi dacewa, to haka idan za
ka dauki kasada ko kuma in ce gwada sa'a, to akwai matakansu daki-daki. Haka nan dai sanin customers
da abun da suke so. Don haka wannan shi ne mataki na biyu da ya kamata mu sani a shiga Digital
Marketing.
Ka san wadannan kuma ka tanade su da kyau. Za ka fahimci haka ne a lokacin da ka fara campaign dinka.
Za ka ga sun fara nuna sha'awarsu a kan business dinka.
iii. Acquisition: wannan matakin shi ne na samun customers. Duk wanda ya bi mataki na farko (ya ga
campaign dinka), sannan ya bi na biyu (ya nuna sha'awarsa game da business dinka), ya zo nan (zama
customer) a nan ne za ka yi kokari ka rike shi don ya zama customer na gaske.
iv. Consideration: mataki na gaba sai lura. Shin wane cigaba kake samu a campaign din da kake yi? Wane
impacts aka samu a tsarin da kake samu a kasuwancinka? A nan za ka rubuta duk abun da ka samu a
matsayin result.
Ka yi evaluating din tsarukanka na campaign da kuma abubuwan da ka samu na tsokaci daga mutanen da
kake musu campaign.
Idan mun gano inda muke samun matsala ko improving din kanmu yanzu sai mu gyara.
Masu tambaya yanzu kofa a bude take, za ku iya yi amma ban da voice note.
Fatan alheri.
Abu na gaba shi ne Blogging. Gaskiya yana da kyau, shi ne abu na farko da na tattauna a kan shi a cikin
littafina eBillions Mastery. Duk wanda ya saba da Blogging ba zai so barin shi ba. Bari na turo muku wani
dan karamin littafina 40 Benefits of Being a Blogger, inda na binciko wasu fa'idojin kasancewa Blogger har
guda 40. Na samu sakonni daga mutane da dama da suka karanta wadanda suka nuna sha'awarsu ga
Blogging sosai, kuma Allah Ya taimaki wasu daga ciki sun tashi.
Idan ka karanta kuma kai ma kana son samun blog naka na kanka cikin sauki da kuma araha, ka tuntube
ni kai-tsaye muna da kamfanin da yake ginawa, idan kana so har rainonsa za mu yi.
Haka nan dai Blogging yana daga cikin sabbin courses din da muka kawo makarantar Flowdiary Academy,
inda za a koya maka shi tare da sirrukansa da matakansa da yadda za ka yi monetizing dinsa ka samu kudi
da shi. Za a fara registration next week ranar Monday, 20th June, 2022 in Allah Ya yarda. Idan za ka shiga
sai ka yi niyya, sannan ga Facebook page namu inda muke saka duk wasu abubuwa:
https://facebook.com/flowdiary
To idan kana da blog ina mai tabbatar maka cewa matukar za ka ware lokaci ka rinka rubutu, walau da
Turanci ko Hausa, za ka samu alheri mai yawa. Kawai audience dinka za ka duba. Misali, yawanci za ka ji
ana cewa ana amfani da Google AdSense don samun kudi a Blogging, amma ba shi kadai ba ne hanyar
samun kudi. Ko ni ba na amfani da shi. A personal blog dina https://mdblog.org.ng sai na shafe watanni
ban yi rubutu ba, amma a haka nake samun wani abu. Akwai abokaina da suke samun sama da N70k duk
wata a blogging ba tare da yin wani babban aiki ba. Idan kuma za ka dage, ai sai ka ba wa N150k+ baya
duk wata. Wasu kamfanonin kuma miliyoyi suke hadawa a nan Nigeria, ka dauki misali da legit.ng, ko
kuma manyan bloggers din Nigeria irinsu Linda Ikeji wacce ke samun sama da N10m a wata da sauransu.
Ba ka bukatar ka yi karya ko yin batsa ko yi wa wasu sharri, hanya ce kawai za ka gina ingantacciya da za
ta zama other source of income dinka. Don haka idan kana bukatar fara blogging cikin sauki kuma ka san
sirrukansa, to ka shiga makarantarmu Flowdiary Academy. Idan kuma so kake a gina maka ka tuntube ni
kai-tsaye, kamfaninmu zai gina maka.
Abu mafi muhimmanci da ake so a blogging shi ne readers. Su waye za su karanta abun da kake
rubutawa, yaya kake rubutun, kuma me ya sa ake karantawa ko akasin haka? Matukar ka fahimci wannan
to ka gama da mataki na farko. Shi ma wannan na kawo bayani a kansa da dabarun samun kudi ta hanyar
rubuce-rubuce a cikin littafina Zo Mu Gina Kamfani. Matukar dai za ka yi rubutu mai kyau kuma a
karanta, to daga nan dabarun samu za su fara fito maka.
Misali mai sauki, akwai wani abokina da muka jima muna tare ana ce masa Yusuf Haruna (AKA Namijin
Duniya) blogger kuma youtuber ne sosai, yana rubutu kuma yana bin tsarin blogging da kyau, sannan
yana flipping digital items wato saye da sayarwan kayayyakin yanar gizo kamar su Google AdSense
account, YouTube channel, blogs da sauransu. Ya rubuta wani littafi mai suna Sirrin AdSense sai ya sanya
shi cikin Android App ta yadda sai ka yi subscribing sannan ka karanta. Yace min a kasa da 24hours ya
samu kusan N100k. Sannan bayan kamar mako guda kuma ya yi discount, nan ma ya kara samun
makudan kudade.
Haka nan dai idan ka nutsu ka fahimci yadda abubuwa suke tafiya, za ka iya hiring din freelancers su gina
maka abubuwa ko su rubuta maka littafi ko su yi maka wasu rubuce-rubuce. Shi kansa abokin nawa yana
sayen articles na sama da N200k kuma ya samu kudade ninkin dinsu.
Duk wadannan ideas din ba za su zo maka ba idan ba ka san Digital Marketing ba. Kun ga dai yana garinsu
yana aikinshi a gida amma yana making makudan kudade, kuma haka matasa da dama suke yi. Wannan
zamanin na na'ura na matasa ne, gaskiya kar ka bari a bar ka a baya. Akwai matan da na sani da suke
wannan aikin sosai, kuma suna samu asirinau a rufe. 'Yar'uwa ke ma kar ki bari a bar ki a baya, Digital
Marketing ku yake nema, kuna zaune a gina kuna making thousands of Nairas.
Don wannan dalilin ne muka kara kawo sabon course din Digital Marketing a makarantar Flowdiary
Academy inda za ka koya kuma ka hau hanya. Flowdiary Academy ba a nan ta tsaya ba, akwai wani
course da muke yi mai suna General Entrepreneurship kyauta wanda yake a matsayin GST, inda ake nuna
wa dalibai yadda za su yi amfani da skills din da suka koya a makarantar don su sarrafa su su samu kudi su
ginu da kansu.
Duk wadannan suna daga cikin abubuwan da za a koyar a ajin Blogging a makarantar Flowdiary Academy
in Allah Ya yarda.
To amma ba a nan Content Writing and Marketing ya tsaya ba, kalmar "Content" ta shafi abubuwa da
dama, kamar rubutu, hotuna, bidiyoyi da designs da sauransu. Wadannan abubuwan matukar za ka iya
hada su ka tallata su a yanar gizo, ina mai tabbatar maka cewa za ka samu alheri matuka
Misali, ka mallaki blog sai kake so ka yi building din email list, to da farko abun da za ka yi shi ne ka fara
ba wa mutane kyautar wani abu, kamar yi musu kyautar wani littafinka ta yadda idan suka sa email nasu
za ka tura musu ta nan. To wannan shi ne misalin content marketing.
To amma kai mece ce ribarka? Na san haka za ka tambaya. Da farko ka san cewa a hankali a hankali ake bi
a samu yarda (trust) a wajen mutane har su zama readers dinka. Idan ka fara da bayar da kyauta, abu na
gaba da za ka yi shi ne yin na kudi (paid) wanda za ka tura musu tallanshi, ka ga cikin sauki za ka sayar da
kayanka.
Na gaba shi ne game da bidiyoyi wanda tuni mun san yawanci yanzu an koma harkar YouTube kuma ana
samun alheri sosai a wajen. Za ka bude YouTube channel kana daura bidiyoyi, ka saita AdSense su kuma
su rinka biyanka. Idan ma ba ka samu wannan ma, da yake yanzu bloggers ba sa damuwa da shi, still dai
suna sarrafa shi ta sigogi da dama a wannan matakin su samu kudinsu.
Digital Assets
A wannan zamanin na yanar gizo, Digital Assets su ne kayayyakin yanar gizo wato Digital Items da muke
gani yau da kullum a yanar gizon.
Ga wasu kamar haka
1. Cryptocurrencies
2. eBooks
3. Videos
4. Audios
5. Graphic Designs
6. Applications
7. Websites/blogs
8. YouTube channel
9. AdSense accounts
10. Social media accounts/pages/groups etc
A matsayinka na Digital Marketer akwai bukatar ka san duk wadannan da kuma yadda ake sarrafa su, da
yadda kai ma za ka fito da taka hanyar sarrafa su ka samu kudi.
Bari in ba ka misali mai sauki, akwai wadanda sana'arsu kawai ita ce saye da sayarwan irin wadannan
kayayyakin.
Digital Advertising
Digital Advertising shi ne tallace-tallace a yanar gizo. Wato yanzu idan kana so harkarka ta bude sosai, to
kawai ka shigo Digital Advertising yadda kowa zai santa.
2. Google Ads
Na biyu shi ne Google Ads wanda na kawo misali a kansa jiya, sai dai shi ya dan fi Facebook Ads tsada,
kuma dole sai kana da website.
3. Twitter Ads
Twitter Ads ma kamar Facebook Ads ne, shi ma ba shi da tsada sosai. Za ka iya promoting account dinka
ko tweet.
...da sauransu
E-commerce Management
Shi ma wannan shi ne abun da muka yi magana jiya a kan E-commerce wanda na kawo misali da
Stackplaza.
Kamar yadda na kawo a bayanin farko cewa idan za ka fara sayar da kaya a yanar gizo, to ka fara duba su
waye customers dinka, me suke so, a ina suke da sauransu.
Duk za ka binciki wadannan ka san yaya suke da yadda za ka bullowa lamarin kasuwancinka. Sannan yaya
tsarin kasuwancin naka gabadaya zai kasance.
Na tattauna batutuwa da dama game da wadannan da tsarukan kasuwanci da yadda ake shiga kasuwa da
makamantansu a littafina Zo Mu Gina Kamfani. Idan kana bukata ka tuntube ni.