Mr. Bello CMPLT

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 198

: *MR BELLO..!

*
_(The young Teacher)_

*NA*

*JANAFTY*💕
*Wattpad:Janafnancy13*

_*Bismillahir Rahamanir Rahim in the Name of ALLAH the most Beneficient the most
mercerfull praise be to Allah lord of the words.....*_

_Assalamu Alaikum my Follow fans,am starting my new Book i ask ALLAH subhanahu
wata"ala to guide me throught and make me it sussufull till End Ameen ya Allah_

*Copycats are not allowed to transform this book by any means without the prior
written permission of the writer.Immediate action will be taken if caught�?*

? _DEDICATED TO: *Bashir Sufyan Sardauna* and *Nazifi yarima*❤️Sakallahu fil


jannah Dudes..For ur all Support,care and Concern..Allah yabar zumunci Ameen_

*....SHIMFIDA....*

*🅿�?1*

*GGUSS KWATAR-KWASHI*

A haraban Babbar Makarantar ta GGUSS, Goverment Girls Unity Secondry School Kwatar-
kwashi Dake Tsakanin Dajin kwatar-kwashi Zuwa Gusau, Da Misalin ƙarfe 10:30am na
Safe.

Daga Cikin Babban Filin Haraban Makarantan Na Hangi ɗalibai Birjit ba Adadi mata ne
Zallah Ta Ko"ina Suna Yawo Wasu Suna Tsaye da Tarin Akwatunsu da Jakunkunansu Wasu
kuma Suna ta Tururuwan Shiga Doguwar Mota Fara mai Ɗauke da Tambarin GGUSS KWATAR-
KWASHI, gefe ɗaya kuma Kowaccensu Tana Sanye da Uniform ne Ajikinta wasu Nasu Wando
light green ne Both Riga da Wando da Ɗan kwali sai Farin Hijabi A yayinda Wasu kuma
ke Sanye da Dark green d'in Wando sai Both Farin Riga da Da'n kwali da Hijabi.

A yadda Haraban Makarantan ta Rikice da Hayaniya da Murna da Iface ifacen Ɗalibai


zaka Fahimci Hutu ne Ɗaliban Suka Samu Tun ma Ba Daga yadda Wasu Iyayen Ɗaliban
keta Zuwa Ɗaukan yaransu Wanda basu yi Register da Motar Makaranta ba, Ayayinda
Wasu ke Ta Fitowa Bakin Get d'in Mkrantar ga masu Mashi nan suna ta Ɗaukansa Zuwa
inda zasu Hau Mota Zuwa Gida.

Daga chan ɓangaren Na Hangi Wasu 'Yan mata su Uku Tsaye A bakin Wata Bishiyar
Dalbejiya Dukkansu Gabansu Akwai Tarin jakunkuna, da Sauran Tarkacensu masu yawa,
sakamakon Wannan Hutun Third term ne ƙarshen Zangon karatunsu na Jss 3 sai Shiga
SS1 Kenan, Suna Sanye da Uniform ɗinsu na Junior, light green both Riga da Wando da
Ɗankwali sai Hijabi Fari, Dukkansu Ukun Tsawonsu Ɗaya Sai dai kuma Biyu Daga Ciki
Farare ne Tas, Sai Ta Ukun Wacce ke Tsakiyansu Ɓaka ce Sulub ammh Bak'inta bamai
Duhu bane mai haske ne, Wanda Ke Shining, Doguwa ce Mai K'arancin Girman Jiki,
Fuskarta tana da Faɗi Ammh ba Sosai ba, Tana da Manyan Idanuwa Masu Ɗauke da Gashin
Ido Zarara sai Ƙaramin bakinta Wanda Yake Baƙi baki, A shekaru Dukkansu bazasu gaza
Shekaru goma Sha Shidda ba Daga Kallon Farko Zaka Fahimci Zallar Ƙuruciyarsu A
lokacin.

Daga bayansu sukaji Ance " *ANEESA...*" atare Suka Waiga dukkansu suna Kallon Ɗaya
Daga Cikin Senoirs ɗinsu Jidda Madaki Waɗanda Suke Kan Zana Jarabawarsu ta Fita
Ma'ana WAEC, Saboda Haka Su Suna Makaranta basu Azuwa Hutu sai Sun kammallah Neco
wanda kuma bazai yi ba Sai ya Tattara ya koma gida.

Itama ɗin Sanye Take da Uniform ɗinsu na Senior, Dark green da Farar riga da
Hijabi, Kyakkyawar Gaske ce Gata Fara gata Doguwa mai Ɗauke Da Daran Daran Idanuwa
masu Haske Cikin Siririyar Muryanta tace "Aneesa Plz D'an zo na ganki..." Ta faɗa
Cikin Yanga Wanda ya Zame mata Halitta.

Jin Abunda tace yasa Aneesa Ta ƙara Haɗe Ran Kamar Wacce Aka Aikoma da Saƙon Mutuwa
Saɓanin Sauran ƙawayenta da Fuskarsu ke Washe na Farin cikin Zasu koma gida yau,
Cikin Sanyi Jiki da Takun Ɓacin Rai Aneesa Ta Nufi Jidda tana Faɗin " *S. JIBIYA,
B. KAITA* Ku jirani bari na Dawo.." Jin Haka yasa S. Jibiya tace "Ok *A. BUKAR
BULAMA*..." Ta faɗa Tana bin Aneesan Da Kallo kafin Ta Maida Kallonta kan B. Kaita
Suka haɗa ido Suna Ƙunshe Dariya.

Aneesa kamar bazata Taka ƙasa ba Haka ta Rinƙa jan ƙafa Zuwa Wajen Jidda Dake Tsaye
tana Jiranta Tana ƙarisowa ta Riƙo Duka Hannayeta Cikin Salon Muryanta tace "Aneesa
Don Allah karki manta da Alƙawarin mu Kinji.." Ta faɗa Tana Sakar mata Fararen
Idanuwanta.

Gyara Tsayuwa Aneesa Tayi Tana Jifan Jiddan Da Wani Banza Kallo A fakaice, kafin
tace "Wani Alƙawari kenan...?" Ta faɗa Da Sigar Rainin Wayau Lokaci Ɗaya Itama tana
Sakar mata Manyan baƙaƙen Idanuwanta masu Ɗauke da Zara zaran Gashinta baƙaƙe masu
ƙara Fito da Salon Kamaninta da *KANURI*, Jidda Ta Saki Ajiyar Zuciya kafin Ta ƙara
Riƙe Hannun Aneesa Tana bin Haraban Mkrantan da Kallo Yadda Taga Kowa na Haraman
Tafiya sai D'ai d'ai Irinsu ne Suke Hidimar gabansu.

Cikin ƙara Kwantar da Murya Tana faɗin "Haba My Anee, har kin manta da mganarmu na
Kiyi ƙoƙarin Saka yayanki Ya Soni koda bai kai Kwatankwacin Irin Son Da Nike mai
ba, plz Anee Ki Taimake ni Don Allah Wlh bazan iya Rayuwa ba Matuƙar babu *MR BELLO
JIƘAMSHI*...." Ta faɗa idanuwanta Sun ciko da Ƙwallah Suna Ƙoƙarin Zubowa.

Cikin Wani Baƙin ciki da Takaichi, Aneesa ke Bin Jidda da Kallo kafin Tace "Oh..!
Na Manta ammh Tunda kin Tuna min zanyi k'ok'ari sosai Anty Jidda.." Ta faɗa tana
Zare Hannunta Cikin na Jidda Wace ke Share Ƙaramar Kwallar data Ziraro mata,
Murmushi ta sakarma Aneesa kafin tace "Yauwa ko kefa Anee, Ammh zaki Dawo ki Ɗora
SS1 Ɗinki Anan ko Aneesa..?"

Ɓata Rai Aneesa Tayi kafin tace "A"a bazan Dawo ba Nifa Na gama Wannan karatun Har
Abada Tunda bana Shiga Aljanna bane.." Ta faɗa Cikin Nuna yadda Ta Tsani Karatun
Gaba ɗaya, Dariya Jidda Tasaki Cikin Aji da Wayewa Tace "Oh Anee Wai ke bazaki
Chanza ba Shiyasa bakwa Shiiri da Mr Bello sam, Kuna gida Ɗaya Ammh Ra"ayinku ya
bambanta Shida baya son Zama da Wanda baya son Karatu.." Tura baki Aneesa Tayi
kafin Tace "Aiko da Muke gida Ɗaya ba Uwarmu Ɗaya ba Kuma ba Ubanmu Ɗaya ba, Ba
Abunda Na Haɗa Dashi Hanyar jirgi Daban na Mota Daban.." Dariya Jidda Ta ƙara
Sakawa Tana kallon Aneesa Wacce ke Kallonta Tana ƙara Haɗe Rai Fuskar nan na ƙyalli
baki da kuma Uban man Vaseline d'in Da Aneesa ta Shafama Fuskarta.

Haushin Dariyan Jidda yasa ta Juya Zata Tafi Da Hanzari Ta Riƙo Hannunta tana 'yar
Dariya tace "Sorry my Anee, na daina Dariyan Kinji ko? Na yarda baku Haɗa komai ba
Ammh dai gidanku Ɗaya, zaki min Abunda na Sakaki ko..?" Aneesa Data Waigo Tana Ƙara
Tamke Fuska tace "Nifa bana Shiga Harkanshi Sai dai nama Anty Rahila mgana Tayi
mishi Tunda Ita Naga Suna Shiri Sosai.."

Da Sauri Jidda Tace "Yauwa Ki Gaya mata Kinji ko, Ga Nombar Wayata In kin koma gida
ki kirani ko da wayar Anty Rahilan ne Kinji ko my Anee.." Ta faɗa Da Sigar Lallashi
Lokaci Ɗaya Tana Saka mata Takardan Data Rubuta mata Lambarta Karɓa Aneesa Tayi
Cikin Ƙosawa Tace "Naji Anty Jidda bari na Tafi Su B. Kaita na Jirana.." Fuskarta
Jidda Ta Shafa tana Faɗin "Ok Aneesa nagode sai naji kiranki.." Da Sauri Aneesa Ta
Ƙwace Hannunta ta Wuce Tana Sakin Tsaki Acikin Ranta Take Faɗin "Ai sai kiyi Tayi
Iska na Wahalar da mai kayan kara Uban Waye zai kiraki kan Wannan Mugun.." Ta faɗa
Harda Tsirtar da yawu kafin tace "Allah ya Tsareni da Haɗa Shirgina Da Mara Imani."

Ta faɗa Tana Ƙarisowa Wajen Dasu S. Jibiya Suke Suna Jiranta Tun kafin Ta Ƙariso ta
Dunƙule Takardan Da Jidda Ta bata ta Wurgar Da Ita gefe Tana Waigon Jidda Wacce ta
Juya ta Nufi Hostels ɗinsu na DAURAMA part 2, Da kallon Mamaki B. Kaita tace mata
"A. Bukar me aka baki kika yaga Haka..?" Tsaki Aneesa Taja Tana Gyara Tsayuwa kafin
tace "Nombar Wayar yar Wahalar ce wai na Kirata in na Koma gida.."

S. Jibiya tasaki Dariya kafin tace "Ikon Allah Toh kan mene..?" Aneesa Tace "Kan
Wannan Mugun mara Imanin Wanda ya baroni da gidanmu ya kawoni Cikin Wannan Dajin
yana Cin Zalina mana.." A tare S. Jibiya da B. Kaita Suka Haɗa baki Suka ce "Wai
*MR BELLO MUHAMMED JIƘAMSHI*....?" Aneesa Ta Ƙara Jan Tsaki tace "Bello dai kam Don
ni bazan ce mai Mr Bello ba Wlh..."

B. Kaita tace "Gaskiya Aneesa bakya kyautama kanki ina Laifin Mr bello Da Kika bi
kika Tsaneshi, taimakon ki fa yayi Daya kawoki mkranta kikayi karatu kika zama 'ya
kamar Kowa.." Da Mamaki Aneesa Ta kalleta kafin tace "Nace ne ya Taimakeni ko Kinji
nace miki ina Buƙatar Taimako ne, King B. Kaita Ki kama bakinki karki gaya min
mganar banza nace Baƙin Mugu Wanda ya Kawoni Wannan Dajin Allah Yana Cin Zalina ko
Zaki Rama mai Ne Domin Naga Alamar Kema Cikin Layin Su Jidda ne na Son Wanda bai
Dace daku ba.." Ta faɗa Cikin Fushi.

B. Kaita ta Harzuƙo ma Aneesa Tana Faɗin "Eh ɗin Faɗi ki ƙara Ina Son Mallam Bello
kuma so na Aure Aneesa Zuciyata Kullum Tana Zafi da Takaichi Duk Sanda Naji Kina
Aibatan Mr Bello, Haba Shikenan kuma don Jininku bai Haɗu ba, baki Sonshi sai ki
Hanamu mu Masu Sonshi mu Soshi ko mu nuna muna Sonshi, Tsakaninki dashi Daban muma
tsakaninmu Daban, Saboda Haka Muma Kibar mu Mu nuna Muna Sonshi Domin Babu Abunda
yayi mana Kuma yayi Dai-dai Da Ra"ayinmu.." B. Kaita ta Faɗa Cikin Nuna Masifarta
Harda Ɗaga Murya.

Aneesa da Wata Zuciya ta Ciyota ta Tsallake S. Jibiya ta Dira gaban B. Kaita taci
Kwalan Hijabinta tana Faɗin "Ina Ruwana da Son da Kuke mai Nidai sai na Faɗa ba
Kuma Zan Fasa Faɗan Bello mugu ne mara Imani ba, Ko zaki iya Rama mai ne...? sai
naga Ƙarewar Son da Kike mai Banza Kawai mara Aikin yi.." Ta faɗa Indanuwanta Sun
Kaɗa Sunyi Jajir.

B. Kaita da Abun na Aneesa Ya kaita Wuya sai kawai ta cakumo Aneesa Suka Fara Dambe
Tana Faɗin"Ni ba banza bace kece babbar Banza butulu mai Raina Alheri.." Tuni Faɗa
ya kacame, S. Jibiya ce ke ƙoƙarin Rabasu da Sauran Student d'in da basu gama
Tafiya ba, suka ƙariso Suna Raba Kawayen Juna Faɗa, S. Jibiya ce ke Faɗin "Haba
Aneesa, Billy meye Haka Wannan ba girmanku bane Aganku kuna Faɗa da Junanku..."
Aneesa Data Shaƙe Wuyan B. Kaita da Hijabi Take Faɗin "Aganmu munayin Mana Uban
Waya ja In ba Ita ba Dama Tuni Billy Take Shigan Hanci Da Ƙudundune Wlh yau kafin
mu bar Mkrantan nan Sai mun Goge Raini Tsakanina Da Ita.." Take Faɗa Tana Haki tana
ƙara Tamke Wuyan B. Kaita Wacce ke Ƙoƙarin Ƙwace kanta.

Daga bayansu Sukaji Ance "Are u Stupid Aneesa Bukar Bulama....?"

Sukaji An Faɗa Daga bayansu Cikin Kakkausan Murya, gaba ɗayansu Suka Waiga Suna
Kallon Uncle Aminu da Mr Bello Suna Tahowa, Hannunsu Sarke da Juna, Kamar Wasu
Tagwaye Dama Duk Sch d'in ba Wanda baisan Abota Da Shaƙuwa Irinta Uncle Aminu da Mr
Bello ba, Uncle Aminu Yana Sanye da Riga da Wando black And White, Sai Wani
Rufaffan baƙin Takalminsa na Fatar Damisa Sai Mr Bello yana Sanye da Riga da Wando
Rigar Dark Blue mai Dogon Hannu sai Wandonshi mai Ruwan Blue mai Haske, Ƙafarsa
sanye da Takalmi Baƙi booth sai kansa Dake Sanye da p cap, wanda ya Rufe Rabin
Fuskarsa Dukkansu Dogaye ne masu Surar Jiki Ƙirar Maza Cikakku Masu Zati da Haiba.
Uncle Aminu Fari ne Mai Faɗin Fuska da Dogon Hanci yana da Gemun Shi ɗan Dai-dai
Wanda yake Ƙara mai kyau mai Haɗe da Zagayayyen Bakin shi mai faɗi Kaɗan, Mr Bello
Fuskarsa bata bayyana ba Sosai Sai dai Daga yanayin Fatar Hannunshi Inda
Rantsantsen Agogo na Kamfanin Rado ke Ɗaure A tsinsiyan Hannunshi na kallah na
Fahimci Fari Ne Sosai Saboda Yadda Fararan yatsunshi ke Kwance da Gashi Sun Kwanta
Zara zara Gwanin Ban Sha"awa, Yana da Faɗi Kaɗan Daga Sama Saboda In yana Tafiya
Zaka ga yana Buɗewa, a kallon yanayin Tafiyarshi kaɗai ya Isa Zatinsa da Jarumtarsa
Su Dakeka Tun kafin kaga Fuskarsa ma.

Duka Ɗaliban Dake Wajen Suka Fara Matswa Jikinsu na Rawa Suna Tsoron Kada A haɗa
dasu Uncle Aminu da Mr Bello A lokaci Ɗaya ai Fire ne, babu Wanda Baisan yadda Suke
cin Ƙaniyar Ɗalibai ba Acikin Mkrantan Musamman 'yan Taurin kai Irinsu Aneesa,
Aneesa Ko Ajikinta Sai ma Ƙoƙarin Ƙara Riƙe Wuyan Hijabin Billy Kaita Da takeyi
Itako Tuni Ta Saki Wuyan Aneesa Tana Ƙoƙarin Ƙwace Kanta Salamatu Jibiya Kuwa Baya
ta Matsa Tana Zare Ido Aranta Tana Addu"ar Allah yasa yanzu Motar gidansu tazo
Ɗaukanta.

A gabansu Suka ja Burki Uncle Aminu ne ya kalli Aneesa Dake Wani Hura Hanci ga
Bakinta na Ƙara Ɗaukan Ido Cikin Tsawa Yace "Leave her Hijab Now Don Ubanki..." Ya
Faɗa yana Sakin hannun Mr Bello Wanda kanshi ke ƙasa yana Danne Danne Cikin
Wayarsa, Kamar baima san Abunda Ke Faruwa Awajen ba, Aneesa na Ƙunƙuni Harda
Ƙwallarta ta Saki Wuyan Hijabin Billy Kaita tana Faɗi ƙasa ƙasa "Nidai ba Ubana ba
Wlh.." Ta faɗa Tana Share Hanci ba Zato ba Tsammani Taji Gam!! An Buge mata baki,
da Hanzari Ta Dafe Wajen Tana bin Hannun Wanda ya Maketa da Kallo Mr Bello ne Cikin
Muryan Sanyi Ammh Cike da Faɗa yace "Ba Ubanki ba sai Ubanwa..?" Ya faɗa ammh Still
kanshi na Kan Wayarsa Dake Hannunsa.

Uncle Aminu ne ya Riƙe Kugu yace "Au haka tace Bello? ƙanwar nan Taka fa Zan ci
Ubanta, Duk da Mun Riga mun basu Hutu.." Mr Bello Dake Danna Wayarsa yace "As u
wish..." Ya faɗa yana Ɗago da kansa Lokaci Ɗaya Ɗaliban Wajen kowani ya fara kama
gabansu Wasu ma Jakunkunansu Suka Ɗauka Suna Nufar bakin Get, Jikinsu na Rawa Kada
Laifin Aneesa ya Shafesu Domin kaf Mkrantan Kwarta-kwashi ba Wanda baisan Waye
Uncle Aminu da Uncle Bello ba wajen iya cin ƙaniyar Ɗalibai Kuma ba Wanda bai san
Wacece Aneesa Bukar Bulama ba wajen Rashin kunya da Rashin Tsoro.

Jin Abunda Mr
Bello yace ne ya sa S. Jibiya ta Marairaice Fuska tana Kallon Aneesa Tana mata
alamun Ta bada Haƙuri Ita kanta Billy Kaita Tsoro ya Shigeta ganin Uncle Aminu ya
isa Bishiyar Dalbejiya yayi Tsalle ya Katso Reshe Ɗaya ya Tsinketa Wata Doguwar
Bulala Ta bayyana Kafin ma ya Ƙariso B. Kaita da S. Jibiya Suka Matsa Gefe Suna
Rawan Jiki Shiko Mr Bello Baya ya Juya Bayan ya Ɗaga Wayarsa ya Ɗaura a Kunni ya
fara Tafiya kamar Zai Fita bakin Get.

Cikin Tsawa Uncle Aminu yace "Kneel Down..." Aneesa Ta kalleshi tana Ɗaga Idonta
sama Irin Banji me kace ba Sanin Raininta yasa bai Jirata ba ya Fara Zuba mata
Bulalar Dake Hannunshi Cikin Ƙwarewa da Mugunta Tun Aneesa na Tsaye tana Cijewa
karta yi Kuka sai da Hawaye Suka Fara Fita Daga Idanuwanta ta Duƙe Ƙasa Tana Kuka
bai barta ba sai da Bulalar Ta gama Karairayewa A jikinta kana ya ƙyaleta ya
kalleta yana Faɗin "Wannan na Bye bye Kwatar-kwashi ne In kika Dawo First Time SS1
akwai Welcome to GGUSS SS1 kwatar-kwashi Tunda Ke Har yanzu bazaki yi Hankali ba
Bush girl kawai wato ba Ubanki ba sai dai nawa ko..?"

Ya fada yana Saka ƙafa ya Shureta Dai-dai Lokacin da Wata Arniyar Motar Buggati
baƙa ta Shigo Cikin Mktanta Kallon Farko Kowa yayi ma motar Suka san Motar da Zata
Ɗauki Mr Bello da Aneesa Ce Domin duk Faɗin Mkrantar babu Wanda Ake Zuwa Ɗauka da
Motocin Alfarma sai Su, Aneesa Dake Duƙe tana Kuka Ko Ɗagowa batayi ba nan Uncle
Aminu ya Juya ya Nufi inda Mr Bello ke Tsaye yana gaisawa da Direbansu Mallam
Inuwa, Tuni Ɗaliban Mkrantan Masu Tafiya Sun Watse Su kuma 'yan SS3 sun Shiga
Jarabawa.
Lokacin da Mr Bello ke gaisawa Da Mallam Inuwa yaja p.cap Ɗinsa Sama kyakkyawan
Fuskarsa Ta Bayyana Wow.. Haƙiƙa Allah yayi Halitta Domin Wata kamilalliyar Fuska
na Hanga mai Cike da Kyau da Haiba Farin Namiji ne mai Ɗauke da Dogon Hancinsa Har
Baka A kallon Farko In kayi mai Zaka Fahimci ya haɗa Nasaba da Fulani Zagayeyyen
Baƙin Sajensa ne ke Ƙara mai kyau Wanda yayi ma ƙaramin Bakinshi Kwanya matsakaitan
Idanuwanshi masu Ɗauke da Wasu Fararen Idanuwa Masu Kyau da Narkan da Zuciyan 'yan
Mata, Sai zara zara gashin Idanuwansa Masu Tsawo da baƙi Da Gashin Girarsa Baƙi
Siɗik Haɗe da Wani Kwantaccen Gashin Kansa Irin na Fulani Mr Bello baya barin Gashi
Ya Taru Akanshi ko A yanzu Ma Babu Cikar Gashi Sosai

*MUHAMMED BELLO MUHAMEED JIƘAMSHI* Kenan wanda Ɗalibai da Malamai kema Laƙabi da
_MR BELLO_ kuma Ƙani ga Cheif Army of Staff na ƙasa Gaba ɗaya Wato *LT. GEN.
MUKTAR MUHAMMED JIƘAMSHI* Cikkaken Namiji ne mai Aji da Zati Wanda Kaf 'yan Matan
Dake GGUSS kwatar- kwashi ke Rubibi Akanshi, Tun daga Kan Malamai da Ɗalibai, Kan
'yan Junior ne da Senior, Kaf Ɗinsu ba Yarinya Da Zatace bata Crushing Ɗinsa,
Mkrantar Tana ji Dashi Domin Tunda Ƙasa Zuwa Sama Shine kaɗai Malami ƙwara Ɗaya Tak
da yake Ɗaukan Su Mathematics Sakamakon yana da Master Digree Akansa Wanda ya
Haɗosa a babban Birnin America Wato U.S.

Da Sauri Billy Kaita da Salamatu S Jibiya Suka ƙariso ga Aneesa Suka Riƙota Billy
na Faɗin "Aneesa Don Allah ki daina Wannan Taurin kan Wahala kawai zaki Dinga
Sha.." Aneesa Na Miƙewa Ta Fizge Jikinta Tana Share Kwalla tace "Bazan bari ba Ki
Rabu Dani Munafuka Ai Burinki ya cika Tunda Yau ɗin ma Ina Murnan zan Bar Uƙuba sai
da Aka ƙara Zalunta ta, In kika ƙara Nuna Kin ma Sanni Billy Allah ya Isa Tsakanina
Dake Domin Duk Masoyina bazai so Wanchan Mutumin ba.." Tana gama Faɗin Haka ta
Ɗauki Trolley ɗinta da ƙaramar Jakarta Da Wata Jaka Ta Rataya abaya kafin ta kalli
Salamatu Jibiya tana Faɗin

"S. Jibiya Sai munyi Waya Ga Mallam Inuwa chan yazo zan Tafi kada yasa atafi Abarni
irin na Wanchan Term din.." S. Jibiya bata samu Zarafin mgana ba Aneesa Ta Wuce
Ruƙu Ruƙu da Kaya Billy da Salamatu Jibiya Suka Bita da kallo Suna Kaɗa kai Sanin
Halin Aneesa na Masifa da Saurin Fushi Ammh Akwai Saurin Sauka Nan da Gobe zata
manta komai don Duk Faɗin Kwatar -kwashi bata da kamar Billy Kaita da Salamatu
Jibiya.

Tana ƙarisowa Mallam Inuwa Ya Tareta da Fara"a yana Faɗin "A"a ga Ɗiyata 'yan
Makranta, Kai Masha Allah Hajiya tace Kin kammallah zangon karatu na Farko.." Ya
faɗa Cike da Murna Cikin ɓata Rai Aneesa Tace "Wlh na gama Dawowa wannan Mkrantan
Baba kama ji gaskiya Haba na gaji da Wannan karatun Mkrantar Ta Isheni Baba Wahalar
Tayi yawa Tunda bana Shiga Aljannah bane.." Ta faɗa Tana Sakar mai Akwatunanta Guda
Biyu Ɗauka yayi yana Dariya gefenshi ya kallah yaga Basu Bello Sun gangara Zuwa
Quarters d'in Malamai Mr Bello zai Ɗauko Jakarsa.

Booth ya Buɗe yana Zuba mata Akwatunan, Hannu ya Miƙa yana Faɗin "Au hakane fa Kin
gama Toh kawo Jakar itama asaka A ciki Karatu kam Kin gama Tunda bana Shiga
Aljannah bace Wanda Kika samu Allah samai albarka.." Washe baki Tayi Tana Faɗin
"Yauwa Baba Allah sa Yadda ka Fahimta Haka *YAYA MUKTAR DA ANTY RAHILA* Suma su
Fahimta ko da yake Ko Sun barni nasan Wannan Mugun bazai barni ba ammh Wlh Wannan
karon ko Guduwa ne Sai na Gudu Borno Wajensu Yaya Ali In dai Aka matsamin sai na
Dawo Mkrantar nan..." Ta faɗa Harda Sharɓe Ƙwallah..

Kallonta yake bayan Sun gama Saka kayan ya Rufe Booth d'in Motar yana Faɗin "A"a
'yata mai yayi Zafi basai kin gudu ba, Insha Allahu Shima Zai Fahimceki.." Ya faɗa
Yana Danne Dariyansa Ganin Tana Wani Taɓe baki gidan baya ya Buɗe mata yana Faɗin
"Ɗiyata kinbar ƙawayenki gasu chan.." Jin Haka yasa Ta Juya Tana kallon Salamatu
Jibiya da Billy Kaita Suna Tsaye Suna kallonta, Harara ta Makama Billy Harda
Murguɗa mata baki Tana Faɗin "Sai Wata rana na bar Muku Mkrantar.." Ta faɗa kai
Tsaye Tana Shigewa Mota, Dariya Suka saka Aran S. Jibiya Tana Jaddada Dawowar
Aneesa SS1 Dole kamar yadda Yake Awajensu.

Basu Daɗe ba sai ga Uncle Aminu da Mr Bello Sun Ƙariso Yana Ɗauke da Wata bak'ar
jakar Baya, Musabaha Sukayi da Aminu Suka Ɗanyi Mgana kafin Suyi Sallama don Uncle
Aminu sai Next Week zai Tafi Sakamakon Ɗaliban SS3 Dasuke WAEC basuyi Darasinshi na
Na Turanci ba shikuwa Mr Bello Da yake Malamin Lissafi Kuma Jiya Sukayi Paper, d'in
Dat Why Shi Zai Wuce Gida Shima Kuma Uncle Aminu Dake Kano sai Sati na Sama Zai
Tafi.

Shi ya Buɗema Mr Bello Ƙofar gaban Motan ya Shiga Suna Ƙara Sallama, kafin ya Rufo
ƙofar Motar Mallam Inuwa ya Tada Motar Suka Fice Daga Mkrantan Uncle Aminu na Ɗaga
musu Hannu Aneesa na Cikin Mota tana Makamai Harara Aranta tana Faɗin "Mugu sai Abi
Wani Sarkin Ba Aneesa ba.." Ta faɗa Harda Yar Dariyanta Karaf Ko Suka Haɗa Ido da
Mr Bello Yako Makamata Harara yana Faɗin "Don Ubanki Ɗauke waɗannan baƙaƙen
Idanuwan naki Akaina ko nasa Mallam Inuwa ya Faka Motar nan na Wurgaki Dajin nan."
Ya faɗa Cikin Tabbatar da mganarsa.

Jin Haka yasa Tayi Saurin Sadda Kanta Cikin Rawan Jiki Saboda Tasan Zai aikata Don
Wanchan Term d'in ma Tafiya yayi ya barta sai da tabi Direban gidansu Salamatu
Jibiya ta tafi gidansu ta Kwana Washegari Akazo Aka Ɗauketa, Haɗe Rai Tayi kanta ta
maida Gefe Tana Ƙunƙuni Acikin Ranta Shiko Gyara Zama yayi yafito da Wayarsa yana
latsawa Mallam Inuwa na gefe yana Tuƙi yana kanne Dariyarsa ganin Yadda Aneesa Take
Tura Baki kamar Zai Tinko Ya Faɗi Saboda Ƙunƙuni.

Suko su Billy, su Aneesa Suna Tafiya ba Daɗewa Kusan Tare Motocin Gidanasu S.
Jibiya da Billy Kaita Suka zo nan da nan Kowacce Ta Ɗauki Kayanta Suka Loda Amota
Sukama Juna Sallamar sai sunyi Waya Kafin Su Dawo mkranta.

*How to pay....�?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?600...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?500 ne,VIP
�?1000, Single one �?300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*Anitha...*
✍️ *MR BELLO..!*
*20/07/2020...*a:
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*🅿�?2*

#Home..

*ABUJA-Area-GARKI*

""Karfe 4pm da wani abu Motarsu Tafara Zuba Hon Abakin Wani Shimfideden
Tamgamemen Get Dake Amguwar nan ta masu Kudi ko Nace Kusoshin Gwannati Wato
Garki,Tunda ga Layin Sojoji ne ke Tsaye Har Zuwa Cikn Haraban Makeken Gidan Mai
kama da Alkarya Guda,Aneesa Bakinta yaki Rufuwa Ganin Sun Kawo Gida,kafin ma Mallam
Inuwa ya gama Daidaita parking a parking Space inda Tarin Rantsantsun Motoci na
Alfarma ke Fake Sunfi guda goma,Kai Daga Ganin Gidan kasan Wani Soja ne Wanda yake
da Mukami mai Matsayi agwannati Tun ballatana ma Dakarun Sojojin Dake yawo a
Haraban Gidaan

Da sauri ta balle murfin mota ta Fito da gudu Ta Kwasa Zuwa Cikin Gida Da Jakarta
ta Mkranta Goyo Abayanta.

Daga Mallam Inuwa Har Bello da Kallo Suka Bita Shi Mallam Inuwa Mirmishi yayi yana
Kada kai, Shi kuma Uncle Bello Tsaki yaja Takaichin Aneesa kamar ya Kasheshi
yarinya kamar Haihuwar Hauka Bai Tsaya Sauraran Gaisuwan Tsiraran Sojojin Dake
Haraban Gidan ba ya Kama Hanyar Wani makeken Mension mai Dauke da upstair Inda nan
na Shashen Uncle Bello Shi kadai Mai kama da Wajen da Za"a Saka mata Goma ma Babu
Wanda ya Matsu Wani.

Itako Aneesa da ihun Kiran Anty Rahila Ta Shiga Wani Katon Falo mai kama da
Aljannar Duniya Tana Fadin"Anty Rahila.,Daada Ku Fito na Dawo Hibbata kina ina Yau
na gama Wahalalliyar Mkrantan nan Na Dawo gida.."Take Fada Daidai Sanda ta Shigo
Tsakiyar Falon Tana Dariya Yayinda Duka Fararen Hakoranta Dake Haskata Suka
bayyana.

Dariyarta da Murnanta Sun Dauke ne Lokacin Da Suka Hada Ido da *Zubaida* da *Zulfa*
wadanda Ke Hakimce Kowacce Ta Samu Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ta Zauna Tana
Dannen Waya Gefe Daya Kuma suna Kallon Katon Wani Magijin Talabijin Wanda yakusa
mamayen Bangon Wajen, yan mata ne masu ji Da kansu,Zulfa ce Fara Zubaida kuma
Chaculate Colour ce,Dukkansu Atare Suka Dago Suna Sakarma Aneesa Wani Matsiyacin
kallo Lokaci Daya Suna mata kallon Sama da Kasa kafin Su Hada Ido Lokaci Daya Suka
Saka mata Dariya Zulfa ce tace"Ikon Allah yan Makarantan boko ko Ansha
Wuya..."Tafada Tana Kara Saka Dariya.

Abun ya mugun batama Aneesa Rai Ta Kallesu Awulakance Kafin Ta Saki Siririn Tsaki
Tana Fadin"Aikin banza Tusa Alasifika Wanda Dai Ake Zuwa Domin Shi bai san Anayi ba
Andai Fadi ba Nauyi Wlh.."Tafada Lokaci Daya Tana Runtumawa Da Gudu Zuwa koridon da
zai Sadata da Sashen Anty Rahila Wacce Taji Karadin Muryan Aneesa Ta Nufo Falon
Hannunta Rike dana Hibba,Suka Ci karo da Aneesa Ta Kwaso da Gudu.

Anty Rahila tace"Innalillhi Anne Bi Ahankali Mana.."Wata Mata nagani Baka mai kyau
da Dogon Hanci Kallo Farko In kamata Zaka Ga Tsantsan Kamar da Suke da
Aneesa,kallonta Aneesa Tayi kafin ta Rumgumeta Tana Fadin"Anty Rahila nagama
karatu.."Take Fada Tana Dariya kafin ta Saketa ta Rarumi hibba yar Shekara Hudu
Dake Mata Dariya Tana Fadin"Annee.."Cikin Muryan yara Cafeta sama Aneesa Tayi Tana
Fadin"Hibbatullahi Kin kara girma.."Anty Rahila na Gefe Tana kallosu Tana Mirmishi
Aranta tana Fadin"Anee Sarkin Rigima wai tagama karatu.."

Dagachan Falon Kuwa Zulfa Ta kalli Zubaida tana Fadin"Kan bala"i Dawa Wannan
yarinyar Take..?"Wani kallon Wacece Sakara Zubaida Tamata kafin Tace"Da wanda ya
Tanka mana Nidai kinsan bana Sakarmata Fuska Tunda na gane bata da Kunya Gashi
Daada Ta Daure mata Gindi Ita da Daddy ba Daman Ayi magana sai Suce yarinta Ke
Damunta.."

Wani Uban Tsaki Zulfa ta Saki kafin Ta Mike Tana Fadin"Ni babu Ruwana Tana Kawomin
Raini Ubanta Zanci ai gwanda mu gidan D'an Kanin iyayenmu muke itafa Kalan Dangin
Daga yayarta na Auren Daddy Shikenan Aka Taremana Agida.."Tafada tana Tafiya Zuwa
Falon Anty Rahila da kallo Zubaida ta Bita Dashi Kafin ta Saki Mirmishi Ta Mike
Tsam Tana Kara gyara Fuskarta Acikin Madubin Wayarta ta Nufi Hanyar da Zai Sada ta
da Waje Cikin Wani Yanga Kamar Wata Wahainiya.

Koda Zulfa fa ta iso Falon Na Anty Rahila Tuni Aneesa ta Dauki Hibba Sun Shiga
Shashen Daada Tsohuwa mai Ran Karfe Kakarsu Bello da ya Mukatar Ita ta Haifi
Mahaifiyarsu Hassatu,Anty Rahilan Kadai Ta Iske Tana ma Mai Aikinsu Jumai bayanin
Abunda Zata Dafa Tunda Bello ya Dawo,Ganin Suna mgana yasa bata Tanka ta ba sai Ta
samu Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ta Zauna Wanda Shima iya Tsaruwa ya Tsaruwa An
Zuba Dukiya Sosai.

Sai da Anty Rahila ta sallami Jummai kana ta Kariso Tazauna Kusa da Zulfa Tana
Fadin"A"ah Zulfa ya"akayi ne...? Dan Sakin Baki kadan Zulfa tayi kafin tace"Wai ni
Anty Rahila Tare da Uncle Bello Aneesa Ta Dawo..."?Anty Rahila ta Murmusa kafin
tace"Eh Tare Suka Dawo.."Tafada Tana Gyara zaman Sarkan Azurfan Dake Wuyanta.

Baki Zulfa ta Washe Cikin Farinciki Tace"La! Da Gaske..?Shine bai Shigo ba..? Anty
Rahila Ta Mike Tana Fadin"Ai kinsan bazai Shigo yanzu ba May be sai Daddy ya Shigo
Tukunnah.."Mikewa Zulfa tayi Tana Fadin"Kai Naji dadin Dawowar Uncle bello Daman
Domin Shi nazo Wannan Hutu bari na Shiga Kichen na hadamai Dinner kafin
Anjuma.."Tafada Tana Nufar Hanyar wani dogon Korido Wanda Zai Sadaka da Kichen din
Gidan Gabadaya.

Da kallo Anty Rahila tabita kafin ta Dan Murmusa Afili tace"Dama baki Wahalar da
kanki ba Zulfa indai Bello ne zaki yi Nadama Kila Sai kinyi kuka.."Tafada Tana
Komawa ta Zauna lokaci daya tana yar Dariya Tuna yadda Zasu kwashe da Bello in ma
ya gansu Acikin Gidan Balle ma Wannan Rawan Kafan da Zulfan keyi kuma ko Ita
Zubaida Itama Saboda Bellon Tazo Gidan Kuma ta sani Duka iyayensu sun Turosu ne
Saboda Ko Bello zai Gani ya kyasa,kamar basusan Waye Bellon ba.

Dagachan Shashen Tsohuwa Daada Kuwa Aneesa na Hango Zaune kusa da Wata Farar
Dattajiuwa mai kimanin Shekarun 66 aduniya Daga ganinta kaga Bufullatana Ta Gaba Da
baya,ga Zanensu na Fulani nan Agefe da gefen bakinta Kana ganinta Zaka Tsinkayi
Inda Bello ya Samu Hasken Fata da Kuma kyau,bata Sha Wuya ba Domin Kudi da Jin Dadi
Sun Zauna mata zaune take kan Wani Lafiyayyen Jan Cafet Dake malale Cikin kayatacen
Hadadden Falon wanda yaji Alatun Rayuwa Tana Sanye da Riga da Zani da Dankwali
Hakoranta Suna Washe ne har Hakoran Makkanta Guda Biyu Suka bayyana Daga ganin
yadda Take Dariya Tana Dafa Cinyar Aneesan zaka san Lbrin da Aneensa Ke bata ya
mata Dadi Sosai

Kanta Daada ta Shafa kafin tace"Dakata da lbrin nan Anee Hakanan Tashi ki Tube kaya
Kiyi Wanka kiyi sallah kici Abinci sai kizo mu Cigaba Ko kin manta yau Tare zamu
Kwana Kiyi Ta bani lbrin Mkrantar Har ki gaji kinji ko.."Aneesa Na Dariya Ta Mike
Tana Fadin"Hakane Kuwa Daaada Naji Dadin Gama Karatun nan Dama na gaji Da Mkrantar
Da Wahalar Cikinta.."Daada tace"Koni nayi Murna Ina Dadi Irin Wannan Uban Wahalan
Dakike bani lbrin Ana baku Ai Shima laifin Mukatar din Dayake Biyema Yaron nan
Bello ne"Aneesa na Dariya Jin Daada ta Ambaci bello wanda ba ta iya kiran sunansa
saboda sunan marigayi mijinta ne kakansu Bellon kenan

Bedroom dinta ta Shige wanda ke kusa da na Daada ta Fada Tiolet Cike Da Fara"a
Domin Tasan Daada bazata bari Akara maidata Wannan Shegiyar Mkrantar mai Aljanun
Tsiya ba.

Shigarta ba Dadewa Anty Rahila ta Shigo Dauke da Trolley din Aneesa da Jakunkunanta
Guda Biyu Tana Fadin"Aneesa ba Hankali chan ta bar Kayan Nata Sai da Mallam Inuwa
ya Shigo Dasu.."Daada dake Wasa Da Hibba Tace"Ina Ruwa Anee yan Mkranta Tadai Shigo
ita kan Abunta.."Tafada tana yar Dariya Cikin Bedroom din da Aneesa ta shiga Ta
Shigan Mata da kayan Ta Fito ta isketa Haryanzu Tana Wanka Bata Fito ba nan ta
Zauna Falon Daada Suna Cigaba da Hira Sama Sama.

****

Zubaida kuwa Cike da yanga Ta Isa Mension din Uncle Bello Wanda Ke upstairs
Matattakalan Benen Tafara Haurawa Tanayi Tana Kara gyara Tafiyarta Har ta Iso Kofar
Falon Nashi Ta saka Hannu zatayi Kooking kenan Taji Kofar ta Bude Kanta Cikin Jin
Dadi Ta Tura kanta Falon da yar Siririyar sallamarta Lokaci Daya Kamshin Turaransa
na MAN ya Daketa Wanda Duk Duniya ba Jikin Wanda Take Jin Dadin Kamshin Turaran
Irin Jikin Uncle Bello Wanda Hatta bangarensa ma ya Saba da Kamshin mai Dakin..

Falon mai kalan Blue and black ne Babu Kowa aciki sai Karan Talabijin Dake Tashi
Shi kadai,Takawa Tafarayi Zuwa Tsakiyar Falon tana bin Ko"ina da Kallo Cikin
Burgewa,Jin Shuru kamar babu Motsin Kowa yasa Zubaida ta Nufi Cikin Bedroom din
Uncle Bello ta Tura ahankali ta Shiga Tana Sanda kamar Wacce Zatayi sata

Wani kamshi mai Hade da Sanyin Dadi ya Daketa Lokaci Daya Lumshe ido Tayi Tana
Sauke Tagwayen Ajiyar Zuciya kafin Tafara bin Dakin da Kallo Komai Very Net,dashi
Koda bayanan Anty Rahila bata barin Bangaren Bello Da Datti Duk Bayan Kwana Biyu
Zata Saka yan Aikin bangaren Share Share Su Shiga Su Tabtacemai,Makeken Royal bed
ne ya Cinye dakin Sai Dressing Mirror sai Wani Wargajen Wardrope na Glass Wanda
Shima ya mamaye Rabin Bango Daga Gefe Kuma Ma"ajiyar Takalmansa ne gasunan Burjit
kama Daga Rufaffu na Fatar Damisa da Budaddu,Sai Wanda yaga Dama zai Saka Daga
Cikin Wani Korido Kuwa Kofar Tiolet Dinshi Ne,Maida kallonta Tayi Bisa Side Drower
din Gefen Gadonshi nan ta Iske Wani karamin Hoto Cikin Frem Da Hanzari Ta karisa ta
Dauka Tana kallo

Shida Muktar ne da Wata Farar Mata Wacce kana ganinta kasan Mahaifiyarsu ne Saboda
Tsabar Kamar da Suke da Juna Kurama Bello ido Tayi yana Rumgume Jikin Mahaifiyarsu
Duka Hakoransa na Waje,Hannu ta Sanya Tana Shafa Fuskarsa Wani Shauki na Kwasanta
Bata ji Fitowarshi ba Sai ji Tayi An Daka mata Tsawa Da Cewa.."Ke.! Waye Anan...?
Yafada Cikin Muryan Sanyi Ammh Cike da Fada

Jin Muryansa Daga Sama ya Sanya Tsoro ya Shigeta Tana Kokarin Ijiye Hoton Jikinta
na Rawa Taji ya kara Daka mata Tsawa"I said Who are u...? Yafada Wannan karon Cikin
Alamun Fushi Tsautsayi ya saka Hoton Bai zauna ba ya Subuce ya Fado Jikake Tass..!
Glass din ya Fashe Gaban Zubaida ya Fadi Jikinta na Rawa Ta Juyo Saboda Sanin Waye
Bello ba Karamin Aikinshi bane ya Mata Dukan Tsiya babu Ruwanshi

Shiko yana Tsaye sanye da Karamin Towel A kugunshi Wani kuma Bisa kanshi yana Tsane
Ruwa Gabadaya Ranshi ya kara baci Lokacin Dayayi Tozali da Zubaida,Ta juyo tana
kallonshi Cike da Tsoro Cak ya Tsaya yana Kallonta Sama da Kasa Cike da Raini
Yace"U....? Yafada yana Sakin Wani killer Smile Wanda Aneesa tama Lakabi da Dariyan
Mugunta

Jikin Zubaida na Rawa tafara Fadin"Am Srry Uncle Bello naji Dawowarka Shine nazo
maka Sannu da Zuwa..."Tafada Tana Hada Numfashi Ko kallonta baiyi ba Ya Juya ya Isa
Dressing Mirror Dinshi Ranshi na kara baci In Ya Budi Ido yakara ma Kallon Fuskarta
Domin Yana kallon Fuskar Mugun Mahaifinta Aciki Wato Abba Kabiru,Shi bai san Meya
kawosu ba,Lokacin da Suke Neman Taimako basu Taimakesu ba Suka Cinye Dukiyar
Mahaifinsu Suka Wofintar da Rayuwarsu yau ba Domin Daada ba Kila da Tuni Yunwa da
Wahala Ta kashesu Shida ya Muktar... ...

Yafada cikin Ranshi yana Gogama Kanshi Wani oil,Cikin Sand'a Zubaida Ta kama
Hanyar Fita ganin Kamar baya Ganinta Ta Dora Hannunta Kenan kan Handle din Kofar
taji yace"Ubanki ne zai Kwashe miki Abunda Kika Fasa...? Ko kuma Ni...? U better be
Carefully In ba Haka ba Wlh Sai naci Uwarki Yanzu Acikin Dakin nan Tunda naga
alaman kin Rainani.."Yafada Bai Waigo ba Kuma Hankalinshi Kwance yana Cigaba da
Abunda yakeyi.

Tsoro ya kara kama Zubaida Aranta Tana Fadin Ta kawo kanta.,Jikinta na Rawa Ta Fara
Fadin"Kayi...yi..Hakuri Zan Gyara..."Ko kallonta baiyi ba Yabuga mata Tsawa"Get
Out...Kazama kawai .."Yafada Harda Sakin Saki Jikinta na kyarma ta Bude Kofa ta
Fice kamar Zata Kifa Wani Bakinciki ya Kamata Ta Fito tana Share Kwallah Wai Har
yaushe ne Bello Zai Daina kyaransu Tasani Tuni ya Fahimci Tana Sonshi Hatta Zulfa
ma ya Dade da Fahimta Ammh Duk Lokacin da Suka Hadu da Juna sai yaci Zarafinsu Wata
Zuciyarta tace karki manta Har iyayenku bai kyale ba.

Ajiyar Zuciya ta Sauke Tana Dauke Kwallarta daidai Lokacin Data Sauko daga Steps
din Motocin Ya Muktar suka Shigo Gidan Shiya Hanata karisawa Cikin Babban Falon
Gidan,Agaban Idonta Wani Soja ya Budemai Murfin Motarsa Benz2k20,ya Fito Sanye
Cikin Kakinsa na Sojoji Hulan kansa Kuma Tana Rike Ahannunshi,Da Mirmishi Zubaida
Ta karisa gareshi Aranta Tana Fadin"Ga mai Kirkin gidan ya Dawo.."

Tundaga Nesa ya Hangeta sai ya Saki Ranshi Ya juya yana Mgana da Wasu Sojojin Dake
bayanshi Cikakken Dogon Namiji ne mai Dattako da Kamala Dan Kimani Shekaru 59
aduniya Fari ne Ammh bai kai Bello Hasken Fata ba Sosai,ammh Kusan yanayin Tsarin
Fuskarsu Daya sai dai Shi Muktar yana da Fadin Fuska Kadan Da Kuma Jiki irin ta
Cikakkun Maza masu Jarumta da Sadaukanta,a kallo Farko Zaka Fahimci Tsantsan
Hakurinsa da Kamewarsa *LT.GEN.MUKTAR MUHAMMED JIKAMSHI* Kenan Chief Army of Staff
na Kasa Baki Daya Namiji ne mai Kishin Kasarsa da kuma kishin kansa Mai Fara'a Da
Barkwancin Sabanin Bello da Yake Miskilanci mara son Jama"a Da Fara"a a komai dai
Sun Samu Sabanin Halaye Sosai.

Cikin Fara"a ya Wareta Mata Hannunshi yana Fadin"My Dota Come here..."Da Hanzari ta
karisa Ta Fada Jikinsa Tana Fadin"Welcm Home Daddy..."Rumgumeta yana Shafa kanta
Kafin ya Dagota yana Fadin"Thanks Dota..,Daga Ina Kike Haka..? Yafada yana Rike
Hannunta Suka Nufi Kofar glass din da Zata Sadasu da Cikin Gidan,Jin tambayan
Dayayi mata ya Sanya Idonta ya Ciko da Hawaye Cikin karaya tace"Shashen Uncle Bello
naje Daddy Naje yimai Sannu da Zuwa ne ya Koroni Harda cemin Kazama.."Tafada Kwalla
Suna Zubomata Tunda ta ambaci Bello yake Mirmishi kafin ya Waiwaiya yana kallon
Motocin Wajen Sai yanzu ya lura da Motar Mallam Inuwa Direba Domin Shine
Amintattacen Direbansa Wanda ke Mu"amalan Cikin Gida da iyalanshi.

Hannu ya Sanya yana Dauke Mata Hawayenta Kafin yace"Don't Wrry Stop craying kinji
ko..?gyada mai kai tayi kafin Takara Share Kwallarta Mirmishi ya Sakarmata kafin
tayi gaba Shikuma ya Biyota Abaya yana Kallonta Acikin Ranshi yana Nanata"Bello
bazai Taba Chanzawa ba.."Yafada Yana Sagale Hulansa Wajen Hammtarshi Lokaci Daya
Kuma yana Sakin Mirmishi Cikin Muryan Zatinsa ya Sako kanshi Falon Tare da Sallama.

*How to pay....�?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?600...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?500 ne,VIP
�?1000, Single one �?300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*
a: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*A page 2 ansamu Kuskure akan Wajen da zanyi Numbaring Shekarun Ya muktar da


Daada,Am very Sorry shekarun ya Muktar 49 Daada kuma 76 ne....Tanque so much Mr
Farooq for d Correction...Na Tabbata bakya karatun littafan Janafty da Zuciya kadai
kina Hadawa Da Sarrafa kwakwalwarki... Son so Fisabilillah*

*🅿�?3*
Falon Farko Babu Kowa Sai Talabijin Dayake Ta Faman yi Shi kadai,Kan Daya Daga
Cikin Kujerun Falon Zubaida ta Zauna Tana Fadin"Daddy Anty Rahila Inaga Tana
ciki.."Kallonta yayi kafin yace"Ok...Taso mu Shiga ya zaki zauna Anan ke
kadai.."Jim tayi kafin Ta Mike tayi Gaba ya Biyota Har Zuwa Falon Anty Rahila Nan
ma Shuru,Suna tsaye sai ga Zulfa Ta Fito Daga Kichen da Faranti Shake da Kolili da
Jug da Kofuna Baki ta Washe Tana Fadin"Lah Daddy u are wlcm..."Mirmishi ya saki
kafin yace"Thanks Zulfa Dota.."Yafada Yana D:an Bin Falon da kallo.

Zubaida Ta kalleta kafin ta Samu bakin Mgana Alheri da Jumai ma"aikata gidan Sun
Fito da Manyan Wasu Food Flks masu Kyau,ganin Daddy Tsaye yasa Suka Ramkwafa Suna
Gaisheshi ya Amsa Cikin Sakin Fuska,Kafin Su Wuce Zuwa Babban Dinning Din Dake Gefe
Guda Daga Cikin Kayatattacen Falon.

Da kallo Zubaida Ta Bisu Kafin Ta maida Hankalinta kan Zulfa Wacce Ta Nufi karamin
Center Table din Dake Falon Ta Dora Farantin Tana Fadin"Daddy inaga fa Anty Rahila
na Shashen Daada..."Tafada Tana yarfe Hannu,kafin yayi magana tace"Let me call
her.."Da Hannu ya Dakatar da Ita yana Fadin"No need Dota bari na karisa
Ciki.."Yafada yana maida Hulansa Bisa kai Mirmishi Tayi kafin Tace"Ok Daddy.."Bai
Kara Bi Takansu ba ya Shige Koridon Da Zai Sadashi da Dakin Daada.

Sai da ya Kule Kana Zubaida ta Kariso gaban Zulfa Tana Fadin"Ke kadai yau zaki
Taking Dinner...? Yamutsa Fuska Zulfa Tayi kafin tace"A'a me kika gani Hala..?
Tafada Tana Kokarin Shashantar da Zencen.

Zubaida tabi Abincin Dake gaban Zulfa da kallo Tace"Dis.."Tana nunawa da Baki Wani
Mirmishi Zulfa Ta Saki kafin tace"Oh..! Is for My Uncle Bello.."Tafada Cike da Wani
yanga Kamar Tana gabanshi Wani Kallo Zubaida ta Watsa mata kafin Tace"Ur"s..? Fari
da ido Zulfa ta mata kafin tace"yes of Course...'"Tafada Tana wani Tsuke baki.

Kallo kallon Suka ma Juna mai Cike da Jin Haushi da Kishi kafin Zulfa ta Kauda kai
ta Tafara Taku kamar Zata Fice Daga Falon tana Fadin"Let me take my Shower
First..."Take Fada Tana Kada Mazaunanta Da gayyah har Tayi Kwana zuwa Wani Korido
inda Shashen Saukan baki yake,Da Kallon Bakinciki Zubaida Tabi Zulfa kamar ta
Shakota Takeji,

Kugu ta Rike Kafin Ta Fada Bisa Kujera Tana Dafe kai Cikin Sanyin Murya tace"Oh my
goodness..."Take Fada Tana Tattare Naman Goshinta Waje Daya Cike da Damuwa Lokaci
Daya Ta Saki karamar Ajiyar Zuciya Ita Fargabanta Daya kada Zulfa ta Sace Zuciyar
Bello da kyawunta Da Kuma kyan Jikinta Domin ba karya Zulfa ta Cika Mace da Kowani
Namiji zai yi Fatan Mallaka Tafita komai Ta bangaren Cikar mace,Tuna Hakan Datayi
ne yasa Ta Mike Tana Fadin"No...it's can be..."Kafin Ta Yi Mirmishi ta Furta.."We
shall See Zulfa..'

Tafada Tana Sakin Numfashi kadan Cikin Sassarfa Ta Nufi Hanyar da Zulfa Tayi Gefe
Daya Kuma Tana kallon Alheri da Jumai da Suketa kaida kawon Jera Abinci Bisa
Dinning Table.

****

Tun Kafin ya kariso Kofar Falon Yaji Muryan Daada Suna Hiran Aneesa Ita da Anty
Rahila Mirmishi ya Subucemai kafin yace Afili"D 2 sturborn are back..."Yafada yana
Tura Kofar Falon ya Shiga Da Siririyar Sallama

"Assalamu Alaikum..."Yafada yana Washe Baki Atare Daada da Anty Rahila Suka Dago
Suna kallon Kofa Lokaci Daya Suna Amsa Sallamarsa,Cikin Fara"a Daada tace"Ah babban
Mutum Andawo...? Tafada Cike da Fara"a Hibba ko Da Gudu Tatashi Daga Jikin Daada ta
Nufeshi Tana Fadin"Daddy..."Takalmin kafarsa ya Salube kafin ya daga Hibba Sama
yana Fadin"Oh my God....my One and Only Dota Hibbatullahi..."Yafada yana Sabata a
kafadansa Tana Dariya da Fararen Hakoranta ta Saka Hannu ta Cire hulan Kansa ta
Dorama Kanta tana Fadin"Daddy Toja..."Tafada da Muryan yarinyata.

Dariya ya Saka yana Fadin"Yes my Princess.."Yafada yana Sakarmata Kiss a gefen baki
Anty Rahila Data Mike Tsaye ta Kariso Tana Fadin"Daddy Sannu Da dawowa Thank god
Mijina Is Back Safely..."Tafada Tana Jifanshi da Wani Shu"umin Kallo.

Dago da kanshi yayi yana Fadin"Thanks Rahi Queen..."Yafafa kafin ya Fara Takowa
Zuwa gaban Daada yana Fadin"Daada wai meyasa Kike da Son Zama kasan nan ne..? Baki
Hawa Bisa Cussion..."Daada Tace"Kai ni Rabani da Wani cusa Nagaji kullum Mutum na
saman Abu ba Hutawa,Kune yaran zamani da Kuka lalace da Hutu mu Ada Waya san Wani
Cusi..."Tafada Tana Dariya..

Dagashi Har Anty Rahila Dariyan Suka saka Kafin ya Zauna Kusa da Daada yana Dora
Hibba kan Cinyarsa Lokaci Daya yana Fadin"An bari Daada Kiyi yadda Zaki fi jin Dadi
kun Wuni Lafiya ina Anee yan Mkranta..? Yau Duka Masu Ciwon kan gidan Sun Dawo
Lokaci Daya..? Yafada yana yar Dariya.

Daada tace"Umh Aneesa kadai muka gani Megidan nawa bai Shigo ba Tukunnah kasanshi
Kila yaji Zuwansu Zulfa ne Shiyasa Yaki Lekomu Daya Dawo.."Gyada kai yayi yana
Fadin"Kobama Haka ba Daada Megidan naki bayajin mgana Har yaushe ne zai Ta Rike
Abunda ya Riga ya Wuce,Ayi mutum da Shegen bakar Zuciya da Naci Haba
Daada.."Mirmishi Daada ta Saki kafin tace"Muhammed bello Sunan nan ya Samo Asali ne
fa Muntari Sunan Kakan ku ne Wanda kaf Halayenshi Bello ya kwaso Shima Haka nayi
Fama Dashi da Shigen Kafiya da Zuciya Shiyasa wani Lokacin in naga Bello na Wani
Abu sai Kakanku ya Dinga Fadomin Araina.."Tafada Tana Share Kwallah.

Ido Muktar ya Zaro yana Kallon Anty Rahila Kafin ya daga mata Gira Yar Dariya Tayi
kafin Ta make Kafada,Ta karisa ga Daada Ta Zauna Kusa da Ita tana Fadin"Daada Wai
har yaushe ne zaki Daina ma Kaka Kukan Mutuwa ne..? Daada na Sharbe Hanci Tace"Har
Abada ne Rahila Bazan Taba mantawa da Megidana Bello ba Kusan Irin yadda ya Soni
bane ya Kula dani sai da fa yayi Shadi kafin ya samu Aka bashi Aurena.."Muktar da
Rahila Suka Kalli Juna kafin Muktar yace"Ah lalle kice Kaka Shima Jarumi ne.."

Daada na Mirmishi tace"Sosai Ku bari Watarana Zan Baku Lbrin Kakanku da Jarumtar
Dayayi Sosai Alokacin Rayuwarsa.."Kai Muktar ya Gyada kafin yace"Tom Daada.."Yafada
yana Wasa da Hannu Hbba kafin yace"Wai Ina Anee yan Mkrantan Kwana Banji Motsinta
bane..?Anty Rahila tace"Tana Cikin Bedroom Dazu dai Wanka na barta tayi yanzu zaka
kaga ta Fito inajin bataji Shigowarka ba Andawo Ana Ta Murnan Angama Karatu
gabadaya.."Tafada tana Dariya.

Shima Dariyan ya Saka Kafin yace"Kai...Ina Ruwan Aneesa Wato Da gaske yanzu batason
karatun,Dazu ma Yaya Ali ya Kirani yana Tambayana Wai ta Natsu Kuwa..? In da Wata
Mtsala na Kirsa har Abuja zai zo ya Sake Cin kaniyarta ."Anty Rahila Tace"Oh ya
Allah..! Ya Ali Dodon Aneesa ne,Bata jin Tsoron kowa kamar yadda Takejin
nashi.."Daada tace"Ba dole Taji Tsoronshi ba Tunda Bai da Hankali yana babba Ammh
ya kama yarinya karama Kamar Aneesa yayi Ta Duka Kamar ya Zauce.."Tafada Cike da
Jin Haushi.

Anty Rahila tace"Daada Kema kin So ganin Laifin ya Ali ne Kinfa Gannin ma Idonki
Rashin Jin Aneesa Nan Ranar da Bello zai Tatafi da ita Mkranta baki ga Abunda Tayi
ba Wlh ba Domin Zuwan ya Ali ba Anee bata zuwa Makrantan nan Bata Shiri da
Makranta Tun tana Borno Koda Baba Nada Rai bata Zuwa Shi kuma Bayason Matsa mata
Shiyasa kika ganta batajin mgana Sam..."

Daada Ta tabe baki tace"Toh Dole ne karatu Ku kyale yarinyarnan Hakanan Don
Allah ,haba Kuduba fa ku gani Shekaru uku ammh haryanzu bata saba ba in Zata Tafi
da Kuka Take Tafiya.."Muktar yayi Dariya Kafin yace"Daada Wannan Hurumim Megidan
ne ki kiyi mai Mgana In ya Kyaleta Shikenan sai Asamata Wata Day Anan sai Ta Cigaba
da Zuwa In kuma yaki Dole Anee ko Tana so ko bata so sai Ta Koma Makrantar nan ta
Dora Daga Inda ta Tsaya Kinfi kowa Sanin Tuni ya ce na barmai Ragamar Karatunta
Ahannunshi Kuma yakawomin Hujjojin Daya sanya Ya kai Aneesa Mkranta Dayake Koyarwa
Kuma Nima na Gamsu In ba Bello ba Bamai iyawa da Rigimar Aneesa.."

Yafada Cikin Sauke Numfashi Anty Rahila Zatayi mgana Kenan Aneesa ta Bude Kofa Ta
Fito Tana Fadin"Daada Ruwa Goma nayi ma kaina Allah a mkranta bama Samun
Ru...."Mganarta yamakale ne na Hada Idon da Sukayi da Muktar Wanda ya Dago yana
Kallonta Tana Sanye da Doguwar Rigar Atamfa Mai Red And Ash,Washe baki tayi kafin
tace"Ya Muktar..."Tafada Hakoranta Duka awaje .

Yana Dariya Shima yace"Aneesa yan Mkranta Wlc back Home..."Da Sauri ta kariso
gabanshi ta Zauna Harda Tankwashe Kafa Tafara Fadin"Nagode ya Muktar Saura Murna na
Biyu..? Tafada Tana kallon Idanuwanshi Zaro Ido yayi kafin yace"Wow..Menene Shi..?
Dariya Tayi Tana Kallon Anty Rahila da Daaada Tace"Baku Sanar Dashi na gama Karatun
bane.."

Tafada Cikin Tabbatarwa,Tare da Anty Rahila Suka Hada Ido Suna Kunshe Dariya Cikin
Shanye Dariya yace"Oh..Anee,Da Sauranki fa Yanzu dai zaki Shiga Shashen manya SS1
Ko ba Haka ba Rahi queen..? Anty Rahila tace"Hakane kam.."Tafada da yar Dariya.

Bata Rai Aneesa Tayi kafin Tace"Wa..? Wai ni zan Koma Wannan Dajin Makrantan Wanda
bakomai Cikinta sai Wahala Tabdijam na Rantse da Allah Wannan karon Ko mai Zai Faru
Sai dai ya Faru bazan Koma ba..."Tafada Idanuwanta na Cika da Kwallah Dukkansu da
Kallo Suka Bita Anty Rahila tace"Bazaki Koma ba Kika ce Aneesa.."?

Idanuwanta na Zubar kwallah tace"Eh bazan Koma Wlh bazan Koma ba.."Tafada Tana
Share Kwallah.

Ido Anty Rahila ta Bude kafin Tace"Lalle ko Ya Ali zai Zo kamar Zuwanki na Farko
kin dai san Halinshi ko..? Toh Tun Wuri Kiyi Shirin Komawa Makranta da Zarar Firt
time yayi Lokacin Shigan yan SS1..."Tafada Tana kallon Aneesa Wacce Tana Jin Haka
ta Kama Buga Kafa Tana Kuka Harda Birgima Tana Fadin"Wlh Allah bazan Koma ba Ko
Za"a kasheni Dama ba"a Sona Wayyo Baba,Baba ka Tafi ka barni bani da mai Sona Sai
kai,Wayyo Baba..."Take Fada Tana Kuka Tana Wani Zabure Zabure Kamar karamar
yarinya...

Anty Rahila da Muktar Suka Kalli Juna na Wani Lokaci Kafin Su Maida Kallonsu kan
Aneesa Wacce ke Shan Hanci da Majina,Daada ce Ta Mike Ta Isa ga Aneesa Tana
Fadin"Aneesa yaki nan Taso maza ki bar Wannan Kuka Matukar ina Gidan nan bamai
Maida ki wannan Mkrantar Tunda baki Sonta "Tana Jin Haka Ta Mike tana Fadin"Da
gaske Daaada.."?

Kai Ta gyada mata Tana Mikar da Ita Tsaye Hannu Aneesa Ta Sanya Tana Share Hawaye
Kafin Tace"Daada To ya zanyi da Uncle Bello..? Wayyo yaya Ali ma Daada in Anty
Rahila Ta gayamai Kasheni zaiyi in yazo.."Daada ta Girgiza kai Tana Fadin"Duka ki
barni Dasu Bamai Tabaki Shima Alin bazai zo ba Insha Allahu Sai dai zaki man
Alkawari Daya..? Tafada Tana kallonta.

Cikin Saurin Aneesa Tace"Fadi komiyeshi Zan yi Miki Daada Aini kingamamin Komai
Tunda Kika goyi bayana ."Daada tace"Alkawarin zaki min Matukar nayi ma Megidana
Bello mgana ya kyaleki Anan To zaki Yarda Anema Miki Wata Mkrantar Anan Sai kici
gaba Kinji ko.."Kuri Aneesa Ta mata da Ido Tana Tura Baki kafin tace"Nifa Daada
nagaji da Karatun ne.."Daada ta Dafa kanta Tana Fadin"Toh Shikenan Zan barki Da
Bellon.."Jin Haka yasa Tayi Saurin Fadin"A"a Daada na yarda Allah da dai Amaidani
Wannan Dajin Da ko Ruwa fa Babu Daada,ga Aljanun Tsiya Allah Daada Muna Shan Wahala
Uncle Bello baisan gaya Muku ne.."Tafada Tana Matse Kwallah.

Daada na Shafa kanta tace"Ai yanzu komai ya kare bazaki koma ba.."Jin Haka yasa
Aneesa Ta Daka tsalle,Ta Rumgume Daada Tana ma Anty Rahila Gwalo Tana Dariya Bude
Ido Tayi Tana Kallonta kafin Tayi Mgana Aneesan Ta Saki Daada Tana Fadin"Daada bari
natafi nayi sallah Ana Kiran Mangariba.."Tafada Tana Shigewa cikin Bedroom dinta.

Ajiyar Zuciya Muktar ya saki kafin ya Shafa kanshi yana Fadin"Daada Bazaki iya
Tankwasa Bello Akan Aneesa ba Why Kika mata Wannan Alkawarin..."? Daada na Kokarin
Shiga Dayan Bedroom Din Tace"Dole ya barta Tunda bata so Shidai dayake so sai ya
Koma Shi kadai kar Abun ya Zama Zalunci.."Tafada Tana Tura Kofar Bedroom Din Ta
Shige Domin Dauro Alwala.

Shuru yayi yana Nazarin Abun Acikin Ranshi kafin ya Dago yana Kallon Rahila yana
Fadin"Bansan ya Zanyi da Bello ba Rahila...Yana Sakani Ciwon kai.."Mirmishi Tayi
kafin Ta Mike Tana Fadin"U will Discuss later yanzu ka Tashi muje Sama kayi Wanka
ka Sauya kaya kayi Sallah sai mu Sauko Dinner.."Baiyi Gardama ba ya Mike Yana Rike
da Hibba Hulanshi ta Sojoji Ta karba kafin ya Riko Hannunta,dayan hannun Kuma yana
Dauke da Hibba Suka Fice Daga Falon Daada Zuwa Sheshen Rahila Steps Suka Haura Zuwa
Sama Inda Dakunan barcinsu yake

******

Zaune Yake Atsakiyar gadonsa yana latse latsan Laptop din Dake gabanshi Sanye da
Riga da Wando Masu Ruwan Toka na Jc,Tun Dazu yakejin Karan Mad Door,bai maida Abun
Serious ba Domin yana Kyautata Zaton Zubaida ne Tsaki yaja ya Cigaba da Abunda
yakeyi kamar bai ji Mad Door din Da"ake ta Danna mai ba,Ransa bace yake tun bayan
Fasa mai Hoto mai muhimmanci datayi dayace ta dawo ta kwashe sai ta gudu dole shi
ya tattara glass din Hoton kuma ya Zareshi cikin gidan Album din ya sakashi cikin
Durowar gadon.

Zulfa Dake Tsaye da Faranti Taci Kwalliya Cikin Wata Doguwar Abaya na Kamfanin
Armani ta yane kanta da Karamin Bakin gyalen Kayan,Fuskarta ta Dauki Haske Saboda
yadda ta Tsaru da Kwalliya Tafi Minti goma Sha Biyar Tsaye tana dannan Ring Ammh
ba Alamun za"a azo Abude Cikin Bacin Rai da Kufuluwa Zulfa tace"Plz Open d Door
Uncle.."Tafada kamar Tayi kuka ganin Tsayuwa na Neman gagararta gashi Tagaji yasa
ta Juya Tafara Saukowa daga Steps Din Jikin Sanyi Jiki da Nadama mai Tsanani.

Dukkansu Suna Bisa Dinning,Anty Rahila,Muktar,Daada,Aneesa Hibba,Zubaida Suna


Dinner Suka ga Shigowar Zulfa Falon da Sauri kamar Zata Kifa Dauke da Tiren Abinci
Riki Riki Tana Kwalama Alheri kira Gabadayansu da Kallo Suka Bita kar Zubaida Taji
lbri Wacce Tun Fitan Zulfa Zuwa Shashen Uncle bello Taji ta Kasa Natsuwa ganinta
Cikin Wannan Fushin yasanya Zuciyarta Tayi Sanyi Har Mirmishi ya Wanzu Akan
Fuskarta.

Cikin Mamaki Anty Rahila tace"Oh"ah...Zulfa ya kuma kika Dawo Da Abincin Bellon ya
Fita ne..? Zulfa na Kokarin Daidata kanta tace"He is not open d Door Anty i Did
know if he is Inside da Room..."Tafada Daidai Lokacin da Alheri ta kariso ta Mika
mata Farantin Kenan Anty Rahila Ta Mike tana Goge Bakinta da Tissue tace"No Wait
Bari na kaimai Tunda ya Dawo fa baici komai ba ya Allah! Bello nasan Horan kanshi
da yunwa.."Tafada tana Karisa wa ga Zulfa ta karbi Farantin Kololin Tana
Fadin"Hibba Bring my phone.."Muktar ya Dauki Wayar Rahilan Dake Kusa Dashi ya
Mikama Hibban ta Sauka Da Gudu Zuwa Wajen Anty Rahila wacce Tayi gaba Tana
Fadin"Keep Follow me Princess.."Jin Haka yasa Hibba Tabita Suka Fice Daga Falon.

Aneesa Dake kallon Zulfa Tunda Ta Shigo Ta Saki Dariyan Datake kannewa Da Mamaki
Zulfa ke kallonta Cikin Kuluwa tace'"Ke Aneesa Wa Kike ma Dariya.."?

Tafada Tana Karisowa Wajen Babban Teburin Aneesa Ta Dago Tana Kallonta Cikin Rainin
Wayau tace"La Anty Zulfa Nifa bada nake ba Me kikayi balle nayi Dariya.."Tafada
Tana Kara Sakin Dariyan Wanda ya kara Harzuka Zulfa ta Kariso Azuciya Zata Daki
Aneesa Daada Tace"Ke miye Haka..? Daga Tana Dariya sai kice da Ke Takeyi Hala Kinyi
Wani Abun Dariyan ne. ? Nifa bana son Mugunta Zulfa'u.."

Tafada Hankalinta Kwance tana Sharban Ferfesun Kayan Cikinta Turus Zulfa Tayi Tana
Bin Daada da kallo Ita da Aneesa Wacce Take Kada kai Tana yar Dariya,Muktar ne
yace"Zulfa Sit..."kallonshi Tayi Hawayen Datake Rikewa Suka Zubomata Mai Zubaida
Zatayi In ba Dariya ba Harda Dukawa kafin ta Mike tana Goge Bakinta da Tissue Cikin
Muryan Shakiyanci Tace"Lost Zulfa..."Tafada Harda Dafata tana Kada mata ido kafin
ta Wuce Tana yar Dariya Zulfa Ta kawo Wuya da Hanzari Ta Bi bayanta tana Kiran
Sunanta Cikin Muryan Kuka Cike da Fada Bayansu Muktar da Daada Sukabi da Kallo
Aneesa Ko kamar ta Zuba Ruwa Akasa Tasha Saboda Jin Dadi Aranta tace"Wahalallu Sai
kuyi Tayi indai Wannan Mugun ne baku ma gama Wulakanta ba.

Ita kanta Anty Rahilan Tayi ta Danna Mad Door din ammh Shuru Sai ta kalli Hibba
Tana Fadin"Bani Wayar Princess.."Da Hanzari Hibba Ta Mikamata Da Dubara ta Rike
Wayar kada Farantin Hannunta ya Subuce mata ta Lalubo Nombar Bello.

Yana Tsakar Aiki yaji Ringing Din Wayarsa Cikin Kasala ya Jawota sunan *ANTY* ya
Fito baro baro Da Sauri ya Daga yana Fadin"Anty...!" Cikin Sauri Anty Rahila
tace"Ina Kofar Mension Dinka Bello..."Tafada da Alamun Gajiya da Hanzari ya Datse
Kiran ya Dira daga kan gadon ya Bude Kofar ya Fice Daga Bedroom Din da Sassarfa
Zuwa Falo da Hanzari ya Bude Kofar yana Kallonta da Hibba Dake Tsaye Cikin Mamaki
ya kariso Fitowa yana Fadin"Am Srry ban..."Is ok bello Help me Wit Dis.."Ta
Katseshi Tana Mikamai Farantin Hanunshi karba yayi yana Basu Hanya Lokaci Daya yana
Fadin"Oh my God Our Little princess u are Wlmc.."

Yafada yana Kallon Hibba Wacce kemai Dariya Tana Fadin"anchu.."da Muryanta na
Yarinya Shigewa Sukayi ya Tura Kofar da Kafa Karamin Center Table din Tsakiyar
Falon yaja ya Ijiye Farantin yana Fadin"Anty Banzaci ke bace.."Tana Zama Bisa Daya
Daga Cikin Kujerun Falon Tace"I know.."Tafada Tana kallonshi Hibba ya Dauka Wacce
Ta Dafemai ya kariso Kusa da Ita ya Zauna yana Fadin"Anty ya gida..? Daada na
lafiya..?

Anty ta kalleshi kafin tace"Bansani ba Bello..Meke Damunka ne Tunda Kuka Dawo baka
Shigo ba ko Abinci baka Nema ba,Kana so kullum yayanka ya Dinga Fushi Dakai bakajin
Mganarsa Komai yace baka bi sai dai Naka Ra"ayin.."Bello ya Zaunar da Hibba kan
Cinyarsa yana Shafa kanta kamar Bazai yi Mgana sai Chan yace"No Anty Ba Haka bane u
know my problem Bazan iya Shiga Barayin ba Indai yaran nan basu Barmana gida ba I
Mentiond it.."Kura masa Ido Tayi Kafin tace"Naji Ammh kasan yayanka bazai koresu ba
kuma Infact is ur Family bello.."

Cikin Halin ko In Kula yace"they are not my Family Anty At All,Only yaya and
Ur,Daada and Hibba...Kune Ahalina..."Yafada yana Kokarin Danne Fushinsa.

Ganin yanayin Daya Shiga ne yasa Tace"Is ok..Take ur Dinner ok.." kai ya gyada mata
kafin yace"Insha Allah Anty.."Yafada yana Kallonta Cike da Kulawa Mikewa Tayi Tana
Fadin"Hibba come let go.."Hibba ta Sauko daga Jikin Bello tana mai Bye bye Yana
Mirmishi ya Daga mata Hannu Mikewa yayi Sanda Anty Rahila ta kama Hannunta Zasu
Fice Daga Falon Cikin Muryansa ta Kasaita yace"Anty ki gaida yaya..Am plz Take Good
Care Of Him karki barshi yayi Damuwa saboda ni U see am ok.."Juyowa Tayi kafin
tace"Ok i Will..."Tafada Kafin ta Fice Daga Falon Shi kuma Ya Bita ya Kulle Kofar.

Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Kimikimi Tiren Zuwa Kichen Cikin Fridge ya Sakashi
Domin baya Jin Wuya yanzu yagama Shan Tea sai dai da Safe Falon ya Dawo yana Faman
zagaye Wajen Duka Hannayensa Sarke Abayansa Fuskarsa Tana bayyana Damuwar Daya ke
Ciki Duk da baya bama Hakan Muhallin Bayyana Cikin Wasu Dakikai Abubuwa Dadama Suka
Fara Dawomai Cikin Kwakwalwarsa..

*How to pay....�?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?600...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?500 ne,VIP
�?1000, Single one �?300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*Shakira...* *MR BELLO..!*


_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*🅿�?4*

*#FLASH BACK...*

🌟 *ALHAJI MUHAMMED HASHIM JIKAMSHI* Shine Asalin Sunan Mahaifin Bello Da Muktar
Wanda ya Kasance Haifaffan Garin Jikamshi ne,Dake Hukumar Da'n Musa Dake Cikin
Babbar Jahar Katsina.

Alhaji Hashim Mahaifin Muhammed Ya kasance Ma"aikacin Hukumar Wutar Lantarki na


Garin Jikamshi Yana da Rufin Asirinshi Daidai Gwargado,Matarsa ta Farko Hajiya
Maryam Ta kasance Yar Dangi ce Auren Zumunci Akayi musu Ita yar nan garin Jikamshi
ne,Wata tara nayi Ta Haifo Kyakyawan Danta Namiji Aka Sanya Masa Suna *KABIRU* Sai
Haihuwanta na Biyu Ta karayin *ABUBAKAR* suna Kiranshi Garba,wanda Tsakaninsu
shekara Daya ne.

Tana da Cikin na Uku Hashim ya kara Aure da Wata Yar Malumfashi mai Suna Aisha
Auren Dayasha Mganganu Sosai Har Saida maryam Tayi yaji Zuwa gida Saboda Ta Tada
Hankalinta kan Hashim bazai kara Aure ba Shi kuma yace Sai yayi Toh iyayensu mata
ba Wanda ya Goyi bayanshi Saboda Maryam Iyayensu maza ne Suka Shiga Mganar Har
Maryam Ta Koma Gidan Hashim Akayi Biki Lafiya Aisha Tatare Agidan Mijinta.

Tun Zuwan Aisha gidan bata taba Jin Dadin zama da Maryam da ya"yanta ba Saboda
yadda Take Nuna mata Tsana Kirikiri Hakama Dangin Hashim Din Sun Koma bayan Maryam,
Aisha ta Zama bata da Wani gata agarin Jikamshi Tunda Ita iyayenta Sunyi Nisa,Tana
Shan Wahala Wajen Maryam da Dangin Hashim Ammh ko Sau Daya bata taba Furtama Hashim
ba Sai ma Kokarin Farantamai Cikin Hanyoyi Dadama Wannan Shi ya Taimaka Wajen Bata
matsayi mai Girma Acikin Zuciyar Hashim Uwa Uba ga Hakuri da Kawaici ga Sanin ya
kamata.

Wannan Kulawar da Hashim ke Nunawa kan Aisha Har saida Maryam ta kai Karanshi Agida
Wai yana Fifita Aisha Akanta Wanda Dangi Sukamai Chaaa Aka Tarasu Dukkansu Akayi
Musu Fada Abun ya bashi Mamaki ammh Kuma baya jin zai Fasa Nuna Soyayyarsa ga Aisha
,Watan Aisha Uku da Zuwa gidan Ta Samu Ciki mai laulayi Sosai yana bata Wahala sai
ya kasance ko Wanka Sai Hashim yayi mata yake Fita Wajen Aiki Wanda ya karama
Maryam Wutar Kiyayyar Aishan da Kishinta Shikuma Hashim yace bazai Fasa ba.

Cikin Aisha na Wata Biyar Maryam Ta Haifi yarta mace Wacce taci Sunan Mahaifiyar
Hashim Wato *RUKAYYAH* Ita Kuma Aisha Sai da Cikinta yakai Wata Goma kana aka mata
Operatin Ta Haifi katon Danta Namiji Yaci Sunan *MUHAMMED* Wanda Dangi Sukayi ta
Ceceku Game da Haihuwar Saboda Yadda Hashim ya Kashe Kudi Sosai ga Hidimar Aisha
Tundaga na Asibiti har Zuwa na Hidimar Suna,Duk da Haka bai kulasu ba Kuma Itama
Aisha bata maida kai ba Duk ko Da mganganun da Maryam din Ke Jifanta Dashi.

Watan Muhammed Goma Sha Tara Aisha Ta kara Samun Wani Cikin Wanda yazo da Sauye
Sauye Dadama Domin An Sallami Hashim Daga Wajen Aikinshi batare Dayasan Laifin Daya
Aikata ba Kuma Sallama babu Biya kowani karin Bayani Abunda ya matukar Tadamai
Hankali Shida iyalanshi Gabadaya Gashi Lokacin Kabiru da garba Asanyasu A mkranta
Harda Rukayyah Muhmmed ne kadai ba'a Sakashi ba,Abunda yafi Dagamai Hankali Shine
Lokacin da Zai Auri Aisha yana gidan gado ne To Shine yaci bashin Banki,ya Siya
Fili ya gina gida Duk Wata yana Cire Wani Abu Daga Cikin Albashinshi yana Biya Toh
gashi An Sallameshi Kuma Banki bata Jira Dole ka a Biyata Kudinta.

Lokacin da Dangin Hashim Sukaji Wannan lbrin Shikenan Sai Aisha Takara Shiga
Gararin Rayuwa na Cewa Itace mai Farar Kafa,Itace Tunda Hashim ya Aurota Karayar
Arziki ta Kamashi Sai dai Ta Shige Daki Tayi ta Kuka Tana Rumgume da Muhmmed ga
Cikinta ya Tsufa Alokacin ne kuma banki Suka Nema Kudinsa Shine Dalilin Saida Duka
kaddarorinsa da Motocinsa Harda Gidan Da Suke Ciki Suka Tattara Suka koma gidan
Gado.

Aisha ta Shiga matsi da gararin Rayuwa Domin ba Inda Takejin Dadi Sai Ta bangaren
Hashim Kuma Koda yan"uwanta Sunzo bata Nuna Musu Wani Abu Sai Dai Su Tafi Suna
Zencen Ramarta Acikin Wannan Halin Ta Haifi yarta Mace mai Suna *HIDIYA* wanda
Tunda Lokacin Da Aisha Ta Haifeta bata kara Lafiya ba Harta Koma ga Mallicinta ta
bar Marayin ya"yanta Hannun Matar Hashim Wato Maryama.

Hashim yayi kukan Rashin Aisha Sosai ga Talauci ga Kewar Aisha Sai Suka Taru Suka
Sanyamai Hawan Jini,Dangin Aisha Kuwa Sukayi ta Kokarin ko Hidiyan Hashim ya basu
Su Tafi da Ita Ammh yan"Uwanshi Suka Hana Wanda ba Kowa bane ya Kitsamusu Haka sai
Maryam Domin bataso Adauke ya"yan Tafison Abarsu Tayi ta gana Musu Azaba Domin
bata taba Son Uwarsu ba Suma bazata Taba Sonsu ba

Haka ko Akayi Dangin Aisha Sunaji Suna gani Suka Tafi Suka bar Muhammed Dan Shekara
Uku da Wani Abu yayinda Hidiya Keda Shekara Daya da Rabi Abun Tsausayi Ammh Sun
Sanar Dasu Cewa Lokaci bayan Lokaci Zasu Dinga Zuwa Dubasu Suka Amince,Bayan sun
Tafi Aka Dauki Amanar su Muhammed Aka Damkama Maryam Wacce Ta karbesu kamar Gaske
nan ko Cikin Ranta Mugun Nufi ne

Tun kafin Rasuwar Aishan Dama Ta Dade da Karantama Duka ya"yaanta Cewa Su Muhammed
ba yan"uwansu bane Abokan Gabansu ne Saboda Babansu yana Fifitasu Fiye dasu Tayi ta
saka musu Mugun Nufi acikin Zuciya Abunga ga yara nan da Nan Suka Haddace Karatun
Nata Shiyaasa Muhammed Da Hidiya Suke Shan Wuya Ahannuta Ita da ya"yanta In Hashim
yayi mgana ta Fashe da Kuka tace ya Raina Kokarinta,Data Fahimci Yana Damuwa da
Halin da Suke Ciki Sai Koma yi musu Mgunta Aboye Abinci ma Kanzo Take basu,Ga
Wahala Akasa Suke Kwana Cikin Sanyin Kasa Kafin Arufe Shekara Daya Yara sun Chanza
Kamanni Tun balle ma Hidiya Wacce Bata da Lafiya Saboda Kwanan Kasa Nomomiya ta
kamata Hashim baidata Cewa Domin Da yayi mgana yan Uwashi Zasu Tasomai da Fadin
Uban me yake Tsinanawa Banda Zaman Banza,Yanaji yana gani sai dai yayita Kuka
Shikadai Saboda Tsausayin Muhammed da Hidiya.

Amkrantar Gwannati Aka Sanyasu Sakamakon Kabiru da garba Dasuke na Kudi Tunda
yan"uwan Hashim Sunfi Son So,Muhammed Tun yana Yaro yasan Gwagwamaryan Rayuwar
Duniya,Sau biyu Dangin Mamansu na Zuwa Dubasu Suna Komawa da Kuka Saboda Tausayin
Halin da Suke Ciki Tun Bama Muhammed ba Wanda Ke Karami Ammh Wahala ta Zama Cikin
Jikinsa.

Tun yana Aji biyar yasan In An Tashi Mkranta ya Kama Hannu kanwarsa Su Shiga Cikin
Kasuwa Yaringa Dako yasamu Abunda Zai Siya musu Abinci Domin Ko Sun Koma Gida Mama
maryam bazata basu ba,Toh Ahakan ma basu Tsira ba In Suka Dawo sai ta kamasu Ta
Masu Duka Hidiya Kuwa Kullum Cikin Kuka Take garba ya Daketa Kabiru ma Haka
Rukayyah ma Sai dai in Muhammesd ya Ramata Mama ta kamashi Tayi mai Dukan Tsiya
basu da Wajen da Suke Jin Sanyi sai Wajen Abbansu Wanda Shima Hawan Jini ya Kwantar
Dashi.
Muhammed Dana Shekara Goma Aduniya Ita Kuma Hidiya Bakwai Allah yayima Hashim
Rasuwar Mutuwar Data Raunana Zukata Dadama Babu Uwa ba Uba Maraici ya Lullubesu
Dama Ganin Abban Nasu ba"a musu Wani Abun Ammh yana Fadi ya Mutu Shikenan Wahalansu
ya Karu Hidiya ta zama Jakar Aiki Itace debo Ruwa,Share Share,aike aike ,Wanki ne
da Guga Ammh Rukayyah na Zaune Jangal batayi Muhammed Kuma Fita yake Tun Safe yana
yawon Dakonsa Sai dare yake Dawowa Ya Siyoma Hidiya Abunda zataci Domin yasan Duk
Wunin Aikin Da Zatayi bazata Bata Abinci ba.

Da Farko Adaki Suke Kwana Tare da Su kabiru Ammh Sai Mama ta Kullama Muhammed
Sharri Akan ta Kamashi yana Turama Rukayyah Ahannu Awando Wanda Iyalan gidansu Suka
Hadu basu Duba kankantar Shakarun Muhammed ba Sukamai Dukan Mutuwa Suka kuma
Koreshi Agidan,Haka yafita yana Kuka Itama Hidiya tana Kuka Wannan Shine Silan
barin Muhammed gidansu Ya bar Hidiya Cikin gararin Rayuwa Bai yi Nisa da garin
Jikamshi ba,Cikin kasuwa yake Wuninshi Sai Dare ya Tafi Tasha ya Kwana yana Tara
Kudinshi Kuma kullum Daddare zai Siyan ma Hidiya Doya da Kwai yazo Zauren Gidan ya
Tsaya ta Sadado ta Fito ya Bata bayan ya Zaunar da Ita taci Tasha Ruwa Haka Zasu
Rumgume Juna Kukan Tsausayin Kansu Hidiya tasha cemai Su gudu Wajen Dangin mamansu
Ammh Muhammed yaki Saboda Shi kanshi bazai iya gane Gidansu Maman nasu ba Don yana
Karami Sosai Lokacin Da ake Zuwa Dashi.

Muhammed bai bar Zuwa Mkranta ba Hidiyace dai Mama ta Kashe mata mkranta Bashi da
yarda Zai yi yanaji yana gani Rayuwar Kanwarsa Tana lalacewa Su kabiru ko Suna
Haduwa Dashi suda Abokansu Haka zasu dingamai Dariya Suna Tofamai Miyau Shiyasa ko
ya gansu yake Saurin Chanza Hanya Hidiya Kuwa Tagama Wahalan Amfanin da Ruwa da
Rana Daddare kuma ta Kwana Akasa nan da Nan Ciwon Nomoniya Takaramata Yawa Sosai
Kullum Cikin Mura take Kwana da Sanyi Ammh ko Muhammed yazo bata Sanar mai Saboda
Karta Tadamai da Hankali Koda yaushe yazo Jikinta yayi Zafi sai ya Tambayeta tace
bakomai.

Adaddafe Muhammed ya kamallah Jss3 sai ya Ijiye Karatun ya Maida Hankalinshi kan
Dakonshi hade kuma da Jari Bola Kwata Kwata Zuciyarsa ta Kekahe Neman na Kanshi
yake ba Domin Shi ba Sai Domin Tilon Kanwarsa Hidiya,yayi kwana Biyu yana Zuwa Baya
ganin Hidiya na Fitowa sai Hankalinshi yatashi Ranar dayazo na Uku Azauren Gidan ya
kwana yana Jiranta Ammh batazo ba,Tundaganan Jikinsa ya bashi ba Lafiya Gudun kada
Wani ya ganshi ne ya sanya ya Koma kasuwa Hankalinsa Duk Atashe Wajen Karfe 1 na
Rana yana Kasuwa yana Sana"ar Dakonsa Wani yaron Kawun Abbansu yazo yake Sanar
Dashi Wai yazo Hidiya zata Mutu Cikin Fitan Hayyaci ya Watsar da Abunda Ke
Hannunshi Suka Rumtuma Zuwa Gidansu.

Sai dai Suka ganshi Kwatsam ya Shigo Har Shashensu Alokacin Wajen Shekara Biyar Bai
kara Shigowa Gidan ba,Hidiya tana Kwance Akasa Siminti Hancinta ya Toshe da majina
Numfashinta baya Fita Ta Rame ta lalace Kasa ya Zube gabanta yana Kuka Hannu Ta
Mikamai Tana Fitar Da Hawaye Daidai Lokacin kuma Kawun nan nasu Suka zo Dama mama
ganin Hidiyan ta Kusa Mutuwa ne Shine taje ta Kirasu Wai Suzo Su gani Ita bama
tasan Bata da Lafiya ba Alhalin Tana sane Itama kema Kara Saka Ciwon Tashi Domin
Wanka take Zuwa tamata Da Ruwan Sanyi Kuma Ta Hanata Sauya kaya Har sai Sun Bushe
Ajikinta.

Muhammed ya Rude da ganin Halin da Hidiya ke Ciki ko Ta kan Kawunsu Dake mgana
baiji ba ya Ciccibi Hidiya yana Kuka Ya Fita Da Ita Waje,yana Ihun Mutane su
Taimakamai Ana Cikin Wannan Halin ne Allah ya jeho Alhaji lawal Acikin Motarsa Zai
Wuce Katsina Alokaciin ganin Muhammed Dauke da Hidiya yana Kuka ya sanya ya Faka
Motarsa ya Fito baima Tsaya Tambayan Muhammed ba ganin Halin da suke ciiki ya sanya
ya karbi Hidiya ya sakata Abayan Mota ya Umarci Muhammed Daya Shiga Su Tafi Agaban
Idon Dangin Mahaifnsa Suka Tafi Asibti da Hidiya ammh ba Wanda yayi Tunanin Binsu.

Babban Asibtin Garin Sukaje sai dai Suna Shigowa Get din Asibtin Hidiya tafara Wani
kakari Muhammed ya Rude ya Rumgumeta yana Kuka yana Kiran Sunanta ganin Idanuwanta
na Kafeewa ne ya sanya ya Kuramata ido hawaye na Fita Daga Cikin Idanuwanshi Yana
ji yana Gani Agaban Idanuwansa Aka Zare Ran Hidiya Abunda ya kasa barin Zuciyarsa
Kenan Har Shima ya koma ga mahallincinsa.

Muhammed yayi kuka Tamkar zai Zauce Saboda Mutuwar Hidiya basu Juya ba sai da Suka
Shiga da Ita Cikin Asibitin Aka Tabbatar da Mutuwar Hidiya Kafin Alhaji Lawal ya
Daukosu Zuwa Gida ganin Kukan da Muhammed Ke Yine yasa ya Tambayesu ina Mahaifinsu
nan Muhammed yana Kuka yana bashi Lbrinsu Wanda ya Matukar bama Alhaji lawal
Tsausauyi.

Abun Mamaki da Suka Dawo da gawan Hidiya ba Wanda ya Nuna Jimami ko Damuwa,Taruwa
kawai Sukayi,Abun Takaichi Muhammed Shi yayima Hidiya Wanka Gawa Yanayi yana kallon
Cikin Idanuwanta yana Kuka Ahaka Har Aka kaita gidanta na gaskiya A makabartan Aka
Watse Aka barshi Alhaji lawal shi ya rikoshi Suka Fito ya Sanyasa Cikin Mota bai
Zarce dashi ko"ina ba sai Katsina.

Alhaji lawal shi da Matarshi Hadiza basu Taba Haihuwa ba Gashi yana da Tarin Dukiya
Ta Dalilin Kamfanonin Dayake Dashi kama daga na Robobi kanfanin Sarrafa Atamafa,na
Takalma ne da Sauransu. ya Tara Kudi masu yawa Tunda yazo da Muhammed yabata
lbrinshi Shikenan Tsausayi ya kamata ta kama Muhammed Ta Rumgume tana Kuka Kuma
Sukaci Alwashi Zasu Rike Muhammed Tsakani ga Allah.

Bayan Rasuwar Hidiya ba Dadewa Dangin Aisha Suka zo ganinsu suka Iske bakin lbrin
Rasuwar Hidiya da Lbrin wai Muhammed ya Gudu ya Shiga Duniya Haka Suka Koma
Malumfashi Suna Kuka Sosai na yadda Rayuwar ya"yan Aisha suka lalace Acikin
Duniya,Shikuma Muhammed ya samu Chanjin Rayuwa ya koma mkranta,bayan ya gama
Secondry Sch Suka Tafi Dangin Alhaji Lawal A malumfashi Alokacin ne kuma Aka gano
Ashe Shi Alhaji lawal Abokin Wasa yake ga Marigayiya Aisha Mahaifiyar su Muhammed
nan fa Sabon Kuka ya Tashi Ana Ta Rumgume Muhammed,Wanda koda da Rana Daya Mutuwar
kanwarsa Hidiya bai Taba Bacemai ba.

Akasar England ya Hado Digree dinsa na Farko Akan Harkan Kasuwanci Haka kuma ya
Wuce Kasar Calponia ya Hado Master dinsa Akan Accouting da Hada Hadar Kasuwanci
Koda ya Dawo Nageria sai Ragamar Dukiyar Alhaji lawal Ta Dawo Hannun Muhammed,Shi
kuma Alokacin A England yayi Aiki da Wani Kamfanin Turawa na Sarrafa Takalmam Maza
so sai Suka Hada Huldar Kasuwanci da Kamfanin Alhaji lawal Dake Nageria kuma
Alhamdulillah Lokaci Kadan Huldar ta kawo musu Kudi Sosai Suka Cigaba,.

Muhammed ya Wuce Duk Tunanin Mai Tunanin jin haushinshi ko Hassda Daga Danginshi
Kuwa Suna da Lbrinshi Domin Alhaji lawal na Matsamai Lokaci bayan Lokaci Yana Zuwa
Dubasu Rukayyah Tayi Aure Akano Su Kabiru kuma Angama karatun Ana Zaune ba Aikin
Mama maryam kuma girma ya Kara kamata da Kuma Hakkin Hidiya da Muhammed Domin Taga
yarda Allah yake Maida bawanshi Lokaci Daya.

Kafin Rasuwar Alhaji lawal Sai da Tabbatar ya mallakama Muhammed Duka Dukiyarsa
bayan Ancire na yan"uwansa,Wannan Abun yabama Mutane mamaki da kuma Girmama
Soyayyar da Alhaji lawal Kema Muhammed Su Kabiru kuwa Hasaada da kyashi bai bar
Zuciyarsu ba,Sai Sukayi lambo Suna Shigema Muhammed Harda Rokonsa Gafara Saboda
Suma Su Shiga Jikinsa Su Samu Arziki Sun kuma yi Nasara Domin Daga Kabiru Har Garba
ya Daukesu Aiki A kamfanonin Alhajin lawal Duk da Abun da Suka Aikata gareshi bai
Taba bacemai ba Ammh in yayi Duba ga Yadda Allah ya Daga Darajansa sai ya Godema
Allah.

Mutuwar Alhaji lawal Da Matarsa Sakamakon Hadarin Mota Shiyakara Fito Da Sunan
Muhammed Aduniya Domin ya Samu Dukiya mai yawa Yawancin Kamfoninin Alhaji Lawal Shi
ya mallakesu Gashi Shima yasan Kan Kasuwanci Kafin Ya Rufe Shekara Daya ya Mallaki
*Jikamshi shopping mall* Jikamshi Store* Jikamshi And Sons Nageria Limited..*
Lokaci Daya Sunanshi yayi Suna A nageria Gefe Daya ya jawo Yan Uwansa Da Dangin
Mahaifinsa yamusu Gata duk da Abunda Suka Aikata garesa Dangin Mahaifiyarsa kuwa
Dama Sune Ahalinsa.

Tuni ya Tattara Kabiru da Garba da Mama Suka koma Katon Gidan Daya gina A Katsina
Komawarsu Wannan Gidan Mai kama da Aljannar Duniya Shiya kara Saka Zuciyoyin Su
Kabiru Gudirtan Cewa Ko Ta Halin kakane sai Sunga bayan Muhammed Sun mallake Duka
Dukiyanshi Ita ko Mama Maryam ta Saduda Ance magaji mafiyi Domin Su Kabiru ya"yanta
ne Ammh Sun Fita iya Kulla Makirci da Sharri Duk da Muhammed na Kanninsu Haka Suke
Sadda kai Suna mai Biyayyah Duk Don ya Saki Jiki Dasu.

Cikin Shekara Uku ya Siya Musu gidaje da Motoci ya kaisu Makka Kuma yayi Musu Aure
Kabiru Akaduna ya auro Karima sai Garba dayayi Aure a Kankara Ya Auro Sahura
Dukkansu Sukazo Suna Cin Arziki da Dukiyar Muhammed Wanda Suka Wulakanta Rayuwarsa
da Farko Mama maryam bata Rasu ba Sai bayan Auren Muhammed,ta rasu ta kukan Neman
Gafaransa kan Abunda ta aikata garesa Shida kanwarsa,muhammed anso a tusamai auran
Dangi A Ammh yaki Domin Allah ya Hadashi da Hassatu Wata Bafullata ne Daga Jahar
Yola

Hassatu marainiya ce Bata da Uba sai Mahaifiyarta Data ke cema Daada Farar
Bafullatana ce Kyakyawa da Ita Dangin Mamansa Suka yi komai na Auran Cikin Lokaci
Hassatu Ta tare Agidan Mijinta Dake Katsina,Tun kuma Daga Lokacin Sai Abubuwa
Sukayi ta Cigaba Arayuwar Muhammed gefe Daya Kuma su Kabiru da Matansu Suna ta Ta
Hada Tuggunsu A boye Ita kanta Hassatu ta sani Domin ba kyashin Da basu Nuna mata
Ammh bata taba Nuna ma Muhammed Ba bataso ta Rabashi da yan"uwanshi.

Karima matar kabiru wabi Takeyi In ta Haihu sai anyi Suna Su koma ga Allah Ita
kuma Sahura matar garba Shuru Haihuwan, Itama Din Shuru Kwatsam Hassatu ta samu
Ciki Su kabiru ba Kulle kullen da basuyi ba kar Hassatu Ta Haihu Ai kuwa hakansu
bai Cimma Ruwa ba Domin A Babban Birnin India Delhi Hassatu Ta Haifi Kyakyawan
Danta Namiji Wanda yaci Sunan *MUKTAR* Basu dawo Ba sai da Sukayi Wata Biyu Suna
Dawowa Kuma ya kaita yola Wajen Daada tayi Wata Daya kana Ta koma Katsina.

Lokacin da Muktar yazo Duniya yazo Cikin Gatan Rayuwa Sosai Saboda Mahaifinshi na
kan Samu Hassatu Ta Fahimci komai Shiyasa Take ta Kafa kafa da D'anta bayan Tana
Sanar da Daada Duk Abunda Ke Faruwa Ita ta Haneta da Karta sanarma Muhammed Ammh
Dai Ta Kiyayi Kanta ta Kuma Dinga Lura Saboda Hakama Dukkansu Suka baro Gidajensu
Suka Dawo Gidan Muhammed ke zaune Shida Hassatu katon Gidane mai Dauke da part part
da Zuwan Wai Sunfi Jin Dadin Zama tare Dashi Shi kuma bai kawo komai ya Amince Suka
Tattaro Suka Dawo nan da Zama.

Inna Rukayyah ma Dake Kano Babu Abunda Muhammed baya Mata tana Kuma Zuwa Akai Akai
Sai dai ita Tunda Tayi Aure Allah bai bata Haihuwa ba Sai da Muktar ya Shekara
Bakwai Aduniya kana Karima matar Kabiru Ta Haifi Danta Namiji yaci Sunan kakansu
*Hashim* Lokacin Tuni Ansaka Muktar A mkranta *International Community School
Abuja* Cikin Gata da Soyayyah mai Tsanani Wanda Ke Kara Wutar Kiyayya Azuciyarsu
Kabiru Suna Tunanin in Suka Kauda Muhammed ya Zasuyi da Muktar Dansa na matarsa mai
Sauki ne.

Hassatu bata kara Haihuwa ba Sai da Muktar ya Shekara 15 aduniya Ta samu Cikin
*MUHAMMED BELLO* Wanda Ikon Allah ne da Kuma Rabo ya kawoshi Duniya Domin Har
mganin Hana Daukan Ciki Kabiru yake bama Karima tana Sanyama Hassatu Acikin Lemo
Tana Sha Sai dai Kuma Abunda Allah ya Riga ya yanke bawa bai isa ya Kauce musu ba.

Wannan karon ma A India Hassatu Ta sake Haihuwan Danta Namiji mai kama da
Mahaifinta Sak Shine Dalilin Dayaci Sunan *BELLO*,Haihuwan Data zoma Muhammed da
Sauye Sauyen Arziki dadama Acikin Rayuwarsa Haihuwarsa da Shekara Suka Tattara
Muhammed Zuwa Kasar Chicago Domin ya Hado Digree dinsa na Farko Tunda yana da
Kokari Sosai Shiyasa yagama Karatu Yana da Kananan Shekaru.

Akabar Bello Agidan


Shida Iyayensa Suna Cigaba da Kula Dashi Shima yana Shekara 4 aka Kaishi Nagerian
Turkish Acadmy,inda Aka kai Hashim Din Wajen Kabiru,Tun Bello na Karaminsa Kowa ya
Fahimci Sadauki ne ga Zuciya ga Riko ga Kuma Kulafuci ga Saurin Fushi,kuma
Iyayenshi na Matukar Sonshi kar ma Daada Taji lbri.

Lokacin da Muktar ya Dawo Nageria yana da Shekara 22 cif ya Hada Digree Dinshi na
Farko Dayake yana Sha"awar Aikin Soja sai Muhammed ya kaisa NDA Nageria Defency
Acadmy Domin karban Horan Sojoji Lokacin Shima Bello na jss1 misalin Dan Shekara 8
saboda kokarinsa ya saka akayitamai Jumping ,Kuma Sannan ne Haihuwa ta Budema Abba
Kabiru da Abba Garba Bayan Hashim yayi Kasim Wanda Tsakaninsu da Bello Wata goma
Sha Daya ne,,Sai kuma Wasu da Sukayi ta Mutuwa basa Tsayawa Dakyar ta Karshen Ta
Tsaya Zubaida sai Sahura matar Garba Keda Zulfa,Ummu salma,Hamdiya Duka mata Suna
Sun Taso Cikin Gata ne Sosai na Rayuwa Daga Dukiyar Muhammed Wanda baya kyashin yi
musu komai na Jin Dadin Rayuwa

Abunda yakara Bata Ran Abba Kabiru Shine Muhammed ya Dauki Hashim yakaishi
University Of lagos bai kaishi Kasar Waje ba Shiya kara Fito da Wutar Kiyayyah
Hakan Acikin Ranshi yana ganin Muhammed na Fifita matanshi da yayanshi Akan nasu
Matan da yayansu Batare da Sanin Kowa bq Sukayi Shawara Shida Garba Sukayi Hayan
Wani mutum ya K'wance Birkin Motar Muhammed Din Wanda Suka Shiga shida Hassatu Zuwa
Yola Lokacin Bello na Makranta Hakama Muktar yana NDA,Kuma Muhammed yaso Suyi
Tafiyan a Ajirgi Ammh Dayake Sun San Abunda Suka Shirya sai Suka Hanasa Tafiya
Ajirgi Garba ne dama mai Cukun Cukun Tiket din Tafiye Tafiyen Muhammed din nan
Yacemai babu Jirgi mai Zuwa Yola Dole Suka Tafi ,Amota Tunda Tafiyar ta Dole ne
Daada ce ba Lafiya Tafiyan da basu Dawo ba Kenan Har Abada sai dai Duka Iyalan
Sukaji Sakon Mutuwarsu nan Take.

Allahu Akbar.

*How to pay....�?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?600...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?500 ne,VIP
�?1000, Single one �?300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*Janafty..*a: *MR BELLO..!*


_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*🅿�?5*

"""Mutuwan Data Girgiza Zukata Gabadaya,Daga Muhammed Har Hassatu da Direbansu


Allah yayi Musu Rasuwa nan Take kuma da Abun yafaru kabiru Aka Kira Aka Fara
Sanarmawa..

Sun Nuna Alhininsu da Kuke kukensu na Rasuwar Muhammed Haka Mutanan Yola Suka Samu
Lbri tun kamar kar Daada Taji lbri Sai Jikinta yakara Rikicewa Shi Kuwa Muktar
Daga Kaduna Aka Daukosa Zuwa gida Harda Bello Wadanda Suka zo Suka Iska Mugun Lbrin
Rasuwar iyayensu Sunyi kuka kamar Ransu Zai Fita Domin Sun Shaku da iyayensu Sosai
Koda Dangin Hassatu Suka Nemi Sanin Komai game da Dukiyar Muhammed Sai Su Muhammed
Suka hada baki da Ma"aikatan Kamfononin Tare da Accountans Din kamfafonin Muhammed
marasa Tsoron Allah Domin alkarukan Makudan kudi su Abba kabiru suka yi musu
alkawari matukar suka goya musu baya
Su suka taimaka wajen Hada Jawabin Karya Wajen Cewa Kamfoninsu Biyu Sun Ci Bashin
Wani Kamfani Domin Farfado Dasu To yanzu Kudi Sun karu kan Kamfanonin kuma Babu
Riba ya Tabbata Kamfanin Daya Hada Hannun Jari Dasu zasu karbi Wadanan Kamfanonin
Guda Biyu Domin Biyan Kudin Da Sukayi Asara Hakan bai Isheshi su ba,Haka Suka Dinga
Kawo bayanan karya da Mahintan Ma"aikata Harda karya n Bashin Banki na Wajen
Miliyan Talatin da Biyar Dangin Hassatu Suna ji Suna gani bayani ya Tafi kan Duka
Dukiyan Muhammed Wai batashi Bane Sakamakon yana Da Hannayen Jari masu yawa kuma
basu kawo Riba ba Illah Binsa Bashi Da Sukeyi.

Muktar na gani Ammh bashi da Ikon Mgana Bello ne mai Zuciyan Shi Kuma yana
Karami ne Lokacin Sunaji Suna gani Abba Kabiru da Abba Garba Suka Hamdame Dukiyarsu
Daga Karshe sai Duka Kamfanonin mahaifinsu ya Dawo Tsakaninsu Shida Abba garba da
Sunan bayan Anyi Gwanjonsu Suka Siya Duniya ta Dawo Musu Sabuwa Hajiya Sahura da
Hajiya Karima ba Wacce bataje Makka da Ummura ba Suna ta Facaka da Kudin marayu su
da ya"yansu basu taba Tunanin cewa Cin hakkin da ba naka ba wani Nauyi ne wanda ko
bayan ranka sai ya tambayeka ba.

Muktar da Bello ko ba Wanda ya kara bi Takansu Domin Dangin Hassatu Na yola bayan
anyi bakwai Suka Koma,sunyi kokarin abasu yaran Hassatu su tafidasu wajen Daada
ammh Abba kabiru yace ba wannan mganar yara suna karatu bazasu lamunci katse musu
karatu ba,suka rabu akan su zasu rike yaran suna ta kukan karya Dana munafunci nan
ko mugun Nufi ne da Tsabar mugunta ke cin ransu kamar Abba kabiru yaji labari yafi
Abba garba Dora buri Bisa Dukiyar da bako zufanshi wajen Tarata.

Daada bata zo ba tana chan Babu Lafiya,Su da gidan ubansu Ammh Sun Rasa Dukkan
gata ba Wanda yayi Tunanin maidasu Makranta Shi Bello Bai koma Negrian Turkish
Academy ba Shi kuma Muktar ba"a Maidashi NDA ba Ammh Hashim Tuni Abba Kabiru ya
Turasa Kasar Spain yana Cigaba da Karatunsa.

Wahala Rayuwa da Matsi ba Wanda Basu gani ba,Acikin Gidan da Ubansu ya Gida da
guminsa ba,Abinci ko Sai dai indan Sun Rage,suna Rabe raben kankaran kanzo ko
ma"aikatan gidan sunfi suvgalihu da Daraja watarana ma sai wanda ma"aikatan suka
rage ne suke samu wani lokacin sai dai muktar yaci girma ya barma Bello,saboda
tsausayin kanin nashi Wani lokaci haka zasu zauna suyita kuka Bello yana ganin
dashi ne keda girma da Shekarun ya muktar wlh da su Abba garba sungane basu da
wayau sai dai kash shi Muktar yana Da sanyin Hali irin na mahaifinsa sam komai za"a
musu acikin gidan baya Daga kai Bello ne Wani lokacin ke Tubure musu,Tuni suka gano
yaron zai iya basu matsala wata rana suka Fara Tunanin yadda zasu maganinsa.

Abba Kabiru ma saboda Samun waje Shashen Mahaifinsu ya koma Shida Iyalanshi Kasim
dasu Zubaida Ana Ta Cin Duniya Da Tsinke Cikin Kwanciyar Hankali Muktar da Bello
Aboy Quaters Suka Koma Kwana Hatta da Masu bama Fulawa Ruwa Asallamesu Da masu
Wankin Motoci domin kaf motocin mahaifinsu Data Mahaifiyar suvdata muktar din Duka
ko Abunda ba"a so basu barsu dashi ba.

Bello da Muktar su suka koma wanke motoci da bama fulawowi ruwa wani Lokaci Bello
ke nuna Taurin kai Sai yaki yi Haka Abba Kabiru zai Ta Marinshi Ammah yakiyi,Yana
da Saurin Saka Abu Acikin Ranshi Shiyasa komai yakasa Bacemai Hajiya Sahura ko da
Hajiya Karima ba irin Wahalan da Basu ba su ba Kamar basu Taba Saninsu ba,Sunsha
lakaba ma ya muktar sata,Mussmman Bello da ya cika bakar Zuciya yafi muktar shan
wuya agidan Hatta da su Zubaida dake yara Suma Sun Iya Wulakanci Musamman ga Muktar
Wanda baya da Fada da Hayani Wani Lokacin bello ke kwatanshi Shiyasa Duk yafishi
shan Wahalansu, Cikin Shekaru uku Suka Chanza Kamanni Rayuwarsu Duk ta lalace Kamar
basu bane ya"yan Hutu ba Tuni Hashim ya Dawo ya Zama Saurayi dayake yana da girman
jiki Har yafara Aiki da Kamfanin da Abba Kabiru ya Hamdamai Wai Muktar ne ke
Budemai get in zai zai Fita Yau ya Hau Wannan Mota gobe ya Hau Wannan yana Cin
Duniyarsa da Tsinke

Basu da inda zasu je Ataimaka musu Dangin Babansu na Jikamshi Duk sun kare sai
D'aid'ai na nesa wadanda suma fama suke da kansu,kuma na nesan ma wadanda ke cikin
kauyuka,Malumfashi ma Sau Daya suka taba zuwa suma duk sun kare Dangin kakarsu ta
wajen Uba basu san kowa ba,sai Dangin mamarsu na yola sai kuwa su Abba kabiru.

Kwatsam Sai ga Daada ta Diro Gidan Halin Data Tarar da Jikokinta Sai da ya sakata
Kuka Ta Dingama Su Abba Kabiru Allah ya Isa Ba Kunya ba Tsoron Allah Sukace Allah
ya isa ya Bita Dukiya ne suncinye In zata Kwatan musu ne Bismillanta Daada bata
Damu ba ko Kwana Batayi ba Tattaro Muktar da Bello ta Taho Dasu Gidan yayanta Baffa
Hadi,Daman bayan Rasuwar Mahaifin Hassatu Wajensa Take Zaune Ta karantamai Duk
Abunda yafaru nan Take ya karbi su Muktar kuma yayi Alkawarin Rikesu Amana su kuma
Su Abba Kabiru yace zai makasu kotu Daada ta hana tace ya kyalesu duk wanda yaci
hakkin maraya sai Allah ya tambayeshi Badai cin Hakkin Maraya ba Zasu girbi Abunda
Suka Shuka ne.

Ya Maida Muktar Kaduna NDA Dole ya Dawo baya a karatunsa domin tuni yan batch
dinsu sun dade da gamawa bai damu ba ya Cigaba da karban Horaswan Sojoji Shi kuma
Bello ya Sanyashi Wata Makranta ta masu Hali Ya Dora Daga SS1 duk Abunda ya Faru
bai bacema Bello ba ya Rikeshi Sosai Acikin Kanshi yakuma Ji Duk Duniya babu Wanda
Ya Tsana kamar Su Abba Kabiru da Iyalansu,Shiyasa Ko Alama baijin Zai iya Hada
hanya ko Wata Mu"amalan Arziki dasu har gaban Abada.

Lokacin Daya kamallah Secondry Sch Dinsa ya Tafi University of Ibadan Shikuma
Muktar yagama Short Service dinsa ya Fito Amatsauyin Second Leutanant,Yana Aiki A
barikin Jaji Dake Kaduna,Bello Dama Tun yana Karaminsa yake da Burin ya Zama
malamin Makranta Yasha Fadama Daada Haka da Muktar Ammh Sai basu Daukan Abun da
Muhimmci,Mathematics yake Karanta sai inda sun Samu Hutu yake Zuwa Gida.

Yana Kara Girma Duka Murdadun Halayansa Suna Kara Bayyana Koda da Rana Daya Bello
bai Manta da Abunda Su Abba Kabiru Suka Aikata Garesu ba Ayayinda Shi Muktar Yake
da Saukakkiyar Zuciya Tuni Abun ya Fitar Mishi Arai bai kuma Rikeshi Ba Sabanin
Bello Wanda Ta Kowani bangare Suna da Bambancin Ra"ayi.

Lokacin daya Kammallah First Digree Dinsa ne,Yatafi Makrantar GGUSS KWATAR KWASHI
yayi musu Bautar Kasa Ko Alokacin Muktar yaso ya Hanashi Ammh Ya Nuna Shifa Abunda
yake Ra"ayi kenan Lokacin Har Muktar yakai Matsauyin Captain ne yana Aiki a Barikin
1 Division Barrak Dake Kaduna.

Bello yaji Dadin Bautar Kasar Daya Gudanar A Makrantan Kwana ta Kwatar
kwashi,Wanda Suma Makranta Taji Dadin Zuwanshi Tunda dama suna da Karancin Malamin
Lissafi Tun Alokacin Bello yayi yaki da Mata Sosai Saboda Yadda ya Tara komai na
Cikar Zatin Da Namiji bai maida kai ba Tunda Kowa yasan Muhammed Bello Jikamshi
bashi da Wasa ko kadan.

Batare da Saninshi ba yayanshi Muktar da Baffa Hadi Suka samarmai Wata Makranta a
Babban Birnin America Wato U.S inda yaje ya Hado Masters Dinshi Akan Mathematics.

Rayuwa tayi ta tafiya yarda Allah ya Tsara Muktar na Aiki yana Kara Samun Girma
Awajen Aiki,har yakai Matsayin Cononel Lokacin ne kuma Bello yadawo Daga America
bayan ya Hado Masters Dinsa yana Da Shekara 26aduniya Shi kuma Muktar nada 40
alokacin kuma Baiyi Aure ba akuma Lokacin ne Su Abba Kabiru Suka Nemesu bayan Duka
Dukiyar da Suka Hamdemai Ta Gudu Ta barsu Dama Hakkin Maraya bazai Taba Zama ba.

Har yola Suka tako Duka Suda iyalansu Suna Kuka Suna Rokonsu Muktar gafara
Sakamakom Sunga Bala"i kala kala Gashi komai na Dukiyar baya Cigaba ga Mugayen
Mafarkai da Kuma Rabuwar kai Tsakaninshi da Abba garba Matayen Suma sai Cin Juna,da
Fada Hakama ya"yansu basa zaman lafiya,Saboda Dukiya wacce kwata kwata batayi
albarka ba Sauran kamfanonin ma Tuni sukayi gwanjensu saboda ba ma"aikata kowa ya
gudu tunda babu albashi ba hannayen jari ba kuma ba Shugaban kwarai kafin kace
kwabo komai Da suka Hamdame ya fara gudu ya barsu kamar kudaden suna kamawa da Huta
gidaje da Filaye dama Tuni shi da Abba garba suka raba kowa yaja rabonsa suma basu
kai labari ba saboda yadda suka sakarma matansu da ya"yansu Ragamar komai suna cin
karensu ba Babba Da Dukiyar ta fara salwanta Kusan mugunta Fitsarin Fako ne sai
suka fara Zargin junansu da cewa cikinsu ne wani ya sakama Dan"uwansa Hannu komai
ya lalace shine Dalilin Rabuwan kansu Dana ya"yansu domin Daga Sahura har Karima
kowa tabi bayan mijinta da ya"yanta.

Suna Kuka Suna Sanar Dasu Abunda Suka Aikata ga Muhammed da Matarsa Hassatu, da
Muktar da Daada ne Keta Kuka Basu da Abun Cewa Domin ko haka aka Tsaya Sunga
isharansu nan da nan Sukace Zasu Mika Sauran Dukiyan ga Muktar da Bello Shi kuma
yace Su Rike kawai Sun bar musu Duk da bai Shawarci bello ba yafi kowa sanin Bazai
Taba Karba ba,Shiko Bello Suna Zuwa Gidan ya Fita bai kuma Dawo ba Har Suka Tafi
Abun yamishi Ciwo yadda yaga Muktar bai Damu ba har yana Sakar Musu Fuska Lokacin
Su Zubaida da Zulfa Duk Sun zama yan Mata Kowacce na SS2 alokacin Ummu salma kuma
Da Hamdiya Suna Wajen Inna Rukayya Dake Kano Hashim Kuma yayi Aure Har ya Haihu Sai
Kasim dake Jami"a Alokacin sunji matukar mamaki da Muktar yace sun bar musu Duka
Dukiyan Daya rage ahannunsu,Dama suna tunanin taya rayuwarsu zata kare in suka
karbi komai tunda hatta hashim yanzu zaune yake baya aikin komai Tunda Duka
kamfononin sun sanyasu akasuwa sun karbi yan kudadansu.

Muktar baiyi Aure ba Sai da ya keda Mukamin Major Shekarunsa Lokacin 44 aduniya
Kana yayi Aure da Matarshi yar Garin Borno Kanuri ce gaba Da baya Mai Suna Rahila
Wacce Suka Hadu Lokacin Daya Jagoranci Wata bataliya Zuwa Maiduguri.

Bayan Aurensu ba Dadewa Ya Dauko Matarsa Daga Yola Zuwa Abuja Inda yake aiki a
Abacha barrak,Shi kuma Bello ya koma Makrantan kwana ta Kwatar-kwashi Yana Koyarwa
Wanda Muktar da Daada Sun yi Sunyi Ammh ya Kafe yace Shi zaiyi Hatta Jami'ar Dayayi
Ta University of Ibadan Suna Nemanshi Su bashi lecturing Ammh yaki Dole Suka
Sanyamai Ido Tunda Haka Allah yayi Shi da Taurin Kan Tsiya.

****

"" *ANEESA BUKAR BULAMA* Shine Cikakken Sunan Aneesa Kuma Itadin kanwa Take ga Anty
Rahila matar Muktar,Ubansu Daya Uwa Kowa da Tashi.

Sun Fito daga Tsatson Yaren Kanuri na Garin Bornon Maiduguri Kanuri ne na Gaba da
baya Irin bakaken nan masu Kyau da Tsari,Suna Zaune a Unguwar Damboa Road.

Ahaji Bukar Bulama Shine Mahaifinsu Wanda ya Kasance yana Da Rufin Asiri Daidai
Gwargwado Tunda Dan Siyasa ne Sosai yana da Matan Aure Biyu Wato *Mama Yana* sai *
Mama Falmata* wacce Itace Mahaifiyar Aneesa.

Su Bakwai ne agidansu Mama yana Keda ya"ya Bakwai Falmata Sai Daga baya Aka
Aurota ,Babban Gidan Shine Yaya Ali,Sai ya Sunusi,sai Anty Nafi,Sai Anty
Yagana,Anty Rahila sai Anty Aisha,Sai ni Aneesa Auta, Falmata Tafi Shekara goma
bata samu Haihuwa ba sai Akan Aneesa,Wacce Tun bayan Haihuwata na Taso Agidanmu
Cikin gata Sosai Daga Duka bangoririn iyaye na Aneesa yarinya ce mai Shiga Rai Gata
Auta Wannan Dalilin ne Alhaji Bukar Bulama ya Sangartata Sosai Duk Abunda Takeso
Shi yake mata.

Aneesa Tataso Tun Tana Karamarta da Tsiwa ga Rashin Kunya da Rashin Tsoro Ko
Falmata datake Mahaifiyarta Bata Isa ta Daketa ba yanzu Alhaji Bukar Bulama zai
Fara Fadanshi na Fama Kan Aneesa Ko Kukanta bayaso yanzu Ran Kowa Zai baci,Wannan
Dalilin ne ya Sanya Aneesa Tataso Cikin Gatan Sangarta Ko yayyinta su Anty Nafi Ba
Wanda ya Isa yaga Tana Abu yayi mgana Yanzu Zata Saka Kuka In ko Alhaji Bukar
Bulama yaji Kukan Aneesa ka Shiga Uku..

Saboda Son Daya ke mata da Kuma Sangarta ta Dayayi ko Ina Zashi Tun Tana karamarta
Tare yake Zuwa da Ita Koda Taronsu na Siyasa ne Shiyasa Duk Wanda Ke Tare da Alhaji
Bukar Bulama yasan Wacece Shalele yar Auta,Tun Tana karamarta Har Zuwa Lokacin Data
isa Zuwa Mkranta da Alhaji Bulama yayi Kokarin Saka Aneesa Amakranta Sai Rigimarta
ya Tashi Kullum Da Dambe Ake Shiga da ita Makranta Su yaya Ali ne ke Kaita Watarana
Sai Sun Hadamata da Duka Kuma Haka za"a Daukota Tana Kuka Batama Tsayawa ta Fahimci
karatun Hakama Islamiya bata Zuwa Duk ko Ranar da Aka Matsamata Haka zata Wuni Kuka
Har Alhaji Bukar ya Dawo Kuma In ya Shigo yaji Kukanta Ran Kowa sai ya baci Agidan
Manya da yara.

Ganin Haka yasa yace akyaleta Tunda batason Karatun yarinta Ke Damunta in takara
Girma Zatayi Haka ko Akayi Dakyar Aneesa Ta Kamallah Primary 2 Shima ba Kullum Take
Zuwa ba Sai yan Rigimarta Basu Kusa,Yaya Sunusi da Yaya Ali Dukkansu Sun kamallah
Karatunsu yaya Ali Ma"aikacin banki ne Shi kuma Yaya Sunusi yana Aiki A Hukumar Man
Fetur ne Wato NNPC,Anty Nafi Tayi Aure acikin Garin Maiduguri Yayinda Anty yagana
Tayi Aure Agarin Ibadan,Suma ba Wacce Batayi karatu ba,Aneesa ce Ta Bambanta Domin
In Tana Kaunar Mutuwarta tana Kaunar Karatu.

Mama falmata ba yadda batayi ba Tayi Lallashin Tayi Fadan Harda Dukan Ammh Abanza
Aneesa Taki Karatu Sam,Shikuma Alhaji Bukar baya som Matsamata Wani Lokacin Sai
yayi Tafiya ne Su Yaya Ali ne zasu Dauketa Sukaita bayan sun Mata Dukan Tsiya Tun
Barema Yaya Ali Sarkin Fushi Da Zuciya ganin Aneesa na Cin Wuya sai ta Hakura tana
Zuwa Makrantan Ammh bawai Don Tana maida Hankali ba Da Kuka Take Zuwa Kuma Da Kuka
Take Dawowa babu Abunda Ta sani sai Rashin Kunya da Tsiwa Domin Karya ne Taje
Makranta Atashi bata Daki yara Goma ba Muguwa ce ta Sosai.

Rana Daya Akayi Auren Yaya Ali dana yaya Sunusi Dukkansu Kanuri yan"uwansu Suka
Aura Matar Yaya Ali Khadija Ita kuma matar yaya Sunusi Sadiya Sunanta Dukkansu Anan
Cikin Gidan Alhaji Bukar Bulama Suke Zaune Saboda Katon Gida ne,Aurensu ba Dadewa
Akayi Auren Anty Rahila da Muktar Anty Aisha kuma Tana Auren Wani Sojan Ruwa a kano
Rana Daya Akayi Bikinsu Gida ya Rage Daga iyayensu sai Auta Aneesa,Wacce Dakyar da
Sodin Goshi ta samu Ta gama primary Daga Nan Alhaji Bukar yace Akyaleta Domin Hatta
Makrantan Kwana sai da ya Ali ya samoma Aneesa Ammh Alhaji Bukar ya Hana Dole Suka
Sakamata Ido Tana Abunda Tagama Dama Sune kadai batama Rashin Kunya Tasan Halinsu
yanzu Zata ci na Jaki ammh matansu Kuwa Duk Ta Ranmusu kuma basu da Cewa don yanzu
sai Alhaji Bukar yaci Mutumcinka kan Aneesa Saboda Yadda bayason Wani yatabamai
Ita.

Aneesa Tanada Shekara Goma Sha uku Aduniya Allah ya Karbi Ran Alhaji Bukar Bulama
Mutuwar Data Girgiza kowa Musamman ma iyalanshi,Wanda ya Kwanta lafiya lau sai
Tashi Akayi Rai yayi Halinsa ba Wanda yafi Gigita da Mutuwanan Irin Aneesa Domin
Sun Dade Suna Hira Dashi kafin Tatafi Daki Ta Kwanta sai dai Wayan gari Sukayi da
Mutuwa Wayyo Rayuwa Aneesa Sai da Tayi Awa Uku Asume kafin Ta Farfado Koda ta
Farfado Har An sallaci Alhaji Bukar Bulama Zuwa gidansa na gaskiya sai da Ta Iske
Su Anty yagana dasu Anty Rahila Sunzo Anata Kuka Gida ya Cika da Jama"a.

Aneesa ta tabbatar tayi Maraici Domin ko bakwai din Alhaji Bulama Ba"ayi ba Tafara
cin Ubanta Domin Adane za"a mata mgana tana Gardama yanzu Kuwa Duk Wanda yamata
Mgana Ta Tsaya Wani Iskanci Sai dai Taji Duka Hatta da mama Falmata Bata ta
Ragamata Tunda Daman Ta Dade Tana Tusama Mutane Haushi da Sangartanta,Bayan
Rasuwarshi Aneesa Ta Tsiri Sangarta kala kala na Ta Wuni tana Kuka batacin Abinci
Ko Mgana Aka mata sai Ta Hau Ihu Tana Kuka Tana Birgima Tana Kiran Sunan Alhaji
Bukar Bulama ganin Haka ya sanya Yaya Ali ya Sanyata Adaki yamata Dukan Tsiya
Wannan Shine Dalilin Daina ma Mutane Kukan Banza da Aneesa Tayi

Sai Abu na gaba Mganar Makranta tun bayan Rasuwar Yaya Ali ya maidata Makrantar
Islamiya Ammh Aneesa bata Zuwa In ta Fita Gida sai Ta tafi Wata Primary Gwannati
Tayi ta Wasanta Har Atashi gida Batasan Yaya Ali na Zuwa Makrantan Dubata ba Ranar
Daya gane bata Zuwa Sai da ya barta kwance Da Duka ya gama Nashi mama Falmata ta
Kara mata Mama yana ce ma Ke Amsanta Wani Lokacin Ammh Duk da Haka Aneesa batajin
Mgana In Lokacin Islamiya yayi sai Anemata Araasa Ta Gudu Su Yaya Ali Sunyi Dukan
Ammh Duk Abanza Sai Suka Zauna Shida Yaya Sunusi Suka kawo Shawaran Barin Aneesa da
garin Borno Gabadaya Kila Awani Wajen Ta zama yarinyar Kirki Tayi karatu.

Haka ko akayi Haihuwan Matar Yaya Ali na Biyu Duka Su Anty Nafi Suka zo Toh Awannan
Zuwan ne Yaya Ali ya bama Anty Yagana ni Tatafi Dani chan Ibadan Da Niyyar ta
Sanyani Amakranta Da Farko Bataso Tafiya Dani ba Ammh Sai Yaya Ali yace Dole Tatafi
Dani,Aneesa bata san da Zencen Tafiya ba sai Ranar da Zasu Tafi Aiko Sai da Yaya
Ali da ya Sunusi Suka Hada Karfi Wajen Sakata Cikin Mota Haka Take Kuka Tana Kiran
Sunan Alhaji Bukar Bulama kamar Wacce za"a Tafi da Ita Inda bata sani ba.

Anty Yagana Tayi Nadamar Tafiya da Aneesa Yafi Cikin Kwando Domin Koda Suka Isa
Ibadan Aneesa Kin Shiga Gidan Anty Yagana Tayi ta Coge bakin Get Tana Ihu Tana Kuka
Tun Tana Lallashinta Harda Karshe Tabata Haushi Tabarta nan Tayi Shigewarta Cikin
Gida Aneesa nan Ta Zauna tana Kuka harda Majina Har Mijin Anty Yagana ya Dawo
Ganinta Awaje yasa yagano Bakin Zaren Wanda Dama Tun Da Suka Iso Anty Yaganar Ta
Mishi Waya ta Sanar Dashi Dakyar da Sidin Goshi ya lallasheta ta Shigo gidan Yan
aikin Anty yagana na mata sannu da zuwa ko kallo basu isheta ba,Dayake Tunda Anty
yagana tayi Aure Allah bai taba bata haihuwa ba.

Kwana Tayi kuka da Gunjin Tana Fadin Ita Akaita gida Tun Anty Yagana na Kallonta da
Takaichi Hartafara Saka mata Hannu Da Zaran Tafara mata Wannan Kukan Banza Cikin
Wannan Halin Aka samar mata Makranta,Ranar ko Da Anty Yagana Da Mijinta Suka kai
Aneesa Makranta Sunga Tijara Domin Cikin Mota ta Coge Tana Kuka da Ihun Ita bazata
Shiga ba Ba Lallashin Duniyan da Mijin Anty yagana bai mata ba Ammh Aneesa bata
Saurareshi ba Karshenta Shida Security,Suka Shiga Da Ita Office din Principal din
Mkranrta Abun Kunya Aneesa Tana Birgima Akasa Tana Kuka Saboda An Kawo ta Makranta
Tun Alokacin Anty Yagana ta Zargi Cewa Aneesa ba Ita Kadai bane tana da Aljanu.

Direba Ke Kaita Makranta yaje ya Daukota,Ammh Kullum da Kuka Take Tafiya Domin ya
Ali Har Ibadan yazo yamata Duka Sai da ya mata Targade,Shine Dalilin Daya Sanya
Take Zuwa Mkrantan Jss1 wanda Kullum sai an kai Sunanta Office din Principal Tasaka
sargent ya mata dukan tsiya saboda rashin jinta da kuma zaluncin yara wadanda tafi
karfi.

Kullun da Case din Da Aneesa Ke Jawowa a cikin makarantar hukumar Makaranta gaji
Suka Kira Mijin Anty yagana Suka Sanar Dashi Suka Kuma Bama Aneesan Suspention Abun
yayima Anty yagana Ciwo Har Itama ta Saka Aneesan Daki Tayi Ta Dukanta,cike da
takaichi Wannan Dalilin Shi ya Sanya Aneesa Ta Hada kayanta Tsab ta Gudu Daga Gidan
Anty yagana Dakyar da Sodin Goshi Aka ganta bayan An Wuni Ana Nemanta Sai Daga Baya
Aka ganta Atashan Mota Ai Washegari nayi Suka Sakata Amota da kayanta sai Borno
Anty Yagana Ta Dawo Da Ita tace Bazata iya ba.

Abun yana Damun mama Falmata Ammh Aneesa Ko Ajikinta Dadima Takeji Ta Dawo Wannan
Abun yabatama ya Ali rai Sosai Batare da Shawara da Kowa ba Ya Dauketa ya kaita
Maiduguri Wajen Anty Nafi,Wanda Ko Sati Daya Aneesa Batayi ba Ta Gudo ta dawo
gida,ba Saboda Komai sai Mugunta Anty Nafi bata da Kirki ga Saka Aiki ga Mugunta
Tayi ta Dukanta Kwatam Rana Tsaka sai ga Aneesa Ta Gudo Daga Maiduguri Zuwa Borno
Abunda ya Hasala Yaya Ali ya sata Daki yana ta Duka,gashi bata jin duka domin da
tanaji da tuni Aneesa ta natsu ta dawo mutum kamar kowa ammh ina dukan ma kamar
kara famdarar da ita yake,kwata kwata bata tsoro ko kadan,wani lokacin ne ma take
jin tsoron ya Ali ya sunusi kuwa tagama Raina kurarsa dama tuni

ya Ali na cikin mata fada yana Kai mata Duka sak Allah ya Kawo Muktar Dashi da
Anty Rahila gidan Suka Tarar da Aneesa na Cin Ubanta Hannu yaya Ali kowa na gani
kuma ba Wanda ya Ceceta Saboda Tafara Isar Kowa da Hallayarta.

Lokacin Ko Wata Biyu Ba"ayi ba da Gwannatin Nageria ta Zana Sunanshi Amatsayin


Chief Amry Of Staff Na Kasa baki Daya bayan Duka Mukaman Daya Taka da
Gwagwamarya,Har Sun koma Katon Gidansu Dake Garki Abuja ya Kuma Dauko Daada Daga
Yola Tunda Shekaru Biyu Kenan da Rasuwar Baffa Hadi

Muktar Shi ya Kwaceta Hannun ya Ali Aneesa na Kuka da Majina Ta Lafe Jikin Muktar
Tana Raba Ido Shiko Yaya Ali Haka yake Fada yana labartama Su Anty Rahila Abunda
Aneesan Tayi Jin Haka yasa Muktar yace Zai Tafi da Aneesa Abuja Kuma Insha Allahu
ya Tabbatar da Cewa Zan Zauna Kuma Zanyi karatu.

Abunda yabama Kowa Mamaki yadda Aneesa batayi Tijaran Data saba ba indai za"a kaita
wani waje ba, Sai dai Har Muka Isa Abuja Ina Kuka Harda Shessheka bakomai ke Sata
kuka ba sai In Ta Tuna Zencen Makranta Shike Kara Sakata Kuka,Aneesa Bata taba
Zaton Akwai Wanda yafi Karfin Iskancinta ba Sai da Anty Rahila tatafi da Ita Abuja
Chan Mafarin Haduwarta da *MR BELLO* the young Teacher Wanda yayi Rugu Rugu da
Aljaninta,na Rashin Son Makaranta ya kuma ya Dauketa yayi Nisa da Ita da Kowa
Nata,ko ahaka aka bar Bello yaci Babbar Nasara wajen inganta rayuwar Aneesa
amatsayinta na ya mace.

*How to pay....�?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?600...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?500 ne,VIP
�?1000, Single one �?300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*Anitha..*
8/19/20, 8:01 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*🅿�?6*

"Farkon Dawowar Aneesa Hannun Anty Rahila bata Saki Jikinta ba Sosai, Ammh Kuma
Hankalinta ya Kwanta da Gidan Anty Rahilar da Mijinta Harma Da Daada Wacce Take
Kaunar Aneesa Har Cikin Ranta Shiyasa ma Shashen Daaada Aneesa Take zaune Tun bata
Sakin Jiki Har Tazo Tana Sakin Jiki da Daada Babu Abunda Aneesa Keyi Daga Wanka sai
Cin Abinci Sai Kallo Akwai masu aiki Biyu Musulmai Biyu kuma Kabila biyu,Larai da
Jumai,sai alheri da Rabeca.

Lokacin da Aneesa Tadawo Gidan Anty Rahila da Zama Muhammed Bello bayanan yana
Chan Makranta So basu Hadu ba,Sai da Akayi Hutu ya Dawo Gida,karon Farko da Aneesa
da Bello Suka Hadu ba Haduwan Dadi bane Domin Ranar Daya Dawo Anty Rahila batanan
Tatafi Asibiti Awo Lokacin Tana da Cikin Hibba Shikuma Muktar yana Vila yaje Suna
da Tattauna da Shugaban Kasa,Daada kuma tana Shashenta Aneesan Ke Zaune Falon Anty
Rahila tana kallo Hankalinta Kwance Tunda ba Wanda ya Mata Zencen Makranta....

Shikuma yana Dawowa ya Shigo Bangaren Anty Rahilan nan ya Ganta Zaune da Farko ma
ya Zata yar Aiki ce Dat Why bai Damu ba sai ma Tsawa Daya Dakamata yace Ta Daukomai
Ruwa,Itako Aneeesa Dama ga Rashin Kunya da Tsiwa mikewa Tayi tana mai Kallon Sama
da kasa Kafin Tayi Tsaki Ta Juya zata Tafi Da Wani Irin Zuciya ya Damkota Ya
Fizgota ya Dauketa da Maruka lafiyayyu Guda Biyu Wanda Sai da Aneesa Ta Zauna Kasa
Saboda yadda Marukan Suka Gigitata

Kan Cafet din Dakin Ta kwanta tana Kuka Tana Ihu Hawaye na Zubar mata tana Kiran
Sunan Babanta,Tsayawa kawai Bello yayi yana kallonta Cikin Ranshi Kamar yayi
Bindiga Saboda Haushi Kafin yayi mgana sai ga Anty Rahila Tashigo Gidan Ganin
Aneesa Akasa Tana,kuka Ga Bello Tsaye tasan Karon ba Dadi kafin ma Tayi mgana
Aneesa Ta Mike Tana Sharban Kuka Ta Shige Shashen Daada Tunkafin Bello ya Tambaya
Anty Rahila tace mai kanwarta ne Daga Borno Suka Daukota Ita da Muktar.

Jin Haka yasa bai ba mganarta Muhimmaci ba Ammh Cikin Ranshi yana Tunanin Rashin
Kunyar Aneesa,Ficewa yayi daga Sashensa Ita ko Aneesa Kayanta Tashiga Hadawa Tana
Kuka Wai Ita Zata Tafi Abun mamaki Har Wajen Haraban Gidan Daada Ta Biyo Aneesa
Tana lallashinta,Itako Anty Rahila Abun ya bata Haushi Dama Anty Nafi Ta Kirata
tana Bata Shawaran Tun Wurima Ta Dawo da Aneesan Domin bazata iya zama da Ita
ba,Mganar gaskiya Taji Haushin yadda Aneesa Ta Gudu Daga Gidanta.

Yana Daga Saman Shashenshi yana Hango Diramar Aneesa Bata Yadda Ta Koma Cikin
Gida ba sai da Muktar ya Dawo ya Lallasheta kana,Bello Ko Acikin Ranshi Tsanar
Aneesa ce Ta kamashi Yana ganin Duk Rashin Dukane yasa Takema Mutane Kukan
Iskanci,Aiko Ranar Kwana Tayi Kuka Da Rigima kamar Wata Karamar yarinya Washegarima
Asheshen Daada Suka Hadu sai da ya Bata Rankwashi Ya murdemata Kunni Wai bata
gaisheshi ba,Daada na mai mgana Ammh Sai da ya Karisa Mangare mata kai kuma yace In
Ta Sake Tamai kuka Sai na Lahira yafita Jin Dadi.

Aneesa Duk Iskancinta Sai da Ta Natsu saboda Bello ya Wuce Duk Tunaninta Duk iya
yadda Takai ga Tsiwa da rashin Kunya sai ta gagara yimai Sai da ta dai Ta Dinga
Kunkuni Tana Fadin Allah ya Isarmata Ashe yajita Ranar Kuwa Kamar Aneesa Zata Mutu
Saboda Kuka Harda Majina Domin Kneel Down ya Sakata Ya Dankwashi kanta Sosai Daga
Karshe ya sata Up and Down,Haka su Anty Rahila Suka Shigo Suka Samesu Shashen Daada
Wacce Tayi ma Bello mgana kan ya kyale Aneesa yafi Akirga yayi banza Da Ita.

Ya muktar Shi ya Kwaceta Hannun Bello,Wanda Tundaga Lokacin Aneesa Ta sanyamai Suna
Mugu,Batasan Cewa Akwai Wata Muguntar na Zuwa ba,Domin Ranar da yaji Ya Muktar da
Anty Rahila na Zencen Halayyar Aneesa Sai yake Tambayan ya Muktar Nan yake gayamai
Dalilin Taho da Aneesa da sukayi Mirmishin Mugunta yayi yace Karsu damu Su bashi
nan da Sati Uku Aneesa Zata Tafi Makranta Kuma Dole Zatayi karatu,Sanin Halin Bello
na Rashin Son Wasa ne ya sanya Muktar ya bashi Dukkan Dama akan Aneesa Wacce
batasan Wainar da Ake Toyawa ba Domin Ta Kulle Duk Wata Kofar da zai Hadata Da
Bello Saboda Taga alamun Shi Din ya Girmi Iskancinta.

Shiko Bello Tunda yaji lbrin Irin Iskancin Aneesa yasan Ba Inda Za"ayi mganinta sai
Bording Sch,Nan ne za'a goge mata Duka Iskancinta da Aljanun Rashin Karatun Nata
Haka ko Akayi Ta Waya Sukayi mgana da Prinpcipal din Makrantar Ya Sanar da Ita
Komai kafin Sati Biyu Duka Shiryen Shiryen Komai na Tafiyan Aneesa ya kamallah Ta
samu Gurbin Shiga Jss1 a mkrantar GGUSS kwatar kwashi,Amtsayin Sabuwar Daliba Da
Sun Koma hutu,Ko su Ya Muktar basu sani ba sai da yarage Saura kwana Uku Hutun
Makrantan ya kare kana ya Sanar Dasu Abunda ya yanke Anty Rahila Taji Dadi Ammh Sai
Ta Nuna Fargaban Aneesan.

Ganin Haka yasa Bello da kanshi yace tayi kitso ta gyara kanta Domin Jibi Zata Tafi
Makrantar Kwana Wannan Lbrin ya Kusa Zautar da Aneesa Haka ta Baje Akasa Tana
Gunjin Kuka bai Dauki Abun Serious ba sai da ya Dawo da Yammah ya Isketa nan Tsakar
Falon Daada Tana Cigaba da Gunjin Kuka,Already Jakar mkranta da littafanta da
Takalmin Makranta sai Akwatinta Trolley da Sauran kayan provision Sun Kammallah
ganin Abun nata bana Karewa bane,Yasa ya Zare mata Ido ya Ciro belt yafara Zubamata
Daada ce ta Hanashi Dole ya kyaleta.
Aneesa Kuwa Ta Kwana Kuka Tatashi Tanayi Haka take Birgima tana Kuka ganin Haka
yasa Anty Rahila ta Kira yaya Ali ta Sanar Dashi baice mata gashi zuwa ba sai ana
gobe Ranar Tafiyansu Aneesa sai gashi ya Iso Ranar Sai da Daada ta Kwaceta Domin
Dukan Tsiya Yaya Ali yayi ma Aneesa sai da ya Barta Kwance ya Kuma Ja mata Kunnin
In bata Tsaya Tayi karatu ba Wlh Har mkranta zai bita yaci Ubanta ko kwana baiyi ba
ya Juya zuwa Borno bayan ya Jadaddama Bello ko Amkrantan Karya sake yama Aneesa Da
Wasa Yarin ka Cin Ubanta,Ranar Kowa ya Tsausayama Aneesa banda Bello Wanda yaji
Dadin Hakan Sosai ko Banza Ta Rage iskanci da Rashin Kunya baison Duka baya
ladabtar da Aneesa ba.

Washegari Kuwa Da Duku Duku Direbansu mallam Inuwa ya Daukesu Ita da Bello Sai
Kwatar kwashi Ita da Kayanta Da Zata Tafi Haka ta Rumgume Daada Tana Kuka Hakama
Anty Rahila Su kansu Sunji Kewa Sosai Daada kamar tace abar karatun Saboda yadda
Aneesan ke kuka kamar Ranta Zai Fita,Aneesa bata ta Zaton Zata Dandani Azaban data
Dandana A mkrantan GGUSS kwatar Kwashi ba.

Ranar da Sukaje,Kwana Biyu ne da Dawowa Hutu,Dalibai Duk Basu Dawo ba Su kansu


Sabbin Daliban Jss1 din Basu Wuce su Goma ba,Office din principal Suka Fara Isa
yamata Sauran Cike Cike Aka bata Uniform da Hostel Maryam Hostel,Aneesa Kuka Takeyi
Wurjajan kamar Wacce Aka yanka Tunda Taga Dajin Allah da Bello ya kawota Wai da
Sunan Mkranta babban Abunda yafi Daga mata Hankalin Dutsen nan Na Kwatar kwashi Ya
Firgita Aneesa Duk sai Taji Duk Wani Hayakin kanta ya Saketa Saboda Fargaba da
Tsoro Zuwan Farko Suka Fara Haduwa da Jidda Ita kuma New Student ce SS1 inda Bello
ya Kirata yace ta Dauki kayan Aneesa Zuwa Maryam Hostel Dogon Daki.

Jidda Ta kaita Har Hostel dinsu Inda Ta Dinga Tambayanta ita kanwar Mr.Bello ne,Ko
kallonta Aneesa batayi ba banda Kuka Babu Abunda Takeyi,Ganin Haka sai Jidda bata
damu ba Azatonta Irin Farkon Zuwan nan ne na kowani Dalibi Haka kowa yake yi sai
yayi Kukan Rabuwa da Gida For d First Time Jidda Ta Hadasu da *SALAMATU S JIBIYA*
Wacce Suke Gado Daya da Aneesa Ita tana sama Ita Kuma Kasa Kuma Itama Jiya Aka
kawota nan Ta Hadasu kafin Ta Fice Zuwa nasu Hostel dinsu Tana Jin Dadin An kawo
Kanwar Mr.Bello domin Tunda tazo Mkrantan Ta kyalla Ido Akanshi Taji ya Tafi da
Imaninta..

S.jibiya Ita ta Jerama Aneesa kayanta Cikin Dirowar gadonsu Ammh Duk da Haka Aneesa
bata Amsa mata Ko Daya Daga Cikin tambayoyin Data ke mata ba, Ko Sunata Dakyar ta
Iya Sanar da Ita Aneesa Tsoro Duk ya kamata ganin Mabambatan Mutane Kuma Hostel din
nasu guda Biyu ne Dogon Daki nasu na Musulmai gajeran Daki kuma na Kabila ne,komai
Dai gashinan Yamata Wani Iri Tundaga Check din da Suke Sakawa Cikin Hostel,su nasu
na House dinsu Ita da S. Jibiya Red Colour ne,Daddare Haka S Jibiya ta Tarata Suka
Tafi Suka karbo Dinner Dare Tuwo miyar Kuka Ranar Aneesa Sai Da Tayi Kuka Tana
Tunanin Kila Bello ya Kawota inda Za"a Kasheta lokacinta baiyi ba bata iya ci ba
S.Jibiya ta Hada musu Complex Suka Sha Suka Kwanta bayan,ko Masallacin basuje ba a
hostel sukayi Sallar, Domin Aneesa Tace Tsoro Takeji,Haka Ta Kwana Batayi barci ba
Saboda Tsoro Dutsen na kwatar kwashi Take gani Yana ci Da Wuta.

Washegari Suka Fara Zuwa Aji Ita da S.Jibiya,sai 10 Suka Tashi Breafsat suka Koma
Duk Da Haka Aneesa bata Saki Jiki ba Sosai Shiko Mr.Bello Saboda Aneesa aka
maidoshi Master din Jss1a Domin ya Dinga Lura da Ita da Karatunsa Ammh Duka
Makrantan Yake koyar Dasu Darasin Lissafin,Kwanan Aneesa Uku da Zuwa Aka kawo
*BILKISU KABIR KAITA* ita kuma Hostel dinsu Daya Kusa da Gadonsu Shikenan Sai Suka
Kulle Su Uku Kuma Akayi Sa"a Ajinsu Daya Kuma Wajen Zamansu Daya Ammh Duk Da Haka
Aneesa na Musu Wuyar zama Domin bata da Sakin Jiki ga Masifa da Saurin Zuciya,Ko
Sati Aneesa bata Rufe ba a mkrantan ba Lbrinta ya Zagaya Ko'ina Ana Fadin kanwar
Mr.Bello Tazo Karatu Jss1 yan Matan Mkrantan Suna ta Zuwa ganinta Musamman ma
Seniors Dinsu da Sunzo Sun ganta Sai kiji Ana Fadin Ya Haka..? Ita baka Kuma basu
kama Itadai Aneesan Ko Ta kansu batayi,Tana Jin yadda Ake Zuzutashi Acikin
Makrantan Itakuwa Abun ma Haushi yake bata ba Kadan ba Tana ganin Duk Duniya bata
da Makiyi kamar Bello.
Aneesa Da Wuya da Komai ta Fara karatu Domin Duka Takeci Wajen Bello ba Kadan ba
Kuma yabama malamai Da dama Daman in Aneesa Bata maida kai Akaratu Su Daketa
Shiyasa Wuyar yamata Yawa ga Wahalan Makranta ba Wadattacen Ruwa sai Sun Tafi
Korama ga Muguntar Senoirs dinsu,Wani Lokacin ma Ana Ragamata Saboda Ita Kanwar
Mr.Bello ne Mussaman ma Wadanda Ke Haukan Sonshi,ga Toilet dinsu ma baka iya Shiga
Abude Babu Kofa Ga Aljanu Sun ma Mkrantan Yawa Domin Duk Ranar Jumma"a Sai Anyi
Bikin Aljanu Hatta da Aneesa Sai Da Ta Kwashi Aljanu Domin Lokacin da Abun ya Faru
Bello Aka Kira Dayazo ya ganta bai Dauka gaske bane ya Zata Iskancinta ne Sai Daga
baya ya fahimci itama ta kwasa A Nan dai Aka samata mgani Ta Dawo Cikin Hayyacinta

Watan Aneesa Biyu Ko Visiting Bello bai bari An Zo mata yace Kada Wanda yazo in ba
Suna Son Karatun Data Fara ya Tsaya bane Don Wuya da Dole Aneesa Ta maida Hankali
Akaratu Tana Enjoy din Sabuwar Rayuwarta Yanzu Sun zama kawaye Sosai Su Uku Dukka
inda zasu Tare kuma kullum In Aka Tashi pref Suna Zuwa Islamiyan Yammah basu Dawo
wa Hostel Sai Angama mangariba da Isha"i Anyi Ta'alim Hade da Addu"o"in barci kana
Suke Komawa Hostel Kafin Aka C.s Kowa ya Kwanta yanzu Sun Waye basu karban Tuwon
Dare sai dai Su Jika Complex da madara Su Sha Ta Wannan Fanni kan Aneesa na Shan
Gata Domin Hatta pad bello ke Siyan mata Babu Abunda Tanema ta Rasa Sai jin Dadi
Acewarta baya mata da Hausa Dukanta yake in Tayi Wani Abu bayama Nuna ya santa
Indai Aharkan Karatu ne Noma Kuwa Sun Sha Zuwa Quarters Dinsu Yasasu Noma tun
barema Ita da B.kaita da basu Jin Mgana Arana In basu Fada da wasu ba basajin Dadin
Seniors kuwa in Suka Rainaki kin Bani Musamman ma Kabila Arnakun nan Sunfi Raina
Musu Kura Gashi Aneesa babu Abunda ya Ragu Ara shin Kunyarta ma sai ma Karuwa yake
Zuciyarta ta kara Kangarewa da Rashin Kunya da Rashin Mutumci Kaf Makrantan Kwatar
kwashi Ba Wanda baisan Aneesa Bukar Bulama ba....

Kafin Su Samu Hutun First Ta Koma Gida Anty Rahila ta Haihu Koda Ta Koma ta Isketa
da yarta Hibba kyakyawan Hafsat Sunanta Cemata Hibba,Dawowar Aneesa Daga Mkranta
yabama Kowa mamakin Ganin Abubuwanta Sun Chanza kamar ba Ita ba Sai dai More Rashin
Mutumcita sai ma Karuwa yayi Domin Cikin Hutun Sukaje Borno Ita da Anty Rahila wai
ya"yansu ya Ali Sun Ci Ubansu da Duka Da anyi Mgana Sai Tace Suma Haka Babaninsu
suka mata🤣Aneesa na Lokaci fa Anty Yagana Datazo Suka Hadu kuwa Sai da ta Mangare
mata kai Tana Fadin"Ja"iran yarinya ta bamu Ciwon kai,Anty Nafi Kuwa Zaginta Ta
kama yi Tana Dunguremata kai kuma bakomai Takejin Haushi ba Sai yarda Aneesan Ta
samu Jin Dadi da Chanjin Rayuwa Haka Ta Dingama Anty Rahila Korafin Wai Suna
Kashemata Kudi Saboda Kunata da Rashin Godiya Cikin kayan da Aneesa tazo Dashi sai
da Anty Nafi ta Dibarma Babbar Yarta Sanah,wai Sun ma Aneesa Yawa itako Abun bai
Dameta ba Bata Kuma gayama Kowa ba sai da Suka koma Take gayama Anty Rahila Wacce
Mamakin Anty Nafin ya Cikata,Tafa Zoma da Sanah kaya ammh Idonta na kan Aneesa Sai
Tuna yarda Ta Dinga mata Surutun wai Sun bar Aneesa na Jin Dadi bata komai Agida
Zasu kara Sangarta ta bata dai Kula Anty Nafin bane Ammh TaFahimci Daukan Aneesan
Datayi bai mata Dadi ba, mama Falmata Kuwa Ko bata Fada ba Taji Dadin Ganin Aneesar
Tayi Hankali ba kamar Da ba,Duk da babu Wani Shakuwa aTsakaninsu Ammh Akwai Soyayya
da Shakuwar Uwa da yarta.

Kwanansu Hudu Suka Dawo Abuja ba Dadewa Takoma Makranta Wannam karon ma Da Kuka Aka
Koma Sai dai bai kai na Farko ba,A term din ma Aneesa Ta yi kokari Sosai Tamaida
kai ga Karatu Ammh Masifarta da Tsiwa bai Ragu ba Kullun a Hostel dinsu cikin Dogon
Daki sai Anyi Fitina da Ita Batajin Mgana Kullum Cikin kai ma Mr.Bello kararta
Akeyi Ya Kirata Har Quaters Dinsu yasata up And Down bayan Tagama yasa Ta Shara Da
Noma sai ta Jigata zai Sallameta,Wadanan Abubuwa Su Suka kara Wutar Kiyayyar Bello
Acikin zuciyar Aneesa,Shi kuma Ba Itace ya Tsana ba Hallayarta ya Tsana Lokaci
bayan Lokaci Wani Abun nata ma Dariya yake bashi da Mamaki.

Tafi Tafi Haka Rayuwa Ta Cigaba da Gangarawa Har su Aneesa Suka gama Jss1 Suka
Shiga 2 sai A second Term Kana Su Daada Suka Zo Mata Visinting Ita da Anty Rahila
Harda Yaya Muktar Wanda Mkrantar Kwatar_kwashi Ta Rude da Zuwan Chief Amry Of
Staffa,na kasa baki Daya Mutane kuma da Sauran Dalibai Suna Mamakin Yadda Bello
yake Koyarwa Alhalin ya Wuce nan Nesa ba Kusa ba Kuma baya Nuna Shi Wani ne Domin
Ko Motar kanshi Bello bai yarda yana Zuwa da Ita Mkranta ba Sai dai in zasu Dawo
Mallam Inuwa ya Kawosu In Anyi Hutu yazo Ya Daukosu Shi Mutum ne Mai karancin
Fara"a Gashi Miskili marason Hayaniya Fushi da Saurin Hasala Ko Acikin Mkratan bai
Cika Shiga Abunda bai Shafeshi ba,Shi Abunda ya Sani Koyar da Dalibai,da Kuma Lura
da Tarbiyansu.

Suna Gabda Shiga Jss3 Uncle Aminu yazo Mkrantan Wanda Tasu Tazo Daya da Bello Kuma
Suna Cikin Gida Daya Cikin Lokaci kankani Suka Kara Haskawa Ciki Mkranta Saboda
kyansu da Kwarjinsu Uwa uba kuma basu da Wasa Kusan Suna gyarama Kowa zama Acikin
Mkrantan Principal kuwa Tafi Kowa Alfahari da Samunsu Acikin Mkrantanta,Wasiku ko
na Dalibai bello ya Tarasu ba Adadi Hakama Uncle Aminu basu Maida kai ne Kawai Kuma
ba"a Iya Taransu Saboda Suna da Kwarjini Ko Cikin Aji ne In Suna Koyarwa kika kawo
Musu Wani Wargi yanzu zasu Waje Dake Su Zane Miki Jiki.

Bello yasan Mata dayawa Suna Sonshi Kuma Suna Rubibi Akanshi Ammh bai Taba Nuna ya
sani ba,Bai Taba yarda yabama Wata Daliba Fuska ba,Bayan Aneesa ba Wacce ya ke
Shiga Harkanta sai ko Kawayenta Su S. Jibiya Wanda Suke kara Girmamashi Amtsayin
shi na Malaminsu Kuma Yayan Aneesa Ammh Ita Akoda yaushe Fadi musu Take Ita ba
Dan"uwanta bane Babu Abunda Suka Hada Mutane dadama Suna Mamakin yadda Aneesa ke
Nuna Tsana ga Bello ko Jin Haushi Masu kama Kafa da Ita,Dayake su B.kaita Sun san
Halinta sai Sukaci Mganin Zama da Ita musamman ma S. Jibiya Gwara B.kaita Wani
Lokacin Suna Taba Tsiyan nasu.

Babu Ranar da Su Aneesa ke Shan Wuya Amkranta Irin Ranar Alhamis Ranar General
Work Kenan Ko'ina sai Angyara An Tsabatace ga Bayinka basu da Kyau Sosai Domin
Akasa Ake Kashi Haka Seniors Zasu Sakasu Kwashewa da Kwano koda Chokali,Abun na
Cima Aneesa Tuwo Akwarya Tagaji da Mkranta Ta Gaji Sosai Ammh yazama Dolenta Domin
Uncle belli na Lura da Duka Motsinta,Sunfi Ji Dadin Ranakun kamar Ranar Laraba
Sport,da Kuma asabar Da"ake Inpection Ranar Hause kenan Inda za"a Bama Dukan House
din Dayaci na Daya Kyauta dama Kuma a K'a kida Hause dinka Toh Hostel dinka Kuma
Kalan Check Dinka Toh Su Aneesa Suna Jida Ranar Saboda House dinsu ke Zuwa Na Daya
Duk Sati ba Laifi Suna da Kokarin Tsabaceshi Ammh da Zararan Angama zai koma Gidan
Jiya.

Hutun da Aneesa Ta Dawo na Farko bayan Shigansu Jss3 Su Zulfa Suka Fara Zuwa
Hutu,gidan Ya Muktar,Wanda Bello kamar yayi Bindiga Saboda Fushi Da Farko ma Yaji
yayi ya Tafi Yola sai da Daada Tayi ta ban Hakura Awaya kana ya Dawo Bai sani ba
Ashe Daga Zulfa Har Zubaida Kowacce Sonshi Takeyi Kuma Daga Abba Kabiru Har Abba
garba Kowanne ya Turo yarsa ne ko Bello yagani ya kyasa Wanda Tunda Abun nan ya
Faru ko Sunzo Abuja in ba Ya Muktar ya Matsamai ba Ko Kallo basu isheshi ba in ko
suka samu Sa"a ya gaishesu sai dai Daada ko ya Muktar Sun Matsamai Ammh bacin Haka
Su kansu Sun Fikowa sanin Basu da Wata Daraja a idon Bello.

Hatta Inna Rukayyah Dake Kano Tana Zuwa Tayi Kwanaki Wai Su yanzu Suka san da
ya"yan Muhammed Wanda Sukayi Sanadiyar Mutuwarshi Har Lahira Shida Matarshi,In
Bello ya Tuna da Mganar Kamar ya Mutu Haka yakeji Saboda Bakiciki Rayuwa Uku fa Su
Abba Kabiru Suka Salwartar Ammh ace baza"a Dauki Wani Mataki baa Domin Daada Ta
basu Lbrin Irin Rayuwar da Muhammed Yayi Shida Kanwarsa Hidiyar Har Allah yayi Mata
Rasuwa,Wannan Abun Shi yake Kara Dakula Zuciyar Bello Yaji Kwata Kwata ya Tsanesu
bayason Hada Ko Wata Mu"amala Dasu Wani Lokacin In Abun ya Tasomai Ko Daada da ya
Muktar Sai Abun ya Shafesu yayi Kwanaki in yana Gida bai Bude Kofar Bangarensa ba
ko masu Aiki Sunje kai mai Abinci Haka zasu gaji da Bugawa Su Dawo Anty Rahila ce
kadai Ke IyaTursasa Bello Wani Lokaci Saboda yana Bata Girma Sosai.

Ko Hashim Dayake Zaune A Cikin Garin Abujan Shida Iyalansa A Maitama yana Aiki da
Wani Kamfani Wanda Shi Muktar da Kanshi ya Neman mai aikin,Bello Bai Taba Taka
Kafarshi Zuwa Gidan ba Ko Gidan yazo bai ma yarda Su Hadu ballo Har Su Hada Hannu
Da Sunan Gaisuwa,lambar Wayarshi Kuwa Kowa Na Dashi Ammh basa ma Gangancin Kiransa
Domin Sanin Waye Bello kamar ma Tsoronshi Sukeji Sunyi Iya bakin Kokarinsu Wajen
ganin ya yafemusu Kamar Muktar Ammh Sun Makaro Domin Har Abada Bello bai Taba Jin
Zai iya yafema Ahalin Datayi Sanadiyar Mutuwar Iyayenshi da Kanwar Babanshi ba.

Ya Muktar da Daada Sunyi Ban Baki da Mganar Ammh Duk Abanza Tunda Haka Allah ya
Halicci Bello ba yadda Suka Iya sai dai Suka kawo Ido Suka Sakamai Shiyasa Wani
Lokacin Muktar Kan Kira Bello da Sturborn Saboda Yana Bashi Ciwon kai Ko Awannan
Koyarwar da yakeyi Bayajin Dadi Domin Kaf kasar nan Asanshi Ansan wayeshi Ammh Ace
Duk Matsayin Daya kai Wai Kaninshi Uwa Daya Uba daya Yana Wahalar Koyarwa Awata
Mkrantar Kwana This dis unpair,Ammh Ina Bello yace Abunda Yake Ra"ayi Kenan Kuma
Albashinshi ya Isheshi baya Neman Kari Akyaleshi Haka yana Jin Dadin Rayuwarsa Haka
Dole Daada Tacema Muktar ya Rabu Da Bellon yayi Abunda ya Zab'a ma Kanshi Tunda
Shi ba Yaro bane.

Ko Kasim Da Suke Sa"anni Yayi yayi Suyi Abota da Bello Ammh Ina bai ga Fuska Ba
Domin Bello Bai Ta ba yarda ko Mirmishinsa Sun Gani ba Shima Ya Muktar ya Nema masa
Aiki yana Aiki da Gidan Ruwa ma Jahar Kaduna ya Mallaki Motar Hawa da Kudade masu
Dama,Ammh ko kallo bai ishi Bello ba Shiyasa Iyayen Kowanne keson Yarsa Ta Jawo
Hankali Bello Domin Suna ganin Zasu iya Mallakanshi kamar yadda Suka mallaki
Muktar,kodan kada tunanin da suke na zai iya kaisu watarana kotu akan hakkin
Rayuwakan iyayensa.

*How to pay....�?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?600...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?500 ne,VIP
�?1000, Single one �?300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*ANITHA....*

8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*


_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*🅿�?7*

#Life Style...

"Hutun Second Term na Jss3 da Su Aneesa Suka Dawo ne Aljanun data kwaso Daga
Makranta Suka Fara Agida,alokacin ne Daada da Ya Muktar da Anty Rahila Suka san
Aneesa na da aljanu, duk da dama wasu iyayyakun nata sunsa ana mata kallon tana
dashi.

Bellon da kanshi yayi mata Karatu Ta Dawo Cikin Hayyacinta Kuma bai yarda ya saki
Fuska ba balle,Har Su Ya Muktar su mai Tambayoyin Dake Cikin Ransu suma ganin haka
sai kowa ya kama bakinsa tunda uban gayyar yaki bada Fuska ajeramai wasu
tambayoyin.
Tsakanin Aneesa dasu Zulfa Kuwa ba Kyakyawan Alaqa Domin Aneesa Kam bata Ragama
Kowa bakinta baya Mutuwa ga Rashin Kunya,bata da aiki sai Musu Dariya in Sun
Shigema bello ya Dizgazu,Haka zatayi ta Musu Dariya,Ko sunyi yinkurin Mata Wani Abu
Daada bata bari balle adake Aneesa bazata Daku ba,Dukkansu Sun Girmemeta Domin
Zulfa tana SS2 Zubaida Kuma SS3,Tsakaninsu babu Nisa, Wani Lokacin Kuma Tsakanin
Zulfa da Zubaida Suyi ta Cin Juna Ta kan Bello Haka Kowacce Takoma gida zatayi
tabama Uwarta Lbrin Abunda ya Faru,Shiyasa Tsakanin Hajiya Karima da Hajiya Sahura
yanzu babu Amintaka Sama sama ne Ko Haduwa Sukayi Ko nama Kowa Kallon Raini.

****

_*MUHAMMED BELLO MUHAMMED JIKAMSHI*_ abangaren Rayuwarsa Zan iya ce muku Shi Namiji
ne Sadauki kuma karkkafa mara Tsoro,mai Cikar Zati da Haiba Yana da Kwarjini
Kyakyawan Namiji ne Ajin Farkon Asahun Zaratan maza masu Aji mai Cike da Baiwan
Zati.

Ya kasance Mara yalwar Fara"a Mara son Dariya baya son Raini Namiji ne mai
Tsayawa kan Ra"ayinsa In ya Riga ya kafe kan Abu Mawuyaci ne Wani ya Iya
Tankwasashi,yana da Zuciyata ta Bala'i sosai ga Riko Zai yi wuya Kama Bello Wani
Abu ya manta Both na Alheri Dana Sharri,Ga Tsautsauran Ra"ayi baka Isa ka iya gane
ina Bello ya Dosa ba ko Ya Muktar Dayake Yayansa Ta Uwa Ta Uba Basu da Shakuwar
Haka Sosai Duk Da ba Wanda Yake Dashi Sama Dashi Ammh Dayake Suna da Bambamcin
Ra"ayi basu Cika Samun Daidaito kan Wasu Abubuwan ba,Ga Shi da Dauriya mai Hadi Da
Jarumta Wanda ganin gazawar Bello Abu ne mai Wuya Shiyasa ba Lalle bane kaga Bello
na Kuka,Sai dai kaga Idanuwansa Sun Sauya alamun Bacin Rai.

In ka ganshi yana Doguwar Mgana ne da Uncle Aminu ne Wanda Zan Iya cewa Wasu
Ra'ayin Bello Yana Tafiya Daidai Dana Aminu Kama Daga yadda Bello yabama Aikin
Koyarwa Muhimmaci Rayuwarshi yana ganin Hakan ya Isheshi ya gama da Duniya
Lafiya,Yana da Karatun Addini mai Zurfi Domin Komawarsu Yola bai yi Wasa ba Kuma
Daada Ta Kasance Tamkar Wata Makrantace garesu babu Abunda bata koya musu ba,Yana
da Riko Da Addini Shiyasa Ko Achan Makrantan In Ranar Bikin Aljanu yazo Shida Uncle
Aminu Suna Kokari Sosai Wani Lokacin ba Da Gayyah Mace Zata Fadi Saboda Akira Bello
yazo ya Tabata,Sune Shugabannin MSS,Abangaren Yanmata Ba Wanda zai iya cewa ga
Wanda Bello yataba Nuna Alamun Tana Burgeshi kai Infact ma baya Shiga Harkan
Mata,Babu Macen Da Bello ke bin Sha"aninta da Rayuwarta Irin Aneesa Wacce Kuma Duk
Duniya bata da Makiyi kamar shi,shi kuma Ba Itace ya Tsana ba,Hallayarta ne na
Rashin Kunya da Rashin Son karatu ya Tsana,Shiyasa basa zama Inuwa Daya ammh Kuma
Tana Cikin Tarihin Bello Banda Ita ba Macen da Bello yake bama Muhimmanci Shiyasa
Wani Lokacin Su Zulfa Sukejin Haushinta Sosai Ganin Ko Banza Tafisu Kusanci da
Bello Itako Aneesa batasan Sunayi ba Ammh mganar Gaskiya Aneesa Nada Wani Hali
Wanda Ita kanta bata san Meke Damunta ba.

Indai Wata zata Nuna Tana Son Bello Yanzu nan Zataji Ta Tsaneta In ma ba"ayi Wasa
ba Tabar Kara Kula ta kenan,Ta Dinga bala"i Kenan Ita kadai Kamar Zararriya,Wani
Lokacin Zuciyarta Ta Dinga Zafi Yan hostel Dinsu Wanda Aneesa Tayi Fada dasu kan
Bello ba Adadi In S.Jibiya da B.kaita Sun Tambayeta Miye Damuwarta Sai Tace Saboda
Ta Tsaneshi Don me Wasu zasu Rinka cewa Suna Sonshi😂Abun mamaki Har S. Jibiya na
Cemata Toh ke Ina Ruwanki Tunda Kedai baki Sonshi Ki bar masu Sonshi Su Soshi mana
Kodai kema Kina Crushing Dinsa ne .?

Fadin Wannan Mganar Yajama S. Jibiya Domin Sai da Aneesa Tafi Sati bata Tanka ta ba
Wai Saboda Mene zatace Tana Son Bello Ko Alama Allah yayi mata Tsari da Soyayyar
Mugu kamar Bello Sai da S.Jibiya Tayi ta bata Hakura Kana Aneesa Ta Hakura,Seniors
Dinsu Kuwa Aneesa Ta zama Tamkar Tsaninsu Tunda ba Iya Taran Bello suke ba Ita Suke
Kira Su bata Sakon Wasika Ko kuma Suce Ta Shigar Dasu Jinsu kawai Take Wasiku kuma
Aneesa batsasan Adadin Data yaga ba Bata kai ma Bello Dukka da yasan Yadda Dalibai
Kesonshi bai san Ana bama Aneesa Wasika Tana yagawa ba,Ciki Harda Jidda Madaki
Wacce Keta Wahala Bello baima San Tanayi ba

Abanagaren Yanayin Rayuwar Bello yafi son Cin Abincin Gargajiya kamar Su
Tuwo,Dambu,Tuwon Shinkafa,Favorite Food Dinshi Kuma Shinkafa da Miya da Salad
ne,Bai cika Cin Tarkacen Abinci ba,Yafison Karyawa da Dumamen Tuwo da Safe,Da Rana
Kuma bai cika damuwa da Abinci ba Yafi cin Gasshen Nama ko Soyayyen Kifi Da
dadaddare Kuwa Yafi Shan Kayan Lambu da Lemon Hollandia,Bandashi Duk Wasu Kyale
kyale basu Dameshi ba Aferfesu Kuwa yafison Na kan Rago da kayan Ciki,Ma"abocin
Tara Yunwa kafin ya iya Cin Abinci,Bangaren Lemuka kuma bashi da zabi yafi Shan
Madaran Hollandian,da Kuma Zobo Baya Shaye Sgaye Lemukan Turawa Gaskiya,kana
Ma'abocin Shan Ice cream ne,Bangaren Ruwa Kuma Bai cika Shan Ruwa zallah ba sai ko
Coffea ko Madaran Hollandia Mawuyacin Abu kaga yasha Ruwan Banza Haka Kurum.

Bangaren Yanayin Kayanshi,kuma Yafi Kauna da Mu"amala da Kananan Kaya,Ko Achan


Makranta Dalibai Dadama Suna Murna Ranar Jumma"a Ta Zagayo Domin Ranar ne Bello ke
Saka Manya Kaya Wadanda Suke Masa Kyau Sosai Fiye da Kananun Kayan Dayake
Sakawa,Yafi Sanya American Suit da Safe kamar Lokacin Shiga Ajujuwa,irinsu Samfarin
Tommy,Hilifiger,Armani,Louls,Button,Doke,and Gabbana,Bersace,DKNY,Etc,Bakake da
Ruwan Toka Lokacin Kuma Dayafi Amfani da Kananun Shine Bayan La"asar Haka yafi
Sanya Irin Masu Dogayen Hannuwa na Kamfanin Armani,bangaren Turara Kuma Guda Biyu
ko Man,ko Azzaro Visit Wanda Shine Kamshinsa

Bangaren Takalma Kuwa Yafison Sanya Booth,ko kuma Rufaffu Na Fatar Damisa,wani
Lokacin bai cika Son Budadden Takalmi ba,ammh Wani Lokacin ya Kan saka,Agogo Kuwa
yafi Mu"amala dana Fata Fiye da Sulba Wani Lokacin Sai dai In Azurfa ne Ammh Haka
Kurum yafi Sanya na Fata Gaskiya,

Mallam Inuwa Kuma Wani Amintattacen Direba ne Wanda Muktar ya yarda Dashi Shima
Bello ya yarda Dashi Daga Yola Daada Tasa Suka Daukoshi Suna Zaune Tare Dashi,Yana
da Karamci da Amana Shiyasa Suke Mugun Dasawa da Aneesa Tana ce mai Baba yana
Kiranta Diyata.

Wannan kenan.

*****
Cikin Sakin Ajiyar Zuciya ya Dawo Daga Zurfin Tunanin Mafarin Rayuwarsu,Karamar
Kwallar Data Zuraromai Ya saka Hannu ya goge Daidai Lokacin Daya Daga ido yana
kallon Katon Agogon Bangon Dake Dakin Karfe 12pm na Dare Kansa ya Dafe Kafin ya
Sauke Numfashi,Hannayensa Duka ya Zura Cikin Aljihun Bakin Wandon Dake Jikinsa
Kichen Din Dake Falon ya Shiga ya Bude Fridge ya Dauko Lemon Hollandian Mai Sanyi
da Wani Karamin Kofi aSaman Cabenet Din Kichen din Cikin Wani Takun Takama da yanga
kamar mace ya Fito daga kichen din zuwa cikin Bedroom dinsa.

Saman Side Drower Din gadon sa ya Ijiye Lemon Hollandian Din da Karamin Kofin
Mikewa Yayi Ya Fada Tiolet Yafi Minti goma Kafin ya Fito Daure da Tawol a kugunsa
Karamin kuma yana Saman Kanshi,yana Tsane Ruwan Kansa Kai Tsaye gaban Makeken
Madubin Dake Dakin Ya Nufa bai Shafa Komai ba Illah Turaransa na Sray daya Dauka ya
Feffasama Jikinsa Kafin ya Nufi Gaban Makeken Wardrope din Dakin,Wanda gabadaya
Glass ne Ajikinsa Kofar glass Din ne Yasaka Hannu ya Bude Ta bangaren Hagu

Sai ga Jerin Kayan barcinsa na Pjms Suka bayyana Kala kala,Masu Ruwan Tokan ya
Dauko Riga da Wando ya saka Kafin ya Koma Cikin Tiolet din ya Shanya Towels din,ya
Fito saman Gadonsa ya Koma ya saka Hannu ya Jawo Laptop dinsa ya latseta ya Kashe
kafin ya Sauko Zuwa Bakin Gadon Madaran Hollandian din ya Dauko kafin ya Dauki
Karamin Kofin ya Tsiyaya sai da ya Cika kafin ya Kafa kai ya Shanye Duka,kan Side
Drower din ya maida ya Ijiye kafin ya Dauki Wayarsa yana latsawa na Tsawon Wasu
Mintuna Kafin ya Mike ya saka Wani Takalmi mai Taushi mai kama da Na Bedroom Ya
Fice Daga Bedroom din Lokaci Daya yana Sanya Wayarsa Cikin Aljihu...
Kai Tsaye ya Bude Kofar Falon Shi ya Fita bayan ya Rufe Kofar,Saukowa ya Farayi
Daga Steps Din yana Hango Sojojin Dake Safa da Marwa Cikin Haraban Gidan Wanda
Gidan yake Gauraye da Hasken Farin Kwayaye masu kyau da Tsari,Cikin Sanyi da Zati
ya Karisa Sauko daga Mension Dinshi Lokaci Daya Duka Hannayesa Cikin Aljihu.

Sojojin Dake Haraban Wajen Basu Damu Dashi ba Domin Sun Saba Indai Bello na gari
Toh Suna yawan Ganinshi Cikin Dare Lokaci bayan Lokaci Wucesu yayi Zuwa Karamin Dan
Madaidaicin Masallacin Dake Cikin Gidan Wanda Suke gudanar da Sallolinsu na Kamsin
Salawatu,Wanda Mallam Inuwa ke bada Sallah In Ya Muktar baya nan Shida Sauran
Sojojin Dake Tsaren Gidan Musulmai da Kuma Sauran Ma'aikatan In Kuma yanan nan
Shima Nan yake Sallah,haka Bello in yana gari Shima Yana bada Sallar Wani Lokaci
Kuma Sannan Yana Yawan Zuwa Cikin Msallacin yayi salla cikin Dare Tare da karatun
Alqur"ani Wani Lokacin nan zai Zauna sai Lokacin sallar Asuba Ta gabato sai dai
Suji yana Kiran Sallah.

Yauma Din Hakane ya Faru Domin Yana Shiga Cikin Masallacin ya samu Gefe ya Tsaya
Wayarsa ya Fito Dashi Daga aljihunsa ya Ijiyeta gefensa Ya Daidaita Natsuwarsa Dama
already ya Dauro alwalarsa Tunda ga Daki ya Tada Sallah Raka'o'i Tara yayi ya
Cikashe da Shafa"i da Wuturi ya Dade yana Addu'o'inshi kafin ya Mike ya Isa Gaban
Masallacin ya Daga kai ya saka Hannu ya Bude Wata Durowa Inda Jerin Alqur"anai Masu
kyau da Ban Sha"awa,Guda Daya ya zaro kafin ya Dawo Ya zauna Inda yayi sallah
Tamkwashe Kafa yayi ya Bude Qur"anin yafara Karatunsa Ahankali Cike da Natsuwa

Bashi ya Dakata da Karatun ba Sai Wajen 4:30am na Asuba kafin ya Tattara ya maida
Qur"anin Ma'ajiyarsa Cikin Wani Karamin Daki ya Shiga Inda Kayan Wutan Suke Daga
Cikin Daki yafara Kiran Sallah Wanda ya Tada Mutanen Gidan Daga Barci,Ya Muktar ne
Farkon Fitowa Shima alwalan yazo yayi Wajen Inda Famfuna Suke Bayan Masallacin,ya
Shiga Cikin Masallacin Ya Tada Raka'atanul Fijir,kafin Lokacin Sallar Asuba ya Cika
Yau din Bello ya bada Salla,Sai bayan An Idar da sallar ne Bello ya Dade Cikin
Masallacin Kafin ya Fito nan ya Iske ya Muktar Tsaye yana Jiransa Karisowa yayi
Cikin Zatinsa Yana Zuwa ya Rankwafa Yana Fadin"Barka da Safiya Yaya..'

Kafadansa ya Dafa kafin yace"Kai zan ma barka da Safiya Yallabai Mallam Muhd
Bello.."Yafada yana Kallonsa Cikin Kunya Bello ya Sadda kai yana Sosa Keya kafin
yace"Afuwan Yaya.."Mirmishi Muktar ya saki kafin ya Dafa Kafadarsa Su Fara Tafiya
yana Fadin.."Ya zanyi Dakai Bello,Kun Dawo lafiya..?

Cikin Sanyin Murya Bello yace"Lafiya lau Yaya.."Yafada yana Kallon Kasa Mirmishi
Muktar yayi yana Lura da yanayinsa Kafin yace"Ina Fatan Watarana Ka chanza Bello
Allah ya baka Mata Tagari Wacce Zata Tayamu Chanzaka Bello.."Yafada Cikin Damuwa
Shuru Bello Yayimai Still Suna Cigaba da Tafiya Gabda Mension Dinshi suka Tsaya ya
Sauke Hannunshi Bisa Kafadanshi Dama bai Tsammaci Amsa Daga bakinshi ba Kafin
yace"Kayi Hakuri da Zuwansu Zulfa Bello k...."Can we go Inside yaya..? Yafada da
Sauri yana Katse Yayan Nashi Saboda Bayason Ranshi ya baci Tun kafin Gari ya Waye..

Fahimtar Haka ne yasanya Muktar yace"Why Not Muje Dama Daada na


Cigiyarka.."Mirmishi kawai yayi,kafin yayi Gaba Hannuwansa Duka Cikin Aljihun
Wandon Barcin Dake Jikinsa Har Zuwa Falon Gidan Wanda Ke Tsit babu Motsin Kowa sai
Kamshin Tashin Turaren Wuta Wanda Har Ma"aikatan Gidan Sungama Tsabtace Ko"ina.

Cikin Kasala Bello yace"Bari na Karisa Wajen Daada.."Yafada Yana Wucewa


Bangarenta Cikin Dan Sassarfa Muktar na Tsaye yana kallonsa Har ya bacema ganinsa
Kansa ya Shafa kafin ya saki Ajiyar Zuciiya yace"When zaka Chanza Bello..? Yafada
yana Shafa Sumar Kanshi kafin ya Daga Kafa ya Fara Haura Stairs Zuwa Dakin Barcinsu

Koda ya Shigo Falon Daada Shima Babu kowa Dama bai Tsammaci ganin Kowa ba Ainihin
Bedroom Din Daada ya Tura ya Shiga sai dai kuma Dakin Babu Alamun Mutum Wutar Dakin
ma Akashe ne,Hannu ya saka ya Kunna Makunnin Wutar,yaga Dakin ba kowa Hannu ya saka
ya Kashe Wutar Dakin kafin ya Fito Lokaci Daya Tare da Janyo kofar Bedroom din..

Dayan ya Tura ya Shiga da Sallama Daidai Lokacin Daada Ta Dago kanta Wacce ke kan
Sallaya Sanye da Hijabi Carbi ne Ahannuta tana Lazimi.Tunda Ta Dago kai Suka Hada
ido Ta maida kanta Kasa Daga bakin Kofar ya Coge yana Fadin"Au ni za"a ma Yar
Shariya Allah sai na Koma Abuna.."Yafada yana Mirmishi ..

Daada ta Dago kanta Tana makamai Harara batayi Mgana ba Dariya yayi Har Fararen
Hakoransa Suka bayyana ya Kariso Cikin Dakin Hannunsa Cikin Aljihun Wandonsa yana
Fadin"Nazata Ana Iya Fushi da Megina Ran gida.."Yafada Daidai Sanda Idonsa ya Sauka
kan Aneesa Data ke baje kan Makeken Gadon Dake Dakin Tana barci Sanye Take da
Doguwar Riga Red Colour Ta barci ce Ammh Tana da Tsawo ammh Saboda Mugun barci Har
Daga kafafunta Duk ya yaye,Kanta kuma Ta bajeshi kan Filo kananu kalabarta Duk Sun
Baje kan Filon Saurin Kauda Idanuwanshi yayi kafin ya karisa gaban Daada ya zauna
daidai Lokacin Datake Shafa addu"arta Sai Suka Shafa atare Hannayenta ya Riko yana
Fadin"Matata Kina lafiya..?

kallonsa Daada Tayi kafin Tace"Lafiyata lau Megida ba Cefane.."Tafada Tana Shafa
Sumar kanshi kamar Wani Yaro,yar dariya Yayi kafin yace"Au Shine Matsalan karki
Damu Cefane sai kin gaji Da gani.."Yafada yana Shafa gefen Fuskarta Cike da Kulawa
Ta bude baki zatayi mgana kenan Aneesa Ta Motsa Lokaci Daya Tana Sakin Tusa mai
kara Daga Daadan Har Bello da kallo Suka Bita Bello ne Yaji Wani Takaichin Aneesa
ya kamashi yarinyar sam bata Da Hankali Jiwai Tana mace ammh Tana barci Tana Sakin
Tusa.

Hade Rai Yayi yana kallon Daada yace"Daada yarinyar nan Ta Tashi tayi sallah
kuwa..? Daada na kanne Dariyanta tace"inafa Nayi Tashin Duniyan nan Ammh Taki Tashi
sai Cemin Take Wai achan Makranta ba"a barinsu suyi barci Sosai."Baki ya Rike ammh
ba Domin yayi mamaki ba Indai Aneesa ce Mikewa yayi ya Isa bakin Gadon Yasaka hannu
ya Toshe Hanci Domin Tusar ta Aneesa Ta bada Wari Gadon ya Daka da Karfi Wanda ya
Tashi Aneesa Tayi Zumbur Ta Mike zaune Tana Mutseke Ido Cikin Barci Take kallon
Bello Cike da Haushinshi Cikin Ranta Kuma Fadi take"Anan din ma baza"a bar Mutum ya
huta ba kai dai baka Da Hali mai kyau.."Tafada Tana Turo karamin Bakinta gaba kamar
zatayi kuka Tsawa Ya Dakamata yana Fadin

"Zaki Tashi Zuwa sallah kokuwa sai na zane miki Jikinki..? Yafada yana Sakarmata
manyan Idanuwansa Aneesa Tayi Jim kafin Tafara Kokarin Tashi Ammh Kuma Tana Kunkuni
kamar Wata yarinya Saukowa Tayi Daga Kan gadon Tana Mika kawai Ta kara sakin Tusa
Daada Dake zaune ta saki Dariya Tana Fadin"Umh Aneesa yau ta zama Bodara.."Belle ko
baya ya matsa kamar ya Shake Aneesa Cikin Hargagi yace"Get out Nonesess Kina Wani
Bude jiki kina ma Mutane Tusa..."

Da Sauri Aneesa ta Waigo Tana kallonshi Harara ya sakarmata kafin yace"I said get
out.."Yafada yana Nuna mata hanya ammh Hannunsa Daya kan Hancinsa Baki Aneesa Ta
Tura tana kama Hanyar Fita tana Fadin"Dadin Abun dai Iska na Fitar na Cuta waya
sani ma Ko Mutum Shima yayi nashi nawace Datayi kara ta bayyana.."Tafada kamar
Badashi Take ba Yaji Abunda tace Cikin Hargowa ya biyota yana Fadin"Ke..ke Don
Ubanki mekika ce..? Ni sa"an Wasanki ne..? Da Sauri Aneesa Ta Bude Kofa ta Fice
Tana Dariyar Mugunta da Harara ya bita kafin yace"Bush girl.."

Daada Dake Dariya tace"Dawo ka zauna Kada Aneesa Ta zauta ka Haka Take bazata
chanza ba yadda kaima bazaka Chanza ba."Tafada kai Tsaye tana kallonsa Fuska ya
yamutsa kafin yace"Don Allah Daada ba Hadani da Wannan Bagidajiyar yarinya Mara
Kunya ni ba Sa"anta bane na Mata Nisa Har Abada.."Daada na Dariya tace"Toh dama
mana Megidana."Jagale yayi Hannuwasa Cikin Aljihun Wondon Barcinsa Zai yi mgana
Kenan Anty Rahila ta Shigo Falon Ita da Hibba Sun Sha wanka Su Turburkallah masha
Allah.
Ganin Bello yasa ya Ta Washe baki Tana Fadin"Teacher Uban karatu ko kuma malamai
Magada Annabawa zan ce ne..? Tafada Tana yar Dariya Mirmishi yayi Lokaci Daya yana
Daukan Hibba Data ke Kiranshi Kansa Tsaye yace"Ina Kwana Anty Rahila.."Tana zama
Kusa da Daada tace"Lafiya lau Bello ya Yimana Yaji kuma.."?,bai yi mgana ba Illah
cigaba da Wasa Da Hibba Dayake yi,itama bata damu ba Illah maida Hankalinta Datayi
Wajen Gaida Daada ganin Haka yasa ya Juya ya Fice Dauke Da Hibba Zuwa Falon Anty
Rahila

Yana Shiga Falon yaci karo da alheri na kaida kawo Tsakanin Kichen Da
Dinining,Gaisheshi Tayi ya amsa Adakile yana Kokarin Ficewa Daga Falon ne Zulfa ta
Fito Sanye da Wasu Riga da Wando yan pakistan kanta ta Sanya Wani bakin Veil
Fuskarnan Tasha Makeup,Da Farko bata ganshi ba Don Hankalinta na kan Waya kamshin
Turaransa Taji da Kuma mganar Hibba ta Dago da Sauri Karaf ko Suka Hada Ido Baki ta
saki Tana kallonshi Cikin Salon Shauki da Muradi mai Girma Shiko Hade Rai yayi
kamar bai Taba Dariya ba Sauke Hibba yayi yana Fadin"Koma Wajen Mommy.."Da gudu ko
Ta Wuce Zuwa Shashen Daada Shikuma ya Juya cikin Izzarsa Zuwa Falon Farko Cikin
Sanyin Murya Zulfa ta Furta

"Uncle Bello...."Ta Kirashi Cikin Wani yanayi Wani Kololon Takaichi ne ya Ciyoshi
Wai Uncle Bello! yajuyo A harzuke Cikin Masifa da Tsawa yace.'

*How to pay....�?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?600...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?500 ne,VIP
�?1000, Single one �?300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*Shakira...*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*🅿�?8*

"Do i look like ur Uncle..? Nace Nayi kama da Wanda ya Hada Wani Abu Dake..? Yafada
yana Sakarmata mayan Idanuwansa Cike da Fushi mai girma lokaci Daya da Wata tsawar
Data nemi Razana ta.

Wanda ya Fito da Zubaida Dake Shirin Fitowa Daga Dakinsu Itama Sanye Cikin Wata
Atamfa mai Ash da Red Dinki Doguwar Riga Wacce ta Fito Da Duka Suran Jikinta,Ganin
Zulfa Tsaye tana Raba Ido ga Bello Tsaye Yana aikamata da Wani Kallo Yasa Ranta
yamata Dadi Cikin Yanga da Iyayi ta kalli Zulfa kafin Tafara Taku Zuwa ga Bello
Tana Fadin"Uncle Bello Gud Mrning..."Tafada Atsume lokaci daya kamar zata Riko
Lallausan Hannunshi Cikin Wani Fushi da Bakinciki ya Saukema Zubaida Wani kyakyawan
Mari Wanda Sai da Ta Duke kasa Tana Ganin Hazo Saboda yadda Marin ya gigita Marin
ya Shigeta sosai domin bayan Hazo Harda jiri take gani kafin Ta Dawo Hayyacinta ya
saka kafa ya Shureta baya tatafi kanta ya Bugu da Jikin Kujera Cikin Sakin Marayan
Kuka Ta Furta"Wayyo Allah na..!

Zulfa Dake Tsaye Duk da Ta Tsorata da Bello ammh Jin Dadin Abunda yayima Zubaida ya
Nuna saman Fuskarta baya taja bayan Tayi Foolling Din Hannuwanta Bisa Kirjinta tana
kallon Zubaida gefe Daya kuma Tana mamakin Wata Irin Zuciya ne Allah yabama Bello
yanzu ma Din Huci kawai yakeyi Cike da Zuciya,wannan Ihun na Zubaida Shi ya Fito da
Daada da Anty Rahila Daga Shashen Daadan Itama Aneesa Tana Dayan Bedroom din bayan
Ta Idar da Sallah Taji kamar Maganar Uncle Bello Daga Falon Anty Rahila da Gudunta
ta Fito Daidai Sanda Bello ya Karisa gaban Zubida ya nunata da Yatsa Cikin Fushi da
Tsana yafara Fadin"

"Bana ce kudaina Kusanto ni ba...? Nace bana Bukatarku Arayuwata..!ban Hada komai
Daku ba..!ko mun Hada ne..? Kusani ku kara sani Ni muhammed Bello Jikamshi ku ba
Ahalina bane bani da Wasu Ahali Awannan Duniyan Face Daada,Ya muktar,Anty
Rahila,Hibba da Aneesa Sune Kadai Ahalina,Saboda Haka ku Fita Daga Rayuwata Bana
Bukatar ganin ku kusa dani,Mgana ta Karshe Kuma Duk Wacce Takara Kuskuran Kiran
Uncle Bello Abakinta Wlh Tallahi sai na Saka Almakashi na Datse mata
Harshe..."Yafada yana Sauke Numfashi Saboda yadda Zuciyarsa ke Gudu lokaci daya.

"Bello..!" Ya Muktar Dake Saukowa Daga saman Stairs Ya Fada gabadaya Suka Waiga
Suna kallonsa Saukowa yake Cikin Kakinsa da alama Fita zaiyi Hulansa Tana Rike a
Hanunsa Ammh Fuskarba Babu Walwala ko Kadan Aneesa dake Tsaye Ta Tura baki
Tace"Lalle nema wannan Ka kama Wala mallam Dama Su karike Sune naka ni Aneesa bazan
Taba zama Ahalinka ba Ina gama Karatuna zan Kama Gabana.."Take Fada Tana kallon
yadda yake Huci kamar Wani zaki.

Tunkafin ya Muktar ya kariso Bello ya Saka Hannu Cikin Zuciya ya Daki Center Table
din glass Din Dake Tsakiyar Dakin Ya watse Gabadaya,Gabadaya Falon kowa ya Razana
Tun bama Daada ba Hannunshi Tuni ya Fara Digan Jini Ammh bai Damu ba Illah Fadi
Daya ke cikin Hargagi "Ya Muktar u better Tell dem Kai kake Bukatar Ahali kamarsu
Ammh ni Bello Har Abada bana Bukatarsu Arayuwata In Har kana son ka Cigaba da zama
dani karkashin Inuwa Daya sai ka sanar dasu kan Su kyale ni nace bana Bukatar su ko
Ana Dole ne...!? Yafada Cike da Tsawa Lokaci Daya gudun Jinin Hannunsa na Kara
yawa.

Ya Muktar ya Nufeshi da Sauri yana Fadin"Bello baka da Hankali ne.? Ko Sauraranshi


baiyi ba kawai ya Juya ya Fice Daga Falon Afusace Ya Saka kafa zai Bishi Kenan
Daada tace"Kul kada ka Bishi Muntari.."Ya Waigo Cike da Tsoro yana Fadin"Meyasa
Daada..? Kinga fa Jini yake Zubarwa..?

Mirmishi Daada Tayi kafin Ta kariso Tsakiyar Dakin Tana kallon Zubaida da Zulfa da
sukayi Wiki Wiki Tace"Ka kyaleshi ko kaje yanzu bazai Taba Sauraranka ba..!Saboda
Fushinsa ya Tashi ba yaro bane zai Kula Da kanshi Ammh Muntari Matukar bazaka daina
Kusantoma Dan"uwanka Abunda bayaso ba To ina kyautata zaton Watarana Zaka nemi
Bello ka Rasa."Kallonta yayi kafin yace"Ammh Daada..."

"Dagamai Hannu Tayi kafin Tace"Bar Mganar Muntari abarta Kawai nace..."Tana gama
Fadin Haka Ta Juya zuwa Shashenta Aneesa Dake Tsaye Tana Kanne Dariyanta sai da Ta
Fito gabadayansu Suka kalleta tana kyakyata Dariya,Harara Anty Rahila Ta maka mata
kafin tace"Zan saba miki Aneesa ki Shiga Ciki.."

Dariya ta kara saki kafin tace"Ikon Allah Shisshigi ba Kwarjini Ance ba"ayi ba"ayi
Dole ne..? Kai Wlh Anyi Asara Tunda Tun Ana ma Mutum kora da Hali Harda yau aka
kure shi ya Furta baya Bukata A kyalesa Dole ne..? Tafada tana kwaikwayon Bello Da
Gudu Rahila ta Bita Tana Fadin"Aneesa..."!Gudu ta Kwasa Zuwa Sashen Daada Tana
Dariya Abun yayi mata Dadi Sosai.

Shiko Ya Muktar Tsaye yayi yana Sauke Ajiyar Zuciya kafin ya Duka Kusa da Zubaida
yana Fadin"Am Srry Kinji...Buh kudaina Shiga Harkan Bello Tunda bayaso ku kyaleshi
Zuwa gaba Nasan zai chanza.."
Kuka Zubaida ta Fashe Dashi Tana Fadin"Daddy Wai Laifin su Abba sai ya shafemu..?
Bafa mune mukayi Wannan Kuskuran ba,sanda akayi bamu da Wayau Meyasa Uncle Bello
bazai Dubemu da Idon Dakake Dubanmu ba.."Tafada Tana Kuka Shuru yayi bai bata amsa
ba Kama Kujera Tayi Ta Mike Tana Fadin"Wannan Abun bazai saka na Kyaleshi
ba...Yanzu Aka Fara Wasan."Tafada Tana Hararan Zulfa Wacce ke karamar Dariya Cike
da Jin Dadi.

Hanyar Dakinsu Ta Nufi Tana Dingishi da Alamun kafarta ta Bugu Sosai da kallo Zulfa
ta bita Tana kara saka Dariya,Anty Rahila Dake Gefe Ta Riko Hannun Muktar Zuwa
saman Dinning Tana Fadin"Relax...Umh...Is ok..."

Kallonta yayi Cikin Raunin Murya kafin yace"Rahila..Ya zanyi...? Bazan guji
yan"uwanmu ba... yayyin Abba ne Wanda Muka Taso muka ga Suna Ci a karkashin
Dukiyarsa Rahila,..Ya zanyi Da Rayuwata..? Bayan Sun aikata mugun Nufinsu akan su
Abba yau wa gari ya waya..? Basu ga Ishara ba .?.!Kuma Allah ya Nuna musu iyakarsu
Tunda Dukiyar Da Suke mawa sun mallaketa ammh Ta kare Ta barsu,Ko Ahaka muka barsu
Sunga Isharan Duniya...! Rahila bari na gayamki Duk Duniya Su Abba Kabiru basu da
Sanyin Idanuwa kamar mu Saboda mun zamesu Bango Abun jinginansu.."Yafada Idanuwansa
na Sauya kala

Anty Rahila na Jamai kujeran Dinning Din Take Fadin"Hakane...Kayi Hakuri kabar
Mganar Hakanan Suma Hutunsu ya kusa karewa su koma Gidajensu Shima ai ba zama zaiyi
ba.."Muktar ya Runtse Ido kafin ya Bude yana Fadin"Meyasa Bello bazai gane bane..?
Yaki bama Zuciyarsa damar karban Kaddara balle yazama Cikin masu yafiya..? Anty
Rahila Tace"Hakuri zakayi mu kuma Cigaba damai Addu"a Tunda Haka Allah yayishi..Sai
Fatan Allah ya Ragemai Fushin Zuciya.."

Bai mata mgana ba Illah Kurama Waje Daya ido dayayi yana Nazarin Wani Abu Ita Kuma
Anty Rahila Tana Kokarin Saving Dinshi,Zulfa ko Na zaune Cikin Falon Tana ta
Danedannen Waya Cike da Nishadi Kamar ba Abunda ya Faru yayinda Da Zubaida ke Ciki
tana Rafzan Kuka Kamar wacce ake yankata Bakinciki Duk ya Cikata na Abunda Bello
yayi mata agaban Zulfa Wacce Tasan Wannan Lbrin bazai Tsaya ba Sai ta kaishi Har
gidan Abba garba Mama Sahura Ta samu Abun yabama Ummanta Mgana Akai.

Anty Rahila bata bar Muktar ba sai Taga ya saki Ranshi,Har Haraban Gidan Ta
Rakashi,Inda Masu Tsoronshi ke Jiranshi ya Shiga Mota Tawagarshi Suka Rufamai
baya,Falon ta Dawo Ta Kira Jummai ta bata Umarnin ta gyara Falon Ta Kwashe Glass
din Da suka Fashe ta Tsaftace komai.

****
Cikin Bedroom Dinshi ya Shiga Hannunshi yana Zubar da Jini ammh bai Bi takai ba
Illah kafa da Sanya ya Shuru gadonsa Wanda ko Motsi baiyi ba Cikin Bakinciki da
Fitan Hayyaci ya Sulale kasan Cafet din Dakin yana Ji kamar Zuciyarsa zata Fito
Fuskar Mami da Abba yake gani Iyayensu Wandanda Sukaci Burun Su zauna Dasu Har
Tsawon Rayuwarsu Sai dai kash Wadanan Azzuluman Guda biyu Wato Abba kabiru da Abba
garba Sun yi Sanadiyar Dakushe Duk Wannan Burin na iyayensu Sukayi Sanadiyar Rabasu
Har Illah Masha Allah.

Runtse idonshi yayi yana Sakin Ajiyar Zuciya,Lokaci bayan Lokaci,Kafin Wani Hawaye
mai zafi ya Kwarayomai Ta cikin kwarmin Idanuwansa Dora kansa yayi Bisa gwiwansa
yana Sakin Marayan Kuka Ahankali Gefe Daya kuma Hannunshi na Digan Jini,Ya Dade
yana Rera Kukansa Wanda ya Dade baiyi Irinshi ba,Saboda Taurin Zuciya kafin ya
Tashi yana Tangadi Saboda Jinin Daya zuba Ahannunshi ya Shige Tiolet ya sakarma
Kanshi Shower,bai Dau Lokaci ba ya Fito ko mai bai Tsaya Shafawa ba ya Bude
wardrope dinshi ya Dauko Wasu Riga Da Wando Na kamfanin Armani black and White ya
Saka Cikin Sauri ya Fice bayan Ya Dauki Wayarsa.
Haka ya Fito Daga Mension Dinsa Yana Duba Hannunsa Wanda Glass Suka yanke Suka
Shisshige,Mallam Inuwa na ganin ya Fito ya kariso da Sauri Domin Dama in ba Bello
ba sai Hajiya Rahila in zata Fita Shine kadai Direbansu,Yana karisowa Tunkafin yayi
mgana Bello yace"Mallam Inuwa Muje Specialist hospital..."

Yafada kai Tsaye yana Wucewa Jikin Motar inda ya Bude ya Shiga Gidan Gaba yana
kwantar Da kanshi Cikin Kujeran Motan lokaci Daya yana Sauke Numfashi Da Mamaki
Mallam Inuwa ya biyosa Ya Bude Gefen Direba ya Shiga ya Zauna ya Tada Motar Ya zuba
Hon Masu gadi Suka Wangale musu Get Suka Sulala Waje Sojojin Dake Tsaron Haraban
Gidan Suka Bisu da Sarawa kamar yadda Suka saba.

Dressing din Hannun Akama Bello Aka bashi Mganguna Kafin Su Dawo Gida,Mension
Dinshi yashige Babu Wanda yakara Jin Motsinsa Kuma ba Wanda yayi gangancin Nemansa
Sanin Halinshi,Bai damu da Abinci Kayan Lambu yayi taci yana Korawa da Madaran
Hollandia Gefe Daya kuma yana Jinyar Hannunshi Wanda ya ma kanshi Rauni.

****

*Washegari..*

Aneesa na Zaune Afalon Anty Rahila Tana kallon Tashar mbc2,Anty Rahila ta Sauko
daga Sama Rike da Waya Ahannunta Tana Fadin"Anee ga Kawarki na Kiranki.."

Tafada Tana Mika mata Wayar Aneesa Dake Sanye da Riga da Sikt yan Kanti ta Saka
Wani karamin Hijabi Fari Ta kalli Anty Rahila Tana Fadin"Kawa kuma.? Ta Ina..?

Hararanta Anty Rahila Tayi kafin Tace"Bansani ba zaki karba Kokuwa zaki Tsaya
Tambayana ne...? Mika Hannu Tayi ta Karba Tana Fadin"Allah baki Hakuri.."Tafada
Tana Tura baki kafin ta saka Wayar Akunne Tana Fadin"Hello..."

Da Kallo Anty Rahila Ta bita kafin Ta Wuce Shashen Daada Tana Fadin""Aneesa Allah
ya Shiryeki Wlh Mijinki yana da Aiki.."Da kallo Aneesa Ta bita kafin Tace"Wake
Mgana..?

Dagachan Bangaren Aka ce.."Aneesa Bukar Bulama..."Cikin Isa Aneesa


Tace"Yes...Bilkisu Kabir Kaita..."Dariya Billy Tayi kafin Tace"Ashe zaki ganeni..?
Tsam Aneesa Tayi kafin tace"Taya bazan ganeki ba B.kaita ban Tsaneki Haka ba.."

Shuru Ya biyo bayan Mganar Aneesan kafin B.kaita tace"Kin yafemin Aneesa...? Kai
Tsaye Aneesa Tace"Me kikamin B.kaita..? Ni babu Abunda Kikamin Fadan Ki so kanki
mukayi Domin Ina Matukar Tsausaya miki kin Fada Son Wanda bai Dace kiso ba
Billy."Mirmishi Billy Tayi kafin Tace"Duk Naji A.bulama,Ammh Duk Fadan na menene..?

Aneesa tace"Na Haushin Duk Yadda Muke Tare B.kaita baki Tayani kin Wanda nake Ki
ba,sai ma Wai kina Kokarin Cewa Kina Sonshi Haba Billy kin bani Mamaki Banga Wani
Abun so Jikin Wannan ba.."Tafada Tana Wani Tabe Baki Dariya Billy Tayi kafin
Tace"Toh naji nidai baki ji nace ina son Uncle Bello kice kika ja nace miki haka
ganin Abun naki yayi yawa..Duk ba wannan ba Ammh dai kinsan Lokacin muna Makranta
Mr.Bello yayi kokari Akanmu Aneesa bazai saka Saboda Takun sakarku mu manta Dashi
ba

Aneesa Tayi Tsaki kafin tace"Mtswss..Sai fa kiyi ni ba Kokarin Dayayi akaina don ba
Rokarshi nayi Nace Don Allah ya kawoni Wannan Makrantar ba Saboda Haka aikin sakai
ne Ni ban yaba ba balle nayabeshi.."Dariya B.kaita ta saki kafin tace"Wow...Aneesa
Wlh bakinki baya Mutuwa,ya zence komawa Makranta Aneesa ki koma Kinga Nima Abba
yace Chan zan cigaba Hakama S.Jibiya Jiya Take Fadamin da Mukayi Waya.."
Aneesa Tace da Sauri.."Tab..Sannunku sai nace Allah bada sa"a Don ni ko zan Shigaba
da Wannan Makrantar ba sai dai Jeka ka Dawo "Cikin Marairaicewa B.kaita tace"Plz
Anee ki Dawo Saboda Mu.."Dariya Aneesa Tayi kafin tace"Ki bar Rokona Karki Cuceni
bakisan yadda na Tsani Makrantar nan bane.."Ajiyar Zuciya B.kaita Tayi kafin
tace"Shikenan Ammh Mr.Bello kuwa ya sani..? Banajin fa zai barki Aneesa..?

Aneesa na Hararan Wayar Tace Cikin Kufuluwa"Allah Sarki Hala Bellon Ubana ne,To ko
Marigayi Alhaji Bukar bulama Allah ya Jikanshi Sanda yana Raye bai Takuramin ba
balle Wani banza Cikon Dangi Ke ni Rabani da Wannan Mganar in Abaya ya kaini
Lokacin Ban kara Wayewa ba Ammh yanzu yadda Nakejin kaina bamai sakani nayi Abunda
Ba Ra"ayina bane.."Tafada Tana Juya Ido Abun sai yabama B. kaita Dariya sai da ta
dara.

Kafin tace"Toh Zamu gani Ammh dai Nasan kwatar-kwashi kamar Dole ne Ciwon Arne.."Da
Sauri Aneesa tace"In Allah ya yarda Bakinki sai ya Sari Kashi Danye ma Kuwa Banza
mara Mutumci,Kinga Malama sai anjuma.."B.kaita na Dariya tace da Sauri"yi hakuri
Don Allah na Bari bazaki dawo Kwatar-kwashi ba karki yanke Kiran Don Allah.."Tafada
cike da Marairaicewa.

Baki Aneesa tatura kafin tace"Kiyi da Hanzari Domin Waya Dake yafara Fitarmin
Aka.."B.kaita ta Rike baki kafin tace"Dallh banza Dama Dalilin kiran Naki zan
gayamiki Sati mai Zuwa zamu Shigo Abuja ni da Umma Biki Insha Allahu zan zo mu
gaisa.."Tsalle Aneesa Ta Daka bayan Ta Mike tana Fadin"Da gaske Billy..?

Billy na Dariya Tace"Wlh Allah.."Aneesa Tace"Kai Naji Dadi Can Wait to see u
B.kaita.."Cikin Farinciki tace"Me too.."

Basu yi sallama ba sai da Kudin Wayar Maman Billy ya kare kana Suka Saurara Saboda
Jin Dadin Zuwa B.kaita da Hanzari Aneesa Ta Lalubo Lombar Wayar gidansu S.Jibiya
dama Tana Dashi Domin Suna waya Lokaci bayan Lokaci Ammh sai Wayar Taki Shiga ganin
Haka yasaka Aneesa Ta Kwashi Gudu Zuwa Shashen Daada Tana sanar dasu Zuwan Billy
Tana Murna Tana Tsalle Daga Daadan Har Anty Rahila da Kallo Suka bita na Mamakin
Halin Aneesa Domin ba Wanda baisha Lbrin Fadan Da Sukayi da B.kaitan ba Ranar Hutu
Ammh Ji yadda Take Murnan Zuwanta,Aneesa kenan Manyan mata.

*******

*BAYAN KWANA BIYU..*

Ba wanda ya sani Ashe Bello baya Abuja ya Tafi kano Tun Washegarin Ranar da Abun ya
Faru Ba Wanda ya sani Daga Anty Rahila Har ya Muktar Wanda bayanan ya Tafi
Maiduguri,Taron Sojoji Shuru taji yasa Ta leka Mension Dinshi Sai dai ga Duk alamu
bayanan Ta Fito zata koma barayinsu Suka ci karo da Mallam Inuwa bayan Sun gaisa ne
yake Tambayanta Ko zata Fita ne..? Sai tace A"a Tazo Shashen Bello ne Ashe baya
nan,Cikin Ladabi Mallam Inuwa ke Fadamata Tun Shekaran Jiya ya kaishi kano gidan
Abokinsa da Suke Koyarwa Tare Uncle Aminu.

Anty Rahila batayi Mgana ba illah Gyada kanta datayi Ta sallami Mallam Inuwa ta
koma Ta koma Cikin Gida Muktar kadai Ta sanarmawa Saboda ya Damu da Bellon sosai
Lokacin Datace yana Kano sai da kwalla ta Taru Acikin Idanuwansa Cikin Tsausayi da
Rauni yace"Rahila Har Wani Aboki yafini Awajen Bello,da zai zabeshi Fiye dani.."?

Anty Rahila Tace"Bai Fika ba Ammh yafika kiyaye Bacin Ranshi Shiysa ya Fifitashi
Akanka.."Shuru yayi yana Jinta kafin yace"Toh ya Zanyi Rahi..."

Gyara Zama Tayi kafin Tace"Kana da yarda zakayi Tunda bayason Hada Komai Dasu Toh
kaima ka koyi yadda zaka Nisantashi dasu..."Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin
yace"Shikenan U took later..Gobe ina Hanya.."Daganan Suka Cigaba da Tattauna
Maganar kuma Duk Akan Bellon ne.
Daada ma sai Daga baya Taji Daga Bakin Bellon Daya Kirata Awaya Daada Batace komai
ba Ammh Tace ya Dawo Gida Shi kuma yace bazai Dawo ba Sai Su Zubaida Sun Tafi,Daada
bata kara matsamai ba Domin Tunda yace Haka toh bazai Taba Chanza Ra"ayi ba.

Su Zubaida kuwa Tunda Suka Fahimci Uban gayyar bashi Agidan Duk sai Gwiwansu Tayi
Sanyi Sati Daya da yin Haka Zubaida Tafara Wucewa gidan Yaya Hashim,Ta bar Zulfa
don Tace sai Sati na sama Aneesa ko Ajikinta Dadi ma Takeji Acikin Ranta Tana
Addu"ar Allah ya sa karya Dawo Domin Ita bata Kaunar Hada Inuwa da Bello Tsabar
yadda Ta Tsaneshi Toh Itama Zulfan bata kara Sati ba Tayi gaba Bayan Muktar ya
Cikata da Kayan Arziki Ta Tafi cike da Takaichin Wannan karon ma babu Wani Cigaba
Ta bangaren Bellon.

*****
Shiko Bello yana Tarauni Dake Kano Gidansu Uncle Aminu Wanda Ke Zaune da
Mahaifiyarsa Ammi da Kanwarsa Raihana Domin Allah yayima Mahaifinsa Rasuwa,Aminu
yaji Dadi Sosai Na Zuwan Bellon Duk da ba Zuwansa na Farko ba kenan Koda Aminun ya
ganshi Cikin Damuwa bai matsamai da Mgana ba sanin Halin Bello marason Hayani sai
ya kyaleshi yana samun Hutu Abunda dai ya Tambayeshi Shine game da Ciwon Hannunshi
Ammh Har yau bai ce Masa Komai ba Shi kuma sai ya kyaleshi Sanin Halin Mutumin
Nashi.

yana Kanon batare da Sanin Kowa ba yagama ma Aneesa Duka Shirin Komawa Kwatar-
kwashi SS1 ta Waya Sukayi Mgana da principal din makarantar Saninshi Amkranta da
Kuma Tasarinshi yasa ba Wani Bata Lokaci ba komai ya kamallah Saboda Haka kamar
Zuwan Farko Aneesa zata Dawo Tare da Sauran Sabbin Daliban SS1,kwana Goma yayi
Agarin kano Kafin Su Dawo Abuja Shida Uncle Aminun Ammh bayan Daada Ta Kirashi Tace
sai ya Dawo Domin Su Zubaidan Sun Tafi

Aneesa Zuciyarta ta Kusa Bugawa Sanda Tayi Tozali da Uncle Bello da Uncle Aminu
Lokaci Daya Cikin Falon Daada Saboda Razana ko Gaishe su batayi ba,ammh Saboda
Salon Mugunta Irin na Uncle Aminu bai Duba Tana Gida bane Haka ya Kirata ya saka ta
Kneel dwon Gaban Daada ya murdemata Kunni ya Dankwasheta akai da Cewar Bata
gaisheshi ba.

Saboda Takaichin Abun Sama Ta Haye Bedroom din Anty Rahila Taje Ta Kwanta Hibba na
Damunta da Surutu ta korata Shashen Daada Tana Kwance Tana Durama Uncle Aminu Allah
ya isa Wayar Anty Rahila Dake kan Dresaing Mirrior ta Dauki Tsuwa Da Sauri Aneesa
Ta Mike ta Isa ga Wayar ganin Wacce ke Kirane yasa Ta Dauka da Sauri nan B.kaita Ke
Fadamata gobe Jumma"a Zasu Shigo Abuja Ita da Ummanta Dayake An Daga bikin basu
samu zuwa Wanchan Satin ba Aneesan Naso Ta gayama B.kaita Zuwan Uncle Aminu Ammh
sai Ta Kashe Wayar Kafa Aneesa ta Buga Tana Kunkuni Ita kadai.

*How to pay....�?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?600...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?500 ne,VIP
�?1000, Single one �?300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*ANITHA*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*🅿�?9*

"Washegari Wajen Misalin Karfe 12:00pm na Rana Sai ga Wayar Security Din bakin Get
Zuwa Cikin gida Suna Tambayan Shin Aneesa Tasan Da Zuwan Wata Bakuwa Wai Bilkisu
Kabir kaita?Alheri ce Ta Daga wayar bata Basu Amsa ba,Sai da Ta Shiga Dakin Daada
nan Ta Iske Aneesa Cikin girmamawa Take Sanar da Ita ko tana da Wata bakuwa..? Ko
Sauraranta Aneesa batayi ba Ta Fice da Sauri Cike da Murna Akan Fuskarta Daada na
Mata Dariya.

Tana Fitowa Haraban Gidan Cikin Daga Murya tace"Plz Open d Get..."Tafada Cikin bada
Umarni,Jiki na Rawa Securitys Din bakin Katon get Din Suka Wangalema Direban daya
kawo B.kaita get Motar su kirar prado Baka ta samu Damar Sulalowa Cikin Gidan.

Bello da Uncle Aminu Dake Zaune saman Wasu Fararen Kujeru,Daidai Wajen Saman
Mension Din Bello Suna Hango Duk Abunda ke Wakana Aharabn Gidan,Bello yana sanye da
Riga da Wando Duka White ammh Rigar bata Da Hannu hakama Wandonsa 3quater
ne,Karamin Tebur ne Agabansu Dauke da Madaran Hollandian sai Farantin kayan lambu
da Ruwa,Gefe Daya Kuma Kafafun bello ne Farare Harde Saman Teburin ya maida kanshi
baya bisa Kujeran Dayake zaune Magzine ne ahanunshi yana Karantawa Ayayinda Shima
Aminu ke sanye da Irin Shigarshi Sai dai Shi Wayarsa ce Ahannunsa yana Faman
latsawa Shiyasa Yafi Bello Lura da Filin Haraban Gidan Wando Sojoji ke ma Safa da
marwa.

Uncle Aminu Idonshi na kai Sanda Aneesa Ta isa da Sauri Ta Budema B.kaita bayan
Mota ta Fito Tana Sanye da Shadda Ruwan kasa Tayi Dinkin Riga da Sikat an mata
Stone Work karamin Gyale ne Akanta Sai Flat Shoe dinta kalan Kayanta Cike da Ihun
da Suka Saba Suka Rumgume Juna Harda Tsalle kamar Wasu yara,Mallam Inuwa Dake Kofar
Barayinsu Daya ke Dakunansu na Kwana yana Ta baya da Sauri ya kariso Wurin Yana
Washe baki yake Fadin"A,"ah Maraba Hajiya Bilkisu.."

B.kaita ta saki Aneesa Tana Fadin"Yauwa Baba Inuwa Kwana biyu..? Yana Dariya
yace"Wlh kuwa anzo lafiya..? Tace"Lafiya lau Alhamdulillah.."Aneesa Tace"Baba,Hira
baza Tayi Dadi ba ba S.jibiya.."Mallam Inuwa ya kada kai kafin yace"Ayyah Sai dai
in kun Hadu Amkaranta,."Da Sauri Aneesa Tace"In sun Hadu zaka ce Baba ka manta ni
Na bar Mkrantan nan Kenan.."Tafada Tana Mirmishi gefe Daya Hannuwansu Sarke da Juna
Ita da B.kaita.

Yar Dariya Mallam Lawal yayi kafin yace"Au hakane fa,Toh sai dai kuyi mgana ta Waya
."Yafada yana Kunshe Dariyanshi Shida B.kaita Cikin Farinciki Aneesa Tace"Insha
Allahu Baba Bari mu karisa Ciki.."Mallam Inuwa yace"Madallah Nima yanzu Zan Fita
zan kai Motarku Wanki ne.."Aneesa bata jishi ba Shiyasa bata bashi amsa ba.

Uncle Aminu Dake Zaune yana Kallonsu yace"Bello kalli kaga kamar Dalibarmu Bilkisu
Kabir kaita nake gani Tare Da Aneesa..?
Bai Dago ba Cikin Rashin kulawa yace"Tunda ka ganeta Ita din ce.."Daga Haka ya
Cigaba da Abunda yake batare Dayabama mganar Aminun muhimmanci ba balle harma ya
kai Duba Zuwa ga Inda yake Nuna mai.

Cikin Saurin Uncle Aminu ya Mike ya Isa Jikin karfen Daya ma Wajen Kwanya Cikin
Kaushin Murya ya Furta.."Bilkisu kaita.."Yafada da Dan karfi,Aneesa da B.kaita Dake
Shirin Shigowa Kofar da Zata Sadasu da Babban Falon Gidan Suka Dago a Tare cike da
Mamaki B.kaita tace"La Uncle Aminu Gud Afternoon.."Tafada Fuskarta na bayyana
Fara"a Domin Daga Inda Suke Tana Hango Uncle Bello Zaune Duk da Jaridar Dake
Hannunsa Ta kare Fuskarsa,Aneesa Ko cin mgani ta Fara Tana Kauda kai Aminu na Lura
da Ita Cikin Ranshi yana Fadin"Dis gal kamar Wata majanunuwa.."

Cikin Sakin Fuska yace"Afteernoon Too Bilkisu How are u.? Ya Hutu..? Fatan zaku
Dawo mana Ku Dora Daga Inda Kuka Tsaya ko .? Cikin Jin Dadi B.kaita tace"Insha
Allahu Sir Nida Salamatu Jibiya nan zamu Kareta,Anee ce dai tace Tabarmu
Uncle.."yar Dariya yayi kafin yace"Haka tace muku..?karya Take Itama Kwatar-kwashi
Dolenta ne.."

Yafada yana Kallon Aneesan Wacce Ta Dago Tana Hararanshi Ta kasan Ido Jin Abunda
yace,ganin Haka yasa yace"Ke Uban Wa kike Harara..? Baki da Kunya ko.? Bar ganin
Ina Gidanku Kina ganin Sojoji na yawo har yanzu ina Mtsayin malaminki ne sai na
Sakko na Chasaki yanzu nan.."Yafada yana Nuna ta baki Ta Tura gaba Tana Kunkuni
Baki ya Rike kafin yace"Oy Say Srry Uncle.."

"Bakaken Idanuwanta Ta Dago Tana kallonshi Lokaci Daya Tana Wani bata Fuska Fara
Saukowa yayi Daga Step din yana Fadin"Dont let me to come Down Aneesa u will be In
Troble.."Yafada Cikin Kakkausan Murya Bikisu ce Tayi Saurin Damke Hannun Aneesa
Tana kallonta ganin ya kusa karisowa ne ya sanyata Rankwafa Tana Fadin"Srry Sir..."

Tafada Idanuwanta Sun kawo Kwallah Tsayawa yayi kafin yace"Bacemin Daga gani Bush
gal kawai.."Jin Haka yasa Aneesa Ta Fizgi Hannun B.kaita Sukayi gaba bakin nan yayi
gaba Sai Allah ya isa Take Durama Uncle Aminu B.kaita na Dariya Kasa Kasa,Bello
Dake zaune gefe Ya Dago da kansa Daga Karatun Jaridar Dayake yana Fadin"Kana Son
saka ma kanka Damuwa Wani Lokacin.."Yafada yana Kallom Aminun wanda ke kokarin zama
Kan Kujeran Daya Tashi.

Tabe Baki Aminu yayi kafin yace"Name fa Sarkin Tsari..? Mirmishin Rainin Wayau
Bello yayi mai kafin yace"Eh mana banda Jama kai Rainin Ina Ruwanka da Aneesa da
kawarta Look nan fa ba Kwatar-kwashi bane Sakaci kadan zakayi yarinya ta zageka
ballatana Dat Nonsees Aneesa bata ganin Girman Kowa.."Yafada Lokaci Daya yana
Mikewa Cikin Kufuluwa Uncle Aminu yace"Ina Ruwanka..It only I know ina da Barkwanci
da Sakin Fuska Kuma yarinya Ta kawomin Raini Wlh Na zaneta,Nafi dai Wanda ko Agida
bai Da Dadin Sha"ani.."Waigowa Bello yayi yana Kallon U.Aminu kafin
yace"Aoh..Better.."Daga Haka ya Shige Ciki ya barshi nan yana Binshi da Harara

Acikin gida Kuwa B.kaita yau Taga Anty Rahila,Hibba da Daadan Da Aneesa Ke basu
Lbri Dayake Wannan ne Zuwanta na Farko gwara S.jibiya tazo Sau Daya Itako Aneesa
Gidan su B.kaita Tataba Zuwa A katsina sanda Sukaje Gidan Abba Kabiru Ita da Anty
Rahila da ya Muktar sai Ta Rokeshi ya saka Direba ya kaita,B.kaita ta Jinjinama
Daular da Aneesa Ke Ciki Duk da Kowa yasan Matsayin Muktar din Afalin kasan nan
Ammh Acikin Ranta Tana mamakin Mr.Bello yadda bai Dauki Duniya Abakin komai ba.

Kafin kace kwabo Ancika B.kaita da Kayan Makuleshi da Abinci Agabanta sai da Sukaci
Sukayi Nak Ita da Aneesa kana Suka Koma Dakin Aneesan Suka Dasa Sabuwar Hira,sallah
kawai ke Tadasu Har Dare,lokacin da Suka Fito Har Ya Muktar ya Dawo nan Aneesa Taje
ta gaisheshi Ita da B.kaita har yana Zolayan Aneesa Da cewa ko Zata koma Zamfara
ne..? Da Sauri Tace"Ta yafe..Akasa Dariya Gabadaya,B.kaita nan ta Kwana Saboda Ta
Kira Ummanta Ta Fadamata So Direbansu shi kadai ya koma Sai Washegari Ranar Biki
Anty Rahila tace Aneesa ta Shirya Ita da Hibba Su Raka B.kaita gidan Biki Haka ko
Akayi Su Aneesa Yan mata aka Chaba Ado,Aka Wuce Mallam Inuwa ya kaisu chan Maitaman
bayan Anty Rahila da Daada Sun Cika B.kaita da Kayan Arziki Tatafi Tana Murna Da
Kuma yabon karamcinsu.

Haka Itama B.kaita achan Gidan Sha"anin sai Nuna Aneesa Take Amatsayin Kawarta
Ummanta sai Ita zata saka Dasu Take,nan Suka Wuni sai Yamma kana Mallam Inuwa yazo
ya Daukesu Suka Koma gida suma bayan anciko Musu kayan Biki niki niki,nan Sukayi
Sallam Da B.kaita Domin Washegari da Safe zasu koma Suka Rabu Akan sai Sunyi yawa
bayan B.kaita tace agaida mata da Uncle Aminu da Kuma Mr.Bello bata Rai Aneesa Tayi
kafin tace In kin matsu kizo da kanki Haka Suka Rabu Cike da Kewa Tun bare ma
Aneesa Ta Datakejin kadaice bata da abokin Hira sai Hibba ko Daada.

****

*KATSINA*

_Area:Kofar Laura_

ABBA KABIRU HOUSE*

Cikin Fada Abba Kabiru yace"Rufemin Baki Sakarya Kedai kice baki da Dubara Irin
ta Yan matan Wannan Zamanin ammh Har ace Wani karamin Halitta bello ya gagareki..?

Yafada cikin kufuluwa da Jin Haushi Baki Zubaida Ta Tura kafin tace"wlh Abba nayi
iya bakin kokarina Ranar fa Kusan Targadi yayi min fa,yace mudaina Kusantoshi shi
ba dan"uwan mu bane Bamu Hada komai Dashi ba.."

Hajiya karima Dake Zaune gefen Zubaida bisa Daya Daga cikin Lumtsuma lumtsuman
Royal Chairs din Dake Falon Ta tabe baki tace"Wai Alhaji Tsoron yaron kake ji ne
hala..?Kake ta wannan Kumfar bakin..? Yarinyar nan tana iya bakin kokarinta ammh ko
yabawa bai Tabayi ba,Hakuri zakayi ku kyaleshi Tunda Bakar Zuciyarsa Haryanzu
batajin zata iya yafe muku.."

Abba Kabiru ya mike yana Saba Babban Rigan sa yana Fadin"Lalle baki da Hankali
Karima Taya zan kyaleshi ai Mafita Daya na samu Sa"ar da zai zama Suruki na,Shine
kadai zai sa ya yafemana laifinmu na baya kamar yadda Dan"uwansa bai Rikemu ba,Kina
ganin yanayin Yaron nan Wlh sai ya iya Makamu Kotu nida garba kuma Tsaf za"a Daure
mu Tunda Mun Aikata..",

Hajiya karima Ta Mika hannu t Kwantar da Zubaida kan Cinyarta Tana Fadin"Kaima
kasan Bazai yi Haka ba,Ai dolensa ne ku nashi ne,Kuma Muktar bazai barshi yayi Haka
ba.."Zubaida tayi Saurin Cewa"Umma Toh Shima Daddy Tsoron Uncle Bellon yakeji,Duka
gidanan Suna Sonshi bamai Dauremin gindi Sai Daada,Kiga fa Ko Fadama bamai son yi
mai Umma gaskiya suna Sonshi Sosai.."

Abba Kabiru ya Tsaki yana Fadin"Nasani Shi nake gudu ammh ke karima baki
ganewa,wannan Tsohuwar Bufullatanan nan Dama Tun Farko ni batamin ba Inama Tunanin
Ita ke Zuga Bellon ba Wani ba,ke ko Zyciyarsa kaf bana Zuru"armu bane chan ya
kwasoshi Wajen Dangin Fulani,kinsan su da bakar Zuciya da Mugun Abu.."ya karishe
Fada yana Rike kugu Cike da Jin Haushi bata samu Zarafin Mgana ba,Abba kabiru ya
Cigaba da Fadin

"umh nifa Abun Daya Nake gudu karima,Kada Wannan Shegiyar Zulfa kinsan Ita da
Uwarta makirai ne Suje su karkatar da Hankalinshi ya Aure ta Ai ni na Kade Haduwa
zasuyi da Garba su yakeni na Shiga Uku.."

Hajiya karima tace"Haba Alhaji yama za"ayi Haka ta Faru Ai Alhaji garba in bai
Taimake ka ba, bazai yake ka ba Sai dai Ita Hajiya Sahuran don bata da Kirki kuma
indai bai Auri Zubaida ba sai dai kowa ya Rasa.."Jinjina kai yayi yana Fadin",Shine
mgana gaskiya..."

Kasim Dake Kofar Falon Tundazu ya Kariso yana Fadin"Abba nifa bana ganin laifin
Bello kune masu laifi Tsakani ga Allah baku kyauta ba kuma ko nine irin matakin da
zan Dauka kenan ."Yafada yana zama kujeran Datake Kusa data Inda Hajiya karima take
zaune ita da Zubaida.

Harara Abba kabiru ya Laftamai kafin yace"Dillah rufemin baki Sakarai kawai,Ai
Hashim yafika kirki Yana Kokarin Zuwa Gidan Muktar din yana Tusa kanshi Duk Domin
Asirinmu ya Rufu Ammh kai baka ma Zuwa balle ma na saka ka alissafi.."Kasim dake
Sanye da Riga da Wando Navy blue Na kamfanin Armani,yace"Ai ina Kiran Ya Muktar ta
Waya kuma Abba bana samun lokci ne kaima ka sani.."

Hannu ya Yarfa yana Fadin"Matsa chan ka bani Waje kaima baka da amfani ko Abota sai
ku kulla Dashi Bellon mana Tunda Dama da kadan ya Girmeka mu samu Asirinmu ya Rufu
kada yaron nan Yace zai yi Shari"a Damu Watarana.."Yamutsa Fuska Kasim yayi kafin
yace"Nifa Abba bana son Raini ni,kaga yadda gayen nan yake wani cin mgani da Isa
Wani Lokacin fa bai ma kaunar Hada Iska Dakai fa,Ni kuma Zuciya gareni ban Iya
Juran Wulakancinsa Tun Kwanaki Dana Taba Kiransa Ya Tambaya ni wanene Inafa cemai
nine kasim Dan Wajen Abba kabiru ammh Gayen nan yace bai sanni ba Kuma kada nakara
Kiransa ya yanke Kiran.."Yafada Cikin Zafin Zuciya.

Shuru Abba kabiru yayi Kafin yayi Mgana Hajiya karima ta Rigashi da Cewa"Sai fa
Hakuri Alhaji Ammh kam kunbi son Ronku,Tsakani ga Allah Ko bakomai Muhammed
Dan"uwanku ne Da Kuke
Uba Daya kowa yaji Aikin Da Kuka yi sai yayi Tir daku.."Wata Uwar Harara ya zabga
mata kafin yace"Rufemin baki Munafuka Ina ce Lokacin bada Shawarki nake amfani
ba.."cikin Daga Hannu tace"A"a Wlh ni Haihuwa nace Ku Hana Hassatu bance ku kashe
Rayu ka ba.."

Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace"Shedan ne,Da kuma Kaddara Kuma duk Garba ne yaja
Shi ya kawo Shawaran Gashi mun cika burin mu na Kauda Muhammed Da matarshi,Munkuma
yi Nasaran Kwatan Dukiyan Ammh Sai gashi komai ya lalace Karshenta ma Namu ya"yan
ne ke Ci karkashin nashi ya"yan da Muka Tozarta Allah kenan.."Yake Fada yana Sauke
Numfashi.

Kasim yace"Abba Tunda kun Tuba Shikenan,Shima Ya Muktar din ai ya yafe muku Shima
kuma Bellon komai zai Wuce Nan da Lokaci kadan.."Zubaida tace"Allah yaya Daada nan
ce ke Bala"in Sonshi Shida Aneesa ko Guda bata kaunar ya Tabasu.."

Cikin Mamaki Hajiya karima tace"Wata Aneesa kuma...? Tafada Tana Wasa da gashin
kanta Gyara kwanciya Zubaida Tayi kafin tace"Kanwar Anty Rahila ce Daddy muktar ya
Daukota Daga Borno Shegiyar yarinya ce Ta nan sai Zuba iskancinta take Ko Ballon
bata Shakka,Mkrantar Dayake koyarwa ma Take ,Tare suke Tafiya kuma in sun samu Hutu
su komo Tare.."

Baki Abba kabiru ya Rike kafin yace"Kaji ko... ? Itama Matar nashi So Take ya Auri
kanwar nata Kinsan Yan Bornon nan ba Kyau Tuni zasu ja Hankalinsa.."Kasim Dake
zaune yayi Dariya kafin yace"Kai Abba Daga mgana sai kace zai Aureta.."zubaida
tace",Anya Abba basa ga maciji fa yadda kasan Annabi da kafurai Shi kadai ke iya
mata Hukunci agidanan Daada Tayi Shuru ko Anty Rahila bata iyawa da Fitinar Aneesa
kamar Mai Bugun Aljanu.."Dariya ta kara Kama Kasim Cikin Nishadi yace"Niko har naji
ina Sonta Domin ina son mace mai Tsiwa.."

Hararansa Hajiya karima Tayi kafin tace"Toh mara kunya.."Mikewa yayi yana Sosa keya
yace"Umma,Abba ni zan Fita zan Shiga Cikin garin Wajen Abokina Shamo.."Hajiya
karima ce Kadai Tace mai adawo lafiya Shiko Abba kabiru komawa yayi ya Zauna yana
Wani Nazari Acikin Ranshi.

****

_GRA-Katsina_

*ABBA GARBA HAUSE*

Suma Duka iyalan gidan Suna Zaune A kayatattacen Falon na Gidan Abba garba,Harda su
Hamdiya da Ummu salma da Inna Rukayyah Wacce Suka zo garin Jiya,kuma Sunfi Dasawa
da Abba garban Shiyasa Take Sauka agidanshi kuma Matar Shi Sahura Wacce Suke Kira
Mama Sahura,Makiran Macece Ta iya Duniyanci Tasan yadda Take Hillatan Mutum Shiyasa
Kaf yan"uwan Mijinsu sunfi yabonta Fiye da Karima Umma kenan,Shiyasa basa zama Waje
Daya Duk da Abaya sunyi Amintakan Munafunci Tunda Rabuwan Mazajensu yazo kowacce Ta
Koma Tsagin Mijinta Shiyasa Inna Rukayyah ke Sauka gidan Abba Garba kuma ko Taje
gidan Abba kabirun Umma bata mata Wani karban Mutumci.

Zulfa ce ke Basu lbrin Irin Wulakancin da Bello yayima Zubaida sai Dariya Suke Sha
Tun barema Mama Sahura Dake Mirmishi Cikin Kissa Tace"Kash..Banji Dadi ba.."Tafada
Tana kallon Inna Rukayyah Wacce Ta kada kai Tana Fadin"Ai ni Wlh naji Dadin
Hakan,Duk da Muma bamu Tsira ba Wajen Ja'irin yaron nan ammh gwara yayi mata Haka
din,ko ba komai ni Nafison In ma Auren Bellon zaiyi ya Auri Zulfa Saboda Daga
Kariman har yarta basu da Kunya sam."

Cikin Kissa Mama Sahura tace"Ah inna ba komai Ai Duk Dayane da Zubaidan da Zulfan
Duka Namu ne,Fatanmu Dai Shine ya zabi Daya Cikinsu yadda bazai Auro na Waje Balle
har tazo Taji Abunda ya Faru ta Zugashi ya Dauki Mataki bq.."Inna Rukayya ta
Girgiza kai Tana Fadin"Hakane...Ammh ni nafi son ya Daidaita da Ita Zulfan,Ai
mganar Gaskiya Su kabiru sunyi kuskure Babba,Rudin Shedann Dana Zuciya ya Debesu
Kuma Tunkafin Su Fada da bakinsu mutane Su ke Zargi Saboda yadda Suka Hau Dukiyar
Marayun,Kinga fa Haryanzu chan Jikamshi Gulmar Dake Tashi kenan.."

Mama Sahura tace"Umh Inna Wlh Alhaji baida Tunanin Kashe Rai,Duk Yaya kabiru ne
Yaja Shine mugun Shi ya Dinga Forcing Dinshi har ya amince,Ammh Haryau kukan Nadama
yake Yana kuma ganin Laifin Yaya kabirun Daya Dorashi kan Wannan Kuskuran.."

Inna Rukayya tace"Hakane Ai Shi kabiru akwai Hange Hange ne,Allah dai ya kyauta don
ma Mun Samu Shi Babban bai Dauki Abun da Zafi ba Shidai Bellon Shine Naga kamar
Yana da Wani Shiri ne.."Mama Sahura ta gyara zama Tana Fadin"Shine ai Inna Mukesi
mu Jawoshi ajikinmu yadda ko Yana da Niyyar Wani Abu Sanadin Hada Surukanta damu
Dole zai Hakura,Ko Zulfan ko Zubaida Duk Wacce ya Aura Insha Allahu Shima zai Manta
komai.."

Jinjina kai Inna Rukayyah Tayi kafin tace"Hakane kam..Toh Allah ya bada Sa"a Kafin
na Koma zanje Abujan Insha Allahu..."Da Sauri Hamdiya tace"Inna zan biki Banta ba
zuwa ba.."Ummu Salma tace"kin ma isa Wlh Dani za"a Je.."Tafada Tana Hararan
Hamdiyan Dariya Inna Rukayyah Tayi kafin tace"toh duk naji Gabadayanku Zamu Tafi Ba
Dadewa zamuyi ba bai Wuce mu kwana biyu ba Dagachan zamu koma kano Saboda Hutu ya
kare.."Jin Haka yasa Suka kama Murna Zulfa na gefe tana latsawa waya cikin Mirmishi
tace"Daddy bai da Mtsala Uncle Bello ne Mai Damuwar Inna Shifa bai kaunar ganin
Wani Daga Cikinmu Agidanman Saboda mu Har yaji yakema Abuja Mutum kamar Zuciyar
kafiran Farko.."

Inna Rukayyah tace"Nagani Zuwana na Farko Diban Albarka da Yaron nan yamin kamar
nayi kwallah ,muktar din na mai mgana ya gaisheni Wlh ko Waigowa baiyi ba ya Fice
Da Hanzari kamar yaga kashi.."Tafada tana Rike baki Mama Sahura tace"Hmm Haka fa
yakema Kowa Ko Su Alhajin basu Tsira ba baya gaishesu..."

Inna Rukayya tace"Gadon Zuciyar Bakaken Fulanin nan ne na Dangin Uwarsu.."Mama


Sahura tace"Wlh Haka Alhaji yace.

Daga haka suka Cigaba da Hiransu Sama sama Duk dai Akan Bello ne da Irin Rashin
Mutuncin Dayake ma Duk Wanda ya Fito Daga Tsatson Abba kabiru ko Abba garba.

*******

Kwanci Tashi babu Wuya Awajen Allah gashi Har Hutu ya kare,Tuni Daliban GGUSS
kwatar-kwashi Sun koma Harda Wasu Daga Cikin yan Jss3 sun Dawo SS1 ciki Harda
B.kaita Ita da S.jibiya Tun kwana uku da Yin Resume Suka Dawo Mkrantan Amatsayin
Senoirs.

Aneesa ko bata da Masaniyar Komai,Duka gidan ba Wanda Yama Bello Mgnar Aneesa,ganin
Tun Satin da Wuce Mallam Inuwa ya maida sa Sch Din sai Kowa ya sakankace kan,Bello
ya Bar Aneesa Ta cigaba da Jeka ka Dawo,ko da Su B.kaita suka ga Me bello Jikamshi
ya Dawo Shi kadai sai Suka Cire rai kan Aneesa baza ta Dawo ba jidda madaki da Suka
Dawo suka Iske Suna Neco sun kusa gamawa Har Dakinsu Tazo Neman Aneesa suka Sanar
da Ita Aneesa bazata Dawo ba,Hakika Yan Ajinsu Sun Dawo Da yawa yayinda Wasu kuma
Basu Dawo ba,Dalibai dadama in Sukaga B.kaita da S.jibiya Sai sun Tambayesu Aneesa
Su kuma Cikin kewa Suce Anee bazata Dawo ba Wasu Dayawa Sunji Dadi wasu kuma basu
Ji Dadi Ba Domin Aneesa Ta zama Cele by Force Ackin mktantar Sabida bakinta da Kuma
Tana kanwar Da Handsome man Mr.Bello jikamshi.

Aneesa Har party Ta Hada Bayan Komawar Bello Makranta Ita Da Hibba Suka chashe,Ashe
Tungunne bata kare ba Duka Duka Satin Bello Daya Da Tafiya yama Ya Muktar Waya kan
Ashiryama Aneesa kayan provisin da Abun Bukata Ranar Monday zai zo su koma Tare,Ya
Muktar Cikin mamaki yace mai"Na zata zaka barta ta Fara Jeka ka Dawo anan Abuja.."

Cikin Gimtse Fuska Bello yace"No...Nan zata Cigaba Har ta Kamallah.."Daga Haka ya
Datse Kiran,Ya Muktar Kuwa kai ya girgiza kafin yace"There is a War In Aneesa Taji
Lbri ."Bai gayama Kowa ba sai Anty Rahila Wacce Ta nuna Taji Dadin Haka Ita ke
Fadama Daada,Wacce Har Awaya Ta Kira Bellon Yana Jin Mganar Aneesa ne yace"Wlh
Tallahi Daada...Mgana Daya bazan Chanza ba Aneesa Bazata bar Kwatar-kwashi ba sai
ta kamallah Secondry Duka Tukunnah.."Tunda Daada Taji Haka batama bata ma kanta
Lokaci ba Ta Kashe Wayarta.

Anty Rahila da Aneesan Direba ya Daukesu Suka Shiga Mall Suka mata Siyayyah ammh
Data Tambayeta sai tace Borno Zata Tura ta ta musu kwana Biyu,Aneesa bata wani
soZuwa barno ba Saboda Takuran ya Ali,gashi ita kuma bata wani Shaku da mama
Falmata ba Tamafi Shakuwa da Hajiya yana,Ga dai Wanda Tafi Shakuwa Dashi Sosai nan
Marigayi Alhaji Bukar Bulama...

Haka dai Suka Dawo Gida Aneesa na Kuncin Zuwa Borno,Daada da Anty Rahila ba Wanda
yace mata Kanzil,Ranar Lahadi kuwa sai ga Bello ya Diro Abuja Shida Uncle Aminu
Wanda Ita Aneesan bata ma san Zuwansu ba sai Wajen yamma Tana Falon Daada Suka
Shigo Tunda Ta gansu sai Jikinta bai Bata ba,Tana gaishesu Aminu ne kadai ya amsa
Bello Cikin Tsare gida ya kalleta kafin yace"Ki Tsefe kanki kiyi Kitso ki kuma
Shirya Abubuwanki masu amfani gobe zamu Wuce Dake.."

Aneesa Ta zaro Ido Waje kafin tace"Zuwa ina kuma...?

Harara ya sakarmata kafin yace"Zuwa Makranta.."Wani Zabura Aneesa Tayi kafin ta


Dora Hannu Akai ta Zumduma Ihu,Wanda Sai da Suka Toshe Kunnuwansu Daada Dake Daki
Ta Fito da Sauri Tana Fadin"Lafiya...?

Tasamu Amsan Tambayanta ganin Aneesa malale Akasa Tana Kuka da Birgima Tana Fadin
Ita babu Inda Zata Tafi sai dai Akasheta.."Uncle Aminu gefe yaja Aranshi yana
Fadin"Yarinyar nan Yar bala'i ce.."Shiko Bello Belt din Kungunshi ya Fara Warwarewa
yana Fadin"sai dai ki Mutu ko..? Lalle ko zaki mutu da duka,kinga sai na Dauki
gawanki na kai makarantan Bushi girl kawai.."

Zaku ga chanjin kudin Novel Daga sama zuwa kasa hakan ya faru ne bisa Roko da kuma
korafin wasu Daga cikin Fans dinmu,na cewa ana cikin wani hali na rashin kudi ne
Duba da Kaddaran wannan yanayin Da Allah ya aikomana Shiyasa muka zauna muka ga ya
kamata mu Duba ku Domin ko bakomai kun Nuna mana Hallacci da kuma kara wajen Siyan
Duka Novels dinmu Muna godiya sosai Allah ya saka da alheri Ameen
*How to pay....�?200 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?400...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?350 ne,VIP
�?600, Single one �?200 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*ANITHA..*

8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*


_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞

*🅿�?10*

""Daada ce tayi Saurin Rikemai Hannu Tana Fadin"Kul karka Tabata...Ka barta Taji da
Abunda ke Damunta yarinyarnan tace batason makrantan nan Bello mezai Hana ku
kyaleta Tunda ba Mkarantan Shiga Aljanna bace.

Tafada Cikin Fushi,Bello ya kalleta kafin ya maida Kallonsa kan Aneesa Dake kara
Saka Ihu Tana wani Fizge Fizge kafin yace"Dama so take akyaleta ta Dinga zama kara
zube ba karatu,Ammh ta iya Rashin kunya ko..?toh Wlh bari kiji In kinga baki Tafi
mkranta gobe ba,kin mutu ne kafin gari ya waye Abunda zai Dakatar Dani Kenan.."Yana
gama Fadin Haka yayi kwafa bayan yaja Hannun Uncle Aminu Suka Fice Daga Falon Daada
Ta bisu da kallon Mamaki da Al"ajabin Zuciya irinta Bello.

Cikin Sigan Lallashi Ta Isa ga Aneesan Tana Fadin"Tashi Anee bar Kukan
hakanan,Megidan nawa ne In yayi mgana baya Chanzata sai dai kiyi Hakuri
kawai.."Aneesa Tatashi Zaune Tana Share Kwallah Cikin Tura baki Da bata rai Tace"Ni
bazan Je ba Daada..Ko za"a kasheni bana so akyaleni..."Tafada tana Shure Shure da
kafanta kamar Wata Yarinya.

Shuru Daada Tayi mata Tana Binta da Kallo bata samu Zarafin Mgana ba Anty Rahila ta
Shigo Ganin Aneesa Kwance kasa Tana Kuka Harda Majina yasa Tasan Kwanan Zencen
Domin Kafin Shigowarta Sun Hadu dasu Bello Tsuke Fuska tayi ta karisa Gaban Aneesa
Bayanta Hibba ne Cikin Haushi Tace"Meye Haka Aneesa..? Dallah tashi kibama Mutane
Waje karatu fa zaki Tafi ba Wani Waje ba,Ammh kin Zauna kina ma Mutane kukan
Banza.."Aneesa bata Saurareta ba sai ma kara saka Kuka Datayi,Ran Anty Rahila ya
baci Ta kalli Daada Tana Fadin"shikenan Karki Fasa Don Ubanki,Ya Ali zan kira na
Sanarmawa Daga za"a Taimake ki zama Mai ilimi ko wa kika ga yana zama ba
Ilimi.."Tafada tana Juyawa Da Sauri Daada Tace"A"a Rahila Karki Kirashi Kyaleta
Zata Hakura.."Da Sauri Aneesa Tace"Wlh bazan Hakura ba..Ni bazan Koma Ba Sai dai ko
In Ya Alin yazo ya Kasheni.."Tafada Tana kara sakin kuka yiyiiii..

Takaichi Ya kama Anty Rahila takalli Aneesa Tace"Toh Wlh bazan zauna Dake ba Tunda
kika ki Makranta sai dai ki koma Borno Kuwa.."Tura Baki Aneesa Tayi kafin Tace"Ba
inda zani Wlh Ina gidan nan.."Tsaki Anty Rahila Taja kafin tace"Baki isa ba...Tunda
bakison karatu Toh Borno zaki koma Ya Ali ya samu Wani ya Aura miki Shi Tunda Kika
ki Karatu Dole ki zauna zaman Aure..."

Kara Mikewa Zaune Aneesa Tayi Idanuwanta Duka Awaje Tace"Aure Kuma Anty Rahila..?
Hararanta Tayi kafin tace"Eh Indai bazaki Koma Mkranta ba Toh Tabbas Aure Ya Ali
zai miki kin manta mganarshi Ta karshe..."Shuru Aneesa Tayi Tana Kifkifta ido Daada
na kallonta kamar Tayi Dariya sai ta kanne Cikin Hawaye Aneesa Tace"Ni bazan yi
Aure ba.."Tafada Cikin Tsawa Zakuda Kafada Anty Rahila Tayi kafin tace"Toh ki zabi
Daya ko karatu ko Aure.."Jin Haka yasa Aneesa Ta Mike Tana Fadin"Ni dai Wlh An
Cuceni Allah ya sakamin.."Tafada kafin ta Zura da Gudu Zuwa Cikin Bedroom dinta
Tana Kuka Daga Daada Har Anty Rahila Dariya Suka Kwashe Dashi kafin Anty Rahila ta
Fice Tana Fatan Allah ya kara Shirya Aneesa.

Anty Rahila na Komawa Dakinta Ta Iske Missed call din Anty Nafee,Nan take ta bi
bayan Kiranta nan Suka gaisa Shine Take Tambayanta Ina ta Shigane Take ta Kiranta
bata Daga ba..? Nan Anty Rahila ke bata lbrin Diramar Aneesa.

Tsaki Anty Nafee Taja kafin tace"Kema Rahila kinso sakama kanki Damuwa ne,Ko Su Ya
Ali Aneesa Ta gagaresu ballatana ke,Kawai ku Tarkato ta Tadawo Gida Tunda Taki
karatu Su Ya Ali su samu wani Garaugarai Su Auramata taje chan Ta karata Tunda Bata
da Mutumci.."Tafada Cike da Jin Haushin Aneesan Domin Tana Bakinciki yarda Rahilan
Ta Dauki Aneesa Taso Ace Sanah Dinta Rahila ta Dauka Domin Duk Ciki batakai su
Karfi ba Mijinta bai da Wani Hali Sosai.

Mirmishi Anty Rahila Tayi kafin tace"Kayya Anty Nafee,Kema kinsan Duk Wanda yama
Anee Aure yanzu Wlh yajama kansa Domin karamar Bazawara zata zama,Bajin mgana take
yi ba Yanzu dai Dole ta koma Makranta Bello ne Daidai da Ita.."Tafada Tana Dariya
Tabe baki Anty Nafee Tayi kafin tace"Hmumm kamar Ta koma Sakara kawai ta samu gata
bata sani ba,In Da ace Sanah ce kika Dauka Rahila ba Ruwanki da Damuwa kindai Santa
yarinya ce mai Natsuwa kamar Uwarta Rahila.."Tafada Tana yar Dariya,Tsam Anty
Rahila Tayi kafin tace"Ammh nake ga Da Aneesa da Sanah Duk Dayane Awajena Anty
Nafee,Kuma karki Manta Aneesa Kanwarmu ce Auta take ga Baba kuma kafin mutuwarsa Ya
bamu Amanarta ne,in muka barta tayi kukan Maraici Allah zai Tambayenmu. "

Tsaki Anty Nafee Taja kafin tace"Toh..Toh Uwar Tsari da Mgana barni Haka,Muyi
mganar dana Kiraki Saboda Ita bana Bukatar Jin Lbrin Aneesa.."Tafada kafin ta
cigaba da Sanar da Ita Dalilin Kiran bata damu ba Ta saki Jiki Suka yi Mgana Sanin
Halin Anty Nafee din Tun Farko bata so ta Dauki Aneesan Tama Nuna Jin Haushinta
Sosai,ko Mahaifiyarsu Hajiya Yana bata Nuna Jin Haushinta Domin Duka Dayane.

Aneesa kwana Tayi kuka Kamar Ranta zai Fita Babu Abunda ke Tadamata da Hankali sai
Dutsen nan da Kuma Debo Ruwa,Kai Gabadaya Mkrantan ma Bata Kaunarta ammh ya zatayi
Bello yasaka ma Rayuwarta Ido kya ce Shine Bukar Bulama,Ko ya Ali yadda yake mata
wani Abu,gani Take yafi kowa iya Shisshigi ,Toh in ba Haka ba,me Suka Hada Daga
Yayarta na Auran Wanshi Itafa ta gaji da Wannan Ikon Nashi Allah sa Tagama Mkrantar
Borno zata koma in ba Haka sai ya kara Sakamata Wani Tsaman.

Bata da yarda Zatayi Tana Kuka da Hawayenta Da Safe Aka saka Duka kayanta
amota,Bayan Tayi sallama Dasu Daada,Bayan Motan ta Shiga Ita da Uncle Amunu Shi
kuma Mallam Inuwa da Bello Suna gidan gaba Wanda ke Kallon Aneesa yana Kunshe
Dariya Ranar ko Ya Muktar batama Sallama ba gani Take Hardashi Aka Hada baki Aka
Maida ta Makranta Har Motarsu Ta Fice Daga Haraban Gidan Aneesa na Kuka Wiwi batayi
Shuru ba sai da Bello ya Waigo yana Kallonta Cikin Dakewa yace"In baki kama bakinki
ba...Zaki Sha Wuya ne yanzu nan.."..

Uncle Aminu kuma Kunnenta ya Murde yana Fadin"Bush gal,Banda Kauyanci Wata Mace
kiga tana Gudun karatu,Zaki zama mara amfani Ko Aure kika yi In dai baki da
Ilimi.."Tura baki Tayi Tana Kwallah Cikin Ranta ko Tana Fadin"eh din naji ina
Ruwanka Mugaye Allah ya sakamin.."Take Fada Tana Share Kwallah Tundaganan Tayi
Shuru sai dai lokaci bayan Lokaci Tana Share Kwallah..

Su S.jibiya sai dai Suka ga Aneesa Kwatsam Bayan Sun Dawo Daga Karatu Wajen karfe
2pm,wannan karon ma Hostel dinsu Daya Dr Karima part 1,Kuma Wannan karon ma Ajinsu
Daya SS1a,Lokacin da Suka ga Aneesa basu gasgata ba sai ta Ta dago Tana kallonsu
Tana Hararansu ga Hawaye na Zubomata ganin Haka yasa Suka Tabbatar da Aneesansu ne
Suka Ruga Suka Fada Jikinta suna Ihun Murna,Da Farko Taki kulasu kuka kawai Take
Sauran yan Ajinsu na Baya Duk Wanda yazo yama Aneesa mgana ko Kallonshi batayi Daga
Baya Taga ba Sarki sai Allah ta saki Jiki,saboda ganin su B.kaita Tare Suka Tayata
Shirya provision Dinta Cikin Lokarta Ranar ko pref basu Fita ba,masallaci ma basu
Fita ba Cikin Hostel Suka yi Shi Sai Washegari Aneesa Tafara Zuwa Aji Domin Suna
Zuwa Mr.Bello ya Damkamata Uniform dinta da Check dinta da Takalmin Mkranta da Jaka
da Littafanta Sabbi,Hakanan Ta karba ammh Cikin Ranta bata gode ba.

Ranar Mkrantan Kwatar-kwashi Ta Dauki lbrin Aneesa Bukar Bulama ta Dawo makarantar
Ranar ko Sai ga Jidda Tazo Wajenta Har Hostel tana mata Mitan Tana ta Sauraran
Kiranta Karya Aneesa Tamata da Cewa Nombar ta bace mata ne Shiyasa Marairaicemata
Jidda tayi Tana Nuna mata Irin Son Datakema Mr.Bello gashi Saura Sati Daya su bar
Mkranta Ta mata Kokari,Gyadamata kai Aneesa Tayi da Cewa ta bata da Zuwa Gobe Insha
Allahu zata san yadda Zatayi Da Haka Suka Rabu da Jidda Tatafi Tana Jin Dadi Itako
Anesa Mirmishin Mugunta Take mata na zakici Ubanki ne,Bayan Jidda ma Iri iritan Sun
Ta Zuwa Wajen Aneesa Suna mata magiya ita kuma tana Sakasu akwana Aranta tana musu
kallon Wawaye.

Wannan karon Seniors Suna Saman Bene ne,Shiyasa Sai Wahalan bata kai na Baya
ba,kuma ba laifi Sun san kan Mkranta sai dai Su kalli Sabbi Dauka in sunga suna
iyayi,barima New Comers Jss1 Dariya ma Suke basu kafin Sati Sunci Kwal Ubansu Ko
Debo ruwa ma Aka barsu ya Ishesu balle Muguntar Seniors Abun da Zai sake Baka
Mamaki Har Ss1 Dinsu Mr.Bello Shine Formaster Dinsu yana Lura da Aneesa Shiyasa Ko
Taso Tayi Wasa Batayi Duk da yanzu ya Rage Wata Muguntar Akanta ganin Ta Dan Fara
Hankali ba kamar baya ba.

Ranar da yan SS3 Zasu yi Candy,Ranar ne Dukkansu Suka Hau Saman Dutsen na Kwatar-
kwashi Suka Debo Gayyayyanki da Sauran Abubuwa wasu da Aljanu Suka Sauko Aneesa
Tace kamar Dole mezai aiketa ko Candy zasuyi Wlh bata iya Hawa Wannan Dutsen Domin
yana bata Tsoro Haka Lokacin Zafi in ya Dauki Zafi Wuta yakeyi Da Kanshi Lokacin
Sanyi kuma yana Fitar da Huturin Sanyi Wani Lokacin ma Bacewa yakeyi Kwata kwata ba
Aganinshi.

Da Jidda Ta Mtsama Aneesa da Magiya sai ta Mata karya da Cewa Uncle Bello yace Taje
ta Sameshi Haka ta Dingama Saura Acikin Ranta Tana Dariyan Mugunta,aiko kuwa Sunyi
Nadama Domin Koran kare Bello yayi musu bayan yayi musu kaca kaca,Kowacce tasha
Kuka kafin ta bar Makranta barin ma Jidda da Takejin Soyayyar Bellon Har Cikin
Ranta Itakuwa Aneesa Boye kanta Tayi Har Suka bar Mkrantan.

*****

Tafiya tayi Tafiya Cikin Jin Dadi Da Akasinsa Domin gashi Har su Aneesa Sun Shiga
Ss2 Abun da zai baku mamaki yadda Aneesa Bukar Bulama ta zama zakaran Gwajin Dafi
Wajen Kokari Acikin Mkrantan Duk Dalilin Bello yanzu Aneesa Ta Daina Kukan Zuwa
Mkranta Tunda ta Fahimci bello bazai Taba kyaleta ba,Tana Da Kokari Afannin
Darasinshi dana Uncle Aminu Domin ita dasu S.jibiya Turanci Abakinsu sai ka Rike
baki,Ahutun da suka samu ne na First Time Anty Rahila ta Haihu Ta Haifi Da Namiji
Wanda Yaci Sunan Muhammed Suna Kiranshi Junior,Lokacin Haihuwan Duka yan Borno sun
Taho Harda mama Falmata mahaifiyar Aneesa da Anty Nafee da Anty Yagana,da Anty
Aisha Daga kano sai Matan Ya Ali dana ya Sunusi da Ya"yansu Harda Sanah Tazo wannan
karon,Hakama bangaren Su Abba kabiru Hajiya karima tazo ita da Zubaida duk da
Zubaidan Tana nan Abujan ne Wajen Ya Hashim tana Shekarar Farko A base University
Zulfa ce Take Katsina Umaru musa yar"aduwa.

Zuwanan da Sukayi kowa yayi mamakin Yadda Aneesa ta kara zama sai dai Fa mai Hali
baya barin Halinsa,Rashin kunyanta da Tsiwanta na nan bai barta ba Sai dai yanzu
ilimi ya Ratsata ta Rage Wasu abubuwa kamar su Faduwa akasa tana Kuka da Wasu
Abubuwan,ko da Sunan sai da Takai Zuciya nesa Ammh Haka Anty Nafi ta Dinga kyaranta
da Anyi Abu sai tace samun Waje ne,Har Sanah ma Ta iya kallon Banza Saboda Tana Da
Girman Jiki tana ganin ta kamo Aneesan Aiko taci Ubanta Don Aneesa bata Daukan
Raini gayamata tayi Ita kanwar Uwarta ce ba abokiyar Wasanta ba,Saboda Haka ta
Shiga Taitayinta,Dole Ta Shiga Natsuwarta Sanin Halin Aneesan Ko Lokacin Data zauna
agidansu bata da Sauki balle yanzu da Girma ya kara kamata ta kara zama yan"mata
sosai.

Falmata har Acikin Ranta Taji Dadin ganin Aneesa ta kara Chanzawa ko bata Nuna ba
Kowa ya kalli Fuskarta zai gano Tana Cikin Farinciki Awannann Zuwan ne Har suka
zauna da Aneesan Suka danyi Hira saboda kwata kwata babu Shakuwa Irinta Uwa
Atsakaninsu Domin kaf Ragamar Kuruciyar Aneesa Alhaji Bukar Bulama ne keda Hakki
Akanshi Shine yasan Komai na Aneesa Saboda gatan Datasamu Awajensa,Wananan Hutun
taso Zuwa gidansu B.kaita da S.jibiya sai bata samu Hali ba Saboda haihuwan Anty
Rahila din,Sai ta bari sai da suka kara samun Hutun Second Term kana ta Roki Anty
Rahila da Daddy Suka barta,Salamatu Jibiya suna Dutse ne da Zama Mallam Inuwa Shi
ya kai Aneesa Ta Kwana Daya agidansu S.jibiya Kana ita da Aneesa Suka Tafi katsina
gidansu B.kaita Hakika kawaancen Kawayen Junan Abun kallo ne Duk da Kullum Cikin
Yin Fada Suke barinma B.kaita da Aneesa basa Iya zama Waje Daya batare da Sunyi
Tsiya ba,Kwansu Biyu Akatsina Direban gidansu B.kaita na Yawo Dasu Cikin gari
Dayake bayan Mallam Inuwa ya kawota sai ya koma,Iyayensu duk sunajin Dadin
kawancensu Sosai Tunda Dukkansu yara ne masu Tarbiya da Hankali Ko Tsiya Tatashi
Tsakanin B.kaita da A.bukar bulama in tana so Ta Harzuka ta tace mata yar Baka,ko
kuma tace mata Tana son Uncle Bello yanzu Aneesa zata Birkice Tafara Tsiyarta
B.kaita ta Biyemata Suyi ta kasa Hali ba Ruwansu bai Hana Kuma anjuma ka gansu Tare
ba,Sai da suka Dawo Ta Dutse kana Baban S.jibiya ya sanya Direba ya Maidota Har
Abuja Booth Dinta Cike da Kayan Arzikin da Iyayen kawayenta Suka Hada mata bayan Ta
Dawo ta kwana Biyu Suka Tafi Borno Ita da Anty Rahila da Hibba wacce ke Mkranta
yanzu a British International School Abuja Suma sun Samu Hutu ne sai Muhammed
Junor Ajirgi Suka Tafi Borno Wanda Suka Shafe Sati Daya,Anty Rahila ta Koma Ammh
sai ta bar Aneesa Da Hibba Anan Suka karisa Hutunsu kafin su Dawo Abuja.

Zuwan da Aneesa tayi ne Wannan Karon ta Sauka Dakin Innarta Falmata badomin komai
sai Domin Tafara Hankali ta Fahimci Uwa ta Wuce Wasa,Kuma Ita Din wani Jinshiki ne
Ashe Falmata na Sonta kawai Hallayarta ne ta Tsana da Kuma kawaici Haka ta Dinga
ina zata saka Da Aneesa,wannan Hutun kam su Ya Ali basu yi Ciwon baki ba Kullum
kuma godiya sukema Bello Domin Yayi Abunda Su baza iya ba Ya Dawo da Aneesa mai
Hankali Ilimi ya Ratsata ba kamar Baya ba,sai dai yaransu suna cin ubansu bata Raga
musu Duk wanda yashi ga Gonarta Dafashi Take ba Ruwanta Balle Hibba da Tsokana in
Ta Tsokanesu Suka Daketa Har Dakin Uwar yaro zata Bika ta Daka Uwarshi bata isa
Tayi mgana ba in ma Tayi Toh yanzu Aneesa Zatace Suma haka babanninsu uka nadeta
kamar Jaka Dole ta rama kan ya"yansu Tunda bazata iya Ramawa kan Su ba.

Bataje gidan Anty Nafee ba Ita Datake Aure aMaiduguri Anty Yagana tabi Ibadan Ita
da Hibba bayan Tazo,wajen Sati Tayi musu achan Mijin Anty Yagana yana ta Tsokanarta
suna Tuna mata Abunda Tayi sai dai Tayi Dariya kawai batacewa komai,Toh me zatace
Ita kanta Tasan Aneesa Tayi Lokaci,Tasani lokacin Akwai yarinyata yanzu kuwa ba
laifi Budurci ne yagama gauraye Jikinta Shiyasa Tabar yayin Wani Abun Ammh Fa Tura
baki da Kunkuni Aneesa Bata Daina ba sai dai Wanda yafi karfinta bai Shiga Harta ba
yanzu bakin nan zai yi Tsini kamar zai Fado kasa

Sunsha Hutu Sosai Kafin Mallam Inuwa yazo ya Daukosu bayan Sun Dawo Borno,Kafin su
Tafi Haka Anty Nafee tazo Tana ta yada mata da Mgana wai saboda Ita bata dashi
Shiyasa taki zama awajenta,ammh sai gashi ta Zauna Wajen Rahila Tunda Mijinta wani
ne Akasar Gabadaya kuma yana da tarin Dukiya Shiyasa Koda tazo batayi Tunanin Zuwa
Wajenta ba,Aneesa na Jinta ta mata Kunnin Uwar Shegu Domin ba Tun yanzu ba tasan
Babin da Anty Nafee ta ijyeta taso ta zauna Wajenta tadinga mata Bauta Tunda
Jakarta ne,mama Yana ce Ta kama ma Nafeen Fada kana Tayi Shuru Falmata kuwa tayi
Tayi da Aneesa Taje gidan Nafeen Tace bafa zata je ba,Wannan karon sai dai Wani
Hutu Wanda Cikin Ranta ta saka Kano zata Gidan Anty Aisha bazata Dawo Bornon ba.
*******

Kwantashi babu Wuya Awajen Ubangiji Domin gashi Har Aneesa Sun Shiga Matakin Karshe
Asecodry,Sun zama Manya yanzu bamai Takura musu Abunda Suka ga Dama Sukeyi,Gashi
Abun Murnan Aneesa Uncle Bello baya Makrantar yanzu Tun Suna Third Time a Aji
biyu,ya Tafi Malesia yin PHD ,dinsa Hakama Uncle Aminu Shikuma ya Haura Kasar
Spain,Shima yaje Hado Master Dinsa Duka Tare Suka Tsara Tafiyan Kusan Lokaci Daya
Suka Tafi Leave Without pay batare da Sun Ijiye aikin koyarwasu ba Hakika Mkrantan
Kwatar-kwashi Tayi Rashi Sosai Wasu Dalibai da yawa basuji dadi ba irinsu Aneesa ko
sai bude Shafin Iskanci Juniors kuwa suna Cin Ubansu Wajen Aneesa ba wanda baisan
Set din 3stars ba Gwara kowa da Aneesa domin Wlh Karonta da Mutum ba Dadi gashi
Lokacin Ita ta Rike Headgal,Uncle bellon Da kanshi ya bata Lokacin da Yan Ss3 suka
Tafi kafin Shima ya bar Kasar kenan,ita kuma S.jibiya House Captain ce,sai B.kaita
Dake Mtsayin labour,sun zuba Lokaci kuma suna gan Zubashi domin ba"a Taba mugayen
Set kamar su ba Na kasa dasu suna Dandanawa Sosai.

*How to pay....�?200 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?400...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?350 ne,VIP
�?600, Single one �?200 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*Shakira..*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*🅿�?11*

Sun Dawo Hutun First Time a Lokacin kuma Duk Wasu gabobin Burdurci Sungama Bayyana
Ajikin Aneesa Bata kara Kiba ba sai dai takara Murjewa Zama Cikin Hutu da kuma
Rayuwa Cikin A.C Don ma In ta Koma Makranta Takanyi baki da Rama Duk da duk Jin
Dadin da Aneesa ke ciki bata yadda ta Chanzama Fatar ta launin sa ba,ammh takan
shafa mayuka masu kyau da taada su suka sa Tayi kyau Fatar ta Murje.

Kirjinta kuma ya Cika da Dukiyar Fulani masha Allah,hakama Kugunta Shima yana
Tsuke,masha Allah ta Ko"ina Aneesa Ta Cika Budurwa domin Lokacin Tana da Shekara
goma sha Tara Aduniya Tana Jinta kamar Babbar Mace,haka zalika yanzu Tafi jin Dadin
Rayuwarta na ganin Uncle Bello baya nan Sai Cin karanta Take ba Babbaka,Uwa uba
Daada da Daddy basu son Laifinta har Gwara Anty Rahila na mata Fada Wani
Lokacin,komai na Bukatar Rayuwa Babu Abunda Aneesa Tanema Tarasa Babu Abunda Zatace
da Anty Rahila da Ya Muktar sai godiya Domin Sun Taimaka Wajen Inganta Rayuwarta
Uwa uba kuma Muhammed Bello,Wanda ko Ayanzu Takan godemai Wani Lokacin badomin Shi
ba da yanzu bata zama mai Ilimi ba balle Ta Rike Shugaban Dalibai na Mkrantan
kwatar kwashi Baki Daya ba,Takan Godemai Acikin Ranta Duk da ko bata daina jin
Haushin sa ba.

Zulfa ko da Zubaida sun Janye kafa da Zuwa Hutu gidan Daddy sai Lokaci bayan Lokaci
Tunda Suka Fahimci Shi Gwarzon nasu basa gabanshi Daga karshe yazo ya bar kasar Duk
da Zubaida na Abujan bata Cika Zuwa ba Balle Zulfa Dake Katsina karatu ya Tasa ta
Gaba,Shiyasa yanzu basu cika Zuwa gidan Akai akai kamar Baya ba.
*****

Tana Zaune A kan Three Sittet na Cikin Babban Falon Gidan,wayar Anty Rahila ce
Ahannunta Tana Game din Tample Run,domin Ita Anty Rahila ta Hana Ya Muktar ya
Siyamata Waya tace ya bari Tayi Candy,itama Aneesa bata damu ba Tabari sai Tagama
Candy Lokacin Ta koma Borno Domin bata da Burin Cigaba da Zama Abuja kuma..

Sanye Take da Doguwar Rigar Jallabiya Baka,wacce Ta Dace da Surar Jikinta,kanta


Kitson kalaba da Alheri mai Aiki ta kama mata Tunda Dama bata son Kitso D'an
Kwallin Jallabiya ne ke Kanta bata Daura ba yama Kusa Zamewa kafarta na kan Cafet
din Dake Shimfide Afalon Wanda Ta dura kafa daya kan Daya Tana kadawa,Daga Kumbunan
ta kuwa Suna Sanye da Jan Lalli daga Saman Kumbunan kuma Ta Cike Da baki Har Zuwa
Hannayenta Dake Rike da Waya,Fuskarta Tayi kyau Sosai Duk da batayi makeup ba ammh
Ta sanya Hoda,da liptck sai Fuskartata tayi kyau Sosai.

Daga Tsakiyar Falon kuma Junior ne kan Wata keke mai Azaban kyau da Tsari Bata da
Tsawo sai dai Fadi,gefe da gefe kamar wajen ijiyema yaro ko madara ko ruwa Daga
baya kuma Wajen zaman Babban ne Daga Alamu dai nKekan koyon zama ne Domin yana
Zaune sai Wasa yake da Fiddar Dake Hannunshi Haka yake Bashi da Rigima Batasan
Hayaniyar Hibba ne yasa ta baro Shashen Daada Ta Dawo nan Anty Rahila kuma tana
sama ta Kwanta bata jin Dadin Jikinta.

*******

Security Suna ganinshi Batare da Wani Tambaya ba Suka Wangalemai get ya Sulala
bakar Motarsa cmry Cikin katon Farfajiyan gidan Da Sojoji suka kawatashi da
Zagaye,cikin Takama yagama Daidaita Motar Bisa parking Space ya Dade kafin ya Bude
Murfin mota ya Fito Wani Cute and Handsome guy nagani Dogo ne,Shi ba Fari ba Kuma
bazaka Sakashi Cikin layin bakaken Maza ba,Irin kalarsa Tafi kama da Labaranawan
Egpt,yana da Zati daidai gwargwado da Kyakyawan Fuska sanye yake da Riga da Wando
na Kamfanin Armani Rigar Blue ce Mai Dogom Hannu sai Wandon kuma Navy Blue ne,ammh
ya matsemai jiki Ba sosai Kafarsa sanye da Wani Bakin Takalmi booth mai kyau da
Tsari,Fuskarsa kuma Toshe da Wani Bakin glass Wanda ke karamai kyau da Zati.

*KASIM KABIR JIKAMSHI* kenan,Matashin Saurayi mai ji da Kudi da Naira,Kasim Irin


Matasan nan ne Masu Budewan Ido Tun Zuwanshi kasar Waje karatu Turawa Suka
lalatashi ba Sharholiyar Da baya yi Har giya yana Sha Neman mata kuwa kamar
Bunsuru,Daya kyal ido yaga mace Toh babban Burinshi ki bada Hadin kai ya kwalfi
Ruwan Dadi Ko da ya dawo Babu Abunda yafasa yana samun Aiki a kaduna wanda ya
Muktar ya samarmai yaje ya Dasa Daga Inda ya Tsaya Duka iyayensa ba Wanda ya Taba
sanin Halin Dayake Ciki sai Hashim Wanda Ya Taba Riskanshi Cikin Halin Buguwar giya
Lokacin Daya kaimai Ziyara agidanshi Dake Kaduna Duk dq ya mai Fada Harda Barazanar
zai Sanar da Abba Kabiru bai sa Kasim ya bari ba,Ko yana so ya bari sai yaji bazai
iya ba Yadai Furtama Hashim Din Daya bari ammh bawai Don Ya bar Abunda yake
aikatawa ba,akallon Farko in kayi mai zaka Gane Cikakken Dan Duniya ne Dayasan
Harkan bariki.

Yau kwanansa Hudu Agarin Abuja Sunzo Wani Worshop ne Daga Wajen Aikinsu Gobe zasu
koma kaduna Shine bayan ya biya gidan Hashim sun gaisa da Matarshi Shi baya
gida,sai kuma yace bara ya biyo ta gidan Ya Muktar su gaisa Da Anty Rahila Duk da
yana da Tabbacin Baya gida yanzu,dama ko chan yakanzo Lokaci bayan Lokaci Duk Dashi
da Bello kowa najin kanshi ya Isa,ammh bai sani ba Bello ya Fishi Iskanci da Taurin
Zuciya,kuma Abunda Kasim bai sani ba Duk Iskancin da Kasim ke aikatawa Bello nada
lbri Saboda Akwai Wani Abokin Aikinshi da Suke Aiki Tare a Kaduna,Tare Sukayi
Universty of ibadan da Bello,Toh ya Taba ganin Hotonshi Awayarshi,inda yake Nuna ma
Wani yana bashi lbrin Irin Iskancin da Kasim ke Zubawa babu babu Abun da yafi
Batama Bello Rai Irin Neman Mata da Shan Giya da akace kasim nayi ko bakomai suna
da alaqar jini,lokacin Har Abokin na Kasim sani na Fadin garinku ma Daya Muhammed
Bello Shima iyayenshi mutanen Jikamshi ne yake kawai yayi koda Wasa Bai Nuna ma
yataba ganinshi ba.

Cikin Isa da Takama ya kama Hanyar Kofar da zata sada ka Da Babban Falon gidan,yana
Tafe yana Cilla key din Motarshi Kofar Falon ta glass ne na Waje in zai Shigo yana
ganin na Ciki Tun Alokaci idanuwansa suka Fara Masa Tozali da Aneesa Barin ma
hannayenta da Suka Fara Jan Hankalinsa sai da kofar Tagama Tatanceshi kana ta
Wangalemai kofa ya Sawo kanshi Falon Cikin Siririyar Sallamarshi.

Aneesa Tayi Nisa Cikin Game dinta batama Jisa ba Kara gyara zama Tayi tana
Sarrafa Game din Cike da Salo har Dan kwalinta ya zame gabadaya Kitson kanta ya
bayyana Cikin Daskarewar Numfashi da Sarkewar Murya Kasim ya Bude baki yana karema
Aneesa kallo Domin Lokaci Daya yaji jikinsa ya Saki Duk yawon Duniyanshi bai Taba
Haduwa da Yarinyar da ko gama kallon Fuskarta baiyi ba yaji tatafi da Imaninshi ba
Kamar Aneesa ba.

Cikin Sanyin Murya mai Cike da Yaudara ya Furta"Tsarki ya Tabbata ga Allah Shugaban
Hallitun Duniya Wanda yayi Wannan kyakyawan Halitar..."

Yafada yana Kafe ta da Ido kamar daga Sama Aneesa Taji Wata Murya na mgana Cikin
Sauri Ta Dago kanta Karaf ko Idanuwansu Duka Hudun Suka Hade Waje Daya,cikin
Numfashi Sama sama Kasim ke kallon Aneesa yana jin Wani Abu na yawo Acikin Jikinsa
Sosai Karon Farko Atarihin Rayuwarsa Daya Hada Ido da mace yaji baya Bukatar ya
lashi Zumarta So Daya ya dauwama yana lasarta kuma yana kallon kyakyawan Fuskarta
cikin zuciyarsa gayamai take Dakai Wannan Cute Face din Ta Dace.

Aneesa ko Kallon ne ya Sanyayamata Jiki ta Sauke idanuwanta Lokaci Daya Tana Mikewa
Dankwalinta taja ta Aza bisa kanta Cikin Sanyin Murya tace"Am Srry Sannu da
Zuwa,Zauna.."Tafada Tana kara kallonshi Tana so Ta Tuna Inda ta sanshi Shiko
Mirmishi yayi kafin yace"La..No problem karki damu Nafiki jin Dadin Hakan Domin
Idanuwana Su samu Damar kallanki Dakyau..",Yafada Cike da Bariki lokaci daya kuma
yana Sakarmata ido,yam Aneesa Taji bata yi mgana ba Ta fara Taku Zata bar Falon
Rigar Jikinta na Rawa Kowani Sako na Jikinta na Rawa Gabadaya Kasim sai Yaji yakasa
Control din kanshi da mayun idanuwanta ya Bita da kallo har Ta fice Daga Falon
Wanda Tana Ajikinta Cewa Idonsa na yawo Akanta Duk sai Ta Tsargu.

Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Karisa Kusa da Junior ya saka Hannu ya Daukeshi
yana Cillashi Sama Shiko yana bangala Dariya Domin Tunda ya Shigo yake Miko mai
Hannu yana Zillo Domin Haka Junior yake yafison Maza Su Daukeshi Fiye da Mata,yana
Tsaye yana ma Junior Wasa Aneesa Ta Dawo Wannan karon ta sanya Wani karamin
Hijabinta Fari Cikin kallon Ido Cikin Ido Tace"Ka kariso Ciki mana ka Tsaya
Anan..."

Lumshe mata ido yayi kafin yace"Toh ai ba"amin Jagora bane...Shiyasa na Tsaya
Anan.."Mirmishi Tayi kafin tace"La..ba Haka bane,.."Yana kallonta yace"Toh yane...?

Yafada yana kallonta Kur Cikin Idanuwasa Sauke idanuwanta Tayi kasa Kafin ta Juya
Tana Fadin"Afuwan Yanzu mu Shiga Ciki.."Bayanta yabi Da kallo yana Fadin"Angama
princess."Wani Iri Aneesa Taji sai Nanata Sunan Take Acikin Ranta Duk da ba yau ne
karo na Farko da Maza ke Nuna Sha"awarsu Akanta ba Ammh Dis is d First time da Wani
Namiji yake mata mgana Taji ya Burgeta......
.

Falon Anty Rahila Suka Shiga,Waje Ta Nuna mai ya Zauna kafin ta Shiga kwalama
Alheri kira da Hanzari ta Fito nan ta Umarceta Data kawo ma Kasim Abun Sha Da
Ruwa,kallonsa Tayi Tana Fadin"Anty Rahila na Ciki bari na Kirata.."Da Sauri
yace"No...Kyaleta Dawo Mu gama Mgana Princess,In zan Wuce sai ki kirata mu gaisa.."
Da baya Aneesa Ta Dawo Ta Zauna kan kujeran Dake Facing Dinshi Bai samu Zarafin
mgana ba Alheri Ta Shigo Cikin Uniform dinsu Domin kaf masu Aikin gidan Suna da
Uniform,Katon Faranti ne Cike da Abun Sha Bisa Dan Madaidacin Tebur din Dake
gabanshi ta ijiye kafin ta Dauki Kofi ta Tsiyayamai Ta Mikamai Karba yayi da Hannu
Daya Yana Fadin"Thanks..."Yafada yana kafa baki Lokaci Daya kuma yana Kallon
Idanuwan Aneesa Ita ko Kai ta Sunkuyar Tana Wasa Da Adom Doguwar Rigar Dake
Jikinta.

Sai da yagama Sha ya maida Kofin Kan Farantin kana yayi gyaran Murya,Da Sauri
Aneesa Ta Dago Cikin Dage mata gira yace"Ya.... ? Kinsanni..? Girgiza kai Aneesa
Tayi kafin tace"Naso na ganeka Ammh kuma na Kasa Tuna Inda na Sanka.."Mirmishi yayi
kafin yace"Ayyah...Niko kinga ina ganinki na ganeki ba.."Ido ta Waro kafin tace"Da
gaske...? To Wacece ni din...?

Dariya ya Saki yana kara Gyara ma Junior zama Wanda ke Ta Wasanshi Cikin Muryan
Takama yace"Ah..Kaji wayau ko..? Bazan Fadi Sunan ba,Sai dai na baki Satar amsa
bake bace kanwar Anty Rahila Dake Zaune Awajenta ba.."Yafada yana kallonta Domin
baisani ba Cinka kadai yayi Saboda bai Taba katarin Zuwa gidan Sun Hadu da Aneesa
ba Domin yafi Zuwa Lokacin Tana Zamfara Abakin Zubaida ne me yake Jin lbrin wata
kanwar Anty Rahila na zaune awajenta kuma yana ganin Aneesa jikinsa ya bashi itace
ko domin kamar da suke da Anty Rahila.

Dariya Tayi kafin tace"La..Da gaske kuwa kasanni,Niko na Rasa Inda na


Sanka.."Dariya yayi mata kafin yace"Sunanki ma Wace...? Cikin Sauri Tace"Aneesa
nake..."Dariyan Nasara yayi mata Ckin Sauke idanuwansa Akanta yace"Wow....Nice Name
Aneesa..."Yafada yana Yar Dariya sai Lokacin ta gano Wayau yayi mata Hararan Waasa
Tamai kafin Tace"Zan Ra ma ne..'"

Bai ce mata komai ba Illah Ido Daya Zuramata kawai yana Kallonta Abun sai ya Dameta
Ta sadda Idonta kasa Tana Jin gabanta na Faduwa Cikin Sarkewar Murya Taji
yace"Kinsan Zubaida..?
Kanta ta Dago Tana kallonsa Lokaci Daya Tace"Zubaida gidan Abba Kabiru..? Kai ya
Gyada mata Cikin Dariya tace"Eh Sosai Ita da Zulfan gidan Abba garba Suna Zuwa Hutu
nan Sosai.."cikin Sanyin Murya yace"Toh ni wanta ne.."Baki Aneesa Ta Rike kafin
tace"Koda naji... Fuskarta nake gani,Shiyasa Na Rasa Inda na Sanka.."Bai ba
mganarta Muhimmaci ba Ya Tsare ta Ido Cikin Dakewa yace"Aneesa...:!Idonta ta saka
Anashi,suna kallon Juna na Wani Lokaci kafin Yace"Kina Sona...?Zaki Aure ni...?

Dam! Aneesa Taji gabanta na Faduwa Sosai,cikin Rawan Baki tace"So kuma...?
Ba..bangane ba.."Mikewa yayi Dauke da Junior ya iso gabanta bai Tsaya ba kawai sai
ya Durkusa kan Kafafunshi Har Gwiwansa na Gogan na Aneesa baya taja da kafarta Tana
kallonshi Cikin Wani yanayi Kallonta Shima yake kafin yace"Eh So nace Aneesa..?Tun
Shigowata idona ya Hadu da Idanuwanki naji kin Sace zuciyata,naji na samu matar
Aurena..plz Aneesa Don"t say no..Ki Amsamin zaki Aure ne...? Kuramai ido Tayi tana
gasgata Gaskiyarsa Cikin Ajiyar Zuciya tace"E....."Bata karisa ba Kasim ya Riko
Hannunta Guda Daya yana Fadin"Thanks So much peincess zan Tababbatar da Kinfi
kowacce, mace Dacen Samun Gwarzo Namiji kamar kamata.."Yafada Cike da Farinciki Da
Sauri Aneesa Ta janye Hannunta Lokacin Dataji Wani yam Ajikinta Domin wannan shine
karon Farko kenan da Wani Namiji,ya Taba Tabata kuma taji wani bakon yanayi ya
Shigeta.,Saurin mikewa Tayi Tana Fadin"Nifa...nifa ban.."Mganarta Ta makale ne
Sanda ya Sakarmata Idanuwansa Da Suka Chanza Launi Suna kallonta Shuru Tayi ta kasa
Mgana sai ma Sun kuyar dakai Datayi ta koma ta Zauna Tana Wasa Da gefen Hijabinta.

Gefenta Kasim ya Zauna yana Cigaba da Marairaice ma Aneesa yana Cigaba da gayamata
kalamai,masu Sanyaya jiki Wanda Daga Dukkan Alamun mganganun nasa Suna Tasiri
Acikin Zuciyar Aneesa Suna Cikin Wannan Halin ne,Anty Rahila ta Sauko ganin Kasim
Kusa da Aneesa Yayi kasa kasa da Murya sai Abun ya bata mamaki ita ta katsesu Cikin
Mamaki take Fadin"A"ah Wa nake gani kamar Kasim..?
Da Sauri Suka Dago Suna kallonta Tashi Yayi kusa da Aneesa Dauke da Junior yana
Fadin"Nine Anty Rahila munzo Workshop ne Anan Abuja na Kwana Hudu so gobe zamu koma
kaduna Shine nabiyo mu gaisa,ina Zuwa kuma Allah ya Hadani da Matar
Aurena..."Dariya Anty Rahila Tayi Tana Fadin"Ikon Allah Ina Matar Auren naka..?
Tafada tana son Tababbartar da Zarginta Cikin Fara"a ya Nuna Aneesa yana Fadin"Gata
Anty Rahila..Princess dina kenan.."Baki Anty Rahila Ta Rike tana kallon Aneesa
Dake Kyafta ma Kasim Ido Dundu Takai mata abaya Cikin Dariya take fadin"Ja'ira sai
ya gayamin.."Bayanta Aneesa Ta Dinga Shafawa Cikin Shagwaba tace"Kai Anty Rahila
kin kusa Ciremin Kashin baya.."Da Sauri Kasim ya Juyo gareta jiki na Rawa yake
Fadin"Wayyo Da gaske..?mugani princess..."Yafada Yana Kallonta Cike da Tsumewa,Da
Sauri tace"Bafa komai.."Tafada tana kauda kai gefe,Dariya kawai Anty Rahila ke musu
Cikin Ranta tana Jin Dadi Domin dama Babban Burinta kenan Aneesa na Gama Mkranta ta
samu Miji Itama Tayi Aurenta,kuma harga Allah zata fi kowa Murna Tunda ita bataga
makusan Kasim din ba

Nan dai Ta Zauna Suka kara gaisawa Dashi,junior ne yafara kuka sai ya mika mata
Shi,cikin marairaice Murya kasim ke kara Sanar da Anty Rahila Shifa Dagaske yake
Domin in ya koma kaduna in zai je katsina Weekend da Mganar zai jema Abba kabiru
Don Allah za"a bashi Aneesa..? Jin Haka yasa Aneesa Tatashi da Gudu Ta bar Falon
Suka bita Dadariya,Anty Rahila tace"Kada ya damu su basu da mtsala yafara Tuntuban
iyayen nashi yaji.."Da Haka suka bar mganar nan yake Tambayanta Lambar Wayar Aneesa
Tace mai bata da Waya Saboda Mkranta sai Tayi Candy,jikinsa na Rawa yace Anty
Rahila bazai yuyu ba Na Dinga Nesa da ganin princess kuma Muryanta ta Dinga min
Shamaki da Zarar su Abba sun zo zan Siyamata Waya Daddy yayi Hakuri
kawai.."Kallonsa kawai Take Tana Dariya Saboda ganin yadda yake Rawan kafa.

Sun Dade suna Hira kafin tamai Jagora Zuwa Shashen Daada,Suka gaisa ya Zube mata
Kudi masu yawa Tana saka albarka Hibba ma Haka ta Daneshi Tana Murnan ga Uncle
kasim,Anty Rahila ce Take cema Daada Toshiyar baki ne kasim ya bata Saboda yaga yar
gidan ta yana so,Cike da mamaki da Fara"a Daada ke Fadin"Toh Hakane,Shiyssa naga ta
Shigo da Gudu ina mgana Akayi banza Dani Aka Shige daki..? Toh maza karo kudi domin
Wadanan Sunman kadan,kuma na janye Godiyata Domin Diyata ta Musamman ce"Aka Saka
Dariya Gabadaya Duk da Wasa take mai masa cikin Shaukin Soyayyar Aneeesa baisan
sadda ya sake Damko Wasu kudadan ya Mika ma Daada ba Tako Amsheta tana Fadin"Karka
damu Aneesa Ta zama naka ka kwantar da Hankali kamar Kana saman Jirgi mai ya
Kare.."Anty Rahila ta saka Dariya ita da Kasim,bai wani Jima ba yace zai Tafi
Faufau Aneesa Taki Fitowa Daga Daki Cikin Bada Umarni Daada tace"Kaga Kasimu Shiga
ka sameta Sabon Shiga ce.."Da Hanzari ko ya Shiga Bedroom din Aneesa na Kwance Ruf
da Ciki Tana Mirmushi Ita kadai Taji mganarshi Asaman kanta da Sauri Ta mike zaune
tana Zaro Ido,gaban gadon ya Durkusa yana kallonta Cikin Sanyin murya yace"Zan Tafi
princess,Ammh inaji kamar Zuciyata tana Zafi,gaskiya bazan iya komawa kaduna ba sai
nazo na ganki da Safe kinji ko.."?gyada mai kai tayi kafin ta Sauko Daga Kan Gadon
Tana Fadin"Nima mun kusa komawa Mkranta Zamfara zan Tai.."

Yamutsa Fuska yayi kafin yace"Haka Anty Tagayamin Allah Da"ace baki kusa kamallah
wa ba,sai dai ki Karashe Karatunki Akaduna bazan yarda da Wata Bording Sch ba,Ammb
bakomai yanzu ma Duk Visiting muna Tare princess.."Da Kallo Ta bishi Tana mamakin
yadda Lokaci Daya Ya Rude Akanta Tare Suka Fito Daga Dakin Nan ko Daada Ta Shiga
mata Tsiya da Sauri Ta bar Falon Tana Rufe Fuska nan yabama Anty Rahila kudi Itada
Hibba da Junor kafin yayi musu Sallama ya Fito Aharaban gidan ya iske Aneesa Tsaye
Tana Jiransa Ranar kasim bai bar gidan ba Sai da yagama Dasa Kaunarsa Azuciyar
Aneesa Taji ko bata Fara Sonshi ba yana Burgeta gashi Tana Jin Wani Abu game Dashi
Sun Rabu da Cewa In ya samu lokaci zai Biyo gobe da Safe In kuma Taji Shuru ya Wuce
zasu yi mgana ta Wayar Anty Rahila da ta bashi Nombar kafin su rabu,Kudi da yawa ya
Debe Daga aljihunsa yabama Aneesa Ta ki karba Daya mtsamata sai Tafara Kwalkwal da
Ido Zatayi kuka,dole ya kyaleta ammh kuma ta kara samun Wani Matsayi mai girma
Acikin Ranshi,Sallama sukayi ya Shiga Mota ya Fice Daga Haraban Gidan Suna Dagama
Juna Hannu.
Tadade Tsaye Awajen Tana Jin kanta kamar ba Ita ba Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin Ta
Juya Zuwa Cikin Gidan Wani Shashe na Zuciyarta na Murna Samun Namiji kamar kasim
wanda bata taba mafarkin samu ba.

_Masha Allah awannan page din na yau na kawo karshen Free page da zan baku na Mr
Bello,Kuna Bukatar sanin yaya Soyayyar kasim da Aneesa zai gudana...? Ko kuwa kuna
bukatar sanin shin su Abba kabiru zasu yarda da mganar kasim na Son Auren Aneesa..?
Ina labarin Mr Bello...?kar ku manta Yana da labarin Duka hallayar kasim din na
Neman mata da Shan giya Shin zai bari Aneesa ta aureshi? Ko kuwa zai sani kuma ya
take sani saboda basu da Shiri da Aneesa..? Yaya Zulfa da Zubaida zasu kare da
soyayyar Mr Bello..? Shin zai auri daya Daga cikinsu ko kuwa kowa zai rasa ne..? Ya
ya rayuwar su Abba kabiru zai kare shin Bello zai yi karansu kotu ne domin Fansar
ran Iyayensu da kuma Dukiyarsu da suka Hau kanta,..? Wani irin Soyayyah ce Zata
faru acikin wannan littafin..? Kina bukatar ganin wani gwarzon ne zai ja Ragamar
Jagoran Rayuwar Aneesa..? Toh zaki samu amsar tambayoyinki ta Hanyar Nuna min kauna
wajen Siyan Novel dina Kun gwada kun gani kun tabbata bazan baku kunya ba siyan na
gari mai da kudi gida_

*How to pay....�?200 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..�?400...or MTN card aturo ta
wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �?350 ne,VIP
�?600, Single one �?200 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu
tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

Happy sallah in Advance zaku iya cigaba da payment dinku bayan sallah in sha ALLAHU
zamu dora Daga inda muka tsaya Fatan zamu sallah lafiya Ameen.

*Shakira...*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞

*🅿�?12*

Washegari Kasim bai samu Dawowa ba yadai kirata Awayar Anty Rahila ya Sanar Da Ita
Sun Wuce Kaduna,basu Wani jima suna waya ba ya yanke Kiran Da cewa Zasu yi mgana in
ya Isa Kaduna.

Tunda Kasim ya koma Kaduna Koda Aiki yayi mai yawa bai Hanashi bama Soyayyar Aneesa
Kulawa ba Wuni Suke Waya da Ita ta Wayar Anty Rahila Kafin Arufe Sati Zuciyar kasim
Ta Rufe Ta Kulle ba Wacce Yakeji Da gani sai Aneesa Itama Duk da Bata Taba Soyayyah
ba, ammh Tana Jin Dadin Soyayah da Kasim ko banza yana Burgeta kuma gashi, ba Laifi
ya iya Soyayyah ga iya Tsara kalamai,lokaci kadan ya samu Matsugguni Acikin
Zuciyarta.

Hatta da Ya Muktar ya samu lbrin Komai yayi murna Sosai, Shima Hardashi Ake Taruwa
Ana Tsokanar Aneesa,bai nemi Kasim ba Tunda Anty Rahila Tace ya bari Shi kasim di
ya Nemishi din kamar yadda yace.

Sati biyu da Haduwarsu Aneesa Ta koma Makranta,yayinda kuma Asatin Suka Rabu da
Kasim kan zaije Weekend Katsina Tatayashi Addu"a zai gabatar da mganarsu Wajen
Abba,da Fatan Alheri Tabishi Suka Rabu Cike da Kewa Harda kukanshi Wai zai yi
kewarta Yanzu ba zai ganta ba..? Kuma bazai ji Muryanta ba Sai nan da Sati Hudu..?
Dakyar ta lallasheshi ya Hakura Dafarko ma Tubure mata yayi akan Shi zai zo ya
kaita Makranta Dakyar ta lallasheshi ya Hakura,Haka suka yi sallama kowanne
Zuciyarsa ba Dadi,Saboda Zuciyoyinsu Sun Saba da Juna.

*******
Karfe 11am na Safiyar Ranar Asabar kasim ya Isa makeken gidansu Dake kofar laura
Katsina,sai da ya Fara isa Shashensa yayi wanka ya Sauya kaya Tukunnah,ya iso cikin
Falon gidan Inda ya Ci karo da,hamdiya Tana Zaune Tana kallo ganinshi ya sanya Ta
Mike Tanamai Sannu da Zuwa Fuskarsa ba Annuri ya Zauna kan Daya Daga Cikin kujerun
Falon yana Fadin"Yaushe kika zo ke kuma...?

Kanta na Duke Tace"Mun kwana Biyu ya Kasim,gobe ma zamu koma Munzo Hutu ne nida ya
Ummu.."gyada kai yayi kafin yace"Ok kuna Wani Aji ne yanzu..?cike da girmamwa
Tace"Ni ina Jss3 ne Ya Ummu kuma Tana Ss2.."

Kai ya Jinjina kafin yace"Oryt..Ku maida Hankali banda Wasa Kunji ko..? Abba na
gida..? Yafada Lokaci Daya yana Fiddo da Wayarsa Cikin Aljihun Bakin Wandon Dake
Jikinsa,kai ta gyada kafin tace"Insha Allahu Yaya..Eh Abba na nan Umma ma Tana
Shashensa.."

Bai ce komai ba Illah Mikewan Dayayi ya Nufi Barayin da Zai Sadashi da Shashen Abba
Kabiru Nan ya sake cin karo da Ummu salma Ta Fito Daga Falon Umma,Rankwafa Tayi
Tana gaisheshi kallo Daya yayi mata ya kauda kai ya amsa a cike ya Wuceta da kallo
Ta Bishi Tana Tura mata Baki Acikin ranta Tana Fadin Ya Hashim ya fishi Kirki Sosai
Shi ko kullum Fuska Ba Annuri,bai Jita ba Ammh yaga Sanda TaTuramai baki bai bi Ta
kanta ba Domin Shi yanzu Aneesa ce Agabanshi.

A kofar Falon ya Tsaya yana Doka Sallama Hajiya karima da Suke Kira da Umma ta amsa
mai Lokaci Daya kuma Tana mikama Abba Kabiru Tea din Data Hadamai Awani kofin
Tangaran Ya karba kenan Kasim ya Sawo kanshi Falon lokaci Daya yana Zame Takalmin
kafarsa Kusa da ,Umma Ya zauna Wacce ke Zaune kusa da Abba kabiru Akan Cafet yana
karyawa Domin ga kayan karyawan nan nashi Bisa Wani Katon Tire Dake gabansu.

Cikin Sanyin Murya yace"Abba barkanmu Da Safiya,Umma ina kwana..? Dukkansu suka
amsa Cikin Sakin Fuska Kafin Abba Kabiru yace"Kasim yanzu kake Tafe..? Ya wajen
Aikin naka.? Yafada yana Kurban Tea din Dake Hannunsa,Cikin girmamawa Kasim yace"Eh
Abba,lafiya lau ba Wata mtsala.."Abba kabiru yace"Masha Allah.."Daga Haka Falon ya
Dau Shuru Abba kabiru na Cigaba da Kurban Shayinsa kafin ya Dire yana Fadin"Ke ko
Karima Wani Lokacin kina da Wauta kinga yaro ya Dawo da Safe,baki Hadamai Abun kari
ba,kila bai karya ba ammh kin zauna kin Zuramai ido Mtseee..."Ya saki Tsaki Cike da
Jin Haushi.

Fuska Umma Ta bata kan Tace"Ikon Allah Alhaji Shi kasim din yaro ne,balle ace sai
an mai Nuniya ko Dole,ko kuwa gidan bakonsa ne? Naga in yana Bukata da kanshi zai
Shiga Kichen ya Nema.."Tafada Tana Kauda kai Dariya Abba kabiru yayi kafin
yace"Wannan ba Hujja bane,Koda yake Dan Gida amatsayin Bako yake Zuwa Tunda Ba Anan
yake Zaune ba.."Baki Ta Tabe kafin Tayi mgana Kasim yayi Saurin Cewa"Ah"a Umma
bakomai Na Riga na Tsaya Kan Hanya na karya sai dai Zuwa anjuma.."dariya Umma Tayi
kafin Tace"Toh kaji ma kai da Kadamu kanka.."Harara ya Jefamata kafin ya Cigaba da
Shan Tea dinshi Umma na Dariya kasa kasa,kasim ma sai da ya Murmusa sanin Halin
Abba Kabiru yana da Fada Sosai Umma ce kuma Daidai Dashi.

Cikin girmawa Kasim yace"Abba Dama ina son mgana Dakai ne.."Abba kabiru na Sauke
Kofin Hannunshi yace"Topha..Wata mgana kenan kasim..? Kan Kasim na Kasa yace"Kan
mganar yarinyar Danake Nema ne.."

Gabadaya Suka Zubamai Ido Cikin Fara"a Umma tace"Masha Allah a Ina ka samu
Yarinyar?kuma yar gidan Wanene ne..?Tafada Tana kallon Abba Kabiru Wanda ya Muskuta
yana Fadin"Ina Jinka Kasim..

Cikin Karfin Hali kasim yace"Toh Shine Nake so Atura chan Gidansu din,"Abba Kabiru
na Mirmishi yace"Ba Mtsala Yar Gidan Waye Yarinyar..? Cikin Sanyin Murya yace"Ai
yar gida ce Abba Agidan Ya Muktar Take.."

Daga Abba Kabiru Har Umma Ido Suka Sakarmai kafin Umma tace"Gidan Wani Ya Muktar
din..? Badai na Abuja ba..? Kai ya gyada kafin yace"Eh Nan Umma,kanwar Matarsa ce
Anty Rahila.."Kafin ma Abba Yayi mgana Umma ta Zabura Tace"Badai Wannan Shegiyar
mara Kunyan Aneesa ba..?

Kallonta Kasim yayi Cike Da mamaki kafin yace"Eh Ita Kinsan Tane Umma..?Dakuwa
tamai kafin Tace "Bansani ba Uban Waye baisan Wannan mara Kunyar Kanwar Rahila din
nan ba,Kul dinka Kasim Bada yawuna ba,nan in kanwarka Taje Huta ba Cin kashin Da
bata mata,kai ko Zuciya baka Dashi Alhaji karka Manta Duk Bin kan yaron nan Bello
da muke yaso Zubaida ammh Abu ya Faskara sai ma Tozarci ne ya Biyo baya,kai Saboda
baka Kishin Iyayenka ko kunya sai kazo kace Zaka Aureta,toh bazaka Aureta ba Kowa
ya Jika Nashi yasha.."Takarishe Mgana ta Huci.

Daga Kasim Har Abba Kabiru da Ido Suke Binta Jikin Kasim yayi Sanyi Cikin Kwantar
da Murya yace"Karki ce Haka Umma,mganar Bello Dabam kamar ki Sako Aneesa Cikin
Mganar nan babu Ruwanta,kuma In kin Duba Shi Ya Muktar din bai Da Mtsala Kuma
kanwar Matarsace..."Harara Umma ke makamai Har yagama Mgana Ta Bude baki zatayi
mgana kenan Abba Kabiru ya Dagamata Hannu yana Fadin"Ya isa Haka karima bana son
Hayaniya.,Kai Kasim ka Hakura Tunda ga Abun Mahaifiyarka tace kuma ko ba Haka ba
Nima Hankalina bai Kwanta Da yarinyar ba, in aure kakeso kaje ko"ina kakeso Cikin
kasar nan ka Nema ni kuma Zan Shige Maka gaba.."Wani Faduwar gaba ta Samu kasim ya
marairaice yana Fadin"Abba karkamin Haka Don Allah..Wlh ina son Aneesa bazan iya
Auren ko Wacce mace ba, bayan ita.."Galala Umma ke kallonsa kafin tace"Kaji ko
Alhaji Abunda nake Gudu kenan,Bata barshi Haka ba,kai ko Muktar din ba Haka kawai
Rahilar Ta barshi ba,bakaken Kanurin nan ba Kirki ne Dasu ba,sai Su Juya maka kan
yaro Kwata kwata bayaji baya gani Daga Su sai Danginsu Ina Dalili Wlh Ahir
Dinka.."Kallonta kawai Abba kabiru keyi kafin ya maida Kallansa kan Kasim wanda
Idanuwansa Suka sauya kala Sukayi Jajir Saboda bacin Rai.

Cikin Lallabi Abba yace"Ka bar Abunda iyayenka Suka ce basu so..Kila ba alherinka
bane Tashi Kaje Allah yayi maka albarka..."Kasim yayi Sukutu kamar zai yi mgana Sai
dai kuma ya fasa Ya Mike yana Rangaji ya Fice Daga Falon Umma Ta Rakashi da Kyafci
Ta Juyo Zata Cigaba Da mgana Abba kabiru ya Daga mata Hannu yana Fadin"Kinga karima
ya Isheni Hakanan Nace ya bar mganar bashi kenan ba..?mitar mene kuma zaki Dame
Dashi.."Yafada yana Mikewa Tsaki ya Saki kafin ya Nufi Hanyar Bedroom yana
Fadin"malama zo ki Fitomin da kayan da zan saka kafin na Fito Wanka ."Daga Haka ya
Shige Cikin Bedroom Dinsa yana Jin Haushin Shigen Korafin Karima,itako da Harara Ta
bishi kafin Ta Mike Tana Fadin"Eh dai koma menene naji Dadai na bari Kasim ya Auri
Wannan yarinyar.."Dahaka ta Rufamai baya Tana mganganu Ita kadai.

Shiko Kasim Sheshensa ya koma ya Fada Bisa gado,hawayen Idanuwansa Suka Gangaromai
Taya zai Fara Rayuwa ba Aneesa Yarinyar Data kwancemai Tunani Lokaci Daya,Duk
barikin shi da Cin matansa bai ga kamar Aneesa ba,Yana ji Ajikinsa Itace Zatayi
Daidai da Rayuwarsa ta Riga Ta zama wani Jigo na Rayuwarsa Wani Irin So yake mata
Wanda baisan Iyaka ba,damuwa ta mai yawa Wanda Tayi Sanadiyar ya kwankwadi Giyanshi
Wanda Rabonshi Da Tashanta Tunkafin ya Hadu da Aneesa Koda ya koma kaduna kullum
yana Cikin Farinciki ne,Sai dai Matan banza Wanda yake Tabawa Domin Kullum gidanshi
na Kaduna sai ya karbi bakuwa,bayajin zai iya Daina Neman mantan Shi,watakila in ya
Auri Aneesa ya Daina.

Sai da yasha yayi Tatil kana Ya Kwarara amai nan bisa gadon,yakuma Sulale kan gadon
yafara Sharan Barci sai yammah Kana ya Tashi Cikin kyamkyamin Halin Dayake Ciki
yana Toshe baki ya Tashi ya Kwashe zanin Gadon ya Shiga Dashi Toilet ya Wurga Cikin
Bucket din Kayan Wankinsa inda mai Wanki ke zuwa ya Kwashe ya Wanko ya gogesu
Tas,kayan Jikinsa ya Cire ya Hada Dasu,wanka yayi ya Dauro alwala ya Fito,Ba laifi
yaji Zuciyarsa Tayi Sanyi Shiryawa yayi Cikin Wani Farin yadi Riga da Wando,da Hula
zanna Bukar,Sallar Azahar da La"asar yayi kafin ya Zari key din motarsa ya Fice
Daga Shashen Gabadaya ko Shashen Iyayen nashi bai kallah ba ya Shiga Motarshi ya
Saki Hon Megadi ya Wangalemai get yafice kamar zai Tashi Sama.

Gidan Abba garba Dake Gra Ya Wuce kai Tsaye yayi Sa"a Kuwa ya Sameshi Agida nan
Kasim ya marairaice yana Rokonsa kan yaje ya Ma Abba kabiru Mgana kan ya Amince da
Zabinsa,Abba garba ya Saurari kasim,ya kuma mai alkawarin Zaije Har gida ya Sami
Abba Kabirun Su Tattauna,cikin Farinciki Kasim ya baro Gidan,shi kuma Abba garba
Mama Sahura ya labartama Abunda Kasim yazo mai Dashi,Nan mama Sahura Ta bama Abba
garba Shawaran ya Taushi Abba kabiru ya yarda Kasim ya Auri Aneesa ko Banza Wanj
kusancin ne ya kara Kulluwa Ko babu komai Muktar bazai bari Bello ya Tozartasu ba
Balle Rahila bazata Taba so Bello ya Tozarta Dangin Mijin Kanwarta ba,Da Wannan
mganar Shima Abba Garba ya Shawo kan Abba Kabiru ya Amince,shima haka ya Dinga Nuna
ma Umma Ammh Taki yarda Tace munafuncin Sahura ne,Bude mata Wuta Abba kabiru yayi
Dole Taja bakinta ta Tsuke ammh Acikin Ranta Tana ganin Har Abada baza Tataba son
Auren ba.

Kasim da Kanshi ya Kira Hashim awaya ya Sanar dashi Abunda Ke Faruwa,shima bai da
Mtsala yayi Murna Ya sama Abun Albarka,Ranar da Kasim ya baro katsina Zuwa kaduna
Ranar Abba Kabiru yama Ya Muktar Waya kan Mganar Aneesa da Kasim yayi Murna Sosai
ya kuma ce Su bashi Lokaci zai Kira Yyayyin Aneesa Dake Chan Borno ya Sanar Dasu
Abunda Ke Faruwa.

Batare da Bata Lokaci ba Washegari Tun kafin ya Muktar ya Fita ya Kira ya Ali
Sukayi Mgana Inda ya Nuna Murnansa Sosai ya kuma ce ba Matsala,nan ya Muktar ke
Sanar Dashi Cewa Suna Tafe Cikin Satin nan,sai ya Ali yace ba sai sun zo ba Shida
ya Sunusi zasu zo Domin Aneesa ikonsa ne, Saboda Haka su zasu zo nan Abuja agudanar
da komai ya Muktar yaji Dadin karan da Su ya Ali Sukamai Har Sai da ya Furtama Anty
Rahila da Daada.

Bayan Sati Daya da Mganar Ranar Lahadi Su ya Ali Suka Diro Abuja dama already tun
ana gobe zasu zo suka yi magana da ya muktar ta waya,shi kuma ya kira su Abba garba
ya sanar dasu ,su ya Ali sun iso ba Dadewa Abba Kabiru Abba garba da Ya Hashim Suma
Suka Iso gidan ya Muktar bayan Gaisuwa da Gaishe gaishe Suka Fara Gudanar Da Abunda
ya Tarasu,Su ya Ali Sukace Mgana na Wajen ya Muktar Su Nasu Yan saka albarka ne,Jin
Haka yasa ya Muktar yaji Dadi kuma ya tabbatar da Yabama Kasim Aneesa Har Abada,Ya
kuma yanke musu Sadaki Dubu 100 ya Hashim ya Ijiye Dubu 200,sai mganar Saka Rana ya
Muktar yace abarshi nan da Wata Shida Lokaci Aneesa Ta kammallah Makranta Tayi
Candy Dinta,kowa yayi Na"am da Mganar Bayan Kowa yaci Yasha Suka Rabu Cikin Karrama
Juna Daga Su Yaya Alin Har Su Abba Garba Juyawa Sukayi Ranar babu Wanda ya Kwana

Sai dai kowa yaji Saka Ranar Aneesa Kwatsam Abun mamaki ,kasim kuwa Da ya Hashim ya
Kirasa yake gayamai Kamar ya Suma Saboda Murna Gashi ba Halin Da Zai gayama Aneesa
Sai ya Kosa Sati Uku Ta Wuce yajema Aneesa Visiting Tare Da lbri mai Dadi,Zubaida
Kuwa da Taji lbri Haka Ta Kira Umma Tana kara Zugata Tana Kuma Aibata Aneesa Ammh
Umma bata da Yarda Zatayi Domin Abba kabiru yace in ya karajin mganar Ranta zai
baci,Bangaren Zulfa ko Bata Wani Damu ba,Ammh Haushinta Daya Yadda Aneesa Zata
Shigo Zuru"arsu Ammh Taji Dadi Tunda Yayan Zubaida ne Zata Aura Ko Banza Zataci
Ubanta Dakyau.

Bangaren Gidansu Aneesa Kuwa Kowa Yaji Lbrin sai yayi Murna Su Yaya Ali sai dai
Suka Dawo da Lbri mai Dadi,Mama yana ko Har Da Taka Rawa Falmata kuwa Duk Da Tayi
Murna bata Nuna ba Saboda Kawaici Sai da Ta Shiga Daki Ta kai goshinta kasa Tana
Godiya Ga Allah,Anty Yagana Da Anty Aisha Anty Rahila ta Kirasu Take Sanar Dasu
Suma Sunyi Murna Sosai Anty Nafee kuwa sai da Tazo Gida Takejin lbri Abakin Matar
ya Ali khadija Abun ko Yamata Zafi Tayi ta maganganu Wai ba"a Dauketa da Daraja
ba,Shiyasa ba Wanda ya Kirata,Mama Yana na Mata mgana ko Sauraran Batayi ba Ta bar
Gidan Ta koma Maiduguri,tana komawa Ta Daga Waya Ta kira Rahila Ta mata tas,ta Inda
Take Shiga bata nan Take fita ba wai Sun Ware ta Suna Abu Su kadai toh da basu
Gayamata Aneesa Zatayi Aure ba Sai mene,Itama Allah zai bama yarta Miji na
gari,Anty Rahila na So Ta mata bayani Ammh Taki Sauraranta,takashe Wayar Ta kuma Bi
bayan Kiran Taki Dagawa Abun yama Anty Rahila Ciwo sai da ta Kira Anty Yagana tana
Gayamata tana Kuka Dariya Anty yagana Tayi kafin tacemata kima Share Hawayenki
Domin Indai Nafee ne bata da Lissafi ki Shareta kamar ma Wannan ya Dameki nan Take
Fadamata Itama ta Kirata ammh Tamata Wal,ko zarafin mgana bata samu ba,Daga Haka
Anty Rahila Ta saki Ranta.

Kasim Kuwa Shiryan Shiryan Zuwa Visiting Din Aneesa Yake Wannan Satin,Babu Abunda
bai Siyan mata ba na Kayan provision,Jira kawai yake Ranar Sati Yayi ya dau Hanyar
Zamfara Domin Yayi kewar Aneesa Sosai,Baisan Itama tana Chan Tana Fama da Kewarsa
ba,ko su B.kaita Sunga Chanji Wannan karon Domin Aneesa Ta kara Chanzawa ta kara
Natsuwa,ga yawan Zama Ita kadai Wani Lokacin Sai dai Suga Tana Mirmishi Ita
kadai,Sunyi Tambayan Duniyan nan Taki Gayamusu komai Sai dai Tace musu Soon Zasu ga
Komai Haka Suka barta Suna Jiran Suga koma miye ya maida Aneesa Haka mai Muhimmaci
ne.

Mr Bello kuwa Yana kasar Malesia,yana karatunsa baisan Halin Da"ake Ciki ba,Duk da
yana Waya da Ya Muktar Da Anty Rahila Daada ma Suna mgana Lokaci Bayan Lokaci,Ammh
bai Taba Tambayan Ina Aneesa ba Itama Bataba Damuwa Dashi ba Suma Ba Wanda yayi
karambanin Sanar Dashi Abunda Ke Faruwa ganin ba Wani Shiri Suke Da Aneesan ba,shi
kuma ko Alama domin yama manta da Wata Halitta Wai Aneesa Karatunshi ya sama Gaba
Gadan Gadan ya kosa ya kamallah ya Dawo kasarsa Ta Haihu.

*wannan littafin na kudi kada ki karatamin Littafin indan baki biya ba,ki biya ki
karanta cikin Salama domin Neman karin bayani ku nemeni ta wannan Nombar kamar haka
09069067488*

*Shakira...*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne kibiya ki karanta cikin salama akan �?200,Vips �?400,kada ki


karantamin Littafi matukar baki bayani ba..Domin neman karin bayani asameni ta
wannan Nombar kamar haka 09069067488.*

*🅿�?13*

"Ranar Lahadi Ta kama Ranar Visiting Dinsu Aneesa,Tun karfe 8am na Safe kasim ya
kamo Hanya Saboda Zumudi Jiyama barcinshi Ragagge ne,saboda yadda ya kosa Yazo yaga
Aneesa Sai dai kana naka ne Allah na nashi ya kusa Talatan Mafara Motarsa ta samu
mtsala,Hankali Kasim ya Tashi Sosai ganin Lokacina Nata Tafiya Dakyar ya Karisa
Cikin garin Talatan Mafaran Bayan Wani mai mashin ya Ragemai Hanya yaje suka zo da
Bakanike ya Fara Duba Motar Shiko yana Gefe sai Faman Duba agogo yake Har pass
12,Hankalinsa ya Rabu Gida biyu yana chan yana Tunanin Kila Aneesa Zata ce ba zai
Cika mata alkawari ba.
Itako Aneesa Tun Safe bata Fito Daga Hostel ba Tana Sanye Cikin kayan Check
dinsu ,Pick clour Su S.Jibiya ne ke Waje Suna kula da Komai Tun Safe Taji kanta na
Ciwo Tana Kwance,Su Ringa sun zama manya Shiysasa basa Murna In Ranar Visiting Tayi
Tunda ba Zuwansu musu Ake ba anfi Zuwan ma na kasa Dasu Su da Suke Sabbin Zuwa,Tun
Safe Take saka Ran Zuwan kasim Tunda ga alkawarin Daya Ijiyemata Daga gida kuwa
bata san Ran Kowa ba Tunda Bello ya Tafi Sau Daya Anty Rahila da Daada Suka zo mata
Visiting Wani Lokacin Sai dai Aturo mallam Inuwa da Sakon kayan provision dinta
Shiyasa Bata Damu Da Wanda Zai zo Wajenta ba kasim ne kuma Tunda Taga 12 ta Wuce ta
Cire rai.

Bayan Ta chanza Kaya zuwa Uniform dinsu ne Suka Tafi Masallaci sukayi sallar
Azahar,Bayan Sun Dawo ne Ita da B.kaita Sukaje suka gaida Wani Uncle din S.jibiya
daya zo mata Visiting Uncle yusuf sunanshi Kanin mamanta ne,Sunsanshi Domin yana
yawan Zuwan mata Tunda yana aiki ne Ahukumar Inec Dake Gusai,Sun Dade Karkashin
Bishiyan Dalbejiya Suna Hira bai wani Jima ba yayi musu sallama ya Tafi bayan ya
basu Kayan Dayazoma da S.jibiya Dashi Wata Junior dinsu Suka Kira Tadauki Ledojin
kayan Zuwa Hostel dinsu Su kuma Suka bita Abaya.

Suna Zaune Suna Bude kayan Su Uku ne bisa gadon Aneesa Murna Suke tayi ganin Harda
Chaculate Din Da Suka ke kauna Dukkansu Kowa ya Dau Daya suka Bare Suna Sha Suna
Zuzuta Irin Kirkin Uncle Yusuf,Aneesa dai Duk bata saki Jikinta ba Har sai da
B.kaita tayi mgana.."Anee..? Wht wrong wit u..?

Kallonta Aneesa Tayi kafin tace"Me kika gani..? Kallon S.Jibiya B.kaita tayi kafin
tace"U look so Silet Today ko Salma..?"Gyada kai S.jibiya Tayi kafin Tace"Nifa Tun
Dawowarmu Wannan Hutun nagane Aneesa Ta kara Chanzawa plz ki Sanar damu meke
Damunki.."Mirmishi Tayi kafin Ta Sauka Daga kan Gadon Tana Fadin"Allah fa bakomai
bana jin Dadi ne.."Da kallon Tsausayi Suka bita kafin Su Hada baki Wajen Fadin"Ayy
Sorry Bari muje Cikin makranta mu karbo miki Mgani,ina Angela Itace Health
prefect.."Bata Tankansu ba Har Suka Mike Suka Fita bisa gadon B.kaita ta koma ta
Kwanta tana lumshe ido.

Wajen Karfe 2pm motarshi Ta Shigo Cikin Makrantan,Kai Tsaye Gefe ya samu yayi
parking ganin yadda Haraban Makrantan ya Rikice da yan Visiting Fitowa Yayi Daga
Motar yana Latsa wayarsa Lokaci Daya yana kara Bin Harabar Makarantar da Kallo
Cikin Nazari Wazai Tambaya,yana Wannan Tunanin Wasu yan Junior su Biyu Sukazo
Wucewa Ta gabanshi Cikin karfin Hali yayi musu sallama Suka Waigo Lokaci Daya Suna
amsawa.

Cikin Sanyi murya yace"Amrm Don Allah in ban Takura ku ba Wata Aneesa nakeso ku
kiramin.."Doguwar Ciki ce Tace"Ok Wata Aneesan..? Kansa ya Shafa yana Tunani kafin
yace"Aneesa Bukar...Something Like Dat dai..."Kallon Juna Sukayi kafin Suyi mgana
Yayi Saurin Cewa"Zaku ganta Wata Doguwa Baka,baka mai Manyan Ido Haka Dai.."Da
Sauri D'ayan Tace"Ok Headgirl.."Kansa ya Shafa kafin yace "I Think so....".

Juyawa Sukayi suna Fadin Bari Su mata mgana,Aneesa na kwance Suka Shigo Tana
ganinsu Ta Mike Tana kallonshi Cikin Girmamawa Suka ce"Good Afternon Anty
Aneesa.."Cikin Halin ko In kula tace"Afteroon How can i help u..? Tafada Tana
kallonsu Domin Indai zakayi mgana Dasu Aneesa u must Speak English Juniors Kuwa Duk
Wacce Ta Kuskura ta musu mgana ba Da Turanci ba,Zata gane bata da Wayau Lokaci Daya
Makranta Ta Fara zama Normal ba Laifi Suna Kokarin Gwada Turanci Koda basu iya ba.

Dayar ce tace"U hv a Vistor..."Kallonsu Tayi kai Tsaye kafin tace"Vistor...?


Who.."? Suka Hada Baki Wajen Fadin"We Don't know Anty.."gyada kai Tayi kafin
Tace"Ok u can go Am Coming..."Daga Haka Suka Fice Daga Hostel Din,Aneesa Kuwa Ta
Dade Tana mamakin Waye yazo Wajenta Wata Zuciya na gayamata kasim ne,Wata kuma na
karyatata Hijabin ta Fari Ta Dauko Ta saka Bayan ta Zura Takalmin ta ta Fice.

Sukowa Suna Fitowa Daga Hostel Dinsu Aneesa Suka karisa Suka Sanar Dashi gata nan
Zuwa Godiya yayi musu,kafin Su Wuce Zuwa Inda Zasu,Shiko Jikin Motar ya Jingina ya
kurama Inda yaga Sun Fito Ido yana so yaga ko Ta Ina Aneesa Zata Fito koda taFito
Ta Dan Tsaya sun yi mgana da Wasu yan Ajinsu suna Tambayanta su B.kaita tace suna
Clinic Daganan Ta gangaro Haraban Makrantan Ta Wulga Ido Da Farko,Kasim bai ga
Aneesa ba sai da Ta kariso Haraban Makranta tana Waige Waige kana ya ganta Wani
Ajiyar Zuciya ya Sauke yana kallon Fuskarta Saboda yadda Ta Fadamai a Ido ganin
bata ganshi bane yasa ya Fara Taku Zuwa gareta Daidai Lokacin Data Waigo Zuwa
gareshi Suka Hada 4eyes balle ma yadda ya kafeta da Ido Sosai.

Wani yam Taji Tana kara Fiddo Ido Waje Tana kallonsa ganin Haka yasa ya saki
Dariyan Jin Dadi Lokaci Daya ya Tsaya Cak yana kallonta bayan ya Saka Duka
Hannuwansa ya Rike kugunsa Kuma yana kallonta,takowa Aneesa Tafarayi Zuwa gareshi
Lokaci Daya Tana Sakin Mirmishin Jin Dadi Har Tazo gabanshi Hannu ya Budemata
Alamar tamai Oyoyo Harara ta sakarmai Tana Tura karamin bakinta kafin ta Wucesa
Zuwa Wajen Motarsa Kirar prado,Bayanta yabi yana Jin Wani Farinciki na
Ratsashi,bakinta yake kallo yana ji kamar ya jawota ya Rumgumeta ya Tsotsi
bakinta.....

Jikin motar Shima ya Jingina yana Langwabemata kai,Hararan sa Take mai Cike da Wani
Salo kallonshi Take Tana Morewa Yana Sanye Cikin Wata Farar Gezer Dinkin Zamani
Riga da Wando da Hula Aikin Jikin Rigan black ne,Hakama Hulan kansa Rufaffen
Takalmin kafarsa ma baki Ne Shima Bakin ya Turamata yana Fadin"Ba gaisuwa wifey..?
tura baki tayi kafin tace"Toh ba kai bane kaki Zuwa Tundazu ba ina ta Jiranka.."
tafada a shagwabe tana wani juya ido kamar wata yarinya.

Hannayenshi ya Hada Waje Daya yana Fadin"Afuwan princess Tun Safe na Fito motata ce
Ta lalace Bisa Hanya sai da na Shiga Cikin gari na Dauko Bakanike Is not my Fuilt
princess.."Yafada yana Kara Narkemata,duk ya kashe mata Jiki Tana kallonsa ya kara
marairaicewa yana Fadin"Kin Hakura Princess.. ? Kai Ta gyada mai Tana Mirmishi
Cikin Jin Dadi yace"Thanks Wifey,I miss u much..Kwanakin da muka Dauka bama waya
bana ganki na Shiga Damuwa in kun lura na Rame ko princess.?"Yafada yana Taba
Wuyansa Hararan Wasa Tamai bata mai mgana ba,Shiko ya saka mata Dariya yana
Fadin"Eh mana ammh ke naga kiba kika Kara kin zama yar lukuta Abunki..."Wata
Hararan Ta kara makamai yayi Gefe Yana Dariya Lokaci Daya yana Fadin"Na bani ni
kasim Amaryar tawa kuma Hukuncin Harara kawai zata Dinga bani in nayi mata
laifi.."Wani kallo Tamai kafin tace"Waye Amaryanka din..?

Kai Tsaye yace"Ke mana Aneesa..."yafada yana Kafeta da Ido Lokaci Daya Suka Shagala
da kallon Juna har su B.kaita Suka kariso Wajensu suna kara Murza Idanuwansu Cikin
mamaki Ganin Aneesa da Wani Abun da basu Taba ji ba balle lbri,bayan Sun Dawo Daga
clinic karbomata mgani Suka koma Hostel bata nan Wata Maryam Dake Barayinsu ne Tace
Ta fita an zo Nemanta koda suka Fito basu Ganta ba,Jamila hadi ce ta Nuna musu Ita
Har Suka kariso suna mamakin Abun ganin basu san da Zuwansu ba ya sanya B.kaita
tayi gyaran Murya Wanda ya Dawo Dasu Daga Cikin Hayyacinsu na kallon Kauna da Suka
bi Juna Dashi.

Cikin Rage girman Idonta Aneesa Ke kallonsu kafin Tayi mgana B.kaita ta Rigata da
Fadin"Sannu mara lafiya ." tafada Tana Hararanta yar Dariya Aneesa Tayi Tana Rufe
Fuska Da Gefen Hijabinta Lokaci Daya Tana Satan kallon kasim Dake kallon Su B.kaita
Shima yana Mirmishi Lokaci Daya yace"Au ce muku tayi bata lahiya..?
Yafada yana kallonta Cike da Soyayyah.

S.jibiya tace"Eh magani ma mukaje Clinic muka karbomata Ashe Ciwon na luv ne ko
Anee..? Ta gefen Hijabinta Take lekosu Tana Dariya Shima dariyan yayi yana Fadin"Ku
mata Uzuri nine na bata mata Lokaci ya kamata Tun Around 10 ina Wajen nan Banzo ba
sai yanzu.."B.kaita ta gyada kai Tana Fadin"Mufa muna Cikin Duhu ke Aneesa kimana
Baya kece kuwa kodai Watace Dabam.."Aneesa Ta Bude Fuska Tana Fadin"Watace Dabam
Don mai garinku.."Dariya Sukayi Gabadaya kafin Aneesa Ta gyara Tsayuwa Tana
Fadin"Kasim meet my Childhood Friend,Bilkisu kaita and Salamatu s Jibiya Abunda
yasa kaji nace Childhood Frnd we are here Together tun Jss1.."Kai ya gyada yana
kallonsu yace"Masha Allah Sannunku kawayenmu.."Mirmishi Suka mai kafin Suce"Kaima
Sannunka..."

Juyawa Aneesa Tayi Tana kallonsu kafin Tace"And u Meet my Boyfriend Kasim..."Tafada
Tana Mirmishi Ido Suka sakarmata Suna kallonta Cike da mamakin mganarta Duk da Tun
Zuwanssu Wajen Suka Fahimci Wani Abu,B.kaita ce ta gyada kai tana Fadin"Aneesa
bukar bulama u ar a great Player Shegiya Wato Duk kin maidamu Hoto,Tunda muka Dawo
Hutu kika zama Wata Iri Ashe Ashe kin Fada Soyayyah ne..."Tafada Tana Hararanta
Dariya kadai Take musu kasim na Tayata kafin yace"Toh ai bakuma sani ba Nacita
gyara am not her Boyfriend.."Cikin wani Kallo Aneesa Tace"Umh...Am whta.?

Yana Mirmishin Jin Dadi yace"Am Ur Husband to be in d Next of 6month Insha


Allahu.."Yafada yana kallon Ameesa Ido ta Zaro ta kallonsa kafin B.kaita
tace"Really..?"kai ya gyada kafin yace"Sure...Albishir din Dana keta Rawan Jikin
Zuwa na mata kenan bayan Tahowarki mkranta ba mun Rabu zanje katsina na samu Abba
Akan mganarmu ba..?

"Kamar Wata kadangaruwa haka Aneesa Ta gyadamai Kai Cikin Sanyin Murya ya Cigaba da
Fadin"Toh ina Samunshi Shikenan mgana ta je Wajen Ya Muktar,Daganan kuma ya Kira
chan gida Borno,Atakaice dai Satin Daya wuce Suka zo Kuma Aka Sanya Rana bayan An
Biya Sadaki,Yanzu dai Kuna gama Candy za"ayi bikin mu ku kaimin Amaryata
kaduna.."Ya karishe Mgana yana kashema Aneesa Ido..

Shewa B.kaita da S.jibiya Suka Saki kafin ta su Tafa Suna Fadin"Allahu Akbar kaji
masu yi Don Allah..Aneesa As a Bride Woww..Allah ya sanya alheri We are so
Hppy.."Suke Fada Suna ma Aneesa Dariya Wacce ke Tura baki Ta bata Fuska Domin
Batata zaton Komai zai zo Haka Lokaci Daya ba,Kasim na Tsokanarta su B.kaita nayi
karshema Wata katuwar Darduma ya Dauko Daga Motarshi ya Shimfada nan kusa da Motar
nashi Suka Zauna Suna ta Hira,kafin su B.kaita su basu Waje suka koma Hostel suna
mamaki Wai Aneesa Zata yi Aure ammh kuma Ransu bai musu Dadi ba yadda Aneesa Ta
Boye musu lbrin kasim Alhalin Su kuwa ko Saurayi Sukayi In Suka Dawo Hutu Jikinsu
na Rawa Zasu kwashe su bama Aneesa lbri Ammh Ita sai ta boye musu Harga Allah Abun
bai musu Dadi ba.

Bangaren Aneesa da Kasim kuwa Hirar Soyayyah Suka Sha kamar bazasu Rabu ba,sai
Wajen 5 na yammah kana yace mata Zai Tafi Shima bawai Don ya gaji da ganinta bane
A"a Saboda kada yayi Dare Ahanya kuma Haraban Mkrantan yan Visiting din Sun Fara
Watsewa,Su B.kaita yace ta kira suyi sallama,koda suka zo nan suka ga Aneesa Tayi
Narai narai kamar zatayi kuka Haka Shima Baki Suka Rike suna musu Tsiya,booth Din
Motarshi ya Bude Ya Fiffito ma Aneesa da Siyayyar Dayayi mata Kaya kamar za"a bude
Shago Har sai dai Tace kayan Sun yi Yawa,yana kallonta Cike da Kauna yace"Antytin
for u princess kuma ga kawayenmu nan u can Share it together..."Mirmishi Tayi tana
mai godiya suma da Godiya suka bishi da Zai Tafi 10k yabama su B.kaita itama 10k ya
bata Dakyar Suka karba Bayan Sunga ya Nuna baiji Dadi ba,Har Motarshi ta Fice Daga
Haraban gidan Aneesa na Tsaye tana Dagamai Hannu kamar Zatayi Kuka,su B.kaita na
kallonta Hostel ta Wuce tana Share Kwallah suka bita da Dariya Wasu Juniors Dinsu
suka Kira suka zo suka Daukan musu kaya Zuwa Hostel dinsu.

Suna Zuwa Suka ganta kwance,banza Suka mata Suka Fara Bude kayan Ciki babu Abunda
Babu Hadda pad Roll guda Duk da Suma kowannnensu yana Zuwa Dashi Daga gida,baje
kayan Sukayi Suna kallo Ciki harda Takeway din Chips dayayi mata Guda biyar,ita da
B.kaita Sukaja nasu suka bude Suka Faraci tana gannin Basu kulata ba Tagane Suna
Fushi Da Ita bata Bi Takansu ba sai da Taje masallaci Tayi sallah kana Ta Dawo
Dakyar ta iya lallashinsu bayan ta gayamusu Farkon Abun Tare da Musu Rantsuwa kafin
Su yarda Su koma Tare Suna Santin kayan Lokaci Daya Suna lbrin Irin Bidirin da zasu
gudanar Lokacin Bikin Aneesa Ita dai Tana Jinsu Tana Tayasu Da Dariya.

*******
Rayuwa Tana ta gangarawa Domin Da gari ya waye Sai ta maidashi Wuni,Daga Wuni yayi
Sai ya zama kwana Da kwana yayi sai Afara Kirga Kwanaki Daga Kirgan kwanaki sai
Afara Kirga Sattitika Daga Satittitika sai Afara na Shekaru Ahaka zamu Ta karar da
Lokacinmu batare da Mun Fargaba

Acikin wannan yanayin ne gashi Yau da gobe bata bar komai ba Shiryen Shiryen Bikin
Aneesa Sai karatowa Yakeshi gashi har Saura Wata Daya Tuni Suka kammallah WAEC sun
Fara NECO,shirye Shirye Ta ko"ina Yinshi Akeyi Ta bangaren Gidansu kasimbkuwa suma
Suna ta Yin nasu Duk da Umma batason Auren Ammh Abba kabiru ya sakamata Ido Dole Ta
Shiga Taitayinta Abunda kuma yafi bata Haushi ganin yadda Mama Sahura ta Shige Gaba
Akan Komai kamar Itace Uwar Ango Domin Tunda kasim ya Fahimci Umma bata kaunar
Auren sai ya koma Wajen Mama Sahura da Ita yake Dukkan Wasu Shawarwari Hatta Kudin
kayan Lefe Ita ya Turomawa Sukaje Dubai Ita da Inna Rukayya Suka Hadomai komai Umma
ko Dataji labari kamar ta Rusa kuka saboda Takaichi Abba kabiru yace Komai ya Faru
Ita taja tunda ta Nuna bata Ra"ayin Auren.

Bangaren Gidansu Aneesa Ko Borno Suma Suna ta Shirin Bikin Domin Aneesa Ta Tubure
kan Borno zata Dawo Tun Ana Saura Sati Daya,Zasu yi bikinsu Ranar Alhamis, jumma
Daurin Aure,Ranar zasu Biyo Jirgi Su Dawo Abuja Shima Ayi biki asabar, Lahadi Akai
Amarya kaduna Inda Angonta ya gyara mata gidan da Ma"aikatan Dayake Aiki Ta bashi
Wanda yake Zaune Aciki Ya Muktar kuma Ya biya Kamfanin MARHABA suka zo Suka kawata
gidan Da kayan alfarma Babu Abunda ba"a Zuba ba Sai Wanda yagani Dukiya ne Aka
Narka Kamar ba"asan Ciwon su ba.

Ana Saura Sati Uku Biki Su Mama Sahura da Inna Rukayyah Matar Hashim Suka kawo
Akwatuna guda goma Gidan Ya Muktar ba laifi an Zuba kaya sai Wanda ya gani Don ma
mama Sahura tayi kwangila ta Rage kudi Da kayan sunfi haka an Karbesu Hannu Bibbiyu
Domin Anty Aisha Tazo Daga kano Nan ta Fara Sauka Wajen Anty Rahila Tare Duk zasu
Wuce borno da Aneesa in Sungama Jarabawa Ta Dawo gida,Harda katin biki Suka Kawo
Tare da 50k na Amarya da kawayenta Sunga kara sosai sai yammah Suka Tafi dama Tun
Jiya Suka iso garin Gidan Ya Hashim Suka kwana,sai Washegari Suka Jiya,suka bar
Matar Hashim din Zasu Taho ita da Zubaida in bikin ya Rage Saura kwana Hudu.

Tsakanin Aneesa Da Kasim Soyayyah sai Abunda yayi gaba...Sun kara Shakuwa da Kaunar
Juna,Domin Duk bayan 4weeks yana Hanyar Zamfara Sai dai ko in Aiki ya Rikeshi,Wata
Soyayyah yake Numa Aneesa kamar zai Cinyeta Danya,shiyasa Itama Take Sonshi Sosai
Kuma yana Burgeta Domin ya Iya kalamai Sosai,ammh Duk da Haba Babu Abunda ya Ragu a
neman matanshi da Shaye Shaye sai ma Abunda yayi gaba,ammh bai ta bari Aneesa Ta
gane ba,ko iyayensa banda Ya Hashim.

Ana Saura Sati Biyu bikinsu yaje mata Visiting Lokacin Sauransu paper Daya Su
kamallah Neco,katin Bikin ya kai mata Dana program of Event Duk da Tace batason
Bidi"a Sai da ya Sanya Lonching wanda Zasu gudanar bayan sun Dawo Daga Abuja Dinner
kuma A kaduna zasuyi bayan an kawota ,sai Walima wanda zasu gudanar agarin Borno
Domin Ya Muktar ya Roki su ya Ali kan Su bari Adaura Auran Anan borno Dakyar Suka
Hakura,Ammh Sunso Komai Ayishi a Agarin Abuja..

Gabadaya Meet Dinsu Sunyi Murna da Auren Aneesa Wanda Su B.kaita Suka yi ta raba
Katin Bikin Har da malamai Sun Bamawa Sukace Suna gayyatarsu,Meet dinsu Da yawa Sun
maAneesa akawarin Inshu Zasu zo Abuja Tunda Borno Tayi Nisa,Bikin ya Rage Saura
kwana goma Sukayi Candy Wanda Ranar Tazo da Dimbin Tarihi bayan kwashe Shekaru
Shidda A GGSS Kwatar-kwashi,Sunyi murna Sosai Harda Saman Dutsenan sai da Suka Hau
Aneesa Tace bazata Hau ba su B.kaita suka Jata ta Hau sai gashi da Tashin Aljanu Ta
Sauko Duk da Sun Dade basu Tashi ba,Haka suka kaita masallaci ba Ita kadai ba kusan
Rabinsu Sai da Sukayi Borin Aljanu Ranar Hatta dasu B.kaita basu Tsira ba, domin
Dutsen Yana da Tarihi dama baka hawa ka Sauko Lafiya.

Mallam Inuwa baizo Daukanta ba sai Washegari bayan Tayi sallama da Su B.kaita kan
Zasu Taho In Biki ya Rage Sati Daya Su Wuce Borno Tare Ahaka Suka Rabu Kowacce
Direban gidansu yazo ya kwashe Ta ita da kayanta Suka Rabu Suna Hawaye da kukan
Sabo na Rabuwa da Juna,Aneesa ta Fara Tafiya sai S.jibiya B.kaita ce ta karshen
Wucewa Cike da Kewar Makrantan kwatar kwashi wanda suka kwashe shekaru har Shidda
suna gwagwarmaya.

*Shakira...*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?14*

Ranar Jumma"a Aneesa Ta Dawo Abuja Ranar Monday kuma Da Yammah Su B.kaita Suka Diro
Ita da S.Jibiya Domin Salamatu Ta Biyama B.kaita Suka Taho Tare,Aneesa Tayi murna
Sosai Haka Suka Kule Adaki suna Hira da Shewa,washegarin Talata kuma Suka Bi Jirgin
Zuwa Borno,ita dasu B.kaita da Daada da Anty Rahila da Anty Aisha Da Hibba da
Junoir,Mallam Inuwa ya kaisu Aiport din Nmandi Azikiwe International Airport,Saboda
Ya Muktar Baya nan Yana Lagos,daganan jirgi bai Diresu Ko"ina ba sai Babban Filin
Jirgin Garin Maiduguri,Daganan Suka Nemi Tashan Mota Zuwa Cikin Garin Borno...

Koda Suka Isa gida Sun Iske gida Cike da Jama"a Yan"uwa da Abokan Arziki,agida Suka
Iske Anty yagana da Anty Nafee,suna Isowa Anty Yagana Taja ta Zuwa Sasan matar ya
Ali Khadija Ita da Su B.kaita Ashe mai gyaran Amarece ke Jiranta Itama Matar
Sunanta yagana,Nan fa batare da bata Lokaci ba Sallah kadai Sukayi Sukaci Abinci
Aka Fara mata Hadadden Halawa Ta garin Maiduguri Su b.kaita na gefe Suna kallon
Aneesa Cike da Sha"awa Wayar Aneesa Dake Hannun S.jibiya kuwa *D.K* sai kira yakeyi
Wato Darling Kasim ammh sai su Dauka suce bata Kusa,Dayake ya Siya mata Waya
lokacin Dayaje mata Visiting din Karshe.

Anty Nafee kuwa sai Harare Harare Take ganin ba Wanda yabi ta kanta yasa Ta kama
Kanta Sanah ma Cikinsu Aneesa Ta Shige Haka Mamarta tace mata Wai ai Aneesan bata
girmeta ba Itadai Aneesa Ko Ajikinta Domin Tunda Suka Iso Borno Taji Kawai Jikinta
yayi Sanyi Sosai,Bangaren Mutan gidan kuwa Waje ya Kachame gashi su Ya Ali sun
gyara gidan Yaji Fenti Haraban Gidan ma Angyara Sosai Saboda masu Daurin
Aure,tako"ina Shiri Ake Mama yana ce kan Komai ita dasu Anty Yagana Falmata kuwa na
Goge Cikin yan"uwana ana ta soyan nama da kaji kamar ba Uwar Amarya ba.

*******

Ranar Laraba da misalin Karfe 10am na Safe Jirgin Daya Dauko Mutane Daga Malesia ya
yada Zango Ababban Filin Jirgin Murtala muhammed Dake lagos Daga Cikin Sahun mutane
goma Da Suka Fito Daga Cikin Jirgin na Hango Mr Bello Cikin Shigar Riga da Wando
Duka black sai Wata Jaket din Dake Jikinsa mai Ruwa toka,kansa babu Hula sai
gashinsa Daya Sha gyara kamar balarabe Kafarsa Sanye Cikin Wani Ubansu bakin Booth
Din Takalmi baki,Fuskar na kallah ya kara kyau da Cika Hancinsa ya kara Fitowa
Sajensa baki ya kara yawa da Kwanciya Idanuwansa Suna Sanye Cikin Wani Siririn
glass mai kyau da Tsari Daga gani na gayu ne sai Hannunsa Dake Sanye da Agagon Fata
na Kamafanin Armani mai kyau da Tsari.
Bayansa goye da Wata Jakar baya,Hakama Hannunsa Rike da Wata karamar Bakar Jaka
dayan Hannun nashi kuma Wayace Hannuna,yana latsawa Tunda ya Sauko Daga jirgin yake
sakin Kayatattacen Mirmishi Shi kadai yana Jin Farinciki Acikin Ranshi na yau gashi
ya Dawo kasar sa na Haihuwa bayan Watanni goma baya Cikinta

Daganan Sake Booking Din Wani Jirgin yayi Zuwa Abuja sai Da yadan Jira kadan,yunwa
yakeji Shiyasa ya Siya Snaks da Hollandia ya Shafa kafin Jirginsu ya Tashi,Around 2
pm na Rana Jirginsu ya Sauka A Nmandi Azikewe International Airport
Abuja,Saukowanshi kenan ya samu Kiran Uncle Aminu,Nan ya Daga Sukayi mgana Inda Shi
Uncle Aminu ba yanzu zai Dawo ba Tunda Masters Dinshi yakeyi Achan Ammh kwananan
Zai zo Hutu gida.

Mallam Inuwa yama waya kan yazo Filin Jirgi ya Daukeshi,Cikin Murna da Farinciki
yazo ya Daukeshi Zuwa Gida Tun Amota mallam Inuwa kesom Sanar Dashi Ai gidan ba
kowa ammh bai ba mganar Muhimmanci ba,Har Suka Iso gida Kai Tsaye Mension Dinsa ya
Nuna Makulli yasa ya Bude Kofar kafin ya Dauki karamar Jakar da Mallam.Inuwa ya
Rakoshi da Ita Zuwa Cikin Falon Lokaci Daya yana Maida Kofar ya Rufe.

Bedroom Dinsa ya Wuce yayi Wanka yayi sallar Azahar ya Chanza kaya yabi Lafiyan
gado Saboda Gajiya,Barci Mai Nauyi ya kwasheshi gashi ya kashe Wayarsa,Sai Wajen 8
ta Wuce kana ya iya Tashi, Salati ya Hau yi yana mamakin barcin Daya sha kafin ya
Sauko Daga kan Gadon Tailet ya Shiga ya Watsa Ruwa kafin ya Fito Jallabiya ya sanya
da Bakin Dogon Wando ya Kabbara sallah Sallar La'asar yafarayi kafin mangarib Ya
kuma Dora da Issha"i sai bai yi Shafa'i da Wuturi ba yabari inda zai kwanta sai
yayi.

Mikewa yayi yana Mika Saboda barcin bai Isheshi ba,Cikinsa ya Shafa yana Yamutsa
Fuska Domin Harga Allah yana jin Yunwa Wajen Ma"ajiyar Takalmansa ya Nufa kamar
Za"a bude Shago,wani Tattausa ya saka Baki mai kama da Silifas ya Fito Falo,bai
Tsaya ba ya Nufi Hanyar Kofa ya Fice Daga Falon yana Saukowa Daga Stairs ya Hango
ya Muktar ya Fito Daga Masallaci Shima yana Sanye da Irin Kayanshi ammh Shi Harda
Hula Mirmishi Bello ya saki Tundaga nesa Sai da Suka zo Gab kana Ya Muktar ya Lura
Dashi Cikin Mamaki yace"Ah..Wanake gani kamar Bakin Turai..?

Yafada yana Dariya,Da Sauri Bello ya karisa gareshi Sukayi Hugging din Juna Lokaci
Daya Ya Muktar na Dukan Bayanshi kafin Su Saki Juna,suna kallon Juna Fuskokinsu
Cike Da Fara"a Kafadansa ya Daka yana Fadin"jiya munyi Waya baka Sanar dani Today U
are Coming ba..? Yafada Lokaci Daya yana Riko Hanmunsa Suka Fara Taku Zuwa Cikin
gida bello na Fadin"Suprise nake son na Baku yaya More Expecially Daadata.."Dariya
yayi kafin yace"Ah lalle Saukan yaushe..?Yafada Daidai Lokacin Da Suke Shiga Cikin
Falon gidan Har Lokacin Hannayensu na Sarke Cikin Na Juna.

Bello yace"Dazu da Rana na Sauka fligt Din Lagos na Shigo Daganan ne na Shigo Wanda
ya kawo Ni Abuja..",Mirmishi Muktar yayi Daidai Lokacin Da Suka Shiiga Baban Falon
na Anty Rahila,Zame Hannunsa Bello yayi yana Fadin"Bari na Fara ganin Daadata kafin
naga kowa.."Dariya Ya Muktar yayi Lokaci Daya yana Zama kan Daya Daga Cikin Kujerun
Makeken Danning Table Din Dake Wajen Alheri Nata Faman Jera Kololin Abinci Bayan Ta
gaishe da Da Muktar din ta kuma yi ma Bello sannu da zuwa,Har ya kama Hanyar part
din Daada yaji ya Muktar na Fadin"Daada fa bata nan Gidan babu kowa ni kadai ne sai
kai yanzu daka Dawo.."Cike Da mamaki ya Waigo yana Tafiya Lokaci Daya yana
Fadin"Ahf...Ita Daadan..?yafada Daidai Lokacin Daya kariso Kusa da Ya muktar Yaja
Kujera ya Zauna Domin Azahirin Gaskiya Duk da yunwa Data Fito Dashi.

Ya muktar na Latsa Wayar Hannunshi yace"Yes yanzu ma su Nake Nema Wayar bata
Shiga.."kai Tsaye Bello yace"ok ina Suka Tafi ne Gabadayansu Lokaci Daya..? Ya
muktar bai yi mgana ba sai da ya Ijiye wayarsa gefe yaja Filet din Da Ke Gabansa
Wanda Alheri ta Cikashi da Shinkafa,jalop gefe kuma Coslow ne,ya Daga Cokali yana
Fadin"Suna Borno Dukkansu Nima ina lagos Sanda Suka Tafi.."Bello bai Damu ba Illah
Zakuda Kafada Dayayi shima yaja Filet din gabanshi Suka Fara Cin Abinci Bakajin
Motsin Komai sai na karan Cokula Cikin Koshi Muktar Daya Ijiye Cokali yace"Baka
Tambayi me Sukaje yi ba..? Yana Tura Abinci bakinsa ya Girgiza kai baiyi mgana ba
Sai Bayan Daya Tauna Lokaci Daya yana Fadin"Nasani ko Sun Raka Anty Rahila ganin
gida ne.."?Yafada yana Cigaba da Cin Abinsa Mirmishi Muktar Yayi kafin yace"Waya
gaya Maka Bikin Aneesa Suka Tafi Jibi Take Aure.."Ruwan Daya kai bakinshi Da niyyar
sha ya Furzai da karfi jin Sunan da Ya Muktar ya ambata Cikin Mamaki da Zaro Ido
yace"Wata Aneesan..? Ya Muktar yayi Jagale yana kallon Bello kafin yace"Wata Aneesa
kasani..? Dalibar ka dai Kanwar Rahila ba.."

Jinjina kai Bello yayi kafin yace"Ikon Allah Yanzu Wannan Kwailan yarinyar ne Ta
isa Aure..? Tab mijinta ya Shiga Uku ni Wlh Kwalkwalwata ta manta da Ita sam Allah
bada zaman lafiya.."Ya Muktar bai ce komai ya Mike yana Yar Dariya Lokaci Daya Yana
Share bakinshi da Tissue yace"Na gida ne zata Aura Dan"uwanka ne Kasim..."

Bello Daya Tura Shinkafa Cikin baki ya kara Fito Da Ita bai Shirya ba,Cikin Faduwar
Gaba da Firgici Bello yace"Wani kasim din Yaya..? Cikin Wani kallon lafiyanka kalau
Ya Muktar yace"Wanda ka sani Kanin Hashim,Dan Wajen Abba Kabiru..."Sake Waro Ido
Bello yayi kafin yace"Innalillahi garin yaya..? Shaye Shaye yake da Neman mata
fa..ko ya Daina ne..? Wani kallo ya muktar ya sakarmai kafin yace"Meka ke fada ne
Bello? Bangane ko ya Daina Shaye Shaye Da Neman mata ba..?

Mikewa Bello yayi yana Fadin"Ya Muktar Kasim fa Dakake gani Ba Namijin Aure
bane,Shaye Shaye yake fa Da Neman mata ko Bunsuru ya Shafamai lafiya,ya kamata ku
Fara Bincike kafin ku yanke Hukunci koda Kuwa Ni nan kaina ne,ya kamata ka Bincika
Personal life dina balle wani.."

Hannu Muktar Ya Dagamai yana Hararansa yake Fadin"Ka bani Mamaki Bello,Ban taba
Zaton Dom Baka Shiri Da Su kasim zai Saka kamai Wannan Kazafin ba Shedar Zina fa
karfi gareta.."Cikin Rantsuwa Bello yace"Wlh Yaya Am Telling u d Truth Naji Abakin
Wanda bazai Tabamin Karya ba.."Tsaki Yaya Muktar yaja kafin yace"Au Ashema Ji kayi
ba gani ba..plz mubar wannan mganar bana son Talking Rubbish kuma Daga bakinka u
better keep ur mouth Shout Domin babu Abunda Mganarka zai Chanza On Firday akwai
booking Flight Zuwa Maiduguri Duka tare dasu Abba kabiru zamu Wuce,Mu Dawo Aranar
tare da Amaryar Asabar Suyi bikinsu Anan on Sunday kuma Akaita gidan Mijinta a
kaduna so in zaka je u are Welcome in kuma U are not Coming No problem u can
Stay..."

" Ya kareshe Fada yana Zakuda mai kafada,Daga Haka ya barshi nan Tsaye ya haura
sama Cikin Sassarfa ransa bace da kalaman Bello Wanda Suka bata ma rai Bai Dauka
Bello yana da Wannan Halin ba sam.

Shiko Bello Jikinsa ne yayi Sanyi Har Ya Muktar ya kulema ganinsa,Ajiyar Zuciya ya
Sauke Cikin bacin Rai da Jin Haushin Yadda Ya muktar yaki Sauraranshi Saboda Wani
Uzuri Nashi mara Tushe Ammh Tsakani ga Allah In Har Suka Auramata kasim Sun cutar
da Ita Abun nashi Yayi yawa bayan Neman mata harda Shan giya Haba Zasu kashemata
Kuruciya wlh,Cikin Bacin Rai Shima ya bar part din ya Muktar din Zuwa part Dinshi
Ranshi na Kona Tiolet ya Fada ya sakarma kanshi Shower Haka Kurum yaji Ransa na
Kara baci na ganin yadda Ya Muktar ya nuna yafi yarda Da Bangaren da Suka Cutar da
Rayuwarsu Fiye Dashi Abun in ya Tuna yana Kara batamai Rai Sosai.

Baisan lokacin Daya kwashe yana Cikin Shower ba sai da ya gaji da Kanshi yayi wanka
ya Fito bayan ya Dauro Alwala,wata jallabiyan ya sake sakawa Wanchan ya Barota
Cikin Bucket din Dake Tiolet,Shafa"i da Wuturi yayi kafin yayi Addu'o'insa Daya
Saba, Gadonsa ya Haye bayan ya Cire Jallabiyan ya Rage Dagashi sai Boxers,jakarsa
ya Bude ya Fito da karamar laptop dinsa Daya Chanza a Malesia,kunna ta yayi bayan
ya Kara Haura wa saman Tsakiyar gadon Sosai,ya sakata Atsakiya yafara Shige
Shigensa.
Duk yadda yaso yayi aikin Abun ya gagareshi,Duk da Ko ya ci karo da Sakon Farinciki
Daga Jami"ar Bayero University Dake Kano BUK tun Yana Malesia ya Tura musu
Takardunshi ta Email Shine yanzu Suka Turomai Sakon Sun Daukeshi lecturing a
Mathematics Department,Yanzu Suna Jiransa yazo ya karbi Appointment latter
dinsa,bayan yazo yayi Reporting,Domin Dama Tunkafin Tafiyarshi yasaka ma Ranshi in
ya Dawo zai bar Koyarwa a Makaranta Secondry ta kwatar kwashi Zai koma Wata Jami"ar
Agida Nageria Suma Su Amfana da Basirarsa.

Ture Computer yayi yana Dafe kanshi Lokaci Daya Aneesa Ta Fadomai Arai,ya Runtse
Ido yayi yana Tunata tun Farkon Zuwanta gidan Har Zuwa Lokacin Daya bar Kasar
Tsiwarta Rashin kunya da Tsoronta yake Tunawa Tare da karamin Bakinta,Aranshi
yanaji kamar in ya bari Aka Aura mata Kasim ba"a ma Maraicinta Adalci ba,Mikewa
yayi ya Fara Zagayen Bedroom Dinshi Lokaci Daya Yana goya Hannayenshi Abaya Kansa
ya Dau Zafi bashi da Wani Hop in ba Ya Muktar ba Aneesa bashi da kyakyawan Alaqa da
Ita koma yana Dashi yanzu Lokaci yakure,Kansa ya Dafe yana Tunanin mafita kafin
Lokaci Daya Wani Abu ya Fadamai Arai da Karfi ya Furta

""Sani....Yes bari na Kira sani Zai Taimakeni Insha Allahu Tunda yasan Komai da
Hanzari ya Nufi Wayarsa ya Dauko Contact Dinshi ya Shiga ya Lalubo Lambar
Sani,wanda yama Saving da Sani kaduna,har sai da Wayar Ta katse Sani bai Dauka
ba,Tsaki Bello yaja kafin ya kara Kira Yana Fadin"Kai pick d Call plz.."Yake Fadi
Lokaci Daya yaji Sani ya Daga Kiran yana Fadin"Ah Malamin makranta Yau Agari.."?

Ajiyar Zuciya Bello ya Saki kafin yace"Sani How are u..? Sani yace"am Fine ka Dawo
kasar ne..? Don kwanaki in ban manta ba kace zaka Haura malesia ko..? Gyada kai
bello yayi kafin yace"Eh naje Yau ma na Dawo kasar."Washe baki sani yayi yana
Fadin"masha Allah Sannu da Zuwa An Dawo lafiya.."Bello Cikin kaguwa yace"Lafiya
lau,Don Allah sani Ranar Friday kana Available..? Yafada yaji ko Sanin zaije Daurin
Auren Ko A'ah..'

Sani yayi jim kafin yace"Gaskiya bana garima gabadaya Borno zamu tafi Wajen Daurin
Auren Wannan Abokin aikin nawa kasim Wanda na Taba Nuna maka Hotonshi nace ko ka
sanshi Shima Iyayenshi y'an Jikamshi ne..?"Cikin Farincikin Bello yace"Oh Allah
Sarki na ganeshi ba Wanda kuke Zencensa kai da Wani Abokinsa kan ya Cika Shigen
Neman mata da Shaye Shaye ba.."?Dariya sani yayi kafin yace"Extaly Malamin
makaranta Baka da Mantuwa Shi kuwa Kasim Kabir Jikamshi ba, Aiko Zaiyi Aure Kanuri
zai Auroma .."Yafada yana Dariya,

Gyara Tsayuwa Bello yayi kafin yace"Ahf toh ya Daina Neman Matan ne Dazai yi Aure?
Sani yace"Umh ya Daina mene..? Sai ma Abunda yayi gaba yanzu Haka ina bakin Titi ne
Muke Wayar nan naga Wucewarsa Amota Shida Wata kasan Abunda kebani Haushi da
kasim..? Bai bashi Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Kazantarshi Tayi yawa bama
zai Tsaya ga ya"yan Hausawan mu ba Harda kabila da Arna marasa Addini,kuma Duk
yadda yake Fadin yana Son yarinyar dazai Auro Wlh bai daina kwana Cikin maye
ba,kuma bai iya Hakura sai ya Kwana Tare da mace,Fisabillahi me Ake da Hali Irin na
Kasim kwata kwata ba Tsari Aini Wlh ina Tsausayama Yarinyar dazai Aura Kawota kawai
Zaiyi Bakincikinshi ya Kasheta.."Bello yayi Ajiyar Zuciya Takaichi na Cikashi
yace"Gaskiya fa..Toh Ba"ayi bincike bane Dagachan barayin Ita yarinyar..'?

Sani yace"Waya saninmu su Kasan yanzu ba Duka Aure Ake ma Bincike ba Indai kana da
Naira Alhaji ka gama mgana,balle Shi naji yana Fadin ko Matar Wani yayanshi to
kanwarta ne.."Bello yayi Saurin Cewa"Ok Nama Tuna Ranar nima zani Maidugurin Wani
Daurin Aure ko zaka Shigo gobe don Allah Sani mu Tafi Tare.."Shuru sani yayi kafin
yace"Kash.Gashi Tare da yan Office,dinmu mukayi Booking din Jirgi zamu Tafi."Da
Sauri Bello yace"No karka damu Sani Nima anan zan mana Booking Din Flight plz Dont
Say No.."Ajiyar Zuciya Sani ya Sauke kafin yace"Shikenan ammh ni bansan Wajen
Daurin Auren bafa..? Bello yace"Karka damu ba ga Waya ba.."

Jin Haka yasa Sani yace"Ok goben Zan Shigo Jirgi Zuwa Abuja in na Shigo zan Kira
ka,long Time Daman bamu Hadu ba.."Cikin Jin Dadi Bello yace"Yauwa..Sai na
Jika.."Daga Haka Suka yanke Kiran Gefen Gado bello ya koma ya Zauna yana Mirmishin
Nasara Kafin lokaci Daya ya mike laptop dinsa ya Dauke ya Kashe ya Ijiyeta kan Side
Drower,Kan gadon yahaye Lokaci daya yana Lullubewa da Blanket,bayan ya Zuro Hannu
ya Rage Hasken Dakin bai Dau Lokaci ba barci ya kwasheshi Cike da Jin Dadi.

******
Washegari Around 4pm Sani ya Kirashi yana Filin Jirgi Shida Mallam Inuwa Suka je
Suka Daukoshi koda suka Dawo Sun Iske Ya Muktar ya Dawo Gidan Dama Meeting ya Fita
Wanda Suka gudanar Afadar Shugaban kasa,koda Asuba Sun Hadu Amsallaci Bellon na
gaisheshi Dakyar ya amsa kamar Wani mai Ciwon baki Shidai Bello bai Bi Tankanshi
Domin yana Ji Aranshi bazai Taba bari Kasim ya Auri Aneesa Ba ko bakomai In
Hallayarsa ta Fito Filo sai anfi ganin laifi Ya Muktar Fiye dana Kowa.

Koda Sani yazo har Falon Ya muktar ya kaisa Suka gaisa Ganinsa da bako yasa ya saki
Fuska Suka gaisa Daganan Mension Din Bello Suka koma Sukayi Wanka Suka Ci Abincin
Da Ya saka Alheri ta Hauro musu Dashi,Sai da Suka kamallah Suka Shiga Hiran Duniya
kana Bello ya gyara zama yana kallon Sani Lokaci Daya ya Warware mai komai kuma ya
sanar dashi Irin Taimakon Daya ke Bukatar ya bashi Gobe in Sun Isa garin Borno.

Zaro Ido Sani yayi Cikin Kaduwa da jin Bayanan Bello yace"Kai Bello gaskiya bazan
iya yima kasim Haka ba kamar nafa Tozartashi ne a Idon Duniya karka manta an Taru
ne za"a Daura mai Aure..kai gaskiya Bello bazan iya ba Wlh ."Yafada yana Kallon
Bello Cike da Wani Tunani.

Mirmishin Yake Bello yamai kafin yace"U hv to do dis Sani kar ka manta Aneesa zamu
Taimaka fa,ni kuma na Cire yayana Daga Zargi yazakaji in mai irin Halin kasim yazo
Neman Auren kanwarka Alhalin bashi da kyawun Hali kuma,in ka Fahimci Haka Koda
Lokaci ya Kure zaka yarda ka Aura mata Shi.?."Tsuru Sani yayi kafin ya girgiza kai
yana Fadin"A"ah gaskiya bazan Bata Shi ba kam..Ammh bello baka..'Hannu Bello ya
Dagamai yana Fadin"Ba ruwanka kadai kawai Shaida zaka bada ni zan karisa Sauran
Aikin ammh Tabbas Ni muhammed Bello Jikamshi bazan Bari Adaura Auren Aneesa da
Lallatattacen yaron nan ba Insha Allahu kawai kamin Abunda na Rokeka plz.."

Sani ya Dade yana kallonsa kafin ya Sauke Numfashi yana Fadin"Shikenan Allah ya
kaimu.."Mirmishin Jin Dadi Bello ya saki Har fararan Hakoransa na Bayyana Waje
yace"Nagode Sani.."Daga Haka Suka Cigaba da Tattauna Batun,Sani na kara bashi Lbrin
Wasu Gurbattatun Halin Akuyancin Kasim Abun ba Dadin Ji,.

Sai bayan Sallar La"asar Bello ya karbi Key din Mota Ya jasu Suka Fita yawo Cikin
gari Shiko ya Muktar Tuni yayi Waya Zuwa Filin Jirgi An Riga an yi musu Buking Din
Flight Dukkansu Harda su Abba kabiru da Kasim da Hisham da Sauran Abokan Tafiya
Wannan Nauyin Muktar ya Daukeshi na Zuwansu Borno da Dawowarsu Batare Daya kara Bi
Takan Bello ba Bai san Shi kuma anashi barayin yagama Shiryama goben ba.

Ki biya ki karanta cikin salama.

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?15*

*BORNO*
_maiduguri_

"""Washegari Ta kama Jumma"a ne Ranar Daurin Aure,Tun jiya Gidansu Aneesa Suka Sha
Bikinsu Sosai In kaga Aneesa Lokaci Daya bazaka iya ganeta ba Saboda yadda Takara
kyau da Haske Duk inda ta Shiga Tana Haskawa Ga wasu Sirrinka kamshi Dake Tashi
Ajikinta Fatarta Ta koma kamar na Tarwada Saboda Santsi,Tasha kyau kamar ba ita ba.

Ita dasu B.kaita akama Kunshi ja da baki Suka kuma je gyaran Kai,Aneesa Ta sanya
kayan alfarma sosai Na Cikin kayan Da kasim yayi mata ne Wanda Suka zo da Wasu nan
Maiduguri Anyi Shagali Sosai Kowa kagani Cikin Farinciki musamman Anty Rahila da
Anty Yagana kamar Sune Suka Haifi Aneesa Saboda Sune kan gaba Bisa Komai.

Yau din An Tashi da Shiryen Shiryen masu Zuwa Daurin Aure ne Daga Cikin Gida kuma
Mata nata Shirin Wadanda Zasu Raka Aneesa Abuja Dagachan kuma Su Mikata kaduna,Daga
Haraban Gidan Kuwa An Share ko"ina Motocin ya Ali dana ya Sunusi Waje Suka maida
su,filin Wajen Aka Kawata Shi Da Fararan Kujeru Daga Cikin Falon su na Baki Dake
Wajen Cikin gida Shima an gyarashi Tsab Saboda nan ne Waliyan duka bangarorin zasu
Shiga Domin Gudanar da Daurin Aure gefe Daya kuma An Baza Tabarmu Abun Sai Wanda
yagani.

Tun karfe 8am na Safe Tawagar ha Muktar Suka Rakashi Zuwa Filin Jirgi na Nmandi
Azikiwe International Aiport Abuja Inda ya samu Abba garba,Abba kabiru,Hashim,Kasim
Ango da Amininshi Haruna Sai Wasu mutane Biyu Daga cikin Abokan su Abba
kabiru,Wanda Tun Jiya suka Iso Gidan Hashim Suka Sauka Wanda Tuni Matarshi da
Zubaida Suna Katsina Ana Shan biki Suma yau ne Taron Bikin nasu.,Kasim kuwa Tun
Ranar Alhamis ya Baro Kaduna Zuwa Katsina Shima sai da Hashim yamai Dirar makiya
Acikin gidanshi inda yakara Tarar Dashi da Wata mace Agida,Abun ya batamai rai ya
Dinga mai Fada Kuma ya matsamai Suka zo katsina Tare bayan yayi mai Rantsuwan ya
bari.

Koda Bello da ya Muktar Suka Hadu Bayan sallar Asuba bai saki Fuska ba Shima bellon
Dauke kai yayi ya Hade Fuska da Sani kadai Suka gaisa Agaban Idonshi Ya Muktar din
ya Fita Zuwa Filin Jirgi Ansha Uban babban Riga Suma karfe 9am na Safe Suka isa
Filin Jirgi Shida Sani Dukkansu Suna Sanye da Manyan kaya,Sani yana Sanye da Wata
Farar Shadda Riga da Wando Dinkin Tazarce Da Hulla zannah Bukar Sai Bello Dake
Sanye da Wata Gezner Mai Ruwan kasa Aikin Jikin Riga Brown Clour ne Haka Rufaffen
Takalmin kafarsa ma Brown clour sai Hulan kansa Zanna Bukar mai sakan Brown Agogon
Hannunsa na Fata ne,Shima Brown Clour ne,Fuskarsa Tana Fitar da Annuru na musamman
kallo Daya zakamai ka Fahimci Lalle Bafullatani ne,Wani Lokacin kuma Sajensa sai ya
Rikidar Dashi ya koma maka Sak Balarabe.

Suna Filin Jirgin kafin Su Tashi Yan Office din su Kasim Suka ma sani Waya kan
gashi Sun Tashi Ta kaduna Shi kuma yace su Hadu Achan gashi Afilin jirgin Abuja
Tanan zai Tashi basu Dauki Lokaci ba around 9 da wani Abu Jirginsu ya lulula
Sarararin Samaniya Domin Daurin Auren Safe Ne 11am bayan An Sauko daga Masallacin
Jumma"a Ayi Walima bayan Daurin Aure, Karfe 4pm na yammah Jirgin da ya Muktar yayi
booking na Amarya da Tawaganta Zai Tashi Zuwa Abuja...

Su ya Muktar Sun Isa Borno ba Dadewa,Domin Waya kadai yayi Daga Babban Headquaters
dinsu na nan Maiduguri Aka zo da Motocin Alfarma Aka Daukesu Zuwa Cikin garin
Borno,Sun iso ba Jimawa Tawagar yan kaduna Suka Iso Wato Abokan Kasim da Sauran
yan"uwa,Suna Zazzaune Aharaban Gidan Bayan Angama gaisuwa Suma barayin Su Yaya Ali
Baki ne Ta ko"ina ke Bullowa kama Daga Abokansu da Abokan Aikinsu Da kuma Toffin
Abokan Marigayi Bukar Bulama,

Ango kasim Kuwa Ya matsu Yaji Ance an Shafa Fatiha Yadda bakinshi yaki Rufuwa
Lokaci Daya,Yana Sanye Cikin Wata Ubansu Farar Shadda Riga da wando Da Babban
Riga,Shima aikin Jikin Kayan nashi Baki ne duka Abunda ke Jikinsa Bakake ne kama
daga Hula agogo,Takalmi Kallon Farko zakamai ka Fahimci Shine Ango Duba da yadda
Duka Fararan Hakoransa Ke Waje Zumudi yake Tayi zai Shiga Cikin gida yaga Aneesa
Abokansa na Rikesa Suna mai Shakiyanci Tun Daran Jiya bai Bar Aneesa Ta wani Runtsa
ba Suna ta waya yau da Safe ma Tun da Suka iso yake damunta da Kira Har Tagaji ta
Daina amsa Kiransa Domin Ita gabadaya Yau Din da Faduwar Gaba tatashi Zuciyarta
Tsinke Jikinta Duk baya mata Dadi Tana chan Bedroom din ya Ali Tana kwance kamar
Zazzabi ne ya Rufeta Su kuma Su B.kaita Suna Tsakar gida Ana Ta Hada Hada Abincin
yan Daurin Auren da Su Anty Rahila Su suka Tsaya Akan komai ya kammallah.

Sun Sauka a Filin Jirgin Maiduguri,Karfe 10am da wani Abu Daganan Tashan Mota Suka
Dauka Zuwa cikin garin Borno Bello yana Ta Uban Duba Agogo kada su Makara Adaura
Auren basu isa ba Sani kuwa Daya daga Cikin Abokan Aikinsu ya kira ya Tura musu
Address din gidan su Aneesa sun Iso Kofar gidan 11am saura Minti goma Sha Biyar
Ajiyar Zuciya Bello ya Sauke Bayan Sun Sauka Daga Motar da Suka Hawo Daga Aiport
sani ya sallameshi Bello Kofar gidan Yake bi da kallo Lokaci Daya da Haraban
Gidan,Domin get din Gidan yana Wangale ne ga Mutane nan Zazzaune Lokaci kawai Ake
Jira Bello bai Taba Zuwa Borno ba Wannan shine karon Shi na Farko Watakila kuma
Zuwan Nashi bazai ma Mutane dadama Dadi ba.

Cikin Haraban gidan Suka Shiga Sani ne ya nufi Wajen Abokan Aikinsu Dake Tare da
Kasim Ango Suna gaisawa Kallon Kallon Akayi Tsakanin Kasim da Bello Lokaci Daya
Kasim yaji gabansa ya Fadi Dayaga Bellon Wanda baisan Dalili ba,shiko Bello
kallonsa yake kai Tsaye Cike da Tsana ammh Fuskarsa bata Nuna ba Takowa yake Cikin
Izzarsa Zuwa garesu su kansu Tsayawa Sukayi Suna kallon Tsabar kyau da Zati Lokaci
Daya Har ya kariso Garesu yana basu Hannu da Ido Suke Binsa Sai da yazo kan Kasim
kana ya Dauke Hannunshi yayi kamar bai Ganshi ba,Kallonsa Sani yayi yana Dan
Zungurinsa Ammh Bello yayi Fuska sai ma Komawa Dayayi gefe ya Fito da Wayarsa
Hankalinsa kwance yana latsawa Lokaci Daya kuma yana Bin Mutanen Dake Haraban Wajen
da kallo..

Cikin Mamaki kasim ya kalli Sani yana Fadin"Sani Dama kasan Bello ne..? Batare da
Sani yabama Mganar Kasim Muhimmamci ba yace"Eh Tare mukayi universiy of Ibadan Mun
zauna Daki Daya He is My Friend Ashe ma Dan"uwanka ne na Biya ta Wajensa Jiya yake
cemin Shima yau din zai zo nan Daurin aure.."

ajiyar Zuciya kasim ya Sauke kafin yace"Umh."Daga Haka shima ya Dauke kai ammh
Azahirin gaskiya Jikinsa Yayi Sanyi Wanda baisan Dalili ba.

Su Abba kabiru da su Ya muktar Suna Daga Cikin Falon cikin gida wanda keda kofa ta
Waje So basu san Bello yazo ba Yaya Ali ne ya Fito Daga Cikin Gida yana Saba Babbar
Rigansa Bello Dake latsa Waya ya Hangonsa da hanzari ya Nufeshi Domin Sun Taba
Haduwa sau biyu Lokacin Dayazo Har Abuja yadaki Aneesa yana gidan Lokacin,kuma ko
ba Haka ba Kana kallonsa kaga Aneesa Agareshi Domin Suna Diban kama yana Isa Kusa
Dashi ya Bashi Hannu lokaci Daya yana mai sallama.

Mikamai hannu ya Ali yayi yana Kallonsa Cikin Mirmishi da mamaki yake
Fadin"Ah...Wanake gani Kamar Muhammed Bello..? Cikin Dariya Bello yace"Nine ya Ali
ya gida..? Yace"Lafiya lau kamar kwanaki naji Rahila na Fadin baka kasar ko? Bello
ya gyada kai yana Fadin"Eh Ya Ali Shekaran Jiya na Dawo kasar.."Ya Ali na Rike da
Hannunsa yake Fadin"Masha Allah..Allah sama Abunda Aka je nema albarka.."Bello ya
Rankwafa yana Fadin"Ameen Ameen Nagode.."

Ya Ali yaja Hannunsa yana Fadin"Shigo Ciki iyayan naka na nan Ciki ."Saurin Tsayawa
yayi yana Fadin"a"ah ya Ali kafin mu Shiga Ciki Akwai Wata mgana Da na Danikeso
kabani Dama mu Shiga Ciki Ayita kafin Adaura Auran.."Jim ya Ali yayi yana kallonsa
kafin yace"Wata mgana kenan Bello? Ina Fatan Lafiya ko..?kada kai Bello yayi yana
Fadin"Lafiya ba lafiya ba..In kabani Izini yanzu zan Kira Wanda muka zo Tare sai Mu
Shiga Ciki.."ya Ali da mganar ta mai Wani iri Yayi Jim kafin ya kada kai yace"To
Shikenan ba Damuwa.."Yafada Lokaci Daya yana Boye Tsoron Daya Shiga Ranshi

Cikin Hanzari Bello ya ciro Wayarsa Dake cikin aljihu ya Kira Sani Wanda ke Wajen
su kasim Suna Shakiyansu na Abokai,yana ganin kiran Bello yayi Saurin matsawa gefe
ya Daga Kiran cikin Muryan Bello mai Cike da karfin Gwiwa yace"Sani Juyo bayanka. ?
Da Sauri Sani ya Juya Suka Hada Ido Da Bello bai mai mgana ba Illah alamar ya Taho
Dayayi mai Da Hannu yanke Kiran Sani yayi ya Nufi Bello Ashe Duk Kasim na Kula Dasu
Haka Kurum yaji jikinsa bai basa ba,yana ganin Sanda Sani ya karisa kusa da Ya Ali
Suka gaisa kafin Su Juya Su Nufi Cikin Falon dasu Abba kabiru Suke kuma gashi
Sauran Mintina a Dauran Yagane ya Ali yayan Aneesa ne Domin Bayan Isowarsu ya
muktar ya kaisa Wajen Ya Ali Daya Sunusin ya gaishesu.

Ganin Zuciyarsa bata basa bane yasa yace ma Abokinshi Haruna yana Zuwa Cikin
Sassarfa yabi bayansu Lokaci Daya yana Jin Faduwar gaba,Suna Shiga Falon Shima ya
biyo bayansu Bello Dake bayan ya Ali ya bayyana Atsakiyar Falon Daidai Lokacin Daya
Muktar ya Dago Suka Hada 4 eyes Dashi Ware ido yayi yana kallonsa Lokaci Daya
gabansa na Fadi ganin Bello Hakama Su Abba Kabiru Suka wani Razana Da ganinsa Haka
Kurum Sukaji Zuwan Bello Waje ba alheri bane Abunda ya basu mamaki yaron Da"a kace
baya kasar kuma ya Suka ganshi anan wajen.

ya Muktar bai samu Zarafin Mgana ba Ya Ali yace"Ga Bello nan yazo ammh ya Rokeni da
Kafin Adaura Aure Akwai Mganar da zai gabatar.."Ya Fada yana kallon ya Sunusu Wanda
ke Zaune kusa da Limamin Masallacin Dake kusa dasu Wanda Shine zai Amshi Auren
Aneesa,Ya Sunusi yayi jim yana kallon Bello ya Dauke kai Fuskarsa ba Annuri kafin
yace"Ok Bismillah muna Sauraransa.."

Jin Haka yasa,ya Muktar Saurin Mikewa kamar Iska sai gashi gaban Bello ya saka
Hannu cikin Zafin Nama da Bacin Rai ya Kama Jansa yana Turashi Waje lokaci Daya
yana fadin"Get out....."Bello Shima ya Cije Cike da Taurin Zuciya yana Kallon Shi
kafin yace"Cos of wht..? U don"t Want us to say d Truth baka Tunanin Hakan Zalunci
ne..?

Yafada Shima Cike da Fushi kasim Dake tsaye Tuni yaji Yafara Zufa Hakama yan Falon
da Hanzari kowa ya Mike ya Sunusi ne Daya ya Ali suka Taho Da Sauri Suna Fadin"Ash
Subhanallah Muktar Lafiya..? Ammh ko Sauransu bayayi kara Damkan Wuyan Bello yayi
yana Fadin"I Said get Out..Wlh in ka sake ka Fada Wata banzar mgana Wacce Ta lalata
Auren nan zan Harbi kwakwalwarka da Bindiga.."Yafada yana Huci Idanuwansa Sun Juye
Daga gani baya Cikin Hayyacinsa Alluran Sojojin Tatashi.

Su Abba Kabiru Suka Zaro Ido Suna kallon Ikon Allah Sani Ma Dake Gefe Jikinsa ne ya
Fara Rawa,kalli Yadda Muktar ya Shake Bello kaninsa Toh ina gashi da basu Hada
komai bs kila sai ya kusa Kasheshi Zufa ce ke Karyamomai yana Kallon Kasim Dake
Jifansa da Wani Mugun kallo.

Bello da Jijiyoyin kansa Suka Mike Radau Idanuwansa Suka Chanza Launi Cikin Harzuka
da Fushi Ya Daddage ya Hankade ya Muktar yayi Baya Ya Tsaya da Kakafunsa Domin
Shima Akwai karfi Gyara Wuyan Rigansa yayi kafin yace"Sai dai ka kasheni ya Muktar
ammh Wlh sai na Fadi gaskiya Bazan yarda Ayi Wannan Auren Cikin Duhu ba,ya kamata
ka Dawo Cikin Hayyacinka kana Kunfar baki kan Wadanda basu Dauke ka da Kima ba har
ka Manta Wadannan Daka ke Tsaye kansu Sun So Da yanzu bama Numfashi a doron kasa
Sukayi Sanadiyar Sakamu Cikin maraici Suka Cinyemana Dukkan Dukiyarmu Suka maidamu
bayinsu Suka Tona mana Asiri ammh Daga Karshe Sune kake Wani Hakilon Kokarin Son
kaga Asirinsu ya Rufi bayan mu sun Taru Sun Tona mana Namu Asirin Shame of u ya
Muktar Whh baka Kishin Abbi da Ummi baka Kishinsu baka Jin Dacin Mutuwarasu Kamar
yadda nake ji Acikin Kirjina baka kwana da Bakincikin kashe maka iyaye da Sukayi
Wlh ko yau Su Abbi Suka Dawo Gidan Duniya bazasu yi alfahari dakai ba..."Yafada
Cikin Wani yanayi Lokaci Daya Kirjinsa na Tasawa kamar ya saki kuka.

Gabadaya Wajen Kowa Jikinsa yayi Sanyi da Kalaman Bello Hatta ko Ya Muktar din
Idanuwansa Sun kawo Ruwa Cike da Rauni Su Abba kabiru kuwa saboda Tsoro kamar su
Saki Fitsari ya Hashim kuwa Zare ido kadai yakeyi ya Ali da ya Sunusi Suka kalli
Juna Cikin mamaki Kasim kuwa Zufa ce ke karyomai kamar An Watsamai Ruwa.

Liman ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Abar wannan kace nace din lokacin Daura Aure
yayi fa,kai Saurayi matso kusa ka Sanar damu muke Tafe dakai in Bayaninka Abun a
tsaya Aduba ne sai Aduba Insha Allah.,kowa ya koma ya Zauna Afahimci Juna.."Jin
Haka yasa Kowa ya koma ya Zauna Jiki ba laka Kasim kuwa Durkushewa yayi Zuciyarsa
kamar ta Fito Waje Saboda Fargaba Gaban Liman Bello ya Zauna bayan ya Jawo Hannun
Sani Sun zauna Tare Cikin Jarumta yace"Allah gafartama Mallam ya Hallata ka Aurama
Mashayi kuma Mazinaci Aure,bayan kuma iyayen yarinyar basu da Masaniya kan Hallayar
Shi yaron da Zai Auri yarsu..?

Shuru Liman yayi kafin yace"A"a gaskiya baya Hallata Hakan Domin Muna Bin Tafarkin
Annabin Rahma ne Sallahu Alaihi Wasallam,Domin Shi yagayama na cewa In Wani yazo
Neman Auren Yarku Toh kafin ku bashi ya kamata ku Fara bincikan Addinsa da
Hallayarsa da Sana'arsa da kuma Mu"amalansa da Mutane,kagane Baya Hallata a Dauki
Mata Abama Wanda Ke Shaye Shaye da Neman mata,Sai dai in Cikin Rashin Sani ne.."

Bello ya Gyada kai yana Fadin"Gud...Mallam Toh Wannan Auren da zaka Daura kamar
Shine misalin dana baka ne.."Da mamaki kowa ke kallonsa Barima kasim Dayaji ya Kusa
kuka bai basu Zarafin mgana ba ya Nuna kasim yana Fadin"Mu"amalanshi da Mutane Bata
Cika,ba Uwa uba kuma Dabi"arsa ba Nagartattaciya bace..Mashayi ne kuma Mazina ci ne
ya Ali Auramasa Aneesa Wlh Cutarwa ne,yakamata ku Duba Wannan mganar.."Gabadaya
Wajen ya Dau Salati Abba Kabiru ya Mike yana Fadin"Karya kake..Don tsani Kasim bai
Chanchanci ka mai Kazafi ba, D'ana ba mashayi bane kuma ba Mazinaci bane Karya
kakeyi.."

Yake Fada yana Nuna Bello Cike da Fusata Lokaci Daya Abba Garba ya Mike yana Rikosa
ammh yana Zillewa Mirmishi Bello yayi kafin yace"Kaga Dattijo Rufe bakinka Tun
yanzu kafin kaji kunya ban Fadi Abunda na Fada ba sai don Ina da Hujja...Sani Da
muke Tare Dashi Abokin kasim ne Wajen Aikinsu Daya Akaduna gashinan zai muku
bayanin komai.."

Yafada yana Nuna Sani wanda Ya Dukkar dakai ganin Ido ya Dawo kanshi Cikin Rawan
Murya ya Ali yace"Muna jinka Bawan Allah..."Sani yafara mgana yana Fadin"Hakika Duk
Abunda Bello ya Fada gaskiya ne Banso Ace na zama Silar bata Auren kasim ba..Ammh
kuma Allah zai kamani matukar na sani kuma na Boye sani mganar gaskiya Kasim
mashayin giya ne kuma Manemin mata ne Shi yasan nasan Komai Domin wajen Aikinmu
Daya Dashi a kaduna, gani gashi ya Bude baki ya karyata Abunda nace.."Sai Aka Fara
kallon kallon Kafin Kallon ya koma kan kasim Wanda ke Tsiyayan Zufa Cikin Bacin Rai
Abba kabiru yace"Bude baki kayi mgana ka karyatamin Wadanan makiyan naka Dake
gabana.."

Kasim kanshi na Duke bakinciki kamar zai Mutu baizai iya Rayuwa ba Aneesa ba,Bazai
iya Juran Rasata ba Cikin karfin Hali yace",Ni bansan Mganar Da Suke ba Karya
Sukemin Wlh Allah Abba...Kumin Rai karku ce bazaku bani Aneesa ba.."

Yafada Hawaye na gangaromai baki Sani ya saki yana Kallon Kasim Ido Cikin Ido Bello
ko Kallonshi Shima yake Cike da Takaichi Mikewa Abba Kabiru yayi yana Fadin"Kunji
ko..? Don Allah karku yarda Dasu..Dama wannan Akwai Takun Saka Tsakaninmu ku manta
da Komai Lokaci ya Kure mu Gabatar da Abunda ya Taramu.."Yafada yana gyara zaman
Babban Rigansa.
ya Ali da ya Sunusi Sukayi Shuru Suna Nazari,Yayinda ya Muktar ke Gefe kanshi
Sunkuye Tunda Aka Fara mganar bai Dago ba...Ya Ali yaace"Shikenan bazamu Yanke
Hukunci ba Domin Shaidar baki ba Shaida bace...Liman Agabatar da Daurin Aure.."Da
Sauri Hashim ya Mike yana Fadin"A"a...Adakata..."

Gabadaya Aka Juya Ana kallonsa Cikin Mamaki Abba garba yace"Adakata kuma Hashim...?
Gyada kai yayi kafin ya kalli kasim kai Tsaye yace"Kasim ya kamata ka Fito Fili ka
Fadi gaskiya Domin karyan bata da amfani...Mganar gaskiya,Abunda Bello da Abokinsa
Suka Fada Akan Kasim gaskiya ne...",

Ai sai Su Abba Kabiru Suka saki baki Suna kallon Hashim,ya muktar ma ya Dago kanshi
Cikin mamaki yana kallon Hashim Shiko kasim Kuka ya Fashe Dashi Yana Fadin"Na yarda
gaskiya Suka Fada...Ammh Allah na bari Tun Haduwata Da Aneesa na Tuba..na daina
komai.."Yafada yana Hada Duka Hannayensu.

Kai Tsaye Hisham yace"Karya kake Baka Daina ba..." Gabadaya sai kallo ya koma sama
Cikin Dattako Hisham yace"Saboda kana Kanina Uwa Daya Uba Daya bazan Ki bin bayan
gaskiya ba...ya juya wajensu ya Ali yana Fadin"Mganar gaskiya Kasim Duka yana
aikata Wadannan Zunuban,Kuma bai bari ba Kuma ko yayi alkwarin zai bari bazai iya
bari ba...Abun ya zamarmai Jiki..Na Fadi gaskiyan Dana sani Bakuma zan Rokeku da
ku Aurama Kasim yarku ba,Saboda ko Ni ne bazan iya bashi Auren yata ba Saboda in
nayi Haka na Zalunceta..."Daga Haka yayi Shuru ya Sadda kai kasa,Abba Kabiru da
Abba garba kuwa Jiki yayi Sanyi Ga Kunya Duk ta kamasu.

ya Ali da ya Sunusi Suka ji Wani Iri Acikin Ransu Lokaci Guda Suna godema Alla da
basu Shiga gaba ba Wajen Ruguza Rayuwar Tilon kanwarsu ba,ya Muktar kuma Kansa yake
Jinjinawa Shima kunya ta kamashi Bello kuwa Mirmishi ya saki yana kallon kasim
Wanda ke kallonsa Yana Zubar Kwallah Lokaci Daya Zuciyarsa na kara Tsanan Bellon

Mikewa Bello yayi batare Daya cema Kowa komai ba ya Fice Daga Falon Waje ya Fita
inda yaga Mutane suna Mganan Lokaci ya Tafi ammh ba"a Daura Aure ba ga masu Shed'a
nan Sunja Tunga,suna jiran afara gudanar da Daurin Aure su fara Sheda, Bisa Wata
Farar Kujera ya samu ya Zauna yana Cigaba da Latsa Wayarsa ransa Fes,ko Alama babu
Damuwa Tare Dashi..

Acikin Falon kuwa Kasim ne ya Tuma Gaban ya Ali yana Fadin"Don Allah kumin Rai
karku Hanani Aneesa..Wlh ina Sonta bazan iya Rayuwa babu ita ba...Na muku alkawarin
na Bari Daga yau.."Yafada yana kuka kamar karamin yaro....

Ya Sunusi ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Karka damu koma ka Zauna.."Yafada yana
Rike kasim Din Komawa yayi ya Zauna ya Share Hawayensa da Babban Rigan Dake
Jikinsa,ya Sunusi ne ya kalli ya Ali kafin yace"In ganka Mana Ali.."Jin Haka yasa
ya Ali ya Mike Lokaci Daya yana ce musu.."Kud'an mana Hakuri yanzu zamu Dawo.."Ba
wanda ya samu Zarafin mgana Illah Gyada kai da Abba garba yayi suka Fice Daga Falon
Suka bi ta Kofar da Sadasu da Cikin Gida,kafin Su Fita Yaya Ali yace"Muktar..."

Ya Dago kansa.."Kaima taso.."inji ya Sunusi..Jiki ba kwari yamike yabi Bayansu Suka


Bace Daga Falon,sai Wajen ya koma kamar gidan makoki bamai mgana Abba Kabiru Tagumi
yayi yana Jinjina kai Hakama Abba garba Shima kasim Kansa na Duke yana Salati Cikin
Ranshi Lokaci Daya yana Jin In Har Bello yayi Sanadiyar Aka Hanashi Aneesa..Wlh sai
ya Dauki mataki akansa.

Shiko Ya Hashim shima kansa na Duke Zuciyarsa kuma Tayi Sanyi Sosai yana Fatan kar
su bashi Aneesa..Hakan kila zai saka Kasim ya Shiryu Liman kuwa Shuru yayi yana
Jadadda Lamarin Acikin Ranshi Sani Kuwa Tun Bayan Fitan Bello Shima ya bi bayanshi.
Ki biya ki karanta cikin salama.

*ANITHA..*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?16*

"Sai da Sukayi Nisa da Falon kamar zasu Shiga Cikin Gidan,kana Suka Tsaya Cirko
Cirko Suna kallon Juna,ya Ali ya kalli Yaya Sunusi yana Fadin"Sunusi ya kake ganin
zamu Bullo ma wannan lamarin ne .? Nifa kaina yakulle...?

ya Sunusi yace",Umh...mganar Gaskiya Ali Indai Mganar mu bashi Auren Aneesa ne bai
Taso ba,karka manta koda Take kanwa garemu Amanace akan mu Lokacin Abba na gabda Da
Rasuwa bai da Wata mgana sai na Mu kula da Aneesa Kada mu barta Bayan bashi tayi
maraici kuma yace matukar muka Bari Rayuwar Aneesa Ta Shiga wani hali bai yafemana
ba, baka ganin in har muka yadda aka Daura Auran nan alhalin kuma mun sani Allah
bazai Tambaye mu ba..?ka fa Duba hakkin yarinyar nan in mukayi Haka Hakika mun
Cutar da Ita.."Yafada lokaci daya yana Saba babban Rigansa Cikin Firgici.

Ajiyar Zuciya ya Ali ya Sauke kafin yace"Wannan ma mganar bata Taso ba


Sunusi,Mganar Bashi Aneesa bata,Saboda kada muyi Abunda zamu zo muna masu Nadama
nan gaba ko ba Haka ba Muktar...?..

ya muktar ya saki Numfashi yana Fadin"Hakane...Toh ammh in Kuka yi Haka ya zakuyi


da Dimibin Jama"ar Dake Waje Suna Jiran Tsammani .? Kai ya Ali ya Dafe yana Sakin
Numfashi Shiko ya Sunusi Dafe goshi yayi Lokaci Daya yana Tura Hularsa baya Cike da
Fargaba da Tashin Hankali,kafin ya juya yana Dora hannayensa Duka biyu Akungunsa
yana Fadin"Ya illahi...Bakomai Haka Allah ya kadarra.."

Cike da Tsausayinsu Ya Muktar yace"Insha Allahu bazan bari ku Tozarta ba..Kuzo


muje,Babu Abunda zai Chanza yanzu Za"a Daura Auren Aneesa da yardan Allah..."

Yafada lokaci Daya yana Juyawa yafara Tafiya Zuwa Cikin Falon Baki Bude ya Ali da
ya Sunusi ke binshi da kallo kafin Sukalli Juna Lokaci Daya kuma Suka Rufamai baya
Har Zuwa Cikin Falon Da su Abba kabiru ke Zaune Suna Jiran Tsammani Tunda kasim
yaga Sun Shigo Fuska ba Annuri Jikinsa ya kama Rawa Hawayensa Suka Cigaba da Zuba
Lokaci Daya Zuciyarsa na Harbawa...

Basu zauna ba Daga Tsayen ya Ali ya kalli Abba kabiru yana Fadin"Kuyi Hakuri da
Abunda zan Fadamuku,mganar gaskiya mun Janye Mganar baku Auran kanwarmu Aneesa
awannan Lokaci bisa la"akari da Abubuwan da Suka bayyana,kuma koda Aneesa Take
kanwa garemu Tana da Hakki mai girma Akanmu matukar muka Rufemata muka Aurar da Ita
ga D'anku Hakika mun Ci Zarafinta kuma Allah bazai barmu ba...Shiyasa muka yanke
Shawaran Mu baku Hakuri Don Allah kuyi hakuri mu bar mganar wannan Daurin Auran
Fata zaku Fahimce mu,bisa yadda muka sa kuka baro garuruwanku muka bata muku
Lokaci.."Daga Abba kabiru Har Abba garba ba baki sai Zufa Suke Sharewa suna kallon
Juna Cike da Kunya da Takaichi.

ya Hashim ne da Liman ke Gyada kai Alamar gamsuwa Liman yace"Mganarka gaskiya ne


Aliyu...Hakan Shine Daidai..."Shiko Kasim kasa ya sake Durkushewa Yana
Fadin"karkumin Haka Don Allah karku ce zaku Rabani da Aneesa Ina Sonta Itace
Rayuwata Na muku alkawarin zan bar Duka Abunda nakeyi Daga yau Don Allah karku
Hanani Aneesa.."Yafada Hawayensa na kara Gudu Lokaci Daya yayi baya Dafe da Kirji
Abba kabiru Dake kallonsa yaji kamar ya Fashe da Kuka Saboda Tsausayin D'anshi.

Baya Yy Ali ya juya bayan ya saka Haban Babban Rigansa,yana Share Kwallar Data
Zuraromai ya Sunusi ne ya Rikesa yana Fadin"Kabi Ahankali kasim,kayi Hakuri Haka
Allah ya kaddara ina maka Fatan Allah yasa Sanadin Shiryuwanka kenan..."ya Hisham
ne kadai ya amsa da Ameen Su Abba kabiru ko kansu na Duke suna Tunanin Wannan Wani
Irin Tozarci ne..

ya Muktar ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Allah gafarta mallam don Allah Ajirani
kadan in Dawo yanzu za"a Daurama Aneesa Aure babu Abunda Zai Chanza..."Yafada yana
Juyawa da Sauri ya Fita Zuwa Waje,Kowa da Ido ya Rakashi Cikin Mamaki Hatta ko da
Kasim Sai da ya Dakata da Kukan Dayake Yaji Zuciyarsa ta Tsaya cak Lokaci.

Ya Dade yana Waige Waige Cikin Haraban Gidan kafin idonshi ya Hangomishi
Bello,Zaune bisa Kujera yana latsa wayarsa,kafin ya karisa Wajensa sai da ya biya
ya bama mutanensa Hakuri kan Yanzu za"a Daura Auren,Bello na Zaune kawai sai jiyayi
an finciki hannunsa Lokaci Daya kuma anfara Jansa,Da Sauri ya Dago Lokaci Daya
yana kallon ya Muktar Dake Jansa Cikin Fushi kuma yaki Bari yaga Fuskarshi bai
Direshi ko"ina ba sai da Suka bar Haraban gidan Suka Fita Daga get Din Gabadaya
kana ya Sakeshi Lokaci Daya yana Fuskantanshi.

Bello ya tsaya da Kakafunsa yana kallon Fuskar ya muktar bai damu ba Illah saka
wayarsa Dayayi Cikin Aljihun Gaban Rigansa,Lokaci Daya kuma yana Saka Duka
Hannuwansa ya Harde kirjinsa ganin kallon Da ya Muktar ke mai ne yasa Ya Dauke kai
gefe ya Raba gefensa zai Wuce,Da Sauri ya saka Hannu Cikin Fushi ya sake janyosa
Zuwa gabanshi Lokaci Daya yana Hararansa,kafin yace"Kayi Nasaran B'ata Auran yanzu
Dawa kakeso Adaura...?

Tamke Fuska Bello yayi kafin yace"Bangane ba ya Muktar...? Look nifa Awannan
al'amarin Taimakon Aneesan nayi,kuma Kaima na Taimake ka Domin da an Daura Auren
Lbrin ya Fito kome ya Faru dakai za"ai kuka."ya fada yana Zakuda kafada Irin ko
ajikinsa din nan.

Ajiyar Zuciya Ya Muktar ya Sauke kafin yace"naji...Toh yanzu ya zasuyi da jama"ar


da Suka gayyata..? Kai tsaye yace"Su basu Hakuri mana Yaya..."Hararansa ya Sakeyi
kafin yace"Ita Aneesan fa...? Baka Tunanin Wani Hali Zata Shiga in ta samu lbri..?
Fuska ya bata na gajiya da Irin Tambayoyin Ya Muktar Cikin kosawa yace"Sai ta koma
mkranta Is dat so..."Kirjinsa Ya Muktar ya kaima Duka kafin yace"U are Animal
Bello...Baka da Zuciyan mutane...Baka da Tsausayi ko kadan,toh baka isa ba Tunda
har Ka lalata wanchan maganar toh kai zaka maye gurbin kasim Wuce muje yanzu Dakai
zaka Daura Auren..."Yafada cikin Tsawa Lokaci Daya yana Fuzgar Hannun Bellon Da
karfi

Shiko Bello Kamar Aradu Haka yaji Mganar,Cikin Zaro ido yace"Ya Illahi ya..muktar
Wht of all dis kuma..? Plz dont do dis for me am begging u ban taba kallon Aneesa
Amtsayin Wacce zan iya Rayuwar Aure da ita ba...infact ma Ban Shirya yin Aure yanzu
ba...plz leave my Hand.."Yake Fada kamar yayi kuka ammh ya Muktar ko Sauraransa
Baiyi ba Haka yake Jan Hannunsa Har Zuwa Cikin Falon Mutanen Dake Waje Suka bisu da
kallon mamaki Sani Dake Cikin Abokansa ganin Haka yasa Shima da Sauri ya Rufa musu
baya.

Ya Muktar bai Dire Bello Ko"ina ba Sai agaban Liman kafin Shima ya Zauna Kusa Dashi
Lokaci Daya yana Dafe Hannunshi,domin yaga Bellon kokarin Tashi yake, Hannu Daya ya
Zura Cikin Aljihun wandonsa ya Fito da Kudi Bandir Biyu Daya ya ijiye gaban Liman
Daya kuma gaban Hashim kafin yace"Wannan Sadakin kasim ne na maido muku da
kayanku..."Yafada yana Nuna da Kudin Dake gaban Hashim kafin ya Dora da
Fadin"Wannan kuma Sadakin Aneesa ne...Zan ma Kanina Bello Walicci..."..

Gabadaya Falon sai ya Dau Shock ya Ali ko Da ya Sunusi ko Junansu Suka kallah
Lokaci Daya kuma Suka Saki Mirmishin Farinciki Abba garba ko da Abba kabiru Wani
yam Sukaji Lokaci Daya da Takaichin Muktar da Bellon Gabadaya,kasim ko Bellon Ya
Zurama ido yana kallonsa Cike da Wata Tsana mai girma Lokaci Daya dawani Irin
Bakinciki Sani kuwa Gefe ya samu yazauna yana Kallon Abunda ke Faruwa.

Liman ya Saki Mirmishi yana gyara Rawanin Kansa yace"Masha Allah Hakika ka cika
Musulmin kwarai...Wajen Kokarin Hana Tozarta wani Ahalin Nawa ne Anan..? Kai Tsaye
Ya Muktar yace"Dubu 100 Allah gafarta Mallam..."Bakinsa Washe
yace"Alhamdulillah...Kai Ali gayama mai Shela ya sanar da Mutane Su matso kusa za"a
Daura Aure.."

Yafada lokaci Daya yana Dora kallonsa kan Bello Wanda kansa Ke Duke yana Faman
Tunanin kila yana Duniyar nan Mafarki ne,Da Sauri ya Ali ya Fice ya Samu masu Shela
yace su Sanar Kowa ya matso kusa Za"a Gabatar da Daurin Aure,nan da nan Suka Fara
Shela Suna Fadin"Kowa da kowa ya matso..Lokaci yayi ammh bana Mutuwa ba Lokacin da
Shaidu Zasu Tabbatar da Daurin Auran Aneesa Bukar Bulama da Angonta Kasim Kabir
Jikamshi..Kowa ya matso.."Nan da Nan Mutane Suka mimmike Dama Sun kagara Wadanda
Suka samu Shiga Falon Suka Shiga Wadanda basu samu ba kuma suka durkusa Daga Waje
Suna Jin Abunda ke Faruwa.

Daga cikin Falon Kuma ya Sunusi ne yayi Saurin Dafa ya Muktar yana Fadin'"Kaga
Muktar Tashi kagani..."Ba musu ya Mike Shi kuma ya koma Inda ya Tashi ya zauna yana
Fadin"Zan karbaman Bello Auran Aneesa..."Yafada yana kallon Bellon Wanda Dakyar ya
kakaro mirmishi ammh Cikin Ranshi kamar ya saka Ihu Gabadaya Wajen Kowa yaji Dadi
barinma Ya Muktar Wanda Suka koma gefe Shida Ya Ali Suka Zauna Cikin Shaidu kafin
Afara gudanar da Neman Aure

****

Aneesa Dake Bedroom Din ya Ali Zazzabi mai Zafi ya Rufeta tana Lullebe Cikin
Blanket Su B.kaita Sunyi Sunyi Tatashi Tayi Wanka Taki Tashi Salamatu Jibiya ce
Taje ta Kira mata Anty yagana Ita tazo ta matsa mata ta Shiga Wanka Koda ta Fito
Haka take Rawan Sanyi Tana karkarwa Dakyar ta yarda Ta Shirya Cikin Wani Ubansu
Swice less Wanda Akallan Farko In kayimai zaka gane Yabama 50k baya Saboda Kyanshi
da Tsaruwanshi,Kalanshi Blue and pick ne,gashi yayi mata kyau Dinkin Diga da Zani
ne,Dakyar sai Da Anty Yagana ta Tsaya Akanta kana Ta Tsaya Sanah ta mata kwalliya
Tunda Ta iya ko gamawa Ba"ayi ba Ta koma ta kwanta Tana Hawaye,Dole Suka kyaleta
sai gabda Daurin Aure ne Anty Yagana tazo Tatafi da Ita Dakin Falmata chan Kurya ta
matsa mata taji Abinci Tasha Mgani Ta kwanta

Lokacin Daura Aure na Cika Sukayi ta Sakin Guda da Turaren Kamshi ammh Shuru basu
ji masu Shela da Maroka na sheda ba, Abun ya basu Mamaki Anty Nafee Har Leke Ta
Dingayi Tana Fadin"Kila akwai Wadanda basu iso bane ."Anty Rahila tace,"Anya Angon
ba Tare suka zo da Abban Hibba fa Munyi mgana Dashi..."Dukkansu Suna Falon Falmata
ne Dakin Mama yana Duka Acike yake da Dangin Babansu.

Cikin Barci Aneesa Tayi Mafarkin wai anfasa Daurin Aurenta da Kasim da Wani Aka
Daura mata,Tana jin jiri da Ciwon kai Haka ta Fito Falo Tana Dafa Bango Daidai
Lokacin da Wani mai Shela yake Fadin"Alkawarin Allah ya Cika Aure ya Dauri Kuma
Shaidu Sun Bada...Aneesa Bukar Bulama Ta Tabbata mata Wajen Muhammed Bello
Jikamshi...Wannan Chanjin Chanjin Allah ne,Lakadan ba ajalan ba..."Da karfi yake
Mganar Kuma ga Hayaniyar mutane na Tashi kowa yaji Mganar Har Cikin Gida karaf kuma
Akunnan Aneesa Data Fito Falon Kirji Ta Dafe Tana kallon Anty Rahila Wacce Ta Mike
Tana Kara Jin Mai Shelan na kara maimata Muhmeed Bello Muhamed Da Aneesa Bukar
Bulama..

Anty Rahila tace"A'ah yanake jin Wani Suna Dabam kuma kamar Bello naji ana
ambata.."Tafada Cike da mamaki tana kallon Mutamen Dake Dakin Anty Nafee ce
Tace"Nima Haka naji ina ce ba Kasim Sunan Angon ba,..?kuma naji ana kiran Wai
Muhammed Bello.."..

Anty Rahila Data Shiga Rudani Tace"Eh kasim Sunanshi...Bellon fa kanin Abban Hibba
ne,baya ma kasar yana malesia abun mamaki Garin yaya aka samu Wannan Chanjin
kuma.."Tafada Cikin Rudewa Basu lura da Aneesa Dake Tsaye ba sai Dai Sukaji
Mganarta Murya Shake Tana Fadin"Ni....Ni..Da Bel...Bello...Kuma..? Ina Kasim din..?
Tafada Lokaci Daya Hawaye na wanke mata Fuska kafin kaji tim ta Zube kasa Sume nan
Fa Daki ya Hargitse da Iface iface Daga Waje ma Mamaki da Cecekuncen Dake Tashi
kenan Su B.kaita Dake part din ya Ali Sanah Tazo Tana gayamusu da Hanzari Suka Mike
zuna Falon Falmata inda Ake Yayyyafama Aneesa Ruwa Data Farfado sai Takara Bajewa
Tana Iface iface Ashe Aljanunta ne Suka Tashi Shigowar Su B.kaita Dakin ya sanya
Suma Suka Zube Nasu ya Tashi kafin Kace me gida ya Rikice Dakyar Aka samu Suka Dawo
Cikin Hayyacinsu.,Daada Dake Dakin Mama yana Itama lbri ya kawo mata Anty Rahila
tazo Da Sauri Tana Gayamata Itama Cike da Mamaki Take Nanata Sunan Bello,acikin
Ranta.

Daga chan Haraban Gidan Kuwa Mutane nata mamaki Chanjin Da Suka ji Musamman Tawagar
Ango Kasim kowa sai mgana yake Cike da mamaki,lokaci daya Kowa na kallon Kowa Cike
da Tambayoyi..

Daga Cikin Falon kowa Cike da Farinciki kowa ya Mike ana ma Juna Musabaha Duk wanda
yace Ya yaji Chanji sai ace matsala aka samu Shiyaasa,Bello kuwa yana Mikewa kansa
ya Sara kamar zai Fadi Sani Dake kula Dashi ne yayi maza ya Rikesa yana Fadin"Bi
sannu fa Bello..."Dago kansa yayi Jajir kafin ya Rike Hannun Sani yana Fadin"Mu
Fita Waje Sani ...kaina kamar zai Fashe..Kaini Waje Don Allah..."

Yafada yana Hura baki Numfashinsa na Fitowa ta Baki,kamasa Sani yayi Suka Fito
Waje,Takalmansa ya Duka yana Zuramai shiko yana Duke Dafe da Bango Har ya gama
shima ya saka nashi ya Riko Hannunshi Zuwa Haraban Gidan Sai ga Kasim Ya Fito
Afusace ya Hashim da Abba kabiru na Rikosa Ammh yana Turjewa Harda dai ya Sabule
Babban Rigan Dake Jikinsa da Hula ya barmusu kafarsa bako Takalmi ya Tako da Gudu
Yasha Gaban Bello Lokaci Daya yaci Kwalan Rigansa Gabadaya Mutane kallon ya Dawo
kansa Abokansa Suka Rugo da Gudu Cikin Tashin Hankali Haruna ne gaba gaba Suna
Tunanin kodai Kasim ya Fara Haukane Jin badashi Aka Daura Auran ba.

Bello Dayaji An Chakumi kwalanshi ya Dago da Jajayen Idanuwansa Wadanda Suka Chanza
launi Saboda Tashin Hankali ya Saukeshi kan Kasim,Kuramai ido yayi yana kallonshi
cike da mamaki bai gama Mamaki ba yaji Hannunsa Bisa bakinshi ya Dungule ya
Nausamai Naushi Wanda Sai da Bakinshi ya fashe Lokaci Daya Kasim yace"Dama Abunda
kake Buri kenan...? Auran Aneesa...? Hhhh,kayi Nasaran Rabani da Ita ka Aureta ammh
Ina so ka sani..."Bai karisa ba ya Hashim ya Finciki Hannunshi Daga Wuyan Bello
yana Fadin"Baka da Hankali ne,kasan kana Sonta baka gyara Halinka ba kafin Zuwan
wannan Ranar,wuce muje Sakarai kawai.."Yafada yana Rikesa Daidai Lokacin da Su Abba
kabiru Suka kariso da Su ya Muktar Bayansu ya Ali da ya Sunusi Waje ya Cika jama"a
da Takaichin Tonon Asirin Da Kasim ke musu Abba Garba yace"Kai Hashim kamashi Muje
Waje.."Yafada da Karfi Da Sauri Hashim ya Kara Damkan Kasim Wanda ke Zillewa,ganin
Haka yasa Sauran Abokansa Suka kamamai Suka yaja kasim Zuwa Waje Wanda ke juyowa
Yana Nuna Bello Lokaci Daya yana Fadin"Wallahi...Tallahi ka Rubuta ka Ijiye
Bello...kayi Nasaran Auran Aneesa ammh bazaka samu Nasaran Rayuwa da Ita ba Ni nan
Kasim sai na Kasssara Rayuwarka kamar yadda ban samu Aneesa ba Haka kaima zaka kare
Rayuwarka Cikin Kila wa kalan Mutuwarka Bello sai na ga bayanka.."Yake Fada yana
Zubar Hawaye Abba garba yakara Turashi Waje ganin Zai kara Sakasu Cikin Wani
Bala"in bayan Wanda Suke Ciki

Gabadaya Jama"an Wajen kowa ya Rike baki yana mamakin kalaman Kasim Jikin Muktar da
Nasu ya Ali yayi mugun Sanyi Duk Sunji Abunda ya Faru Abakin Rahila na yarda Su
Abba kabiru Suka Hamdame Dukiyarsu ammh kuma Tunda komai ya Wuce ba amfanin Tada
mgana Bello Dake bin kasim da kallo Har Sukayi Waje Suda Tawagarsu,Wani Mirmishi ya
saki kafin ya saka hannu ya Share Jinin dake Gefen Bakinsa,Ya kara Rike Hannun Sani
yana Fadin"Muje Filin jirgi Sani..."Yafada Yana kallon kasa.

ya Muktar yace"Sani kuje,muna Tafe muma Don Allah ku kula.."Yafada Cike da


Tsausayin Bellon,Ya Ali Dake gefe har Sun Fara Tafiya ya Daga kafa yana
Fadin"Muhammed Bello..." cak Bello ya Tsaya Bayan ya Waigo yana kallon ya Ali Wanda
ya kariso Garesu ya saka Hannu ya Rike Hannun Bello Guda Daya,Yana Fadin"Nasani
Cewa Domin Kada Mu Tozarta Muktar ya yanke Shawaran Aura maka Aneesa Bello...Bamu
yi Fushi ba,mun karbi Zabin Allah Hannu Bibbiyu,muna Fatan Allah ya Zaunar Daku
lafiya,Don Allah ka Rike Maraicin Aneesa Tamkar yadda Yayanka ya Rike Maraicin
Yayarta Rahila.Kuje Allah ya kaiku Lafiya,Babu Abunda ya Isa ya samu bawa sai da
Izinin Allah.."Yafada Lokaci Daya Idanuwansa na kawo kwallah Sakin Shi yayi lokaci
daya ya juya cikin karfin Hali Bello yace"Insha Allahu..."Daga Haka ya Juya Cikin
Dafe kanshi Dake Saramai.

Sani ne ya Taimakamai Suka Fice Daga Haraban Gidan Mutane na Binsu da kallo,nan dai
Suka Dinga gaisawa da Mutane ko Waliman da"a kace za"ayi ba Wanda ya Tuna da
Ita,Gida ba kwanciyar Hankali Haka kowa ya Watse yana Mamakin Al"amarin Daya Faru
gidan Marigayi Bukar Bulama.

Su Abba Kabiru Daganan Filin Jirgin maiduguri Suka Wuce suna Zuwa Hashim yayi musu
Cuku cukun Samun Fligt Zuwa Katsina,Abunga da Kudi nan da nan Ko 30m basuyu ba
Jirgin ya Debesu Dukkansu Harda Abokan Kasim din Zuwa katsina,wasu kuma da Yawa Sai
Suka bi Wanda Zai koma kaduna,Suma Su Bello Jirgin su Kasim din ya Tashi da Awa
Daya Suma nasu Wanda zai yada Zango a Abuja ya kwashesu,bello jikin Sani ya Kwantar
dakai,Saboda Yadda kansa ke Sarawa kamar ya cire kan ya y'ar Saboda Halin Dayake
Ciki.

Bayan su ya Ali Sungama Sallaman Baki Suka Nufi Cikin Gida Saboda Susan Cewa Su ake
Jira Aji Bayanin Taya aka samu Wannan Chanji,kai Tsaye Dakin Falmata Suka Shiga
inda Gabadaya Su Anty Rahila ke Ciki Da Aneesa Wacce Tunda ta Dawo Cikin Hayyacinta
take kuka Su B.kaita ne ke lallashinta ammh kamar kara Zugata Suke,Ya muktar ya
Shigo Dauke da Hibba Wacce yacikaro,Atsakar gida tana Wasa,waje suka samu Suka
Zazzauna,sai da aka kira Daada Mama yana,Da Falmata da Wasu Daga Cikin Dangin
Babansu kafin ya Ali ya Fara kora Jawabi Tunda farko Har Zuwa Karshe Aneesa Dake
kwance ta Mike tana Fadin"Da kun Auramin kasim din Hakanan Ina Sonshi Haka Duk da
yana Shaye Shaye da Neman mata ya Fiyemin Wanda kuka Auramin So Dubun Dubata...Bana
son Bello na Tsaneshi ban taba Sonshi ba,Dama Baida buri kullum sai na lalatamin
Dukkan Farincikina Wlh bazan iya Zaman Aure Da Bello ba Dana Zauna Dashi Gwara na
kashe kaina.."

Tafada Tana kuka Lokaci Daya Ya Ali ya Mike jikake Fau!Fauyau.! Ya Kwasheta da
Maruka lafiyayyu Guda Biyu ya kuma bita da Hauri da Kafa da Sauri Daada Ta Mike Ta
Shiga Tsakani Tana Fadin",A"a Tana da gaskiya Ku barta ta Fadi Ra"ayinta ita din ba
Akuya ba ce Mutun ne kamar kowa kuma Tana Da Hakkin Akan Zabin Mijin Da zata Zauna
Dashi meyasa Kuka yanke Hukunci batare Da Kun Nemi Shawaranta? Ba a haka mganar
Gaskiya Baku Kyauta ba,Kuma Shima Bello bai kyauta ba domin Ya yi kokarin Tona
Asirin Dan"uwanshi Musulmi Wanda bai kamata ba ko a Addininmun in ka Rufama Wani
Asiri Ranar Gobe Kiyama Kaima Allah zai Rufamaka...Dukkanku Baku Kyauta ba,baku
kyautama Aneesa Ba kuma baku mata adalci ba.."

Tafada Tana Share Kwallah Anty Rahila ne tazo Ta Riketa tana Fadin"Daada zo ki
zauna kada ki Fadi..",Tafada Tana Rikota cikin Fushi ya Ali yace"Mama yana Da
Falmata ku Shaida Wlh Tallahi Inhar Aneesa bata Zauni Gidan Mijinta ba Na Zare
Hannu na Akanta Har Abada...Mganar bamu kyauta mata bai Taso ba Daada..Mashayin
zamu Aura mata Kuma Mazinacin.? Muma Allah zai kamamu da yin Hakan,kuma mganar baki
sonshi karki soshi don Ubanki baki da gatan Daya wucesa,da Har zaki Bude baki ki
Cima Mutanen Da suka maidake Mutum Mutumci ba Mutuwa zakiyi ba yau ko Gawanki ne
sai An mika ki Gidan Mijinki.."

Yafada yana Daidaita Numfashinsa,Ya Sunusi ya mike Shima yana Fadin"Wannam Shine
mgana ke Yagana da Rahila ina Nafeeesa da Aisha..? Suka mike Suka Hada Bakin Wajen
Fadin"Gamu ya Sunusi..",kai ya gyada kafin yace"Ku cigaba da Shirin komai karfe
Hudu kamar yadda Aka Tsara zaku Rakata chan Abuja Allah barshi Dagachan Sai ku
barsu musu ita ku Dawo..Duk Abunda Suka yanke Daga Baya Daidai ne Domin Tafita
anamu Tundama chan Ita Din Tasu ce..."Daga Haka Suka Nufi Hanyar Fita ya Ali na
Fadin"Mgana ta kare..:Muktar Taho muje.."Suka Fada Suna Ficewa,Nan Suka bar Aneesa
na Kuka Harda Ihu Anty Rahila Dake Gefe Tayi Jagale Falmata Tashi Tayi Ta Fita
Gefen Ranta kuma na Cike da Tsausayin Yarta.

Mama Yana ce Ta saka matar Ya Ali Khadija dasu B.kaita Suka kama Aneesa Tana kuka
Suka Nufi Da Ita part din ya Sunusi,Sauran Kuma tace Su Cigaba da Shirin Tafiya,sai
Lokacin Kowa ya Fita Tsakar gidan Aka Fara Hada Hadar Abinci Ammh Fa Kowa bai ga
laifin Hana kasim Aneesa ba Domin Hallayanshi basu da kyau Anty Nafee ne Acikinta
ranta taso da Mashayin Aka Aurama Shegiya Data gane bata da Wayau.

Ki biya ki karanta cikin Salama.

*ANITHA..*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?17*

"Tunda ya Ali yabada Umarni su Anty yagana Suka Cigaba da Shiryen Shiryen Tafiya
Abuja da Aneesa Wacce Ke Dakin ya Sunusi Tana Kuka Kamar Zata Shide gashi dama Ga
Zazzabin Jikinta bai barta ba nan da Nan ta kara Rafkewa B.kaita da S.jibiya sun
gaji da bata baki Sun Koma gefe Sun Zabga Tagumi Ammh har Acikin Ransu Basu Damu da
wannan Chanjin ba Domin Uncle Bello yafi Kasim Sau Dubu Sai dai Don Ita Aneesan
Allah bai Hada Jininta da shi Bellon bane.

Su ya Ali kuwa Falon Waje Suka Koma Suka Cigaba da Tattauna lamarin anan aka kawo
musu Abinci Suka ci,suka Sha,Daga Cikin gida kuwa Sun gama Hada Komai Na kayan
Aneesa da Suka zo Dashi sai Turaran Wuta da Aka Hadamata Dana Daki dana jiki sai
Abunda Ba"a rasa ba Wasu kayan ma Anbarsu ne Daga baya za"a zo dasu Saboda Tafiyar
Jirgi ne bata Mota ba.

Anyi Anyi da Aneesa Tatashi Ta sake wanka Taki Tashi Aiko Anty Yagana da Anty Aisha
Suka zo Suka Ciccibeta sai Bayi Suka Dirjeta Tana kuka da komai basu Sauraramata
ba,sai da Suka Shiryata Cikin Wata Shadda Doguwar Riga mai Ruwan kasa,cikin Sabbin
kayan da Anty Rahila ta Dinkamata ne na Akwatunan ta ya Ali yace Ahadasu Waje Daya
za"a maida musu kayansu ne,Duk da taki Tsayawa sai da Suka mata kwalliya suka
Jikata da Turaran Jiki Dana kaya,Suka Nadeta cikin Lifaya Fara mai Duwatsu Masu
Kyal kyali,kallo Daya zakama Aneesa ka Ga Tsabar kamar Kanuri Tare da Ita
Idanuwanta Suna Rufe ammh Haka Take Tsiyayan Kwallah Tana Shessheka,Abinci kuwa
anyi anyi Taki Ci ta ki ci Da Anty Yagana ta Fusata sai tace kowa ya Fita
batunta,haka Aka barta kwance ga Zazzabi ga Yunwa ga Tashin Hankali,Gashi tana son
Kiran Kasim ammh kuma Ba Wayarta ahannunta ko Tana hannun Waye bata sani ba,Dole
Tayi Shuru Tana kukan Zucci Bakinciki kamar ya kasheta In Ta Tunda yadda Aka mata
Tozarci Saboda Anga Baba bashi da Rai.

Koda Karfe 3:30pm na Rana tayi Dukkan masu Tafiya Sun Shirya Domin Jirgin da ya
Muktar yayi musu booking karfe 4 ne zai Tashi Zuwa Abuja,Anty Yagana da Anty Nafee
ne Suka Dauko Aneesa Daga Sashen ya Sunusi Zuwa Cikin Falon da su ya Ali ke Zaune
Suka Sata Atsakiyarsu Lokaci Daya Suka Fice Suka barsu,ya Sususi ya kalleta yadda
Take Kuka cikin lafaya yayi gyaran Murya yana Fadin"Aneesa...'..

Ya kirata Muryansa ba Alaman Wasa Bata amsa ba ammh Ta Dago Lokaci Daya Tana
kallonsa Nuna ya Ali yayi yana Fadin"Ni da Shi Matsayin Suwa muke agareki..? Tana
Hawaye tace"Ku Yayyena ne kuma kuna mtsayin kamar Mahaifi ne Awajena.."ya Ali yace
"Gud...Nagode da Kika Fahimci Haka Babu Abunda Zamu ce miki sai Ki Shiga Hankalinki
Domin Daga Muktar Har Rahila,Sun miki gatan da Mu bamu miki ba Abu Daya Zakiyi musu
ki saka musu Shine ki Zauna Da Mijinki Lafiya kiyi Mai Biyayyah..Allah ya baku
Zaman Lafiya da Zuru"a Dayyiba.."Yafada Yana kallon ya Ali Wanda ke Wasa da Hibba
yace"Bazaka ce komai ba..?

Kallonshi yayi kafin yace"Nagama Maganata Tun Dazu Sunusi In ta kwantar da


Hankalinta Ruwanta in ma Taki Duk Daya,tabar ganin ta girma har yanzu baki girmi
Duka Ba Aneesa ko da Wasa naji kinma Mijinki Wani Diban Albarka Wlh Har Abujan zan
Biyoki na Miki Dukan Tsiya Kinji ko Baki Ji ba.."Ya karishe Fada Cikin Tsawa Aneesa
Da Rawan Jiki Dana baki tace"Na..naji.."Tafada Tana Fashewa da kuka ya Ali ya kalli
ya Mukar yana Fadin"Ko bayan kun koma Gidan karku mata da Wasa Ko kadan.."Mirmishi
kadai yayi baiyi mgana ba

ya Sunusi ne ya Fita ya leka ya Kira Anty Yagana Tazo ta Tafi da Aneesa Daganan
Dakin Mama yana Aka kaita inda Dangin Babansu yake suma suka mata Nasu Nasihan Mama
yana ma Ta Rumgumeta tana Fadin"Allah yayi ma Rayuwar Aurenki Albarka
Aneesa..."Take Fada Tana Shafa kanta,Lokaci Daya Itama Taji Tana kwallah,ita da
kanta ta Jata Har Zuwa Dakin Mahaifiyarta Falmata ta Dukar Da Ita agabanta tana
Fadin"Gata nan Falmata ki Bude baki kiyi mata mgana Wannan karon Tafiyan Aneesa
tasha Bambam da Sauran Tafiyoyin data keyi..Gidan Mijinta Zata ki bata Abunda Zai
zama Wani Jingina gareta amtsayinki na Mahaifiyarta.."Daganan ta Umarci kowa ya
Fice ya barsu Su kadai.

Falmata tadade tana kallon Aneesa Wacce Ta Dunkule Cikin Lifaya Tana kuka batare
Datayi mgana ba ta Mike Zuwa Cikin Dakinta Ta Dauko Qur"ani Izifi Sitti da Littafin
Addu"o'i na Hisnul Muslim,Bata mata mgana ba Sai da ta ijiyemata kan Jikinta kana
Tace"Bani da Abunda Zan gaya miki Aneesa Wanda Yayyinki basu Gayamiki ba..Kuma bani
da Abunda Zanbaki Wanda basu Taba mallaka miki ba,Umarni na gareki Shine ko da
Darana D'aya kika ji kina jin Haushin Wani Daga Cikinsu ban yafe miki Ba Aneesa
Ban yafe miki ba..."Tafada Tana Kallonta da Hanzari Aneesa Ta Dago Tana kallonta
Lokaci Daya tana Zubar kwallah.

Gyada mata kai tayi kafin tace"Eh ban yafemiki ba..Saboda Sune ginshikinki..Kuma
Bangonki kuma garkuwanki ko Bayan Raina Ban yafe miki ba Matukar kika Bijirema
Umarninsu Dukkansu ba.."Kuka Aneesa Ta Fashe dashi mai karfi Falmata Dake Danne
Hawayenta ta cigaba da Fadin"Ina miki Fatan Samun Gidan zama har Abada..Ya
albarkaci Aurenki kuma ya Raya Zuru"ar Da zaki Haifa,Tashi kuje Aneesa In kika Rike
Abunda na baki Har Abada zaki Rabauta Tashi kuje..Allah yayi miki albarka.."Tafada
lokaci daya Hawaye Suna wanke mata Fuska.

Da Gudu Aneesa Ta mike ta Isa jikinta ta Fada mata Tana Shesshekan Kuka,Lokaci
Daya Falmata ta Rumgumeta tana Bubbuga bayanta,na Tsawon Minti Biyar kafin ta
Saketa ta Juya ta Shiga Cikin uwar Dakinta da Sauri Tana Share Kwallah,Dukewa
Aneesa Tayi Tana Gunjin kuka Lokaci Daya Ta Dauki Qur'anin da Hisnul muslim din
Data ijiye Agefe Ta Rumgume Tana kuka Lokaci Daya Wani Son Mahaifiyarta ya kara
Lullubeta Domin Ta bata Abunda ba Wanda ya taba batashi.

Koda 3:50pm tayi Suna Filin Jirgin Maiduguri,4pm Daidai na Yammah Jirginsu ya Tashi
Zuwa Abuja Acikin Masu Rakiyan akwai Anty Yagana,Anty Nafee,Anty Aisha,khadija
Matar ya Ali,sai Cikin Dangin Babanta Guda biyu,sai Aneesa da
Sanah,B.kaita,S.jibiya,Da Anty Rahila da Hibba da Junoir,sai Ya Muktar sai Daada,
kadai Suka Tafi Mama yana Ita sai bayan kwana Biyu Zata zo da Sauran kaya,Har
Jirginsu Ya Daga Aneesa Na Dunkule kanta Cikin Cinyoyinta Tana Kuka,mai Cin Rai ba
wanda yabi ta kanta Tunda batajin Lallashi.,gefe Daya kuma Tana Rike da Abunda
Falmata ta bata bata yarda ta bama wani Ajiya ba.

*******

Tawagar su Kasim Duk Agidan Abba kabiru suka yada Zango,Lokacin Gida ya cika ya
Tumbatsa da yan"uwa da Abokan Arzuka anata Hada Hadar Arziki,Hatta gidan Abba garba
Duk suna gidan Abba kabirun,Inna Rukayyah ma Tazo Ita da gayyarta.

Sai ga shi Sun Dawo da Mugun lbri Wanda ya girgiza mutane Dadama,Gabadaya a Falon
gidan Suka yada Zango Abba kabiru na maida Bayanin Abun ya Faru Kasim na gefe Kan
Cafet Shida Abokinshi Haruna,Sauran Abokansu kuma Wasu Daga Filin jirgi suka Dauki
Tasha Mota Suka Koma Kaduna,Haruna ne kadai Tare Dashi Domin Shine Babban Abokin
Ango.

Lokacin da Abba kabiru ya Furta da Bello Aka Daura aure Zulfa da Zubaida Atare Suka
Mike Dafe da Kirji,lokaci Daya Suka Kwalolo ido Zubaida ce Tace"Wani Bellon Abba..?
Dakuwa Abba Kabiru ya sakarmata kafin yace"Bellon Ubanki Shegiya,bama zaki
Jajantama Dan"uwanki ba bisa Tozartanshin da Bellon yayi ba,A'ah ke Naki Tunanin
Dabam Sakarya Kawai.."

Yafada Cike da Takaichi kamar ya Fashe da Kuka,zubaida da Zuciyarta ke Bugawa ta


saki kuka kafin ta Fice Daga Falon ita kuwa Zulfa Dabas ta koma ta Zauna Kusa da
Mama Sahura tana Jin kamar Hajijiya zai kwasheta ganin Haka yasa Mama Sahura ta
Rikota Lokaci Daya tana Girgiza mata kai Inna Rukayyah ce ta Mike Tana
Fadin"innalilahi...Ammh Wannan yaron Bello anyi Tijararre ya Kabiru,toh ku Wani
mataki kuka Dauka Akanshi..?

Abba Kabiru yace"Hmm Rukayyah kenan Wani Mataki Zamu Dauka Tunda bamu da Gaskiya
inda Shi kasim din ya Rike Mutuncin kanshi da Duk Sonshi daya Tozartamu Ai bazai
samu Dama ba,Ammh Dayake ka Haifi Da baka Haifi Halinshi ba Abunda Yakeso Shi yaje
yana Aikatawa.."Yafada yana Hararan kasim din Wanda kansa ke Duke yana Tsiyayan
Kwallah

Abba garba yace"Toh kai Yaya Kana Wata mgana Allah ma ya Taimake mu ba wani Jami"in
Tsaro Ai da Tuni muna an Tsarenmu yaron Daya Dinga mganganu yana nuna mu mukayi
Sanadiyar Mutuwar iyayensa kuma muka Cinye musu Dukiya ku godema Allah da Abun ya
Tsaya iya Haka Yayi Hakuri ba ita kadai bace Autan mata zai samu Wacce Ta Fita,kuma
ka Kyaleshi karmuji kace zaka Dauki mataki domin Wannan yaron yafika
Tantiranci..."Umma tace"Wlh kuwa Allah nagode maka ma da Abun Bai Tabbata ba,Domin
Wannan yarinyar ba matar kwarai bace..."Tafada Ranta ya mata Dadi Sai Abu Dayane ya
bata mata rai yadda Aka Tozarta Hallayan Danta a idon Duniya.

Hashim dai na Zaune kanzil bai ce ba Sai da Kasim ya Mike yana Rangaji zai Fice ya
kallesa yana Fadin"Saura kuma ka koma Shashenka kasha giya har ka kasa Tashi,Domin
ba Hankali gareka naga Abunda ya Faru dakai bai zama izina gareka ba,In zaka bar
Hallayarka ka bari in bazaka bari ba Wlh ko gaba ka Nemi Aure Abunda zai sake
Faruwa dakai kenan.." kasim Dake kokarin Fita ya Waigo yana Kallon Kowa Dake Falon
kafin yace"Kada ku aika akarbo duk Abunda nakai...Na barma Aneesa Har Abada.."

Yafada yana Juyawa Da Hanzari Umma tace"Ka ce me..? Wlh bata isa ba sai an karbo
komai.."Abba Kabiru yace"Ina Ruwanki ba Kudinshi bane,Kuma Tunda yace ya barmata ki
kama bakinki kawai malama.."Yafada Yana Hararanta Mama Sahura da Sai yanzu ta saka
baki tace"Gaskiyan kam.."Wani Banzan Kallo Umma ta Watsamata itako Mirmishi Ta Saki
alamun ke keda Haushi kuma.

Ko jiyowa Kasim baiyi ba ya Fice yana Rangaji Haruna yabi bayanshi Dauke Da Babban
Rigarsa da Hula Har part Dinshi,Kan gadonsa ya Fada Lokaci Daya ya Fashe da Kuka
Kan Stool Haruna ya Zauna bayan ya Watsa kayan Dake hannunsa kan Wata Kujera Dake
Bedroom Din Cikin Bacin Rai yace"Na gaji dajin kukan ka Kasim ka mike ka Share
Hawayenka,kamar yadda kace ya samu Nasaran Auren Aneesa ammh kuma Shima yakamata ya
kare Rayuwarshi Cikin Kila wakala.."Kasim ya mike yana Share Hawayensa yace"Raina
na Kuna Haruna...Aneesa Wacce na gama Tsara Duka Rayuwata da Ita..Kai ina Bazan
kyaleshi ba sai na saka an kashemin Shi Har Lahira.."Dariya Haruna ya saki kafin ya
Mike ya Dawo Kusa Dashi yana Fadin"Ka kashe shi fa kace..? Haka kurum ka dora ma
kanka Diyyah...? Manta kawai Abokina So nake amai Kisan Rayuwa Wanda yana Raye ammh
Shida Mattace Duk Daya.."Da mamaki Kasim ke kallonsa kafin tace"Bangane ba..? ..

Mirmishi ya saki kafin yace"Kawo kunnanka kaji.." Nan da nan Kasim ya mikamai
kunnansa ya Fadamai Wata mgana Wanda nikaina banji kome Suka ce ba sai dai naga
Kasim ya Zaro Ido yana Fadin"Kai don Allah..."Gira Haruna ya Dagamai yana
Fadin"Zakace na gaya maka.."Hannu ya bashi Suka Tafa kafin kasim yace",Nagode
Abokina....Har kasa naji Farincikina ya kamani Wlh...",Dariya Haruna ya Saki yana
fadin"Tashi ka shiga Wanka ka Fito mu karisa mgana.."Jiki na Rawa Kasim ya Mike ya
Shiga Tiolet yana Dariya kamar bashi ne yagama Kuka yanzu ba.

*****

Sai Bayan Mangariba kana tawagar Motocin ya Muktar,Suka je Filin Jirgi Suka Taho
Dasu Bello Dake Kwance Cikin Bedroom Dinsa Cikin Bargo yaji Dawowarsu Kansa ne ke
bala"in Ciwo Tunda Suka Daawo Ganin Halin Dayake Ciki ne ya saka Sani bai Wuce
kaduna ba Aranar ya bari sai Washegari,ya Zauna Tare Da Bello,Daga nan ya saka Sani
yayi Waya Zuwa Cikin Shashen ya Mukrar akwai Telephone direct Zuwa Kichen,Alheri ce
tazo ta kawo musu Abinci da Abunsha Sanin ne kadai yaci Shi Bello Fruit kadai yaci
Yayi Taking pracetamol ya koma ya kwanta Zuciyarsa na Kuna Gabadaya Ya Muktar ya
batamai bajet,Aneesa fa Bata Daga Cikin matan Dake burgesa ammh Kuma bakin alkalami
ya Rigaya daya Bushe.

Shashen Daada aka Sauke Aneesa ita da Kawayenta da yan"uwan babansu,Sauran kuma Su
ka koma Shashen baki,agajiya Suke Shiyasa Abinci kadai Suka ci Kowa yabi Lafiyan
gado yana Warware gajiya,Aneesa ko yunwa ce Taji Zata kasheta Tatashi Taci Abinci
kadan Ta koma ta kwanta Kusa da B.kaita Barci Ranar barawo ne ya Sace Aneesa ammh
kwana Tayi kuka,ga Zazzabin Jikinta Saura kuma Suna Dakin Daada chan Suka
Kwana.....

Sai da Safe kana ya muktar ya Shiga part din, Bello inda ya Tarar Dashi kwance
Cikin Blanket,sai Sani Dake Shirin Tafiya,Gaisawa Sukayi da Sanin kafin ya karisa
Gefen Gadon ya Zauna yana yaye bargon da Bello ya Lulluba Dashi Lokaci Daya Yana
Taba goshinsa.

Bello Dayaji Motsi sai ya Bude Idanuwansa Da Suka kumbura ya Sauke kan ya Muktar
Kokarin Mikewa yake da Sauri ya Rikesa ya Taimaka mishi ya mike Zaune yana Dafe
kanshi Cikin Tsausayi Ya Muktar yace"Sannu kan ne..? Gyada kai Bello yayi yana
Yamutsa Fuska,Ajiyar Zuciya Ya Muktar ya Sauke kafin ya Mike yana Fadin"Ka Shirya
muje Asibiti Anjuma.."Bello ya Dago kansa yana kallonsa bai yi Mgana ba,Saboda
Bakinsa yamai Nauyi Lokaci Daya Ya Muktar ya Nemi Hanyar Fita Daga Bedroom din yana
cema sani.."Badai Tafiya Zakayi ba.? Kai tsaye sani yace"Eh Ranka ya Dade."

Ya rike Handle din Kofar ya Waigo yana Fadin"Ayyah badamuwa Mungode..In zaka Wuce
ina Haraban gida..mungode.."Daga Haka yafice Daga Bedroom din yana Fitowa da
wayarsa Wacce ke Aljihun Wandon jallabiyansa.

Sani ya karisa kusa da Bellon yana Fadin"Malamin mkranta Ni zan kama Hanya.."Gyada
kai Bello yayi Kafin ya Furta.."Nagode Sani.."Mirmishi yayi kafin
yace"Bakomai..Ango plz ka cire Damuwa Aranka Dama chan itace matarka,Mganar kasim
kuma karka damu bai isa yamaka Abunda Allah bai maka ba.."

Kallonsa yayi Ido Cikin Ido kafin yace"Nagode Sani..Ammh ni kasim baya gabana
karamin alhakine,kai ne zan ce ma ka kula Kada yace zai bataka Wajen
aikinka.."Yafada Cikin Sanyin Murna Sani ya Rausayar dakai yana Fadin"Haba bai isa
ba ai bashi ya Dauke ni ba,Allah ya baka lafiya.."Yafada Lokaci Daya Suna musabaha
kafin Sani ya Dauki Wayarsa ya Fice Daga Bedroom Din Bello yabishi da kallo.

A haraban gidan ya Iske Ya Muktar na mgana awaya sai da ya Jira yagama,kana Suka
sake Sallama 50k cash Ya bashi da Farko kamar bazai karba ba sai da Ya Muktar din
ya mtsamai,musabaha Sukayi Ya Muktar na karamai godiya Mallam Inuwa Direba ya
Daukesa Zuwa Filin Jirgi inda Zai Shiga Wani Jirgin Zuwa Kaduna garin Gwamna

Sun wayi gari Cikin Hidima Abunsu Kamar Babu Abunda ya Faru,Kafin karfe goma baki
Sun Fara Zuwa kawayen Anty Rahila na nan Abuja,can sai ga Maman B.kaita ta
iso,maman S.jibiya ne Bata samu Zuwa ba bata nan Taje Jibiya,Tuni Dama su Alheri
Sun kamallah Girke girke,dama Tun Safe Ya Muktar ya Fice Daga Gidan,Aneesa ko
kwanciyarta Tayi Taki Tashi tayi Wanka Tana gani su B.kaita Sukayi Wanka Suka Dau
kwalliya bata yi Wanka ba sai da Taga yan Sch dinsu na Kwatar kwashi Sun Fara Zuwa
Wata Rabi daga Suleja sai Mariya Daga kaduna Shiya Tilastama Aneesa Wanka ta Shirya
Cikin Wani material Riga da Sikat,ta yane Mayafin Material din kamar Lifaya,bata
wani yi kwalliya Ba Fuskarta Kodai kodai ba Wanda ya Bi ta kanta gwarama Daada ta
Shigo ta mata Nasiha Shine Har ta saki Ranta ta Shige Cikin Kawayenta anata Hira,Su
B.kaita Su suka Fara kyankayasama Su Rabi Wanda Aneesa Ta Aura nan suka saka guda
Abunda ya kara saka Aneesa Ta Fashe da kuka Suko Suna mata Dariyan Shakiyanci.

Ba laifi Yan makrantarsu Aneesa Sunzo musu,zasu kai goma Kowa Tazo Taji Aneesa ce
ta Auri Mr Bello sai Taji Aneesa Tayi Sa"a,Domin Samun Namiji kamar Mr bello abu ne
mai Wahala,sai Tambayanshi Suke sai ace musu baya nan Alhalin yana part dinshi yana
Fama da Ciwon kai Da Tunanin yaya Makomar Rayuwarsa,Anyi Biki lafiya Sha"ani Yayi
Dadi Kowa kagani Cikin Farinciki banda Aneesa da Bello,Wanda Anty Rahila Ya Muktar
ya Kira yace Ta Shiga Ta Dubashi da yammah Mallam Inuwa zai kaishi Asibiti.

Duka bakin Washegari Ranar Lahadi Kowa yayi Haraman Tafiya Kawayen su Aneesa Wasu
basu kwana ba,Wadanda suka kwana kuma da Safe suka Tafi,Haka B.kaita Tabi mamanta
Tun Jiya S.jibiya ne Direban gidansu yazo Ya Dauketa Suka Rabu da Aneesa da
Kuka,Anty Yagana da Anty Nafee,da Sanah da Yan"uwan Babansu kuma da La"asar Aka
kwashesu Zuwa Filin Jirgi inda Suka Shiga Jirgin Maiduguri,Anty Aisha kuma mijinta
ya aiko aka Dauketa ta Wuce kano nan Suka bar Aneesan Falon Anty Rahila bayan Sun
mata Nasihohi da kuma Lallashi Data Rumgumi Auranta,Haka Suka barta Tana ta kuka
kamar Ranta Zai Fita Daada ma kasa lallashinta Tayi Saboda Tsausayinta.

Sai bayan Sallar Mangariba Bello ya Fito daga Shashensa Cikin Riga da Wando,Duk ya
Rame kamar bashi ba,Mallam Inuwa ya kaishi Specialist hop,ya karbo manguguna Dama
anan Suke da Fayel,daya Dawo Dakyar ya iya Shiga Masallaci yayi sallar Isha"i yana
Komawa Shashen nashi ya Shiga Bedroom dinsa kenan yaji Mganar ya Muktar Da Daada
bai kai ga Fitowa ba ya Muktar ya Bude Kofar Bedroom dinsa yana Shigo yana
kallonsa.

Kibiya ki karanta cikin Salama.

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?18*

"Kallonsa Bello yayi Lokaci Daya yana Lumshe idanuwansa,bai kariso Tsakiyar Bedroom
din ba yace"Ya Jikin naka...? Cikin Sanyin Murya yace"Am better Now..."

Kada kai ya Muktar yayi kafin yace""Daz gud...Ka samemu Afalo zamu yi mgana
dakai.."Kai Shima ya gyada mai baiyi mgana ba Har ya Muktar ya Fice Daga Falon da
Kallo ya Bisa Lokaci Daya yana Tura Hannunsa Bisa Sumar kanshi Lokaci Daya kuma
yana Sakin Ajiyar Zuciya,bai Fito ba Sai da yadan Bata Lokaci kana ya Fito
Falon,nan ya Tarar da Daada Da ya Muktar suna kan Kujera mai zaman mutum Biyu Sai
Anty Rahila dake kan Mai zaman Mutun Daya Aneesa ke Zaune akasa kanta Duke Cikin
Farar Lifaya,Hibba na gefen Abbanta Junior ne ke kusa da Aneesa yana wasa da Gefen
Mayafinta.

Cikin Sanyin Jiki ya kariso Gaban Daada ya Zauna Kusa da Kafafunta,kanshi ta Dafa
Tana Fadin"Babban Megidana,Duk ka Rame.."Tafada tana kallonshi Mirmishi ya
Sakarmata Kafin ya Rike Hannunta yana Fadin"Nayi kewarki Daada.."Yafada yana Sauke
Kwayan idanuwansa kasa Lokaci Daya yana gaida Anty Rahila,ta amsa cikin Sakin
Fuska,Da Gudu Hibba ta Dane Jikinshi Tana Fadin"Oyoyo Uncle.."Riketa yayi yana
Shafa Kumatunta lokaci Daya yake Fadin"Hibbatullahi Ta zama yan mata ko.."Baki ta
Washe Ita adole ance Ta zama yan mata Dukkansu Sai da Suka saka Dariya Banda Aneesa
dake Hararan Bello ta Cikin mayafinta Shiko Tunda ya Shigo Falon ko kallon Barayin
Datake baiyi ba Ballatana ma Har ta samu Wani kyakyawan kallo ..

Ya Muktar ne ya gyara zama yana Fadin"Bello...."Yafada Cikin Muryan ba Wasa,Dago da


kansa Bello Yayi daga Wasa da Hibba yana Fadin"Na"am yaya..."Bai Tsaya Sauraransa
ba yacigaba da Fadin"Nasan kasan Dalilin Zaman mu anan ko?kowa yasan yadda lamura
Suka Chanza yanzu dai ka Tabbata miji ga Aneesa itama ta Tabbata matarka toh
gatanan An kawo Maka ita ina Fatan Zaka Riketa bisa amana da adalci.."Yafada yana
kallonsa kansa Bello ya Maida kasa yana kananan Sauke Numfashi Cikin Muryan Sanyi
yace"Insha Allahu Yaya..."Mirmishi Daada Ta Saki kafin tace"naji dadi Hakan Sosai
Megidana naasan bazaka bamu Kunya ba Don Allah ku Zauna Lafiya da Junanku Tasanka
kaima ka santa Tunda Duk Gida Daya Kuka tashi...Allah ya baku Zaman lafiya,Ayita
Hakuri Aneesa kamar kanwa Take gareka Itama tamkar wa kake gareta In kun saka
Hakuri Acikin Zamanku kubama kowa mamaki in kuma kowa yaki Saukar da Halinshi kuma
Kusha Wuyan Juna..."Bello kansa na kasa bai yi Mgana ba Illah Wasa da yakeyi da
Hibba,nan da Daada Da Ya Muktar suka kara yi musu nasiha Sosai Aneesan ma Suka ja
mata kunni Sosai Anty Rahila ma ta mata nata Nasihan Sosai kafin Su Rufe Wajen da
Addu"a Sun mike zasu Tafi kenan ya Muktar yace"Ku cigaba da Maneji anan Kafin
Kagama Shegen Ra"ayinka ka Fara Aiki mai kyau domin Nasan Ko Cewa nayi ka Shiga
Daya Daga Cikin Gidajena na nan Abuja bazaka yarda ba.."

Bello ya Mike yana Rike da Hibba yana Fadin"Allah ba Haka bane Yaya..Na Riga Na
Turama BUK C.v Dina Ta Email dinsu Har Sun Turomin da Sakon naje na karbi
Appiontment letter.."Kallonsa Ya Muktar yayi kafin yace"Ok..Chan din Dai yayi
maka,ga University of Lagos Tun yaushe Suke Nemanka.."Bata Fuska Bello yayi yana
Fadin"Nifa Yaya bana son Zama a kudu Allah..."Jinjina kai yayi kafin yace"Ba
mtsala Duk Dayane Allah yabada Sa"a.."Da Ameen Dukkansu Suka amsa kafin Su yi musu
sallama su fice Daga Falon Bello na Biye Dasu Dauke da Hibba Junoir ko Da Kuka ya
yarda Anty Rahila ta Daukeshi ya makalema Aneesa Wacce Ke Hawaye.

Suna Fitowa ya Muktar ya juya ya karbi Hibba yana Fadin"Ka koma Ciki...Gud
Nite.."Mikamai ita Yayi Tana Dagamai Hannu Shima Dagamata yayi Har Suka Sauka Daga
kan Steps din Suka Nufi Shashen ya Muktar din Suna Tafe Suna Hira ya Dade yana
kallonsu Har Suka bacema ganinsa Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya koma Cikin Falon
Lokaci Daya yana Kulle Kofar Dakin da Makulli kallo Daya yayima Aneesa Dake
Durkushe Inda Su Anty Rahila Suka barta ya sake Hade Rai,Wucewa yayi Zuwa bedroom
dinsa cikin takun Sa na isa yana Shiga ya Turo Kofar lokaci Daya kuma ya saka ma
Kofar key da Harara Aneesa Ta bishi kafin Ta Dago da kanta Lokaci Daya Tana
yaye,Lifayan Jikinta,Doguwar Rigar Atamfa Dake Jikinta ta Bayyana,Kan kujera ta Hau
Tana Karema Falon kallo lokaci Daya Tana Tabe baki Aranta tace"Falo kamar na wata
mace.."Domin Ita Tunda Take bata Taba Shigowa Shashensa sai Sau Daya Shima Anty
Rahila ce ta matsa mata ta kai mishi Coffea Wai bayason su Alheri na Shiga mai Part
lokacin kuma Data Shigo bata lura Da Falon ba Sosai

Saboda leke leken Aneesa Har Kichen Ta leka Tana Dube Dube Tana Tabe baki,ammh
Sanda Take kar yaji motsi ya Fito Kichen Din Shima kamar na wata macen Aure,komai
na Bukatar Girki akwai aciki Cikin Frigde din Kuwa Shake da Madaran Hollandian da
Kayan Marmari Tabe baki tayi Tana Fadi afili.."Oh wato Shiyasa bai damu ba Cin
Abinci ba,ashe ga Abunda yake sakama Cikinsa nan..."Fitowa Tayi Daga Kichen Din
Cikin Takaichi,Gashi Wayarta Batasan Wanda ya karba ba Tun a borno bata kara
ganinta ba,Tana so tasan Halin da Kasim yake Ciki,ammh ba Hali kan Doguwar kujera
ta Haye,Tana Tura baki ita kadai Cikin Ranta Tana Fadin Andai Cuceta an Hadata da
Mugun Mutum kuma wai Kowa Ahaka gani yake ta dace,Kodai Bata Dace ba.

Tun Tana Tunani da Zencen Zucci Ta gama Tunanin kasim da Halin Dayake Ciki,Har sai
da Tayi kuka Daganan Batasan Sadda barci ya Kwasheta ba,Dama already Tun Adakin
Daada Tayi sallar Isha"i Dinta Hade da Shafa"i da Wuturi Shiyasa Taasaki Jiki bisa
Kujera tana ta Sharar barcinta hankali kwance Kamar tana Dakinta Saboda Gajiyar
Baki dama gashi kwana 2 bata samun Barci ba Sosai.

Bangaren Bello Kuwa Da Gayyah ya Rufe Kofar Bedroom Dinshi Saboda Kar Aneesa Tayi
karambanin Shigowamai Daki,Bedroom ya Fada yayi Wanka tare da Dauro alwala yana
Fitowa ya Zura kayan Barcinsa Pjs,Riga da Wando masu Ruwan Kasa bai kwanta ba Sai
Da yayi Shafa"i Da Wuturi Har ya Kwanta sai ya Tuna bai Sha Mgungunansa ba Gashi
kuma Cikinsa na Kiran Yunwa,Mikewa Yayi ya Zura Takalminsa na Bedroom ya Bude Kofa
yaFito Falo nan yaga Aneesa Ta Dunkule Kan Kujera tana barci Har Dankwalin kanta ya
Sabule,Kitsonta kanana 2 Step Wanda Anty Aisha Ta mata Suka Bayyana Awaje,kallo
Daya yayi mata ya kauda kai kichen ya Shiga ya Dauko Madaran Hollandian Guda Daya
da karamin Kofi kashe Wutar kichen din yayi kana ya Fito Har Ya Wuce Zai Shiga
Bedroom Dinsa sai kuma ya Dawo Baya Ya Saka Hannu Daya ya Dauki Remot din A.C din
Falon ya Rage mai Iska Lokaci Daya kuma ya Rage Wutar Falon Ya kunna mata Dumlight
kafin ya Kada kai ya Shiga Bedroom ya Rufo kofarsa yana Sakin karamin Tsaki

Sai da yasha Madaran kana ya Balli magungunar yasha,ya maida Komai bisa Side Drower
din gadon kafin ya Shige Cikin Blanket Lokaci Daya yana kashe Hasken Dakin ya Kunna
Dumlight,sai da ya kashe Wayarsa kana ya Dora kansa Bisa Filo yana Lumshe
ido,Tunanin Abunda Likita ya Fadamai,Ya dawo mai Fadamai Jininsa ne yayi sama
Saboda Damuwa kuma baya barci kwana Biyu yayi kokarin Ya Dinga Samun barci Ajiyar
Zuciya Ya Sauke kafin ya Runtse idanuwansa Lokaci Daya barci mai Nauyi ya
kwasheshi.

Bai Farka ba,sai Wajen 5am Shima Kiran Sallan Mallam Inuwa ne ya Tadashi Domin Dama
In bai kira ba Mallam Inuwa ke Kira Watarana ma Har sallah ma yana Badawa,Tashi
yayi Zaune yana Mika Lokaci Daya Yana Salati,Wayarsa ya Dauka ya Kunna nan yaga 5
ta Wuce Kafafunsa ya Zuro Zuwa Saman Cafet din Dake Dakin,Takalminsa Dake bakin
gadon ya Zura lokaci Daya mikewa Wutar Dakin ya Kunna haske ya Gauraye ko"ina kafin
ya Fada Tiolet,Wanka yayi agurguje kafin yayi alwala ya Fito Wardrope dinsa ya Nufa
yana Goge Jikinsa da Karamin Towel din Dake Hannunsa,Jallabiyansa Baka ya Ciro Ya
saka Da Hula,gaban Dressing Mirrior Dinshi ya Isa ya Dauki Turare yana Fesawa
Hanzarin Fita yayi jin kiran Sallah na Biyu Wayarsa ya Dauka Lokaci Daya ya Bude
Kofar Bedroom Din ya Fita Yama manta da Wata Halltta Aneesa Shiyasa ya Fice kai
Tsaye Daga Falon Batare Daya Damu ba.

Bai Dawo part Din Nashi ba Sai Wajen 6am na Safe Domin yau Mallam Inuwa ya bada
sallah Shikuma ya Tsaya yayi karatu,yana Shigowa Falon Cikin Takunsa na Jarumta
idanuwansa Suka Mai Tozali da Aneesa Dake Kwance Tana Barci Saboda Dadin Barci Tayi
Rigingine Ta matse Lifayanta Awajenta Cikinta Gabadaya Cinyoyinta Suna Waje,Saboda
Doguwar Rigar Tayi sama Saurin kauda kai yayi yana Tsaki Lokaci Daya kuma da Karfi
Wanda ya Farkar da Aneesa Daga Barcin Datake sha.

Tana Mitsike Ido Ta Hango Wucewarsa Kamar Wani Sarki yana Wani Taku D'aid'ai da
kallon Rainin Kallo Ta bishi har ya Shiga Cikin Bedroom Dinshi zai Rufo kofar kenan
ya Waigo Suka Hada Ido da Sauri ta Kauda kai tana Sakin karamin Tsaki Ido ya Waro
yana kallonta Cikin mamaki ya Fasa kulle Kofar sai ma Fitowa Dayayi yana Fadin"Ke
Don Ubanki wa kika ma Tsaki yanzu.." ?Yafada Yana Sakarmata manya Idanuwansa

Saurin Mikewa Tayi tana Raruman Dankwalinta ta Maida Bisa kai Bakin nan ta Tura
gaba cikin Ranta tana Fadin"Badai ubana ba Sai dai na Mutum Tunda Uba baifi Uba
ba.."Tafada Tana Tura baki,Tsaye yayi yana kallonta Cike da Bacin Rai kafin ma ya
Sake magana Ta Dauki Lifayanta ta Yafa ta kama Hanyar Fita Bakin nan kamar ya Fado
Saboda Kunkuni ..

Cikin Kuluwa yace"Ke...ke...Bada ke nake Mgana ba..."Yafada yana Maida Hannuwansa


Cikin Aljihun Jallabiyansa Ko Waigowa Aneesa Batayi ba ta Fice da Sauri,Numfashi ya
Fesar kafin ya Kada kai ya koma Cikin Bedroom dinsa Aransa yana Fadin Yarinyar nan
ta manta ni ne Sai na kara Tunasar da ita komai.

Ya Cire Jallabiyan kenan ya Kwanta Wayarsa ta Dauki kara yana Dubawa Yaga Principal
din Mkrantam Kwatar-kwashi ce Dauka yayi Bayan Sun gaisa Take Tambayanshi Ashe ya
Dawo yace mata Eh Cikin Dariya take Fadin Mallam muna Jiranka fa"Mirmishi yayi
kafin ya Fara mata bayanin komai Duk da Bataji Dadin Rashin da GGUSS,tayi ba na
Malami kamarsa ba Ammh Tasan ko bajima Dole Mr bello zai Tafi Sakamakon Ko Kudin da
Suke Biyansa bai kai mtsayin Karatunsa ba kawai Ra"ayinsa ne Haka Har Sunyi sallama
take Tambayanshi da Gaske lbrin Dataji Wajen Dalibai wai yayi Aure kuma Aneesa
Bukar Bulama ya Aura.?mamaki yadda Lbrin yakai Mkranta yake bai mata Wani Dogon
bayani ba ya Dai amsa mata da Hakane Fatan alheri ta mai kafin Su Yanke Kiran Ya
barta Cikin mamaki Duk da Ta san Cewa Babu Abunda Zata samu Daga Bello Saninshi
Marason Hayaniya,Daganan Kashe Wayarsa yayi gabadaya ya Kwanta bayason kuma Damu.

*****
Daada na Zaune Tana Lazimi Aneesa Ta Shigo Dakin nata Tana Tura baki Cikin Mamaki
Daada Ta Dago Tana Binta da kallo Baki Bude bata samu Zarafin mgana ba Aneesa
Tace"Daada ina kwana.."Bata amsa ba illah cemata Datayi.."Daga ina kuma Haka..? Kin
manta yanzu ba da bane.."?

Tura baki Aneesa Tayi kafin tace"Yo Daada Nazo yin sallah ne da Wanka.."Dakuwa
Daada ta Mika mata tana Fadin"Kinga naki Ja"ira Chan babu Wajen Yin Alwala da
Wankan ne..?."Bata rai Aneesa ta karayi kafin tace"Toh wai ni Daada meye laifina
Yafa Kulle Dakinshi kuma na Duba Falon ba Tiolet kuma ma ko Akwai bani da kayan
Chanzawa..".

Tafada Harda Buga kafa kafin Ta Fice Daga Dakin Tana Tura baki Dayan Bedrrom Din ta
Shige Tana Kunkuni,Da ido Daada Ta Rakata kafin ta Sauke idonta tana Fadin"Allah ya
Shirya.."Cigaba Tayi da Lazamin ta bata kara jin Duriyar Aneesa ba sai da Tayi
Wanka Tayi sallah TaChanza kaya Cikin Atamfa Riga da Sikat batayi Kwalliya ba
Shiyasa Fuskarta Tayi Fresh Da Ita Dakin Daadan Ta Dawo Ta Haye gadonta tana
Fadin"Allah ya isana Jiya A Kujera na na kwana Duk Wuyana ya Sage..."Tafada Tana
Shafa Wuyanta ko mgana Daada Bata mata ba Tana dai Binta da Ido ..

Anty Rahila ce ta Shigo Ita da ya Muktar wanda ke Dauke da Junior Gefensu kuma
Hibba ne,Dukkansu sun sha gayu gwanin Ban Sha"awa,Daga gani yau Ya Muktar din bazai
Fita ba,Sanda Suka Shigo basu lura da Aneesa ba sai da Suka kariso Tsakiyar Dakin
Cike da Mamaki Anty Rahila ke Kallon Aneesa Kafin Ta maida kallonta ga Ya Muktar
Shima Wanda ke kallon Aneesa Harda gyara Kwanciya tana lumshe ido ..

Baki Anty Rahila ta Rike kafin Tace"Daada wa nake gani kamar Anee.."Daada tace"Nima
Haka nagani na mata mgana tace Tazo yin Wanka ne da Saka kaya,daganan kuma aka Hau
gado sai Tura baki take bansanin mata ba Don ko Tankata banyi ba.."Haushi yakama
Anty Rahila ta Isa bakin gadon ta Dagamata Duka Lokaci Daya Tana Fadin"Tashi Don
Ubanki ki koma Shashen Mijinki kiyi barcin achan.."Mikewa Tayi tana Soshe Soshen
Wajen Tana Fadin"Kai Anty Rahila.."Tafada Harda Matse Kwallah.

Daada Tace"Wai ni kayan ma Datake Sakawa ba Maidama yaron chan za"ayi ba..? Ya
muktar yace"No Yanzu da Safe Hashim ya Kirani yace Kasim yace Ya barma Aneesa Duka
kayan..."Daga Daada Har Anty Rahila Hada baki Sukayi Suna Fadin"Allah
Sarki.."Aneesa ko Kuka ta Fashe Dashi Tatashi ta Fita tana Fadin"Allah Sarki My
Kasim Allah ya saka maka.."Da kallo Suka Bita kafin Anty Rahila Ta Daga Murya tana
Fadin"Karki Dawo Nan ki Wuce ki koma Shashen Mijinki yanzu Jummai zata Hawo muku da
Breafast dinku.."Aneesa na Jinta ta mata banza sai da ta koma Dakinta ta gama
Kukanta kana ta Dauki Mayafinta ta Fita Bayan ta Kwalama Hibba kira tazo Suka Fita
Tare...

Wannan Koran Bai Rufe Kofar Falon ba,Shiyasa Suka Shiga Diret,Ita da Hibba Suketa
Hiransu Ita cema ta mtsa Shiyasa ta Kunna mata Cartoon,gefe ta kuma ta kwanta Har
Jummai ta Hawo musu da Faranti Cike da kayan karyaewa Dama Yunwa Takeji nan Suka
Baje ita da Hibba Suka karya kafin ta tattara komai na maida Kichen,Suna nan Zaune
sai ga Anty Rahila da Alheri Sun Hauroma ta Akwatunanta,ko kallonsu batayi ba sai
ma Tura baki da take Tana gani Anty Rahila ta Kwankwansa Kofar Bedroom din Bello
Sai da ya bata Lokaci kana yataso ya Bude domin ma ganin Anty Rahila ce da kanta in
ba Haka ba bamai Shigar mai da Tarkace Daki,Haka ta Shigan mata Dashi Har chan
Kurya Wajen Madubin dakin ta Jeramata su Bello dai na gefe yana bata rai bata Tsaya
ba ta mishi sallama ta Fice Daga bedroom din tana Fita ya maida kofa ya saka key
yana Sakin Tsaki Shi kadai.

*****

Sati Daya kenan da Auren Bello da Aneesa Ammh babu Abunda Ya chanza na
Zamantakewarsu,Kullum Aneesa Bata Wuni Acikin Ashashen Bello Daada da Anty Rahila
Sunyi fada har sun gaji sun zubamata ido,Wani Lokaci sai yammah take komawa Shashen
Sai ta tafi da Hibba da Junoir Kayanta Kuwa Baya barin ma Bedroom din Abude Sai ta
mamayeshi ne sai tayi wuf ta Shiga Ta Debo kayanta Kuma,kullum Shashen Daada Take
wanka da Cin Abinci Sun Gaji da mata mgana Sun saka mata ido...

Shiko Tundaga Ranar Wata Mgana bata kara Shiga Tsakaninsu ba,Afalo take kwana ko
kallo Bata Isheshi ba Shiryan Shiryan Tafiya Kano yake tayi Shikadai batare Da
Sanin kowa ba,Ita ko Aneesa Ko Waya ma Dakyar ta samu Ta Kira Su B.kaita Sau daya
suka gaisa tayi musu bangajiya Wayarta kuma Tun achan Anty Nafee ta karba Hannun
S.jibiiya Sai da Sukayi Waya Take Fada mata batayi Mamaki ba sanin Halin Anty Nafee
Mirmishi kadai Tayi Acikin Ranta Tana Jin bakin Ciki Toh Ta Hakura da mai Wayar ma
Ballatana Waya,Taje tayi ta kaya...

Ranar da zai Tafi kano Shi ya Tuka Kansa Cikin Daya Daga Cikin Motoci Guda Biyun da
ya Muktar ya siyamai ammh basu Taba Dadashi Da Kasa ba,Direct Cikin Mkrantan BUK ya
isa Ya karbi Appoiment Letter dinsa yayi Report,Sun bashi gida nan Cikin Mkranta
ammh Baya Sha'awar Zama Cikin Makaranta Dat Way ya kira Ya muktar ya sanar mai Shi
kuma ya Turamai Address din Gidanshi Dake BUK road, Wanda ko Shekara baiyi Da Siya
ba katon gida ne ammh ba Sosai ba Sai dai baida sama flat ne mai kyau mai Dauke da
2 floor da 3 Bedroom sai kichen,kowani Daki yana Dauke da Tiolet dinsa sai Haraban
Gidan mai girma da kuma Dakin me Megida,Wanda Ke Zaune yana Tsaran Gidan,Bello ya
yaba da Gidan Sosai Bayan sun gaisa da Megadin ya Shiga Ciki Nan ma ya kwana Saboda
yayi yammah Da Safe bai Wuce ba sai da ya Leka gidansu Uncle Aminu Suka gaisa da
Amminsa kana ya Dawo Abuja Da Shirin Jibi In Allah Ya yarda zai yo parking Zuwa
kano,domin ya kosa ya Daina Shakan Numfashi da Aneesa Yana Cikin Takura Sosai.

Ki biya ki karanta cikin Salama.

*Anitha..*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?19*

*KATSINA*

"Achan katsina kuwa Haka Biki Ya Tashi Zuciyiyo Babu Dadi Dangin Umma sai maganganu
Suke na An Tozarta Dan yar"uwansu Abba Kabiru yajama Umma Kunni kar karyaji Wata
Mgana,Bayan Shida Abba garba Sun Kira Ya Muktar Suna mai Rantsuwan basu san Abunda
Kasim ke aikatawa ba kenan da bazasu Taba Fara Shigemai gaba Aneman Aure ba,Sunyi
Haka ne Saboda Suna Tsoron Bello Domin Ko Ranar Daurin Aure A bornon Tsoron Nashi
ne ya Hanasu Wani Motsin Kirki.

Kasim kuwa Kwana Hudu Tsakani ya Tattara ya koma Kaduna,Shi Haruna Tun Washegari ya
koma Kano,dama chan yake sun Rabu da Niyyar sai Sunyi Mgana ta Waya,Da zai Tafi
Abba kabiru Yayi mai Fada Sosai kuma yaja kunnansa kan ya Fita Harkan Bello Kar ya
Kuskura yace zai Dauki mataki Yaga dai Suma basun Fita bane Duk Ranar Daya makasu
kotu yana da Hujjan da Za"a Dauresu har Igiya Tayi Rara bamai Sakawa a Sakosu.

Kasim Jin Abba Kabiru kawai yake kawai Don Mganarsa na Shiga Kunnansa ne tana Fita
Domin yaci alwashin Daukan Fansa Akan Bello Domin Bazai kyale Wanda yayi Sanadiyar
Kwacemai Aneesa ba,gashi sai kiran Wayanta yake Ba"a Dauka Ranar Dai da aka Daga
Anty Nafee ce tamai Zazaga tace karya kara Kira domin Aneesa Tana Gidan
Mijinta,Kwana yake Cikin maye Saboda baya Jure Tuna ya Rasa Aneesa Ko ya Hashim
kafin su koma Abuja Shima ya Sameshi yayi ta mai Nasiha Ammh kasim Jinsa kadai yake
bawai Domin maganganun Suna Shiga kansa ba.

Umma kuwa Da Abba Kabiru kemai Fadan ma yadaina Abunda yake Cewa tayi ya daina ma
Danta Fada Ita yaronta baya Neman mata Sharri bello ya Kullamai kuma Allah ya isa
Bata Yafe ba,Sai da Abba kabiru Ya Daka mata Tsawa kana ta kama Bakinta Mama Sahura
kuwa Duk da Abun bai mata dadi ammh ko Jaje batama Umma Aranta ma Allah ya kara
take mata Domin Tafi kowa Nuna son ya"yanta kafin Inna Rukayyah Ta koma kano sai da
Sukayi da ita kan Zubaida Kwata Kwata Umma bata iya Siyasar Duniya shiyasa Ko Abba
kabiru yake Girmama mama Sahura don ko da Take matar kaninshi Bata iya Gardama
Dashi ammh Umma gaban Ya"yansa ma Tsinka sa takeyi

Zubaida Dai Ya Hashim ya Tarata suka koma Abuja Saboda Makaranta ammh Tayi kuka
kamar Ranta Zai Fita Jin Aneesa ta Auri Bello Domin Ita harga Allh Haryanzu bataga
Namijin Daya Riga yagama Tsari da Rayuwarta Irin Uncle Bello ba,Hakura tayi ta
lallashi Zuciyarta ammh Tana ji Aranta bazata Hakura ba,zata Cigaba da Gwada
Sa"arta Domin Aneesa babu Abunda Zata Nuna mata Daga Bangaren Jiki Zuwa na Fuska.

Zulfa ko sai da Tayi Zazzabin kwana Biyu Mama Sahura ce Tayi ta lallashinta Tana
Nuna mata Gwara da Kowa ya Rasa Tsakanin ita da Zubaida,Ko da Bikin nan Da Suka
Hadu haka Dinga Jifan Junansu da Mugun kallo kan Wanda baisan ma Suna yi ba, kuma
kana uwa uba kuma Kowa na Bin Tsakin Uwarshi Ballema Mama Sahura da iya Kissa bata
nuna Akwai Takun Sa"a Tsakaninta da Umma gaban Mutane Shiyasa sau Tari ko Taro ake
Umma tafi Bada kanta Don Ita Zatayi ta yada Habaici Tana Zagin Mama Sahura Mutane
suyi ta yabon Mama Sahura Domin bata Biyemata sai dai ma tadinga Fadin"Yaya kiyi
Hakuri.."Kowa kuma Awajen sai ya bama Umma Rashin Hakuri Saboda ita Haryanzu batayi
karatun Duniya ba.

****

Tunda Kasim ya koma Kaduna ya Cigaba Daga Inda ya Tsaya yan Wajen Aikinsu suna ta
mai Jaje,Sani kuwa koda Suka Hadu shi yama kasim din Sallama ammh yaki
amsashi,Tunda ga Lokacin Shima ya Fita batunshi,Domin kowa ya ganshi yasan bashi da
Natsuwarsa Duk ya susuce ya lalace bawani gayu sai Tarin kasumba Wajen aikin ma Bai
Cika maida Hankali ba,Kwana Biyu da Dawowarsa Haruna ya Biyo masa Suka Tafi Chan
Wani Kauye Cikin Niger Delta Wajen Wani Boka Wanda kwana Sukayi Suna Tafiya kafin
Su iya Sumai bayanin Abunda ke Tafe dasu Shi kuma yace Su koma su Sati daya
tak..Komai zai kamallah basu bashi komai ba Domin ka"idan Aikinshi sai ya kamallah
Ake biyanshi Haka Suka Juyo Cike da Farinciki basu damu da Wahalan Tafiya ba Haka
Suka Sake kwana Suna Tafiya kafin su Dawo Hankalinsu kwance Suna Jiran Sakamakon
Aikinsu.

*****

*Abuja*

Tuni ya gama Duka Shirinsa Na Tafiya kano agobe,Bai Sanar da Ya Muktar da Daada ba
sai Daren Washegarin da Zai Tafi kana ya Shiga Shashen Daada inda ya Tarar da Anty
Rahila da ya muktar nan yake Sanar dasu gobe zai Tafi kano,Su Hibba Suna Wajen
Aneesa Sune Dama abokan Hiranta.

Cikin Murna Daada keta saka albarka Kafin tace"Daga kai Har Aneesa zaku barma na
kewa ko,Zaku tafi lokaci Daya..".

Tamke Fuska Bello yayi kafin yace"A"a Bada ita Zani ba Daada Ita tana nan..."Wani
kallo ya Muktar ya Jefeshi Dashi kafin yace"Bangane anan Zaka barta ba kabarma wa
kenan..? Yafada Fuskarsa ba alaman Wasa ganin Haka sai Anty Rahila ta mike tace
bari tazo Ta fice ta basu Waje.
Tattaren naman Saman Goshinsa yayi Waje Daya kafin yace"Me zataje tayi achan bafa
zama zanje yi ba,Shima kamar wanchan ne Koyarwa Ne.."Harara ya Muktar ya Makamai
kafin yace"Ok wannam Dalilin ne,zaisa ka Tafi kai kadai ka barta karfa ka kamanta
Yanzu ba Da bane Kai Mijin Aure ne Aneesa kuma matarkace kuma Tana da Hakki
akanka,Dole ka Tafi da Ita domin Babu amfanin kabar Matarka anan kuma kai ka
Tsallake katafi Wani gari..".

Shuru Bello yayi kansa na Kasa Ji yake kamar yayi Bindiga Saboda Fushi Hura Hanci
kadai yakeyi Zuciyarsa na Tafasa banda Tauye Hakki da Son Atakuramai ya Tafi da
Aneesa tamai Uban mene..? Bai gama Tunani ba Daada tace"Ai mganar banza ma
yakeyi...Dole ya Tafi da Ita in ta Zauna anan mezata mana,Kai Bello ka Tafi da
matarka kajima na gaya maka.."Tafada kai Tsaye Haushi ya kamashi ya Dago yana
Fadin"Daada bai zai yuyu ba...Nifa ba Wani Abu Takemin ba Da Zuwanta da Rashinta
Duk Dayane plz karku mtsamin Na Tafi da ita zaku karamin Nauyi da Takura.."

Dakuwa Daada ta Makamai kafin Tace"Kaga Naka nan Bello mu kake Fadama Da Rashin
Zuwanta da Zuwanta Duk Dayane Awajenta..? Bama son Mganar Banza Tafiya dai dole ka
Tafi da ita kamaji na gayamaka bana son na karajin Wata mgana.."Rage girman
Idanuwansa Yayi yana kankance su cike da Fushi a Harzuke ya mike zai yi mgana Ya
Muktar ya Dakatar dashi da Hannu Lokaci Daya Shima ya Mike yana Fadin"Da Matarka
zaka Tafi mallam...Dis is our Final Desicion..."Daga Haka ya Fice Daga Falon Daada.

Numfashi Bello ya Sauke yana Shafa Suman kanshi kamar ya Fashe da kuka Daada dake
mai Mgana yamata Banza shima ya Fice Daga Falo cikin Fushi da kallo Ta bisa tana
Tabe baki,Haraban Gidan ya koma ya Zauna Bisa mota yana Shafa Sumar Fuskarsa Yana
Tunanin yadda Rayuwarsa Zata kare akano Shida Aneesa,Wacce Tun bayan Aurensu banda
Sau Daya da suka taba mgana bai kara ko kallon inda take ba,kullun afalo Take
kwana babu Ruwanshi da Ita,Sau daya itama Tataba Gaisheshi bai amsa ba,Daganan
bata kara ba,Mganar Shiga Bedroom dinsa kuwa Sai da Daada ta mai Zazaga Domin
kullun Aneesa nan take Zuwa Tayi Wanka kaya ma Tabar mai Sabbin Ta koma saka
Tsoffin ta na gida Tun da baya barinta Shiga Dakin Dalilin Mganar da Daada Tayimai
ne ya Daina Rufe Bedroom din nasa,Da Asuba in ya Fita Sallah Ta lallaba ta Shiga
tayi Wanka ta Chanza kaya,ta Fito ta koma Falo kamar Wata Munafuka,Ranar Data Fara
Shiga Saboda Shegen Gulman Aneesan Har ya Dawo Masallaci batagama Abunda Zatayi ba
inda bata leka ba Saboda Gulma,yana Shigowa ya ganta gaban Dressing Mirror dinshi
tana Fadi Cikin Ranta Ji kayan kwalliya kamar Wata macen,batama san ya Shigo ba,shi
kuma yana ganin ta Daure da Towel ya koma Da baya yana Tsaki Falo ya koma ya Zauna
yana latsa waya sai da Aneesa Tagama Kallen kallenta kana Ta Shirya ta Fito sai
taci karo Dashi Dauke kai Tayi tana Tura baki cikin Ranta tana Fadin"Andai Cuceni
Wlh...Saboda mugun Hali Tiolet ma in mutun zai Shiga sai yana Sata.."Yana kallonta
ta gefen Ido bai tankamata ba Saboda sanin Bata ma kansa Rai kawai zaiyi,Kwata
kwata Yanayin Rayuwarsu bai zo Daya ba gashi An Riga An Daureshi da Jijiyoyin
Jikinsa,Ya muktar,Daada,uwa uba kuma Anty Rahila yana ganin Girmanta ga su Ya Ali
Wanda bazai iya Cin Zarafin Aneesa ba ya gama duk iya hangensa bai gano ma kansa
mafita ba

Haka Ranar Cikin Dare Cikin Aneesa ya baci taji Zawo Ta rasa ya Zatayi ganin Wankin
Hula Zai kaita ga Dare yasa Ta isa bakin Kofar Bedroom din Bello tana Bugamai Cikin
Barci yaji Muryanta Harda kuka Take Hadawa Wajen Rokansa ya Bude Domin Har tafara
Zawon Awando,Saurin Saukowa Yayi Daga kan gado ya Bude Duk atunaninshi Wani abu ne
ya sameta ko gama Bude kofar bedroom din baiyi ba ta Tureshi da Karfi ta Shige Ciki
Cike da mamaki ya juya yana kallonta ta Fada Tiolet Aguje Saboda Sauri ko Rufe
Kofar tiolet din batayi ba yana Tsaye yake Jin karan Zawon nata irin mai Fata Fata
din nan ne,Yamutsa Fuska yayi Lokaci Daya yana Toshe hanci Saboda Warin Dayake
Fitowa Daga Tiolet din Zuwa Cikin Dakin,ganin zai halaka da Wari ne yasa ya Fice
Daga Dakin haryana ja mata kofa Bakinciki kamar ya kasheshi karshenta dai Ranar kan
kujeran da Aneesa ke kwana ya karishe Daren Farkawa kawai yayi da Asuba ya ganshi
kwance ya Dunkule Cikin Hijabin Sallarta Cikin Takaichi ya mike saboda kyamkyamiv
ko Bedroom din Bai Leka ba ya Fice a masallaci yayi alwala Abunda bai tabayi ba
Sallar Asuba batare Da yayi Wanka ba.

Ita ko Aneesa bata Dawo Hayyacinta ba sai da tagama barin Wuta,tayi floshing kana
ta Tube kaya tayi Wanka Tana ajiyar Zuciya afili ko Fadi take kai kashi Rahma ne
babu Abunda yafi kahi Daraja Wlh..,bata Fito ba sai da Ta Fesa Airfresher jin Bayin
ya Chanza ganin bata ganshi adakin ba yasa ta kyakyale da Dariya tana Tuna Sanda ta
Tureshi ta Shige Bayi,Kaya ta Sauya kafin ta Leko Falon ta ganshi Zaune kan kujera
yana Hamma,Baya ta koma Harda sakama Kofar key Tana Dariyan Mugunta,cikin Ranta
tana Fadin"Mugu yau kaima ka Dandana kwanan Falo,Ta ko Haye gado Harda Shigewa
Cikin Bargonsa Tana Shakam kashim Turaransa Tana lumshe ido Cikin Lokaci kankani
barci ya kwasheta bata Farka ba sai da Taji Yana Dukan Kofar tashi Tayi Tana mika
Lokaci Daya take Fadin"Waye ne...?

"Tafada tana Kunshe Dariyanta Ransa bace yace"U better open d door Bf4 i loss my
Temper..",Yafada Cikin Sanyi ammh Cike da Fada,Dariyarta ta saki yana jinta Tadaka
tsalle akan gadon tana Dariya Sai da ta saka hijabi kana Ta Bude Kofar,ta Rabe a
bayan Kofa,Shiga dakin yayi yana Hararanta Lokaci Daya yana Kara Toshe bakinshi
Cikin Tsawa yace"Ke wata irin kazama ce zaki gama Amfani da Tiolet baki Wanke ba..?
Yafada yana kara Rufe Hanci Abun ma Dariya ya bata ta kama baki tana Fadin"Ikon
Allah kashin nan fa kowa nayi.."Hannu ya saka ya make mata baki yana Fadin"Sa'an
wasanki ne ni...? Yafada yana Nuna ta da Tsaya baki ta Tura tana Sosa lebenta har
ya Tashi,Hanyar Tiolet ya Nuna mata yana Fadin"Wuce maza ki Shiga ki wanke min
Tiolet Tas,Zan Shiga nayi wanka kuma In kin isa karki Wanke Dakyau kiga yadda zan
Dake.."Yafada yana Direct dinta da Hannu Wucewa Tayi Tana Kunkuni Tsawa ya Dakamata
yana Fadin"Wai ina wasa Dake ne...?kinsan Allah zan Zaneki fa.."Yafada Lokaci yana
yunkurowa ai da gudu ta Fada Tiolet din tana Hawaye Cikin Ranta tana Fadin mugu
kawai,Haka ta Cire Hijabi ta Zage Ta wanke bayinan tas,ya koma yana kamshi kana ta
Fito tana Haki Duk ta Jika kayanta Da Harara yabita kafin yace"Now get Out..Next
time in kinji kazanta go to Anoder room don"t came back Here again...".

Tabe baki tayi ta Dauki Kayanta Dake saman Akwati Wanda ta Fito Dashi ta Fice Zuwa
Shashen Daada Cikin Ranta kuma Dariyan Bello Take in ta Tuna yadda yake Toshe hanci
afili tace"Ji yadda yakeyi sai kace shima baya kashin Waya sani ma ko Shima Zawon
yake kamar nawa.."Tafada Tana Dariya Haka Dataje Shashen Daada tana mata Fada ammh
Tana Dariya ta bata lbrin Abunda ya Faru Hartana kwatanta Yadda Bello ke rufe Hanci
Ita kanda Daadan Sai da ta Dara Tana Girgiza kai Cikin Ranta tana Addu"ar Allah ya
Shiryi Aneesa.

wai kuma duk wadanan Abubuwa kuma ace Dole sai ya Tafi da ita yana nan Zaune sai
gashi Ta Fito Sanye da Hijabi Tana Dauke da junoir Hannunta kuma na Rike da Hibba
Suka sauko Zuwa Shashen su ya muktar yana kallonsu har Suka Shige baisani ba ko ta
ganshi itako batama lura dashi ba tana Shiga ta Hadu da alheri sai ta mika mata su
ta juya ta koma Ta Fara Taka steps kenan taji taku mutum Abayanta ko Waigowa batayi
ba Tadaga Hijabi da kafa ta Rumtuma da Gudu ta Shige Dakin Tana Dafe Kirji Tsaki
yaja a Cikin Ranshi yana jin Takaichi kamar me,ko zama bata samu yi ba ya Shigo
Falon bai kalleta ba illah Wucewa Dayayi gaban Tibi ya Dauki Remot ya Rage karan
Cartoon din da ta kunna ma su Hibba,Takowa yayi Zuwa Tsakiyr Falon Lokaci Daya kuma
ya juya Zuwa Bedroom dinshi.

Karamin Tsaki Aneesa ta Sauke kafin Ta kwanta Harda Juyamai baya bai damu ba Tunda
ya Sake Juyowa ya kalleta ya Dauke kai yana Fadin"Ke ki shirya gobe da Safe zamu
tafi kano.."Yi tayi kamar bataji ba Ackin Ranta tace"Kaga ke mallam."Ganin Yadda
Tamai ne yasa ya Hadiyeshi Fushinsa yana Fadin"Ke wai badake nake mgana ba..ke
Aneesa.."Sai Lokaci ta juyo tana Wani Tura Kirji Sauri kauda kai yayi yana Kara
girman idanuwanshi yana Fadin"Kina jin Abunda nace..?..

Baki ta Motsa kafin tace"Hum..Me kace..? Wani Haushi ne ya kamashi Cikin Fushi ya
Nufota yana Fadin"Ok bakiji ba ko..?bari nazo na Kara gayamiki ."jin Haka kuma
ganinshi ya Nufota yasa ta Zabura ta Mike tana Fadin"A"ah Wlh naji naji..Ba cewa
kayi gobe na Shirya zamu kano ba..? Tafada Tana Takurewa Jikin Kujera Fuska ya hade
kafin yace"Gud...karki batamin Lokaci in ba Haka sai dai ki sameni achan..."yafada
yana Shigewa Cikin Bedroom Dinsa da harara Ta bishi kafin tace"Baza"a je din
ba.."Sai kuma tayi Sauri Ta Damke bakinta tana kallon Bedroom Dinsa da kallo Sanin
yadda Kunnansa yake kamar na Maciji saboda ji.

****
Washegari Tun karfe 7:30am Bello ya gama Duka Shirya Shiryansa Abun da yabama
Aneesa mamaki ganin Uban kayan da zai Tafi Dashi Jakunkuna Uku,mallam.Inuwa yazo
Har Falon ya Dauka ya Saukan mai Dashi Zuwa Cikin Motarsa,kirar 4matic baka,kuma
komai na amfaninshi ya Diba,ita azaton zasu gidan Anty Aisha ne,sai da ya barmata
bedroom din tayi Wanka Ta Shirya Cikin Riga da Zani na Wani leshi mai kyau kalan
milk da ja,ta sanya Jan mayafi da jan Takalmi kuma Duk Cikin kayan Auren da Kasim
ya bata ne,Sai da ta Shiga Sashen Su Daada gaishesu ne Taji Daada na Zolayanta zasu
barsu da kewa,Sai lokacin ta gane Tafiyan ba na Dawowa bane,Nan da nan Hankalinta
ya Tashi Cikin Son tayi kuka tace"Daada chan zamu koma da Zama..?kai Daada ta
Dagamata kafin tace"Chan mijinki ya samu aiki.."Bata rai Aneesa tayi Daganan kuma
sai kuka Daada na lallashinta Anty Rahila dai bata mata mgana ba ganin iskancin na
Aneesa nada yawa sai da Suka zo Tafiya ta gane kukan sabo ne itama sai da ta Share
kwallah hibba ko da Junoir Haka Suke kuka Aneesa nayi Shikanshi ya Muktar ya sani
Yasani zasu ji kewan Aneesa Hatta su Mallam Inuwa Sunji ba Dadi da Tafiyar
Aneesa,Alheri da Jummai suma Harda kwallansu Aneesa dai Haka Suka Fice Daga Haraban
Gidan Tana gaban Mota Tana Kukan Rabuwa dasu Daada,gashi Bello ya hanata Daukan
kayanta Duka Akwatuna uku Ta Dauka yace takoma ta mayar dasu ta Dauko Daya Hala
chan zata tare,waye zai Dinga mata Jigilan Zuwa da kaya yana maidamata,tana kuka
tana komai haka ta maida akwati biyu Acikin yar Babban ta saka Duk Abun
Amfaninta,bawai don zasu Isheta ba,sai don muguntar Bello Cikin Ranta ko Allah ya
isa takemai domin ai Shi ya Diba kayansa Duka sai itane zai Hanata batasan ko
Kwatan kayansa bai Diba ba,Wardrope dinsa maa baisan an Dibi kaya ba Saboda Tsabar
yawansu.

Ki biya ki karanta cikin salama

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?20*

Sun Fara nisa kukan Aneesa,yafara isar sa Dole ya gangara gefen titi ya faka motar
Cikin Tsawa yafara mgana"ke kukan me kike ma Mutane...? Ko dai salon iskanci kine
ya tashi..?ko kuma salon mutane suganki kina kuka Suyi Tunanin Sato ki Nayi..?

Ko kallonsa Aneesa batayi ba,illah Cusa kanta Datayi Cikin Cinyoyinta tana Cigaba
da Shesshekan kuka Tsaki yaja kafin yatada Motar yana Fadin"U better keep u mouth
Shout in ba Haka ba wlh kinfi kowa sanina Sai na Watsaki Cikin Dajin nan na barki
na kama gabana.."Jin Haka yasa Aneesa Tayi Dif sai dai na Zuciya sanin Halin Bello
Tsaf zai Iya aikata Abunda yace don ba Mutumci ya cika ba...

Wajen 10am na Safe suka isa Gidan nasu dake Buk road,Megadin gidan Wani Bafullatani
ne,mai kirki sai faman musu barka da Zuwa yake yi,Fitowa Aneesa Tayi Daga motar
Tana karema Haraban gidan kallo Bello ko takanta bai bi ba ya Bude Booth ya kwashi
jakunkunarsa ya bude Kofar Falon gidan ya Shige ya barta,don mugunta yasan fa
bazata iya Daukan Akwatinta ba Ganin Tana jansa ne yasa Salihu maigadi wanda ya
Fadamata Sunanshi bayan sun gaisa ya Dauka ya kai mata Falon Farko.

Aneesa Tsayawa tayi afalon Tana ta uban kalle kalle,Falon Farko Shi keda 1 bedroom
da Kichen Guda Daya Shima duka ko"ina yaji kayan alfarma na Morewan Rayuwa,Wani
korido tabi tana jan Akwatinsa sai gata ta bayyana awani katon Falo mai kyau da
Tsari Wanda yaji Ubansu Rolay Chairs,Daga ganin Falon Zaka san Ankashe kudi,Kuma
yafi na Farkon Girma,shi yana da wajen Dinning da Kichen mai girma sai Kofofin 2
bedroom Kusa da Juna,Tana Tsaye tana Faman Wurga ido Bello ya Fito Daga Daya
Bedroom din yana Waya ya Fice ko kallonta baiyi ba,ganin haka yasa taja kafa Zuwa
Dayan Bedroom din Shima ya Hadu karshe makeken Royal bed da Madubinsa,sai Wardrope
babba da Tiolet,bata zauna ba ganin kura Adakin sai Ta Hau gyara wajen itace Har
Falon da Kichen sai da ta Share tayi mooping Dayake ta samu Abun Shara agidan,Sake
komawa Tayi Falon Farko ta gyarashi Shima Da Bedroom din Acikin Ranta tana Tunanin
kila anyi Wajen don Baki ne.

Sai Wajen Azahar ta gama Tagaji Tubus Wanka ta Fada Tare da Dauro Alwala,cikinta
Kugin Yunwa yake yi Domin bata karyaba rabonta da Abinci Tun Jiya Da Daddre,gashi
kuma Tunda Bello ya fice bata karajin Motsinshi ba ta fito Falo ta leka ta taga ba
taga Motarsa ba, kenan yayi Nisa ya manta da ita,gabas ta Saisaita ta Tada sallah
ko kayanta Data so ta jera cikin Wardrope kasawa Tayi Saboda ta gaji Tana sanye da
Wata Bakar Doguwar Riga tabi lafiyan gado Duk da yunwa dake damunta haka barci ya
Kwasheta..

Bata Farka ba sai bayan La"asar ta Tatashi ta Dauro alwala tayi sallar
la"asar,Yunwa yafara illatata Domin Jiri take gani in ta mike,kichen ta Shiga tana
Bude bude ammh babu komai na girki sai kayan Tukwane dasu gas,har Fridge ta bude
bakomai,fridge din ma Daga gani Babu Abunda Aka Taba sakamai Falo ta Dawo Tana
Rangaji ta Zube bisa kujera tana maida Numfashi harda kwallanta,Shuru Shuru ba
Bello sai Bayan sallar mangariba kana ya Shigo gidan Hannunsa da Lodoji guda Hudu
manya,Lokacin Tana kwance nan kan kujera Saboda yunwa ma ta kasa Tashi tayi sallar
Mangariba.

Yana Shigowa kallo Daya yayi mata ya kauda kai Cikin kichen din ya Shiga ya
ijiyemata Duka Ledojin kana ya Fito Hannunsa Rike da goran Ruwa yana Fadin"Ga
Abinci chan a kichen da Wasu kayan Cefenan,ban samu Lokacin Shiga kasuwa ba gobe in
na Fita za"a saka komai Cikin Store.."Jin yace ga abinci can yasa wani karfi yazoma
Aneesa ta mike da Hanzari Tana ganin Jiri kamar zata Fadi sai da Ta Rike bango da
kallo ya Bita kafin yace"zaki dinga dafa Duk Kalan Abinci da kike so buh ke kadai
Karki sake kice zaki yi girki dani don ni ba sa"anki bane,Su Daada ne suka matsa na
Nataho dake amnh ni zuwanki da Rashinsa Duk Daya ne, so zaki iya Dafa abinci ki ke
kadai sai ko megadi in zaki samai and kuma ki Duba komai kiyi list dim Abunda Babu
ki bani gobe in na Fita zan Shiga kasuwa na Siya miki komai ga bedroom dinki nan
Nima i hv my Own so karki Shiga Harkata nima bazan Shiga Taki ba Kowa yayi
Rayuwarsa Am i Clear.."Yafada yana Kurban Ruwan Daga Tsaye ko jinsa batayi Sosai ta
gyada kai Tsawa ya Dakamata kafin yace"Bakin ki na Ciwo ne.? Da zaki amsamin da
kai.."Jikinta na Rawa saboda yunwa tace"Naji insha Allahu Zan kiyaye..."Juyawa yayi
yana Fadin"Gud.."Daga Haka ya Shige Bedroom dinsa ya Rufo.

Dakyar ta iya karisawa Kichen din Tana laluben Hanya Saboda Yunwa ledar Farko ta
Raruma nan Taga Take away din Shinkafa da Miya da Salat,sai Kaza Gashasshiya da
Yoghourt,sai ruwan Faro mai Sanyi ai Aneesa bata tsaya wasa ba ta Zauna Dirshan
Atsakiyar kichen din ta Tura Abinci gabanta ta Faraci ko Takan Cokalin Dake Ciki
batayi ba Tana ci tana Hadawa da yoghourt,Sai da ta Shareshi Duka ta kuma Shanye
duka yoghourt din ta jawo Ledan kazan itama taci Rabi ta Hada da Ruwa kana Tayi
gatsa tana Shafa Cikinta kafin tace"Kai yau naji ta Babuwa..",Gaskiyan almajiri ne
Dayace Yunwa bata da Hankali.."Take Fada Tana Dariya,sai da ta gama Hutawa kana Ta
iya mikewa Dakyar Fridge ta bude ta saka Sauran kazan Tana Fadin'Na gobe don ba
lalle bane ya Tuna Dani da Wuri.."Sauran Ledojin ta bude,kifi,Nama,kayan miya,green
beans,Karas,Cabeji da Cray Fish,sai kwalin indomie guda Biyu,sai katan din Ruwa
guda Daya Tana ga dai ya Siyo ne kafin gobe,Duka kayan Ta saka Cikin Fridge din shi
kuma indomie ta barshi nan domin Store din yana Kulle ne sai Lokacin Ta iya Fitowa
Falo tana Tura Ciki Hakikanin gaskiya Tayu Mugun Ci Daki ta koma ta Fada Tiolet
wanka Tayi kana Ta Dauro alwala ta Fito tayi sallar Mangariba ta Hada da Isha"i
Shafa"i da Wuturi tayi kana Ta Bude Akwainta ta Zaro Doguwar Rigar barcinta ta
saka,sai dai ta Hau gado zata kwanta kana ta Tuna da,Abunda Bello yace ta Rubuta
mikewa Tayi ta Bude Zip din Jakarta Inda ta Sako Littafanta Da Biro sai Qur"anin da
Falmata ta Bata da azkar ta Yago Fallon Takarda Tayi Zaman Dirshan Akan gado ta
Fara Rattaba Rubutu Wani Abun ma Harda mugunta su Semovita ne,wai harda aya da
Dabino ta saka,wai na yin Kunun aya,hartagama Sai ta tuna da Abun Zobe Haka ta sake
Rubutawa sai da ta Cika Takarda kamar Hauka,wani Abun ma Saboda Mugunta ta saka ba
domin Tana ci ba,bata kwanta ba sai Wajen goma kana ta Nannade Cikin bargo sai
barci.

*****

Karfe 7:3am na Safe ya Fito Daga Dakinsa Cikin Shirin Fita,Sanye Yake Cikin Wasu
Ubansu American Suit,Ash And black,Ya matse Wuyansa da Tie baki kafarsa Sanye Cikin
bakin Takalmi Rufaffe Na Fatar Damisa Haka Tsitsiyan Hannunsa Sanye da Agogo Baki
na Fatar na kamafanin Rado,kallo Farko zakamai ka Fahimci Kwarjinsa Tare Dashi Wata
karamar Jakar Briefcase ne Ahanunsa sai Wayarsa Dayake latsawa da Hannu Daya babban
yatsansa na Sagale da key din motarsa.

karfe 8:00am yake da lecture din Yan level 1,Baya so yayi African Time Domin baya
Cikin Tsarinsa,tun jiya bayan isowarsu Fitan dayayi Cikin makaranta ya Shiga ya
karisa Abunda bai gama ba,bai Fito har sai da komai ya kamallah Har Office dinsa an
basa mai girma da Tsari Saboda Samun Sa Very Young Teacher ga Talend da
Brilliant,Kasashen Wajema Nemansa Suke ammh yaki yafison Aiki a Kasar Haihuwarsa.

Lokacin Aneesa na Kwance bata tashi ba Tun bayan Sallar Asuba,gashi bayason ya
makara ita kuma ta bata masa Lokaci Kofar Besdroom din nata ya isa yana kwankwasa
bayan ya lallashi Zuciyarsa Aneesa Cikin barci Taji Ana Kwankwasa Kofar Bedroom din
data ke ciki ta tashi da Sauri sanin kowaye Hamma ta saki Lokaci Daya tana mika ta
Bude Kofar Suka ci karo da Fuskokin Juna,Harara ya Zabgama Lokaci Daya yana Dauke
kai saboda Rigar barcin Dake Jikinta mai kwashashiyar Wuya ne,gabadaya saman
Nonuwanta abude Suke ita ko Lura batayi ba bai mata mgana illah hannu Daya mika
mata,tana Hamma tajuya ta koma cikin Dakin Saman Side drower din gadon inda ta jera
harda Qur"anin Datazo Dashi,ta Dauko ta kawomai bai Tsaya kallonta ba ko Duba
Takardan ba ya juya yana Wani Fitar da kamshi ya Fice Daga Falon,Da kallo ta bishi
tana Tabe baki kafin tace"Mutum Har mutum...Ammh ba kyan Hali.."Tafada kafin ta
maida kofa ta Rufe ta koma ta kwanta tana Fadin Shegiyar katifan nan Dadin Kwanciya
gareta kara Shigewa blanket Tayi tana lumshe ido Ita Adole Wata Hegiya.

Da salihu maigadi Suka gaisa kafin ya Shiga motarsa ya Fice Daga gidan,sai da ya
Fara Tafiya kan Titi kana ya Duba Takardan,Zaro ido yayi yana mamakin inda Aneesa
tasan Wasu Abun Akwai Abubuwan da bai gane ba,harda cimansu na Kanuri,dariyan
Takaichi yayi kafin yace Afili.."Wannan yarinyar fa bata da Hankali duk ina Zata
kai wamnan kayan? Yaushe ma ta iya girkin..'Tabe baki yayi kafin ya maida Takardan
Bisa Karamar Jakarsa Lokaci daya yana maida Hankalinsa kan Tuki.
Aneesa bata tashi ba sai Wajen 9 ta Fito bayan tayi Wanka ta sanya Wani Riga da
Zani na Atmafa Indomie ta Dafa musu ta Hada Da Sauran kazan Jiya da kanta Tasaka
Mayafi ta fita ta kaima Salihu mai gadi nashi ya karba yana ta Godiya Aneesa na
Dariyan Hausanshi Sun Dade Suna Hira Hartana Fadamai zata Dinga Zuwa yana Koyamata
Fillanci Dariya kawai yayi yace mata sai tazo Haka yaci ya koshi yana Ta sakama
Bello da Aneesa albarka

Itama bayan ta koma taci nata ta wanke Abunda ta bata ta Adana kana ta Dawo Falo ta
Jona kallo Wanda Dakyar ta iya Kunna faskeken Tibin mai kama da Magijin Cinema,Haka
ta Wuni Cikin Gida tana kallo sai Sallah ke Tada ita tun bayan Indomie safe bata
kara Dafa komai ba sai Dare Har takaima maigadi nashi ta karbo Kulan Dazu da Safe
ta Shigo ta kai kichen ta Dauko nata ta Fito Falo sai ga Bello ya Shigo da kwalaye
a Hannayensa Bayanshi kuma salihu Magadi ne Dauke da Kaya Suka Shiga Kichen,ganin
Sun Fito ga Salihu maigadi Awajen yasa tace"Sannu da Zuwa."

Dakyar ya amsa yana Wani Cije baki aranta tace lalle ne ma kama samu ne na gaisheka
ne,,Daganan Salihu maigadi sai Shigo da kwalayan Abu yake da buhunhuna da Ledoji
Wajen Sahu Uku Kana yagama,Bai mata mgana ba Itama bata kara bi ta kamshi ba ya Dai
Shiga kichen Bai Dade ba ya Fito Da Apple Ahanunsa da Madaran Hollandian ya Shige
Bedroom dinsa kana tayi Wuf tatashi ta Fada Kichen din Nan Taga Store Abude Shake
da kaya Abunda ya bata mamaki Duk Abunda ta Rubuta sai da aka Siyosu,Dama already
kichen din Fridge guda biyu ne,harda Freezer sai ta jera Duka Abun Amfani Wanda
bazai yi Saurin lalacewa ba kamar su Kwai da Sauransu,aya da Dabinon ma Aciki ta
saka Dayan kuma ta jera Ruwa da Madaran Hollandian sai Maltina da kayan Fruit wands
ita basu dameta ba tasan kayan Bello ne,Su maggi kuma ta Zuzzuba su Cikin Wasu
kananam Robobi data gani a Drower din Kichen din,komai dai ta sakashi Amullalinshi
Tayi murna Data ga Harda Fulawan Datace ya Siyomata,abinci su na Kanuri ne Dai bata
ga ko Daya ba Acikin Ranta tace"Ahakan ma Ni keda Godiya Mr Bello.

*****
Sati Daya kenan Da zuwansu kano Tunda ga Ranar Daya Siyo mata kayan Abinci Wata
Mgana bata kara Hadasu ba,sai ma ta kwana bata sakashi a idoba sanda Zata Fito daga
Daki har ya Fita Wani Lokacin kuma Tana Daki tana sallar Isha"i zai Shigo Babu
Ruwanta Dashi baya Neman ta itama baya gabanta,Iyakarta tatashi da Safe ta musu
Abun karyawa ita da Megadi ta fita takai mai nashi itama taci nata,Tana Share Duka
Dakunan Dakinshi ne bata taba Shiga ba Wani lokacin ma Tafi zama Afalon Farko,
girki ko bata iya ba sai ta kwabashi Hakanan Don ma Wasu girken girken zamani
Wajensu su alheri ta koya wasu koma amkranta Kafin Sati Dayan Aneesa ta sake cika
tayi kiba Tunda tana cin Abinci mai kyau ta kwanta Waje mai kyau bata da Damuwar
komai sai kewar su Daada gashi bata da Waya Ahannunta abokin Hiranta Shine Tibi Ta
Wuni tana kallo bata gajiya.

Shiko Bello kafin ya Rufe Sati Amakarantan BUK sunansa ya Zaga ko"ina barinma
Department Dinsa na Mathematics,Yan mata Dadama Kamar su sume saboda ganinsa,Gashi
ya iya koyarwa duk Dakikanci ka in har ya koyar dakai sai ka gane,fa iya Sarrafa
Harshe Wajen Turanci kace wani mangafok ne,Ga iya Dressing ga Aji da Zati komai dai
ya Hada,cikin Lokaci sunansa ya Zagaya cikin Jami"ar ta bayero Kowa sai labrin
Sabon malamin Dapartment din Lissafi yake The young Teacher Mr bello muhmeed
Jikamshi,Tunda ya Fara daukansu karatu bai yarda Mu"amala ta Shiga Tsakaninsa da
Kowa ba ko Acikin Hall din karatu Fuskarsa ba"a sake take ba,abunda ya kawosa kadai
yake yi ya Fita ya basu Waje,Tundaga Yan level 1 har Zuwa High clss din yana Dauka
kafin Ya Rufe Satin Wasiku sunfi goma Cikin Office dinshi na masu son Kulla
Soyyayyah dashi Baya Damuwa Domin Tunyana Makaratan kwatar kwashi yasaba da Irinsu.

*****

Washegari Ta kama Jummatu Babban Rana ne,kuma garin Antashi da Ruwan safe ne
sakamakon lokacin Damina ne,Aneesa tana jin anfara Ruwa ta Sake Shigewa cikin bargo
barcin na kara mata Dadi ba Ita tatashi ba Sai After 10 lokacin Ruwan yadan
Tsagaita,wanka tayi ta Shirya Cikin Doguwar Rigar Material mai kalan ja da Baki ta
Nade Dankwalin kayan Bisa kanta yayi Tuntu saboda Gashinta Data Tsife ta Daure da
Band, ..

Kichen ta nufa tana Duba Abunda Zasu karya dashi,Dankali ta Fere ta soya musu da
kwai sai Tea da Soyayan Biredi da kwai,sai da tafara mikama Megadi nashi kana ta
Dawo Falo taci nata Hankali kwance duk Zatonta Bello ya Fita baya gida,Wuni Tayi
Afalo tana kalle kalle sai Wajen la"asar kana ta koma Daki tayi sallar la"asar ta
sake Fitowa Abunda yabata mamaki Shine Data Fita Falon Farko Ta Bude windown Falo
Iska ya Shigo Domin Nefa sun Dauke Wuta kuma Falon Farko yafi Iska Motar Bello Ta
Hanga Aharaban Gidan Sai da Taji gabanta ya Fadi Haka Kurum Taji Jikinta bai
bataba, Dama bello na nan ne ko kuwa dama yanzu ya Shigo,Ganin bata dame bata amsa
yasa ta koma ta kwanta Bisa kujera tana Tunanin Zucci.

Karfe Biyar na yammah ta Tashi ta Sake Labulen Windon nan Falon ta koma
Falonsu,kichen ta koma ta Dafa musu Taliya da Miyar Kifi,ta Zubama Megadi bata
kaimai ba sai da ta koma Daki ta yi wanka Tayi sallah kana Ta Fito ta saka Mayafi
ta kaimai Bayan ya karba ne yana Godiya har Zata tafi taji yace"Hajiya wai ni ko
Alhaji Lafiyanshi kuwa yau kwata kwata bai Fito ba..?

Gaban Aneesa ya Fadi ta Waiwayo Tana kallon Salihu megadi Karo na Biyu gabanta ya
kara Fadi Dakyar tayi Dariyan yake batasan Sanda bakinta ya Furta"Bayajin dadi ne
ammh yaji Sauki,"Cikin Jimami Salihu maigadi ke Fadin"Ayyah..Haba koda na gani yau
kwata kwata bai Fito ba Allah ya kara Afuwa.."

Bata samu Zarafin amsamai ba ta Wuce Zuwa Cikin Gida gabanta Haka Kurum ke
Bugawa,Koda ta koma Falo tatasa Abincin gabanta Haka kurum Jikinta ke bata ba
lafiya Wata Zuciya tace"Karki damu kanki kinsanshi da Shigen zaman daki kamar
mace.."Fara cin Abincinta tayi ammh kuma Wata Zuciyarta na Cike da Fargaba bata
wani ci sosai ba ta mike ta kai Kichen ta Rufe ta wanko Hannu ta Fito Har zata Wuce
daki sai taji kamar Zuciyarta najanta ta Shiga Dakin Bello batare Data sani ba
kawai ta Juya ta Tura Kofar bedroom din nashi sai kuma gashi ta Bude Cikin Karamar
sallama ta Tura kai Dakin Tana dan kalle kalle.

Gabanta ne ya Harba da karfin bala"i ganin Bello Kwance Akan gadonsa Yana kallon
Silin,Irin kwanciyan Dayayi ne ya bata Tsoro,tana Shigowa ya Wulgo idanuwansa yana
kallonta,Daga bakin kofar ta tsaya tana Kallonsa Cikin mamakin ganin Idanuwansa
Sunyi jajir,kwallah Duk ta Bushemai ta gefen Fuska Domin Dakin yana gauraye da
Haske.

Harda Zata Juya tatafi sai kuma ta Fasa tasake Waigowa tana Fadin"Ashe lafiyanka
kalau.."Tafada Tana kallonshi bai iya mata mgana ba sai dai Taga ya Lumshe ido
lokaci Daya Taga Wasu Hawaye sun Biyo gefen Kunnansa,Zaro ido Aneesa Tayi tana
Kallonsa Cikin mamaki da Faduwar gaba Cikin Sarkewa murya take Fadin"baka da lafiya
ne...? Tafada tana Kuramai ido Ammh sai taga ya kara Rufe idanuwan ya Bude Wasu
hawayen sun sake Zubowa su suka kara sata tagane ba lafiya domim ita bata taba
ganin kukan Bello ba Tunda take dashi.

Da Hanzari ta karisa kusa dashi ta Durkusa ta Dora Hannunta gefenshi Taji Wajen ya
Jike da Ruwa,idonta takai Wajen tana Dubawa lokaci Daya Ta Taba Kayan barcin Dake
Jikinsa Jike da Ruwa,harda Zarni na tashi Hannunta takai hancinta Lokaci Daya ta
Zaro ido "Fitsari kayi akwance..?"Tafada Lokaci Tana kallonsa,yana so yayi mgana
ammh bakinsa kamar an Daure yana so ya motsa hannunshi ya kasa,yana so ya
tashi,shima ya kasa ga mganar dayakeso ya Fada Tana Cikin Zuciyarsa ammh Ta gagara
Fita Daga Harshensa,kansa ne yake kokarin Dagowa sai ya koma ya langwabe gefe Miyan
bakinsa na Zuba Dalala lokaci daya Hawaye yana Fitowa Daga Cikin idanuwansa.

Aneesa Dake kallob yanayinsa,Kirjinta na Dukan Tara tara tace"ka kasa tashi ne..?
Kokarin Dagamata ido yake ammh ya kasa,Riko Hannunsa Tayi Idanuwanta Sun Cika da
kwallah tace"Kamin mgana mana Uncle Bello meya Faru dakai..? Bai iya mgana illah
hawaye kawai yana binta da ido Lokaci Daya bakinsa na Zubar da Miyau,Aneesa Taji
kuka ya kamata ta Fashe dashi Tana Fadin"Innalillahi Wa"inna ilaihirraju"un...Karda
ace kadaina Mgana,kadaina Tafiya na Shiga uku ni Aneesa.."Tafada Tana Kara sakin
kuka,Shima Hawayen yakeyi yana kallonta Lokaci Daya Hallitarsa ya Chanza ya Dawo
kamar Wani Gaula.

Gabanta ke Fadi Fat..Fat..Tana kallonsa tana Share kwallah Afili Tace"Allah


kenan...Garesa mukazo kuma garesa zamu koma.."Take Fada Wani Tsausauyin Bello na
Ratsata na ganin yadda ya koma Lokaci Daya Mr bello fa Shine a kwance Cikin Fitsari
bakinsa na Zubar da Miyau kilama Tun Kwanciyaar jiyane Abun ya Sameshi,Hada kai
tayi Ta gwiwa tana kuka Wurjajan Tana Tunanin Wajen Wa Zata kai kukanta Wajen wa
zata Neman Taimako.?

Wayarsa Dake kan Side Drower din gadon Ta Shiga Neman Dauki,Da Hanzari Aneesa
Tadago tana Hawaye ta Dauki Wayan,Bata gane Sunan mai Kira ba Domin Hankalinta Baya
jikinta Da Sauri Ta Daga Kiran Lokaci Daya Tana Fashewa da kuka...

Cikin Firgici da Taahin Hankali Muktar Dake gaban Daada d Anty Rahila yace"Aneesa
ta Dauka ki wayar kuma tana kuka.."Kuka Daada Ta Fashe dashi Lokaci Daya tana
Fadin"Haba ni naji ajikina Wlh Wani Abu ya Faru da Bello ko Aneesa.."

Cikin Tsoro da Tashin Hankali ya Muktar yace"Aneesa Ki daina kukan nan ki sanar
damu meyafaru Tun Wajen karfe 2pm na rana nake Kiran Lambar bello baya Dagawa
Gabadaya Hankalinmu ya Tashi meya Faru ne..? Cikin kuka Aneesa Ke Fadin"Bazaku
sameshi ba Ya Muktar..Yana jin kana Kira ammh bazai iya mika Hannu Ya Daga Kiranka
ba.."

Cikin Tsoro ya Muktar yace"Innalillahi meya Sameshi..? Yafada yana Jin Zufa na
ketomai Daada ko kuka take Anty Rahilama Tashiga Tashin Hankali Cikin Sharbe Hawaye
Aneesa dake kallon Bello Take Fadin"Ya Muktar Uncle Bello ba ya iya Tafiya ba iya
mgana baya iya motsa kowata gaba ta gangan Jikinsa Sai da ido kadai,ko Fitsarima
akwance yayi kuzo ku Taimakamana Don Allah..."Take Fada Tana Gunjin kuka Shima
Bellon Dake Jinta Hawaye yake Lokaci Daya miyau na kara Dala la Daga bakinsa

Gabadaya ya Muktar da Daada da Anty Rahila Suka Dau Salati Domin Wayar Tana Speaker
ne,zamewa Daada Tayi ta Zauna Tana Fadin"Innalillahi Wa"inna Ilaihirraja"un...Wani
irin lamari ne ya Faru da Bello...?

Ki biya ki karanta cikin salama.

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?21*

Dafe kai ya muktar yayi lokaci D'aya yana Fadin"Innalillahi Wa'inna


illaihirraju"un..."Anty Rahila ko kasa Tayi Ta Dafa Daada tana hawaye,Daada ko
kanta ta Dafe tana Sharban kuka tana Share Hawaye da Gefen zaninta.

Numfashi ya muktar ya saki kafin yace"Daada ku Shirya mu tafi Saboda Aneesa yarinya
ce bazata iya da Bello ba.."Da Sauri Daada ta mike tana Fadin"Toh...toh...Muntari
mu Hanzarta muje muga Halin da Bello ke ciki ."Bai kara mgana ba ya Fice Anty
Rahila ta mara mai baya basu Tsaya Daukan Komai ba Daada ta Dauko mayafi Haka Anty
Rahila tana goye da Junior ya Muktar na Dauke da Hibba Wayarsa kadai ya Dauka Suka
Fito mallam Inuwa ya Tukasu Sauran Tawagarsa kuma suka Rufa musu baya,kafin su Fita
Anty Rahila tama su Alheri magana tare da Sanar dasu su kula da gidan sai sun dawo
suma sun jajanta lamarin Jin Mr bello ba lafiya.

****

Aneesa ta Salubar da Wayar Daga Kunnanta tana kara Sautin Kukanta,Bello yana
kallonta yana so yayi magana aammh kuma ya kasa sai dai yana kallonta da idanuwansa
Wanda Suka gaji da Zubar da kwallah,Aneesa Ta matso Kusa dashi ta Rike Hannayensa
tana kallonsa kai Tsaye bata samu zarafin mgana ba illah Fashewa Datayi da kuka
Saboda Tsausayin Dayake bata in ta kalleshi gefen gadon ta jinginar da kanta tana
kuka kuka mai cin rai da Tsausayin bawa sun Dauki Tsawon Lokaci Ahaka kafin ta mike
zaune tana Share kwallah kallonsa tayi tana Fadin"Nasan kagaji da kwanciya ko..?
kuri yayi mata da ido cikin zubar hawaye tace"Nasan kuma kana bukatar achanza maka
kaya da wajen kwanciya ko..? Lumshe ido yayi ya bude yana kallonta Kuka Aneesa
takara Fashewa Dashi kafin tace"Ya zanyi...?bansan ya zanyi ba.."Take Fada tana
kara Dukewa kuka nakara Ciyota nan ma sai da Tagaji da kukan kana ta tashi ta Fara
Kokarin Dagashi ammh ta kasa sai ma Fadawa datayi kanshi tana Nishi Dagowa tayi
tana kallonsa tana Share kwallah rasa yadda Zatayi dashi tayi sai kawai ta Fice
Daga Dakin tana Share kwallar Tsausayin Halin da Bello ke Ciki.

Haraban gidan tafita tana kuka Salihu megadi na ganinta Haka Hankalinsa ya tashi
yana Tambayanta ko lafiya Cikin kuka Aneesa tace"Don Allah kazo ka
taimakamin..."Cike da Tsausayinta ya kalleta kafin yace"Jikin Alhajin ne...? Kai ta
gyada mai kafin ta juya ta koma Cikin Gida yabi bayanta Tiryan Tiryan har Zuwa
Bedroom din Bello Halin da Salihu megadi ya Iske Bello aciki Shima sai da yamai
kwallah Cikin Hawaye ya Durkushe gaban gadon yana Fadin"Hasbunallahu wani'imal
wakil..Alhaji Meyafaru dakai haka..? Aneesa Dake Sharan kwallah kanta haryafara
Ciwo saboda Kuka tace"Don allah ka taimakamin mu Chanza masa Kaya..."Tafada Tana
Share Hanci.

Cikin Sauri ya mike yana Fadin"Toh..Toh..Allah Sarki.."Yake fada yana Share Kwallah
Shima,wajen kanshi ta Dago Shi kuma yakama wajen kafafunsa,Suka Sauya mai Wajen
zama suka maidashi Tsakiyar gadon Saboda Wajen ya Riga ya baci da Fitsari,Da
hanzari ta Bude Wardrop dinsa ta lalubomai Jallabiya,ta mikama Salihu maigadi,ita
tayi karfin Halin zaremai Rigar Barcin dake Jikinsa Tana yi tana Sharan
kwallah,Haka zalika ita ta Ciremai wandon barcin jikin Nashi Salihu na taimakamata
Kasa Juran kallonsa tayi baya ta juya tana Fadin"Ka chanza mai Wandon Jikinsa bazan
iya ba.."Tafada tana Share kwallah Wajen Wardrope din ta koma ta Sake
Ciromai ,Boxers ta mika ma Salihu Duk da Haka bata Juyo ba Salihu megadi shi ya
ciremai boxers din Jikinsa wanda yagama jikewa da Fitsari,Ya saka mai wanda ta
mikomai wajen saka Jallabiyan ne sai da ta taimakamai,Suka maidashi suka kwantar
yana binsu da ido wannan karon babu hawaye sai dai Daga ganin yadda yake Lumshe ido
zaka Fahimci Tsantsan Halin Dayake Ciki.,Kwashe Kayan Da Suka ciremai tayi ta Shiga
Tiolet dasu Ta Jikasu cikin botiki ta fito.

Nan Salihu megadi ya Fice ya barta tana Zaune Akasan Cafet din Tayi Tagumi Lokaci
bayan Lokaci Tana Share kwallah,Wayarsa Dake yashe akasa ta dauka kodata Duba Wayar
ta mutu,Saboda Tsabar kira Tun Safe,tanan nan Zaune tana kalllonsa Lokaci Bayan
Lokaci Shima yana kallonta Kafin kuma taga ya Lumshe idanuwansa Sai ya Dade Ahaka
kafin ya sake Budewa Tun tana Share Hawaye har idanuwanta Suka bushe Tunawa Datayi
batayi sallah bane yasa ta Zabura ta mike tafada Tiolet dinshi ta Dauro alwala,Ta
Fito kenan sai Ta Tuna
Bata da Hijabi adakin,Da hanzari ta kama hanyar Fita daga bedroom din sai taji
kamar yana kallonta tana juyawa Taga idanuwanta Akanta Tsausayinsa ya kara kamata
cikin muryan kuka tace"Zan dawo hijabi zan Dauko..."Yana so yayi mgana aammh kuma
ba Halj Lumshe ido yayi bude har ta Fice Daga Dakin Zuwa Dakinta Hijabinta ta
Dauko,Ta Dawo bedroom din Yana kallonta ta kabbarta sallah Shima yana so Tun Dazu
yace Zaiyi sallah ammh babu baki kuma babu alamar da zai nuna Haka.

Bayan ta idar Da sallar isha"i Shafa"i da Wuturi tayi Ta Dukar Dakai tana Addu"a
tana Hawaye tana waigowa suka hada ido Cikin Tsausayinsa tace"kana so kayi
sallah...? Lumshe ido yayi ya Bude mata alamar Eh mikewa Tayi ta cire Hijabi kafin
ta isa kusa Dashi Dakyar ta iya Dago kansa ta karamai Wani Filon Abayansa yadan
Dago,baya Taja Tana Numfashi tana kallonsa sama ya maida Idanuwansa kawai yana
Kisima yana alwala kallonsa Take Cike da Tsausauyi Lokaci bayan Lokaci Tana Sharban
kwallah.

Yanayi miyau na Zuba ta gefen bakinshi,in Aneesa na kallonsa Ji take kamar ta saka
kuka ammh Kuma Zuciyarta ta kekeshe da Tsausayin Bello tanan nan Zaune ta tasashi
gaba tana kallonsa Karfe 10pm na Dare Aneesa Taji karan Bude get, da Shigowar
Motocin Tawagar ya Muktar Salihu maigadi ne ke musu barka da Zuwa Basu da Sukunin
karbawa Suka nufi Cikin Gida Daada ce agaba kamar tayi Tsintsuwa ta gabanta Gaban
Bello...

Sun wuce Falon Farko Suka ji basu Ji motsin kowa ba Sun isa Falo na Biyu Suna Rafka
sallama Aneesa Ta Zabura ta mike ta Bude Kofa idanuwanta Sun kumbura saboda
kuka.Tana ganin su Daada ta isa jikin Daada Tafada lokaci Daya tana Sakin kukan
Datake makalewa Tundazu Cikin zuciyarta Rumgumeta Daada Tayi tana Fadin"Bar kuka
Aneesa.."Take Fada itama tana Sharan kwallah Ya Muktar bai tsaya ba yanufi Cikin
Bedroom din Dauke da Hibba Datayi barci Anty Rahila tabi bayanshi Daada ta Riko
Hannun Aneesa suka mara musu baya Aneesa nata Sharan Kwallah...

Dukkansu Turus sukayi akofar Dakin ganin Bello gashi kwance Filon da Aneesa ta
karamai baya Dashi ya Zame kanshi yayi gefe miyau na Zuba Daga bakinshi Jikin ya
Muktar ya Shiga Rawa Daada kuwa sai ta Damke Hannun Aneesa saboda jitake kamar Zata
Fadi,Anty Rahila ko Tana kallonsa Tana Hawaye Lokaci Daya tana Fadin"Bello..."Cikin
Wani yanayi mai kama da Dimaucewa.

Cikin Sanyi jiki ya Muktar ya karisa gefen gadon ya Durkusa Bisa gwiwoyinsa bayan
ya kwantar da Hibba gefen gadon,.yana kallon Bello Bakinsa na rawa Cikin Taruwan
Hawaye acikin idanuwansa ya Riko Hannunsa Guda Daya yana Fadin"Bello...Bello...Kai
ne Haka...? Yafada Duk yadda yakai da Dauriya da Taurin Zuciya sai da Hawayen
idanuwansa suka Zubobganin yadda Shima Bellon ke kallonsa Tunda Suka Shigo Yake
Tsiyayan Hawaye lokaci Daya Muktar ya Rumgumesa kawai ya saki Muryansa Cikin Kuka
yana Fadin"Ka tashi don Allah..Bello kai kadai nake Dashi Dan"uwana Danake gani
naji Dadi..Don Allah katashi Zuciyata tana Rawa in na kalleka acikin Wannan Halin
Daada...Zoki gani Zokiga yadda Bellonki ya Dawo.."Yake Fada yana Sakin Shesshekan
kuka.

Daada Dakyar ta saki hannun Aneensa ta karisa ga Bello da Muktar Hawaye na Zuba
Cikin kwarmin idanuwanta Kallon Bello take bayan ta Hau kan gadon ta Karbi Dayan
Hannunshi ta Jimke Cikin nata,Kallonta yake Cikin idanuwa,Hawayensa na Zuba Lokaci
Daya Da Miyan bakinsa Hannu Daada ta saka tana Share mai gefen bakinsa Take
Fadin"Innalillahi..Wa"inna illaihirraju"un..."Allah gareka muke Muka gareka zamu
koma Allahuman Ajirni fi musubatihi..."Take Fada kafin itama ta kifa Hannun Bello
kan Fuskarta tana kuka mai Taba Zuciya Bello kuka ya Muktar kuka Daada Kuka Aneesa
ma Durkushewa Tayi tana Kuka Hakama Anty Rahila kukan Take,Sosai na Tsausauyin
Bello da Makusantanshi.
Sai da Suka yi kuka mai Isarsu kana ya Muktar ya Dago ya saka Hannu yana Sharema
Bello Hawaye da miyau lokaci Daya yace"Na maka alkawarin koda Zan Rasaka Duka
Dukiyata zan Tashi na Nemarka lafiya Bello..Da Izinin lahi zaka warke zaka kara
takawa da kafafunka Dat iz my promise.."Yafada kafin ya mike Lokaci Daya yana Share
kwallah Dakin ya Fita yakoma Falo wayarsa ya Fiddo ya lalubi Dr Nura na Asibitin
Murtala Aminu kano yaci Sa"a bugun Farkon ya Daga Ko gama gaisawa basuyi ba Muktar
yake sanar da Dr.Nura zai kawomai Wani Emergency yanzu Cikin mamaki Dr.Nura ke
Fadin"Bataliyan Sojan kasa Waye ba lafiya kuma..?

Cikin Share kwallah Muktar yace"Bello ne...Kanina ne Bello Muhammed


Jikamshi.."Cikin Tashin Hankali Dr.Nura yace"Subhannallah meya sameshi..?.

ya muktar ya Hadiye Kukan Dake Cin Ranshi yace"Don"t know How to Explain Dr.Buh dai
muna Tafe Dashi yanzu..? Yafada yana Jin kamar ya kara rushewa da kuka,Jin Haka
yasa Dr.Nura ya amsamai asanyaye Suka yanke Kiran Dr.Nura da Muktar abokai ne Tun
na yarinta Domin tare Sukayi primary sch dinsu har Zuwa matakin Secondry kuma Tare
Suka Tafi kasar Chicago Hado Digree dinsa na Farko Shi Bayan sun gama ya Dawo yayi
Joining din Amry,shikuma Dr.Nura yatafi kasar Malesia ya karancin Liktanci Bangaren
kashi ammh.

Ya Mukrar bai koma Dakin ba sai da ya Zauna Bisa Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya
Rufe Fuskarsa da Tafukan Hannayensa ya Sharbi kuka son Ranshi Sai da yayi ya koshi
kana ya Share Hawayensa ya Mike ya koma Daki Haryanzu kukan Suke Babu mai Rarrashin
Wani Daada gwanin ban Tsausayi ga Tsufa da Jarabawan Allah eh mana Jarabawa ce mana
Wanda bawa bai yi Tsammani ba,bai kuma bai isa ya tsallake ba

Dafa Kafadan Daada ya Muktar yayi wacce ke Faman Share ma Bello Hawaye da Miyan
Dake Zuba Daga bakinsa,yace"Daada kibar kuka Hakanan Jarabawan Ubangiji ne Addu"a
zamu tamai Allah ya bashi lafiya.."Daada na kallon Bello take Fadin"Dole nayi kuka
Muntari Kaduba kaga Bello fa lafiyanshi kalau Aneesa Tace Jiya koma miye Cikin Dare
ya sameshi Zuciyata na Bugawa ina Tunanin meya samu Bello Haka..? Ko kuma waye yama
Bello Haka..? .

Tafada ta Tsiyayan Hawaye ya Muktar ya cije baki yana Fadin"Bamu sani ba Daada
Wannan bayanin sai Bello ya samu lafiya,yanzu dai Asibiti zamu Wuce yanzu nagama
mgana da Abokina Dr.Nura.."Gyada kai Daada Tayi kafin Tatashi Tana Share kwallah
kai Tsaye Ya Muktar ya Sunkuya yana Fadin"Zan kai kai Asibiti Kaji Da yarda Allah
zaka samu lafiya.."Da ido yabishi da kallo Lokaci Daya yana lumshe ido,Cak Ya
Muktar ya Dago Bello ya kuma Sabashi kafadanshi Zuwa waje yana Fadin"Daada ku zauna
anan Zan Tafi Asibitin dashi Abunda ke Ciki zan kira Wayar Rahila na Sanar daku.."

Kafin Daada Tayi mgana Aneesa Ta Mike tana Fadin"Don Allah Zani...Zan biku..",Take
Fada Tana Hawaye Batare da Wani Tunani ba Ya Muktar ya Gyada mata kai kafin ya Fice
Daga Falon ta Gudu ta bi bayanshi tana Fama da Hijabin Datayi Sallah Daada batayi
gardama ba Domin Jiri take gani kartaje ta Fadi Har Waje Suka rakasu Shikanshi
mallam Inuwa Daya Taimaka Suka saka Bello amota sai da ya Fitar da Kwallar,Ya
muktar ya Shiga Gidan gaba Aneesa ta Zauna baya tare da Bello ta Cicccibi kansa ta
Dora bisa Cinyarta Tana Shafa kanshi Hawayenta na Diga Bisa Fuskarsa,Suka Fice Daga
Haraban gidan Motar tawagar Ya Muktar ta mara musu Baya.

11pm daidai Suka yi parking Afilin Asibitin Haraban Murtala Amunu kano,Kiran Dr
Nura yayi Nan da nan Sai ga Nurses da Gadon marasa lafiya,Tare da Dr.Nura Tunda aka
Fito da Bello Daga Motar aka Dorashi kan Gadon marasa lafiya Nurses suka Shiga
gungungara sa da Gudu Aneesa na binsu Abaya Dr.Nura ke Sarke da Hannun ya Mukrar
yana jin bayanin kan Ciwon bello Cikin karfin Gwiwa yace mai..

"insha Allahu i will Try my Best Naga Bello ya samu lafiya."Yafada Daidai Lokacin
da Suka iso Kofar Emargency inda Aka Shiga da Bello gyada kai Muktar yayi kafin
yace"Ina godiya Abokina..Allah yaasa.."Daganan Suka saki Hannun Juna Cikin Sauri da
Sassarfa ya Shige Emergency Room din ya bar Ya Muktar tsaye yana Sauke Numafashi
Aneesa ko Waje ta nema ta Zauna tana Share Kwallah.

Su Daada na gida Tun bayan Fitarsu Muktar suna Fama da Zullumi Ciki Zukatan su suna
Fatan Allah yabama Bello lafiya.

*****

Sai wajen Karfe 4am na Asuba Dr.Nura ya Fito Daga Emergency Room,Lokaci Daya ya
yafito Muktar Dake Tsaye awajen yana Safa da marwa barci ko kadan baizo idanuwansa
ba gwarama Aneesa ta bingere nan Bisa Teburin Datake Zaune ammh barcin baiyi Nisa
ba,Fitowar Dr.Nura yasa Ta Farka Tana ganin Ya muktar ya bi bayanshi itama ta
Rufamusu Baya

Suna Shiga Office din,Aneesa Itama ta Shigo Cikin mamaki Dr.Nura ke kallon Aneesa
Wacee kallo Daya zakamata ka Fahimci bata Cikin Hayyacinta,cikin mamaki yace"wannan
fa tare kuke..? Gyada kai Ya Muktar yayi kafin yace"Matarsa ce.."Cikin Tsausayawa
Dr.Nura yace"Ayyah...Srry Hv a sit naga kamar ma Jiri take gani.."Yafada adaidai
domin Aneesa bata gani Sosai yunwace da Rashin barcin ke Dawainiya da Ita da Sauri
Ta Nemi waje ta Zauna tana Sharbe kwallah Dr.Nura da Ya Muktar Suna mata kallon
Tsausayi.

Shima ya Muktar kujeran ya nema ya Zauna yana Fadin"Dr ya ake ciki..? Kungane
mtsalan Data Faru da Bello..? Kan Dr.Nura na Duke yana Cigaba da Rubuce Rubucensa
sai Zuwa chan ya Dago yana Zare Siririn Glass din Dake idonsa yace"Agaskiyan mgana
Muktar jikamshi..Mun iya bakin kokarinmu Wajen gwaje gwaje kan Bello ammh bamu gane
menene mtsalan ba Duk Na"urorinmu Normal suke Nuna ma Sai dai zuwa gobe da Safe
zamu Mai scaning din kugunsa da Bayansa Muga ko ta nan ne mtsalan take.."Dafe kai
ya muktar yayi yana Fadin"Ya Allah..."Kawai yake fada cikin Dauke kananan Hawayensa
Aneesa ma Danne kukanta take Tana kallon Ya Muktar yadda yake Dauke Hawayensa yana
Cigaba da jin bayanin Dr.Nura

"Wannan Shine karon Farko da muka taba samun irin wannam Case din akawo mana
patient Ba lafiya haka ammh kuma mu Dorashi kan Duka Na"u'orinmu Ammh Basu Nuna
mana komai ba, Nuna mana Suke komai na Jikinshi Normal ne.."ya muktar ya Girgiza
kai yana Fadin"Allah kadai ne masanin Abunda ya Faru.."Yafada Lokaci Daya yana
mikewa hannu ya mikama Dr.Nura yana Fadin"Nagode Dr..Zuwa goben dai in baku gane
komai ba zan mana Booking din Jirgi na Fita Dashi wani Babban Asibitin kashi Dake
New Delhi India."

Mikewa Dr.Nura shima yayi yana Fadin"Insha Allahu...Ina bayanka Domin Sunfi
kwararru akan Harkan abun ya shafi kashi.. Allah dai ya bashi lafiya so painfull.."

Ya muktar bai yi mgana ba illah Jinjina Hannu Da Sukayi Lokaci Daya yana cema
Aneesa"Muje gida..'Dr Nura yace"Kafin ku Dawo zamu kaishi Daki na Musamman.."ok
kadai yace Suka Fice Daga Office din yana gaba tana binshi abaya bai bita Zuwa gida
ba,Ita kadai ya saka Inuwa Direba ya koma da Ita Shikuma ya Wuce masallacin Cikin
Asibitin..

Haka Aneesa takoma gida ta iske Su Daada ba wanda ya Runtsa sunyi kuka har sun gaji
ita tadaina kukan Sarari sai dai na Zucci nan ta zayyanemusu bayanin Likita sai
kukan Daada ya karu,Anty Rahila na lallashinta Suna nan Zaune har Lokaci sallar
Asuba tayi Aneesa batayi Wanka ba sai da Wanke kayan Bello wanda ya bata Ta Shanya
Cikin bayi kana tayi Wanka da Dauro alwala ta Fito,Dukkansu bayan sun idar da
sallar addu",an samun sauki ga Bello suketa jerawa,Karfe 7am na Safe Ya muktar ya
kirasu awaya yana Sanar dasu an Shiga da Bellon yin Hoton kugunsa da Baya aga
Abunda Sakamako ya Fita Ammh Bello dai yana nan yadda Suka kawoshi babu Abunda ya
Chanza.
Kafin Rana tayi lbrin Abunda ya Faru da Bello ya karade Dangi Daada Har waya tayi
Chan Adamawa ta sanar musu Hakama Anty Rahila ta kira Borno ta sanarmusu Halin da
Ake Ciki Shima Ya Muktar Daga barayinsa kuma Shi ya kira Su Abba kabiru ya sanar
dasu Abunda ke Faruwa,Kowa yaji sai Abun ya Dafashi Sosai Wani Abun Tsausayin ma
basu sai Wanda Suka zo suka ganshi.

Kwana biyu Bello yana Asibitin Murtala Duka sakamakon Hoton da Akayimai Sun Fito
ammh kuma Babu Abunda ya Nuna Wani mtsala ya Faru da Bello kugunsa lafiya lau haka
bayanshi,Ammh kuma ya na nan yadda Suka kawoshi Nurses ke kula dashi Zuwan wannan
Lokaci Daga Daadan Har Anty Rahila da Aneesa Sun fige sun gama ramewa Saboda
Zullumi Tuni kuma lbrin Halin da Bello ke Ciki ta kai kunnen Hukumar Jami"ar Bayero
Universty,Daga Dalibai har malamai Haka Suke Taruruwan Zuwa ganinsa Duk da ba"a
bari a Shiga agansa sai dai ta glass jikin Kofar,duk wanda yazo haka yake Fita da
Kuka in yaga Mr bello Cikin Wannan Halin Wai The young Teacher kwance yana Kashi da
Fitsari duk Akwance baya iya Tsinanamai kanshi komai ,ko wanda baisanshi ba in ya
samu lbrinsa sai ya Zubarmai da kwallah

Arana ta Uku ne Su Abba kabiru suka zo Asibitin Shida Abba garba da ya hashim Suma
sun Tsausayama Halin dq Bello yake Ciki sosai kuma sun goyi bayan Fita Dashi kasar
Waje,acikin ransu basu taba kawo a ransu suna Dansu na da alaqa da Cutar bello
ba,Tun Asafiyar Ranar Muktar ya gama musu booking din jirgin da zai kwashesu zuwa
Kasar india,Washegari kuma su ya Ali Suka zo suma Wayyo Sai da Suka Zubarma Bello
kwallah,saboda Tsausayi Ga Muktar Shima Daya Zabge Lokaci Daya saboda Damuwa basu
Tafi ba Sai Washe garin Ranar da su ya muktar Suka Lula Kasar India,ya muktar ya
Sunusi Daada,Aneesa,Anty Rahila,Junior da Hibba sai Ya hashim Daya bisu Sai Fatan
Allah yasa adace.

Ki biya ki karanta cikin Salama.

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?22*

*INDIA*
_New Delhi_

Suna Sauka Ababban Filin Saukan Jirage na Kasar India New Delhi,Motar Babban
Asibitin kashi na kasar Wato *FORTIS HOSPITAL NEW DELHI* Asibitin da Aka kawo
*CAPTAIN ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU* (Littafin ALIYU GADANGA).

Already dama Tun Suna kano Dr.Nura ya Turamusu Dukkan Wasu Bayanan Gwaje gwajen
da Suka ma Bello zuwa asibitin Bayan sunyi magana Da babban Likitan kashi na
Asibitin Dr Khabirkhan ba Idiyan Likita ne wanda ya karanci Shashen kashi,Hatta Da
hotel din da Zasu sauka Sai da Dr.Nura yayi musu booking.

Suna Zuwa cikin Asibitin Dr.Khabirkhan ya karbesu Hannu Bibbiyu nan da nan aka
Shiga da Bello Zuwa Cikin Dakin Bincike Duk da bayanan da Dr Nura ya Turomishi ta
Email dinsu dokar asibiti ne kuma da Tsarin aiki Daga Barayinsu sai sun Sake
Dorashi Bisa Na'u'rorinsu domin gano Inda mtsalar take,Nan Suka Wuni a Asibitin
basu samu wani bayani ba Tunda har Zuwa Lokacin basu Fito da Bello Daga Dakin Gwaji
ba

*JW MARROTT HOTEL NEW DELHI..* Suka Sauka Aneesa da Daada Dakinsu Daya ya Muktar da
Anty Rahila da ya"yansu Dakinsu Daya sai Ya Hashim Da ya sunusi suma Dakinsu
Daya,kowa kagani cikin damuwa Sukuku,Kamar ma Aneesa Taji lbri Wacce Duk ta Zabge
Atsaye Idanuwanta Sunyi Zuru zuru ga Rashin barci ga Damuwa kukan kam sai na Zucci
ta daina yin na Sarari.

****
*KADUNA*

kasim tsaye Cikin Falonshi Wayace Akunnansa yana mgana Lokaci Daya yana Daga Lemon
Maltinan Dake Hannunshi yana Kurba,Lokaci daya ya saki Wata Dariya mai cike da
Nishadi kafin ya Dakata yana Fadin"Wato Haruna na yarda da Aikin wannan Bokan,Kai
kaji lbrin kuwa Dazu Abba Kabiru ke gayamin Duk likitocin Dake Asibitin Murtala
Aminu kano Sun kasa gano mtsalan komai yanzu Haka suna India Sun Kaishi inda
kwarraru Suke...Hhhh..Lalle araina nace Haka zasu je kuma Haka zasu Dawo.."

Ya karishe Fada yana kara Kecewa Da dariya kafin ya Dakata yana Sauraran Haruna
Dake Fadin"Bana gayamaka ba...? Ai ko Duka asibitocin Kasashen Duniyan nan zasu
zagaya dashi Wlh Haka zasu Dawo Dashi domin babu likitan da Zai iya sanin mafarin
komai sai wanda ya kullashi Shi kadai zai iya warware komai.."Dariya Kasim ya sake
saki kafin yace"Tun bayan Faruwan lamarin bantaba jin kaina Cikin Farinciki ba
Irin na Yau...Nagode Sosai Haruna kasa na Farajin kamshin Aneesa ta kusa Zama
nawa.."

Haruna yayi wata Dariyan kasaita kafin yace"Karka damu Mutumina,Kawai ka jira
lokaci suna gama yawan kasashen zasu Hakura su Dawo Dashi gida nasan Daga Lokacin
ko ita Aneesa bata Fara tunanin komai ba iyayenta Zasu Fara Tunanin Rabata
Dashi,Domin zama da Nakashasshe sai Dole ko nace Gawa mai Rai.."Yafada yana Dariya
Lokaci daya Suke Dariyan muguntan da Haruna kafin Kasim ya tsaigata da Dariyan yana
Fadin"Zan so na ganshi fa..? Zan so naga idanuwan izza da takamar nashi naga yanzu
yana dasu kokuwa.."

Haruna yace"Ina ai sai dai kaga Tarin kashi da Fitsari Daga Zaune mallam.."Kara
saka Dariya Sukayi kamar Wasu mahaukata,sai da sukayi ya ishesu kana Kasim yace"zan
Tura maka duka kudin aikin kaje ka kai mai kamika sakon godiyata garesa,saboda
office yasa bazan samu zuwa ba.."

Haruna yace"No wahala karka wani Damu.."Daga Haka suka yanke Kiran Bisa Kujera
Kasim ya Fada yana Sakin Dariya Lokaci Daya yana Jefar da gwangwanin maltinan Dake
hannunsa Wanda yagama Shanyewa Dariya yake Cike da Nishadi kafin ya Saki Mirmishi
yana Shafa Sajensa yana Fadin"Aneesa kin kusa Dawo gareni Dama ke din Tawa ce Ni
kadai..",yake fada yana kara sakin Wani mirmishi mai cike da Ma"anoni.....

****
_New Delhi_

Kwanansu uku kenan da zuwa kasar ammh haryanzu Dr khabir khan bai musu wani bayani
ba Kuma Har Tsawon Wadanan kwanakin Bello na Cikin Dakin gwaje gwaje ba'a fito
dashi ba saboda abunda ya matukar basu mamaki yadda duk sakamakon gwaje gwajen Dake
Fitowa,Normal babu mtsalan Komai Shine Abunda yake basu mamaki ga Bello yana nan
Jiya iyau abinci ma sai Cikin Ruwan Alluran dasuke Sakamai ne yake samun Karfin
Jiki.

Akwana na Hudu ne Dr kabir khan ya kira ya Muktar Da ya Sunusi Da ya Hashim Zuwa


Cikin Offce dinsu yana kora musu jawabin Sakamakon gwajen gwajen da Suka ma Duk
wasu kasusuwan Bello Dake da alhakin Tashinshi ko Tsayuwarshi Haka bangaren
Mganarsa ma Hatta Hotoon kansa da kwakwalawarsa sai da Sukayi ammh komai Normal
yake Nuna musu.

Bayani yake musu Lokaci Daya yana Nuna musu gwajen gwajen Hotunan,ya muktar Daya
Shiga wani yanayi Cikin Harshen Turanci yace"Dr bawani Taimako da zaku mana ne ,?
nan ne kadai Hop dinmu.."Shuru Dr khabir khan yayi kafin yace"agaskiya bazai iya
cewa komai ba yanzu Ammh mganar gaskiya Wannan ne Karo na Farko da Suka samu Irin
wannan case din sai dai zasu jaraba sanyashi cikin Wasu Injina Na Tsawon Wata Daya
Sukagani in Har Bai tashi ba zasu koma bangaren kashi toh gaskiya indai Duk Hakan
bai sa ya tashi ba Toh basu da wani Abunda zasu ma Bello.."Hankalinsu Duk ya Tashi
Sosai Da jin wannan bayani Cikin Daukewar Hawaye Muktar yace"ajaraba agani Insha
Allahu inaji ajikinsa Bello zai Tashi.."Da wannan Shawaran Suka Rufe
Tattaunawansu,sai kuma Ranar ne aka Fito da Bello Daga dakin gwaji zuwa dakin
matakin Farko,Ba"a barsu sun Shiga ba ammh daga bakin kofar suna iya Hangensa ta
Cikin galisan Wajen,Aneesa Ranar da kuka Wiwi Suka koma Masauki Saboda yadda aka
sanya Bello Cikin Wani Inji mai Jijjigar da Jikin Mutum,Daada kuwa ta koka ta koka
kamar Ranta Zai Fita Duk ta Zabge ta rame kamar ba Ita ba Wani Abun Tsausayin ma
Mai Rai kwance ba mgana ba motsi sai dai Numfashi,rai mai alfarma kawai ammh kowani
bawa yaga Halin da Bello ke Ciki sai ya Koka mai.

Kullum sai dai suzo su lekasa su koma Aneesa sai tafi awa Daya Tsaye tana kallonsa
tana Share kwallah Ranar da Suka Cika Sati da Zuwa Ya Sunusi da ya Hashim suka
barsu anan suka koma Nageria cike da Fatan samun lafiya ga Bello,Ya muktar kuwa da
Anty Rahila sai da Sukayi Sati Uku kana Suka koma Shida Yara saboda mkranta da kuma
Aiki aka bar Daada da Aneesa Wajen Bello wanda sai yayi Wata Daya Cikin Wannan
Na"uran injin din kana Za"a Fito dashi asake sabon Gwaje gwaje.

Shikanshi Ya Muktar din yana Nageria ne ammh Zuciyarsa gabadaya suna india kafin
Tahowarasu ya Siyama Aneesa Waya saboda jin Halin da Suke Ciki kullun dai Jiya iyau
Kullum Ya Muktar Cikin Waya Suke da Dr Khan Amsa Daya ne,Sai wa"adi ya cika Kana za
su sake Gwaji suga ko ansamu Cigaba,Kullum baya barcin kirki Salloli yake da
addu"an Allah ya Tashi kafadun Bello,mutane Dadama sunzo har gidan Yimai jajen
Abunda ya Faru Duka iyalan Abba kabiru da na Abba garba mama Sahura da Umma Zulfa
da Zubaida wanda kowacce Dataj lbrin Abunda ya Faru da Bello sai da ta girgiza
Cikin Zuciyar iyayensu kuwa Hamdala Suke Da ba wacce Ya Auri yarta da yanzu an
sakasu Acikin Wahala Umma Harda cema Anty Rahila Aneesa ne Abun Tsausayi Da
kuruciyarta Zata kare da Aikin gaton kwance Anty Rahila dai bata tanka mata ba
Saboda Ta gane inda ta Dosa,Hatta Inna Rukayyah Daga kano tazo,ta kwana biyu ta
koma,Shikanshi Kasim ya kira Ya Muktar awaya yana mai jaje harda Nuna Tsausayi
Kamar na Allah Nan ko yana kashe Wayar yayi ta Dariya.

Mutanen Borno Kuwa Ya Ali yazo Shida Anty Nafee,sunyi kwana Daya Suka koma,bayan
suma Anty Yagana tazo gwanin ban Tsausayi ba wacce suke Tsausayamawa Irin Aneesa
Tana karamar yarinya ta Hadu da Jarabta Rayuwa.,Kawayen Aneesa Kuwa B.kaita ce Taji
Aneesa Shuru sai ta kira Wayar Anty Rahila nan taji lbri mara Dadi ita ta Kira
S.jibiya take gayamata Dukkansu sun jajaantama Aneesa Tare da yin alkawarin saka Mr
bello Cikin Addu"o'insu.

Uncle Aminu Ko Dake Kasar Spain bai da Lbrin Abunda ke Faruwa Domin Tunda yayi ta
kiran Nombar Bello bai samu ya Hakura tunda bashi da Nombar ya Muktar ammh kullum
sukayi mgana da Ammi sai ya Tambayeta ko Bello yazo.? Nan take gayamai Tun Zuwanshi
lokacin Daya sanar da ita zai Fara Lecturing a Buk kano bai kara Dawowa ba,Aminu ya
Shiga damuwa sosai ammh yana kokarin ya kamallah abun ke gabanshi ya Dawo domin
Sauranshi Wata Biyar yagama komai ya Dawo gida.

Sani bai samu lbri ba Sai Daga baya Har Abuja yazo yama Ya Muktar Jajen Abunda ya
Faru ya kuma ce in zasu koma India zai bisu yaga Halin da Bello ke Cikin,achan
india kuwa Daada ta bama Muktar Shawaran yaje Adamawa ya Taho da Modibbo,Mtsayin
Jika yake gareta Saurayi ne irin bai yi karatun Boko mai Zurfi ba iyakarsa
Sakandiri sai na Addini,aikin Gyaran Motici yake agarin Adamawa tace ya Daukosa Su
Taho tare koda An Fito da Bello Aneesa Tayi kankantan Iya kula da Bello itakuma ta
Tsufa ga jikin Girma Nan da nan ya karbi Shawaranta yaje har Adamawa ya Taho da
Modibbo iyaye da yan"uwa nata Faman addu'an samun Sauki ga Bello.

Ana saura kwana Uku Afito Da Bello Suka Dira Akaasar india Shida Sani da
Modibbo,Daga modibbo har Sani Suna Tsaye Cikin Kofar Dakin da Bello yake suna
Hangensa Kwance sambal cikin Na"ura mai amfani da Na"urorin Computer,Sani na Hawaye
modibbo nayi suna Tunanin bawa mai Rai ne Cikin Wannan Abun Lalle Allah kadai ne
Mai Nuna aya alokacin dayaso Shi kanshi Ya Muktar yanzu bashi da wani karfin gwiwa
kamar mace zaki ga yana Share Hawaye Shar Shar kamar ba Soja ba wanda yasha
gwagwamaryan Rayuwa...

Awannan Dawowar ne ya Razana da Ganin yadda Aneesa ta koma Dama ba Auki ba,ta kara
ramewa duk tayi baki,nan Daada ke Fadamai bata cin abinci sai kuka zama yayi yana
ta lallashinta Tare da Sanar da ita bayan anfito da Bello sun ji sakamako in zai
koma Nageria zai Tafi da ita nan Aneesa Taka Rushewa da kuka Tana babu inda Zata
ita zata Zauna anan kukan Datakeyi sai da ta saka Ya Muktar share kwallah Saboda
Tsausayinta.

Ranar da za"a fito da Bello Daga Cikin Wannan Injinan Dukkansu ba Wanda ya Runtsa
kwana Sukayi Addu",an Allah ya sa ansamu Nasara matakin Farko Da Sassafe suka yi ma
Asibitin Tsinke Likitoci Sunfi Goma Suka Shiga Dakin sun Dauki Tsawon Awanni Aciki
kafin Su Fito basu ma kowa bayani ba Illah Dr khabir khan dayace musu Suyi ta
Addu"a yanzu za"a kara Tafiya dashi Dakin gwaji abunda sakamako ya Fitar Shine zasu
yi Aiki Dashi.

Aneesa Sulalewa Tayi Jikin Daada Tana Kuma duk Addu"an da tazo bakinta Daga gida
Nageria ma Duka ya muktar Duk ya Kira su yana Rokon atayasu da Addu"a Anty Rahila
ma Tuni ta Kira borno ta sanar dasu Kowa dai Yana ta Addu"an Allah ya sa Anyi a
Sa"a.

Agaban idonsu aka Fito da Bello Zuwa Dakin Gwaji kamar gawa ya yi Fari kasumba ta
cikamai Fuska da jiki,Numfashi ne kadai zai sa kagane Bello yana Da Rai,Tsawon awa
Hudu Suka kwashe Cikin Dakin gwaji kafin Likitocin Su Fito,Yadda ya muktar yaga
Fuskar Dr Khan ne yasa Yaji gwiwansa Tayi sanyi Hawaye Sun Taru Acikin kwarmin
idanuwansa Daga yadda Indiyanwan Likitocin ke mgana zaka san Abun ya basu mamaki
basu samu ganin Dr khan ba sai da Suka Fito Daga Meeting din Da Suka Shiga Akan
Cutar Bello.

Gabadayansu Suka D'uru Cikin Office din Dr khan Lokacin yana Tare da Dr Sunhat,suna
kara Duba Duka Record din Bello Suna kara mamaki Dr Khan ya Zare gilashin
Idanuwanshi yana kallon Ya Muktar kafin yace"Am Srry to say...Ammh wannan Gwajin
matakin Farko bamu Samu Nasara ba,Munyi matukar mamaki ganin yadda ya Fito Daga
cikin Wannan Na"uran ammh kuma Duka Sakamakon Farko gwajin ke Nuna mana Gabadaya
kanmu ya Daure babu Wanda aka taba sakashi cikin Wannan matakin ba batare da Kaga
An samu Naasara ba.."

Gabadayansu suka Dau Salati Ya Muktar ya Dafe kai yana Fadin"Ya Allah gareka
muke...Kuma gareka zamu koma...Mun yarda mu musulmai ne Mun karbi Jarabawanka
Hannun bibbiyu ina Fatan Dukkanmu Allah ka bamu ikon Cinye wannan Jarabawan.."Yake
fada yana Kifa kanshi bisa Tuberun Gabanshi yana kuka,Sani ma Hawayen yake Shida
Modibbo Daada ko kanta na kasa Tana Share kwallah Aneesa Fita Tayi Daga Office din
Tana kuka.

Dr khan da Dr.sunhat ne keta basu baki Cikin Harshen Turanci Lokaci daya suna mai
Sanar dasu Akwai wani Baturan Likita Daga Kasar babban Birnin America U.S Wato Dr
Philphil,kwararan Likitane kan Harkan Gaashin kashi,Duk bayan wata Shida yake Zuwa
Asibitin nan yana musu aiki na Wata Uku,Toh insha Allahu zai zo nan da Kwana goma
Saboda Bello Domin Sun Turamai Duka Record din Gwajen gwajensa Suna Fatan Wannan
karon ayi Nasara.

Koda suka koma masauki bamai lallashin Wani,Shi kanshi Bello bayan anfito Dashi
Daga Dakin gwaji wani Daki na Musamman aka kaishi,Ya muktar bayajin Wahalan Fitar
da kudi indai Akan Tilon kaninsa ne,ya kashe Miliyoyin kudi wanda baisan iyakarsu
ba,Duk dai domin Yaga Bello ya Tashi kafafunsa kuma Bakinsa ya Bude,Haka suka Shiga
Dakin Suka taru kanshi Suna kuka sani yana Rike da Hannayensa yana kallon Bello
bello fa,Bello shinre yanzu Cikin Wannan Halin Lalle kuduran Allah,Aneesa kuwa Tana
Daga gefe Sau Daya ta kalleshi bata kuma Saboda Yadda Bello yayi Tsufan karfi da
yaji kasumba da gemu sun cikamai Fuska.

Anan Asibitin Suka bar Ya Muktar da Modibbo Shima Dakyar Hukumar Asibitin ta yarda
Akidarta bata barin Majinyaci saboda Su Atsarinsu komai akwai masu kula Dashi Tunda
ga Yima Patient wanka,Bashi abinci kula da bashi magani chanzamai kaya Goge goge
inda yayi ba haya ko Fitsari,Ammh Ya muktar ya Dage Dole Suka kyaleshi da gargadi
Dagashi ba kari,ahaka ya yarda tunda ko yaya naka Awaje yake yafi da"ace wasu
Turawa ne ke kula maka da Naka.

Achan gida Nageria kuwa Haka suka samun Lbrin Rashin Nasaran Matakin Farko aikin
Bello sai dai kowa ya koma Addu"an Allah yasa Mataki na Biyu ayi Nasara,Tunkafin
Dr.philphil Ya kariso Ya Muktar ya Riga yagaama Biyan Duka Kudin Gashin gashin da
Za"a ma Bello Kawai Jiran Likitan Suke da kuma Lokaci.

Kwana goma na Cika kuwa Sai ga Dr philphil ya Diro kuma yana Zuwa da File din Bello
yaFara Cin karo dama already ya Fara Duba bayanan da Dr.khan ya Turamai ta Email
dinshi sai bayan ya gama Duba komai ya sanar dasu Ya Muktar cewa za"a ma Bello
gashin kashi na Tsawon Wata Biyu kwana Sitti kenan In Har kwanaki suka cika bawani
Chanji He is Srry to say su koma gida kawai Domin Zasu cigaba da Bata kudinsu ne a
Banza Bello haka zai kare Rayuwarsa Cikin Mutuwa da Rayuwa.

Ki biya ki karanta cikin salama.

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?23*

Cikin Nasara da Fatan Dacewa Aka farama Bello gashin kashi,kwana uku Tsakani Sani
ya juyo ya dawo gida Nageria,su ya muktar kuwa sai da aka kwana goma da Farawa kana
suka dawo gida shida Daada da Aneesa wacce Dakyar da sidin goshi,ta yarda ta biyosu
sai da yamata alkawarin in an kwana biyu zasu dawo tare.

Anan suka bar modibbo ba domin ko Zai Dingama Bello wani abu ba sai domin ba"a bar
Bellon Shikadai ba ammh komai na Bukata Ma"aikatan Asibitin kemai kama Daga
Wanka,cin abinci,Wankemai Najasa da Sauransu,Arana sau uku ake mai gashin Kashin da
safe,da rana,da yammah.
Tun da Aneesa ta dawo gida sai damuwarta ta karu Gabadaya ta Fige ta rame kamar ba
ita ba dama gata ba kiba sai ta kara zama wata iri sai ido da suka Fito,in kaga
Aneesa taci abinci sosai Daada ce ta matsamata Zakaga taci abinci da yawa,in ko ba
Haka ba,bazata ci ba,Ko Anty Rahila tamata mgana bataji sai ta fashe mata da kuka
Ya muktar kuwa shima yayi Rauni Sosai Kallon Aneesa ma saka masa Rauni yake
shikanshi Raman yake atsaye Bello ke chan India ammh Gabadaya Rabin Hankalin Muktar
yana kanshi baya iya samun barci gabadaya kwana yake addu"an Allah ya sa asamu
Nasara Bello ya mike kan Kafafunsa

Dawowarta yasa ta saka wani Layi ta kira Su B.kaita ta sanar dasu ta dawo,Kwana
biyu Tsakani sai ga B.kaita Direban gidansu ya kawota koda tazo Aneesa na Dakinta
tana kwance sai da Ta gaisa da Daada da Anty Rahila kana ta Shiga wajen Aneesa Tana
ganinta ta tashi da Gudu ta Rumgumeta Lokaci Daya ta saki kuka Bubbuga bayanta
B.kaita keyi Cike da Tsausayi kafin Ta Dagota Lokaci Daya tana Share mata kwallah.

Cikin Tsausayawa B.kaita ke Fadin"Kibar kuka Aneesa..Insha Allahu Uncle Bello zai
Warke.."Kada kai Aneesa Tayi kafin ta Riko Hannun B.kaita su Zauna gefen
gado,Lokaci Daya tana Fadin"Yaushe...? Wata rana Billy,Likitoci fa sunce matukar
Akagama wannan matakin bai mike ba toh Haka zai kare Rayuwarshi cikin Mutuwa ko
Rayuwa.."

B.kaita tayi Tagumi Tana Fadin"Kai in bawa na raye bai gama ganin Rayuwa ba..Kibar
yawan Kukan nan Kinga yarda kika Rame duk kin chanza,Addu"a zakitayi mai Allah ya
bashi lafiya muma masoyanki zamu Tayaki Addu"a Insha Allahu zai mike.."

Mirmishin Dayafi kuka Ciwo Aneesa ta saki kafin ta mike tana cemata bari tazo Fita
tayi ta samo mata Abun motsa baki,kafin Alheri ta gama Shirya mata abinci,Bayan ta
Dawo ne Suka kara gaisawa da B.kaita Suna Zaune bisa cafet din Tsakar Dakin B.kaita
ta kalli Aneesa bayan tasha Ruwa tace"Kin samu lbrin Resuilt dinmu ya Fito..?jiya
Rabi Suleja ta kirani ta ke gayamin."

Girgiza kai Aneesa tayi kafin tace"Wazai gayamin B.kaita..? Duka duka yaushe na
Dawo garin,Ni yanzu ba wanna ne agabana ba Gabadaya bana cikin Natsuwata.."Dan
mirmishi B.kaita Tayi tana Fadin"Nifa ina mamakin Wani Abu Aneesa Bukar Bulama..."?

Kallonta Aneesa ta kalleta tana Fadin"Kamar na me kenan..?B.kaita ta gyara zama


tana Fadin"Mamakin ganin yadda kika damu da Halin da Uncle Bello ke Ciki,in naga
Haka sai Na Tuna kece fa kike Tsanar duk wanda ya Nuna yana Son Uncle bello ko kuma
yana Burgeshi sai gashi yanzu wai kina kuka Saboda Halin Da Mr Bello ke ciki Abun
ne ke Matukar bani mamaki.."

Tafada kai tsaye tana kallonta Mikewa Aneesa tayi ta isa gaban Madubin Dakin ta
Harde Duka Hannuwanta kan Kirjinta Lokaci Daya Aneesa tafara fadin"Karki manta
Lokacin Akwai yarinta da Kuruciya Tare dani,lokaci na Tafiya girma na kara kamamu
B.kaita ko alokacin bawai ina kin Uncle Bello bane A"a ina ganin bani da makiyi
kamarshi sakamakon Shine ya karyamin kwarin Rashin son Mkranta ta Sai Daga baya na
gane Bayan iyayena Shine Mutum na biyu Daya Inganta Rayuwa Tunda ya Tursasamin na
Zama mai Ilimi kuma nayi karatu,kuma ko ba Haka Ko makiyinshi ya ganshi Cikin
Wannan Halin sai ya kokamai balle Ni da nake da Igiya uku Rataye Awuyana
amatsayinshi na Mijina..."Tafada Hawaye suna cika mata karmin Idanuwanta...

B.kaita ta gyada kai kafin tace"Kuma fa Hakane kinyi Mgana kema.."Aneesa ta saki
Numfashi tana Fadin"Ni ba ina Sonshi bane ko yana Burgeni ba kawai Tsausayin Halin
Dayake cike ke sakani kuka,Ki Tuna Abaya yana Tafiyansa,yana cin abinci,yana iya
Fadin Abunda yakeso da wanda bayaso yanzu fa yana kwance komai na Bukatar rayuwa
sai anyi mai Baya iya mgana sai dai ya bika da ido koda yana da Bukatar wani Abu
bakinshi bazai iya Furtawa,Shikadai ne in na Tuna sai naji kuka yazomin bana iya
Sarrafa kaina Billy kaita.."Tafada tana Rushewa da kuka.
Mikewa B.kaita tayi ta isa gareta ta Dafa ta tana Fadin"Bar kuka Anee don
Allah,kukan ki na Dagamin Hankali kuma kuka ba Mgani bane,Addu"a itace mafita bake
kadai ba Kaf Daliban Kwatar kwashi Zasu koka da Halin da Mr Bello ke Ciki bama ke
da kike Mtsayin matarsa ba.."Kan Kafadarta ta yada kanta tana Cigaba da kuka
B.kaita na lallashinta sai da tayi Shuru kafin su koma su zauna,Tana janta da Hira
har ta saki jikinta nan B.kaita ta kira S.jibiya tana gayamata gata gidansu
Aneesa,nan ta bata wayar suka gaisa ta mata yamai jiki,Kafin su rabu sai da
S.jibiya ta bama Aneesa Hakuri kan cewa Suna Jibiya an musu Rasuwa sai Sati na sama
zata Dawo in Allah yarda da Zaran ta dawo zata zo Har Abuja Sunsha Hira kafin su
yanke Kiran,Sai La"asar B.kaita tayi Shirin Tafiya bayan sunyi salla Sunci abinci
Direban gidansu wanda ya kawota ya juya da Ita Har Haraban gidan Aneesa ta Rakata
bayan tayi musu Daada sallama tana Dagamata Hannu Har suka Fice Daga Haraban
gidan...

Ba laifi Zuwan B.kaita ya saka Aneesa ta saki jiki kadan,Tadaina yawan kuka da
Damuwa ta maida kanta Daga kwanciya sai Karatun Qur"ani domin koda yaushe Sukayi
Waya da Mama Falmata Abunda take kara Jaddamata kenan Aneesa ki rike Allah,shi zai
zama gatanki,in ta gayamata Haka sai Hawaye sun Fitoma Aneesa,Tagama tabbatarma
kanta Bayan Allah iyaye sune kan gaba kan komai Musamman ma Uwa,wacce tafi kowa
sanin Damuwa Dan data Haifa,Gabadaya Aneesa ta koma bama yayyinta Tsausayi Ba wanda
baya Kiranta yana Bata baki Anty Nafee ce kadai bata taba kiranta tace ya mai jiki
ba bata sani ba ko tana kiran Anty Rahila ammh Anty Yagana da Anty Aisha Kusan koda
yaushe sai sun Kirata,Haka mama Yana itama tana iya bakin kokarinta ganin Aneesa ta
saki Ranta ta dawo da Jikinta kamar baya.

Achan india kuwa ana ta ma Bello gashin gashi ammh kam Babu Wani Chanji,Modibbo
Kullum Cikin kula Dashi yake,Shi ke kiran ya muktar Vedio call ya Rinka
Haskomai,Bello yana ganinshi,Muktar yana kallonsa yana Share kwallah Shiko Bellon
sai dai ya kafama wayar ido yana kallon Ya Muktar kansa na Lamgwabewa gefe miyau na
Zubomai kamar Wani gaula gwanin ban tsausayi Muktar ya riga yagama Sarewa Domin Abu
harzuwa Tsawon Wannan Lokaci ba Chanji game da Bello yana nan yadda Suka kaisa sai
dai Abunda Allah yayi kuma.

Daga Jami"ar Bayaro kuwa Malamai Shida ta Wakilta Suka je Har india suka Dubo Mr
Bello,suma Haka suka dawo gabadaya Jikinsu yayi sanyi Lokaci Daya Suna kara Tsorata
da Duniya,Kuma sun kara yarda bawa awajen Allah ba"a bakin komai yake zai iya yin
ikonshi Akanka Koda bai Rabaka da Numfashinka ba.

*****

Sannu Sannu bata Hana Zuwa sai dai Adade ba"a je ba,Gashi har Bello ya cike kwana
Sittin Da Faramai Gashin gashi har an kammallah ana gobe za"a maidashi Dakin gwaji
ya Muktar suka sauka akasar Shida Ya Ali,Washegari aka Shiga daBello dakin gwaji
Wanda Suka Kwashe Tsawon awa uku kafin Afito Dashi Tundaga yanayin Fuskar Dr
Philphil da Dr.khan suka Fahimci babu Nasara kan Kafadan ya Ali ya muktar ya Sulale
yana Kiran Sunan Allah Cikin Karfin Hali Ya Ali ya rikesa Suka karisa Cikin Office
din Dr khan.

Dr.philphil Shine yayi musu Bayanin komai Wanda ya kara Raunana musu Zuciya ya basu
Tabbacin Bello bazai taba warkewa ba domin Wannan ne karo na Farko da suka taba ma
wani wannan Aikin kuma basu samu Nasara ba,ammh basu sani ko kila nan gaba ya Tashi
ammh Azhirin batu Duka gwajin Sakamakon Suna Nuna Normal ne Abu ma daya kara
Dauremusu kai Duka Joint dinshi lafiya kalau basu da Mtsalan komai Komai na
Jikinshi yana lafiya ammh kuma gashi kwance ko yatsan Hannunshi baya iya Dagawa
Daga karshe ya basu shawaran Su koma gida kawai Domin Ko wani Asibitin Suka je sai
dai su sake Wani Asaran kudin kawai."

Kasa ya Muktar ya Sulale ya Rufe Fuskarsa da Tafukan Hannayensa yana Shesshekan


kuka Ya Ali ne da Modibbo suka Rikosa suna bashi baki,Su kansu Jikinsu yayi sanyi
Waje ya Fita yana Share kwallah Daada ya kira awaya tana Dauka yasaka mata kuka
tana jin Kukansa tace"Ba"a samu Nasara ba ko Muntari..?

Yana Sharban Majina da Hawaye yace"Daada sunce Bello bazai Taba Tashi ba...Kuma
Duka sakamakon gwajinsa ya nuna bashi da Mtsalan komai ammh Daada bello yana nan
kwance yadda kika barshi ba"a samu wani Cigaba ba..."Daada ta Sulale Bisa Kujera
tana Kiran Sunan Allah Lokaci Daya tana Dauke Hawayen idanuwanta da Haban Zaninta
cikin Dashewar Murya Daada tace

"Ya zamuyi Muntari bamu da yarda zamuyi In Har Haka Allah ya Tsarama Bello bamu da
yarda Zamuyi sai dai mu Tayashi Rumgumar kaddaranshi..."Ya muktar ya Share kwallar
idanuwanshi wanda ke Zuba ba Control ya rasa Dalili yana da Jarumta kan komai ammh
banda Kan Abunda ya Shafi Bello sam Baya da wani Jarumta Cikin Muryan Amo yace"A"a
Daada Insha Allahu ba Haka Allah ya Kaddaroma Bello ba...Da Izinin Lahi matukar ina
da lafiya da kudi da Mukami Sai na yawata da Bello Duka kasashen Duniya wajen Nema
mai mgani yanzu ma na yanke Hukunci gobe zan Wuce Dashi spain suma su Gwada nasu
Mugani Daada.."

Cikin Sauri Daada tace"A"a karma kafara Muntari Maza ka Dauko kaninka ku dawo gida
ina ji ajikina Cutar Bello bata yawon kasashen Duniya bace,ku dawo gida mu
Jarabamai na Hausa ko Allah zai sa Adace.."Ya bude baki zai yi mgana ta Dakatar
Dashi da Cewa"Kayi Abunda Nace Muntari ka Dauko Kaninka Bello ku Dawo Gida.."Daga
Haka ta yanke Kiran tana Sharan Kwallah shima Daga barayinshi kwallarsa ya Share
kafin ya koma office din wajen su Dr.khan

Bayan godiya daya yi musu,nan take yace Su Rubuta musu Takardan Sallama zasu koma
gida,Gobe in Sha Allahu,Duk da Abun ba Dadi ammh iya gaskiya kenan gwara su koma
gida ajaraba achan kila adace,kafin Zuwa Waye wan garin sun gama Duka Shiryan
Shiryansu na Tafiya,koda Aka Fito da Bello kan WheelChair,likitocin indiyawa da
Turawan sai kama Hannunshi Suke suna mai bye bye,Haka Dr khan da Dr.philphil suka
Rikemai Hannu Cike da Tsausaya Shikuma sai dai ido kadai ya ke saka musu,Fatan
samun lafiya suke mai Har Suka Sakashi amota suka Fice Daga Asibitin da suka kwashe
tsawon Wata Uku Aciknsa Shikan Modibbo ya saba da Wasu Da yawansu saboda Zama,duka
Rocord din Gwaje gwajen Na bello suka basu bayan sun ijiye ainihin Original din.

****

Babu wanda ya sanar da Aneesa Da dawowar Su Ya Muktar da Bello,Ta damu bayan


tafiyarsu bataji wata mgana ba tayi ta Tambayan Daada ita kuma taki gayamata sai
cemata datayi wai Ya muktar din bai kira Waya ba,duk ta damu Ciikin Zuciyarta
Zullumi ya isheta.

Ranar da zasu dawo Haka tatashi Bata jin Dadi Ciwon kai take Fama Dashi Dakyar ta
iya yin Wanka ta saka wata Doguwar Riga kirar Armani,tunda Tu bayan dawowarsu ta
Dauko sauran kayanta Daga Shashen Bello Tunda Sauran na kano mgani tasha ta koma ta
kwanta nan da nan kuwa barci ya kwasheta mai cike da mafarkin Bello.

Karfe 3:30Pm na Narana Jirgin daya kwasosu Daga Birnin Delhi Zuwa Babban Filin
Jirgin Nmandi Azikiwe Internatinal Airport, ya sauke su Tawagar ya Muktar suka zo
Daukansa Daga Filin Jirgin Shi ya Gunguro Bello Daga Cikin Jirgi wanda ke kan Wheel
Chair,akallon Farko bazaka taba Zaton yana da wata mtsala ba,saboda yadda yake
sanye Cikim Riga da wando na Kamfanin DKNY,wandon Sky blue ne Rigar kuma mai Dogon
Hannu ce Navy Blue ce,Fuskarsa ta kara Fayau ,ya kara Fari da kyau,hancinsa ya kara
Fitowa Sumar kansa tafara yawa Haka ma Sajen Fuskarsa ya kara yawa Baki Silub,fatar
Jikinsa ta kara kyai da Murjewa Duka Jikinsa lullube da kananun gashi kafarsa sanye
da wani bakin Takalmi mai igiya Hatta Tsitsiyan hannunsa yana Sanye da bakin Agogon
Fata na kamafamin Rado

Kowa yamai kallon Farko zai ji yana Son kara kallon Fuskarshi ammh Daya Kara
Nazarinsa ya Fahimci yadda Wuyansa ke Zuwa gefe Lokaci Daya kuma miyan bakinsa na
Zuba sai ka mai kwallah Namiji har Namiji sai dai kuma ya Nakasa,Modibbo ne ke Fama
da Tissue tun acikin Jirgi yake Faman gogemai da Zarar ya Fito dashi saboda kar ya
batamai gaban Riga.

***

Bata Farka ba Sai 4 da wani Abu Shima wai mafarkin Bello tayi ya Shigo Cikin Dakin
Datake da kakafunsa,shi ya Farkar da ita tatashi afirgice Duk Jikinta yayi sanyi
sai kuma taji Hayani a Falon Daada,Mamaki ya kamata kodai baki akayi sai ta kuma
Tuna Dazu taga ana ta gyara bangaren baki,bata kawo komai acikin Ranta ba sai tayi
Tunanin Dangin su na Adamawa ne domin Taji Daada na Tadinsu kwana nan..

Cikin kasala ta mike ta Fada Toilet ta Dauro alwala tazo tayi sallar azahar ta hada
da la"asar ta dade tana addu"an Allah yabama Uncle Bello lafiya kafin ta mike
Lokaci Daya tana kwabe Hijabin Data gama sallah Dashi,gaban madubi ta isa tana
kallon kanta,tana Daura bakin Dankwalin Doguwar Rigarta Kai Tsaye ta Bude kofa ta
Fito Falon na Daada saboda cikinta ba komai yunwa takeji.

Turus tayi ganin Mutane Cike da Afalon idanuwanta suna ta Wulgawa,Ya muktar,Ya
Ali,Anty Rahila Dasu Hibba sai Modibbo da Daada gefenta kuma Bello ne kan
Wheelchair dinsa,idanuwansu suka sarke cikin na Juna Lokaci Daya ya Saki Boyayyiyar
Ajjiyar Zuciya dama Ita yakeson gani Tun bayan Dawowarsu ammh kuma baisan ya zai yi
yayi mgana ba,ganinta Dayayi yasa yaji Dadi ya kafeta da ido yana Budewa yana
Rufewa alamun Murna,gefen bakinsa kuma na Zubar da miyau.

Kasa gaba tayi ta kuma ta kasa Baya Ya Ali ne yace"yau ga iskancin banza irin na
Aneesa mijinki ya Dawo ba lafiya ba sannu ba komai sai kallon Mutane ."Daada
tace"Mamaki take Ali Bata san da Lbrin da Dawowarku ba.."Tafada Tana kallon Aneesa
wacce ke kallon Bello Lokaci Daya tana Toshe bakinta kar kuka ya kwace mata Juyawa
Tayi ta koma Dakinta ta Fada Bisa gado tana Fadin"Bai Warke ba..mafarkina ba
gaskiya bane.."Take fada tana kara saka kuka.

Har ta Shige idanuwansa na kanta Kuri yayi gwanin ban Tsausayi ya Ali yabi Aneesa
da kallo har ta shige yana Fadin"Tsiyana da Aneesa fa wani Lokacin Sakara ce,toh
miye Abun kuka keda kullum ke kukan kina so ki koma ki ganshi yau kuma ya Dawo kuma
kina wani Sakarci.."Anty Rahila ta Murmusa tana kallon Bello yadda ya wani bata rai
Lokaci Daya take Fadin"Har ka manta Auta ne fa.."Tafada Cike da Tsausauyin
Bellon,Daada ta lura da yadda ya tsurama wajen ido sai ta kama hannayensa duka
biyun tana Fadin"Karka damu zata Fito haka take kuka kullum saboda Tsausayin halin
da ta barka koni da Dan"uwanka Aneesa bata kaimu Damuwa ba...Ka Riketa ko bayan
Raina Bello in ka Warke ka sota kuma ka Hidinta mata Ita din mace tagari ne
awajenka"Tafada tana kallonsa Hawaye na taruwa acikin idanuwanta Shima kallonta
yake Lokaci daya kuma ya Lumshe idanuwansa.

Ko abinci da ya Muktar ke bashi abaki Bai wani da ci da yawa ba,Duk da dama Rabi ya
Shiga ne rabi ya Fito Daga bakin,Duka Rabin Hankalinshi naga kofar Bedroom din
Aneesa Data Shiga Tundazu Bata Fito ba,Modibbo ne ya gogemai jiki,inda ya babbata
da Abinci,lokacin mangariba ta kawo Jiki da zasu Tafi maallaci dashi suka Tafi
saboda ko achan bayan an Faramai gashin kashi Da Lokacin sallah yayi modibbi zai
mai alwala ya saitashi agabas ya barshi bayan ya gamai yayi sallah yanzu ma Haka
suka mai Ya Ali yamai alwala suka Turashi Zuwa Cikin masallacin cikin Sahu aka yi
jamm"i Dashi Sukansu ma"aikatan gidan sun zubar ma da Bello kwallah hatta Sojijin
dake Tsaran lafiyan gida na Lt.gen Muktar muhammed Jikamshi.

Haka kuma suka Turoshi Zuwa Cikin gida har Shashen Daada,inda Suka bar Ya Muktar da
Ya Ali Shashen Anty Rahila suna mgana,Modibbo ne ya kariso Dashi Daada kuma na ciki
na Sallah,yana ijiyesa Cikin Falon yadinga kallon Kofar Bedroom din Aneesa Kansa na
lamgwabewa ammh bai gaji ba,Modibbo bai kula dashi ba sai da Daada ta Fito daga
daki Hannunta rike da Chasbaha ta kariso Falon ta Zauna kujeran dake Fuskantan
Bellon tana Fadin"har kun dawo sallar..?

Modibbo dake latsa waya yace"Eh Daada.."Bello ta Kurama ido ammh sam shi baya
kallonta Juyawa tayi ganin inda yake kallo yasa tace"Gunta zaka..? Da Sauri ya
lumshe ido yana Kallonta Mirmishi tayi kafin tace"Allah Sarkin Baiwa...Modibbo
kaisa Dakin Aneesa Wajen matarsa yakeson zama.."Tafada Cikin Tsausayin Bellon
Dariya Modibbo yayi yana Fadin"Kinga laifinsa Hajiya Daada lallashi zaka ko Baffa
Bello.."(Haka suke kiranshi saboda Bello baban Hassatu Baffansu ne..)

Yafada yana Dariya,Daada ma Murmusawan Tayi tana cigaba da Jan carbi shikuma ya
Turasa Zuwa Dakin Aneesa Tura Kofar Modibbo yayi da sallama yana Fadin"Toh kefa
matar baffa mijinki yagaji da jiran Fitowarki ya biyo ki.."Yafada yana Shigowa
dashi Dakin.

Tana Zaune kan sallaya tana Addu"a suka Shigo Da Sauri ta waigo Jin Abunda Modibbo
yace Saurin mikewa tayi tana kallonsu Shiko Bello ido ya kafeta Dashi yana so ya
Tambayeta meyasa take kuka..?ammh kuma ya kasa Mgana balle ya tambayeta Yana kallon
Cikin idanuwanta wani Abu na Shiga Zuciyarsa Tun Ranar da Abun nan ya Sameshi Kukan
Aneesa ya tsayamai arai Bai taba Tunanin zata iya damuwa dashi bayan shi kuma bai
damu da Ita,bashi da bakin mgana sai dai yayi ta mgana da Zuciyarsa.

Mirmishin yake tayi kafin tace"La...dama yanzu nake shirin Fitowa.."Dariya yayi
yana Fadin"Kedai kyaji dashi jan aji ne kawai a sassautama Baffalenmu kinganshi dai
ba lafiya ne dashi ba"Yafada yana Ficewa.

Ki biya ki karanta cikin salama.

*Shakira..*
8/19/20, 11:17 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?24*

Fitar Modibbo yasa tayi Saurin Sadda kanta kasa Tana wasa da gefen Dankwalin kanta
Shiko Kura mata ido yayi bai ko Kiftawa Domin yanzu idanuwansa Sune gabadaya Jin
kanshi.

Jin kamar yana kallonta yasa Ta Dago kanta karaf suka Hada ido kansa ya karkace
gafe ammh kuma bai daina kallonta bq Tsausayi ya bata ta Zauna gefen gado tana
fadin."Kun Dawo lafiya...?

Tafada kai tsaye tana kallonsa bai mata wani alamu ba illah Taga ya maida
idanuwansa kasa,Shuru kawai tayi tana binsa da kallon Tsausayi kwallah na Taruwa
acikin idanuwanta,Lokaci bayan lokaci sai ya dago ya kalleta kuma ya maida
idanuwansa kasa,kusa dashi ta kariso tana Fadin"Kana son wani abune..?ko yunwa kake
ji..?
Lumshe mata ido yayi ya Bude alamar A"a,ajiyar Zuciya ta sauke tana kallonsa
Araunane tana Durkushe agabansa,Miyan Dake Zubane Duk ya bata gaban Rigansa bata
san sadda ta saka gefen Dankwalin abayarta ba ta Shiga goge mai ammh bata yarda ta
kalli Fuskarsa ba,Kuramata ido yayi Cikin Zuciyarsa yana jin Wani game da ita wanda
ya kasa ganewa sai da ta gama ta koma ta Zauna agabanshi bata bari sun Hada ido ba
Shiko ya kafe ta da ido kamar ita kadai yake iya gani yaji Dadi.

Sun Jima Zaune Shuru batacemai komai,Cikinta ne keta Faman Kugi Saboda yunwa yasa
ta mike Zata Fita saboda kallonta yana so ya juya kansa ya kasa kadan ya Rage bai
Fado bisa Wheelchair dinsa ba,Da hanzari ta dawo garesa Batasan sadda ta Riko Duka
hannuwansa ba Tana Fadin"Ina zaka..? Zaka koma wajen Daada ne..?bai lumshe mata ido
ba illah Kada idanuwansa kadai da yayi alamun A"a,Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin ta
sakeshi ta kama hanyar Fita Harta bude kofar ta Sake Juyowa tana kallonsa ganin
yana so ya waigo ne ya Kalleta ammh kuma ya kasa.

Mirmishi Tayi kafin ta girgiza kai Tana Fadin"Yanzu zan dawo abinci zan sako ina
jin yunwa.."Sai Lokacin ya Sauke Numfashi Ficewa tayi ta barshi Zuwa Shashen Anty
Rahila babu kowa Kamar sun Tafi sallah ne,Kichen ta Shiga Alheri kadai ta Iske ta
gaisheta ta amsa,da kanta ta Dauki Filet ta Zuba Sakwaran da Akayi Miyar
Agushi,Kadan ta zuba domin Aneesa bata wani cin Abinci Fridge ta bude ta Dauki Ruwa
mai Sanyi,Har ta Fita ta Dawo ta ce Alheri ta yanka mata Fruit nan da nan ko ta
Dauko Wani Babban Faranti ta yayyanka mata aciki ta ce ta biyota dashi har Zuwa
Cikin Dakinta,cikin ladabi Alheri ta ijiye tana gaida Bello da kacokan Hankalinsa
ke kan Aneesa.

Gabanshi ta Zauna ta Fara cin Abincin Dagowa goma sai sun hada ido mirmishi tayi ta
Nuna mai Cokali take Fadin"Zaka ci..?Ido ya Lumshe mata ya Bude Gyada kai tayi
batace komai ba sai da Taci kusan Rabi tasha Ruwa,ta jawo Filet din Fruit din ta
Fara ci nan ma ya saka mata ido Karamar Wukar ta soka cikin yankakkiyar kankanar ta
mikamai sai kawai Taga ya Bude baki Cike da mamaki ta mike ta isa gabanshi ta saka
mai abaki ya karba Dariya ta saki kafin tace"Oh hakane fa na manta kai dama abinci
bai dameka ba Masoyin kayan lambu ne.."Tafada tana Dauko Farantin kayan marmarin
Gefen gado ta Zauna yarda zatayi Tsawo dai dai da kansa ta Dinga basa abaki yana
karba,lokaci Daya yana kallon kwayan idanuwanta,Ita kuma kallon Dayake mata yana
kashe mata Jiki sai ta dinga kauda kai,kusan shi ya cinye ita ko Tunda ya Nuna yana
so ta hakura ta barmai Yana so yace itama taci ammh babu baki,sai da ya koshi zata
karamai kawai ya Langwabe kai Sauran na bakin nashi na Fitowa Waje,Mirmishi tayi
kafin tace"Ka koshi ne..?ido ya kada mata mikewa tayi ta Dauki Filet din Data ci
abinci da na Fruit din ta Fita chan sai gata ta Dawo da Tissue ahannunta ta gogemai
baki tas,dagaban Rigansa kallonsa tayi tana Fadin"Zanyi sallar Isha'i kaima bakayi
ba ko..?bai kauda idanuwansa ba Yadai Rage musu Girma yana kallonta bata kara mgana
ba takoma ta bayansa ta Shiga Turasa Zuwa Cikin Tiolet dinta,Tattare Hannayen
Riganta Tayi Tafaramai alwala ko kafin ta gama Tajika kanta Shima Duk ta Jikamai
kayan Jiki,Kallonsa Tayi tana marairaicewa tace"Kayi Hakuri Na jika maka kayan Jiki
Ban iya ba ko .?

Yana so yayi mirmishi ammh kuma ya kasa sake lamgwabe kai yayi
Yana kallonta Mirmishi tayi tana Fadin"Yauwa baka ji haushi bako..? Karka damu da
haka zan koya Na dinga maka Tunda Modibbo Watarana Tafiya zaiyi,In mun koma gidanmu
na kano Har wanka zan dinga maka kana so..? Tafada tana kallonsa kara girman
idanuwansa yayi alamar mamaki ganin Haka yasa ta Rufe Fuska Tana Dariya Lokaci Daya
take Fadin"Bazan kalle ka ba,Rufe idona zan dinga yi.."Lumshe idanuwansa yayi ya
Bude yana kallonta bata kara mgana ba itama alwala ta Dauro ta Turoshi Suka Fito
Daga Tiolet din,Gabas ta karkatasa Itama ta Zura Hijabinta Suna Sahu Daya Takallesa
tace"Muyi sallah kaji..? Ido ya kada mata Kafin ta Tada sallah shima sallar ya Fara
har ta Idar tagama Addu"o'inta,ta juyo tana kallonsa tace"Ka idar kaima...?

Lumshe ido yayi ya Bude Gabansa ta koma ta tankwashe kafa tayi Tagumi kawai tana
kallonsa Shima ita yake kallo,idanuwanta Suka kawo kwallah Tayi Saurin maidasu Tana
Fadin"Kowa na gaisheka yan gidanmu na Borno gabadaya,Mama yana,mama Falmata mamata
kenan.."Tafada tana kallonsa kafin ta ci gaba da cewa"Su B.kaita ma sunce na gaida
ka zasu kara zuwa Su dubaka ka ganesu kuwa..? Kawayena Bilkisu kaita da Salamatu s
Jibiya.."Tafada tana kallonsa Rage girman idanuwan yayi Tayi mirmishi tace"Allah
Sarki Sai da kayi mgana da ido.."Tafada hawaye na gangaro mata,Bata rai yayi yana
kallonta Wuyansa na karyewa gefe Tana Share kwallah ta Tura mai baki tana
Fadin"Miye kuma kake bata Rai..?

Idanuwansa ya Kara ma girma yana kallonta Hawayenta ta Dankwalo tana


Fadin"Wannan..?ido ya lumshe mata mirmishi tayi tana Fadin"Na goge ka gani..? Sai
lokacin ya saki Ransa Haka ta tasashi gaba tana mai lbrai kan kukan Datasha bayan
ta Dawo Gida ta barshi achan,wani Lokacin sai ta gaji da mgana ta Tura baki tana
Fadin"Sai mgana nake ni kadai ko kanuna ma kana jin dadin lbrin.."Sai ya lamgwabe
mata kai sai tayi Dariya tana fadin"Karka min kuka mu cigaba.."Sun Dauki Tsawon
Lokaci tana mai Hira har Su ya muktar suka Shigo dakin bamu sani ba Sun Dade suna
kallonmu cike da Tsausayi Modibbo ne yayi gyaran Murya nayi Saurin Dago kai ina
kallonsu Daada tamin mirmishi tana Fadin"Matarsa ta Rike sa da Hira.."Dariya nayi
ina Sadda kai ganin ya Ali Awajan

Ya muktar yayi mirmirshi yana Fadin"Dare yayi gobe da safe sa karisa modibbi kama
sa ku Tafi ku kwanta.."Daada tace"ammh badai ba Shashensa ba ko..? Yace nan mana
Daada na saka Mallam inuwa ya Bude barayin Tun dazu ya gyara.

Girgiza kai Daada tayi tana Fadin"A"a zaka wahalar da mai Wahala dashi shi kanshi
Bello zai Wahala bene ne fa hawa da Sauka ka barsu su zauna Shashen baki.."Ya Ali
yace"Hakane Saboda kada ajikkata Shi Bellon mara lafiya.."Jinjina kai ya Muktar
yayi yana Fadin"Shikenan Modibbo kama sa kuje ku kwanta."Cike da ladabi ya isa
Bayan Bello ya Fara Karkato Dashi shiko Rai yabata yayi Kicin kicin da Fuska kamar
zaiyi kuka yana kallon Aneesa ya muktar ne ya lura dashi Cikin mamaki yace"Bello
kwanciya zai kai ka kayi ka Huta sai gobe ko..? Kallonsa yayi sai kuma ya karkata
kai yana kallon Aneesa Wacce ta Ware mai ido tana Fadin"awajena zaka kwana.? Da
Sauri ya lumshe ido yana kallonta Gabadayansu suka Tsaya Suna kallonsa,Daada
tace"Ikon Allah toh kaji wajen matarsa zai kwana"

Ya muktar yace"A"a Daada Modibbo ya Tafi dashi yaushe Aneesa zata iya da
Dawainiyarsa."Da Sauri Aneesa tace"Allah zan iya ya muktar.."Tafada kamar zatayi
kuka ya muktar zai yi mgana Ya Ali yace"Ka kyaleshi mana Muktar,ko bata iya ba ya
kamata takoya,ai modibbon zai koma Shima bakin Sana'arsa ko..? Dole dai itace zata
Dinga kula Dashi.".

Ya muktar yayi jim kafin yace"Hakane..Ammh bazata iya Dawainiyar Dagashi Daga kan
keken nan ba.."Da sauri Aneesa tace"In ba zan iya ba Zan kira Daada ta kamamin ko
Daadata..? Kai Daada ta gyda mata kwalla na Taruwa acikin idanuwanta ganin Ya
Muktar yayi Shuru ne yasa Aneesa Tace"Don Allah Ya Muktar kabar shi ya kwana anan
kaga fa yadda yayi zai yi kuka.."Tafada Lokaci Daya hawaye na Wankemata Fuska
kallonta yayi yana Tunanin Wani Abu Cikin Ransa Ajiyar Zuciya yayi kafin
yace"Shikenan...'Daga haka ya juya zai Fita yana Dauke kwallar idanuwansa,.

Sai da ya Rike handle din kofar kana ya waigo yana Fadin"Modibo ku Tafi Da Ya Ali
Chan Shashen ku kwanta sai da Safenku.."Daada tace Allah tashe mu lafiya,Ransa ya
saki ganin baza"a tafi dashi ba Karamar Jakar kayansa Modibbo ya Dauko ya kawo ma
Aneesa Shi da ya Ali Suka kama shi Suka Sauko Dashi Daga kan keken Nashi Zuwa kan
gado,Modibbo ya ciremai Riga da Wandon Jikinsa ya sakamai Wata Doguwar Jallabiya
saboda yaji Dadin barci bayan ya gama ya kalli Aneesa yana Fadin"Da Asuba zan zo na
masa wanka..."

Kai ta girgiza tana Fadin"Basai kazo ba zan masa Da kaina.."Kai tsaye yace"Kin iya
ne..?baffale na Nada Nauyi fa bazaki iya Daga sa ba.."Yafada yana mata Wasa ganin
Ya Ali ya Fita ne yasa Tace"Toh shikenan na yarda gobe da Safe kazo ka gwadamin
yadda Ake mai wanka Daga gobe Ni zan Dinga karban ladan wanda ka samu ya isa
Hakanan ko Daada.."Tafada tana Tura baki Dariya Modibbo yayi yana Fadin"Ah maida
Wukar zan koya miki komai Matar Baffale kema ki samu ladan Jinyar Mijinki.."Yafada
Yana Dariya Daada na Tayashi Haka Suka Fita suna Musu Sai da Safe binsu Tayi ta
kulle Kofar ta Dawo ta kwabe Hijabinta Duk yana Binta da kallo,wardrope dinta Ta
Bude ta Dauko Doguwar Rigar barcinta tana Juyowa suka Hada ido kunya Taji yasa ta
Dauki Hijabinta ta Shige Tiolet ta saka Rigan barci da Hijabin ta Fito,

Keken da Matsar gefe tana Fadin"Kana jin barci..? Ya kada mata ido Tashi tayi tana
Fadin"Toh muyi karatu kafin mu kwanta gobe da Safe kuma ma cigaba da lbrinmu ko..?
Ido ya Lumshe mata Mirmishi tayi tana kallonsa Har ta Dauko karamin Qur"aninta
Gadon Ta Hawo gefensa ta Zauna ta Bude Tana Fadin"Bismillah mufara ka dinga yin
naka acikin Zuciyarka kaji ko.? Ido ya kada mata taciga ba da Fadin"Kullum mukayi
Waya da Mamata tana Fadamin cewa na Laminzi karanta Qur'ni koda yaushe,Shi
alQur"ani mganin kowani Waraka ne"

Kallonta kadai yakeyi kansa yayi gefe Bisa Filon Ta Bude Suratul Maryam Tana
Fadin"Suratul Maryam zamu karanta.."Daga Haka tayi Bismillah ta Fara karatun cikin
Siririyar Muryanta mai cike da gardi Cikin Zuciyarta tana kara godema Bello Domin
Shi ya Jajirce Har ta samu wannan Ilimin,Kullum Suna karatun islamiya lokacin Suna
Mkranta sai da tayi Haddan Talatin,kafin su gama Tana ta karatu Shima cikin
Zuciyarsa yake binta Cike da Farinciki Saboda gajiyarvtafiya yasa Lokaci kadan
barci ya kwasheshi bata sani ba sai Zuwa chan ta Juyo ta ganshi ya Bingire kai yana
Sauke Numfashi Miyau ya bata Gefen bakinsa Mirmishi ta saki kafin ta Saka Gefen
Hijabinta ta Share mai Miyan daya Zuba Saukowa Tayi Daga kan gadon Ta maida
Qur"anin bisa Side Drower din gadon,Sake komawa Tayi kan gadon ta Zauna kusa dashi
ta karanto Addu"ar barci ta shafamai Duka Jikinsa Itama ta Shafa,inda kafafunsa
suke ta maida kanta Bayan ta rage Hasken Dakin,itama bata wani Dade ba barci ya
kwasheta mai Dadi

Karfe 4am na Asuba modibbo Ya Shigo Shashen Daada Lokacin Daada ma ta Dade da tashi
tana ta salolinta knooking din Dayayi Shi ya tada Aneesa Shiko Bello ya Dade
Datashi Daga kwance,Aneesa kuwa cikin barci ta Cukwikweye Kafafunsa Ta yi Filo
Dashi Bata sani ba gashi tasakarmai Nauyi,bai iya Motsa kafar ba,ammh Aneesa ta
gajiyar dashi Tashi tayi tana Salati ta Kunna Hasken dakin karaf ko Suka Hada ido
kafarsa ta bi da kallo Lokaci Daya ta Zaro ido ganin inda ta kwanta Har ya Tara
Jini Tsausayinshi ya kama ta abunka da Farin mutum Shafa wajen Tayi tana Fadin"Am
Srry Bansan na Danne maka kafa ba wayyo.."Lumshe ido yayi ya Bude yana kallonta
itama shi take kallo tana Fadin"Yanzu shikenan ko Cutar dakai za'ayi bazaka iya
mgana ba..? Take fada tana Dauke kwallar idanuwanta lokaci Daya ta Sauko Daga gadon
Hijabin Jikinta ta maida wanda ya ya zame Saboda barci kofar ta Bude Modibbo ya
Shigo yana mata Tsiyan Taji dadin barci da Baffalensa ta kasa tashi.

Bata mai mgana ba Mirmishi kadai Tayi mai,Ita ta Taimakamai Suka Daukosa Daga kan
Katifa zuwa Bisa Wheelchair,Abun mamaki bai bata Jikinsa ba Modibbo ke Fadamata bai
cika yin Fitsari ba ko wani abu sai ya kwana biyu saboda bai da ciye ciye,Toilet
suka Shiga Dashi Modibbo na gwada mata yarda yake mai wanka Dagosa yayi ita kuma ta
taimaka suka ciremai jallabiyan Jikinsa,Runtse ido Aneesa Tayi sanda ya Zare mai
Boxers din jikinsa,saboda bazata iya kallonshi Naked ba,ko Kirjinsa kasa Kallo Tayi
ganin ko"ina ya Cika da kananun gashi,baya ta Juya musu Sadda Modibbo kemai Wanka
Shiko Tsiya yake mata yana Fadin"Ashe baki son ladan.."Rufe baki tayi tana
Fadin"Ina so ammh sai dai na mai da kaya ajkinsa bazan iya ganinsa Ahaka
ba.."Dariya Modibbi yayi yana Fadin"Ba"a wanka da kaya ai...Mijinki ne bawani Abu
ba kuma lalurace babu yarda za"ayi.."Itadai batace komai ba Kuma bata waigo ba sai
da ya gama mai ya gogemai jiki da Towel,Aneesa ta mikamai Boxer dinshi da Vest
dinshi ammh bata Juyo ba Bello sai kallon bayanta yakeyi,Sai da ya sakamai kana
yace"Sarkin Tsoro toh an gama.."Sai lokacin ta Waigo ita ta mai alwala tace Modibbo
ya Tafi zata shiryashi yace"a'a bari ya Shiryasa sai su tafi masallaci tare..Fita
yayi dashi Daga Tiolet din itakuma ta maida kofa ta Rufe ta Tube ta Shiga wanka
bayan ta saka kayan Bello Cikin kwandon Wanki koda ta Fito Daga wanka Har Modibbo
ya Shiryasa ya Turasa Zuwa masallaci Itama manshafawarta ta shafa na olive ta Saka
Wani Riga da Sikat yan kanti na kamfanin DKNY,ta saka Hijabi ta Tada Salla
Raka"atanul Firjir tayi kafin tayi sallan Asuba bayan ta idar tayi karatun
Alqur"ani Har Zuwa Wajen bakwai na safe sai Lokacin Taji Muryansu Falon Daada bata
Fito ba gado ta koma ta Haye ta kwanta sai barci bata Farka ba sai Wajen 9am na
Safe Shima Anty Rahila ce tazo ta tasheta Kan tazo ya Ali zai tafi,Fita tayi Falon
Daada sukayi sallama da Ya Ali yamata Nasiha sosai Yatafi akan Sati mai Zuwa Zasu
dawo gabadaya hadda su Mama Yana,Ya Muktar da Tawagarsa,suka rakasa Har Airport
kafin ya Wuce Fadar Shugaban kasa suna da Meeting.

Tare suka karya da Bello ita ta Dinga bashi abaki,domin yaki cin Komai ko an bashi
sai ya ki karba,ammh Aneesa na Fitowa ya Daina bata rai,Bayan Sungama Karyawa ne Ta
Goggemai baki ta Turasa Suka koma Daki ta zaunar dashi kan kujeran Madubi ta saka
wani Abun Aski Tana Fadin"Nidai bari na rage maka wannan Gemun ya maida kai wani
Tsoho da yarintarka..",Tafada tana Tura baki kallonta yake bai ce komai ba Tsab ko
ta Rage mai tamai gyaran Fuska sai gashi ya Fito sak Handsome Mr Bello,Yana ta
kallon kanshi Amadubi ita kuma ta Haye saman madubin tana mai Dariya,Bayan ta gama
mai ta Kwashe gashin ta kai Cikin Tiolet Ta zuba cikin dustbin din tiolet din ta
dawo ta Zauna Agabanshi tana bashi lbrai saboda Samun Waje na Aneesa Harda
Tsatsuniya take bashi Har da lbrin Rayuwarta a Borno Da Irin Dukan Data ci Wajen ya
Ali tana bashi lbri yana kallonta wani waje tayi Dariya wani waje tayi kuka wani
waje harda bata rai chan kuma sai ta Tura baki tana bata Rai,Shidai yana kallonta
Zuciyarsa tana cike da Farinciki in yana Tare da Aneesa Shiyasa koda Minti Daya
baya son Tayi Nisa Dashi.

******
Bayan Sati Daya da Dawowar Bello,Har Aneesa ta kware Wajen kula da Bello,wanka ne
kadai sukemai tare da Modibbo Wani Likacin ma kafin yazo tamai,sai dai bata Ciremai
boxer dashi take mai wanka in modibbo yazo ne yake Ciremai ya chanzamai,ammh wani
bashi abinci,gogemai baki da komai ita ke Wahala dashi,Tare suke kwana Wani Lokacin
Daada ke kama mata su maidashi bisa gado in Modibbo baya kusa,ko Ya Muktar wanda
shima ke iya bakin kokarinsa,Aneesa kuwa bata Nuna gazawarta Duk da tana da
karancin Shekaru Kowa ita yake Tsausayi Domin Nakasan Miji ba"abu bane mai Dadi.

Baki ta ko"ina sai Zuwa gaisheshi Suke,Su Abba kabiru da Duka iyalansa sunzo Hakama
Ya Hashim da matarshi da Zubaida wacce ta Kurama Bello ido cike da Tsausayin Halin
Daya koma,Sai da ta Share mai kwallah Zulfa ko da Suka zo Acikin Ranta Hamdala take
da bata Aureshi ba Da yanzu ita ce ke cikin Wahala kamar yadda Aneesa ke Dawainiya
Dashi,Mutanen Borno ma Sunzo Mama yana,mama Falmata ya Ali,Ya Sunusi,Da matansu da
Ya"yansu Duka Suka kwana Daya Suka koma,Sai ga Malaman Chan Jami"ar Bayero,sun sake
Zuwa Dubashi har da Dn na Sch din,lalle Bello mai Mutane ne Hatta da Gungun Malamai
da Daliban Mkrantan kwatar-kwashi Tare da Jagorancin Principal din Mkrantan Sun zo
Dubashi,Haka suka Tafi da kukan Tsausayin Halin da Bello ke Ciki,S.jibiya ma tazo
ita da Mamanta Suka Wuni Suka koma Anty Yagana ma tazo ita da Mijinta suka kwana
Daya Suka koma Hatta da Sauran yan"uwansa da suka rage na Jikamshi sunzo Duba Bello
kowa kuma da Abunda yake Fadi,ana bada Shawaran Ayi mai na Hausa agani ko Allah zai
saka adace.

Anty Aisha Tazo Daga kano,itama da Megidanta Hatta da Inna Rukayyah ma tazo
Dubashi,Kasim ne kadai bai zo ba Kuma Abba kabiru yamai Waya kan Bello ya dawo Gida
yaje Dubashi yace Aiki yamai yawa in ya samu Lokaci zai leko nan ko bai da Niyyar
zuwa yanzu Duk da yana son Zuwa yaga Halin da Bellon ya koma yayi Dariya Sosai ammh
yanzu Lokaci bai yi ba yadai kusa Lokacin da Aneesa zata koma tashi har Abada.

Mutanen Adamawa sun zo,Mota guda suma Baffa Hardo,wani Tsohon ne wanda yake
Mtsayin Yaya ga Daada ya Tsufa Domin gabadaya Kansa Farin gashi ne tunda suka zo ya
ke kallon Bello yana Girgiza kai Sai da Zasu Tafi ya kebe da Daada yana Sanar da
ita yaga Sihiri mai karfi Ajikin Bello saboda Haka su Dage da mai karatun Qur"ani
da kuma Addu'o'i Shima zai koma yayi Nashi kokarin Daada tayi mamaki ammh sanin
Baffa Hardo yasan irin wannan Abubuwa yasa batayi mamaki ba ammh yace tayi Shuru da
Bakinta da Haka suka koma Adamawa,zuciyarsa cike da mamaki waye yama Jikansa wannan
Mugun Asirin.

Ki biya ki karanta cikin salama...

*ANITHA..*
8/19/20, 11:20 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?25*

Baffa Hardo bai gayama kowa ba Shikadai yake ta bincikensa,a binciken da yayi ne
ya gano Sihirin Dake jikin Bello mai karfi ne kuma bazai taba Barin Jikinsa ba sai
An Hako Abunda Aka binne da rai acikin Rami,kuma babu wanda yasan ina aka Binne
wannan Abun sai wanda ya Aikata mugun Nufin Nashi,ko wanda aka Biya yasa aka aikata
ma Bello haka domin a nakasa Rayuwashi cikin Nakasa da kasawa

Sai dai ya kira Daada awaya ya Sanar da ita a nemi Ruwan zamzam rika karantamai
Suratul Yasin,Falaqi kafa uku Nasi kafa uku,Qul"huwal lahu kafa uku,ayatul kurusiya
da Amanar Rasulu kafa uku uku cikin Ruwan Zamzam din arika bashi ya sha kuma arika
Shafemai jiki dashi Safe da maraice,Shima Dagachan nashi Bangaren ya Dage danashi
Addu"an Har Aga Abunda Allah zaiyi ammh al"amarin ya wuce Misali,Sihirin mai girma
ne anyi aiki akan Sihirin Sosai.

*****

Duka Wahalan Dawainiya da Bello Aneesa ce keyinshi Wani Lokacin sai in ta kasa ne
take Kiran Modibbo ko Daada su Taimakamata,wani wanka ne cin Abinci wanke mai jiki
in ya bata babu Abunda batamai,Cikin Lokaci kankani ta kara Zabgewa ta Rame kamar
ba Aneesa ba ta kara yin baki saboda Wahala ammh ita ko Ajikinta Alokacin Takejin
ma wani karfi na Zuwan mata,Babu wanda baya Tsausayamata ya muktar yayi yayi ta
barshi Modibbo ya Dinga kula dashi taki dole aka kayleta Shima gogan bayason na
Modibbo yafison na Aneesa,ko wanka ne in ba ita tamai ba baya sakin Fuska Ranar
Haka zai Wuni yana bata rai In ko Aneesa ve tamai ko Fuskarsa tana bayyanar da jin
Dadinsa,Duk da Shakuwar da sukayi su kwana tare su tashi tare bai sa Aneesa ta saba
da kallon Wasu gangan jikinsa ba ko wanka zatamai da Boxers dinsa zatamai sai ta
gama ta Runtse idanuwanta kana ta Zame mai wando kuma idanuwanta na Rufe zata Rufa
mai Towel ta gogemai,jiki tana yi tana Runtse ido ita adole bazata kallesa ba Shiko
sai dai ya kalleta yana Dariya acikin Zuciyarsa,ko abinci taresuke ci tana bashi
tana mai Hira Wani Lokacin taita mgana ya Kuramata ido baya Ko son Kyaftawa sai
tayi Fushi tajuya baya Tana Tura baki,sai ta Huce don kanta ta juyo tana Hararanshi
Shidai yana ganin Rayuwa,Kullun Dare basu kwanciya sai sunyi karatun Qur"ani kafin
su kwanta kuma ba laifi ita tana ganin Chanji Tunda yanzu ya Rage karkatar da kai
da Zubar da miyau ammh bawai ya bari Duka bane,Ruwam zamzam kuwa bata mantuwa kafin
su kwanta sai ta tofa Addu'o'i aciki ta Safemai Jiki dashi itama ta Shafe Ajikinta
kafin su kwanta,kowa ya Fidda rai da Bello zai Taka itako Tana ji Ajikinta Cewa
Watarana Bello zai Taka da Kakafunsa.

Sun Shaku da juna Tare da matsanancin Son juna batare da sun sani ba,In akwai
Abunda ke saka Bello yaji Ransa na kuna toh Yaga Aneesa na hawaye ko kuma yaga
Ranta ya baci yanzu nan idanuwansa zasu kada suyi ja yayi ta karkace kai yana zubar
da miyau,Itama bata kaunar ganinshi Haka Wahala dashi take sosai,Haka zata zauna
tayi ta bashi lbrai harda lbrin Irin Wasikun da yanmatanshi ke rubutamai,Su aikota
dashi tana yagawa Tun Suna Mkranta,shiko bai iya mgana sai dai kawai ya sakarmata
ido yana kallon Siririn bakinta wanda yake matukar Burgeshi yana Bala"in so yaga
Aneesa na Tura baki Tana mishi kyau sosai Shiyasa yake kunnata sai ta bashi abinci
yaki Bude baki ya tsaya yana kallonta yanzu zata Hau Turamai baki ko kuma tana
mishi Hira ya lumshe ido kawai yana jinta yanzu zatayi Fushi Tatashi ta Haye gado
tana Tura baki Shiko sai dai ya Bita da Ido yana Mirmishi Cikin Ranshi.

Ko Wanka fa Ta Fito inzata Shirya sai ta Juyar da kekensa Ya kalli Bango kana zata
saka kaya Daga baya kuma sai ta dinga kallonsa tana Fadin"Rufe idonka kaji tunda
nima banta kallon ka ba ."Dariya yake cikin Ranshi sai yayi kamar ya Rufe ido yana
Satar kallonta ta gashin idanuwansa,Aneesa nada Surar jiki mai Rikita Duk wani
Lafiyayyan Namiji mai Lafiya,Ranar da Bello yaci karo da Aneena Cikin Surarta kwana
yayi Cikin Zazzabi da Ciwon kai Saboda kukan Zucci yana Tunanin Tabbas Watarana
Za"a iya Rabashi da Aneesa Tunda bazata Dauwama Ahaka babu Abokin Debe kewa ba shi
yana kwance komai sai dai ayimai bashi da lafiyan dazai kare mata Dukkan
Hakkinta,Kwana Aneesa tayi kuka jin jikinsa yayi Zafi,sai da Safe Ya Muktar ya
kira likita Daga Specialist hop Dr.barau wanda ke Zuwa Duba bello Kowani Bayan mako
Biyu.

***
Wata Biyu da Dawowa da Bello, gida Yan"uwa da Abokan Arzuka suna iya bakin
kokarinsu wajen zuwa Dubsshi Sani kuwa cikin kowani sati Daga kaduna yana Hanyar
Abuja zuwa Duba bello,Kamar dan"uwa haka yake kallon Bello da Tsausayib yadda
Rayuwarsa ta koma Haka,Barayin Borno kuwa suma Lokaci bayan Lokaci Ya Ali da Ya
sunusi suna Zuwa Dubamu,Su Anty yagana kuwa da su mama yana koda yaushe cikin waya
suke kowa zai bada shawaran acigaba da addu"a in da rabo sai Bello ya warke kamar
bai taba ciwo ba.

Uncle Aminu ya Diro Daga Kasar Spain bayan yagama Duka Karatunsa,Kwanansa Biyu da
Dawaowa ya Diro Abuja dama Bello na cikin Ranshi Tun Lokacin Daya Daina samun
Wayarsa,wacce aka barta tana chan kano,Mugun Labri da kuma Halin Daya Tarar da
Amininshi ya sakashi Zubba da kwallah,haka ya Durkushe gaban Wheellchair din Bello
yana kamkame da Hannayensa yana kuka,shi kanshi Bello ganin Aminun ya tuna mai da
Rayuwarsu ta baya Shima sai Hawaye,In Aminu ya kalli Bello sai yaji kamar ya Rushe
da kuka haka ya Dinga Nunamai Hotunan da sukayi Lokacin suna rayuwa amtsayin
malaman mkratan Kwatar-kwashi Bello na Share kwallah shima yana Sharewa,sai lokacin
yaji lbrin Auren Aneesa da Bello Daada ke karantamai ya Dade yana mamaki da Jinjina
a"alamarin Ubangiji ita kanta Aneeesa sai da ya Tsausayamata Domin Hakika dukkansu
Ababen Tsausayi ne.

Kwana D'aya yayi ya juya kano ya labartama Ammi komai Washegari ya Dawo Tare da
ita,Itama ta jinjina lamarin sosai sai da tama Bello kwallah tana Tuna sanda yaje
gaisheta na karshe da kafafunsa,Itama tabama su Daada Shawaran bata jin Ciwon Bello
na Asibiti ne su mike Tsaye ga Neman Taimako su kuma Dinga Tofamai Addu"o"i Suna
shafemai jiki dashi basu kwana ba Aranar suka koma cike da Alhini.

Washegari kawai sai ga Anty Nafee ta iso Abuja Daga ni Har Anty Rahila munyi
mamakin ganinta domin kowa yazo banda ita kuma ko awaya bata kira kowa ba Haka Aka
Sauketa Cikin Farinciki Lokacin data shigo Shashen Daada ita da Anty Rahila, Ina
Falon Zaune kan kujera Bello na saman Wheelchair dinsa ina bashi ruwa yana Shan
Rabi,rabi kuma yana ta Zuba ta gaban Rigar Yadin dana sakamai Harda Hula,da hanzari
na Dauki Tissue ina gogemai sai gata ta Shigo koda na gaisheta sama sama ta amsa
tana karemin kallo Daada na wajen ammh bata lura da ita ba tafa Hannun takamayi
lokaci Daya Tana Fadin"Innalillahi Aneesa kinga yadda kika koma kuwa kamar wata
kwarangwal....Haba ina Adalci anan ace ke zaki dinga Dawainiya da katon gardi kamar
wannan Da babu Abun mamora tare Dashi.."

Tafada tana Nuna Bello cikin Tabe baki,Ba Aneesa kadai ba Hatta Anty Rahila sai ta
Muzanta Niko idona Tuni yaciko da Hawaye saboda naji ta tozartamin miji itakuma
Anty Rahila kunyar Daada ne ya kamata Cikin karfin Hali Tace"Anty Nafee baki gaida
Daada ba.."Sai lokacin ta Lura da Daada Cikin Son baras da Zencen ta Zauna suna
gaisawa da Daada wacce ta amsa mata Cikin sakin Fuska kamar Babu Abunda ya Faru nan
ko Cikin Zuciyar Daada kwata kwata bataji Dadin kalaman Anty Nafee ba Tunda Bello
dai lalura ce ta sameshi ammh ada kowa yasan Duk inda Namiji yakai toh Bello ya
Zarce nan..

Shi kanshi Bello kallon Anty Nafee yake da Fararan idanuwansa yana narkewa da bacin
rai,Gabadaya da Aneesa ta kalleshi sai ya bata Tsausayi Shima ba Haka yaso ba Komai
ya Faru da bawa Daga Allah ne,Kama Keken Bello tayi ta turashi Zuwa cikin Dakinta
Suka Bita da kallo Anty Nafee kuwa baki ta Rike tana bin Aneesa da kallo Cike da
mamaki ganin tana so ta kara sakin wata mganar ne yasa Anty Rahila ta tattarata
suka koma Shashenta karta kara kunyata ta gaban Daada,Allah ma ya taimaketa Muktar
baya nan sunfita tare da Modibbo.

Duk yadda Aneesa taso ta Tsaida kukanta sai da ta Sakeshi Suna Shiga Dakin ta Zame
bisa kafafun bello ta Fashe da kuka Tsurama kanta ido yayi wanda ke Daure da
Dankwali Atamfa kitson kalaban Dake kanta sun zubo Daga kafadanta Zuwa bayanta,so
yake ya Daga hannu ya dora bisa gadon bayanta ya lallasheta ammh bazai iya ba nan
da nan idanuwansa suka kada sukayi jawur kawai sai ya shiga maida Numfashi sama
sama alamun Bacin Rai da damuwa.

Sai tayi ya isheta kana ta Dago tana Goge Hawayenta,Kallonsa cikin Tsausayawa da
Kauna mai Tsanani Cikin Muryan kuka tace"Kayi Hakuri da Abunda Anty Nafee tace..Har
Abada ni Aneesa bazan taba gajiya dakai ba..,ai ba kai ka Dorama kanka ba Allah ne
ya Doramaka saboda Haka ina tare dakai mutuwa ce kadai zata rabamu kaji karka damu
don Allah..."

Bata ankara ba kawai taga Hawaye suna Zubomai mikewa Tayi Tasaka Hannuwanta Duka
biyu tana Sharemai Hawaye tana Fadin"Bana so...Kabari nima in ina kuka sai ka bata
rai,kadaina kuka kaji ko ina tare dakai mudum rai.."Tafada Lokaci Daya tana
Gyaramai zaman Hulan kansa Mirmishi tamai tana Fadin"Don Allah kamin mirmishi ko
Sau Daya Kaji B.Luv dina.."Tafada tana Sakarmai wani kallo,cikin idanuwansa yake
kallonta Lokaci daya kawai taga kamar Yayi mata mirmishi Tsalle ta Daka tana
Fadin"Wlh kayi min...plz dan sake min nagani.."Wannan karon lumshe ido kawai yayi
ya bude yana kallonta,Dariya ta saki tana Kallonshi Cikin so da kauna tace"Kaga
kyan da kayi yau..?Bari na maka Hoto kagani.."Wayarta ta Dauko ta Shiga Daukansa
Hotuna kala kala,Ta zagayo ta bayansa Ta Dinga Daukansu Self tare,tana Dariya Sunyi
bala"in kyau,Wajen tazo ta gabanshi sai Sikt dinta ya Sarke cikin kafafun keken
kawai sai ta Dawo da baya ta Fada Bisa Cinyarsa,cikin kunya Ta Dago tana kallonsa
Shima ita ya kafe da ido yana jin kamar su Dauwama Ahaka,kallonsa take cikin Wani
Shauki mai wuyar Fassara bata san Lokacin data Sulalar da kanta bisa Kirjinsa ba
tana Sakin mirmishi ita kadai Shiko Cikin Ranshi ji yake dama yana Da Hannu daya ya
Rumgume Aneesa ko zai samu sauki radadin Daya keji acikin Zuciyarsa Sun Dade ahaka
kafin tatashi tana kakkare Fuska wai ita kunya kallonta kawai yake cike da Sha"awa.

Acikin Bedroom din Anty Rahila kuwa Anty Nafee ce keta Fada tana Fadin mganganu wai
Rahila na gani ana cutan Aneesa Tayi Shuru suma su Ya Ali sunyi Shuru da bakinsu,Ta
kalli Anty Rahila tana Fadin"Kunfa san zamansu bazai taba yuyu ba Aneesa mace ce
iya mace kuma mai lafiya,zama da Wannan Mijin nata a nakashe bazai yuyu ba tana
bukatar kwanji Namiji da kuma Wanda zai bata kwan Haihu in akayi Shuru topah Haka
Aneesa zata Dauwama tana Wahalan gardi ita bada Jin Dadin Aure ba kuma ita baga
Haihuwa ba Wahala haka zata taru ta kasheta kuma in akayi Haka tsakani ga Allah
ba"a mata adalci ba.."Tafada tana Gyada kai kamar wata kadangaruwa.
Anty Rahila Da Jikinta Duk ba Dadi da manganun Anty Nafee Tace"Kidaina Fadin Haka
Anty Nafee Insha Allahu Bello zai Warke kuma da kike mganar Wahala dashi Aneesan ne
Taki mana ammh Har mai kula dashi fa Muktar ya Dauko Daga Adamawa yana nan Tare
damu Modibbo..."Cikin Kallon Banza Anty Nafee tace"Dillah yiman Shuru Sakarya Daga
ke Har Aneesa baku da Wayau ita kuruciya kedamunta ke kuma fa..? Wato kar kiyi
mgana aga laifinki ko..? Toh tsakani ga Allah ko Baba keda rai bazai bari acucu
Yarinya ba Tunda Ita bata da Wayau mu sai mu kyale Rayuwarta ta kare ahaka yakamata
dai aduba wannan lamarin gaskiya.."Itadai Anty Rahila Shuru ta mata bata kara mgana
ba.

Ya muktar Dake kofar Bedroom din Anty Rahila ya Dawo kenan ya Shigo ya sanar da
Anty Rahila zai Tafi Lagos yanzu sai ya iske suna mgana da Anty Nafee sai ya Dagata
daga bakin kofar sai da yagam jin Duk manganun Anty Nafee,wanda sai da suka kusa
sakashi kwallah,baya ya koma yana Dafe kanshi ba Shakka gaskiya Tafada In har Aka
bar Aneesa da Bello ahaka ba"a mata adalci ba kuma an cuci Rayuwarta.

Shashen Daada ya isa ya sameta Cikin Bedroom dinta,ganinshi cikin Damuwa yasa ta
dago tana kallonshi cikin Muryan Tsufa tace"Muntari lafiya kuwa..? kafita lafiya
lau kuma ka dawo cikin Damuwa.."?
Gabanta ya koma ya Zauna yana Fadin"Daada na yanke wani Hukunci kuma ina Fatan zaki
bani Hadin kai bayan kin Dubi Abun da Fuskar Fahimta.."

Cikin Gyada kai tace"Insha Allahu ina Sauraranka..?yayi jim kafin ya Sauke Numfashi
yana Fadin"Daada Na yi Tunani na gani cewa bai dace mubar Aneesa Haka ba Ma"ana
kwaruwace da Zalunci muyi Shuru mu barta ta Zauna da Bello don yana Namu ba..Bisa
adalci ya kamata arabasu ta samu wani mijin mai lafiya ta aura Shi kuma mu cigaba
da Kula Dashi,In Allah yasa yasamu lafiya Falillahil Hamdu ,in kuma Allah bai
kaddara zai kara takawa kinga yan"uwanta bazasu sakamu cikin masu zalunci
ba.."Yafada cikin son maida kwallarsa.

Shuru Daada tayi Tana kallonsa kafin ta murmusa tana Fadin"Hakane kam mganarka
Muntari nima dazu nayi kuka cikin Raina Danaji wata mgana...Sai nake Tunanin Ada fa
ba Haka Megidana yake ba lalurace ta Fadamai,ni yanzu Tunani Daya ya zaiji in muka
ce zamu rabashi da Aneeea,Alhalin na Lura dukkansu sun Fara Son Junansu barin ma
Shi da Baya son kowa kusa dashi sama da ita itace Farincikinsa..."

Tafada tana Share kwallah Ajiyar Zuciya ya sauke kafin yace"Nima na lura da Haka
Daada..Bazamu iya godema yarinyar nan ba...Banta Zaton zata kula da Bello Haka
ba,Tana mai Dawainiyar da ko Ni bana mai kamarta ammh Duk da haka Hakuri zai yi
Modibbo ya cigaba da kula dashi,muna tayashi da Addu"a inda Rabon zai mike sai kiga
lokaci Daya Allah yayi ikonsa ammh Dole suyi Hakuri Duka Domin bama kowani bangare
Adalci.."

Gyafa kai Daada tayi kafin tace"Shikenan Muntari Allah ya Shigemana gaba..."Mikewa
yayi yana Fadin"Ameen Daada yanzu zan Wuce lagos taron mu na Sojojin kasa,sai zuwa
jibi zan Dawo,Zan kira ya Ali da ya Sunusi ta waya muyi mgana sai suzo mu hadu mu
Warware komai in nadawo insha Allahu..."

Daada ta gyada kai tana Fadin"Shikenan hakan ma yayi...Allah kiyaye Hanya ya kuma
Tsaremana kai sai ka dawo..."Da Ameen yake ta amsawa Har ya Fice Daga Shashen na
Daada Dakin Aneesa yayi kooking tazo ta bude tana gaisheshi,amsawa yayi ya karisa
ga Bello yana kallonsa Cikin Sha"awa ganin yadda Aneesa ta sakamai manya
kaya,gabansa ya Tsaya yaDurkusa Lokaci Daya ya Riko Hannuwansa yana Fadin.."Anee ta
gayamaka kayi kyau kuwa..? Yafada yana kallonsa.

Lumshe ido yayi ya bude yana kallonsa,Mirmishi yayi mai lokaci Daya ya mike bayan
ya saki Hannunshi yana Fadin"Zan tafi lagos sai jibi zan dawo ka kula da kanka kaji
ko .? Yafada yana Shafa kanshi,Rumgumesa yayi kafin ya sakeshi ya fice Daga Dakin
Aneesa na mai Allah ya kiyaye Hanya.
Falon Anty Rahila ya koma ya kirata Awaya yace ta Fito Falo yana Jiranta sai gashi
ta Fito Dauke da Junior bai wani Tsaya ba yadai yagamata ga inda zashi,suna mganar
ne sai ga Anty Nafee ta Fito suka gaisa bai Nuna mata komai Suka gaisa cikin sakin
Fuska,yana Sauri ne Tawagarsa na waje tana Jiransa ya Fito ya Shiga mota suka juya
Zuwa Airport yana cike da Tsausayin Kaninsa da kuma yadda Zaiji in yaji Hukunci da
ya yanke.

Daada bata gayama kowa mganar ba Tayi Shuru da bakinta Anty Nafee kuwa Kwana biyu
tayi kafin ta koma maiduguri akwanakin Datayi kuwa sai da Aneesa ta gaji da ita
haka ta sakata Daki tana mata Fadan wai bata hankali ne haka takeso ta karishe
rayuwarta cikin Wahala bata biye mata sai dai tayi ta Tura mata baki In ko ta ganta
tare da Bello ta dinga sakin mata mgana kenan tana fadin yana Nakashasshe bazai
kyale mai lafiya ba,Abun dai ba Dadi Daada na ganin komai bata mgana Wani Lokacin
Daki ta ke shigewa tana Share kwallah Shiko Duk wannan baya damunsa Abu Dayane ke
cin Ransa kada aace za"a rabashi da Aneesa in ko Haka ta Faru bayan ciwon jiki
harda na Zuciya zai iya kamasa.

*Kibiya ki karanta cikin Salama..Ke da kika Siya kike Fitarwa da ku da kuke


karantawa baku Biya ba Bazan ce komai ba Illah Allah ya bada Sa"a ammh ki sani! na
sani! mun sani!.kuma ku sani..! Akwai ALLAH.*

Zakuman Uzuri Vips may be zuwa Dare kujini Tsint Saboda wata Sabga data
tasomin..Nagode

*Anitha...*
8/19/20, 11:21 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?26*

Tun ya muktar na lagos kira ya Ali sukayi magan kan in ya dawo Don Allah yana son
ganinsu shida ya Sunusi in kuma ba damuwa Harda su mama Yana saboda Muhimmancin
mganar,Jin Haka yasa Ya Ali yace karya damu insha Allahu Da zarar ya dawo zasu zo.

Bai dawo ba sai da ya dauki tsawon kwana biyar kana ya Dawo Abuja ranar Daya Dawo
ya kira ya Ali ya sanar Dashi inda yacemai insha Allahu ya Saurari Zuwansu.

Abba hardo ya kira Daada yace ta aiko Azo akarbi Ruwan zamzam din Dayama Bello
addu"a aciki adinga zubamai cikin Ruwan wanka Kuma ya zama Ruwan shanshi,kullum
kuma da Daddare in zai kwanta Ashafemai jiki,insha ALLAHU za"a samu Nasara Ahankali
kowacce gaba zata Dinga saki Cikin Jin dadi Daada tayi tamai Godiya

Muktar na Zuwa gaisheta ta labartamai yadda Sukayi da Baffa Hardo Shima yaji Dadi
Sosai,Yaso yaje da kanshi ne sai kuma ya Ali yamai wayar gobe suna Tafe shiyasa
yafasa ya Tura mallam Inuwa,modibbo ya bisa Zaije ya kwana Biyu ya Dawo,Tare da
Dauko Takardun Makrantansa wai Aikin Dan Sanda yake son yi Shine Ya muktar yace ya
Daukomai Takardunsa.

Washegari sai ga ya Ali da ya Sunusi sai Mama yana da Mama Falmata Zuwan yabama
Aneesa da Anty Rahila mamaki Tunda su basu san meke Faruwa ba,Sukansu Iyayen na
Aneesa Sunga Ramarta da yadda Duk ta lalace,Mama falmata kuwa cikin Ranta tana
Fatan Allah yabama Aneesa Aljannah Dalilin Jinyar Mijinta,Cikin Ran Mama yana kuwa
karfin Halin Aneesa take ganin Yadda Tana yarinya karama ammh ta iya Dauke laluran
Bello,wanda ko alama bata barinshi da kazanta Ko cikin Wani Hali koda yaushe zaka
Sameshi cikin kyawawan Kammani Yana zaune bisa wheelchair dinsa.

Sai da suka ci abinci kana Aka Zauna Zaman Dalilin Zuwansu afalon Daada Nima muna
cikin Daki Nida Bello ina karantamai wani Littafin Hausa mai Suna Ajininsa yake na
Zulaihat sani kagara Anty Rahila tace na Fito Nazo tare da Bello Ya muktar na son
mgana damu Daga ni har Bello sai da muka kalli Juna,dama ni cikin raina Tunda naga
Zuwansu Mama yana Lokaci daya dasu Ya Ali jikina yayi sanyi Haka shima Cikin Ransa
yana ta Fargaba Allah sa ba Tunaninsa bane zai Tabbata...

Hijabin sallah ne na Zumbula,ina kallon Bello wanda ya kafeni da ido Ajiyar Zuciya
na Sauke kafin na karisa ta bayanshi na Shiga Turasa Zuwa Falo gabadayansu suka
sakarmana idanuwa har muka kariso Tsakiyar Dakin kusa da Daada na ijiye Bello ni
kuma na koma Kasa Kusa da Anty Rahila na Zaune kaina na kasa,Daga chan kuwa ido
kadai Bello ya sakarmin Lokaci Daya kuma yana karye Wuya.

Ya muktar ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Alhamdulillah naji dadin yadda muka taru
lokaci Daya..Mama da Fatan zaku man afuwa na taso ku Daga gari mai Nisa ni ya
kamata ace nazo toh saboda muhimmancin mganar da kuma Halin da Bello ke cike yasa
Na zabi kuzo nan mu tattauna mganar.."Kowa gyada kai yayi cike da gamsuwa mama
yana ce tace"Ayyah babu komai Baban Hibba Yanayin Aiki ne...kana ma kokari Allah ya
saka da alheri.."

Gabadaya suka amsa da Ameen,Aneesa kanta na kasa tana Wasa da gefen Hijabinta Mama
Falmata ma kanta na kasa batace komai ba wanda ya damu sanin Hallayarta na kawaici
da Rashin son kwaranniya.

Cikin Gyara murya Ya Muktar ya cigaba da Fadin"Na taramu ne Dukkanmu Awannan wajen
Domin Mun riga da mun zama yan"uwa Dalilin Auratayya daya Shiga Tsakaninmu Harda
Zuru"a.."ya Ali yace"Hakane kwarai.."Jinjina kai ya muktar yayi kafin ya cigaba da
Fadin"Dalilin Hakane naga ya dace muma Junanmu Adalci,bako wace mgana bace Illah
Mganar Aneesa da Bello.."

Dam! Gaban Bello dana Aneesa ya Fadi lokaci Daya,Atare suka kalli juna Lokaci Daya
cikin Wani yanayi kowa na lura dasu barin ma Daada dataji har tafara tara kwallah
cikin Mamaki ya Ali yace"Aneesa kuma...? Kardai Wani Iskancin tayi domin Nasan mai
hali baya fasa Halinshi sai dai yayi lambo yagamin Wani Dibar albarkan tayi ma
bawan Allah dake Zaune ba lafiya yanzu naci Ubanta wlh.."Yafada cikin Fada dama shi
akwai Saurin Fushi.

Baki Aneesa ta Tura kwallah na Taruwan mata a ido wato ita haryamzu bata girmi Duka
Hannun Ya Ali ba,Bello Dake kallonta Duk ransa ba Dadi Ya Sunusi ne yace"Zata
aikata kasan Haka take akwai lambo Cikinta fal iskanci kedai kam bansan yaushe zaki
hankali ba,Baba bai bar gidan Duniya ba sai da yagama Sangartaki.."ya fada yana
Nuna ta shima Lokaci Daya yana Hararanta.

Dukar dakai Aneesa tayi cikin Ranta tana Fadin"Toh ni me kuma nayi.."Ya muktar ya
katsesu da Fadin"Ashsd..Meyasa kuke Hakane...? Bafa laifin datayi Wlh Aneesa tafi
kowa kula da Bello Acikin gidan,gabadaya Shikanshi in ba ita tamai wani Abun ba sai
ga yana bata rai..Babu Abunda zamu ce mata sai godiya da Fatan Allah yasa ta gama
da Duniya lafiya.

Suka amsa da Ameen Mama yana tace"Ai daman Aikinta ne ta kula da Mijinta kuma inda
tasan Dimbin ladan da mace take samu wajen kula da mijinta ko jinyarsa data kara
zage damtse ina Fatan Allah muma yaraba mana ladan damu.."Tafada cikin barkwaci aka
amsa da Ameen Ana Dariya.

Cikin Jimami Ya Muktar yace"Ina Nufin kan makomar Aurensu ne..,Ina Tunanin Ya dace
ace mu zauna muyi Duba kan Rayuwar ita Aneesa,kada mu tauye mata Hakki kamar yadda
na Dauke bello kani gareni itama tamkar kanwata take gareni...Zan so mata Abunda
zan so ma kaina na Zauna nayi dogon Nazari da Tunani na Fahimci zaman Bello da
Aneesa waje Daya amtsayin Ma"aurata bazai yuyu ba,Akwai kwaruwa aciki,shi bashi da
lafiya bazai iya Sauke mata Duka Nauyin Daya Rataya Awuyansa na Aure ba,ita kuma
macece mai lafiya dole watarana tana Bukatar abokin Rayuwa wanda zai Sauke mata
Hakkinta da wannan dalilai na yanke Shawaran mu taru anan domin na sanar muku Bello
zai saki Aneesa,saboda ta samu damar samun miji mai lafiya ta Aura..."Yafada yana
Shanye kwallar idanuwansa lokaci Daya yana kauda kai bayaso Bello ya Zuba masa
manyan Idanuwansa.

Mganar ta Daki Zuciyar kowa Tun ballatana Bello da Aneesa,wanda ta dago a razane
tana kallon Ya muktar wanda yayi kasa da idanuwansa,Shima Bello shi yake kallo
cikin wani Dukan Zuciya da Rauni mai Tsanani kokarin motsa bakinsa yake ammh yakasa
mgana sai kuma ya maida kallonsa kan Aneesa Wacce ta Rufe bakinta Hawaye na
Zubomata Lokaci Daya tana girgizamai kai ganin Idanuwansa sun kada sunyi jawur
lokaci Daya kuma sun Fara tara Ruwan kwallah,Daada ma kanta ta Sadda tana Share
kwallah Mama falmata ta Dago tana kallon Aneesa da Bello lokaci Daya taji Sun kara
bata Tsausayi Aneesa yarta ce ammh Tana mata kwadayin samun Aljanna dalilin Auren
Bello Dake kanta.

Ya Ali ne ya sauke ajiyar Zuciya kafin yace"Wannan mgana Daka Fada Hakane Muntari
Aduka mganganunka Babu na Banza...Kuma Abun adubane sai...",Tim suka ji karar
fadowar mutum,Da gudu Kowa ya mike suka Nufi Bello Dake kokarin tashi ya Fado daga
kan keken,kafin su isa Aneesa ta rigasu isa cikin Kuka da Fitan Hayyaci ta Rarumosa
Lokaci Daya ta Fashe da kuka sai kowa ya tsaya yana kallonsu.

Kan Cinyarta ta dora kansa Lokaci Daya Hawayensa suna gangarowa ta gefe da gefen
kumatumsa,Da ido ya kafeta itama Shi take kallo tana Fadin"Kaji ko zasu rabamu..?
Sun manta kaima abaya ba haka kake ba! Kana tafiya kamar kowa..! Kana Mgana kamar
kowa! Kaci abinci da kanka..Bayan ka zabi Duk Abunda kake so..! Ka saka kayan da
Ranka keso..! Komai zakayi na Rayuwa yau da kullum kana ma kanka ne..! Basa Tunanin
kaima Allah ne ya Dora maka..? Bazan bari su Rabamu ba Ina tare dakai Muddim
rai.."Tafada tana Kara Rumgumshe,lokaci daya tana Sharemai Hawaaye

Ba wanda magaganun Aneesa basu kashemai jiki ba,Barin ma Daada da Anty Rahila
hawaye Sukeyi Cikin Tsausayin Halin da Bello yake ciki,Mama falmata Dake tsaye taji
Zuciyarta ta karye kawai sai ta Durkusa gaban Bello Ta Riko Hannunsa tana
Fadin"Kana son zama da Aneesa..? Kallonsa ya maida kanta Lokaci Daya ya gyada mata
kai Cikin Taruwan Hawaye,mirmishi tayi kafin ta saka hannu ta Sharemai Hawaye tana
Fadin"Kadai na kuka..Bamu zo nan,domin mu Raba ku ba..Ba kasafai nake shiga
Sha"anin Aneesa ba,ammh yau tsausayinka yasa na Shiga,koda Aneesa bata son zama
dakai zan Tursasa mata ta Zauna dakai Muddin Rai ballatana itama tana son zama
dakai saboda Haka,ku zauna tare Har Abada ina muku Fatan Rayuwa mai cike da
Farinciki har gidan Aljannah Firdausi.."Tafada itama kwallah na Zubomata Daga
Aneesa har Bellon Fuskarsu Ta Nuna Farinciki kawai sai Aneesa Ta Shiga Sharewa
Hawaye tana Fadin"Nagode mama...Yau ce Rana ta Farko da kika Taba Shiga Sha"anin
Rayuwata...Kin kuma Shiga alokacin Daya kamata..Nagode mama.."Take fada tana kuka
lokaci Daya da Dariya.

Gabadaya kowa sai da Kwallah ta kawomai cikin idanuwa Ya Muktar baya ya juya yana
Share kwallarsa,Anty Rahila ce ta matsa Kusa da Aneesa tana Fadin"Anee tashi na
kama miki Shi mu maida Bello kan kujera.."Tafafa Tana Share kwallarta itama,cikin
sauri Aneesa ta mike Anty Rahila da Daada Har da Mama yana Suka taimakamata suka
maidashi kan kekensa,Aneesa bata rabu dashi ba, kusa dashi ta Zauna Lokaci daya
tana Kamkame hannunsa Guda Daya,shima lamgwabe kai yayi miyau na Zuba Daga bakinsa
ammh Cikin ranshi Farinciki ne.

Jikin kowa asanyaye ya koma ya Zauna ya Ali ya Saki Ajiyar Zuciya yana Fadin"Tabbas
Mama Falmata tayi gaskiya...Ko abaya bamu da Niyyar Raba Auren Aneesa da Bello koda
itace ta Nuna batason zama dashi..Muktar kayi hakuri Duka Hujjojinka masu kyau ne
ammh karka damu mu mun yarda Aneesa tacigaba da Zama da Bello amtsayin Mijinta,in
ya warke Alhamdulillah in ma bai Warke ba toh Taji ta gani Dukkansu sun yarda zasu
Rayu da Juna Ahaka ka cire Tunanin Cutar da wani Allah da Zuciya yake amfani.."Ya
muktar ya Share Hanci yana Fadin."Bansan da wani baki zan muku godiya ba...Kun mana
Abunda yan"uwanmu suka gagara yimana...Allah ya saka da alheri ya kuma bar zumunci
dama ina alhinin yadda Rabuwar Aneesa zata kaya da Bello domin Dukkansu sun Shaku
da Juna.."

Daada ta muskuta tana Fadin"nima Haka Muntari..Zuciyata na cike da Tsoron Faruwar


Haka..Domin bayan Mutuwar Jiki,harda Mutuwar Zuciya zata iya kama Bello Aneesa
Allah yayi miki Albarka..Mama falmata sannu da Kokari.."Tafada tana Share kwallah
mama falmata batace komai ba,illah ma ta kauda kai kawai tana kokarin maida
kwallarta.

Nan kowa ya tofa albarkacin bakinsa Lokaci daya kuma suna bin Aneesa da Bello da
kallo wacce ke gogemai baki da gaban Riganan jikinsa na kanfamin Armani,da gefen
Hijabinta tana mai mgana kasa kasa,cike da tsausayi Ya Sunusi ke fadin"Duk Abunda
kaga Allah yayi shi...toh ka saka ido zai nuna ayarsa Afili."Yafada yana kallonsu
shi da kanshi yakeji acikin ransa wanda yayi sanadiyar raba wannan ma"aurata toh
Allah bazai barshi ba.

Ana Shirin tashi taron,Domin su ya Ali sunce bazasu kwana ba,Aneesa tace"Don Allah
ina neman wata alfarma..."Gabadaya suka kalleta suna jiran mganarta Ya Muktar ne
yace"Wata alfarma kuma Anee..?

Bello ta kallah kafin ta maida kasa tana Fadin"Ku mana alfarma mu koma gidan mu na
Kano da Zama,zamu fi sakewa achan...Shima kuma zai fi jin dadin hakan domin yana
kaunar garin kano sosai.."Tafada tana kara Kallon Bello ido ya Lumshe mata Alamun
Hakan yayi daidai.

Ya muktar yayi Shuru kafin yace"kano kuma Anee..?Baki tunanin zamanku anan cikin
yan"uwa kamar baifi ba.."Kai ta girgiza kafin tace"Yafi mana ya muktar ammh ka
kalli Fuskarsa zaka ga yana Farinciki sosai..Don Allah kar kace A"a kaji.."Tafada
tana Hada hannuwanta cikin Sauri Daada tace"Mganarta gaskiya ne,Matsayin mata da
miji suke kuma Zaman Aure suke..Bazasu daumawa tare damu ba..Ka barsu su koma
kano,kila Yafi jin dadin chan zama waje daya ba Dadi.."

Ya Ali yace"Hakane..Kuma Hakan zai ragemai wasu Tunanin kullum kana Zaune waje
daya.."Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Shikenan...Ammh Dole Modibbo yabiku Har
Zuwa Lokacin da zan nema mai police militry sch Jos,lokacin kun saba da garin
sosai.."Daada tace"Hakan yayi ma..Allah ya Kara lafiya.."gabaya aka amsa da Ameen
sai da suka rufe taro da Addu"a kafin su tashi matan suka Shiga ciki sukayi sallar
azahar,mazan kuma suka Fita har da Bello Zuwa masallaci wanda ya muktar ya
turasa,Suna Dawowa suka su Fito,bayan Mama falmata ta kara bama Aneesa wasu
addu"o'in tace ta yawaita karantamai Amanar Rasuli kafin ya kwanta Tafiyar Jirgi
sukayi daman kuma da Zasu koma ma Jirgin suka bi Zuwa Maidiguri Dagachan zasu Shiga
mota Zuwa Borno.

****
Wannan Dalilin shi ya karama Aneesa da iyayenta kima acikin Zuciyar Daada da Ya
Muktar sukaji Duk Duniya basu da kamarsu su Abba kabiru ne dama ya muktar ke jawosu
inta Bello ne ko Daada ko Ajikinsu suma sai suyi wata ko kira basu yi ta waya ba
Yanzu Hankalinsu ya kwanta suna ganin mai basu mtsalan yana kwance ba lafiya babu
Abunda zai iya yi Shiyasa lokaci daya Shifa da Abba garba Suka cire fargaban
watarana Bello zai iya maka su ga Hukuma Tunda bashi ma da lafiya ta kanshi yake.

Hashim ne ke zuwa dubashi in yasamu lokaci shima ba sosai ba,matarshi ko Sau biyu
ta taba Zuwa Zubaida kuwa sai D'ayan datazo bata dawo ba dama son bana Allah da
Annabi bane na tsabar kyanshi ne,kuma yanzu Babu amfani Tunda ba ma mora,sai dai
bare ne ke tafe Zuwa dubashi kowa na kawo nashi Taimakon,Sani da Aminu sune aminin
kwarai ga Bello cikin kowani sati suna Hanyar Abuja Duk da Aminun zai Fara Koyarwa
da University of lagos kwanan nan ammh hakanan yake Fizgan lokaci yana Zuwa,kasim
kuwa ko Sau daya bai taba Zuwa ba,Duk da yana da lbrin duk halin da Bello da Aneesa
ke ciki,abakin Abba kabiru ko Hashim sai ya kirasu yana Dukan Ruwan cikinsu Har Ya
Muktar din yana ma haka ya kirashi yana Tambayanshi ya Bello..? Aneesa na nan tare
dashi,Abun yana matukar bashi Haushi ganin Shuru Target din shi bai yi aiiki
ba,shiyasa yayi lambo yana kara Tunanin ya kamata kota karfin tsiya ne Aneeea ta
Zama tashi,wacce ta ma manta da wani Hallita wai kasim.

Tun washegarin Tafiyar su Ya Ali Modibbo da mallam inuwa suka Dawo,da sakon Baffa
Hardo Aneesa Aka damkamawa bayan an mata karin bayani,gefe guda kuma tana ta Shirin
komawarsu kano haka kurum takejin gwara su koma chan suyi zamansu kamar zasu fi jin
dadi,Kayansu ta riga tagama Shiryamusu Sauran kayanta ma Ashashen Bello taje ta
kwaso,duk da bata Diba da yawa ba,Tunda suna da Wasu achan ana gobe zasu koma chan
ta yima Bello aski ta gyaramai kai da Sajensa ta askemai gashin jiki tas,itama tayi
Tsifa Alheri ta mata kalaba,bayan angama tazo tana Nuna ma Bello ya Dinga kallo
acikin ranshi yana ta yabawa Sabawar datayi Dashi yasa take Fahimtar wani Abu Game
dashi in yana son Abu ta Fuskarshi take ganewa toh Ranar ma ta gane yana son ta bar
kanta abude karta maida dankwalinta,haka kota Zauna sai in zata Fita ne sai ta
saka Vail ta Rufe kanta.

Washegari suka koma kano Ita da Modibbo da Anty Rahila da Daada ,hibba da junoir
suka rakasu,Tuni Modibbo yazoma Ya Muktar Da takardunsa shikuma yayi mai alkawarin
zai cikamai burinsa,Ya muktar bai bimu kano ba,Ranar ma yana Zaria yazo Jaji
passing out,Tun kafin suje Aminu ya kai kanwarsa Raihana taje gidan ta gyara
ko"ina hatta kichen duk angyara an zuba sabon cafane an zubar da wanda na bari Duk
sun Rube,abinci kuma Ammi ta Dafo suka zomana Dashi bayan mun Sauka Salihu Maigadi
kuwa baki har kunne yana ta kwarara ma Bello Addu"ar samun lafiya.

Basu samu komawa Aranar ba sai Washegari ammh kafin su wace sai da suka biya
gidansu Aminu suka gaida Ammi kana suka Wuce su kabar ni Daga ni sai Modibbi wanda
muka sauke cikin Bedroom din Falon Farko koda Suka tafi ma Bello na Haraban gidan
Uncle Aminu da Modibbo sun Fita dashi Suma sun saka Fararren kujeru suna hira
Lokaci Daya suna Shan iska ko Bello baya mgana ammh kallo Daya zakamai ka Fahimci
yana cikin Farinciki.

Niko ina cikin gida ina Jeramana kaya Cikin Wardrope tare da wasu kayayyakinmu,Duka
Ruwan Addu"an munzo dashi harda su na Fito dasu Kusa Tunda Amfanin kullum ne,bayan
na gama kuma na Fada kichen nema mana Abunda zamu ci daddareg gefe daya kuma
Hankalina kwance Tunda Bello na tare dasu Modibbo..

Ki biya ki karanta cikin Salama...

*Anitha..*
8/19/20, 11:22 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400
ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?27*

Farar Shinkafa Na dafamana da Miyar ganye,sai na Dafamana Zobo na saka cikin


Fridge,kafin na karisa girkin ya riga yayi sanyi Fruit na yankama Bello Domin yafi
sonshi sosai.

Bello saboda ganin Uncle Aminu ne yasa ya bari Modibbo ya bashi abinci har ya
karba,shikanshi Moddibon yana ta mai Tsiya,Sai dai kawai ya sakamai ido,Nan suka
Wuni tare Ko sallah zasu tare suke Tafiya da Bello daya ke akwai wani masallaci nan
kusa damu nan suka turasa suka je,sai yammh kana Uncle Aminu yamana Sallama ya tafi
kan gobe zai dawo suyi sallama da Bello jibi Zai wuce lagos.

Washegari dayazo mai sallama bai Tafi ba sai da ya Daukesa suka Fita cikin gari shi
da modibbo Sun dan jima kana suka Dawo gidan,Bayan Uncle Aminu yayi muna sallama
kan sai bayan Wata Daya zai dawo ammh kanwarsa Raihana zata dinga Zuwa tana
taimakamin Tunda tana gida bata Zuwa ko"ina Tun bayan candy dinta,Ba wata babbace
kamar sa"a tace ko zan girmeta bai wuce da Wattani ba,kullum zata zo mu wuni tare
muyi girki tare tatayani na gyara gidan muna yi muna Hira Dayake babu Ruwanta tana
da Kirki sosai,ta gayamin cewa School of Hygen take son Shiga da Zarar Result dinsu
ya Fito,Ni kuma nace mata namu ya Fito ban Duba bane dayake na abayanmu suka Rubuta
nasu jarabawan kenan ina gabanta da Shekara Daya kenan.

Rayuwarmu muke gudanarwa cikin Farinciki Sosai Nida Bello,Raihana da Modibbo na


Debemana kewa,Mu zauna muyi ta Hira Bello sai dai ya Dinga bin mu da ido,Sai yammah
tayi kana Modibbo zai maida Raihana gida amotar Bello Dayake Tun Muna Abuja Mallam
Inuwa ya koya masa Tuki,Bama cikin matsala Nafara maida jiki na,duk ba Ban koma
kamar da ba,shikanshi Bello ya kara kyau sai dai Ramar Jiki kawai na ciwo,Koda
yaushe y muktar cikin kiran mu yake awaya yana tambayanmu ko muna cikin
mtsala,hakama Daada itama kullum cikin kira suke suna tambayanmu lafiyanmu
Hankalinsu ya kwanta jin muna cikin Farinciki ba wata mtsala.

Haka zan tsala wanka nayi kwaliya Shima namai gayu Modibbo da Raihana suyi ta
kashemana Hotuna suna mana Dariya,Niko a jikina domin na gama Sabawa da mijina Fiye
da kowa na Duniya Sirrinsa nawa ne Hakama Sirrina nashi ammh haryanzu bana iya
kallonsa Tsaf sai dai na dinga Runtse Runtsen ido Ranar bayan na gama mai wanka zan
ciremai gajerun wando na Runtse idanuwana cikin Mistake hannuna ya taba mahood
dinshi jin na taba abu kamar icce ya sani bude ido Abunda na gani ne ya Tsorata ni
na Kusa sakin ihu jikina na kyarma sakinsa nayi Na Fita Daga Tiolet din Da Sauri
kirjina na Bugawa Ranar wankan daban karisa mai ba kenan modibbo ya karisa mai ya
shiryashi,kuma Haka na Wuni ban bari mu hada ido ba duk ko na cin kallona dayake
yi,Kullum Dare kuma bana kwanciya sai munyi karatun alqur"ani bayan mungama sai na
Shafemai cikin da Ruwan zamzam din da Baffa Hardo ya aiko mai dashi,,in zamu kwanta
gefe nake kwanciya,ammh saboda ina da mugun barci kafin gari ya waye na gama hayowa
cikinsa na kamkamesa ko Tunanin bai da lafiya bana yi toh ina na sani Tunda Cikin
barci ne sai gari ya waye na Dinga Dariya ni kadai,kuma bai hana gobe na Sauya
wajen kwanciya ba ammh Duk da Haka sai na isa gareshi,na saba kwanciya ina Juye
juye Kamar wata yarinya.

Muna yawan Fita Yawan Shakatawa Nida Modibbo da Raihana Watarana ma har gidan Ammi
muke zuwa mu Wuni sai yammh mu dawo duk domin muyi keeping Bello company kuma
Abunda na lura yana jin Dadin Haka,wani lokacin ma Restaurant muke zuwa muci abinci
ayita kallonmu ana Mamaki ga Mutum har mutum aamh babu Lafiya,masu tsausayi kuma
suna tayamu addu"a acikin Ransu,Cikin Haka ne Watarana muka Fita Shooping bayan mun
je wajen Siyan ice cream,tunda ina bala"in son kayan sanyi,harda gashshiyar kaza,da
Kifi ina sonshi sosai domin modibbo na Fita ya siyomana watarana
Shopprite muka je bayan mun gama Siyan ice cream sai muka Shiga Al-pen
store,Raihana da Modibbo na baya ni kuma ina gaba Ina Tura Wheel chair din
bello,jikina sanye nake da Doguwar Riga kirar bahrain,Baka nayi Rolin da Vail din
Rigar karamar jakace Rataye agefen kafadata,sai kafata tana sanye da Ruffafen
takalmi mai kyau da Tsari Fuskata babu kwalliya ammh nayi kyau sosai,hannu na sanye
da agogon Fata na gucci,Bello ma na Shiryashi ciki wata Shadda saky blue sakamakon
Ranar Jumma ce,Riga da wando dinkin zamani kansa kuma na aza mai Hula zanna bukar
kafarsa kuma Takalmi ne baki budadde na Fatar damisa,Hannunsa sanye da agogon Fata
na kamfanin Rado,Kallo daya zakamai sai ka kara saboda yadda yayi kyau sosai
Fuskarsa Na fitar da Annuru kyau da koshin lafiya.

Muna tafe ina Duba Wasu jerin turaren miski,na Sunkuyar da kaina ina Fadin"Na siya
mana miski..? Na fada ina kallonsa Kallona yayi kafin ya Lumshe idanuwansa,dariya
nayi kawai na Daga hannu zan Dauko ni ban ma Lura da mutanen dake wajen ba sai ji
nayi ance"Wanake gani kamar Mr bello..."Aka Fada Daga gabanmu cikin Sauri na Daga
kaina ina kallon mai mganar Ido na Zaro ina kallonta Lokaci Daya nace"Anty Jidda
madaki.."

Nafada cikin Bayyana mamakina,Hankalinta na wajen Bello sai kuma taji muryata cikin
Sarkewa Numfashi tace"Anee...Aneesa Bukar Bulama u again..",Tafada tana nunani
cikin Farinciki muka isa ga Juna muka Rumgume,Cikin Fara"a Ta Dagoni tana
Fadin"Anee kin girma fa sosai yanzu anyi hankali ko..? dariya nayi mata ina gaida
wanda suke tare har su Modibbo suka kariso hannu na ta Rike tana Fadin"Meye haka
Anee..? Yana ga Mr bello kuma bisa Wheelchair..?

Tafada muna kariswa gabansa niko sai binta da kallo nake ganin ta kara kyau ta zama
babban yarinya,kafin na bata amsa Modibbo yace mata"Ayyah...Baya da lafiya ne Tun
bayan wata Takwasa Da suka Suka wuce yake Rayuwa Ahaka.."Ido jidda ta Zaro tana
kallon Bello lokaci Daya tayi kasa Agabanshi idanuwanta na Taruwa da kallo cikin
Sarkewar murya tace"Innalillahi meya sameshi Hatsari yayi..?

Na girgiza mata kai kafin tace"Ba daya...Daga dare zuwa safe ya tsinci kansa cikin
wannan Hali watansa uku akasar india an Dora misa Gwaje gwaje da kuma Ayuka har
guda biyu ammh kuma babu wani cigaba shiyasa aka dawo dashi gida ana gwada na
Islamic har Allah yasa a Adace..."Hawaye suka zuboma jidda ta dago tana kallon
Saurayin da Suke tare Hannunshi ta Riko tana Fadin"Habibi Da"iman kalleshi shine Mr
bello dana ke baka lbrin He si my Fisrt luv shina fara so Tun bansan kaina ba..Ka
tuna ina baka lbrin He is handsome,brilliant,..Ammh kalli yadda yau Allah ya
maidashi.."Tafada tana kara gudan Hawayenta,kusa da ita ya Durkusa yana Fadin"Allah
sarki...Sannu Allah baka lafiya a head alot abount u Awajen Jidda my Wife to
be...nice to meet u.."Yafada yana mikamai hannu Shuru yayi yana binsu da kallo
Aneesa ta kama hannun Bello ta mikamai tana Fadin"Bazai iya baka hannu ba sai
dai...Kai ka kama nashi.."Tafada cikin wani yanayi Cike da Tsausayi ya kama hannun
nashi yana Mai sannu da Jiki,kafin su mike yana Rike da Hanmun Jidda Jakarta ta
Bude ta ciro katin bikinta tana Fadin"Here is my Weeding programme Anee,ina fatan
zaki zo ko..? Kai ta girgiza kafin tace"Ban miki alkawari ba...In na tafi baizai ji
dadi ba.."Da mamaki ta kalleta kafin tace"Meyasa...?

Cikin Wani kallo Aneesa tace"Saboda Mijina ne..."Ido jidda ta waro tana Fadin"Are u
sure..? Modibbo yace"An daura musu aure ba dadewa Lalurar ta sameshi.."Cikin Wani
yanayi jidda tace"Allah Sarki...Anee dama na taba fadamiki watarana Kiyayyarki ga
Mr bello zata Rikide ta koma soyayyah Allah ya bashi lafiya.."Suka amsa da Ameen
kafin su rabu sai da suka karbi Nombar juna,suka rabu jidda na jadaddamata zata zo
har gida suka wuce suma suka cigaba da Tafiya,miskin da bata dauka ba kenan sai dai
suka karisa wajen Ruwan Zamzam tana kokarin Daukowa taji muryan wata Abayanta tana
Fadin"Feedy kalli Namiji har Namiji ga kyau da Zati ammh ya nakasa.."Tafada tana ya
fito wacce suke tare Lokaci Daya tana Nuna mata Bello.
Fasa Daukan Goran Ruwan Zam-zam din tayi ta waigo afusace kamar wata zakanya tana
bin yanmatan da wani matsiyancin kallo cikin Masifa tace"Ina ruwanki da mijina da
zaki dinga Gulmarsa har kina nunashi a kalle shi..? Uban wa yace miki mijina
Nakashashe ne,Shegu kawai yan iska masu kallon mazan mutune.."Na fada ina jijjiga
jiki tsayawa sukayi suna kallona Modibbo da Raihana suka kariso suna Bani Hakuri
shiko yana Zaune bisa kekensa yana kallo yana so yace na bari ammh bashi da baki.

Wacce aka nuna mawan ne ta kalleni ta saki wani Shewa tana Fadin"Au Ashema mijinki
ne..? Su masu miji an ji jiki wlh.."Wlh kin ci Sa"a mijin naki dakike hakilo
akanshi bai da mamora kemabai miki ba balle ni,da wlh sai nanuna miki ke karamar
yar isk..."Bata karisa ba na saka Hannu na Tsinketa da mari Lokaci Daya naci kwalan
Riganta ina Fadin"In kika kara Fadin mijina bai da Mamora wlh sai na Datse miki
harshe...Kin ci sa"a kura tayi lafiya da lokacin da nake amsa suna Aneesa bukar
bulama ne wlh da yau kin gane kuranki banza sakaara kawai.."Nafada ina Huci lokaci
Daya ina Ingizata baya ta Fada jikin yar"uwanta,

Dafe kunci tayi tana kallona cikin Mamaki Raihana ne da Modibbo ke basu hakuri niko
ko ta kansu banbi ba na isa ga Mijina na Shiga Turasa ina masifa ni kadai kamar
Wata Zararriya bansa ya suka kare ba,nidai abakin mota suka sameni ina ta bala"i ni
kadai shiko yana Zaune yana ta bina da kallo,Su modibbo na karisowa Rike da ledojin
shooping din da mukayi ina ganinsu na Fara masifa ina Fadin"Meye na basu hakuri..?
Bakuji me suke fadi ba shegu yan iska kawai wlh sunci babbar Sa"a da ace ada ne wlh
sai na koyamata Hankali.."Ta inda nake shiga bata nan take Fita,kawai sai naga sun
kalli juna sun kwashemin da Dariya Raina ya baci harda Hawaye na Bude bayan mota
ina Tura baki na Shiga kici kicin Sauke shi na sakashi cikin mota,Da Sauri modibbo
yazo ya taimakamin muka sakashi cikin mota,shi kuma ya Nade Wheelchair din ya saka
Cikin Booth,Raihana ta shiga gaba Shi kuma Modibbo ya Shiga bangaren Direba muka
bar Mall ina ta Tura baki da bata rai kansa na kam cinyana ya dameni da kallo ammh
naki bari na Mu hada ido.

Har muka koma gida ban saki Fuskata ba,Raihana ko da modibbo da sun kalleni sai su
saka Dariya Sai na kara kufuluwa,Har ta tafi gida ban Shiga Harkansu ba,Da na tuna
sanda naji suna yabamin miji sai naji wani bakiciki ya cika ni haka in na tuna
sanda tace wai namiji har Namiji ba mamora sai naji kamar Zuciyata zata Buga saboda
Takaichi har na gama mai Abubuwan da nike mai kafin mu kwanta,ban yarda mun hada
ido ba Ranar ma wajen kafafunsa na saka kaina ina tura baki kamar wata
yarinya,kamar shi yayimin laifi ko ina ruwan mara lafiya.

Har Washegari ban saki ,Fuskata ba Fara"a ko kadan,Modibbo kuwa bai takaleni ba,sai
da Raihana tazo ne na dan saki kadan,har na warware,Shiko Bello cikin Ranshi ma
Dariya nake bashi ganin irin salon kishina,Ransa na masa Dadi in ya kalleni
Zuciyarsa ta gama Tababbartamai ba iya tsausayinshi nake ba har da soyayyarsa kamar
yadda Nawa Son yayi mishi kamun kazan kuku.

*****

Haka muka cigaba da Rayuwarmu cikin jin Dadi da kwanciyar Hankali,Duk bayan sati
biyu Ya muktar kan zo ya Dubamu ya barmana kudi duk da bamu da bukatar komai na
bangaren Rayuwa sai dan Abunda ba"a rasa ba,iya kula muna samu ba laifi Modibbo da
Raihana sun taimaka wajen Debemana kewa sosai,Bello kuma nine Farincikinsa Komai
nakeyi yana Nanike dani ko kichen nake ina girki muna tare yana kallona Modibbo da
Raihana kullum cikin mana Tsiya suke wai wannan irin Luv haka Sai dai na Zabga musu
harara bana bi ta kansu ba.

B.kaita ta kirani awaya take Fadamin sun Dubo Resuilt dinsu ita da Salamatu
jibiya,kuma Alhamdulillah sunci duka,har ma zasu Rubuta jamb,in suka ci zasu shiga
jami"a nayatasu murna sosai,ammh ni na gayamusu ban Dubo nawa ba domin baya gabana
Tunda ko na Dubo ba wani amfani,kula da Mijina Shine Aikina da kuma jami"ata,
Achan borno,kuwa Anty Nafee sai da tayi magana dataji wai har mun koma kano har ni
ta kira naki Dagawa Domin kiran Anty Nafee bana alheri bane,ina gani naki Daga
kiranta bana son ta Dagamin Hankali ina Zaune lafiya Nida Mijina,aiko tayi ta
zagina tana fadin ta cire bakinta,akaina naje na karata babu Ruwanta Ba wanda ya
gayamin ni kuma ban damu domin Anty Nafee bata gabana ko Cikin yan"uwana dama bama
da wani Shiri sosai.

*****

Yau tun safe dana tashi naji ina kwadayin koko da kosai,Tun bayan da nayi sallar
Asuba ban koma ba,Bayan na ma Bello wanka na Shiryashi cikin riga da wando black
and white na kamfanin Armani,Da zan tafi kichen ya chanza fuska sai na Turasa muka
tafi tare.

Ina sanye cikin Riga da wando na pakistan kaina yana Daure cikin Gyalen kayan,yana
ta baya ni kuma ina gaban gas din ina ta faman Juya kosai gefe daya kuma na saka
ruwan zafi,na dauko Wata karamar roba inda na Dauko garin kuni na wanda na saka
Raihana tazo min dashi Daga Gidansu,Bayan na kwashe Kaskan farko na zuba wani,sai
na koma wajen Dama kokon na Dauko karamar tukunyar da ke cike da Ruwan zafi kawai
tsautsayi sai Hannu Daya ya Subuce Ruwan ya kware,da Sauri na saki Tukunyar nayi
tsalle gefe ina Sakin kara,lokaci daya ina yarfe kafata inda Ruwan ya Tabeni ina
Hawaye cikin Son ya mike ya kasa Cikin ikon Allah kawai naga ya Daga Hannnunsa na
Dama yana miko cikin Razana da Tashin Hankali.

Ai mancewa nayi da Kunan danayi na isa gabanshi da Sauri ina kallon hannun nashi
Dayake mikomin cikin hawaye nace"Kalli fa..ka daga hannunka..."Nafada cikin mamaki
yana Rike hannun Shima kallona yake yana kuma bin Hannun nashi da kallo,Gudu na
kwasa zan Fita muka ci karo da modibbo yaji ihu na ya Fito cikin Tashin hankali
yace"Matar baffale lafiya naji kamar ihunki.?

Ina Haki ga hawaye afuskata nake Fadin"Kalli modibbo ya yi motsi da hannunshi harma
ya Daga,duba kagani.."take fada tana nunamai hannun Bello wanda haryanzu yake ta
motsi dashi cikin Farinciki da Sauri ya karisa garesa yana Fadin"Allah mai iko..Wlh
da gaske. Kuwa..! Yafada cikin murna da Dariya Bansan sanda na isa kusa dashi na
Fada jikinsa na Rumgumeshi ina Murna kamar amafarki naji ya saka hannunsa guda
dayan ya Rumgume bayana dashi,saboda Farinciki bansan Lokacin dana kai bakina saman
bakinshi namai sumba mai tsawo ko modibbo banji kunya ba Shiko cikin Farinciki ya
shiga turamu nida shi Saman Wheelchair din yana Dariya har zuwa falo.

Nida Modibbo akasa rasa wayafi wani rawan jiki wajen kiran Waya,ni Daada na fara
kirana ina murna ina gayamata shi kuma Modibbo Ya muktar ya kira ya Fadamai
gabadaya lbrinmu ya Sanyaya musu rai,haka Ya muktar ya kira modibbo Video
call,bayan ya koma gida suka hadu dasu Daada suka gani suka Tabbatar,Farinciki ya
cika zuciyar Daada Data ya muktar sai da sukayi kwallah lalle mai Rai kar ya cire
hop,shi kuma Bello Ranar Wuni yayi Daga hannu yana Tunanin kamar in ya maida zai
koma ya kwanta kamar baya,Allah Sarki....

Ki biya ki karanta cikin Salama...

*Anitha...*
8/19/20, 11:22 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?28*

Ashe haka kowacce mace takejin Farinciki in Wani Abun cigaba ya samu
mijinta,Hakance ta faru dani domin nafi kowa murna nice lbri har Borno na kira su
Mama yana ina sanar dasu suma sunyi murna Mama falmata ta sake bani Shawaran na
Dage kar na Nuna gajiyawata da Kula da Bello Watarana zai mike ya taka da kafafunsa
kamar bai taba irin wannan ciwon ba...

Hakama Daada cikin Farinciki tayi waya chan Adamawa tana Labartama Baffa Hardo
cigaban da aka samu shima yana Nuna Tsantsan Murnan,kuma yace acigaba kar
afasa,shima yana nan yana tayasu da addu'an Allah ya karya koma menene,saboda jin
dadi Kwana uku da Faruwar Haka sai ga Ya muktar dasu Daada sunzo,Sunga ko Abun
mamaki Domin Yana iya Rike abu mara da Nauyi da Hannun,Har Junior dake hannuna sai
da ya rikemai hannu Muko gabadaya Farinciki yaki barin Zukatanmu nan suka kwana sai
washegari suka koma Abuja Sunbar Hibba agida saboda Makranta wajen Jummai.

Ganin irin Cigaban da Aka samu ne ya sanyani na Dage da Karatun Qur"anin da nake
mana Duk Dare kafin mu kwanta bayan Ruwan zamzam din da Baffa Hardo ya aiko Daga
Adamawa nima ina yin nawa na Tofe da Addu"o'i na bashi yasha kuma na Shafemai duka
Jikinsa Safe da rana da yammah,Fatana kawai Watarana Naga Mijina ya mike da
kafafunsa kamar kowani Namiji mai Cikar zati da Haiba.

Samuwar lafiyan Hannunsa Guda Daya sai yabashi wani karfi,ko Wucewa nazo yi ta
gabanshi yanzu zai saka hannu ya jawoni na Fada kan cinyarsa ya saka hannu ya
zagayo dashi Daga bayana yana Kallona domin na lura har karkacewar kan daya keyi
yanzu ya Rage hakama Zubar da miyau sai mu Wuni kansa bai karkace ba,Ko wanka nake
mai ina kokarin kauda kai bana so mu hada ido ammh sai ya Shammace ni ya Fizgoni na
Fada Jikinsa,ya Kuramin ido yana kallona Ni kuma Duk kunya sai ta kamani na Dinga
Hararansa ina Turamai baki.

Yana kokarin taimaka min in zan Rikosa,sai ya rikeni da hannu Daya wani lokacin in
na Dafa bango mu iya tsayawa in ko ban Dafa ba sai mu tafi kasa,nafadamai ni dashi
muna Haki,Duk lokacin da Na tsinci kaina bisa kirjin Bello sai na samu kaina cikin
wani Farinciki mai girma wanda baya wuce misali,Yanzu salon daya koya da daddare in
zamu kwanta bayan nagama shafemai jiki da ruwam zamzam sai yarike hannuna gam,yana
kallona ya nace sai na saka idanuwana cikin nashi wanda suke kashemin jiki na Fada
jikinsa bansani,Haka zan lafe bisa kirjinsa ina jin Bugun Numfashi,Zuciyata na
bugawa,Haka zai sanya Hannun sa mai lafiya ya zagayo Kuguna Dashi,kawai shi dai
yajini cikin Jikinsa yana sanyanshi Natsuwa sosai ni kuwa Bugawar Zuciya yake sani
jikina ya mutu..Gabadaya na kasa katabuka komai kamar mara lafiya.

Tun bayan Hannunsa Guda Daya Fara samuwa,babu kuma inda Shima yamotsa bayan
Hannu,muna dai cigaba da gayama Allah,jidda ta cika alkwari munyi waya da ita tazo
kuma har gida tare da mijin da zata Aura basu dade ba suka Tafi bayan ta kawo mana
kayan ciye,ciye dama Tun Ranar da mukayi fada da yan matanan na Shopprite ban kara
marmarin komawa ba Ko Raihana da Modibbo sunce bazamu Fita bane,sai na Daure Fuska
nace bazamu kara Fita ba in zasu ne su daawo lafiya Duk ko naga Bello na jin Dadi
in muka Fita niko na Dakile Haka saboda basai mun Fitan bane balle har Wata mace ta
ganshi ta yaba ko kuma tace mai baida Mamora ba Shidai sai dai ya kalleni kawai
cikin Ransa yana Mirmishin komai na Aneesa bai chanza ba.

****
*KATSINA*

Tun last Week Kasim ke gida,Yana Hutun karshen Shekara wato Annual Leave kenan,har
kuma Zuwa wannan Lokacin bawai kasim ya Daina Neman matanshi bane da Shaye shaye
a"a sai ma Abunda yayi gaba Shiyasa bai cika zuwa katsina ba saboda baya samun
yarda yake so..yafi jin dadin Rayuwarsa Abariki kaduna.

Neman matan nasa ma ya karu ne bayan ya rasa Aneesa wacce ko Da Rana daya Sonta bai
ta Fita Daga Ranshi ba,yana jin Duk Duniya in bai Dandani Zumar Aneesa ba bakinciki
da Sha"awarta zasu iya kasheshi,yan mata kuwa Da inda yaga Baka doguwa shikean kuma
Zai tayaki dakin sallama Shikenan in kuma suna cikin Harkan ne sai ya fara kiran
sunan Aneesa yana ihu kamar mahaukaci Yanmatan Shashancin nashi suna matukar mamaki
wacece wannan Aneeesa da Kasim yake kiran sunanta in suna Tare,shi kuwa sai in ya
gwada su da Aneesa ne ma yake samun jin Dadi ammh in ba Haka ba ko alama Zuciyarsa
basu kawomasa jin dadi da kowacce mace sai Aneesa.

Cikin Lokacin ne ya Hadu da Wata Aisha Maiduguri,Saboda yanayinta da Aneesa gasu


kuma yan gari Daya ya sanya Suka Dinke itama karatu tazo nan kasu,tabi Rudin Duniya
ta lalace Duk Soyayyar kasim din ne ta Rinjayeta atakaice ma Shine ya Fara saninta
amace bayan ya mata alkawarin zai aureta,Haduwarsa da Aisha yasanya take debemai
kewar Aneesa Domin suna da yanayin Tsarin Halitta hatta bakinsu Kuma itama
cikakkakiyar kanuri ce,Agidanshi ma take da zama suna Sheke ayarsu karatu kuma sai
tayi sati bata shiga cikin makaranta ba Allah ne ya Doramata soyayyar Kasim Acikin
Ranta mai zafi wanda takejin in babu shi bazata iya rayuwa ba,saboda ita baya son
zuwa gida yan zuma hutu suka samu Dakyar ya lallaba ta tafi gida akan zai zo insha
Allahu,shiyasa tatafi shi kuma yazo gida ammh cikin ranshi baya jin zai iya Auran
Wata mace bayan Aneesa wanda duk kwakwan Aisha ta kasa gano wacece Aneesa Awajen
kasim abunda ke bata mamaki ko giyanshi yasha ya bugu har ya Dawo hayyacinsa yana
kallonta amatsayin Aneesa ne,in ko suna Masha'arsu Ya dinga Kiranta Aneesa kenan
abun na damunta in kuma ta tambayeshi baya gayamata,alhalin kuma hatta Fuskar
wayarsa Hoton Aneesa ne Ko Haruna Dayake abokinsa tayi tayi ya Sanar da ita yaki
saboda Kasim bai bashi da damar Haka ba tasha yin Fushi da Bar gidan ta koma
mkranta ammh kasim baya Damuwa da kanta take gajiya ta dawo kalmar Daya yake
yagamata albarkacin Aneesa take ci in ba haka da yanzu ya Rabu da ita jin haka yasa
ta Shiga Taitayinta domin bazata jure ganin Rabuwarta da kasim ba,Tunda ta lura ma
kamar Aneesa bata kusa dashi sai take kokarin Danne kishinta akan Aneesa kodon ta
samu cikar Burinta.

Wannan karon ne ya yi niyyar Zuwa gidan Ya muktar ya Duba Bello kuma yaga Aneesa
bawai don Abba kabiru ya matsamai ba sai domin yana son ya kara Tozali da Aneesar
bayan Kwashe Shekara bai saka ta cikin idanuwansa,Su Abba kabiru bama su san Bello
ya koma kano sun koma kano ba Duk da shi Kasim yana da lbrin komai toh bazuwa
sukeyi ba,Dama saboda Zullumin Bello ne toh yanzu basu da wani mtsala da
hakan,Gabadaya ma Dukiyar da suka hamdama ta kare dama kanfani Daya ne ya Rage
shima bashi ya saka sun saidashi batare da sunga ma wanda ya siya kamfanin ba.

*****

Da yammah ya Shirya cikin Riga da wando black and White na kamfanin DKNY,ya tafi
gidan Ya Muktar koda yaje bai sameshi ba sai dai Anty Rahila duk da yasan Su Bello
basu agidan,sai ya zauna suka gaisa da Anty Rahila cikin Hikima ya Hillaceta da
cewa yazo gaida Bello ne sai tace ai suna kano ya nuna jimami sosai nan take yace
ta bashi Addreess din gidan nasu dake kano bata kawo komai acikin Ranta ba ta bashi
bai jima ba yatafi ko Shashen Daada bai shiga ba,yana Sauri harda bata 5k ta bama
Junior ta karba tana ta godiya duk da tafi karfin Haka ammh alheri nada Dadi.

Yana cikin mota yana Dariya Shikadai cikin Muryan Tsausayi yake Fadin"Aneesa...Ban
so nayi miki Haka ba,buh ammh ke kika Nuna Taurin kai kinki gane Cewa Nine mai
sonki har Abada kika zabi ki Zauna da nakashasshe Saboda Taurin kanki..Zan Ji dadi
Dake kuma agaban idanuwanshi ina Fatan Hakan yayi sanadiyar Bugawar Numfashi ya
mutu...Ki zama tawa har Abada."Yafada Idanuwansa na kadawa Lokaci Daya kuma ya kece
Da Dariya kamar mahaukaci yana Buga Sitiyarin Mota.

****
Yau Tunda na tashi najini bana jin Dadi ganinan ne dai ban gane kaina ba,Dakyar na
iya mana Breafsat,Tun safe Modibbo baya nan ya fita Jugging ni na saka mayafi na
kaima Salihu maigadi na Shi na Dawo cikin gida,Bello kadai nayi ma wanka na
gyarashi ni kuwa kaina ne yamin Nauyi Sosai,Lokaci Bayan Lokaci kuma gabana sai ya
Dinga faduwa

Muna cikin bedroom dinmu Ina Zaune Bisa gado shi kuma yana Gabana Bisa Wheelchair
dinsa ina bashi Soyayyen Arish din dana mana da kwai ina Hadamai da Kofin Tea din
dake hannuna,Tun da muka tashi ya lura bana walwala kamar bana jin Dadi yana ta
nacin kallona ni kuma bana so ya Fahimci wani Abu yanzu nan duk zai Shiga damuwa.

Kofin tea din na Kai bakinshi da Sauri ya saka hannunshi mai lafiya ya Rike min
hannu Lokaci Daya yana kallona ,Marairaicewa nayi kafin nace"Kasha mana..? Ko ka
koshi ne..? Bai min wata alama ba illah ido kadai Daya sakarmin ganin Haka sai na
zame hannuna na Dauki Kofin Tea din da Filet din Dankali na Fita Dashi Zuwa kichen
na Dawo,Ina Shigowa jiki na rawa na Nufi gado jin Kaina kamar zai Zage gida biyu na
Fada ina Sauke Numfashi cikin damuwa yake bina da kallo yana so ya tambaye ni meke
damuna ammh kuma bashi da baki tasani kadai yayi yana ta kallona..

Ganin kwanciya bazai min bane ya sa na tashi ina Rangaji na Bude Side drower din
gadon na Dauko Pracetamol na balla guda biyu na Sha da Ruwan zam-zam Din Bello Dake
saman Side drower din gadon na koma na kwanta ina Runtse dafe da kaina Lokaci Daya
naji ya Sauke Ajiyar Zuciya Dagowa nayi ina kallonsa Cikin Fitar hawaye
nace"Kaina...ke ciwo B.love.." Dama Haka nake cemai,Ido ya sake kuramin yana
kallona cikin Zuciyarsa yana Fatan Allah sa ba aljanun dana kwaso amkaratan bane
suke neman taso min,ina nan kwance ina juye juye kaina kamar zai tsage gida
biyu,Kuka nake ahankali lokaci Daya ina Salati Ya Shiga damuwa da Hannun Dayan ya
ke Danna Abun kekensa ya Shiga Turashi Zuwa gaban gadon Danike sai dai ji nayi ya
Dora hannunsa Bisa goshina da Sauri na Dago kaina Jajur ina kallonsa kamar wata
mayya,shi kuwa cikin Zuciyarsa yake karantamin addu"a,Cikin ikon Allah sai naji ya
Fara Sauka natsuwata na Dawo wa jikina Zufa na ketomin ko ta ko"ina Hannunsa na
Rike ina kallonsa Hawaye na bin gefen Kumatuna nace"Nagode garkuwata..."Lokaci Daya
kawai naga ya sakarmin mirmishi har Kumatunsa ya lotsa da Sauri na mike Zaune har
ina Bige masa kafa na tallafi kumatunsa na Duka hannayena Guda biyu ina Fadin"Kaga
mai kayi..?Mirmishi fa kamin.? Sau biyu kenan kataba min mirmishi Don Allah karamin
nagani.."Tafada Lokaci Daya hawaye na Zubomin.

Kallona yayi kafin ya saka hannunsa yana gogemin kwallah Zuwa Saman goshina yana
Sharemin Zufa,Kaina na lamgwabe ina kallonsa wani madaran kaunarsa na kara shiga
Raina hannunsa na riko na Sumbata Lokaci Daya na matse Bisa Kirjina ina lumshe ido
Zuru yayimin yana kallona niko cikin Raina Fadi nake I love u B.love..."

Ban bude ido ba na,kara Sulalewa na kwantar dakaina Bisa Filo ina Rumgume da
Hannunsa,Shikuma bai cire ba illah ido Daya sakarmin Cikin kankanin Lokaci barci
yayi Nasaran kwasheni,Yana zaune yana kallona kuma bai yi yunkuri cire hannunsa
dana Nannade bisa Kirjina.

Barcin mai yi wani Nisa ba Na tashi sai lokacin naji kunya ganin yadda na matse mai
Hannu,Tashi nayi ina Kauda ido kar mu hada ido Shiko ajiyar ya Sauke ganin namike
garau na Fada Tiolet,wanka nayi na Fito,ganinshi Zaune yana kallona yasa na Isa
gabanshi na Dauko karamin Qur"ani na Budemai Suratul Bakara na saka mai ahannunshi
ina Fadin"Karanta kafin na Shirya kaji..? Bai min gaddaama ba ya karba aransa yana
mamakin wai zan mai wayau kar ya kalleni,Ina Shafa mai ina kallonsa ta Wutsiyar ido
shikuma sai ya maida kansa ya Jingina da Wheelchair dinsa kamar yana karatunsa
Harda mai da kai gefe ganin Haka yasa na Dauko kayana na saka Riga da Sikat na Less
mai kalan Blue da Pick,ina Tunanin hankalinsa na wajen karatu Ashe Duk Abun da nake
yana kallona sai zan Dago kai sai ya sauke idanuwansa kasa kamar bani yake kallo
ba.
Sai da na gama Shiryawa tsab nayi irin Daurin Zahra buhari na Daure gashina da
Band,wanda Raihana ta matsamin mukaje aka Gyaramin Kaina,nayi kyau sosai Harda jan
baki na Shafa da kwalli bayan na gama na juya ta gabanshi ina Fadin"ya kagani...?
Nayi kyau..?kuri yayimin da ido Lokaci Daya naga idanuwansa sun chanza launi Kasa
yayi da idanuwan nasa yana mikamin Qur"anin Hannunsa da Sauri na karba,Na maidashi
mazauninshi ina Fadin"Ko ka nuna alamun nayi kyau kuma fa wa kai nayi mawa kaima
kaji kanka amatsayin Namiji da matarka zata maka kwalliya kagani...."Ban gama
mitana ba naji ya saka Hannu ya Fizgoni na Fado Kan Jikinsa,.

yarr."Naji lokacin Daya Rike kuguna da Dayan Hannunsa Dagowa nayi,Ina kallonsa
Lokaci Daya hancinmu na haduwa waje Daya,cikin idanuwan nake kallo Shi kuma yana
kallona cikin wani Shauki,Lumshe idanuwan yayi ya kara matsoni sosai ni kuma na
lafe ina Sauke Jiyar Zuciya bayan na saka hannuna na Dafe kirjinsa Bansan Lokacin
Dana Fara Shafa kirjinsa ba Cikin wani Salo,lokaci Daya ina kallonsa Idanuwansa ya
lumshe yana maida Numfashi sama sama,bakinsa ya Karkato kaina,Hancinsa na Fitar da
Hucin Numfashinsa cikin Wani Shauki da bansan ni Aneesa ina da Shi ba kawai naji
lebena saman lebenshi na Dora Lokaci Daya ina kallon kyakyawan Fuskarsa.

Mun Dade Ahaka batare da Nayi yinkurin yimai wani Abu ba Shi kuwa Jira kawai yaji
na Fara Sumbutar lebensa Tunda shi bazai iya Sarrafa bakina ba Ganin yadda naga
Zuciyarsa na bugawa yasa nayi Saurin Kwace Jikina na Tashi Daga kan jikinsa Lokaci
Daya kuma naji Muryan Raihana na kirana Daga Falo Ajiyar Zuciya na Sauke ina
Kallonsa Lokaci Daya ina Tura baki,Zuwa nayi gabanshi ina Hararanshi ban Lura da
jan baki Dana Shafamai saman kumatunsa ba,da kuma saman lebensa,na Shiga Turasa
Zuwa Falo.

Muma Fitowa Naga Raihana Zaune Bisa Cafet suna karyawa Ita da Modibbo baki na Rike
ina kallonsu cikin Dariya Suke gaisheni Harara na sakarma Raihana bayan na kai
Bello gaban Kujera mai zaman mutum biyu na Koma na Zauna bayan na juyashi yana
kallon Modibo.

Raihana ta Shagwabe tana Fadin"Ya modibbo wai me nayi ma Amaryan gidan ne take ta
Harara ta Tun Dazu..? tafada tana Dariya yana Tura kwai cikin bakinsa yace"Ah ina
zan sani Raiha..Kila Haushi Takeji Suna cikin Soyewarsu da Baffale kika
katsesu.."Yafada yana kallon Bello yana Dariya kasa kasa.

Itama Sai Lokacin ta Lura da Jambakin Daya bata ma Bello Fuska Kallon Juna Sukayi
suka kara saka Dariya na Harzuka na mike ina Hararan su cikin Bata Rai nace"Eh
din,wai ku lafiyanku kuwa kuna ta dariya kamar wasu Shashashun madina.."Raihana ce
tace"Gani mukayi Yau kwalliyar Ya Bello har da su jambaki ne."Sai da ta Fada na
kallesa na gani sai kunya ta kamani na Rufe Fuska na Kwashi Sauri Zuwa Daki Gabana
na Bugawa,Bisa gado na Fada ina Fadin"Karsu cemin wannan anyi zalamarmiya Mutum na
Zaune ba lafiya ina kwakwaminsa.."Wata Zuciya tace"shifa ya kwakwumuke Aneesa.."Ido
ta Runtse tana Tunanin Yanayin Lokaci daya ta saki Mirmishi ita kadai ..

Modibbo ko Da Raihana Dariya suka kara sakawa Shima Bello ido ya lumshe yana Dariya
Cikin Zuciyarsa,Sai da nagama goge kunyata kana na Fito ina Hade rai kamar su
karamin Wata mgana basu tankani ba sai Dariya kasa kasa,ban tankasu ba illah
Littafin dana maida Hankalina ina karantawa Kwana Sittin na Sumaiyyah
Abdulkadir,tun muna mkarata Nida su B.kaita muke taba karatu Dawowarmu kano da
Haduwata da Raihana yasa na kara gwanancewa,ita ke siyo min in sun Fita da
Modibbo,In ta karatu ina karantama Bello,Alhamdulillah ina karuwa sosai Musamman
Littafan marubuta na kamar su Halima Abdullahi k/mashi da Zulaihat sani
kagara,Rahma hassan Zaria,Sa"adatu waziri gombe,Sumaiyyah Abdulkadir Takori,gaskiya
Yana jin dadin littafinsu su ka kara sakani na kara zama mace sosai na kara wayewa
da sanin Duniya,nan ne nake kara koyon wasu girke girken,saboda karatun littafin ne
nagane cewa na kamu da matsananciyar soyayyar Bello.

Tunda ni ba Whatsop nakeyi ba B.kaita tayi tayi na Bude mu dinga Haduwa


Naki,Raihana,ma har Budemin tayi na goge gani nake Dana Fara Hankalina Zai Dauke
Daga kula da mijina.

Raihana ta tattara komai ta kai kichen ta Wanke min Duka Abubuwan Dana bata ta
gyaramin Kichen din,ta kuma Fito falo ta gyarashi tsaf ta yi mooping Ta goge Komai
na Cikin gida Harda Falon Farko na Modibbo ina jiyo Hiransu Daganan Don na Lura
suna yar gyada,Haka takemin koda yaushe In taga Aikin gida sai Ammi ta Turo ta
taimakamin Babu Abunda Zamu ce ga Uncle Aminu sai godiya Domin Sun mana komai
agarin kano Raihana ina jinta tamkar yar"uwata ta jini,Duk da Anty Aisha ma ta
yawan Zuwa Dubamu ita da mijinta.

Muna Zaune suka Shigo Modibbo an sha wanka wai zasu Fita Cikin gari,ko zamu Fita..?
Nace adawo lafiya ba inda zamu nida mijina muna gida Dariya suka samun Suna Tsokana
na wai ina kishi Bello ne shiyssa na daina yarda muna Fita tare na Tura baki ina
Fadin eh din haka suka Fice Ina Fadin suyomana Tsaraba.

Ko Minti goma Sha biyar basu yi da Fita ba na mike ina Fadin"B.love na kawo maka
Fruit? Ido ya kada min,Na ijiye littafin Hannuna saman kujera na Nufi kichen yabini
da kallo,ina cikin yayyankamai kankanan naji Shigowar Mota nayi Dariya ina
Fadin"Tsegumanmu ko sunyi mantuwa ne..? Duk azatona na Su modibbo ne.

Hankalina kwance na gama Shirya komai na Zuba bisa wani Filet mai Fadi na Dauko
mana karamin knife guda Daya,wanda zan bashi dashi nima naci Tunda ya koyamin Nima
cin Fruit ina Kokarin Fitowa naji motsin Shigowar Mutum Falon da muke ban kawo
komai ba na Fito ina Fadin"Meya dawo da ku..?ko kunyi mantuw...."

Sauran mganarne ta makale ne ganin wanda ke tsaye cikin Tsakiyar Falon,yana sanye
cikin Riga da wando Na Kamfanin Armani,Rigar jikinsa mai Dogon Hannu ce,fara mai
Ratsin baki haka wandonsa kafarsa baki me sai Rufaffen takalmin dake kafarsa,ya
kara girma da haske,Fuskarsa na cike da wani munafukin mirmishi Lokaci Daya yana
Kada key din hannunsa cikin wani izgilanci.

Filet din hannuna na saki lokaci Daya naja da baya ina Nuna shi da Yatsa bakina na
motsi..."K...

Ki biya ki karanta cikin Salama...

*Anitha...*
8/19/20, 11:23 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?29*

"KASIM....." Tafada muryanta na rawa Cikin kaduwa.

Mirmishin mugunta ya saki kafin yace"Yes princess...." Yafada yana Kura mata ido
cikin kallon Kurillah Cikin kwarewa a bariki Har wani Shafa sajensa na Fuska yake
Lokaci Daya yana Sakin Mirmishi.
Aneesa Da jikinta ke rawa ta juya tana kallon Bello wanda Gabadaya Hankalinsa da
idanuwansa na kan Kasim ne yana kallonshi cike da mamaki Lokaci Daya Kuma Tsoro ya
bayyyana akan Fuskarsa.

Kasa karisowa cikin Falon nayi illah kaina Dana Sunkuyar ina Raba Ido Duk da Nasan
kasim da Bello yan"uwan Juna ne ammh Jikina bai bani da Zuwansa awannan Lokacin ba.

Cikin Takun sa na yan Duniya yafara Taku Zuwa gaban Aneesa bata sani ba sai dai
kawai Taji Hucin Numfashinsa Bisa Fuskarta tayi kokarin Taja da baya yayi Saurin
Riko Habarta Lokaci Daya yana kallon kwayan Idanuwanta,Cikin Aneesa ya sake Daukan
Rawa Cikin Rawar murya tace"Don...Allah...Ka....Ka sakeni.."Tafada tana kokarin
kwace kanta,sai ma ya Hada da hannunta duka ya rike da Dayan Hannunsa,Yana Dariya
cike da mugunta ya waiwaiya yana kallon Bello Wanda Saboda Bacin Rai idanuwansa sun
Chanza Launi..

Cikin Wata Murya ya Shiga fadin"Kalli yadda na koma Saboda ke princess na rame na
lalace Tunda na rasa ki ban kara samun Farinciki ba,Ammh ke kalleki kina Zaune Babu
Abunda ya Dameki meyasa kikeda Taurin kaine..Kice ya sakeki Kizo mu Rayu Tare domin
Dani kika fi Dace bada shi ba..."Yafada cikin Muryan Rauni Lokaci Daya kuma yana
Sakarmata Makirarrun Idanuwwnsa wanda yake amfani Wajen yaudaran yaran Jama"a.

Itama kallonsa take Cike da Tsana da Takaichi kafin ta Daddage ta Fizge kanta
Lokaci Daya da Hannunta Tana Hararansa,Nishi take saki cikin Fada tace"Mallam ka
Fice mana Daga gida bama Bukatarka...Kuma ka Rubuta ka ijiye ni Aneesa Bukar Bulama
ko Yau aka wayi gari B.luv ya bar gidan Duniya Wlh Tallahi sai dai ka Mutu na Mutu
ammh bazan Taba Auran ba..Na Shafe Babinka Acikin Rayuwata sai Bayan Haka ta Faru
ne ma na Fahimci ko Abaya ban soka ba kasim kawai Wani Kadadaren al"amari ne Daga
Ubangiji yasa na amince Dakai..."Tafada idanuwanta Sun kawo kwallah..

Ran kasim yafara baci cikin Budewar ido yace"Kina Nufin Kindaina sona saboda wannan
Musakin Nakashashe mara amfani balle Mamora..?yafada yana Nuna Bello wanda ke Zaune
yanaji da zai iya tashi da yanzu kasim yazama sai Tarihi.

Wani mirmishi Aneesa ta saki kafin ta koma bayan Bello Tana Fadin"Eh...kaga
wannan,bata bashi Zarafin Mgana ba tacigaba da Fadin"Yafi ye min kai Sau Dubu
Miliyan Goma..Kai ne mara amfani kuma wanda baida Mamora ammh ni mijina Yana da
matukar amfani awajena da Kuma Rayuwata..."Tafada Tana Dawowa ta gaban Bello Ta
Tsaya Lokaci Daya tana Harde Hannuwanta Bisa Kirjinta.

Dariya ya saki harda Rike ciki kafin ya dago yana Fadin"Karya Kike princess Bazaki
Fada bane kawai Ammh kina Cutuwa Wata Mamaora awajen wanda ko kansa bai iya ma wani
Abun...princess ki bar wannan Maganar kizo mu tsara rayuwarmu Kibar wannan na Zaune
bazai iya yi miki komai ba,Ni ne Cikakken Namiji mai cikakken Mazantaka.."Yafada
yana kashe mata ido Daya.

Cike da Haushi Aneesa tace"Sai kayi kuma..Dama Ai mai Hali baya fasa Halinshi kayi
kuskure Tunanin Haryanzu kana Raina...Tuni na Shafe babinka Acikin Rayuwata,Kazo ka
Fice mana Daga gida tun kafin na Tara maka jama"a.."

Dariya kasim yayi kafin kuma ya koma Daure Fuska yana Fadin"Taurin kanki Zai ja na
aikata Abunda ba Haka naso ba princess..."Cikin mamaki da Tsoro take kallonsa Cikin
Kaasa kasa da ido yace"Yes...Na lallasheki kin ki jina,toh yanzu ai zakiji ni
dakyau...Naso sai acikin gidan Auren mu akuma kan gadonmu,zan Dandani Zumarki
princess,ammh kin kasa Fahimta ta Saboda Haka yanzu zan Karbi Abunda yake dama
nawane a gaban idon Wanda kike kira Mijin naki .."Yafada yana Sakin Siririyar
Dariya...

Aneeea data Tsorata Taja Baya Lokaci Daya tana kallon Bello Wanda Shima Fuskarsa ta
bayyana Tashin Hankali,ganin Kasim na Nufota yasa tafara ja da Baya Hawaye sun Fara
gudu Bisa Kuncinta Cikin Magiya ta shiga Fadin"A"a kasim kar kamun Haka Karka manta
Nifa matar Aure ce Don Allah karka ketamin Mutumcina..."Tafada Tana Hada
hannuwanta,cikin kuka.

Dariya ya saki yana Fadin"Ki adana Rokonki Nima bazanji kiba kamar yadda ke ma
kika jin nawa..."Ganin Ya kusa cimmata yasa tabi ta bayan Bello ta kwashi Guda Zuwa
Daki Zaraf ya Bita Cikin kwarewa ya saka kafa ya Tarota tatafi luu sai gata Bisa
Kirjinsa tana ganin Haka tafara kokarin kwaceta kanta tana Fadin"Ka sakeni mugu
kawai...Zan maka ihu zan tara maka jama"a.."Yana Daga mata gira yake
fadin"Dagaske...? Toh yi ihun mugani ko za"a iya kwatanki Ga Mijin naki nan Zaune
agaban idanuwansa zanji Dadi Dake In ya isa ya tashi ya kwaceki.."Yafada yana kai
kanshi Bisa Wuyanta kuka ta saki da kara Lokaci Daya Tana Fadin"Na shiga uku...Wani
ya taimakeni.. "

Take fada tana kallon Bello Wanda ke kallonta Idanuwanta Sunfara Zubar da
kwallah,Kokarin Tashi yake kakafunsa Suna rawa ammh ya kasa,Shiko kasim bakinsa
yakai wajen Wuyan Aneeesa yana Shinshina Lokaci Daya kuma yashafa Kanta gashin
kanta wanda ya Sabule mata Dankwali,zuwa bayanta da Tudun Kugunta yana wani lumshe
ido kamar Tsohon maye,Aneesa ta kurama Bello ido Hawaye na Zubomata Hannunta ta
Mika mai cikin Kuka tace"Ka taimake ni...Kada ka bari ya ketamin Haddina don
Allah..."

Dariya kasim ya saki yana yana Tura kanshi Cikin Kirjinta Lokaci Daya ya saki
Numfashi yana Fadin'Bazai taba iya kwatanki ba...Har Abada bai da amfani..."yafada
yana Tura Aneesa Bisa Kujera cikin Dariya yake kokarin Balle Blet dinsa cikin
Farinciki,bai ankara ba sai yaji Anbugamai wani Abu Asaman keyarsa wanda ya kusa
shashi Faduwa yana ganin Jiri

Taga Taga yayi zai Fadi ya Sunkuya yana Rike kujera Da Hannu Daya,Dayan hannun kuma
yana Dafe keyarsa data Fara Zubda Da Jini,Da Sauri ya waiga yana kallon Bello Wanda
Ya saka dayan Hannunsa ya Dauki Wayar Aneesa Dake kan Kujera ya saita keyar Kasim
ya Bugamai,wayar tafadi gefe ta rabe,Aneesa cike da mamaki take kallon Bello Kasim
kuwa Dariyar Rainin Hankali ya saki yana Kallon Jinin Daya Tabo Daga kansa
yace"Au...Ashe kana da Mamora.."

Yafada yana wata Dariya kafin ya Juya yana kallon Aneesa Cikin Mirmishi yace"Bazai
taba iya hanani Kudirina ba.."Yafada yana Nufarta Cikin,Sauri tafara matsawa Jikin
Kujera ammh ya saka hannu ya jawota ya karisa Cire Belt dinsa ya Danneta yana
kokarin Hada bakinsu Waje Daya kara Aneesa ta saki taneman kwatan kanta Mari ya
kifa mata yana Fadin"wlh in baki tsaya ba Zan miki dukan Tsiya kuma na aiwatar da
kudurina..."Yafada yana lasan Wuyanta.

Kuka take tana Tureshi Bata Saki Wata kara ba sai Dataji yana Taba kasanta da
Hannunsa yana kokarin Cire mata Sikat din Jikinta karar Daya karade gidan gabadaya
Hatta Salihu maigadi Dake Zaune sai da ya mike Afirgice,cikin tashin Hankali yana
Kallon Cikin gidan.

Bello kuwa karar Da Aneesa Tayi Ita ta dinga mai amsa kuwwa acikin kunnansa
Idanuwansa suna ganin Dishi Dishi ganin kasim ya fara Kokarin Raba Aneesa da Rigar
Jikinta Cikin Mika Hannu yana Kokarin mikewa ammh ya kasa Sai kawai ji yayi ya
Furta..."Aneesa...!

Cikin Wani Amon Tashin Hankali Daga ita har kasim sai da Suka waiwaya suna
kallonshi Cike da mamaki,ganin Hannun sa na Dama yadagashi yana miko mata Duka
hannuwansa,Ganin Yadda kasim ya shagala da kallonsa ne yasa ta sakarmai cizo mai
Zafi adamtsen Hannunsa ya saki kara tayi Saurin ingijeshi Ta mike tana Sakin
Numfashi Tana kokarin gyara Rigarta Daya fara Sabule mata Cikin kuka ta Nufi bello
Daidai Lokacin kuma da Modibbo da Raihana da Salihu mai gadi suka Shigo.
Cikin mamaki Suke bina da kallo lokaci Daya kuma suna kallon Kasim Daya mike yana
Gyara wandonsa Cikin Dan Rudewa,Modibbo ya ware ido yana Fadin"Matar baffale wai
meya ke faruwa ne..? Mun shigo Salihu ke fadamana yaji ihu acikin gida wani Abun ne
ya Faru..? Wannan fa..? Yafada yana Nuna kasim.

Na kasa mgana sai kuka nake Ina kallon Bello Kukan Farinciki nakeyi bana Komai
ba,ban gama mamaki ba naga ya saka Duka hannuwansa ya Dago kafadata na mike ina
kallonsa Bisa Cinyarsa ya Zaunar dani Yana kallona Cikin wani yanayi Hannunsa Ya
sanya yana Sharemin Hawaye,yana kuma kallon Kwayan idanuwanta,Bani kadai ba Hatta
su Modibbo sun Daskare da mamaki Bamu kara Sakin baki ba sai da muryansa ta Daki
Dodon kunnuwan mu..

"Ku Fita dashi...Har Abada kar a kara bari ya sake shigowa gidan nan
Salihu.."Yafada cikin kasaitattaciyar muryan nan nasa mai Cike da amo da Zati,ai
sai modibbo yayi kasa kawai bayan ya kalli gabas,yana kwarara kirari ga
Allah,Raihanaa ma baki yaki Rufuwa,Haka Salihu maigadi dayayi kasa yana Fadin"Allah
Abun Godiya yallabai..bakinsa ya Bude.."

Kasim kuwa Jikinsa ne ya Fara rawa mai Hakan ke Nufi Bayan ance har Abada Bello
bazai kara mgana ba Balle Motsi da wata gaba na Jikinsa,Gabadaya Zufa ke
ketomai,ganin modibbo ya Nufi Bello ne yasa ya zare jiki ya Fice Ba wanda ya Lura
dashi ammh Bello na kallonsa Suka kuma Hada Ido Lokaci Daya Bello ya sakarmai Wani
Boyayyen Mirmishi.

Kasim har yana Tuntube ya Fice Zuciyarsa na Buguwa taya ya kuma Haka Zata Faru...?
Alhalin Kuma An Tabbatar mai da Cewa haka zai kare rayuwarsa Cikin Mutuwa ko
Rayuwa..? Cikin rawan Jiki ya Fada Motarsa ya Bata Wuta Allah ya taimakeshi Tun
Sadda Salihu maigadi ya Budema Modibbo get yana Cikin Rudani bai Rufe ba Shiya
bashi Damar Ficewa Da Gudu ko Da Salihu ya Fito ya fice maida get din yayi ya
Rufeshi yana Tunanin Duk yadda akayi Kasim ba Mutumin Arziki bane..."

Modibbo kuwa Bakinsa yaki Rufuwa Fadi yake"Baffale wai yau kai kake mgana..Allah
Abun godiya.."Yafada yana kwallan Farinciki Nima kwallar nake ina kallonsa shiko
kawai Mirmishi kadai yake sakarmana bai kara mgana ba Modibbo ya Mike Jiki na rawa
yana Fadin"Bari nayi ma Ya Muktar albishir..."Yafada yana Dariya nan take kuwa ya
kirashi yana gayamai Ya Muktar Dake Shashen Daada ya mike da karfi yake
Fadin"Midobbo bama irin wannan Waasan dakai are u Telling me d Truth...."?

Bai yi mgana ba Illah Saka Wayar Cikin Speaker Dayayi ya kanga ma Bello yana
Fadin"Gashi zai maka mgana..."Shima ya Muktar din wayar ya saka cikin Speaker
Daidai Lokacin da Bello yace"Ya Muktar....."Cikin Sanyin Muryansa.

Allahu Akbar.....Ai Dagashi Har Daada sai gasu sun Zube kasa Suna kwaroroma Allah
Kirari na Godiya da Yabo Cikin Hawayen Farinciki Daada ke Fadin"Zaka Tashi da
izinin lahi..Zaka taka da kafarka da yardan Ubangiji Megidana..."Cikin Mirmishi
yace"Ameen Daadata..."Ya Muktar yace"Gamu nan tafe yanzu...Gani nake kamar ba gaske
ba..",Daga Haka ya yanke Kiran Anty Rahila na Bedroom dinta Ya Muktar ya Shigo da
wannan Lbrin bayan ya Dagata sama yana Juyi da ita Cikin Farincikin Data Dade bata
gani ba.

Raihanaa kuma Yayanta ta kira Uncle Aminu ta sanar dashi Shima bai gasgata ba sai
da aka bama Bello yaji Muryansa,Nikuwa Farinciki ma ya Hanani mgana,Dakyar ya yarda
na Sauka Daga kan Jikinsa na Dauki wayata na Hadata sai gata ta dawo da aiki Mama
falmata na Fara kira na gayamawa Ita ma tayi Murna sosai Daga ita sai Ya Ali Shima
wai kin yarda yayi sai dai aka bama Bello sukayi Mgana Duk wanda yaji lbri sai ya
Jinjinama Kudaran Ubangiji mai Hikima da kari ga Mgana Lokaci Daya kuma Hannunsa na
Hagu ma ya Mike yanzu Abunda ya Rage kawai Shine kakafunsa da kugunsa Suma Insha
Allahu Komai Zai Daidaita.

Kasim kuwa Tun yana Mota ya Kira Haruna yana bashi lbrin Abunda ya gani Cikin
mamaki Haruna yace"Kai toh garin yaya Haka ta faru...? Kasim yace"Ban sani ba ammh
tabbas hannayensa Duka suna motsi kuma naji da kunuwana yayi mgana..."Cikin mamaki
Haruna yace"Ikon Allah...Gaskiya akwai mtsala Toh yakamata mu koma Muji Yadda Abun
ya koma Haka.."Kasim yace"Ya kamata Har Abada bana Bukatar ganinshi yana Taku
adoron kasa,yadda na rasa Aneesa Shima ya rasata har Abada.."Haruna yace"Ba mtsala
zan shigo katsinan sai mu tsara tafiyan.."Daga hakan kowa ya yanke Kiran cike da
mamaki.

Ya Muktar,Daada,da Anty Rahila Hibba da Junior wajen La"asar sai gasu Jirgi suka
Biyo Modibbo yaje Filin jirgi ya Taho Dasu,koda suka zo na sake ma Bello wanka na
gyarashi tsab yau wankan yasha Bambam Domin munyishi ne Cikin Farinciki,yana so mu
hada ido ni kuma Kunya nakeji,wajen samai kaya ma Jawoni yayi jikinsa Cikin
Muryansa mai cike da Izza yace"Bai miki komai ba ko..? Kallonsa nayi kafin na
Rausayar dakai na girgizamai kai,Ajiyar Zuciya ya Sauke Lokaci Daya yana maida
Numfashi,Miskili kenan Koda bakinsa ya Bude baiyi Mganar Data kai goma ba sai dai
kawai ya Dinga Bina da Ido......

Raihana ta taimakamin muka Shiga Kichen muka Dafa Musu Farar Shinkafa da Miya sai
slat,Sai muka hada musu da kunun Aya,Sanda suka iso ina wanka,murna kamar bakinsu
bazai Rufe ba Ya Muktar Rumgume Bello yayi yana Murna da jin Dadi Haka Daada,Hibba
ko da Junoir Duka kan Jikinsa ya Dorasu cikin Sanyin Murya yake Tambayan Hibba ya
makaranta itako Fadi take Uncle ka warke ne .? Kai ya gyada mata yayi yana
Mirmishi.

Sai da na Shirya kana na Fito Cikin Riga da Sikat,na atamfa Rumgume Juna Mukayi
Nida Anty Rahila da Daada Ya Muktar kuwa Fadi yake sannu da kokari Anee ta
Bello.."Mirmishi kadai nake ina Satan kallonshi wanda ke Sauraran Hirar Hibba.

Sai da akayi sallah kana aka baje Afalo aka ci Abinci Shidai ne bai ci ba Domin
dama baya wani Cin Abinci Sosai yana Zaune Bisa Wheelchair dinsa Yana bin mu da
kallo Kuma wani Ikon Allah Dagani har shi ba wanda ya sanar ma da kowa Abunda ya
Faru na Zuwa kasim muka ja bakinmu mukayi Shuru.

Kwana biyu su Daada Suka mana,Kafin su koma Bayan sun Biya gidan su Uncle Aminu Sun
kara musu godiya Harda Ya Muktar,Komawarsu Abuja dama Tun kafin su tafi Ya muktar
ya sa akawo masa Tirela guda na Shinkafa yace Duk arabama Mabukata tare da Addu"ar
Allah ya Kara bama Bello lafiya.

Daada kuwa Baffa Hardo ta kira tana gayamai Mirmishi yayi mata yana Fadin"Karki
damu...Tafiyarma Lokaci kadan ne zai zama Tarihi..."Daada taji Dadi sosai kuwa nan
da nan ta saka Suma Ya Muktar ya aika musu da Tirela guda na Shinkafa da masara da
Kudi arabama Dangi mabukata,tare da addu"ar Allah ya kara bama Bello lafiya.

Kibiya ki karanta cikin salama

*Anitha...*
8/19/20, 11:23 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400
ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?30*

*AFTER 1 WEEK...*

Duk wanda ya kamata yaji Abun Farincikin Daya samemu yaji Barin ma ni,Gani nake duk
wanda bai zo ya tayamu murna ba,ba masoyin mu bane,Hatta Uncle Aminu Dake lagos
yazo Yaga Bello ya kara Tabbatar da Idanuwansa Haka suka Sarke hannayen Juna Suna
Mgana Cike da Shaukin Abota da kuma Farinciki mai girma.....

Abba kabiru kuwa Abakin Ya Hashim yaji labarin Budewar Bakin Bello bai zo ba sai da
ya kira ya muktar din ta waya sukayi mgana hakama Abba garba,Shidai ya Hashim din
ne yazo har kano shima bai Dade ba ya koma,Zubaida ce kadai ta damu da Halin da
Bello ke ciki ammh banda Zulfa wacce Ta Dinga Godema ma Allah,Inna Rukayyah ma
Tunda muka zo kano bata leko ba Tun Muna Abujan ma Sau Daya tazo,ba wanda ya damu
Hatta ko Shi Uban gayyar Ya muktar Tunda Abun nan ya faru Hankalinsa ya koma kan
Bello toh balle Shi Gwarzon da basa gabanshi da Zuwansu da rashin Zuwansu Duk
Dayane shi awajensa,Kokarin da Shakikansa Sukeyi akanshi yafi komai yin Tasiri
acikin Ransa.

Bangaren kasim kuwa Haka ya koma katsina yana cizon yatsan Rashin Cimma Buransa kan
Aneesa,Da kuma Fargaban Samuwar Bakin Bello tare da Motsuwar wasu sassan
Jikinsa,gefe Daya kuma ga Aisha ta dameni shi da kira,Akan wai yazo gida ta riga
tagama gayama iyayenta komai akanshi Haushi ta bashi ya Rufeta ta daina samunshi
Sam,Yariga yasakama Ranshi bayan Aneesa babu wata macen da zai iya zaman Aure na
har Abada da ita sai dai ya Yaudareta yaji dadi da Jikinta kawai.

Kwana Biyu Tsakani Haruna yazo Suka Tafi chan kauyen Niger Delta suka samu Bokan
Suna mai Complain Abunda ke Tafe dasu ya dade yana Dube Dube kafin ya kora musu
Bayanin Halin da"a ake ciki ya sanar dasu Aljanu sunyi kyau Sosai akan Bello Domin
Jaki ne Da Ranshi aka Binne Acikin kasa bayan An Cire ransa ankawo masa nan ya
Asirceshi kuma yana Sarrafa Numfashinsa Tunda Sunce basu bukatar Bello ya Mutu
yanzu suna Bukatar yaciga da Rayuwa ahaka har Abada.

Ya sanar dasu sakamakon Addu"o" da kuma Tsarin Dake jikin Bello shi yake Dakula
Sihirin Har Jakin Dake cikin Rami yake iya Motsi da hannayensa ya kuma Iya bude
baki yayi kuka,Shine Dalilin daya sanya Bello bakinsa ya Bude Ammh ya sanar dasu su
kwantar da Hankalinsu Bello bazai taba Takawa ba matukar ba"a hako wannam Jakin
Dake Cikin Rami ba,Wanda kuma ba Mutum bane ya binne ba Aljanun ne suka yi aikin
Saboda Haka karsu damu Su koma kawai su zura ido Bello Haka zai kare rayuwarsa Sai
Ranar Daya mutu.

Da wannan Lbrin suka juyo gida,Kasim yaji Dadi dama Baya Burin Bello ya warke domin
in ya warke Har Abada bazai Samu Aneesa ba,Daya sanar da Haruna Zuwanshi kano Fada
ya shiga mai kan yayi kuskure Babba Da"ace Lokacin da su Modibbo suka Shigo sun
kamashi Dumu Dumu fa ya zai yi..? Bafa zai taba Fita ba Har Abada,Shidai Kasim Ba
wannan ne agabanshi ba yadda Aneesa zata dawo mallakinsa ne kadai ke yawo Acikin
Ranshi..

****
Abubuwa Dadama na Dawainiyar Bello ta ragu Domin yanzu da kanshi zai Tura kansa
Zuwa Tiolet in yana cikin matsuwa Tunda Wheelchair din nashi mai amfani da Abunda
zaka danna kacigaba da Tura kanka ne,sai dai in yana Bukatar wani Abu ya kwalama
Aneesa Kira tazo ta mikomai ko kuma ta taimaka mai yatashi,koda Bakinshi ya bude
Bai cika yawan mgana ba,Halinsa na nan ya Dawo sai dai yayi ta nacin kallona,yana
Min mirmishi Wani Lokaci..
Ni kuma sai na rage Shigemai ganin,haka ba kamar baya ba,Sai dai ban fasa Duka
Abubuwan Danike mai ba,Yanzu na Rage zama dashi ina mai hira kamar baya sai dai na
barsa da Modibbo afalo ni da Raihana mu Shiga ciki muyi ta Hira,sai in tatashi
tafiya Modibbo ya maidata gida,Miskilansa na nan In kaga ya bude baki sai in yana
Bukatar wani abu ga wani mugunta Daya samu sai nazo wucewa ta gabanshi ya saka
hannu ya Rikoni lokaci Daya ya Fizgoni Zuwa kan Jikinsa,Ina jin kunya da Nauyi
sosai shi kuma ko Ajikinsa sai ma saka Hannu da zai yi ya Rumgume Ni Ya saka kaina
Bisa Kirjinsa yana Sauke Numfashi haka zamu Dauki Lokaci sai yayi Ra"ayi don kanshi
yake sakina,lokaci Daya kuma ya Hade rai ko kuma ya kauda kai,Yafi son zama
abedroom ko yaushe in ba Modibbo yafito dashi Falo suna Hira ba..

Samuwar Hannnayensa Sai laptop dinsa ta koma tana Debemai kewa,Sai na Doramai ita
Bisa Cinyarsa yayi ta kallensa kallensa aciki wayarsa ne dai har yau take
akashe,Ranar ma wayata yace na bashi bansan me zai yi da Ita ba Ashe gabadaya
Hutunan mu da na dinga mana Lokacin Baya Duk ya Maidasu cikin laptop dinsa ban sani
ba,sai ranar mun shiga zan taimaka mai yayi wanka Bayan na Fito tunda nakan Shiga
na Taimaka mai da wani Abun ina Cikin gyaramana Gadon,na Daga hannu zan Dauke
Laptop dinsa na ci karo da Hoton mu Nida shi wanda na Taba Daukanmu Ina ta baya na
Sunkuyo da kaina ina Dariya na Daukemu Shine ma akan Fuskar Laptop din baki na Rike
ina Tunanin yaushe ya samu wannan Hoton,Ban mai mgana ba na Rufemai na Ijiyemai
saman Side Drower ina Tunanin kona mai mgana ma bazai bani amsa ba Sanin Halin
gogan nawa miskilanci da Aji.....

Haka Ranar Babu kowa agidan Modibbo ya Fita kuma Raihana bata zo ba Ranar Ammi bata
jin Dadi,da mukayi waya da Safe ta gayamin inajin ma Chan Modibbo ya tafi domin
Bangane musu ba Dagashi Har Raihanar,Bayan na gama gyara Falon na tsaftace kichen
din na wanke Abubuwan da muka taba,Na koma cikin Bedroom din ina Sauri yau ban
taimaka mai yayi wanka ba Nima Tun na Asuba ban karayi ba,Yana Zaune kan gado ya
Jingina Bayanshi da Filo guda Daya,Laptop ne agabansa yana latsawa,ina shiga ban
tsaya ba na shiga Tiolet na Hadamai Ruwan wanka na Fito ina Cire karamin Hijabin
Dake jikina,Wanda na Dora Bisa Doguwar Rigar Dake jikina mai Hannun Vest.gashin
kaina ya bayyana kalaba ce wanda Raihana ta kamamin Tunda bana son kitso kwata
kwata.

Cikin Sanyin Muryata nace"Muje ayi wanka ko..? Na fada ina kallonsa Lokaci Daya
ina Tura Wheelchair din gabansa,bai dago ba illah yayi man Banza na kallesa cikin
mamaki Lokaci Daya na Tura baki ina Fadin"Mgana fa nake..? Bai kalleni ba
yace"Shiwa kike ma mgana...? Yafada cikin Husky Vioce. ..

Ware ido nayi ina Kallonsa kafin nace"Kai mana..."Na fada cikin Shagwaba Mirmishi
yayi kafin ya Dago yana Fadin"Ni wa..? Na lura tun bayan fara mgana ta kika daina
kiran Sunana mai ma kike cemin B.luv ko..? Yafada yana min Wani kallo kasa kasa
Baki na Rike ina Zaro ido kafin na Juya ina Rufe Fuskata cikin Kunya Tattare Naman
goshinsa yayi yana Fadin"oya come here..."

Yafada cikin Muryan Amo,cikin Sanyi jiki na karisa gabanshi na Tsaya ina kauda
Fuskata laptop din ya Gauda Daga Gefensa Tunda baya iya lakwashe kakafunsa sai dai
ya mikar Tunda su haryanzu baya iya amfani dasu,ban ankara ba naji ya saka hannu ya
jawo ni Jikinsa,ido na Zaro ina Binsa da kallo Shima ni yake kallo,mutsu mutsu na
Fara yi Jina kusa da abar Domin naji tana harbawa Tsakanin Cinyoyina da kuguna.

Sake rikeni yayi kafin ya matseni Sosai har na kwanto Bisa Kirjinsa ina Sauke
Numfashi jin Ina Shiga Cikin Wani yanayi Muryata tana Sarke na Dago ina Fadin"Kar
na..Zauna kan kafarka tana ci..."Bai bari na karisa ba ya aza lebensa bisa bakina
Lokaci Daya yana kallona,Ban iya motsi ba Illah jikina Daya fara rawa Idanuwansa ya
lumshe kafin ya Fara Tsotsan Lebena na sama yana Hadawa dana kasa cike da kwarewa
nan da nan Jikina da Zuciya ta suka Fara karba sokonshi Tallafemin keya yayi nikuma
na Rike Rigar Jikinsa da Wuyamsa ina karban sakonsa Cikin Fitan Hayyaci,
Hannunsa Daya ya maida Bayana yana Shafani Daga Saman Wuyana Zuwa kuguna,yana min
tafiyar Tsutsa Tuni na Rikice na sake Rikeshi ina makarkyata Jin yadda yake Shafa
Tsakiyar bayana da Babban yatsanshi,kila ganin ina neman Fita Hayyacina ne yasa ya
Sakarmin baki yana kallon Cikin idanuwasa runtse ido nayi ina Rike da Rigar Jikinsa
da Hannuwa na Biyu Cikin Rawar Murya nace"Zan ta...shi..."

Nafada lokaci Daya Ina jin Sarkewar Numfashi,Kansa ya maida Cikin kunnina cikin
Sarkewar Murya ya Furta.."Ai bam hanaki ba,madam ke kika Ji Dadi kika Rikeni ko
baki gani bane..? Yafada yana sakin yar Dariya.

Da sauri na Bude ido ina kallon yadda na Rike rigansa da Sauri na Sakeshi na mike
ina Jin Kunya Gira ya Dagamin yana Fadin"Kunyar me..? Bayan kin gama
lafemin..."yafada yana kallon yanayinshi Ni kuwa ban Kula Dashi ba na Fada Tiolet
Cikin Jin kunya,Har na gama wanka Fuskata tana cikin Mirmishi ina Daure da Towel na
Fito ina ganinshi zaune inda na barshi muka hada ido na Turamai baki,na Wuce da
Sauri na Dauki Hijabi,na saka da Kallo yabini kafin yace""Malama kizo ki taimakamin
nayi wanka Tunda kin jamin.."Yafada kansa Tsaye.

Da Sauri na waigo ina kallonsa Kunu yasha Lokaci Daya yana Daga min gira,Kai na
Sunkuyar ina Rufe Fuska na kariso kusa dashi na taimakamai na maida shi saman keken
shi,ni na ciremai T.shirt din Jikinsa da Vest wando kadai na barmai na Turashi Zuwa
Toilet ina Kauda kai bana son muna Hada ido,ina kaisa na Juyo da Gudu na Fito ina
jinsa yana Kira na naki dawowa kunya kamar na Nutse wai Na sakashi wanka Lalle
nema.

Ban bari ya fito ba nayi Saurin Shiryawa na Fice Zuwa Falon, Shikuwa da gaske sai
da yayi wankan Tsarki kana yayi wanka ya Turo kanshi ya Fito dama yasan bazai ganni
ba,na gudu yar dariya yayi,shi ya tura kanshi gaban Madubi ,ya Shafa mai ya tura
kanshi Zuwa gaban Wardrope ya bude ya Dauko Riga da wando na wani Farin
yadinsa,vest dinsa da boxers dinsa wanda suke Daga kasa na Jeramai,Shi ya shirya
kanshi Tunda ko ya kirani bazan dawo ba,Ina Zaune afalo naga ya Turo kansa ya
Fito,kallona yayi yana Fadin"Kin kyauta..Kin sakani aiki kuma kin gudu kin
barni..."

Dariya na saka ina Boyewa kaina Cikin Cinyoyina Shi kuwa Cikin Kauna mai Tsanani
yake bina da kallo Ranar Wuni yayi Tsokanata ko kuma da mun hada ido ya Dagamin
gira yana Dariya Duk sai na Tsargu kunya ta hanani sakin Jiki.

******

Yau ta kama Asabar ne Tun Safe na tashi da aiki, Sakamakon Tun Jiya B.kaita ta
kirani tana Tafe,Tunda tun satin Daya gabata tashigo kano,ita da Salamatu Jibiya
sun zana jamb kuma sun samu Nasara B.kaita har ta samu Admssion,anan Buk zata
karanci Microbiology,ita kuma Salamtu Jibiya Tana Federal University Dutse Dukkansu
tun Wanchan Satin kowacce ta Wuto mkrta,B.kaita nan cikin Makaratan ta samu Hostel
take Zaune

Girke girke kala nayi mata Ita da Anty Aisha wacce itama suka dawo Daga Benin inda
Mijinta ke aiki,ta kira ni da safe tace min Zata zo anjuma ita da Megidanta,Raihana
tazo Tun Safe ta taimakamin Bayan mun gama Girkin ita na Barma gyaran Kichen Din da
kuma gyara Falon Duk da na gyara da Safe Daki na Koma na Shiga wanka ganin Bello na
kwance bai tashi ba,har nayi wankana na Fito ban Lura dashi ba Ashe Tun Shigowata
yatashi Daga barcin yana dai kwance ne yayi kamar yana barci.

Mai na Shafa agurguje Na Bude cikin Akwatunan da kasim yayi min na Dauko wata
Shadda Doguwar Riga,mai ruwan kasa,cikin Wardrope dina na Dauko bra da pant na saka
kafin na Zura Rigar,bai min mgana ba sai da na gama kwalliyata na Daura Dankwali na
waigo kenan muka hada ido yana Daga kwance kokarin Tashi yake na Taimakamai bayan
na sakamai Filo Ta bayanshi ina Fadin"ashe ka tashi..?

Nafada ina kallonsa cikin Lumsassun idanuwansa yace"Tun dazu ma.."Ido na waro ina
kallonsa Gira ya Dagamin yana Fadin"Yes Tundaga Fitowarki Wanka har gama
Shiryawanki.."Baki na Rike Lokaci Daya naja baya ina Buga kafa Cikin Shagwaba nake
Fadin"Ni..ni wlh ban yarda ba..Koda yaushe kai ta ganemin jiki.."Dariya ta kamashi
ya kanne yana Fadin"ah kajimin yarinya Ni bance kina min wayau ba sai ni..Tsaya Tun
yaushe kike ganin nawa Jikin .? Yafada yana saka hannu cikin bakinsa alamun Tunani,

Zaro ido nayi ina Dariya nace"Ni fa Bana kallonka idona nake kullewa sai na
gama.."Kafada ya make yana Fadin"ban yarda ba ko Yaya ne kin kalla dai.."Yafada
yana Hade rai Baki na Tura ina Fadin"Shikenan Tunda ka rama Daga yau bazan kara
wanka anan ba Dayan Dakin zan koma.."Zakuda kafada yayi yana Fadin"Bakomai..Nagama
ganin komai.."Kamar zan saki kuka Haka na juya ina Tura baki cikin Amon Murya
yace"Wannan kayan fa..?

Cikin Mamaki na waigo ina Fadin"Kaya kuma..? Kai ya Dagamin, bai yi mgana ba Cikin
mamaki nace"Cikin wanda Kasim ya bar min ne.."Cikin Daure Fuska yace"Ki cire rigar
nan yanzu ki sauya wata...Kuma kada ki kara saka min Kaya Daga Cikin kayansa ki
tattarasu waje Daya malama...."Yafada yana Kauda kai.

Cikin mamaki nace"in cire fa kace.? Bani da wasu kaya anan Duk suna Abuja.."Harara
ya sakarmin kafin yace"Nace ki cire ko..? Kuma karki kuskura ki sake amfani da ko
Tsinke Cikin kayansa Nagama mgana.."Yafada Lokaci daya yana dafe kansa,Kallonsa
nayi cikin mamakinsa na Bude baki zan Sake mgana kawai ya jefamin wani kallo yana
Fadin"Karki karamin Mgana malama...juz do as i say.."Yafada yana kokarin Zura Hannu
ya Matso da Kekensa da Sauri na karisa na tura mai,lokaci Daya na Saka Hannu na
Riko kafadansa na tayasa ya Sauko Daga kan gadon,ya Zauna Bisa Keken hannu na saka
ina Kokarin Taimakamai na Ciremai Rigar barcin Dake jikinsa kawai ya Ture Hannuna
bai kalleni ba ya Tura kekensa ya saka Hannu ya Bude Kofar Tiolet ya Shige ya barni
nan tsaye ina Binsa da kallo Tuni idanuwana suka kawo kwallah.

Rigar na cire na Sauya da Material Dingin Doguwaar Riga Itama Cikin Wanda Anty
Rahila ta Dinkamine gab da Bikina,Kwalliyar Fuska tawa ma gogeta nayi ina Tunanin
Toh miye Abun Fushi kuma..? Na dade Ciikin Bedroom kafin na Fice bayan Kiran B.
kaita ya Shigo cikin Wayata nan take Shaidamin Tana Buk raod din na mata kwatancen
Gidan,nan nayi mata Dayake muna bakin Titi ne

Ko Minti Goma ba"ayi ba sai gata ta iso ita da Wata Cousin dinta Aliya wacce Suka
samu Admission tare,Nan muka Rumgume Juna Cike da Farinciki,Dagoni tayi tana
Fadin"Kai Anee kinganki kuwa..? Na mata far da ido ina Fadin"Allah na amarci
ne..."Duka ta Dagamin kafin mu saki Dariya Lokaci Daya muna Tafawa,riko hannunta
Nayi muka karisa Falon Lokaci daya muka Zauna.

Sai da muka gaisa da Aliya Raihana ma ta gaishesu kana na mike naje na kawo musu
Ruwa,Raihana kuma ta Dauko Kololin Abinci nan muka baje afalon Tare muka ci abincin
muna Hira B.kaita ta kalleni tana Fadin"Wai ina Uncle din namu ne..? Ko kin fara
Boyemana Shi ne..?

Dariya na saki ina Fadin"Ah ko Daya na barshi cikin Daki ne Mu gama cin Abinci
Tukunnah zaki ganshi.."Nafada ina Dariya Dariyar itama ta saka Haka dai muka gama
cin Abicin Raihana ta kwashe komai ta maida kichen Dakina ada na kaisu sukayi
sallar Azahar Ni kuma na Shiga Bedroom dinmu na Sameshi Zaune Bisa Wheelchair dinsa
yana kararun Qur"ani Daga Nesa na Tsaya ina Fadin"Bilkisu fa tazo Tun dazu kuma
tana ta tambayarka..."

In kun tanka ya Tankani sai ma Maida Qur"anin daya yi ma"ajiyarsa,ya Shiga Tura
kansa ,Yana sanye yau ma Da Riga da wando kirar Armani Fuskarsa tayi haske sosai
ina kallo ya Bude kofar Bedroom din da Hannunsa ya Fice ya barni nan tsaye,kuncina
na kama ina mamakinsa inaji suna gaisawa da Su B.kaita Har yana tambayanta karatu
tana amsamai da lafiya kalau ba wata mtsala,Kwallah suka kusa Kawomin nayi Saurin
maidasu kafin na Fito ko barayin Dayake ban kallah ba na maida kaina gefe na Wuce
kichen Ina Taku Daya Bayan Daya.

Da Kallo yabini kafin ya Kauda kai Shima Cikin fushi,Abunda ya batamai rai yace ta
cire kaya ta Zauna tana jajjaya dashi wato Haryanzu kasim yana Cikin Ranta kenan..?
Bai kara cewa komai ba yashiga Tura kansa Zuwa Falon Farko wajen Modibbo B.kaita ta
bishi da kallon Tsausayi ta juya suna mgana da Aliya,nikuwa wanke wanken Karya na
Shigayi Duk don Damuwar Dake Raina ta Ragu Jina Shuru yasa B.kaita ta Biyino ganin
ina aiki ne yasa ta kwabe gyale tafara tayani,nayi nayi ta bari taki,sai na kyaketa
Muka Fara Hirar yau gamo nan take fadamin tayi wani Saurayi Dan Bauchi Sunanshi
Usman yana lecturing A Umaru Musa yaraduwa Univeestiy Katsina ammh yana da mata
kuma ya nuna mata da gaske yake yana so yazo yaga iyayenta ammh taki bashi
dama,kallonta nayi ina Fadin"Saboda mene...?..

Ta marairaice tana Fadin"Ina tsoron matarshi ne Anee Allah kuwa.."Tsaki naja ina
Fadin"Dillah ina Ruwanki da wata matarshi kanta Zaki Zauna...Don Allah ki bashi
dama ayi awuce wajen indai ba baki son shi bane.."Cikin Sanyi Jiki tace"Allah ada
bana sonshi ammh yanzu na kamu da sonshi yana da Kyakyawan Dabi"a.."Jin Haka yasa
na Zage ina ta bata wasu Shawarwari har muka gama wanke komai muka adana,muka Dawo
Cikin Bedroom dina muka cigaba da Zantawa Inda muka bar su Raihana da Aliya suna
hira suma Daga gani taso tazo Daya.

Sai bayan la"asar suka tafi,Modibbo na Roka ya kaisu,bai ma Dawo daga kaisu ba Anty
Aisha tazo ita da Mijinta,na Rumgumeta ina Murnan ganinta Ita kuma tana Dariya ta
Dunguremin kai tana Fadin"Ke kam ko"ina akaje aka dawo sai kin Nuna ke Auta
ce.."Dariya na saki ina Fadin"Eh mana Auta dan gatan gida.."Dariya mijinta Ya saka
Bello ko sai dai ya murmusa.

Sai bayan mangariba suka tafi bayan Anty Aisha ta kawomin Gumbar mata da Humra,ta
kuma bani Shawawari Sosai wajen yadda Zan kula da kaina,Na kuma jita na kuma
karu,Sai da Suka Tafi kana Modibbi yatafi maida Raihana gida wanda naso na bishi
naje na gaida Ammi ammh gogan ya hade rai yace bazani ba Dole na Hakura Na Shige
Daki ina Tura baki Ranar Tun 8 na kwanta na Juyamai abaya acikin Raina ina Fadin
naga mai taimakamaka ka hau gadon...

Ki biya ki karanta cikin Salama.

*Anitha....*
8/19/20, 11:26 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �?


400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani
zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?31*

Ina jinsu Suna Hira sama sama Shida Modibbo,Bansan sadda Barci mai Nauyi ya
kwasheni ba Saboda Daura ma kai Fushi katon Hijabin Sallaana na Zumbuda na kwanta
Dashi Ko Zafi banaji ni adole an batamin Rai ina Tura bakin da Fushin Da Komai
barci yayi awon Gaba Dani.

Shiko bai Shigo Dakin ba sai Around 10pm har kofar Bedroon din namu Modibbo ya
kawosa kafin yayi mishi Sai da safe ya juya Zuwa Shashen Dayake kwana Da Hannu ya
sa ya bude Kofar Dakin ya Tura kanshi ya Shigo kuma ya maidata ya Rufe da kallo
yabini yadda na kwanta chan karshe gado na Dunkule Cikin Hijabi,ya dade yana
kallona kafin ya Kada kai Cike da Jin Haushina da kuma kishin kasim Dayaki barin
Ranshi yana ganin kamar saboda yahani saka kayanshi ne Nima na Dauki Fushi Dashi.

Kusa da Gadon ya Gungura kanshi bai batama kansa Lokaci ba wajen Tashina da kanshi
ya Dauki Ruwan Zam-zam dinsa ya Shafa ma kanshi inda zai iya,inda Hannunsa kuma bai
kai ba ya barshi Rigar Jikinsa ya Cire ya Rage Dagashi sai Vest da Dogon Wando bai
zai iya Sauka Daga kan Keken ya Hau gadon ba shiyasa ya Jingina bayanshi da Bayan
Wheelchair din Lokaci Daya yana saka hannu ya Rage Hasken Dakin Zuwa Dumlight
Addu'o'in barci ya karanta ya Tofama Jikinsa Cikin Duhun Dakin yake kallon
Aneesa,kafin ya sake maida idanuwansa ya Lumshe Yana Sake sake acikin Zuciyarsa.

Ban Farka ba sai Wajen 4:30am na Asuba na tashi ina mika Lokaci Daya ina Zare
Hijabin Jikina daya Nannadeni Nida na kwanta Chan karshen gado Shegen Mugun barcina
ya kaini Farkon Gado,hannu na sanya na kunna Hasken Dakin ina Tunanin Kodai Bai
Shigo Dakin banecYabi Modibbo Sunje sun kwana Tare,Sai dai Halin Dana ganshi Sai da
Jikina yayi Sanyi yana Zaune Bisa Wheelchairs dinsa yana barci Cikin kwanciyar
Hankali Fuskarsa na Tsurama ido Idanuwana Sun Ciko da kwallah Tuni naji ban kyauta
ba na Sauko Daga kan gadon ina Tattara gashin kaina Daya watse Zan saka mai Band ya
Bude Idanuwansa Yana Bina da kallo.

Mirmirshi na sakarmai ina Fadin"Ina kwana...Jiya baka taashe ni na taimaka maka ka


Hau bisa gado ba.."Kauda kai yayi kamar badashi nake mgana ba,Sai ma Salati Daya
saka yana karanto Addu"ar Tashi Daga barci Naji na Muzanta ban kara mgana ba na
Wuce Fuskarta na Nuna kalan Tsausayi Na Bude Kofar Tiolet na Shiga Ya Bini da kallo
kawai yana Sakin Mirmishi shi kadai.

Ina wanka ina Sharan kwallah Wata Zuciya tana gayamin Kin manta Aneesa dama Bello
baya Sonki Dole Tunda ya samu Lafiya ya Dinga Nuna miki Kiyayya kiri kiri,Abun ya
Zauna acikin Ranta Sai da tasha Kukanta Sosai kana Tayi wanka ta Dauro alwala ta
Fito Tana Daure Towel,lokaci Daya Tana kare Fuskarta,Bata ma son ta kalleshi Shima
ta kasan Ido yake kallonta ammh bai bari ta gane ba

Gaban Dressing mirrior ta isa Tana Kokarin Shafamai Shi kuma yana Kokarin Juya kan
keken nashi Zuwa Tiolet kafarsa ta Turgude,yayi kamar zai Fadi Da Sauri ta isa kusa
Dashi ta manta ma Da Abunda ke Jikinta Riko Hannunsa Tayi kafin ta Duka Ta gyaramai
Zaman kafarsa,bata kalleshi ba Tana kokarin Fara Turasa Ya saka hannu ya Cire
Hannunta Dake saman Wheelchair dinsa,ya Fara Tura kanshi Har ya Shige Cikin Bandaki
ya Turo kofa tana Kallonshi Hawaye suka Ciko Cikin Idanuwanta tayi Saurin Shanyesu
Jikinta Asanyaye ta Koma ta Cigaba da Shafa manta,ta Gyara gashinta ta Daure Ta
Bude Wardrope ta Dauko Doguwar Rigarta baka ta saka,Ta Dauki karamin Farin
Hijabinta Datake Sakawa In Zata Fita kichen ko Falo ta Saka,Wani Hijabin na Dauka
Daga Cikin Wardrope wanda Zanyi Sallah Dashi, tana Jin yana Kokarin Fitowa ta Fice
da Sauri Tana Tunanin Lokaci ya kusa Da zata bar Rayuwar Bello Tunda Baya
Bukatarta.

Dayan Bedroom din nashiga nayi sallata na Dade ina Addu"a ina kuka kuma bana komai
bane sai na Chanjin da Bello yayi min ina Jin Zuciyata tana Zafi Saboda na Shaku
dashi na yarda dashi Fiye da kowani Namiji kuma Zuciyata tana Tsananin kaunarshi
Ashe Nayi Kuskure wajen Fara son wanda Baya sona Na manta Lokacin yana Cikin Ciwo
ne kuma yana Bukatar wanda Zai Zauna Dashi ya taimakeshi,Wato yanzu yafara samun
kanshi Zai iya yin Komai da kanshi Baya Bukatarta,tayi kuka sosai ta share
Hawayenta ta nan Zaune Har 7 tayi kana tatashi ta cire Hijabin ta Fita Zuwa Kichen.
Saboda Bata Cikin Mood dinta Doya da kwai kawai ta soya musu sai Tea da Zallar
kwai,ita kuma Kunu ta Dama ma kanta Zata Sha hakan nan kawai Domin Shi Take
Sha"awar sha,Hada ma Bello nashi Tayi Kan wani Babban Faranti Shi kuma Modibbo ta
Hadamai komai Da nashi da Maigadi ta barshi Acikin Kichen din nan take barin mai in
ya Tashi Zai Dauki Nashi ya mika ma Salihu maigadi nashi.

Koda ta koma Bedroom din ta Iske Har ya Shirya Cikin Riga da wando na kamfanin
DKNY,kansa yasha gyara kallo Daya zakamai kaji kana Sha"awar kara kallonsa karamin
Qur"ani ne Ahannunsa yana karatunsa cike da Natsuwa,Koda ta Shgo Dauke da Faratin
kayan karyawansa Karamin Center Table din Dake gefe ta jawo ta Dauramai Bisa ta
Duka Tana Kokarin Zubamai Ruwan tea din Cikin karamin Kofi taji yace"Karki
Zubamin...Ba yanzu zan karya ba.."

Yafada yana maida Hankalinsa bisa karatunsa,kallonsa Tayi kafin Ta Kada kai ta
maida komai ta ijiye ta mike zata Fita kenan Taji yace"Ina wayarki..."?

Bata waigo ba Ta isa Saman Drower din Dake gafen gadon ta Chan barayin ta Dauko
tazo gabanshi ta mikamai Bayan ta Kauda kai Shima kallo Daya yayi mata ya kauda kai
yana karban Wayar ta Fice Daga Dakin da Sauri ya Bita da kallo,Yana kada kai Lambar
Anty Rahila ya Lalubo Ya Danna mata Kira Dayake Wayar bata da Security.

Anty Rahila na Zumudi ta Dauka ganin Kiran Aneesa tana Fadin"Amaryar Mr


Bello..."Mirmishi ya saki kafin yace"Ina kwana Anty..."Baki ta Rike kafin tace"Ashe
Babban Mutum din ne da kanshi Mun tashi Lafiya ya karfin Jiki..? Yace"Alhamdulillah
Anty Ina Hibba ina Junior dina,Ina Kuma yayana da Daadata...?

Tace"Kowa lafiya Junior na wajen Yayanka suna Shashen Daada..Ita kuma Hibba mallam
Inuwa yatafi kaita Sch.."Kai ya gyada yana Fadin"Masha Allah..Anty Rahila wani
taimako nake so kiyimin Don Allah.."Tace "Allah yasa Zan iyi Bello.."

Rage girman idanuwansa yayi yana Fadin"Kaya nake so don Allh Ahadama Aneesa Tunda
ga Nu" in kayan sakawa da komai da komai kamar za"a Hada Lefe..."Dariya Anty Tayi
kafin tace"oh..kayan Auren Za"a Hada Tun yanzu baka bari kagama warkewa ba sai mu
sake sabon Biki.."Tafada tana Dariya Mirmishi yayi yana Fadin"No...Bata da wasu
kaya anan ne Shiyasa Anty.."Baki ta Rike kafin tace"Ina kayanta Data Taho
Dasu.."Kansa ya shafa yana Fadin"Ni na hanata saka wannan,Nafi son ta Dinga saka
wanda Zan Siya mata Da Gumina..."yafada kai Tsaye Yar Dariya Anty Rahila ta saka
Kafin tace"Au hakane Abun..."Tafada Tana Dariya Bai yi mgana ba Illah Shafa kansa
Dayake Yana Mirmishi

Cikin Dariya tace"Shikenan karka Damu zan kira Hajiyar Jummala ta Dubai nace ta
Hado komai kawai Dagachan Ta sako a jirgi akawomin nan..."Gyada kai yayi kafin
yace"Zan saka miki Kudin ta account dinki Insha Allah..."

Batayi mgana illah Dariya Datakeyi Ganin Ya Muktar ya Shigo Sallama sukayi Kafin su
yanke kiran,ganin Tana Dariya yasa yace mata"Keda wa kuma kina Dariya kamar kin
samu kwangilan Tallan makilin.."

Shewa ta saki kafin tace"Bello ne ya bani mamaki wai kishi yakeyi Kar Aneesa ta
saka kayan da kasim yace ya barma Aneesa yanzu ya kirani yacemin Ahada mata Lefe
Domin ya hanata saka wanda Taje dashi..."Dariya Ya Muktar yayi kafin yace"Luv bird
kenan...Shegen gora baya Fara Samuwa ba Yanzu iko zai Tashi..."Yadada yana mika
mata Junior Ta karbeshi Tana Fadin"Harda cewa zai min Transfer din kudi ta
bankina..."Baki ya Rike yana Fadin"Eh lalle...Mijin Aneesa Manyan Duniya."Dariya
Suka saka Gabadaya Suna Cigaba da Tattaunawa,Duk mganar na Bello ne Suna Dariya
Abun yayi musu dadi Cike da Nishadi Cikin Zuciyar Anty Rahila,ganin Bayan Samuwar
Bello bai Juyama Aneesa baya ba.

Cikin kichen Na Koma na Sha Kokona,ban yi wanke wanke ba na barshi sai kowa yagama
karyawa Falo na Dawo na Shiga gyarawa sai ga Modibbo ya Shigo Yana ganina ya Kama
Dariya yana Fadin"Amaryan gida nan..."Hararansa nayi ban mai mgana ba Dariya yayi
yana Gaisheni na amsa ina Fadin"Lafiya lau angon Raiha.."Da Sauri ya waigo yana
kallona Cikin mamaki yana Rufe baki Dariya nayi kafin nace"Karyan Tsiya kuke ai na
ganoku.."Shafa kai yayi yana Fadin"Allah sa dai zaku bani ita Anty
Aneesa.."Mirmishi nayi kafin nace"In ka shiga cikin layib masoya ba.."Ido ya Zaro
yana kallona Ni kuma ina mai Dariya Shima Dariyan yayi ya Nufi Kichen ya Dauko Na
megadi ya Fita ya mikamai yazo ya Dauko nashi yazauna afalo ya karya muna Hira sama
sama,Har ya kammallah ya maida komai kichen ya Fice yacemim zai je yayi wanka Ni
kuma na karisa gyara Falon na Koma Kichen na wanke komai,kafin na koma Bedroom din.

Yana Zaune inda na barshi Sai dai yanzu ya ijiye Karatun,yana Rike da karamin kofin
Tea,da alama Tea din ya Tsiyaya yana Sha ina Shigowa ganin ya sakamin Ido sai na
Daburcewa na Juya Zan Fita naji yana Fadin"Am srry for my mistake ban Zata Zakiji
ba Dadi domin na Hanaki saka kayansa ba Ashe Har yanzu ya nan a matsayinshi ni ne
nake yaudaran kaina..."Yafada kai tsaye yana kallonta kafin ya Maida kofin Bakinsa
yana Kurban Tea din Dake Hannunsa ..

Chak ta tsaya Ammh bata waiwayo ba Jikinta ya kara yin Sanyi Cikin Sanyin Jiki ta
Ta Juyo Tana kallonsa tace"Me kake Nufi...? Tafada Idanuwanta na Cikowa da
kwallah,Kallonta yayi ido Cikin ido kafin yace"Abunda Kunnanki ya jiyemiki,Kiyi
Hakuri ban zata Cewa Haryanzu kina Sonshi ba..."Yafada kafin ya Maida idanuwansa ya
Lumshe,.

Kuri tamai da ido Tana Kallonsa Cike da Mamaki Lokaci Daya Hawaye na Zubo mata
acikin Kwarmin Idanuwanta,cikin Rawan Murya tace"Ni..Ni .na fada maka Haka..? Ni ba
Fushi nake ba kai ne Naga ka Shareni kadaina Neman Taimakona Ko mgana na maka baka
amsani.."Tafada tana Fashewa da kuka kafin ta cigaba Da Fadin"Ammh Shine kake
Zargina kana Tunanin Zan Cigaba da Son wani ne alhalin akwai igiyar Aurena
akanka,zuciya ta taji Zafin kalamanka Ban Dauka wannan kallon kake min ba...Wlh
Tallahi Tunda Aurenka ke kaina Bantaba Tunanin Wani wai shi kasim ba na Riga na
gama Shafe Babinsa Acikin Rayuwata...Ammh bakomai.."Tafada Cikin kuka kafin Ta Fice
Daga Bedroom din da Gudu Tana kuka

Da kallo ya Bita har ta Fice,Rausayar dakai yayi Acikin Zuciyarsa kuma baiji Dadi
ba sai dai Hankalinsa ya kwanta Jin Hashashensa ba gaskiya bane Aneesa bata son
kasim,Dama Abunda ke sakashi Fushi kenan da bacin Rai,Kansa ya Dafe da Hannu Daya
yana Furzar da Numfashi kofin Tea din ya ijiye ya saka Hannu ya Ture Center Table
din gefe,ya Fara Tura Keken nashi Ya Fice Daga Bedroom din.

Ganin bai ganta afalo bane yasa yasan Tana Cikin Dayan Bedroom din,Tura kansa ya
Nufa cikin Bedroom din,ya Saka Hannu ya Tura kofar ya Shigo Tana kwance Bisa gadon
Tana kuka Jikinsa ne yayi sanyi Jin yadda Take Fitar da Shesshekan kuka har gaban
Gadon ya karisa yana kallonta Cikin Wani yanayi Sai Daya gama kallonta kafin ya
Kira Sunanta Ahankali..

"Aneesa...."yafada cikin Husky Vioce dinsa Tana Jinsa tamasa banza Matsowa ya
sakeyi ya saka Hannu ya Riko Hannunta yana Fadin"Haba Anee taso kiji don Allah
Tashi...Kukanki na Kona min Rai kinsani kuma.."Yafada Cikin Wata Murya mai cike da
Muradi,Dago kanta Tayi idanuwanta Cike da kwallah ta Zabgamai Harara,Rausayar Dakai
yayi yana Fadin"Am Srry...Kinji..."

Kallonsa Tayi kafin Ta Tura baki Sake Riko Hannunta yayi yana Fadin"Kinji
taso..Kiji Don Allah ba Domin Halina ba.."Yafada yana Sakar mata Lumsassun
Idanuwashi Mikewa Tayi Zaune yana Rike da Hannunta Harta Sauko Daga kan gadon Kan
Cinyarsa ya Diresa Yana kallon Fuskarta ita kuwa gefe tayi Da kanta tana Share
kwallah Lokaci Daya tana Share Hawayen Idanuwanta,.

Mirmishi ya sakar mata yana Fadin"Am Srry For wht i did...Baran kara ba Insha
Allahu..."Yafada yana leka Fuskarta,Ture kansa Tayi tana Fadin"ammh kasan dai baka
kyauta ba ko..? Taya zaka ce ina son wani alhalin kuma inada Miji..."Ido ya waro
yana Fadin"Hakane fa...Nayi Laifi...Toh kina son mijin naki ne? Ya jefa mata
Tambaya yana kallon Cikin kwayan Idanuwanta.

Kura mai ido Tayi Tana kallonsa Cikin Wani yanayi Jikinta ne yayi Sanyin Jin
Hanmunsa Dake Kugunta yana yawo Dashi ga Idanuwansa Da Suke sakata Jin kasala,kanta
ta Sadda kasa Tana Kifta ido Cikin Son Kureta yace"Umh ina jinki Kina son mijin
naki...?

Kin mgana tayi sai Mirmishi Data ke Saki,ganin Haka yasa ya Matsota Jikinsa,lokaci
daya yana Sakin Ajiyar Zuciya hannuwasa Duka ya Saka ya Zagayowa Da ita ta Kugunta
Cikin Kunnata yake Rada mata"Kiyi hakuri Kinji Haushi naji Danaga kina Fushi Dani
sai naga kamar don na Hanaki Saka kayan nashi ne..."Baki Ta Tura tana Dukan
Kirjinsa tana Fadin"Kaji ka ba kai bane ka Fara Fushi dani ba Ka daina min
mgana..Ni kuma na Damu Sosai..."Mirmishi yayi yana kallon kwayan idanuwanta kafin
yace"Anee i wan to tell u Sometin..."Yafada Muryansa na Chanzawa Alamun yana Cikin
wani yanayi .

Ido ta sakarmai kafin tace"Mene...? Bakinsa ya kawo Wajen Bakinta ya sakarmata


Numfashi Kafin yace"Kin yarjemin nayi kissing dinki kafin na gayamiki Abunda ke
Raina..."Yafada yana Narkar da idanuwansa Cikin Nata,Lum tayi Jin tana Cikin wani
yanayi Runtse ido tayi kafin ta gyada kai Mirmishi ya saki kafin ya Tallabi kanta
Ya dora Lebensa kan nata yafara Tsotsa Cikin Wani yanayi Aneeesa Datake jin kanta
Cikin Wani yayi itama hannayenta ta saka ta Tallabi kan Bello Hannunta Guda Daya ta
saka bayan keyarsa tana Shafa Sumar kanshi Cikin Fitan Hayyaci ya Lulubi Harshenta
ta sakamar ya Fara Sumbatarta Itama Cikin Zakuwa ta Damki Harshensa ta Shiga
Taimakamai Suna Sumbatar Juna Cikin Wani Salo da Muradi mai girma

Hannunsa Guda Daya Suna kara kaina Bisa Jikinta Har Zuwa Bayanta,Wani Salo yake
mata wanda yake mantar da Ita take bata ankara ba taji Hannunsa Bisa Tudun
Nonuwanta Sai da Aneesa ta Sauke Zuciya Domin Sandar girmansa ta Mike tana Zagye
Tsakanin Cinyoyinta,ta kara sakata cikin wani Shauki Rike Hannunsa Tayi Idanuwanta
na Runtse Bakinta ya saki Numfashi ta saki tana Fadin"Shiii...Ka...bari..."Tafada
Tana kara kankame shi Jin Kasanta yana Zil,zil kamar wani Abu na Fita,Shima Bisa
Kirjinta ya koma ya lafe yana Sakin Numfashi Kadan kadan Lokaci Daya yana kara
kankameta

Sai da suka samu Natsuwa Dukkansu kafin ya Dago yana kallonta ta lafe Bisa
Kirjinsa,Dago kanta yayi yana Fadin"Anee plz open ur eyes.....zanfi so ina gaya
miki mganar ina kallon Cikin kwayan idanuwanki.."Bude ido tayi tana kallonsa Kunya
Duk ya kamata ganin yadda Duk tayi laushi,Gyara mata Zama yayi yana Kara Matseta
yafara mgana Cikin Husky Voice dinsa...

"My Anee...Bansan da Wata kalma Zan Fara ba...Kin Chanchanta kuma kin Zarce komai
awajena...Alokacin da Nake Halin Lafiya ban mu"amalanceki da Kyakyawan Dabi"uba
ammh sai gashi bayan Lalura ta sameni kinyi Hidima dani kin Soni kin kuma Zauna
Dani Kin Min Abunda babu Wata macen Da Zata iya Zama dani Ahaka...Aneesa Zuciyata
ta gama Girmama Alherinki da Karramawarki...Ta Shaku Dake...Tana Mutumtaki Kilama
Tana Tsananin Sonki..."Yafada Cikin Sanyi da Kauna mai Tsanani.

Da sauri Aneesa Ta Sakarmai idanuwa Cike da mamaki yace"Eh Aneesa...Zuciyata ta


kamu da Sonki...Da Muradinki..Kirjina yana Cike da kaunarki...I love u so much
Aneesa...I love...U..."Yafada kamar zai saki kuka,Kukan ta Fashemai dashi ta kara
kamkameshi Cikin Farinciki kafin Ta Dago Kanta,kansa ta kama da Hannun Biyu ta
Shiga Sumbatarsa Cikin Shauki Da Salo mai girma,Shima kanta ya Tallab,yana Taimaka
mata wajen Nuna mata Tsananin Son Da yake mata.
Sai da tagaji ta saki bakinshi kafin Ta Tsuramai ido tana Fadin" _i want to be a
good mother to ur childreen..and a good wife to u always...I love u to infinity
B.love...._ "Tafada Tana sakarmai kiss ta ko"ina akan Fuskarsa.

Shima Cikin Farinciki yake karban Sakona nata yana Fadin"Love u too..My
Anee .."Yake Fada Sun Dau Tsawon Lokaci Suna Jiyar da juna Dadi Lokaci Daya kuma
Kowa na gayama Dan"uwansa Kalamai masu Dadi da kwantar Da Zukata.

Ranar dai sai da Bello ya saka Aneesa Sabom Wanka bayan Shima ta sakashi kuma ya
matsa mata Suka Shiga wanka tare,Aneesa Taji matukar Kunya Sanda Bello ya Tubeta
Naked agabanshi Ya Tsaya yana kallonta Cikin Shauki da Sha"awa yana kara Gidiya ga
Allah,Ita ko Runtse ido tayi kunya ya kamata Haka ta Fada Bisa Cinyarsa Tana
Dariya,Shima ya saka Hannu ya Runguneta yana Sakarmata kiss a Tsakiyar kanta,Duk
kunyar Aneesa Sai da Bello ya Nemi Ciremata Shi yana Daga Zaune in yayi wani abun
har mamaki yake bata,Ahaka dai sukayi wankan Tsarki Suka Fito Cikin Farinciki,ko
wajen Shiryawan nasu ma sai da suka sake Shiriricewa Domin Bello yagama Rasa
Natsuwarsa akan Aneesa.

Ki biya ki karanta cikin salama..

*Anitha...*
8/19/20, 11:26 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �?


400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani
zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?32*

*KADUNA*

Kasim Har yagama Hutunshi a katsina bai yarda ya bude Aisha ba Saboda Agaskiyan
mgana bai taba jin zai iya auranta ba Har Haruna ta kira,tana kuka tana gayamai
Kasim baya amsa wayarta Daga baya ma sai ya kulleta Hakuri ya bata yace zai mai
mgana yakuma kirasa awaya ammh sai kasim ya nuna mai ya kyaleta ita so take ya
aureta shi kuma Har Abada bayajin Zai iya zama da Aisha jikinta yakeso kuma ya riga
ya samu.

Haruna bai iya gayama Aisha Haka ba sai yayi mata karyan kasim din baya jin Dadi ne
jin Haka yasa ta Rude Hutunsu ko karewa bai yi ba tattaro Daga maiduguri ta dawo
kaduna wajen kasim Dayake D'an Duniya ne sai yayi mata bariki ya Dinga lallabanta
yana nuna mata ta kwantar da Hankalinta wasu Shirye Shirye kadai yake son karisa
ammh Karta damu Zuwa Daya zai yi Maiduguri sai zuwan magabatansa da wannan karyan
ko nace yaudaran ta yarda ta kara sakin jiki dashi suna More Iskanci da
Sharholiyansu son ransu...

Aisha tana bala"in son kasim shiyasa bata kaunar yin Nesa Dashi Bata taba kawo mata
Ranta Watarana kasim zai iya cin amanarta ba,Shiyasa ta sakankace Soyayyah tagama
Rufe mata ido bata ji bata gani Sch ko sai tayi Sati bata Shiga ba,Kawayenta sun
gaji da gayamata gaskiya sun kyaleta Domin Gabadaya ta yanke alaqa dasu...Bata
Shiri da Duk wanda zai Fadi Aibun Soyayyarta da kasim,Ta riga ta gama Sadaukar ma
kanta Cewa Shi kadai take ji kuma take ganin amatsayin Cikakken Namiji.
Duk azaton su Abba kabiru Kasim yadaina Halinsa,Hakama ya Hashim Domin har rantsuwa
Kasim yayi mai akan ya Tuba Duk da bai yarda ba ammh ana so ka dinga kyautatama
Dan"uwanka Musulmi Kyakyawan Zato Shiyasa yacire Zargi da Shakkun kasim bazai Taba
Daina Halinsa ba.

Bangaren Umma kuwa Bata taba yarda ba haryanzu tana kan gabanta wajen cewa Sharri
aka kullama Kasim Hartana Fadin Kilama Harda Hadin bakin mama Sahura Tunda ba
kaunarta Take ita da ya"yanta ba zata iya hada kai da gidansu Aneesa ko da Bellon
Domin Atozarta ta,Da mganar ta Fita mama sahura batayi mgana ba saboda ta iya
bariki Sai ta kira Inna Rukayyah Daga kano ta gayamata cikin Siyasa harda kuka Tana
rantsuwan yadda Bello baya mutumtasu itama baya Mutumta Tunda take dashi ko
gaisuwan arziki basayi balla ace da Hadin bakinta acikin Abunda ya faru.

Ran Inna Rukayyah ya baci domin bata kaunar bacin ran Mama Sahura nan da nan ta
kira Abba kabiru tana gayamai Abunda ke Faruwa nan yafara Fadanshi ya kira Umma ya
mata kaca kaca yace in ya karajin wannan mganar abakinta sai ta Raina kanta tafi
kowa sanin Halinshi Mafadaci ne kamar mene,Shiyasa badomin Ranta yaso ba ta bar
mganar ammh Cikin Ranta Tsanar mama Sahura ne Damkan kamar ba sune Lokacin Baya
suke da kyakyawan alaqaa wajen Taya mazajensu aikata Mugun Abu ba.

******
Tabbas Hausawa sunyi gaskiya Sukace kaji tsoron wanda bai taba Soyayyah ba ya Fada
cikin Tarko Shikenan sai ya Susuce toh Hakan ne ta Faru Da Bello da Aneesa Domin
wata salon Soyayyah kulawa da kauna mai tsanani suke bama juna Aneesa ita kadai
indan ta zauna sai tayi ta mamaki Bello in yayi mata wani Abun Tana Tuna anya
wannan Mr Bellon Data sani ne ko wani ne Dabam,ita wanda ta sani abaya baya yawan
mgana,baya dariya,baya fara"a kai baka isa ka gane ina ya Dosa ba Zuciyarsa ba
Soyayyah balle Jinkai sabanin na yanzu,Mai yalwar Fara"a ne gareta,mai Surutu,mai
sakin jiki,mai zuciyar Soyayyah da kulawa,yagama Narkewa Cikim kaunarta koda yake
Zaune Kara"insa kadai yake ci Shida Aneesa wacce Tun Tana Kunyarsa Har tazo ta
daina saboda sun Ruga sun zama jini da hanta Kuma Duk Ragowar kunyar ya Riga yagama
cireta tsab,yana Zaune kan kekensa ammh Basu Tsauyama Junansu ba haka zai Dafe
Aneesa suyi ta romancing Ahaka sai ya Fitar da Abunda ke damunsa yake kyaleta itama
Duk ta Riga tasan Duk wata Hanyar da Zata saka ya kunno shi haka Shima yaa san
gaban da Zai Taba ajikin Aneesa ya kunnota wanda ba domin laluran a kugunsa take ba
da Tuni ya D'ura ma Aneesa ciki

Modibbo kuwa Soyayyar su na Burgesu Shiyasa shima Lokaci daya yaji Shaukin Aure ya
Shiga Ranshi,Sunyi kiba sunyi bul bul kamar basu ba Babu Ruwansu Suna Cikin
kwanciyar Hankali koda yaushe suna tare a kichen ne,a Falo ne abedroom ne Kafarsa
To kafar Aneesa ne kamar Cingam dinta Haka ya koma Daidai da gyaran gashi zata Tare
zasu Fita Modibbo ya kaita ya Zauna amota har agama mata

Haka Sanda zasu je gaida Ammi bayan sunje tayi tayi ya barta ta Wuni sai yammah
Modibbo yazo ya Dauketa su sukoma gida ya Hade rai yace mata karma ta Fara in
tafiya gida tafiya gida in kuma Tsayawa toh tsayawa Taso ta tsaya ammh sanin Bello
fa kunya Zai ta bata shiyasa suna gaishe da Ammi Suka Tattara suka koma gida tana
Tura baki ammh Duk da haka sai da ya Lalubeta yana Fadin"Allah Anee baki da
Tsausayi kinfi kowa sanin bana iya kyakyawan Minti Talatin Ban jiki Cikin Jikina
ba..Taya Zaki tafi wani waje ki wuni ai zaki ragemin Jin Dadina.."Yafada yana mata
Dariya Harda dagamata Gira Tura baki tayi ta Ture kanshi Hannunta ya Ciza da
hakoransa yana Fadin"Kajita kamar kema baso kike ina tabakin ba..nafa gano kina
cikin Jinsin mata Harijai..."

Ido ta zaro tana kallonshi Lokaci Daya tana Rufe bakinta Da Hannuwanta Gira ya sake
Daga mata yana Fadin"Karya nayi...? Karki Damu ni mijinki ne naji Dadin Haka nima
Ina Cikin Jinsin maza masu yawan Bukata Tanque Anee For coming into my
life...Dalilin ki ne na zama Cikakken Mutum Har nake iya gane kaina ina Rokon Allah
ya bani lafiya na warke na Kure wannan Kwadayin naki.."Yafada yana jan karan
Hancinta,.

Harara ta sakarmai kafin ta Fada Kirjinsa tana yar Dariya mganar gaskiya Bello
baiyi karya ba Ita kanta bayan Girmanta ta fahimci tana Daga Cikin mata masu
Sha"awa Ammh har gashi shi ya gane koda yake dole zai gane in Tana Jikinsa yana
Sarrafata kasa Daidaita kanta take,Wani Lokacin sai taji kamar ace yau Sex zasuyi
ba iya Romancing ba,Sautari zai gama Jagwalgwalanta bayan sunyi wanka Haka zata
kwanta Bisa gado tayi lamo tana maida Numfashi Zuciyarta na Bugawa Domin sai taji
wani irin Feeling din Sex na Shigarta Dahakane ya Fahimceta Sau tari sai ya Dinga
ja baya wajen Taba ta sai ita idan ta Kunno Shi,Bata sani ba Shikadai sai yayi ta
kukan Zucci in ya kalleta yana ji acikin Ranshi kamar ya Tauye mata Hakki,tana
cikakkiyar mace mai lafiya Shi kuma bashi da lafiyan da zai kara maidata mace sosai
Abun na Damunshi yana Fargaban kar watarana Aneesa ta kasa Iya Control din kanta
tace Zata barshi Saboda haka.

******
Tuni Bello ya Turama Anty Rahila Kudi ta account dinta 3m ita kanta sai datayi
mamakin yawan kudin kuma yace akashema Anee duka komai na Bukatar rayuwa asiya mata
shi,Aneesa bata da labari Taga dai yace ta kunna mai wayarsa Yafara amafani da
ita,Ranar Daya kunna wayarsa bayan Tsawon Lokacin Data Dauka tana kashe ya iske
tarin sokonnin Mutane abokai da yan"uwa da abokan Arzuka suna fatan samun Lafiya
garesa,alokacin bai so fara amfani da wayar ba Saboda zai ma Anty Rahila transfer
ne Daga layinsa,sai kuma yaga Mutane na Nemansa ta wayar shiyasa ya barta yana
amfani da ita.

Lokacin da mutane sukayi ta samun Sa ta waya suna gaishesa da Jiki,jami"ar Buk ma


sun nunamai so da kauna Sun Turamai sako cewa ko yau ya warke ya Dawo Tana maraba
Dashi amatsayin Malaminta,Yaji Dadin haka sosai duk da yana da wasu tsare tsare
Dadama acikin Ranshi yana Fatan Allah ya bashi lafiya ya mike da kafarsa,sai komai
yatafi Daidai...

Waya kadai Anty Rahila tama Hajiya Jummai Dubai Sukayi Mgana ta tura mata kudi tare
da Size din Aneesa na bra,Da pant,sai na takalma gudun samun mtsala Sati Uku
Tsakani ta gama Hada komai ta sako kayan ta Jirgi kwana Biyu sukayi kafin su
iso,akwatuna yan Ubansu masu kyau da Tsari Daya Daya Guda 12 shake da kayan
Arziki,sai wanda ya gani.

Data kirashi ta sanar dashi kaya sun iso sai yace ta kira chan Borno ga kayan Auren
Aneesa nan inda wanda zai taho ko Anty Nafi ko Anty Yagana ko Cikin matan Ya Ali
sai su taho tare nan kano sukawo Daada taji Dadin Tunanin Bello sosai Nan da nan
Anty Rahila takira ya Ali tana Sanar dashi Cikin mamaki yace"Ikon Allah Rahila
wannan wani Rashin hankali ne Mutum na Zaune ba lafiya har wani Tunanin kayan
akwati kuke,Saboda Sakarci.."yafada Cikin Fada Marairaicewa Anty Rahila tayi sanin
Halin ya Ali Da Bambamim Fada tace"La ya Ali shifa da kanshi ya Turo da kudin
da"aka Siya komai yanzu haka ma Shiyace na gayamuku..."

Tsaki yaja kafin yace"Kaji Shanshanci karya kuke ban yarda ba...Ina Tunanin yanzu
haka ja"iran yarinyarnan Aneesa ce zata matsamai sai ya mata kayan Akwati Tunda na
santa bata da Tunani kema Dayake Sakarace irinta sai kika Biyemata,Ana ta lafiya
watake ta wani Kawan Duniya banda kuruciya Mijinka Bashi da lafiya yaushe zaka
tsaya tunanin wani kawan Duniya da kyale kyale.."Anty Rahila ta kwaso Rantsuwa tana
Fadin"Na Rantse ya Ali Aneesa bazatayi Haka ba Barima kaji Dalilin siyan kayan
bata da wasu kaya ne achan kano wanda tatafi dasu kuma na wajen kasim ne Daya
barmata Kuma Shi Bellon yace karta kuskura takara sakawa Kaji fa Dalilin ya
Ali.."Takarishe Fada Cikin Fargaba Domin ya Ali akwai Fada sosai

Numfashi yaja kafin yace"Umh...kudai kuka sani Ki kira Yaganar kila ta samu Zuwa
mudai nan ba wacce zata zo..Shanshancin banza wanda bai da amfani kuma zan kira
Bello Shima sai na Sabamai Tunda yana Zaune ba lafiya yana Biyema Shirmen
mata..."Yafada Lokaci Daya yana Tsinke kiran,wayar Anty Rahila tabi da kallo tana
ajiyar Zuciya sanin Halin Ya Ali na Fada Allah Khadija ba karamin Hakuri takeyi
dashi ba.

Anty yagana ta kira sukayi mgana bayan tagama gayamata yadda suka kare da ya Ali
sukayi ta Dariya Anty yagana tace"Kema Rahila Allah kara miki meya kaiki..? Kinfa
san ba"a ma ya Ali gwaninta ya iya gwasale mutane Dama ya Sunusi kika kira Kila shi
ya Fahimceki,Nima bazan samu Zuwa ba,Saboda Mahaifiyar mijina ba lafiya,Ammh naji
Dadin wannan Tunanin na Bello ko Banza kanwarmu ta kara Daraja a idon Dangi ki kira
Anty Nafee kiji ko zata samu zuwa..Duk da bani da Tabbacin Zata zo din...."Ajiyar
Zuciya Anty Rahila ta Sauke kafin tace""Kai Anty Yagana kinfa san Halinta ni banaso
na kiratane ta Hau Chabamin mgana kin Manta yadda mukayi da ita kan komawar Aneesa
kano sai da nagayama ya Ali yashiga tsakanina da ita Tunda ga Lokacin tace na fita
Daga Sha"anina Tunda na Nuna nafison Aneesa akanta..."Tafada Cikin Rashin Jin
Dadi .

Jinjina kai Anty Yagana tayi kafin tace"Hakane kuma...Bari na Kirata Naji in zatazo
Shikenan in kuma Ba zata samu zuwa ba Sai kawai ki kira Aisha ku hadu achan Ba wani
abu Tunda Duk Daya ne..."Anty Rahila tace"Shikenan ina jiranki..."Daga Haka suka
rabu Anty yagana kuma ta kira Anty Nafee tana gayamata baki ta tabe tana Fadin"Ikon
Allah...Ita Rahilan bata da baki ne ko kuwa bata da Nombar wayata ce...? .

Anty yagana tace"Ah.."a ba Haka bane kiyi hakuri tana ta kiranki bata samu ba
Shiyasa tace na kiraki na gaya miki in zaki samu Zuwa..."Shewa tayi kafin tace"Ai
na zata nagama amfani kenan awajen Rahila ai ni nace wlh ni Duwawu ce Dole Azauna
dani Wlh ba Domin Zumunci ba ba inda zani ,nan yarinyar nan tadaina Daga Kirana
Daga Taimakonta,abun ya batamin rai yadda Rahila tamin Ammh bakomai na Duba
Zumunci.."Tafada tana kwafa

Itadai Anty Yagana bata tofa ba illah Fadi Datake""Kiyi hakuri...Gaskiya bata
kyauta ba..."Tabe baki tayi tana Fadin"Shikenan ya wuce...Zan shirya na tafi gobe
dama ina Shirin kiranki ne yarki ce Sanah Takeson Zuwa Hutu wajenki kinsan Sunyi
Candy suna Zaune agida,.."Anty Yagana tace"Allah Sarki...Naji Dadi sosai..Sai abar
Saratu agida kenan."

Anty Nafee tace"Eh Ita zan bari Tare da Sanah zan tafi Abujan in mun Dawo sai ta
taho insha Allahu.."Anty Yagana tace"Hakan yayi Allah yabada iko...Nagode.."Da haka
sukayi sallama,Anty yaganar ta kira Anty Rahila take sanar da ita yadda Sukayi da
Anty Nafee kuma ta kwabeta da cewa ko tazo tana wani mgana karta Biyemata Tunda Ita
haka Allah yayi ta komai aka mata ba Daidai bane.,Anty Rahilan ta mata alkawarin
bazata Biye mata ba.

Itako Anty Nafee tace zata ne Domin taje Taga uwar Kwal Daka,Da kuma Sanah Data
matsamata tana so taje gidan Mami Anee,uwa uba kuma itama taci Uban Aneesa Taji
Dalilin Rashin Daukan wayanta da batayi,Tana gayama mijinta ya amince Domin Dama
kamar ita ke juyan gidan Saboda Korafinta Washegari suka kama Hanyar Abuja tabarma
Sarah mai Bin Sanah din kula da gida da Sauran kannenta.

Sai Dare suka iso Abuja Anty Rahila ta musu Tarba sosai kuma bata Nuna mata wani
Abun ba,Itama Anty Nafeen bata tanka ba,Nan suka kwana Anty Nafee duk Kushenta ta
kasa Kushen kayan nan sai kallo take tana Jinjina Nairar Da"aka batar har sai da Ta
tambayi Daada Dake Gefe"Ammh Daada nace kodai Yayan nashi ne ya Hadamai wannan
kayan..?

Daada tayi Dariya kafin tace"Ah..a Uban gayyar ne da kanshi Muntarima Dabaya gari
Yatafi ina ne ma Rahila...?"Anty Rahila"Singphore yaje Check up ammh may be ya Dawo
Cikin Satin nan Domin yacemin yana so ya dawo cikin satin nan Zaije passing out
din da za"ayi anan Cikin Barkin Sojoji na Basawa Zaria.."Kada kai Anty Nafee tayi
kawai batayi mgana ita kuwa Sanah sai Santin kayan take.
Washegari Mallam Inuwa ya kwashesu da kayan ita da Anty Nafee da Sanah,Daada na
gida ita da Hibba saboda makaranta,Sai da suka taso Anty Rahila ta kira Bello
Tasanar mai suna tafe,bai gayama Aneesa Zuwansu ba,Sai dai yace mata ta Kira
Raihana ta tayata aiki zasu yi baki,bata damu Da ta Tambayeshi su waye bakin ba,ta
kira Raihana wacce ma ke Shirye Shiryen Tafiya School Of Hygen kano,Da Sauri kuwa
sai gata,ta kama mata tayi Tuwon Shinkafa Miyar ogun mai Namn Rago da manshanu sai
kunun aya da Zobo wanda suka saka Cikin Fridge yayi sanyi.

Raihana ta bari tana kara gyaramata Kichen din ita kuma ta Shiga wanka Ta Fito
tashafa mai Tana Cikin Sanya kaya taji kamar Muryans Anty Rahila Daga Falo,Daman
kuma Bello yana Falon Tundazu zaune yana Faman latsse latse bisa System
dinsa,Saurin karisa saka Rigar Atamfa nayi,na Daura Dankwalina Daurin Zahra Buhari
Banyi Makeup ba ammh na Shafa Hoda da Liptick,Na fice Falo da Sauri Harda mayafi na
ni azatona ma Ko abokansa malamai ne na nan BUK.

Mamaki ya kamani ganin su Anty Rahila ga akwatuna nan Mallam Inuwa da Salihu megadi
na Jerawa Bayan su daukosu Daga waje,Sanah ce ta Daka tsalle ta Rumgumeta tana
murnan ganinta itama murnan take ta saketa ta karisa ta Rumgume Anty Rahila wanda
Junior ke ta Kamo Sikat din Jikinta Tunda yafara Tafiya,Anty Nafee ce ta Harari
Aneeesa tana Fadin"Ni kenan ba yar"uwanki bace da bazaki min oyoyon ba.."Kunya ta
kama Aneesa tace"La..Ba haka bane.."Tafada tana Rumgumeta tabe baki tayi ta
Rumgumeta tana kallonta cikin mamakin ganin tayi kiba ita da Bello wanda Taga
yakoma kamar wani balarabe har sai da Sanah ta Furta mata da cewa"La Mami Anee dama
Balarabe kika Aura..? Dariya tayi tana kallonshi ta gefen ido irin zaka sani
dakamin Suprise Junior ya Tada Rigima sai da ta Daukeshi ta goya yako yi Lum Harda
su barci Bello sai kallonta yake yana Hararanta kasa kasa Duk Ashe Anty nafee na
kula dasu acikin Ranta tace"Kana Daga Zaune sai iskanci.."

Sai da suka kara gaisawa,Raihana ma ta gaishesu Dayan Bedroom din ta kaisu sukayi
sallah kafin ta kawo musu Abunci,suka ci suna santi suka Sha ruwa sai bayan sun
Huta ne sai ga Modibbo ya Dawo Shima Suka gaisa,Sanah nata kallonshi Taga Dan Farin
Bullatani Shikuwa Gabadaya Hankalinsa naga Raihana,wacce ta kosa tatafi ni na
Hanata.

Nayi mamaki da Farinciki lokacin Da Anty Rahila ta kaini Gaban akwatunan tace Duka
nawa ne Inji Mijina,Farinciki da Murna Suka Rufeni,Na Rumgumeta ina kuka Haka na
Zauna ina Bude kayan cike da Farinciki da Annuri Sanah na Tayani da Raihana,muna
cikin ganin kayan ne sai ga Anty Aisha ta so nan fa aka hade ana Hira da Zantawan
Zumunci,.Tashi nayi na barsu anan na wuce Bedroom dinmu na sameshi Zaune yana Shan
madaran Holladian gefe Daya kuma yana faman latsa wayarsa.

Kuramai ido nayi ina hawayen Farinciki Shi kuwa Kallona yake yi Lokaci Daya yana
girgizamin kai,daga gudu na tafi gareshi na Fada Jikinsa na zauna Bisa
Cinyarsa,Kofin Madaran ya ijiye Bisa Side drower din gadon lokaci Daya da wayarsa
ya saka Hannu Bibbiyu ya Rumgumoni ya matseni yana Fadin"Anthing For u My
Happiness.."Ina kuka Hawaye Shabe Shabe na Dako Kaina na tallafi Fuskarsa nafara
Sumbatarsa Cikin kauna Da Nuna godiya Sumba mai tsawo kafin mu saki bakin juna ido
Cikin Ido nake kallonsa kafin nace"U are my Dream...My Reality...My
Everthing...Bani da Abunda zan cemaka sai godiya kabani Dukkan Soyayyarka da
kulawarka...Thank so much B.love..I so much Love u..I love u..alwys Forever and
every single Day of Forever."Nafada ina Hawaye Lokaci Daya ina Sakar mai Wani Hot
kiss Bisa Lebensa Gabadaya kalamaina ya kashemai jiki kara kamkameni yayi yana
Fadin

"" I promise to Love..Today..Tomorrow..next tomorrow...Till Infinity..."Yafada yana


Lashemin hawayen Fuskata da Harshensa Lokaci Daya na kara shigewa jikinsa yana
Sakin Ajiyar Zuciyar kauna da muradi mai girma.
Sai washegari suka tafi Anty Aisha kuwa da Daddare Mijinta yazo yatafi da Ita Sanah
kuma Kiri kiri tabi Raihana Gidansu Wai chan zata kwana Modibbo ke sanar damu bayan
ya Dawo Daga kaisu, Sai da mukayi Lunch tare kana suka koma Cike da Farinciki,ammh
sai da suka Fara biyawa suka gaida Ammi Daganan suka Dauki Sanah da suka kulla
kawance da Raihana,harda karban Nombar Juna,Daganan sai suka kuma Biya gidan Anty
Aisha sama sama suka gaisa.

Cin kaniyata ko sai da Anty Nafee tayi agaban Bello ta kama kunnina ta murde kafin
ta sakarmin rankwashi bisa kai nayi gefe ina Kukan Shagwaba harda Hawayen Karya
Shiko harda min gwalo Ni ko nace akansa zan Rama,Suna komawa kwana Daya Anty Nafee
ta takara ta koma Maiduguri ita kadai ta bar Sanah anan zatayi sati kafin ta wuce
ibadan wajen Anty Yagana

******

Tun da Asuba Da muka tashi naji kaina na Bala"in ciwo kamar zai Tsage gida
Biyu,wanka ma Ban iya yi ba Dayake ina Fashin Sallah ganin bana jin Dadi ne, sai ya
kyaleni Dakayar na Taimakamai ya Koma Bisa kekensa ya Tura kansa Zuwa Tiolet yayi
wanka ya Dauro alwala,yazo ya chanza kaya ya tada sallah Duk ina Jinsa Sama sama
bayan ya idar ina Jinsa yana karatun Qur"ani wanda ya kara Dagulamin Lissafin Cikin
wani yanayi na Mike Cikin kayan barcina Riga da wando kaina ba Dankwali Gashi na
Duk ya bazu.

Cikin Tangadi na Diro Daga kan gadon ina Rike kaina ,bai lura Da Saukowa ta ba sai
dai ji yayi ina Fadin"Mallam kadaina karatun Qur"anin nan ko.." Na fada cikin wata
kakkausan murya kamar ba tawa ba Cikin mamaki ya Dago yana kallona cikin Nazarina
ganin ina Rike da kaina ina yarfa Hannu yasa ya K'ada kai Lokacin D'aya ya gano
mutanen kai na ne suka tashi Kansa ya maida yacigaba da karatunsa Cikin Muryansa
mai cike da Sanyi

Kara na saki mai Firgitarwa ina Layi hannuna saman kaina ina Fadin"Nace
kabari...Nace kabari....Bamaso....."Na fada cikin Tsawa bai tsaigaita sai ganin ina
layi Cikin Wata Murya nace"Baza....Ka...bariiii..ba..."Sai na Tafi Luu zan fadi ta
wajen Dressing mirror ga kwalaben Turare wanda ya tabbata in na Fadi Fuskata zata
samu mtsala Cikin Wani Kuzari da karkashi ya ijiye Qur"anin da Sauri yana Kokarin
Tura kekenshi Zuwa gareni Ganin zai bata Lokaci ne yasa yayi kokarin Tashi.

Ban san wani Hali nake ciki ba ammh sai ji na yi natafi Luu....Bisa wani Tattausan
Hannun Lokaci daya kuma ana Rumgumeni Bisa wani Faffadadan Ingarman Kirjin mai
cike da Zatin Haiba da mazantaka.

Ki biya ki karanta cikin salama..

*"Anitha...*
8/19/20, 11:26 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �?


400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani
zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?33*
Duk da yana cike Rudani tare da Farinciki Hade da mamakin Ganinsa tsaye Bisa
kafafunsa bai hanasa Rumgume Aneesa ba Lokaci Daya ya Dagata cak sai kan Tsakiyar
gadon ya kwantar Da Ita Haka take Fizge Fizge tana Kokarin Tashi Hawa kan gadon
yayi Sosai ya Rikota Kanta ya Daura Bisa Cinyarsa,Hannunsa kuma Guda D'aya ya saka
ya Rike mata Hannuwa ya cigaba da mata karatu acikin kunnunta.

Zabure Zabure takeyi Idanuwanta Suna Runtse Lokaci Daya tana fadin"Ka
bari...Ka..Bari bana so ka na Kona mu..."Ko takansu bai bi ba, yacigaba da mata
karatu Lokaci Daya yana Sake Riketa Sosai ganin tana Neman kwace kanta

Cikin karaji take Fadin"Ka bari...Muna konewa...Zamu Fita zamu Fita...Mun


Fita...Mun Fita..."Take fada kafin ta saki Numfashi Lokaci Daya kuma sai Atishawa
ajera guda uku Sai kuma Jikinta ya saki,Hannayenta ya saki yana Sakin Ajiyar Zuciya
Lokaci Daya yana gogemata Zufar Data Tsatsafo Daga goshinta.

Cikin Abunda baifi Sakwan Goma sha Biyar ba tafara Bude Idanuwanta Dishi Dishi har
ta waresu akan Fuskar Bello wanda ke Zaune yana kallonta,kuri ta mai da ido tana
kallonsa Shi kuma sai ya Sake Dafa goshinta yana Fadin"Sannu...Kan ya bari..? Da
mamaki take binsa da kallo kafin ta mike da Sauri tana kara kallonsa ganinsa Bisa
gado,cikin mamaki da in ina tace"Ya a...aka...yi kata..shi...? Tafada Bakinta da
Muryanta na rawa

Mirmishi kadai ya sakarmata kafin ya Sauko Daga kan gadon ya Tsaya Bisa kafafunsa
Lokaci Daya yana sanya Hannu Cikin Aljihun Bakin wandon Dake Jikinsa,Kura ma Aneesa
ido yayi yana mata wani kallo mai cike da Farinciki da kauna mai Dorewa.

Cike da mamaki da wani al"ajabi Aneesa ke binsa da kallo Lokaci Daya tana kara ware
Idanuwanta Akanshi Cikin Fitar Hayyaci Take Nunashi tana Fadin"Ka...wa..r...ke...?
Tafada tana Kara Murza idanuwanta Yar Dariya ya sakarmata kafin yace"Really..My
Happiness Na warke da ikon Allah kuma da Kuduransa.." yafada yana ware mata
Hannuwansa Cikin Sauri da Zabura Aneeesa Ta Dirko Daga kan gadon ta Fada Jikinsa ta
Dane kafafunta Bisa Kafarsa,shima riketa yayi Dakyau ya kara kamkameta yana
Fadin"Ke yar baiwa ce Anee...Duk sadda wani Abu zai Faru dake...Sai Allah ya kawo
mana mafita...Dalilink na fara motsa Hannayena Dalilinki na Fara Mgana yau gashi
Dalilin kar ki Shiga wani Hali na ganni Tsaye Bisa kafafuna...Tanque For coming
into my Life Aneesa...U are Such a give From god...I love u so much my wife..."

Yake Fada cikin wani yanayi mai cike da Muradi mai girma Aneesa Tadago Tana
kallonshi Lokaci Daya Hawaye suna Zubomta Cikin Farinciki da Annuwasha Ta Shiga
Furta"Alhamdulillah..Alhamdulillah...Allah ne Abun godiya.."Tafada Tana Dariya da
kuka Lokaci Daya,Harshensa ya Zaro yana Lashe mata Hawayen Fuskarta ita kuma tana
Faman Shafa kwattacen Sajensa Dayake karamasa kyau bai gama lashe Hawayenta ba ta
kama kansa ta aza bakinta Bisa Lebensa tafara Sumbata Cikin Fitar Hayyaci da Muradi
mai girma Shima Kugunta ya kara Rikewa yana Enjoying din Abunda Aneesar kemai
Lokaci Daya suka Cafki Harshen Juna da Sauri da Sauri Suke Aikama juna Sumbatar
kamar zasu cinye bakin juna Lokaci Daya kuma Suna kara Shafa Sassan Jikin Juna sai
da suka Shafe minti Goma sha Biyar suna jiyar da juna Dadi kafin su saki Bakin juna
Lokaci daya kuma suka Zurama junansu ido kafin su saki Dariyan Farinciki Dagata
sama Bello yayi yana Zagaya Dakin Da ita kamkanme kanshi tayi tana Dariya mai cike
da Annuri kafin ya Sauketa kasa,.

Baya taja tana kara kallonsa Farinciki yaki barin Ranta Cikin Zumudi ta Nufi
wayarta Dake kan Gado zata Dauka sai ya Rigata Dauka cikin Sanyin murya yace"Not
Now....Kyalesu mu basu Suprise ni yanzu Babban Burina na ma matata amfani ta yadda
Zata gane na warke yanzu...Ina so na Kure Jarabarta yau insha Allahu.."ya fada yana
sakarmata Manyan idanuwansa.

Baki ta rike tana Dariya bai tankamata ba ya isa Kusa da Ita ya Rumgomta Lokaci
Daya yana saka wayarta cikin Aljihun wandonsa,Lafewa tayi Bisa Jikinsa ba wanda ke
mgana sai saukar da Numfashi suke da Farinciki Lokaci Daya Zuciyarsu na Bugawa na
kauna da muradin Juna.

Nanike mata yayi ko kichen tare Suka Shiga tana Firan Dankalin Turawa Yana ta
bayanta ya Sakalo Hannayensa kan Cikinta ya Dora kansa Bisa Wuyanta Suna Hira sama
sama,Lokaci Daya kuma yana Dan yawo da Kugunsa Dake hade,ahaka suka gama Firan
Dankali ta dora musu ruwan zafi,Ta koma ta fara Soya Dankalin,Shi ya fasa mata kwai
Suka kuma Soya tare ammh duk sun bata Lokaci ana aiki ana Tsotsen tsotsen Juna oh
ni Jamila naga Bala"in

A kichen din suka karya ya taimakamata ta gyara wajen da suka bata In ka kalli
Fuskokinsu Bazaka taba Tsammanin sun taba zama cikin Rashin so ba..Zakayi Tunanin
sun Dade suna Nitso cikin Soyayyar Juna nan suka bar ma Modibbo nashi Dana Salihu
megadi suka koma Bedroom dinsi suka Shiga wanka Cikin Jazucci din ma Babu Inda
Bello bai Lasheshi ajikinta ba Bakinta kuwa har ja yayi saboda Tsotsa shima bakinsa
bada kyau take mai kamar zasu Tsinke bakin Juna Nipples dinta kuwa sun gayama aya
zakinta domin Bello yafi son Nonuwan Jikin Aneesa da komai yau din nan sun kara
Shan jagula dama tun yana Zaunensa Dayaji sa kan Jikinsa Bayan Bakinta Hannunshi na
rawa zai kai shi cikin Riganta yana mamulan Nonuwanta,kuma ya riga ya gano Lagon
Aneesa In yana Taba mata Nono nan da nan take rasa Natsuwarta..

Itama Zagewa tayi tana Nunamai Salon Soyayyah mai tsayawa azuciyar Masoyi,Lokacin
Datake Shafa saman Nipples din sa Daya,Dayan kuma ta saka Harshe Tana kadawa
Matseta Bello yayi Tana ji mahood dinsa ta mike sambal tana Wasa da tsakanin
Cinyoyinta matse bakinta yayi lokaci Daya yana sakin Numfashi cikin Wata Sarkewar
murya ya Furta.."No..Not now..Anee...ki bari in ba so kike na Haukace na Haike miki
cikin Bayin nan ba...Ki Kyaleni plz..."Yafada yana kara kamkameta Jin yadda yayi
mganar yasa ta Dago tana kallonsa ganin yadda idanuwansa suka chanza launi ne yasa
ta sakeshi tana Dariya Fita yayi Daga Cikin Jazuccin din bayan ya Daure Jikinsa Ya
bar mata Tiolet din Cikin mamaki tayi wanka ta Fito,sai lokacin ya Shiga sai da
yayi wankar Tsarki kana yayi wanka ya Fito,Lokacin har na Shirya Cikin Abayas din
da Dake cikin akwatunana da su Anty Rahila suka kawo,Tunda Wasu kayan kadai ta diba
ta tafinmu dashi zata bada a dinka min.

Ganin yanayinshi yasa ta Karisa garesha ta taimakami ya Goge Jikinsa ya Shirya


cikin Riga da wando na wani Farin yadi mai kyau da yarari,Shara shara ne domin
Hatta Farin Vest dinshi ana iya gani bai saka Hula ba Illah Cubing dinshi da Aneesa
ta mai tana kallonshi Lokaci Daya Ta Sakarmai mirmishi tana Fadin"Meke damunka...?

Hannuwansa ya maida Cikin Aljihu yana Fadin"Babu...Ammh kece kika maidani


Haka..."Yafada yana karkace haka Waro ido nayi ina Fadin"Ni kuma..? Da nayi mene..?
Na fada cike da Shagwaba,Fuska yadan yamutsa kafin ya juya yana Fadin"Ki bar min
wannan Shagwaba Allah..In ba haka ba i will Change my Mind yanzu nan kuwa..."Jin
Haka yasa na Dawo Daidai ina Dariya kasa kasa Bin Bayansa nayi Lokaci Daya ina Rike
Hannunsa Bina yayi da Idanuwansa ganin yadda nayi kyau Cikin Rolling din Da nayi da
Jan Vail duk da banyi kwalliya ba ammh Fuskata tayi kyau muna Rike da Hannun Juna
muka Nufi Falo muna Rangaji Cike da Sona da kauna.

Modibbo na Zaune Asaman Cafet yana karyawa muka Fito Lokaci Daya muna kanshin
Turare,Dagowa yayi yana kallonmu Daidai ya Tura kwai cikin Bakinshi ganin Bello
Tsaye Bisa kafafunsa ne yasa ya Dawo Dashi waje yana Zaro Ido harda kwarewa Dariya
Aneesa ta saka Shi kuma Bello ya Murmusa,Modibbo ya mike Yana Fadin"Wai gaske Nake
gani Baffale ne ke tsaye gabana ko kuwa mafarki nake..."Yafada yana Murza
idanuwansa,Kusa dashi Bello ya isa ya Dafa Kafadansa yana Fadin"Hau na goyaka sai
ka tabbatar..."Yafada yana Dariya kasa kawai Modibbo yayi ya Daidaici gabas,yayi
Sujjada yana mika godiya ga Allah kafin ya Dago yana Fadin"Masha...Allah..Allah
mungode maka.."Lokaci Daya yana Hawaye Bello ya saka Hannu ya Dagosa suka Rumgume
Juna Suna Murna Aneesa na gefe tana kallonsu cike da Farinciki.
Abincin da Modibbo bai gama ci ba kenan Saboda murna Shima yana rawan Jiki zai kira
ya mukatar Bello ya hanace yace ya bari gobe zasu tafi gabadaya sai dai su gansu
kwatsam da Abun mamaki,Suna zaune suna Hira sai ga Raihana itama Haka ta ware ido
tana kallon Bello ta kasa yarda cewa Shi take gani,Murna kuwa ba"a mgana Farinciki
ya cika Zukatansu.

Salihu megadi sai dai yaga Bello Tsaye agabaansa shima Haka ya Tuma yana kallonsa
Cike da mamaki ya Rikesa yana Zubama Allah Kirari sai gashi Ranar Bello ya Tsaya da
kafafunsa yayi sallah,ya Dade yana ma Allah Kirari tare da godiya gareshi Daya Nufa
zai kara Takawa a Doron Duniya da kafafunsa.

Sai gashi Ranar Abisa Dining mukayi Dinner cike da Farinciki Ni da Bello da Modibbo
da Raihana bayan mun gama Modibho yatafi kai Raihana gida mu kuma muka koma
Daki,mukayi sallah ba wanda muka Kira munyi Shuru da bakinmu Tunda gobe in Allah ya
yarda zamu tafi Abuja.

*****

Mun idar da sallar Isha"i kenan na mike ina Kokarin Tube Hijabin Jikina yana Daga
Zaune Bisa sallaya ya mike yana Fadin"Zamu yi sallah fa.."

Da mamaki na kallesa ina Fadin"Sallah kuma...? Kai ya gyadamin kafin yace"Eh sallar
godiya ga Allah...Daya bani lafiya sai kuma Babban na rokon zaman lafiya da Fatan
Allah yasa Bugu Daya Kwallona ya Shiga Raga.."Ya karishe Fada yana kashemin ido
Daya.

Jikina ne naji yafara rawa Ashe da gaske yakeyi bai Saurareni ba yajuya ya Tada
sallah,bani da kwarin Jikina na maida Hijabin na bishi sallar Ra"aka Shida mukayi
kafin mu sallame,Zaman Dirshan yayi gaban alkibla yana kwaroromana addu'o'in zaman
lafiya kafin ya waigo ya kama Kaina yana min addu"a ni kuma ina amsawa da amin Duka
Jikina yayi Sanyi ina Tuna girman Abun nan wai yau ni Zata ratsa,

Bayan mun idar ya mike yana kallona cikin Kulawa yace"Muje muyi wanka.."Kafada na
make ina Fadin"A"a Shiga ka Fito.."Baki ya saki yana kallona kafin ya zakuda kadafa
yana Fadin"Orl..Komai wayan Amarya dai sai ansha manta..."Banza nayi Dashi ya Shige
Tiolet yana yar dariya da kallon Fargaba na Bishi kafin na Nufi wayata Dake kan
Dressing Mirror Datake neman Dauki S.Jibiya ne na Dauka muka gaisa na tambayeta
karatu tace Alhamdulillah mun taba Hira sama sama Saboda bana cikin Natsuwata ina
tsaye muna mgana ya Fito Daure da Towel da Sauri na ma S.jibiya sallama na Datse
kiran Ina Raba ido kamar wata Munafuka.

Bai kalleni ba yana Tsane Ruwan kansa da karamin Towel din Dake Jikinsa yace"Toh na
Fito ki shiga kiyi gimbiyata..."Yafada yana yar Dariya Harara na sakarmai ina Tura
baki Hade Rai yayi yana Fadin"ko kin gaji ne nazo na taimaka miki ."Yafada yana
Nufo ni jin Haka yasa na Runtuma da Gudu zuwa bayi ina Kunkuni Dariya ya saka yana
Fadin"Drama Aneesa..."

Ina wanka ina Fargaban Abunda Zai Faru awannan Daren,Ammh haka na Wanke kowani
Lungu da Sako na Jikina na Kuma saka Sheving cream na kankare Sauran gashin Dake
gabana da Hammatana,Na dade kafin na Fito ina Daure da Babbam Towel ban sameshi
adakin ba ya Fita Zuwa kichen da Hanzari na Shafa oil dina na Fesa Turare Humrata
kuwa wacce Anty Aisha ta kawomin nayi amfani da ita,Gumbar kuwa Tuni na gama da Ita
na Bude wardrope dina ina Kici kicin Ciro Rigar barci yaBude Kofa ya Shigo da Sauri
na Dago muka hada ido sai da gabana ya Fadi ganin yadda ya sakarmin ido yana Rike
da Kofin glssa mai cike da Madaran Hollandian aciki ganin na Rude ne yasa ya kauda
kai ya isa gefen gado kan Wheelchar dinsa Dake wajen ya koma Zauna dana kallesa sai
ya Tunamin da ko Jiya yana Zaune akai lokacin ina Shirin Barci.

Dakyar na iya barin Gaban Wardrope din na koma Tiolet na saka Rigar wata baka ce
mai budewar gaba kuma iyakarta Rabin Cinyata pant kadai na saka Tundama bana kwana
da Bra,kunya ta hanani Fitowa na Tsaya kawai gaban Madubin bayin Ina bin kaina da
kallo ina Tunanin taya zan Fita ahaka,wai ni nake jin kunya yau.."Ban gama mamaki
naji kawai ya Bude Kofar Tiolet din ya Shigo Kokarin kare kirjina nake na manta ya
gama Gani Tuni,Mirmishi ya saki yana Kallona Cikin Karyewar Murya yace"Anee so kike
Allah yayi Fushi Dake..? Girgixa kai nayi kaina na kasa karisowa yayi ya Riko ni
yana Fadin"Kinsan Tun yauahe nake kwana cikin Son kasancewa tare dake..? Aneesa..Na
dau tsawon Lokaci ko Tabaki nayi bana iya barci...Kibar ni na mori lafiyata kila ma
kafin gobe da Safe na koma gidan jiya.."Da Sauri na kallesa idanuwana sun kawo
kwallah nace"No..Ka warke kenan Har Abada..Zuciyata bazata kara Juran Ganinka cikin
wani Hali ba."Mirmishi ya saki kafin ya Dagani cak yana Fadin"Na yarda dake....U ar
my happiness...Muje na Nuna miki yadda kike acikin Zuciyata ina so na Shiga Cikin
koramarki koda Shine na Farko kuma na karshe.."Yafada yana Ficewa Dani Daga Tiolet
din.

Kan gado ya Direni yana Bina da kallo nima shi nake kallo Hawaye na Taruwa acikin
Idanuwana,kissing din goshina yayi kafin ya kalleni yana Fadin"Should i.."?Kai na
gyada ina Kokarin maida kwallata Mirmishi ya saki yana Fadin"I love u.."Yafada yana
Sunkoyo da kanshi Zuwa Jikina Lokaci Daya ya saka hannu ya rage Wutar Dakin ya
kunna Dumlight.

Kissing dina yake in a romantic way,kamar zai tsinkemin Baki Da harshena nima
tayasa nake Lokaci Daya na Riko wuyan rigar barcinsa,Ina shafa saman Kirjinsa
Lokaci daya kuma ina Zame mai Rigar cikin Fitan Hayyaci,Bisa Kirjina ya Dawo bayan
ya saka hannu ya zame Rigar Jikina Hannunsa Duka Biyu ya saka yana ta mamula cikin
Fitan Numfashi Nima Numfashin nake ja Cikin Dadin salon da Bello keman,tafukan
hannayensa ya Kifa Bisa Nipples dina ya Murzawa kamar zan Suma saboda Dadi kara
Tasowa nake ina bangaremai kirjin lokaci Daya ina Wasa da Hannuna Bisa kwarmin
Bayansa.

Ban kara haukacewa ba sai da naji bakinsa bisa Breast dina yana Sucking dina,Bansan
Sadda na kamkameshi ba ina Sakin Numfashi mai hade da wani kara ,kai B.love karshe
ne sai da yagama Kunno ni Na kamu sosai na Fita Daga Hayyacina,Ina jin sanda ya
sabule wandon barcin Jikinsa,ni da kaina na sake Bude kafata ina Turamai
kaina,Nauyinsa ya Doramin gabadaya ya shiga karatan Addu"ar Saduwa da iyali kafin
ya Tura kai sai Lokacin naji Abun ya Tabani jin yana Turawa yasa na Fasa Ihu yayi
Saurin Hade bakinmu waje Daya ya ja da baya kadan kafin ya Sake Turawa Wani Azaba
naji wanda ya gigitani da karfi na Fizge bakina ina Fadin"Wayyo Allah na...Na mutu
na lalace.Don Allah kayi Hakuri na Tuba.."

Nake Fada ina kuka Tsausayi na bashi ya Dakata yana Fadin"Oh..Srry kinji...Bazan
miki da Zafi ba...i promise to be a gentle man Insha Allahu.."Yafada yana kallona
ta cikin Duhun Hasken Dakin kai na gyada ina Rikesa Cikin Tsoro bakin mu ya Sake
Hadewa kafin ya ja baya kadan ya sa kai da karfin gaske sai gashi ya Shige ji nayi
kamar an yankani da Reza ina so na Saka ihu ammh ya Damki bakina yana tsotsa kamar
zai Tsinkamin Kuka nake ina Dukansa ammh ko gizau sai ma Fita hayyacinsa Da yayi
Jin Sa cikin Wata koramar Ni"ima Kara kaimi yayi kawai yana Driving dina Crazy Duk
da yadda yaso yabini ahankali kasawa yayi sai da ya kwashe Mintuna Arba"in yana
Hakarta kafin yaji Abun yazo Kamkameta yayi Lokaci Daya ya Fitar da Abunda ke
Damumsa komawa yayi Jikina ya Lafe yana Sauke Numfashi ni kuwa bana iya Daga ko
yatsana Saboda Wahala

Sai da ya Dawo Cikin Natsuwarsa kana yaga aika aikan Da yayimin Duk Jini ya bata
zanin gadon,Cikin Rudewa ya Daukeni Cak sai Tiolet ya hadamin Ruwan Zafi ya sakani
aciki,Haka na Gantsare ina Tsala Ihu Rikeni yayi yana Fadin"Am srry....Uhm.Bazan
kara ba kinji my Anee.."Yafada yana Rumgomta Dakyar da lallashi na yarda Na Zauna
ya gasani ammh ina Tura baki ina Dukansa Ina Hawayen zafi ammh duk da Tabara da
shagwaba.
Ruwa uku ya chanzamin kafin ya barni nayi wankan Tsarki Bayan na Fito ne Naga ya
chanza zanin gadon,na Fito ina Dafe bango ina tafe ina Tale kafa,cak ya Daukeni ya
maida Bisa gado Ina Daure da Towel Ya Lullube ni da Blanket,na kallesa ina Tura
baki zan yi mgana ya dora hannunsa Bisa bakina yana
Fadin"Shiiii...Barci...Kinji."Yafada yana sakarmin kiss a kumatu Lokaci Daya yana
Fadin"dis one...Is for my Wonderful wife.....Tanque for u gift...Tanque For
yesterday i relli apprecient...",Kuri Aneesa ta mai da ido kafin ta Rike hannunsa
Tana Ta sakarmai kiss lokaci daya tana Fadin"Karka damu...It my pleasure...I love
u.."Na fada ina Lumshe ido kaina ya shafa yana Fadin"Oya Sleep bari na wanke zanin
gadon da nayi aiki...Nayi wanka.."Kai na gyada mai ina mirmishi da kallo na Bisa
har ya Fada Tiolet din yana sanye da Wandon Rigar barcinsa Cikin So da kauna gajiya
ce tasa barci ya kwasheni ban ma san sadda ya Fito yazo ya kwanta kusa Dani ba ya
Rumgomoni yana ta sakamin albarka acikin Ransa Shima Cikin Farinciiki barci ya
kwasheshi..

*******

Da safe shi yahadamana Breafasat,Tea da Soyayyen Buredi,Shi kuma ya Shiryamana kaya


Tunda ina kwance bana jin Dadi koda asuba sai da nasha pracetamol..na koma na
kwanta sai 8 na tashi shi ya taimakamin nayi wanka na Shirya ina Tura baki ina
Zubamai Shagwaba,ina kan Cinyarsa muka karya ina Zubamai Shagwaba Duk da naji Rauni
ammh ina karin Raki Sosai yadda nake narkewa kamar wacce aka yanka.

Naso mu fasa Tafiya Abuja Aranar Saboda yanayin Tafiyata ammh kuma sai naga Shi
yana ta Zumudi sai ban Nuna ba Na Dinga Daurewa,na Shirya cikin Riga da Sikt na
wata atamfa Mai kalan Ja na saka mayafina ja da Takalmi ja,sai jakata ma Haka banyi
Makeup ba ammh kallon Farko zakamin ka Fahimci bana jin Dadi,Shima yana sanye da
wata Shadda Fara gezner Dinki Zamani Riga da Wando,harda Hulansa Zanna Bukar mai
kalan Sararin Samaniya kalan Aikin Jikin kayan yayi kyau sosai kamar wani Balaraben
Sudan.

Shi ya Fitarmin da karamar Jakata inda ya sakamana kayanmu Nida shi,Modibbo ma


Andau wanka sai tashin kamshi,yake kulle gidan mukayi kafin mu Fada Mota modibbo ya
Ke jan Motan mu muna gidan Baya Bamu wuce ba sai da muka biya Gidansu Uncle Aminu
Ammi sai da Ta Rumgume Bello Domin Murna da Farinciki Raihana taso Binmu ammh
Rashin Lafiya Ammi ya hanata Tunda ba wanda Zata bari tare da ita bamu Jima ba muka
yi musu sallama muka Dau Hanyar Abuja ina kallon Modibbo shi kanshi bai ji Dadin
Rashin Zuwan Raihana ba.

Niko Zazzabi ne ya sake Rufeni na Lafe Jikin Mijina ina maida Numfashi sama
sama,kara Rumgume ni yayi yana Jin kamar ya maidani Ciki saboda so da kauna.

Kibiya ki karanta cikin salama...

*Anitha...*
8/19/20, 11:26 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �?


400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani
zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?34*
Karfe 11:30am na safe Modibbo ya zuba hon akofar tamgamemen get din gidan ya
Muktar Securitys suka Bude mana get bayan sun tabbatar da mune.

Ban san mun iso ba Sai da naji Bello na Shafa Fuskata na Farka Ina Matse ido cikin
Tattausan Mirmishi yace"Sleeping Beauty mun iso.."lum nayi da ido kafin na Riko
Hannunshi,modibbo ya Fito Daga bangaren Direba ya Budemana kofar Baya shi yafara
Fitowa sai ni wanda muke Rike da Hannun Juna Mallam Inuwa da Sauran Securitys din
gidan gabadaya suka zubamana ido Barin ma Bello da suke kallonsa cikin mamaki
ganinsa tsaye bisa kafafunsa.

Da hanzari mallam inuwa ya karisa bakinsa har kunne yake Fadin"Yallabai kai ne nake
gani tsaye agabana..? Kai ya gyada mai kafin yace"Nine mallam Inuwa..Allah ya bani
lafiya.."Yafada yana sakarmai Mirmishi.

Zubewa yayi agabanshi yana Mai Nuna Farinncikinsa Cike da murna,haka ma Securitys
din gabadaya suka Saramai alamun Barka da Arziki Gajiya nayi da tsayuwa yaji na
Fara zamewa zuwa Jikinsa yasa ya kalleni yana Fadin"Kin gaji ko..? Sannu mu shiga
ciki ki kwanta.."Rausayar Dakai nayi ina Fadin"Zazzabi nake ji.."Rumgomini yayi
yana Fadin"Ayyyh..Am srry Duk nine ko.? Bazan kara baki wuya ba kinji My
Anee..."Batayi mgana ba Illah kara lafewa bisa jikinsa datayi tana Shakan Kamshin
Turaranshi.

Modibbo Tuni ya Shige ya barmu Afalon Farko muka Ciro da Alheri Itama cikin mamaki
ta zube Tana gaishemu shine kadai ya amsa ni ban iya mgana ba sai dai binta da ido
har muka wuce zuwa Falon Anty Rahila tana binmu da kallon Mamaki,nan muka tarar da
Jummai tana gyara Falon Tana ganinmu ta zube itama tana gaishemu Lokaci Daya tana
mamakin ganin Bello yana Tsaye da kafafunsa kamar bashi bane aka Fita dashi Cikin
keken Marasa lafiya.

Modibbo Shashen Daada ya Iskesu ya muktar da Anty Rahila Sakamakon Jiya ya Dawo
Daga India Checkup yana gida bai Fita ba Ganinsa kawai sukayi kwatsam ya muktar ya
kallesa sanda yake zama Bisa Daya Daga cikin Kujerun Falon Cikin mamaki yake
Fadin"Ikon Allah Modibbo Allah yasa dai lafiya..? Yafada yana kallonsa Mirmishi ya
saki kafin yace"La lafiya lau...Ji idanuwan Daada toh sha kuruminki taremuke da
Baffalen da kanshi.."Hararansa Daada Tayi kafin tace"Kaji dashi dai..Nidai nace
banayi Dakai Bello dai shine megidana ayi gaba.."Dariya ya saka yana Fadin"Allah ya
raka taki gona..Daada Ai ni ko akafa aka Dauran ke na kwance.."

Dakuwa Ya muktar ya sakarmai yana Fadin"Kaniyarka Daadar ce zaka ce ma haka..?


Dariya ya karasakawa kafin yayi mgana Bello da Aneeesa sun sawo kansu Falon Bakinsu
Dauke da sallama Gabadaya Daada da Anty Rahila da ya Muktar suka zubama kofa ido
Kusan Daskarewa sukayi ganin Bello Yashigo Shida Aneesa Dukawa yayi ya Sabule Sawun
cikin Dake kafarsa itama Aneesa ya taimakamata ta cireta nata suka Dago Atare suna
kallon Juna kafin su Damke hannun juna suna bin Fuskokin su Ya muktar da kallo
wadanda gabadaya suka mike sun kame waje Daya kowa na Salati da hailala acikin
Zuciyarsa.

Cikin Mirmishi Bello yace"Daada,ya mukatar,Anty Rahila...Nine dai...Jiya Allah yayi


ikonsa Na tashi Bisa kafafuna ni na Hana akiraku saboda ina so na baku mamaki
ne."Yafada kamar zaiyi kwallah ai sai Ya Muktar ya Zube kasa ya Daga Hammu sama
yana Fadin"Alhamdulillah...Alhamdulillah...Allah mungode maka..Allah mungode maka
kai ne Shugaban Halittun Duniya...Baka Haifa ba kuma Ba"a haifeka ba...Godiya ta
tabbata ga Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam.."Yafada Lokaci Daya Hawaye
suna kwaranyowa Daga kwarmin idanuwansa,Daada da Anty Rahila suma godiyar sukema
Allah suna Share kwallah Cikin Farimciki Bello ya Saki Hannun Aneesa ya karisa ga
Dan"uwansa ya Duka suka Kamkame juna Lokaci Daya Cikin Tsantsan Farincikin ahaka
suke mike tsaye Daada tazo ta Hadasu ta Rumgumesu cikin kuka take Fadin"Allah
mungode maka...Allah Abun godiya.."Ita kanta Aneesa sai da taji Tahowar kwallah
Cikin Sanyin Jiki ta karisa ta Fada Jikin Anty Rahila suka Rumgume Juna,anan ne
taji jikinta da Zafi da sauri ta Dagota tana Fadin"Aneesa baki da lafiya ne..?
Jikinki ya Dau zafi.."?

Da Sauri Bello ya saki ya muktar da Daada yana Fadin"Eh bata jin Dadi...Taho my
Anee kije ki kwanta ko zamu tafi kiga Dr ne.."?Yafada yana Rikota kai ta girgiza
tana kwanciya Bisa kafadansa cikin Sanyin murya tace"Zan kwanta.."kura mata ido
yayi yaga har ta Dan Fada Rikota yayi sosai Bisa Jikinsa yana Fadin"Oya muje ki
kwanta ki Huta...In kin tashi in zazzabin bai sauka zai mu tafi kiga likita ko..?
kai ta gyada mai suka Fara Tafiya su Daada suka bisu da kallo Cike da Sha"awa
tafiyar Aneesa ne ta Fallasata Mirmishi Anty Rahila tayi cikin Ranta tana
Fadin"Aneesa ta girma..."cikin jin Dadin mara misaltuwa Ya muktar ko baki yaki
Rufuwa Shi ya Dauki waya ya kira y Ali yana Labatarmai wannan Daddalan Labari
kowayaji sai ya saaki kabbara cike da Farinciki Ita kuma Daada ta kira Adamawa ta
sanar ma Baffa hardo Shima haka yayi ta kabbara yana Zubama Allah kirari yaji Dadi
sosai kuma ya tabbatar da Babu Abunda ya karfin Allah Tabbas Kudaran Allah ne yasa
wani Abu ya Giffta aka hako wannan Jakin da aka binne da Rai wanda akayi Ma Bello
Shihiri dashi.

Haka Abun yafaru dama an binne Abun atsakanin Dajin Abuja da Minna ne, Cikin Ikon
Allah sai Titi yabi ta wajen nan da nan Turawa suka saka inji suka markade kasar
wajen suka hako abun batare da sun sani ba,dama kuma makarin karyewar Asirin Shine
ahako wannan Jakin Dake cikkin Rami wanda aka Daure Wuyanshi da layan Sihirin,toh
wajen hako Abun Inji ya Darkake jakin Shi kuma layar ya bar Wuyan Jaki bayan injin
din yayi Fata Fata dashi ,wannan Shine Dalilin Daya sanya Bello ya Taka da
Kafafunsa kamar bai taba wani Abu mai kama da Jinya ba.

Dakinta na da ya shiga da ita ya kwantar da ita bisa gado ya lulluba mata blanket
yana kallon Fuskarta yace"I love...U my Anee...Banajin Dadin ganinki ahaka..Ki
gafarce ni banyi da niy..."Bai karisa ba ta rufemai baki tana girgizamai kai
tace"Kadai na bani Hakuri kada Allah yayi Fushi dani Abunda yake mallakin ka ne fa
ka karba B.love...Ko yanzu kace kana Bukatata ni mai mika Wuya ce...Kasani ni
matarkace kuma Rufin Asirinka...Ina sonka Gwarzona ina Kuma alfahari da samunka
amatsayin mijin Aurena..."Tafada tana Sakarma Hannunsa Kiss Dadi ya kamashi ya Duka
ya bata sumba mai tsawo kafin ya mike ya zauna kusa da ita yana matsa Tafin
Hannunta yake Fadin"Kece Abun Alfaharina Aneesa...Naso na Tafka asara da na bari
kasim ya Aureki da yanzu bana cikin Farincikin Danake ciki yanzu..I realy Love u
my wife.."Yafada yana Kara matsemin Hannu Lumshe ido nayi cikin so da Kauna
nace.."Love u...Forever and Ever...B.love.."Nafada ina jin kamar na Bude Zuciyata
na sakashi Saboda yadda Zuciyata ke Bugawa da kowani Harafi na Soyayyarsa.

Yana ta matsa min Hannuna yana min kalamai kauna mai Tsayawa azuciyar Masoyi Har
barci ya kwasheni sai da nayi barci kana ya lallaba ya Fito Falon Daada nan fa aka
hadu ana ta Hira kafim kace kwabo labari ya kai kunnen yan"uwa da abokan Arzuka sai
kiran waya ake ana Tayasu murna,Uncle Aminu ma sai gashi ya kira kila Ammi ta
gayamai Su Abba kabiru ne kadai ya muktar ya manta dasu bai kirasu ba,kuma ba wanda
ya Tunamai yan'uwana sai kiran wayata suke domin Tayani murna ammh basu samuna
Domin ina kwance ina barci Anty Rahila ya baiwa wayar take dauka tace nazo bana jin
Dadi ya muktar kuwa yana Cikin Farinciki wanda saboda murna yace gabadayansu zasu
tafi su sauke Farali wannan Shekarar Harda Baffa Hardo Tunda Daada ta sanar da
Bello komai na taimakon shi Dayayi kan wannan Ciwon nashi Bello yaji Dadi kuma yace
insha Allahu zai taka har Adamawa ya kaima Baffa hardo gaisuwa tare godiya Modibbo
kuwa Tundazu ya koma shashen Bello ya Shige ya kwanta yana ta waya da Raihana,yana
sanar da ita Wannam Shekaran Allah ya kirasa zai sauke Farali nan tayashi Murna
kafin su shiga Hiran Soyayyahrsu.

Aneesa bata tashi ba Sai Bayan la"asar kana ta tashi Shima Anty Rahila ce ta tada
ita ta mike tana Mika Lokaci Daya tana Fadin"Anty Rahila anyi Azahar ne..? Hararan
wasa ta kai mata tana Fadin"Eh lalle toh har la"asar anyi Azahar kuma sai dai na
gobe..ki tashi kiyi sallah mijinki ya hana atasheki yanzu ma yatafi shashenshi
ne,yasa na shigo na Tadake."Saukowa Tayi Daga kan gadon Tana Fadin"Allah Sarki
B.love.."Tafada tana gimtse baki jin kasanta na mata Zafi Da kallo Anty Rahila ta
bita kafin tace"Kin shiga ruwan zafi kuwa..? Cikin jin kunya Ta Daga kai batare
Data waigo ba Anty Rahila bata mata mgana ba ta nufi Tiolet din ta Hada mata ruwa
mai Zafi ta Fito Tana Fadin"Ki gasa jikinki sosai...In kina so kidaina Dingishi
kuma wajen yayi Saurin warkewa..Ba"a taurin kai awannan harkan in baki kula da
kanki ba ke kika sani.."Tafada tana rabata ta Fice Daga Dakin Kunya ta kara kama
Aneesa tayi mirmishi ta Fada Tiolet din.

Taji Dadin Ruwan Dumin sosai Ruwa biyu ta chanza kafin tayi wanka ta Dauro alwala
ta Fito,cikin kayan ta Tun na gida ta saka wata Doguwar Rigar Atamfa Tunda kayansu
na Mota ba laifi taji Dadin Jikinta ta Daina ma Dingisa kafar sai da nayi sallar
Azahar nayi la"asar na sallame kenan Bello ya Turo kofa ya Shigo yana Fadin"Anee
wannan barcin yayi yawa.."Yafada kenan sai kuma ya ganni tsaye ina Kokarin kwabe
Hijabin jikina

Mirmishi ya sakarmin yana Fadin"Ashe kin tashi..? Kaina Gyada mai ina Fadin"Anty
Rahila ce ta tasheni nayi sallolin dake kaina.."Na fada ina hamma Riko ni yayi yana
karba Hijabin hannuna ya ijiye yana Fadin"Sai da fa nace karta ta tasheki..ya
zazzabin..? Ya sauka..?kai na Damgwabe ina Fadin"Daidai nake jina sai dai yunwa
dana ke ji.."Mirmishi yayi yana lakacemin Hanci yace"Oya muje na baki abinci ki ci
ki koshi har ki kasa tashi.."ware ido nayi shi kuma sai ya Riko hannuna yana Dariya
kan Kafadarsa na yada kaina Muka Fita Daga Dakin Zuwa Falo.

Babu kowa cikin Falon na Daada,Zaunar dani yayi kan kujera yaje ya Karbomin Abinci
a kichen yazo ya Zauna kan Cinyarsa ya Zaunar dani yana Bani abinci har sai da na
koshi,Yana cikin bani ruwa sai ga Daada ta Fito Daga Daki baki ta rike tana
kallonmu Lokaci Daya take Fadin"Lalata..Kai Bello miye haka nan fa ba gidan ku
bane.."

Kallonta yayi yana Fadin"Daada ki koma ciki kawai in dai bazaki iya gani ki kyale
ba...Nifa bana iya zama ban rabi my Anee ba itama Haka.."Dariya Aneesa tayi ganin
yadda Daada tayi,bata samu Zarafin mgana ba Modibbo ya Shigo ganin mu Ahaka yasa ya
shafa keya yana Fadin"Au Daada kema kin gani ko..? Haka nake fama muna kano Baffale
na kan keke ya iya barna.."Yafada yana Dariya Hararansa mukayi Duka Tare Kada kai
Daada tayi kafin tace"Umh...Naga alama Marasa kunya.."Tafada tana juyawa zuwa Cikin
Bedroom dinta muka Bita da Dariya,Modibbo ko Waje yayi yana Fadin"muma mun kusa
shiga wannan Stage din..".

Mudai bamu bi ta kansu ba..Bayan ya gama bani Abinci Muka koma muka lafe Bisa
kujera ina kan Jikinsa ina waasa da Sajensa muna Hira sama sama sai da aka kira
sallar mangariba kana muka rabu yatafi masallaci ni kuma na shiga daki nayi tawa
ina idarwa sai ga Hibba ta shigo Dakina da gudu tana Fadin oyoyo Anty
Anee..Rumgumeta nayi na Dagata sama ina Murnan ganinta Daganan muka Fita Falon Anty
Rahila inda na isketa tana waya da Ya Sunusi har tabani muka gaisa yana min Barka
da Arziki naji kunya sosai,nan ya bama su Mama Yana da Falmata mukayi Mgana suna
kara nuna Jin Dadinsu Ashe hardasu a wadanda Ya Muktar ya zana zamu hajji bana naji
Dadi sosai.

Dakyar Daada ta kori Bello ya koma Shashensa Da yace anan zai kwana ga matarshi
bazai kwana da kato ba Modibbo na Dariya yana Fadin Allah ya sakamun Baffale nine
kato,hararansa Bello yayi yana Fadin"Toh in ba kato bane mace ne kai.."Daada ko ta
iza keyarsa tace ya Fice mata Daga Shashe bata son Rashin Kunya bai da yarda zai yi
Haka ya Tafi Ni kaina banji Dadi ba Domin na saba kwana Bisa Kirjin Mijina Nima ina
Tura baki da kunkuni na Nufi Dakina ina Fadin"Daada wai ina ruwanki da Shiga
tsakanin miji da matarsa.."Tace an shiga din ba anan zaku man rashin kunyarku na
Diyan zamani ba..Su ya muktar naji suna Dariya Dole dai kanwar naki Hibba nace tazo
Tatayani kwana,ammh Kusan Raba Dare mukayi muna waya na Tambayeshi ina Modibbo yace
yana cikin Daki shi kuma Falo ya Fito bayaso yaji Sirrin ma"aurata Dariya kawai
nayi muka cigaba da Soyewarmu.

*******
*Kaduna...*

Kasim da Aisha kuwa suna Cigaba da soyewarsu bata Tunanin wani Abu zai iya Faruwa
anan gaba cikin wannan Halin ne ta fara ciwo,zazzabi komai taci baya zama acikinta
Tunda kasim yaga Haka Hankalinsa yatashi yafara zargin Ciki ne nan ya dauketa suka
tafi Asibitin Barau dikko dake Kaduna agwajin Farko Ciki dan Wata uku ya bayyana
ajikin Aisha

Ta firgita sosai nan ta Shiga Rusa kuka,Ammh sai Kukanta ya tsaya Jin Kasim na
rokar likitan ya taimakamai ya Zubar da Cikin Jikin Sadiya cikin mamaki ta waro ido
tana kallonsa kafin tace"A zubar fa kace..? Toh saboda mene..?.

Kasim ya wurgamata wani bazan kallo kafin yace"Eh haka nace..Saboda mene kike
Tambaya? in kika Haifi D'an Shegen wa zai zama Ubanshi balle har yamai
Dawainiya.."Cikin mamaki da Nadama Aisha ke kallonsa kafin tace"Akwai wanda ya
kamata ya Zama Uban abunda ke cikina Bayan kai,Saboda kaine Ubansa kafi kowa sanin
banta sanin wani Namiji ba bayan kai.."Wani Banzan Kallo ya Cigaba da Jifanta dashi
bai mata mgana ba illah yafice ya barta Domin Tuni Likitan yace su barmai Office su
wannan Asibitin ba asibitin Zubar da ciki bane..

Da Hanzari Aisha ta mara mai Baya Cikin kuka yana Shirin Tada motar ta Fada Motar
tana Haki Bata samu zarafin mgana ba ya Figi motar suka bar Haraban Asibitin sai da
suka Dauki Hanya kana ya kalleta cikin Kakkausan Murya yana Fadin"Ki tabbatar da in
baki bari an zubar da Cikin nan ba...Toh sai dai ki zama uwarshi da Ubanshi ke
kadai Domin ni ban Shirya fara Haihuwan Shege ba.."Aisha ta Kuramai ido tana Hawaye
tace"Kasim kasan kuwa me kake Fada..? Hararanta yayi kafin yace"Bansani
ba..."Yafada Cikin bacin Rai kara Rushewa Tayi da kuka tana Fadin"Wlh bazan Zubar
da cikin jikina ba...Da Farko munyi kuskuren aikata Zina bazamu Tuba ba bayan
Abunda muka Dade muna aikatawa yafito Fili ba..Ba zan yadda na kara aikata wani
Zunubin ba Kila ma wajen yunkurin zubar da Cikin Jikina na Mutu me zan ce ma Allah
in na mutu cikin wannan Halin..?

Ko kallonta bai yi ba Daidai Lokacin da suka kariso gida ya kashe motar yana
Fadin"Alrigt...Tunda Haka kika Zaba ki sani Lokacin Rabuwarmu Tazo kada ma ki
kuskura ki Nuna kin Taba sanina.."Ya fice yana Daukan wayarsa da Sauri Aisha ta
Bude Murfin Mota ta Fice Da Gudu ta tari gaban kasim tana Fadin"Bangane Nufinka
ba..Ina alkawarin da kamin na zaka Aureni komai Runtsi..? Ka Rifamin Asiri kasim ka
Aure ni mu Rufama juna Asiri.." tafada tana Kara sakin kuka Kamar Ranta zai Fita

Dariya ya saki kafin yace"Na Aureki..? Kinyi kuskure Babban Aisha Da kike Tunanin
zan iya Auranki kinganni nan Bazan iya Auran kowacce mace ba sai Aneesata,in kuma
ba ita ba sai dai na samu wata yar mutumci na Aura bake ba gantalalliya wacce taci
amanar Tarbiyar iyayenta ba.."Yafada yana Kallonta Cike da Raini.

Aisha ta Dago tana kallon Kasim Cikin mamaki tace"Ka cuceni kasim...Tsakani na
dakai Allah ya isa..Kuma Aneesa Dakake mgana har Abada bazaka taba samunta ba Mugu
Azzalumi insha Allahu sai kagani.."Tas..! Ya sharara mata Tafi sai da ta kife Cikin
Fushi yake Fadin"Ke kika Cuci kanki Aisha Domin bani nakira ki ba ke kika kawo
kanki da Kafarki..Kuma bari kiji na gayamiki albarkacin Aneesa kikaci har na Kulaki
ammh ke baki kai matsayin Da zan Hada Jiki da ke ba..Na dai mori jikin ki ne kawai
Malama ki tashi ki kwashe kayanki ki Ficemin Daga Gida Asarrrariya mara
Tarbiya.."Yafada yana Nuna ta da yatsa Lokaci Daya ya Shure ta da kafa ya Shige
cikin Falonsa.

Kuka Aisha take na Nadama da Danasani,kafin ta rarrafa ta mike tana Tangadi ta


shiga cikin Falon yana Zaune kan kujera yana Daga kwalba ko kallonshi batayi ba Ta
Shiga Cikin Bedroom din ta Shiga Hada kayanta tana kuka Tana Cikin Tura kayanta
Cikin Akwatunta ne taci karo da wani karamin Littafi mai Dauke Adireshin wani gida
akatsina tana gani jikinta ya bata Adireshin Gidansu Kasim ne bata tsaya wani
Tunani ba ta Dauka ta Tura cikin akwatinta ta Fito Tana kuka jaye da Trolley dinta
ta Tsaya gaban Kasim tana Fadin

"Zan tafi...Ammh ina so kasan wani Abu Daya Zan dawo...Zan dawo na kawo maka Abunda
kayi Sanadiyar samuwarshi...Da izinin Lahi yadda kayi Sanadiyar Lalatamin Rayuwa
sai rayuwarka Ta D'aidai'ce...Allah ya isa Tsakanina dakai...Na barka da Allah shi
zai min sakayyah mafi girma.."Tafada tana Sakin Gunji kuka kafin taja Jikinta ta
Fice Daga Falon tana kuka ko kallomta Baiyi ba banda ma Mirmishin Mugunta da Kasim
ke saki Wayarsa ya jawo ya Kira Haruna yana gayamai Abunda ya Faru.

Cikin Rashin Jin Dadi Haruna yace"Kash...Meyasa kayi mata Haka kasim ina tsoron fa
watarana..? Cikin maye Kasim yace"Dillah manta da ita babu abunda ta isa tayi
karamar yar iska ce.."Yafada yana Dariya Shidai Haruna Jinsa kadai yakeyi ammh kuma
wata Zuciyar nashi na Tsoron Faruwar wani Abu.

Sadiya tana kuka Ta Shiga Adaidaita zuwa Tashar mando nan ta samu motar
maiduguri,Ta Shiga ta Rufe Fuskarta da Hijabi tana Rusar kuka Lokaci Daya tana ma
kaduna kallon karshe,Domin ta yarda bayan Rasa mutumcinta datayi harda karatun da
iyayenta suka ci Buri akanshi shima ta Rasashi Kasim ya Cuceta da izinin lahi sai
yaga Sakayyah.

*****

*ADAMAWA..*

Tafiyar jirgi mukayi Zuwa Adamawa bayan mun kwana Biyu agarin Abuja Dukkanmu muka
Tafi Ya muktar,Daada,anty Rahila da Hibba junior sai modiboo da ni ba Bello,muka
tafi kai naga Tarin Dangin su Daada kyawawa Farare Ashe anan Mijina ya Debo kyau da
Tsari irin na Fulani,

Baffa Hardo kuwa Rumgume Bello yayi yana Murna Haka Yan"uwa aka zagayemu ana Nuna
ni amatsayin matar Baffale,suna mamakin yadda nayi Namijin Kokarin Kula Da Bello
kai gaskiya naji Dadin Zuwan mu Adamawa Sosai Sai da muka Shafe kwana Hudu kana
muka Dawo Abuja nan muka bar Modibbo sai ya kwana Biyu zai Dawo bayan mu rabu kan
in zai dawo zai zo da passpost din Baffa hardo saboda Shirin tafiya aikin Hajji nan
da wata Biyu,Tunda shikadai ya rage musu duk sun rasu sai dai ya"ya da suke tasowa
sukayi Aure suka Hayyafa.

Mun Dawo Abuja da kwana Daya Bello yakoma kano Saboda zai Shiga Cikin Jami"a ya
saka Hannu dawowrshi aiki ammh bazai Fara zuwa ba sai bayan mun Dawo Daga Aikin
Hajji Tukunnah Dakyar na Rokeshi ya barni ya tafi da yace kafata kafarshi,Sai da
Daada tamai Tsiya kana ya kyaleni Duk na Fahimceshi kewata ce tamai yawa Domin Tun
Haduwar Farko bamu kara samun Dama ba sai dai in mu hadu muyi Tsotse tsotse da
Tande Tanden juna,ni kaina nasan nayi kewar mijina ammh naji Dadin yadda yadagamin
kafa saboda na warke sarai kamar babu Abunda ya sameni.

B.kaita da S.jibiya Hoton da muka Dauka Nida Bello yana Tsaye ina Rumgume
Jikinsa,Muka Dauki Hoton Lokacin Muna Adamawa ne na Bude whattap na tura musu
Dukkansu sai ga kiransu suna tambayana ya haka..? Nan nake gaya musu komai ihu suka
saka suna Murna Dukkansu suna gida ne sunje Hutun Farkon Semester,nan nake basu
labrin zamu tafi aikin Hajji Sun tayani murna Sosai tare da mana Fatan Allah ya
Daawo damu lafiya.
Ki biya ki karanta cikin salama...

*Anitha..*
8/19/20, 11:26 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?35*

Dakyar ya iya kwana Biyu ya tattaro ya dawo Abuja,daya shiga Cikin makaranta kuwa
Dalibai da malamai sunyi matukar Farincikin samuwar lafiyansa Kuma Suna maraba
dashi akoda yaushe,Ya sanar dasu sai bayan ya Dawo Daga aikin Hajji kana zai dawo
aiki insha Allahu Sauran Cike cike ne yayi da Report kafin ya Dawo Abuja kamar yana
kan kaya Kwana Daya yayi ya tatttaro ni muka Dawo,Lokacin angamamin Duka Dinkunana
sai muka taho tare Dasu

Adaren da muka Dawo na gayama Aya zakinta Duk da Zafin bai kai na Farko ba ammh na
Dandana Gud'ata,Da Asuba bayan mun idar da sallar ina kwance Bisa Kirjinsa na
lafemai,shi kuma yana Wasa da gashin kaina yace"Anee in dan kara Daya.."?Baki na
Tura ina Fadin"Kai B.love nidai A"a na gaji Tun jiya fa kake ta karawa ."Na Fada
ina kokarin sakamai kuka.

Rumgumeni yayi yana Sakin Ajiyar Zuciya kafin yace"Once fa Anee Allah minti 30
bazan wuce ba.."Kukan shagwaba na sakamai ina Fadin"Wajen fa yana ta zafi ne Dama
bai gama warkewa ba...Nidai A"a.."Nafada harda matse kwallar karya.

Numfashi ya sakarmin Bisa dokin wuyana kafin yace"Shii..Is ok na Hakura Tunda baki
so kwanta Kiyi barcinki kinji ko babu Abunda Zan miki.."Yafada yana kallon kwayan
Idanuwanta.

Tsausayinshi da kaunarsa suka Ratsani na Sakarmai kiss a kumatu kafin nace"Bazan


zama mai gardama ga mijina ba...Gani a gareka kayi yadda kaga dama dani.."Nafada
ina Shafa kirjinsa wanda ke cike da gargasa Nipples dinsa nake shafowa cikin
kwarewa da Shauki,cikin Farinciki ya kankame ni yana Fadin"U d best...I love u my
Anee.."Yafada Lokaci Daya ya Hade Bakinmu waje Daya cikin Wani Salo yake sabule
Doguwar Rigar Dana saka da zamuyi sallah ni kuma Ina ta shafa Kirjinsa Zuwa bayansa
Zuwa Kansa da bayan keyarsa.

Kafin wani lokaci mun taru mun Rikita juna da Salonmu kafin muma Juna
Rumfa,Rumgumeni yayi yana sakim min Numfashinshi Bisa Dogin Wuyanta cikin Fitan
Hayyaci da wani gardin Dadi yake Fadin"Ya salam...! Aneeta...Plz dont let me go..I
can do Without u...I Love u Forever and Ever my happiness Wife..."Yafada lokaci
Daya hawaye suna zubomai Bakinsa na Hade Da nawa Saboda na lura haka zai tamin
Sumbatu.

Shafewar mintuna Arba"in kafin mu samu Natsuwa Kamkame yake Dani yana maida
Numfashi Nima Numfashin Nake maidawa sama sama,Yadda naji yana sama sama da
Numfashi ne,yasa na Dago ina kallonsa cikin Daga gira nace"Ya ne...? Lumshe ido
yayi kafin yace"D'adi Anee..."Yafada yana kara kamkame ni,nima kara Kamkameshi nayi
kamar wani zai rabamu ina Dariya nace"Dadin mene kuma..?
Cikin kunni na ya Radamin"D'adinki mana My Anee...U are so Sweet..More Than Sweet
Babby..."Yafada yana Lasan gefen Wuyana da Harshensa Zillo nayi ina Kara kamkameshi
Cikin Farinciki,ina Dariyan Murna Haka muka cigaba da Gayama juna kalamai,kafin mu
tashi mu shiga wanka tare,chan ma sai da muka kara Lalacewa kafin muyi wanka tsarki
mu fito,tare muka Shirya muka Fita Zuwa Kichen muna Abun karyawa Muna Rumgume da
juna Kamar wasu Tantabaru mayun Soyayyah.

Duk wanda yazo yaga irin Rayuwar Da muke gudanarwa sai Abun ya bashi Sha"awa Anty
Aisha ce tazo ta wunin mana mukasha Hira da zata tafi tayi ta bani Shawarwarin
yadda zan kara kula da kaina ta kuma Shawarceni da na Dinga Shan kayan lambu da
maadara sai zuma da Abu mai Romo romo Da zatafi ta Bani gumbar mata datazo min
dashi tace na Dinga sha da Nono Kindormo,Nayi mata godiya sosai muka Rabu akan sai
nazo...

Raihana ta rage zuwa gidana yanzu saboda Dagani Har Bello bama kunyarta muna manne
da juna ita kuma kunya ke sata bata zuwa kana kuma Habibin nata baya nan yana
Adamawa wato Modibbo,Satin mu biyu da dawowa Sai ga B.kaita da S.jibiya sun zo min
dukkansu zasu koma makaranta ne nan muka wuni muna Hira da Shewa sukayi ta Zuzuta
kyan da nayi da kiba nidai sai dariya domin nasan gaskiya suka Fada Namiji ya
budani na zama wata Big mama

Wajen la"asar S.jibiya ta shiga mota zuwa katsina ta koma Makaranta B.kaita kuma
sai Dare,kana ta koma cikin Makaranta Ita da yar"uwanta Aliya,suka barmu nida
B.love dina muka Dasa Daga inda muka Tsaya akullum wani Sabon kulawa muke bama juna
kamar zamu lashe juna saboda so da kauna Duk da mukan samu sabani ammh bama bari
yayi tsawo zamu bama juna hakuri saboda bazamu iya taba Rayuwa babu Daya Daga cikin
mu ba.

Bello ya Dubomin Result dina nima na samu Duka 9 creadit din Da"ake Bukata bai ce
min komai ba ammh yace akwai Shirin Daya ke mana ne kila na Fara karatun anan gida
Nageria in kuma Shirin nashi ya Tabbata ko na Fara sai dai mu koma Abraod na
cigaba,Nayi murna sosai Domin Nima ina bukatar nayi karatun Tunda na Fahimci
makullin komai na rayuwa sai da Ilimi.

Modibbo yana Adamawa Raihana tatafi Sch of hygen tatafi da Sati Daya,kana shi kuma
ya Dawo yayi ta Cizon yatsa Duk da Suna mgana ta waya shima din muna Dawowa Daga
Hajji zai wuce Military sch Jos,Tunda angama komai Dama Abunda ya Dakatar da Ya
Muktar Rashin lafiyar Bello yanzu kuma Tunda ya samu lafiya sai ya cikamai Burinsa.

*****

Aisha kuwa Haka ta isa maiduguri tana kuka kamar Ranta zai Fita tayi alkawarin
bazata Boyema mahaifiyarta komai ba ita da w'anta wanda dama mahaifinsu ya rasu
yayanta ne ke rike da ita,da ita da Mahaifiyarta

Sun kansu sunyi kuka da Jin wannan Labarin sun kuma yi Tir da wannan Soyayyar da
Aisha kema Kasim,Nan mahaifiyarta ta bada goyon bayan Aisha ta Haifi Cikin Jikinta
Tunda tasan Uban da yayi mata cikin in ta haifeshi zasu Daukeshi su kaishi inda ya
Dace.

Aisha tayi nadamar Biyema Soyayyah da Sharin Zuciya daya kwasheta ta Biyema kasim
ta lalata Rayuwarta Kullum Cikin kuka take da Neman gafaran Ubangiji Inda Allah ya
Taimaketa Mahaifiyarta bata juya mata baya ba,gwara ma yayanta din yana cikin
bakincikin Abunda ta aikata ko gaisheshi tayi baya amsawa,toh ya zasuyi Hannunka
baya taba Rubewa ka yanke ka yar....

Haka Aishaa ta cigaba da Renon Cikinta,Tsakaninta kuwa da Kasim ya yanke duk wata
alaaqa da Ita Tuni ya goge Nombarta acikin wayarsa ita kuma gabadaya Layin ta
chanza Saboda bata kaunar Duk Abunda zai Tuna mata da Rayuwarta Bata Fatan Wata
mace ta sake Tafka kuskure irin nata,Duk yadda suka so boye Abun sai da ya bayyyana
sun sha mganganu da Zagin makota Harda masu Shigowa ganin kwaf,Aisha tayi kukan
yadda ta saka kanta da iyayenta Cikin damuwa ammh acikin Ranta tana kara Tsinema
kasim da Fatan Allah ya saka mata akan Abunda yayi mata.

****
Dawowarmu da Sati Hudu aka Fara Azumi,modibbo na nan Tare damu a kano,Wata rayuwa
muke gudanarwa mai cike da Sha"awa,har akayi azumi aka gama muna kano Da sallah ne
muka Sha yawo Nida Bello mune har Borno Sai da muka kwana uku kana muka Dawo,Sai
gashi har maiduguri munje gidan Anty Nafee tayi murna sosai Kunsan Ita tana bala"in
so a girmamata,Da zamu tafi muka cikata da kayan arziki,Su ya Ali sunyi Murna da
Zuwana ganin na kara kyau na Zama babbar mace Uwa uba kuma Mijina bai iya Boye
Soyayyar Dayake man Ko agaban ko waye Mahaifiyata tafi kowa Murna ganin Inganta
rayuwata Ni kaina naji Dadin Zuwan mu gida Daki na musamman aka ware mana muna cin
Duniyarmu da Tsinke Nida Bello,munyi kiba mun chanza kamar bamu ba.

Har Ibadan sai da muka je,gidan Anty Yagana muka kwana mata Biyu ita da mijinta
Sunyi murna da ganinmu,Haka muka Zauna anata Hira muna Tuna baya Mijin Anty Yagana
nabama Bello Labarin Tsiyar danayi Lokacin da aka kawoni Ibadan na Zauna Dasu sai
dariya nake ina Tuna Lokacin acikin Raina na Shaida lalle nayi Rayuwa,Bello kuwa
sai dai ya kalleni yana Mirmishi Domin kaf halayan na ba wanda bai sani ba kuma ba
wanda ban gwadamai ba.,Sanah na nan Ibadan tana Wajen Anty Yagana ta kara girma ta
zama babban Budurwa Duk da tana da Girman jiki.

Munsha yawo Sosai bayan mun dawo kano Har kaduna muka je gidansu Sani Tayashi
Murnan Aure yayi Aure Lokacin Bello na Zaune baida lafiya Shima yayi murna da
ganinmu dashi da amaryasa mai kyau Mariya bamu so kwana ba Suka matsamana sai da
muka kwana Washegari kuma muka Dawo gida Sai da muka Huta kana Mukaje gidan Anty
Aisha na Wunin mata Shi kuma Bello suka Fita da Megidanta sai Dare suka Dawo sai da
mukayi Dinner kana muka yi musu sallama muka koma gida.

Rayuwarmu gwanin ban Sha"awa ga wanda ya ganmu Bello dai ke ta complain din ya kosa
na samu ciki,ni kuma bana son na samu ciki nafi so sai munje Hajji mun Dawo kana
kada mafarkina yaki Tabbata na Ganina gaban Dakin ka"aba.

******

Shiryen Shiryen Tafiyarmu Hajji ta kankama sosai,Dayake zamu Tafi da wuri ne,Madina
zamu Fara isa,Shiyasa Duk Abunda ya kamata komai ya kammallah ta Abuja Dukkanmu
zamu tashi,Ana saura kwana goma Tafiyar tamu ya muktar ya samu Waya Daga Abba
kabiru yana sanar dashi kasim ya samu matar aure in bazai damu ba kuma baida wani
Uzuri zai jagoranci Tafiya zuwa kaduna domin Nema masa Auren,Ya muktar bai damu ba
yace ba matsala indai nan kusa ne Saboda zasu tafi aikin Hajji sati na sama,sai
lokacin Ya muktar ke Fada ma Abba kabiru Warkewa Bello da Dalilin Tafiyarsu makka..

Abba kabiru yaji Abun kamar almara,sai dai kuma ya Shanye mamakinsa,Shi ya kira
Abba garba yana Fadamai shima yaji mamaki sosai Acikin Zuciyarsu Tsoro ya
Darsu,basu nuna ma bane,Jin haka yasa Suka gaggauta Shirya tafiyan Saboda Suna so
Muktar ya jagoranci Tafiyar Tunda Shima wani ne akasar kamar yadda mahaifin yarinya
Shima sananne Tunda Dan Siyasa ne.

Ana saura kwana Biyar Tafiyarmu Su ka tafi kaduna nema ma Kasim Aure wanda ba wanda
ya sanar dashi warkewar Bello shi azatonshi Haryanzu yana nan Jiya yau saboda
Dogara da Maganar Boka.,Dayake ba yawan Zuwa gida yake baida labarin Wasu abubuwa
ya Hashim ne shima Sabgogi sun mai yawa bai cika bi takan kasim din ba...

Bayan tafiyar Aisha da wata Biyu Kasim ya hadu da Zainab yar kaduna ce gaba da baya
anan anguwar kinkinau,take mace ce kyakyawan kin kowa kin wanda ya Rasa,Tunda
mahaifiyarta Bafullatan Yola ce,Lokacin da suka hadu harta kammallah Digree dinta
Service take shine aka Turota wajen aikinsu Kasim shikuma ya na ganinta yaji zai
iya Auran Zainab bayan Aneesa,Lokacin Daya gabatar da kanshi bata mai gaddama ba
Saboda yakai karshe Wajen sace Zuciyar yan mata,Nan da nan suka Fara soyayyah wanda
yake jin kamar ma bai taba son wata ya mace ba,sai zainab gata tafito Daga Babban
gida Suna da Kudi na Rufin Asiri.

Basu wani jima suna Soyayyah ba Babbanta yace ya Fito Shine Dalilin Daya sanya yaje
katsina ya sanarma Abba garba wannan karon Umma tafi kowa murna Domin Har katsinan
Kasim ya kawo mata Zainab suka ga Juna ta yaba da ita sosai ga kyau da Hankali ga
Nasaba,tayi ta yabonta tana Fadin ko shi fa yanzu ya zabo Abu mai kyau ba wanda
yayi Tunanin kasim ya cigaba Da hallayarsa Haruna ne kadai ya sani Shima abokin
Shamshancin nashi ne Duk da bai kai Kasim zama Bunsuru ba.

Zuwan ya muktar ya karama musu kima sosai Chief army of Staff na kasa baki Daya
Dole akayi komai cikin girma Sadaki Dubu Dari uku Ya muktar ya Biyama kasim su kuma
suka Fito da kayan saka Ranar da suka zo Dashi nan take aka saka Ranar Auren nan da
wata uku masu zuwa In Allah ya yarda Aka Rabu Cikin Aminci da mutumtawa Haka suka
dawo da labari mai Dadi dama su uku suka Tafi Ya mukrar ya Hashim da Abba garba.

Kasim Daya samu labari yashiga Farinciki kansa ya kara Fashewa Jin Zainab na Zuzuta
Danginsa masu arziki ne da Sanin yakamata,Ya gama sankanceewa wannan karon kam zai
Tubanma Allah ya rage neman mata duk da bawai ya Daina Duka bane,Sai Shaye shaye
shikan duk dare sai yayi Tatul yake iya barci bai taba Tunanin wani Abu zai kara
Faruwa Dashi ba shiyasa yakara Sankankacewa zai mallaki Zainab Hankali
kwance,Aneesa kuma ya Tarrata ya maidata gefe Duk da haryanzu bawai ya cire rai da
Ita bane.

*****
Ana gobe tashin Jirginmu Mallam Inuwa yaje ya Taho da Baffa Hardo,Tun safe kuma Su
Ya Ali suka iso da Mama yana da Mama Falmata da Ya Sunusi matansu na gida zasu kula
da komai kafin su dawo Mu kuma sai Dare muka iso Nida Bello da Modibbo washegari
kuma karfe 6:00pm na yammah Tawagar Ya muktar suka kaimu Filin Jirgi Nmandi Azikiwe
international Airport Atafiyar Hibba ne kadai da Junior yara,suna Rike wajen
iyayensu ni kuma ina Sanye da Bakar Abaya na Nade kaina da bakin Vail din rigar
jikina Ajirgin yawo zamu Tafi jirgin na musammane domin Ina Rakube Jikin Mijina,Ya
muktar da Ya Ali da ya Sunusi suna tare sai Daada da mama yana da mama falmata sai
Anty Rahila ita da Hibba sai modibbo da Baffa Hardo junoir na wajen Babanshi.

Sai karfe 8:30pm na dare Jirgin mu ya Lula zuwa Sararin Samaniya,lokacin da Jirgi
zai tashi kamkame Bello nayi ina Rawan Jiki bai yi Tunanin komai ba ya hade bakinmu
waje Daya Bai sakeni ba sai da Jirgin ya Daidaita tafiya a sararin samaniya kunya
ta kamani ina waigawa bayana Naga su Ya Ali nasan suna kallonmu kau da kai sukayi
Tunda mu da su Baffa Hardo muna First class ne,Bello na kallah Shima ya kalle ni
ina Tura baki nace"Kaga fa su ya Ali suna kallonmu.."Hancina ya lakace yana
Fadin"sai me...? godiya ma zasu tamin sun samu gwarzon namiji mai kula da yar
Autansu Da kyau."Yafada yana Dariya Duka na kaima Kirjinsa ina Tura mai baki na
lokaci daya ina kukan Shagwaba Rikeni yayi yana Dariya kafin na Fada jikinsa ina
Boye Fuskana ganin munhada ido da Ya Ali yyi Saurin kauda kai Shiko Bello ko
ajikinshi Sai Ma kara gyaramin kwanciya dayayi ajikinsa yana min Rada acikin
kunnina.

Mun Sauka agarin Madinatul munawarra Acikin Hotel masu Tsada kuma Duka Dakunan mu
suna jere da juna ne,Ni da Mijina Daki Daya ya muktar da ya Ali, sai Daada da su
mama yana Anty Rahila dai ita da hibba ne sai Modibbo da Baffa Hardo,Tunda muka iso
Kowa ya maida kai ga Ibada munyi Ziyarce Ziyarce sosai,kullum nida Bello acikin
masallacin madina muke Wuni kaf khmasin salawati acikinsa mukeyi sai Dare muke
komawa masauki Gabadayanmu kai sai da nayi kuka Lokacin Dana ganni agarin Annabin
Rahma kwana Goma sha biyar mukayi Muka isa garin Makka..
Sai gani gaban ka"aba ina kuka sosai na Farinciki Allah ya Cikamin Burina ina
Rumgume Jikin Mijina ina kwararo Addu"o"in gamawa da Duniya lafiya na Rokarma
mijina Fatan Nasara na Rokarma mahaifina gafara da Rahma na koramar Duka yan"uwana
da Abokan Arzuka ina yi ina kuka gani nake kamar acikin mafarki,Tunda muka zo kowa
ya Dukufa ga Ibada bayan angama aikin Hajji kwana Bakwai muka kara Nida Bello muka
bar su Ya muktar garin makka sai sunyi Siyyayya nan da kwana Hudu zasu koma gida mu
koma muka Lula Babbar Birnin kasar Ameriaca wato U.S wanda ban ma san da Tafiyar ba
Ashe Tuni ya Shirya Abunshi yace akallah zamu kwashe wata uku muna Zagaye kasashen
Duniya kafin mu Dawo gida Nageria,yana,kuma Fatan Allah yasa kafim mu dawo muyo
Tsaran Honey moon.

Lokacin Daya Fadamin Haka muma cikin Jirgin da zai kaimu America ne,Rumgumeshi nayi
ina Hawayen Farinciki ina Fadin"Bansam da wani kalma zan Nuna godiyata ba
mijina...I love..Tanqur for all ur care ...Concern,And Support and Tanque for Treat
me like a queen..."Na fada ina sakamar kiss agoshinsa Hawayen Idona ya Shiga
Sharemin da harshensa Lokaci Daya yana Fadin"U deserve...More Dan dat...My Anee I
love u my Wife...."Yake Fada yana kara kamkameni nima Kamkameshi na sakeyi ina jin
kamar na bude Zuciyata na sakashi.

Ki biya ki karanta cikin salama

*Anitha...*
8/22/20, 7:45 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?36*

....."Akallah mun kwashe Tsawon Kwana goma sha uku a babban birnin America wato
U.S,Munyi yawo Sosai kama daga wajen Shakatawa Bicth kala kala,koda yaushe muna
manne da juna wata irin soyayyah muke gwadama juna wanda mu kanmu bamu san iyakarta
ba,Iyaka dai kowa yana kokarin ya nuna yafi kowa sanin muhimmancin Dan"uwansa.

Hatta Makaratan Dayayi Masters dinsa sai da ya kaini na gani,Nayi matukar mamaki
wanda yazo yayi karatu cikin turawa da jajayen Fata ammh Duk da haka yazo yana
koyar damu a Makaratan Secondary ta kwatar-kwashi Hakika mijina Dabam ne kuma aikin
koyarwa Tana yawo acikin Jinin jikinsa ne.

Kafin mu baro garin mukayi waya dasu ya muktar nan yake gayama Tun kwana biyu da
suka gabata suka koma gida Nageria,Nan yace musu mukan ba yanzu ba,ya muktar yace
maza karmu Dade ya kamata yadawo ya koma bakin aikinsa ai ya Huta sosai,ya amsa dai
da insha Allahu bazamu wuce wata biyu ba zamu dawo.

Daganan muka tsallake zuwa portagul,shima sai dai muka Shafe kwanaki goma muna Shan
Hutu,nan din ma ba zama mukayi ba mun yawata sosai Naga wurare da ko amafarki banta
Tsammanin Ni Aneesa Bukar Bulama zan Taka da kafata ba sai gashi Dalilin Gwarzon
Mijina Mr Bello Muhammed jikamshi na taka kuma yasa na zama cikakkiyar mace mai iko
da Fariya,Tuni muka gano cewa dukkanmu Muna son juna Tun Lokacin da muke fama da
rashin Jituwa,mune bamu gane ba sai yanzu da muka zauna waje Daya kowa ke kokarin
Fito da Soyayyarsa ga Dan"uwansa.
Daganan kuma muka yada Zango Ababban Birnin India wato Delhi Dama ina son garin
Delhi sosai Bani da wani buri Bayan zuwa Dakin Allah Daya wuce na ganni Ababban
garin na India,Duk da nazo Lokacin da muka zo da Bello ammh bana cikin Natsuwata
ban tsaya na mori garin ba sai wannan karon,Jin Dadi yafi koyaushe Tunda wannan
karon kafata kafar Gwarzona sai gashi har cikin Asibitin kashin daya kwanta na
kaishi Dr kabirkhan,da Sauran ma"ikatan Jiyan Dake Asibitin sunsha mamakin ganin
Bello Tsaye Bisa kafafunsa,Saboda mamaki sai da sukayi Hoto da Bello yace zai Tura
ma Dr philphil domin har yau har gobe yana cikin mamakin Ciwonsa.

Munsha Hutu da yawon Bude ido akallah kwana Kwana 20 kafin mu Daga Egypt,nan ma mun
dan jima Domin munji Dadin garin Sosai,Daga Egypt muka Sauka a london wanda Daganan
muke Tunanin komawa gida,kwananmu mu Biyar da zuwa muka fara zuwa Manyan Plaza
dinsu Siyayyah Jiri ya Debeni zan Fadi Bello Ya tareni na fado jikinsa,Daganan sai
Asibiti ya kaini aka bani gado Bayan an sakamin Drip sauran gwaje gwajen da suka
biyo baya sai ga Ciki na Tsawon wata Hudu ajikina Wanda Nida Bello bamu sani
ba,Sai da aka fada muka yarda muka D'auki Sauna domin na kara zama katuwa nayi
Haske Hips dina da Boobs dina sun kara Cikowa yawancin kayana sabbi Bello ya
siyamin saboda wanda nazo dashi sun ma kadan nabude na ban mamaki Shikanshi in ya
kalleni Sai yayi mamaki ganin yadda na koma ya dinga tsokana na wai naji Dadin
kokarinshi nabude na zama big mama,Tura mai baki nake na Fada kanshi ina Dukanshi
Lokaci Daya nake fadin kai ma haka kake... Ji beka harda da Tumbi kayi kana ta
kwasar Dadin Anee,Dariya zai saka yana kara tsokanata.

Ashe haka mijina keson Haihuwa murnan Dayayi wlh bata da iyaka haka ya Rumgume ni
yana Zagaye Dakin Da"aka kwantar Dani,nima Farincikin nake domin akoda yaushe nayi
sallah sai na Roki Allah ya bani ciki mai albarka ganin Bello Yadamu da rashin
samun cikina,ashe ma ina dashi makale acikina bansani ba nan suka rikemu sai da na
kwana hudu kafin su sallamemu saboda yanayin jikina yasa muka Dade agarin kafin
mufara shirin komawa gida Wajen Sati uku muka Shafe kafin mufara Fita Siyayyah
Tunda mun kusa komawa gida

Bello ba wanda bai kira ya Yada Labarin samun cikina ba,yan"uwa sai kira suke suna
min sannu,Ni kunya duk ta kamani ammh wlh shi ko ajikinsa yana bada labari yana
Dariya,Maza basu da kunya ko kadan balle gwarzona duk Abunda ya Shafeni baya Hadasa
da komai,Anty Rahila ce ta kiramu tana Fadama cewa Cikin satin nan za"ayi Bikin
Kasim suma zasu tafi chan katsina Itada yara da Daada,nayi mamaki Domin ni na ma
manta da wani kasim,ni nake gayama Bello labarin Bikin sai da nayi nadama domin
tsayawa yayi yana kallona kafin ya Tamke Fuska yana Bina da wani kallo wanda ya
Tsinkamin ya"yan hanji Bai min mgana ba yafice ya barni kwance Adakin Hotel din da
muka Sauka.

Duk yau din take Fadamin Modibbo ya tafi military school jos tun bayan
dawowarsu,ammh bai tafi ba sai da ya Furta shikan Anema mai Auren Raihana domin ita
yakeso ya muktar yace kar ya damu Tamkar an bashi,na tabbata Bello ya sani shine
bai sanar dani ba,Raihana kuma Tunda muka zo sau daya mukayi waya,Gwara ma su
B.kaita suna kirana Lokaci bayan Lokaci,basu dai cika min waya ba sunce gwara subar
malaminsu ya kwashi kayan Harka sosai.

Ashe sanda ya fita Uncle Aminu ya kira awaya sukayi mgana kafin ya Dawo,ko kallona
baiyi ba niko ganin haka sai na saka mai kuka ina yi harda Sheshheka yana Zaune
Bisa kujera ya dora kafa Daya kan Daya yana latse latse Bisa System dinsa bai Dago
ba balle na saka ran zan samu wani kyakyawan kallo ko lallashi ganin kukana bai zai
saka ya kulani ba sai na mike Dama ina Sanye ne cikin Riga da wando Black and white
wadanda suka Dame min jiki sosai har dan matashin cikina yafito.

Mikewa nayi Daga kan gadon ina Sharbe Hanci ganin ko Kallona baiyi ba yasa na tsaya
ina cije baki ina kallonsa cikin Takaichin nasan kishi ne ke cinsa jin nace mai
kasim zai yi Aure kuma ni bada wata manufa nayi mganar ba naga yamai ne,kila bai ji
labari ba,nima Allah karamin da bakina wanda baya iya yin Shuru,Tsalle na Fara yi
Bisa gadon ina kuka da karfi Harda matso kwallar karya Cikin mamaki ya Dago yana
kallona Lokaci Daya kuma yana Tattare naman goshinsa,ganin yana kallona yasa na
kara kaimi har ina Dukan gefen cikina cikin Kissa,Ware idanuwansa yayi yana kallona
Lokaci daya kuma ya kada kai yana Dariya cikin Ranshi Anee sarkin wayau..

Ganin banyi nasara ba yasa na tsaya ina Haki Lokaci Daya na Dirko Daga kan gadon Da
karfi har Sai da ya Dago yana kallona cikin Fushi yace"Meke damunki ne..? Be
carefully Aneesa kinfi kowa sanin bazan juri ki Salwartar min da cikina ba.."Yafada
yana wani Kara hade Rai.

Jin Abunda yace ne yasa nayi Dariya acikin raina sai da naga ya maida hankalinsa
bisa Laptop dinsa yasa na Fara taku kamar zan shiga Tiolet na juyo naga baya
kallona sai na Duke ina Fadin"Wayyo Allah...Zan mutu...Cikina zan mutu..."Nake Fada
ina Dukawa harda yarfe hannu da Sauri ya Ture Abunda ke gabansa ya karisa gareni
yana Rikoni cikin Rudewa yake fadin"Menene..? Ciki kuma Anee..?kinganni ko..?kinga
Abunda nake gudu ko..?muje Asibiti kar asamu matsala.."Yake Fada yana Kokarin
Daukana Tsab na Lamgwabe ya Daukeni har ina kara lafewa bisa Kirjinsa ina Dariyan
mugunta,yana Sauri ya Dibi gudu zuwa Falo Dariyan da nake boyewa ta fito cikin
mamaki yake kallona ganin haka yasa na gimtse Dariya,Ware ido yayi yana min wani
kallo kafin ya ijiye ni yana Fadin"Oh....ni zaki hadama wayau ko..? Shagwabe Fuska
nayi ina Fadin"Yo bakai bane kaki kulani ba.."Nafada harda matse kwallah.

Hannunsa yasa yana Zagaye Habansa cikin Daure Fuska yace"Ok...Wato ke nan mai wayau
ko .? Jikinsa na fada ina Mai kukan Shagwaba cikin Matse kwallah lokaci daya ina
matseshi cikin
Jikina ina Fadin"Am srry...Kaina bisa Wuya..bani da kwanciyar hankaki matukar
gwarzon Aneesa na Fushi da ita..."Nafada ina kallonsa ido cikin ido Ajiyar Zuciya
ya sauke kafin ya Kara Rumgumeni yana Fadin"Ina da Kishi sosai akanki Aneesa...Bana
kaunar naji kina ambatan sunan wani Namiji wanda kikaso kafin ni agabana...Kirjina
na Zafi ina Ji kamar zan mutu in na tuna cewa shi kika fara so kamin ni.."Saurin
Dage nayi na Hade bakina da nashi,Saurin Rike kaina yayi nima na rike kansa ina
Shafa Keyarsa zuwa Dogin Wuyansa,Sai dai mukayi sumba mai tsawo kafin na sakeshi
ina Fidda Numfashi cikin So da kaunar Mijina nace"Karka ka sake jin Zuciyarka na
zafi saboda wani chan kasim..Wlh sai bayan na Aureka na Fahimci ban taba son kasim
ba,kawai burgeni yakeyi,kai ne kadai namiji wanda nakejin Sonka na Zagaya dukkan
Jinin jikina,Kallon kyakyawan Fuskarka kadai kan sakamin Natsuwa kaina Jarumina
kuma gwarzona Uban ya"yana...I love u B.love ka yarda kai na fara so acikin
Zuciyata..."Nafada ina kara Fadawa Bisa faffafan Kirjinsa Cikin magagin so ya kara
matseni yana Fadin"Love u more....And more my Anee.."Yafada yana sakarmin kiss
asaman kaina Lokaci Daya yana Dagani sama cikin Dariya yace"Muje na gwada miki
cewa..U are my only one..."Sakala hannayena nayi ina Fadin"Nima zan kara gwada maka
No one but u Mr Bello muhammed jikamshi..."Nafada ina hade bakinmu waje Daya Haka
muka Nufi Bedroom dinmu bakin na cikin Na juna muna kara Rikita da juna da Salon da
muka saba.

*********
*NAGERIA*
_Katsina..._

Tuni Shiryen Shiryen Biki ya Dade da kamkama baki na nesa dana kusa Tuni suka cika
gida Umma sai wani Fariya take tana wani Bude hanci adole wannan karon dai tana
maraba da Auren haka ta kakkane komai ko mama sahura ba wanda ya nema,Ita kuma sai
taja kanta gefe ta sama Umma ido tana kallonta,Tun ana Saura kwana biyu biki Anty
Rahila da Daada da hibba suka Iso gidan Abba kabiru wanda ke cike da baki zuwa
yammah kuma sai ga matar Ya hashim da Zubaida sun iso Zulfa"u dama Tana gidan Duk
da ba kwana take ba da yammah take tafiya gida ita da Mama Sahura Inna Rukayyah ma
tazo ita dasu Hamdiya sai da kuma suka Raba Hali da Umma saboda yadda take nunawa
kamar Kasim ba Danta bane ba,ba nuna kara ba komai Shine Inna Rukayyah tamata
mgana ta nemi zaginta har sai da takai ta tsinketa da mari,wanda ya harzuka
Zuciyar Umma ta kama kuka har yan"uwanta suka Shigar mata suna Fadin maganganu
Zubaida ma Sai da tayi mgana saboda mene za"a mari Ummanta Ran Inna Rukayyah ya
baci itama ta Fashe da kuka.,Anty Rahila dasu Daada sune ke bada Hakuri Mama Sahura
kuwa Abba Kabiru ta kira tana kuka Kissa tana Shaidamai Abunda ke Faruwa.

Cikin bacin rai ya Shigo gidan,Ai kuwa Umma sai da ta raina kanta,domin Abun kanta
ya koma gaban yan"uwanta da ya"yanta Abba kabiru yaci mata Zarafi bai raga mata
kuma ya bata Rashin gaskiya su kansu yan'uwan nata yace su shiga Taitayinsu ko kuma
su bar mai gida yanzu sanin Halinshi na Tijara yasa suka kama bakinsu ita kanta
Umma tana kuka tana komai ta shige dakinta Mama Sahura Tabi da kallon Kadan kika
gani Zulfa kuwa da Zubaida sai Harare hararen da kallon Juna akarkarce suke
haryanzu basu daina kishin Juna ba Duk da kowa ta Fidda ranta ga Bello har gwara
ma Zubaida takan Tunashi Watarana ita kuwa Zulfa tunda ciwon nan ya sameshi taji ya
Fita Ranta dama bashi take so ba kyanshi take so da lafiyansa yanzu ya nakasa bata
Bukatarshi.

Dukkansu kowaccensu na aji biyu ne going to 3,gwarama Zubaida ya Hashim na saka


mata ido tafi maida hankali kuma ya hanata tara samarin banza ammh Zulfa Duniyarta
take ci da Tsinke duk ko da Sa"idon da mama Sahura ke mata.

Kasim kuwa yana kaduna bai Dawo ba Saboda suna chan suna ta partys kala kala,kamar
ba Auren Sunna ba,Haruna ne Babban abokin ango,sakamakon Baban Zainab dan Siyasa ne
yasanya Gabadaya kafafen yada labarai tagama yawo da sanarwa katin bikinsu,sosai
kasim ya saki kudi akayi Hidima,gidanshi ya saka aka gyarashi sosai aka Fitar da
Duka kayan gida aka saka wasu,dama tun na wanda aka sama Aneesa ne ba wanda yabi
takansu,Ita kan Zainab din iyayenta sun mata bajinta sai wanda yagani,yamata
akwatuna Wanda suka fi ma na Aneesa saboda yadda yakejin Zainab aransa kamar Tafi
Aneesa ma Saboda yana Tunanin in har ya samu Zainab toh har Abada bai da wata
damuwa da Aneesa kuma.

******
Rana bata karya sai da uwar Diya taji kunya ayau Asabar 03/03/2020 da misalin karfe
11:00am na safe aka Daura Auran Zainab Alhaji isa kinkinau,da angonta Kasim kabir
jikamshi akan Sadaki mafi Daraja.

Daurin Auren Daya samu Hallatar manyan mutane kama Daga yan Siyasa Abokan Harkan
Babanta da kuma Kososhi acikin gwannati kama Daga Tawagar Sojoji wato su ya muktar
kenan da kuma Wasu Daga cikin yan Sanda yan kasuwa,da abokan aikin Kasim din Sun
musu kara sosai domin itama Zainab din sun saba da ita,da yan"uwanta yan Corpas,An
Daura Auren ne A babban masallacin Jumma"a dake Kinkinau,Inkaga Bakin kasim kamar
Gonar Aduga saboda Yadda Fararen Hakoransa ke yawo awaje,yana gaisawa da mutane
yana saba babban Riga ana cikin wannan Hayaniyar na gama Daurin Aure sai ga Motar
yan Sanda guda biyu sun iso wajen Suna zuwa suka Sassauko Rike da Bindigogi babban
Cikinsu ne yace ina kasim kabir jikamshi aka nuna musu shi yana kallonsu cike da
mamaki kafin yayi magana sun fito da ankwa suna Fadin"Ure a under arrest..."Baki
mutanen wajen suka Bude suna kallon Abun mamaki kasim bai samu Zarafin magana ba
suka Sakamai ankwa Lokaci Daya suka iza keyarsa zuwa cikin mota ko kafin su haruna
su kariso tuni motar yan Sandan ta saki Jiniya ta bar wajen

Su Abba kabiru na cikin masallaci suka samu Labarin Daya kusa girgizasu wai an kama
kasim koda suka fito sai dai masu baida Zence,Cikin Tashin Hankali da dimuwa baban
zainab yashiga kiran waya Heaquater dinsu yan sanda na Jahar kaduna ammh suka ce
basu da wani lbrin mai kama da Haka wasa wasa dai ko"wani Offishin yan Sanda Dake
Jahar kaduna ba kasim ba labarinsa Hankali fa sun Tashi Abba kabiru da Abba garba
zufa kadai sukeyi Hashim kuwa kai ya Dafe yana salati,Ya muktar ne ke kokarin
kwantar musu da hankali ta hanyar ce musu kar su damu za"a samu kasim.

Tuni mutane suka watse da Labrin Abunda ya Faru Duk yadda akaso Boye mganar sai da
takai gidan su Zainab amarya na cikin kawayenta an gama Shiryawa Domin bayan
andaura aure sun shirya Lonching lafiyayyiya,sai kuma sukaji mugun labari suma ne
kadai Zainab batayi ba ammh sai da jiri ya kwasheta tayi kasa tana Gunijin kuka Nan
da nan gidan Biki ya Rikice,Gashi kuma ba wani karin bayani domin ba wanda ya Dawo
balle aji bakin zaren Daga bakinsu.....

*****
Gidan Abba kabiru ya Tumbatsa Da makota da yan"uwa da abukan Arzuka anata Shagali
Sha D"aya nayi yan"uwan umma suka dau gud'an Lokaci yayi ammh bana mutuwa ba na
Auren kasim,wanda dama bayan an Daura aure sunyi Lonching katsina zasu wuto da
amarya anan suka shirya dinner, zata fara zama a nan shahensa in sukayi sati sai su
koma kaduna.

Umma kuwa an ci wanka cikin wani Dakakken leshi mai kyau da yarari sai wani Kai da
kawo ake bakin nan har kunni, basu da labarin Abunda ke Faruwa a kaduna wajen karfe
12:30am na Safe sai ga Aisha sun Dira agidansu Kasim ita da Mamarta da W'anta Auwal
Abunda zai kara Ruda mutane shine ganinta Dauke da Jinjiri sabon Haihuwa.

Aisha tacigaba da Renon Cikinta,har Allah ya Sauketa lafiya Kwana uku kenan da
Haihuwarta ta samu ya mace Shine Yayanta Auwal yace maza ta Shirya su je har
katsina su kaima iyayen kasim aikin Daya aikata mata in ma basu da labari ta"asar
dayake ma ya"yan mutane yau su sani Adireshin Data Taba Dauka Lokacin da zata bar
gidan kasim suka yi amfani dashi sai gasu kuwa har kofar gidansu kasim.

Tun shigarsu Haraban gidan suka Fahimci ana wani Taro,ba wanda yabi ta kansu har
suka Shiga cikin gidan Auwal kuma ya Tsaya Daga Haraban gidan da mama Sahura Suka
ci karo ta kallesu cikin mamaki tana Fadin"Sannnunku da zuwa...Ku shiga
ciki ."Maman Aisha ta gyara zaman mayafin kanta tana Fadin"Yauwa...Baiwar Allah don
Allah ko kece mahaifiyar kasim..?

Mama Sahura ta girgiza kai tana Fadin"A"a bani bace uwar ango tana ciki ammh ni
Matar kanin Babansa ne Daga ina kuke..? Maman Aisha ta riko hannun yar"ta wacce ke
kunshe kanta cikin mayafi tana Rike da Jinjirar Data Haifa cikin Towel tace"Koma
Daga ina muke muna Bukatar ganin Uwar kasim da Ubansa Domin Muna tafe ne Daga waje
mai nisa muna Bukatar Gama Abunda ya kawomu zamu koma inda muka Fito ne.."..

Mama Sahura tayi jim tana kallonsu kafin ta kada kai tana Fadin"Shikenan mu shiga
ciki..Yaudin ma taron bikin kasim din ake duk mazan suna chan kaduna Sun tafi
Daurin Aure basu Dawo ba.."Aisha taji kuka yazo mata tayi Saurin Dannewa Kai tsaye
cikin Falon Umma ta kaisu kafin tace su zauna inda yan"uwan Umma ke cike sai ma
mama Sahuran wani Kallo suke bata damu ba,ta shiga cikin Bedroom din Umma inda take
Zaune iya kawayenta ta gayamata tafito tayi baki cikin Yauki da murna ita uwar ango
ta Fito tana Fadin"Sahura Tace nayi baki ina suke..? Kuma Daga ina..?

Tafada tana kallon su Aisha Dake zaune suna bin kowa da kallo Maman Aisha
tace"Gamu,Ba dole bane ki sanmu ko kuma ki gane daga ina muke Nidai Sunana Hajiya
Amina Daga maiduguri wannan Sunanta Aisha yata ce tare muke da yayanta Auwal yana
waje yana Jiranmu."Cikin mamaki Umma ke fadin"Topha Bayin Allah lafiya..? Maman
Aisha ta mike tana Fadin"Lafiya ba lafiya ba...Abunda D'anku ya Shuka Muka kawo
muku Dukkanmu mu taru mu girbe...Aisha mikomin Jinjiran nan.."Tafada tana mika
Aisha Hannu Da Sauri Aisha ta mike tana kuka tana komai ta mikama Hajiya Aminar
Jinjiran Dake Hannunta tana jin wani daci acikin Ranta na za"a raba ta da Abunda ta
Haifa domin yayanta Auwal yace ko zata mutu sai an kai ma iyayen kasim Abunda ya
aikata.

Cikin karfin Hali Hajiya Amina ta isa Kusa da Umma tana Mikamata Jinjiran Dake
hannunta Lokaci Daya tana Fadin"Wannan Shine sakamakon Abunda D'anku ya aikatama
yata...Ya yaudare ta da kalmar Aure yayi mata ciki Daga baya ya Koreta bayan yace
bazai aureta ba bayan ta dawo gida,muka rumgumi kaddarar data Fadamana Aisha dai
itace yarmu mun karbeta ammh wannan Jinjiran data fito Duniya Shekaran Jiya bamu da
wani Iko akanta shiyasa muka yanke Hukunci kawota inda ya dace.."Tafada tana
sakarma Umma ita wacce ta sandare atsaye cike da mamaki tana Bin Hajiya Amina da
kallo Lokaci Daya kuma tana bin Jinjiran Dake hannuta idanuwanta kyar tana kallonta
ba Shakka wannan Jinin kasim ne domin babu inda ta baroshi.

Gabadaya sai falo ya hargize kowa ya mike yana Salati Mama Sahura ta karisa kusa da
Umma tana lekan Jaririyar cikin Zaro ido Tana Tafawa take Fadin"Innalillahi..Ba
Shakka wannan Jinin kasim ne.."Take Fada Tana Rike haba Umma kuwa tana Tsaye sai
tsiyayan Hawaye take Lokaci Daya tana Zufa kafin kace kwabo ta sulale zata Fadi
Mama Sahura tayi Saurin Tare Jaririyar ita kuma cikin yan"uwanta wata ta tareta Sai
waje ya Dau ihu da hayaniya,Durkushewa Aisha tayi tana kuka itama Jinjiran jin
Hayaniya sai ta Saki kuka mutanen Dake Dayan Falom suka garzayo kowa yazo yaga
Jinjira sai ya koma baya yana Kada kai Inna Rukayyah kuwa sai da Taji Guduwa kuka
take tana Tsinema kasim Umma kuwa Tuni akayi Daki da ita ta sume ana kwaramata
ruwa.

Akaro na Biyu gidan Biki ya sake Rikicewa tarihi zai maimata kansa,Daada da Anty
Rahila sai al"ajabi kawai Zubaida hannu ta saka akai ta Fashe da kuka mama Sahura
ko Cikin Ranta Dariyan mugunta take ma Umma Allah kara Domin tafi kowa sanin yadda
take mata gorin Haihuwa yaya maza tana Fariya da kasim Tun Abunda ya Faru na Farko
ta karyata toh gashi ya Haike kuma am Haifa ta ganin ma idanuwanta sai ta goya
Shegiya abayanta lokacin ta gasgata.

Ganin gida ya Rikice Hajiya Amina ta ja Hannun Aisha zasu Fice Mama Sahura dake
Rike da Jinjirar tana kara kallonta tabisu tana Fadin"Ina kuma zaku..? Ai tafiya
bai ganku ba ku jira kadan yanzu nasan duk inda Mazan gidan suke suna hanya Don
Allah kujirasu in sukazo ku warware musu komai Waka abakin mai ita tafi Dadi.."Da
kamar Hajiya Amina zatayi musu mama Sahura ta lallabesu tajasu chan Shashen Abba
kabiru,ta kebe gefe ta Kira Abba garba awaya

Su kuwa suna chan ana ta Fadi tashen neman inda aka kai kasim ammh har zuwa wajen
karfe 1 bawani labari ma Dadi Kaf offishoshin yan"Sandan Dake kaduna an bincika
babu kasim ba Dalilinsa sun bar komai a Hannun Mahaifin Zainab saboda yace yana
zargin kila yan"uwansa yan siyasa ne suka ma mijin yarsa cinne,su Kuma suka Dauko
Hanya cikin Tashin hankali zasu koma suma su bincika Nan suka bar ya muktar saboda
shi da tawagarsa zasu wuce Barikin sojoji dake nan 1 Division kaduna sai kuma na
jaji akwai Taron da zai Hallata ne Shima kuma yana ta Kiran waya Domin Samun wani
bayani

Suna Hanyar katsina cikin Tashin Hankali Abba kabiru kuwa baya magana sai kukan
Zucci,harda Haruna suka taho,Hashim ne ke Tausan Abba kabiru domin kadan ya Rage
bai Fadi ba suka Tallabosa zuwa cikin mota,Suna Wajen malumfashi sai ga Kiran Mama
Sahura tace suna ina ne..? Yace gasu bisa hanyar Dawowa cikin Tashin hankali tace
toh suyi maza su dawo gidan biki ba lafiya Cikin Tashin Hankali yake Tambayanta
meke Faruwa..?kin sanar dashi tayi sai dai tace kawai akwai mtsla jin haka yasa
Abba garba sakin salati yana Fadin"Gamunan zuwa...Insha Allahu."

Koda ya gayama su Abba kabiru Abunda mama sahura tace ba wanda ya kawo wani Abu sun
dauka lbarin kama kasim ne yaje musu kusan mata da Rudewa shine gidan biki ya Rude
gabadaya.

Kibiya ki karanta cikin salama.

*Anitha....*
8/22/20, 10:24 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?37*

"....Sai da sukayi sallar la"asar a Dutsenma kana suka shigo katsina Yadda suka ga
gidan ya Haigitse ne,yakara sakasu cikin Zullumi kowanne kagani Fuska ba walwala
Auwal Dake Zaune acikin Haraban gidan yayi alwala yayi sallah Tunda Hajiya Amina ta
kirashi ta gayamai yadda komai ya wakana.

Ganin Shigansu Abba garba cikin Gidan cikin alamun Damuwa da Tashin Hankali yana
musu mgana ko lura dashi basu yi ba yasa ya mara musu baya,cikin Falon gidan suka
yada zango inda Mutane ke zaune jumgum,Abba garba ne ya Fara mgana Da
Fadin"Rukayyah meke Faruwa ne...?

Inna Rukayyah ta mike tana Share kwallah tana fadin"Garba kasim ya cucemu...Kuma ya
Cutar da Zuciyarsa...."Hashim yace"Inna Rukayyah ku kwantar da Hankalinku haryanzu
bamu gano wani Station aka kaishi ba balle muji wani laifi ake Tuhumarshi dashi
ba.."Zaro ido kowa yayi Umma dake fitowa Daga Cikin Bedroom dinta wata kanwarta na
Riketa da ita tace"Sun kama shi ne Alhaji...? Mun shiga uku.."Take Fada tana kuka
lokaci Daya tana karisowa cikin Falon.

Abba garba yace"A"a wani zence kuma kuke dabam,Inace labarin kama kasim da akayi
awajen Daure ne labari yazo muku.."Gabadaya Falon ya Dau Salati Umma ta sake
Rushewa da kuka tana Fadin"Innalillahi...na shiga uku ni karima.."Inna Rukayyah ta
karbe da Fadin"Baki shiga uku ba karima goma kika Shiga iyakarki ne Allah ya Nuna
miki bayan Dan Shege dan naki ba"asan wata Ta"asar ya kara aikatawa ba aka
kamashi..Allah wadaran naka ya lalace wlh.."

Ya Hashim yana bin Umma da kallo Cikin mamaki yake fadin"Umma wani Abu ya faru ne
bayan wannan.."?Bata samu zarafin mgana ba Mama Sahura ta Sawo kanta Falon Dauke da
Jinjira Bayanta kuma Aisha ce da Hajiya Amina Wajen Hashim ta Nufa ta mikamai
jinjirar Tana Fadin"Tabbas....Kun tafi ba Dadewa Wadanan bayin Allah suka zo mana
da wani labari...Harda karin Shaidama..."Tafada tana sakar mai yar ahannunsa Da
Sauri ya karbeta yana kallonta ilahirin Jikinsa na rawa Saboda yadda Kamanin
Jinjirar ya zama kamar Kasim ne sanda yana Jajiri Abba garba da Abba kabiru suka
leka suna kallon Abun mamaki Haruna ma yana lekawa ya kafe Jinjirar da ido kafin
yayi baya yana karema Aisha kallo wacce ke bayan Hajiya Amina tana kuka ammh
idanuwanta Tsab akan Haruna.

Jikin Abba kabiru na rawa yace"Bangane me kuke son Fada ba.."?Auwal dake tsaye Tun
Dazu ya kariso tsakiyar Falon yana Fadin"Yakamata ka gane Tunda kaga
Shaida...Sunana Auwal ni yaya nake ga Aisha wacce D'anku kasim ya yaudara ya
Dirkama ciki da Cewa zai aureta Daga karshe yamata Wulakanci ya koreta...Munyi kuka
kamar ranmu zai fita mun sha zagi da Tsangwama Duk akan Abunda Danku ya aikatama
kanwata na Daina Fita jama"a saboda Nuni.Nayi alkawarin Duk Ranar Da Aisha ta haihu
bazan yi kasa agwiwa ba sai na tattarota munzo mun kawo muku Abunda Danku ya aikata
in ma kunsani baku yarda ba Daga yanzu sai ku Fara gasgata hakan..."Yafada cikin
Bacin Rai Gabadaya kowa Jikinsa yayi sanyi sai Sharan kwallah.

Abba kabiru yana neman Faduwa Domin Jiri ne ya Debeshi Abba garba ya rikeshi da
Sauri ya Zaunar dashi kan Kujera,ya Hashim, kuwa Jikinsa ne ya kama Rawa,Duk da
yadade da sanin Mugayen Hallayar kasim ammh baita taba kawo ma kanshi haryanzu bai
daina Halinsa ba,Hawaye suka cika idanuwansa ganin yadda Umma ke kuka ita da
Zubaida Ga Abba kabiru zaune ya sadda kai kasa bakinciki yamai yawa nanata Sunan
kasim kadai yake cike da wani Kunci.

Cikin Dauriya Abba garba yace"Taya zamu yarda daku...? Cewa wannan yarinyar Cikin
kasim ne .? Hajiya Amina tace"Jaririyar Dake hannunku bata isa Shaida ba...? Tafada
kai tsaye Kai ya Gyada yana Fadin"Eh babu shaida mutum...Wanda zai tabbatar mana da
Hakan,kuma kasim bashi anan wajen balle mu Turkeshi ya sanar damu gaskiyan
Lamarin..."Baki Bude Hajiya Amina ke kallon Abba garba kafin tayi mgana Aisha ta
yaye mayafin kanta Fuskarta ta bayyana lokaci Daya kowa ya saka mata ido.....

Cikin Zubar kwallah take Fadin"Akwai shedan mutum...Kuma yana nan anan
wajen.."Tafada kai tsaye tana Kurama Haruna ido da Jikinsa ya Fara rawa,cikin
mamaki kowa ke kallonta Mama Sahura tace"Ki fade shi ko kuma ki nunashi kowa ya
ganshi.."Aisha tace"Ba kowa bane Face Haruna abokin kasim Domin yasan Alaqata da
Kasim kuma ina da Tabbacin Abunda Faru yasan komai Tunda Amininshi ne bai iya
Boyemai komai..."Tafada Tana Sharbe Hawayenta.

Kallo sai yakoma kan Haruna Ya Hashim ya kallesa cikin Rauni yana Fadin"Haruna me
ka sani game da Abunda ya Faru..? Karka boyemana komai Duk da ni Tuni Zuciyata
tagaama yadda da komai Tun bayan Tozali Da nayi da wannan Jinjiran.."Haruna yayi
kasa dakai yana Share Zufa kafin ya Fara Bada labarin Duk Abunda ya sani tsakanina
da Kasim Har zuwa Wulakancin Dayayimin ya kirashi yana Fadamai ya karishe da
Fadin"Kuyi Hakuri ammh zencen gaskiya Abunda iyayen Aisha da ita kanta suka zo
dashi gaskiya ne.."Gabadaya waje sai ya kara Kaurewa da Hayaniya masu Salati nayi
masu kuka nayi.

Cikin Fitan Hayyaci Umma ke Fadin"Mun shiga uku..Yanzu ya zamuyi da wannan


Jaririyar sabuwar Haihuwa bata da laifin komai bayin Allah Don Allah ku Debeta ku
Tsausaya mana ."Auwal yace"Ba wannan Mganar Na Rantse da Allah Aisha bazata koma
mana gida da wannan Yarinyar ba...Taku ce mun Kuma zo mun Damka muku amanarta...In
mahaifinta yazo kuma ku sanar dashi...Hakkin Aisha bazai taba barinshi ba..Mun
barku lafiya,Aisha Mama muje..."Yafada yana Juyawa suma suka Rufamai Baya Aisha
tana kuka jin Nononta yadda yake Zuba Saboda cika Umma na kuka Inna Rukayyah ta
mike zatayi mgana Abba kabiru ya Dakatar da ita da Fadin"Karki ce komai Rukayyah
barsu...Su Tafi Abunda suka aikata Shine Daidai...ko ahaka Allah ya bar kasim
yagama Nuna mai Ishararsa...Ni bai cutar dani ba kansa ya Cuta kuma ya Zalunta
Wanda muka ji kenan bamu san kuma wani Aika aikar ya sake aikatawa ba aka
kamashi...Nidai Allah na gani Ban bama kasim irin Wannan Tarbiyar ba ban kuma san
ina ya Koyota ba.."Yafada yana Dauke Siraran Hawayensa.

Kowa Sai mutuwar Jiki,Jugumjugum ba mgana Umma kuka kawai take bamai Rarrashinta
Daga karshe Abba kabiru ya mike yana layi ya Fice Abba garba ya maramai baya Hashim
kuma ya mikama inna Rukayyar Jaririyar taki karba Tana Fadin"Mikama Uwarka..Ta Fara
Rike sakamakon Hallayarta...Bani zaka bamawa ba.."Bai kalleta ba ya Waiwaya inda
Umma ke zaune tana Kuka bai Kalli barayinta ba ya mikama Mama Sahura tasa hannu ta
karba Tana Fadin"Allah Sarki...Bataji bata gani ba kinzo Duniya cikin Wahala..."Ba
wanda yabi Takanta mazan duk suka Fita zuwa Shashen Abba kabiru kowa ya zauna ya
Dafe kai cike da Tashin Hankali,umma kuwa ita keda kuka Inna Rukayyah kuwa Fada
take tana saka mata mgana Mama Sahura ne ta Dama madara ta bama Jinjirar ta kama ta
goya sai ga yan"uwan nata yabonta wanda abaya sune kan gaba wajen zaginta,Umma dai
ba baki sai kuka Zubaida ma Kukan Take Hatta Zulfa sai da Abun ya Daketa.

Su Daada da Anty Rahila sukayi Tsuru da ido Tsoron Allah ya sake kamasu,haka
gabadaya Iyalan gidan suka kwana suna cikin Damuwa gashi mgana ta Fita domin
makotan dake gidan ajiya sanda su Sadiya suka zo sun Fita da mgana waje domin Tun
wajen sallar Asuba aka Dinga Nuna Abba kabiru ana Zunde gabadaya sai Ya Raina
kansa,Ya zabge lokaci Daya har washegarin kuma ba wani labarin inda Kasim yake Ya
muktar yana Zaria Sukayi mgana da Ya Hashim shi yake sanar dashi Abunda ya kara
Faruwa Shi kanshi ya girgiza da jin labarin,Daga Zaria kaduna ya sake komawa Cikin
ikon Allah ya samu labarin Kasim yana kaduna State C.I.D waya yayi musu Abba kabiru
kan suzo saboda su isa wajen atare lokacin da Labarin yazo musu Abba kabiru cewa
yayi ba inda zashi Dakyar Abba garba ya Tausheshi suka Tafi kaduna da Ya Hashim sai
Haruna wanda bai koma ba haryanzu.

Sun isa kaduna State C.I.D,Sai kuma Abu yaci Tura saboda Sun Riga Ya muktar ya isa
Shi lokacin yana Cikin Barikin Kaduna,kiri kiri aka hanasu ganin kasim kuma Suka ki
bada wani bayani akanshi wai ba"a basu izinin ba,Sai da Ya muktar yazo kana Aka
Fito da Bayanan kasim bayan Dogon Turanci Inda ake Tuhumarsa da Shiga cikin gidan
Matar Aure da Niyyar kokarin keta mata Haddi,wanda ya Shigar da karar yana Bukatar
ya makashi a kotu ne,Kuma sunki su bayyana suna sai da Ya Muktar yayi waya da
Commissioner yan Sanda na Ajahar kaduna nan da nan sai gashi yazo zuwansa ya saka
Dole sunan wanda ya saka aka kama Kasim ya Fito....

Bakowa bane face Mr Bello Muhammed Jikamshi ta Hannun Uncle Aminu Domin Shi yazo ya
Shigar da karar,anan kaduna State C.I.D Bayan sun Ji ta bakin Bellon Ta wayar
hannu,Mamaki ya cika Fuskar kowa barin ma Ya Muktar cikin Sanyi jiki yake
Fadin"Haba dai...Bello fa baya kasar nan wajen wata Uku da suka gabata Taya zai
saka a kama Dan"uwansa.."

Yafada cikin Mamaki Abba garba kuwa da Abba kabiru tsoro ya cika musu mara,Bello fa
yafara musu Dauke Daya Daya Saura su kenan Wayasani ma ko ya Shigar da nasu karan
ganin ba mafita yasa Ya muktar ya Danna ma Bello kira Lokacin ma muna Shagon
Siyayyar kayan Babbys ya barni ya Fita yana Daga Kiran Ya Muktar yashiga
Fadin"Bello wani irin Abu ne ka aikata..?

Cikin Mirmishi yace"Finally ya Muktar ina Fatan an zayyano muku korafina da kuma
Akan me nake karas sa.."Cikin bacin Rai Ya muktar yace"Ba wannan na Tambayeka ba
Why..? Kar ka manta ko"ina akaje kasim Dan"uwanka ne,ko me ya maka bai dace kasa a
tozartashi irin Haka ba.."Cikin Fada Bello yace"Wlh bai isa ba Yaya koda ciki Daya
muka Fito da Kasim bai isa ya Shigo har cikin gidana ba Yaso ya ketama matata Haddi
na kyaleshi ba...Sai na kaishi Kotu ta yankemai Hukuncin Daya Dace dashi.."Daga
haka kawai ya yanke Kiran zufa ta dinga Ketoma Su Abba kabiru domin Suna iya Jin
Maganganun Bello Cikin Bacin rai .

Ya muktar ya Dafe kai yana Fadin"Innalillahi...Bello he is very Storeborn


wlh...bashi da ikon kai Kasim Kotu Tunda bashi da Shaidan Hakan.."Haruna dake Tsaye
yace"Nine shaida...Sir."Gabadaya kallo ya koma kanshi cikin mamaki ya Muktar ke
Fadin"Kaima kasan ya Je har gidan Bello yayi kokarin ketama Aneesa Haddi.."Haruna
ya Sharbe Hawaye yana Fadin"Na sani Bayan yaje har gidanshi Dake kano Lokacin yana
cikin Rashin lafiya,wanda kasim din baida labarin warkewar Bello wanda Nima sai
yanzu na sani,Tabbas yayi kokarin ketama Aneesa Haddi sai kuma Allah bai bashi sa"a
ba,Shi da bakinshi yake sanar dani komai har namai Fadan Abunda yayi bai kamata
ba."Yafada kawai sai ga Hawaye Lokaci Daya kowa yayi kuri kawai yana binsa da kallo
Yan sanda kuwa nata Daukan Bayanai cikin Sharan kwallah Haruna yafara Fadin"zan
fadi wata gaskiyan ma bayan wannan.."

Gabadaya aka sakamai ido ana kallonsa cikin Rawan Murya Abba Kabiru ke Fadin"Ya isa
Haka Haruna...Na tabbata in ka kara Fadin wata mgana zuciyata zata fashe saboda
bakinciki.."Haruna ya girgiza kai yana Fadin"zan fada...na gwammace na Fada
Tunkafim Lokaci ya kuremin na Tabbata Abunda muka aikata ne nida kasim yafara
bibiyarsa,Mganar gaskiya mune Silan Ciwon Bello.."Gabadaya kowa sai ya koma yana
Sauke ajiyar Zuciya Cikin mamaki ya Muktar ke Fadin"Kamarya fa bangane ba..?

Haruna ya sadda kai yana Fadin"Ni na bama kasim Shawaran zuwa wajen wani boka
agarin Niger na rakasa mukaje akayima Bello Asirin da zai Rayu kamar
matattace,Kuma an tabbatarmana Haka zai kare rayuwarsa bai tashi ba,Sai gashi kuma
Tun ba adau Lokaci ba yafara warkewa wanda kasim yayi Hakane Domin Aneesa ta Daawo
Hannunsa kuma Burinsa bai cika ba.."Yafada yana Kara Rushewa da kuka gabadaya sai
wajen ya Dau Salati Ya muktar kanshi ya kama yana Kiran Sunan Allah.

Sai da ya Daidaita kanshi kafin yayi mgana..."Abu baiyi Dadi ba..."Abba kabiru na
Hawaye yace"Barewa bazata yi gudu Danta yayi Rarrrafe ba Muktar ka manta muma irin
Zaluncin da mukayi muku Nida Garba..Ya zama Dole mu ma mu karbi Hukunci..."Da Sauri
Ya muktar ya Dakatar Dashi da Fadin"A"a Abba wannan kuma wata mgana ce
Dabam...Commissioner plz mu na bukatar Belin Kasim.."

Commissioner yace"Zasu bada Belinsa ammh har sai Dan"uwanka yazo sun cike Takardun
Bayan kuma Hukuma Ta Shiga Tsakani Duk da Abun na cikin gida ne.."Kai ya muktar ya
Gyada kafin yace"insha Allahu nan da kwana biyu zamu zo tare.."Daga haka suka Rabu
da Commossiner yabi tawagarsa ya koma Suma Daganan suka Dumgumo zuwa katsina
Dukkansu wanda ba yarda basuyi ba kan Su ga kasim ba ammh aka Hanasu bawai domin
matsayin Muktar bai kai ba sai domin Bello yasan cewa Muktar zai iya zuwa ya nuna
karfin iko akan hakan shine ya Shirya komai cikin Hikima.

Ya muktar yajinjina ma lamarin Sosai ta wani Fannin kuma baya ganin Laifin Bello
Domin An Zalunceshi.Allah nagani baitaba Rike kowa acikin Zuciyarsa ba...Kosu Abba
garba Tuni yaji ya yafe musu har cikin Zuciyarshi Suna komawa gida Abba kabiru shi
yatara su Umma yana Fada musu Abunda su kasim suka aikata Haruna dama tun Akaduna
suka Rabu yana Neman gafaran Ya muktar Shuru kadai ya mai Domin Abun ya gama
Kashemai jiki,Duk wanda yaji labarin Abunda kasim ya aikata sai yayi Tir dashi
Daada Da Anty Rahila Ranar suka bi Ya muktar suka koma Abuja sai da suka isa gida
yake basu lbarin da Haruna ya basu na Asirin da suka ma Bello.

Daada ta rike Haba tana Fadin"Haba...Koda naji...Dama na san Ciwon Bello yana da
Nasabarsa Mutum fa ya kwanta Lafiya lau,yatashi cikin lalura...Allah mun gode maka
Dama ba Tunyau ba Bello baya Kaunar Ahalin nan naku Zuciyarsu kwata kwata bashi da
kyau.."Ya muktar dai ba magana Domin wannan karon baida tacewa.

Washegari Ya muktar ya kira Bello awaya yace rokeshi kan Don Allah mu dawo Dama
Aranar Daddare Jirgin mu zai Tashi Zuwa Nigeria dama Siyyayyar Kayan Haihuwa muka
Tsaya yi,Ranar da Daddare Jirginmu ya Tashi Daga Epypt zuwa Gida Nageria ta Filin
Jirgin Murtala Muhammed Lagos muka Sauka da Safe muka bi wani Jirgi Zuwa Abuja
Mallam Inuwa yazo ya Daukemu Da muka Sauka afilin Jirgin Nmandi azikiwe
Internatinal Airport.

Kowa yayi mamakin ganin yadda Dagani Har Bello muka chanza Ni kuwa ga Kibar ciki ga
kyau Dana kara Anty Rahila sai kallona Take cike da Sha"awa Ya muktar ne suka Shiga
Shashen Bello Suka Dade suna mgana kafin su fito,Dakyar yayi Convicing dinshi kan
zuwa kaduna gobe,Da Sassafe kuwa suka Tafi kaduna Uncle Aminu ma ya Dawo Shima Ya
muktar ya sanar dashi su hadu a kaduna din Hakama Bangaren su Abba garba wadanda ke
cike da Nadamar Abunda suka aikata Tunda gashi yana Bibiyarsu.

Karfe 12 na safe su Ya muktar suka shiga kaduna State C.I.D Koda suka iso sun iske
su Abba garba,Abba kabiru kuwa karfin Hali kawai yake yi Domin Tun ranar da Suka
bar kaduna bai da lafiya Dauriya kadai yake sun iso ba Dadewa Aminu ya iso nan da
nan ko aka Fito da kasim wanda yagama Ramewa ya lalace Duk da ba Duka ba Zagi ammh
zaman Cell ba Wasa ba, Duk Fuskarsa ta kode da Kuka Da cizon Sauro yana Shigowa
Office din da Bello yafara cin karo Tsaye kan kafafunsa yana Sanye da Ameriacan
Suit Baki da Ruwan Toka ya matse Wuyansa da Tie baki Fuskarsa Toshe da wani bakin
glass na Rashin mutum su kansu su Abba kabiru basu iya kallonsa ba saboda Shakka
Dukka da Sun Shirya karban Hukunci Tun agidan Duniya

Cikin mamaki kasim ya Shiga Nuna Bello yana Fadin"ka...ka...warke ne....? Yafada
yana zaro ido.
Cikin Mirmishin sai ka Raina kan ka Bello ya kariso gaban kasim yana Fadin"Eh na
warke Tun Wata Hudu da suka Wuce baka so haka ba ko..?kaso Abunda makaryacin
bokanka ya Fada akaina ya tabbata ko..? Toh kayi kuskure kasim Tun ina yarona Ni
Bello muhammed Jikamshi bansan Faduwa ba Nasara na sani..koda Kasheni ka sa akayi
Har Abada Aneesa bazata zama mallakinka ba.."Yafada yana Dukan Kafadarsa.

Cikin Mutuwar Jiki kasim ya Sulale kasa,zai yi mgana Hashim ya saka hannu ya
Tsinkeshi da mari yana Fadin"Bama son jin bakinka anan wajen...Ka zama Dabba acikin
Mutane,Bayan ka karbi Sakamakon anan zaka koma gida ka karbi Cikin Shigen da kama
Budurwanka.."Yafada Daidai Lokacin da Zainab da Mahaifinta Alhaji isa suka Shigo
Cikin Offishin kuma a kunnansu Mganar da Hashim ya Fada sun manta sam sun suka kira
Alhaji isan Suka sanar dashi an samu kasim din a State C.I.D Basu taba zaton zasu
iya zuwa ba.

Gabadaya sai kallo ya koma sama cikin Firgici zainab ta Dafe kirji Tana Fadin"Ciki
kuma...? Tafada tana kallon Kasim daya kwalalo ido Cikin Karfi Hali Hashim
yace"Kwarai kam...Kuyi hakuri mun Rufeku ammh azahirin batu Kasim bai chanchanci
Auran yarku ba.."Yafada yana kallon Kasim din baya Zainab taja tana Kallon kasim
Hawayen idanuwanta na Zuba

Cikin Kunar Rai Hashim ya cigaba da Fadin"Aisha Tsohuwar Budurwanka Daka yaudara
kama ciki Ta haife maka Cikin kuma ta kawo Abunda ta Haifa yanzu haka tana katsina
an ijiye maka Abunda ka Shuka,in kazo ka girbeta kai kadai..."Ido kasim ya waro
kafin yace"Aisha...."Idanuwan Hashim sun kada yace"Eh Aisha maiduguri...Kuma Haruna
ya Tabbatar da gaskiyan labarin..."

Kai kasim ya sadda yana Jin Nadama da danasani sun gama Lullubeshi wannan Shi ake
Kira yau ma Tubulal sara"i...Ranar Tonin Asirinsa gaban iyayensa Gaban matarsa,da
Danginta,Kaico kaico na kasim yake Fada acikin Ranshi kafin ya Daga kansa Yana
hawaye ya fara Fadin.."N.....

Kibiya ki karanta cikin salama.

*Anitha...*
8/22/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?38*

...."Na tuba nabi Allah...Don Allah Abba,ya Hashim kuman Aikin Gafara..."Yafada
Hawaye suna kara zarya asaman Fuskarsa.

Ya Hashim ya kallesa cikin Raunin Murya yana Fadin"Kasim ba mu zaka nema gafara
ba...Kanka ka cuta da Rayuwarka Bello zaka nema gafara domin shi kafi Cuta...Bayan
ka mai Asirin zama cikin lalaura na tsawon wani Lokaci bai isheka ba sai da kabi
matarshi har gida Da Niyyar keta mata Haddi...Yanzu ya kai karar ka Kotu sai kace
bai maka adalci bako..?.."Yafada cikin Kunar Zuciya.
Kasim ya Dago kansa yana kallon Bello yana Fadin"Nasan Ni mai laifi ne
awajenka..Kuma ban Chanchanci yafiyar ka ba....Karka ga laifina Sharrin Shedan ne
Dana Zuciya da kuma Zugan mugun Aboki Don Allah ku yafemin Nayi Nadamar Duk Abunda
na aikata na Shagalan Duniya banta Tsammanin akwai Ranar Da Asirina zai Tonu Lokaci
Daya ba.."Yafada yana Gunjin kuka gwanin ban tsausayi.

Abba garba yace"Kana fadin Shedan...? Waye Shedan din in ba kai ba...Tsakani ga
Allah ka Cutar da Rayuwarmu kuma ka Cutar da kanka domin ko D'aya bamu da Masaniya
da Abunda Muguwar Zuciyarka ke kitsa maka."Kasim na Hawaye yana Fadin"Nasani
Abba...Kumin aikin Gafara don Allah..".

Abba kabiru Dake kuka Hawaye na Zubar mai ya saka hannu ya Sharbe yana Fadin"Hakika
Dama Haka Rayuwa ta gada..Duk yadda ka kai ga muguwar Zuciya,sai ka samu wanda ya
shanyeka...Ni na kasance abaya bani da Zuciya mai kyau sam,wani Lokacin ni nake
Dora Garba kan wata Cutarwa..Bayan mun tuba mun gane gaskiya bantaba tsamanin
Watarana Abunda na aikata zai bibiyeni ba..Sai gashi ya bini Ta hanyar bani D'a
irinka Kasim..Bazan maka baki ba sai da zan Roki Allah ya Sa wannan Abun ya zama
Hanyar Shiriyanka,Kuma bana bukatar amaka afuwa a kaika kotu ta yankema Hukunci
Daidai da Abunda ka aikata.."Yafada yana Kuka Sosai Abba garba na Dafa Kafadarshi
Cikin Alamun lallashi.

Alhaji Isa Mahaifin Zainab dayayi Tsuru yana kallon Ikon Allah Cikin Ransa kuma
yana kara godema Allah da Lokaci bai kuremai ba Jami"an tsaro kuwa sai Daukan
Bayanai suke suna jiran Umarni Zainab ce Dake kuka ta karisa gaban Kasim ji kake
Kau...kau..! Ta Daukeshi da Maruka Har biyu cikin kunar Rai Take Fadin"Dama Halinka
kenan..? Dan Akuya ne kai Ko nace Bunsuru ne mai Haikema ya"yan Jama"a kuma kake
Tunanin ka zama mijin Zainab..? Kayi kuskure kasim Har Abada ni Zainab Alhaji isa
bazan taba Zama da Fasiki mazinaci irinka ba...Ka Bani Takardan sakina yanzu ko
kuma ka Fada da bakin ka sakeni in ba Haka ba Wlh sai na Shigar dakai kara akotu
mutumin Banza da Wofi.."Tafada tana Jifansa da wani Wulakantattacen kallo Lokaci
Daya tana Zubar kwallah.

Dafe kuncinsa Kasim yayi yana Bin Zainab da kallo Alhaji isa Dake Tsaye yace"Kimin
Daidai Diyar albarka...Koni ban goyi bayan ki cigaba da zama da Bara gurbi irinsa
ba...Ka sakarmin yata ko ni nayi karanka akotu.."Yafada yana Kallon Hashim wanda ke
kallonsa cikin Takaichin Abunda kasim din ya jazamusu..

Kafar Zainab Kasim ya kamo yana Fadin"Haba zainab taya zaki ce Haka.? In kika bar
ni a halin Danake ciki Wazan kama...? Ki Rufamin Asiri Don Allah Whl nayi miki
alkawarin Daga Rana mai Kama ta yau na Daina Shaye Shaye da Neman mata...Aneesa
kuma bazan kara Shiga Sha"aninta da Mijinta ba Har Abada..."Yafada yahada
Hannuwansa alaman Roko Da Sauri Zainab ta kwace kafarta tana Fadin"Au ashe ma kai
Mugayen Halayyan naka basu da iyaka bayan Duk wadanan Harda Shaye Shaye ma
kakeyi...Tab...? Wlh baka isa ba sai ka sakeni.! Ka sakeni yanzu ina Jiranka na
gwamnace a sakani Layin Zawaran Layinmu da asakani Cikin Layin Da Auren Zainab
gwara zaman gida ba..."Tafada tana Jifansa da wani Wukatattacen Kalo..

Kasim ya juya yana kallon Ya Hashim yana Fadin"yaya don Allah ka saka baki...In
zainab ta rabu dani wazai sake bani yarshi..? Abba kabiru yayi Saurin Taran Hashim
yana Fadin"Babu...Domin ka Riga gama yima Rayuwarka wani bakin Fenti wanda har
Abada bazai Taba goguwa Daga Jikinka ba,Tana da gaskiya nima na goyi Bayanta..Maza
ka saketa yanzu Tun kafin Dan gutun Kimarka Dake cikin Idanuwana su sake
Zubewa.."Yafada cikin bacin Rai Kasim na Kuka yana kallon Ya muktar wanda ya so
saka baki Bello ya Dafa Kafadarshi yana Dagowa ya girgizamai kai alaman Ba Ruwanka
Dole ya Tsuke bakinshi.

Bello kuwa Hannuwansa ya Harde Bisa Kirjinsa yana Watching din komai cikin Nishadi
Domin Harga Allah Zuciyarsa bata samu wajen da Zata Tsausaya musu ba...Uncle Aminu
ma yana gefe akasan Ransa kuma yana jin Tsausayin su Abba kabiru da Kasim.

Kasim ya Sadda kai yana Kuka kasa kasa yace"Na sake ki zainab Saki Daya..."Cikin
Farinciki Tace"Madallah nagode...Ko kaga kayi D'aya karka saka acikin Ranka zan iya
Dawowa gareka...Nagodema Allah da baka Doramin idda ba.."Tafada Lokaci Daya Tana
Share Hawayen Idanuwanta Ta Fice daga wajen da Gudu Alhaji isa ya mara mata
baya,cikin Tsausayin Halin Da ya jefa yarshi Shima Rashin Bincike ne yajamai haka
saboda samun Tushe mai Asali,Suna hanya ya Kira gida yace maza atura mota ta kwaso
kayan Zainab Daga gidan kasim,Bai tsaya Neman Yayi karin Bayani ba ya Datse kiran.

Gabadaya Kukan kasim ya cika wajen ya muktar ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Duk
abar wannan mganar...Bello ka saka hannu abada Bellin kasim..Koma miye in muka
karisa gida sai mu Cigaba Da Tattaunawar.."Bello bai yi gaddama ba aka bashi
Takarda ya saka Hannu Shima kasim ya saka Bayan kuma an yi Takardan iyaka wanda in
aka kara kamashi da irin Wannan laifin ba Shakka sai yaje gidan yari......

Tun kafin agama cike Takardun Abba Kabiru ya koma mota saboda Jirin Dake
kwasarshi,Basu Dauki Lokaci ba Aka bada Belinsa,Bello dai Tawagar ya Muktar yabi
suka koma Abuja Uncle Aminu kuma Daganan ya koma kano,Su kuma su Abba kabiru suka
iza keyar Kasim zuwa katsina,Tun da suka shiga gidan yake ta Rufe Fuska Saboda
Kunya Umma kuwa Haka ta zauna gabanshi tana kuka mai Cin Rai tana Fadin"kasim
meyasa ka kunyatani a idon Duniya...? Kacutar da Zuciyata kuma kabama yardata
akanka Kunya.."Take Fada Tana kuka Su mama Sahura suna nan basu koma ba Hakama Wasu
Daga cikin Dangin Umma,inna Rukayyah ma tana nan ita ta karbi Jaririyan Dake Hannun
mama Sahura wacce Duk ta Koma wata karama Saboda Rashin Nonon uwa ta Ijiyema kasim
bisa Jikinsa

Kura mata ido yayi yana kallonta yana Hawayen Tsausauyin Kanshi Da kuma Nadama
mganganun Aisha na Karshe suna mai amsa kuwa acikin Kunnuwansa,Runtse ido yayi yana
Fitar da kuka mai Sauti bama wanda ke Tsausayinshi Domin Komai ya Faru Shine
Sila,Kasim yadda yaga Rana Haka yaga Dare kwana yayi kukan Zucci dana Sarari,Allah
ma ya taimaka Mama Sahura na Kula da Jinjiran da ko suna ba"a saka mata ba,Da
Farkoma Inna Rukayyah Cewa Tayi abashi ita ya kwana da Ita bamai wahalan Iskancin
daya aikata Daga baya yazo ya bar Mutane da aiki.

Washegari Wajen sallar Asuba Abba kabiru ya yanke jiki ya Fadi Aka kwasheshi Ranga
Ranga zuwa Asibitin Federal medical Center Katsina Suna zuwa bayan gwaje gwaje suka
samu Jinin Abba kabiru ne yayi mugun Hawa Hawan Jini ya Fadeshi,ya fadi Dalilin
Haka ya samu Shanyewar Barin Jikinsa Guda Daya,iyalai sai kuka Kowa kasim yake gani
aSilar Faduwar Abba kabiru, Abba garba kuwa Tuni Duniya ta Fitarmai Bisa kansa
ganin Daki Daki Abunda ke Faruwa da Rayuwar Abba Kabiru kafin Ta Juyo kansa Domin
yana da Tabbacin Shima Allah bazai barsa ba...Hakkin Rai da kuma Cin Dukiyr marayu
bazai taba barin Ahalinsu su Zauna lafiya ba sai Abunda suka aikata ya Bibiya
Ahalin nasu.

*******
Labarin da su ya Muktar suka zo mana Dashi bamai Dadi bane Naji na kara Tsanar
Kasim Jin Shine Silan Laluran Mijina Kuma Gwarzona,Wanda naga Tunda suka Dawo ya
Kule kanshi Cikin Shashenshi Ranshi bace Mutuwar iyayensu Ta dawomai Sabuwa har
sai da ya Fitar da kwallar,ammh sai wata Zuciya ta Tausheshi da Fadin Ka karka damu
Bello ka Zurama Sarautar Allah ido kabarsu da Hukuncin Allah kamar yadda ka Fada
Tun afarko kadan suka Fara gani.

Da Labarin ciwon Abba kabiru ya samemu ba wanda ya Tsausaya musu sai Ya muktar Daya
kwashi Jiki yaje Dubashi kuma ya Zubemusu kudi masu yawa na Hidimar Asibiiti
Shikanshi Hashim din bawai Kudin Yake dashi ba,Gabadaya Albashinshi Dashi yake
Hidimar gidanshi Data iyayenshi,kasim kuwa bai san komai ba sai Shanshanci da Neman
matan Banza babu Abunda yake Tsinanama iyayen,Abba garban ma Ta wajen Hashim ne
yake samun Wani Abu domin kaf Dukiyar da suka hamdama ta Riga Ta kare ci tayi tayi
kamar gara kafin su ankara ta kare,Taimakonsu Allah Aikin da Muktar ya samoma Kasim
da Hashim Shine Rufin Asirinsu,Hatta karatun Zulfa da Zubaida duk Hashim din ne ke
Daukan Nauyin komai Bawan Allah Duk ya Rame Lokaci Yana ta karban Laifin iyayensa
ba laifi yana ji acikin Jikinsa.

Kasim kuwa sai ka Tsausayamai in ka ganshi Saboda yadda ya koma,kwana Hudu da


Faruwar Abun Sakon Takardan Korar Shi Daga wajen aiki Wanda Haruna ya kawo mai har
gida,Tare aka sallamesu saboda an diba Sabbin ma"aikata sai aka Rage Malalata
wadanda basu da wani amfani,Zama sukayi suna ta kuka Lokaci Daya Da nadamar
Rayuwarsu...

Jaririya kuwa An sakamata Suna Fauziya,ba wanda yabi takan Yimata Shakika,Mama
Sahura da iyalanta Tuni sun koma gida sai dai tana zuwa Asibiti Kullum Tana Taya
Umma zama wacce ta zama mara mgana sai dai Sharan kwallah,ita kanta Mama Sahura
jikinta yayi sanyi ganin yadda Komai yake Faruwa Daki Daki Tana cikin Fargaban Su
menene nasu sakamakon,Tunda shi kam Abba kaburu yafara kirban nashi Tun agidan
Duniya,Shi kanshi Hashim shida iyalansa sun koma shi kuma ya koma bakin
aikinsa,Zubaida ma ya Tafi da ita saboda karatunta ita kanta Duk Tayi sanyi Inna
Rukayyah ma ta koma ita dasu Hamdiya,Abba garba ke kwana Dashi Su Umma na Wuni
Dashi Kasim kuwa na gida yana Fama da Rayuwa Shi ke Rainan Fauziya wacce ake bata
madara ya tasata yana kallo yana kukan Tsausayin Rayuwarsa

*****
Sati Daya mukayi a Abuja muka koma Kano Saboda Bello zai koma bakin aikinsa,tare da
Hibba na Taho Tunda sun samu Hutun Makaranta,mun samu gidan duk yayi kura Dani
Dashi muka zage muka Tsabtace ko"ina ya fita yayo mana sabon Cefane Tunda ya wanci
Wadanda muka bari sun lalace sai muka Fitar muka Zubar,Salihu megadi sai Murnan
Dawowarmu yake,yana ta Tambayan Modibbo muna munyi kewarsa sai dai muna mgana
Lokaci bayan Lokaci Dashi ta waya,yana chan yana cigaba da karban Hora a makaratan
Military Sch Jos.

Kwana 2 da Dawowarmu Bello ya Fara Attending Lectures dinsa,Murna wajen Sauran


Daliban da malaman ba"a gama Student din Daya Fara Dauka Har suna Ug 2 Abun ba Wuya
sai ya koma yana Daukan Tunda ga Ug1 zuwa 4,Tamkar baya komai nashi bai chnza ba
Tuni Sunanshi ya Dawo yan mata suka Fara Rubibinsa kamar Baya da Tsoffin Wadanda
Suka sansa Tun baya da Sabbin Shigowa,Tun bana ganewa har nafara ganewa Tunda wani
Lokacin sai muna tare naga ana kiranshi ko Turamai sako baya maida kai,Nima ban
wani Damu ba sanin Halin Mijina na taka tsantsan da Aji bazai iya Kula wata mace
ba.

B.kaita ita tazo har gida ta ankarar Dani Domin kaf Buk ta Dauka da Zencen kyawun
mijina da ajinsa Yanmata basa Jin kunyar Fadar Suna son Mr Bello ko kuma yana
Burgesu Daga masu Fadin ya iya Wanka sai masu Fadin Dreesing dinsa ke Daukan
Hankalinsu suna Fatan koda gaisawa suka Rinkayi dashi masu Burin Auraansa kuwa suna
da yawa Harda masu Shan Alwashin koda boka da mallam ne,Sai sun Aure shi Akwai
wadanda ke Fadin in yana Turanci kamar su saceshi sukeji.

Ranar da B.kaita tabani labarin nan Kamar zan mutu Saboda Kishi,domin akan Abunda
ya Shafi Mijina Bani da Wasa Dama ga cikin jikina Wanda ya Shiga Wata na Shidda na
lura ba karamin Sakani Fada yake ba Abu kadan za"amin yanzu zan Hau sama nayi ta
fada wani Lokacin baya Biyemin sai dai ya kyaleni yamin Banza na gaji na bari wani
Lokacin kuma ya toshe bakina da nashi ya shiga yimin Salonsa wanda bana iya Juya
baya Saboda matuka gwarzona yasan Hanyoyin da zai sakani natsuwa Lokaci Daya Duk
Fitinata na nemeta na Rasa sai ma kara kwakwumarsa Danake kamar wata mage.

Koda ya Dawo Bayan Sallar Isha"i bai Dade ba yace mu Shirya muje Waje muci Abinci
Duk da ina jin Fitinata ban musamai ba na Shirya muka Fita Zuwa wani Restaurant Cin
Abinci Ni dashi da Hibba wanda Dukkanmu muka Sha Kwalliya sosai,Tunda yaga Take
take na sai bai Tankani ba Har muka isa wajen yamana Odar abunda muke so,An kawo
mana ko Faraci bamu yi ba,wata budurwan mace Daga bayanmu tataso cikin Fara"a tana
Fadin"Wow...So masha Allah Happy Family Mr Bello..."Tafada tana Shafama Hibba
kumatu....

Dagowa nayi ina Kallonta cikin Takaichi na Hade Rai ina Hararanta Shi kuma sai ya
basar dan yake yamata kafin yace"Thanks..."Daga Haka ya maida kanshi yafara cin
Abinci Kamar baisan da Zamanta ba,Kallonsa ta karayi tana Fadin"Am Nadra Famtami Ur
Student Mathematics Depertement...Level 1..."Bai Dago kai ba ya Gyada mata kai ammh
kamar mayya tanace har tana kallona tana Fadin"Hy....Madam.."Ko kallonta banyi ba
sai ma naji kamar zan saki kuka ganin yadda take kure Mijina da manyan Idanuwanta
ko Taba abincin banyi ba Na mike na Fizgi Hannun Hibba muka Fice Daga Wurin bai
Dago ba sai ma Mirmishin Daya saki Lokaci Daya.....

Cikin Mota muka koma Sai Da yadau Lokaci kafin ya Fito niko kafin ya Fito na cika
nayi Fam Abun Haushi Tare suka Fito da wannan mayar yarinyar kuma suka Jero har
wajen Motarmu Bakinciki kamar nayi Bindiga,Ina kallonsu ta cikin Mota har yana mata
mirmishi Shiyasa koda ya Shigo Bangaren Direba na Kara Tamke Fuska Harda kau da kai
Kallo Daya yayimin ya Dauke kai Cikin Ranshi kuma yana Mai Jin Dadin yadda nake
nuna Kishi akanshi.

Har muka karisa gida ba wanda ya Tanka Dan"uwansa,Ban Jira ya Fito ya Budemin ba
kamar kullum na Balle murfin Mota na Fice Hibba ma Datayi barci Shiya
Daukota,yakaita har zuwa cikin Dayan Bedroom Din Datake kwana Koda ya Shigo namu
Bedroom din na Fito Daga wanka ina Daure da Towel gaban Dressing Mirrior ina Tura
baki Kallona yayi baiyi Mgana ba ya Sabule Rigar Jikinsa na Kamfanin DKNY,da wandon
Ina kallonsa ban Tankashi ba ya Fada Tiolet Tsaki naja ganin yadda yayi Biris Dani
Sama sama na Shafa mai na Saka wata Rigar barci Doguwa mai Taushi yana cikin Tiolet
din na Bude na Shiga Yana tsaye Cikin Shower yaga Shigowata Cikina Daya bayanna
yake kallo sai karamin Bakina Daya kusa Tabo Hancina saboda yadda nake Tura
bakin,ko Barayinsa ban kallah na Sagala Towel na Shanya cikin Hangers dinsa na Fice
da Kallo yabini yana Fadin yanzu zan yi maganinki nasan Abunda kikeso.

Kichen na Shiga na Hada Tea nasha Domin Yunwa nakeji,wajen Hibba na Leka na
Ciremata kayan Jikinta na saka mata na barci na mata addu"a na Sake Lullube ta da
Blanket,ban damu ba Saboda Dazu kafin mu Fita Tasha Tea so nasan Batajin Yunwa
bedroom dinmu na Koma na iske ya Fito yana goge Jikinsa da karamin Towel din Dake
hannunsa,gadon na Haye ina Kara Dunkulewa cikin Bargo lokaci daya ina Juya Baya

Yana saka Wandon kayansa na Pjms,yace mata"Haka zaki kwana da yunwa..."? Tana jinsa
ta masa Banza,Mirmishi ya saki kafin yace"Ok...Bari nazo nayi Lallashin My
Anee..."Yafada yana yar Dariya bai saka Rigar ba ya Hauro gadon ina Jinsa ya Shigo
Cikin Bargon ya Rikoni nayi Saurin Zamewa ya kara Rikoni Sai na Fara Kokarin
kwacewa,Da Sauri ya Saka Duka Hannuwansa ya Rikoni yana Fadin"Wai ni Duk miye Haka
ne...? Kinfa san bana son Fushin Ba Dalili.."Yafada yana kara Tsananta Rikon Daya
yimin ganin na kasa kwace kaina yasa nayi lamo ajikinsa,Lokaci Daya na sakamai kuka
kaina ya Shiga Shafawa yana Fadin"Shi..iii...Gayamin Laifina Matata ni kuma zan
nemi afuwarki.."Cikin Jan kukan Shagwaba nace"To..ba...ba kai bane kowa sai cewa
yake yana sonka ance achan Jami"a kamar mata su cinyeka kuma naga Shaida Dazu da
muka Fita cin Abinci.."Nafada ina Kara Sakin kukan Shagwaba Da Tabara.

Kara Rumgumeni yayi Lokaci Daya yana Kasa Da Hannunsa Zuwa Cikina yana Fadin"Karma
ki Fara saka wannan acikin Ranki my Anee...Mijinki Is a Teacher kuma Dole zai yi
Harka da Cakude cikin Mata da Maza Buh karki Taba Zaton Ni Bello Wata macen zata
Taba burgeni Bayan ke...Bansan sunayi ba Kema kin sani Tun muna Zamfara...Kina da
Shaida akaina Mata basa gabana Tunkafin nayi Aure balle yanzu Da kika zama uwar
D"anq ko y'ata Dake cikin ki...Ki Rubuta ki ijiye Bello Muhammed Jikamshi is For
Aneesa Bukar Bulama...Only U...Only U Aneeesaa....."yafada Cikin Wani Salo,Da Sauri
na Kara kamkameshi Cikin Farinciki Shi kuma yana ta Shinshinar Wuyana Cikin Fitan
Hayyaci na Dago kaina na Hade bakinmu Waje Daya Cikin Shauki da muradi mai girma
Shikenan Fushi ya Tafi sai kuma muka Hau Siradin Neman Ladan Allah.

Kibiya ki karanta cikin Salama.

*Anitha...*
8/22/20, 10:26 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�?39*

..."kalaman da Mijina ya Fadamin su suka saka na watsar da Duk Wani Tunani acikin
Raina na Rumgumi Mijina muna cigaba da gudanar da Rayuwarmu cikin Farinciki da
Muradin Juna..

Na toshe kunnuwa na kamar yadda yace ko B.kaita tazo zata fara gayamin zan Dakatar
da ita da cewa nafi kowa sanin Waye Mijina bazai taba yin Abunda zai yi Failing
dina,ba mganar wasu yan matan Jami"a nasan basa gabansa da wannan na samar ma kaina
lafiya bana jin Labarin komai sai na samu lafiya,wani lokacin yana Dawowa gida zai
Kashe Duka wayoyinsa saboda Bani Dukkan Lokacinsa kuma Hakan na matukar min Dadi.

Sai lokacin na Fara zuwa awo anan Wani Private Hospital mai Suna International
Hospital Dake Cikin Birnin kano,shi yake kaini Duk bayan sati hudu nayi Awo kuma ya
Jirani ya Dawo dani Wahala da kuma Dawainiyar mijina akaina Shiyake karamin
Kaunarsa acikin Raina.

Wata Daya Hibba tamana kafin Hutunsu ya kare Nida shi muka je Abuja muka
Maidata,chan mukayi Weeked din mu sai Saturday muka dawo da yammah,ba inda nake
zuwa koda yaushe ina gida ina Fama da kewa in nagaji da kallo na koma latsa waya
domin ni haryanzu ban saba da Chart ba,wani lokacin nayi karatun Littafi Tuni kewar
gida ta Fara zuwarmin Raihana kuwa nafikowa matukar kewarta Ita da Modibbo Saboda
Sanda Suna nan ban Shiga wannan kewar ba,ganin zaman kadaicin yamin yawa yasa na
sakashi in zai Fita zuwa wajen aiki sai ya kaini gidan Ammi ko Wajen Anty Aisha na
Wuni sai in ya tashi Daga cikin Makaranta ya biyo ya Daukeni bama komawa gida sai
mun Biya Munyi Takeway watarana kuma muci awaje kafin mu karisa gida,Rayuwarmu dai
muke gudanarwa gwanin Ban sha"awa.

Ranar kawai tun 7 zai shiga cikin Makarnta ina kwance ina kallonsa yana gyara zaman
Hulan kansa sanye yake cikin Wani Farin Boyel,mai Sharara domin Har ana iya hango
Farar Vest din Dake Jikinsa babu aiki jikin kayan Domin Dinkin Zamani ne,sai links
din da akama Gege da Gefen Hannun Kwalliya kanshi bakar hula ce yake murzawa kamar
yadda kafarsa ke sanye da bakin Sawu ciki na Fatar Damisa Haka Agogon Hannunsa ma
baki ne na Fata na kamfanin Rado.

Kallona yayi yana Mirmishi kafin yace"Mai ciki yadai..? Fuska na tabe kafin nace"Ni
wai Fita zakayi ka barni ni kadai acikin gidanan...? Yana Fesama jikinsa Turare ya
juyo yana Fadin"Naga yau kina jin Lalaci ne,zan Fita baki Shirya ba Balle na
ijiyeki Gidan Ammi ko Wajen Anty Aisha..."Baki na Tura na Yunkura na mike da
Cikina wanda ya Fito sosai kamar ba Wata bakwai ba domin ya Turo sosai Shiyasa Duk
wasu aiyuka ma Ya Daukemin in bai yi da Safe ba in ya dawo da yammah zai Share Mana
Falo da Bedroom dinmu ni kuma kafin ya Dawo na gyara kichen na goge abunda na
bata,bancika yin girki ba Tunda ya Hanani sai dai mu fita muci ko kuma in zai Shigo
ya Shigomin Dashi.

Sai da na mike kana nace"Nifa na gaji da zuwa gidan mutane Hakanan B.love,Zaman
kadaici ya Dameni ko zaka maidani Abuja ne wajen Su Daada zan fi Jin Dadin zamana
achan.."Harara ya sakarmin kafin yace"Ni kuma ki barni kadaicin ya kasheni ko..?
comon jare shirya mu tafi Sch tare yau 12 zan bar cikin School din.."Kallonsa nayi
kafin nace"Da gaske...? Lum yayi da ido kafin yace"Zan sauya Ra"ayi ."Ai da gudu na
Fada Tiolet ina Murna da kallo yabini baki Bude yana Dariya.

Agurguje nayi wanka na Fito Shiya taimakamin na Shirya Cikin Riga da zani na wani
Leshi Domin yanzu bana saka Riga da Sikt Tunda Cikina ya girma Matseni Suke Duk sun
man kadan,dogon Hijabi yace na saka Dama Tuni ya hanani saka karamin mayafi sai
babba yau kuma Ra"ayin Hijabi yake ji Hakanan na saka Muka Fito yana Rike da
karamar Jakata da wayata da key din mota muka Fice ko karyawa bamu yi ba yace Karna
damu zamu karya in muka isa office dinsa.

Salihu megadi ya wangalemana get yana Fatan Dawowa lafiya,Muna Tafe muna Hira har
muka Shiga cikin Makarantan,Tun Shigarmu naji Dama banzo ba saboda yadda gabadaya
Hankalin Dalibai dake wajen parking space Daga Nesa suka sakarma ido,shi ya fito
Cikin Kasaita bayan ya kashe motar ya zagayo ya Budemin Ya Taimakamin na Fito Tunda
yanzu nayi Nauyi Kuma Duk da Dogon Hijabin Dana Sanya bai Hana cikin jikina Fitowa
ba.

Shi ya Daukomin Jakata, kuma muka Sarke Hannayen Juna muka Fara Tafiya zuwa cikin
makarantan ta ko"ina ido ne ke kanmu,saboda yanayin yadda Jikina ya bani na gane
kallonmu kawai ake da Gayyar na Sadda kaina Bisa kafadansa ina Marairaicewa Da
Hannu Daya ya Rike Jakar Dayan Hannun kuma ya Zagayo kuguna Dashi ahaka muka Ratsa
Filin Haraban na Mathematisc Dep,har zuwa Cikin Kayatattacen office din Mijina

Ya zaunar dani bisa Kujeran Dake Office din ya Dauko min Madaran Hollandia da cake
ya bani yace na Jirashi zai shiga karatu yanzu ammh bazai Dade ba zai fito kai na
gyada mai na Kishingide ina Jan iskar A.C Dake Kadawa Lokaci Daya tana bada wani
Sautin kamshin mai Dadi.

Ranar Gabadaya Jami"ar BUK ta Dauki labarin MR Bello Jikamshi yazo da matarshi,Kai
wasu da basu ganni ba suna Fadin zasu so ga wata mai sa"a ce ta samu Nasaran Zama
matar The young Teacher,harda labarin ma ina da ciki cikin Hakane B.kaita ta Tsinci
labarin a Department dinsu tana jin Haka ta Daga waya ta Kirani Lokacin ina ta
Danne danne Bisa System din mijina ina kara Jinjina ma baiwar da Allah yayimai,na
daga muka gaisa nan take Tambayata na shigo cikin Sch ne nace mata eh ina Office
dinshi shi kuma yashiga karatu jin Haka yasa tace bari su zo ita Aliya.

Wasu Dadama jin Billy kaita ta sanni yasa sukayi gayya suka Biyota har cikin Office
din Mijina Domin Su ganni su karemin kallo,ban nuna wani Abu ba duka na basu hannu
muka gaisa wasu har suna Min murna samun gwarzo Miji kamar Mr Bello nace ina
godiya,muna nan tare aka kirasu zasu shiga lacra sai gani nida abaya bana bama
karatu muhimmanci naji nima ina Sha"awar Kasancewata Daya Daga cikinsu nan suka
barni suka min sallama suka tafi,Aji daya yama karatu Ranar ko 12 din bamu kai ba
muka bar cikin Makaratan muka koma gida Ranar Wuni mukayi Cin Soyayyarmu kamar Babu
Abunda ya Damemu,Tun kuma Daga Ranar in zai shiga makaranta tare muke Shiga Ya
barni office dinshi,watarana ma in na saka tsiya Dani yake tafiya Class din na samu
waje na zauna ina kallon Bakin Mijina Yana Turanci kamar bai taba Jin Hausa ba,shi
kuma Duk da ina cikin Ajin baya nuna ina wajen har sai yagama Abunda yake in zai
Fita ya Yafito ni da Hannu,na taso ya kama Hannuna mu Fita,Dalibai dadama
Soyayyarmu na Burgesu Wasu yanmatan da suka mutu kan sonshi sun ma cire rai Dashi
ganin baya ji baya gani sai akaina.
*****

Cikina na Shiga Wata Na Tara Daada Ta ma ya muktar mganar ya kamata Bello ya


maidani gida chan Borno na Haihu cikin Yan"uwana da Dangina Tunda Haihuwan Fari
ce,ya muktar shi ya kira Bello yamai mganar kai Tsaye yace shi bai yarda ba ba inda
zani haihuwa a kano zan Haihu,sanin halin Taurin kan Bello yasa Daada bata bi ta
kanshi ba Ta tacema Anty Rahila ta Shirya su Tafi kano su Taho dani bata mata musu
ba,suka Taho kano ni ban ma san da maganar ba Jiya Dai Daddare naga baiyi wani
barcin kirki ba Lokaci bayan Lokaci sai yayi ta sakin Tsaki Shi kadai.

Basu min wani bayani ba suka Shiga Hadamin kayana wai tafiya dani zasu yi Abuja
gobe Mallam Inuwa yakaini Borno Achan zan Haihu Duk da naji Dadi ammh kuma sai naji
na Damu Saboda nafikowa sanin Halin Mijina Belle ma Naga kamar baisan da Tafiyar ba
kuma ko ya sani bada Yardanshi bane,Dana ce zan Kirashi ma Daada ta Hana ni kiransa
ina ji ina gani suka gama Hadamin kusan Rabin kayana su ka kuma kwashi na Haihuwan
da muka Taho dasu Daga Eygpt,Suka Tisa keyata sai cikin Mota ina kuka ina komai Sai
da muka Dauki Hanya kana Daada ta Kirashi tana sanar dashi tazo ta tafi dani gobe
zan Wuce Borno achan zan Haihu banji mai yace mata ba,ammh Daga yanayin Nagane Fada
yake ta ma Daada ta kashe Wayarta bata Biyemai ba,Shiko yana cikin Office dinsa
Daada ta kirashi tana gayamai Abunda ya kusa sakashi ya Rasa Control dinshi kawai
saboda an maidashi Sakarai sai azo atafi Dani batare da saninshi ba kuma Hardani
aka taru aka Raina masa Wayau meyasa ban kirashi na gayamai ba Ransa yayi mummunar
Baci Ranar Sukansu Dalibai Sun gane an Tabo Mr Bello domin Motsi kadan kikayi sai
kiji yace out.

Har muka isa Abuja Ban saki Raina ba,Tun muna mota naketa kiranshi yaki Daga
kirana,Sai na Hakura na kyaleshi sai da Daddare na Turamai sako

_Salam B.love....My Love am srry da Abunda ya faru ba laifina bane naso kiranka na
gayamaka Daada ta hanani...Kasani nima ina cike da kewarka kamar yadda kake cikin
kewata...Zuciyata ta cika da Kuncin Rashin Ganinka akusa dani...Ina cikin Kukan
Kewarka Mijina..._

Na turamai sai da ya tafi na kwashe wayar na kwanta ina Hawayen kewar mijina da
Tsausayinshi.,Shima anashi Barayin Hakane koda yayi Fushi Dani Haka ya Dinga Juye
Juye saboda kewata sakona kuwa ya karanta yafi sau goma shi ya Debemai kewa Har ya
iya yin Barci Washegari Haka ya tashi Duk bayajin Dadi ko Sch kasa Shiga yayi
Gabadaya bai saba Rayuwa Bani ba ya saba dani,yasaba da komai nawa Sai yanzu kuma
Lokaci Daya azo aragemai jin Dadi.

Kamar Yadda Daada tace ko Washegari Aka Duramin kayana cikin Booth din mota,Mallam
Inuwa ya kaini Har Borno kafin mu isa kafafuna sun kumbura saboda Zama,mutanen
Gidanmu sunsan da zuwana Tunda Anty Rahila takira Mama yana ta Fadamata kafin mu
iso ta gyaramin Cikin Uwar Dakinta inda zan Sauka,mallam inuwa yaso ya koma sai Ya
Ali ya hanashi Sai da ya kwana Washegari ya koma Duk da ina cikin Damuwar Rashin
Mijina Domin yayi Fushi Dani ko na kirashi baya Dauka sai dai na Turamai sako ya
Karanta bazai bani amsa ba Duk na Damu ammh ganina cikin Dangina yasa na Saki
Jikina Mama yana dasu Ya Ali bansan wanda yafi wani kula dani ba,Haka matansu Ya
Ali komai nace suna Rawan Jiki su bani Mama Falmata kuwa Sai kawaichi ammh cikin
Ranta tana min Addu"ar Allah yasa na Bude ido lafiya.

Sati na Daya Da zuwa Borno ammh haryanzu Bello bai sakko ba Abun yafara Damuna
Sosai Duk da Cikin Jikinna sai na Fara rama,gashi ba"a san masu Juna Biyu su Shiga
Tunani,nan da nan kuwa sai ciwon kai mai zafi sai da aka Dangana ni da Asibiti nan
akace Jinina ya Hau na kiyaye Da Tunani Saboda zan iya sanun Mtsala Nida Da Abunda
ke Cikina nan suka Rikeni sai da na kwana na Wuni kana muka koma gida Ranar ina
zaune Kan gadon Mama Yana ina Shan Mangwaro sai ga Kiran Wayata ina Dubawa naga
B.love ne.
Duk da Abun yabani mamaki ban yi Saurin Dauka ba na Zubamai ido yana ta Kira ban
Daga ba,har Sau uku kafin ya Dakata da Kira ni kuma ban Daga ba Domin Azahirin
gaskiya yagama batamin rai kuma yabani mamaki ban taba zaton koma mai nayi ma
B.love zai iya yayimin Irin wannan Hukunci ba balle kuma yafi kowa sanin Bani da
laifi.

Nagama Shan Mangwarona kenan Sai ga Khadijan ya Ali ta kawo min Wayar ya Ali wai
mijina na Mgana Karba nayi ina basarwa bata Tsaya ba ta Fice ta barni,Ba a dauki
Lokaci Ba sai ga Kiransa ya sake Shigowa Tana gabda Tsinkewa kana Na Daga Tunda na
Dauka banyi mgana ba cikin Sanyin Muryansa ya Furta"Wani Tunani kika saka Aranki
Har yana neman ya Tabamin lafiyanki da Abunda ke cikin ki..?..

Yafada cikin Kaushin Muryansa Ina jin Abunda yace na sakamai kuka,Wiwi Shuru yayi
bai cemin komai ba Har nagaji nayi Shuru na koma ina Sharbe Hanci Cikin Muryan Kuka
nace"Har ma tambayata kake meke damuna..? Ina da wata damuwan Data wuce ka ne..? ka
manta da ni Kwata kwata Baka Daukan Kirana kuma baka Kirana.."nafada ina Tura
baki,Mirmishi ya saki kafin ya Koma ya Kwanta yana Dafe Kirjinsa Cikin Wata Irin
Murya ya Furta.."Laifi kikaman Anee Shiyasa.."Cikin Tura baki nace"Laifin me nayi
maka kuma...?

Yace"Laifin kin tafi kin barni mana my Anee kinfi kowa sanin Ba wanda na saba dashi
sama dake....ammh baki damu ba kika Biyema Daada ta Rabani Dake...Ya kike Tsamanin
bazan Damu ba...Bana iya barci Saboda kewarki Akullum Sakon ki ne ke Debemin kewa
ammh Jiya najiki Shuru kuma nayi ta kiran wayarki Tana kashe na Damu sosai sai na
kira Ya Ali shine yace min kina Asibiti baki da lafiya Jininki ya Hau...Na Shiga
Damuwa Sosai My Anee Duk da kin Batamin rai buh na Riga na yafemiki fata nima zaki
yafemin Kuskurena.."Yafada cikin Alamun Shagwaba..

Ido na lumshe Lokaci Daya ina Jawo Filon Dake kan gadon na Matse Bisa Kirjina ina
Fadin"Naki wayon bayan kasa Babynka ma yayi kewarka..."Cikin Mirmishi yace"Zan zo
anjuma na lallashi kayana ba Ruwanki.."Dariya na saki ina Fadin"Anee tayi kewar
Mijinta sosai..."Cikin Wani Shauki ya gyara kwanciya yana Fadin"Mr bello ma yayi
kewar Matarsa Sosai Fiye da yarda Tayi kewarsa..."yafada lokaci Daya yana Sakarmin
Kiss Cikin Kunnena Kasa nayi da ido kawai ina Sauraran Labarin Irin kewata
Dayayi,Nima nan na shiga bashi labarin Kewarsa Danayi Tuni muka manta da wani
Fushin Juna muka Shiga hirar Soyayya sai da muka ji Kiran Mangariba kana muka
Hakura wayar Ya Ali kuwa Sai kira mutane suke muna sakasu cikin Call Waiting,muna
gama wayar na lallaba na tashi Zuwa Shashen Ya Ali tunkan na Shiga na cikaro da
Yarsa Samiha na mika mata na juyo ina Dariyan Sanin Halin masifan ya Ali.

Bayan sallar Isha"i muka Dasa Daga inda muka tsaya Muna waya Yana kichen yana Dafa
Indomie haryagama yaci muna mgana sai da zai shiga wanka muka Hakura bayan ya Fito
kuma koda ya Kirani barci ya kwasheni sai da safe naga sakonsa.

*Sleeping Beauty...My Wife...*

Mirmishi nayi Lokaci Daya ina Sumbatar waya kamar Shi nake gani,Tunda muka Shirya
sai muka koma bamu da aiki sai waya,in yana gida ko yana makaranta sai dai kuwa in
ya Shiga Clasa ne zamu Hakura yace min zai zo ammh sai Weekend.

****
Ranar Jumma"a Tun Safe Dana tashi naji bana jin Dadi Ciwon baya,sai ban Nuna ma
kowa ganin Dama ya sabamin irin haka,Ashe Naguda nake bansani ba Sai wani Lokacin
naji marata ta Daure Duk ban kawo komai ba sanin naji labarin Haihuwa ba Haka take
ba,Su Ya Ali duk basu nan sun tafi masallacin Jumma"a na Shiga Tiolet zanyi alwala
na Durkusa zanyi Fitsari naji Wani Ruwa na Biyo nayi kokarin Tashi na Duba ban iya
ba Saboda wani Azaba danaji ya kamani Bansan sadda na Fasa Ihu ba Saboda ji nayi
kamar zan mutu ne.
Mama yana nake kira Kamar Muryata zata Fashe ita da Falmata suka Rugo zuwa cikin
Bayin na Dakin Mama yana suna Saka kansu Cikin Tiolet din na saki Nishi jin Wani
Abu na Shirin Fitowa Daga kasata,dafa kasan Bayin nayi ina kuka lokaci Daya da
Hawaye Zanin Jikina Tuni ya yaye kanshi Saboda azaba,ko kafin su kariso kusa dani
na Saki gatso Lokaci daya ina Fadin"Innalillahi...Hasbunallahi...Mama...mama ki
Dubamin kashi ne yaki Fito ko menene.."Na bani Zan mutu..."Haka na ke Fada kafin na
saki Nishin da karfi sai ga D'an Da ya Fito Lokaci Daya mama yana ta saka hannu ta
jawoshi tana Fadin"Alhamdulilah...Lalle kin gado Falmata Haka tayi Nakudar ki Daga
zuwa Fitsari sannu Kinji Aneesa.."Tsakar bayin na koma na kwanta ina maida Numfashi
Mama Yana ta mikama Falmata Yaron Daya cika wajem da kukansa Ita kuma tayo kaina Ta
shiga matsamin Ciki sai ga Uwa ta Biyo Baya,Mama yana ta Shiga gyarani ita kuma
mama falmata ta yanke Cibiyar ta Nade Yaron Cikin zani ta Fita dashi nan da nan
Mama yana ta hadamin Ruwan zafi mai zafi ta min wanka ta kamo ni muka Fito,ita kuma
Tuni Mama Falmata ta gaya su Khadija Haihuwan sun saka Ruwan zafi sun Wanke Jaririn
Tas,sun sakamai wasu kayan sanyi masu kyau,Kafin kace kwabo sun gama gyaramu Nida
Jaririna kato mai kama da Ubansa sak,sai dai su Ya Ali suka Dawo suka ganni kwance
kan gadon Mama yana nida Jaririna bayan Sun Hadamin Faten wake mai cike da Kayan
ciki,da kunun Tsamiya na Daddaka kana na koma na kwanata,kowa sai mamakin Naguda ta
yake Cikin Lokaci wai na Haihu kuma agida.

Ni na Turama Bello Text da cewa..." _Alhamdulillah...MR BELLO MUHAMMED JIKAMSHI is


Now a father..._ na Turamai ko minti goma ba"ayi ba sai ga Kiranshi cikin Rawan
Jiki yana Fadin"Anee wai da gaske kike..?ina Dariya na karamai kukan yaron wanda
Tunda ga Fitowarshi Duniya na gane yana da da Rigima Hawayen Farinciki suka Kawo
cikin Idanuwansa cikin Murna yake Fadin"Masha Allah Alhamdulillah..Allah Nagode
maka Wlcm to the World...Muhammed Amin.."Yafada yana Dariya cikin Farinciki Nima
Murnan nake kafin kace kwabo Haihuwata ta Zaga Dangi da Abokan Arzuka,waya kuwa har
nagaji da amsawa,sai washegari kana Muka tafi asibiti aka dubamu Nida Jaririna aka
tabbatar da komai lafiya kana muka Dawo

Tuni Ruwan Nonona yazo Saboda Mama yana batamin da Wasa abinci nake ci kamar
gara,Dama gashi yaron akwai Rigima ga Tsotso,Kwana biyu da Haihuwarmu ango karni ya
Diro Shida Takwaranshi wato Uncle Aminu,Haka suka tasa yaron nan gaba suna kallo,ni
kuwa agabansu Anty Nafee da Matan su Ya Ali Bello ya Rumgumeni tsam yana Juyi Dani
nine ma naji kunya ammh Shi ko ajikinsa sai wajen la"asar suka tafi dama Tafiyar
Jirgi sukayi,Su Daada kuwa kwana biyar da Haihuwana Suka Diro borno ita da Anty
Rahila da Niki nikin kayan da Bello yamin Wajen akwati Biyu na Fitar Suna
Da kuma Raguna guda biyu na Ya muktar tare suka zo yayi min Barka yabi Jirgi ya
koma.

Abun mamaki ana gobe suna Billy kaita da Salamatu Jibiya suka iso basu Dade da zuwa
ba sai ga Ammi da Raihana da Anty Aisha na Daka Tsalle muka Rumgume juna da Raihana
Saboda Murna nan muka Hade da Sanah sun zo tare da Anty Yagana,Yan"uwana ba karamin
kara sukamin ba Komai na Abunda za"aci sun hana Bello da Ya muktar aiko da komai su
suka Dauki Dawainiyar Abunda za"a ci Asha Raguna biyar aka yankama Muhammed
Amin,Biyu na wajen Ya Muktar Biyu na wajen Mijina Daya kuma Ya Ali ya
yankamin,wayyo Farincikina Baya iya Boyuwa saman Fuskata Saboda yadda na zama zarah
cikin Wata.

Na shiga na fita cikin kayan alfarma Wuyana Zinare ne ke kyalli,Na samu kyatuttukan
kudi Daga wajen Yan"uwana sosai Domin Sun min kara sun kuma Nuna Nidin Auta nake
garesu Daga Bangaren gidansu Abba Kabiru kuwa ba Wanda yazo ko matar Hashim bata zo
ba,Saboda Jikin Abba kabiru dai yaki dadi An ma maidashi gida ana cigaba da
Jinyarsa Komai ya kare,sai Hakuri kawai da Rayuwa Sai dai Sun kirani ta waya suka
min Barka,Abun mamaki Harda Zubaida acikin masu kirana gwanin Ban tsausayi mama
Sahura ma ta kirani tamin Barka suma Babu komai Inna Rukayyah ce Dake kano take dan
Taimakosu itama Babu karfin Hali ne ga Su Hamdiya Dake hannunta komai nasu itace.
Anyi suna lafiya Antashi lafiya Hatta da matar Sani sai da tazo ta kwana
daya,Washegari ta Tafi maiduguri,yarta na Aure achan Su B.kaita kuwa Uncle Aminu
Suka bi,tun safe yazo Daga lagos yake suka bishi suka koma Ajirgi yana ta mamakin
Girman Su B.kaita wai yaana musu Tsiyan sun zama yanmata,Harda Ammi da Raihana dama
yazo ya tafi dasu ne,Da zasu tafi nayi ta musu Godiya sosai na basu nama da Sauran
Abubuwa.

Hatta Anty Nafee da bama Shiri yanzu mugun Mutumci muke,Saboda Tunda na gane
Halinta na Ci mganin zama da ita Duk Abunda tace dashi mukayi amfani Mun nuna mata
Itace Babba damu Abun yayi mata Dadi ta saki ajiki anata Harka kamar ba ita ba.

Wajen sati biyu Anty Rahila sukayi kafin su koma Abuja Ita da Daada dasu Hibba
Tsakaninsu da Anty Aisha kwana Uku Itama tasha Na gida,Anty yagana kuma Kwana Biyar
tayi ta koma sai ta bar Sanah anan muna tare,Anty Nafee kuma Dama yar kusa ne
Kwanata Biyar ne itama ta koma gida ya watse Dagani sai Sanah Mama yana ce keta
kokari akaina itakemin Wanka Khadija matar Ya Ali Ta ma Amin wanka,Mama falmata
kuma ita ke kula dani ta bangaren Abinci Ta damamin Kunun Kanwa,nasha ta Hada min
tea nasha mai kauri basu barina da yunwa Shiyasa Ruwan Nono ke zuwa sosai,kafin mu
Rufe Sati Uku Muhammed Amin yayi Kato Dashi Saboda yana samu Dukkan kulawa ta
kowani bangare.

Kibiya ki karanta cikin salama

*Shakira...*
8/22/20, 10:27 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan �?200 kachal,Vips �? 400


ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku
iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*END*

"Haka na cigaba da Jego na agida Hakika Duka iyayena suna kokari akaina Sosai kafin
muyi arba"in Dagani har Muhammed Amin,Mun chanza munyi kiba Sosai Barin ma ni Ashe
Zanyi kiba Duk Rashin Kibata na zama yar Lukuta yanzu jikina ya Murje kamar bani
ba...

Duka duka sau uku Bello yazo ya ganmu sai dai koda yaushe muna tare awaya,saboda
aiki yayi mai yawa kuma y sanar dani zai bani wani mamaki ne akwai Shiryen Shiryen
Dayake mana ne,Ban damu ba sanin komai mijina kuma gwarzona zai Shirya mai kyau ne
kuma na musamman ne agareni.

Bangaren Kayan gyara kuwa Babu Abunda zancema Mama yana sai godiya domin bata barni
haka ba,Koda yaushe cikin Sakani take na shiga Ruwan zafi wacce aka dafa da
bagaruwa,magungunar mata na Tsari wanda Addini ya yarda dashi kamar kayan
itatuwa,madara, zuma da Shan Abu mai Romo Anty Nafee kuwa Da kanta ta hadomin
Gumbar Hadi mai kyau da Turaran Humra mai saka kamshin Dadi,Hade da Hadin kaza mai
mgani naji Dadi sosai ban kuma Taba zaton Zatamin Haka ba Shiyasa da Sanah tatashi
komawa gida na hadamata kaya sosai,da kudi Nace ta kaima Anty Nafee kuma ta
gayamata in Bello yazo tafiya Dani ko kafin yazo zan zo na mata kwana biyiu,Taji
Dadi sosai Domin Haka ta kirani Ta waya tana min Godiya Naji Dadi Sosai na yarda
Anty Nafee ta yarda da komai takuma Fahimci Allah kadai keyi.
Ranar da mukayi Arba"in da Haihuwa na Gayama Bello zan Dan yawata gidajen Yayyina
kafin na Dawo bai hanani ba yace naje ammh nan da Sati Daya zai zo yatafi
dani,Maiduguri na fara zuwa gidan Anty Nafee wacce Taji Dadin Zuwana kwana Biyu
nayi mata ta dinga mana Rawan Jiki,Dagani har Muhammed Amin,haka zata mai wanka ta
Shiryashi ta goyashi Tsab,Kafin mu tafi sai da ta kara hadamin wasu mgungunar karin
Ni"imar wanda zan koma kano Dashi,Daga gidanta Sanah ta Rakani Ibadan,gidan Anty
Yagana Itama na mata kwana uku kamar kar mu dawo Saboda kewa Ashe haka yan"uwa ke
Da Dadi Duk da ina Bala"in son Mijina na kuma yi kewarsa Baisa naji ina Dokin
Komawa ba...

Ya Ali da ya sunusi sukayi ta Shirin Komawata Kano,da Satin ya kare Bello bai zo ba
bai samu Lokaci ba ganin Haka yasa batare da jiran komai ba,ya kira Anty Nafee yace
tazo ta rakani na koma zaman ai ya isa haka,Washegari kuwa har kofar Gida Ya Ali ya
samarmana Tashar mota aka zubamin Duka kayana aciki,Da zan tafi Haka na Rumgume
mama falmata da Mama yana,ina kuka da matan su ya Ali sukansu sunshiga kewa barin
ma Muhammed Amin da kowa ya saba dashi yaro mai Shiga rai,Har motarmu ta mika ina
ta koke koken Rabuwa da gida Anty Nafee namin Dariya.

Ba kano muka fara zuwa ba,Abuja muka nufa sai dai suka ganmu kwatsam kamar Daga
sama Mallam Inuwa na shiga da kaya,Murna wajen su Anty Rahila kamar Daada taji
labari Haka ta Dauki Muhammed Amin tana mai Rawa,Ni kuwa ina gefe duk ban Ji dadi
kewar Borno taki barina koda wasa ban gayama Bello mun taho ba,koda muna Abujan
Adaran Ranar da muka iso ban gayamai yana ta kokarin Gayamin insha Allahu yana tafe
wasu abubuwa ne suka Rikesa.

Da daddare Ya muktar yadawo Shima yayi murna da Zuwanmu Ya Dauki Muhammed Amin yana
Cillsa sama,Hibba da Junoir suna Fadan Wai suma sai sun Daukesa Hibba Tana iya
Daukansa Dakyar Junoir kuwa,Sai dai su fadi duka Tunda Shima Muhammed Amin ya samu
Nono mai kyau,Sai kiba yake yi Abunshi.

Kwana Daya mukayi A Abuja washegari Mallam Inuwa ya kwasheni Nida da Anty Nafee da
Anty Rahila zuwa kano,Tun Safe muka Tafi wajen 11am muka isa Salihu megadi nata
murna har ya Dauki Muhammed Amin yana sakamai albarka,Koda muka Shiga cikin Gidan
Gabadaya an Sauya komai na gidan,Kama Daga Falon Farko zuwa Falon mu Da Dakunan
barcin mu Kamfanin MAHARBA ya kira suka zo suka Sauyamana komai.

Ashe mamakin Daya ke cewa zai bani kenan naji Dadi sosai yadda Mijina ya Shirya
Dawowata,Duk da gidan bai yi wani Datti ba Su Anty Rahila suka zage suka kara
gyaramin ko"ina suka Tsabtace kichen Tunda Anty Aisha ma tazo muna zuwa Suka mata
waya Su sukayi mana Abincin Rana mukaci muna Hira,Sai bayan la"asar sukayi Shirin
komawa Abuja,Washegari ita kuma Anty Nafee ta koma Maiduguri.

Nayi nayi su Bari Bello ya Dawo sukaki saboda zasu yi dare,Duk da shima Uban gayyar
baisan da Labarin Dawowata ba ban yadda na gayamai ba,har haraban gidan na rakasu
ina Dauke da Muhammed Amin ina Daga musu Hannu har Mallam Inuwa ya Fice dasu Daga
Haraban gidan sai gashi ina kwalla Allah Sarki Duk Duniya baka da kamar yan"uwa
kome kuwa Namiji ke baka Na Dadi baka isa ka maye gurbinsu dashi ba.

Daganan Gidan Anty Aisha Suka biya basu wani jima suka ijiyeta suka juya daganan
Suka biya Suka gaida Ammi A tsatsaye shima Sun iske Raihana Bata nan Tuni ta koma
Makaranta sai dai sun Tarar Da Uncle Aminu agida,Dayake bayan Tafiyar Raihana
makaranta Sun samo mai kula da Ammi Tunda ba Lafiya bane ya isheta,Daganan Suka
Dauki Hanyar Abuja.

Suna Tafiya Na Fara kokarin Hadama Mijina Dinner Suprises din Dawowata,Nono na bama
Muhammed Amin na lallashesa har yayi barci na kwantar Dashi acikin Daya Daga cikin
kujerun Falon,Ni kuma na Shiga kichen inda Allah ya taimakemu mun Dawo mun Iske
Fridge din Shake da Cefane,Kamar bai Dade da Siyo komai ba,White Rice na Dafamana
da Miyar kayan miya wanda na Nika sama sama a blander miyar nayi ne da Ruwan Naman
Rago zallah,bayan kuma na Sanya mata naman Sosai Sai Salt nadanayi mana bamu da
cabbage da Cocumber Fita Haraban Gidan nayi na Roki Salihu megadi,Shi ya taimakamin
ya Shiga kasuwa ya Siyomin na Hadamana komai,Da naso na Hada Zobo ne sai kuma babu
ganye zobon sai na Nahadamana Lemon kankana Na kuma Hadama na,Gwarzona Fruit salt.

Ana kiran sallan Mangariba na gama komai na jera bisa Dinning Table din,Na Dauki
Muhammed Amin muka Shiga Bedroom dinmu,Muka shiga Tiolet mukayi wanka sai da na
Shirya shi cikin wasu Riga da wando masu kyau cikin Wadanda muka Siyo ne da zamu
dawo Gida Nageria,Sai da na gama Dashi na Feshishi da Turare ina Mirmishi ni kadai
kana na kwantar Dashi Kan gadon na saka Hijabi na Tada Sallar mangariba dama
already na Dauro alwala.

Sai da na idar kana ta Fara Shiryawa Manshafawata na Olive na Shafa,Dama already


Tun kafin na Taho Anty Khadija matar ya Ali ta min irin kitson mu na Borno Hiri
Hiri kanana Sosai 2Steps Sunyi kyau sosai,ita kuma Anty mariya matar Ya Sunusi ta
min Kunshi irin namu na Kanuri Abun sai wanda ya gani.

Sai da na bi kowani Lungu na Jikina da Turaren Humrata.Kafin na saka kayana Wata


Shadda na saka Wagambari mai kadan Ash da Ja,Riga da sikat wadanda suka kamani
sosai suka kara kuma Fitar da Surata na tsaya na bata Lokaci na Tsantsara kwalliya
mai burgewa,Kafin na koma na Dauko Daya Daga cikin Sabbin lifayan Da nazo Dasu mai
kalan ja Shima da Zanen Ash yana da Tarin Duwatsu masu kyau ajikinsa,na Nadashi
acikin Jikina,ina tsaye ina kallon kaina acikin madubi Turaran jiki na Dauko na
gama Feshema Jikina Daga nan naji Karar Bude get da Rufewa ,alamun gwarzona ya Dawo
kenan.

Saurin Daukan Muhammed Amin nayi na Koma Falo na Boye ta Bayan labulan Window
Daidai Lokacin da Naji Suna gaisawa da Salihu megadi,Mirmishi nake saki araina ina
bayyyana adadin kewar mijina Danayi,Ina jin Takunsa Zuwa cikin Falonmu har ya Shigo
yana bin ko"ina da kallo Cikin mamakin jin kamshin Turaran Wuta mai Dadi,lumshe ido
yayi Lokaci Daya yana Karisowa Tsakiyar Falon,yana Tunanin ko wani yazo gida nan
ne,Domin ko"ina tsab sai kamshi ke tashi Alhalin yasan ba Haka ya Fita ya bar gidan
ba Duk da bai barshi cikin Datti ba ammh na yanzu is Different.

Yana cikin Waige Waigen ne,Ya ci karo da Dining Table Shake da kolilin Abinci Shuru
yayi yana bin Wajen da kallo kafin ya karisa ina ta cikin labulen Dayake Shara
Shara ina karemai kallo,ya dan rame kadan ammh ba sosai ba,Sanye yake da American
Suilt masu Ruwan Toka ya matse Wuyansa da Tie,kafarsa sanye cikin Takalmi mai Rufi
na Fatar damusa.

Karisa yayi ya saka hannu yana Bude Kolilin Abincin Daya Bayan Daya kamshin ya
Dakeshi,Lumshe ido yayi ahankali yana Fadin"Anee....My Anee.."Yake Fada cikin Sanyi
da murna kafin ya waigo yana Waige waige cikin Muryan Fushi da Lallashi yake
fadin"My Anee where are u plz come out...Karki sakani cikin garari i know wannan
kashin baza"a sameshi wajen kowa ba sai wajenki Matata..."Yafada yana lumshe ido
Ina kallonsa ina Danne Dariya Dawowa yayi tsakiyar Falon yana neme neme,kafin ya
Shiga Duka bedroom dinmu yana kiran Sunana,yagama Dube Dubensa bai ganni ba ya fito
ya shiga dayan Bedroom din nan bani ciki Haka ya Dawo falon yana Rike kugu cikin
Sarewa yake Fadin"Anee...Wai bazaki Fito na ganki ba...? Yake fada yana Kara ware
idanuwansa cikin Tsakiyar Falon.

Bakina na Rufe kada Dariyata ta Fito kaawai sai Muhammed Amin ya tona ni inda yana
Wasa da Hannunshi ya Bude Labulen Lokaci Daya yana bare baki da Kuka dama inayi ina
Jijjigashi yasa bai sakamin kuka ba cak ya tsaya yana kallona Ni kuma sai na Yi
jagale ina binsa da kallo kafin na saka Hannu na Dungurema Amin kai lokaci Daya ina
Tura baki kafin na Fito Daga wajen labulen ina yar Dariya Shima Amin kukan ya Daina
yana bin Babansa da kallo kur.
Kansa ya Dafe yana kallona cikin Wani yanayi kafin yace"Anee ni zaki bama wahala
ko..? Yafada yana Sakarmim Manyan idanuwansa,Kai na lamgwabe ina
Fadin"Suprises...."Na Fada ina Dariya bai yi watawata ba ya isa gareni sai ji nayi
ya Hadani Nida Muhammed Amin ya Rumgumemu ya kamkame Lokaci Daya yana sakin Ajiyar
Zuciya Nima Numfashin na Sauke jina Akirjin mijina Da Nadade ina kewa cikin Rashin
Hayyaci yake Sumbatar Wuyana yana Fadin"I love u....Miss u like Crazy my Wifey..."

Yafada cikin Wata murya mai cike da Muradi mai girma nima kara kamkameshi nayi ina
Fadin"Love u...more and more...Nayi matukar kewarka Mijina.."Mundade muna Rumgume
da juna kafin mu saki Juna muka Bi juna da kallo Lokaci Daya muka sakarma Juna
Mirmishi Muhammed Amin ya karba yana Dagasa sama yana Fadin"My Bomboy kana son
Appanka sosai Tunda ka Tona ma mamnka Asiri ko.."Kansa na Tallaba ina Fadin"Waya
gaya maka..? Toh yafi son mamarsa akan Babansa.."Kallona yayi yana Fadin"Kaina fa
kika Dungure.."

Baki na Tabe kafin yayi mgana ta kara Tallabe kanshi ina Fadin"Eh ko zaka rama
ne..?Na fada ina Dagamai girata Guda Daya,Ido ya zaromin ni kuma na Murgudamai baki
ina Dariya Fuska ya Shagwabe yana Fadin"Mr Bello guda kike Dunguri kamar wani
Danki..Karki manta ni ta wani barayin yayanki nake kuma Malaminki nake karma muje
Bangaren Aurattaya zan iya Lallasaki bamai min mgana sai ma Godiya da za"a bini
Dashi.."Yafada muna Shiga cikin Bedroom dinmu Kallonsa nayi ina Fadin"Au ni zaka
Daka...?

Kai ya gyadamin yana Hade Rai,Yar Dariya nayi kafin na Juyamai ina wani taku Lokaci
Daya ina Fadin"ai ni yanzu nafi karfin Duka...Mutum ya Dakeni Wlh Anjuma..."Ban
karisa ba yashiga Fadin"Allah baki hakuri Anty Anee...Bomboy tayani ba mamanka
Hakuri kartamin Horan Da bazan iya Dauka ba.."Dariya na saka shima Dariyan yake
yana Fadin"muguwa kawai.."Tiolet na Fada ina Fadin"Ban kai ka mugunta ba Mr
Bello.."Yana jina bai bani amsa ba Farinciki ya cikashi Har nagama Hadamai Ruwan
wanka na Fito yana ta wasa da Amin,Karban Amin nayi na ijiyeshi kan gado shi kuma
na taimakamai na ciremai kayan Jikinsa na rakasa Har Tiolet din yaso ya batamin
kwalliyata na Zille ina Dariya na Fice Daga cikin Toilet din na Rufo masa kofa.

Koda ya Fito har Muhammed Amin yayi barci yana shan Nono Shikenan ya bingire yana
barci daman Shi Nono ne mtsalanshi yana Jin mai Dumi acikin Cikinsa Shikenan,ni na
taimakamai ya Shafa mai ya saka wata bakar Jallabiyansa kafin na kama hannunsa mu
fita zuwa Falo sai samam Dining,Ranar nasha yabo da Santi nan take ya bani 50k cash
saka albarka kuwa sai da na Rufemai baki Farincikina ya cika bakina yaki Rufuwa
Ashe mata Dadamama haka Sukeji in sukayi Wani Abun don Mazajensu suka ci suka yaba
musu nidai kam Farincikina ya kasa Boyuwa akan Fuskarta nan yake Tambayata waya
Dawo dani na Fadamai Duk Abunda ya Faru Dariya yayi yana Fadin"Allah sakama Su Ya
Ali da Abarka...Dasu mama gabadaya....Sun yi matukar kokari wajen gyara min Anee
sosai Duk da ta bangaren girki nafara Harba Dashi bansani ko Dayan Harka kuma ya
zata kaya dani ba.."Kirjinsa na Buga ina Dariya nace"Kila sai ka Zauce ka Faramin
kuka.."Fuska ya Shagwabe yana Fadin"ai ni Tuni nake miki kuka My Anee baki sani
ba.."Kallonsa nayi kafin na Sumbaci goshinsa,ina Fadin"Bana Fatan na Rika saka
Mijina kuka.."Hannuna ya kama yna Fadin"Ai bana wahala bane na Tsabar Dadi ne...U
Drive me Crazy Wifey...Allah yayi miki albarka..."Da Amin na amsa ina kara lafewa
bisa jikinsa muna jin Bugawar Numfashin Juna.

Yadda Bello ya Susuce akaina Dakyar ya bari muka karayin Wanka mukayi sallar Isha"i
Muhammed Amin cikin Dan gadonsa na Sanya shi chan gefe mu kuma muka Fada Tsakiyar
gadon Naked ba komai ajikin mu,Fatarmu na gogan Juna muna Kara samun Body Contact
atsakaninmusu,ina kallon Cikin Idanuwansa na saka hannu nayi kasa da Hasken Dakin
ko Dumlight din ban kunna ba Sai Hasken Dake Fitowa ta Tsakanin Labule Ana ta
walkiya Domin Hadari ne ya Hadu sosai agarin Tunda Anshiga Lokacin Damina.

Cikin Fitar Hayyaci muke Sumbatar Juna Lokaci Daya Hannayenmu na kara kaina Jikin
na Juna,lalle na yarda Dagani Harshi munyi kewar juna Domin Dagani Harshi Hawaye
muke Shabe Shabe,Shi kuwa gabadaya mangungunar Danasha Sun Taimaka wajen Fitarsa
Daga Hayyacinsa,ya shiga cikin Wata Ni"ima wacce bazai iya Fassarrata ba,ana Tsuga
Ruwan sama sanyin Damuna ya Hade da yanayi mai Dadi Haka muka kamkame juna muka
Shige Blanket muna kara Caccakan juna cikin so da kauna.

Har bayan sallar Asuba sai da muka Dasa,Haka ya Kamkameni yana sakamin albarka
alkawruka kuwa sai da na Rufemai baki wasu Magnganun ma baisan yana Fada ba,kalmar
ina Sonki kuwa ya Fada yayi cikin Botiki,Nima kamkamesa nayi ina maida Numfashi
cikin Muradi mai girma wanda baki bazai iya Furtawa ba,kuma alkalami bazai iya
Rubutashi ba balle har ya wallafa.

Dawowata yasa muka Bude Sabon Shafin Soyayyah bamu gajiya da juna gefe Daya kuma
muna Kula da Danmu Muhammed Amin kamar mu lasheshi,Bama iya Boye Soyayyar damu ma
Juna ko agaban waye kuwa,Ban yarda na bar kaina na lalace Daga Haihuwa Daya ba na
mike ina gyara kaina Da Jikina Sanin Halin mijina mai son Ado da kwalliya kuma yana
Bukatar kullum ya dinga jin Dadin wajen Harka yan"uwana suna Taimakamin sosai kuma
na tabbata ko yau Baba ya Dawo gidan Duniya bazai Tirr dasu ba Saboda sun kula dani
kuma sun bani kowani irin Gata

*****

Wata uku da Haihuwa ta Bello yagama Dukkan Shiryen Shiryensa sai dai kawai yazo
yana Fadamin ya tura C.V Dinshi Tun last 8 month din Da suka gabata ya Tura ma
jami"ar *CLARKSON UNIVERSITY NEW YORK* kuma Alhamdulillah sun Riga sun karbeshi Tun
Wata Daya Daya gabata so ya tura musu Duka komai ta Email dinsu yanzu nan da wata
Daya zamu tattara mu koma chan da albishir din Nima achan zan Cigaba da karatu na
sun bashi gidan zama har illah masha Allah da Motar Hawa sai dai in Shine ya gaji
ya Daina aiki Dasu.,Ammh sai yaki karban gidan ya neman mana wani mension mai kyau
ya siyan mana komai ta Waya ya gabatar.

Wayyo Dadi murna ta cikani na Daka tsalle na Rumgume Mijina Saboda Farinciki Haka
na Shiga Kiran yan"uwa da abokan Arzuka ina gayamusu suna Tayani Murna B.kaita da
Salamatu Jibiya sun fi kowa murna,Duk d B.kaita tana Tunanin bazan samu zuwa
Bikinta ba wanda aka sanya wata Biyar masu zuwa zata auri wannan dai lacran na
Umaru musa yar'aduwa Universtiy.

Iyayena da yan"uwa sun fi kowa Murna Ko Ya muktar bai sani ba sai da muka je musu
sallama Jinjina kai yayi yana Jinjina ma Kanin nasa wajen kwanya ya Tabbata kaf
jami"o"in Dake cikin Duniyar nan ba wacce Bello zai nemi aiki da ita ta ki bashi
Dama Gabadaya Da grade A yake Fitowa Shi kanshi Dayake yayan nashi yana Jinjina ma
baiwar kanin nashi Sosai.

Daga Abuja Borno mukaje yi musu sallama Kwana Biyu mukayi Munje Maiduguri wajen
Anty Nafee ammh bamu kwana ba,muka Dawo aranar Washegari kuma Muka Hawo Jirgi zuwa
kano Anty yagana sai dai mukayi sallama awaya Anty Aisha dai Naje gidanta na Wuni
Haka gidan Ammi wanda zuwa Lokacin Bello da kanshi yama Uncle Aminu mganar Raihana
da Midibbo wanda ya kusa kamallah Military sch ya kusa Dawowa Itama Raihanar Ta
kusa gama nata karatun su Baffa Hardo suka zo wajen Dangin Su Uncle Aminu suka nema
ma Modibbon Auran Raihana,An saka Lokaci Wata Goma masu zuwa Lokacin Dukkansu
sungama karatunsu Har Modibbo yafara aiki.

Mun gama Duka Shirye Shiryen mu komai namu ya kamallah ba Da wasu kaya bane zamu
tafi sai Abunda Ba"a rasa ba,Jami"ar BUK tafikowa Damuwa da kuma Ganin Asaran Rasa
Mr Bello,ammh basu da yarda zasuyi Tunda dai cigabane ya samesshi haka Daga Daliban
Har malamai aka rabu ana kewar juna Uncle Aminu da Anty Aisha da Megidanta suka
Rakamu Aiport Din Mallam Aminu kano Da karfe 8:30pm na Daren Ranar Asabar jirginmu
ya Daga zuwa Birnin New york.

Mun Sauka a babban Filin Jirgi na New york a inda muka samu Taxi har zuwa cikin
anguwar da Jerin Gidajen da Bello ya siyama suke wato *maahattan Midtown* gida ne
mai upstsir mai kyau da Tsari mai Dauke da Falo da 2 bedroom Daga sama sai kichen
da Dakin baki Daga kasa Daga waje sai aprtment haka wajen parking din motoci,Muna
da makota Wadanda ke kusa damu,Daya barabiya ce karatu Mijinta yazo yi sai Daya
kuma Yar Nageria ce ammh kuma bayarbiya ce Mijinta Likitane Shima aiki ya kawoshi
Sunanta Adija Tunda muka zo kasar itace ta shigo muka gaisa naji Dadin samun Wani
Dan kasata kusa dani.

Dama tun muna gida Nageria Yariga ya karbomin Resuit dina,Ban Fara karatu ba sai da
Muhammed Amin yayi Wata bakwai kana na Zama Daya daga cikin Daliban makarantan Da
Mijina yake koyarwa,ina karanta Biology,Muhammed Amin kuma Dashi nake tafiya Dayake
makaratantar akwai Nannys masu kula da yara wajensu nake kaishi sai mun tashi
tafiya gida mu karbosa mu Dawo gida Soyayya muke gudanarwa mai cike da Tsabta kamar
zamu lashe juna.

Ban samu zuwa Bikin B.kaita ba sudai na Tura mata kudi masu yawa Gudunmmuwa,duk da
Banjin Dadin Rashin Zuwana ba Bani da yarda zanyi ko ba domin komai ba Saboda
karatuna...ga Kuma Mijina ban zan so na zama ina Rabamai Hankali ba ammh koda
yauahe muna waya da yan"uwanmu da iyayenmu Lokacin da muka samu Shekara Daya a New
york Anty Rahila da Ya Muktar suka kawomana Ziyara nan ne naga karamin cikin
Jikinta yawon Bude ido suka zo Domin Hibba da JUnior Suna gida wajen Daaada.

*****

*SHEKARU UKU BAYA...*

Acikin Shekarun ukun Da Suka gabata bazamu ce komai ba sai Dimibin Godiya ga
Allah,Domin Ababen Cigaba ne suka Lullube Duka Rayuwarmu,Duk da mun Kurbi Ruwan
Rashi Sosai na Rasuwar Daada wanda shine Dalilin Zuwanmu gida na Farko Allah yasa
Lokacin mun samu Hutun Makaranta mun ji Mutuwar Daada sosai barin ma Bello da ya
muktar da suke ganin Tamkar Daada itace uwarsu da Ubansu,

Bamu koma ba sai da muka Tsaya Bikin Uncle Aminu Wanda suka Daidaita da Salamatu
Jibiya muka Sha biki Tabi angonta Zuwa Lagos Raihana kuwa kaduna take Zaune ita da
Mijinta Modibbo wanda ke aiki anan Heaquaters na yan sanda Dake Jahar kaduna suna
Zaune Shida Matarsa Raihana,Munje mun yi musu kwana 2 har gidan Sani sai da mukaje
nayi ma matarsa barka ta kara Haihuwa,Naje katsina gidan B.kaita na isketa da
cikinta, Muhammed Amin kuwa yayi yawo ba inda baya zuwa,Sanah ma an saka Lokacin
Bikinta da wani Ma"aikacin Costome Dake aiki a partacourt,

Da zamu koma New york bamu koma da Muhammed Amin ba muka bar ma su ya muktar Tunda
ina da karamin ciki alokacin,Dawowarmu ko Wata Biyu bamu yi muka samu Labarin
Rasuwar Abba kabiru damam Tun Zuwan mu Rasuwar Daada muka samu labarin yana halin
Jinya sosai Tunda ga lalurar Data sameshi,gabadaya duka arzikisun ya kare wajen
siyan mgani Hatta gidan da suke ciki sai da suka Saida Gidan Hashim suka koma da
zama,Gashi bashi kadai bane domin Ramin mugunta ya koma ma Kasim Ya zame a bandaki
kashin bayanshi ya karye yanzu Shine ke Rayuwa Bisa Keken guraku,Abokinsa Haruna
kuwa Hatsarin Mota yayi Allah yamai Rasuwa komai nasu yagama karewa Shi kanshi
Hashim din karfin Hali ne da Godiyar Allah ammh aikin kamfani Har yaushe zai
Rikeshi Inda Allah ya taimaka Zubaida ta Samu miji cikin Abokansa ta aura Matansa
Biyu itace ta uku tana Abuja ammh tana cikin Jin Dadin Rayuwa har ma tana taimaka
ma iyayenta.

Bangaren Su Abba garba kuwa Abun yayi muni sosai,Suma komai ya kare ga cikin Shigen
da Zulfa data Dauko musu bakin ciki kamar ya kashe Mama Sahura Inna Rukkayyah ce
kadai Allah ke Rike da ita ta samu ta Aurar Da Hamdiya anan garin kano Ummu ce ke
gabanta yanzu itace kedan Taimakonsu itama babu komai sai godiyar Allah,Bello ne
kadai yazo gaisuwar mutuwar Abba Kabiru sai Alokacin yaji azuciyarsa ya yafe musu
ko ba komai sunga Hukuncin Allah Tunda agidan Duniya Shiyasa wani lokacin da gwara
ka bayyyana kan ka a gaban Hukuma ta yankema Hukunci,da ka zauna Hukuncin Allah ya
Faru dakai tun agidan Duniya Haka Abba garba ke kuka yana Rokan Gafaransa,Kasim
kuwa Duk yagama lalacewa yana Zaune Bisa Wheel chair din da Bello ya tashi
akai,Yarsa kuwa Fauziya da Kudiran Allah ta Rayu ammh fa cikin kaskastacciyar
Rayuwa, Rayuwa kenan nan yake Shaida musu shi ya siya Ragowan kamfanin mahaifinsu
Dake Lagos wanda yanzu haka ya na nan yana aiki ta hannun manajan mahaifinsu Mr
James,sunyi matukar mamaki Abun da kuma ya basu mamaki Shikanshi ya muktar ya
Jinjina mai kanin nashi sosai inda yace"Yaya bazamu bari...Komai na mahaifinmu ya
kare ba...Zamu ji Dadin in muka Tsira Dako Da Abu Dayane.."Rumgume juna sukayi suna
kukan Rashin Iyayensu.

Ba Dadewa da mutuwar Abba kabiru,Gidan da ya Ragema Abba garba cikin Dare aka tashi
da gobara Dakyar suka Fita sai dai Zulfa ce dake cikin Daki ta kone sosai Asibiti
aka kaita kwanta Biyu tace ga garinku nan Gidan kuma ko Tsinke ba"a Fitar ba komai
ya gama konewa Wanda ba wanda yasan Daga ina gobarar da take,Mama Sahura tayi kuka
kamar ranta zai Fita,Komai ya kare yar nata kuma Allah yayi ikonsa da ciki
ajikinta karshenta dai Kauye suka koma Wato Jikamshi dangi Duk sun kare Gidansu na
baya wanda yagama Zubewa suka samu Daki Daya Hashim ya tallafa musu suka gyara
wajen zama saboda shima bashi da wajen da zai ijiyesu sakamakon Shima an ragemai
matsayi acampany Dayake aiki Ya muktar kuma Bello yahanashi basu Taimako Yace ya
kyalesu bazai iya karesu ba Hakkin Rai ne da kuma hakkin Dukiyar marayu da suka ci
bazai barsu ba.

Aisha maiduguri Tuni tayi Aurenta agarin maiduguri wani Dan"uwanta ta Aura,dan
kasuwa ne a kano yake kasuwanci yadaukota suka dawo kano inda yayi gida,Yariga
yagama sanin labarin Abunda ya Faru da Aisha Tun Farko,sai bayan Rasuwar
Mahaifiyarta ne tayi Auren ya"yanta biyu yanzu Saboda Mijinta yana da Fahimta yasa
suke zuwa Har Abuja ganin Fauziya Suna mata alheri Aisha tayi kuka kukan Nadamar
Rayuwarta ta baya da yadda Rayuwar yarta ya kasance,Yayanta ya riga yayi Rantsuwa
Aisha bazata Rike Fauziya ba,Dangin Ubanta zasu Riketa Kasim kuwa yana kuka Yana
Rokon Aisha gafara domin yana da Tattabacin Harda Hakkinta ya kamashi,Me zatace
banda ta yafemai ko ahaka Kasim ya Tsaya Allah ya nuna mai Isharsa Zainab Alhaji
isa ma Tuni tayi Aurenta Kasim dai yana Zaune yana Girban Abunda ya Shuka In ya
Tuna Rayuwarsa sai yaji da ace Allah zai bashi dama daya Sauya Rayuwarsa ya dawo
Nagari,sai dai kuma kash Lokaci ya Riga ya kuramai.

Danaji labari sai da naji ba Dadi acikin Zuciyata ina Addu"ar Allah ya Rabamu da
Cin Dukiyar maraya da kuma aikata Abunda zai zo ya dinga bibiyar alhalinmu Ameen.

Ayanzu haka na kara Haihuwan Mai sunana Wato Aneesa kenan muna Kiranta Anee,sai
kuma mai sunan Daada muna Kiranta Daadan,cikin Shekaru uku na haifesu ni kaina na
san na Taka gwarne,B.kaita ta haihu namiji Hakama Raihana Sun haifi Little
Aneesa,Sanah ma tuni har anyi Bikinta ta tare agidan mijinta Muhammed Amin kuwa
yana Wajen Anty Rahila achan aka sakashi a makarata mukuma muna New york nida
mijina da Ya"yana Lokacin har na kamallah karatuna ina Service ne.

*****
Ina cikin kichen da misalin karfe 7am na safe cikin kayan barcina Riga da wando
masu Taushi ina Hadamana kalaci sakamakon yau Weeked ne Dagani har Mr Bello muna
gida

Ina cikin Soyamana Fanke dama ina zuwa da abubuwan amfanina in mukaje gida Nageria
naji Kukan Daada Da hanzari na Fito Ina Tambayan meke Faruwa,Ganin Anee tana Dariya
Dauke da Choculate din da na bama Little Daada Dake zaune bisa kekenta na zama na
gane Dalilin kukan ban tsaya bata Lokaci ba na isa kusa da Anee na make mata kai
ina Fadin"me nagaya miki Don kaniyarki..?

Nafada ina jan kunnata,Baki ta bare,Ban tsaya Sauraranta ba na kwace mintin bakinta
ina Fadin"Muguwa kawai...katuwar banza,wacce batasan kanwarta ba Wlh in nakara jin
kukanta na Fito sai na lahira yafiki jin Dadi.."Nafada ina Turata baya ta Saka kuka
kiris sai ta Fada Jikin Babanta wanda ya Sauko Daga sama yana sanye cikin Kayan
Barci na pjms Masu Ruwan Toka,Yayi kyau ya kara kiba kamar ba Mr Bello da alama
yana kara jin Dadi Sosai.

Riko Anne yayi wacce ke kuka Harda majina kamar wacce ake yankawa yana Fadin'"Me
kuma tayi Tun safe kin Fara zaluntarmin ya..? Yafada yana Sharemata hawaye Ko
kallonsu banyi ba na Duka ina lallaban littale Daaada na saka mata mintin Cikin
bakinta kafin na mike ina Fadin"Dukan Min y"a tayi kajama yarka kunni Wlh in tace
mugunta ce Dabi"arta zata sha Wuya ahannuna.."Nafada ina Huci Saboda Rashin ji
Aneesa yafara isata wlh yarinya kamar bugun jinnu.

Mirmishi yayi yana Kara Rumgume Anee yana Fadin"Koma miye dai Kar a takura
mana...Ai gado tayi.."Ina kallonsa nace" gadon wa...?gira ya Dagamin yana yar
Dariya Mirmishi nayi kawai na koma kichen ina Ma iyayena Addu"a acikin Zuciyata
saboda indai ko Hakane sun shaa fama dani sosai.

Ina cikin Juya Fanken Dake cikin Mai naji Hannunsa bisa cikina ya Rumgume ni ta
baya ajiyar zuciya na Sauke lokaci Daya ya saka kansa zuwa wuyana yana Sumbata ta
dan zillewa nayi yayi Saurin Riko hannuna yana Rikewa Lokaci Daya muna juya fanken
atare Cikin Sanyin Murya yake Fadin"Hausawa fa sunce magaji mafiyi..Anee gabadaya
kece sak daga kamaninku zuwa Hallayanku...So ki godemana yadda muka Wahala
akanki.."Ban yi mgana ba illah Dariya Da mirmishi dana saki Lokaci Daya ..

Tare muka gama Kwashe Fanken Cikin mai cikin Sauri na kashe gas din najashi wajen
fridge ina Fadin"Me kace...? Waro ido yayi yana Fadin"Banyi mgana ba Madam
Aneesa.."Dariya na saka kafin na Rike Kumatunsa ina Fadin"Na yarda Anee duk Kinjina
ta Dauko..Ashe haka su ya Ali keji lokacin ina yarinya...Lalle..."Dariya yayi yana
Riko kuguna cikin Sanyin Murya yace"Nima yakamata kigodemin nima kin bani wahala
musamman makaratanmu ta Kwatar kwatashi.."Kirjinsa na Fada ina Fadin"Godiya kake
so..? Kai ya Gyadamin,Dagowa nayi ina kallonsa kafim nace"Godiyarka ba irin tasu
bace ..Kai naka na musamman ne.."Na fada Lokaci Daya ina sakarmai kiss akumatu
kafin na Dago ina Fadin"Dis one is for my Uncle Mr Bello muhammed Jikamshi..'Na
kara sakarmai wani a gefen kumatun ina Fadin"Dis one is for my Husband..."Na
karshen na Sumbaci bakinsa mai Tsawo lafin na Dago ina Fadin"Dis one is for my
B.love...Tanque For u love,Support and care...And a very big thank to u for been
Thier for me...I love u so much..."Nafada ina fadawa kirjinsa na kamkamesa ganin
kuka na neman kwacemin Kara kamkameni yayi yana Fadin"Thanks so much my
Anee...Kedin ta musammance ina matukar sonki..."Yafada yana Sumbatar Wuyana cikin
Fitan hayyaci na Dago kaina na Hade bakinmu waje Daya Cikin kwarewa muke Sumbatar
juna Lokaci Daya muna Shafa Sasaan Jikin Juna,Dagani yayi sama na makale acikin
Jikinsa muna Sumbatar juna,Kan Fridge din ya Dorani yana Salube rigar barcin Dake
Jikina Nonuwana suka bayyana ya Saki bakina yana kallona cikin Fitar hayyaci
yace"Nasha my Anee...?

Lum nayi da ido banyi Mgna ba na Tura kanshi ina Sakin Siririya kara Kamar wani
karamin yaro yashiga Sarrafa Breats dina yana Shan Daya,gudan kuma yana wasa Dashi
sai da ya Dauki mintina kafin ya Dago yana layin Ido yace"Na....go...de...."

"Nima anan zan cema masu karatu Nima NA...GO...DE..."

*TAMMAT BIHAMDULLAH..*

*Alhamdulillah..Godiya tabbata ga Allah (SWA)daya bani ikon Farawa Wannan Littafin


cikin Aminci da yardansa,gashi kuma yau Allah yayi ikonsa na kamallah muku shi
hakika Allah ne Abun godiya Salati kuma Aminci ya Tabbata ga Shugaban Hallitun
Duniya Annabi Muhammed (SAW) Tsira kuma da Aminci suka Tabbata ga Ahalayansa da
Sahabbansa Ameen...Fatana zaku Dauki Abunda ke Amfani cikin Wannan Labarin nawa ku
watsar da mara amfani,ya kuma bamu ikon Daukan Darasin da muka karanta Kuskuran
dake ciki kuma Allah ya yafemin ladan dake ciki kuma Allah ya Rabamana dani daku
gabadaya Ameen*

_Godiyata ta mussaman ga Masoyanmu wadanda suka Siya littafanmu,mun gode Sosai


Allah ya saka da alheri...Allah ya kuma ya bar zumunci Ameen ya Allah bakina yayi
kadan wajen Nuna muku kalmar Godiyata Sai dai nayi Fatan Allah ya biyaku da gidan
Ajannah Firdausi,godiya ta mussaman ga Masoyana na nesa Dana Kusa,godiya ta
mussaman ga Malamai na marubuta da kawayena da yan'uwa ina godiya ga Kwarin
gwiwanku...Allah yayi albarka ya kuma kara girma_

Fatan alheri....Fatan sai mun sake Haduwa cikin Sabon Novel din da zamu Rubuta muku
Nida Sisinah Aisha alto fatan bazaku bamu kunya ba zaku nuna mana kauna wajen
Rububin Siyan Sabon labarinmu wanda zai zo nan bada Dadewa ba Mungode

Daga karshe zan miki godiya ke mai Hannun Bera ko kuma masu hannayen beraye da kuke
ta Sharing din wannan Novel din Into groups groups...Bazan ce miki komai sai godiya
Allah ya saka miki da Abunda kikamin Sai dai kuma kisani akwai Ranar Tsayuwa Gaban
Allah Ranar da Gabbai ma bazasuyi mgana ba Aranar zaki biyani Dukkan hakkin da kika
Dauka nawa Dake da wadanda suka karanta basu Biya ba...

*Anitha...*
*Shakira..*
*Janafty..*
*Jamila umar...*
*intelligent writer's asso...*
*20/7/2020..*

You might also like

pFad - Phonifier reborn

Pfad - The Proxy pFad of © 2024 Garber Painting. All rights reserved.

Note: This service is not intended for secure transactions such as banking, social media, email, or purchasing. Use at your own risk. We assume no liability whatsoever for broken pages.


Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy