Kwai Cikin Kaya Book 2 CMPLT

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 375

Typing

ƘWAI cikin ƘAYA!!


Bilyn Abdull ce
Assalamu alaikum, barkanku da wannan lokaci, barkanmu da sake dawowa filin daga,
insha ALLAHU zan cigaba da littafin ƘWAI CIKIN ƘAYA kamar yanda na fara, inafatan
haɗin kai daga gareku, haɗin kan kuwa shine tsaftataccen Comments da zai iya
zaburar dani akan abinda nake rubutawa, masu ɗaukar littafi su ɗaura a youtobe wlhy
wlhy na rantse duk wanda ya ɗauramin ƙwai cikin ƙaya a youtobe kar yay kuka dani
akan matakin da zan ɗauka yay kuka da kansa. Masu cewa kuma na maida littafin na
kuɗi kudaina yimin ƙarya, inda naso hakan da tun a 1 zance na kuɗine. Masoya kumuje
zuwa, yanzu za'a fara wasan .
BOOK TWO
(1)
............Kowa yana cike da murnar dawowar aunty Shahudah a gidan amma banda ni,
ba komai ya jawo hakanba kuwa sai irin tarbar dana samu daga gareta bayan dawowata
aiki a randa ta dawo.
Cikin ɗokin ganinta da kewa na nufeta, amma saita kalleni cikin wani yanayi na
wulaƙanci da ƙyama kamar yanda ta sabamin a baya, daga ƙarshe ta koma dariyar
aikina. Hakan ba ƙaramin ciwo yayminba, musamman yanda naga harsu Mom sun biye mata
suma suna tayata dariyar. Daurewa nai nima na tayasu, dan na ɗaukama kaina
alƙawarin insha ALLAHU sun daina ganin raunina a yanzu. Sai da muka gama dariyar
sannan na nufi ɗakina nabarsu, su Aunty Aamilah na bata labarin yanda akai nazama
dss a yanzu.
Ina shiga ɗakina na faɗa saman gado na fashe da kuka, tabbas wulaƙanci bashida ƙyau
sam a rayuwa, ƙasƙanci ga mutum abune mai muni, amma a wannan duniyar babu abinda
mutane suke alfahari dashi kamar ƙasƙanta ɗan uwansu musulmi.
“Sai kaga mai dukiya yana ƙasƙanta talaka koda da magana ne, mai ilimi na ƙasƙanta
marashi, mai mulki na ƙasƙanta mabiyansa, miji na ƙasƙanta iyalansa, ɗan uwa na
ƙasƙanta na ƙasa dashi. koyaya mutum yafi wani saikaga yana hura hanci wajen ganin
yayi tozarci ga wanda bai kaisaba, kaicon mutane da wannan ɗabi'a, kamanta ALLAHN
daya baka shima bai manta da shiba, sannan badan ka fisaba ya baka shi ya hanashi,
ikonsane wannan yabama wani ilimi yayi wani jahili, ya bama wani dukiya yayi wani
talaka, ya bama wani haihuwa yayi wani babu ɗa, ya bama wani mulki yayi wani
mabiyi, ya bama wani lafiya yayi wani mara lafiya, kowa a rayuwa akwai jarabawarsa,
kaine wane bashike nuna kafi kowa ba, kai ka samu kaza ko kake da kaza bashike nuna
ALLAH yafi sonka ba, nima ALLAH yana sona, kuma ina sake gode masa da yanda yayini
aunty Shahudah.......”
Tun daga wannan ranar na sake jabaya ga kowa da komai na gidan, Dad dama bai
dawoba, hakama Yah Qaseem yayi tafiya tun washe garin dawowar aunty Shahudah gidan.
ko a wajen aiki bani da wata walwala, Ummie da wasu abokan aikina sai suka danganta
rashin walwalar tawa da kewar Yah Qaseem da bayanan, dan zuwa yanzun mutane da yawa
sun san alaƙar dake a tsakanina dashi.
Ni kuma a ɓangarena ba damuwar rashin yah Qaseem bane da lamarin gidanmu kawai
kecin raina, akwai wani abu daban danaketa ƙoƙarin tureshi a raina, dan bana fatan
gaskata zancen zuciyata koda da wasa kuwa.
★★★★★★★★
Yau data kasance juma'a dai-dai da dawowar aunty Shahudah da kwanaki huɗu Dad shima
ya dawo, kowa yay murnar dawowarsa tamkar yanda muka saba, ya kuma samu tarba daga
matarsa harma da Aunty Shahudah dake ganin wannan dawowar tatace. Nidai ina daga
baya-baya dukda jana a jiki da Dad keyi, dan motsi kaɗan ya sako sunana a cikin
zancensa, hakan na kula baƙaramin sosa zuciyar Aunty Shahudah ya keyi ba, hakama
Mom. Dana kula abin zaiyi tsamari saina zare jikina na gudu ɗaki, dama dai muna
zaune ne muna cin abincin dare.
Ban sake yunƙurin fitowaba kuwa har safiyar washe gari domin nima naji a raina
yakamata na basu waje su gana da mahaifansu. duk da kasancewar asabar ce babu aiki
ban iya komawa barci ba, dan narigada na saba yanzu da yanayin tashin sassafe. Ina
zaune akan abin sallah tun bayan idar da sallar asubahi ban tashiba, na lazimci
azkar nai karatun Qur'ani, rashin abunyi ya sakani tashi nahau gyaran ɗakina, hakan
sai ya jani tsayin lokaci har kusan tara da wasu mintuna.
Sama-sama nake jiyo hayaniya kamar na kuka, kukan kuma yaymin kama da muryar Mom.
Nai azamar ajiye tawul ɗin dana ɗauka zan shiga wanka na fita. Sosai gabana ya faɗi
saboda cin karo da Mom dake kuka iyakar ƙarfinta, Dad na riƙeta, daƙyar na iya haɗa
maganganunsu, daga ƙarshe na fahimci ƙanin Mom ɗine ALLAH yayma rasuwa mai suna
Usman, tabbas naji suna yawan faɗar sunan Uncle Usman, sai dai ban sanshiba, ban
taɓa ganinsaba, dan duk zamana a gidan ban taɓa zuwa gidansu mom ɗinba, bankuma
cika ganin ƴan uwanta suna zuwaba, kowa dai yasan halin wasu ƴan bokon nan da
aƙidar rashin son takura.
Nima dai tausayin Mom ya sakani bin sahun masu sharar hawaye, nan dai Dad ya cigaba
da lallaɓata, kafin yajata sama, muma yace duk mu shirya domin tafiya can gidan.
Hakanne ya saka kowa nufar ɗakinsa mu duka.
______________________________
A daren jiya juma'a misalin ƙarfe sha biyu da wasu mintuna mummunan labari ya iso
gidansu Jawaad, cewar Uncle Usman ya samu haɗarin mota a hanyarsa ta dawowa daga
tafiyar da yayi ta kwanaki biyu.
Lallai wannan gida sun fuskanci tashin hankali na bazata, dan bayan mahaifin Jawaad
basu ƙara rasa ko ɗaya a cikinsuba, kaf ƴaƴan malam Yusif Abdul-aziz ne kawai ALLAH
yayma rasuwa. Saiko shi malam Yusif ɗin da matarsa ɗaya sai mama maryam, idan ka
cire waɗanan huɗun sauran duk sunada ransu, saima yaɗuwa da suka sake yi saboda
haihuwar jikoki harma da tattaɓa kunne.
Ruɗanin da mama Atika ta shigane ya sakata yanke jiki ta faɗi, dan abune da
tunaninsu bai taɓa kawo musuba anan kusa duk da sunsan mutuwa tabbacice ga duk mai
rai, ba Uncle Usman ba ko ita kanta data tsufa sosai bata tuna mutuwar zata iya
ɗaukarta a yanzu balle shi da ayanzune ake ƙara shiryama duniyar filin zama.
Lokacin da gidansu Jawaad ke cikin wannan ruɗanin shi yanacan suna gumurzu da wasu
gungun ƴan ta'adda da suke fako tun kusan sati uku da suka shige, sai a yaune ALLAH
ya basu nasarar yin fito na fito dasu, sun sami nasarar kama wasu a cikinsu,
yayinda wasu suka gudu.
Kusan ƙarfe huɗu na dare suka iso station ɗinsu da waɗanda suka cafko, sunyi tiɓis
da gajiya, ga yunwa dake cin hanjinsu ta bala'i ma kuwa, sai dai jarumtarsu da
juriya mai haɗe da trianing ɗin da suka gogu a ciki duk ya ɓoye gazawarsu. Rose
cema dai kawai ta kasa juriyar kasancewar ƙarfin zuciyar mace dana namiji ba
ɗayaba, dukda itama ta cancanci a kirata jarumar kuwa, Jawaad ma baiso akai aikin
da itaba, amma ta matsa akan sai taje, badan yasoba ya barta ta bisu.
A station ɗin suka ƙarasa kwanan, washe gari safiyar asabar ana idar da sallar
asuba Jawaad ya kira gimba akan yazo ya ɗaukesa. Yanda yaji muryan gimban ne ya
bashi mamaki, cikin yanayin gizagonsa yake jefa masa tambayar lafiya?.
Sanin halinsa baya son ɓoye-ɓoye a magana ya saka Gimba faɗa masa gaskiyar tashin
hankalin da ake ciki a gidan nasu.
Dukda halin da yake ciki da matsalolin dangin mahaifin nasa hakan bai hanashi shiga
ƙololuwar tashin hankaliba, a take ya birkicema su Jabeer, waɗanda suma jin rasuwar
tai bala'in sakasu a ruɗani. Basu wani ɓata lokaciba suka nufi gidansu Jawaad ɗin
kai tsaye, duk da halin gajiya da buƙatar hutun da suke a ciki. Sun iso gidan ƙarfe
kusan bakwai da wasu ƴan mintuna, hankalin Jawaad ya sake tashi sosai ganin halin
da ahalinsa ke a ciki, tuni ya manta da gajiyar dake tattare dashi.
Bai zaunaba su Uncle Nasir suka jashi zuwa asibitin da gawar Uncle Usman take domin
su amso, abinda yasa ba'aje tun jiyaba saboda ba'a nan cikin gari bane, inda ya
baro yafi kusa da inda yay haɗarin, shiyyasa aka maidashi asibitin can garin.
★★★★★★★
Ƙarfe goma da wasu mintuna muka iso gidansu Mom, katafaren gida na alfarma da ƙawa,
dukda cikin tashin hankalin mutuwa mukazo hakan bai hanani mamaki da jinjina dukiya
irinta wannan ahaliba, lallai dolene su aunty Shahudah suyi wulaƙanci yanda sukeso,
kaga gida tamkar ba hannune ya ginashiba, harabar gidan kawai naganimafa kenan, sai
mutanen gidan da zakaima kallo ɗaya ka fahinci ƴan bokone na haƙiƙa tun zamanin da
boko keda tsada da daraja kuwa......
Ina cikin wannan tunanin ne nafara jiyo ƙarfin koke-koke na ƙaruwa, babu shiri na
dawo hayyacina, a sannanne na lura ashe an iso da gawar mamacinne.
Har ciki sosai Ambulance ɗin dake ɗauke da gawar ta shigo, ta tsaya dai-dai sashen
danaji wasu na ambata da sashen mama Atika mahaifiyarsu Mom. Zuciyata tai masifar
harbawa saboda ganin wanda ya fito daga Ambulance ɗin.
Cikin tsagwaron mamaki na furta “Boss kuma anan?” akan laɓɓana, kamar yanda nakejin
zuciyata aduk sanda ta samu kusanci dashi yanzunma bata canja zaniba, dole na shiga
karanto addu'a gudun kar nayi abinda zai jawo hankalin mutane a kaina.
Nayi nisa a tunanin da har aka fidda gawar ban saniba, saida suna gab da shiga
sashin ne nakai idanuna kansu tare da sauraren koke-koken mutane, su biyune kawai
ke ɗauke da gawar a mankara, tana lulluɓe da farin ƙyalle da yay face-face da jini,
alamar dai mamacin ya bugu sakamakon Accident ɗin da yayi, nantake sai zuciyata tai
rauni saboda tunowa da mutuwar nawa mahaifin, sai kawai na durƙushe a wajen na
fashe da kuka mai cin rai da zuciya.
Isowar gawarce ta saka gidan ya kuma cika sosai, koke-koken da akeyi ya sake
ƙaruwa, ban kuma ganinsaba kuma har aka sake fitowa da gawar kusan sha biyu na
safe, da alama dai yanzu an masa sutura za'a miƙashi gidansa na gaskiyane. Wani da
nake ƙyautata zaton ɗansane ya rugo da gudu ya riƙe mankarar da aka ɗakko yana kuka
da roƙon su ajiye masa Dadynsa, yarone da bazai gaza shekaru sha uku ba a duniya,
sai ƴanmata guda biyu da zasu iya kawai 23 da 20 suma sukazo suka riƙe. Hakan ya
kuma tada hankalin jama'a, ni kaina sunyi masifar bani tausayi, suma kenan da suke
da gatan dangi dana jin daɗin rayuwa, na tuna sanda baba ya tafi ya barni, har aka
binnesa ma ni bansan ina nawa hankalin ya keba.
Na share ƙwallar dake gudu bisa kumatuna, dai-dai isowarsa, wajen da alama yanzune
ya fito, shine ya janye yaron ya rungumesa a jikinsa yana bubbuga bayansa, hakan ya
saka ƴan matanma sakin mankarar suka durƙushe a wajen suna kuka. Bai saki yaronba
har saida aka fita da gawar, ya shafa kansa yana ɗago fuskarsa, babu wanda yasan
miya faɗama yaron, amma kowa ya kula magana yay masa kafin ya sakesa ya fice shima
zuwa waje inda za'a sallacesa.
Tashin hankalin da ake cikine yasa ban samu damar tunanin alaƙar gidan da boss ba
sam, bankuma sake ganinsaba, sai dai ganin nasa da nayi yana nan daram a zuciyata,
dan kwanaki kusan shida kenan ban gansaba ko'a office, tun fitar da sukai ranar sai
yaune na ganshi. A mamakina sai naji raina sakayau, bakamar yanda na tsinci kaina
cikin ƙunci ba a kwanakinan.
★★★★★★
Tun bayan zuwanmu gidan ban sake sanya ƴan gidanmu a idonaba, har zuwa yanzu da
aketa hada-hadar sallar azhar da cin abinci, garama dad bayan sun dawo daga binne
gawar ya shigo cikin gidan shi da wasu manyan mutane sunyi gaisuwa, daga haka ban
sake saka ko ɗaya a cikinsu a idanunaba.
Mutane nata shiga sassan gidan domin gabatar da salla, sai dai ni narasa ina zan
dosa koda na tashi, waɗanda nazo dominsu ban sake ganinsuba, ina zan shiga nikan
nace zanyi salla? Tunda babu wanda ya sanni babu kuma wanda na sani.
Ina nan zaune ina saƙa mai fishsheni a zuciya budurwar dake zaune a kusa dani ta
miƙomin jakkarta da waya akan na riƙe mata tana zuwa, kamar zanyi magana sai kuma
na amsa ina maida mata murtanin murmushin da takemin, ina zaune a wajen ban motsaba
nai uban tagumi harta dawo.
Na miƙa mata kayanta, ta amsa tana min godiya, harta tafi sai kuma ta dawo da baya
idonta a kaina.
“Ƴar uwa kozaki taso muje muyi sallane? Naga kowa na harama amma ke koma motsi
bakiyba, ko dai kina hutune?”.
Murmushin yaƙe naimata, sai dai ban motsaba, nace, “Karki damu zan nema waɗanda
mukazo tare sai nayi a wajensu”.
Tai ɗan shiru tana kallona, kamar bazata tankaba, dan harna fara murnar ta barni,
sai na tsinkayi muryarta tana faɗin, “Yanda mutane ke cike a gidannan kafin ki
ganosun ai kin wahala, sannan duk inda zakiy salla a gidannan yau bazai kai
nutsuwar inda zamujeba, dan sashen yaya ne kawai nasan babu mutane, indai ba kina
tsoron karna saidaki bane”.
Ta bani dariya, amma sai banyiba saboda yanayin da ake ciki, sai kawai na miƙe
batare danace komaiba, dan na lura akwaita da surutu.
Tun shigowarmu sashen na yarda da zancenta, dankuwa tsit yake babu wata hayaniya
anan, tamjar ba cikin gidan yakeba. Sai wani daddaɗan ƙamshi daya shige mini hanci,
batare dana shiryaba na shaƙa na haɗiyeshi cikin maƙoshina, karon farko a rayuwata
da naga falon da yafi na gidan Dad ƙyau da tsari, ada tunanina yana bani babu gidan
da yakai na Dad haɗuwa da tsaruwar kayan alatu, dan dukkan gidajen iyayen su Ummie
basu kai na Dad ba, amma a yau dana tsinci kaina cikin wannan aljannar duniyar duk
sai na raina wancan alfaharin nawa, yanda aka ƙawata matattakalar benen dake falon
kawai abar kalloce ga mai kallo duk wayewarsa kuwa. Ban gama bama idona abinciba
budurwar taja hannuna zuwa wani ɗaki, mun iske mutum uku suna salla, sai ɗaya data
fito daga bayi da alama alwalar itama tayo, sai wata kwance a kan gadon dake ɗakin
da yara biyu suna kallon waya. Duk suka zubomin ido na rashin sani, wadda ta fito
daga bayice tace, “Wai ina kikajene haka Nabeelah? an aika Ammar ya kiraki amma
yace bai gankiba”.
Hannuna ta saki tana saɓule jakkarta dake a kafaɗa, “Babu inda najefa Aunty
Hanifah, ina can jikin sashen Uncle Sulaiman zaune, nima yanzu saida na leƙo naga
kuna nan sannan ai na taho”.
Batace mata komaiba, hakanne ya sakani gaisheta dan naga babbace ta girmeni, na
juya ga wadda ke a saman gadon tare da yara itama zan gaisheta sai tai saurin
gaisheni. Murmushi kawai nayi, dan ita zan iya girmarta, suma yaran sai suka
gaidani, na amsa musu da kulawa ina tambayar sunayensu. Namijin yace Ammar, macen
kuma Islam. Yaran sun birgeni, gasu masu ƙyau. Wadda muka shigo tare da aka kira da
Nabeelah ce tace min na shiga bayin nayo alwala, cikin tsokana take faɗin “Karnayi
abin kunya gashi bansan sunan ƙawar tawabama”.
Ƴar dariya nai babu shiri, ina ƙoƙarin shigewa nace mata sunana Bilkisu. A tare
naga duk sun kalleni suna ɗora hannu a bakunansu, hakama biyu a masu sallar da suka
idar suma suka juyo suna kallona. Yanda naɗanyi diri-diri na alamar shakkune ya
saka ɗaya a cikin waɗanda suka idar da sallar babbar mace tai murmushi da cewa “Mai
babban sunace ashe”. Numfashi na sauke a hankali kafin na gaisheta cikin risinawa,
ta amsamin tana sake faɗaɗa dara'ar fuskarta, kafin tace naje nai alwalar kar
lokaci ya ƙure. Shigewa nayi bayin nima da tunanin ko sunan waye nasu Bilkisun?
Daga gani kam dai suna girmama mai sunan sosai.
Ina fitowa Nabeelah ta shiga, suma duk sun tashi daga abin sallar alamar sun bamu
waje, sai wadda muka iske tayo alwala kawaice ke salla a wajen, na gaida sauran
biyun da bamu gaisaba suma sannan na kabbara sallata.
Bayan mun idar da sallar a cikinsu babu wanda ya tambayeni game dani, sai dai
sunata ƙoƙarin sakoni cikin hirarsu wadda duk ta karkata ga mai irin sunana danaji
manyan na ambata da Yaya Bilki, yaran kuma na kiranta Mah-mah Yanda suke hira
akanta cikin damuwa da kewane ya sakani tunanin ko bata da raine? Bani da mai bani
wannan amsar, dan haka na haɗiye abina cikin rai ina cigaba da saurarensu....
Kusan mintuna talatin ina sauraren hirarsu mai cike da birgewar kasancewarsu ahali
ɗaya, kafin na miƙe domin tafiya, dan ya kamata naje na binciki inda su Mom suke
koda su basu damu da nemanaba.
Duk kallona sukai cike da alamar tambaya.
Murmushi nayi, nace, “Zanjene kar abokan tafiyata suyita nemana”.
Suma duk murmushin sukaimin, Nabeelah ta miƙomin wayarta tana faɗin, “To sakamin
Number ki muke zuminci, danni dai nayi ƙawa daga yau”. Ban musaba na amsa wayar
tata fuskata har lokacin da murmushi, na saka mata Number ta ina miƙa mata wayar,
wadda naji suna kira Aunty Batool tace, “Lallai kin jajubarma kanki kuma Ummien mu,
dan shegen surutun Nabeelah takai a guji ƙawance da ita, gaki keman daga gani
bakida yawan magana”.
Sanin dani take yasani faɗin, “Aunty ai sunfi daɗin ƙawance irinsu Nabeelah”.
Atake kowa ya shiga faɗin a'a-a'a, yayinda Nabeelah keta ƙoƙarin kare kanta, niko
ina musu dariya. Godiya na sake musu kafin nai musu sallama.
Zuciyata tai wani irin harbawa lokacin da akai knocking ƙofar ɗakin tare da sallama
cikin wata irin sassanyar murya dake nuna mai ita yana a matuƙar gajiye, tattare da
tsagwaron damuwa. Akusan tare suka amsa, nikuma na janye hannuna dana ɗora akan
mariƙin ƙofar cike da fargaba, ban gama tattara fahimtata waje gudaba aka turo
ƙofar aka shigo, kaɗan ya rage ya bugeni, nai saurin ja baya kaɗan dan na bashi
hanya sosai.
Idanunane suka fara sauka akan ƙyaƙyƙyawar ƙafar da baƙin wandon jeans ya sake
haskawa, jijjigar da zuciyata keyine ya dasamin tsoron yarda da hasashena, dan haka
na kasa ɗago idona naga wanene? Dukda ƙamshin turarensa ya nema saka zuciyata faso
ƙirjina ta fito......
Ganin yaƙi shigewa ya bani hanyane ya sakani ɗago idanuna a hankali nakai dubana
gareshi, a lokaci ɗaya idanunmu suka shige na juna saboda shima dai-dai ya kalleni.
Naɗan sake ja da baya na alamun mamakin sake ganinsa anan, amma shi a mamakina sai
naga ya janye nasa idanun babu wani alamar mamakin ganina da ya nuna.
Yanda naji su Nabeelah na rige-rigen gaishesane ya sakani aro jarumta nima nabi
layinsu na gaidashi, sau ɗaya ya amsa mana tare da amsa ta'azziyar da mukai masa ya
ƙarasa ga iyayensu Nabeelah, hakanne ni kuma ya bani damar saurin ficewa cike da
sassarfa daga ɗakin..........
ALLAH ka gafartama iyayenmu .
4 hrs · Public
Save · More
36Bilqeesa Ibraheem Bilyn Abdull Ce:
Alhmdllh inama kowa fatan alkairi, nakumaji daɗin wannan tarba, naso ace zan iya
jurewa na biku ɗai-ɗai na amsama kowa Comments ɗinsa, sai dai nace kuyi haƙuri,
kamar yanda matsalan ido ta dakatar dani da typing dolene yanzuma na ringa
lallaɓawa saboda kunada ɗunbin yawa, akwai group insha ALLAHU da aka buɗe a shafin
manhajar Telegram, masu amfani da wannan shafi su maza su garzaya idan suna buƙata,
domin canne zai zama dandalin tattaunawa akan littfin ƙwai cikin ƙaya da sada
zuminci, duk mai karatu yana buƙatar dandali na tattaunawa akan littafi, dan da
yawanmu hakan na bamu nishaɗi da sake fahimtar da mu abinda bamu fahimtaba, kuma
yana ƙarama writer ƙarfin gwiwar typing koda batai niyyar hakanba, ku maza kar a
baku labari. Zakuna samuna koda yaushe a can domin ku tabbatar ina tare daku,
masoyan bily kuma na isar da saƙonku gareta akan ta daina tsoron jay😂, masoyan
Shahudah tana miƙo muku gaisuwa itama🤓.

https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g

Wannan shine link ɗin group namu mai suna MASARAUTAR BILYN ABDULL A manhajar
Telegram😘😘.

..............Koda na fito daga ɗakin saida na huta a falon saboda yanda zuciyata
ke mutsu-mutsu a cikin ƙirjina, ina matuƙar mamakin wannan al'amari dake yawan
faruwa tsakanina da mutumin nan, na kuma rasa wazan tunkara da maganar halin da
nake tsintar kaina akansa kozan samu fashin baƙin saɓanin wanda zuciyata ke kissima
min, nidai nasan ba tsoronsa nakeba, to minene dalili? Wannan amsar nake neman mai
bani.
Gwiwa a sage naja ƙafafuna na fice daga sashen zuwa harabar gidan. Yanzunma
dai ban sami ko ɗaya daga cikin su aunty Aamilah ba, gashi banida Number kowa a
cikinsu. Dole na sake nemar guri na zauna inda babu yawan hayaniyar mutane, sai
jefi-jefi nakan ɗanga sun gittani.

★★★★★

Yanda Jawaad ya nuna halin ko in kula da ganin na Bilkisu bazaka taɓa tunanin
yama santaba, sai dai harta fice daga ɗakin yana kallontane ta wutsiyar ido, acan
ƙasan zuciyarsa na raya masa “Ita kuma miya kawota nan?” sai dai a fili bazaka taɓa
fahimtar komaiba.
Zama yay a saman ƴar dirowar dake farkon shigowa ɗakin, cikin girmamawa ya
gaisa da iyayensa, sukai masa gaisuwar ta'aziyyah tare da jero addu'ar neman gafara
ga mamacin, har suka cigaba da ɗan tattaunawa akan rasuwar wadda ta jasu tunowa da
rasuwar mahaifin Jawaad ɗin shima da ɓatan mahaifiyarsa.
Haɗiyar zuciya kawai Jawaad yake famanyi, amma bakinsa ya kasa furta
komai, daga ƙarshema saiya miƙe yana faɗa musu zaije ya ɗan kwanta, gimba zai kawo
musu abincin da zasu ci.
Basu hanashi tafiyaba, dan yanayinsa ya nuna yana buƙatar hutun sosai.
★..::..★

Sai kusan ƙarfe biyar na hangi Mom suna gaisawa da wasu gungun baƙi da
sukazo musu gaisuwa, da sauri na miƙe na nufeta karta sake ɓacemin, dan matuƙar
gajiya na gaji da zaman ni kaɗai, danma naɗanyi cheating dasu Rebecca ne a group
ɗin da muka buɗe iya mu biyar kawai na rage kaɗaici. Daga gefe na tsaya harta gama
gaisuwa da mutanen suka tafi kafin na ƙaraso gareta, gaidata na farayi a ɗarare,
tunda nasan bani da wata fawa a gareta, amma a mamakina sai naji ta amsa harda
tambayata ina na shiga tun ɗazun bata ganniba? wani sanyi ya ratsa zuciyata,
kasancewata marainiya ina matuƙar buƙatar kulawar mahaifiya koda kaɗanne, rashin
samu kuma na sakani a ƙunci sosai, sai dai ina ƙoƙarin shanyewa ba kowa ke fahimtar
hakanba. Cikin girmamawa na bata amsar tambayarta, saita bani umarni akan muje ciki
naci abinci.

Ban sake sakashi a idonaba har zuwa dare bayan sallar isha'i da muka fito
domin tafiya gida, ƙiri da muzu Aamilah da aunty Shahudah suketa ƙoƙarin zamewa
haɗa tafiya dani, duk da basu fito fili sun faɗaba na fahimci haka da kaina, dan
kafin nagama kimtsawa harsun fice daga sashen na Mama Atika, sai tare muka fito da
Mom, sai muka iske harsun tafi wai tare da Yah Salman.
Banji haushiba, saima murmushi da nayi kawai, driver ne zai tafi da Mom, dan
haka nima su zanbi dole. Mom ta tsaya gaisuwa da wasu mata da suma zasu tafi, ƴan
gayune sosai da kallo ɗaya zakai musu ka fahimci naira ta zauna musu, nidai bayan
na gaishesu jikin mota na koma na

jingina kawai ina kallonsu da mamakin yanda naga Mom ta sake dasu sosai, yanda na
santa da wulaƙanci, koda yake masu iya magana kance wata gaban tafi gaban raini ai.
Zuciyata ta motsa da ƙarfi a cikin ƙirjina, hakan ya saka tsoro ziyartar
raina, koban faɗaba nasan hakan na nufin Dodona ya kusanto wajen koma yana wajen,
zuwa yanzu nafara sabawa da wannan SABON AL'AMARIN namu.
Ilai kuwa ina ɗago idanu akansa na sauke, tsaye yake ɗan nesa damu kaɗan,
hannunsa ɗaya cikin aljihun wando, ɗayan kuma ya riƙe waya dake kunnensa, wadda ke
nuna alamar yana magana da wanine, ɗan taku yake ɗaya biyu cike da nutsuwa da cikar
haiba, ba kayan ɗazun bane a jikinsa, daga wando har rigar jikinsa na yanzu duk
fararene tas, gefe wando na duka ƙafar biyu akwai ratsin dogon zare jaa daga sama
har ƙasa, sai agaban rigar shima anyi rubutu da ja, hasken dake ƙwanyar a tsakar
gidanne ya sani ganin abinda aka rubuta, sai silifas fari shima, sosai kayan sukai
masa ƙyau, har na iya kasa janye idona a kansa dukda wutsilniyar da zuciyata keyi
kuwa.

Haka kawai Jawaad dake waya da Jabeer yaji a jikinsa kallonsa akeyi,
kallon kuma irinna wanda keda kaifin gani da baiwar ƙarfin kwarjinin idanu, duk
yanda yaso basarwa tamkar yanda ya saba hakan sai ya gagara, dole ya fara wulƙita
nasa fararen idanun kozai samu nasarar cafko wannan mayen idon dake neman saukar
masa da gajiya. Karaf kuwa idanunsa suka sauka akanta, shima ƙirjinsa ya motsa
alamar harbawar zuciyarsa. Tabbas yaji a ransa itace ke kallonsa, amma a mamakinsa
sam idanunta da hankalinta basa kansa, karon farko da miskilancin yarinyarnan ya
motsa zuciyarsa, tun ganinsa da ita na farko a airport ya fahimci miskilace ta
bugawa a jarida, kasancewar ALLAH ya azurtashi da ilimin karantar hallayyar ɗan
adam cikin lokaci ƙanƙani, zuwa yanzu mamakin ganinta yabar ransa, dan ya kula
akwai alaƙa tsakaninta da Qaseem.......
“Hello...hello...” Da Jabeer keta ambatane ya sakashi dawowa hayyacinsa, dan
tuni ya saki wayar da suke ya kama sabgar bilkisu, abinda bayayi sam a rayuwarsa
(wato shiga abinda bai shafesa ba), yaja siririn tsaki yana murza goshinsa da
hannunsa daya ciro daga cikin aljihu.
Dai-dai lokacin da Bilkisu ta buɗe gaban mota ta shiga ta zauna, dan Mom
harta shige baya itama.
Wani irin harɗaɗɗen numfashi ya sauke har Jabeer na tambayarsa “ko
lafiya?”.
Gutun tsaki yaja yana yanke wayar batare daya bashi amsaba, yakuma jan wani
tsakin har sau biyu yana takaicin kansa da shiga hurumin da ba nasaba.

___________________________

Washe gari ban biyosuba, dan inama barci suka fice, babu wanda yace a tasoni,
nima koda na tashi kuku ke sanarmin sun tafi banji komaiba a raina saima daɗi,
tunda nasan zuwana bazai ƙara komaiba koya hana, hasalima banason gamuwa da Dodona.
Bayan na karya ɗaki na koma nai wanka, nai shiri cikin doguwar riga ta
atanfa data samu zaunannen ɗinki, bawata kwalliya naiba, nasaka turare sama-sama na
fito bayan na yafa ƙarmin gyale.
Kai tsaye gate na nufa wajen baba maigadi dake zaune shida mai bayin filawar
gidan suna hira, suna ganina suka shiga gaisheni cikin girmamawa, sam banason hakan
da sukemin, dan kuwa niba kowa bace a gidan face maicin alfarma, sannan duk sun
girmeni, baba maigadi ma a haife ya haifeni, shima mai bayin fulawar kobai haifi
kamata ba nasan yanada manyan ƴaƴa.....
“Hajiya fita zakiyine?”.
Baba mai gadi ya katsemin tunanina, kaina na girgiza masa ina murmushi. “A'a baba
ba fita zanyiba, hasalima wajenka nazo muyi magana idan ban takura makaba dan
ALLAH”.
Da sauri yace, “Haba wace takura kuma” yay maganar yana miƙewa da sauri, babu
jimawa sai gashi da farar kujera, ajiyemin yay gefensu alamar na zauna, mai bayin
fulawa kuwa yay mana sallama akan zaije gida yakai cefane.

Sake gaisawa mukai da baba maigadi, yay min ta'aziyyar rasuwar da akayi,
nako amsa masa tare da tambayar lafiyar iyalansa, bayan amsamin da yay muka ɗanyi
shiru, tunani nake ta ina zan fara abinda ya kawoni garesa?. Zuwa wasu ƴan mintuna
sai dabara ta faɗomin, nai murmushi ina sake maida hankalina ga

reshi da kunna voice recorder dan na samu damar kwashe dukkan abinda zamu tattauna
nayi nazari a tsanake a kansu.
“Uhm... Baba dan ALLAH niko wata tambayace dani?”.
Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “ALLAH Yasa na sani hajiya”.
Murmushi naɗan masa, nace, “Insha ALLAHU inada tabbacin kama sani ɗin”.
Baice komaiba sai hankalinsa daya maido kaina baki ɗaya, nima sai na sake
nutsuwa sosai.
“Baba dan ALLAH ko zaka iya tuna ranar da abinnan ya faru da Amina a
gidannan da wanda ba'asan ko waneneba?”.
A bazata maganar tazo masa, dan haka kawai saiya hau tari babu shiri. A
rikice na shiga masa sannu, na jawo ruwan dana fito dashi daga ciki na miƙa masa da
sauri bayan na ɓalle murfin, amsa yay har hannunsa na rawa ya kafa goran a baki ya
ɓaɓɓaka, saida yasha kusan rabi kafin ya sauke, idanunsa harsun kaɗa sunyi jajur,
sai naji tausayinsa ya kamani, koda ya dawo dai-dai shiru nai ban sake masa
tambayarba har tsawon wasu mintuna.
Na sake jeho masa tambayar a karo na biyu, yanzunkam a mamakinawa shiru yay
bai tanka minba, sai dai yanata ƴan kalle-kalle tamkar mai tsoron a ganmu ko wani
ya jimu. Jin bashi da niyyar bani amsa ya sakani kallonsa, a karo na uku na sake
maimaita masa tambayar da sigar kwantar da kai.........
“Ɗi!! Ɗi!!! Ɗi!!...” mukaji horn ɗin mota daga waje, hakanne ya sakashi tashi
da sauri ya nufi gate ɗin, na tabbatar dama hanyar da zai gudu yake nema, sai kawai
na samu kaina da ƙura masa idanu ganin yanda har yanzu jikinsa ke mazarin rawa.
Hancin motar Dad ne ya danno kai cikin gidan, na sauke ajiyar zuciya ina
miƙewa tsaye, saboda tsayawar da driver yayi a saitin da nake zaune, shi kuma Dad
ya sauke glass ɗin ɓangarensa yana mani murmushi.
Nima murmushin nake masa ina miƙewa na nufesa, da hannu yaymin nuni nazo,
dole nabi motar da direba yaja zuwa ciki inda zaiyi fakin.

Tare da Dad muka shige cikin falo yana tambayata miyyasa banbi su Mom ba
can gida?, cikin girmamawa na bashi amsa akan sun wucene ina barci lokacin. Nayi
zaton zaiyi faɗa, amma sai naji kawai yay ƙaramar dariya. Mun yada zango a falon
ƙasa, ya bani Umarnin naje nasa kuku ya haɗa masa abinci mara nauyi yunwa ya keji,
ya fita bai karyabane.
Koda naje kicin ɗin sai ban fitoba na zauna mukayi abu mai sauƙi wa Dad ɗin
ni da kuku, dan zuwa yanzunkam Alhmdllh hannuna yay masifar faɗawa akan girki kala-
kala na zamani, na gargajiya kuwa dama bani da matsala a kansa, innata tarigada
tayi min wannan horon tun ban gama fahimtar muhimmancin girki ga ɗiya mace ba.
Bayan mun kammala nice da kaina na kawoma Dad, lokacin yana waya, na ɗora
tiren bisa tebir ɗin tsakkiyar falon na jasa gabansa, buɗe masa komai nayi tare da
tsiyaya masa ruwa a kofi sannan na koma gefe na zauna, a haka ya faracin abincin
yana cigaba da wayarsa data jashi tsayin lokaci, sai yazam yanacin abincinne kawai
a shiririce. Dan harya kammala wayar baici ko kashi ɗayaba bisa uku, ya ajiye wayar
yana maido hankalinsa gareni, “Taso muci mana ɗiyata”.
“Lah Dad nakane, ni ban daɗema da karyawaba fa”.
Cike da kulawa yacemin, “Da gaske?”.
Na langaɓe kai gefe ina ɗagawa alamar eh. Murmushi yayi ya cigaba dacin
abincinasa yana mani hirar data bani mamaki, dan kuwa akan kasuwancinsane ya
ɗakkomin hira, yana faɗamin alkairi da kullum kamfaninsa ke samu da yanda kuɗaɗe ke
shigo masa babu ƙaƙƙautawa. Banda masha ALLAH da ALLAH ya ƙara sanya albarka babu
abinda nake iya cewa, danni kam dai ban fahimci dalilin mani labarinba, tunda a
ganina ai sirrinsane wannan, ko a cikin ƴaƴa kuwa a ganina sai wanda ka aminta da
amanarsa.
Kamar kuwa ya karanci mike raina, sai cewa yay, “Kinji inata baki labarin
abinda bai shafekiba ko?”.
Murmushin yaƙe naɗanyi ina gyaɗa kaina, shima ya murmusa yana mai kai cokalin
romon farfesun daya ɗobo a bakinsa.
“Karkiji komai a ranki Bilkisu, na yarda da kene kawai shiyyasa, dan na
fahimci keɗin yarinyace mai hankali da tarin nutsuwa, sannan sam baki da yawan
surutu, waɗanan halayyar taki na ƙaramin ƙaunarki sosai”.
Murmushi yanzunkam nayi har haƙorana na bayyana

, nace, “Nagode Daddy”.


Ƙaramar dariya yay yana miƙewa bayan ya ajiye kofin da yasha ruwa, “Kinga bara
naje naɗan kwanta na huta, zuwa yamma saimu tafi gidan rasuwar muma”.
Kaina na jinjina masa kawai, dan nima tuni nake buƙatar keɓancewa, inason yin
nazari akan halinda mai gadi ya shiga akan tambayar danai masa ɗazun kafin zuwansu
Dad daya gaza amsa mani.

Koda Yammar bamuje ko inaba, dan banga Dad ba sai bayan la'asar lokacin da
yah Salim ke dawowa gidan. Harare-hararen da yaketayine ya sakani tashi na barmusu
falon na koma ɗaki.

★..★...:::::...★..★

Washe gari litinin kowa yasan tushen aiki, hakanne ya sakani shiri tun a
farar safiya, lokacin dana fito babu wanda ya fito a mutanen gidan, tea kawai nasha
driver ya ɗaukeni zuwa station ɗinmu kamar yanda a yanzu da Yah Qaseem bayanan
kullum shine ke kaini.

Nayi mamakin rashin ganinsa yauma a office, bayan nasan ya dawo, daga baya
sai nayi tunanin kodan dai rasuwarcan ne da bansan minene alaƙarsa da mamacinba,
dan har yanzu ina mamakin ganinsa a gidan su Mom ɗin, dukda wani sashe na zuciyata
na rayamin shima ɗan uwansune ƙila sunje gaisuwane.
Daga haka ban daɗaba ban ragaba har lokacin tashi yayi muka tashi.
Tare muka tafi a motar Ummie, dan ita Dadyn ta ya bata mota ƴar ƙarama tun
fara aikinmu, tun tafiyar Yah Qaseem sai yazam direba na kawoni da safe, ita kuma
mutafi tare idan mun tashi sai ta ajiyeni gida ta wuce nasu gidan.
Kiran da Nazifa tai minne a waya muke amsawa tare da Ummie dake tuƙi, dan a
amsa kuwwa (Hans free)na saka wayar yanda itama zataji, munzo dai-dai shataletalen
(roundabout) ɗin da zamu ɗauki hanyar gida danja (traffic light) ta tsaidamu, sai
kwasar dariyar labarin da Nazifa ke bamu mukeyi.
Kusan minti goma muna a haka, saina fahimci sam motocin basa motsawa ma, buɗe
motar nai na leƙa, hayaniyar mutane sosai ke tashi, dan motocin dake tahowa a
dukkannin titinan huɗune suka cure waje guda, watama ta mugun bugama wata, sun saka
jami'i mai bada hannu a tsakkiya sunata zabga masa masifa. Mamaki ya sake kamani,
nadai dawo na zauna, mun cigaba da hira kusan ta minti ɗaya nadai sake jin abin bai
zaunamin a raiba, dan wannan go slow ɗin yafi kama da wanda aka haɗa da gangan,
gashi motoci sai sake taruwa sukeyi titin na sake cinkushewa. Ummie na bama Nazifa
amsa ni kuma na maida kallona ga mirror ɗin waje, har yanzu dai babu alamar motsin
motocin a dukkanin titinan huɗu da suka raba kansu, sai naɗan kalli Ummie ina
yamutsa fuska, dan na lura har yanzu ita bama ta fahimci halin da ake cikiba.
“Ummie akwai matsalafa, tabbas wannan cinkosan haɗashi akayi akan sani”.
Da sauri ta katse wayar tana cema Nazifa muna zuwa.
Kashe motar tai duk muka fita a hanzarce, tabbas an haɗashine da gayya,
hakkanne ya sakamu fara ƴan dube-dube muna kutsawa tsakanin motoci domin san isa
ainahin wajen da danjar take.
Gaba ɗaya wajen ya hargitse, sai hayaniya ke sake tashi, duk yanda mai bada
hannun keson dai-daita komai hakan ya gagara, ga waɗanda motarsu ta gogi junama sun
fara faɗa na shirin danbe. babu yanda za'ai muyi magana muma wani ya sauraremu, dan
abin yafi karfinmu.
Kalle-kalle na maida hankalina wajenyi sosai kozan samo bakin zaren,
Idona ya kasa barin wata baƙar mota mai baƙin gilashi {tinted glass}, na wuceta
yafi sau uku ina sake dawowa gareta, dan sai buga azababben horn mai motar yake
nason a bashi hanya ya wuce tamkar shi kaɗaine yafi kowa buƙatar titin kosan
tafiya.
Glass ɗin na ƙwanƙwasa, dan na tabbata koma wanene a ciki shi yana kallon na
waje ai, ba'a saukeba na sake bugawa, dan haka kawai nakejin wata irin jarumta da
ƙarfin zuciya da bansan daga ina tazo minba........
A fusace aka bugo mirfin motar ya bugeni, kafin na dawo daga jin zafin da
nayi kawai naji ƙarar harbin bindiga har sau biyu.
Take wajen ya hargitse da ihu, nima na toshe kunnena ina mai duƙewa ƙasa,
mutane sai fita suke daga mota suna gudu, masu dabara kuma na kwanciya a ƙasa, tuni
jama'ar dasuka taru suna hayaniya kowa ya kama gabansa, wasu sai son jan ababen
hawansu baya suke suna k

omawa da baya-baya domin ƙoƙarin barin wajen.


Cikin tunanin da yazomin daga UBANGIJINA ya sani fahimtar akwai matsala.
Murfin motar da bai gama buɗuwaba aka ziro hannu ahaka aka ƙara wani harbin
na kalla, da ƙafa na turashi ya bigi motar, hakan yasaka hannun da yay harbin ya
matse sosai, ƙara ya saki yana sakin bindigar itama ta faɗi ƙasa.
Jan motar sukai da wani irin ƙarfi, dukda motsocin dake gabansu bila adadin,
tuni wajen ya sake ruɗewa, jikake garraaam!! Kaccaam!! Na haɗewar motoci, wata na
bugar wata, gilasai sai fashewa suke famanyi, waɗanda suke a motocin basu fitaba
sunata ihu na firgita.
Saura kaɗan su takemin ƙafa, nai azamar sunkuyawa na ɗauki bindigarsa data
faɗi, banyi zato ko tsammanin zan iya abinda nake yunƙuriba, amma cikin amincin
UBANGIJI koda na harba sai harsashin ya sauka akan tayar motar ta baya.
Tangal-tangal motar ta fara, hakan kuma ya sake hargitse wajen da ihun mutane.
Kuma harbin ɗayar tayar nayi, hakan ya saka motocin dake gefenta, sukuma suka bigi
fitilar dake a tsakkiyar titi ta tsaya cak.
Gaba ɗayansu suka fito kuma lokaci ɗaya, dukansu sanye cikin baƙaƙen
kaya, gaba ɗayansu bindigace a hannayensu, hatta da wanda na bugama hannu da ƙofa
na ɗauka tashi yana tare da wata, hannunsa dana buga sai faman jale-jale yake
tabbacin na jimasa ciwo.......
Da ƙarfi naji an fisgi hannuna, dai-dai shigar ihun Ummie cikin kunnena
tana faɗin “Bily!!! harsashi!!”..................✍🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Typing📲


ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 3

...............Shuuuu yazo ya wuce sai jikin glass ɗin wata motar bus.
Saurin kallon wanda ke riƙe da hannuna nayi, gabana yay masifar faɗuwa saboda cin
karo da nai da fuskar da ban taɓa tunanin gani a wajenba ko tsammani, ya sake
fisgar min hannu muka duƙe bayan wata mota saboda tahowar wasu harsasan huɗu kanmu.
Cikin matuƙar fusata ya girgizamin hannu yana faɗin, “K shashasha ki dawo
hankalinki!!”.
Yanda yay maganar da wata firgitacciyar muryace ta dawo dani duniyar mutane, amma
hatta da kunnuwana da sun doɗe baki ɗaya ko ƙarar harbin banaji.
Ya jefamin wata bindigar a jiki, cikin zafin nama na cafeta.
Sosai Jawaad yaji mamakin salon na bilkisu, sai dai babu wannan lokacin a garesa
yanzun, dan haka ya maida hankalinsa akan abinda ke gabasu.
Wajen ya sake hargitsewa da musayar wutar harbe-harbe, kowa burinsa ya kare kansa,
mutane kam bamuda tabbacin halin da suke ciki a yanzu.
Bazan iya tantance muku halin dana tsinci kainaba a ciki a wannan lokacin, amma ni
kaina nasan na zama jaruma mai ban al'ajabi..
Kowa ya jigatu a wajennan. Bagamu jami'an tsaronba baga ƴan ta'addaba, balle kuma
jama'ar gari da suka fimu shiga ruɗani da tashin hankali. Sai dai abin farin cikin
shine mutum biyune suka haɗu da tsautsayin harbi a farar hula, ɗaya a ƙafa ɗaya a
hannu, amma Alhmdllh babu wanda ya rasa ransa sai a cikin ƴan ta'addar da aka harba
a ƙirji. Mun sami nasarar cafkesu baki ɗaya, su biyarne, ɗaya ya mutu, ɗaya naji
masa ciwo a hannu, sai raunika da sauran suka samu da wasu a cikinmu harda ni da
gilashin wata mota ya yanka a hannu.
Wannan shine karon farko dana taɓajin mummunan rauni makamancin haka a rayuwata,
sai dai lokacin dana jisa ruɗani baisa na maida hankaliba dukda inajin wani
masifaffen zafi da raɗaɗi na ratsani, a cikin ƴan uwana kuma babu wanda ya lura sai
da ƙura ta lafa, zuwa sannan na zubar da jini sosai, harma takai ina ganin jiri a
idanuna, dama gashi inajin yunwa sosai. Rose da hankalinta ya fara kaiwa kainace ta
iso gareni da hanzari, dan tuni hayaniyar mutane data ababen hawa data cika wajen
ta fara yima kunnuwana nisa, duhu ya fara mamaye idanuna, hakama numfashina sai
tattarewa yake waje guda yana dunƙulewa a cikin ƙirjina, abinda kawai zan iya
tunawa shine taroni da tai na faɗa jikinta, daga haka ban sake fahimtar komaiba
daga duniyar mutane.
★★..::..★..::..★..::..★★
A hankali nake buɗe idanuna da sukaimin masifar nauyi, naɗan motsa kaɗan ina cije
leɓe kafin na samu nasarar buɗe ido da ƙyau. ‘Asibiti kuma?’ na ambata a hankali
ina waige-waige da kallon ɗakin dana buɗe ido na ganni cikin bazata. A saman
hannuna dake naɗe da bandegi na sauke ganina, sai yanzune abinda ya faru yake
ƙoƙarin dawomin a zuciya, a hasashena zan iya cewa jiya kenan abin ya faru, dan
yanzu dai ranace ƙwanyar na fahimta, idan kuma ban mantaba ƙurar jiya ta tashine da
yammaci har zuwa duhun mangariba, kenan a cikin asibiti na kwana?.
Bani da amsar tambayar tawa, kamar yanda babu alamun akwai mai amsa mani ita a
kusa, dan babu kowa a ɗakin sai ni kaɗai.
Na ɗauki tsawon wasu mintuna da bazan iya ƙididdige yawansuba sallamar Ummie ta
riski kunnuwana, nakai dubana gareta yayinda take ajiye madaidaicin kwandon data
shigo dashi a hannu,
“Bily ashe kin tashi ma?”
Tai maganar tana matsowa daf dani. tare da taɓa hannuna da naji ciwon. murmushi nai
mata, kafin na buɗe baki a hankali ina bata amsa da “eh”. Zama tai a kujerar gaban
gadon, tana murmushi, tace, “Kai Alhmdllh, bily kin bala'in rikitamu jiya, wlhy mun
zata bazaki sake buɗe ido ki ganmu ba”. Da tsagwaron mamaki nace, “Miyasa?”. Tai
ƙaramar dariya tana miƙewa, “karki damu zan baki labarin komai, yanzu dai bara na
kira Doctor danya dubaki, daganan kici abinci ko, dan tun kiran sallar farko na
tashi domin na haɗa miki shi”. Kaina kawai na iya rausayarwa gefe ina binta da
murmushi, tare da tarin ƙaunar da nake jinmu tamkar jini guda.
Ba'a ɗauki wani dogon lokaciba Doctor yazo, yaymin tanbayoyi kafin ya bama Ummie
Umarni akan ta taimakamin nayi wanka ga bayi nan, idan na kammala naci abinci nasha
magani, zuwa yamma ƙilama su sallameni tunda sunga komai normal.
Da taimakon Ummie na sakko a gadon, sai yanzune na kuma fahimtar a ɗaki na musamman
nake, kuma ni kaɗaice a ciki, na kalli ledar jini dake rataye a ƙarfe cikin mamaki,
Ummie data lura saita bani amsa da faɗin, “Ke aka ƙaramawa, dan sanda muka iso
jininki ya zuba da yawa, amma Doctor yace babu wata damuwa a hakan, idan an ƙara
miki zai amfaneki, idan kuma ba'a ƙaraba bazaki cutuba, sai dai boss ya dage akan a
ƙara miki jinin dole, anbuƙaci gwada su oga Hafiz koza'a samu na ɗaya a cikinsu yay
dai-dai da naki, amma sai boss ya hana a gwada kowa, a cewarsa jininsa yana rukunin
da zai iya bama kowa, dan haka a ɗeba nashi, kowa yasha mamakin furucinsa, amma
bawan ALLAHN nan ya fuske abinsa, babu ma wanda ya samu ƙofar kawo masa wargin
tambayar dalilin hakan, daga ƙarshe dai jininsa aka ɗiba aka saka miki.......”
Lokaci ɗaya nai masifar zabura da zaro idanuna waje, har ina bige hannuna mai ciwo,
hakan ya sakani cije lip ɗina na ƙasa kafin nace, “Jininsa fa kikace?”.
Sosai ta ƙyalƙyale da dariya, “Wlhy karkiji wasa, jinin Boss ne ke gauraye da naki
suna aiki a kowacce kafar jijiyarki a halin yanzu”.
“Na shiga uku ni Bilkisu” nai maganar ciki yanayin ta ƙaremin. Dariya Ummie ta
cigaba dayi, dan na lura sam bata fahimci tashin hankalin da nake a cikiba da
gaske, ban sake iya maganaba har taimin rakkiya cikin toilet ɗin ɗakin dake tsaf
babu datti, ga ruwan ɗumi ta haɗa mani kuma.
A cikin dabaru nake wankan gudun karna jiƙa hannun dake naɗe da bandeji, sai dai
zuciyata sam bata tare da hankalina, sai faman juya maganar sakamin jinin Boss da
Ummie tace anyi nakeyi, haka kawai naji hawaye masu ɗumi suna sauka bisa kumatuna,
bansan na mineneba, sannan bansan dalilin zubar tasuba, sai dai wani gefe na
zuciyata na danganta saukarsu da ganin kamar bankai matsayin da za'ace jinin wannan
bawa ya gaurayu da nawaba, da kuma zaka tambayeni dalilin faɗar haka a lokacin
bazan iya cewa komaiba balle yin fashin baƙi. Haka dai na kammala na fito, da
taimakon Ummie na kimtsa cikin kayan da tazomin dasu, ta shafa min mai harda ƴar
hoda fara ta sakamin dan karna zauna fuska na ƙyalli, na zauna a saman gadon
jingine da filo ita kuma ta haɗamin tea, tare da zubamin farfesun kan rago daketa
ƙamshin kayan yaji.
“Ummie ƴan gidanmu kuwa sun sani?”.
Sai da ta miƙamin tea ɗin kafin tace, “Eh, tun jiya da daddare sukazo ai, Daddy,
Mom sai Aamilah da Shahudah da Salim, lokacin bakisan inda hankalinki yakeba, anama
ƙara miki jinin ne”.
Kaina na gyaɗa mata sannan na amshi kofin, cikin suɓucewar harshe nace, “Sanda
sukazo Boss na nan?”.
Tsareni tai da kallon tuhuma, ni kuma na basar cikin kauda mata shakkun dake neman
yin ƙutse a ranta, fahimtar hakanne ya sakata daidaita yanayinta itama, tace, “A'a
sun tafi lokaci harsu Oga Aliyu, ni kaɗaice kawai, saboda nima Daddy ne yace na
jirashi shida Mami zasuzo su dubaki saisu tafi dani, tunda Doctor yace basa buƙatar
kowa ya zauna dake”.
Bansan miyasaba sai kawai naji zuciyata tamin daɗi da rashin haɗuwar tasu, na
cigaba da shan tea ɗin a hankali, Ummie ce ta kuma maido hankalina gareta da faɗin,
“Ammafa kin bala'in burgeni jiya wlhy Bily, wai dama baki da tsoro ashe?”.
Murmushi nayi kaɗan ina lumshe idanuna tare da muskuta zamana yanda zanji daɗi
sosai, “Ummie ba tsorone banda shiba, wani lokacin tsoro da kansa yana jin tsoron
mai tsoronsa, sai dai ba kowacce ƙwarin gwiwa ke fahimtar da hakanba, a duk lokacin
da kikejin tsoron abu to kawai ki tunkareshi koda kina tunanin zaki halaka ne, ina
mai tabbatar miki shi wannan abin tsoron shine zai koma tsoronki, da gaske daga
jiya na ƙarajin ƙarfin gwiwar yima ƙasata aiki bakin rai bakin fama , alƙawarin
danai da izinin ALLAH bazata tashi a banzaba, daga yanzu zan cigaba da tunkarar
kowanne irin abin tsoro daka iya tsoratar da al'ummar ƙasata koda zai sakani
fuskantar ƙalubale, bani da kowa sai kaina Ummie, akwai irina da yawa a faɗin
duniya, waɗanda sukafini shiga gararin rayuwa da buƙatar jin ɗumin duniya a dalilin
rashin majingina ta iyaye, wadda mutuwa ta nisantasu, kokuma iyayen na raye ƙaddara
ta nisantasu, sai dai ita duniyar ta juya musu nata bayan saboda bata buƙatar nasu
ɗumin, waɗanda kuma keda kusanci da duniyar suna hantararsu saboda basu da buƙatar
taimakonsu koda da nuna tausayawane, irina da sukasan wannan zafinne kawai yakamata
ace suna iya tunawa dasu da waiwayensu a lokacin da suka sami damar ƙutsawa jikin
duniya ta ƙarfin tsiya. Na shiga aikinnan ne domin ALLAH, zanyi hidima wa ƙasata
domin ita ƙasata ce, zan rungumi marayu irina domin ƴan uwanane, zan kare haƙƙin
ƴan ƙasata domin suɗin ahalinane, nabar kallon allon tsoro a gabana a yanzun, allon
jajircewa kawai nake burin cinmawa insha ALLAHU, abokan tafiya kawai nake buƙata,
waɗanda basai naje farautarsuba, da kansu nakeso suzo gareni, hakkane kawai zaisa
na tabbatar da sun cika sharuɗɗan abokan gwagwarmaya dai-dai da yaƙar tsorona, jiya
ta wuce, yanzu a yau muke, abi mafi muhimmanci shine mu fiskanci gobanmu idan muna
cikin masu rabon gani”.
Sosai Ummie keta faman jinjina kai da dogon bayanina da bani da tabbacin zai zama
abin fahimta ga kowa har ita kanta, wani zai iya kallonsa ta fuskar ƙuruciya, wani
yace rashin hankali na mata, wani yace wauta ta mara gata, wani yace zaƙewa ta ƴaƴa
mata masu san nuna daidaita kafaɗunsu da maza, hakan bazai dameniba a duk yanda
fahimtarka ta baka, abinda na sani kawai zuciya sirrin mai ita kawai takeji, duk
bin diddigin ma'abocin kusanci koya kasa kunnuwa bazaiji komaiba sai bugawarta,
idan kuwa har mun yarda gaibu sunanta gaibu, to yazama tilas muyi imani da hankali
koda bama ganinsa a zahiri saita yaƙini kawai.
“Maganganunki irin na mutanene masu himma bilkisu, sannan masu duba gabansu
mizatazo dashi, bawai yau ɗinsu kawaiba, da jiyansu data shuɗe ta zama tarihi, tun
haɗuwata dake ta farko na fahimci kinada wata baiwa ɓoyayya da bakowa ALLAH ya bama
ilhamar hasasotaba, daga lokacin kuma da muka kasance ma'abota kusanci na tabbatar
da zamu ribantu da junanmu, sai dai taki ribar da zamu samu saita ɗara tamu
muhimmanci da amfani a garemu, k.......”
“Sam ban gamsu da bayanankiba Ummie” na faɗa cikin ɗaga mata hannu saboda yanda ta
kwararo zance.
“Miyasa kikace haka Bily?”.
“Banason faɗa kice na maida hannun agogo baya, mubar zancen kawai watarana ma
ƙarasa, mizai hana kije wajen Doctor kimasa maganar ya sallamemu haka, banason
zaman asibiti a rayuwata”.
kafin Ummie ta samu damar yin magana aka turo ƙofar aka shigo da sallama, Dad ne,
hakanne ya sakani faɗaɗa murmushi akan fuskata, saurin tashi tsaye Ummie tayi ta
bashi kujerar da take zaune akai, kafin ta gaidashi cikin girmamawa. Nima gaidashi
nai, ya tambayeni jikina cike da kulawa. Naji daɗin ganinsa sosai, nakumaji daɗin
alhinin daya nuna akan halin dana tsinci kaina, sai dai nayi ƙoƙarin daƙile
alwashinsa na buƙatar nabar aikin, danshi kam ya fara tsorata dajin cewa wannan
aikin namu da gaske bai dace da ɗiya mace ba, musamman ma irina da nake yarinya
ƙarama.
Cikin murmushi da girmamawa a garesa nace, “Dad addu'arku kawai muke buƙata, idan
har zamu cigaba da sakawa a ranmu mata basu dace da irin kowanne aikiba saboda
matsalolin cikinsa, to lallai yankinmu bazai daina fuskantar koma bayaba, hakama
sauran mata masu tasowa bazasu daina fuskantar ƙalubale na daƙile burinsu akan
kansu da ƙasarsuba”.
Sosai Dad yay murmushi, ya shafa kaina da cewar, “ALLAH yay miki albarka kinji,
lallai tunaninki ƙyaƙyƙyawane Bilkisu, ALLAH ya kiyaye gaba to, nabiya ta wajen
likita, ya baki sallama yanzu haka, sai dai ya tabbatarmin daga office ɗinku an
turo ɗaukarki, ɗan aiken na hanya kuma, dan haka ni zan wuce, dama daga nan airport
na dosa”.
“Dad badai har zaka sake wata tafiyar ba?”.
Murmushi yaymin mai ƙayatarwa yana jinjina kansa, “Hakane bilkisu, masu iya magana
nacewa na kwance baiga gariba, muma addu'arku muke buƙata tamkar yanda kuke buƙatar
tamu kinji, wannan karon kuma bazan jimaba, dan sati ɗaya kacal zanyi, idan na wuce
hakan kuwa bazan zarta gomaba”.
“To Dad ALLAH ya tsare hanya, ya kuma bada nasarar abinda za'a fita nema mai
albarka”.
“Amin ɗiyata, nagode sosai”.
Itama Ummie tai masa addu'a, ya amsa mata da kulawa kafin ya ajiye mana kuɗaɗe masu
kauri ya fice daga ɗakin”.
Koda Dad ya fice fuskarsa ɗauke take da murmushi tare da ɗunbin tausayin yarinyar a
ransa, shidai haka kawai ALLAH ya dasa masa ƙaunarta a zuciya, yaɗan juya ya kalli
ɗakin yay murmushi kafin ya cigaba da tafiya........
Gaff sukaci karo da mutum, Gimba yay saurin fara jero kalamun ban haƙuri a gareshi.
Batare da Dad yay masa wani kallon arziƙiba yace babu damuwa, yay wucewarsa. Binsa
da kallo Gimba yay cikin wani tsagwaron mamaki da juya abinda ya gani a cikin
zuciyarsa, sarai ya gane mahaifin matar Boss ɗinsace ta da, kuma mijin Gwaggonsa,
afili yace, “To mikenan? Mi yazo yi nan? Minene ma'anar wannan kallon da yayma
ɗakin nan? Minenema haɗinsa da ɗakin?”. Bashi da mai amsa masa wannan tambayoyin,
dan haka yaja bakinsa ya tsuke dan bai dace ya shiga abinda babu ruwansaba, Boss na
yawan masa nasiha da kiyaye abinda ba huruminsaba koda a inane, kuma koda akan
minene.
A ɗaki kuwa bayan fitar Dad yabo Ummie ta shiga jero masa, yayinda Bilkisu ke
tayata tare da ƙara buɗe ƙyawawan halaye na Dad waɗanda Ummie batasan da suba. A
haka gimba yay sallama a ƙofar ɗakin, sai da na suturta jikinna kafin mu bashi
damar shigowa, dukda bamusan shiɗin waneneba.
Mun gaisa da juna cikin girmamawa, sannan ya kora mana bayani akan cewar Boss ɗinsa
Jawaad ne ya bada umarnin yazo yakaimu gida dan an bani sallama.
Kallon juna mukai ni da Ummie, kowanne baki a hangame, sai dai bamu da damar bin
ba'asi akan wannan umarnin, dan kuwa dai yana sama damu, mizaisa mu tuhumesa da
abinda bamu da bakin zarensa. Haka muka shiga kimtsawa har Doctor ya shigo, ya ƙara
mana bayani akan yanda zan kula da cuwon saboda gudun karya zarta haka, tare da
kwanakin da zan ringa zuwa asibitin domin tabbatar da ingancin kulawar da nake
bashi.
___________________________
JAWAAD
___________________________________
Zaune suke a office ɗinsa su huɗu, aminan juna kenan da sukejin kansu jini guda,
sannan abokan amanar juna masu taruwa wajen magance matsalolin juna da ƙarfin
zuciya dana aljihu.
Sunyi nisa cikin tattauna abinda ya faru a yammacin jiya ne, domin dai da gaske
Jabeer ne ya haɗa cinkoson jiya da gangan saboda son cimma burin kama tsagerun da
suka biyo, amma sai suka ɓace musu, ganin zasu rasa wannan damarne Jawaad ya bama
Jabeer umarnin nuna ƙwarewarsa kasancewarsa masani sosai ta ɓangaren na'ura mai
ƙwaƙwalwa.
A take kuwa ya nuna gwarzantakar tashi, ya haɗa cinkoson da su Bilkisu suka riska
saboda tabbacin nan kaɗaice hanyar da masu laifin zasubi su tsira da wuri, ita kuma
Bilkisu tayi tarar aradu daka akan abinda bata da tabbaci.
Aliyu ne ya fara faɗin, “Maganar gaskiya na daɗe banga jarumar mace mai ƙarancin
shekaru irin yarinyarnanba, a yanda labari ke fitowa da ga bakunan mutane na yanda
ta tari motar mutanen da suka fara ganin farkon al'amari da yanda ta tunkari
mutanen zai baka tabbacin da gaske tanada kaifin zuciya akan aikinta”.
Cikin jin jina kai na tabbaci Jabeer yace, “Lallai maganarka tana akan gaskiya wlhy
Aliyu, nifa abindama ya sake birgeni da ita shine, dukda mugun ciwon da taji, amma
saita dake dan tabbatarma da duniya lallai ita ma'aikaciyar tsaroce ta gaske ba ƴar
burgaba”.
Fuska shimfiɗe da murmushi Hafiz yace, “Sosaima kuwa Jabeer, dolene ƙaimin yarinyar
ya burge kowa, dan kuwa da ƙwaƙwalwa tai amfani wajen fahimtar motar tana da alaƙa
da rashin gaskiya, ta kuma nuna himmarta na sadaukarwa koda hakan na nufin zata
cutu a wajensu, ta cancanci kowanne irin jinjina ga hukumarnan tamu, musamman idan
akai la'akari da shigowarta cikin aiki jiya-jiya kawai, bana tunanin kuma an taɓama
fita da ita wani aiki makamancin haka koda sau ɗaya”.
Duk wannan zance da suke faman zubawa akan yabon Bilkisu da jinjina himmarta Jawaad
na zaune shima a cikinsu, yana sanye cikin baƙaƙen suit kamar sauran da a kullum
suke ƙara masa kwarjinin kasancewarsa ma'aikaci, sai dai ya cire rigar sama, yana
zaune ne kawai da baƙin dogon wandon da rigar ciki mai dogon hannu kalar kore mai
haske, maɓallan rigar uku a buɗe, hakanne ya bayyana singlet ɗinsa kaɗan fara tas,
yaci zanzaro, ya tsuke ƙugunsa da belt kalar shirt ɗinsa.
Abinda zai baka mamaki ko tari bai yiba akan maganar, baima nuna ya fahimci mi suke
tattaunawarba sam, yana zaune ne ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani basarake, kansa
sunkuye yanata faman danne-danne a cikin tab... ɗinsa ta kamfanin Apple, sam
fuskarsa babu wata walwala, kuma ba'a tsuke take sosaiba.
Aliyu ne yakai dubansa garesa, tare da faɗin, “Ka fuskanci abinda muke tattaunawa
game da yarinyarnan kuwa Jay?”...............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 4
...............Shiru tamkar bazai tankaba, kusan sakanni sha biyar kafin yay magana
batare daya bar danne-dannen tab... Ɗinba balle ya kallesu, “Wace yarinya kenan?”.
Yay tambayar cikin nuna halin ko'in kula balle su sami ƙwarin gwiwa akan ya jisun.
Duk kallonsa sukai da mamaki saboda yanda sukasanshi dason mutum mai himma, amma
yanda ya amshi maganar ya matuƙar basu mamaki a yanzun.
Jabeer ne yace, “Yarinyar jiya daka bama jini mana Jay”.
“Humm” yace kawai ya sharesu bai sake tankawa ba, tsawon mintuna duk sun zura masa
idanu suna jiran ƙarin bayani, dan sunyi tsammanin fara jin yabon yarinyar da ga
bakinsa ma kafin su su furta, amma ya share kamar ya manta dasu ma a office ɗin.
“Wai boss lafiya kuwa?” Hafiz yay tambayar a wani yanayi.
Sai yanzune ya ɗago ya kallesu su duka, kallo irin a taƙaice ɗinan ya janye
mayatattun idanunsa masu cikar gashi da haske tamkar madara, ya taɓe baki kaɗan
kafin ya miƙe daga wajen ya nufin kujerarsa ta zama, dan da suna zaunene a rukunin
kujeru da'aka shirya a office ɗin domin hutawa ko ganawa da baƙi na musamman.
Sai da ya zauna sosai ya juya kujerarsa tana fuskantarsu kafin yace, “Abun harinmu
a yanzu shine mutuwar jami'inmu da sir Ahmad yamin bayani, minene shawararku akan
hakan?”.
Aliyu ne ya samu damar faɗin, “Bincike akan shi ɗin wanene? Tunkan fara aiki a
wannan hukumar har zuwa farawar tashi, tare da sanin masu bashi gudunmawa akan
aikin da yazama sanadinsa, da kuma sanin a ƙarƙashin wa ya samu umarnin”.
“shawara mai ƙyau” Jawaad ya faɗa yana lumshe idanu da kwantar da bayansa jikin
kujerar yana lilawa a hankali fuskarsa ɗauke da murmushi, kusan sakanni biyar kafin
ya sake ɗagowa yana kallonsu da nazartarsu. Ya ɗauke idanunsa tare da sake komawa
jikin kujerar ya kwanta, “Idan an sallamota daga asibiti zatayi bincike akan dukan
bayanan Aliyu”.
Cikin matuƙar mamaki suka kallesa, cikin harɗewar harshe Jabeer yace, “wai kana
nufin yarinyar?”.
Kallonsa kawai yay ya janye idanu, sai dai baice komaiba. Sun fahimci amsar kenan,
dan haka Aliyu yace, “Amma boss baka ganin aikin zai mata girma? Musamman idan
mukai dubi akan shine na farko?”.
Cikin halin ko in kula ya taɓe baki, ba tare daya kallesu ba yaja wasu takardu dake
saman tebir ɗin nasa yana faɗin, “Maybe hakan, maybe kuma ba hakan baneba, naga
kuma da kanku kun yarda da ƙwazonta, to miye kuma na kokwanto yanzun?”.
Babu wanda ya sake cewa komai. sai dai a ƙasan ransu duk sai suka kasance cikin
nadamar kwarzanta ƙwazon yarinyar da yawa irin haka, dan a ganinsu bata kai ƙwarin
da za'a sakata a irin wannan babban aikin hakaba mai haɗari, musamman idan sukai
dubi da ko rose data daɗe a cikinsu baya bata irin wannan damar.
Takardar da ya maida hankali a kanta ya ɗago saitin Hafiz, “Hafiz wanene da wannan
bayanan haka?”.
Tasowa Hafiz yay ya dawo gabansa, ya zauna a ɗaya daga kujerun gaban tebirin yana
mai amsar takardar, nazarin mintuna biyu ya ɗago kai yana kallonsa, “Akan case ɗin
yaron nan da aka samu makamai a shagonsu ne, Aliyu ne akan binciken kuma”.
Jawaad ya maida kallonsa ga Aliyu, hakan ne ya saka Aliyun tasowa ya nufosu shima.
__________★★__________
BILKEESU
_________________________________
Wani irin mayataccen ƙamshi ya shiga rige-rigen zirarawa cikin ƙofofin hancinanmu
yayinda muke shiga motar da boss ya turo ɗaukarmu, batare da kowannenmu ya fargaba
muka tsinci kawunanmu da lumshe idanu muna sake buɗe hancunan namu sosai. A haka
yaja motar muka bar asibitin, tabbas wannan ƙamshine daya cancanci ajiyeshi a
ma'ajin zuciya da ƙwaƙwalwa saboda ya kasance na musamman, bansan miyasa na kirashi
na musammanba, sai dai kawai zan iya fassara hakan da kasancewarsa na musamman a
duk lokacin da hanci ya shaƙa koda ba namuba. Naji tamkarma kar motar ta tsaya ace
na daina shaƙar wannan ƙamshin, sai dai babu yanda zanyi dan hakan tilasne. A
wannan yanayin muka isa gida, ya ajiyemu a gate ya juya, mukuma muka shiga ciki
bayan mun masa godiya.
Mun iske gidan babu kowa, suna gidan rasuwa su duka, dan haka mukai zamanmu dagani
sai Ummie da tace boss ya bata umarnin ta zauna dani harna warke tun a jiya. Ban
tambayeta daliliba, kamar yanda itama bata kawo komai a rantaba game da hakan, sai
dan tana ganin ya fahimci bani da wadda nakeda kusanci da shi sama da ita a station
ɗin namu.

__★.:.★__________★.:.★__
JAWAAD
_____★.:.★__________★.:.★_____
Suna tsaka da cigaba da magana shi da su Aliyu kira ya riskesa daga office ɗin B.G,
duk da kiran ya bashi mamaki daga shi harsu Jabeer ɗin hakan bai hanashi fita domin
cika umarni ba.
Galala nai da baki ina kallon haɗuwa da tsari na office ɗin da Jawaad ya shiga,
komai yaji babu algus. Banma kaina buƙuluba nabi ko'ina daki-daki da kallo a office
ɗin, kafin na sauke idanu ga mai ikon faɗa aji na hukumar tasu. Danƙari, na ambata
a zuciyata dan kuwa munzo ƙarshen zance, sam babu alamun fara'a balle sassauci
tattare dashi, Jay ya miƙa gaisuwa cikin girmamawa kafin ya samu izinin zama daga
gareshi.
“Sir Ance kana kirana” Jawaad ya faɗa cike da girmamawa.
A cikin maƙoshi ya bashi amsa da cewar, “Uhhm” daga haka yaja bakinsa yay tsit.
Gani nai shima Jawaad ɗin ya sake kame kansa ba tare daya sake tankawa ba, kusan
mintuna huɗu suna a haka kafin ya ɗago kai tare da juyama Jawaad fuskar lap-top ɗin
dake gabansa, hotone mai motsi (video), Bilkisu ta bayyana tana harbi da bindiga
har guda biyu a rikicin jiya, gaba ɗaya bidiyon bai wuce na minti ɗaya da wasu
sakanni ba, saboda iya itaɗin kawai aka nuna, ƙarewarsa ce ta saka Jawaad kallonsa
cikin rashin fahimta.
Cikin zafin rai da fusata ya zazzaroma Jawaad ɗin idanunsa jajaye, “Wannan yarinyar
tanada izinin yin harbi ne kamar haka dama?”.
Jawaad da ya tsuke fuska shima ya girgiza kansa kawai.
“Ya akai tayi kuma?”.
Sai da Jay ya furzar da huci kaɗan kafin yace, “Sir bamu da wani zaɓine bayan
hakan, domin musayar wutace, idan kuma bata da makamin kare kanta a hannu rayuwarta
na cikin haɗari, musamman daya kasance da taimakonta muka riski masu laifin”.
“Hakan yana nufin shine matakin ƙarshe da kuke da mafita kawai?”.
Shiru Jawaad yay bai motsaba, sai maƙogwaronsa ne keta kai kawo a cikin wuyansa,
yayi kicin-kicin da fuska.
“Da kai nake magana Captain!”.
“Sir nasan munyi kuskure, amma a duba uzirinmu muma, musamman na isa wajen a
ƙurarren lokaci, sannan a duba irin rawar da yarinyar ta taka, duk da kasancewarta
ƙaramar ma'aikaciya, wadda ta shigo jiya-jiya cikin wannan hukumar tamu, ta nuna
ƙwazon da ya kamata a jinjinama ƙoƙarinta ba ƙalubalantar taba, domin kuwa ita bata
da laifi, nine mai laifi dana bata bindigar”.
“Uhyim, kana nufin yanzu dai ka kareta?, sannan dukkan hukuncin da zai biyo baya
zaka ɗauka kuma?”.
Shiru tamkar bazai amsaba, sai kuma ya ɗago idanunsa harsun kaɗa da ɓacin rai, a
kasaushe yace, “Aimin duk hukuncin da za'ai matan babu damuwa”.
Shiru B.G yay kawai yana kallon Jawaad ɗin, yasan yaron dama akwai taurin kai, dan
tun shigowarsa hukumar ƴan sanda ma da tsaurin ido ya shigo, kasancewar wanene
mahaifinsa yasa aka hana kowa nuna masa yatsa, himmarsa da zafin nama ne ya saka
aka maidoshi cikin hukuma DSS, shi kuma har cikin ransa yaron bai masaba, sanin
dalilin kuwa wannan sirrinsane....
“Kaje zamu nemeka” B.G ya faɗa a daƙile.
Uffan Jawaad baice ba, ya miƙe kawai tare da yin salute nashi ya fice abinsa yana
haɗiyar zuciya, duk wanda zai iya ganinsa a wannan lokacin dolene ya fahimci ransa
a matuƙar ɓace yake, mai makon ya wuce office ɗinsa sai ya nufi office ɗin L.C,
wato sir Ahmad barewa, canne kawai zai kai damuwarsa ya samo mafitar da yake
buƙata.
Bayan yay knocking ƙofar aka bashi izinin shiga, ya riga da yasan ya gansa ta cctv,
tunda ya turo ƙofar ya shigo sir Ahmad ya fahimci akwai damuwa, ya kafeshi da idanu
kuwa, yayinda shi kuma Jawaad ɗin yaƙi yarda su haɗa idanu.
Sai da ya miƙa gaisuwa Sir Ahmad yay masa nuni da kujera alamar ya zauna.
Koda Jay ya zauna sai baice uffanba, sai ajiyar zuciya kawai yake faman yi, sir
Ahmad yay murmushi irin nasu na manya masu kaifin tunani, kafin ya miƙe daga
mazauninsa ya nufi firij ɗin dake a office ɗin, goran ruwa ya ɗakko ya miƙa masa
batare da yayi magana ba, babu musu ya amsa, ya ɓalle murfin yana kai goran
bakinsa, sai da ya shanye fin rabi sannan ya ajiye yana sauke numfashi a jajjere.
Wani murmushin Sir Ahmad ya kumayi, sannan ya zauna a kujerar dake kusa da Jawaad
ɗin suna kallon juna “Captain! Lafiya kuwa? Waya zinguro mazajene?”.
Idanu Jay ya ɗago ya kalli Sir Ahmad, sai kuma ya janye yana shaƙar numfashi da
zafi.....
“Jay!”
Sir Ahmad ya kirayi sunansa yana ɗora hannunsa bisa kafaɗarsa.
A karo na Biyu Jawaad ya sake kallon Sir Ahmad barewa, ya cije leɓensa da ƙarfi
yana faɗin, “Daga office ɗin B.G nake Sir”.
“Na sani ai” cewar sir Ahmad yana murmushi.
Cikin sauri da tsagwaron mamaki Jawaad ya kalli Sir Ahmad, kallo irin na tuhuma.
Ƴar dariya sir Ahmad yayi, ya kuma kai hannu ya bubbuga kafaɗar Jawaad ɗin a
hankali, “Kar kai fushi yarona, karkuma ka shiga ruɗani, banason ka manta kanka a
cikin mutane masu kaifin basira, za'ai amfani da yarinyarne kawai ai wasa da
hankalinka, kaga kenan an samo lagwonka da damar bama maƙiyanka yin wasoso a saman
mutuncinka, kar kaga laifin B.G, shima sashi akayi, domin bana tantama umarni ya
samu daga sama, sai dai wanene? Akan minene? Shine ban saniba”.
“Zuutt!” wani abu dake tsaye a maƙoshin Jawaad ya faɗa cikin cikinsa, ya sauke
nannauyar ajiyar zuciya, saboda dai Sir Ahmad ya dawo dashi a hayyacinsa da wuri...
Sir Ahmad ya miƙe yana murmushinsa na kamilallun mutane, ainahin kujerar zamansa ya
koma ya zauna..
“Abin bai baka mamakiba ace iya inda take harbin kawai aka kawo masa, sannan kuma
ita kaɗai, bayan kuma batakashin da kuka gwabza a wajen ku kusan goma ne”.
“Sir ai abinda ya matuƙar ɓatamin rai kenan, taya za'ai ace itace kawai za'a
ɗauka?....”
“Saboda ita kaɗai tazo da salon da ya ajiye ruɗani a zukatan masu fargaba akan
jajircewarka”.
“Salo kuma sir?!”.
“Yes! Jawaad, salo mai ƙayatarwama kuwa, andaɗe ba'a samu mai ƙaracin shekaru
irinta da wannan ƙwazonba, abin ƙarin mamakin kuma gata mace, yarinyar da alama
zata ajiye tarihi a wannan hukumar, dan alamomin hakan sun farane daga jiya”.
“Sir! to amma su wanene ke ganin hakan matsayin ƙalubale garesu? Miyasa kuma....?”.
“Nima ban saniba Jay”.
Shiru Jawaad yay na wasu sakanni kafin yace, “Saboda mi suka zaɓi hukuntata bayan
karramawa ta cancanta dashi sir?”.
Sir Ahmad yay gajeruwar dariya idonsa akan Jay, yace, “Saboda ƙwazonta abin
dubawane ga mai hankali, sannan abin tunani ga irin waɗanda basa buƙatarta, wannan
shine aiki na farko da yarinyar tayi, kuma ba sakata akayiba, sai dai ƙwazonta ya
girmi matsayinta da gogewarta a aikin, hakanne ya sakasu saka maka alamar tambaya
(?), musamman daya kasance tare da kai aka fara ganin baiwar ta ta”.
Karan farko da Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya harda dukan tebir ɗin gabansu, Sir
Ahmad dake kallonsa shima murmushinsa ya faɗaɗa, ya juyo sosai yana fuskantarsa,
har yanzu kuma fuskar tasa da sauran dariyarsa irin wadda kafin yayita akan kai
ruwa rana,
“Sir kasan minene kuwa?”.
“Saika faɗa Jawaad”.
“Sun bani dariya ALLAH, danni Ko sunanta ban saniba fa”.
Dariya shima sir Ahmad ya shiga ƙyalƙyalawa, kafin yace, “Cakwakiya kenan, to
tabbas kuwa daga masu wannan ƙullin abun ba haka bane ba Jawaad, kallon ƘWAI CIKIN
ƘAYA sukema lamarin”.
“Nima na fahimci hakan a yanzu sir”.
“Yayi ƙyau. Miya faru jiya?”.
Tun daga farkon zuwansu inda abun ya faru har ƙarshe Jawaad ya bama Sir Ahmad
labarin komai bai ɓoye masaba.
Kai kawai Sir Ahmad yake jinjinawa har Jawaad yakai ƙarshen jawabinsa, ya sauke
numfashi kaɗan yana faɗin, “Zamu shiga meeting anjima, kuma nasan akan wannan
maganarne, shawara ɗaya dazan baka yanzu shine, kai ƙoƙarin gano wanda ya ɗauki
wannan bidiyon, sannan kayi gaggawar samo bidiyon da yafi wannan na wajensu tsaho,
ka kumayi saurin rubuta bayanai akan komai ka tura office ɗin L.G tare da bidiyo
ɗin daka samo ɗin”.
Kamar Jawaad zaice wani abu, sai kuma yay shiru yana miƙewa da faɗin, “Okey sir,
zanyi ƙoƙari insha ALLAH”.
★★★★
Gaba ɗaya kan Jawaad ya kulle da wannan lamari, ya rasama ta yaya zai fassara
al'amarin, maganganunsa da Sir Ahmad kawai ke masa kai kawo a cikin zuciya, tare da
zuwansa office ɗin B.G, ya rasa ina zai kama ma shikam? Yana buƙatar ganin su
Jabeer tare dashi yanzunan, sai dai tabbas bazai yuwu a station ɗinanba, dan yanzu
dukkanin motsinsa abin bibiyane.
Ƙaramar wayarsa ya ɗauka ya turama Hafiz saƙo, kafin ya tura wayar aljihu bayan ya
kasheta gaba ɗaya ma, wasu takardu ya ɗiba ya fito a hanzarce, hana kowa ya bisa
yayi, ya shiga mota shi da Gimba kawai suka fice daga station ɗin.
Danne-danne yaketa famanyi a lap-top, hakan ya saka gimba kallonsa ta cikin madubi,
“Boss! Ina zamuje?”.
Ba tare da ya ɗagoba yace, “A.Y Street”.
Cikin girmamawa Gimba ya amsa, tare da juya kan motar suka nufi hanyar gidan Jawaad
ɗin dake anguwar A.Y street.
Sunyi wajen mintuna talatin da zuwa kafin su Aliyu su iso. A falo suka iskeshi har
yanzu yanata faman danne-danne a lap-top, a haka ya amsa sallamarsu ko ɗagowa
baiyiba ma. Sai da suka zauna da kusan mintuna biyu sannan ya ɗago ya kallesu,
kallo ɗaya yayma Rose ya ɗauke kansa, hakan yay bala'in sosa ranta, dan akwai
kwallin data shafa, an kuma tabbatar mata idan suka haɗa ido da shi zai haukace
mata, yabar kallon kowacce mace da gashin arziƙi sai ita, amma ɗan rainin wayon
tun'a station takeson su haɗa ido da shi hakan ya gagara...
“Boss! Lafiya dai ko?”.
Aliyu da ya kafeshi da idanu ya faɗa.
Lap-top ɗin ya ajiye yana faɗin, “Da dai sauƙi Aliyu, an yanka ne ta tashi”.
“Kamar ya?;” suka faɗa cikin haɗa baki su uku, rose ce kawai da bata fahimci
hausarba batace komaiba.
Cikin takaici Jawaad yace, “Ƴan uwana wasan jiya ya koma yaƙi, kukan tsuntsuwa mai
zanen kanari ya zame mana abin magana”.
Sun fahimci zaurancensa, saboda wannan yana ɗaya daga cikin salonsu, musamman akan
aikin da suka samu gamayya da waɗanda basa cikinsu, sai dai basu fahimci dalilin
zaurancenba a yanzu, saboda duk sune a wajen babu baƙon ido.
Jabeer yace, “Jay bansan miyasa ka zaɓi ƙin buɗe zancenba, bayan kuma duk mune babu
wani bare a cikinmu?”.
Jawaad yace “Nima bansan miyasa harshena ya zaɓi hakanba Jabeer, sai dai saƙon
kamar tun daga zuciyane”.
“Idan na fahimta, kamar zuciyarka na ɗarsa maka akwai ɗan baya ga dangi kenan a
cikin tafiyar?”. Hafiz yay maganar cikin taraddadi.
Cikin sauke nannauyan numfashi Jawaad yace, “Bani da tabbas, sai dai zuciyata na
rayamin akwai idon mikiya a bayanmu”...............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻[11/30/2020, 1:02 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:


Typing📲

Page 5

.............Duk Kasa cewa komai sukai, sai idanu da suka zubama Jawaad
tamkar wani bakonsu.
Rose da zuciyarta ke tafasa akan rashin kallonta da jawaad baiyiba ta
kasa daurewa, ta dubesu baki ɗaya a wani yanayi, “Boss wai mike fauwane? tai
maganar cikin harshen turanci da tsare Jawaad da idanu tana fatan ta dace yanzun.
A mamakinta yanzunma dai ƙin kallonta yayi, sai Lap-top ɗinsa ya miƙa mata
kawai, ya koma ya zauna tare da ɗaukar tab.. Ɗinsa ya shiga tafa saƙo da hanzari.
Gani nai Aliyu ya ɗago ya kallesa, yay masa wani salo da ido tare da cije
baki, murmushi Aliyu yayi kawai ya maida kansa, kafin ya miƙe yabar falon, hakama
Jabeer da Hafiz duk ya tura musu suma, Hafiz shima tashi yay ya fita, Jabeer kuma
ya koma kusa da Rose dan kawai ya ɗauke hankalinta da aikin da Jay ya bata itama.
Bayan fitar su Aliyu da kusan mintuna tara ya miƙe yabar falon ya nufi
bedroom ɗinsa. Sai da ya kulle ƙofar kafin ya ciro ƙaramar wayarsa yay kiran Hafiz.
“Hafiz yaya? An dace kuwa?”.
“Ba'a daceba Boss, amma ga shawara mana?”.
“Micece shawarar taka?”.
“Mu bincika kowanne manhajar yanar gizo ko zamu dace wani ya ɗauka, kasan yanzu
ba'a raba mutane da ƴan ɗauke-ɗauke a waya, maganar gano wanda ya kaima su B.G kuma
ba abune mai sauƙiba ace yanzu da gaggawa, sai dai mu canja shawara ta wannan
gaɓar”.
“Na fahimceka Hafiz, yanzu kayi duk yanda ya dace, amma inaji a raina koma
wanene yakai wannan bayanan yana da kusanci damu Hafiz, amma banason zargin kowa”.
“Boss zargi dolene, kuma koma wanene ya daɗe a jikinmu, a sannu zamu cinmasa
da ƙarfin ƙudirar UBANGIJI, dan shine ke haska mana hanya a dukkan lamuranmu”.
“Insha ALLAHU Hafiz, yanzu dai sai na jika”.
Yana yankewa yay kiran Aliyu shima, sai dai daga ɓangaren Aliyun an dace, dan
ya turo masa dukkan bayanai akan Bilkisu da abinda ya shafi shigowarta hukumar
tasu, da horon data samu, da ƙwazon data nuna tun a wajen horaswa, alaƙarta da
Qaseem, sai dai babu wani bayani kafin zuwanta gidansu Qaseem ɗin, hakkanne yaɗan
tsayama Jawaad a zuciya, har yakejin dolene ya sake binciken, dan karfa nan gaba ta
zame masa ƘWAI CIKIN ƘAYA kuma kamar yanda ƴan bayan fage ke hasashe.

Daga ɓangaren Hafiz ma an dace daga baya, dan kuwa cikin amincin ALLAH ya
samo bidiyon faruwar komai tun daga lokacin da Bilkisu ta kaima motar masu laifin
caffa kafin zuwansu, har zuwa sanda abubuwa suka lafa.
Yaci karo da Bidiyon ne a wani chennal na youtobe, bayan ya shiga manhajar
Google yay Searching, sai dai abinda ya bashi mamaki yana kammala sauke video'n
akan manhajar ta youtobe wanda ya ɗora ɗin ya saukeshi daga accaunt ɗin, hakan sai
yay bala'in ɗarsa mamaki a zuciyar Hafiz, harya kasa haƙuri ya kira Jawaad ya
shaida masa.
Murmushi Jay yayi yana shafa kansa, “Ba abin mamaki bane Jabeer, musamman
idan mukai la'akari da babu wata kafar yaɗa labarai da dama ta saki bidiyon mai
tsawon hakan, sai wasu ɓangarori da dukansu iya inda muke musayar wutane kawai”.
Hafiz yace “Hankalina sam bai kaiba sai yanzu kam, koma miye yake a ɓoye
ALLAH zai bayyanashi ai, mudai domin ALLAH mukema ƙasarmu aiki, duk mai yunƙurin
daƙilemu kuma ALLAH zai mana maganinsa”.
“Insha ALLAHU kuwa Hafiz” Cewar Jay cike da takaici.
Kafin dare duk sun haɗa bayanan da ya kamata akan maganar, sun tura iya waɗanda Sir
Ahmad ya umarcesu zuwa Office ɗin, L.G, sauran kuma sun adana a wajensu domin ya
zame musu hujjar kare kai, hatta da bidiyon suma gutsira sukai suka tura, sauran
kuma suka adana a wajensu.

_______★__________
SHAHUDAH
_____________________________

Tunda suka fara zuwa gidan rasuwarnan sau ɗaya taga Jawaad,
harga ALLAH ita kuma dominsa take zuwa, a tunaninta idan suka haɗu zai matuƙar
rikicewa da ganinta, musamman ma yanda ta sake canjawa da ƙyau mai ƙayatarwa, sosai
ta gama shirya shika-shikan rama dukkan abubuwan da yay mata kafin ta yarda da
buƙatarsa ta komawa gidansa.
Sai dai abin mamaki da al'aj

abi dukkan tunaninta sai bai zama gaskiyaba, dan kuwa ko a randa suka haɗu kallo
ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, komai kuma a kan idanun Mom ya faru, dan suna a falon
mama Atika ne a washe garin rasuwar ya shigo da baƙi su Sir Ahmad da sukazo
gaisuwa. Sarai idanunsa sun gane masa Shahudah, amma sai ya ɗauke idanu cikin nuna
halinsa na ko'in kula da abu.
Abin ya sosa mata rai sosai, amma saita danne da yaƙinin ƙila yayi hakane
saboda ganin suna cikin jama'a. Koda suka koma gida sai basuyi maganar da Mom ba,
saboda kowa ya dawo a gajiye wajen bacci yafi buƙata. Washe gari kuwa kwalliya tayi
ta musamman dan Jawaad nanma babu sa'a, dan har dare da suka baro gidan bata
sakashi a cikin idanunta ba, washe gari kuma suna isowa gate ɗin gidanne motar
Jawaad ɗin ke fita da alama ya nufi office ne. Waɗanan akasin da akaita samune suka
jefata a cikin damuwa har yau ta kasa daurewa.

“Mom kinga abinda Bb ya kemin kuwa? Bayan ya kamata ace ya nuna zalamarsa da
kewata na shekarun da muka kwashe bama tare”.
“Huhm” Mom ta faɗa tana shafa kan Shahudah dake saman cinyarta, dan kuwa suna
cikin bedroom ɗin Mama Atika ne ita da Shahudahn kawai, dan ta fahimci ɗiyar tata
na tare da damuwa, yau tunda sukazo gidan ta shigo ɗakin Mama Atika bata sake
fitaba, shiyyasa ta biyota, sai ta isketa cikin damuwa, hakanne ya sakata zama ta
dora kan Shahudah a cinyarta tana shafawa, itakuma take bata labarin ruɗanin data
shiga akan tarbar data samu daga wanda batai tsammaniba daga Bb ɗinta (Jawaad).
Mom ta haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi tana sake yamutsa sumar
Shahudah'n, “Kar taurin kan yaron nan ya ɗaga hankalinki fiye da haka Shahudah, ki
barsa, ni da kaina zan sauke masa wutar dake ci a kansa, bara dai a gama hidimar
rasuwarnan kinji”.
Kai Shahudah ta ɗaga mata cike da shagwaɓa, har ƙwalla na sakko mata a kan
kumatu tace, “Amma Mom wane mataki zaki ɗauka to?”..
Mom ta share mata hawaye tana murmushi, “Karki damu Shahudah zaki gani, kedai
sonake kicigaba da kwantarmin da hankalinki, nan kusa kaɗan zaki dawo ɗakin
mijinki”.
Kai Shahudah ta ɗaga mata tana murmushi da rungume mom. Murmushi mom tayi
taci gaba da lallashinta cikin so da ƙauna.

Nikam nace, “Mai uwa a gindin murhu baya cin tuwonsa gaya ai Shahudah😋😜🤸🏼.

..::..★__________★..::..
BILKEESU
____★..::..★__________★..::..★____

Kwanaki huɗu cir bana zuwa Office ina gida ina jiyyar hannuna, yayinda
kullum Ummie ke tare dani, ƴan gidanmu kuwa basa yini suna gidan rasuwa, barci
kawai ke kawosu gidan. A kwana na biyar nai shirin komawa aiki, dan naji sauƙi
sosai, a kuma daren ranarne Yah Qaseem ya dawo, nayi farin cikin dawowar tasa, dan
nikaina nasan idan nace banason Yah Qaseem na yaudari kaina, a ƴan kwanakinan da
bayanan sosai nayi kewarsa.
Tun a daren yake jeramin tambayoyi akan hannuna, bai samu amsa ko ɗaya ba
daga gareni sai murmushi kawai.
Koda muka tashi da safe ma dai bai fasa sonjin musabbabin ciwonba, da naga ya
damu sai kawai nace masa tsautsayine ya gitta mani a wajen aiki, badan ya yardaba
ya ƙyaleni kawai, kasancewar yau zan koma aiki nima sai na bisa muka tafi tare
kamar yanda muka saba kafin yay tafiyar.
Yah Qaseem na gama daidaita fakin motarsa wani jami'inmu na isowa wajen, ya
isarmin da saƙon kira daga office ɗin B.G, maganar da jami'in yazo da itane ya
sakamu kallon juna ni da yah Qaseem ɗin.
Idanuna na janye daga cikin na Yah Qaseem daya tsatstsareni da kallon
tuhuma, da ƙyar na haɗiye yawun da ya tarumin a baki, dan girman office ɗin mai
kiran nawa na kalla da kuma tunanin minene dalilin kiran?.
Yah Qaseem da har yanzu idanusa ke kaina da alamar tambaya na kuma kallo, ya
gyara tsaiwarsa yana mai jehomin tambaya,
“Bilkisu mikike ɓoyemin ne?”.
Da sauri na girgiza masa kaina, “Wlhy Yah Qaseem bana ɓoye maka komai, nima bansan
minene dalilin kiranba, amma bara naje najiyo”.
Ban jira amsarsaba na bar wajen cikin tafiyar sassarfa, zuciyata sai bugu take
da sauri-sauri, dan inaji a raina wannan kiran bana lafiya bane ba, musamman

idan nai dubi da ƙaramin matsayina a hukumar.


Koda na iso sai da na jira aka bani izinin shiga sannan, wannan shine
karon farko da zan shiga office ɗin a rayuwata, ba shi kaɗai bane a cikin office
ɗin, jinai wani abu ya tsargamin daga saman kaina har zuwa yatsan ƙafata, na aro
jarumtar dole na yafama kaina tunda bansan minene dalilin kiranba. Na miƙa musu
gaisuwa cikin girmamawa kafin na zauna inda aka nunamin.
Tambayar farko da aka jefamin ta sakani ɗago idanuna na kallesu badan na
shiryama hakanba, ba firgici ne ya sakani kallon nasu ba, nutsuwace ta zomin
saɓanin yanda na shigo a rikice, dan kuwa a nawa tunanin inhar akan rikicin daya
faru kwanaki biyar da suka wucene banga wani abin kuskure dana aikata a cikiba,
zamana na gyara na fara amsa musu tambayarsu da iya gaskiyata dana sani.

Yanda Bilkisu ke amsa musu kowacce tambaya kanta tsaye babu ko ɗigon firgici
ko rawar harshe ya sakasu kafeta da idanu, su kansu iya zallar gaskiyarta suke gani
a saman fuskarta da furucinta.
Sun mata tambayoyi sosai, domin sake tabbatar da gaskiyar tata suka sake
maimaito mata dukkan tambayoyin da sukai matan a farko, abinda ta faɗa daga farko
shine ta sake maimaitawa saboda hakan shine gaskiyarta.

Kusan awa ɗaya da wasu mintuna suka sallamoni na fito, a raina sai juya wannan
al'amari nakeyi...

_____________________________

JAWAAD

Zaune yake a office yanata aikin duba wasu tulin takardun dake gabansa
yaji knocking ƙofa, siririn tsaki yaja dan baya buƙatar kowa a irin wannan lokacin,
izinin shigowa ya bada batare daya ɗago ba balle kallon wanene?.
Ƙamshin turarenta kawai ya bashi amsar wacece, harta zauna bayan gaisheshi da
tayi bai ɗago ɗinba, a haka ya amsa mata.
“Mi kike buƙata?”
Ya faɗa yana cigaba da aikinsa batare da ya ɗago ɗinba.
Duk da taji haushi sai ta danne, abinda ta gani kuma ta jiyo game da kiran
Bilkisu da akayi office ɗin B.G ta zayyane masa, karon farko da ya ɗago ƙyawawan
idanunsa ya sauke akan rose, sai dai baice komaiba. Duk da tsawon kwanaki kenan
tana buri da buƙatar irin wannan kallon daga garesa saboda kwallin da take sakawa
na jawo hankalinsa kanta sai ta kasa jurewa, dan wani irin kwarjininsane ya kuma
cika mata idanu da gangar jikinta, tai azamar janye idanun nata ƙirjinta na wata
irin harbawa.
Har lokacin idon Jawaad na akanta, ya cigaba da ƙare mata kallon nazari har
kusan mintuna biyu kafin ya janye ya maida ga aikinsa.
Ɓoyayyen numfashi rose ta sauke, daga can ƙasan ranta kuma wani daɗi na sake
mamayeta, dan kuwa dai tasan ta gama da taurin kan Jay kamar yanda bokanta ya sanar
mata, inhar suka haɗa ido wannan kwallin na idonta to lallai tagama da mallakarsa
har abada, ba kuma zai sake kallon kowacce maceba bayan itaɗin.
Sakanni kusan ashirin bai tankaba, bai kuma sake kallonta ba. Takaici ya
sake mamaye zuciyar rose, ta buɗe baki da nufin yin magana ya miƙe tsaye,
bindigarsa da wayoyinsa dake saman tebir ya ɗauka ya tura cikin aljihun Blue jeans
ɗinsa, tare da ɗaukar tab... ɗinsa a hannu. “muje” ya faɗa batare da ya kalleta ba.
Binsa tai da kallon mamaki, harya buɗe ƙofar office ɗin ya fice, dole itama ta
tashi da hanzari ta bisa, a ranta tana ayyana cewar ‘Yau ƴan wulaƙancinne a kansa
kenan?’.

Fitowar Jay daga office yay dai-dai da fitowar Bilkisu daga sashen office's
ɗin su B.G, kaɗan ya rage suyi karo, kasancewar hanyar data haɗa shataletalen
office's ɗin ɗayace kafin su ƙarasa su hau lifter da zata kaisu kasa.
Da sauri naja baya ƙirjinna na motsawa, cikin dakewar harshe da banyi zaton
inada shi ba nace, “Kayi haƙuri dan ALLAH , bansan ka taho bane”.
Ƙyawawan fararen idanunsa ya zubamin kansa tsaye, kusan sakan biyar tamkar
zai cinyeni dasu sannan ya janye batare da yace dani komaiba. ya raɓani zai wuce,
hakan yasa na matsa baya na bashi hanya, tafiya ya fara tare da faɗin,
“Biyoni”..............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻


[11/30/2020, 1:03 PM] HASNA ✍🏻
: Bilyn Abdull :
😂🤣😂🤣😆😆😆Kunsan miyasa nake dariyarnan? Akan yanda kuke ganin kamar bily tsoron Jay
takeyi, dukfa halin da take shiga shiba fahimta yakeba, hasalima kallon miskila
idan kun lura yake mata, akwai masu samun kansu a irin yanayin bily akan wani ko
wata, sai daga baya suke fahimtar dalilin shigarsu irin wannan halin, itama bily
lokaci zai warware mata komai har muma mu sami amsa, ina muku fatan alkairi aduk
inda kuke, sosai Comments naku na sakani nishadi da sani typing kodama ban niyyaba.
I love you wujiga-wujiga irin trillions ɗinnan🤸🏼🤸🏼🤸🏼 😍😘😍😘😍😘🤗.

Page 6

Ko kaɗan ban fahimci dani yakeba, musamman dana waiga naga rose data fito
daga office ɗinsa a bayanna, wani kallo naga ta watsamin mai kama da takaicin tabi
bayansa. Numfashi na sauke mai nauyi na shafa ƙirjinna dai-dai saitin zuciyarta
dake harbawa da sauri-sauri, duk da na fahimci kallon da rose tai mani sai hakan
bai dameni ba, dan bata ita nakeba. Nima fita nai daga wajen, na fito ainahin
harabar station ɗin domin nufar sashenmu.
“Ɗi! Ɗi! Ɗi!!” gimba ya danna mata horn kamar yanda Jay ya bashi umarni.
Duk da naji horn ɗin hakan baisa na fahimci da ni akeba, saboda idan
akai dubi da sauran jami'ai irina daketa kaikawo a harabar wajen, kowa da
hidimarsa.
“K! Wace irin daƙiƙiyace da baƙya fahimtane? A haka kike tunanin zama jami'ar
tsaron al'umma!!?”
Maganar Rose a tsawace ta shiga dodon kunnena ina gab da shiga lungu da zai
sadani da office ɗinmu. Da sauri na juyo, idona ya sauka akan rose dake huci da
jifana da kallon takaici mai nunin tsana. Duk da naji zafin kalaman datai amfani
dasu a gareni sai na danne saboda tana sama da ni, a ladabce nace, “Kiyi haƙuri
maa! Bansan dani kike ba”.
Tsaki rose ta buga, tare da juyawa tabarni a wajen, wani jami'i dake tsaye
kusa damu ya kalleni da tausayawa, dan shi dai yarinyar tunda tazo station ɗin
ɗabi'unta birgesa sukeyi, ganin ban fahimci manufar rose ba sai yay min fassara
akan nabi bayanta maybe kirana akeyi.
Godiya nai masa, kafin nabi bayanta cikin nutsuwata, sam ban iya sauri ko
rikita kaina a tafiya ba koda kuwa a tsorace nake, a yanzunma duk da zuciyata na
cike da tunani da baƙin cikin abinda tamin ban rikita kainaba a yayin bin bayanta,
can na hangota jikin wata farar mota mai ƙyau da ɗaukar hankali, na cigaba da
takawa a nutse gareta, ina isa jikin motar ita kuma tana buɗe gaba ta shige, hakan
sai ya sakani a duhu, dan bansan kuma wajenwa zanje ba. Saitin inda take na ƙarasa,
na ɗan risina yanda zata ganni ina faɗin, “Gani maa!”.
Kafin ta bani amsa ƙofar murfin baya naga ta buɗe, ita da drivern naga duk sun
kalli bayansu, hakanne ya sakani kallon murfin ta waje nima, muryar drivern ta
katse min tunani, “Ki shiga” ya faɗa yana nunamin bayan.
Duk da na shiga ruɗani, ga harbawar da ƙirjina keyi hakan bai hanani bin
umarninsaba, koda wasa ban kalli waye a bayanba, na shiga kamar yanda aka umarceni,
sai da na zauna ne wani mayen ƙamshi ya samu cikakkiyar damar surɗaɗawa a ƙofofin
hancina, da sauri nai ƙoƙarin kallon gefena, gabana ya faɗi dan ganin wanda banyi
zatoba, fuskarsa babu alamar wasa kamar yanda na gansa yanzu da mukai karo.....
“Sai kin gama kallona zaki rufe ƙofar ne?” muryarsa ta daki dodon kunnena
babu zato, kaina na girgiza da sauri ina tattaro busashen yawun bakina da ƙyar na
haɗiye, tare da jawo murfin motar na rufe. Nama rasa yanda zan fassara wannan
al'amarin sam, gashi yanayin dana tsinci kaina ya hana mani damar yin nazarin daya
dace da hakan.

Ɓangaren Rose da Gimba kuwa mamakine fal a rayukansu, gimba shaidane akan
bai taɓa ganin rose ta shiga bayan motaba kusa da boss, baima taɓa bata wannan
damarba koda a fuskane, idan har kaga wani ya zauna a kusa da shi to lallai sai dai
cikin su Aliyu ne, amma yau abin mamaki sai gashi shi da kansa yasa hannu ya buɗema
yarinya ƙarama murfin mota, ya kuma bata lasisin zama a gefensa, ‘Anya kuwa?’ ya
ayyana akan laɓɓansa yana mai satar kallonsu ta mirror.
Ita kanta rose a kume take da mamaki, ita duk zatonta wani abun zai saka
yarinyar, b

ata kawo a ranta wannan abar zuwan jiya hukumarsu har tanada lasisin shiga cikinsu
ba, balle harma ta shiga motar da boss yake ciki, a kusa da shima, shi da kansa ma
ya bata lasisin zaman, abinda ita bai taɓa bata fuska a kaiba, ko zaman gaban motar
da yakema sai ya gadama yake barintayi koda taso hakan kuwa, idan ko bata mantaba
wannan itace shekara ta bakwai cif tare da shi tana aiki a ƙarƙashin group ɗinsa,
‘To mi hakan ke nufi?’ tayi tambayar a zuciyarta.
Shi kansa Jawaad mamakin kan nasa yake, amma da yake shi kogine babu mai
gane gabansa balle bayansa sai bai nuna koda a fuskaba, hasalima tunda suka fice
daga station ɗin kansa na duƙene yana danna tab.. Da alama wani abun yakeyi, sai
dai ƙamshin turaren bilkisu duk ya addabi hancinsa.
Kowa da abinda yake kissimawa ransa har suka iso inda yake buƙata, gimba ya
samu waje yay fakin, babu wanda yay yunƙurin buɗe motar a cikinsu balle ai tunanin
fita, duk suna jiran umarni daga garesa. Shiko yay burus tamkar baiji motar ta
tsayaba, sai faman danne-dannensa yake cigaba dayi a tab ɗin.

Sosai zaman ya gundureni, ba komai ya jawo hakanba sai matsuwar da


zuciyata ta samu saboda kusancin dana samu da shi tare da lokaci mai tsayi da hakan
bai taɓa faruwa ba, da gefen ido na saci kallonsa, sanye yake da wandon jeans kalar
bulu, sai t-shirt fara, ta kwanta a jikinsa luf, dan yanda ƙirarsa ta bayyana ta
cikakken mutum mai motsa jiki kawai ya isa baka amsa, dogon hannu gareta, amma ya
tattareshi sama ya koma iyakar gwiwar hannun, sai agogon fata baƙi mai azabar ƙyau
a tsintsiyar hannunsa da gashi ke kwance na alamar jin daɗi, na sauke idanuna bisa
yatsansa dake cakalar tab ɗin, sanye yake da zoben azurfa mai tambarin stone babba
tamkar diamond, da gani kasan zoben zaiyi tsada koda ba'a faɗa makaba........
“Gimba ka tabbatar nanne wajen?”.
Maganarsa ta katse min dogon nazarin dana tafi na babu gaira babu dalili.
“Eh wlhy boss nanne, kuma wannan shine dai-dai lokacin da a kullum yake
zuwa cin abincin safe shi da abokin nashi, a yanzu haka kuma inada tabbacin abokin
nasa na cikin wajen, nanda mintuna ƙalilan zai iya fitowa”.
Uffan bai ceba, ya kuma cigaba da sabgarsa tamkar bashine yay tambayar aka
bashi amsaba, a fuska dai baiyi kama da miskiliba, abinda kawai na fassara halayyar
wannan mutumin shine Ɗan wulaƙanci ne lamba ɗaya kuwa, babu wanda ya sake magana
tsahon wasu mintuna, bansan mi sauran sukeba, ni dai ina takure ne jikin ƙofa idona
a waje ina kallon shiga da fitar mutanen dake fitowa a cikin wajen cin abincin
(Restaurant), kasantuwar gilashin motar mai duhune nasan babu mai ganinmu, sai dai
mu mu gansa, hakan ya sakani baje idanuna nake kallon komai daki-daki.
“Yauwa boss ga shinan ya fito” gimba ya faɗa da sauri yana nuna ƙofar shiga
da fita na gidan abincin. Nidai kallon wajen nayi, shikam ko motsi baiyiba, bai
kuma ɗago ya kalli abinda drivern ya nunaba, sai cewa da yay “Rose! Kibi wancan
mutumin, duk yanda zakiyi kiyi magana ta shiga tsakaninku, magana kuma irin wadda
zata iya zama mai kusanci”.
“Okey boss” ta amsa da sauri tana buɗe motar ta fice, sai lokacinne naga ya
ɗago kansa ya kalli wajen, ba tare da ya sauke gilashin motarba, “Gimba ka tabbatar
ka ɗaukesu a hoto mai motsi” yay maganar idonsa a kansu.
Saurin amsawa drivern yayi, tare da buɗe motar ya fice da sauri. Gabana ya
faɗi dan ganin an barni daga ni sai shi a motar, sai dai nayi ƙoƙarin kamewa gudun
karna zubda darajata da akasan ɗiya mace mai tarbiyya da ita, kallonsu na cigaba
dayi kamar yanda shima na fahimci hankalinsa na kansu.
Muna kallo rose ta bigi saurayin da ya fito daga wajen cin abincin yana
latsa waya, wayar hannunsa ta faɗi, kusan a tare suka duƙa domin ɗauka, bakin rose
ɗin na motsawa, sai dai mu bamajin mi take faɗa, saurayinne yay murmushi suka miƙe
tare bayan ita ta samu nasarar tattara wayarsa data tarwatse a hannunta, magana
yake mata tana bashi amsa da murmushi saman fuskarta, sai dai shima bamajinsa, ta
miƙa masa wayar tana faɗaɗa murmushin fuskarta tamkar yanda shima yake faɗaɗa
nashi, bai amshi wayarba

sundai cigaba da magana, sai kuma mukaga suna ƙyalƙyata dariya a tare, hanya ya
nuna mata alamar suje, babu musu kuwa tabi umarninsa, tana gaba yana biye da ita
har wajen wata Blue ɗin mota, shine ya buɗe mata ta shiga ta zauna sannan shima ya
buɗe ya shiga sashen mai tuƙi, munata kallonsu har suka bar harabar restaurant
ɗin......
Numfashi ya sauke a hankali yana ɗauke idanunsa da ga wajen, hakan ya sakani
nima sauke nawa a ɓoye ina gyara zama cikin alamar takura, addu'ata da fatana bai
wuce drivern ya dawo cikin motarba kona samu sauƙi, babban fatana kuma yace na koma
gaba inda rose ta tashi, sai dai har tsahon mintuna biyar da barin su rose gidan
abincin baiko motsaba balle ya kalleni, saima kansa da ya kwantar jikin sit ya
lumshe idanu, “Ƙil!-ƙill!!” tab dinsa tai motsi alamar shigowar saƙo, bai motsaba,
hakan yasa mamaki ya kamani......
“Ɗauki ki duba mi tace?” ya faɗa ba tare da ya motsaba. Gabana ya faɗi, dan
nadai fahimci dani yake, kuma yana nufin tab.. Ɗin tasa zan ɗauka, ganin bai sake
maganaba ne ya sakani kallonsa, a ɗarare nace, “Dani kake sir?”.
“A'a da kaina nake” ya faɗa a daƙile......
Kafinma ya rufe baki na kai hannu na ɗauki tab ɗin da ya ajiye a tsakkiyarmu,
gabana sai wata irin faɗuwa yake tamkar zan haɗiye zuciyata a cikin bakina,
madannin na danna ta kawo haske, wani haɗaɗɗen hotonsa ya bayyana, duk da son
kallon hoton da naji ya tsargamin hakan baisa na tsayaba, saima mamakin ganin babu
lock a jikin tab din ne ya kamani, naja hoton yay sama kawai, a take apps da yawa
suka bayyana, baza ido na shigayi wajen neman messeges app, da ƙyar na tsaida
hankalina na ganosa, ina buɗewa kuwa da sunan rose na fara cin karo, na buɗe saƙon
nata, abinda ta turo bai shige kalmomi hamsin ba. “boss ya buƙaci nabisa, duk
abinda ake ciki zakaji daga gareni”.
Cikin ɗan rawar baki nakaranto masa kamar yanda ta rubuto da harshen
turanci, bai motsaba, bai kuma tanka mani ba, hakan yasani ajiye tab ɗin ina mai
satar kallonsa, sai da ya ɓata lokaci kafin ya jehomin tambaya.
“Ya sunanki?”.
‘Ikon ALLAH’ na faɗa a raina kafin na bashi amsa da, “Bilkisu Adam makaho”.
Yanda ya buɗe idanu da sauri a kaina ba ƙaramin firgitani yay ba, mayun
idanunsa masu saka tsigar jikina tashi ya dasamin, bansan miya bashi mamakiba,
sunan nawane? Kokuwa na babana? Kokuwa makahon dana ambata a ƙarshe?. bansan
amsarba, bani da ƙwarin gwiwar tambayarsa kuma. Tsahon minti ɗaya da sakanni yana
kallona kafin ya janye idanunsa yana motsa baki tamkar mai son cewa wani abu,ni dai
ta wutsiyar ido nake kallonsa shi da jin kansa.
Baice dani komaiba ya buɗe motar ya fita, ajiyar zuciya na sauke, dan fitar
tasa sai naji kamar ya bani wani ƙaton filin cin karena babu babbaka ne.......
“Ko sai an fiddoki?”. Furucinsa ya daki kunnena, da azama na buɗe murfin na
fice nima, gani nai ya wani zubomin idanu, bansan mi yake nazartaba daga gareni,
sai jefani a ruɗanin zuciya dana takurar kaifin idanunsa da yayi, hakan yaja nai
ƙasa da kaina dan bazan jura kallonba.
Takunsa kawai naji alamar ya matsa daga kusa dani, na saci kallonsa, sai
naga yana ƙokarin ciro abu daga cikin but ɗin motar da ya buɗe, nufonin da yayne ya
sani saurin ɗauke idona, ya miƙomin farar coat ta mata da tsayinta zai iya kaiwa
gwiwa, ban musaba na amsa, sai dai ina buƙatar ƙarin bayani, “Saka” ya faɗa yana
wuceni.
Sosai naketa mamaki, na warware rigar na saka a jikina saman Uniform ɗin dana
sanya, sai ya zam rigar ta ɓoye bayyanar ni wacece, baƙin wandon kawai ake iya gani
ta ƙasa, daga sama kuwa farin baby hijjab ɗinane ya bayyana, sai rigar ta fiddamin
da wani tsari daban daya bayyanar da sirrintaccen kwarjinina da wasu ke iya ambata
da ƙyawu. Bai cemin komaiba yay gaba na bisa a baya, dan zuwa yanzu kam na fara
fahimtar hallayarsa da hanyoyin maganin zama da shi.
Sai da muka gabato shiga ƙofar wajen sannan ya tsaya muka daidaita tafiya,
ƙasa-ƙasa na tsinkayi muryarsa yana magana.
“Ki kula sosai, sannan ki tabbatar da yanayinki ya canja tamkar munada
dangantaka, idan kikamin shirmen da aikina ya buɗe

lallai sai kinyi nadamar hakan”.


Sosai maganganunsa suka tsirgamin zuciya, dan kuwa ban gama fahimtar
ma'anarsu ba balle manufarsu har muka ƙarasa shiga wajen.
Wajen yay bala'in haɗuwa, daga gani kasan masu abokan magana a aljihune
kawai keda hurumin shigarsa, dan danan akai mana tarba ta mutuntawa, yanda ya
ƙawata fuskarsa da murmushi ne ya ɗauren kai, hakan yasani nima aro irin basajar
tasa na yafama kaina ina murmushin, ɗaya daga cikin yaran wajenne ya nuna mana
wajen zama, bayan mun zauna yake tambayarmu komi muke buƙata.
Boss ya juyo yana kallona fuskarsa shinfiɗe da wani murmushin da ya kusa
zautani, “My princess! Mi kike buƙata?”.
Wata masifar harbawa zuciyata tayi, kaɗan ya rage ban fallasamu ba, nai azamar
haɗiye zuciyata dake niyyar fitowa ta baki saboda salon da yay amfani wajen kiran
sunana da yanayin fitar sautin, da ƙyar na iya dai-daita kaina nai wani farin da
bansan na iyaba da idanu, ina wani narke murya nace, “Duk abinda ka zaɓa mana yayi
my king”.
Ɗauke idanunsa yay daga kaina, har zuwa yanzun fuskarsa ɗauke da murmushin da
ya fidda lotsar dimples ɗinsa masu ɗaukar hankali, ya duba waiter ɗin yana bashi
umarnin ya bashi list ɗin abinda suke da shi ya duba.
Da girmamawa ya amsa yana barin wajen, saurin yin ƙasa nai da idanuna ganin ya
maido kallonsa gareni, murya ƙasa-ƙasa yace, “Ina sake gargaɗinki a karo na biyu”.
Kaina na jijjiga masa ina saurin gyara yanayina. Sallama wata matashiyar
budurwa taimana saɓanin wanda yazo ɗazun, sanye take da Uniform ɗin wajen itama,
cikin girmamawa ta ajiye goran ruwa biyu da kofuna dake saman tire ƙarami, kafin ta
miƙa masa ɗan littafi dake a hannunta. Amsa yay yana dubawa, tare da yin alama da
pen ɗin data haɗa masa da shi akan duk abinda muke buƙata, baifi sakan sha biyarba
ya miƙomin littafin yana fadin, “Duba yayi?”.
Amsa nayi ina kuma matse nutsuwata, nai nazarin duk abinda ya zaɓadin kafin na
ɗago ina murmushi, cikin salon da bansan nayiba na ɗaga masa gira ɗaya da juya
ƙwayar idona kaɗan alamar yayi.
Idanunsa ya lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana sakin wani lallausan
murmushi da yafi na ɗazu.
‘Innalillahi....’ Na iya ambata ina saurin maida fitsarindake neman kufcemin.
Tana barin wajen ya kalleni da sauri, murya ya rage ƙasa sosai, wanda yake
nesa damu zai ɗauka soyayya mukeyi, maganar da ya faɗamince ta sakani jinjina masa
kai da sauri, ina kuma murmushi, badan tanada alaƙa da murmushin nawa bane, sai dan
kawai barin murmushin akan fuskar tawa ya zama tilas saboda kiyaye
gargaɗinsa...........✍

🙄saura kuma ai gulmar Jay😏

ALLAH ka gafarta iyayenmu😭🙏🏻Bilyn Abdull 📚:


😂🤣😂🤣😆😆😆Kunsan miyasa nake dariyarnan? Akan yanda kuke ganin kamar bily tsoron Jay
takeyi, dukfa halin da take shiga shiba fahimta yakeba, hasalima kallon miskila
idan kun lura yake mata, akwai masu samun kansu a irin yanayin bily akan wani ko
wata, sai daga baya suke fahimtar dalilin shigarsu irin wannan halin, itama bily
lokaci zai warware mata komai har muma mu sami amsa, ina muku fatan alkairi aduk
inda kuke, sosai Comments naku na sakani nishadi da sani typing kodama ban niyyaba.
I love you wujiga-wujiga irin trillions ɗinnan🤸🏼🤸🏼🤸🏼 😍😘😍😘😍😘🤗.

Page 6

Ko kaɗan ban fahimci dani yakeba, musamman dana waiga naga rose data fito
daga office ɗinsa a bayanna, wani kallo naga ta watsamin mai kama da takaicin tabi
bayansa. Numfashi na sauke mai nauyi na shafa ƙirjinna dai-dai saitin zuciyarta
dake harbawa da sauri-sauri, duk da na fahimci kallon da rose tai mani sai hakan
bai dameni ba, dan bata ita nakeba. Nima fita nai daga wajen, na fito ainahin
harabar station ɗin domin nufar sashenmu.
“Ɗi! Ɗi! Ɗi!!” gimba ya danna mata horn kamar yanda Jay ya bashi umarni.
Duk da naji horn ɗin hakan baisa na fahimci da ni akeba, saboda idan
akai dubi da sauran jami'ai irina daketa kaikawo a harabar wajen, kowa da
hidimarsa.
“K! Wace irin daƙiƙiyace da baƙya fahimtane? A haka kike tunanin zama jami'ar
tsaron al'umma!!?”
Maganar Rose a tsawace ta shiga dodon kunnena ina gab da shiga lungu da zai
sadani da office ɗinmu. Da sauri na juyo, idona ya sauka akan rose dake huci da
jifana da kallon takaici mai nunin tsana. Duk da naji zafin kalaman datai amfani
dasu a gareni sai na danne saboda tana sama da ni, a ladabce nace, “Kiyi haƙuri
maa! Bansan dani kike ba”.
Tsaki rose ta buga, tare da juyawa tabarni a wajen, wani jami'i dake tsaye
kusa damu ya kalleni da tausayawa, dan shi dai yarinyar tunda tazo station ɗin
ɗabi'unta birgesa sukeyi, ganin ban fahimci manufar rose ba sai yay min fassara
akan nabi bayanta maybe kirana akeyi.
Godiya nai masa, kafin nabi bayanta cikin nutsuwata, sam ban iya sauri ko
rikita kaina a tafiya ba koda kuwa a tsorace nake, a yanzunma duk da zuciyata na
cike da tunani da baƙin cikin abinda tamin ban rikita kainaba a yayin bin bayanta,
can na hangota jikin wata farar mota mai ƙyau da ɗaukar hankali, na cigaba da
takawa a nutse gareta, ina isa jikin motar ita kuma tana buɗe gaba ta shige, hakan
sai ya sakani a duhu, dan bansan kuma wajenwa zanje ba. Saitin inda take na ƙarasa,
na ɗan risina yanda zata ganni ina faɗin, “Gani maa!”.
Kafin ta bani amsa ƙofar murfin baya naga ta buɗe, ita da drivern naga duk sun
kalli bayansu, hakanne ya sakani kallon murfin ta waje nima, muryar drivern ta
katse min tunani, “Ki shiga” ya faɗa yana nunamin bayan.
Duk da na shiga ruɗani, ga harbawar da ƙirjina keyi hakan bai hanani bin
umarninsaba, koda wasa ban kalli waye a bayanba, na shiga kamar yanda aka umarceni,
sai da na zauna ne wani mayen ƙamshi ya samu cikakkiyar damar surɗaɗawa a ƙofofin
hancina, da sauri nai ƙoƙarin kallon gefena, gabana ya faɗi dan ganin wanda banyi
zatoba, fuskarsa babu alamar wasa kamar yanda na gansa yanzu da mukai karo.....
“Sai kin gama kallona zaki rufe ƙofar ne?” muryarsa ta daki dodon kunnena
babu zato, kaina na girgiza da sauri ina tattaro busashen yawun bakina da ƙyar na
haɗiye, tare da jawo murfin motar na rufe. Nama rasa yanda zan fassara wannan
al'amarin sam, gashi yanayin dana tsinci kaina ya hana mani damar yin nazarin daya
dace da hakan.

Ɓangaren Rose da Gimba kuwa mamakine fal a rayukansu, gimba shaidane akan
bai taɓa ganin rose ta shiga bayan motaba kusa da boss, baima taɓa bata wannan
damarba koda a fuskane, idan har kaga wani ya zauna a kusa da shi to lallai sai dai
cikin su Aliyu ne, amma yau abin mamaki sai gashi shi da kansa yasa hannu ya buɗema
yarinya ƙarama murfin mota, ya kuma bata lasisin zama a gefensa, ‘Anya kuwa?’ ya
ayyana akan laɓɓansa yana mai satar kallonsu ta mirror.
Ita kanta rose a kume take da mamaki, ita duk zatonta wani abun zai saka
yarinyar, b

ata kawo a ranta wannan abar zuwan jiya hukumarsu har tanada lasisin shiga cikinsu
ba, balle harma ta shiga motar da boss yake ciki, a kusa da shima, shi da kansa ma
ya bata lasisin zaman, abinda ita bai taɓa bata fuska a kaiba, ko zaman gaban motar
da yakema sai ya gadama yake barintayi koda taso hakan kuwa, idan ko bata mantaba
wannan itace shekara ta bakwai cif tare da shi tana aiki a ƙarƙashin group ɗinsa,
‘To mi hakan ke nufi?’ tayi tambayar a zuciyarta.
Shi kansa Jawaad mamakin kan nasa yake, amma da yake shi kogine babu mai
gane gabansa balle bayansa sai bai nuna koda a fuskaba, hasalima tunda suka fice
daga station ɗin kansa na duƙene yana danna tab.. Da alama wani abun yakeyi, sai
dai ƙamshin turaren bilkisu duk ya addabi hancinsa.
Kowa da abinda yake kissimawa ransa har suka iso inda yake buƙata, gimba ya
samu waje yay fakin, babu wanda yay yunƙurin buɗe motar a cikinsu balle ai tunanin
fita, duk suna jiran umarni daga garesa. Shiko yay burus tamkar baiji motar ta
tsayaba, sai faman danne-dannensa yake cigaba dayi a tab ɗin.

Sosai zaman ya gundureni, ba komai ya jawo hakanba sai matsuwar da


zuciyata ta samu saboda kusancin dana samu da shi tare da lokaci mai tsayi da hakan
bai taɓa faruwa ba, da gefen ido na saci kallonsa, sanye yake da wandon jeans kalar
bulu, sai t-shirt fara, ta kwanta a jikinsa luf, dan yanda ƙirarsa ta bayyana ta
cikakken mutum mai motsa jiki kawai ya isa baka amsa, dogon hannu gareta, amma ya
tattareshi sama ya koma iyakar gwiwar hannun, sai agogon fata baƙi mai azabar ƙyau
a tsintsiyar hannunsa da gashi ke kwance na alamar jin daɗi, na sauke idanuna bisa
yatsansa dake cakalar tab ɗin, sanye yake da zoben azurfa mai tambarin stone babba
tamkar diamond, da gani kasan zoben zaiyi tsada koda ba'a faɗa makaba........
“Gimba ka tabbatar nanne wajen?”.
Maganarsa ta katse min dogon nazarin dana tafi na babu gaira babu dalili.
“Eh wlhy boss nanne, kuma wannan shine dai-dai lokacin da a kullum yake
zuwa cin abincin safe shi da abokin nashi, a yanzu haka kuma inada tabbacin abokin
nasa na cikin wajen, nanda mintuna ƙalilan zai iya fitowa”.
Uffan bai ceba, ya kuma cigaba da sabgarsa tamkar bashine yay tambayar aka
bashi amsaba, a fuska dai baiyi kama da miskiliba, abinda kawai na fassara halayyar
wannan mutumin shine Ɗan wulaƙanci ne lamba ɗaya kuwa, babu wanda ya sake magana
tsahon wasu mintuna, bansan mi sauran sukeba, ni dai ina takure ne jikin ƙofa idona
a waje ina kallon shiga da fitar mutanen dake fitowa a cikin wajen cin abincin
(Restaurant), kasantuwar gilashin motar mai duhune nasan babu mai ganinmu, sai dai
mu mu gansa, hakan ya sakani baje idanuna nake kallon komai daki-daki.
“Yauwa boss ga shinan ya fito” gimba ya faɗa da sauri yana nuna ƙofar shiga
da fita na gidan abincin. Nidai kallon wajen nayi, shikam ko motsi baiyiba, bai
kuma ɗago ya kalli abinda drivern ya nunaba, sai cewa da yay “Rose! Kibi wancan
mutumin, duk yanda zakiyi kiyi magana ta shiga tsakaninku, magana kuma irin wadda
zata iya zama mai kusanci”.
“Okey boss” ta amsa da sauri tana buɗe motar ta fice, sai lokacinne naga ya
ɗago kansa ya kalli wajen, ba tare da ya sauke gilashin motarba, “Gimba ka tabbatar
ka ɗaukesu a hoto mai motsi” yay maganar idonsa a kansu.
Saurin amsawa drivern yayi, tare da buɗe motar ya fice da sauri. Gabana ya
faɗi dan ganin an barni daga ni sai shi a motar, sai dai nayi ƙoƙarin kamewa gudun
karna zubda darajata da akasan ɗiya mace mai tarbiyya da ita, kallonsu na cigaba
dayi kamar yanda shima na fahimci hankalinsa na kansu.
Muna kallo rose ta bigi saurayin da ya fito daga wajen cin abincin yana
latsa waya, wayar hannunsa ta faɗi, kusan a tare suka duƙa domin ɗauka, bakin rose
ɗin na motsawa, sai dai mu bamajin mi take faɗa, saurayinne yay murmushi suka miƙe
tare bayan ita ta samu nasarar tattara wayarsa data tarwatse a hannunta, magana
yake mata tana bashi amsa da murmushi saman fuskarta, sai dai shima bamajinsa, ta
miƙa masa wayar tana faɗaɗa murmushin fuskarta tamkar yanda shima yake faɗaɗa
nashi, bai amshi wayarba

sundai cigaba da magana, sai kuma mukaga suna ƙyalƙyata dariya a tare, hanya ya
nuna mata alamar suje, babu musu kuwa tabi umarninsa, tana gaba yana biye da ita
har wajen wata Blue ɗin mota, shine ya buɗe mata ta shiga ta zauna sannan shima ya
buɗe ya shiga sashen mai tuƙi, munata kallonsu har suka bar harabar restaurant
ɗin......
Numfashi ya sauke a hankali yana ɗauke idanunsa da ga wajen, hakan ya sakani
nima sauke nawa a ɓoye ina gyara zama cikin alamar takura, addu'ata da fatana bai
wuce drivern ya dawo cikin motarba kona samu sauƙi, babban fatana kuma yace na koma
gaba inda rose ta tashi, sai dai har tsahon mintuna biyar da barin su rose gidan
abincin baiko motsaba balle ya kalleni, saima kansa da ya kwantar jikin sit ya
lumshe idanu, “Ƙil!-ƙill!!” tab dinsa tai motsi alamar shigowar saƙo, bai motsaba,
hakan yasa mamaki ya kamani......
“Ɗauki ki duba mi tace?” ya faɗa ba tare da ya motsaba. Gabana ya faɗi, dan
nadai fahimci dani yake, kuma yana nufin tab.. Ɗin tasa zan ɗauka, ganin bai sake
maganaba ne ya sakani kallonsa, a ɗarare nace, “Dani kake sir?”.
“A'a da kaina nake” ya faɗa a daƙile......
Kafinma ya rufe baki na kai hannu na ɗauki tab ɗin da ya ajiye a tsakkiyarmu,
gabana sai wata irin faɗuwa yake tamkar zan haɗiye zuciyata a cikin bakina,
madannin na danna ta kawo haske, wani haɗaɗɗen hotonsa ya bayyana, duk da son
kallon hoton da naji ya tsargamin hakan baisa na tsayaba, saima mamakin ganin babu
lock a jikin tab din ne ya kamani, naja hoton yay sama kawai, a take apps da yawa
suka bayyana, baza ido na shigayi wajen neman messeges app, da ƙyar na tsaida
hankalina na ganosa, ina buɗewa kuwa da sunan rose na fara cin karo, na buɗe saƙon
nata, abinda ta turo bai shige kalmomi hamsin ba. “boss ya buƙaci nabisa, duk
abinda ake ciki zakaji daga gareni”.
Cikin ɗan rawar baki nakaranto masa kamar yanda ta rubuto da harshen
turanci, bai motsaba, bai kuma tanka mani ba, hakan yasani ajiye tab ɗin ina mai
satar kallonsa, sai da ya ɓata lokaci kafin ya jehomin tambaya.
“Ya sunanki?”.
‘Ikon ALLAH’ na faɗa a raina kafin na bashi amsa da, “Bilkisu Adam makaho”.
Yanda ya buɗe idanu da sauri a kaina ba ƙaramin firgitani yay ba, mayun
idanunsa masu saka tsigar jikina tashi ya dasamin, bansan miya bashi mamakiba,
sunan nawane? Kokuwa na babana? Kokuwa makahon dana ambata a ƙarshe?. bansan
amsarba, bani da ƙwarin gwiwar tambayarsa kuma. Tsahon minti ɗaya da sakanni yana
kallona kafin ya janye idanunsa yana motsa baki tamkar mai son cewa wani abu,ni dai
ta wutsiyar ido nake kallonsa shi da jin kansa.
Baice dani komaiba ya buɗe motar ya fita, ajiyar zuciya na sauke, dan fitar
tasa sai naji kamar ya bani wani ƙaton filin cin karena babu babbaka ne.......
“Ko sai an fiddoki?”. Furucinsa ya daki kunnena, da azama na buɗe murfin na
fice nima, gani nai ya wani zubomin idanu, bansan mi yake nazartaba daga gareni,
sai jefani a ruɗanin zuciya dana takurar kaifin idanunsa da yayi, hakan yaja nai
ƙasa da kaina dan bazan jura kallonba.
Takunsa kawai naji alamar ya matsa daga kusa dani, na saci kallonsa, sai
naga yana ƙokarin ciro abu daga cikin but ɗin motar da ya buɗe, nufonin da yayne ya
sani saurin ɗauke idona, ya miƙomin farar coat ta mata da tsayinta zai iya kaiwa
gwiwa, ban musaba na amsa, sai dai ina buƙatar ƙarin bayani, “Saka” ya faɗa yana
wuceni.
Sosai naketa mamaki, na warware rigar na saka a jikina saman Uniform ɗin dana
sanya, sai ya zam rigar ta ɓoye bayyanar ni wacece, baƙin wandon kawai ake iya gani
ta ƙasa, daga sama kuwa farin baby hijjab ɗinane ya bayyana, sai rigar ta fiddamin
da wani tsari daban daya bayyanar da sirrintaccen kwarjinina da wasu ke iya ambata
da ƙyawu. Bai cemin komaiba yay gaba na bisa a baya, dan zuwa yanzu kam na fara
fahimtar hallayarsa da hanyoyin maganin zama da shi.
Sai da muka gabato shiga ƙofar wajen sannan ya tsaya muka daidaita tafiya,
ƙasa-ƙasa na tsinkayi muryarsa yana magana.
“Ki kula sosai, sannan ki tabbatar da yanayinki ya canja tamkar munada
dangantaka, idan kikamin shirmen da aikina ya buɗe

lallai sai kinyi nadamar hakan”.


Sosai maganganunsa suka tsirgamin zuciya, dan kuwa ban gama fahimtar
ma'anarsu ba balle manufarsu har muka ƙarasa shiga wajen.
Wajen yay bala'in haɗuwa, daga gani kasan masu abokan magana a aljihune
kawai keda hurumin shigarsa, dan danan akai mana tarba ta mutuntawa, yanda ya
ƙawata fuskarsa da murmushi ne ya ɗauren kai, hakan yasani nima aro irin basajar
tasa na yafama kaina ina murmushin, ɗaya daga cikin yaran wajenne ya nuna mana
wajen zama, bayan mun zauna yake tambayarmu komi muke buƙata.
Boss ya juyo yana kallona fuskarsa shinfiɗe da wani murmushin da ya kusa
zautani, “My princess! Mi kike buƙata?”.
Wata masifar harbawa zuciyata tayi, kaɗan ya rage ban fallasamu ba, nai azamar
haɗiye zuciyata dake niyyar fitowa ta baki saboda salon da yay amfani wajen kiran
sunana da yanayin fitar sautin, da ƙyar na iya dai-daita kaina nai wani farin da
bansan na iyaba da idanu, ina wani narke murya nace, “Duk abinda ka zaɓa mana yayi
my king”.
Ɗauke idanunsa yay daga kaina, har zuwa yanzun fuskarsa ɗauke da murmushin da
ya fidda lotsar dimples ɗinsa masu ɗaukar hankali, ya duba waiter ɗin yana bashi
umarnin ya bashi list ɗin abinda suke da shi ya duba.
Da girmamawa ya amsa yana barin wajen, saurin yin ƙasa nai da idanuna ganin ya
maido kallonsa gareni, murya ƙasa-ƙasa yace, “Ina sake gargaɗinki a karo na biyu”.
Kaina na jijjiga masa ina saurin gyara yanayina. Sallama wata matashiyar
budurwa taimana saɓanin wanda yazo ɗazun, sanye take da Uniform ɗin wajen itama,
cikin girmamawa ta ajiye goran ruwa biyu da kofuna dake saman tire ƙarami, kafin ta
miƙa masa ɗan littafi dake a hannunta. Amsa yay yana dubawa, tare da yin alama da
pen ɗin data haɗa masa da shi akan duk abinda muke buƙata, baifi sakan sha biyarba
ya miƙomin littafin yana fadin, “Duba yayi?”.
Amsa nayi ina kuma matse nutsuwata, nai nazarin duk abinda ya zaɓadin kafin na
ɗago ina murmushi, cikin salon da bansan nayiba na ɗaga masa gira ɗaya da juya
ƙwayar idona kaɗan alamar yayi.
Idanunsa ya lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana sakin wani lallausan
murmushi da yafi na ɗazu.
‘Innalillahi....’ Na iya ambata ina saurin maida fitsarindake neman kufcemin.
Tana barin wajen ya kalleni da sauri, murya ya rage ƙasa sosai, wanda yake
nesa damu zai ɗauka soyayya mukeyi, maganar da ya faɗamince ta sakani jinjina masa
kai da sauri, ina kuma murmushi, badan tanada alaƙa da murmushin nawa bane, sai dan
kawai barin murmushin akan fuskar tawa ya zama tilas saboda kiyaye
gargaɗinsa...........✍
🙄saura kuma ai gulmar Jay😏

ALLAH ka gafarta iyayenmu😭🙏🏻Bilyn Abdull 📚:


Barka da juma'a.

Page 7

.................Mintuna kaɗan budurwar ta dawo da tire babba a hannu, wanda aka


jero abubuwan da muka buƙata a kansa.
Tana ƙoƙarin ajiyewane Jay ya miƙa hannu zai ɗauki ruwan da aka fara
kawo masu, a salon da babu wanda ya isa fahimtasa har bily bata kulaba ya tanƙwaɓi
tiren ya suɓuce, jikake “Tarats!!! Tass! Tatass!!” kwanikan da suka zube na
fashewa, abinda ke cikinsu gaba ɗaya sun koma jikinsu sun wankesu, duk jikinsu ya
ɓaci daga shi har bily da bata san mafari ba, a take duk hankalin mutanen dake kusa
dasu ya dawo kansu.
Na ɓata fuska saboda harga ALLAH banji daɗin yanda jikina ya ɓaciba.
Cikin langwaɓe kai na kallesa kamar zanyi kuka.
Da ƙyar Jay yay ƙoƙarin haɗiye dariyar dake neman kufce masa saboda yanda
Bily tayi fuska kamar zata fasa ihu, ga mai da yay tsalle harkan fuskarta sai naso
yake.
A fusace na miƙe saboda ganinma dariya yake neman yimin, dan da gaske haushi
naji har raina, maimakon ya mata faɗa amma kuma tsabar wulaƙanci yake neman yimin
dariya a cikin mutane, bamma san sanda na fara zazzaga mata masifa akan tayi
hakanne da gangan ba, yanda ta rikice ba ƙaramin tausayi ta baniba, amma kuma uwar
mi take kallo da zata wankemu haka?, shima jinake kamar na juya na talle masa ƙeya
yasin.
Jawaad ya tsaya kawai yana kallon bakin Bily dake masifa, babu shiri
murmushi ya suɓuce masa, ganin tamkar abin nata da gaskene shima sai ya miƙe, cikin
son maidota hayyacinta ya nema riƙo hannunta, amma sam taƙi yarda, dan danan wasu
ma'aikatan nasu sukazo, da alama suɗin manyane, haƙuri suketa bamu amma naƙi
saurarensu, daga ƙarshema nai ficewata, shikuma yay azamar biyoni yana faɗin,
“princess! Princess! Please ki tsaya mana”.
Ƙo juyowama banyiba na nufi motarmu na buɗe zan shige, saurin riƙe murfin yayi
yasha gabana alamar hanani shiga motar, ya wani marairaice yana lallashina, wlhy da
kunsan yanda zuciyata ke harbawa sanda muke a wannan yanayin da kun bala'in
tausayamin, a haka budurwar da wasu ma'aikatan wajen suka iso suka taddamu, haƙurin
suka cigaba da bamu, sai da muka ɗan garasu da kalamun cewar bazamu sake zuwa
wajenba tunda basusan kimar Customers ba kafin na nuna na haƙura da ƙyar, dan zuwa
yanzu na dawo hankalina akan shirinmu.
Sun buƙaci mu koma wajen a bamu wani abincin amma na tubure akan bazan koma
ba, sai dai a haɗo mana takeaway, ba musu suka amince da bukatata, ganin sunbar
wajen ne ya sani sauke ajiyar zuciya ina matsawa baya saboda kusancin da muka samu
ni da shi neman karya ƙwarin gwiwa da nake bama kaina ya keyi, gashi yay masifar
tsareni da idanunsa.
Shima matsawa yayi, ya nuna min mota alamar na shiga yana zubamin harara,
“saurin shigewar nayi kuwa, ya rufemin murfin ya zagaya ɗayan ɓangaren, da sauri
gimba dake bayanmu tsaye yana kallon dramar tamu ya buɗe masa, hanasa rufewa yayi,
saima ya zauna ƙafafunsa duka a waje. A haka budurwar ta dawo ɗauke da takeaway ɗin
da muka buƙata, gimba ya amsa ledojin, shi kuma ya miƙa mata atm card ɗinsa tare da
wata takarda yana magana ƙasa-ƙasa, “Saboda baƙwason ya tona muku asiri kuka
kasheshi?”.
A firgice budurwar ta kalli Jay, sai kuma ta hau waige-waige jikinta sai tsuma
yakeyi.
Ya sake faɗin, “Ki daina ɓatama kanki lokaci, akwai address ɗin inda zaki
sameta (ya nuna bily) a jikin takardar nan ranar lahadi, yarage naki kizo ko kiƙi
zuwa, sauran bayani mahaifinki zanyimawa”.
Sake rikicewa tayi, jikinta sai wata masifar tsuma yakeyi. Yanda taketa
kallonsa a firgicene ya sakani tabbatar da maganar bamai daɗi ya faɗa mataba, tabar
wajen da sassarfa, yayinda gimba ya take mata baya domin amso atm ɗin idan sun cire
kuɗinsu.
Wato dai duk yanda nake tunanin aikin nan namu yafi ƙarfin tunanina, irin
wannan makirci haka tamkar wani shirin film.

Gimba bai wani jimaba ya fito da ɗan hanzarinsa, motar shiru tamkar babu
mutum mai numfashi, nidai takurace ta hanani yin ƙwaƙwƙwaran motsi, danma ALLAH ya
soni yanzu a gaba nake ba kamar yanda muka zoba, shiko bansan mi yakeyiba, dan
nakasa kallonsa koda ta mirror ne, abinda ya faru a wajen da

wanda nayi keta dawomin a rai, sai naga kamar na zaƙe da yawa, ko a gidan uwarwama
na samo ƙwarin gwiwar zuba masifar irin haka?’.
Sai da gimba ya tada mota sannan yace, “Boss zamu koma station ne?”.
Shiru bai bashi amsaba har muka fice daga gate ɗin wajen muka hau titi, ni nama
ɗauka ko barci yakeyi, sai jinai ya bashi amsa da,
“A.Y....”
Ban fahimci ma'anar maganarba, amma shi gimban naga kamar ya gane mi yace. Wayata
daketa vibration tun ɗazun na kalla, yah Qaseem ne yanzuma, wannan shine kira na
kusan bakwai kenan, tun muna cikin wajen cin abinci kiransa keta shigowa, sai dai
bansan miyasa nakasa ɗagawa ba, a hankali na sauke ajiyar zuciya jin wayar ta
yanke, kasheta nai baki ɗaya ma, dan bansan dalilin kiranba, idan kuma na ɗaga
bansan mizance masaba, bankuma saniba ko ɗagawar zai iya zama laifi a wajen wanda
muke tare. Isowarmu wani gida mai ƙyau da tsarine ya yanke tunanina, tunda aka buɗe
mana gate muka shigo naketa bama idona abinci nidai, gimba ya tsaida mota ya buɗe
ya fita, ni dai banyi yunƙurin fitarba harshi aka buɗe masa ya fice, akan idona
yabar wajen ya nufi wata ƙofa mai alamar shiga ainahin cikin gidan, na sauke ajiyar
zuciya kaɗan ina lumshe ido, fatana yazam shikenan yace a maidani station.........
Kallon gimba dake bani umarnin shiga nai da sauri, yay murmushi yana sake
maimaitamin, “Ki shiga inji boss”.
Jinai tamkar na fasa ihu, amma bani da ikon cewa ba hakaba, dole na fito ina
sake bin harabar gidan da kallo, gimba ne yaymin jagora har ciki, ‘Masha ALLAH’ na
faɗa akan laɓɓana saboda haɗuwar da falon yayi, babu kowa a ciki sai ƙamshi mai
daɗi dake tashi a cikinsa....
Gimba yace, “Ki shiga nan saiki gyara jikinki”.
Murmushi naɗan masa ina jinjina kaina, na nufi ƙofar raina cike da tsoro da
mamaki, sai faman tambayar kaina nake ko ina matar gidan? Dan naji gidan tsit.
‘Kika sani ko tare suka shige ciki?’ zuciyata ta ayyana min haka, bakina naɗan
taɓe, na tura ƙofar na shiga da sallama. Ɗakine babba, akwai komai na amfani kuma a
ciki, sai dana gama ƙare masa kallo kafin na nufi ƙofar da nake ƙyautata zaton
bayine, bayan na rufe ƙofar sai kuma nai tsaye ina ƙarema kaina kallo ta cikin
madubin dake toilet ɗin, Toni ta inama zan farane? Ni bawasu kayane dani ba, gashi
kayana sun ɓaci sosai, na zare rigar saman da ya bani, wadda kasancewarta fara ta
ɓaci sosai, hakama wandona, amma da yake baƙine shi ba gani akeba, sai ƙamshin miya
da yake da mai dakemin naso a jikine zaisa ka gane ya ɓaci shima sosai, shawarar
cirewa na wanke nayi, dan haka na cireshi a ɗarare.
Ban fahimci kuskurena na jiƙa wandonba sai dana gama wankesa nanfa tunanin
inda zanje na shanya, da kuma ta yanda zanma fita shanyawar tunda bawasu kayanne
daniba yazomin. jinai hawaye sun cika idona, ‘Ni balki naga takaina’ na faɗa a
hankali ina haɗiye kukan dake neman zuwamin. A bayin na shanya wandon na fito ɗaure
da sabon tawul dana gani, na zauna a bakin gadon na rabga tagumi ina addu'ar neman
mafita.
Nai firgigit jin an turo ƙofar kamar a fusace, fuskarta a haɗe ta shigo
hannunta ɗauke da leda yellow mai tambarin M&N, cike da kallon tsana ta miƙamin
ledar, amsa nai nidai cikin girmamawa amma ina mamakin yanda takemin a ƙasan raina.
Juyawa tai zata fice na bita da kallo, sai da ta buɗe ƙofar sannan tace, “Ana
jiranki” kawai ta fice abinta.
Numfashi na sauke a hankali, na buɗe ledar na fidda kayan ciki, wandone da
riga duk baƙaƙe, sai baby hijjab fari irin waɗanda nake sakawa, tashi nai na saka
kayan, sunmin bala'in ƙyau, sai dai inajin kunyar fita a haka sosai, dan sun wani
lafe a jikina dukda dai rigar bata matseniba, bani da zaɓin daya wuce daurewa na
fita a hakan kawai, danma baby hijjab ɗin ya rufemin ƙirji, na maida kayan dana
cire a jikina cikin ledar harda wandon dana jiƙa ɗin, kaina a ƙasa na fito daga
ɗakin, zuciiyata sai harbawa take da sauri-sauri.
Wani iri naji a raina ganin kusan su biyar ne a falon, sai na kumajina a
matuƙar takure musamman saboda kayan dake jikina, ƙarasawa nai cike da aro jarumtar
dole ganin su hankalinsuma ba'a kaina yakeba, sallama nai duk su

ka amsa mani, na gaishesu da girmamawa nanma suka amsa, na kula kamar kallon mamaki
sukemin irin kamar basuyi tunanina ganina a wajenba, hakan sai ya sakani jin wani
iri, na saci kallon dodon nawa, dan tunda na fito baiko ɗaga kai ya kalli sashen da
nakeba, yana zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani basarake, idonsa na bisa takardun
dake hannunsa, shima ya canja kayansa zuwa farin wando da baƙar t-shirt mai gajeren
hannu, rigar ta kwanta masa a jiki, hakan yasa ta fidda ainahinsa na ƙaƙƙarfan
mutum.......
“Bismillah zauna mana”
Oga Hafiz ya katse min satar kallon boss dana shagala yi, kaina na jinjina na zauna
a inda ya nunamin ɗin a ɗarare.

Tun fitowar Bilkisu a idanun Jawaad ne, duk kuma abinda take yana kallonta ta
gefen ido, amma babu wanda zai iya fahinta, idan akai dubi da yanda ya maida dukkan
hankalinsa ga takardar hannunsa, ɗago idanunsa yay yana kallon Aliyu dake danna
lap-top, yace, “Aliy ya buɗe ne?”.
Girgiza kai Aliyun yayi yana guntun tsaki, ya juya masa fuskar lap-top ɗin da
faɗin, “Ni banama zaton yana amfani da accaunt ɗinnan gaskiya, boss wai mizai hana
mu aika wani cikinsu kawai, sai naga haka kamar zaifi komai sauƙi da muzauna a
bayan fage muna wahal da kanmu, tunda bamu da tabbacin yarinyar zata bamu haɗun
kai”.
Kafin Jawaad ya bashi amsa Rose dake gefensa tanata wani cika da batsewa tai
caraf ta amshe zancen, “Boss dabaran Aliyu yayi sosai, kaga sai a aika yarinyarnan
kawai cikinsun”.
Wani mugun kallo da ya bama kowa mamaki a wajen Jawaad ya watsama Rose, sai
kuma ya ɗauke kai batare da yace mata komaiba.
Duk zuba masa ido sukai suji ko zai bama rose amsar maganarta, ni dai
kaina a ƙasa ban ɗagoba inata wasa da yatsun hannuna, na ɗan saci kallon nasa nima
sai naga ya cigaba da duba takardar hannun nasa ma tamkar baisan mi akeba. Tsawon
mintuna bakwai muna a haka kafin muga ya ajiye takardan hannun nasa ya miƙe, wata
ƙofa ya nufa, duk suka sake binsa da kallo harni da nakeyi a munafunce. yana
shigewa duk suka maido dubansu gareni, inaga ganin yanda na takura kaina ne da
ganin kamar bare a cikinsune ya saka oga Jabeer sakarmin murmushi, cikin tsokana
yace, “Anya kuwa wannan ƙanwar tamu ba matsoraciya bace?”.
Karon farko da nai murmushi, na ɗan kallesa na ɗauke idanuna da faɗin, “A'a
Sir”.
Dariya duk sukayi, amma banda Rose da ta ɗauke kai tana taɓe baki.
Oga Aliyu dake danna lap-top har yanzu yace, “To idan ba matsoraciya bace ki
saki jikinki damu, munan duk yayunkine ba surukaiba, minene sunanki?”.
Naɗan kalli sashen da yake fuskata ɗauke da murmushi nace, “Bilkisu Adam
makah..o”.
Na ƙare maganar a hankali saboda yay dai-dai da fitowarsa daga ɗakin daya
shiga, ya ɗoro baƙan jacket saman kayansa, ido muka haɗa, nai saurin janyewa nawa
ina haɗiye murmushin kan fuskata saboda maganar da su Hafiz sukeyi na cewar “Ashe
mai babban sunace, duk mai wannan sunan kuwa jarumace”.
Duk dariya sukayi, amma banda rose da shi da muka sake haɗa ido a bazata,
saurin janye idanuna nayi zuciyata na wata irin harbawa, hanyar ƙofa ya nufa yana
faɗin, “Kumuje” Yana ƙoƙarin gyara baƙar jacket ɗin daya ɗoro saman rigarsa.
Rose ce farkon miƙewa ta fice, niko ban motsaba sai da suka gama fita sannan
na zama ƙarshe.
Jikin motar da mukazo na hango rose tsaye, ta wani haɗe fuska, shi kuma
yana daga gefe waya a kunnensa, hannunsa ɗaya a aljihun farin wandonsa, ido muka
haɗa nai saurin janye nawa nidai, dan sam banyi zaton sashen da nake yake kalloba
ma, a raina ina mamakin yanda duk sanda zan saci kallonsa nakan kama idanunsa a
kaina shima, sai naji haushi na balla masa harara ta gefen ido duk da baisan
inaiba.
Duk tsaye mukai muna jiran ya kammala, kusan mintuna uku kafin ya sauke wayar
ya tako wajen motar da rose ke tsaye, muma duk muna kusa, ya kalli Hafiz yana
faɗin, “Yanzu yaya za'ai kenan?”.
Hafiz yace, “Boss inaga ku koma Office, ni da rose da Aliyu zamuje can
anguwar mu sake bincikawa, maybe mu samu wani a gidan yanzun”.
“Okey hakan yayi” yay maganar yana yunƙurin buɗe motar, dole Rose data cika
fam da haushi ta mat

sa, har zai shiga ta katse hanzarinsa da faɗin, “Boss nikam da sun wuce, sai na
biku, zan ɗauka wayata dana manta a office, zan bisu a baya tunda nasan anguwar”.
Ɗagowa yay yana kallonta fuskarsa babu walwala, ya janye idanunsa a kanta
batare da ya bata amsaba ya maido kaina dan duk kallonsu mukeyi, “Mimaa! Shiga mota
muje, ke kuma ki bisu kubiya ta station ɗin tare sai ku ɗauka wayan ku wuce”.
Duk da naga idanunsa a kaina suke sai ban fahimci dani yakeba saboda sunan
daya ambata, gashi har yayi shigewarsa motar.
Jabeer dake kusa dani yay murmushi, “Dake yake fa, kije kutafi”.
Kaina na jinjina masa kawai ina murmushin ƙarfin hali da sake juya sunan a
raina, ‘Mimaa;? To wannan sunan kuma daga ina haka?’. Na ƙarasa zan shiga gaba, sai
dai rose taƙi matsawa a wajen, na kalleta nace, “Zan shiga ciki maa”.
Shiru bata motsaba, bakuma ta tanka minba..............✍

Rose yau kinga idi wajen bily team, dama hauhinmu sukeji😥🤐.

Asha weekend lafiya😜😑😉🤗🤗.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻[11/30/2020, 1:00 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:


Page 8

.............Jawaad dake kallonsu daga ciki yay murmushi kawai yana girgiza kai,
dan ya fahimci wani abu daga Rose ɗin. hannu ya miƙa ya buɗe murfin ɗayan gefensa,
Hafiz dake ta wajen tsaye yace, “Kinga mai sunan Momcy zo tanan”.
Amsa masa nai da “to” na nufi can duk da a raina banso hakanba dai, sai dai
haka kawai naji inason bama shegiyar rose ɗinnan haushi yanzun, dan na kula sam
bata ƙaunata dai, su mutanen duniya dasun ganka shiru-shiru saisu dinga ɗaukarka
sakarai ko bakasan abinda kakeba, indai nice kuwa tasa kanta a ramin damisa wlhy.
Ina shiga Hafiz ya rufe murfin, gimba yay ma mota key, bansan yanda aka ƙare da
rose ba mukabar gidan bayan oga Jabeer ya shiga gaba bisa umarnin Boss da yay masa
magana.

Har muka isa station oga Jabeer da gimba na hira, amma ni dashi kamar
mun haɗiyi kwaɗo. Yanda na takurama babu abinda nake buƙata kamar mu iso na sauka
nidai. koda gimba ya tsaida motar ban fitaba saida duk suka fita, baiko kalli
kowaba a cikinmu yay gaba abinsa zuwa hanyar office ɗinsa, Jabeer ne kawai ya
kalleni fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “To mai sunan mom sannu da ƙoƙari, ki ƙara
ƙaimi da jarumta dan aiki da boss sai jarumi na gaske”.
Duk da ban fahimci zancensaba nai murmushi ina ɗaga masa kai, sannan nace,
“ngd” a ƙasan raina kuwa ina tunanin wai sunan wa? gareni suketa wani boyen suna.
Murmushi yay shima, ya nunamin cikin motar yana faɗin, “Karki damu babu godiya
a tsakaninmu, ki tattara masa tarkacensa kibisa office dasu, ai kinsan office ɗin
ko?”.
Tamkar na fasa ihu haka naji, amma sai na daure nace, “Ban taɓa shigaba
dai, amma na sani”. Yace, “To Alhmdllh saiki kaimasa ni na wuce office ”. Kaina na
jinjina masa batare da nace komaiba, shima yay murmushi kawai ya wuce abinsa.
Duƙawa nai na tattaro wayoyinsa da tab da wasu takardu daya bari sai bindiga da
keys da bansan kona miyeba, sai ƙamshi suke tamkar suma turaren ake fesa musu,
ledar takeaway ɗinmu gimba ya bani, ban musaba na amsa, dan duk zatona duk shi zan
kaimawa, sallama nai masa na nufi hanyar da zata kaini office ɗin da kaya riƙi-riƙi
saikace wata ƴar gudun hijira, danma na barma gimba ledata akan idan na fito zan
karɓa dukda yacemin gida zaije. Sai da na hau lifter domin office ɗinsa na hawa na
uku ne, sai saƙawa da kwancewa nake ina zancen zuci, na iso shataletalen da ya raba
hanyoyi uku na offices ɗinsu, ɗaya nasan hanyar dazata sadaka da offices ɗin su B.G
ne, wanda suke a hawa na ƙarshe, sai kuma ɗayar hanyar bansan offices ɗin suwayeba
a wajen, sai ɗayar hanyar da naga ya fito ɗazun, nan na nufa kai tsaye, dogon
corridor ne da ƙofofi jere kusan goma, hakan yasa na fara bi ina karanta rubutun
saman gudun kuskure, sai da naje na bakwai sannan naga an rubuta Captain Jawaad A
yusif, inada tabbacin nanne, dan tunda aka gayamin cikakken sunansa bantaɓa
mantawaba koda a second ɗaya ne kuwa. Sai da na daidaita kaina da sake ƙarfafa
zuciyata da ke neman faso ƙirjina ta fito sannan nai knocking har sau uku, amma
banji an amsa maniba, nai jim kusan na minti ɗaya kafin na ƙara yin knocking ɗin
kamar mai tsoron a jita, nanma shiru, nakai hannu zan sake aka amsa mani. Ajiyar
zuciya na sauke a hankali kafin na tura ƙofar da sallama na shiga, office ne da ya
amsa sunansa office, dan kuwa yayi ƙyau, babu wasu tarkace komai kuma tsaf, ga
mayen turarensa ya kama office ɗin haɗi da freshener mai daɗin ƙamshi, sai suka
bada ƙamshi na musamman, kallo ɗaya naima inda yake zaune a kujerarsa ta office na
duƙar da kaina, shima kuma bai kalleniba, baikuma cemin komaiba, yanata rubuce-
rubucensa hankali kwance tamkarma baisan wani ya shigoba. Jinai tsayuwar ta isheni,
dan haka na gyara kaɗan ina yamutse fuska, batare dana ɗago na kallesa ba nace,
“Sir gashi inji oga Jabeer”.
Jay da tun ɗazu ya daina rubutun ya kwantar da bayansa jikin kujerar kawai
yana kallonta da jinjina shegen miskilancinta ya lumshe idanunsa ya buɗe a lokaci
ɗaya, sai faman goga ƙasan biron hannunsa yake a jikin laɓɓansa, ko motsi baiyiba
ballanta ya amsa mata. Tsabar miskilancin yarinyarne kawai ke bashi mamaki, ya ɗan
taɓe baki t

are da maida kallonsa ga Computer ɗin dake kan desk ɗinsa, bironsa ya ajiye yana
lafe jikin kujerar ya fara sarrafa keyboard ɗin Computer ɗin.
Ƙaran danna keyboard da najine ya sakani ɗago idanuna nai masa kallon
second 2 na janye, karan farko a rayuwata dana sake jinjina wulaƙancin mutuminnan,
‘kenan bazai tanka mani ba komi yake nufi?’ na ambata a zuciyata ina maijin
takaicinsa. Satar kallonsa na sake yi sai muka haɗa idanu, da sauri na janye nawa
ina tura baki gaba batare dana san nayima hakanba.
Sautin fitar ƙaramin tsakinsa ya sakani saurin sake kallonsa, yako dallamin
harara alamun har yanzu idonsa a kaina suke, “Kin zama bodyguard ɗinane shin?” yay
maganar a hankali kamar baison yi.
Kaina na girgiza masa, duk da bani da tabbacin kallon nawa yake har yanzu,
takawa nai zuwa gaban tebir ɗin na ajiye kayan harda ledar abincin, ban kallesaba
bai kuma tankaminba na juya zan fita.
“Zonan”
Na tsinkayi umarninsa. Juyowa nai kaina a ƙasa batare dana kallesa ba, “Zauna” ya
sake faɗa a daƙile. ‘Kai nikam na shiga uku da wannan mutumin’ na ambata a zuciyata
ina mai jina a matuƙar takure, zuciyata sai faman harbawa take da sauri-sauri.
Shiru office ɗin ya sake ɗauka na kusan minti ɗaya, sai ƙarar keyboard da yake
dannawa kawai kake ji. Knocking ƙofa akai ya bada izinin shigowa, matashin sauriyi
ma'aikacinmune ɗauke da takardu a hannu, kallo ɗaya nai masa na ɗauke idona, duk da
shi na lura sai kallon mamakin ganina a nan ɗin ya keyi, har takai boss ya daka
masa tsawa.
“Kallon mutane aka turoka yine!?”.
Cikin sauri da ladab yace, “Sorry sir”.
Banji ya tanka masaba, danni kaina a duƙe banma ɗagoba, sai sautin siririn
tsakinsa naji kawai, shidai saurayin sai faman nanata kalmar haƙuri ya keyi kusan
sau huɗu kafin ya fara masa bayani akan takardun hannunsa, banji ya tankaba, hakan
yasani satar kallonsu, gani nai ya miƙa hannu ya amsa takardun yana dubawa, kafin
ya ɗago ya kallesa da sake miƙa masa ta kardun yana faɗin, ”Ka kaisu office ɗin
Lieut..; Richard, kace ya duba, zuwa anjima sai yazo dasu ina nemansa”. “Okey sir”
ya faɗa cike da girmamawa kafin ya amsa ya fita ko sau ɗaya bai sake gigin kallon
sashen da nakeba.
Ɓoyayyen numfashi na sauke bayan ficewarsa, saima naji yaɗan bani
tausayi........

“Bani malt.. A cikin fridge”. maganarsa ta dawo dani hayyacina, miƙewa nai ina
ɗan dube-dube a office ɗin danson gano fridge ɗin, shi kuma yaja ledan abincin ya
buɗe, ganin fridge ɗin da nayi bayansa kaɗan ya sakani nufar wajen, kasancewar
ƙaramine madaidaici yasa saida na sunkuya, malt ɗin ne kawai a ciki da coc... nidai
na ɗakko abinda ya sakani tare da kofin dana gani a saman fridge ɗin kusan guda
shidda saƙale jikin wani ƙarfe mai ƙyau, gabansa naje na ajiye ina haɗiye yawu da
ƙyar, dai-dai yana buɗe takeaway ɗin gasashen naman kaza daketa ƙamshi, ina ajewa
nabar wajen na koma inda na fara zama a ɗaya daga kujeru biyun dake gaban tebir
ɗinsa, ganinai kawai ya turo naman gabana, na ɗago na kallesa muka haɗa ido, kuma
tamke fuska yay ya nunamin naman. Tamkar zan fasa kuka nace, “Nifa na ƙoshi,
azumima nakeyi”. Banza yaymin tamkar baima jiba, ya ɗauki gwangwanin malt ɗinsa ya
ɓalle hancin ya kai baki, kafin ya ajiye ya maida hannunsa kan keyboard ɗin
Computer ya cigaba da daƙilarsu. Mun kwashi kusan minti uku a haka, bai tankaniba,
nikuma banci namanba dukda ƙamshinsa ya addabeni.
kamar daga sama naji yace, “Karki bari na sake miki magana, kiyi ki fitarmin a
office”.
Batare dana shiryaba bakina ya suɓuce wajen faɗin, “Toni nacefa azumi nake,
sokake na karya azumina ne?”.
Tunda ta fara magana ya dakata daga daƙilar Computer'n ya zubama laɓɓanta
idanu da kumatunta da take ɗan kumburawa, sai da takai aya sannan ya janye ya maida
ga abinda ya keyi batare da ya nuna yamaji mita faɗaba.

A matuƙar takure nake gaba ɗaya bugun zuciyata da numfashina sun dawo a
maƙoshina, kaɗan nake jira na amayota kowama ya huta, yaƙi kulani, sannan yaƙi
cemin na tafi, ganinfa yama manta dani saina miƙe abina na nufi hanyar ƙofa, bai
tanka maniba har saida na kama ƙofar zan

buɗe sannan yace, “An taɓa karyaki?”. Cak na tsaya, ni ban fitaba, ni ban komaba,
bamma iya sakin mariƙin ƙofarba saboda yanda furucinsa ya daki ƙirjina, sai da na
shaƙi iska na fesar sannan na juyo a hankali ina kallonsa, kauda kaina nayi saboda
ganin shima niɗin yake kallo, ya wani haɗe fuska tamkar hadarin tsakkiyar ogusta.
“Idan kika bari na sake miki magana ki kuka da kanki”.
A yanda yay maganar da tsananin kaushi sai tsoro ya sake tsirgamin, dama dai
ƙarfin hali nake kawai, dole na dawo na zauna ina sake haɗe fuska dan nikam gaskiya
an sakama rayuwata ido, komawa nai kujerar dana tashi na zauna. Ina zama shikuma
yana miƙewa ɗauke da wasu takardu ya fice daga office ɗin abinsa batare da yace
dani komaiba. Na sauke nannauyan numfashi ina kallon naman, bani da zaɓinda ya wuce
nacin kawai kodan ya barni na tafi, na ɗauki cinya nakai bakina ina ambatar
bismilla, ɗanɗanon naman da laushinsa ya sakani lumshe idanuna, ko ba'a faɗaba dama
namannan zaiyi ɗankaren daɗi ai, ban ankaraba na laƙume cinyar na sake ɗaukar wata
tsoka irin ta haƙarƙarinan, (Damafa inaso shegen gulma ne. Lol) ina gab da cinyeta
aka turo ƙofar da azabar ƙarfi aka shigo, a tsananin razane da ganin wanda ya shigo
ɗinne ya sakani miƙewa babu shiri ina kallonsa. Shima idanunsa ya zubamin tamkar
zai cinyeni da su.
“Ubanmi kikeyi nan Bilkisu?!!”
Idanuna na lumshe saboda tsawar tashi ta rasha kunnuwana, na buɗe a hankali kansa,
cike da dakiya na zubasu a kansa nace, “Yah Qaseem miya faru?”.
Wata malalaciyar harara ya zubamin kamar zai juye idanunsa ƙasa, ya fara
takowa inda nake, taku baifi ukuba tsakaninmu ya rage aka buɗe ƙofar office ɗin aka
shigo. Ni da shi duk kallon ƙofar mukai, sai dai shi a take ya janye nasa idon yana
jan uban tsaki. Nikam numfashi na sauke a ɓoye dan koba komai na samu kuɓuta daga
wannan yunƙurin na yah Qaseem da bansan mi zuciyarsa ke kissima masa yaminba.
Jay da ya shigo kuwa kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa ya taka zuwa ga
kujerarsa ya zauna.
A mamakina sai naga yama cigaba da daƙilar Keyboard ɗin Computer ɗin
hankalinsa kwance kamar baisan damuba. Shima yah Qaseem ɗin bai tanka masaba ya
kalleni yace, “Wuce muje”.
Jawaad daketa danne-dannensa batare daya ɗagoba yace, “Kai ka kawotane?”.
Dogon tsaki yah Qaseem yaja yana damƙar hannuna da faɗin, “Miye na azarɓaɓi ƙaramin
tsagera, ai zan dawo kanka idan na gama da ita”. Ya ƙare maganar da fisgar hannuna
muka nufi ƙofa. Jinake tamkar na kurma ihu, ‘Nikuma wannan wace fitinace na shigo
ciki haka?’..........
“Wlhy kika fita daga office ɗinan saina saɓa miki kamanninki!”
Muka tsinkayo kakkausan furucin boss yayinda yah Qaseem ya murɗa ƙofar zamu
fice. Bani kaɗaiba hatta da yah Qaseem ɗinma tsayawa daga yunƙurin fitar yay, ya
juya yana kallonsa, nidai kaina a ƙasa na gaza kallon kowa a cikinsu, addu'ar ALLAH
ya kuɓtar dani daga tsakaninsu kawai nakeyi a raina, dan bansan wazan bijiremawaba?
Wakuma zanma biyayya ba?. Yarfar da hannuna yah Qaseem yay ya nufesa, zafin da
najine ya sakani durƙushewa a wajen ina sakin siririyar ƙarar azaba.
Qaseem daya ƙarisa gaban Jawaad ya bugi tebir ɗin gabansa har wasu abubuwan
na faɗuwa, “A matsayinka na ubanwa zaka saɓa mata kamannin?”. Ko motsi Jawaad
baiyiba balle ya kalli Qaseem, aikin gabansa kawai ya cigaba dayi hankalinsa
kwance. A kausashe Qaseem ya sake maimaita tambayar tamkar zai mari Jay ɗin. Ɗago
idanu Jawaad yay ya zubasu akan Qaseem, cike da gadara yace, “Qaseem fitarmin daga
office!!”.
“Anƙi a fita, kayi duk abinda kaga zaka iyayi” Qaseem ya maida masa amsa a
zafafe shima.
Jawaad bai sake magana ba, ya miƙe ya nufi Bilkisu dake durƙushe tana hawaye
saboda hannunta dake zugi.

Tsayuwar mutum kawai naji a kaina, cikin bada umarni yace, “Tashi”. Miƙewa
nai babu musu, na saci kallonsa, ganin shima kallon nawa yakene yasa na janye nawa
ina goge fuska, kafin ya sake wata magana yah Qaseem yazo ya shiga tsakkiyarmu,
”Wuce muje” ya faɗa yana nunamin hanya, haushin murɗamin hannu da yayne yasa naƙi
motsawa. Ganin naƙi motsawarne ya sake hasalashi ya

ɗaga hannu zai saukemin mari.


Rufe idona nai da sauri naja baya saboda masifar firgita da nai da ihun da
yaymin akai, na ƙanƙame jikina ganin ya ɗaga hannu zai makeni, shirun da naji
yasani ɗago kaina kaɗan naga miya hanashi dukan nawa da yay niyya.. Saurin waro
idanu nai waje ganin boss riƙe da hannun Yah Qaseem da ya ƙara kumbura sai hura
dogon hancinsa yake.
“kika fita saina karyaki a office ɗinan Miemaa” boss yay magana a dake
kamar yanda na fahimci halittarsace yin magana kai tsaye koda a gaban wa yake.
Saurin duƙar da kaina nai saboda tsatstsareni da yay da idanu, nai baya daga kusa
dasu cike da tashin hankalin sakani tsakkiya da sukai.
yah Qaseem ya fisge hannunsa dake cikin na boss ya kai hannu zai damƙoni
ina ƙoƙarin matsawa. Cikin matuƙar zafin nama boss ya fisgi yah Qaseem ɗin gefe,
hakan sai ya bani damar mannewa a bango na sake musu kuka kawai, dan zuciyata
bazata iya ɗauka ba.

A cikin tsagwaron fushi Qaseem ya damƙi wuyan rigar Jawaad zai shaƙeshi,
“Amma kasan zan iya illataka ko?”.
Murmushi Jawaad yayi yasa hannu ya ture hannun Qaseem dake damƙe da wuyansa,
cikin halin ko in kula yace, “Ka illatanin mana Qaseem, kai wai wace irin banzar
zuciyane da kai haka? Mace zaka ɗaga hannu ka daka?”. A matuƙar masife Qaseem yace,
“ina ruwanka? Miye matsalarka?” baki Jawaad ya taɓe yana watsa hannayensa da ɗage
kafaɗa yace, “Banda” ya ƙare maganar da juyawa zai koma kujerarsa. Saurin maidoshi
baya Qaseem yay, hakan ya saka Jawaad tsayawa sai dai bai juyo ya kalli Qaseem
ɗinba, ƙoƙarin danne zuciyarsa yake dan bayaso su raba hali gaban yarinyarnan kamar
yanda ya kula Qaseem yana buƙata. Cikin nunashi da ɗanyatsa Qaseem yace, “Wannan ya
zama na farko kuma na ƙarshe da zaka sake saka Bilkisu! cikin lamarinka, itaɗin
matar dazan aurace, ya rage naka ka kiyayi ko kaci gaba”.
Rumtse idanu Jawaad yayi saboda jin yanda Qaseem ya ambaci sunan
mahaifiyarsa gatsal, ya juyo a hankali yana kallon Qaseem cikin ido, cikin ƙunar
zuciya yace, “Ko wacece ita a wajenka baya gabana, sai dai kai kasani baka isa
hanani sakata aikin dana gadamaba tunda har tazo station ɗinnan a ƙasana, kasa a
ranka yanzu aka fara wasan kuma, ina gargaɗinka Ka kiyayi kai hannu kan mace da
nufin duka”. ya ƙare maganar a wani irin yanayin rainin wayo. Hakan sai yay masifar
sake fusata Qaseem, a tsawace yace, “Matsayinka na ubanwa?”..............✍

Qaseem team & Jawaad team banda faɗa kuma 🚴🏼🏋🏼🤼🏼😂😖.

Ina Bil-Qas team nidai😜🤫🤸🏼.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻


[11/30/2020, 1:01 PM] HASNA ✍🏻
: Typing

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 9
............A matsayinka na ubanwa?” cewar Qaseem a fusace.
Cike da rainin wayo Jay yace, “Lokacine zai nuna maka”.
Jabeer da ya shigo office ɗin kusan mintuna biyar da suka shuɗe, amma jaraba ta
hanasu ganinsa yay gyaran murya.
Duk kallon ƙofar mukai, Cikin nuna alamun tamkar baima fahimci mike faruwa a office
ɗinba ya kalleni tare da miƙamin kwalin dake a hannunsa, “Momcyn mu kikai wannan
Office ɗin MM; daga nan ki wuce ƙasa naga ana nemanki”.
Kaina na ɗaga da sauri, na amsa kwalin na fice ina mai godema ALLAH da zuwan oga
Jabeer da yay belina hannun waɗanan zakunan.
Babu wanda yay magana tsakanin Jawaad da Qaseem ɗin har Bilkisu ta fita, Jabeer ya
maida kallonsa kansu yana ɗan murmushi, “Haba basawanmu, ya zaku saka yarinya
tsakkiya kuna yaƙi? Ai saiku rikitata, miye nata a ciki tunda batasan miye
tsakaninku ba?, yakamata kumata adalci, aiki take kamar yanda kuke aiki, ku sakata
abinda zaku sakata matsayinku na waɗanda suke sama da ita, amma bawai ku sakata
tsakkiya akan abinda ke zukatanku ba”.
Juyowa Jay yayi, kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kansa kawai ya juya yana
mai ɗaura hannunsa a kafaɗar Qaseem ɗin yaɗan bubbuga kaɗan ya koma mazauninsa.
Binsa da kallo Qaseem yay cike da takaici da baƙin ciki, a ransa yana rayama kansa
inhar Jawaad yay gigin cigaba da kutse a al'amuran Bilkisu wlhy wannan karon sai ya
karta masa rashin mutuncin da bazai taɓa mantawa da shiba har ƙarshen numfashinsa,
yaja tsaki tare da harar Jabeer ya fice daga office ɗin..
Jabeer dake binsa da kallo ya girgiza kai kawai sannan ya juyo ga Jawaad da ya
cigaba da harkar gabansa, ƙarasawa yay ya zauna yana ɗora wayarsa a tebirin Jay
ɗin, “Boss dan ALLAH son yarinyarnan kakeyi ne?”.
A bazata maganar ta zoma Jawaad, dan haka babu shiri ya ɗago idanunsa da sukai
sirkin jaa da ƙara girma ya watsama Jabeer ɗin wata uwar harara, sai kuma yaja
tsaki ya maida kansa ƙasa.
Jabeer ya haɗiye dariyarsa yana gyara zamansa, “ALLAH ba wasa nakeba Jay, kuma idan
hakan ta kasance wlhy zanyi murna, dan nutsuwar yarinyar na burgeni, g......”
“Motsoww! Jabeer banason shirme, wace irin banzar maganace wannan, Please banaso
karka sake”.
Hannu Jabeer ya haɗe waje guda alamar ban haƙuri, Jawaad ya kuma hararsa ya ɗauke
kai. Shidai Jabeer yay murmushi kawai, cikin son kauda zancen yace, “Yanzu nakeji
su Sir Ahmad sun sake shiga meeting akan batunnan”.
Jawaad da kansa ke durƙushe yana aiki yace, “Basai suyi tayiba tunda basu da
tunanin kansu sai abinda aka ɗorasu a kai”. Jabeer yace, “Wlhy Jay ni mamaki suke
bani ma, saboda ALLAH maimakon subama yarinya ƙwarin gwiwa akan abinda ta fara sai
kawai su ɓige da tsugunne-tsugune, kai yanzu mi kake tunani akan batun?”.
Kallonsa Jay yayi fuska a taɓe, sai kuma yaja tsaki ya maida kansa ga abinda
yakeyi, “Tunanin mizanyi akan wannan shirmen Jabeer, iyakaci suce zasu dakatar da
ita na wani lokaci ta huta, ko su canja mata wajen aiki ai dai ko? Tunda basu isa
suce ta ajiye aikiba akan hakan”.
“To ai babu wanda ya kamata kabari ya kasance a ciki” cewar Jabeer yana kafe Jay da
idanu.
Shiru Jawaad yay bai tankaba, tsahon mintuna biyu harma Jabeer ya fidda rai da
samun amsa sai yaji yace, “Akanmi zan hana ni kuwa? A matsayina kuma nawa? Dukansu
ogannina ne, suna sama dani nesa ba kusa ba, to mizan iya musu kona hanasu?”.
“Jay! Saboda ina ƙwaɗayin yarinyar ta shigo tawagarmu”.
“Humm” Jawaad ya faɗa a taƙaice.
Jabeer da ya fahimci amsar kenan sai ya cigaba da faɗin, “Ba ƙaramar nasara bace
hakan a garemu Jay, dan inaji a raina zata ƙara kawomana nasarori, amma kadaiyi
tunani akan hakan”.
Ƙin cewa komai Jawaad yayi, hakan yasa Jabeer sakin zancen shima ya ɗakko masa na
aikin da suka fara yau kawai, ananne Jay ɗin kuma ya bashi dukkan attention ɗinsa
suka shiga tattaunawa.
★★★★★★★
lna fitowa daga office ɗin MM naci karo da Ummie, bansan miyasa na tsinci kaina da
gyara yanayinaba na sakar mata murmushi, hararata tayi ita kuwa tana fusgar hannuna
mukai gaba. Masallaci muka nufa dan lokacin sallar zuhur yayi.
Bayan mun idar da sallane mun fito Ummie ke tambayata akan ina naje? Mi kuma ya
sami kana?. Ban wani ja zancenba na bata labarin abinda zan iya, sai dai ban bata
labarin miya faru tsakanina da yah Qaseem ba da kuma ceton da boss yay min a
hannunsa yanzun.
Sosai naga mamaki a wajen Ummie tattare da labarin nawa, harna kasa haƙuri nai mata
tambaya, tai ƴar dariya kawai da cewar, “Abunne da mamaki ALLAH, wannan mutum mai
fuska kamar hadarin tsakkiyar damina ɗin?”.
“Ba abin mamaki bane Ummie, ni kawai na danganta lamarin da abinda ya farune ranar,
ganina yake kamar wata jarumar gaske, baisan lamarin duk buge bane kawai” sosai
Ummie ta kwashe da dariya cike da shaƙiyanci, nakai mata duka ta kauce tana cigaba
da dariyarta, sai da tai mai isarta sannan ta dawo tana bani haƙuri muka shirya,
daga haka muka cigaba da tsokanar junanmu da aikin dake gabanmu kuma.
Har lokacin tashi yayi ban sake saka boss da yah Qaseem a idanunaba, dama bai zama
lallai na gansunba kasancewar bani da hurumin hakan sai idan sune sukaso, haɗuwarmu
a inuwa ɗaya dama sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Haka kawai na tsinci kaina da tsoron
bin yah Qaseem, sai kawai nabi Ummie ta saukeni a gida

★★★★★
Bayan sallar magriba ina zaune a saman abin salla ina azkar aka turo ƙofar ɗakina
aka shigo, kaina na ɗaga ina kallonsa, yanda fuskarsa ke a tamke saida naji gabana
ya faɗi, amma sai na dake abina nace, “Yah Qaseem ka dawo?”. Baice dani uffanba sai
wata uwar harara daya makamin, ɗauke idona nai tamkar ban ganiba, ya ida shigowa
cikin ɗakin yana bin ko ina da kallo, bakin gado ya ƙarasa ya zauna, hakan sai ya
sakani jin wani iri, dan kuwa ni kaɗaice a gidan, koda na dawo ban iske kowa ba, su
mom basu dawo daga gidan rasuwaba. A daƙile yace, “Waye ya maidoki gida?”.
Kaina tsaye nace, “Ummie ce, na jiraka naga baka fitoba gashi magrib ya gabato, sai
kawai na biyota”.
Shiru yay tamkar bazaice komaiba, sai numfashi yake saukewa da sauri-sauri, hakan
yasani tsira masa ido, “Yayah lafiya kuwa?”.
Wata harara ya sake danƙaramin kamar idonsa zai faɗo ƙasa, “Uwar miye haɗinki da
shi Jawaad ɗin? Da har zaku fita tare? Ban miki Warning akansa ba?”.
Zamana na gyara sosai akan abin sallar saboda jin ƙafata ta fara yami, duk da na
lura bawai maganar wasa yakeminba inata ƙoƙarin dakewa.
Bansan yanda zan bashi amsa ya fahimtaba, amma ni banajin kuskure nayi tunda akan
aikine ai. “Dake nake magana Bilkisu!!”. Saurin kallonsa nayi danjin yanda yay
maganar a kausashe, nace, “Aiki muka fita fa”.
“Aiki? Duk jami'an dake cikin Station ɗin babu wanda zai ɗauka suje aiki sai ke?”.
“Yayah ni wlhy ban saniba”.
Saida yasake watsamin harara dayin ƙwafa sannan yace, “Su kuma waɗannan kayan na
jikinkifa da nagani ɗazun? Ina kayan da kika fita dasu daga gida da safe?”.
Kaina tsaye nace, “A wajen aiki da muka fita ne a mistake jikinmu ya ɓaci, to
shinefa sai... Sai... Sa.........”
“Sai ubanmi? Bilkisu!!”.
“Sai Rose ta bani wasu kayan na zanja”.
“Harda ita kuka fita?” yay maganar cikin kakkafeni da idanu. “Eh” na bashi amsa
cike da ƙwarin gwiwa.
Karon farko da yaymin murmushi, ya sakko daga saman gadon ya zauna kusa da ni sosai
ya tanƙwashe ƙafafunsa (Dan zuciyarsa tayi sanyi jin basu kaɗai bane, amma hakan ba
yana nufin zaiƙi saka musu ido bane ba). Yanda muka samu kusancine ya sakani
matsawa baya kaɗan, baice komaiba, saima hannuna daya kamo cikin nashi, nai ƙoƙarin
amshewa amma sai ya hanani damar yin hakan, murya a sanyaye yace, “Bilkisu!”.
Amsawa nai idona na kawo ƙwalla, dan banason kama hannuna da yayi......
“Kinsan kuwa yanda nake sonki da kishin ganin wani ya raɓeki?”. Shiru nai bance
komaiba, shima bai jira amsata ba ya cigaba da faɗin, “Daga yau karna sake ganinki
da Jawaad, idan kuma ba hakaba to lallai zan saɓa miki kuwa! Domin koba aurenki
zanba yayankine ni, dolene na saka miki ido gudun karki lalace”.
Yanda ya ƙare maganar sai yaban dariya, a raina nace, ‘Kaima ka samu dama ai
lalatanin zakai’, amma a fili sai, nace, “Yayah nifa banice naje wajensaba, bayan
na fito daga kiran da akai minne mukai karo dashi a hanya, shi kuma ya fito daga
office ɗinsa, shine yace na biyosa, da farko ma bansan dani yake ba sai da ya sake
aikowa sannan, amma dan ALLAH kayi haƙuri”.
Murmushi yay min yana jinjina kai, yace, “Nasan dama ba laifinki bane, amma zan
takama al'amarin birki tunkan yay nisa kinji, ina sonkine da yawa shiyyasa bazan
juri ganinki da waniba ballema maƙiyina Bilkisu...”
Ya ƙare maganar a hankali yana matsowa jikina sosai, gabana ne ya shiga faɗuwa, nai
ƙoƙarin ja da baya amma sai hakan ya gagara saboda riƙon da yaymin bana wasa bane,
sannan ƙarfina da nasa ba ɗaya bane, matsananciyar rawa jikina na fara sabida
ƙoƙarin kawo fuskarsa kan tawa da yake, na shiga girgiza masa kai ina hawaye,
roƙonsa nakeson yi, bakina sai motsawa yake amma na kasa furta komai, ya riƙe kaina
da ƙyau yana ƙoƙarin ɗora bakinsa kan nawa na ƙwalla ƙara.
Da sauri ya sakeni shima yaja baya saboda tsorata da ƙarata, jikina sai ɓari yake
na tashi a guje na shige toilet ɗina na banko ƙofar harda murza key. ‘innalillahi
wa inna ilaihirraji'un’ naketa ambata, wace irin masiface kuma wannan ni Bilkisu,
kuka na shiga rusawa a bayin sosai, duk da inajin ƙwanƙwasa ƙofar da yaketa famanyi
yana kiran sunana da bani haƙuri banko tankashiba, kusan mintuna talatin naji shiru
alamar yabar wajen, ban buɗe ƙofarba har sannan sai bayan wani lokacin sannan na
buɗe kaɗan na leƙa, babu kowa a ɗakin saima ƙofa dana gani buɗe alamar ya fita,
komawa nai toilet ɗin na ɗauro alwala na fito, sai da na sakama ƙofar key kafin na
tada sallar isha'i.
Haka nai kwanciyata da yunwa ban fitaba duk da inajin motsin su mom da suka dawo
kusan ƙarfe goma, ina idar da sallar asuba nai shirin barin gidan, dan gwarama na
shiga gidansu Amina daga baya sai na wuce wajen aikin, bazanbi yah Qaseem ba.
Sauri-sauri na kammala na fito, gabana ya faɗi ganinsa zaune a falo yana shan shayi
alamar dai shima harya gama shirinsa, yanda ya tsatstsareni da idanu kuma ya sakani
tsayawa cak nai ƙasa da kaina, “Kizo kisha shayi mu wuce, dan sauri nake yau”.
Bance dashi komaiba na wuce zuwa kicin, kaɗan na haɗa tea a kofi na zauna a kicin
ɗin ina sha, dan kuku ma bai kai ga fitowaba, saurin kallon ƙofar nai jin an shigo,
nai masa kallo ɗaya na ɗauke kaina gefe, baice komaiba nima banceba, sai ajiye
kofin da nai na nufi ƙofa, matsawa yay ya bani hanya, a ɗarare na raɓashi na fita
yabi bayana.
Badan raina yaso ba na shigar motar Yah Qaseem yau ɗinnan, shiru motar babu mai
cewa komai ni da shi, ko redio bai kunnaba, tuƙi yake a hankali kamar bayaso, mun
ɗanyi nisa da gida ina lafe a jikin kujera da karanto addu'ar neman tsarin ALLAH
daga shaiɗanin dake ingiza zuciyar yah Qaseem ga abinda bai daceba gareni naji
motar kamar ta tsaya, idanuna dake cike da barci na buɗe, naɗan waigo na kalleshi,
ganin ni yake kallo sai na janye idanuna ina sake gyara zama, wlhy bazan ɓoye
mukuba a tsorace nake, bani da ƙarfin dazan kare kaina ga murɗaɗɗan namiji irin yah
Qaseem koda ace yay shirin cutar da nine, cikin dauriyar dole nace, “Yah Qaseem
lafiya muka tsaya?”.
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, har lokacin inajin idanunsa na yawo a kaina, sai
dai baice komaiba, kusan mintuna biyu suka sake shuɗewa, a bazata na tsinkayi
muryarsa, yace, “Kiyi haƙuri Bilkisu akan abinda ya faru jiya, banyi hakan da
niyyaba tunda kinsha faɗamin baƙyaso”.
Ajiyar zuciya na sauke inajin daɗin kalamansa, na share hawayen da suka zubomin, ba
tare dana kallesa ba nace, “Na haƙura Yah Qaseem, amma dan ALLAH ka rufamin asiri,
kaji tausayin maraicina ka barni da mutuncina, gidanku itace mafakata ta ƙarshe da
nake alfahari da ita, idan shaiɗan ya lulluɓe maka ido ka tuzguɗemin ita bansan ina
zan dosaba, haramunne a addininmu, sannan cutarwace a garemu, wannan ba shi bane
soyayya kamar yanda yake a tunanin yahudu da nasara, ƙoface kawai ta saɓon
UBANGIJI, kuma tushen fasiƙanci, daga kama hannuna da kakeson yi a koda yaushe
matsala zata fara, tun inaji banason hakan wataran sai kaga shaiɗan ya ƙawatamin
nafara jin daɗi, a tafi matakin sumbata, makulin buɗema shaiɗan ƙofa kenan da komai
na baɗala zai iya wanzuwa tsakanin namiji da mace, duk takatsantsan ɗinmu wataran
kafin mu farga sai akai ga aikata zina, ‘Wa'iyazubillah’. Yah Qaseem namiji da mace
duk hukunci ɗaya garesu wajen ALLAH idan suka aikata zina, amma a zahirance ta
rayuwar duniya mace itace ke fara ƙasƙanta a idanun al'umma makusantanta dama na
nesa da ita, domin itace ke ɗaukar ciki, itace wasu almomi ke fara bayyana a
gareta, farko rasa mutunci, ƙasƙanta mutincin gidansu dama ahalinta, tabon da zaita
bibiyar rayuwarta har ƙarshen zuri'arta, ita ake fara aibantawa kafin abokin
tarayyarta, itace ke rasa mijin aure, ita akafi nunama ƙyama, itace keda rauni.
Abin tausayi da tashin hankali ƴa mace na fuskantar waɗanan matsalolin koda ace
fyaɗe akai mata. Yah Qaseem indai sona kace da gaske dan ALLAH ka daina min waɗanan
abubuwan, wlhy banaso, basa burgeni......”
Qaseem yaja wani bahagon numfashi saboda tausayi da bily ta bashi, harga ALLAH
sonta yake da gaskiya ba yaudaraba, ALLAH ne ya jarabcesa da sonta batare daya
shiryama hakanba, yanda take kuka sai ya kumajin tausayinta sosai a ransa, murya a
sanyaye yace, “Na fahimceki Bilkisu, insha ALLAH kuma zan kiyaye, idan kin amince
zanma Dad magana akan aurenmu”.
Sauran hawayena na share tare da kallonsa, ganin ni yake kallo sai na ɗaga masa kai
alamar na amince. Ya saki wani murmushi najin daɗi yana sake tsatstsareni da
idanunsa farare tas, a hankali ya furta, “Inasonki da yawa Bilkisu na, gara dai
nayi na mallakeki kusa dani na huta da wa'azinnan”. Murmushi nayi ina ɓoye fuskata,
shima yay ƙaramar dariya yana mai tada motar muka cigaba da tafiya. Hira yaytamin
har muka ƙarisa station ɗinmu duk da ba amsa nake bashiba sai dai eh ko a'a da
murmushi kuma.
BAYAN KWANA UKU.
A kwanaki ukunnan Boss bai sake shiga harkataba, harna ɗauka gargaɗin Yah Qaseem ne
yasa ya barni, tunda ina ganin dai yana sama dashi. Shima a ɓangaren Yah Qaseem na
samu sauƙin yawan kai hannunsa jikina da yakeyi, sai dai wasu take-taken Yah Salman
a gidan yanzu suke cazamin kai, ya masifar samin idanu, kowane motsina sai ya tanka
magana a kai, Aunty Shahudah cema naga dai tayi sanyi, bansan mike damuntaba, amma
saina lura kamar bata cikin nutsuwarta.
Ban sake cema baba maigadi komaiba game da zancen Amina saboda saka idon Yah Salman
a kaina, amma inata wasu shirye-shirye a gefe nabin matakan da zan gano bakin
zaren, dan abinda baba mai gadi yayi ranar yana nan tsaye cak a zuciyata bai
gogeba. Da wannan tunaninma yau na fita wajen aiki.
Tunda muka dawo sallar zuhur muna a office ɗinmu da boss ya dunƙulemu, kowa yana
hidimar aikin daya dace, yayinda Ni da Ummie muna aikine muna ƴar hirarmu data
shafemu, hakama sauran kowa nayi da abokin maganarsa, hakanne yasa ɗakin ɗaukar
kananun surutai sama-sama. A bazata naji office ɗin ya ɗauki shiru tamkar ruwa ya
cinye kowa, batare dana ɗagoba nai ƙaramar dariya ina faɗin, “Ummie mutuwace ta
gitta a office ɗin namu ne?”.
Shiru naji Ummie batace komaiba, hakanne ya sani ɗagowa a tunanina batajini ba.
‘kutumelecy’...............✍

Assalamu alaikum.
Inason naɗanyi bayani da nake fatan a fahimceni, akan maganar aikinsu Jawaad,
inason mai karatu ya fahimci wani abu anan, aikin da muka dangantasu dashi bawai
yana nufin ainahin abinda ya shafi ma'aikatan zahirin bane, bamusan komai da ya
shafesu ba, tayaya zamuce komai nasu sai ya shigo labarinmu, domin ba'akan hakan
muke rubutu ba, da yawanmu ma idan za'a tambayemu bazamuce munsan waɗanan
ma'aikatanba kai tsaye, domin su aikinsu bawai a bayyane yakeba kamar ƴan-sanda da
dai sauransu da suke cikinmu ba, aikine na wanda kai kanka idan ba wani daliliba
bazaka taɓa ka gansu suna yawo gama gari ba ko wani aikinsu a bayyane, so na
danganta waɗanan jaruman littafine da hakan saboda mutunci da himma da ƙwazo na
irin jami'anmu da mu kanmu bamu saniba, matasanmu kuma su zama masu himma dason
bama ƙasarsu gudunmawa da zuciya ɗaya a kowace ƙasa suke ba lallai sai tamu ba, tom
inaso ku kalli wannan kawai a matsayin labari bawai lallai abinda yake a zahiri ba,
ko yake lallai mu bibiya, matsayinsu, misukeyi? Mizasuyi? Duk iyakarsa labari irin
na marubuci {ƙirƙira}, bani da hurumin shiga abinda bani da lasisi a kai, domin
bamma sani ba, waɗanan jami'an littafine bawai na zahiri dake aiki a ƙasarmu ba,
idan kun kula sam babu wani sunan gari dake nunama a ina suke, ko a wane waje suke,
musa a ranmu kawai ƙirƙirarren labari muke karantawa, ilimantarwa, nishaɗi, da
faɗakarwa, ba akan kowaba, domin ba'akan kowan mukeyi ba, duk abinda zamu iya ganin
yaci karo da waccan rayuwar ta zahiri to kawai fiƙira ce irin ta marubuci bawai dan
inada ilimin sani ba ko bibiya balle bincika, ina fatan duk wanda ke bibiyar wannan
littafi a ko'ina yake zai kasance maiyin ƙyaƙyƙyawan fahimta akan inda muka dosa,
sannan abinda kake ganin na karkace ko shiga hurumin da banawaba ina fatan zakuyi
gaggawar dawo dani hanya, ALLAH yasa mu dace, ALLAH kuma ya ƙarama dukkan jami'an
tsaronmu lafiya da ƙwazo da nagarta a duk duniyar da suke.🙏🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻[11/30/2020, 12:59 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:


Page 10

............‘Kutumelecy’ na faɗa a cikin raina ina saurin janye idanuna dana


ware a kansa da tsaida taunar cingam ɗin da nakeyi lokaci ɗaya, ganin yanda ya
tsatstsareni da muggan idanunsa. Zungurin ƙafata dana ɗora saman tebir ɗina Ummie
tayi.
Kallonsa na sake sata sai naga shima idanunsa yanzu akan ƙafar tawa suke harma
da sauran ƴan uwana, da sauri na sauke ƙafar ƙasa na nutsu kamar yanda kowa yayi.
Bai tankama kowaba ya ida takowa tsakiyyar ɗakin yana binmu da kallo daki-daki, har
tsawon mintuna biyu muna a haka tamkar ɗan doka da ƴan gidan kallon ƙwallo ko
ɓarayin agwagi, nidai sai faman jan addu'a nake saboda jin yanda zuciyata ke bugawa
da sauri-sauri tamkar ko yaushe idan na samu kusanci da shi.
Ganin bazai tankaba sai muka shiga gaisheshi ɗaya bayan ɗaya, hannu kawai yake
ɗaga mana amma bai sake kallon kowaba baikuma amsa mana da bakiba. Yaja kujerar
dake gaban tebir ɗin Uchie ya zauna, bamusan mi suke tattaunawaba har kusan tsawon
mintuna sha biyar kafin ya miƙe ya fice. Yana fita muka shiga sauke a jiyar zuciya,
yayinda wasu suka shiga gulmarsa musamman ma matan cikinmu, nidai sabon cingam na
ɓare na jefa a baki na cigaba da sabgar gabana.

________________________________
A gidan su Jawaad kam taron meeting Mom ta tara da ƴan uwanta,
sunɗau tsahon lokaci suna tattaunawa akan Jawaad da maganarsa da Shahudah, duk da
dai da farko Uncle Nasir yaso bijirewa, a cewarsa suma sunada ƴaƴan da zasu bama
Jawaad ɗin ai ya aura. Shahudah ta kiya musu hankalin da bai kamata su sake sakata
a sabgarsu ba.
Kuka mama Atika ta fasa musu, tare da ɗakko musu maganar data saka suka
nutsu waje guda.
“Munsan Sabira tayi laifi da tafka kuskure a baya, amma kuyi haƙuri munada
tabbacin zuwa yanzu ta magantu za'a samu gyara musamman idan mukai dubi da yanda
take son yaron, amma ni na yarda da shawarar Nasiru, mu fara ma Jawaad maganar
auren wata a cikin yaran gidannan, idan ya nuna rashin amincewa saimu tirsasashi ya
maida Sabira ɗakinta, dan baikamata mu zubamasa ido yana yawo sakaka babu aureba,
shekararsu kusan biyar kenan da rabuwa, amma yaƙi aure, inba neman matan banza
yaron nan yakeba yaza'ai mutum mai lafiya kamarsa ace yanaƙin aure?, su waɗancan
dangin uwar tasa sakarkaru da yake tsoronsa sukeji sun gaza masa magana kuma, tomu
bai kamata mu saka masa idoba, dan kuwa mune duniya zata zaga basuba, amma yaya
kuka gani? Danni dai shawarace na kawo matsayina na uwa a gareku, da Badiyya nada
isashiyar lafiyama tare zamuyi muku, yanzu saiku zauna ku yanke shawara a
tsakaninku” ta ƙare maganar da tashi ta fice daga falon.
Duk binta sukai da kallo harta fita, Uncle Sulaimam ya sauke numfashi yana
faɗin, “Nidai ƴan uwana na yarda da maganar mama, dan nidai zaman Jawaad bayamin
daɗi a haka, da Abdul-aziz nada rai bazai zubama gudan jininsa ido kamar yanda mu
muka kasa riƙe amana mukaiba, duk da bana zargin Jawaad da neman mata, dan mu
shaidane akan tarbiyya da sanin yakamata na yaron nan”. Duk shiru sukai basu ce
komaiba, wasu na hararsa ta gefen ido wasu na ƙunƙuni a cikin rai, dan suma sunsan
ƴaƴan Mama Badiyya sam nasa tare da burinsu a gidan, su kaɗaine masu ƙaunar Jawaad
dan ALLAH badan dukiyarsaba. Jin shirun yayi yawane ya saka Mom yin magana. “Nima
na aminta da maganar mama, kuma ina goyon bayan ɗan uwana Sulaiman”.
Daga maganar Mom sai kowama ya fara faɗar abinda ke ransa, daga ƙarshe dai
suka ajiye shawara akan zama da Jawaad ɗin idan ya dawo aiki da wuri yau, kokuwa
weekend idan ALLAH ya kaimu.

_________________________________

A makare yau Jawaad ya tashi a wajen aiki, saboda fitar da sukai shi
da Hafiz zuwa wani waje da yamma, basu dawoba sai bayan magriba, akwai abinda zai
ɗauka a office shiyyasa suka dawo, amma da daga inda sukaje gida zai wuce. Bayan ya
tattaro abinda zai ɗakko a office ɗin nasa sai yaga lokacin sallar isha'i ma yayi,
dan haka suka tsaya sukai a station ɗin.
Koda suka fito yunwar dake cin cikinsa yasa yace su tsaya wajen wani
haɗaɗɗen gashin kaji, gimba ya amsa masa da girmamawa. gimba ne ya fita domin

amsowa, kasancewar wajen ba baƙonsu bane akaima gimba tarba ta sanayya, kamar yanda
Jawaad ya bashi umarni takeaway biyu akayi sai fura da yogurt masu sanyi aka saka
ɗaɗɗaya a ciki, gimba ya bada kuɗin sannan ya dawo mota suka ƙarasa gida.
Ganin da sauran mutane da keta shigi da fici a sassan gidan sai ya bashi
mamaki, a ganinsa dai tunda anyi addu'an bakwai mikuma mutane keyi tunda ba taron
biki bane. Saurin kauda abin yay a zuciyarsa dan a ganinsa hakan ba huruminsa bane,
yaso shiga sashen Uncle Usman ya gaida Mama Zainab matarsa kamar yanda yakeyi
kullum tunda akai rasuwar, sai dai a matuƙar gajiye yake, ga masifaffiyar yunwa
dake cin hanjinsa.
Tare suka shiga sashensa da gimba dake ɗauke da tarkacensa, bayan ya ajiye
masa a falon ƙasa yay masa sallama ya fita, shima bai iya ƙarasawa bedroom ba ya
yada zango a falo, sai da ya huta na wasu mintuna sannan ya miƙe ya haura sama, duk
da yana buƙatar fara cin abinci haka ya daure, dan shi mutumne mai yawan cin
abinci, idan bai samu bane dai yakanyi haƙuri kawai. Ɗakin barcinsa ya ƙarasa ya
watsa ruwa, kusan ƙarfe tara ya fito tsaf dashi sai baza ƙamshi yake. Ya shiga
kicin ya ɗakko kofi da filet, a falon ƙasa ya zauna ya kunna tv domin kallon
labarai, yana kallonne yana cin abinci, lokaci-lokaci kuma yakan amsa waya idan an
kirashi, ya daɗe zaune a falon har aka kammala labaran kafin ya miƙe yay ciki dan
yana matuƙar buƙatar hutawa.

SHAHUDAH

Saboda son haɗuwa da Jawaad yasa yau taƙi binsu Mom gida, a cewarta nan zata
kwana, Mom bata hanata ba, suka tafi ita da Aamilah kawai saboda Salman ne yazo
ɗaukarsu dama ba driver ba.
Wajen ƙarfe goma ta kammala kwalliyarta, tai shiga cikin kayan barci masu
taushi da ƙyau, dan sunyi masifar fidda mata surarta, sai ƙamshi take kamar jikar
gidan mai turare, a ranta ta ƙudiri aniyar maido hankalin mijinta kanta yau, dan ta
gaji da wannan wasan ɓuyan da sukeyi, ta kuma shirya karɓar cikin da yake buƙata.
(Karku manta Shahudah batasan Jawaad ya saketa ba fa😥🤦🏻, ɓoye mata shine kuskuren
dasu mom suka tafka).
Hijjab ɗin mama Atika da ya kai mata har ƙasa ta ɗauka ta saka, babu kowa a
sashen na mama Atika, itama tayi barci ma tun ɗazun, kai tsaye Shahudah ta nufi
sashen Jawaad tanata zuba murmushi, dan ita kaɗai tasan abubuwan data shirya masa,
yau ɗinan basai gobeba sai ta zautar da gayen nan, ta sake sakin tattausan murmushi
lokacin data murɗa ƙofar taji ta buɗe. Jawaad ya manta shaf bai rufeba ya haye
sama, sai da ta gama ƙarema falon kallo, komai tsaf tamkar ba namiji ke zauneba,
tasan Jawaad yanada tsafta, sam bayason ƙazanta, duk jin kan nan nasa baya ƙyashin
tashi yay shara yay morping wa sashen,, ya samu wannan horonne a zamansa da kakarsa
Mama maryam, hatta da girki Jawaad ya iya, kawai rashin isashen lokacin kai ne ke
hanashi yi. batasan miyasa bayason masu hidimaba. Ta sake sakin murmushi kafin ta
fara taka steps ɗin a hankali tana wani yauƙi saikace tarwaɗa, a falo ta cire
hijjab ɗin ta jefa saman kujera, ta kuma gyara rigarta da gashinta sannan ta nufi
hanyar ɗakinsa.

Jawaad kam a gajiye yake matuƙa. hakan yasa yana shigowa bayan yay brush da
alwala yay adduar barci ya kwanta, bai wani jima da kwanciyaba barci yay gaba
dashi, fitilar gefen gado ce kawai a kunne, itama ta ɓangare ɗaya, hakan yasa ɗakin
yay dim babu haske sosai, bai kumayi dunɗum ba. Shahudah data murɗa ƙofar ta shigo
a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana mai shaƙar ƙamshin da ɗakin keyi, komai na
Bb'n ta daban yake dana kowa, bata ganin fuskarsa, dan ya juya ma ƙofar bayane,
sannan ya lulluɓa da bargo saboda uban AC'n daya ƙure ɗakin da shi, ‘ko tsoron
murama bayayi’ ta faɗa tana ɗaukar remote ɗin acn ta rage ƙarfinsa.
Jawaad da baisanma hidimar da akeba barcinsa yake hankali kwance da mafarki
mai daɗi, hakan yasa yaketa faman sauke numfashi a hankali. Ya sauke ajiyar zuciya
lokacin da Shahudah ta hawo gadon a hankali ta kwanto bayansa bayan ta ɗaga bargon
ta shiga, itama ajiyar zuciyar ta sauke ƙwallan kewarsa na taruwar mata a idanu,
jitake tamkar ta haɗiyesa ta hutama kawai. Cikin salon data shirya masa a wa

nnan dare ta fara yawo da hannunta a jikinsa, Jawaad dai bai motsaba, amma da alama
jikinsa na karɓar saƙwannin Shahudah kamar yanda tai fata. Mafarkin da Jay keyi da
saɓanin Shahudah yay dai-dai da abinda take masa a zahiri, hakanne yasa ta samu
haɗin kan gangar jikinsa har takai ya gyara kwanciyarsa yana sake rungumeta, hakan
yayma Huda daɗi kuwa, ta ƙara ƙaimi kan abinda takeyi, kamar wasa saiga tafiya tayi
nisa a tsakaninsu, dan tuni ya fara maida mata murtanin sumbatarsa da takeyi.
Yanda take sauke numfashi ne da sauri-sauri akan fuskarsa ya sakashi
farkawa, dan kuwa tabbas wannan al'amarin ya wuce a mafarki kawai, a matuƙar razane
ya hankaɗeta daga jikinsa yana ambaton “Innalillahi wa-inna ilaihirraji'un. Wace
ƴar iska ce haka ta shigomin ɗaki?”. Yay maganar yana ƙoƙarin kunna fitilar ɗakin.
Shahudah daya jefar gefe duk da taji zafi tai ƙoƙarin tashi zaune tana sauke
numfashi a gwame, hasken daya gauraye ɗakin ne ya basu damar ganin juna. Kansa ya
dafe yana ƙara ambaton “Innalillahi....” Shahudah ta matso jikinsa tana neman
kwantawa a kafaɗarsa ya sake tureta a fusace, “Wai ke wane irin dabbanci ne wannan?
shin baki da hankaline Hudah?”. Tabbas maganganunsa sun mata zafi, amma saita daure
cikin dakewa da tsiwarta tace, “Dan nazo wajen mijina zakacemin banda hankali?, to
ka ɗauka ni da kai duk mun zama mahaukatan”.
Karon farko Jawaad ya waro idanu waje, yace, “Miji!?, Hudah rashin ilimin
addinin naki harya ƙara faɗaɗa haka? Kinga bani da lokacin wannan haukar tashi ki
fitarmin daga sashe kafin na saɓa miki kamanni, kuma wlhy wannan yazama na farko na
ƙarshe da zaki sake shigomin nan”.
Kuka Shahudah ta saki, ta nuna kanta tana faɗin, “Yanzu nan tsanar da kaimin
bb har ta kai haka? To wlhy babu inda zanje, dan inada haƙƙi a kanka ai, duk ma
abinda zakayi sai kaitayi, amma ka sani niba ƴar iska bace, amma wlhy da tuni naje
na nema wani namijin a waj.......”
Mari ya kai mata tai saurin kaucewa, cikin daka tsawa yace, “Tashi ki fita a
ɗakinan kafin na raba kanki da wuyanki wawuya kawai!!”. Saurin sauka tay a gadon,
dan yanda ya harzuƙo ɗinan zai iya maketa, batasan ma bashi da wannan ƙarfinba a
yanzu, dan ta sakashi a kwale-kwale. Da ƙyar Jawaad ya iya sakkowa a gadon saboda
tashin hankalin da Shahudah ta sakashi, duk ƙoƙarin kame kansa da dauriyar da
yakeyi yau ta kwanto masa liƙi, ya murzama ƙofar key ya dawo saman gadon jiki babu
ƙwari. Gaba ɗaya kansa ya toshe, yama gaza yin tunani akan Shahudah.
Duk yanda Jawaad yaso yayi barci a wannan daren ya kasa, gashi maganin da
yake sha ya barsa a office saboda ya ƙare ya sayosu jiya, sai kuma ya manta bai
ɗakkoba, ya watsama jikinsa ruwan sanyi yafi sau shidda kafin asuba, sosai mararsa
ke masa masifar ciwo, ko sallar asuba bai fitaba a ɗaki yayi, sai bayan ya idarne
barci ɓarawo ya sacesa, shima a matuƙar wahale yayisa.

Shahudah kuwa da kuka rurus tabar sashen zuwa sashen mama Atika, a falo ta
zube tacigaba da kukanta har barci ɓarawo ya saceta.

_______________________________

Yau ma har muka fito Office banga kowa a cikin ƴan gidanba,
cikin nishaɗi muke ƴar firarmu da Yah Qaseem har muka iso, saida na rakashi har
office da tarkacensa sannan na fito nima zuwa namu.
Ummie bata isoba, hakan yasa na zauna bayan mun gaisa da waɗanda na tarar,
ƴan abubuwan da baza'a rasaba na shiga yi, gefe ɗaya kuma ina amsa hirarsu Dawood
sama-sama akan aiki, a hankali mukaita ƙaruwa har kowa ya gama isowa, Ummie ta
zauna saman tebirina tana faɗin, “Bily gulma da ɗumi-ɗuminta fa”.
Kallonta nai ina faɗin, “Ƴar sa ido mikika samo mana?”. Ƙaramar dariya
tayi da sauke murya ƙasa tace, “Ankawo kuɗin Nazifa”. “Dan ALLAH da gaske?” nai
maganar cikin waro ido waje bakina washe da fara'a. Ummie tace, “Wlhy da gaske
nake, kema tace ta kiraki bai shigaba, amma ta tura miki saƙo ai”. Wayata na ɗauka
ina faɗin, “Kashewa nai da zan kwanta, tunda na tashi kuma ban buɗe data ba, oh ni
su Nazifa an mana wayo, da Al-mustaphan dai?”. “Shi kuwa” cewar Ummie tana dariya.
Fita mukai zuwa can baya nai

kiran Nazifa a waya, bugu biyu ta ɗauka tana faɗin, “Inba gulmaba Bily miye na
kirana da farar safiyarnan?”. Dariya mukai ni da Ummie, nace, “Ai gara dai muci
gulmar da ɗuminta basai ta huceba, yarinyarnan da gaske dai kin dage aure kikeso?”.
“Ban isa bane?” Nazifa ta faɗa tana dariya. “Kin isa kuwa tsaf” Ummie ta bata amsa.
Haka muka cigaba da hira cikin so da ƙaunar juna har bamusan lokaci yaja ba.
Daƙyar muka iya katse hirar muka koma office gudun kar'a nememu.

JAWAAD

Kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan kuwa dai daga kwanciyar da
Jawaad yay bayan sallar asuba sai zazzaɓi mai azabar zafi ya rufesa, duk yanda yaso
ƙoƙarin tashi yay shirin office lamarin ya gagara. Wani wahalallen barcin nema ya
sake awan gaba dashi bayan ya koma saman gado yaja bargo.

Gimba yay shiri da wuri kamar yanda yasan suna sammakon fita, sai dai yafi
tsayuwar awa guda wajensu baba maigadi babu alamar boss ɗin nashi, dama kuma bai
gansa a massallaci ba yau da asuba. Bai dai tambayi kowaba ya cigaba da jira har
zuwa ƙarfe tara, zuwa lokacin dai kam abin ya fara bashi mamaki, abinda zai riƙe
boss har ƙarfe tara bai fita office ba to lallai dole ya saka kokwanto a zuciyar
duk wanda yake tare da shi, wayarsa yay kira har sau uku ba'a amsaba, ya sake
daurewa dai ya zauna awa ɗaya ta kuma shuɗewa goma tayi. Yanzu kam tilas ya miƙe ya
nufi sashen, yay knocking har kusan sau goma baiji motsin kowaba, hakan yasashi
murɗa ƙofar, cikin sa'a kuwa ta buɗe, sai dai koda ya shiga babu kowa a falon,
babuma alamar wani ya fito cikinsa. Nan kawai yake da hurumin shiga dan haka bai
ƙara gaba ba ya juya ya fita. Yabar wayarsa a mota har baisan su Oga Aliyu nata
kiransaba suma jin Boss baizo office ba, sun kuma kira wayoyinsa duka babu wacce ya
ɗaga, shine suke kiran Gimban suji ko wani waje sukaje? Amma shima kuma bai amsa
musu ba.
Misalin sha ɗaya da wasu mintuna sai ga Nabeelah da Ummansu sunzo gidan
domin sake yima mama Zainab gaisuwa, dan rabonsu da gidan tun ranar rasuwar. Bayan
sun shiga sashen mama zainab sun fito sai suka shiga wajen mama Badiyya don su
gaisheta da jiki, basu jimaba suka fito zuwa sashen mama Atika, ananne suka iske
Shahudah babu lafiya, tana kwance cikin doguwar kujera lulluɓe da bargo, sun mata
addu'ar samun lafiya suka miƙe zasu tafi amma sai mama Atika ta tsaidasu da zancen
auren Jawaad, murmushi Ummah tayi kawai, tabama mama Atika haƙuri akan zasu masa
magana, baki kawai mama Atika ta taɓe, su Umma kuma suka fito abinsu Nabeelah nata
ƙunƙuni akan ansama yayansu ido. Basuyi zaton samun Jawaad a gidaba, dan haka sukai
yunƙurin barin gidan, Gimba daketa dakon jiran fitowarsu yay azamar isowa garesu
yana gaida Umma, da mamaki ta amsa masa, “A'a gimba baku fita office bane ko dawowa
kayi kai?”.
“Wlhy mama bamu fitaba, har yanzu boss bai fitoba, bansan ko lafiya ba? Nai
knocking na kirashi amma duk babu wani amsa”.
Shiru Ummah tayi na wasu sakanni, sai kuma ta fasa shiga motar ta nufi sashen
Jay, Nabeelah ma data tuƙosu harta shiga mota ta kunna ta kashe ta fito tabi bayan
Ummah.

________________________________

kasancewar juma'a ce yau ɗin bayan an sakko salla mun fito zamu fita
neman abinci saboda yunwar da nakeji mukaci karo da Oga Jabeer zai shiga mota, har
mun gaishesa munwuce sai kuma yay kirana. Dawowa nai ina amsa masa da girmamawa,
yace, “Shigo mota ki rakani wani waje”.
Duk da banso ba sai ban masa musuba na shiga Ummie kuma ta wuce tana min
dariyar mugunta............✍

“Saura muji wani yace Hudah🙄 ehe😏.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

[11/30/2020, 12:59 PM] HASNA ✍🏻


: Bilyn Abdull :
Page 11

...............Tafiyar da batafi mintina talatin ba muka iso inda ya bani


mamaki, bandai cema oga Jabeer komaiba har aka buɗe mana gate muka shiga. A dai-dai
sashen da mukai salla ranar rasuwar Uncle Usman yay fakin, ya kashe motar yana
faɗin, “Muje ko”.
Bance komaiba na buɗe murfin na fita kamar yanda shima yayi, yana gaba
ina biye da shi har zuwa ƙofar falon, sai kalle-kalle nake ina ƙara jinjina girman
wannan gida, koba'a faɗaba kasan an narkar da dukiya wajen ginashi, Oga jabeer ne
yay knocking, babu jimawa akazo aka buɗe ƙofar.
Cikin murmushi Nabeelah data buɗe ƙofar tace, “Yah Jabeer sannu da zuwa”.
“Yauwa Nabeelah” ya amsa yana mata murmushi shima. Sai da ya shige sannan ta ganni,
cike da mamaki ta waro idanu alamar ganina a bazata da tai, kafin ta daka tsalle
ta ɗaneni tana dariya, “Lah ƙawata dama rai kanga rai?”. Murmushi nayi ina mai
jinjina wautar Nabeelah a raina, cikin surutunta tace, “Dama kinsan Yah Jabeer?”.
Amsa na bata da cewar, “Eh, wajen aikinmu ɗaya”. Zata sake jehomin wata tambayar
Jabeer ya katseta, “To Akku mai bakin magana kaimu ɗakin da yake”.
Yanda tayi da fuskane ya sakani yin murmushi, ita a dole taji haushin
ance mata Akku, hannuna ta kama tana tuttura baki gaba tai mana jagora har sama,
bansan minene ya kawomuba balle tunanin wajen wa mukazo, ni dai kawai inabin
Umarnine. ‘Tabɗi’ na faɗa a raina saboda ganin yanda falon saman ya haɗu matuƙa
shima, sai sassanyan ƙamshi ke tashi, muryar kamilar mace ta amsa mana sallamar da
mukai tare da faɗin, “Jabiru sannunku, ku shigo mana”.
Oga Jabeer ya amsa da “Yauwa Umma, ashe kema kina nan?”. Tace, “Eh muma bamu
jima da zuwaba, nazo na sakema Hajiya Zainab gaisuwane sai Gimba ke cemin basu fita
Office ba, yanata jiran Jawaad ya fito bai fitoba, shinefa na shigo na iskesa
kwance rijif cikin zazzaɓi”.
“Ya salam, wlhy muma a office tun ɗazu muke zuba idon ganinsa amma shiru,
mun kirasa bai ɗaukaba hakama Gimba, tomu tunaninmu koma wani wajen sukaje tunda
munga jiya lafiya lau yabar office, sai daga baya ne gimba ya kira yasanar mana ai
baida lafiya, ko sallar juma'a ma da ƙyar in zai iya fita, shinefa nace bara mu
sakko massalaci nazo naga jikin nasa, tunda su Hafiz sun fita wani aiki”.
Sosai gabana ya faɗi da jin sunan Boss a zancensu, harda ƙarin furucin
rashin lafiya, banji amsar data bama Jabeer ba saboda tunanin dana tafi.......

Hannuna da aka riƙone ya katse mani tunani, na kalli Ummah data riƙonin nai
ƙasa da kai ina faɗin, “Ina yini”. Ummah tace, “Lah kece Auntyna? Aini bamma
ganekiba da farko wlhy nama zata Maman Areef ce (Matar Jabeer). “A'a Umma nice” na
bata amsa kaina a ƙasa, kafin ta samu damar yimin tambaya Jabeer ya bata amsa da
cewar, “A'a Umma ba Fannah bace, Mom ɗinmu ce, da alama ma kin santa kenan?”. Ummah
tai murmushi tana zaunar dani a kujerar kusa da ita, tace, “Nasanta Jabiru, ƙawar
Nabeelah ce ai, ina ka samo mana ita ne haka? Ko dai ta biyu ce?”. Yanzun kam
ƙaramar dariya Jabeer yay yana girgiza kansa, “Wai Ummah ta biyu kuma? A wannan
marrar ɗayarma ya aka ƙare, sai dai idan zaki nemarwa ɗanki ne, shine gwauro, wajen
aikinmu ɗaya da Mom ɗinmu” ya ƙare maganar idonsa a kaina.
Dariya tayi tana sake riƙo hannuna, cikin sigar tambaya tace, “ɗiyata kina
son ɗana?”. Kasa cemata komai nai sai ƙasa dana ƙarayi da kaina, a raina ina faɗin,
‘Ni inada Yah Qaseem ɗina’. Jin bance komaiba ta maida kallonta ga Jabeer,
Cike da mamaki tace, “Waima tsaya Jabiru, kana nufin itama irin aikin
naku takeyi?”. “Sosaima kuwa Ummah” ya bata amsa cike da karsashi. Haɓa ta riƙe
tana sake damƙe hannuna, “Oh ni ɗiyata, kekuma abinda ya burgeki kenan? To Nabeelah
kinji fa jaruman mata, ba irinki matsoraciya ba” Nabeelah da mamaki ya kashe tace,
“Wai dan ALLAH da gaske?”. Hararta Jabeer yay yace, “Da gaske mana”. Nabeelah tace,
“Tab, wlhy bari Yah Jay ya warke nima ƴar sanda zan zama”. dariya Umma da Jabeer
sukai mata, nidai na murmusa ina kallonta da faɗin, “Dakin burge kuwa, kinga ƙawata
ta dawo kusa dani”. Da sauri ta cafe da faɗin, “Karki damu ƙawa in

a nan tafe, kam Nabeelah ƴar sanda, ashe zan ragargaji ƙattai”.
Jabeer yace, “ko kuma ke su ragargajeki ba”. Ɓata fuska tai da tura baki,
“A'a wlhy Yah Jabeer kar kai min baki tun yanzu”.

Kafin ya bata amsa Ummah tace, “Kaga Jabiru kubar wannan ba gajiya zataiba,
ku shiga yana ciki, amma ban saniba ko idonsa biyu dan Doctor ya saka masa ruwa tun
ɗazun”.
Miƙewa mukai muna faɗin ALLAH ya bashi lafiya.

Oga Jabeer na gaba ina biye da shi har cikin ɗakin nasa da ya gama haɗuwa,
babu wani datti balle tarkace, nayi zaton zamu sami matarsa a cikin ɗakin, amma sai
naga shi kaɗaine kwance a kan gado lulluɓe da farin bargo, hannunsa ɗaya liƙe da
ruwan da ake saka masa, ya ɗora ɗayan saman cikinsa, fuskarsa tayi wani irin fayau
alamar yaɗan rame. Yauce rana ta farko dana iya masa kallon kai tsaye kuma na
tsawon mintuna, ƙyaƙyƙyawane, komai nasa dai-dai da fuskarsa.........
“Momcy zauna mana” Oga Jabeer ya faɗa cikin katsemin tunani, kaina na jinjina na
zauna saman stool ɗin daya ajiyemin kusa da gadon kaɗan, shi kuma ya zauna a bakin
gadon kusa da shi, hannu yakai saman kansa yanason jin yanayin jikin nasa, ni dai
ɗauke kaina nai na maida wajen kallon ƙaramin hoton dake drawer gefen gadon, da
gani tsohon hotone, ƙyawawan mata da miji da suke a ganiyar shekarun ƙuruciya,
sunyi ƙyau sosai da dacewa da juna, ga hoton ya ɗauku duk da bana wannan zamanin
bane.

Jawaad ya buɗe ido a hankali saboda hannu da Jabeer ya ɗaura masa a


goshi, akan Bilkisu dake saitinsa ya saukesu, ya ɗan lumshe ya sake buɗewa akan
nata, sunɗan kumburo sannan sun sake girma, daga ciki sunyi jaa kaɗa alamar dai
bayajin daɗi. Jabeer ya kalla kafin ya sake maida idonsa kan Bilkisu, ya kuma
janyewa yabi inda yaga idonta na kallo shima, hankalinta nakan kallon hoton Mamansa
da Abbansa daya ajiye a bed side drawer, shima Jabeer kallon wajen yayi, amma a
mamakinsa sai yaga Jawaad yakai hannu ya juya hoton. Murmushi Jabeer yay yana
girgiza kansa.
Hankalina na dawo ganin an juya hoton, nai saurin bin hannun daya juyaɗin
da kallo har zuwa fuskar mamallakin hannun, idanunsa a kaina suke, dan haka na
janye nawa ina ɗan yamutsa fuska, a raina nace, ‘Baida lafiya ma bazai bar shegen
kallon mutane ba’.
Jabeer dake binsu da kallo shidai yay ƴar dariya kawai, kafin yace, “A
kacema ka warke mu tashi muje kawai?”. Harara Jawaad ya zuba masa, sai kuma ya miƙa
masa hannunsa da aka saka ruwan, yay masa alama da ido akan ya cire masa. Kallon
ledar ruwan Jabeer yay, yace, “Ya za'a cire bai ƙareba?, saura kaɗan ai, kaɗan sake
haƙuri”. Jawaad da sai yanzune zaiyi magana ya yamutse fuska da motsa laɓɓansa a
hankali saboda rashin jin ƙarfin jiki, “To sannu likita, kaga ni ciremin, dama
Ummah ce ta takura aka sakan”.
Kafin Oga Jabeer yace wani abu na katsesu da cewar, “Ina yini, ya jiki”. Ban
yarda na kallesa ba. hakan yasan bansan a yanda ya amsa minba.
Kallonta Jawaad yay ya janye idanunsa, akan laɓaɓansa yace, “Alhmdllh”.
Sallamar Ummah yasa duk muka kalli ƙofa, tace, “A ya ake cire ruwan bai
ƙareba?”. Jabeer yace, “Wlhy Ummah kema ƙya faɗa, cayay a cire wai”. Ummah tace,
“Kaci gidanku Jawaad, saurin mikake to? Duk abinka dai bazaka fita aikiba yau, dan
a gidannan ma zan yini, dan karna tafi ka saci jiki kace zaka tafi ma agogo sarkin
aiki”. Fuska ya ɓata, yace, “Kai Ummah ni nagaji da kwanciyarnan, kumafa naji
sauƙi” “Haka mukeso dama ai kasamu sauƙin, amma babu inda zakaje, barama na haɗa
maka ruwa kai wanka kaji daɗin jikinka”.
Yanda ya cuskule fuska ni saima yaban dariya, a raina nace ‘duk girman ɗa a
gaban uwa shi yarone’ Har Ummah ta nufi haɗa masa ruwan sai naga kamar bai dace ba
ina zaune na barta da aiki, miƙewa nai ina faɗin, “Ummah ki barshi bara na haɗa,
inane bayin?”. Murmushi Umma tayi tana kallon Bilkisu da yaba hankalinta, tace, “To
ɗiyata kuma Yayata nagode kinji, ga shinan shiga”. Kaina na jinjina mata na nufi
inda ta nuna mani.
Jabeer da yaji daɗin abinda Bilkisun tayi yay murmushi yana kallon Jay,
“Jay wlhy yarinyar nan tanada hankali”. Banza Jawaad yay m

asa tamkar baijiba. Jabeer yace, “Nasanfa kaji minace”. “Malam ka cikani da surutu,
zaka fita a ɗakinan fa” dariya Jabeer ya kwashe da ita, dan shikam dai ransa na
bashi abubuwa da dama. Idanun Jawaad dake harar Jabeer tamkar zasu faɗo ya nuna
masa hanyar fita. Jabeer yace, “ALLAH babu inda zani, dama kasamu mukazo dubaka,
bara na kira su Hafiz nace karma suzo ka warke”.

Koda na shiga toilet ɗin saida na tsaya nagama ƙare masa kallo, ‘Humm’
kawai na iya faɗa, dukda babu wani datti sai naga dacewar fara wankewa kafin na
haɗa ruwan, cikin mintuna ƙalilan na gama tsaftace bayin kafin na haɗa masa ruwa
mai zafi sosai, a ganina idan yazo bai masa dai-daiba sai ya sake sirkawa, lokacin
dana fito iskesa nai zaune a bakin gadon, kayan barcine jikinsa farare, wandon dogo
har ƙasa, hakan yasa banji na takuraba, maganar aiki sukeyi yanzunkam, sai dai shi
yana dafe da kansa alamar yana masa ciwo ko yay masa nauyi. nace, “An haɗa ruwan”.
Jabeer ne kawai yacemin “Sannu da aiki” shiko baima kalleniba ya miƙe ya nufi bayin
yana tafiya a hankali.
Bayan shigewarsa Oga Jabeer ya miƙe yana faɗin, “Bara na sayo masa abu na
dawo, kiɗan gyara masa ɗakin”. Kaina kawai na ɗaga masa dukda banso hakanba, sai
mita nake a raina akan ‘to ina matarsa da ita bazatazo ta gyaraba, ni kofa haɗa
ruwan wankanma dan naga Ummah ce zatayi, a matsayinta na babba kuma bai kamata na
bartaba bayan ina zaune a wajen’ haka naita mita ina aiki, na gyara gadon tsaf tare
da jera filolin a wani style mai ƙyau, nidai kawai nayine saboda inason gyaran gado
dama can, balle irin wannan da yaji kayan shinfiɗa na alfarma, ga filos da yawa.
Ina cikin gyaran gadon ne Nabeelah ta shigo da kayan shara. Tace, “Lah ƙawata daga
zuwa dubiya sai a sakaki aiki? Ummah tace kije ki huta bara na gyara”. Murmushi na
mata nace, “A'a ki barsa kawai, ɗakinma ai babu datti”. ƙasa tai da murya tana
kallon toilet tace, “Yayanmu ba'ai masa abin arziƙi ai, kaɗan daga aikinsa ya fito
ya sakaki wani aikin kuma”. Tabani dariya yanda takeyi tana kallon bayin, nace,
“Dama ya fito ya jiki”. Kafin na rufe baki ta fice a ɗakin da gudu tana faɗin,
“Saikin fito, dama girki nake masa”. Kaina na girgiza kawai naci gaba da aikin ina
jinjina wautarta, gata dai zamuyi sa'anni, amma nakula Nabeelah autace kodan
shiriritarta.
Har na gama gyara komai tsaf bai fitoba, na kammala morping tsaf kafin na
ɗauka turaren ɗaki dana gani saman ƴar dirowar farkon shigowa ɗakin kala-kala,
ɗauka nai nahau fesawa jikin labuloli da saman gado dama ɗakin gaba ɗaya, a bazata
naji an buɗe ƙofar bayin, hakanne ya sakani kallon wajen babu shiri, ai kallo ɗaya
nai masa na juya da sauri na nufi ƙofar fita ɗakin, gwangwanin freshener ɗin na
ajiye na ɗauki bokitin danai morping nai waje abuna.
Jawaad dai yana tsaye a ƙofar bayin yana binta da kallo harta
fice, shima baiyi zaton samun kowa a ɗakinba shiyyasa ya fito kansa tsaye, dukda ma
dai sanye yake da rigar wanka a jikinsa ba towel ba, cikin rashin jin ƙarfin jiki
ya tako zuwa cikin ɗakin, har yanzu mararsa a ƙulle take, dukda dai bakamar jiya da
dare ba, da kuma safiyar yau, danma ƙin faɗama Doctor ɗin ainahin abinda ke damunsa
yay, cayay kawai zazzaɓine ke damunsa, shi kaɗai yasan yanda yakejin haushin
Shahudah da kuma matakin dazai ɗauka a kanta. Idanunsa suka sauka akan gadon da
yanda akaima filolin, kasa ɗauke idanunsa yay har na tsahon mintuna kusan biyu,
sosai gadon yay masa ƙyau, sai yaga tamkar ba gadonsa ba.

Tunda na fito Ummah keta faman jeramin sannu, ni dai murmushi kawai nake,
na gyara falon saman ma duk da babu datti, falon ƙasa dai Nabeelah na iske ta gyara
harma tana morping. Kiran da Umma taimin daga kicin na amsa, ta miƙamin ƙaramin
tire data ɗaura kofin tea a kai yanata turiri, “Yauwa ɗiyata dan ALLAH miƙama
yayanku wannan ya fara sha kafin wannan uwar shiriritar ta kammala girkin, daga nan
sai kiji ko yana buƙatar wani abun kuma”. “To” kawai na iya ce mata na amsa na
fito. Koda na fito sai na roƙi Nabeelah tazo ta rakani, catai ALLAH naje ni kaɗai,
dan inhar mukaje mu biyu cazai anmasa gayya.
Badan nasoba

na nufi saman ni kaɗai, addu'a nake a raina Oga Jabeer yazo mu wuce. Sai da nai
knocking ya bani izinin shiga sannan na shiga da sallama, kaina a ƙasa ban yarda na
kalli ko inaba sai gabana, saida naje dab da shine sannan na kallesa sau ɗauya na
ɗauke idona, har ya saka kaya, baƙin wando da yellow ɗin riga folo, yana zaune ne a
bakin gado da waya a hannunsa, hannunsa ɗaya dafe da kansa yanzu ma, nidai na ajiye
tiren a gabansa ina faɗin, “Gashi inji Ummah, tace kanason wani abune?”. Banji ya
tankaba, bankuma damu da yace ɗinba dama na miƙe zan fita.
“Zonan” ya faɗa a hankali. Dawowa nai ina jan numfashina da ƙyar, dan duk a
takure nake, danma zuwa yanzu kamar naɗan fara sabawa da kasancewarmu tare zuciyata
ta sassauta min wajen bugun da takeyi idan har muna tare. Nace, “Gani”. Shiru
yaymin kamar ba shine yay kiranaba, sai da yaja wasu sakanni kafin ya nunamin dogon
table ɗin dake a gaban gadon ta gaba, “Ɗauka waɗancan keys ɗin, kije Gimba ya kaiki
station, zaki ɗakkomin abu a office”.
Duk yanda naso daurewa sai da gabana ya faɗi, ta yaya zanje na buɗe office
ɗinsa nikam? A matsayin wa? Na shiga uku, mutumin nan nason jefani a matsala shidai
na lura......
“Miemaa!” ya faɗa a ɗan tsawace ganin dukma bayanin da yake mata hankalinta
baya tare da shi. Firgigit na kawo numfashi tare da kallonsa, yanda ya danƙaramin
harara ya sakani saurin duƙar da kaina. “Ina miki magana kina wani banzan tunani”.
“Sorry sir” na faɗa da sanyin murya, dan harga ALLAH banji miya faɗaba”. Ƙaramin
tsaki yaja, ya miƙomin waya batare da ya ce min komaiba, amsa nai ina jiran ƙarin
bayani, amma sai ya shareni yama ɗauki tea ɗinsa ya fara sha.
“Tashimin a kai kafin na canja miki kalar fuskarki”. Fuska na kumbura na
juya na fita ina ƙunƙuni a raina.
Jawaad dake binta da harara yay ƙaramin tsaki da faɗin, “Miskilar banza
kawai”.

Banason zuwa ni kaɗai, hakan yasani cema Nabeelah tazo muje ya aikemu, da
yake batasan gaskiyar zancenba sai ta bini muka bar Ummah na haɗa masa abinci. A
jikin mota muka iske gimba da alamar yasan da tafiyar, zai buɗe mana mota nace ya
barsa kawai, murmushi yayi ya shiga mazaunin driver yana tambayarmu “ya jikin boss
ɗin” da sauƙi, muka faɗa kusan a tare sannan muka gaidashi.
Tunda muka tafi Nabeelah ke zuba mana surutu, Gimba nata biye mata, nidai
murmushi ne nawa idan sunyi wani abun dariyar, har mamaki nake yanda Nabeelah bata
gajiya da zance saikace wata akku.
Nidai har Gimba yay fakin addu'a nake ALLAH yasa karna haɗu da Yah Qaseem,
gefe kuma ga maganar shiga Office ɗinsa bansan yanda za'a fassarani ba, sauƙinma na
taho da Nabeelah ne, tunanin zuwa office ɗin Oga Aliyu ko Hafiz nayi, saisu kaimu
office ɗin, a ganina hakan sai yafi, jan Nabeelah nai zuwa Office's ɗin nasu sai
dai munyi rashin sa'a duk a rufe alamar bamasa station ɗin kenan................✍

“Team Bil-Qas & Jay-Hud. Saura wani yace sunan baiyiba😏😜😂”

Fatan alkairi a gareku baki ɗaya😍😍😘👌🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[11/30/2020, 12:58 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:


Page 12

.............Babu yanda na iya dole naja hannun Nabeelah muka nufi office ɗin, sai
dai tunma a hawan farko aka dakatar da Nabeelah, ni kaɗai aka bari na wuce, kamar
na fasa kuka haka naji, sai dai nayi mamaki a raina yanda babu wanda ya tambayeni
mizanje yi?.
Office ɗin na nan tsaf, duk da yau ba'a gyaraba tunda baizoba babu wani
datti, yau kam ban cuci kainaba saida nagama ƙare masa kallo gabas da yamma kudu da
arewa, hatta da hotunan saman tebir ɗinsa sai da na gama kalleso, tsabar jan magana
irin tawa na zauna saman kujerarsa ina gwada yanda yake zama, nakai kusan mintuna
huɗu ina shirirtata kafin kira ya shigo wayar da ya bani, ƙurama wayar ido nayi
tamkar mai tsoron ɗauka har sai da ta kusa katsewa sannan na ɗauka nasa a kunne
batare da nayi maganaba. Daga canma shiru anƙi cewa komai harna tsahon sakanni.
“Baki iya sallama bane?” muryarsa ta daki kunnena a bazata, idanu na zaro
waje dan wlhy banyi zaton shi bane, nace, “Sorry Sir” bai amsa minba sai cewa da
yay, ki buɗe ƙaraman drawer na jikin table akwai faran leda da kwali a ciki ki
ciroshi” na amsa da “to”. Ina ƙoƙarin jawo ledan kwalin ya fita a ciki, hakanne ya
sani cirosu ɗai-ɗai shi da ledan, haka kawai na tsinci kaina dason karanta abinda
aka rubuta a kwalin, dan da alama na magani ne, shaf na manta da wayar a kunne take
bai kasheba, na hau karatun rubutun jikin maganin ina faman zaro idanu saboda
fahimtar danai maganin na miye. Daga can Jawaad da yaji a jikinsa akwai abinda ta
nutsu takeyi wanda ya ɗaura zarginsa akan maganin cikin sanyin murya yay magana
saboda cikinsa dake murɗa masa a lokacin, “Bincike kike mini?” a bazata naji
maganar tasa, shiyyasa na saki kwalin ƙasa batare dana shirya ba, cikin rawar baki,
nace, “A...a'a sir” shiru Jawaad baice komaiba idanunsa a lumshe yana faman cizon
lip ɗinsa na ƙasa, sai da ya lafa masa sannan ya sake maida hankali akan wayar,
nikam duk a tsorace nake, gani nake tamkar ya gane mi nakeyi, cigaba yay da lissafo
min duk abinda yake buƙata, na sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya jin yabar waccan
maganar, na ɗauka kwalin maganin na maida a ledar ina cigaba da ɗaukar duk abinda
yace, inda kuma ya faɗa anan nake ganinsa, bayan na haɗasu na zuba a wata leda baƙa
na fito.

A ƙasa na iske Nabeelah ta cika tai fam da haushi, taban dariya, hakan yasa
na murmusa ina kamo hannunta, ƙwafa tai tace, “ALLAH yayanmun nan ko, saina rama
abinda yay min”. Nace, “Miyay miki?” ta sake yin ƙwafa, “Bakiga yasa a hanani shiga
office ɗinsa ba, ALLAH nima duk randa na fara aiki bazan bari yazomin office ba”.
Yanzunkam kasa jurewa nai saida na dara, “Oh Nabeelah yaushe ya hanaki shiga Office
ɗinsa, jami'anmu dai sun hanaki”.
“Kutt wlhy bakisan halinsaba ne, nasan shine yace karsu barni”. Nace, “To
kiyi haƙuri, Yaya yayi laifi”. Tunanin zamu dawo yanzu da oga Jabeer yasa ban shiga
ko inaba, Mun isa wajen Gimba ya ɗaukemu muka koma, yanzu kam a falon ƙasa muka
iskesu harda su Aliyu, mamaki ƙarara na gani a idanun Rose saboda ganina, a tare na
gaishesu gaba ɗayansu na ƙarasa gaban sarakin dake kwance a doguwar kujera, cikin
girmamawa na ajiye ledan da keys ɗin da wayar a table ɗin dake gabansa nace,
“Gashi”. Idanunsa dake rufe ya buɗe ya zubasu a kaina, “Dama tare da Nabeelah na
aikeki?” yay maganar yana hararata. Ƙasa nai da idanuna ina girgiza masa kaina
alamar a'a. Ƙwafa yay ya ɗauke kansa, ganin hakan yasani barin wajen da nufin bar
musu falon ma.
“Waye zai ɗauke miki kayan nan”. juyowa nayi, kafin na ƙaraso wajensa
Rose dake zaune a kujerar dake inda ƙafafunsa suke ta miƙe ta ɗauki ledan da cewar,
“Ƙyale shashasha boss ina za'a kai?”. Banza yay bai tanka ba, niko na sake juyawa
zan fita. “K! Ina wasa dake ko?”. Nazata da Rose ɗin yake hakan yasa nai yunƙuri
cigaba da tafiyata Aliyu ya kirani.
“Momi zoki amsa ki kai masa sama kinji”. “To” nace, na dawo na miƙama rose
dake ɗauke da ledan hannu alamar ta bani, wata banzar harara ta zubamin ta
dangwarar da ledar ƙasa ta koma ta zauna, bance da ita uffanba na ɗauka ledar da
keys ɗin na nufi sama, dama duk abinnan da ake tuni Nabeelah ta haye tund

a muka shigo ta gaida su Hafiz ta haye abinta.


Bily na gama hayewa Jawaad ya miƙe cikin dauriya ya ɗauki ɗaya daga ruwan
da aka ajiyema su Hafiz yabi bayanta yana tafiya a hankali, dan inhar yace zaiyi
hanzari dolene a fahimci matsalarsa, ca yay musu yana zuwa. Rose ta bisa da kallo a
wani irin yanayi maisa ƙuna a zuciya, a ƙufule ta kalli su Aliyu tana faɗin, “Wai
miye haɗin wannan yarinyar da Boss ne?, shishshiginta yayi yawafa” dukansu da
mamaki suka kalleta, duk da sun fahimci tsagwaron kishi tattare da zancenta, Jabeer
ya kare bakinsa da hannu yana dariya ƙasa-ƙasa, sai da Hafiz ya hararesa sannan ya
haɗiye da ƙyar, ya kalli sama sannan ya maido dubansa ga Rose data sake cika fam.
“Wai Rose kina nufin sonta yake?”. Da sauri tace, “Itaɗin banza, kaima kasan Boss
ya wuce da ajinta, kawai dai itace ke shishshige masa”.
Hafiz yace, “Humm” Aliyu dake murmushi ne ya bata amsa, “Toke tunda kinsan
haka miye na damuwar, dan ya sakata aiki sai ya zama wani abu, sau nawa ke ya
sakaki ayyuka da sukafi wannan?”. Baki ta taɓe, cikin hausanta da bawani fita
yakeba tace, “Amma tunda muke nama taɓa zuwa nan gidan ne? Itako daga gani tana nan
tun ɗazun”. Cike da jin haushi Hafiz yace, “To idan ya sakko saiki masa wannan
tambayar kuma ai”. Harar Hafiz tayi, dan tun dama can basa shiri, baya shiga
sabgarta sai dole, dama sunfi ɗasawa da Jabeer duk cikinsu, Aliyu kuwa baida yawan
hayaniya, dan harma yafi Jawaad rashin son magana. Babu wanda ya sake cewa komai,
sai Rose daketa kallon hanyar benen tana cika da batsewa da sauke tagwayen ajiyar
zuciya.

A sama kuwa koda na isa Nabeelah na bama kayan akan yace takai masa su
ɗaki, har Nabeelah ta amsa zata wuce sai gashi ya hawo, hakan yasani saurin riƙo
ledan saboda wata uwar harara daya sauke min, Nabeelah ta juyo zatai magana itama
ta samu rabonta na harar, sakarmin ledar tayi da sauri tana barin wajen, ni kam dai
ƙasa nai da kai kawai.
Duk abinda sukeyi Ummah na zaune tana kallonsu, sai dai tayi kamar batasan
sunayiba.
Jawaad ya wuce ɗaki batare da yace komaiba, dan shikuma baima lura da Ummah
ba, bayansa nabi gudun karna sake wani laifin. baice dani komaiba harna ajiye ledan
nai hanyar fita. Na sauke numfashi ganin na fito lafiya, a raina ina mitar ‘mutum
sai baƙar takura’ matarka dai taga banu yasin, a can ƙasan raina kuma tunani nake
yanada mata to miya haɗashi da shan magani irin wannan?, nifa dukma sai naji inajin
kunyar abun yasin, nikam bazan sake yarda idona ya shiga cikin nashiba, wannan abun
kunya har ina haka. Muna a falon Nabeelah na fama dani akan abinci data zubo ya
fito, bai kalli kowaba a cikinmu ya sauka ƙasa.

Ban sakko ba har saida suka tashi tafiya Jabeer ya ƙwalamin kira, lokacin
dana ƙaraso duk sun fice daga shi sai Jabeer ɗin, inda yake Jabeer ya nunamin
alamar yana kirana, na ƙarasa gabansa dan yanzu ya tashi zaune, batare da ya
kalleni ba yace, “Ranar lahadi ƙarfe goma na safe kije ku haɗu da wannan yarinyar,
Jabeer zai baki address ɗin wajen”. nidai nace masa to ina jiran ƙarin bayani, sai
dai bai sake cewa komaiba, oga Jabeer yace, “muje to, Boss ALLAH ya ƙara sauƙi”.
“Amin” ya faɗa akan laɓɓa, nima nace ALLAH ya ƙara sauƙi nai gaba batare da jiran
ya amsaba, dan yaban haushi.
Ni da Jabeer a motarsa muka koma, su Aliyu kuwa suna a motar Hafiz da
sukazo a ciki, ina kallon yanda Rose keta bina da baƙar harara nai tamkar ban
ganiba.
Munzo fita daga layinne naga motar Mom zasu shiga su kuma, nace, “Lah ga
mom can”. Jabeer dake tuƙi yace, “Ƙila itama zataje ganin boss ne ko?”. Kallonsa
nai nace, “ganinsa kuma? Wai da gaske Ƴan uwansu ne?” dariya yay yana harba motar
kan titi, yace, “Momin mu kemafa na kula akwai shiririta wani sa'in, bakiga gidansu
ɗaya bane, ai da mom da Abban Jay babansu ɗaya, sannan Jay shine ya auri Shahudah
kafin su rabu”.
Mugun waro idanu nayi baki a hangame, nace, “Wai dan ALLAH oga kana nufin
dama shine mijin aunty Shahudah?”. Jabeer dake murmushi yace, “Ƙwarai kuwa, ammafa
a da kenan, amma ke yaya kuke dasu Shahudah da har bama kisaniba?”. Daƙyar na iya
ce masa

kamar yanda Mom suke da Abban Boss, nima da Abbansu Aunty Shahudah da Mamana
babansu ɗaya”.
Kai Jabeer ya shiga kaɗawa yana faɗin, “Tab cakwakiya kenan, kice shiyyasa
Qaseem beson kowa ya raɓu dake? Kodai ƴar gida zamuyi?”. Murmushin yaƙe kawai nai
masa bance komaiba, danni gaba ɗaya kaina ya toshe, koda wasa ban taɓa kawo cewar
boss mijin aunty Shahudah bane ba, to yama akai na kasa fahimta? Koda yake bai taɓa
zuwa gidanba ina nan, bankuma taɓa ganin koda hotonsa ba a gidan, amma kuma inban
mantaba nasha jin sunan Jawaad a bakin ƴan gidan, ‘ya salam, miya toshe min kaina
haka?’. Har mukaje station wannan tunani ne keta kaikawo tsakanin ƙwanyata da
zuciyata batare da nasan ma'anar hakanba, shima kuma oga Jabeer bai sake cemin
komaiba saima redio daya kunna.
Koda muka iso office nabi oga Jabeer kamar yanda ya umarceni, ya bani
ƙaramar takarda ta address ɗin wajen da boss yace sannan na fito. Na iske su ummie
sunata shirin tashi, dan biyar tayi, ALLAH ma ya soni nayi sallar la'asar yanzu da
muka koma gidansu boss, nima ɗaukar tarkacena nai muka fito tare, dan Ummie zanbi,
na leƙa office ɗin yah Qaseem bayan na fito daga wajen oga Jabeer na iske bayanan
ya fita wai. Daurewa nai na cire alaƙar Aunty Shahudah da boss data tsayan a rai ba
gaira ba sabar na biyema Ummie mukaita hirarmu, har gida ta kaini, sai dai bata
shigaba iyakarta gate na sauka ita kuma ta juya.
Na iske su a falo aunty Shahudah kwance Doctor na saka mata ƙarin ruwa, ba
hurumina bane tambayar abinda ya sameta, na gaishesu tare da mata sannu cikin
jimami sannan na wuce ɗaki abina. Bansan miyasa na tsinci kaina cikin rashin jin
daɗin komaiba, nai wanka na canja kaya, ganinma magrib tayi saina bari nai salla
sannan nai zaman yin azkar har aka kira sallar isha'i, itama tashi nai nayi sannan
na fito falon dan sake duba Aunty Shahudah, dan banajin yunwa, tun abincin da naci
a gidan boss bai sauka ba, duk da saida Nabeelah ma tai fushi sannan naci bayan
ummah ta saka baki.
Na iske aunty Shahudah ta koma ɗaki, sai yah Qaseem kawai a dining yana cin
abinci, sannu da dawowa nai masa, yay murmushi yana min alamar nazo. Ban musaba
naje garesa, naja kujera nima na zauna, “Kinyi ƙyau” ya faɗa yana kashemin ido
ɗaya, murmushi kawai nayi bance komaiba. Haka yayta ɗan jana da hira harya kammala,
ya miƙe domin zuwa yay wanka, nima miƙewar nai nace bara na sake duba aunty
Shahudah naje na kwanta na gaji.
Zaune na isketa Aunty Aamilah na bata magani, na sake mata sannu da ALLAH
ya ƙara sauƙi na fito, ɗaki na koma nai kwanciyata duk da nasan gobe idan ALLAH ya
kaimu babu aiki, amma inason na kira Dad da safe idan ya bari sai naje gidan Inna
Zainabu na gaishesu, da wannan tunanin barci ya kwasheni.

A ɗakin Shahudah kam bayan fitowar Bilkisu Aamilah ce ta sauke ajiyar zuciya
tana mai fuskantar ƴar uwar tata da ƙyau. “Sister ga shawara mana” Shahudah da duk
tazama kalar tausayi ta jinjina mata kai alamar tana saurarenta. Aamilah ta sake
jan numfashi kafin tace, “Ina ganin yarinyar nan Bilkisu zamu iya sakata tai mana
wani abu” murya a dasashe Shahudah tace, “Ban ganeba Aamilah ”. “Sister ina magana
ne akan Brother Jawaad, da nayi tunanin Broth ne a farko, sai dai daga baya nasan
bamai yuwuwa bane, musamman idan mukai dubi da yanda basama shiri tun suna yara,
sam jinin Qaseem da Jawaad bai haɗuba, bankuma san lokacin dazai haɗunba, so idan
mukace zamu ɗorasa akan ya taimaka mana sai dai ya ɓata komai tunda dama can bason
aurenku yakeba, yanzu da yarinyar nan ta shigo, sai naga mizai hana mu amfanu da
ita, dan kinsan bata da yawan hayaniya da surutu, sannan mutumin dake da irinki
bazai kalletaba da sigar birgewa balle akai ga so, ballantana zuciyarmu tayi
tunanin ko zata iya cin amanarmu, ko shi yaji wani abu a kanta”. Shahudah datai
shiru tana kallon Aamilah tace, “Maganganunki kawai naji Aamilah, amma ban gane ina
suka dosaba sam, wane taimko zamu nema akan Bb?”. “Yauwa, yanzu kikai tambaya mai
ƙyau Sisi na, inaji a raina Yarinyar zata taimakemu, sai dai bani da tabbacin wajen
aikinsu ɗaya, duk da dai naga kullum tare take fita da Broth, ku

ma Broth da Brother Jawaad wajen aikinsu ɗaya ne, amma wannan ba wani abu bane,
zamu iya tambayarta”. Kai kawai Shahudah ta jinjina alamar gamsuwa, Aamilah tace,
“ki kwanta ki huta zamu tattauna zuwa da safe, tunda weekend ne tana gida babu inda
take zuwa”. Nanma da kai Shahudah ta amsa mata..

★★★★★

Washe gari da safe na tashi nai ƴan ayyukan dazan iya harda kayana da sukai
datti, na gyara ɗakina tsaf nai wanka sannan na fito, babu kowa falon dan har
lokacin ma bana tunanin wani ya tashi a jama'ar gidan, kicin na nufa na samawa
cikina abinci naci, kafin na sake komawa ɗaki na shiga neman Number dad da ya
kirani kwanaki uku da suka shige, kusan duk Numbers nashi na ƙetare inada ita, dan
yakan kirani lokaci-lokaci idan yay tafiya tamkar yanda yakema sauran ƴaƴansa, bata
shigaba, na sake gwadawa har sau uku saina haƙura, bazan iya zuwa ko inaba bayan
wajen aiki saida umarninsa, dan banida wani jagora sama da shi a halin yanzu a
duniya, sai ko yaya Qaseem da nake fatan ya zama na biyu a matsayin miji. Na aje
maganar zuwa gidan Inna zainabu akan sai idan ALLAH ya kaimu gobe, idan naje inda
boss yace na gama abinda nakeyi sai na shiga wajen wanke kai daga nan na wuce can
koda ban jimaba sai na gaishesu na taho gida, da wannan tunanin na miƙe da nufin
zuwa gidansu Amina.
Harna fice babu motsin kowa, muka gaisa da baba mai-gadi na fice
abina. Da sallama na shiga gidan, Amina dake a tsakar gida tana wanke-wanke ta amsa
tana kumbura fuska, dariya nayi ganin yanda tayi, dan nasan dalili, ta ɗauke kanta
da faɗin, “Munyi fushi, ki koma a binki”. Kafin nace wani abu mama tace, “Kwarai
kuwa Amina ina bayanki”. Kunnuwana na kama duka biyu na kneeling alamar dai na
tuba, dariya suka sanya daga mama har Amina da yayan Amina daya fito da ga bayi,
shine yace, “A ni dai na yafe ma ƴar ƙanuwata, nasan aikine ke mata yawa”. Nace,
“Yauwa Yayanmu, shiyyasa nake yayinka a koda yaushe”. yay dariya da haɗe yatsun sa
babba da manuniya alamar dai-dai👌🏼 kenan.
“Oh, mu baƙya yayinmu kenan? To kin ƙarama kanki laifi har tsallon ƙwaɗo sai
kinyi” Amina ta faɗa tana miƙewa ɗauke da kwandon data saka kwanikan. Mama tace,
“A'a auta nimafa na huce, ama mai-gadon lu'u-lu'u haƙuri”. Dariya muka saka gaba
ɗayanmu saboda furicin mama, Amina tace, “Shikenan na haƙura tunda mama ta saka
baki, amma da yau ɗinan saina tsamar da ƙafafunki”. Harararta nai kafin na zauna a
inda ta tashi na gaida Mama da Yaya Sule, daga nan muka hau hirarmu.

Wajen sha biyu Amina na tayani tsifar kai muna hira, mama kuma nata ƙoƙarin
ɗaura awara da muka tace da Amina bayan munje munkai markaɗe, nace, “Amina!”.
“Na'am” ta amsamin tana leƙo fuskata. Ɗalli namata a fuska da ɗan yatsa, ta
matsar da fuskarta tana ɓata fiska saboda zafi, niko na kwashe da dariya, “Ke ɗince
kin wani kawomin fuska saikace maison leƙa ramin gwal”. Dariya itama tayi tana
ranƙwashina a kai, “Ai bazakici bulusba kuwa”. “ALLAH da zafi” na faɗa ina
harararta” tace, “Nima ai naji zafin shiyyasa na rama”. “Ba komai zaki gane shayi
ruwane. Maganarnance dai zamu sake”. Shiru tayi kamar bazatace komaiba, tsifar da
takemin ma ta koma min ita a hankali, na zungureta da hannu dan nasan ta faɗa kogin
tunanin nata. Numfashi ta kawo a hankali, tace, ”Ina saurarenki”.
“Amina, a zaman da kikai gidanmu na tsahon wasu shekaru, nasan zakisan
halayyar kowa dake cikin gidan nan”. Tace, “Hakane” “Alhmdllh, mizan iya sani akan
Qaseem da Salman?”. Shiru tai na wasu sakanni kafin ta sauke numfashi, “Duk abinda
kikeson sani zan iya faɗa miki Bilkisu inhar na sanshi, wanda kuma ban sanshiba
zance miki ban saniba, kimin tambaya zanfi fahimtar mikike son sani game dasu?”.
Cike da gamsuwar maganarta nace, “Hakane, Qaseem da Salman suna neman
mata?”................✍

Asha weekend lafiya🤫🤭😉😍👌🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

Yau ƴan wattpad sai haƙuri yaƙiyi wlhy, da ƙyarma nai copy ɗin wannan a can ɗin,
amma zan cigaba da gwada muga in za'a dace😔
[11/30/2020, 12:58 PM] HASNA ✍🏻
: Bilyn Abdull :
Page 13

.................Shiru tai na wasu mintuna kafin tace, “Ban taɓa ganinsu da


idanunaba a gado ɗaya da mace, amma tabbas Salman yakansha zuwa da ƴammata gidan
idan kamar basa nan, ko kuma suna barcinsu na ƙaddara, dan akwai lokacin farkon
dawowarsu da yataɓa zuwa da wata yarinyar ƙabila suka kwana a gidan, da safe ta
fito zata tafi ALLAH ya haɗasu da Alhaji a bazata, koda ya tambayeta daga ina?
Saita faɗa masa Salman ne ya kawota, wlhy a lokacin nazata Alhaji zaiyi kiran
Salman yaymasa tatas a gaban yarinyar, ya kuma gargaɗesa sake kawo wata sai kawai
naga ya sallami yarinyar ta tafi, shikuma ya shiga mota abinsa ya fita rai a ɓace,
dan ko driver hanawa yay ya tuƙasa da kansa yaja mota ranar. Bilkisu bansan miyasa
Alhaji keda sakaci wajen tsawatarma yaransa akan abinda ba daidaiba, ya gwammaci ya
shanye ɓacin ran a ransa komin zafin da abun yay masa da kuma illarsa garesu da
yazauna ya nuna musu kuskurensu, gaskiya ban taɓa ganin wanda yayma boko da rayuwar
yahudu ƙazamin ruƙo irin Uncle ɗinkiba, sai dai ina tausaya masa, dan banyi tunanin
waɗannan ƴaƴan nasa zasu masa addu'a ba a lokacin da ƙasa ta rufe idanunsa, sai dai
dayake UBANGIJI gafurunne kuma rahimun ba'a shigar masa al'amari, ikonsane ya
canjasu kosu ƙare rayuwarsu a haguggunce kamar yanda suka tashi. Qaseem kam dai
bazance na taɓa ganin ya kawo mace gidan nanba, sai dai nakanji yana waya, dan
kusan sau uku ko biyu inajin yana waya da ambatar sunan hotel, ba sunan hotel daya
shigo ciki bane kawai yasa nai tunanin hakan, sunan mata dakan shigo a zancen nasa
da salon yanda yake wayarne kawai dai ya ɗarsa mani haka. Sai kuma faɗa da naji
wataran Hajiya na masa akan batun aure, take cewa ya zauna yanata shashanci a waje
sai ya gama tsufa baiyi aureba, idan soyake wata ta haifa mata jika a waje sai ya
bada himma. Kinga a zancenta yana nuna kenan yana yin abinda bai daceba ta kamashi
ko aka kawo mata labari. Sai dai shima babu tabbas, tunda ba ido da ido nidai na
gansaba. Abu na biyu kuma Qaseem baya shaye-shaye, baida wulaƙanci tamkar Hajiya,
dan baya shiga huruminka sai idan kaine ka saka kanka a ciki ko wani dalili ya
haɗaku, da wahala kiga yana hantarar masu aiki sai idan sun ƙuresa gaskiya,
shiyyasa lokacin da kikazo gidan naga yanata biyema su Hajiya akan abinda suke miki
nata mamaki, dan nasan ba halinsa bane, sai daga baya na fahimci soyayyace yake
miki batare da shima ya saniba, shiyyasa baya iya yin shiru akan al'amarinki.
Salman yana shaye-shaye, dan ɗakinsa ma zaki gansu zube baya shakka balle shayin
kowa, sannan ɗan wulaƙancine dason yanƙwana mutum, sai dai shi kuma akwai ƙyauta,
dan bashi da rowa, akwai kuma tausayi idan ƴan mutuncin na kansa bai cake ba, dan
wani rashin mutuncin nasa abinda yake sha ne ke azashi bisa hanyar aikatawa. Haka
rayuwa take, duk inda kika samu mutum da mugun hali zaki samesa da ƙyaƙyƙyawa
kuma”.
“Hakane kam Amina” na faɗa ina sake juya maganganunta a cikin raina.

Tunda na dawo gida maganganun Amina ne kawai keta kai kawo a raina, na
idar da sallar la'asar ina cikin naɗe abin sallar Aunty Shahudah ta shigo, sosai
nayi mamakin ganinta harma fuskata ta kasa ɓoyewa, dan tunda aka bani ɗakinta bata
sake shigowaba, hasalima a wancan lokacin catai ƙyanƙyami kayan ciki take tunda na
taɓasu.
Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo sannan ta zauna a bakin gado, fuskarta
wasai babu alamin turɓune wa kamar yanda takeyi da, sannan babu kallon banza balle
hantara.
“Oh, sai kallona kike tamkar kin samu tv Bilkisu”. Murmushin da ban
shiryaba nayi, dan inaga yaune karan farko dana fara jin sunana a bakinta, nace,
“Aunty Shahudah ai mamakin shigowarki nan nake, nasan dai.....” sai kuma nai shiru
ban ƙarisa ba. Batace komaiba sai gefenta data nunamin da hannu alamar na zauna.
Nima ban musaba na zauna ɗin inata ƙara mamakinta dai. Cikin katsemin tunani tace,
“Bilkisu aiki nazo kimin, konawa kike buƙata zan biyaki”. Kallonta nai da
mamaki, sai kuma na girgiza kaina, “Aunty Shahudah ni yanzu dan zaki sakani abu har
sai kin biyani? Bana buƙatar ki dinga kallon haka tsakanina dake, ki sakani
kominene kike da buƙ

ata a matsayinki na wacce take sama dani kuma nake ƙanwarki, nikuma nai miki
alƙawarin inhar baifi ƙarfin himmata ba zan yimiki shi”. Tai guntun murmushin da ke
ƙarama ƙyaƙyƙyawar fuskarta ƙyau tana jinjina kai, Tace, “Bansan haka kike da
kirkiba ai, amma duk da haka zan biyaki, domin aikin ya cancanci hakan”.
“Humm” kawai nace mata.
Ta sake muskuta zamanta da cewar, “Waje ɗaya kuke aiki da Broth ko?”. Nasan Yah
Qaseem suke cema haka, dan haka nace mata “Eh”. Tace, “Yauwa, a Station ɗinku,
akwai wanda nakeson kimin aikin a kansa, sunansa Jawaad, bai zama lallai ki
sanshiba, dan shi mutumne da baya shiga kowane tarkace, yanzu ɗinma sai munyi
shawara da dogon nazarin da har zaki iya samun kusancin taimakon nawa a wajenshi,
dan nasan bazai kulaki ba kai tsaye”. Ta ɗanso bani dariya a maganganunta, amma sai
na danne banyiba, dan nima nasan gaskiya dukta faɗa akan halayyar Boss, to amma
yanda take faɗan magana a habaice kuma tanason na mata aikine ya saka abin son bani
dariya. Tace, “Abinda yasa na zaɓeki a aikin nan saboda, baki da surutu, sannan kin
iya hausa sosai, zaki fimu sanin hanyoyin da zaki fahimtar dashi ya fahimta saboda
shi mayen son yaren hausane”. Yanzunkam kasa daurewa nai sai da na murmusa, banda
shirme irin nata dasu da suka ɗauki yaren wani wata tsiya, ai sai sakarai ke ƙin
yarensa.
“Tom aunty Shahudah, yanzu mikikeso nayi ni?”. Jim tayi alamar tunani akan
abinda ke'a ranta, sai kuma zuwa can ta sauke numfashi, “Zan ringa baki saƙo kina
kai masa kulum, wannan shine kawai aikinki, idan kuma ya tambayi wani abu game
dani, sai kisan yanda zaki tsarashi da manya-manyan hausarnan naku. Amma dai
Aamilah zata sake miki bayani yanda zaki fahimta, danni harma narasa yanda zaki
sake ƙara fahimtata”.
“Karki damu Aunty, ko a yanzunma na fahimceki, matsalar kawai shine yanda
zan samu kusancin dashi, da har zan sako masa babbar magana data shafi rayuwarsa
ne, dan kinga wannan babbar maganace data kasance sirrinsa da ya shafesa ba zancen
aikiba, amma namiki alƙawarin zan gwada ta wasu hanyoyi, saiki dage da addu'a
kuma”.
“Okey, zuwa anjima zamu fita ni da Aamilah, zamu sayo abinda zakije masa
dashi ranar Monday”. Na jinjina mata kaina kawai, dan bansan miyasa take bani
tausayiba yanzu, na kula tana sonshi sosai, to ai Boss ya cancanci a soshi, sannan
ita kanta ina mamakin yanda ya iya sakaci da wannan ƙyaƙyƙyawar halittar, ba namiji
irinsaba hatta dani mace aunty Shahudah na birgeni, tana cikin mata ƙyawawa ajin
farko da ba cikin baƙaƙeba kosu kansu fararen ta shiga cikinsu saisun yabata, sun
dace sosai matsayin ma'aurata ita da Boss, ‘sai dai nikam ta yaya zan tunkaresa da
maganar nan?’.

JAWAAD

Tun sanda yasha maganin sai ya dinga samun nutsuwa a hankali harya
farajin ɗan ƙarfi bayan tafiyarsu bilkisu, sai kuma yaƙi da zuciya, sosai maganin
na masa aiki, amma yasan wataran zai daina tamkar yanda na bayama sukai yayi suka
shuɗe, ko abokinsa Doctor Sooraj ɗin da ya bashi shawarar amfani da wannan maganin
ya tabbatar masa na wani ɗan lokacine kawai, babbar mafita shine yay aure, inba
hakaba ƙwayoyin da yakesha domin kare kansa daga faɗawa halakar da yake gudu to
lallai zasu iya masa illa ma wataran, tunda har ALLAH ya bashi lafiya da muhalli,
dukiyar aure mi yakema zaman jira? Idan matarsa yakeso ya dawo da ita mana yabar
cutar kansa. A lokacin da Dr Sooraj kema Jay wannan maganar ƙin ce masa uffan yay,
daga ƙarshema sai yay masa sallama ya baro office ɗin.

Da daddare bayan tafiyar su Ummah gida ya samu kira daga Uncle Nasir,
duk da bayajin ƙwarin jikinsa haka ya tashi ya fita bayan ya saka dogon wando a
jikinsa, dan harma ya riga yay shirin barci shi. Kansa tsaye falon Uncle Nasir ya
nufa, bayan yay sallama aka bashi izinin shiga sannan ya shiga, Uncle Nasir na
zaune shida matarsa suna hira da kallon labarai, ya gaishesu da girmamawa. Duk
fuskokinsu ɗauke da fara'a suka amsa masa, Uncle Nasir yace ya taso susha Fruit
salad ɗin da yake sha, Jawaad ya amsa da, “Alhmdllh Uncle na ƙoshi”.
“Aiko saika shashi” cewar Hajiya Sumayya matar Uncle Nasir, ta cigaba da
faɗin,

“kai yanzu Jawaad kenan ka girmi cin abincin kowa a gidan nan?, tunda kai aure
shikenan, da ai ba haka kakeyiba, mu yanzu ka yayemu daga iyayenka kenan?, inaga ko
shayin wajenan rabon daka shashi tun daren ɗaurin aurenka da Shahudah, to ni dai
yanzu kamar yanda na saba a baya kullum zan zubo abinci na aiko dashi sashenka,
idan kaso kaita jerenshi kamar ɗakin amarya”.
Murmushi yayi tare da kai hannu ya shafi kansa, yace, “Nayi laifi Ammi, amma
ayi haƙuri, kinsan yanayin aikinmune yasa, wani lokacin bana shigowa da wuri, kuma
ina fita da wuri, amma daga yanzun indai na dawo da wuri zanyi magana a kawo
mani”. “To yanzu naji magana, bara na zuba maka fruit salad ɗin”.
Uncle Nasir dake saurarensu yace, “
Ke nama lura sake ɗaure masa ƙugun zama babu aure kikeyi, yanzu ba zancen adinga
kai masa abinci nai zamanyi ba, zancen wadda zata dinga dafa masa kamar kowane
magidanci zanyi”. Tace, “Ah Alhaji indai nan ne aini ina bayanka, ga ƙannensa nan
su Abdur-rahman za'ai musu haihuwa ta bibbiyu, shiko ya zauna ruwan ido kamar wanda
bai ɗanɗana auren yajiba”.
“Barsa, ai na shirya maganinsa wannan karon, idan har bai shiryaba ni a
shirye nake na zaɓi ɗaya daga yaran gidanan na aura masa”. Da sauri Jay ya kalli
kawun nasa harda waro idanu. “Kalleni da ƙyau fa, ALLAH inhar baka yunƙuro a cikin
shekararnan ba, a yaran gidanan zan aura maka, karkuma ka ɗauka maganar wasa nake
maka, gobema insha ALLAH zanje na sami Alhaji babah muyi magana (Kakansa mahaifin
Mamansa), idan kuma matarka kakeso ka dawo da ita”. Shiru Jawaad yayi baice komaiba
har Uncle Nasir ya gama masa faɗa sannan ya bashi haƙuri akan insha ALLAH zaiyi
abinda sukeso, amma su ƙara masa lokaci.
Uncle Nasir yace, “Ba damuwa, ALLAH ya kawo mafita, amma ranar lahadi idan
ALLAH ya kaimu akwai meeting da za'ai ƙarfe huɗu, sai kai ƙoƙari ka halarta, karka
bari ayi kuka da kai kamar ko yaushe dan ALLAH”.
“Insha ALLAHU Uncle zan kiyaye”.
Ya daɗe a sashen suna hira dan sai kusan ƙarfe ɗaya ya koma sashensa,
kasancewar yasha barcin rana sai bai iya yin na darenba da wuri, lap-top ya buɗe ya
shiga wasu ayyukan, sai wajen biyu da rabi ya rufe ya tashi, alwala yayo yay
nafilfili tare da jero doguwar addu'a akan mahaifinsa da mahaifiyarsa, dama sauran
al'umma baki ɗaya.

Sakamakon rashin kwanciya da wuri ya sashi makara sallar asuba, ya tashi a


gaggauce ya nufi toilet ya ɗauro alwala, bayan ya gabatar da salla yay wanka ya
gyara gadonsa sanan yay shirin fita, Gimba ya tafi gida weekend, dan haka shi da
kansa yaja motarsa sai ƙaton gidan gonarsa da ya gada wajen mahaifinsa dake can
asalin ƙauyen kakansa Alhaji Yusif, inda sukai rayuwa da kakarsa mama maryam, garin
kuma da mahaifinsa yay rayuwar ƙuruciya harma data girma. Sosai an samu cigaba da
abubuwa masu dama a cikin ƙauyen wanda duk sanadin mahaifinsane, an musu titi, an
kuma kai musu wuta, ga dam ɗinsu da har yanzu suke noman rani, dan garin yana ɗaya
daga cikin manyan garuruwan da ake amfanuwa da nomansu da kiwo a jihar tasu dama
maƙwaftanta baki ɗaya. Alkairin mahaifinsa da shi kansa wanda yakeyi yasa a kullum
yake mai daraja a wajensu, idan yaje ji suke tamkar su haɗiyeshi, saika rantse wani
sarakine.
Kamar yanda ya saba gidan mai gari ya sauka, dan haka ya keyi a duk lokacin
da yaje ƙauyen, hakan na ƙara masa daraja da kwarjini, kamar yanda shima yakejin
daɗin abinda suke masa ɗin, dan maigari yana masa abu tamkar uba, kasancewarsa
abokine ga mahaifinsa Abdul-aziz tunna ƙuruciya. Ya samu tarba kuwa ta mutuntawa,
inda akaita haba-haba dashi da abincin gargajiya masu tsafta kamar yaune aka fara
ganinsa matsayin baƙo. Sam Jawaad bashi da girman kan zaɓar cima ko raina cimar
ƙauye, hasalima suna masa saɗi fiye dana zamani, idan har yaje ƙauyen nan komi suka
bashi cin abinsa yake, saboda yanada yaƙini akan tsaftar iyalan baba maigari, tun
yana ƙanƙanin yaro mahaifinsa ke zuwa dashi, hakama mama maryam na kawosa kafin ta
rasu, hankalinsa kwance yaci ya ƙoshi, dan dama da yunwarsa yazo, bayan sun gaisa
da baba maigari da jama'ar dake fada suka nufi gidan gona shi da Abbati ɗan b

aba maigarin da zasuyi sa'anni da Jawaad, dan abokinsane na amana, dukkan sirrin
gidan gonarsa yana hannun Abbati, shike kula da komai, Abbati dukda yayi karatu har
matakin degree na biyu yana zaune ne anan ƙauyen tare da iyayensa, iyakarsa yaje
birni wajen aiki ya dawo garinsu ya kwanta, matarsa ɗaya da ƴaƴa huɗu, yayi ɗan
gininsa na zamani saboda ƙauyen yanzu yanada dukkan cigaban da ake hangensa a
birnin, kuma mafi yawansu sunada aƙidar son zaman gida sai dai waɗanda aiki ya
tilastama komawa birnin akan dole, dan a dalilin Abdul-aziz mahaifin Jawaad ƙauyen
yanada manyan ƴan boko matasa masu jini a jika dake taka rawar gani sosai a sassan
ƙasar.
Suna tafe suna hirarsu cikin nishaɗi, inda Abbati keta kiran sauran abokansu
dake gida ta waya yana sanar musu Jawaad yazo. Jawaad ya fige wayar yana hararar
Abbati, “Malam ya isheka haka, sai gayyatomin ƴan iskannan kake salon kuzo ku
addabeni da surutu mara ma'ana”. Abbati ya kwashe da dariya, “Oh ashe kana tsoron
surutun namu? Ai indai kaga munbar maka surutu kuwa sai kayi abinda mukeso, ka
dubemu daga mai yara uku sai masu huɗu amma kai ka zauna ruwan ido Jay, ai kosu
Jabeer da kuke tare a birni sunada iyalansu, wai kodai da kurwanka Shahudah ta
tafine bani labari kafin su Isa su zo”.
Kafin Jay yay magana sukaji ance, “Ai gamu mun iso”. Daƙƙuwa Jay ya watsama
abokan nasa huɗu da suka iso wajen yanzu-yanzu, waɗanda suma duk sunyi karatu kowa
da abin yinsa, kuma suna bada gudunmawa a gidan gonarsa suma. “Duk kunci ƙaniyarku
zomayen banza, uwarwa ya gayyatoku nan?”.
Dariya suka sanya baki ɗaya, Labaran ya dunƙule hannu ya bigi damtsen hannun
Jawaad yana faɗin, “Bar wani mazurai gaye, munfika ƙarfi fa inma hayaƙin kakeji,
dan mu kullum matanmu ƙara mana sukeyi” duka shima Jawaad ya kai masa, Labaran yay
saurin duƙewa. “Ɗan iska da ka tsaya naima fuskarka damage sai naga ƙarfin da
Asiyan ke baka, mara mutunci”. Dariya suka sanya su dukansu, Aminu yace, “Mudai mun
gaji da ganinka haka ALLAH kuwa”. “Gaskiyane Aminu, ya kamata ka duba Jay” cewar
isa. “Hakane kam lokaci baya jira fa, kullum girma muke ƙarawa ƙuruciyarmu na
guduwa” cewar Salisu dake dafe da kafaɗar Jawaad. Murmushi kawai Jawaad yayi, yasan
halin abokan nasa, tunkan yay auren farkoma haka sukaita addabarsa, sai da akai
bikinsa da shahudane suka sama masa lafiya, yanzunma ko waya yake dasu faɗansu
kenan, shi kansa ba auren bane bayaso, gidan jiya yake tsoron komawa........ Adam
ya katse masa tunani da cewar, “Idan kuma a birnin babu wadda tai maka ka duba a
garin nan mana, auren nan shine cikar martabar mutum”. Abbati yace, “Maganarku
nakan hanya ƴan uwa, ko ɓato maka rai akai daga waje kana shigowa gida kaga
iyalanka sai kaji ka huce, musamman idan kayi dace da macen datasan yanda zata
tattali dukkanin farin cikinka, koda gajiyarka ka kwaso kanada inda za'a nuna
tausayinka a sauke maka ita da kulawa”. Jawaad ya shafa kansa yana sauke numfashi
da girgiza kai, “Kudai baku da magana saita aure dai jarababbu, ko hutawa bakwayi,
karku damu zanyi, kumin addu'a kudai. a tare suka shiga masa addu'ar kuwa kafin su
fara bashi hannu suna gaisuwa.
Jawaad nason abokansa na ƙauyensu, dan suna bashi nishaɗi da faɗa masa
gaskiya komai ɗacinta, shiyyasa ko kansa ɗaukar zafi yay a wajen aiki tuni yake
ƙoƙarin ware weekend ɗin da zai shigo, dan yasan zai samu nutsuwa
sosai..............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[11/30/2020, 12:57 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:


Page 14

Guys ɗinan anya kunaso na mutu da idanuna?, kusan words dubu uku nakeyifa a kullum
amma sai naji kuna farautar ƙari🤔, aradu inason ƙulla shekara ɗari da idanuna kuyi
haƙuri😂🤣😂. Ga zaɓin lokacin posting, 11pm ko kuma 6am. Waɗanda naga sunfi rinjaye
sai abi ra'ayinsu. Amma masu cewa dama Jay yana dariya?? nima kun bani dariya wlhy
sosai, waye baya ya dariya a duniya, sai dai idan bata kamaba😂. Harda ƙyaƙyƙewa
zakuji yayima wataran🚴🏼🚴🏼👌🏼.

Ina muku fatan alkairi😍😘😍😘😘😘.

................Zagayen gidan gonar suka farayi suna hira mai daɗi da mutunta juna,
sashen dabbobin da ake kiwo da sashen da ake noma, sashen kaji, kifi, su talo-talo,
zabi, agwagi, kajin gida, zomaye, harda tantabaru, sai sashen itatuwan fruits,
komai yana tafiya yanda yake buƙata, sun nufi inda Jawaad ya gyara shima suke fidda
yankakkun kaji dasu zabbi da sauran duk nau'in ƙananun dabbobin da ake kiwo a wajen
ana packaging nasu a ledoji a shiryasu a wasu robobi manya masu haske domin masu
sari dake kaiwa birni, hakama ƙwan kaji da zabi dana talo-talo, sai inda ake tace
tsaftatacciyar madarar shanu kuma ana sakawa a galoli shima, kowacce galon da
adadin litar da take ci, da inda ake shirya dukkanin nau'in kayan itatuwa suma.
Abin dai dolene ya burge mai kallo da ƙayatarwa sosai. Sai da suka shiga lungu da
saƙo, ya kuma gamsuwa da yanda komai ke tafiya, yana ta ma ma'aikatan jinjina da
sake basu ƙwarin gwiwa, inda yaga kuskure kuwa cikin hikima yake musu gyara ba
yanda zasu fahimci gazawarsu ba, yanda yake tafiyar da al'amarinsu na ƙara masa
girma a idonsu sosai da daraja. Bayan sun kammala zagayawa suka yada zango
ƙarƙashin bukkar bunu da tasha gyara domin hutawa, gefenta kuma anyi ɗan gini mai 2
bedroom kawai, domin idan yazo da shirin kwana nan yake kwana ko gidan baba
maigari, hirarsu suka cigaba dayi cikin nishaɗi, lokaci-lokaci Jay yakan amsa waya,
wadda ta shafi aiki kuwa yakan tashi ya koma gefe idan ya gama ya dawo. Da rana sai
ga abinci lafiyayye daga gidan baba maigari an aiko musu, harda fura mai ƙyau da
tasha damu. Yini guda anan suka yisa, Jawaad yaji matsalolin jama'ar garinsa
waɗanda zai iya kawo gyara da iya ƙarfin aljihunsa yace zaiyi, dan dama ya daɗe bai
zoba kusan wata uku. wanda sukafi ƙarfinsa kuma zasu haɗa hannu domin neman
taimakon wanda zai iya musu, Jawaad ya gaji mahaifinsa a abubuwa da dama, komai
nashi na al'ummane, dukiyar da mahaifinsa ya bari bata rufe masa ido ya zama
asharari ba, sai ya ɗora kyawawan aiyukansa akan wanda mahaifinsa ya fara, tare da
nasa da ya ƙirƙira shima, yanda yake rayuwarsa a sauƙaƙe bazaka taɓa tunanin an
tara masa irin wannan dukiyarba, dan ko iya gidan gonarnan ai al'amarine babba,
balle kuma akwai wanima bayan wannan, bayan sauran abubuwa da shima nasa ƙoƙarin.
Bayan sunbar gidan gona gidan baba mai-gari suka koma, sun samu zama dashi
da manyan gari suka tattauna akan maganar da sukai a gidan gona na abokansa, sai
bayan sallar magriba Jawaad ya baro ƙauyen cike da tsaraba daga jama'a, duk da
sunsan yanadashi hakan baisa suji ƙyashin ƙyautata masa da ni'imar da suma ALLAH
yay musu ba. A hanya ya tsaya yay sallar isha'i kafin ya ƙarisa gidan Umma ƙarama.
Tayi murnar ganinsa ita da yaranta, ya sauke mata tsarabarta anan da ɗibar mata
wadda mutane suka bashi yay mata sallama ya tafi dan bai jimaba sosai, daga nan sai
gidan Ummah babba, gidansu Nabeelah kenan, nanma sunyi murnar ganinsa, inda suka
fara faɗansu shi da Batool kamar yanda suka saba, itama dai tsarabar ya ajiye musu
ya tafi, a gida ya yada zango, kasancewar kowa ya shige sashensa shima nashi ya
shige akan da safe zai fiddama kowa nasa kason, sauran ya kaima kakansa nasa shima,
sai nasu Hafiz.

WASHE GARI LAHADI.

Washe gari lahadi, na tashi da burin abubuwa da dama, dan da daddare na


samu Dad da yah Qassem ya kirashi, na faɗa masa zanje na gaida Inna zainabu yace
naje sai driver ya kaini, na sanar masa zanhau napep saboda zan fara zuwa wajen
aiki da aka sakani kafin naje canɗin idan na fito wajen saloon. Ina kammala gyaran
ɗaki nai wanka, na fita nai breakfast sama-sama na koma ɗaki nai shiri. Doguwa

r rigace na saka ta Material baƙa da ratsin fari, ta zaunamin ɗas a jiki, gashi ta
buɗe daga ƙasa bata wani matseniba sai a ƙirji kamar yanda tsarin ɗinkin yake,
maɗaurin da akai mata na kama na ɗaure a bayana, sai ta kuma fita da ƙyau. Gashina
dake a tsefe na kuma gyarama zaman ribbon, sanan na saka farar hula mai ƙyau, na
kawo ƙaramin gyale baƙi na yana a kaina, tare da kalmashesa a ƙirjina ya rufe ruf
na ɗora a kafaɗa ƙasanshi suka sauka bayana, basai an faɗaminba, ni kaina nasan
nayi ƙyau, hakan yasa naita kallon kaina a mirror ina murmushi, a gurguje na ƙarasa
kimtsawa na fito sagale da ƴar jikkata a kafaɗa ina ƙamshi mai sanyi, sai takalma
masu ɗan tudu kaɗan, na riga na faɗama Mom zan fita dama tun da daddare, hakan yasa
yanzu nai ficewata kaina tsaye tunda babu wanda ya tashi har Yah Qaseem da baisan
zan fitaba, dan banfaɗa masabama gudun matsala.
Da ƙafa na taka har titi na tari napep na hau zuwa inda Oga Jabeer ya bani.

Bayan fitar Bilkisu daga gidan Mom ta fito daga ɗakinta, tanason tayi
magana da Shahudah ne, shiyyasa tun ɗazun taketa dakon fitar bily, tana tsoron
halin da Shahudah zata iya shiga da har bily zata sani, dan a ganinta bily ita
kaɗaice bare a cikinsu da bai kamata tasan sirrinsu ba. Sam jiya batai barciba akan
bayanin da Shahudah tai musu na zuwa ɓangaren Jawaad da tayi, ta fahimci sunyi
kuskuren ƙin sanarma Shahudah gaskiyar lamari akan sakinta da Jawaad yayi tun
lokacin da wancan al'amarin ya faru, ba damuwarta abinda Shahudah ta aikataba,
damuwarta kar Jawaad ya sake gudun Shahudah akan hakan, dan ita kanta inhar zata
faɗi gaskiya bata taɓa kama Jawaad da abun rashin gaskiya ba dangane da fasiƙanci,
dan ko lokacin da basa ƙasar ma idan yaje musu hutu duk jarabar Shahudah da naci
akan yazo suje club baya zuwa, ita kanta ma faɗa yake mata, shiyyasa da yaje take
kame kanta. To tasan akan hakan Jawaad zai iya sake bijire musu ne dangane da maida
Shahudah.
Tashin Shahudah kenan a barci tayo brush da alwala ta fito mom ta shigo, ƙarfe
goma saura sai yanzune wai ake alwalar sallar asuba😭🤦🏻.
“Mom lafiya?” Shahudah dake ƙoƙarin saka gyale ta faɗa tana kallon mom. Mom ta
zauna bakin gado tana faɗin, “Magana nazo muyi”. Zama Shahudah tai ta fasa sallan,
Mom tace ba salla zakiyiba ne?” “Eh salla zanyi, amma muyi magana sai nayi daga
baya”. “Karki damu tashi kiyi sallar zan jiraki”. Shahudah batace komaiba ta miƙe
ta kabbara salla, wadda ALLAH kaɗai yasan mima take karantawa, dan a mintuna
ƙalilan ta idar da kayarta ta dawo wajen mom dake zaune tai tagumi da juya abinda
zai iya biyo baya a ranta. Motsin Shahudah ne ya maidota hayyacinta ta gyara zama,
tare da kamo hannayen Shahudah duka cikin nata ta kafeta da idanu, “Shahudah magana
zanyi miki, inason ki nutsu ki fahimta, domin muma a yanzu haka hanyar gyara ɓarnar
da kikayi muke, munada tabbacin samun nasara kuma, abinda yasa muka yanke hukunci
sanar mikin a yanzu dukda mun ɓoye a baya saboda gudun halin da zaki shiga, yanzu
kam saboda karki sake ƙara tafka irin kuskuren da kikayi ranar na zuwa wajen
Jawaad”.
“Mom ni dan ALLAH kimin magana kai tsaye, ki daina yimin wannan manya-manyan
hausan naki da ba wani fahimtarsu nakeba, minene ya faru”. Yanda tai maganar da
kumbura bakin shagwaɓa yasa mon yin ƴar dariya tana shafar kumatunta, “Nifa daɗina
dake taɓara maman Dadynta, karki damu ai zan kaiki, kumani sonake ki iya hausar ai
tunda yaren mamanki ce”. Shahudah batace komaiba sai ɓata fuska data sake yi. Mom
ta ɗauka takardan data shigo dashi ta miƙama Shahudah. Babu musu Shahudah ta amsa
tabuɗe takardan batare da tace komaiba.
Kasancewar Jawaad da turanci ya rubutama Shahudah takardan saki sai ta
fahimci komai dallah-dallah. Hannunta na rawa da bakinta ta ɗaga takardar, “Mom
kina nufin BB ne ya aiko min da wanan dan naje wajensa?”.
Kai Mom ta girgiza mata, “Badan kinje wajensa bane, wannan takardar shekararta
biyar kenan a gidannan, mune dai bamu bakiba tun lokacin da akai rikicin zubar da
cikin nan, munƙi bakine saboda gudun karki sake shiga wani hali akan wanda kika
tsinci kanki a wancan lokacin, dan muna

ta ƙoƙarin duk bin hanyar data dace ki koma ɗakinki, sai dai zuwan da kikai wajensa
ya ɗakko hanyar ɓata dukkanin shirin namu, shi bazai fahimci bakisan ya sakekiba,
zai fassara abinne ta wata siga daban”.
Matsanancin kuka shahudah ta fashe dashi, ta dafe kanta dake juya mata
lokaci ɗaya, yanda tai baya zata faɗine yasa Mom azamar tarota tana kiran sunanta a
razane, rungumeta shahudah tayi tana kuma kuka tamkar ranta zai fita, sai dai
ƙarancin tunaninta na raya mata cewar tamkar sakin a banzane, dan Jawaad yayi ƙarya
ya kwana da yunwa, aurensu baida maraba dana zobe, babu kishiya babu saki, ta daka
tsalle ta dire a gaban Mom tare da wawaso rantsuwa ta sake direwa akan baima isaba.
Yanda ta birkicema Mom tana kuka da rantsuwar Jawaad bai isabane ya jawo hankalin
Aamilah data fito falon ƙasa neman abinci, sai Qaseem dake a d/table zaune yana
karyawa shima, a guje Aamilah tay sama, Qaseem ma ya miƙe yabi bayanta. Yanda
Shahudah ta rikice Mom na rirriƙeta sai abun ya basu mamaki suka shiga tambayar mom
ko lafiya?. Basu samu amsa daga bakin mom ɗinba sai a takardar sakin da Shahudah ta
jefar ƙasa, Qaseem yace, “K dalla malama nutsu mana anan” yanda yay maganar a
tsawace yasa Shahudah nutsuwa sai dai ta maka masa harara tamkar zata makesa.
Bai kulata ba ya maida dubansa ga Mom yana kaɗa takardar, “Ita wannan ɗin
kuma daga ina Mom? Wata ya sake aikowa?” mom tace, “A'a waccance dai, kasan bata
saniba, shinefa ranar Alhamis datasa muka barta can taje.........” Mom ta zayyanema
Qaseem komai daya faru tsakanin Jay da Shahudah a daren juma'a wato ranar alhamis,
wanda shine sanadin ciwonta. Jiyay tamkar ya make Shahudah dan takaici, Aamilah kam
da yake Shahudah ta faɗa mata komai sai bataji abun a saboba, ya nuna ta da yatsa
yana faɗin, “Kedai wlhy daƙiƙiyace, wai ubanmiye a jikin wannan wawan Jawaad ɗin da
sauran maza suka rasa har kika nace masa?”. A fusace Shahudah tace, “Sai dai idan
kaine daƙiƙin, kaiɗin ubanmiye a jikin yarinyarnan da sauran mata suka rasa ka nace
mata (Bilkisu take nufi) (hakan ba sabon abu bane dan babu wani girmama juna a
tsakaninsu). Duka yakai mata yana faɗin, “Idan kinajin iskancinki a gidannan kibar
sakkoni, inba hakaba wlhy saina ɓallaki watan Shahudah. “Ka ɓallani ɗin tunda kai
ɗin ubanane, saika gayamin banza na kasa maida maka amsa da wofi, uwarwa yama
sakaka cikin maganar? Bansan shishshigi”. Dukan ya sake kaimata Mom ta tare. “Wai
wane irin iskancine wannan!! Taya zaku sakani tsakkiya da shirme, ku barni naji da
abinda ya dameni mana!!”. Duk dakatawa sukai kowa na huci kamar wasu ƴan dambe.
Daga ƙarshe Qaseem ya juya zai fita Mom ta dakatar dashi ta hanyar kamo hannunsa,
ƙin juyowa yay yadai tsaya, “Kayi haƙuri, ni banason wannan saurin fushin naka
Qaseem, kasandai halin rashin kunyar Shahudah a gidanan, yakamata ka cigaba da
haƙuri dasu a matsayinka na babba a cikinsu, kaji”. Ajiyar zuciya ya sauke, ya kaɗa
kansa kawai. Tace, “To ku zauna muyi magana, Aamilah jeki kira Salman”.

BILKEESU

Gurin ya haɗu matuƙa, bawani mugun ƙato baneba, madaidaici ne da akayisa


domin masu hutawa kawai, yasha gyara da korayen ciyayi da flowers masu ƙamshi,
nidai saima na zama baƙauya, dan duk zamana garin bansan da zamansa ba, koda yake
inama nake zuwa, dama yawona dasu Ummie ne idan mun dawo hutu, to ƙafarmu bata taɓa
zuwa nanba kuma, sai dai a zahiri na kame kaina ina tafiya cikin nutsuwa, ƙarƙashin
ɗaya daga cikin ƙananun bukkokin da aka ƙawata wajen na nufa, naja kujera ɗaya
cikin huɗu dake a kowacce ruffa na zauna tare da ɗora jikkata akan tebir ɗin na
buɗe na ciro waya. Motsi naji a kaina, dan haka na duba wanda yazo wajen, ɗaya daga
ma'aikatansu ne, ya gaisheni yana mai dire tiren hannunsa. Amsa masa nai tare da
jeho masa tambaya akan kuɗin abinda ya kawo, duk da bani nace ya kawoba, tunanina
tsarinsu kenan. “Karki damu Madam, an rigada an biya” ya faɗa yana barin wajen.
Binsa kawai nai da kallo harya shigema ganina, mamakina shine ‘waye ya biya?’. bani
da mai bani amsa, hakan yasani kauda abin a raina na duba abinda ya ajiye ɗin.
Popcorn ne sai robar ice-creem da Malt ɗaya da ruwa, n

a ɗauke idona inajan guntun tsaki tare maida hankalina ga wayata na fara tafama Oga
Jabeer saƙo. Bayan na tura masa naga ya wuce sai kawai na shiga yin Game batare
dana kula abinda aka ajiye min ɗinba dan a ƙoshe nake.
“Hy Babie!” aka faɗa dai-dai kunnena, a tsorace na ɗago idanuna dan a bazata
abin yazomin, banji motsin kowaba. Ƙyaƙyƙyawan saurayi fari tas kuma ɗan gaye ya
sakarmin murmushi da ɗage gira ɗaya sama, “Sorry na tsorataki ko?”.
Janye idanuna nayi daga kansa batare dana tanka masaba ko magana. “Kin
cancanta” ya faɗa yana zama kujerar dake facing ɗina. Nanma dai ƙin kulashi nayi,
yaja ɗan kwalin da Popcorn ɗin ke ciki ya fara ɗiba yana afawa a bakinsa tare da
lumshe ido alamar dai akwai daɗi. Janye idanuna nai daga satar kallonsa na tura
wayata a jikka na miƙe zan bar masa wajen. Da sauri shima ya miƙe yazo gabana ya
tsaya, baya naja kaɗan ina ɓata fuska. Yace, “ALLAH bazaki tafiba sai kin kulani”.
Na dafe kaina ina lumshe idanuna irin na ka kaini bango ɗin nan......
“Please babie kice wani abu mana”.
Nabuɗe baki zanyi magana kawai naji baƙon ƙamshin turare a wajen tare da motsi,
waigawa nai saboda yanda, nakejin bugun zuciyata na sauya salo. Wanda nai tunanin
kuwa shine na gani. ‘Boss!’ na ambata a cikin zuciyata, duk da ya rufe fuskarsa
sosai da facing cap baƙa datai masa masifar ƙyau hakan bazaisa naƙi ganesa ba,
ƙamshinsa ma kawai amsatace dan bana manta ƙamshin turarensa sam, dana jisa nake
shaida yazo waje. sake ja baya daga gaban gayen da shima shi yake kallo nayi.
Jawaad kam yayi tamkarma bai gansu ba, sai ƙoƙarin buɗe gwangwanin Malt..
Ɗin da aka kawoma Bily kawai yake hankalinsa kwance, sai dai fuskarsa a matuƙar
ɗaure take babu alamun sassauci, ya zaro wayarsa da ga aljihu tare da gyara
zamansa, ya kwantar da bayansa jikin kujerar sosai ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai kace
wani saraki, yana sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa masifar ƙyau da fidda
cikar haibarsa, sai hula hana salla inji hausawa😂, a samanta an rubuta favourite da
ruwan gwal mai ƙyalƙyali, idanunsa toshe da baƙin glasess, hakan yasa babu mai
fahimtar ina idanunsa suke kallo kai tsaye. A zuciyata nace, ‘glass nama Boss ƙyau
matuƙa idan ya saka, bansaniba koni kaɗai ke iya ganin hakan banda sauran mutane,
amm.....
“Babie!” saurayin ya ambata da ɗan ƙarfi ganin hankalin Bily baya tare da
shi. Kallona na maido kansa, nace, “Ba sunana Babie ba” yay murmushi mai ƙayatarwa,
“To a faɗamin sunan mana uhum”. “Bana doguwar magana da wanda bai iya sallama ba”.
kansa ya dafe alamar ya fahimci kuskurensa, yace, “Sorry Assalamu alaiki”.
“Wa'alaikassalam”. Na amsa masa.
Murmushi ya sake yi, yace, “Na gode da kika tunatar dani abinda na manta,
hakan na sake tabbatarmin na samu abokiyar rayuwa ta gari, irin wadda ta cancanci
zama uwar ƴaƴana. Sunana Kamaludden shehu Manya, matar tawa fa?”. ni dariyama yaso
bani wlhy, wai matarsa, daga ganin sarkin fawa sai miya tai daɗi. kaina na girgiza
masa kawai na juya zan bar wajen, amma sai yay azamar sake shan gabana, “Haba
babie, naga na gyara kuskuren da yasa aka ƙi kulani tun a farko ai, koda bazaki
kulani a nanba ki bani Number mana. Sonake ya barni, shiyyasa na miƙa masa hannu
alamar ya bani wayarsa na saka masa. Cike da ɗoki ya ciro wayarsa a aljihu ya
miƙomin, sai dai kafin na kai hannu na amsa wani hannun ya amshe
wayar..............✍

ALLAH ka gafartama
iyayrnmu😭🙏🏻

[11/30/2020, 12:57 PM] HASNA ✍🏻


: Typing

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 15

To yau page ɗin ƙwai cikin ƙaya na ƙuɗine, duk wanda ya karanta ina roƙonsa dan
girman ALLAH ya biya da addu'ar ALLAH ya kawo mana iyakar tashin hankalin dake
damun wasu yankuna namu na arewaci, dan ALLAH ina roƙon har ƴaƴanmu ku saka suyi
wannan addu'ar a dukkanin sallolinsu biyar na wannan yinin, domin addu'ar yara
abuce mai muhimmanci a garemu mubar sakaci da ita, idan baki aureba ki roƙa mana
jama'ar gidanku suyi da kanninki, duk da munsan anayi dama, sai dai ina fatan
wannan ta zama ta musamman domin ALLAH, dan ALLAH kar'a manta, kar'a manta, kar'a
manta.

Ya rabbi ka kawo mana ƙarshen waɗanan tashin hankali, ya ALLAH ka ruɓanya rahamarka
da rangwame a garemu, ya Rabbi ka yafe mana kurakuranmu, ya Rabbi kaimana maganin
abinda bazamu iyaba harma da wanda zamu iya ɗin, ya rabbi ka taimaki bayinka dake
cikin gararin rayuwa da hali na buƙatar agaji, ya rabbi ka kawoma muhallansu zaman
lafiya, kasaka kwanciyar hankali a zukatansu suma su sami cigaba da rayuwa a
yankunansu kamar kowa, ya rabbi ka kawoma ƙasarmu zaman lafiya baki ɗaya da
dukkanin duniyar musulunci, ya rabbi ka bamu ikon cinye jarabawa kasa ta zama
rahama a garemu duniya da lahira🙏🏻😭.

Idan kasan bazaka biyaba karka karanta, bayin ALLAH na buƙatar tallafin addu'oinmu,
dan girman ALLAH karmu wofantar da lamarinsu saboda mu muna barci a gidajenmu da
iyalanmu bayan munci mun ƙoshi, ba'a zahiri kawai nakeson ayiba har abaɗi ma ita
mukafi buƙata😭.
Masu 6am sunyi winning, wannan shine zaizama lokacin posting ɗinmu kafin na daina
fushi da kamfanin masu yellow'n tambari 🙄🙄🙄.

................Daga ni har shi kallonsa mukai. Nidai na sauke idanuna da hannuna a


hankali ina haɗiyar yawu da ƙyar. Kamal yace, “Haba malam ya haka?” Jawaad bai
tanka masaba, sai wayar daya daddana alamar wani abun yayi a ciki ya miƙa masa. A
ƙufule Kamal ya amsa yana faɗin, “Wanan rainin wayone ai, ya zakazo ka shiga abinda
bai shafeka ba?”.
Ban jira amsar da boss zai bashiba nabar wajen nidai, saboda wata muguwar harara
daya makamin dan ya cire madubin idonsa.
Jawaad ya maida kallonsa ga kamal yace, “Karka damu ka kira Number dana saka maka
zaka sameta”. Kamal yay ɗan shiru alamar nazari, sai kuma yay saurin taɓa hannun
Jawaad dake shirin barin wajen, Jay ya juyo yana kallonsa, sai dai baice komaiba.
“Sorry, dan ALLAH ko ƙanwarka ce dai?” wani munafukin murmushi Jawaad yayi tare da
ɗagema kamal gira ɗaya sannan ya wani juya kansa da lumshe ido yabar wajen. Sam
Kamal bai fahimci komai daga yaren na Jawaad ba, sai dai kuma ya haƙura akan zai
nema waje ya zauna harsu tashi tafiya ya bisu a baya, dan shifa yaga matar aure.
Tsaye yazo ya sameni ina waya da Zuhrah, baiko kalleni ba yaja kujerar da ya fara
zama ɗazun ya sake zaunawa yana maida glasess ɗinsa a ido kamar ma ya manta dani,
nima ɗin dai ƙasa-ƙasa nake satar kallonsa yanda nasan bazai fahimtaba ina wayata,
a ƙasan raina inata tunanin komi ya cema Kamal? Number wa kuma ya saka masa a waya?
Dan nidai nasan baisan tawaba. Zuwan ɗaya daga ma'aikatan wajen ne ya sakani janye
idona a kansa, umarnin kwashe kayan wajen ya basa tare da sake kawo wasu, dai-dai
lokacin da muka ƙarisa wayar, sai da yabar wajen ne cikin dauriya nace masa, “Ina
kwana sir”.
Shiru bai tanka minba, saima ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya
ɗauke kansa, duk a tsorace nake, gani nake zaimin faɗa akan ganina da Kamal, amma
har aka sake kawo abinda ya saka ɗin baice dani komaiba.
Ni kuma har lokacin ina tsaye duk da ƙafafuna sun gaji haka na fuske abina, shiko
ya buɗe sabon Popcorn ɗin da aka kawo ya hau ci yanayi yana danna waya, baifi ɗiba
uku ba wata mata mai sanye da hijjab har ƙasa da niƙaf ta iso wajen, sallama tai
mana, na amsa mata, shiko bangama ya motsaba har sai da taja kujerar gefensa ta
zauna, sai da ta ɗage niƙaf ɗin tana gaishesa sannan na fahimci wadda muke jirace.
Batare da ya amsa mata gaisuwarta ba yace, “Kinsan irin ɓata mana lokacin da
kikai?” haƙuri ta bashi. Kallona yay ya ɗauke kansa batare da yace komaiba, hakan
ya sakani gyara kujera nima na zauna.

Munja tsahon lokaci tare da ita yana mata tambayoyi kala-kala, wasu ni kaina idan
yayi hanjin cikina saisun kaɗa balle ita da akemawa, gaba ɗaya duk ya gama rikitata
da gizagonsa, sai dai ina jinjina masa akan yanda ya samu ƙwarewa akan kutse cikin
al'amuran mutum yay bincike, har kai da yakemawa ɗin ka kasa saita kanka wajen
bashi amsa ta gaskiya, dan lokacin da yarinyar ta iso a take-takenta na farko banga
alamun zata bada haɗin kai ba, amma yanda ya fara bi da ita sai naga tuni ta zurma
tana faɗin harma wanda bai tambaya ba ɗin. Ina kuma ƙara samun ilimi na aiki nima a
wajensa sosai. Lokacin da muka kammala anata kiran sallar zuhur, dan haka mukayi a
cikin wajen har shima da wasu mutanen, dan akwai masallaci ƙarami da sukayi, hakan
yasa wajen ya sake burgeni da ƙaramin nutsuwa. Koda muka idar tafiya tayi, nima na
samu waje na zauna ina jiran ya fito nai masa sallama na wuce.
Kiran da ya shigomin a waya na ɗaga, Ummie ce, bayan mun gaisa take tambayata ina
inane? Dan taje gidanmu akace na fita. Amsa na bata da cewar naje wani wajene,
yanzu kuma zanje na wanke kai na wuce gidan inna Zainabu, daga haka mukai sallama
akan zata sameni a wajen saloon ɗin ko gidan inna zainabu, na amsa da to na ajiye
wayar. Ina ɗagowa muka haɗa ido da boss dake magana da wani da nake ƙyautata zaton
sunsan junane. Janye idona nai kamar yanda shima ya ɗauke nasa, basu wani jimaba
wancan yay ciki shi kuma ya nufi hanyar fita. Bin bayansa nayi ina ƙunƙuni, danni
ɓatamin lokaci aketa famanyi.
Kusan a tare muka ƙarisa jikin motar da nake ƙyautata zaton da ita yazo, nayi zaton
gimba ne ya kawosa, amma sai naga saɓanin hakan, dan mazaunin driver ya buɗe ya
shiga, ta gefen nasa naje na tsaya, nace masa zan wuce gida nima.
Kallona yay ya ɗauke idonsa, sai da yay ma motar key, batare da ya kalleni ba yace,
“Kina ɓatan lokaci fa, ko jira kike na ɗaukeki na sakaki ne?”.
‘Innalillahi...’ kuji sabon sharri, na faɗa a raina ina kumbura fuska, danni dama
abinda nake gudu kenan yace mu tafi tare, to amma yaya zanyi, babu fuskar wargi a
garesa, dan haka na zagaya na buɗe gefen mai zaman banza na zauna.
Baice komaiba yay reverse tare da harba motar saman titi da ɗanbanzan gudu. Idanu
na lumshe ina faɗin ‘Ga wanda yafi Yah Qaseem shegen gudu da mota’. Babu mai magana
a cikinmu, sai shi da ke murza sitiyarin a hankali tamkar bayaso. Bai tambayeni ina
zaniba, nikuma ban sanar masaba inajin shakkar magana dan sai wani shan ƙamshi
yakeyi fuskarsa a ɗaure sosai.
Tafiyar da bata wuce mintuna goma sha biyu ba muka iso wani waje, da mamaki na
kalli abinda aka rubuta (LADIES MIRROR) sannan na kallesa shima, ta yaya akai yasan
saloon zanzo to?, cikin ƙarfin hali nace, “Nifa ba nan nake zuwa ba”.
ATM ya miƙomin batare daya kula maganata ba, nai ƙasa da kaina ina sake faɗin, “Ai
ambani kuɗin a gida”. Bai tanka minba nanma, sai ajiyemin atm ɗin da yay a kan
cinya tare da ƙaramar takarda. Tamkar zan fasa kuka haka naji, na buɗe motar na
fice ina sake juya al'amarin mutumin nan a raina, aunty Shahudah tasha wahala
yasin, ni saima ta bani tausayi, ƙilama wannan halin nasane ya sakata gudowa gida
‘Mtsoww’. Da wannan tunanin na ƙarasa cikin wajen da ya gama haɗuwa, dan yafi inda
nake zuwa nesa ba kusaba. gashi ƙaton gaske. Yanda ma'aikatan wajen suka tarbeni
sai abin yaban mamaki, abin akwai birgewa. Sai da na zaunane bayan na sanar musu
abinda nake buƙata sannan na sami duba takardar daya haɗomin da ita, sai naga ashe
password ɗin Atm ɗin nasane ya rubuta min, samun kaina nayi dayin murmushi.
An wanke min kaina tsaf da tafin ƙafa, aka gyaramin ƙumba, wadda ta wanke min kance
ta bani shawarar nayi kitso, a cewarta su inhar zasu maka aiki suna duba yanayin
gashinka su ɗoraka a ƙyaƙyƙyawan tsarin da bazai karye ba, kuma zai dinga tsaho,
daɗin hakan da mutane ke shigane ke sakasu sake dawowa daga nan saisu zama basu da
wajen zuwa sai nan. Murmushi na mata, ina cewa “Kodai za'amin daɗin bakin ƴan
kasuwa ne?”. Kanta ta girgiza tana murmushi, “Sam ba haka bane auntyna, duk abinda
zakiji daga bakina shine gaskiya, Gimbiya tana ajiye ingantattun kayan aiki da
nagarta a wajen nan, waɗanda daga kowacce duniya kake zaka yaba”. Kasancewar nasan
boss ba jirana zai tsaya yiba sai nace, “Okey babu damuwa amin kaɗan to”.
Wani sashen daban da inda akai min wankin kai aka kaini, mutum uku kawai akema
kitso, muka gaisa sannan na zauna nima, wadda zataimin ce ta iso kusa dani, muna
cikinyi idanuna suka sauka akan ƙaton hoton dake sama a wajen, wanda naga wanima a
can inda na baro, sai dai nesa da yay danine yasa banga waɗanda ke a jikiba, anan
kam ras nake kallonsu kamar nayi magana su amsa, ƙyaƙyƙyawar mace hamshaƙiya ta
gaske ce, tasha alƙyabba mai azabar ƙyau dake nuna jinin sarautace ita, gefenta ma
ƙyaƙyƙyawan namijine mai tarin kamala da cikar haiba, kai tsaye na ganesa shi, dan
kuwa dai sarkinmu ne Muhammad Sameer Saifudden, a raina nace ‘to ko matarsa ce
wannan ɗin?’....... Maganar wadda kemin kitso ta katse min tunani da faɗin, “Duk
wanda ya zauna nan baya gajiya da kallon hoton nan na sarauniya MUNAYA uwargida ga
adalin sarkinmu, ita kanta wani lokacin har kishin hakan takeyi idan ta shigo takan
juya hoton ya ɗau tsahon lokaci a kife”. Duk yanda naso shareta saina kasa, nai
guntun murmushi, nace, “To miyasa zata barshi tunda ba dokar ƙasace ta tilasta a
ajiyeba?”. kafin ta samu damar bani amsa, ƙyawawan ƴammata uku da yara biyu suka
shigo wajen, biyu masu tsananin kama da Sarki Sameer, sauran kuma naɗan yanayi dasu
sai dai basa tsananin kama, ukun zamu iya sa'anni dasu, biyun kuwa bazasu wuce
shekara goma sha uku ba. Cike da girmamawa naga ma'aikatan na gaishesu, sai dai
yanda suke amsawa babu wulaƙanci sai suka birgeni, gashi sai murmushi suke mana,
nima sai na maida musu murmushin kamar yanda sukeyi, cikin manyan ɗaya ta miƙomin
hannu mukai musabaha tana faɗin, “Kitsonki yayi ƙyau”. “Nagode” nace mata a
taƙaice. Sauranma duk muka gaisa, suka kuma gaisa da sauran da muke zaune.
Ɗaya a Ƙaramar tace, “Aunty Amaturrahman nidai irin kitson auntyn nan nakeso” tai
maganar tana nunani. Wadda aka kira da Amaturrahman ɗin ta amsa mata da cewar,
“Okey Safah sai a miki ai, burina dai ayi kitson kamar yanda Ummu tace”. Ɗayar tai
ƴar dariya idonta akan waya, tace, “Mudai dan ALLAH karki cikamana kunnuwa da
ihunkin nan Safah, Marwah dai nasan bamai jinta, inba hakaba ALLAH muka koma saina
bama kowa labari a masarauta har Momma”. Ɓata fuska yarinyar tayi, tace, “Ai
bazanyiba, salon kisa su Jalaludden Su ringa rainani ko Aunty Meenal? Ni wlhy wajen
Uncle Sauban zan koma india can babu ruwan mutum da wani kitso ko nabi Aunty
Amatullah Niger”. Dariya sukai mata, banda wadda suka kira Marwah shugabar
miskilanci da jin kai, daka ganta kaga Sarki Sameer Saifudden sak kamar yay kaki ya
ajiye, ni dai ina saurarensu ne sama-sama. Bayan an gama minne na miƙe nai musu
sallama na fita, ashe wajen ɗaukko Atm ɗin boss dana saka a jakka gudun basai naje
wajen biya naita dube-dube ba na yarda ɗan abinda ID cards ɗina suke ciki da wasu
passport ɗina dake a tare.
Ina cikin biyan kuɗin wayata tai ring, na kalla kamar bazan ɗagaba saboda sabuwar
Number ce sai kuma na ɗauka na saka a kunne batare da nayi magana ba, daga canma
shiru akayi, hakanne ya sani cewa, “Asslamu alaikum wanene?”. “Kin gama?” muryar
wanda banyi zato ko tsammaniba ta daki kunnena a bazata. Da sauri na cire wayar a
kunnena na sake kallon Number, gabana sai faɗuwa yakeyi, dan nasan nidai baida
Number ta, jin an yanke wayar na amshi atm ɗin da ake miƙomin na fice da sauri
domin tabbatarwa.
Jinai wani abu ya tsirgamin daga saman kai har yatsan ƙafa saboda ganin motarsa
fake a inda ya tsaya ɗazun, a fili nace, “Mikenan? Zaunawa yay jirana?’. Azababben
horn ɗin daya danna ne ya sani nufar motar tamkar mai tsoron hakan. Nasan duk
abinda zan zaunayi bayan shiga motar laifi zai zama kuma, hakan yasa na buɗe na
shiga. Baiko kalleniba ya tada motar muka fice. Sai da muka ɗauki hanya nai
dauriyar cewa, “Dan ALLAH kayi haƙuri sir, wlhy nazata tafiya kayi ne, shiyyasa da
suka ce na zauna sumin kitso na yarda”. harara ya ballamin ya ɗauke kansa ya maida
ga titi. Ban sake cewa komaiba, nacigaba da kallon titi, kamar yanda shima yake
gudu kamar shi kaɗaine a titin. Wayarsa ce ta shiga ruri, batare da ya kalli waye
ba ya ɗaga da hannunsa na haggu yasa a Hans free, daga can akai sallama, ya amsa
cikin ladabi tamkar bashiba, “Ya mukai da kai ranar juma'a akan zuwa meeting ɗin
nan Jawaad?”. yay saurin dafe kansa da faɗin, “Oh ALLAH, kayi haƙuri Uncle, naɗan
fita wani wajene amma insha ALLAH gani nan zuwa”. “To ALLAH yasa” daga can aka faɗa
ana yanke wayar. Huci ya furzar yana ɗan bugar sitiyarin, Na ɗan saci kallonsa na
ɗauke kaina, sai kawai naga ya canja hanya saɓanin inda muke. Nidai ban iya cewa
komaiba, domin ko wainar dake cikin tanda a yau ta fini samun freedom ɗin kanta.
Sai da naga ya shigo layin gidansune na iya kallonsa tamkar zanyi kuka. “Sir wlhy
nifa akwai inda zanje”. bai kulaniba, yay fakin a waje batare da mun shiga cikin
gidanba, sai da ya kashe motar sannan ya juyo ya kalleni.
A bazata kawai naji yace, “Inga kitson”. “Uhyim!” na faɗa ina ɗago kai da sauri da
waro masa idanu cikin tsagwaron firgicin jin abinda yace. Banga alamun shi ya
fuskanci abinda yay ɗin kamar yanada ban al'ajabiba, dan ya wani sake haɗe fuska
fiye da da.
“Karki cinyeni da idanunkin nan malama, ɗaukesu a kaina, zan ganine idan sun iya
sai nake kai matata can”.
Fuska na kumbura cikin suɓutar baki nace, “Aunty Shahudahr da batason kitso ɗince
zataje?”. Saukar yatsun hannunsa kawai naji kan laɓɓana ya ɗallamin da ƙarfi,
azabar zafin danajine ya sakani saurin dafe bakin idanuna na cika da ƙwalla na
kalleshi, ya dallamin uwar harar tamkar zai haɗiyeni da idanun, saurin maida kaina
nayi gefe hawayen da suka cikan ido suka sami damar silalomin, dan da gaske naji
zafi. kafin nagama fita daga zafinne, naji hannunsa saman kaina ya zame gyalen dana
yana da hular, ya saukesu saman kafaɗata, yana faɗin, “Magulmaciya waye ya
tambayeki to?”. Maybe idan nace muku kaɗan ya rage zuciyata ta fito ta baki a
wannan lokacin bazaku yardaba, jikina kansa tsuma yake, lokaci ɗaya dukkan ilahirin
gashin jikina ya miƙe domin jin ya ja jelar gashina dake ɗaure da ribbon yana faɗin
“Ashe ba ƙwaiƙwaido bace?” yay maganar a can ƙasan maƙoshi yana ɗauka hular yana
ƙoƙarin maidamin a kai, na rintse idanuna ina fisgar numfashi da ƙyar tamkar mai
Asthma, ya ɗauka gyalenma ya naɗamin kamar yanda ya gansa sannan ya kalleni fuska a
matuƙar ɗaure, yace, “Kalleni nan”. Daƙyar na iya juriyar ɗagowa na zuba idanuna
cikin nashi, yanda ya kafeni da idanu sai na kasa jurewa nai ƙasa da kaina saboda
wasu abubuwa danaga suna fitowa a idanunsa waɗanda ban taɓa ganiba, ga idon ya kaɗa
da jaa kaɗan tamkar wanda yake cikin fushi. Cikin ɗacin murya da saukemin wata
harara mai firgitarwa da ban mamaki yace, “Hankalinki ya kwanta waɗanda kika fitama
tallan jikin sun gani harsun tanka, Saina sauyama wannan fuskar taki kamanni idan
na sake ganin kin fita ba hijjab”. Yana gama faɗa ya buɗe motar ya fice abinsa
batare da ya sake kallona ba.
Tamkar sokuwa haka na bisa da kallo, shiko ko waiwayena baiyiba har ya isa jikin
ƙaton gate ɗin ya tura ƙaramar ƙofar ya shiga. Baya nai luuu na faɗa jikin kujerar
na jingina bayana, ina sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanu, nace,
‘Na shiga uku ni balkisu’. naja kusan mintuna uku a haka kafin na samu numfashina
ya dai-daita. Gaba ɗaya man kaina ya gama tsiyayewa, nama rasa yanda zan fassara
abun nasa, nakai hannu na shafa laɓɓana da har yanzu sukemin zafi, sai kuma na buɗe
ido na kalli mirror, har laɓɓana sunyi ja, a fili nace, ‘Mugu, aiko Yah Qassem dake
dani bai kafan wannan dokarba saishi daga mijin Auntyna’. Sai kuma nai saurin dafe
bakin na kalli inda ya tashi sai kace ancemin gashi ya dawo. Da sauri na sake
rintse idanu da dafe kai, a fili na sake faɗin, ‘Ya rabbi ka kawomin ɗauki, Mutumin
nan zai kasheni’. Sai kuma na harari ƙofar gate ɗin na buɗe motar da sauri na fice
abina,
★★
Jawaad kam Haka kawai ya tsinci kansa dayin murmushi lokacin daya buɗe gate ɗin ya
shiga gida, sai kuma ya taɓe baki tare da jan ƙaramin tsaki ya nufi sashen mama
Atika yana ƙwafa mai nuna takaicin wani abu da har yanzu yake cimasa rai. yasan dai
taron meeting ɗin bai wuce can ɓangaren mama Atika ba saboda shegen fitinar
tsohuwar. Da sallama ya shiga, suka amsa kusan su duka alamar shi ake jira, wani
iri yaji a ransa saboda ganin harda kakansa dasu Umma, yadai samu waje ya zauna
sannan ya gaidasu.
★★★★★★★
A LADIES MIRROR kuwa lokacin da abinda ID cards ɗin Bily suke ciki ya faɗi akan
idon Safah ne, amma sai taƙi magana, sai da ta tabbatar bily ta daɗe da barin wajen
sannan ta ɗauka tana faɗin, “Lah Aunty Meenal diba kiga auntyn nan da nace amin
irin kitsontace ta yarda”. Duk kallonta sukayi, Amaturrahman ta dalla mata harara
da faɗin, “Shine dan iskanci bakiyi maganaba sai yanzun?”. Baki ta tura gaba tana
langaɓe kai gefe, “To ai mantawa nayi ko”. Amatullah tai dariya da cewa, “Kai Safah
lamarinki sai ke wlhy, saiki bada a ajiye mata dan nasan zata dawo nema”. Da sauri
tace, “A'a aunty Ama mu kai mata dai”. Marwah da tun ɗazun bata kula kowaba tanata
game a ipad ɗinta ta harari Safah. Ramawa Safah tai, cikin tsiwarta data gada wajen
Munaya tace, “Miye kike wani hararana ke kuma malama?”. Lips Marwah ta cije like
Sarki Sameer, ta ɗauke kanta batare data tanka mataba.
Duk yanda sukaso Safah ta bada a ajiyema bily saboda idan ta dawo nema ma'aikatan
wajen su bata fir taƙi, daga ƙarshe Amaturrahman tayi kiran Ummu ta sanar mata,
Sarauniya Munaya dake kishingiɗe a kilisarta ana tausa mata ƙafa ta girgiza kai
kawai da lumshe ido, babu abinda Safah ta bari na halayyarta, ta tabbatar kuma
akwai dalilin da yasata yin hakan, a hankali tace, “Kubarta tazo dashi, sai a nema
yarinyar”. Amaturrahman tace, “Ummu yanzu nan biye mata zakiyi?” yanke wayar Munaya
tayi batare da ta bama Amaturrahman amsaba. Dole badan sun soba akabi abinda Safah
keso sukatafi dashi bayan an kammala musu kitso su duka kamar yanda Ummu ta korosu
suyi badan sunso hakanba..............✍

Maison zuwa gagara badau ya shirya muje gaida Sarki Sameer Saifudden da gimbiya
Munaya😉😉lol.

ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[11/30/2020, 12:56 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:


Page 16

...............Napep na samu na tare nai tafiyata gidan Inna zainabu. Can nai
zamana mukasha hira da Lawusa da a yanzu muke ɗasawa har bayan sallar isha'i sannan
na nufo gida.

★★★★★

Bayan an buɗe taro da addu'a Uncle Nasir ya fara jawabi kamar haka.
“Kamar yanda kowa ya sani mun fara tattaunawa akan maganar zaman Jawaad babu aure a
kwanakin baya, har takai mukai masa tayin cikin yaran gidannan ko akwai wadda ya
keso, sai dai ya nuna a lokacin zaiyi tunani, tun daga wancan lokacin ban sakeji
daga gareshiba, to magana ta gaskiya mun gaji da ganinsa yana yawo a gari haka ana
zaginmu, shi kansa bama girmansa bane, ƙannen-ƙannen bayansa ma gasunan duk da
iyalansu har da ƴaƴa, yakamata Jawaad kaima kanka faɗa, dan lokaci bawai zai zauna
jiranka baneba, kai kaɗai Abdul-aziz ya haifa, zamuso ganin ƴaƴanka a duniya kamar
yanda mukasan da yanada rai zai ɗokantu da haka shima. A wannan karon ba shawara
muke bakaba, umarnine, shiyyasama mukazo da Alhaji Baba domin ya zama shaida, tare
da iyayenka, dolene a wannan karon kayi aure, ka zaɓi mace ɗaya a cikin ƴaƴan
gidannan koma fiye da ɗayar mukuma zamu aura maka”.
Jawaad da kansa ke ƙasa yay guntun murmushi domin son ɓoye ɓacin ransa, batare
da ya ɗagoba yace, “Uncle ku gafarceni, bazan jaku da nisaba, duk cikin yaran
gidannan bazan iya auren kowaba, dan kallon ƙannena nake musu tamkar ciki ɗaya...”
da sauri Uncle Uwaisu yace, “Ai tamkar kace, bawai hakan bane, tunda babu ta inda
ALLAH ya haramta maka, Jawaad bamason shirme, garama ka zaɓa komu mu zaɓa maka,
kokuma ka ɗauki zaɓi na biyu, wato ka maida matarka ɗakinta kuje kuyi haƙuru da
juna tunda yarinyarnan ta horu kuma tana sonka”. Yanzu kam kasa daurewa yay saida
ya ɗago kansa ya kalli Uncle Uwaisu, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru saboda
gargaɗi da Alhaji Baba yay masa da ido, kansa ya maida ƙasa yana sauke ajiyar
zuciya.
Uncle Sulaiman yace, “Son!” ɗago kai Jawaad yay ya kalli Uncle ɗin nasa da
yake matuƙar so saboda ƙyawun halinsa, yace, “Na'am Uncle”. “Ko Kanada wadda kake
sone?”. Ƙasa Jay ya maida kansa yana motsa laɓɓansa, sai dai babu maijin mi yake
cewa, Uncle Taheer ya katsesa da faɗin, “Kai muke saurare Jawaad”. Batare daya
ɗagoba ya girgiza musu kai alamar a'a. Shiru falon ya ɗauka kowa ya zuba masa
idonu, shi kuma yaƙi kallonsu. Mama Zuhurah da bata da yawan magana tace, “To
Jawaad ya kakeso ayi kenan? Yanzu kai kafijin daɗin kullum aita zaman meeting
akanka akan maganar kaƙi aure, ka rufa mana asiri ka fidda kanka damu iyayenka daga
zargi da zunɗen al'umma kaji, ƴar uwarka na sonka, tayi nadamar kuskuren datai a
baya, kayi haƙuri a maida aurenku kaji”.
Ɗagowa yay zaiyi magana fitowar Shahudah ta katse masa hanzari, gabansa
taje ta durƙusa tamkar yanda Mama Atika da Mom suka kitsa mata, ta fashe da kuka
tare da kama ƙafafunsa, cikin gurɓatacciyar hausarta da harshen turancin da tafi
ƙwarewa ya cinye tace, “Bb dan ALLAH ka gafarceni, wlhy nayi nadamar abinda na
aikata, nakumayi alƙawrin bazan sakeba, na yarda zan haihu maka yara komai yawan da
kake buƙata yanzun, idan ka barni mutuwa zanyi wlhy, dan ALLAH ka ceci rayuwata
Bb...” hannunta ya ture daga saman ƙafarsa yana hararta, “Kima daina ɓata
lokacinki, indai haihuwace bana buƙata daga gareki Hudah, karki damu kije kicigaba
da cin moriyar ƙuruciyarki kinji, indai nine kima saka a ranki baki taɓa sanin mai
kama daniba dan mun rabu kenan”. Fashewa tai da matsanancin kuka yanzunkam fiye da
da, dan har ƙasan ranta kalamansa sun masifar sosa mata zuciya, ta dafe kanta dake
juya mata, babu zato sai kawai ganinta ƙasa sukai ta yanke jiki ta faɗi. Gaba ɗaya
ƴan falon da suka zuba musu ido suka miƙe, shi kansa Jawaad ɗin kallonta yake, dan
ya zata salon iskancinta ne, sai daga baya da aketa jijjigata babu alamar rai
tattare da itane ya fuskanci babu wasa a lamarinta, gaba ɗaya falon ya rikice, dan
iya ƙoƙari anyi Shahudah taƙi farfaɗowa, Mom sai kuka take da sambatu.
Dole aka kwashi Shahudah zuwa asibiti da gaggawa kuwa, dan wasunsu harsu
fidda ran da gaske ta mutu.

★★★★★★★

Tun a gate baba maigadi yake sanarmi

n ai babu kowa a gidan duk suna asibiti aunty Shahudah babu lafiya, hankalina ya
tashi sosai, dan haka nai azamar tsayar da mai napep ɗin dake shirin juyawa dan
harma ya fara tafiya, shiga nayi na sanar masa asibitin da baba magadi ya sanarmin
an kaita. Asibitine mai ƙyau dan na kuɗine, kasancewar bansan ina zan nufaba sai
nai kiran aunty Aamilah, saidai bata amsa ba, na sake kira nanma babu amsa, maida
kiran nai kan Yah Qaseem, sai da ta kusan tsinkewa sannan ya ɗaga, faɗa masa nai
gani a asibitin a ina suke?. Muryarsa a sanyaye yace na jirasa yazo ya shiga dani.
A yanda na gansa kawai na tabbatar akwai babbar damuwa dangane da aunty
Shahudah, kasa daurewa nai na shiga jera masa tambayoyi. Amsa ɗaya na samu daga
garesa, shine ta farfaɗo, sai dai sun mata allurar barci, sun kuma hana kowa
ganinta sai banzan Jawaad ɗin da taketa sambatun kira. Ta bani tausayi matuƙa, dan
na sake fahimtar tsananin son da takema Boss.
Duk sai da na gaida waɗanda na tarar a wajen, sannan na tambayesu ya mai
jiki, sai dai babu Boss babu dalilinsa a wajen, zama nai kamar yanda suke zaune
jigum-jigum, kusan mintuna biyar sai naji ƙamshin turarensa. Ɗago kai nai dan
tabbatarwa, karaf kuwa muka haɗa ido dashi, ya dalla mani harara sannan ya ɗauke
kansa tamkar baiyiba. Nima janye nawa nai, dan nasan laifina dai bai wuce tafiya
bada izininsa ba. Cikin nutsatstsiyar muryarsa dake tattare da alamun gajiya naji
yana faɗima Uncles nasa da matansu ya kamata su tafi gida su huta, tunda dai Doctor
yace bazasu bari a gantaba har sai zuwa safiya.
Cike da nazari nake satar kallon yanda wasu suke masa kallon harara dajin
haushi a kaikaice, amma a zahiri suna amsashi cike da kulawa, sai al'amarin nasu
yay masifar ɗaure min kaina, to amma abinda babu ruwanka ai daɗin kallo garesa, dan
haka nai ƙasa da kaina kawai ina sauraren mahawarar da suke akan wanda zai zauna ya
kwana, ance Mom taje gida Aamilah ta zauna, sai dai ita aunty Aamilah ta tubure
akan tsoro takeji ta kwana asibiti, da sauri Salman yace, “Kedai wawuyace Aamilah,
to sai wannan yarinyar tazauna ku kwana ai”. Yay maganar yana nunanu. Da sauri Yah
Qaseem yace, “Itakuma aikin tafa? Itadai Aamilah da babu inda take zuwa itace ta
cancanci kwana da itan”. Shiru kowa yay, sai kuma daga baya wasu sukai na'am da
batun Yah Qaseem ɗin, na saci kallon Boss da uffan baiceba, yama ɗauke kansa daga
garemu tamkar baisan mimukeyiba, nikam lamarinsa kan bani mamaki wani lokacin
gaskiya.
Wata mata da nake ƙyautata zaton cikin matan Uncles ɗin nasune ta kawo
shawaran haɗa Aunty Aamilah da ɗaya daga cikin yaran gidansu ɗin da wata dattijuwar
mai aiki, akan wannan shawarar aka zauna, dan haka duk sai muka fara shirin tafiya.
Har mun fito baki ɗaya Mom tace gaskiya bazata iya tafiyaba, itama anan zata kwana,
duk kallonta mukai da mamaki, sai kuma naga tsoro akan fuskokin wasu, dan koni naji
wani iri saboda ganin Mom na sharar ƙwalla, nasan yanda ƴan gidanmu ke masifar son
aunty Shahudah, hakan ya samo asaline saboda so mai tsanani da Dad ke nunamata
kasancewar sunan Mahaifiyarsa taci, sai naji a raina kamar zamu iya rasa aunty
Shahudah, duk yanda aka lallashi Mom taƙi aminta da hakan, sai kawai aka barta.
jinai wani iri, dan tundafa Mom zata zauna nikaɗaice mace zan kwana a gidan, nima
da sauri nace to zan zauna a asibitin, da sassafe sai naje gida.
Harara Yah Qaseem ya dallamin da cewar bazan zaunaba gida zani. Niko na fara
roƙonsa akan ya barni, shikuma yaƙi saurarena, kowa kuma yaƙi saka mana baki. Na
kalli inda Boss yake tsaye a jikin mota hawaye na gangaromin akan fuska, sarai
nasan duk yanajinmu, amma yayi kunnen uwar shegu da kowa, harna yanke ƙauna daga
taimakon kowa na tsinkayi muryarsa yana faɗin,
“Ita Aamilah ta fito ku wuce gidan tare mana, dan sunmayi yawa anan
tunda Mom zata zauna, na tabbata sai ma'aikatan asibitin sunyi ƙorafi”. Harararsa
Yah Qaseem yayi, sai dai baiyi maganaba.
Uncle Nasir ne yay na'am da shawarar Jawaad, dan haka ya aika aka kira
Aamilah. Naji daɗin hakan da samun nutsuwa sosai. Daɗin da najine ya sakani matsawa
inda yake

nace, “Thanks you Sir”. Banza yaymin tamkar bai jiniba, sai daƙilar waya yake
abinsa, na ɗaga ƙafafuna zanbar wajen naji yace, “Uhm”. Kallonsa kawai nai sau ɗaya
nabar wajen zuwa motar Yah Qaseem daketa antayomin harara tamkar idanunsa zasu zubo
ƙasa.

Tunda muka tafi yah Qaseem keta zabga jarabar da babu wanda yasan
kanta, daga ni har Aunty Aamilah da Yah Salman babu wanda ya kulashi, yana gama
fakin kowa yay ficewarsa, dama nice farkon fitama nai cikin falo dan banaso ya
tsaidani, nayi masifar gajiya wajen hutu kawai nake buƙata. Ina shiga ɗakina na
murza key, na zaresu na ajiye saman mirror tare da jikkata dana cire a kafaɗa.
Idanuna har lumshewa suke saboda gajiya, haka na daure nayo wanka da alwala na
fito, daƙyar na iyayin shafa'i da wutiri na faɗa saman gado, sama-sama ma nai
addu'a sai barci.

Cikin barci na ringajin saukar numfashin mutum a jikina, na


buɗe idanu a razane ina ambaton ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ tabbas a jikin
mutum nake, na buɗe baki zan ƙwalla ƙara aka dafe bakin da hannu, cikin wata irin
murya da bantaɓa jin mai itaba a gidan ake magana da shafamin jiki, “Bazan iya
saduwa dake baƙya cikin hankalinkiba kamar sauran, shiyyasa na zaɓi baki damar
farkawa, kiyi haƙuri ki bani haɗinkai cikin sauƙi bilkisu, samunkine kaɗai ya
ragema cikar burina yanzun, karki lalatamin tanadina na tsahon shekaru, nai miki
alƙawarin zan biki a sannu bazan cutar dakeba kodan son da nake miki, sannan zaki
moru da tagomashi mai yawa a gareni saɓanin sauran da basu sami komaiba sai baƙin
ciki, tun farko kece tsanin nasarata da na ɗauku dakon jira tsahon lokaci”.
Tsabar tashin hankalin da nake ciki sai zufa nake kwararwa dukda ac
dake aiki a ɗakin, jikina wata irin muguwar rawa yake da ɗaukar azababben zafi
lokaci ɗaya, gashi ya rufemin baki, hawayenma sunƙi fita daga idona sai zuciyata ke
kukan, duk addu'ar da tazomin bakina yi nake da taimakon UBANGIJI na.

‫ َو َنُعوُذ ِبَك ِم ْن ُش روِرِهْم‬، ‫ َالَّلُهَّم ِإَّنا َنْج َع ُلَك ِفي ُنُحوِرِهْم‬.


“Allahumma inna naj'aluka fee nuhoorihim wana'oothu bika min shuroorihim”.

Ya ALLAH! Mu mun sanya ka a gabansu, kuma muna neman tsarinka daga sharrace-
sharracensu.

‫ ِبَك َأُجوُل َو ِبَك َأُصوُل َو ِبَك ُأَقاِتُل‬،‫ َو َأْنَت َنِص يِر ي‬،‫َالَّلُهَّم َأْنَت َعُض ِد ي‬.
“Allahumma anta 'adudee, wa-anta naseeree, bika ajoolu wabika asoolu wabika
oqatil”.

Ya ALLAH kai ne mai karfafa ni, kuma kai ne mataimakina, da karfinka ne


nake yin dabarun yaki, kuma da karfinka ne nake kai hari, kuma da karfinka ne nake
yin yaki.

‫َح ْسُبَنا اللُه َوِنْع َم اْلَو ِكيُل‬.


“Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel”.

ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro.

‫ َع َّز‬،‫ َو َأْح َز اِبِه ِم ْن َخ َالِئِقَك ؛ َأْن َيْفُر َط َع َلَّي َأَح ٌد ِم ْنُهْم َأْو َيْطَغى‬،) ‫ ُك ْن ِلي َج اًر ا ِم ْن (ُفَالٍن‬، ‫ َو َر ِّب اْلَع ْر ِش اْلَعِظ يِم‬،‫َالَّلُهَّم َر ِّب الَّس َمَو اِت الَّسْبِع‬
‫ َو َال ِإَلَه ِإَّال َأْنَت‬، ‫ َو َج َّل َثَناُؤ َك‬، ‫َج اُرَك‬.
“Allahumma rabba s-mawati s-sab'i wa rabba-l-'arshi-l-'azimi. Kun li jaran min
(fulanin) wa ahzabihi min khala'iqika, an yafruta 'alayya ahadun minhum aw yatgha.
'Azza jaruka, wa jalla thana'uka, wa la ilaha illa anta”.

Ya Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al'arshi mai girma, ka kasance


mai tsari gare ni daga wane dan wane, da dukkan rundunarsa daga cikin halittunka
kar wani daga cikinsu ya yi gaggawar azaba a gare ni, ko ya ketare haddi, kariyarka
ta buwaya, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai kai.

‫ اْلُمْمِسِك الَّس َمَو اِت الَّسْبِع َأْن َيَقْع َن َع َلى‬، ‫ َأُعوُذ ِباللِه اَّلِذ ي َال ِإَلَه ِإَّال ُهَو‬،‫ َاللُه َأَع ُّز ِمَّم ا َأَخ اُف َو َأْح َذ ُر‬، ‫ َاللُه َأَع ُّز ِم ْن َخ ْلِقِه َجِم يعًا‬، ‫َاللُه َأْك َبْر‬
، ‫ َج َّل َثَناُؤ َك َو َع َّز َج اُرَك‬، ‫ َالَّلُهَّم ُك ْن ِلي َج ارًا ِم ْن َش ِّر ِهْم‬،‫ ِم َن اْلِج ِّن َو ْاِإل ْنِس‬،‫ َو ُج ُنوِدِه َو َأْتَباِعِه َو َأْش َياِعِه‬، ‫ ِم ْن َش ِّر َعْبِد َك ُفَالٌن‬،‫ْاَألْر ِض ِإَّال ِبِإْذ ِنِه‬
‫ َو َال ِإَلَه َغ ْيُرَك " َثَالَث َم َّراٍت‬، ‫َو َتَباَرَك ِاْس ُم َك‬.
“ALLAHU akbaru. ALLAHU a'azzu min khalqihi jami'an. ALLAHU a'azzu mimma akhfu wa
ahdharu. A'udhu billahi lazee la ilaha illa huwal mumsikis samawatis s

ab'i an yaqa'na 'alal-ardi illa bi'izinihi, min sharri 'abdika (fulanin) wa


junudihi wa atba'ihi wa ashya'ihi minal-jinni wal-insi. Allahumma kun li jaran min
sharrihim Jalla thana'uka wa 'azza jaruka, wa tabaraka smuka, wa la ilaha
ghayruka”.

ALLAH shi ne mafi girma, ALLAH shi ne mafi buwaya daga dukkanin halittarsa, shi
ne mafi buwaya daga abin da nake jin tsoronsa kuma nake shayinsa. Ina neman tsarin
ALLAH, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, mai rike sammai daga su ruguzo a
kan kasa sai da izininsa, daga sharrin bawanka (ya ambai sunansa), Ya ALLAH! Ka
zamo mai tsari gare ni daga sharrinsu. Yabonka ya girma, kuma kaiyarka ta buwaya,
kuma alherin sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba kai ba”.

Duk da na rigada na sadaƙar tawa ta ƙare ban fasa karanto addu'oinba ina
faɗama ALLAH kukana, koda a wani wajen bana haɗa kalmomin dai-dai saboda ruɗani
karantowa nake, wata razananniyar ƙara mukaji a dukkanin illahirin gidan, hakan ya
saka koma waye sakarmin baki ya miƙe a firgice kamar yanda nima na samu damar
ƙwalla tawa ƙarar saboda firgita da nayi, ɗif naji kunnuwana sun daɗe banajin
motsin komai, dukda ɗakin a duhu yake dunɗum, jinai an sake rungumeni an fashe da
kuka, yanzunkam a tare muka ƙwala ihu da koma wanene duk da naji jikin ya banbanta
dana wancan, ɗakin sai naga yana wani irin juyamin tamkar ina cikin hajijiya,
rumtse idanuna nai da ƙarfi na sake ƙwalla ƙarar da ni kaina bansan iyakar ina
muryata ta tsaya ba a gidan, daga nan ban sake sanin mi duniyar ke cikiba kuma.

Duk wanda yake a cikin gidan kunnensa saida ya jiye masa ƙara maiban
tashin hankali da tsoratarwa da aka ƙwala da farko a wannan dare, wadda taɗauki
adadin mintuna biyar kafin ta gushe ihun bilkisu ya biyo bayanta, Aamilah da
ɗakinta ke kusa dana Bilkisu ce ta fara fitowa a razane saboda kiɗimar data shiga
na tsoro itama, cikin lalube ta afko ɗakin bilkisu batare data saniba itama tana
ihun, fitar sautin ihun bilkisu ne ya bata damar isa inda take suka ƙanƙame juna
suna kuka maiban tashin hankali. A daidai lokacin da Qaseem da Salman harma da kuku
suka shigo sashen suma a razane, dan duk wanda yake gidan yaji ƙarar farko, sannan
a yanzu yana jiyo ihun su Aamilah dake nuna alamar tsoratar da sukaice ta gusar
musu da hankali suka tsinci kansu a yanayin. Kuku ne ya samu damar kunna fitilar
ɗakin haske ya gauraye ko'ina, dukansu kansu Bilkisu sukayi, dan hakan yayi daidai
da ɗaukewar numfashinta daga gangar jikinta.
Babu mai iya musalta tashin hankalin da suke ciki a wannan dare, kan
kowa ya kulle daga abinda ya faru, cikin ƙarfin hali Salman ya ɗakko ruwa ya miƙama
Qaseem dake taya Aamilah jijjiga Bilkisu, bai tsaya yayyafa mataba ya bulbule
matashi kawai a fuska, wani nannauyan numfashi Bily ta kawo, sai dai jikinta babu
alamun ƙarfi, ta buɗe idanu a hankali ta kalli kowa sai kuma ta maida ta lumshesu
hawayen da bata samu yiba ɗazun suna ziraro mata a kumatu masu ɗumi.
Sama-sama nake iya jiyo muryar yah Qaseem daketa jeramin sannu shida Aamilah
da Kuku, bandaiji muryar Salman ba sai daga baya, tsahon wasu mintuna muna a haka
kafin barci yaɗan fara fisgata, addu'a nake buƙatar ko yaya wani ya dinga karantowa
yana tofamin kozanji sauƙin abinda nakeji a jikina tamkar ana kunna garwashin wuta,
sai dai nasan ba samu zanba, dan duk waɗanda suke a kaina babu mai irin wannan
tunanin. nesa-nesa nake jiyo maganar Yah Qaseem dake cewa Aunty Aamilah mutashi
muje mu kwanta, da taimakonta na koma saman gado, sai daifa tace itama anan zata
kwana bazata koma ɗakintaba, sannan suma dan ALLAH su kwanta anan ɓangaren basai
sun koma nasuba. Bansan amsar da suka bataba saboda idona ya rufe ruf da barci.

★★★

Kiran sallar farko na asubahi na farka, sai dai abin mamaki da al'ajabi
na mance kaso mafi yawa na abinda ya faru jiya a gidan, na tashi zaune ina kallon
Aunty Aamilah dake mamuƙe dani alamar a tsorace tai barci, ajiyar zuciya na sauke a
hankali inason tuno koda wani abune kaɗan, sai dai sam ƙwaƙwalwata ta gaza aiki,
tamkar ansa murfi an toshe bututun dake kai saƙo tsaka

nin ƙwaƙwalwa da zuciyata, addu'a na shiga karantowa kozan sami sassaucin da nakeji
dangane da ƙuncin da zuciyata ta shiga da zafin da nakeji a cikinta.

‫ َو َأْص ِلْح ِلي َش ْأِني ُك َّلُه َال ِإَلَه ِإَّال أْنَت‬،‫َالَّلُهَّم َر ْح َم َتَك َأْر ُجوَفال َتِكْلِني ِإَلى َنْفِس ي َطْر َفَة َعْين‬.
“Allahumma rahmataka arjoo fala takilnee ila nafsee tarfata 'ayn, wa-aslih lee
sha'nee kullah, la ilaha illa ant”.
Ya ALLAH! Rahamarka nake kauna, don haka kar ka kyale ni da kaina ko da
kiftawar ido ne, kuma ka kyautata mini sha'ainina dukkansa; babu abin bautawa da
gaskiya sai kai.
Sai da aka fara kiran salla ta biyu sannan na samu ƙarfin sakkowa daga
gadon, banda ƙuncin zuciya babu abinda nakeji a jikina, sai kaina dake ɗan ciwo
kaɗan-kaɗan da marata, ban ɗauki hakan komaiba, dan nasan hakan alamun zuwan period
ɗinane, da sam bana ciwon mara idan zanyi al'ada, amma a shekararnan gaba ɗaya haka
nake fama dukda bawai yanamin tsanani baneba. Saida na duba na tabbatar babu alamar
zuwansa ciwon mararne kawai sannan nai wanka dan na samu ƙwarin jikina, daga nan
nayo alwala na fito. Nayi ƙoƙarin tada aunty Aamilah amma sam taƙi koda motsi, haka
na haƙura na barta nai sallata ganin nima lokaci na neman ƙwace mani. Bayan nayi
azkar karatun alkur'ani nayi har zuwa 7am sannan na tashi, shirin office nayi
abina, harna kammala aunty Aamilah batako motsaba har lokacin, nakuma ƙoƙarin
tadata salla amma taƙi tashi, ƙyaleta nayi na fita kicin danna samu koɗan tea na
sha dukda banajin cin komai.

★★★★★★★

Tunda suka shigo gidan daga asibiti daƙyar ya iya dauriyar yin wanka
saboda barcin da yakeji, ya samu yay shafa'i da wutiri a daddafe ya haye gadonsa,
ya fara addu'a, amma bashi da tabbacin ya kammalata barci yay awan gaba dashi. Can
tsakkiyar dare ya farka a matuƙar razane saboda mummunan mafarkin da yayi.
‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’.

‫ َو َش ِّر ِعَباِدِه َو ِم ْن َهَم َز اِت الَّش َياِط يِن َو َأْن َيْح ُضُروَن‬،‫َأُعوُذ ِبَك ِلَم اِت الَّلِه الَّتاَّم اِت ِم ْن َغ َض ِبِه َو ِع َقاِبِه‬.
“A'oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa'iqabih, washarri 'ibadih, wamin
hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon”.
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa, da ukubarsa, da
sharrin bayinsa, da kuma wasuwasin shaidanu, da kuma kada su zo mini (a cikin
al'amurana).
‫َأُعوُذ ِباللِه ِم َن الَّش ْيَطاِن الَّر ِج يِم َثَالٍث َم َّراٍت‬.
a'uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem’. ya faɗa sau uku, yay addu'a ya tofa gefen
haggunsa da dama sau uku, sannan ya sauka a gadon, alwala yayo yazo yay salla
raka'a biyu saboda idonsa cike yake da barci, yay addu'a sama-sama ya koma saman
gadon ya kwanta, sai dai ya canja sashen da yay mafarkin dashi ɗazun. Babu jimawa
barcin ya sake awan gaba dashi.
Ana kiran sallar shiga massalaci ya farka, hakan ya sakashi ɗaura al'wala ya
fita massalaci dan har an tada sallah. Koda aka idar bai wuce motsa jikiba yau sai
ya shigo gida duk da yana buƙata saboda jikinsa yayi nauyi, gyara ɗakinsa yay ya
shiga wanka, bayan ya fito yay shirin office. Ƙarfe bakwai da kwata Gimba ya
ɗaukesa suka fice daga gidan..............✍

Gaskiya an fara sakama boss ido a gidannan fa😑, yana koyama yarinya aiki anacewa
yayi🤐🙄 nayi nan, karkuma ace na koma team Beejay ne🚴🏼.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[11/30/2020, 12:56 PM] HASNA ✍🏻
: Typing

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 17

................Bayan na kammala shan tea ɗin dana sakama suga kaɗan sai na fito
daga kicin ɗin, a falo na iske Yah Qaseem zaune yana waya da Dad, da alama abinda
ya faru a daren jiya yake bashi labari, sai dai yanda naji yana faɗama Dad ɗin
shima wai ba komai zai iya tunawaba, shidai kawai an bamu tsoro jiya a gidan.
Bansan mi Dad ya faɗa masaba, nadaiji ya amsa masa da cewar, “To Dad ALLAH ya
kawoka lafiya, itama yanzu zamuje asibitin muji yaya jikin nata”. Yaɗanyi shiru
yana sauraren mi Dad ɗin ke faɗa daga can, sai yace, ”Okey gata”. Wayan ya bani,
muka gaisa da Dad, daga can yace, “Ɗiyata yaya jikin naki?”. Muryata a sanyaye da
har yanzu nakejin jikina wani iri nace, “Alhmdllh Dad, banajin ciwon komai sai na
kai, gashima nayi shirin Office ”. “To ALLAH ya kiyaye gaba ya ƙara sauƙi kinji,
nima insha ALLAHU ina tafe, anjima kaɗan zan iso”. Nace, “To Dad ALLAH ya kawoka
lafiya”. “Amin” ya faɗa mukai sallama, na miƙama Yah Qaseem wayarsa. Miƙewa yay
yana faɗin, “Muje dan mu samu mubiya asibitin”. Kaina na jinjina masa, har mun fara
tafiya nace, “Yah Qaseem bazakasha ko tea ba?”. Kansa ya girgizamin a sanyaye, haka
kawai na samu kaina da tsura masa idanu, gani nai fuskarsa tai jazur kasancewarsa
farin mutum, idanunsama haka, duk ya wani fita hayyacinsa, gashi tamkar a firgice
yake. Cikin katseni yace, “Bilkisu lafiya?”. Firgigit na dawo hayyacina, saina
girgiza masa kai kawai nai gaba ya biyoni a baya.
Tunda muka fice daga gidan babu mai iya cema ɗan uwansa komai, yau ko redio bai
kunnaba, sannan sam baya gudu kamar yanda ya saba, duk yanda naso tuno wani abu na
daren jiya na kasa hakan a yanzunma, iyakar firgitar da mukai kadaice ban mantaba
da abinda ya biyo bayanta, amma miye musabbabin hakan? Amsar itace ban saniba ba,
tamkar anma ƙwaƙwalwarta formatting ɗin komai lokaci ɗaya, haƙura nai dason tunawar
na cigaba da maimaita ‘Hasbinallahu wa ni'imal wakil’ a cikin zuciyata.
Motar Jawaad na fita daga asibitin bayan yasa gimba ya biyo sun duba Shahudah su
Bilkisu na shigowa, shi Qaseem yaga fitarsu Jawaad, amma bily bata luraba dan
hankalinta baya tare da duniyar mutane.
Shiga suma sukai suka duba Shahudah, har yanzu barci take, sundai leƙata ta Window
suka fito, gudun karsu makara yasa sukaima Mom sallama suka wuce office.
★★★★★★
Koda muka iso yau ban samu damar yima Yah Qaseem rakkiyaba, shima bai nema hakanba,
da kansa ya kwashi kayansa ya wuce office nima na wuce. Sama-sama nai gaisuwa da
kowa na zauna a mazaunina, Ummie kanta yau takula bani da walwala, koda ta dameni
da tambaya sai nace mata aunty Shahudah ce bata da lafiya tana asibiti. “ALLAH ya
bata lafiya” kawai tace cikin rashin ɗaukar abun da muhimmanci.
Ban iya cewa da ita komaiba na cigaba da aikin gabana, kusan sha ɗaya akai kiran
wayar landline ɗin office ɗin namu, Ada dake kusa ta ɗaga, da hannu taimin nuni
nazo. Na ajiye biron hannuna na nufeta, miƙamin kan wayar tayi tabar wajen, na saka
a kunne nace, “Hello”. “Ki sameni a office” kawai akace aka yanke. kamar nayi kuka
haka naji, da inada dama dana roƙesa ya ɗagan ƙafa zuwa ɗan anjima, dan marata a
ƙulle take tamau ga wani azababben ciwon kai dake cina tamkar jijiyoyin kan zasu
katse. Mazaunina na koma na ɗauki ATM ɗinsa dana manta jiya ban bashiba na saka a
aljihu na fita, ina kallon su Ada na gulmata, na girgiza kai kawai na fice abina
dan banida lokacinsu.
Halin da nake ciki ya sake haddasama tafiyata sanyi, ga fuskata a cinkushe sosai,
wadda harni kaina nasan bana cikin yanayin farin ciki gaba ɗaya yau, abinne ya
haɗemin da yawa, zuwan period kan sakama mace ɓacin rai na babu gaira babu sabar,
tausayin aunty Shahudah da ganinta yau ya sake ɗagan hankali, damuwar abinda ya
faru a daren jiya dason tuna koda ƙanƙanin abune amma hakan ya gagara, ciwon kai ga
mara dakan saka mutum takura yaji baya buƙatar yin koda magana ma.
Nai knocking ƙofar a hankali tamkar banaso, shirun da naji ya sakani sake
ƙwanƙwasawa, umarnin shigowar da aka bani daga cikine ya sakani tura ƙofar na
shiga.
Ƙamshin dana shaƙa a office ɗin ya sakani jin ɗan sanyi a raina, na ƙarasa inda
yake ina mai satar kallonsa, sanye yake da suit yau, sun masa ƙyau sosai kamar koda
yaushe, bai ɗagoba tunda na shigo, yanata rubuce-rubuce a takarda. nace, “Ina kwana
sir” bai amsa minba, hakanne ya sakani kallonsa da haushi, sai da na kalli abinda
ke a kunnensa na fahimci waya yakeyi, yaɗan ɗago ido ya kalleni yana faɗin, “Okey
Sir” cikin jinjina kai. Da hannu yaymin nuni da kujera, kaina na gyaɗa masa kawai
na zauna, cigaba da abinda yakeyi yayi. Bawani sauraren abinda yake nakeba balle na
fahimta saboda halin da nake ciki, kusan mintuna bakwai kafin suyi sallama ya
cigaba da rubuce-rubucensa baice dani uffanba.
Cikin dauriya na kumace masa “Ina kwana”. “Lafiya” kawai yacemin yana cigaba da
sabgarsa. Ɓoyayyen numfashi na sauke ina ƙoƙarin son daidaita gudun zuciyata, na
ɗora masa ATM ɗinsa saman table ɗin nace, “Gashi nagode, ALLAH ya ƙara buɗi mai
albarka”.
Karon farko da tunda bilkisu ta shigo office ɗin Jawaad ya ɗago ya kalleta.
Yanda ya zubamin idanun ne ya sakani saurin duƙar da kaina, baiyi maganaba ya maida
kansa ga abinda yakeyi yana ɗan lumshe idanu. sai kuma ya ɗago kansa, takardun dake
gefen hannun damarsa ya ɗakko, buɗesu ya shigayi na wasu mintuna sannan ya miƙomin
yana kafeni da muggan idanunsa, “Ki fara tattare dukanin bayanan wannan case ɗin a
file ɗinnan, komai dake aka farashi, ki nutsu kiyi abinda ya dace”. Kaina na
jinjina masa, ya sake miƙomin hotuna guda biyu, batare da ya kalleni ba yace, “Ki
sakasu a ciki” suma amsar nai na buɗe na saka a farkon takardun ina cije lip saboda
wani mugun katsawa da marata tayi. Babu shiri na ajiyesu na kwantar da kaina jikin
tebirin ina ambaton sunan ALLAH da ɗaura hannuna na haggu bisa cikina.
Idanu Jawaad ya zuba mata na wasu sakanni, sai kuma ya ɗauke kansa, duk yanda yaso
basarwar sai ya kasa, a hankali yace, “Miemaa” shiru Bilkisu bata amsaba, bakuma ta
motsaba, ya zuba mata ido a karo na biyu, ganin taƙi ɗagowa sai ya miƙe ya zagaya
inda take. Kujerar dake kallon wadda take zaune yaja baya kaɗan ya zauna, nanma
idanunsa a kanta, dan yarasa kuma mizai mata, sunanta ya kuma kira yanzunma a
hankali.
Ƙwallan da suka cikamin ido na share sannan na ɗago kaina ina amsawa da “Na'am”
Ganin idonsa a kaina suke ya sakani maida nawa na risinar ƙasa. yace,
“Lafiya?”
Kaina na jinjina masa alamar eh babu komai, dan ko giyar wake nasha bazan iya
cemasa marata ke ciwoba, fatana kawai ya sallameni na koma.
Ƙaramin tsaki naji yayi, cikin ɗan kausasa murya yace, “K kalleni”. Ɗagowa nai na
kallesa danjin babu wasa a furucinsa, yanda ya zuba idanunsa cikin nawa bazan iya
jurewaba, naɗan risinar da nawa ina haɗiye busashshen yawun dana tattaro daga
bakina da ƙyar.
“Ni zakima ƙarya?”
Da sauri na girgiza kaina. Ya sake cewa ”Mi akai miki?”. Saboda ya barni nace,
“Kaina ke ciwo”. Shiru yay baice komaiba, hakan yasa na ɗago kaina a tunanina bani
yake kalloba. Sai dai anyi rashin sa'a idanunsa ƙyam suke a kaina. Ɗauke nawa nai
ina kumbura fuska danni banason wannan kallon takuramin yakeyi.
Huci naji yaɗan fitar kaɗan mai kama da ajiyar zuciya, yace, “Tashi kije ki
kwanta”. Kallonsa nai da mamakin maganarsa, ni ina zani na kwanta to?. Doguwar
kujerar dake rukunin kujerun office ɗin a gefe ya nunamin fuskarsa a matuƙar ɗaure
babu wasa.. Gabana ya faɗi, na kallesa cikin waro idanu da rawar baki dan nakasa
cewa komai. Harara ya zubamin, a ɗan tsawace yace, “Na fara wasa da kene?”. Saurin
girgiza kaina nayi na miƙe.
Kasancewar dama kwanciyar nake buƙata saina shiga sauke tagwayen ajiyar zuciya
lokacin dana kwanta, na takure waje ɗaya saboda azabar da nakeji, bammasan hawaye
nabin kumatunaba, kusan mintuna uku kafin ta lafamin, na buɗe idanuna a hankali na
saukesu akan Boss dake zaune saman centre table ɗin rukunin kujerar ya zubamin
idanu, saurin maidawa nai na rufe ina ƙoƙarin haɗiye kukana. Baice dani komaiba,
amma inajin yanda idanunsa ke yawo a jikina har yanzun. Yunƙurawa nai zan tashi
yace, “Koma ki kwanta”. cikin marairaice fuska nace, “Ya daina ai, zan koma
nacigaba da aikina”. Yanda yay kicin-kicin da fuska ya tilasta min komawa na kwanta
yanda yake buƙata. “Mike miki ciwo?” ya jehomin tambayar a kausashe. Bansan sanda
na tura baki gaba ba nace, “Nifa kainane kawai sir”. Bai tanka minba yamiƙe yabar
wajen, ban sake sanin mi yakeyiba saboda ciwon ya dawo. Saida ya lafamin ne na buɗe
ido naga Ummie durƙushe a gabana tanamin sannu, hannunta na kama na riƙe ina
hawaye, “Ummie ki taimakeni kiyi masa dabara mubar office ɗin nan dan ALLAH”. Kanta
ta jinjinamin tana gogen hawayen, tace, “Mararki ke ciwo ne?” da sauri na ɗaga mata
kaina ina cije baki. Nace, “Koda yaushe zai iya fitowa wlhy Ummie”. Cikin ƙara rage
murya ƙasa Ummie tace karki damu bara nai masa magana”.
Jawaad da duk ke saurarensu daga inda yake zaune ya girgiza kai kawai. Mutum ne shi
da ALLAH yayma baiwar jii, dukda ahankali suke maganar yana jiyosu batare da sunyi
tunanin hakanba. Koda Ummie ta miƙe zuwa inda yake domin ta tsarashi kamar yanda
Bilyn ta buƙata sai yace ta tafi. Babu ƙofar yimasa musu, dan haka tabi umarni ta
fice tana waigen bilyn. Waya ya ɗauka shikuma ya tura saƙo. Cigaba yay da aikinsa
kamar ya manta da Bilkisu a office ɗin, lokaci-lokaci yakan amsa waya koshi ya
kira. Kusan mintuna ashirin da tura saƙonsa aka kawo masa abinda ya buƙata, Gimba
ne ya shigo ya ajiye ledan hannunsa bayan ya gaishesa.
Sama-sama nake jin muryar gimba a office ɗin, kafin kuma naji alamar fitarsa.
Ƙamshin turaren Boss da naji a akaina ya sakani buɗe idanu, yace, “Tashi zaune”
babu musu na tashi, a raina ina murna zai barni na tafi, abinda ke cikin ledar ya
fiddo sai naga magunguna ne, batare da ya kalleniba yace, “Kinci abinci?”. A
hankali nace, “Nasha tea tun a gida”. Baice komaiba ya miƙe. Naɗan bisa da kallo
sai kuma na janye idanuna ganin ba fita zaiyi daga office ɗinba, bansan mi yakeyiba
saboda ya juyamin baya, a ɗan ƙanƙanin lokaci ya juyo ɗauke da kofi, ya zauna a
table ɗin tamkar ɗazun yana miƙomin tea ɗin daketa turiri, sai cake, yanda yay da
fuskane ya tabbatarmin babu wasa, ya miƙe yana faɗin, “minti biyar na baki kuma”.
Bance komaiba nidai sai fuska dana kumbura. Dayake yunwar nakeji kuma tea ɗin ya
haɗashi dai-dai yanda zan iyasha gashi babu suga sai gashi na shanye naci cake ɗin,
ina ajiye kofin yana dawowa wajen hannunsa ɗauke da ruwa, nidai kaina a ƙasa naƙi
kallonsa, dan dauriya kawai nakeyi kar yaga na cika raki, sai haɗiye kukan dake
tahomin nakeyi da sauri-sauri, da kansa ya ɓalla maganin ya miƙamin. Amsa nai babu
musu na zuba a baki, ya miƙamin ruwan shima, na kammala sha ya amsa yana min nuni
dana kwanta. Ban musaba dan babuma damar yin musun na koma na kwanta kamar ɗazun,
shikuma ya miƙe zaibar wajen. Bansan lokacin da harshena ya suɓuce nace, “Sir dan
ALLAH kai min addu'a a ruwa ka bani nasha, sannan ka tofamin, jinake jikina kamar
ana kunna garwashin wuta”. Cak ya tsaya, sai kuma ya juyo a hankali tamkar mai
ciwon wuya ya zuba min idanu. Lumshe nawa nai hawayen da nake maƙalewa suka silalo.
Wani irin bugu ƙirjin Jawaad yake da sauri-sauri, ga wani irin sanyi na ratsashi
daga saman kai har yatsan ƙafa tamkar wanda ake tsundumawa cikin ƙanƙara,
mafarkinsane na daren jiya yake rige-rigen dawo masa a kwaƙwalwa. Bayan gushewar
kuwwar halittu masu ban tsoro da ya samu damar yin addu'a ta koresu, sai furucin
ƙarshe na cikin mafarkin daya fito daga bakin wata murya mai amo da baisan daga ina
ta ɓulloba ita kuma, yay masa tsaye cak a zuciya yakuma kasa fashin baƙi a kai
harya iso office ɗin nan, {Ƙaddarar haɗuwar Jini a cikin jini da zai zama jini ta
tabbata, rashin gaggawa zai tabbatar da zubewar jinane, hhhhhhhhh karku manta!
Karku manta!! Karku manta!! Hhhhhhhhhhh!!!!}......... “Innalillahi wa'inna
ilaihirraji'un” ya shiga ambata lokacin da yaji gilmawar abu shuuu ta bayan
kunnensa, da dawowar maganar tamkar a yanzu ake mai ambatonta ke faɗinta,
hankalinsa ne ya dawo jikinsa. ya kalli inda bilkisu take kwance har barci ya fara
fisgarta, samun kansa yay da tsira mata idanu a zahiri, a baɗini kuma taurarin
cikin mafarkinsa ne daya koma barci bayan yayi addu'a da nafila ne suke masa
kaikawo, yay ƙoƙarin tuno furicin mahaifinsa aka taurari huɗu da sukafi kowaɗanne
haske acikin taurarin da ya gani, sai guda ɗaya shima mai tsananin haske amma ya
matsa nesa dasu sosai, ya kasa tuna komai da Abba ya faɗa masa akan taurarin, kansa
ya shiga yamutsawa cikin wani irin yanayi, a fili ya furta, “Jiya wace irin
ranace?”. “Ranar da zata zama cikin ranakun tunawa daga nan har ƙarshen numfashi”.
Bily da idanunta ke rufe har tana sauke numfashin tabbatuwar barci ta faɗa cikin
motsa labɓanta da sauti mai sanyi, badan ALLAH ya yisa mai jii ba da bazai taɓa
fahimta ba. Dukda yaji wani abu a ransa game da amsar tata sai ya tureshi da
tunanin ai a fili yay magana shima, tajisane shiyyasa ta bashi wannan amsar, to
amma abin tambaya anan miyasa ta bashi amsar a haka?. Ƙirjimsa yay wani irin
motsawa, kiran sunata ya shigayi amma ko motsi bataiba alamar barcinta yayi ƙarfi.
Ƙwaƙwalwarsa ma saita gaza tunanin komai, samun kansa yay da fara mata addu'ar data
buƙata kawai ya shiga tofa mata akan fuska, gani yay ta saki wani lallausan
murmushi tana motsa laɓɓanta, yay saurin kai kunnensa amma bayajin komai, ɗagowa
yay ya kalleta sai kuma yaga ta yamutsa fusaka ta maida fuskarta ta haɗe. Yay shiru
yana kallonta kafin ya miƙe yabar wajen.

Cikin ƙanƙanin lokaci barcin Bilkisu yay ƙarfi sosai saboda maganin na saka barci,
gashi dama bawani isashen barci ta samu a daren jiyaba, Jawaad kam ya cigaba da
ayyukansa har akai kiran sallar zuhur. Tashi yay ya shiga toilet yay alwala ya
fito, idanunsa suka sauka akan bily dake takure cikin kujera alamar sanyi takeji.
Takawa yay a hankali wajen zamansa, rigar suit ɗinsa dake jikin kujerar a rataye ya
cire ya nufeta, lulluɓa mata yay dukda bata rufe har ƙafafuba, cikin barci ta sauke
ajiyar zuciya jin ɗumi ya ratsata, ya ɗan lumshe ido ya buɗe yana girgiza kai, sai
kuma ya kalli agogo ya nufi hanyar fita da hanzari ganin zai makara salla.
Koda aka fito salla bai dawo office ɗinba ya amsa kiran da Sir Ahmad ke masa a
office ɗinsa.
★★-:-:-:-★★★-:-:-:-:-:-★★★-:-:-:-★★
Ƙarfe biyu da wasu mintuna Dad ya isa asibiti, daga airport bai zarce ko gidaba
yasa driver ya wuto dashi dan ya matsu yaga jikin mamansa, zuwa lokacin Shahudah ta
farfaɗo, sai dai daka ganta kasan tanajin jiki, tayi zuru-zuru, farar fatarta tai
jajur musamman fuskarta ma, Dad ya zauna a bakin gadon kusa da ita yana mai shafa
gashin kanta fuskarsa a ƙwaɓe tamkar zaiyi kuka dan tausayinta. “Sannu kinji
mamana, ALLAH ya baki lafiya”. Hawayene suka ziraro a kumatun Shahudah, ta kama
hannun Dad ta riƙe tana magana a hankali saboda nauyin da ƙirjinta yay mata, “Dad
bazan samu lafiyaba, mutuwa zanyi, tunda Bb baya buƙatata gara na mutu, Dad cayayfa
mun rabu kenan har abada, ya daina sona Dad, Dad mut......” saurin ɗora hannunsa
yay akan bakinta yana girgiza kansa, “Mamana bazaki mutuba, ni da kaina zan roƙesa,
ko durƙusa masa ta kama zanyi Mamana danki samu farin ciki, indai ina raye a duniya
babu ɗayanku da zai nema abu ya rasashi ko menene shi, danku kawai nake neman
arziƙi, nai miki alƙawarin saikin koma wajen Jawaad kinji, zaku sake rayuwarku ta
jin daɗi fiyema da da har ki haifamin jikoki, nidai abinda nakeso dake ki
kwantarmin da hankalinki ki samu lafiya, namiki alƙawarin daga nan ko gida bazaniba
office ɗin Jawaad zanje kinji”. Kanta ta ɗaga tana zubda hawaye, tace, “Kaje dan
ALLAH Dad, ka faɗa masa ina sonsa, idan ya barni mutuwa zanyi, wlhy namasa
alƙawarin ko a daren yau yakeso yamin ciki na haihu gobe, na kuma samin wani jibi,
ko ƴaƴa ɗarine zan haifa masa indai zamu kasance tare har abada”. Wata irin kunya
ce ta tsargama Doctor jin furucin Shahudah wai ko yau ai mata ciki ta haihu gobe, a
ransa yace anya kuwa wannan ƴa da ubane? ‘to irin wannan manya-manyan zance haka
babu risinawa’ yaɗan girgiza kansa yana mamakin yanda tarbiyyar yaran hausa fulani
keta ƙara ƙuɓucewa a hannun iyayen wannan zamanin, a ganin ko uwa mace ya dace ƴa
taji nauyin buɗe wani lafazin a gabanta inba doleba balle uba namiji, gashi ya kula
shi Dad ɗinma ko a jikinsa, saima biyema Shahudah da yake sakeyi yana lallashinta
da alƙawarta mata samun duk abinda takeso, anya kuwa wannan hanyar ɓullewace iyaye
ke ginama ƴaƴansu?, a yanzu tarbiyya da al'adun kunyar da aka sanmu dashi na
tangal-tangal ɗin ɓarewa a hannayenmu tamkar kwale-kwale a ƙaton kogi inaga ƴaƴan
dake tasowa waɗanda suke jiran amsar tarbiyya a hannun ƴaƴanmu, anya kuwa zamu
girbi abinda iyayenmu suka shuka a garemu na alkairi?......
Maganar Dad ta katsema Doctor tunaninsa, ya miƙe yana mai ranƙwafawa ya sumbaci
koshin Shahudah da kumatunta, sannan ya shafa kanta cikin sigar lallashi da nuna
tsagwaron soyayya da ƙaunar da yake mata yace, “Ki kwantar da hankalinki Mamana,
yanzun nan zanje na isar ga saƙonki ga bb'n ki kinji, ki cire komai a ranki indai
Jawaad ne kamar kin samu”. Kaita gyaɗa masa, murya a sanyaye tace, “I love you so
much my Daddyna, duniyata, farincikina”. Cikin jin daɗin kalamanta Dad ya sake
shafa kanta yana murmushi, yace, “I love you more mamana sanyin idaniyata, ki bani
awa ɗaya kacal zan dawo miki da zance mai daɗin gaske”. Kanta ta ɗaga masa tana
lumshe idanu tare da murmushi.
Dad ya matsa daga gaban gadon tare da kamo hannun Aamilah dake tsaye jikin Window
tana kallonsu, “My autana zo mana”. Baki taɗan tura gaba tana ƙoƙarin ƙwace
hannunta, tace, “Bayan bakama kulaniba sai mamanka”. Jawota yay jikinsa ya rungume
yana murmushi, “Waneni da ƙin kula autar Mom, ayi haƙuri bazan sakeba ihuyim”.
Kanta ta jinjina masa kafin ta taso daga jikinsa tana kallon fuskarsa, cikin magana
a hankali dankar Shahudah taji tace, “Dad dan ALLAH kasaka mai shegen taurin kan
nan yay sanyi, kaga sister tana cikin damuwa, son da take masa yayi yawa tausayi
take bani”. Murmushi Dad yayi ya shafa fuskarta, “Karki damu autana, insha ALLAH
komai yazo ƙarshe kinji, bara naje na dawo kafin Mom ɗinku ta dawo”. Kanta ta
jinjina masa, shikuma ya saketa ya fice.
★★★★★★
A station kuwa, bayan an fito salla Rose ce ta nufi Office ɗin Jay domin kai masa
wasu takardu, tai knocking dan batai tunanin bai dawoba, jin babu amsa kusan sau
uku saita tura ta shiga, dan sarai tasan randa yakejin wulaƙancinsa haka yakeyi,
takuma tabbatar yana kallonta ta cctv. Babu kowa a office ɗin sai ƙamshinsa, saita
shiga waige-waige, hangen kamar mutum a kwance a kujera ya sata takawa ta nufi
wajen, ƙirjinta yay masifar bugawa saboda yin tozali da fuskar bily dake barci tana
sauke numfashi a hankali tabbacin lafiya ta samu, ga rigar boss lilliɓe a jikinta.
Cikin gurɓataccen hausanta ta lailayi ashariya ta direta tana kaɗa jiki da hura
hanci, kafin takai hannu da nufin finciko bilkisu ƙasa, dan ta rantse yau sai tayi
maganin shegiyar baƙar yarinyarnan koda boss zaiyi markaɗenta ya murza a turmi
jininta ya zama mai, tsokarta da ƙashinta da fatarta su zama tunkuzar ƙuli-
ƙuli.............✍

To baza'ai tankaɗe da rairaya a gabanaba Rose nayi nana🚴🏼. Yau words dubu uku harda
ɗari uku da hansin da hida nayi yanda zaku karanta har lahadi🤭🤫🤥🤐.

Barkanmu da juma'a, kar'a manta da saka bayin ALLAH a addu'ar juma'a😥🙏🏻.

Musha weekend lafiya😍😘🚴🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭Bilyn Abdull 📚:


Page 18

...............“Wannan shine kuskure mafi girman da zaki aikata a rayuwarki inhar


hannunki ya sauka kanta!!”.
Kakkausan furuci daya karaɗe illahirin office ɗin da kunnuwan Rose kenan a
lokacin da hannunta ke gab da kaiwa jikin Bilkisu da batasan Rose ɗin na kantaba
ma, dan barci take cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, harma ta manta a inda take
kwance.
A firgice Rose ta janye hannunta tare da ɗago idanunta da juyowa domin
tabbatar da abinda take zato, ilai kuwa shine fuska a murtuke babu alamar wasa
tattare dashi balle sassauci, ya saki hannunsa dake harɗe a ƙirjinsa yana cigaba da
watsa mata wani mugun kallon daketa tsitstsinke jijiyoyin jikinta da hanjin
cikinta, “Mi kike shirin yi da?” ya faɗa muryarsa cike da tsanarta irin wadda bata
taɓa ganiba a gareshi. Da ƙyar Rose ta haɗiye ɗan yawun data tattaro a maƙoshinta,
tace, “Ni babu abinda zanyi, kawai dai na shigone na ganta anan kwance____” “Shine
zaki tada ita saboda a kanki take kwance?”. Yay saurin ƙarasa mata zancen data
ɗakko yana tsatstsareta da idanu. Fuska ta sake tsukewa cikin tsananin kishi tace,
“Ni wlhy yarinyarnan batai minba”. Wani banzan kallo sama da ƙasa yay mata ya ɗauke
kansa yana faɗin, “Saiki kasheta ai”. Kamar zatai kuka tace, “Amma boss wai miye
haɗinka da ƙwailar yarinyarnan? dako mace bata gama zamaba ma”. Tsaki yayi ya juya
zaibar wajen yana faɗin, “Duk abinda ke ranki shine tsakaninmu, kozaki hana?”.
Tamkar rose zata fasa kuka tabishi da kallo, yana zama Su Hafiz na shigowa da
sallama, hannun Aliyu ɗauke da leda mai tambarin gidan abinci, duk kallon Rose
sukai ganinta tsaye tamkar gunki tana kallon Jawaad da tamkarma baisan da itaba, ga
fuskarsa a matuƙar ɗaure alamun zuciyar na kusa, mai tsautsayi ya taɓa a fashe masa
ita. Hafiz ne ya fara janye idanunsa daga kan Rose ya sauke akan Bilkisu dake
kwance tana barcinta lulluɓe da rigar Jay, har yanzu ko motsi bataiba dukda ihun da
yayma Rose ɗazun, kafin suma su Jabeer su lura da ita. Babu wanda yace komai a
cikinsu, shi kuma Jay baiko ɗago yama kallesuba balle su saran zai tanka.
Aliyu ya matsa inda Jay yake ya ajiye ledar yana faɗin, “Ga abinci, kasa
munje munata jiranka a wajen ashe kai kanama nan ka manta damu Boss”. Ɗago ido Jay
yay fuska a yatsine ya harari Aliyu batare da yace komaiba, shi dai Aliyu zama yay
abinsa bai kulashiba, Jabeer ma yaja kujerar kusa da Aliyu ya zauna yana haɗiye
dariyarsa, dan ya lura Rose suman tsaye tayi a wajen kokuma ta samu gushewar
hankaline na wasu mintoci.
Hafiz yay guntun tsaki yana harar Rose, “Ke kuma lafiya kika wani tsaya
ƙiƙam kamar wata dogariya?”. Numfashi Rose ta kawo cikin dawowa hayyacinta, ta
watsama Hafiz harara kafin ta nufi ƙofar fita batare data tankama kowa a cikinsu
ba, jikinta sai rawa yakeyi. Tana fita Jabeer ya kwashe da dariya, duka Hafiz yakai
masa ya duƙe, Jay ya galla masa harara da faɗin, “Dilla malam miye haka?”. “Me nayi
ni?” cewar Jabeer dake rama harar da Jay yay masa, ya cigaba da faɗin, “Kai ka dace
da wannan tambayar baniba boss, sai neman haukatar da yaran mutane kake kana wani
cijewa, gwara idan son yarinyarnan kake kafito ka sanarma duniya ka kuma shiga
cikin ƴan takara ko Rose ta dawo hankalinta, kuma ka kwana da sanin Qaseem son
yarinyarnan yake, yasin ka tsaya kallon ruwa ƙwaɗone zaima ƙafa, saboda gida ɗaya
suke kwana suna tashi, dan a ruwa kake kusa da kada malam”. A fusace Jay da dama
kaɗan yake jira ya miƙe, ƙofa ya nunama Jabeer yana huci, “Tashi ka fita a office
ɗinan Jabeer kafin nama rashin mutuncin da bazaka taɓa mantawaba, banason wasan
banza kaima ka sani ko”. Miƙewa Jabeer yay yana taɓe baki, yasan fitar tasa shine
mafi alkairi dan Jawaad a wuya yake, shikuma idan yay zuciyar da har ɓacinta ya
fito a muryarsa kai nesa dashi yafi komai alkairi, idan ya huce da kansa zai nemeka
yay maka bayani harma daban haƙuri idan yasan yamaka abinda bai daceba. Ficewa
Jabeer yay yana murmushi da girgiza kai. Jawaad ya koma ya zauna yana ƙwafa, sai
kuma ya miƙe ya nufi toilet yabar su Hafiz dake binsa da kallo.
A sanyaye Aliyu yace, “Sonta yake amma kamar shima bai fahi

mci hakaba Hafiz”. Cikin damuwa Hafiz ya bama Aliyu amsa da cewar, “Na daɗe da
fahimtar haka Aliy, ba fahimtace baiyiba kuma shima, sarƙaƙiyar dake cikin
al'amarin yarinyarne yake sakashi ƙoƙarin haɗiyewa, sai dai kuskuren daya kasa
tunawa shine, ba kowanne irin SO bane yake haɗiyuwa lokacin da ake buƙata, wani
koda ka korashi da ruwan haƙuri dana juriya a maƙoshi yake tsayawa ya tsaida
dukkanin muhimman al'amuranka wucewa cikin zuciya da ƙwaƙwalwa, ni kaina na waiga
ta kowacce kusurwa bashi da wani magoyin baya akan al'amarin yarinyarnan sai sashe
ɗaya, shi kuma baida wani ƙarfin iko akan hakan”. ajiyar zuciya Aliyu ya sauke mai
ƙarfi yana dafe kansa, sai kuma ya ɗago ya kalli Hafiz dake kallon inda Bilkisu
take, yace, “Minene mafita yanzu Hafiz? Jay yana buƙatar mace a kusa dashi sosai ta
kowanne ɓangarema kuwa, yarinyarnan kuma tanada mafi yawan nagartar data dace ta
zame masa abokiyar rayuwa, mizai hana mu bashi shawarar ya sanar mata ABINDA KE
RANSA”. Numfashi Hafiz ya sauke yay shiru na wasu sakkani yana nazari da bubbuga
yatsansa akan baki, ya kalli Aliyu yana kaɗa kai, “Aliyu ita kanta yarinyarfa
bamuda wani ƙwarin gwiwar samun goyon bayanta, dan tayi nisa wajen son ɗan uwanta,
sannan bana tunanin zata iya barin Qaseem kodan halaccin mahaifinsa a rayuwarta ta
ɗauki waninsa, shiyyasa nace maka akwai sarƙaƙiya takowacce kusurwa, Kasan Jabeer
yanada fiƙira akan irin waɗannan al'amuran, sai dai shi matsalarsa saka wasa a
dukkan lamarinsa, bansan lokacin da zai dinga kallon abu mai muhimmanci a muhallin
daya dace ba, amma mubari zuwa weekend sai muyi zamana musamman akan maganar”.
Cikin gamsuwa Aliyu yace, “Shikenan ALLAH ya kaimu”. Fitowar Jay daga bayi fuskarsa
jiƙe da ruwa ya sakasu yin shiru, babu wanda yace dashi komai yazo ya zauna a
kujerarsa, Hafiz ne ya fara miƙewa yana faɗin, “Bara muje zuwa anjima ma dawo muyi
maganar idan ka samu lokaci”. Kai kawai jay ya ɗaga amma baice uffanba.

Fitar su Aliyu babu jimawa Dad ya iso station ɗin su Jawaad, ba'a bashi damar
shigaba saida ya kira Jawaad a waya, tamkarma Jawaad bazai ɗauka wayarba sai wani
tunani yazo masa a rai, hakan yasa bayan wayar ta katse yabi bayan kiran Dad shi ya
kirashi. Koda ya sanarmasa yana gate sosai mamaki ya kasheshi, amma sai yabama
securitys ɗin umarnin a rako Dad office ɗinsa, shaf ya manta da Bilkisu dake kwance
tana barci.
Bai nunama Dad komaiba yay masa tarba ta mutuntawa, bayan sun gaisa ya
bashi ruwa Dad ya fara magana cikin karyar da murya. “Jawaad”. Yanda ya kira
sunansane ya sakashi ɗaga kai ya kallesa, ya amsa da “Na'am”. “Jawaad wajenka nazo
gwiwoyina a ƙasa da tarin magiya da roƙon da idan kamawa tai na duƙa a gabanka
zanyi hakan. Dan ALLAH ka tausayama Mamana ka dubi al'amarinta, bazan musamaka ba
akan ita mai laifice damu kanmu, sai dai ince dan ALLAH mu manta da baya domin ta
shuɗe, wlhy ina mai tabbatar maka duk wautar dake kan Mamana a yanzu babu ita, dan
ta gurzu da horonka, ka tausayamin kodan ciwon dake tare da ita na hawan jini da
likita ya sanar mana, badan tanada sauran shan ruwaba faɗuwar da tai jiya a gidanku
likita ya tabbatar mana da sai ta kamu da paralysis, wlhy yarinyarnan tana sonka
fiye da yanda kake zato ko tsammani........” Jawaad da kansa ke ƙasa yace, “Kayi
haƙuri Dad ban katsekaba, da Huda na min irin wannan son da bazata guji haɗa zuri'a
daniba, yakamata mu fahimci Hudah ta huce sahun ƙuruciya yanzun, bai kamata ace duk
abinda yazo zuciyarta tai tunanin aikatashi shine mafi dai-dai a rayuwarta ba,
sannan kuma abinda takeso ace dole saita samesa, dolene duk inda akwai take wataran
za'a samu babu. batason haihuwa yanzun miyasa ta yarda tai aure? Bata shirya zama
kamar kowacce macen aureba miyasa ta zaɓi muyi aure? A ganina da sai ta bari sai
lokacin da duk ta shirya waɗan nan, Dady ni bahaushene, uwata bahaushiyace,
mahaifina bahaushene, dukkanin dangina hausawane sai fulani, addinina shine
musulunci, addinin iyayena da dangina duk musuluncine, tayaya Hudah take tunanin
zan biye mata na ajiye dokokin UBANGIJINA na ɗauki son zuciyarta?, tayaya take
tunani zan ajiye al'adun yarena dana tashi

cikinsu na ɗauki ra'ayinta data aro a wajen wasu?, ai duk duniyar da zan shiga dady
ina alfahari da abubuwannan guda biyu, YARENA ADDININAH, banajin kunyar nuna kaina
a gaban kowanne mahaluki da tambari kasancewata musulmi, dan rahamace babba a
gareni da wofantar da ita babbar asarace da bata da madadi duniya da lahira, a duk
duniyar dana shiga zan kira kaina bahaushe, koda wanda nake tare dashi baitaɓa jin
sunan yaren hausa ba ma zan tabbatar masa da yaren ya fara saninsa a lokacin kuma
nai masa AlFAHARI dashi saboda yarena ne, shine harshen da UBANGIJINA yafi ganin ya
cancanta na fito a ciki ya zama abin maganata, to mizaisa na ƙyamacesa saboda yaren
wasu da ko za'a kashesuma basusan nawa ba, wlhy Dady idan ka cire LARABCI daya
kasance yaren MANZON ALLAH (S.A.W) to babu wani yare da yakai muhimmancin dazan
fifitashi sama da yarena na HAUSA, duk yaren da kaji yafita a harshena saɓanin
LARABCI da HAUSA to inayinsane saboda lalurar mu'amulla da mutane badan ina
kallonsa a saman nawaba. Kayi haƙuri Dad mubar wannan maganar kawai, ku tayamu
addu'ar ALLAH ya bama kowa dai-dai da ra'ayinsa ni da ita, dan nikam Hudah tafi
ƙarfina”.
Jikin Dad duk yayi sanyi da maganganun Jawaad, dan kuwa dukkan abinda ya
lissafa matsalace mai tushe da shima yanada kaso mafi yawa wajen ƙirƙirarta ga
ahalinsa, to amma yanzu bata wannan akeba, matsalar mamansa itace gaba da komai. Ya
nisa cikin girgiza kai da raunana murya fiye da farko yace, “A karo na babu adadi
Jawaad zan kuma cewa kayi haƙuri, ina mai tabbatar maka a yanzu zaka sami mamana a
yanda kakeso kuma kake buƙata”.
Shiru Jawaad yay yana mai kallon Dad cike da tausayi, dan yasan shine
ginshiƙin ruguza gidansa wajen sakaci, gashi a yanzu abinda ya raina yayi gawurtar
da al'amarinsa yafi ƙarfinsa amma shi baima fahimtaba, cike da girmamawa yace,
“Kayi haƙuri Dad zanzo gida na sameka idan na tashi aiki insha ALLAH, wannan
maganar bata nan baceba, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. Shiru Dad yay ya
kasa tashi, dan gani yake tamkar Jay yawo da hankali zai masa, saboda yasan taurin
kan yaron da kafiya idan ya juyama abu baya, tun yana yaro ya fahimci wannan
shegiyar halayyar tattare dashi, shiko buƙatar ƴaƴansa bai haɗata da komai a wannan
duniyar ba. A bazata Jawaad kawai sai yaga Dad tsuggunne gabansa yana faɗin,
“Jawaad dan girman ALLAH karka wofantar da maganar n....” da sauri Jawaad ya miƙe
jikinsa har rawa yake ya tanƙwaɓe wayarsa dake kan desk ɗinsa ta faɗi ƙasa, baibi
takantaba ya kama hannun Dad yana faɗin, “Ya ilahi, Dad dan ALLAH ka tashi, minene
kakeyi haka? Wlhy na tabbatar maka zanzo muyi magana a gida” da ƙyar Jawaad ya samu
Dad ya tashi tsaye, gaba ɗaya al'amarin yana neman birkita masa ƙwaƙwalwa, wane
irin ubane Dad? Wane irin kalar mugun so ne wannan yakema ƴaƴansa? Abin yayi yawa
matuƙa, kowanne iyaye nason ƴaƴansu amma na Dad yana neman wuce hankali. Shidai
Jawaad sai ya koma lallashin Dad ɗin ya samu suka fita yay masa rakkiya ya tafi,
gaba ɗaya kansa a cinkushe yake, harma ya fara masa wani masiffen ciwo tacan ciki.

Koda ya dawo office da shashshekar kukan Bilkisu ya fara cin karo, tun
shigowar Dad ta farka, dukkan maganganun da Dad sukai da Jawaad kaf ta jisu, takuma
fahimci kaso mafi yawa na dangane da matsalar data raba aunty Shahudah da mijinta,
Dad ya bata tausayi matuƙa gaya yau, babban mutum kamarsa da ya haifi ɗan da yafi
Jawaad amma yake tsugunawa a gabansa domin kawai farin cikin ƴarsa, wanne irin
makahon so ne haka Uncle ɗin nata kema zuri'arsa?, a ganinta lokaci yayi da zata
bada gudunmawarta ga Dad ko ƴar kaɗance......
Jawaad tsaye yay a ƙofa hannunsa duka biyu cikin aljihun wandonsa ya zuba
mata ido, ransa a dagule yake, sannan ita kuma baisan ma'anar kukan nataba balle
inda ya dosa, hakanne ya sakashi jan wani shegen tsaki ya cigaba da takowa cikin
office ɗin batare daya sake kallonta ba. Har cikin zuciya da ruhi tsakinsa ya taɓa
Bily, hakan ya sake jawo gudun ruwan hawayenta babu ƙaƙƙautawa, ta cigaba da
kukanta na tsawon wasu mintuna shi kuma yana cigaba da aikinsa tamkarma baisan da
zamanta a office ɗinba. Dan

kanta taji kukan ya isheta ta share hawayenta ta tashi ɗauke da rigarsa a hannu ta
nufesa. A tsorace zuciyarta take, amma wani sashe na bata ƙwarin gwiwa akan abinda
take shirin yi. Gaban Jawaad taje ta durƙusa kanta a ƙasa. Jawaad da yaƙi ɗagowa ya
kalleta dukda yanajin motsinta ya cigaba da aikinsa.
Karan farko a rayuwar Bilkisu data shirya ambaton sunan Jay a harshenta
harma da ƙarfin halin furtawa a gabansa, sai dai tayi imanin bazata iya ambaton
sunansa da kallonsaba a yau, dan haka ta duƙar da kanta tana durƙushe akan
gwiwoyinta, rigarsa riƙe a hannunta ajiye akan cinya, tace, “Yah Jawaad!.…….”
Cak Jay dake rubutu a wasu takardu ya tsaya tamkar wanda aka tsaida da remote,
shi bai kalleta ba, kuma bai cigaba da abinda yakeba, saima lumshe idanunsa da yay
yana sauraren sarawar da kansa ke masa da harbawar jijiyoyinsa harma da gudun
jininsa daya tsinke a lokaci ɗaya. Bilkisu daba kallonsa takeba ta cigaba da faɗin
“Dan girman ALLAH Yah Jawaad kayi haƙuri karka wofantar da magiyar Dadynmu, wlhy ni
shaidace aunty Shahudah na matuƙar sonka, duk da bansan ainahin matsalarkuba inada
yaƙinin zaka iya amfani da son da take maka ka canjata, matsalar da duk kake
ganinta da ita ƙirƙirarriyar matsalace dakeda tushe a gareta tun tana tsumman
haihuwa, ba laifinta bane ita kaɗai haka ta tashi taga kanta itama, bata isa
banbance baƙi ko fariba a buƙatar jin zafi saboda an nuna mata hakan shine dai-dai
da rayuwarta kuma nasararta, Mahaifina yasha faɗamin, {Bilkisu, aduk lokacin da
zama ya haɗaki da mutane ki fara nutsuwa ki fuskanci halayyarsu da tsarin rayuwar
da suka rayu, dan babu wata zuciya dake gogayya da ƴar uwarta akan hallayya iri
ɗaya, lokacin da k tarbiyyarki ta baki dai-dai a wajen wani shi kuskurene, abinda
yake kuskure a yaƙininki a wajen wani dai-dai ne, idan har kika kasance cikin
mutane masu fahimtar ilimin duniya ina mai tabbatar miki zaki zama nasararki sama
data kowa koda ace ke kaɗai kike kallon kanki a wannan nasarar, daga lokacinda
ilimin sanin hallayar ɗan adam ya dawo tafin hannunki inada yaƙinin zaki gyara
ɓarna da yawa, domin zakibi mutum da halinsa ki ɗorashi akan hanyarki mai nagarta
batare dashi yasan ya afkaba ma, munzo zamanin da halin ɗan adam dashi ake cinsa da
yaƙi bada takobiba, zauna dame ƙinki da zuciya ɗaya, ƙyautata masa kuma da yaƙinin
neman sakamo wajen mai badawa ba ga shiba, koda shi a kullum zai kasance mai
bibiyar bayanki da sharri, karki zama mai damuwa da zama gwana a duniya, dan wani
lokacin nasarar duniya faɗuwace gamai ita, koda idanun duniya na kallonsa a saman
kowa, mai kuma sa'a fiye da kowa}, Yah Jawaad ba soyayyarka kawai aunty Shahudah ke
buƙataba, a yanzu tafi buƙatar ka jingina da soyayyar tata ka ɗorata a hanyar tsira
domin kaikaɗaine zata iya saurara, saboda girmamaka a matsayin gwaninta, na yarda
dakai ta kowanne fanni koda banida ilimin sanin ɓoyayyun halayenka, ina sake
roƙonka a matsayin Yaya ba shugabana a wajen aikiba, dan ALLAH ka ceto rayukan
bayin da zukatansu suke a rufe ruf akan sanin gaskiya da makomar bin hanyarta,
yahudanci da nasaranci duhune, wannan duhun kuma shike mamaye da jama'ar gidanmu,
sai dai hasken ruɗani da gushewar banbance mai tsafta ya hana ijiyarsu ganin
kowanne tsani sai wanda suka hau, kullum fatana ALLAH ya kawo musu drivern dazai
fidda rayukansu a kwale-kwale saboda ni nayi ƙanƙanta ƙarancin matsayin yin wannan
jagorancin, kaiko inada yaƙinin zaka iya, domin son da sukema aunty Shahudah
gyaruwarta tamkar gyaruwar kaso mafi yawane daga ahalin gidan, ciki kuwa harda Dad
da tuni ya fahimci gaskiya, sai dai ƙarfin riƙonta a garesa da tafi ya hanashi
nunawa ko a fuska, ya gwammaci ya haɗiyeta a rai yacigaba da rainon ƴaƴansa tamkar
ƴaƴan agwagi da basa bin uwa sai dai ita ta bisu” na ɗago kai a karo na farko tunda
na fara maganar na kallesa, sai dai a mamakinna shi ba ni yake kalloba, gashi yayi
kicin-kicin da fuska irin yanda ban taɓa ganiba a tun sanina dashi, na raya a raina
saitna dire abinda na fara, dan haka nace, “Dan ALLAH Yaya Jawaad ka yarda a maida
aurenku da aunty Shahudah a karo na b....i...y...u.”
A yanda y

a juyo ya sauke rikitattun idanunsa a kainane yay masifar hargitsani na ƙarasa


kalmar ƙarshe da ɗai-ɗai.............✍

Tab wlhy badaniba nayi nan, idan ya huce na dawo na ƙarasa muku yanda aka ƙare🚴🏼🚴
🏼🚴🏼🚴🏼🚴🏼kuma bily addu'ar fitowa lafiya itama, dan inaga ba'a taɓa karyata ba😂🤣.

Barkanmu da dawowa, inafatan kowa yayi weekend cikin ƙoshin lafiya?.😍😍[12/1/2020,


12:26 PM] HASNA ✍🏻
: Bilyn Abdull :
Telegram link group ɗinmu kenan, dan wasu sunata tambaya cewa ya zasu shiga, indai
kana tele to kawai ka antaya MASARAUTAR BILYN ABDULL tanan.

https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g

Page 19

................Idanunsa sunyi masifar kaɗawa sunyi jajur, batare da yace dani


komaiba yaymin nuni da ƙofa alamar in fita, kasa koda motsi nayi, sai hawaye dake
cigaba da ambaliya a kumatuna tamkar an buɗe fanfo.
Cikin matuƙar kaushin murya da tsawa na tsinkayi furucinsa cikin
kunnuwana, “Miemaa! niɗin sa'anki ne ko?!”. Da sauri na shiga girgiza masa kai
jikina na rawa saboda harga ALLAH na matuƙar tsorata da yanayinsa. Ya sake faɗin,
“Tashi kifita a office ɗinan kafin naimiki duk abinda yazomin kai, Yanzunan har
idonki yakai tsaurin kallona ki faɗamin abinda ya dace dani?!, ki fitar min anan
kona sauya miki kamanni!!”. Kuka na sake fashewa dashi ina saurin jan jikina nai
baya gudun karya makeni, dan harga ALLAH tausayin Dad na tsaga dukkan jijiyoyin
jikina harda aunty Shahudah, na tabbatar samun boss ga aunty Shahudah shine farin
cikin gidanmu, Hawayen dake ziraromin na share tare da faɗin “Kayi haƙuri dan
ALLAH, bazan sakeba”. Cikin faɗan dana rasa abinda ya fusatashi irin haka yace.....
“Baki jiniba ko?!” yay maganar a hasale yana tasowa kaina, Baya na shiga jan
gwiwoyina batare dana tashiba, matsanancin fushin dana gani akan fuskarsa ya bani
tsoro matuƙa, bantaɓa tunanin yanada zafin zuciya irin hakaba, ya nunani da
ɗanyatsa yana faɗin, “Badai kece kika buƙata da kanki ba, to duk abinda ya biyo
baya kiyi kuka da kanki ba daniba Miemaa, zan aureta tamkar yanda kike buƙata, amma
wlhy ko sau ɗaya kikai ƙorafin hakan wataran saina hukuntaki da mafi girman
hukunci, indai Hudah ce gaki ga tanan shashashar banza”. Ya ƙare maganar yana
ranƙwafowa kaina ya fisge rigarsa dake hannuna ya fice daga office ɗin”.
Ɗif naji komai na ya ɗauke wuta yabar aiki, sam narasa awane mizani zan
ɗora ruɗaɗɗun kalamansa marasa tushe balle makama, man kaina gaba ɗaya ya tsiyaye,
babu wata jijiya dake ɗaukar saƙon ƙwaƙwalwa zuwa zuciya dake aiki a jikina har
tsahon wasu mintuna da naji saukar abu mai ɗumi a jikina. Zumbur na miƙe domin
samun dawowar hankalina daya gushe na wucin gadi. Ban sami damar gama tattaro
abinda ya shuɗeba idona ya sauka akan Oga Jabeer dake bakin ƙofa a tsaye yana
kallona. murmushi yaymin kafin ya ƙarasa shigowa office ɗin, “Tashi ki shiga toilet
ki wanke fuskarki kinji” Ya faɗa yanamin nuni da hannu. Ban musa masaba na miƙe,
dan koba komai ina buƙatar duba halin da nake a ciki.
Bani da isashen lokacin fashin baƙi akan ruɗaɗɗun kalamansa, dan kaina
tsaye ina dangantasune kawai da rufewar ido ga mamallakin furtasu, to danmima
zuciyata kesan rikitani da hasashen abinda bazai taɓa zama hakaba, na ƙurama kaina
ido a madubin dake cikin toilet ɗin ina mai tariyo kalaman dallah-dallah yanda zasu
bani fassarar da nake buƙata, “{Duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki badaniba
Miemaa, zan aureta tamkar yanda kike buƙata, amma wlhy ko sau ɗaya kikai ƙorafin
hakan wataran saina hukuntaki da mafi girman hukunci, indai Hudah ce gaki ga tanan
shashashar banza}”. ‘Kenan yana nufin inhar aunty Shahudah ta sake koma masa da
halinta na baya akwai hannuna wajen cutar dashi? Kuma nizai kuhunta ba itaba? To
miyasa? Miyasa zan zama laifi akan ƙoƙarin ganin na inganta auren sunna, na haɗa
zukata biyu masu ƙaunar junansu, na tabbata shima yana sonta kawai halayyarta yake
ƙyamata, to miyasa ni laifin zai tattara a kaina kuma?’ “Saboda kalamanki ne suka
tursasashi yarda ta koma” wata zuciya ta ayyanamin daga can ƙasan rai, ‘To miyasa
zai amince da abinda bai zama wajibiba? Ni shawara na bashi da nuna masa ƙwaɗayin
samun lada ai ba tilasba, sannan na ceto zuciyar Dad daga ɓacin ran tashin hankalin
gudan jininsa, kenan hakan yana nufin kuskure nayi?, ni wacece da har zai amshi
roƙona ya wajabtama kansa?, nasake tambayar kaina hawaye na silalomin. Nima kaina
sai yanzu naga ƙarfin halina da wautata akan taryarsa, banyi tsammanin zan iya
hakanba koda a cikin mafarkine kuwa, zan cigaba da roƙon ALLAH ya hana faruwar mat
salar da yake hangowar, insha ALLAHU lafiya zasu zauna abinsu. Haƙura nai da
tunanin na kimtsa jikina da tissue ɗin dana gani a toilet ɗin dan inada tabbacin
zai riƙeni har zuwa a tashi insha ALLAHU, na sake ɗauraye fuskata na fito. Zaune na
iske oga Jabeer, yana ganina yay ƙaramar dariya da faɗin, “Anya maman nan tamu ba
raguwa baceba?” murmushin da ban niyyaba ya suɓucemin, na girgiza masa kai ina
faɗin “a'a sir”. Dariyar ya sakeyi da cewar, “To ALLAH yasa, yanzu daga nan sai ina
kuma?”. Nace, “Zan koma Office ne, akwai aikin da boss ma ya sani tun ranar waccan
monday ɗin ban kammalaba”. Ya miƙe yana faɗin, “To masha ALLAH, nima bara na koma
office, amma daga yau idan kikaga Jay a irin wannan matsanancin fushin ki daina
masa naci akan koma wane irin maganace, dan idan yay fushi irin haka akwai matsala,
ALLAH ne ya taimakeki ya zaɓi ya fita yabar miki office ɗin, amma dabai fitanba ke
kuma kika cigaba da taurinkan kin fita komai zai iya biyo baya, ki kiyaye kinji,
boss ya wuce duk yanda kike zatonsa, mutumne murɗaɗɗe mai wahalar sha'ani matuƙa,
idan yaso kaji dadinsa baka taɓa fahimtar tsaurinsa, idan baiso hakanba wahala
zakasha ta gaske”.
Nace, “Insha Allah zan kiyaye nagode sosai”.
“Hakan shine dai-dai, ALLAH ya kiyaye gaba”.
Tare muka fita, shi ya nufi office nikuma na sauka ƙasa, harna fara tafiya sai
naji ina buƙatar ganin yah Qaseem, dan tunda mukazo yau ban gansaba kuma bai
nemeniba, ko a waya.
Nayi knocking kusan sau uku babu amsa, hakan yasani tura ƙofar office ɗin a
hankali na shiga, zaune na sameshi a kujerarsa, ya kwantar da bayansa jikinta
idanunsa a lumshe, na sake maimaita sallamar tawa idona kafe a kansa. A hankali ya
buɗe idonu yana kallona, sai kuma ya tsashi zaune sosai yana murmushi damin alamar
nazo da hannu. Takawa nai a hankali zuwa garesa, na zauna a ɗaya daga kujerar gaban
tebirinsa idona har yanzu a kansa. Wani murmushin ya sakemin, kafin ya buɗe baki a
hankali cikin sanyin murya yace, “Har yanzu jikin dai bilkisu?”. “A'a Yah Qaseem
naji sauƙi, mike damunka? Tunda muka baro gida baka da walwala, gashi har yanzu ina
ganinta a saman fuskarka kuma, mike faruwane?”.
“Humm” ya faɗa yana cije baki, kafin yace, “Babu komai, kawai dai banajin
ƙarfin jikinane”. Numfashi na sauke a hankali fuskata na nuna tausayinsa, nace, “To
ko zamu tafi gida kaga likita”. Nanma kansa ya girgiza mani, cikin kauda maganar
yace, “Kinci abinci ko?”. Kaina kawai na iya ɗaga masa, dan jinai dukna damu da
halin da yake a ciki, shiru mukai na wasu mintuna kafin na miƙe nace, “bara na wuce
dama leƙoka nayi dan naji shiru”.
Baice komaiba saida na doshi hanyar fita daga office ɗin, “Ki ƙoƙarin gama
abinda kikeyi, da anyi la'asar zamu wuce dan yanzu Mom ta kirani jikin Shahudah ya
sake rikicewa”. Sosai naji gabana ya faɗi, na kaɗa masa kai kawai ina haɗiye
ƙwallar data cika mani ido, “ALLAH ya bata lafiya” “Amin”. ya amsa mini akan laɓɓa.

★★★★★★★

A ɓangaren Jay kuwa gaba ɗaya yarasa gane kansa, haka kawai ya
tsinci zuciyarsa da fushi mai tsanani, koda ya fita daga station rasa ina zai dosa
yayi, yata zagaye gari daga wannan titi zuwa wannan har ƙarfe biyar na yamma,
sallar la'asar kawai ya tsaya yayi da lokacinta yayi, ganin yamma tayi saiya juya
kan motar Jabeer daya ɗakko daga office ya nufi gidan Alhaji baba kakansa.
A ƙofar gida ya iske Alhaji baba da tsaaffin anguwar a bishiyar dalbejiyar
dake ƙofar gidansa, inda yake zama duk yamma yasha iska koda hantsi, sai yazam
tsaffin dake anguwa sukanzo suma su zauna suyita hira, a kusa dasu yay parking,
yaja kusan mintuna uku bai fito a motarba, tsoffin nata magana akan wanene? Amma
bai tankaba balle ya fita, shiko Alhaji baba bai tankaba, dan yaji a ransa Jawaad
ne dukda yasan ba motarsa bace, kuma glass ɗin motar nada duhu ba'a ganin na ciki.
Sai da ya mula dan kansa ya buɗe ya fito. Alhaji Baba ya bisa da kallo kawai
batare da yace komaiba. Jawaad ya rissina ya gaida tsoffin kafin ya miƙe ya nufi
hanyar gate ɗin gidan batare da yacema Alhaji baba komaiba. A falo ya zube saman
doguwar kujera ko takalmi bai cir

eba, ya lumshe idanunsa yana maijin kewar iyayensa na tsarga masa da zafi-zafi, a
yau babu abinda yake tsananin buƙata sama da ɗumin mahaifiyarsa, burinsa kawai ya
ɗora kansa a cinyarta tana shafawa da tambayar damuwarsa, shiko ya juye mata duk
abinda ke ransa ta bashi shawara da masa addu'a. Sai dai kuma gashi ƙaddara ta daɗe
da hana hakan a jerin farin cikin rayuwarsa, ƙilama tuna tabar masa duniyar bai
saniba, kokuma ta fita hayyacinta fiye da yanda zata iya tuna ita wacecema balle
abinda shi ta haifa, amma duk yanda take yanason abinsa, zaiyi farin ciki da maraba
da ganinta a duk yanda take.
Buɗe idanunsa yay saboda saukar hannun Alhaji baba a saman fuskarsa yana
share masa ƙwalla, Alhaji baba yay murmushi cikin zolaya yace, “Kullum kai saika
kwaso ragwantakarka ka kawomin gida, ina namijin dake filin daga ina kuka
Muhammadu”. Murmushi Jay yayi tareda lumshe ido yana rungume hannun kakan nasa a
cikin wuyansa, baidaice komaiba, hakan yasa Alhaji baba ɗaga kansa ya zauna sannan
ya maida kan saman cinyarsa ya ɗora, ahankali ya shiga shafa kan Jay dake cinyar
tasa, hannunsa ɗaya kuma na shafa fuskarsa da ƙananun gashin saje da bai askeba ke
kwance a jiki. Shiru sukai gaba ɗaya, Jawaad yay lamo a jikin kakansa yana sauke
numfashi a hankali, tuni kaso mafi yawa na damuwarsa yaji ya gudu, tsahon lokaci
suka ɗauka a haka babu wanda yay magana, ganin lokacin salla ya gabato Alhaji baba
ya shafa fuskar Jay yana faɗin, “Muhammadu tashi kaje kai wanka kayo alwala muje
masallaci”. Buɗe idanu Jawaad yay a hankali, sun ƙanƙance sosai alamar yanajin
barci, tashi yay ya nufi ɗakin kakansa dan baida matsalar kaya tunda yana ajiyewa
anan. Cike da tausayawa Alhaji baba ya bisa da kallo, yana tsananin son jikan nasa
tilo namiji da tausayinsa matuƙa, a kullum baya gazawa da yimasa addu'ar kariya
daga dukkanin abin ƙi da maƙiya.

Ana ƙoƙarin shiga sallah Jawaad ya fito a gaggauce cikin jallabiya


ruwan siminti, sai ƙamshin turaren kakansa yake mai sanyin daɗi, tare suka tafi
massalaci dan Alhaji Baba yayi alwala a toilet ɗin falo. Koda aka idar sai sukai
zamansu acan har isha'i, bayan sun fitone Alhaji baba yay sallama da mutane da
neman gafara ga wanda ya ɓatamawa bisaga al'adarsa, dan acewarsa bai zama lallai
yana cikin jerin masu tashi suga safiyar gobe ba, shiyyasa duk bayan kowacce sallar
isha'i yakanyi sallama da maƙwaftansa da neman gafararsu kafin ya shige gida. Sun
iske Nabeelah ta kawo masa abinci kamar kullum, tunda ta gaida Jay sau ɗaya ya amsa
yay kwanciyarsa a doguwar kujera, sai hira suke ita da Alhaji Baba, zuwa takwas da
rabi tai musu sallama ta tafi dan tare suke da driver dama. Tana fita Jawaad ya
sakko ya shiga buɗe kulolin da aka jero cikin kwandon mai ƙyau daga gidan Ummah,
tuwone kamar kullum dare da Alhaji baba ya wajabtama kansa, jay ya miƙe zuwa kicin
ya ɗakko filet da cokali, tuwon alkamar ya dawo ya ɗiba da miyar ɗanyar kuɓewa,
shidai Alhaji baba nata tsokanarsa da gwauro kafi tuzuru. Wani ya tanka wani yay
shiru, sai kuma a hankali ya saki jikinsa sukai hira sosai kamar yanda Alhaji baba
ya buƙata, cikin hikima kuma yake masa nasiha, sai wajen sha ɗaya suka kwanta, dan
Jay yace anan zai kwana yau, da yayi sallar asuba sai ya wuce gida.

★★★★★★

Ƙarfe huɗu da rabi muka bar office, daga nan asibiti muka nufa, mun
iske jikin aunty Shahudah kan babu daɗi, dan yanzunma dai saida tasha allurar
barci. Anan muka zauna har magriba saboda kowa yana nan sannan muka tafi kamar
yanda Dad ya bamu umarni. Har zuwa yanzun dai Yah Qaseem bashi da wata walwala,
muna isa gida kuma kowa yay ɗakinsa, naji haushin ganin ɗakina kaca-kaca, yanda
Aunty Aamilah ta tashi haka ta barminshi uwa turken jakai, gadon na fara gyarawa
nai shara sannan na shiga wanka, dama gaba ɗaya a takure nake, saidai maganin da
boss ya bani ya mugun taimaka mani, dan jina nake sakayau babu ciwon marar sai
abinda ba'a rasaba. Kamar yanda na saba har alwala saida na ɗaura dukda ina fashin
salla, sannan na fito nai shirin barci, gado na haye na buɗe data, dan munada
meeting dasu Ummie akan bikin Nazifa, munyi nisa a firarmu

sosai Nazifa tai wata maganar data saka zuciyata bugawa lokaci guda, “Sisters wlhy
akwai matsala, ko kunsan a daren jiya anyima jikar marka mai aikinmu fyaɗe, kuma
kamar dai namu ne itama saida aka bugar da ita”. Ina gama karanta abinda Nazifa ta
rubuta na saki wayar a kan gado jikina na wata irin rawa, a wani irin firgici
maiban tsoro na tsinci kaina a ciki, na shiga waige-waige a cikin ɗakin tamkar mai
tsoron ganin wani abu, a wani irin matsanancin ihu na shiga faɗin, “Ya isa!! Nace
ya isa!!! Ya isa haka nan Pleaseeeeeee” na ƙarashe faɗa da sanyin murya ina fashewa
da kuka, Aamilah Da Dad ne sukai rige-rigen shigowa ɗakin saboda jiyo sambatun
Bilkisu.
Dad ya riƙo hannunta data tattare bedsheet ta matse a ciki yana faɗin,
“Daughter! K daughter miya faru??”. Bilkisu ta kuma fashewa da kuka tana kallon Dad
dake riƙe da hannunta, Aamilah a gefensa, “Dad dan ALLAH kuce dasu ya isa haka, su
bari hakanan” ta cije baki tana zazzaro idanu cikin ficewar hayyaci ta fisge
hannunta ta tashi zaune a kan gadon, ta bubbugashi da ƙarfi na alamun ɗaukar
alwashi, kafin tacigaba da magana cikin kaushin murya, “Wlhy wlhy Dad, inhar basu
dainaba, ni da hannuna saina kakkashesu, gunduwa-gunduwa zanyi da namansu naba
karnukan office ɗinmu su cinye, kamar yanda suke bibiyarmu wlhy nima zan cigaba da
bibiyarsu, subar ganina mace, duk mai hannu a ciki sai ya shiga uku a hannuna, wlhy
halakashi zanyi Dad, saina halakashi” ta ƙare maganar da fashewa da kuka tana
faɗawa jikin Aamilah.
Sam Dad bai fahimci komai daga zantukan Bilkisu ba dake fita a murɗe,
yama fara tunanin yarinyarnan ko aljanune da ita, jiba jiya yanda suka bashi
labarin an basu tsoro a gidan, kuma ita tafi kowa firgita da shiga ruɗani, ahankali
ya juya ga ƙofa saboda jin motsi, Salman ne da Qaseem, Qaseem ya jiƙe sharkaf da
zufa dukda fanka dake aiki a ɗakin, gashi idanunsa sun kaɗa sunyi jazur har ana iya
hango yanda jijiyoyin kansa sukai ruɗu-ruɗu.
“Qaseem kaikuma mike damunka?” Dad ya faɗa da tsagwaron mamaki, Salman da
shima dai jikin nasa a sanyaye yake ya kalli Qaseem tare da dafa kafaɗarsa,
kallonsa Qaseem yayi shima, sai dai babu wanda ya iya cema ɗan uwansa komai, saima
Qaseem ya zame hannun Salman a jikinsa ya juya ya fita daga ɗakin.
Dad ya sauke nannauyan numfashi, dan shifa al'amarin ƴaƴan nasa ya fara
bashi matsanancin tsoro, shin mike faruwane haka wai?. Babu mai bashi amsa dan haka
yay shiru kawai ya zubama Bilkisu dake shashshekar kuka a hankali idanu. Ita kanta
Aamilah duk iskancin nan nata yau a firgice take, dan tsaf bata manta tsoratasun da
akai jiyaba, hakan yasa Bilkisu na fara sambatu itace farkon jiyota.
Dad ya kamo hannun Bilkisu yana rabota da jikin Aamilah, “Bilkisu tashi ki
faɗamin mike faruwa?”. Babu musu Bily ta tashi zaune, Dad ya sake cewa, “Miya
farune? Jiya ance an tsorataku musamma k, yau kuma gashi mun jiyoki kinata
sambatu?”. Hawayen daketa faman ziraro mata ta share.
Naɗan kalli Dad ƙaɗan na maida kaina ƙasa, cikin muryata data
dishashe a yinin yau gaba ɗaya nace, “Dad fyaɗe akaima ƴar mai aikin gidansu
Nazifa” shiru yay kawai yana kallona har nakusan sakanni ashirin, kafin ya girgiza
kansa cikin wani yanayi yace, “To Bilkisu shine kuma kike irin wannan mahaukacin
kukan?, ƴar gidan waye a cikin ƙawayen naki abin ya faru a gidansu?”. “Gidan
Alhaji Sufyan magashi”. “To ALLAH ya kiyaye, ki kwantar da hankalinki shima ai zai
ɗauki mataki, inake ina shiga irin wannan maganar ƴar ƙaramarki dake, sannan kuma
ma k miye naki a ciki? Ai can matsalar family ɗinsuce, muma muji da tamu gatanan
kinji”. Kaina kawai na ɗaga masa cikin tsantsar takaicin furucinsa, yaukam na sake
girmama al'amarin Dad fiye da tunanina, miyasa shi kansa kawai ya sani sai ƴaƴansa?
Yanzu da ace Aamilah ko aunty Shahudah akaimawa ai da bazaice hakaba ko, anya kuwa
koda a kaina wannan abun ya faru Dad zai nuna damuwarsa kuwa?. Sosai gabana ya faɗi
da zuwan wannan tunanin a cikin raina, nayi nisa sosai a tunanina har bansan
lokacin dasu Dad suka bar ɗakinba, kawai juyawa nai na jini kwance a gado har an
lulluɓeni da bargoma, a

unty Aamila na kwance a gefena da alama ta jima dayin barci ma, nasan badan tsoron
da takejiba bazata taɓa zuwa ta raɓeniba.

Dad kam koda suka fita a falonsa na sama ya iske Qaseem zaune yana
jiransa, da mamaki ya kallesa. “Kana nufin dama ba zuwa kai ka kwantaba?”. Kai Yah
Qaseem ya jinjina alamar eh. Dad ya zauna kusa dashi cikin kulawa yace, “Mike
faruwa?”. Kallonsa Qaseem yayi, murya a sanyaye yace, “Dad inason a saka ranar
aurenmu ni da Bilkisu”. Shiru Dad yay kawai yana kallon Qaseem tamkar yaune ya fara
ganinsa, kusan mintuna biyu kafin ya jinjina kansa, yace, “Shikenan za'ayi hakan,
to amma ita kaji ra'ayinta akan ta shirya aure yanzun?”. Kai Qaseem ya jinjina,
yace, “Munyi magana da ita ranar, dama dawowarka nake jira Dad, banason asa bikin
da nisa kuma, karya wuce wata ɗaya”. Dad yay murmushi cike da tsokana yace, “A
lallai wannan angon a shirye yake, yanzu dai kaga Ramadan baifi saura kwana goma
sha uku ba ya rage mana, lokaci yazo a ƙure kenan, saimu saka bikin bayan salla
kenan kamar da sati biyu, zan fara nemar dangin mahaifinta muyi magana dan wannan
huruminsune dukda sun wofantar da al'amarinta, kaga sai a haɗa tare dana mamana
kawai ayi a huta”. Fuskar Qaseem ɗauke da murmushi yace, “Shikenan Dad nagode
sosai, ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana”. “Amin ya rabbi” Dad ya faɗa yana
mamaki a ransa yau Qaseem ya masa godiya akan abu, lallai kusanci da Bilkisu ya
kawo cigaba a wani ɓangare na rayuwar yaransa, dan shikam bazai iya tuna randa
yayma Qaseem abu yaymasa godiyaba balle akai ga addu'a ma baki ɗaya. Sallama Qaseem
yay masa ya sakko, sai da ya leƙa ɗakin Bilkisu yaga sunyi barci ita da Aamilah
sannan ya wuce sashensu zuciyarsa najin daɗin ya kusa mallakar bilynsa.

★★★★★★

A ɓangaren Jawaad kuwa bayan an idar da sallar asuba yanayin azkar ya


fita daga massalacin, motsa jiki yaɗan zagayo ya koma gidan Alhaji baba, a falo ya
iske tsohon zaune yana duba wani littafin addini, Jay ya gaidashi da girmamawa
kafin su koma tsokanar juna, ganin lokaci yaja ya miƙe yana faɗin, “Bara nai wanka
nazo naje gida na shirya daga can na wuce office”. Cikin zolaya Alhaji baba yace,
“To agogo sarkin aiki”. Dariya Jay yayi yana miƙewa da faɗin, “Nikam sunayen da
kake jeramin sun isa hakanan”. Alhaji baba yace, “To gwauro na daina”. Juyowa
Jawaad yay zai bashi amsa hannunsa ya tanƙwaɓi ɗaya daga cikin hotunan da Alhaji
baba ya jera saman wata ƙyaƙyƙyawar drawer dake hanyar shiga bedroom. A take hoton
ya kifo ƙasa ya shiga bada ƙarar fashewa................✍

Gaisuwa da tarin fatan alkairi a gareku ƴan wattpad, wannan page ɗin yau nakune ku
kaɗai, kuyi birgima a ciki ku more😂😘😘😘😍😍😍.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

✍🏻
[12/2/2020, 11:36 AM] HASNA : Billyn Abdul:
Page 20

.................“Ya salam” Jawaad ya faɗa tare da ranƙwafawa ya ɗaga frame ɗin da


hoton ke ciki, a bisa tsautsayi ya ɗaura hannunsa kan glass ɗin da ya maƙale kaɗan
bai ida fitaba, yay tsini siriri, “ouch!!” ya faɗa yana yarfe hannunsa saboda
shigar zafin bazata. Alhaji baba ya taso da hanzari garesa, hannun da yake yarfewar
ya kama, abinka da jiki babu wahala tuni jini sai rige-rigen fita yake, abin mamaki
har yana neman wuce girman ciwon da yajin. Daga Alhaji baba har Jawaad sai fitar
jinin da yawa ta basu mamaki, dan sosai yake ɗiga a ƙasan tiles ɗin tamkar wanda
yay wani uban yanka, Jawaad yay ƙoƙarin ajiye hoton saman drawer batare da ya
kallesa ba sai kawai ya sake ɗora ƙafarsa akan glasess ɗin dake zube ƙasa. Da sauri
ya ɗaga ƙafar tare da sake damƙe hoton a hannunsa yaja da baya yana faɗin, “Yah
ALLAH”.
Alhaji baba yace, “Subahanallahi sake takawa kayi?, to kaga zauna ina
zuwa”. Zama Jawaad yayi ya ɗora fasashshen frime ɗin da ya rage katako da katin
hoton kawai a cinyarsa yana tarbe ɗigar jinin hannunsa da ɗayan hannun wanda tuni
jinin ya ɗiɗɗiga a hoton ma. Sai dai hankalinsa bai kaiba, har Alhaji baba ya dawo
ɗauke da ruwan ɗumi a roba mai ɗan faɗi da guntun towel, a hannun kujerar ya ɗora
ya kama hannun Jawaad ya saka a robar tare da jiƙo towel ɗin da ruwan zafi ya goge
masa hannun tas dukda dai jinin yaƙi tsayawa har yanzu yana ɗiga, kamar yanda sukai
hasashen ɗan yankan bawani mai yawa baneba, tissue ya warwaro ya ɗora masa dai-dai
yankan yana mai tsokanarsa da cewar, “Lallai cin kayan daɗinka yay yawa na wajena,
kaga ɗan yanka kaɗan amma jini yayi rabin botiki”. Babu shiri Jawaad ya ƙyalƙyale
da dariya, “Oh ALLAH, tsohon nan kana hawa kaina da yawa wlhy, idan yakai rabin
botiki ai saidai a ɗiba naka a ƙaramin kenan”. Dariyar alhaji baba yake shima, ya
durƙusa tare da kamo ƙafar Jawaad ɗin itama dake jinjin ya saka a robar, kwalbar
data sokesa anan tana ciki, hakan yasa Alhaji baba shammatarsa ya cirota, “Ouch!!”
Jawaad ya faɗa yana rintse ido dan yaji zafi, ciwon ƙafar yanada ɗan girma, Alhaji
baba ya ɗaure masa dan su samu jinin ya tsaya.
Batool ce ta shigo da sallama ɗauke da abincin kakan nasu. A tsorace take
kallon jinin da ƙafar Jawaad ɗin, “Ɗan uwa garin yaya haka?”. Fuska yaɗan yamutsa
yana kallonta, yace, “Tsautsayi mana”. Sannu ta shiga jero masa, ta ajiye basket
ɗin ta ƙaraso ta amshi tsintsiyar hannun Alhaji baba danta share kwalban kamar
yanda taga yana niyyaryi. Jawaad ya sake kai hannu zai ɗauke hoton daga cinyarsa
dan yanason ya tashi yaje yay wanka, sai idanunsa suka sauka akan waɗanda ke jikin
hoton, dukda jininsa dukya ɗan ɗiɗɗiga a jiki, hakan bai hanashi ganin fuskar
mahaifiyarsaba ras a jiki, tayi ƙyau sosai tana murmushinta mai birgewa, ya maida
idonsa akan ta kusa da ita, autarsuce da suke kira aunty Mammah, itama ALLAH yay
mata rasuwa shekaru masu tazara bayan ɓatan mahaifiyarsa, haka kawai ya samu kansa
da tsura musu ido harna tsahon lokaci, sai da Batool ta ɗauke hoton daga hannunsane
ya dawo hayyacinsa. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke yana miƙewa. Batool dake
kallon hoton tai murmushi da share guntayen hawayen da suka cika mata ido saboda
tuno da Gwaggonnin nata guda biyu da suka rasa a ƙaddarar mutuwa da ƙaddarar taɓin
hankali.
Koda Jawaad yay wanka ya kimtsa ya fito bai zauna cin abincin da Batool
ta kawoba, sai ya ɗauki hoton daya fasa zai tafi dashi akan zai sabunta masa glass,
babu yanda Alhaji baba baiyiba amma yaƙi ya ajiye. Cikin tsokana Batool tace,
“ALLAH yasa ba sace maka zaiyiba Alhaji baba”. Harararta Jawaad yay ya fice, batare
da ya jira amsar da Alhaji baban zaiba Batool ba.
Maimakon ya nufi gida kamar yanda yay niyya sai kawai ya wuce office, ta waya
ya kira Gimba yasanar masa shi yana office anjima yazo ya samesa zasu fita. Cike da
girmamawa gimban ya amsa masa sannan suka ajiye wayar.
Koda Jawaad ya shiga station kai tsaye office ɗin Jabeer ya nufa, shima da
alama bai jima da isowarba, ya ɗago yana kallon Jawaad daya shigo office ɗin da
sallama, murmushi yay masa, shikuma Jay ya hararesa yana ƙarasowa ya z

auna a kujerar dake gaban tebirin ɗin. Hannu ya miƙa masa sukai musabaha, murɗe
hannu Jay yay har saida Jabeer yay ƴar ƙara, ya fisge yana hararsa da faɗin,
“ALLAH kai mugune na bugawa a takarda, ciremin hannun zakayi boss”. Murmushi Jawaad
yayi yana miƙa masa key ɗin motarsa da faɗin, “Gobema ka sake yin gulma”,. Jabeer
ya sake hararsa yana juya hannunsa, “Kasan ALLAH Jay, yau da ace ba sunan momine da
itaba da akanta zan rama, ALLAH ya ceceta kuwa”. Murmushi Jay yayi yana taɓe baki,
yace, “Kaje ka rama mana ina ruwana, Am sorry jiya na maka tsawa, rainane duk a
jagule kaikuma kazo zaka sake cazamin kai da naka shiriritan”.
Murmushi Jabeer yay yana shafa kansa dajin ƙaunar abokin nasa cikin rai,
“Ni dama ban ɗaukesa komaiba, nasan wanene Jay ɗinmu idan yay fushi, ina fatandai
itama Momin tamu ka bata haƙuri, dan na koma office ɗinka kusan 3:45 na isketa tana
kuka”. Haɗe fuska da lumshe idanu Jay yayi yana sauke numfashi, “Ai yarinyarnan
bata da kunya. manta da zancenta, ina fatan su Hafiz sun iso, dan inason muyi
magana”. Kamar yanda ya buƙata sai Jabeer ya bar zancen bily, ya amsa masa da,
“Okey bara na kirasu to, nasan duk sun iso yanzun”. Gyara zama Jay yay, yayi shiru
har Jabeer ya gama kiransu. Babu wani jimawa sai gasu duk sun shigo, saida suka
gaggaisa sannan kowa ya nema wajen zama, Aliyu da idonsa ya sauka akan yatsan
Jawaad dake naɗe da bandage yace, “Boss miya samu hannun kuma haka?”. Hannun Jawaad
ya kalla yana ƙaramin tsaki, “Wlhy Aliy wani ɗan ciwo naji, shinefa Alhaji baba
yaymin wannan naɗin”. Dariya duk sukayi, Hafiz yace, “Shi ka kaima fushin jiya
kenan?”. Hararsa Jay yayi amma baice komaiba.
“Kunga ku ajiye shiritarnan taku muyi magana yau inada aiki a office
saboda jiya banyi komaiba”. Duk hankalinsu suka maida gareshi, Jabeer ya direma
kowa kofin coffee daya haɗo, “Thanks ” Jawaad ya faɗa yana ɗaukar kofin, suma su
Hafiz sukai masa godiya, Jawaad yakai kofin bakinsa sanan ya janye idonsa a kansu,
sai dai yay matuƙar canja fuska saboda maganar da zaiyi tana zafarsa a cikin rai,
“Guys dolene yarinyarnan tabar cikinmu a wannan karon, bazan iya cigaba da zama da
itaba ta isheni haka nan”. Kallon juna suka shigayi kowa da tsoro akan fuskarsa,
Aliyu yay ƙarfin halin faɗin, “Wa kake nufi a cikinsu boss? Kasan yanzu sun zama su
biyu”. Kallon Aliyu yayi tamkar bazaice komaiba, sai kuma cikin takaici yace, “Rose
nake nufi”. Shiru sukai duk suna jinjina zancen a ransu, kafin Hafiz yace, “Banƙi
ta takaba Boss, sai dai hakan zai iya zama wata matsala daban, duk da bansan
ainahin abinda tai makaba na kula tanason takurama rayuwar mami ne, abinda kuma na
fahimta itafa gani take son Mami kake gaskiya shiyyasa take duk waɗanan abubuwan”.
Tsaki Jawaad yaja yana yamitse fuska cike da takaici amma baice komaiba. Suma
shirun sukai basu damu da rashin bada amsarba, dan a ganinsu idan son Bilkisu yake
wataran ai dole ta fito fili ko. Jabeer ne ya katse shirun nasu da faɗin, “Gaskiya
boss hakan ba shine mafitaba, na farko Rose tasan sirrikanmu da yawa, yaƙi take
akan soyayyarka a yanzu, idan kace ta barmu zaitai amfani da wannan fushin ta koma
cin dunduniyarmu, munada muhimman ayyuka a ƙasa waɗanda munyi zurfi sosai na kaiwa
ga nasara, sune zata fara harin ɓatawa, karka manta zagaye muke da maƙiya, ƙaramar
ƙofar da za'a kutsa cikin mutuncinmu kawai ake nema dama, magana ta ƙarshe kuma
Rose zatabi duk hanyar da zuciyarta ta ƙawata mata ta cutar da mai sunan mom batare
da munsan tayaya ta shirya hakanba, kaga kuwa tako ina korarta ba mafita zata
bamuba, domin iyakar gudunmu dai bai wuce kabi ta ƙasa kasa aimata transfer ba, duk
nisan da kake tunanin zatayi damu ALLAH saita dawo koda ta hanyar saka wanine yay
mata aiki kuwa”.
Dukansu sun gamsu da maganar Jabeer. Aliyu yace, “Maganar Jabeer fa gaskiyace
Jay, sawa tabar cikinmu ba mafita bace, gara ace muna ganin duk motsinta, sannan ni
a ganin idan kanason Mami ɗin miza hana ka fito ka bayyana mata kawai a wuce wajen,
da zafi-zafi ake bugun ƙarfefa a wannan zamanin”. Fuska sosai Jawaad ya haɗe, cikin
nuna halin ko in kula ya wani taɓe baki yaƙi cewa

komai a karo na biyu kan maganar Bilkisu. Duk idanu suka zuba masa na mamaki, sun
rasa miyake ɓoyewa. Sai da ya shaƙi iska dan kansa sannan yay magana, “Kuna ɓatamin
rai da shirmennan naku, kunefa dalilin shigowar wannan yarinyar cikin tawagarnan,
amma miyasa kuke son maida zancenta wani abu daban, to inagama ba rose bace ta
cancanci yin nesa damu, Miemaa zansa aima transfer, ince dai shikenan”.
Da sauri Hafiz yace, “Ba shikenanba, yarinyarnan yanzune ta fara aiki, ƙwazon
data fara nunawa yana buƙatar a cigaba da horar da ita akan gaskiya, munji ba sonta
kakeba, kuma insha ALLAH babu mai sake maka wannan maganar, inaga kawai mu zauna
dasu ita da Rose kajama Rose dogon gargaɗi akan wannan haukar tata mara tushe,
domin munutsu mu fuskanci sauran ayyukan dake gabanmu, yanzu aikinan da muke wlhy
yanada matuƙar sarƙaƙiya da haɗari, amma gashi muna wasa dashi, sai dau ku yaya
kuka gani?”. Jabeer dake wani shegen murmushi yana satar kallon Jay yace, “Hakan
yayi nidai a wajena, gara a bar mana Miemaar mu muyita kwasar albarkacin sunanta”.
Hafiz da Aliyu sukai dariya, dan sunsan shaƙiyancin Jabeer ne ya motsa, Jawaad kam
uffan baiceba, saima miƙewa da yayi yay musu sallama ya fita.
Yana fita duk sukayi dariya, Aliyu yace, “ALLAH Jabeer kasama boss ido da
yawa, nakula son ƙureshi kake kawai,, ka barshi yasha iskar duniya malam”. Nanma
dariyar sukayi, Hafiz yace, “kunga nima bara na koma Office, gayenan addu'armu
kawai yafi buƙata”. “Hakane kam” cewar Aliyu dake miƙewa shima.

Fitowar Jay daga office ɗin Jabeer yay dai-dai da fitowar Bilkisu daga
motar Qaseem suna murmushi ma juna, dukda a sama yake kuma ta glass yake ganinsu
hakan bai hanashi ganin murmushin yamata ƙyauba, dayake ba yawan ganin murmushin
nata yakeba sai yazam idan tayi yakan kasance na musamman, ya taɓe bakinsa yana
barin wajen.
Bilkisu kam da batasan yanayiba rakkiya tayoma Qaseem dake bata labarin
maganar da sukai akan aurensu jiya da Dad.
hakan sai yasani jin daɗi da raguwar nauyin da zuciyarta tayi tun a daren
shekaran jiya, a ganina garama nai auren na huta, dan na kula zamanmu a haka
haɗarine babba a gareni, maganganun Dad na jiya akan fyaɗen mai aikin su Nazifa ya
mugun tsaya mani a rai, inada yaƙinin irin wannan ƙaddarar ta afka tsakanin ni da
ƴaƴansa to wlhy nikaɗai zanyi kukana, dan tabbas zai goya musu bayane, a yanda kuwa
Yah Qaseem ke kaima jikina hari da halayyar Salman da batai minba komai zai iya
faruwan, to maganin ayi kar a fara kawai.
Saida nai masa rakkiya har office ɗinsa sannan na juya na sauka namu,
saida na gaisa da kowa sannan na zauna mazaunina, Computer ɗin gabana na kunna
domin duba gajeren video da boss ya bani nai sharhi akan abinda na fahimta ciki,
gaba ɗaya hankalina na maida akan aikin har Ummie data makara yau ta shigo, gaisuwa
tayi da sauran sannan ta matso inda nake ta bani hannu muka gaisa idonmu akan video
mu duka. “Bily jiya wai miyasa kika gudu bayan kinsan magana mai muhimmanci muke
tattaunawa a group?”. Murmushi nai mata ina cigaba da control ɗin mouse ɗin
Computer a hannuna na haggu, na damar kuma ina riƙe da pen ina rubutu a takarda.
“Hankalina ne yay masifar tashi Ummie, al'amarinne akwai ruɗani a ciki, dan na fara
zargin mai aikata ɓarnarnan ba mutum ɗaya bane sai dai ƙungiya garesu”. Kujera ta
jawo ta zauna saɓanin da da take tsaye ta ranƙwafo jikin tebirina, tace, “Miyasa
kikai wannan tunanin bily?”. Kallonta naɗanyi na ɗauke kaina ina cigaba da aikin
gabana, nace, “Saboda Amina mana, kinga su su Nazifa a gida ɗaya akai musu ita da
marigayiyya, sai kuma na yarinyar jiya, amma ita Amina ai a gidanmu akai mata,
yanda ake salon fyaɗen duk iri ɗayane, sai an bugar dasu ake cutar dasu, sannan
babu wandda ta taɓa ɗaukar ciki a cikinsu, zuwa yanzu ina buƙatar mu haɗu waje ɗaya
mu duka biyar ɗin, dan yadace mushiga binciken neman sauran waɗanda hakan ta faru
garesu, inaji a jikina Ummie basu kaɗai bane akwai wasu”. Na ƙare maganar da
kallonta idanuna cike da ƙwalla. Kanta ta girgizamin a hankali alamar karnai kuka,
na ɗauke kaina ina haɗiye abinda ya tokaremin maƙoshi mai nauyi d

a ƙyar.
Nuna mata Computer ɗin nayi ina zooming ɗin wani waje cikin video ɗin da
faɗin, “Ummie kalla dan ALLAH mikika fahimta a wajen nan?”. Matsowa tayi sosai tana
kallon wajen cike da nazari, kafin ta amshi mouse ɗin hannuna ta maida video'n
slowly, “Kai bily kilura da ƙyau wani kasuwancin kurame akeyi a wajen nan fa, ki
kalli zuwan yarinyarnan wajen da ƙyau, kafin ta ƙarasa wajen shi wannan mai kifin
saida suka kalli juna da mai raken can sukaima juna wata inkiya da idonu, sannan
bakin mai kifin ya motsa alamar magana yayi”. Kaina na shiga jinjina mata, nace,
“Haka nima duk na fahimta Ummie, to amma sam na kasa fahimtar mi mai kifin ya faɗa,
na maimaita wajen yafi sau goma wlhy, amma kuma abin lura anan shi wacan mai facin
minene ya ɗauka cikin tayoyi ya bama gurgun yaron can almajiri?”. Baya ummie ta
dawo da video dai-dai wajen, da alama mai ɗaukar video bai saka da mai facinba a
ɗaukar, dan acan gefe yake yana harkokinsa shi kaɗai, hakan yasa ba komai ake iya
fahimta dangane da shiba. “Bily kinsan mizakiyi?” nace, “A'a saikin faɗa”. kije
office ɗin boss kimasa bayani, inba hakaba zamu iya rikita komai anan”.
Gabana ne ya faɗi jin ta ambaci boss, abinda ya faru jiya ya shiga mani
kaikawo, gashi yau yanda na lura baije duba aunty Shahudah bama tun jiya da safe
kamar yanda naji iyayenmu na tsogumi a asibitin, ALLAH dai yasa ba maganata bace ta
jawo hakan, dan yakamata ace ya cika alƙawarin daya ɗaukama Dad na zuwa gidanmu a
daren jiya......... “Lafiya kuwa? Ina magana kin tafi tunani”. Numfashi na kawo ina
dafe kai, nace, “Babu komai, bara nakai masan”. Nasan yanda nai maganarne a sanyaye
ya sakata bina da kallo, ban yarda mun haɗa idoba na cire flash ɗin daga
Computer'n na ɗauki takardun danake rubuta bayanan na tattare cikin file ɗin daya
bani jiya na fita. Maimakon na nufi office ɗin nashi saina tafi office ɗin Oga
Aliyu. knocking nai aka bani izinin shiga, su biyu na iske a ciki, hakan yasani
gaishesu na tsaya gefe su kammala, dan naga magana suke. Basu wani ɗauki lokaciba
wancan ya miƙe ya fita, oga Aliyu ya nunamin kujera alamar na zauna, sake gaidashi
nayi sannan na zauna ina ɗora takardun hannuna a tebirin gabansa. “Mami ta samune?”
yay maganar cikin zolaya. Murmushi nayi nima na bashi amsa da “Sosai ma”. Yay
ƙaramar dariya yana amsar takardun, “To ALLAH yasa mai washa-washa ne da zamuci mu
more”. Yanzunkam saida naɗan dara kaɗan, dan bansan yana magana mai tsaho hakaba,
yaɗan duba takardun sannan ya kalleni, “Mami ban fahimci komaiba anan, na minene?”.
Hannuna naɗan matsa kaɗan sukai ƙara, na muskuta zamana, “Oga Aliyu bayanan daga
wani video suke” nai maganar ina miƙa masa flash ɗin hannuna da cigaba da faɗin,
“Nice na haɗasu anan, to kuma na cije a wani waje shine nazo neman haske”. shiru
yay na sakanni batare daya amshi abin hannunaba, kafin yace, “Okey, wanene ya baki
aikin a cikinmu?”. Nace, “Boss ne”. Takardun ya miƙomin, “Kinga to kije wajensa,
dan bansan case ɗin miye ba, nasan zai miki bayanin duk da zaki fahimta”. Shiru
nayi na kasa amsar takardun.
Aliyu dake kallonta yace, “Da matsalane?”.
Kaina na ɗago na kallesa, sai kuma na sauke idanuna ƙasa, “ALLAH oga shi ya
cika faɗan tsiya, yaytama mutane mazurai”. Dariya sosai Aliyu yayi da wannan magana
tawa, saida ya gaji dan kansa yay shiru, sake miƙomin takardun yayi har yanzu
fuskarsa da murmushi, “Ai sai an masa ba daidaiba yake mazurai, tunda akan aikine
zai fahimceki bazaiyi faɗaba kinji”. Kaina na jinjina masa, badan nasoba na amshi
takardun na fita. Jinake kamar karnaje, amma wani sashe na zuciyata na bani
shawarar naje dan akan aikine, bai kamata kuma na sanya wasa akan aikinaba, nidai
na kiyaye duk wata hanya da zata sake haɗani dashi harnaga fushinsa kamar na jiya
kawai. Da wannan ƙwarin gwiwar na nufi office ɗin, knocking nai aka bani izinin
shiga, gabana sai faman faɗuwa yake na tura ƙofar da sallama a ƙasan maƙoshi na
shiga.
Tarin aikine jibge a gaban Jawaad, ko buƙatar shigowar wanima babayi
office ɗin, hakan yasa koda Bily ta shigo sallamarta kawai ya amsa amma bai
ɗagoba, ƙarasowarta gabansa ƙamshinta

ya tabbatar masa itace, sake ɗaure fuska yay sosai fiye da yanda ta shigo ta
sameshi.
Kallo ɗaya naima fuskarsa na ɗauke kaina, a ɗaure take fiye da kullum ma
dana sani, gaba ɗaya ƴar jarumtar dana shigo da ita saita gudu itama, gashi yaƙi
kallon ko inda nakema dukda inada tabbacin yasan nice na shigo. Da ƙyar na iya
daurewa nace, “Ina kwana Sir”. Batare daya kalleniba yanzunma yace, “Lafiya”. Shiru
nai nakasa cigaba da magana, dan yanda ya amsa gaisuwar tawa a daƙile ya sake
sanyayamin jiki sosai, ganin tsayuwar tawa bata da amfani na daure nace, “Sir dama
akan aikin daka bani ranar monday ne”. Harna fidda rai da samun amsa sai naga ya
nunamin kujera batare daya ɗagoba. Ɓoyayyen nunfashi na sauke ina ƙara ƙoƙarin
ƙarfafa kaina. Na ajiye takardun hannuna a gabansa kafin naje na zauna a kujerar,
shiru muka sakeyi na mintuna, saida ya tattare wasu takardun gabansa waje guda ya
ajiyesu gefe kafin ya kalleni. Saurin nuna masa takardun dana ajiye nayi. Janye
idanunsa yay daga tsatstsarenin da yay dasu ya ɗauki takardun, shiru tsawon wasu
mintuna yana dubasu kafin ya ɗago, yace, “Kin gama ne?”.
Sau ɗaya na kallesa na ɗauke idanuna ganin ni yake kallo, na girgiza
kaina, “A'a ban gamaba, akwai wani wajene a video'n to sai nakeson ka gani kafin na
shigar da bayanansa” na ƙare maganar da miƙa masa flash drive ɗin, bai amsaba ya
ɗauke kansa daga gareni ya maida ga Computer ɗin gabansa, “Taso kisa”. kamar nai
kuka haka naji, sai dai bani da wata mafitar daya wuce bin umarninsa, inda yake
naje, a mamakina sai naga ya tashi daga kujerar tasa ya nunamin alamar na zauna,
batare da yace uffanba............✍

Yau shafin nakune ƴan telegram, kuma ku warwasa da wannan, alkairin ALLAH yakai
gareku aduk inda kuke, ammafa babu canji mun ƴan hud-jay team ne😜😂😂😂😍😍😘😘😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭.


✍🏻
[12/3/2020, 3:35 PM] HASNA : Billyn Abdul:
Page 21

...............Kallonsa nai ya zubamin harara, babu shiri na ɗauke idanuna na zauna


kamar yanda ya buƙata a lallausar kujerar tasa dariya nazomin a cikin rai, danni
mamakin yanda ya iya harara wa mutane nake, sai kace wani mace. Da ƙyar na iya riƙe
dariyar daketa son fallasa na saka flash ɗin a jiki, duk abinda nake yana tsayene a
kaina harna kunna video ɗin. Har ya kai karshe ya sake komawa baya baice komaiba,
ganin mun maimaitashi sau uku yaƙi magana saina juyo dan inga koma dai nikaɗai nake
kallon. Mamaki ya kamani ganinsa tsaye a bayana hannayensa duka biyu cikin aljihun
wandonsa, idanunsa akan Computer alamar duk yana kallona. “Idan kin gama kallon
nawa saiki nuna inda baki ganeba”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa, kamar wani mai tsoron a jisa.
Fuska na kumbura tare da ɗauke kaina, a raina nace, ‘Kai wama ya kaika iya
kallon mutane’. hannuna na ɗaura saman mouse ɗin nai zumin dai-dai wajen mai faci
ina faɗin, “Akan mai facin nan ne dama, kamar akwai alamar tambaya dangane da shi,
dan......” kasa ƙarasa maganar nai saboda kusancin da muka samu, a dalilin
ranƙwafowar da yay har munajin saukar numfashin junanmu, ya ɗaura hannun hanggunsa
saman table ɗin, na damar kuwa saman nawa dake kan mouse. Da sauri na rumtse
idanuna, tare dayin azamar janye hannuna dake ƙasan nasa, saboda wani mugun harbawa
da zuciyata tai. Baice komaiba, shikam ko a jikinsa, saima ƙoƙarin maida video
slowly da yay. Nayi matuƙar takura da tsorata da wannan kusancin namu da yay
matuƙar yawa, har takai jikina ya fara rawa, idanuna suka ciko da ƙwalla, sam bana
fahimtar bayanin da yakemin ma, dan sama-sama nake jin sautin muryarsa.
Jawaad da duk abinda yake akan sani yayisa ya juyo yana kallonta, ta rumtse
idanu zufa dukta tsatstsafo mata a goshi tamkar babu ac a office ɗin. “Hummm” ya
faɗa acan ƙasan maƙoshi ya janye jikinsa. A mamakinsa sai yaji ta sauke ajiyar
zuciya mai ƙarfi, hawaye sun silalo saman kumatunta, saurin ɗauke kansa yay tamkar
bai ganiba.
Har bigewa nake da shi wajen rawar jikin miƙewa daga kujerar jin ya matsa,
na goge hawayen dake bin kumatuna batare da na bari ya ganiba, gefen tebirin na
koma na tsaya kaina a ƙasa nace, “Sir, bara kawai naje can dashi saina ƙarasa
tattara bayanan”. Jawaad da har yanzu yake binta da kallo yaɗan lumshe idanu ya
buɗe yana ƙoƙarin danne dariyar dake son kufce masa, murya a daƙile yace, “Barshi
zan ƙarasa, ɗauka waɗanan files ɗin ki kaima Hafiz, zuwa anjima ki dawo zamu fita”.
Bawani fahimtarsa nakeba, kai kawai na ɗaga masa na ɗiba files ɗin na fice cikin
sassarfa. A raina banda takaici babu abinda nakeji, miyasa halin mazan wannan
zamanin kusan duk ɗayane? Burinsu kawai su taɓa macen da ba muharramarsu ba a
matsayin wayewa, ashe shima mutumin nan haka yake ban saniba?, “Aikam na daina
sakar masa fuska wlhy” na faɗa a fili cike da takaici.

★★★★

Ƙarfe biyu muka fita cin abinci ni da Ummie, sai da muka gama nai ƙoƙarin
biya sai nagama kuɗin dake jikkar tawa bazasu isaba, kusan koda yaushe Ummie ke
biya mana inhar bada Yah Qaseem mukazo ba, sai naga da kunya hakan tacigaba da
faruwa ai, ATM ɗina na shiga lalube dan na basu su cire, amma sai shima ɗin dai ban
gansaba, gabanane ya shiga faɗuwa, dan bama shi kaɗaiba duk cards ɗina basa ciki
kenan tunda a tare nake ajiyesu waje guda, kuma inada tabbacin itace jikkar danasan
na fita da ita daga gida last. “Wai mikiketa lalube hakane kamar wata makauniya?”
Ummie dake shan ruwa ta faɗa bayan ta ajiye kofin. Guntun tsaki naja ina mai bata
amsa da, “Ai namafi makauniya yau Ummie, wlhy banga duk Cards ɗinaba, kuma inada
tabbacin anan ciki suke”. Tasowa tai tana tayani, sai dai kumafa da gaske babu ɗin,
hankalina yayi matuƙar tashi, “Ummie na shiga uku, a ina na jefar nikam?”. “Bily
bazan saniba, amma nasan baki da mantuwa, yaushene rabonki dasu?”. “Ummie A ranar
lahadi fa da hannuna na sakasu cikin nan dazan fita”. Tace, “Ai da sauƙima, ki tuna
ranar ina da ina kikaje tunda kin tabbatar a ciki suke?”. Zama nai idona cike da
kwalla ina tunano dukkan abinda ya wakana a wannan yinin, da sauri na kalli Ummie,
“Ummie idanma har yardawa nai to

bazai wuce wajaje biyu ba wlhy”. Ummie tace, “Ina da ina ne?”. “Saloon da wani
garden, amma bara na bincika a saloon ɗin dan inada Number ma'aikaciyarsu ɗaya”.
Ummie ta biya kuɗin muka fito a wajen, sai da muka koma office sannan nai
kiran Number danai saving da Ladies mirror, bugu biyu kuwa aka ɗaga, bayan mun
gaisa nace, “Dan ALLAH kiyi haƙuri, na kiraki maybe ba'a lokacin daya daceba”. Daga
can tai dariya da faɗin, “lah babu komai”. Nace, “Okey ngd, ranar danazo wajen nan
naku ina tunanin na yarda wallet ɗina, sam hankalina bai kaiba sai yanzu, ina fatan
anan na yardar ɗin?”. tai ɗan jimm na wasu sakanni kafin tace, “Eh tabbas anan kika
yarda, amma bata wajenmu, tana masarauta wajen su aunty Amaturrahman, dama sunbar
saƙo akan idan kinzo nema a baki card ɗinsu, yanzu yaya za'ai kenan?”. Wani sanyi
naji ya ratsani, na sauke numfashi da cewa, “Babu damuwa, idan na tashi aiki zan
biyo na amsa, nagode sosai”. ta amsa da “Babu damuwa, sai kinzo”. Bayan mun kashe
wayarne na faɗama Ummie duk yanda mukai, daga ni har ita mamaki muketayi na cewar
wallet ɗin na masarauta.
Ban samu kiran boss ba kamar yanda yace zamu fita har lokacin tashi yayi,
zuwa nai na sanarma yah Qaseem ya wuce gida ni zamuje nida Ummie wajen wanke kai,
yanzunma da damuwa na iskesa, dan haka bai wani jamin zanceba yace mu haɗu a gida.
Nidai al'amarin nasa sake ɗauremin kai yay yanzunma, har muka isa Ladies mirror
banbar mamakin wannan canjin nasaba. Sosai Ummie ta rikice da haɗuwar wajen, harda
ma kanta alƙawarin zuwa wannan weekend ɗin su mata aiki, bamusha wata wahalaba muka
samu wadda na kira ɗin, ta bani card ɗin da suka bari. bamu daɗeba muka fito dan
magriba ta gabato.
Ummie ta ajiyeni a gida ta wuce, koda na shiga saina iske an sallamo auntu
Shahudah, falon cike da dangin Momy, da sukazo dubata, nidai na gaishesu itama nai
mata yaya jiki na wuce, saboda a rayuwata na tsani kallon wilaƙanci, sukuma naga
alamar indai ba nasuba to kowa banzane. Wanka na farayi harda wankan tsarki saboda
baƙona ya gudu, na fito na gabatar da sallar magriba nai azkar, ina zaune a wajen
har aka kira isha'i, har lokacin inajiyo hayaniyar ƴan gidansu Momy, dukda yunwar
da nakeji saina zaɓi haƙura na kwanta a haka, ɗan kayan maƙulashen da yah Qaseem ke
yawan siyamin nakan ajiye a ɗaki su nai zamanci, gefe guda kuma ina ƙoƙarin kiran
Number jikin card ɗin da aka bani, saida ta kusa tsinkewa aka ɗaga, munyi gaisuwa
da wadda ta ɗagaɗin a mutunce dukda bansan wacece ba, kafin na mata bayanin kaina.
Nayi mamakin yanda tai saurin ganewa, kai tsaye tace na tura mata address ɗin inda
nake kawai, zasuzo su kawomin har gida. Sosai na ƙara mamaki da jinjina ƙyaƙyƙyawar
tarbiyyarsu gaskiya, sam basuda girman kai tamkar ba waɗanda suka fito daga babban
gidaba. Godiya nai mata mukai sallama, ban zauna ɓata lokaciba na tura mata number
dan inada buƙatar cards ɗina su dawo hannuna da gaggawa.
Jin gidan yayi shiru yasa na miƙe, dan fitar motoci da naji ya bani
tabbacin duk sun wuce, ƙaramin hijjab na saka saman wando da rigar kayan barcina
kalar ruwan hoda na fito, wata irin muguwar yunwa nakeji wlhy, rabona da abinci tun
wanda mukaci da Ummie da rana. Babu kowa a falon duk sun tafi, na wuce kicin
hankalina kwance, plates kawai nagani zube wanda sukaci abinci, sai dai babu komai
a kulolin duk an cinye, cike da haushi na fara ƙoƙarin ɗora noodles dan bazan iya
haƙurin kwanciya banci komai ba, dan danan na kammala dafawa na fito, mamaki ya
kamani jin ƙamshin turaren da banyi zatoba, zuciyata sai harbawa take da sauri-
sauri, waige-waige na shigayi a falon, saiko idona ya sauka akan wanda zuciyar tawa
ke rayamin, tsaye yake dafe da ƙarfen benen dake falon waya a kan kunnensa, kamar
koda yaushe ƙananun kayane a jikinsa, ido cikin ido muka kalli juna, nai azamar
janye nawa ina damƙe plate ɗin indomie ɗina daketa tururi, inaji a jikina har yanzu
kallona yake, hakan saiya haifarmin da tafiya a hankali kamar wata hawainiya harna
shige lungun ɗakinmu ni da aunty Aamilah.
Jawaad daya kasa ɗauke idanunsa a kanta har saida ta shige sannan ya sauke
ajiyar zu

ciya yana lumshe ido da cije lip ɗinsa na ƙasa, sannan ya cigaba da wayarsa, bai
wani jimaba sukai sallama ya maida wayar aljihu idanunsa akan lungun da bily ta
shiga, cike da kasalar data saukar masa yanzun ya haye saman ya koma wajensu Dad da
Alhaji baba da Uncle Nasir da sukazo tare suke tattaunawa.

Ban kawo komai a rainaba dangane da ganin boss gidanmu, tunda ai dama yayma
Dad alƙawarin zuwa, sannan kuma ga aunty Shahudah ta dawo gida itama, abincina naci
hankali kwance nai brush na kwanta domin na hutama raina.

ALLAH YAY DARE.

Washe gari safiyar alhamis, koda na tashi sai naci karo da abubuwa
uku na farin ciki sun samemu, na farko samun sauƙin aunty Shahudah da har aka
sallamo daga asibiti a daren jiya, na biyu maganar aurenta da Boss bayan ansha
gumurzu ya amince da ƙyar saboda saka baki da kakansa yay a maganar, na uku tsaida
maganar aurena da Yah Qaseem bayan Dad yaje wajen dangin mahaifina ya samesu ashe a
jiya da rana, an tsaida aurenmu rana ɗaya dasu aunty Shahudah bayan salla ƙarama da
sati biyu. Koba komai na samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, dan nikam
abubuwan dake faruwa na wannan lokacin suna matuƙar tsoratar dani da sakani
firgici.
Ban ƙara tabbatar da ina son Yah Qaseem ba sai da aka tsaida ranar auren nan
namu, shi kansa wani sake lallaɓani yake da ji dani a yau, dukkan abinda zai saka a
gidansa kuma sanda muke tafiya wajen aiki ya nema shawarata, hakama kayan lefe
saida yace na faɗi duk abinda nake buƙata, nidai kunyace ta kamani nace kawai na
bashi zaɓi.
Sai dai abu mafi bani mamaki sune jama'ar gidanmu, musamman ma Momy, koda
wasa ban taɓa tunanin zata goyi bayan aurena da Yah Qaseem ba, amma sai gashi koda
a fuska bata nuna komaiba, saima shirye-shiryen gagarumin biki take na nunama sa'a
akan babban ɗanta namiji da zata fara aurarwa. Yah Salman ne kawai da aunty Aamilah
sun shafema idanunsu toka suna ƙara faɗaɗa hantarata da muguwar tsana akan ban
cancanci zama matar ɗan uwansuba, ƙiri-ƙiri suke nuna hakan babu ko kara a wannan
safiya, su Dad dai basu tsawatar musu ba, sannan basu goya musu bayansu ba, Yah
Qaseem ne daifa da yay kansu da masifa har saida na roƙesa yayi haƙuri kafin yay
shiru muka fito.
Tom nidai lamarinsu bai ɓatan rai, Alhmdllh tunda wanda zan zauna dashi yana
sona, sannan iyayensama suna sona, dansu ƙannensa sunce basayi miye a ciki. A
dangima dai akwai ƴan adawa, dan harda inna zainabu faɗa taitama Dad akan haɗani
aure da ɗansa da yay kamar yanda Aunty Aamilah take faɗamin cikin gori da tsana,
wai acewar inna Zainabu duk ƴaƴan manyan mutane masu kuɗi abokan Dad Qaseem ya rasa
wadda zaiso saini? Haka taita jaraba tamkar itace ta haifi Dad ko yah Qaseem ɗin.

Duk wanda ya kalleni a office yau yasan banda wata damuwa tattare dani, dan
waɗandama suke faɗin basa ganin dariyata yau sun gani harma da haƙorana, sai dai
abinda ya ɗaure kaina da mamaki rai a ɓace naga Boss yau, dan koda nakai masa saƙo
office baiko amsa gaisuwataba bayan sallama, sannan harna fito baice dani uffanba,
idanunsa jajur, hakama jijiyar kansa duk sunyi ruɗu-ruɗu, duk sai naji babu daɗi,
dan koba komai nima ranar danai ciwon mara ya bani kulawa da nuna damuwarsa a
kaina, da alama kuma yau shima baida lafiyarne. Kasa zama nai waje guda nakoma
office ɗinsa wai naji mike damunsa?, ‘kuji ƙarfin halifa irin nawa’ to aiko dai ban
jiyota da daɗiba, dan fatattakoni yay tamakr zai gaggallamin marukama, ALLAH dai ya
taimakeni na gudo. A ƙofar office ɗin mukaci karo da gimba kamar a rikice yake,
nidai na bashi hanya ya shige ko gaisuwa bamuyiba, sauka nai ƙasa abina ina
ƙunƙunai, ban sakebi takansaba har aka tashi aiki kuwa, sai a wajen Ummie nakejin
gulmar wai taga boss ya fita ɗazun ransa a ɓace kamar zai tashi sama, ban kulataba
ita da zancen nata, dan haushinsa nakeji akan abinda yaymin ɗazun..

Mamaki yay matuƙar kamani da muka isa gida na iske aunty Shahudahr data
kwana biyu a asibiti rai a hannun ALLAH zaune suna hira mai nuni da tsare-tsaren
biki, a raina nace, ‘Dama ciwon so ke damunta ashe, ta samu yanzu kunga ta miƙe
harda tsara

biki kamar wani auren farko mtsoww’ na ƙare zancen cike da takaicin da bansan
dalilinsaba nima. koda nai sallama basu amsaminba sai Momy kaɗai, sannunma ita
kaɗai taimin hakama amsa gaisuwata, jikina duk sai yay sanyi, na wucesu ƙwalla na
cikamin idanu, nasan dolene saina sake ɗaura ɗammarar haƙuri kam, dan matsalolin
dama sukafi haka zasu biyo baya akan aurena da Yah Qaseem, har nai wanka na fito
hawaye basu daina gudu a idanunaba, bayan sallar isha'i saima naji gidan tsitt,
koda na leƙo iskewa nai duk fita sukai, daga ni sai Yah Qaseem dana iske a d/table
yanacin abinci aka bari gidan da alama, zama nai mukaci tare muna ƴar hira, bayan
mun kammala ya fita sashensu ni kuma na koma ɗaki nai shirin kwanciya dan barci
nakeji kuma. Ina kwance har tara na dare barcin bai ɗaukeniba bankumaji motsin
dawowar su Momy ba, sai naji wani tsoro na shigata a hankali, addu'a nai na kwanta
ina fatan barci ya ɗaukeni mai nauyi kozan samu nutsuwa, UBANGIJI kuwa sai ya amsa
roƙona barcin yay gaba dani babu zato.

‘Innalillahi...’ na ambata cikin farkin barci lokacin da abinda ya faru


kwanaki huɗun da suka shuɗe dana manta shi gaba ɗaya a raina yake neman maimaita
kansa a wannan daren tamkar ranarma a yau, a matuƙar gigice na farka jikina na
mazarin rawa haɗe da bugawar zuciya tamkar zata faso ƙirjina ta fito, na fashe da
kuka ina mutsu-mutsun fita daga jikinsa, sai dai hakan ta gagara a yau, dan yaymin
riƙo bana wasaba, ga bakina an ɗaureshi da yanda bazan iya maganaba . Wata irin
siririyar dariya ya saki a cikin kunnena, yauma dai muryar tamkar irin ta wancan
ce, “Hhhh sannu Jaruma, yauma na dawo gareki, ranar kinyi nasarar korata ko, to
kisa a ranki yau duk gudunki bazaki iya tsereminba, harke wacece da kika isa
ruguzani? Nazo miki da lallami ranar amma kikaƙi saurarata, hhhhhh ke baki isa zama
matar aureba yarinya saina karɓi abinda yake nawa, gashi kina a cikin yanayin
danafi buƙata ma kina haila, kina bani shikenan, dan samunsa bada igiyar aure a
kankiba shine yafi komai muhimmanci, bakuma zan sake bibiyarkiba dana samu cikar
burina, hhhh bilkisu kece kammaluwar nasarata, kece ƙarashen nasarorina, da dukkan
wahalhaluna na tsawon shekaru zan cika nasarata! Hhhh taya kike tunanin zan bari ki
kufcemin, ɗaura miki igiyoyin aure tamkar ni aka ɗaure da igiyoyinne, taya zan bari
hakan ta kasance ban amshi abinda yake cikamakin nasarorina ba?, abinda naketa
bibiya tsahon shekaru kenan, karki yaudari kanki da tunanin ranar kin tsira yauma
zaki tsiran, namiki shiri sosai a yau bilkisu, na shiryama wannan ranar, dan tana
cikin damammakin da idan na rasasu babbar asarace a gareni, bana asara yarinya sai
dai nasara! hhhhhhh!........”
Duk wannan maganganun da yakemin a cikin kunne na zama tamkar wata gawace
a kwance, gangar jikina ne kawai a duniya amma numfashina da tunanina basa tare da
duniyar, ba'a maganar zubar hawaye ma dan waɗanan dama ke sakasu fitowa, wata irin
hasala zuciyata keyi da kumburar ɓacinrai irin wanda ban taɓa tunanin inada shiba,
haka kawai yau nakejin zuciyata ta bushe dukda inajin tsoron ya samu nasarar da
yake fatan kuwa, sai dai ban fasa gayama UBANGIJINA ba, addu'a nake kawai ina
ƙiyasta tunanin shaidar dazan iya barma koma wanene wannan shaiɗanin, bazanyi sake
irin na wancan darenba a yau insha ALLAHU, koda ace zaici galaba a kaina nima saina
ribantu dashi da izinin UBANGIJINA.
Lokacin da naji ya sassauta min riƙon da yaymin yana shirin hawa kaina saina
samu damar bada dukkan ƙarfina da yazomin daga mahaliccina wajen ƙoƙarin son
tureshi, sam hakan bamai sauƙine a gareni, dan da alama ba ƙaramin mutum bane,
danni sam kusani bana kawoshi a jerin aljanu, inada tabbacin mutum ne tamkar ni da
rigar shaiɗanu. Wata sassanyar dariya maicin rai da nuna tsantsar mugunta da
bushewar zuciya ya saki, tare da komawa gefena ya kwanta da faɗin, “Bara na baki
damarki, kafin nai yaga-yaga dake yanda bazaki taɓa ganuwaba a safiyar gobe, na
kula tausayin banza nake miki, tsaurin idonki yayi matuƙar yawa yarinyarnan”. Ya
ƙare maganar da cire abinda ya ɗauremin bakina. Kukan zuci nake da babu hawaye ina
kai masa du

ka ta ko ina da masa gargaɗi cikin zafin rai, “Karka cutar dani dan ALLAH, minai
maka kake ƙoƙarin ɓatamin rayuwa?, kaji tausayin maraicina dan ALLAH, kobaka tsoron
mahaliccinka ne? ina buƙatar zuwa da martabata gidan mijina tamkar kowacce mace mai
mutunci, idan ka ketamin haddi wlhy ALLAH bazai barkaba, zan ƙare rayuwata ne wajen
jifanka da munanan addu'oin da koka samu cikar burin naka saiya zame maka musiba,
mugu azzalumi, ALLAH ya gagauta tona asirinka dama kosu waye kuke aikatama ƴaƴan
mutane ɓarna, ALLAH ya ruguzaku sheɗanu, insha ALLAHU wutar jahannamace makomarku
inhar baku tuba kun koma ga ALLAH ba tare da neman yafiyar bayin da kuke cutarwa,
la'anannu masu ado da rigar musulunci suna cin dunduniyar bayin ALLAH, insha ALLAH
bazaka cika burin nan nakaba koda kuwa kasamu nasara a kaina.........
Shiiiiii!!!! Ya faɗa yana dannemin baki tare da birkiceni ƙasa ya fallamin
wani gigitaccen marin da komaina yay tsaye cak na wucin gadi kafin na ƙwalla ƙara,
yasa hannu ya dannemin baki tare da kaina da azabar ƙarfi, kiciniya na fara dan
harda hancina ya haɗa gaba ɗaya, tako ina yakushinsa nake dukda babu farce a
hannuna sosai, hannunane ya sauka akan wuyansa, jin wani abu a ɗaure kamar sarƙan
bit na samu damar fincikarsa da masifar ƙarfi saboda fita a hayyacina da nayi
lokacin da numfashina ke gab da barin jikina................✍

Ƴan WhatsApp kuma ga naku saƙon, gaisuwa da fatan alkairi gareku baki ɗaya. Saura
kuma yau naji wani yacema Yah Qaseem ko Dad kwarto🙄🚴🏼🚴🏼😍😍😍😘😘😘😍😍.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

✍🏻
[12/4/2020, 6:12 PM] HASNA : Billyn Abdul:
Page 22

...............“Bazai yuwuba, Ka gaggauta fita!! Ka gaggauta fita!!!” na jiyo wata


murya mai amo sama-sama tana amsa kuwwa a cikin ɗakin lokacin da numfashin ke gab
da barin gangar jikina. Daga haka ban sake fahimtar komaiba dake a cikin duniya sai
wayar gari nai na ganni kwance a ɗakin Momy.
A hankali na shiga buɗe idanuna da sukaimin nauyi, na shiga bin ɗakin da
kallo daki-daki, dan bamma fahimci inda nakeba da farko saboda zan iya irga
shigowata ɗakin Momy a tsawon zama gidan, da ƙyar na tashi zaune ina sake mamakin
abinda ya kawo ni nan ɗin, hakan yayi dai-dai da shigowar Momy ɗakin.
“Yauwa kin tashi Bilkisu?”. Kaina na ɗaga mata a hankali, saboda jikina
yaymin wani masifar nauyo, na buɗe baki da ƙyar nace, “Momy miya faru na ganni
anan?”. Hankalinta nakan ciro abu a cikin drawer ta bani amsa, “Za'a gaya miki daga
baya, tashi kije ɗakinki kiyi wanka”. Da “to” kawai na amsa mata na sauka jikina
duk yana wani masifar ciwo, ga tunani fal raina, wani abin mamakinma na sake
tararwa a folon ƙasa, dan kuwa cike yake da dangin Momy, na gaisar da waɗanda zasu
iya jina na wuce ɗaki kaina na kuma ɗaurewa. Akan gadona dake mugun yamutse na fara
sauke ido, ‘Kowaye yay masa haka kuma?’ na ayyana a cikin raina, dukda banajin
daɗin jikin sai nai tunani bara na fara share ɗakin, gadon na shiga kakkaɓewa,
ƙarar faɗuwar abu naji kamar ƙwandala a ƙasa lokacin dana ɗaga zanin gadon, dube-
dube na fara, sai dai banga komaiba, sharewa nai kawai na gyarashi tsaf, nakoma
shara. A wajen shararne na sharo abinda ya faɗi ɗazun ashe wajen gado ya shige,
Wuri ne kalar ja, sai dai wannan yafi wurin dana sani girma, haka kawai na samu
kaina daƙin maidashi a sharar, saima na jefashi cikin jikkar islamiyya ta dake kusa
dani, na cigaba da sharata. Da ƙyar na kammala aikin na lallaɓa bayi nai wanka,
ganin baƙona ya tafi saina haɗa da wankan tsarki. Ina shiri ina mamakin barcin
danai daga daren jiya zuwa safiyar yau ace bamma farkaba kamar yanda na saba a
lokacin sallar asubahi dukda bana salla, yanzu hakafa sha biyu ma, ni saima yanzu
maganar zuwa aiki tazomin a rai, gaba ɗaya wani iri nakejin kaina tamkar
birkitacciya, wayata na shiga dubawa, sai dai kuma ban gantaba, ƙarasa shirin nai
da tunanin naje ɗakin Momy na duba ko tana can idan na gama. Sallamar Momyn ce ta
kacemin tunani na juya ina kallonta. taci kwalliya cikin rantsatstsen lase ɗan
ubansu sai walƙiya yake, ga gwalagwalai ta zuba a wuya da hannu, taimin murmushi
irin wanda tsahon zamana da ita ban taɓa cin karo da shiba sai yau, “Bilkisu irin
wannan kallo haka” kunya naɗanji, dan haka na murmusa ina mai duƙar da kaina, nace,
“Kinyi ƙyaune Momy”. “To nagode sosai” tafaɗa tana zama a bakin gadona da ajiye
ledan data shigo dashi a hannu. takai dubanta gareni, “Kinga cire waɗannan kayan
waɗanan zaki saka, nasan akwai tambayoyi fal ranki, karki damu zamu baki dukkan
amsoshinsu zuwa dare idan baƙi sun tafi, fatanmu dai kizama maiyin biyayya a garemu
kamar yanda kika saba, batun zuwa aiki kuma yau bazaki jeba”. Shiru nai kawai ina
kallonta, sai kuma nace mata, “To momy, wayata fa?”. Miƙamin tayi tana faɗin “kin
ganta nan, dama anata kirankima kuwa tun ɗazun”. Amsa nayi, itakuma ta miƙe ta
fita. Da kallo na bita kaina na sake ɗaurewa da abubuwan da ban saba ganinsuba sai
a mafarki, ganin ta ɓacema ganina saina sauke nannauyar ajiyar zuciya, wayar na
duba, miss calls kam da yawa harma bansan dawa zan faraba, Yah Qaseem, Ummie,
Amina, harma da Numbers ɗin da bansan na wanene ba, kafin nayi wani yunƙuri kira ya
shigo, sunan Masarauta danai saving ne ya fito ɓaro-ɓaro a jiki, ɗagawa nai muka
gaisa a mutunce kamar ranar, daga ƙarshe take sanarmin bayan an sakko massalaci
zasuzo kawomin cards ɗina, murmushi nayi ina mata godiya, kafin mu yanke wayar.
tunanin yaya zanyi na shigayi, dan yakamata ace koba komai nai musu tarba ta
girmamawa ko badan gidan da suka fitoba, to amma yanda gidannan ke cike ta ina
zanma fara nikam? Wlhy gaba ɗaya yau kaina ya ɗauki zafi, sam tunanina baya tafiya
dai-dai dana sauran mutane. Kasa yin komai daya dace nayi, nai zaune a inda Momy ta
barni, niba

n canja kayan datace ba, bankuma miƙe na nemawa baƙin abinda zasuciba idan sunzo
balle kuma cikina dake Masifaffen ƙugin yunwa kamar zanci babu. Ina a wajen har
ƙarfe ɗaya ta buga, tashi nai jiki a sanyaye na ɗauro alwala, gabana sai wata
iriyar muguwar faɗuwa yake wadda ban taɓa jiba, idan girata ta haggu ta harba sai
ta dama ma ta harba, sai kuma inji wata faɗuwar gaba ta biyo bayansu. Haka nai
sallar azuhur batare dana fahimci abinda nama karanta a sallarba, dan wasu irin
mugayen halittu na rinƙa gani suna zuwa gabana, haka dai na dake raina na cigaba da
sallar inata faman kwarar da zufa tamkar wadda take a cikin ruwan zafi, a sujidar
ƙarshema sai naji wata iriyar muguwar dariya a ɗakin tamkar za'a fasashi, sai kuma
aka fashe da kuka, zuwa can aka kuma saka dariyar datafi ta farko. Na kasa ɗagowa
daga sujidar ma gaba ɗaya tsahon lokaci, saida naji an taɓani ne a baya da magana
kamar muryar Ummie sannan ALLAH ya bani ikon ɗagowa. Shiru naji ɗakin ya ɗauka
sannan bana ganin komai a gabana harna kammala na shafa addu'a. Na sauke idanuna
akan Ummie dake zaune da a bakin gadona tana latsa waya, sai dai na kasa cemata
komai saboda wani irin yanayi da nakejin kaina mai masifar tashin hankali, jina
nake tamkar ana kunnamin garwashin wuta a jiki........
“Bily! Bilyy!!” na tsinkayi muryar Ummie na faɗa tana girgizani. Kallonta
nai na amsa da ƙyar, dan bansanma tazo kainaba, bana gane komai a yanzu bana kuma
fahimtar komai hatta da kaina neman suɓucemin ya keyi. Tace, “Na shiga uku, Bilkisu
lafiya kike kuwa? Wai mike faruwane haka?”. “Ban saniba nima Ummie” nai maganar
hawaye na ziraromin akan kumatu. Kafin ta samu damar jehomin wata tambayar muka
jiyo matsananciyar hayaniya ta kaure illahirin gidan tamkar ana faɗa. Mu duka
kallon ƙofa mukai, hakan yay dai-dai da bugo ƙofar da aunty Shahudah tai hannunta
ɗauke da wuƙa tana kuka.
A tare muka miƙe da Ummie, dan lokaci ɗaya wani ƙarfi yazomin da bansan daga
inaba kuma, ganin kaina tayo da wuƙar saina zaro idanu waje ina faɗin,
“Au...aunt...aunty Shahudah lafiya? kuw....” bankai ga ƙarasawaba ta kawomin suka
tana faɗin, “Wlhy kasheki zanyi, tsinanniya jinin asara jinin masifa, jinin
tsafi....” wani mugun tsalle nai na kauce mata, amma dukda haka saida taɗan yankeni
a damtsen hannuna. Ɗakin ya cika sai ƙoƙarin janyeta ake tana ihu da tabbacin yaufa
ita saita halakani.
Bansan hawaba bansan saukaba kawai naji aunty Aamilah da wasu ƴammata sun
rufeni da duka sukuma, tun ina ƙoƙarin kare kaina harna gaza dan sunfini yawa,
gashi kuma bayan Ummie babu mai yunƙurin karɓata.

Tun Bilkisu na fahimtar abinda ke faruwa harta sume, amma idanunsu ya rufe
bama su fahimci bata numfashiba, haka suka jawota ƙiyyy!! waje har tsakar gida suna
duka, abinda zai baka mamaki babu wanda ya hanasu acikin manyan iyaye irinsu Momy,
suma kansu ruɗanin abinda yazo musu babu zato baisa sun kula da abin ƴaƴansu sukeba
na yunƙurin kisan kai, Ummie ce kawai ke kuka da Amina da mama da suka shigo gidan
saboda jin matsananciyar hayaniyar dake tashi.
Shahudah kuwa tun tana kuka da iƙirarin kashe Bilkisu har itama ta yanke
jiki ta faɗi ƙasa babu numfashi, nanfa gidan ya kuma harmutsewa, babu mai iya
fahimtar yaren wani balle ka samu tabbacin abinda ke faruwa dahar ya kawo wannan
tashin hankalin.

____________________________

Abinda ya faru shine, a daren jiya su Mom sun dawo misalin ƙarfe sha
ɗaya da wasu mintuna sai sukaci karo da wani irin ihu maiban tashin hankali da saka
firgici a gidan, babu wanda bai tsoraba a cikinsu dan Aamilah harda fitsari ta jiƙe
jikinta, sai bayan wasu mintuna komai ya lafa sannan suka fahimci daga ɗakin Bily
wannan ƙara ta fito, sai dai a cikinsu babu wanda ya iya jarumtar shiga ɗakin. Mom
ce ta ɗaga waya ta kira Dad hankalinta a tashe ta sanar masa komai, shima hankalin
nasa a tashe ya tabbatar mata gashinan zuwa gidan dama ya fita rakkiyar su Alhaji
baba ne da sukazo.
Duk wannan ihu yau Yah Qaseem bai jisaba sam, yana ɗakinsa yana barci, saida
Shahudah taje ta tasoshi bisa umarnin Momy. Kafin isowar Dad Yah Qase

em ne ya fara shiga ɗakin, sai ya tadda bily a sume, ga ɗaki a hargitse tamkar anyi
sukuwar salla a cikinsa. Babu wanda abun bai taɓa zuciyarsaba a gidan har Dad daya
iso yanzun, sun shiga yayyafama Bilkisu ruwa amma ko motsi bataiba. sunkuma bi duk
wasu dabaru shima bata farfaɗoba, hakan yasa Dad bada shawarar a maidata ɗakin Mom
ta kwana a can, shikuma zuwa safiya zai ɗauki mataki akan wannan abun dake faruwa.
Daga Aamilah har Shahudah suma a ɗakin Mom suka kwana, da ita kanta Mom ɗin
harma da Dad kansa saboda a firgice suke yaran da Mom. Har ALLAH ya wayi gari
lafiya Bily kam bata dawo hayyacintaba sai kusan ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna ko
nace sha biyu saura na rana.

Abinda ya farunne ya saka Dad yanke shawarar ɗaura auren Bily da Qaseem a
wannan safiya ta juma'a dan kowa ya huta duk da basusan ainahin abindama ake
bibiyar Bilkisu da shiba, ɗari bisa ɗari Mom ta bashi goyon baya. Ana idar da
sallar asuba Dad ya nufi gidan Alhaji baba ya sanar masa halin da ake ciki tare da
neman alfarmar haɗawa dana Shahudah da Jawaad, zuwa bayan salla idan ALLAH ya kaimu
a cewar Dad sai ayi biki su tare. Alhaji baba bai musaba, dan yana fatan jikan nasa
matsalarsa ta zama babu aure tazo ƙarshe. Daga gidan Alhaji baba gidansu Jawaad Dad
ya wuce, a canma sun tattauna dasu Uncle Nasir kafin ai kiran Jawaad dake shirin
tafiya Office.
Koda suka sanar masa shirinsu shima babu musu ya amsa musu, harma amincewar
tasa da gaggawa ya basu ɗunbin mamaki, amma shi saiya fuske abinsa tamkar baiga
mamakin nasuba sam ko bai fahimtaba, ya kuma fiddo kuɗin sadaki a take ya direma
Uncle Nasir har dubu ɗari biyar. Kasa haƙuri kam sukai saida suka tanka akan hakan,
batare daya kallesuba yace ai Alhaji baba ne ya kirasa ya sanar masa kafin su
sukirashi, cikin gamsuwa da maganarsa Dad yace to ya rage kuɗin sunyi yawa, dubu
ɗari sun isa. Murmushi Jay yayi yana wani susar ƙeya, kansa a ƙasa yace, “Karka
damu Dad nariga na fidda kuɗin matsayin sadakin, Uncle kuje dasu wajen ɗaurin auren
kawai please. Albarka suka saka masa tare da sallamarsa, yay musu sallama ya tafi
fuskarsa ɗauke da wani shegen murmushi daya tsayama Uncle Nasir da Dad a ƙahon
zukata. Dad ya dawo gida, yayinda Jay yanufi office ya nema alfarma tare da gayama
Sir Ahmad abinda ake ciki. Sannan ya sanarma su Hafiz ma, sunyi matuƙar mamaki,
amma ganinsa a wani yanayin da suka kasa yima fassara sai basuja zancen da nisaba
suka shiga faɗama mutanensu nanan office da waɗanda suke kusa irinsu Abbati ta
waya.
Maza nata haramar tafiya massallaci, inda daga canne za'a ɗauro auren
bayan idar da sallar juma'a, yayinda ahalin gidansu Momy keta tururuwar zuwa gidan
harma da tsiraru na ɓangarensu Dad kamar su inna Zainabu. Duk wannan abunda ke
faruwa babu sanin bily, tanacan tanata barci abinta.
Massallaci ya cika tab da al'ummar musulmi yara da manya da matasa da tsoffi
harma da mata dakanje sallar juma'a kasancewar wannan ranar ranace ta musamman a
garemu, bayan an idar da sallar juma'a kamar yanda aka saba akai sanarwar ɗaure-
ɗauren aure daza'ayi daban-daban wanda harda nasu Qaseem a ciki. Duk wanda yaga
Qaseem a yau zai tabbatar yana cikin farin ciki, dan kuwa yaci ado da wata ɗanyar
shadda fara ƙal da Dad ya bashi ya sanya, sai walƙiya da walwalin angwanci yakeyi
kamar ka sacesa ka gudu, ga haƙoransa farare tas sun kasa rufuwa. Sai dai nayi iya
dubana da waige-waige bangano ko mai kama da Jawaad ba balle shiɗin kansa, saisu
Aliyu da suma duk suke sanye da shaddoji a yau, da alama dai gida suka koma bayan
zancen ya riskesu suka canja shiri.
An fara ɗaura aure guda biyu da baida alaƙa dasu Dady, kafin a ɗaura wani da
yaso bama kowa mamaki, wato dai Sabira da wani waishi Habib, ankuma roƙi Uncle
Nasir dake kusa ya zama wakilinsu saboda wai wakilan amarya masu isoba har lokacin,
wannan shine ya gogema mutane da yawa abinda ya taɓa musu zukata, ɗaurin aure na
huɗu daya biyo baya shima bashi da alaƙa dasu Qaseem ɗin, saida akai kusan na mutum
uku kafin a ɗaura na Qaseem da Azeema, jikin Qaseem har rawa yake ya miƙe zaiyi
magana amma sai Uncle Uwaisu ya maida

shi ya zaunar yana mai sanar masa bafashi ake nufiba maybe wasune daban, ajiyar
zuciya Qaseem ya sauke dukda dai hankalinsa bai kwantaba, gashi iya dubansa baimaga
Dad a wajenba, bayan kuma tare dashi sukazo masallaci, ɗaurin aure na ƙarshe baki
ɗaya shine ya tada hankalin dukkan mai alaƙa dashi, wato Jawaad Abdul-aziz da
amaryarsa Bilkisu Adam, Alhaji Baba wakilin amarya Uncle Nasir da yay zaton da
Shahudah ya kasance wakilin Ango, saida aka ambatanefa yaji wasan ya canja salo.
Qaseem yama manta a ina suke, take yanke yaci kwalar imam da masa tambayar yaya
haka ta faru?. Da ƙyar ƴan agaji suka ɓanɓare imam a hannun Yah Qaseem, cikin
tsagwaron tashin hankali Dad da Qaseem ya gaza gani ɗazun a masallacin ya shiga
jeroma imam tambayoyi shima. imam da duk bai fahimcesuba yace shifa a haka aka kawo
masa sunayen anguna da amaren da za'a ɗaurama aure a yau, kuma iyakarsu kenan ya
kammala gama takardar. Yay maganar yana nuna musu.
Ganinfa za'a iya bama hammata iska a massalacine ya saka ƴan agaji sallamar
kowa akace su Dad su fito a shiga inda ya dace ayi magana, sannan ana neman dukkan
angunan da aka ɗaura aurensu ba dai-dai ba.
Yah Qaseem kawai aka gani a cikin anguna, amma babu Jawaad babu Habibu
da aka ɗaurama Shahudah, kuma kowa yayi imanin yaga Jawaad a massallaci kafin a
tada sallah, yanzukam an nemesa ƙasa da sama tamkar allurar mayya an rasa. Kowa
ƙoƙarinsa ya kira wayar Jawaad amma sam taƙi shigama, gefe kuma ana jajen wanene
habib ɗin da aka ɗaurama aure da Shahudah?.

Lokacin da ake waccan dambarwar a lokacinne shikuma Salman ya kira Shahudah


ya sanar mata komai, kafin ya kira Momy itama, yana tsaka da sanar mata abinda ke
faruwa Shahudah ta nufi ɗakin Bilkisu da wuƙar data ɗakko daga kicin tsirara tana
iƙirarin yaufa saita kasheta.

A masallaci komai ya hargitse, imam ya tara dukkanin ƴan agajin


massallacin dake da alhakin rubuta sunayen waɗanan anguna da amare anata jera musu
tambayoyi, dan kuwa dai Dad da kansa shine ya kawo list ɗin farko kuma an tabbatar
yanada banbanci da wanda yake a hannun imam a yanzu. Sudai ƴan agajin dakeda wannan
alhaki sun tabbatar abinda suka gani kenan, sannan kuma ga takardar farko da Dad ya
kawo an samo kuma bata da alaƙa data yanzun. Abun ya ɗaurema kowa kai hatta da imam
ɗin kansa, dan shidai yanada yaƙinin babu yanda za'ai ƴan agajin su bada abinda ba
haka yakeba, dan invitations ake kawo musu na ma'auratan da duk za'a ɗaurama aure a
satin, sukuma saisu rubuta sunayensu a takarda gabaki ɗaya domin samun sauƙi, nasu
Jawaad kuma a rubuce Dad ya kawo tunda ba'a buga invitation card ba abin yazo a
ƙure. TO A INA MATSALAR TAKE?.
Wannan itace tambayar dake a bakin kowa a wajen musamman lokacin da Yah
Qaseem ya yanke jiki ya faɗi a sume shima. Dai-dai kuma da kiran da akaima Dad akan
tashin hankalin dake faruwa a cikin gidansa. Abin tausayi sai kawai Dad ya fashe da
kuka shima yana neman faɗuwar, cikin amincin ALLAH Uncle Sulaiman ya samu damar
tarosa da faɗin, “Haba Alhaji Ali, ka kwantar da hankalinka mana, na tabbata saɓani
aka samu ko kuskure, kuma abune mai sauƙi da nake ganin zamu warwaresa da gaggawa,
Jawaad ya sakima Qaseem matarsa, haka shima wannan da bama asan ko wanenen ba ya
sakema Jawaad matarsa”. Kasa magana Dad yayi, dan babu abinda yake fahimta daga
kalaman Uncle Sulaiman, gaba ɗayama numfashinsa neman barin gangar jikinsa yakeyi.
Shugabannin massallacin dai nata ƙoƙarin binciken tushen wannan matsala da
basu taɓa cin karo da itaba a tsahon rayuwarsu, anɗaura auren da babu adadi a
shekarun wanzuwar massallacin amma hakan bai taɓa faruwaba koda da kuskure kuwa,
babban tashin hankalinsu ma shine wanene Habib da aka ɗaurama Shahudah aure dashi?,
dan kuwa dai an nema wakilan nasama an rasa balleshi kansa, matsalar Qaseem da
Jawaad kam kowa yana ganin tanada mafita tunda su an rigada an sansu gasu kuma ƴan
uwan juna.
Imam da kansa ya gama ɗaukar zafi gaba ɗaya ya cire rawanin kansa yana
sharce gumi da faɗin, “Wannan wace irin matsalace haka? Tayaya za'ace an ɗaura
auren da sam bashi da alaƙa da juna?”. Qaseem shi

ne mijin Bilkisu, an ɗaurama Jawaad, Shahudah itace matar Jawaad an bama Habib,
Habib shine mijin Azeema, an bama Qaseem, Qaseem da Jawaad ahali ɗaya suka fito, a
tare kuma aka kawo sunayensu, to yaya akai shi Habib mai mata azeema suka shiga
cikin wannan sarƙaƙiyar? Idanma ance wajen haɗe sunayen waje ɗayane dan a sauƙaƙama
liman wahala to tayaya abin ya kasance haka? Kenan suk yandama akai aka dawo akwai
saka hanun hadiman masallacin kenan?. hakan bazai kasance mai yuwaba dan gashi
dukkan bincike anyi babu wani baƙon al'amari daya shigo har aka bama imam ainahin
takardar amare da angwayen wannan satin, wadda kuma kowane ɓangare suke nuna ba ita
bace imam yay amfani da ita, kenan dukkan matsalar a yanzu tadawo ta tattarane gama
shi imam ɗin dan kowa shi yake zargi.

★★★★★★

Ganin babu wata mafita anan Alhaji baba ya shawarcesu da tafiya gida
kawai aje a samu nustuwa kafin a fuskanci matsalar cikin kwanciyar hankali a nema
masalaha a kanta.
Kowa yay na'am da batun Alhaji baba, dan haka aka ɗunguma zuwa gidan Dad da
tushen matsalar take.

Isowar motocin su Dad yay dai-dai da isowar motar gidan Sarki Sameer
Saifudden dake ɗauke da ƴaƴansa ƴanmata a ciki, waɗanda suke cikin farin cikin
samun fita yawo a wajen da basu saniba. Babu wanda ya fahimci su wanene su ɗin?,
saboda kowa baya cikin hayyacinsa, ga matsananciyar hayaniyar data fiddo ƴan anguwa
gaba ɗaya dake tashi daga gidan Dad.
Su Amaturrahman da kansu ke a kulle sunbi ayarin masu shiga gidan ganin
shine gidan da Bilkisu ta tura musu address ɗinsa, sai dai gidan a harmutse yake
har basu da damar fahimtar komaima. Isowar su Dad kuma ya sake harmutse gidan
saboda ganin halin da Bilkisu da Shahudah ke ciki, ita kanta Momy bata cikin
hayyacinta, ga Yah Qaseem can an wuce dashi asibiti shima, sai kawai Dad ya yanke
jiki ya faɗi shima ganin ƴaƴan nasa biyu ga Qaseem kwance tamkar sun mutu.
Tashin hankali wanda ba'a saka maka rana kenan ke wanzuwa a wannan lokaci,
a take aka kwashesu su uku aka fita dasu daga gidan zuwa asibiti domin ceto
rayukansu, tuni suma sauran jama'a suka bisu a motoci, ƴan anguwa kuma suka shiga
tattaunawa, danma anguwace ta manya kowa yana harkar dake gabansa babu ruwan wani
da wani, amma a yanda lamarin yazo duk rashin shiga harkar junansu yazama dole a
tattauna.
A wannan kace nace na ƴan anguwa su Amaturrahman suka fahimci wasu
abubuwan, ciki kuwa harda fahimtar wadda sukazo gurintama tana cikin waɗanda aka
fita dasu tamkar gawa daga gidan. Jikinsu a sanyaye suka koma mota driver ya jasu
sukabar anguwar, Safah sai kuka take akan itafa subi suga wane asibiti aka kai
Bilkisu, saida Amaturrahman tai kamar zata bugeta sannan ta nutsu tai musu shiru.

★★★★★

A ɓangaren su Jabeer kuwa tun dambarwar farko ta massallaci suka shiga


ayarin ƴan neman Jawaad, sai dai komai kama dashima basu ganiba, bayan kuma a tare
suka shigo dashi massallacin har aka tada salla, bayan an idarne suka nemesa suka
rasa gaba ɗaya, a lokacin basu kawo komai a ransuba saboda ba'akai ga ɗaura
aurenba, sai bayan an ɗaurane tsoro ya kamasu da tunanin kodai yanada masaniyar
komai, to amma mizaisa yayi hakan kuma? Tunda sunsan halinsa sarai, suk son da
yakema Bilkisu inhar babu wani dalili bazai zama mai aikata wannan abunda dake
faruwaba domin kawai ya aureta, dolene su nemesa domin jin minene ke faruwa? Shine?
Kokuwa shima bai saniba.
Sun fara da station, sai dai bai koma canɗinba kamar yanda kowa ya
tabbatar, sannan gidansuma bai komaba, gidansa dake Abdul-aziz Yusif street nanma
dai baima jeba, gaba ɗaya kuma sai kansu ya kulle ɓam akan komai.
Suna tsaitsaye a ƙofar gidansa na A.Y street ɗin saƙo ya shigo a wayar
Jabeer. Jikinsa har rawa yake ya buɗe saƙon ganin Jawaad ɗinne ya turo.
“Kubar wahal da kanku wajen nemana, zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu zan
bayyana, akwai aikin dana tafi yine, sannan karku zargeni akan abinda ya faru kamar
yanda nasan rashin ganina anjima kaɗan zai ɗarsama wasu daga cikin ahalina, sam
bani da hannu a ciki, akwai ɓoyayyen al'amarin danima ban sanshiba, lokacine ka

wai zai warwareshi. Inason kuyi duk yanda zakuyi kafin nan da awa uku a canjama
Miemaa asibiti, dan nasamu labari yanzunan akwai matsalar data faru gidansu, karku
barta ta kwana a asibitin da aka kaisu, karkuma wanda yasan kun ɗauketa daga
asibitin har Alhaji baba”.
Kallan kallo aka komayi tsakanin Jabeer da Hafiz da Aliyu akan wannan saƙo
na Jawaad da ya kuma ɗaure kansu akan wannan al'marin............✍

Yau dai gashinan na muku words 3700😲 kuci ku ƙoshi har safiyar litinin.😉👌🏼

Barkanku da juma'a, kar a manta da saka bayin ALLAH a addu'a dan ALLAH.

Ƴan facebook kuma ga naku saƙon, gaisuwa da fatan alkairi a gareku a duk duniyar da
kuke.

Asha weekend lafiya my sweet fans, banda taƙaddama kuma.😂😂😘😘😘😍👍🏻👌🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻


✍🏻
[12/7/2020, 11:22 AM] HASNA : Billyn Abdul:
Page 23

...............Tunkan su isa asibiti Dad ya farfaɗo, lokacin kuma da suka iso sun
iske shima Qaseem ya farfaɗo, duk yanda Doctor yaso yayma Qaseem ɗin allurar barci
danya huta yaƙi yarda, hakama Dad bai yarda ko dubashi ayiba, cayay babu damuwa su
barshi. Bilkisu da Shahudah kawai aka shiga bama taimakon gaggawa, wanda daga farko
Momy da catai baza'a duba Bilkisu ba, sai da Dad ya nuna mata ɓacin ransa a fili
sannan ta nutsu, sai dai tanata ƙananun magana akan hakan.
Haka suma sauran family dake harabar asibitin saboda yawan da suke dashi aka
tsaidasu nan kowa nata tofa albarkacin bakinsa, saidai mafi yawan kalamansu suna
ɗora laifinne akan Bilkisu ce tai asiri. Yanda suke jifanta da mugayen kalamai
dolene kaji tausayin Bilkisu, dan zaka ɗauka akan wata uwar mata suke maida yanda
akayin. Hayaniyarsu ce ta saka Uncle Nasir cewa duk su wuce gida domin zamansu anan
ɗin bashi da wani amfani. Badan sunso hakanba sukabi umarninsa.

Motocinsu na cikin fita su Jabeer suka iso asibitin suma domin cika
umarnin Jawaad, mamakine yay masifar kamasu ganin wannan uwar gayya tamkar anan ake
bikin. Shi Hafiz ma abin haushi ya bashi, ya buga tsaki cikin magana ƙasa-ƙasa
yace, “Mutanen nan suna bani mamaki da al'amarinsu, to wannan gayyar kuma ta
miye?”. Aliyu dake jinsa yace, “Kaima dai ka faɗa”.
Fitowa sukai a motar suka isa inda su Uncle Nasir ke tsaitsaye shi da Dad, da
Uncle Sulaiman, sai Qaseem dake zaune cikin mota, Salman kuma yana zaune a saman
motarne yanata latse-latse a waya tamkar baida wata damuwa a duniya. Gaishesu suka
shigayi cikin girmamawa, tare da musu jajen abinda ya faru. Cike da kulawa suma
suka amsa musu, Uncle Sulaiman yace, “Ina Jawaad ɗin shi yake? Tun ɗazun sai neman
wayarsa muke taƙi shiga”. Duk kasa cewa komai sukai, dan kuwa suma dai basusan
amsar daya dace ace sun basuba akan inda Jay yake, tunda suma basu saniba.
Uncle Nasir ya buɗe baki zaiyi magana ya fasa saboda shigowar motar Jawaad
harabar asibitin, duk bin motar sukai da kallo harsu Jabeer, cike da mamaki suka
tsatstsareshi da idanu lokacin daya fito a motar, yana sanye cikin wata dakakkiyar
shadda ƴar ubansu ruwan zuma, sai maiƙo take, sosai ɗinkin ya zauna masa a jiki
cif. Kosu kansu su Uncle Nasir ɗin ya musu ƙyau, dan kafin kaga Jawaad da manyan
kaya akan daɗe saboda yanayin aiki, shiyyasa idan ya saka ɗin sai ya zama na
musamman. Nufowa yay inda suke fuskarsa sam babu walwala, Qaseem da babu wanda ya
lura da fitowarsa a mota yasha gabansa.
Kallonsa kawai Jay ya tsayayi batare daya iya cewa dashi komaiba, cike da
ɓacin rai Qaseem yakai hannu zai shaƙosa, da sauri Jawaad ya ɗaga masa hannu, da
watsa masa wani irin kallo mai razani dake gauraye da ɓacin rai, “Qaseem bani
hanya”. “Anƙi a baka ɗin” Qaseem ya faɗa a zafafe. Jawaad baice komaiba ya
raɓashi zai wuce, sake shan gabansa Qaseem yayi, Jawaad yay wani murmushi mai ciwo
idanunsa na sake ƙanƙancewa tsabar masifar dake cin zuciyarsa, cikin wata irin
muryar data bama Qaseem mamaki Jawaad yace, “Qassem ka riƙe girmanka, banason ka
kaini bangon da zan sakaka dana sani mara amfani”. Kafin Qaseem yace wani Abu Uncle
Sadiq ya ƙaraso wajen. “Ku wane irin shashancine haka kukem mutane anan?”. Jawaad
baice komaiba, sai Qaseem ne ya bama Uncle Sadiq amsa da, “Uncle bazaka ganeba,
wannan yaron munafukine, wlhy ko rantsuwa nai babu kaffara nasan yanada hannu akan
wannan abun daya faru, kuma wlhy dolene ka saki Bilkisu a yau ɗin nan basai
gobeba”. Murmushi Jawaad yay cikin taɓe baki ya raɓasu ya wuce batare da yace
komaiba.
Ƙarasawa yay wajen su Uncle Nasir ya gaishesu, Uncle Nasir yace, “Kaikuwa
ina kaje anta nemanka tun ɗazun Jawaad?”. “Amin afuwa Uncle, naje wani wajene”. “To
amma saika kashe wayarka? Minene amfanin hakan?”. Jawaad dai baice komaiba.
Uncle Uwaisu yace, “Amma dai kasan miya faru a wajen ɗaurin aure ko?”.
Cikin nuna halin ko in kula Jawaad yace, “Uhmmm na sani”. Ran Uncle Nasir a ɓace
yace, “Ka sani? Amma shine dan wulaƙanci katafi wani waje ka barmu da nemanka?”.
Kafin Jawaad yace wani abu Uncle Sadiq yace, “Ya

ya nikam inaga wannan ba maganar nan bace, kamata yay muyi haƙuri yaranan su dawo
cikin hayyacinsu sai ayi maganar a nutse a gida kamar zaifi, sannan kuma mu maida
hankali wajen neman shi wancan angon da aka ɗaurama Shahudah aure dashi da ita
Azeema take kowa”. Duk sunyi na'am da hakan, Jay ya kalli Uncle Nasir a wani
yanayi, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru kawai.

Bayan sallar la'asar su Uncle Nasir suka wuce gida harda Dad da Qaseem
da aka tilastama dole akan yadace suje su watsa ruwa kodan suji ƙarfin jikinsu,
anbar momy kawai wajen Shahudah, Ummie da maman Amina kuma suna tare da Bilkisu,
Jawaad bai shiga duba kowaba a cikinsu.
Suna isa gida ya shige sashensa, wanka yay yasha magani saboda kansa ciwo
yake masa sosai, duk yanda yaso ya kwanta ya huta hakan ya gagara, ya shiga zagaye
bedroom ɗinsa cikin faɗawa wani dogon tunani akan wannan dambarwar da suka wayi
gari da ita yau, tabbas yasan kaso mafi yawa na abinda ya faru, musamman akan
sarƙaƙiyar ɗaurin auren, sai dai akwai wani al'amarin daya ɗaure masa kai sam ya
kasa samun amsa akai, kuma yazama dole ya nemo wannan amsar, Tabbas saiya nemota,
itace zata zama tsanin buɗe masa hanyar fahimtar abinda ya kasa fahimta a yanzu da
duk sauran jama'a ma. Ya sauke numfashi mai zafi tare da kwanciya a kan gadonsa
ƙafafunsa a ƙasa.
Shi da kansa shine ya canja list ɗin ɗaurin aure a masallaci, sai dai
daliline mai ƙarfi ya sakashi aikata hakan, kuma duk wanda zaiji dalilinsa anan
gaba zai tabbatar abinda yayi shine dai-dai kuma shine ya dace, to amma tayaya zai
fahimtar da mutane sukuma su fahimta batare da ya fito da ainahin maganar filiba?.
Wannan tambayar itace keta cin ransa da sukarsa a ƙahon zuciya. Barci ɓarawo shine
ya sacesa a wannan lokacin batare daya shiryama hakanba, bai farkaba sai gab da
magriba, wasu massallatanma har sun fara kiran sallar. Wanka yay a gaggauce yay
shiri cikin ƙanan kaya ya fita riƙe da key ɗin mota da wayoyonsa, mota ya buɗe ya
zubasu sannan ya nufi massallacin ƙofar gidansu sukai sallar magriba.
Koda ya dawo bayan an idar mota ya shiga ya fice daga gidan.

★★★

MASARAUTAR GAGARA BADAU


Koda su Amaturrahman suka iso masarauta sai suka iske gimbiya Munaya
tana sashen mai martaba, haƙura sukai akan idan ta fito saisu sanar mata da duk
abinda ke faruwa. Safah dai batace komaiba, tana ganin yayun nata sun nufi ɗakinsu
ta zare jiki zuwa sashen mai-martaban batare da sun saniba. Sai dai koda ta nema
Jakadiya tai mata iso saitace mata gimbiya na tare da takawa, tasan kuma babu mai
shiga ganinsa inhar yana tare da matansa. Tarbiyyar da su Safah suka tashi ciki
akwai girmama hadiman gidan, dan koda wasa Gimbiya Munaya bata yarda yaranta suce
zasu taka koda bawa na gidan yanda suke soba, tsaye take kan tarbiyyarsu daga ita
har mai martaba da Mommah. Safah sai ta kwantar da kai cike da shagwaɓa tana
lallaɓa jakadiya, harda bata ƙyautar dubu biyar. Baki Jakadiya ta washe, tace, “A
uwar masu gida ai dolene nai miki iso, ammafa inhar basa falon farko to saidai kiyi
haƙuri anjima saiki dawo.
Safah tace, “Na yarda, amma dai ba falon farko kawai ba, dan ALLAH harna
biyu, dan kinsan inhar Ummu na tare da Abbu bazasu zauna a falon farko ba, nikuma
maganace mai muhimmanci zanma Ummu”. Rigimar Safah da Jakadiya ta sani yasa ta
amince zataje har falo na biyun. Safah na nan tsaye a ƙofar ƙatafaren falon mai-
martaba Jakadiya ta shiga domin mata iso. Iyakarta falon farko tai kira ta wayar
landline kamar yanda tsarin Sarki Sameer yake. Munaya ce dake masa tausa ta ɗaga,
cike da girmamawa Jakadiya ta isar da saƙon Safah. Daga can Munaya zata fara faɗa
akan Safah ta jirata saita fito Sarki Sameer yaymata nuni data bari Safah'n tazo,
badan tasoba tabi umarninsa.
Cike da ɗoki Safah ta shiga kamar yanda Jakadiya ta sanar mata anbata
izini, tun daga falon farko har zuwa na uku bata iske kowaba, hakan yasata wucewa
ƙaramin falon da bakowa keda lasisin shigarsaba saisu da iyayensu. Tai sallama a
bakin ƙofa suka amsa mata kafin a bata izinin shiga. Sarki Sameer na kishingiɗe a
ƙasan lallausar daddumar da

aka ƙawata falon da ita, ya zubama ɗiyar tasa da bazata gaza shekaru sha uku ba ido
yana murmushi, itama murmushi take masa tana satar kallon Ummu dake zuba mata
harara ta gefen ido. Ganin tayi tsaye taƙi ƙarasowa garesu mai-martaba yakai
dubansa ga gimbiya Munaya, hannu yakai yanda Safah bazata ganiba ya Mintsineta,
gimbiya Munaya ta ɓata fuska irin taji zafinnan, gira ɗaya ya ɗaga mata yana
murmushi da cewar, “Kin tsaremin yarinya da ido takasa ƙarasowa, Ummuna kinga zo
naji mike tafe dake?”. Da sanɗa Safah ta raɓa gefe taje ga mai-martaba daya tashi
zaune sosai, hannunta ya kamo ya zaunar da ita kusa dashi. Safah akwai shagwaɓa da
ƙulafucin iyaye, gashi tsiwarta data gada ga Munaya yasa Sarki Sameer ke tsananin
sonta sosai, danshi idan tana abu Munaya kawai yake gani a zamanin ƙurciya. A
jikinsa ta lafe tana kumbura fuska, cikin raɗa tace, “Abbu dan ALLAH kacema Ummu
tabar hararata ni tsoron idanunta nakeyi, kumafa abu mai muhimmanci zan faɗa”.
Murmushi mai-martaba yayi, ya maida dubansa ga Ummu data tsume fuska. “Ummu Please
kiɗan saki fuska mana, kinga dai tsoron idanunki mukeji”. Yanda yay maganar cikin
marairaice fuska ya sakata yin murmushi ta ɗauke kanta daga garesu.
Safah ta gyara zama ganin Ummu tabar harararta tace, “Abbu kasan miya faru a
inda mukaje kuwa?”. “Saikin faɗa Ummuna”. duk abinda suka iske na rikici a gidansu
Bilkisu shi Safah ta zauna tsaf ta zayyanema mai-martaba da Ummu, sosai abin ya
basu mamaki, sai dai basuce komai akan batunba Ummu tace, “Tunda kin gama faɗa
tashi kije idan na fito zanyi magana dasu Amaturrahman”. Sosai Safah ta kumbura
harda hawaye, tace, “Abbu kajifa ni bandani za'ayi maganar bayan aunty nace”.
Murmushi takawa yay yana mai girgiza kansa, ya shafa kanta yana faɗin, “Ai dolenema
ayi magana da magajiyar Ummu, bayan ma kece kika kawo zancen”. Cikin ɗoki tace,
“Yauwa Abbunmu shiyyasa nake sonka, bara naje na faɗama Mommah itama”. Kafin wani
cikinsu yay magana ta fice da gudunta.
Ummu tace, “ALLAH dai ya shiryeki Safah, nikam bansan irinkiba”. Murmushi
takawa yay tare da ɗora kansa saman cinyarta, yakai hannu ya shafi kumatunta yana
mai lumshe idanu, “Dukfa rawan kan Safah a wajenki ta gada, kinsan kawai dai shi
ɗan gado idan ya gaji abu saiya zarta mai shine”. Murmushi gimbiya Munaya tayi
itama tana shafa kansa, tace, “Kaikuma gashi baka mantuwa yallaɓai”. Sosai ya buɗe
idanunsa a kanta yana mata wani sassanyan kallo, cije lips ɗinsa da yay tare dayin
ƙasa-ƙasa da murya kamar mai tsoron ajisu yace, “Yallaɓiya ai Sameer bai cancanci
mantawa da ƙuruciyarki ba, kin bani wahalafa da yawa madam”. “Kamar yanda nima ka
baniba”. Dariya sukayi a tare. Saida suka tsagaita takawa ya tashi zaune sosai
idanunsa akan gimbiyar tashi. Yace, “Ban fahimci zancen Safah ba, mike faruwane?”.
Cikin nutsuwa gimbiya munaya ta zayyane masa komai akan farkon haɗuwar Bilkisu dasu
Safah ɗin a wajen Saloon ɗinta, har tafiyarsu yau domin kaimata l'd cards ɗin da
Safah ta zama sanadin ɗakkosu. Shiru baice komaiba tsahon wasu mintuna, itama Ummu
bata sake cewa komaiba. Harma ta sakin zancen sai y jeho mata tambaya akai “Toke
yanzu mi kika fahimta a zancen nata kenan?”. “Eh to inason nasamu ƙarin bayani
wajensu Amaturrahman ne, daga nan sainaga idan maganar nada muhimmancin da zamu
shiga ciki, dan na lura a zancen Safah kamar ita yarinyar ba ƴar gidan bace”. Kansa
ya jinjina mata kawai, daga nan suka saki zancen suka cigaba da hirarsu.

_________________________________

Kai tsaye asibiti Jawaad ya nufa, Ummie ta wuce gida tun ɗazun
bayan zuwansu Batool da Jawaad ya kira Ummah babba ɗazun yace taje asibiti ta kwana
a can wajen Bilkisun, babu musu batool ta amsa sukazo tare dasu Ummah suka duba
Shahudah da bilkisu, su su Ummah sai suka koma gida akabar batool din anan, da
Nabeelah ma ta tubure nan zata kwana tana ta hawaye ganin halin da Bilkisu ke ciki,
harda rantsuwar saita rama mata, saida ummah ta lallabata saboda sunyi yawa, kuma
Jawaad tunda ba ita yaceba idan yazo ya sameta tasan kaniyarta zaici ne..
Batool na zaune suna ɗan hira itada maman Amina aka

n abinda ya faru yay knocking ƙofar, a zatonsu Doctor ne ya dawo. Ganin Jawaad ya
saka Batool mamaki, dan cayayma Umma sai da safe zai dawo daga inda yaje, zatai
magana yay saurin saka yatsansa saman baki alamar tai shiru, shirun kuwa tayi. Ya
gaida Maman Amina cikin girmamawa dan dama sunsan juna tun lokacin da take aiki
gidansu Shahudah kafin ta barma Amina saboda matsalar ciwon ƙafa data isheta.
Takawa yay zuwa gaban gadon da Bilkisu ke kwance dama tunda ya shigo idanunsa a
kanta yake, baya ganin fuskarta saboda ta juyama ƙofar baya. Cikin dabara maman
Amina ta fita daga ɗakin.
Ta inda bily ta juya fuska Jay ya zagaya, tsaye kawai yay ya zuba mata
manyan idanunsa da sukai jazur da ɓacin rai, tsawon mintuna uku kafin ya kalli
Batool dake tsaye itama tana kallon bilyn. Cikin ɗacin murya yace, “Waye yay mata
wannan dukan?”. Itama Batool muryarta da alamun baƙin ciki ta bashi amsa da cewar,
“Su Aamilah ne akace, inason dan ALLAH kaci uban yarannan Brother, saboda wannan
abin da sukai tsabar cin zaline ai da hauka, yaran gidannan naku sam tarbiyya bata
ishesuba na lura, mtsoww!”.
Baice da Batool komaiba, sai dai yanda fuskarsa ta ƙara tsukewa zakasan lallai
ran ƴan maza sun ɓaci, tsahonsa ya rage tare da ranƙwafowa akan bily da duk batasan
anaiba, yakai hannun damarsa a hankali gefen kumatunta da yafi ko ina kumbura,
motsawa tai tare da yatsine fuska alamar taji zafin taɓawar da yay ɗin, ya sauke
nannauyar ajiyar zuciya yana mai janye hannunnasa. Tsaye ya miƙe idonsa har yanzu
akan Bilkisun yace, “Mi Doctor yace yanzun?”. “Sunyi magana da Ummah, bansan miyace
mataba gaskiya”. Bai sake cewa komaiba ya cigaba da kallon Bilkisu na tsahon
lokaci, kafin ya sauke numfashi da zare hannunsa ɗaya daga aljihun wandonsa ya
ɗauki file ɗin daya gani a drawer gefen gadon, saida yagama dube-dubensa sannan ya
ajiye yay ficewarsa batare da yacema Batool komaiba. Itama da kallo kawai ta bisa,
haka kawai yau takejin matsanancin tausayin ɗan uwan nata da ya kasance shi ɗaya
tilo, babu wa babu ƙani, babu iyaye baki ɗaya sai dangi.

Magana yaje sukai da Doctor, ko kallon ɗakin da aka kwantar da Shahudah


baiyiba yay ficewarsa daga asibitin, daga nan gidan Alhaji baba ya nufa.
Kiraye-kirayen sallar isha'i da akeyine ya sakashi shiga massallaci, saida
aka idar ya shiga gidan. Shima Alhaji baban shigowarsa kenan babu jimawa, Jawaad ya
zauna ya gaishesa, amsawa Alhaji baba yay idonsa akan jikam nasa. fuskar Alhaji a
ɗaure baba yace, “Daga ina?”. Batare da Jawaad ya kallesaba yace, “Gida”. “Ɗazun
kumafa da akaita nemanka a wajen ɗaurin aure?”. “Aiki naje”. Alhaji baba yace,
“Humm aiki? Kenan bakasan miya faru a wajen ɗaurin aureba ma?”. Kan Jawaad a ƙasa
dan yaƙi yarda su haɗa ido da kakan nasa yace, “Na sani, ninema na canja list ɗin
ai”. Idanu Alhaji baba ya ɗago daga littafin addu'oin dake hannunsa ya kafe Jawaad
ɗin da kallo, cikin sake ɗaure fuska yace, “Ai nasan bazai wuce kaiɗinbane daman,
miyasa kai hakan?”. Kallonsa Jawaad ya ɗago yayi sai kuma ya ɗauke kansa yana wani
ɓata fuska, dama yasan ko kowa bai gano shi bane da wuri Alhaji baba sai ya gane.
Alhaji baba yay ƙwafa yana maida kansa ga littafin da faɗin, “A
hatsabibancinka dana sani hakan ƙaramin abune a gareka Jawaad, amma ince tun randa
mukaje gidan Alhaji Ali akan maganarnan ya tabbatar mana da ɗansa zai aurama
yarinyarnan kace ka haƙura?”. “Hakane baba, kamar yanda na faɗa a gabanku na haƙura
na barmasa da gasken na haƙuran, sai dai kuma dalilin daya biyo bayane yasa na
canja shawara”. Ran Alhaji baba ya fara ɓaci, dan haka cikin zafi yace, “Kasan zan
iya saɓa maka ko Muhammad? Har wane irin banzan dalili ka riƙe da bazakazo ka
sanar minba kafin ka yanke masa hukunci? Banason wannan shegen taurin kan nakafa
kaima ka sani”. Sosai idanun Jawaad suka sake kaɗawa sukai jajur, jijiyar kansa
dukta fito ruɗu-ruɗu, yasan duk sanda zaiyi abu saiya zo ya sanarma Alhaji baba,
dan a halin yanzu shine kawai ke iya nuna masa ɓacin rai idan ya aikata ba dai-
daiba kuma ya tsawatar masa akan ya kiyaye gaba, to amma akan wannan shi kansa
baisan miyasa zuciyar

sa taƙi aminta da ya nema sharar kowaba akan batun har sai bayan ya
aiwatar..........
“Ina maka magana ka tafi tunani”. Jawaad da maganar Alhaji baba ta maido
hayyacinsa yay ajiyar zuciya, cikin sanyin murya yace, “Nayi laifi kayi haƙuri,
amma zuwa nan gaba kaɗan zaka fahimci hakan danai shine dai-dai baba......”
“Dai-dai ɗin ƙaniyarka, ka sakar musu yarinya ta auri wanda suka zaɓa mata,
shikuma wancan habibun halan shima kaine ka kawosu shi da Azeemar? Tunda kasan har
cikin ranka bakason maida yarinyarnan miyasa ka amincemin zaka maidatan?”.
“Baba nifa bani na kawosuba, su Uncle Nasir pretending kawai suke akan
maganar suma, dan sunsan wacece Azeema, tunda da saninsu aka ƙulla aurama shi
Qaseem ɗin ita, sannan sakin yarinyar zai zama babban kuskurene, akwai wani abu da
suke ɓoyewa akan yarinyar, ka bani damar bincikosa sanan, na yarda inhar nine banda
gaskiya ka ɗauki kowane hukunci”. Shiru Alhaji baba yay yana kallon Jawaad da
nazarin kalamansa a ƙwaƙwalwa, kusan mintuna biyu suna a haka shiru kafin Alhaji
baba ya ɗauke kansa daga kallon Jawaad ɗin ya maida ga littafinsa, “Ka dainamin
ɓoye-ɓoye, ka fito fili kasanar min abinda ke faruwa?”. Ajiyar zuciya Jay ya sauke
da faɗin, “Duk abinda zan faɗa a yanzun zai iya zama kuskuren abinda yake a zahirin
gaskiya ne, nima a yanzu bakomai na saniba baba, sai dai insha ALLAH zan binciko
duk abinda yake a binne nanda ƙanƙanin lokaci insha ALLAHU”. Tsagwaron gaskiya
Alhaji baba ya hango a kalaman Jawaad, hakan yasa bai sake cewa komaiba.
Miƙewa Jay yay ya nufi bedroom ɗin kakan nasa yay kwanciyarsa.
Alhaji baba ya bisa da kallo har saida ya shige, tabbas ya fahimci akwai
abinda Jawaad ke ɓoyewa, kuma da alama yanada alaƙa da Uncles ɗin nasa, bazai matsa
masaba akan sai yaji komai a yau, dan yasan idan yana fushi takura masa akan abu
sake busar masa da zuciya yake, sai dai yasan duk abinda Jawaad ya dage a kansa to
lallai akwai abinda ya hango a cikinsa, shi kansa akwai mafarkan da yake a
kwanakinnan suna damunsa, ya kuma rasa ina suka dosa?, abin mamakin shine kullum
mafarkin maimaita kansa yakeyi, kayi mafarki sau ɗaya sannan ka sake maimaitashi
gobe, har tsahon wasu kwanani dolene kasaka masa alamar tambaya koda kaso tureshi a
ranka. Tsahon lokaci yana zaune a falon yana tunani bai shiga ɗakinba sai kusan sha
ɗaya, lokacin tuni Jawaad yay barcima shi. Shirin barcin yay shima ya hau gadon,
idanu ya tairama Jawaad dake barci fuska a ɗaure alamun cikin ɓacin rai yay barcin,
Alhaji baba ya sauke numfashi tare da shafa kan jikan nasa, a ƙasan ransa yanajin
tausayinsa, gefe kuma yana jin matuƙar tsoron irin hatsabibancin Jawaad da rashin
tsoro, yana tsoron kar wani yay amfani da wannan halayyar tasa ya cutar dashi
wataran. Da waɗanan tunane-tunanen fal ransa yay barci shima.

★★★★★★
Bayan tafiyar Jawaad Maman Amina ta dawo ɗakin, macece ita mai yawan
ibada dama, bata wasa da ibada ko kaɗan, dan haka koda ta dawo saita ɗauro alwala
takoma gefen bilkisu ta zauna a kujera dan ganin wata irin zufa da Bilkisu keyi
mara dalili, gashi sai mutsu-mutsu take kamar wadda aka saka cikin wuta, Batool
kuwa tana gadon mara lafiya ɗaya daya rage a ɗakin tai kwanciyarta itama. Addu'oi
maman Amina taita tofama bilkisu dan zufar ta bata mamaki da tsoro, gashi akwai
fanka a ɗakin tana aiki kuma, bakuma wani uban zafi akeba a garin balle ace, da
alama dai mafarki Bilkisun keyi. Ahankali-ahankali gumin ya fara tsanewa daga
goshin bilkisu, ta koma sauke numfashi ahankali saɓanin da datake yinsa da sauri-
sauri, takuma nutsu waje ɗaya. Tajima tana mata addu'ar har kusan ƙarfe ɗaya kafin
ta miƙe ta shimfiɗa abin salla ta fara nafilfilinta data saba a zaune saboda
ƙafarta bata jimirin tsaiwa.
Wani irin sukur-sukur maman Amina keji a ɗakin, tun tana ɗaukar motse-
motsen da takejin a wasa hartakai ta fara waige-waige, tabbas tanaji a ranta akwai
wani abu a ɗakin da itama bata iya hasasowa ba, tashi tai ta ɗakko jikkarta datazo
asibitin da ita ta ciro Qur'anin da tazo da shi, karatu ta fara cikin suratul
baƙara, sai motsin da takeji ya ƙara ƙarfi, ɗa

ga kan da zatai sai idanunta yaci karo da wata irin halitta mai kama da ƙadangare
yana fitowa daga ƙarƙashin gadon da bilkisu ke kwance, sai dai kuma shi wannan
farine fat tamkar babu jini jikinsa, sannan ƙaton gaske kamar kada ta cikin ruwa,
jikinsa sai wata iriyar muguwar walƙiya yake tamkar ruwan dake kwance cikin teku,
dukda zuciyarta ta girgiza da kallon wannan halitta mai ban tsoro dake nufota sai
bakinta bai daina karanto ayoyin alƙur'anin ba kasancewarta jaruma mai dakakkiyar
zuciya, tsayawa yay cak a tsakkiyar ɗakin batare da ya ƙaraso gareta ba, ya shiga
goga kansa a ƙasan ɗakin kamar wanda ake duka, kafin kuma ya juya bindinsa har gab
da ita ya fuskanci ƙofar fita, da gudu ya fice tamkar an masa umarni. Cigaba tai da
karatunta har lokacin ta gaza ɗauke idanunta daga ƙofar. Sam Batool batasan wainar
da ake toyawaba, barci take kashirɓan, bily ce dai bazamuce ga halin da take
cikiba. Sautin karatun alkur'anin da Mmn Amina keyine ya tada Batool, itama samun
kanta tai da shiga bayi tayo alwala, ta idar kenan ta miƙe tana gyara ɗan kwalinta
zata fito taga wani ƙaton maciji jajur dashi yana silalawa ta Window toilet ɗin zai
fita, ƙara ta ƙwalla tare da fitowa a guje jikinta na masifar rawa. Tazo ta ƙanƙame
maman Amina dake cigaba da karatu dukda hankalinta yayi masifar tashi da ƙarar
Batool ɗin, tanaji a ranta itama wani gamon tai a bayin................✍

Sannu sannu bata hana zuwa saidai a daɗe ba'a zoba. to aljanin daya canja takarda
ya bayyana😂, sai muje zuwa domin jin dalilin Jawaad na canjawar da kuma tayaya ya
canja ɗin, da alama kuma ya fara bankaɗo wani sirrine da zai bamu hasken sanin ina
muka dosa🚴🏼. ALLAH ya daidaita sahun Jawaad akan lokaci😂, bara na fece nidai kafin
ya karyani🚴🏼🚴🏼🚴🏼.

Barkanmu da dawowa, ina fatan kunsha weekend lafiya?.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


✍🏻
[12/9/2020, 4:09 PM] HASNA : Rasheeda Usman:
Page 24

Godiya ta musamman ga UMMINRASHIDA CARE FOUNDATION, saƙo ya iso gareni, ina muku
fatan alkairin nima, tare da godiyan bangirma da jinjina, alkairin ALLAH yakai
gareku aduk inda kuke. Nagode da wannan girmamawa taku a gareni, duk da har yazu
dai bilyn Abdull rarrafe takeyi, Inai muku so irin trillions ɗinnan😍😍😘😘👍🏻

................Jin Alhaji baba ya fara sauke numfashi Jawaad ya buɗe idanu a


hankali, juyi yay domin ya tabbatar barcin baba yay nisa tamkar a cikin barci yake,
shiru baiji Alhaji baba ya motsaba, yay murmushi tare da sauka daga gadon a
hankali, cikin sanɗa ya fito daga bedroom ɗin, a falonma yanayi yana waiwaye harya
fice, gudun matsala yasa yabar motarsa anan ya fice daga gidan baki ɗaya, wayarsa
ya ciro a aljihu ya duba time, sha biyu saura kwata, ya maida wayar a aljihu yana
furzar da iska. Daga gidan zuwa titi babu nisa sosai, hakan yasa ya taka da ƙafa ya
samu napep. Saida suka fara tafiya ya sake fiddo wayarsa ya duba saƙon su Jabeer
daya shigo tun ɗazun, ɗan typing yayi kaɗan ya tura musu cewar gashinan a hanya.
Cikin mintuna kaɗan suka iso gidansa na A.Y, sai dai bai bari sun ƙarasa
gidanba ya sauka, dubu guda ya miƙama mai napep, yana ya tsaya ga canji amma Jawaad
bai saurareshiba yay wucewarsa. Mai napep ya cusa kuɗinsa a aljihu yana faɗin “gaba
ta kaini inma bakasan ka baniba”.
Oho Jawaad baisan yanaiba, tunima ya shige gidan. A falo ya iske su Aliyu,
kowa da hidimar da yakeyi, ya zauna cikin kujera yana faɗin, “Kuyi haƙuri na
rikeku anan ga madams suna jiranku a gida”. Hafiz dake aiki a lap-top yace, “Babu
damuwa ango, yanzu dai mike faruwa?”.
Ajiyar zuciya Jawaad ya sauke yana faɗin, “Akan abinda ya farune yau,
nasan kuma duk a ƙage kuke da sonjin yadda akayi?”.
Hakane boss. Suka faɗa a tare idanunsu na akansa.
Bayansa ya jingina da kujera yana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, cikin ɗacin
murya yace, “Kamar yanda nasan tunaniku na akan nine na canja komai hakane, nayi ne
saboda labari dana samu daga majiya mai ƙarfi akan abinda Momy ta ƙulla ita dasu
mama Atika. A zahiri sun tsaida bikin Qaseem ne da yarinyarnan Miemaa, sai dai a
baɗini sun tanadarma Qaseem mata batare dashi kansa ya saniba. Azeemar da aka ɗaura
aurensa dashi ɗiyace ga Gwaggo Hajarah ƙanwar Momy da suke ɗaki ɗaya”.
Sosai mamaki ya cika zukatan su Jabeer, Hafiz yace, “To amma miyasa sukai
hakan?”.
“Wannan itace amsar da nakeson mu nemo nima Hafiz, har yanzu mamaki baibar
ɗawainiya da zuciyataba akan wannan al'amarin, miyasa zasu aurama Qaseem Azeema
bayan sunsan ga wadda yace yanaso?”. Jabeer yace, “Nidai a nawa ganin kamar dama
basason aurensa da Mami ne, sunsan kuma kosun hanashi bazai hanuba, shine suka zaɓi
bi ta bayan fage su haɗa masa guda biyu, zaɓinsu da kuma nashi zaɓin”. Hafiz yace,
“Maganarka akwai ƙamshin gaskiya Jabeer, to amma idan hakane shi Habib ɗinan miya
kawosa cikin wannan al'amarin, sannan wanene shiɗin kuma?”.
Aliyu datun ɗazun baice komaiba yay ƙwafa, “Ni wlhy kusan kawai minake
saƙawa a wannan lamarin kuwa; Duk kallonsa sukayi suna jiran ƙarin bayani. ya
cigaba da faɗin, “Inagafa su sun tsara al'amarinne akan boss ya auri Shahudah,
Qaseem a bashi Azeema, ita kuma Mami su aura mata Habib ɗin, inhar ba hakanne
tsarinsuba miya kawo shi habib ɗin a zancen tunda alama ta nuna babu matarsa a
cikin list ɗin ɗaurin auren?”. Zaune sosai Jawaad ya tashi idanunsa akan Aliyu,
yace, “Aliy wannan maganar taka haka take, abinda yake cin raina anan inhar hakanne
to kenan shi Dad bai fahimci Mom batason aure Miemaa da Qaseem ba kenan? Kokuwa
shima ta shirya cin dunduniyarsa ne? Tunda ɗiyar ƴar uwarsa ce”. Hafiz yace, “To
nima dai abin yasani wannan hasashen, amma kuma idan mukai dubi da yanda ya tada
hankalinsa bayan faruwar abun harda suma hakan na nufin baisan su Momyn Shahudah
sun shirya hakanba?”.
Shiru duk sukai suna nazarin maganar Hafiz ɗin, Jawaad ya miƙe tsaye hanayensa
duka cikin aljihun wandonsa, kallo ɗaya zakai masa ka fahimci ransa a ɓace yake,
yace, “Basu kaɗai suka shiryaba, hardasu Uncle Nasir, abinda yasa abin ya tsayamin

arai shine, miyasa shi Uncle Nasir zai zama munafuki a tsakaninmu? Shinefa ya
jagorancemu wajen Dad ni da Alhaji baba akan maganar Miemaa ɗin, saboda Ummah ta
matsa akan sai dai Alhaji baba ya nemamin aurenta tare da Hudah kodan hakan ya zama
gargaɗi gareta, kenan yasan shirinsu da Momy, amma kuma ya amsama Alhaji baba cewar
muje muyima Dad ɗin maganar a haɗamin auren Miemaa da Hudah? Sannan sarai yasan
Qaseem an tsaida masa ranar aure da Miemaa! ɗin kuma?”.
“To tabbas kam wannan matsalar daga nan take boss, Uncle Nasir yasan
komai, amma kam bai ƙyautaba, dan nikam ina bala'in ganin girmansa wlhy saboda
yanda ya riƙeka, ashe ba har zuciya bane, wannan wane irin zumincine muke fama
dashi a wannan zamanin?, kaga yanda aka cukurkuɗe abu saboda kawai buƙatun wasu
dason faranta musu, kuma duk idan kaje ka dawo zaka fahimci ita Mami itace akai
shirin sakawa a tsaka mai wuya, miyasa sukaso mata wannan mugun ƙullin to?”.
Duk hankalinsu suka maida ga Jawaad da yay shiru yana nazarin kalaman
Jabeer na ƙarshe akan uncle Nasir da maganar ƙullin da akaso yima Bilkisu. Cikin
son maidosa hankalinsa Hafiz ya zunguresa, kallonsa yay. Hafiz yace, “Mi muke ciki
yanzun? Dan ko game da Mami muna buƙatar bincike mugano gaskiyar maganar Jabeer,
mizaisa suyi shirin cutar da ita?”.
Guntun Murmushi kawai Jawaad yay ya koma cikin kujera ya zana, kwantar da
bayansa a kujeran yana mai lumshe idanunsa, a hankali ya furta, “Wannan shine
dalilin zamanmu anan, dan inaji a raina wannan ƙiyayyar da sukaso nuna mata tawuce
naƙin son aurenta da Qaseem kawai, akwai wani abu da bamu saniba, dan haka inason
sanin anahinma alaƙarta da mutanen gidan”.
Jabeer ya ajiye cokali yana faɗin, “Kamar ta taɓa gayamin Dad yayan
mahaifiyartane ubansu ɗaya, kaga kuwa bazai wuce Momy ta ƙitaba akan ƴan ubancin
dake tsakanin Dad da mamata, sai dai kuma zata iya yiwuwa ɗin akwai wani abu a ƙasa
damu bamu saniba harsai mun bincika tukunna”.
“Kai lamarinfa akwai ɗaurekai, sannan akwai lauje cikin naɗi, aganina
tunda basa sonta da ɗansu su rabasu kawai basai sun zalinceta sun haɗata aure da
wanda bata saniba”. Hafiz yay maganar cikin takaici.
Aliyu yace, “Kai dai bar son zuciya Hafiz, amma harma nawa Mami take da
za'a mata irin wannan muguntar? Yanzu dai boss mikace kai akan batun? Tunda dai
ALLAH yasa ta fita daga tarkonsu, yanzu aikin farko dake gabanmu shine Qaseem da
Shahudah, baƙaramin yaƙi zasuyi a kankaba da Mami tunda. Shin Ka sanar musu kaine
ka canja sunayen ne?”.
Jawaad da duk yake saurarensu cike da nazari yace, “Eh na sanarma Alhaji
baba ɗazun, na nuna masa nine na canja, nakuma saka masa zancen Azeema ciki, na
tabbatar zuwa safiya zai nema su Uncles da maganar, mukuma sai muyi amfani da
wannan damar”.
“Amma Boss baka ganin ka ɗaure kanka da yawa? Taya za'ai ka amshi laifin
kai tsaye bayan bamusan mike a ransuba game da batun?”. .
Muryarsa cike da damuwa yace, “Jabeer hakan shine kawai hanya mai sauƙi da
zamu bama koma waye ƙafa, sannan Bazaka ganeba, rikicin tsohon nan ya wuce dukkan
tunaninka, gara nafito na faɗa masa gaskiyar maganar, harfa ya kafamin sharaɗin
saina saki Miemaa, yanzu dai nagama da matsalarsa”.
Dariya sukayi a tare, cike da tsokana Jabeer yace, “To tsakani da ALLAH
gaskiya Alhaji baba ya faɗa, ka bama Qaseem matarsa”. Banza yayma Jabeer ɗin, ya
miƙe yana kallon agogon hanunsa, “Kunga ɗaya harta wuce, mu tsaida maganar iya
haka, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu nasan Alhaji baba zaisa ai zama akan batun,
anan zan fahimci yaren kowa, daga nan saimu ɗora da abinda ya dace kawai”.
Duk sunyi na'am da jawabinsa, kowa ya miƙe yana tattare kayansa kafin su
fito, Jawaad tare suka tafi da Hafiz zai ajiyeshi gidan Alhaji baba saboda hanyarsa
ce shi, su kuma su Aliyu kowa ya shiga motarsa.

★★★★★

Da sanɗa Jawaad ya shigo bedroom ɗin duk dan karyay motsin da zai tada
Alhaji baba, a bazata yaji yace, “Daga ina?”. Tsam Jawaad yay ya kasa ƙarasawa,
cikin sauke ajiyar zuciya yace, “Nafita akan wani aikine”. Alhaji baba baice
komaiba, hakan yasa Jawaad

nufar toilet dan ya watsa ruwa.

_________________________________

A asibiti kam daƙyar mama ta kwantarma Batool hankali, Cikin sarƙewar


numfashi da tsananin tsoro tai mata bayanin abinda ta gani a toilet, shiru maman
Amina tai tana nazari da haɗa komai a mizanin daya dace, a fili kuma sai tayi
murmushi tana mai girgiza kanta, cikin bama Batool ƙwarin gwiwa ta umarceta akan ta
tashi tai sallarta koma minene ALLAH zaiyi maganinsa. Jiki a sanyaye Batool tabi
umarnin Mama.
Haka suka kusan kwana akan abin salla suna gayama UBANGIJI damuwarsu, gabannin
asuba bilkisu ta farka tana ambaton a bata ruwa. Fita Batool tai ta kira Doctor'n
daya kwana duty, babu jimawa suka dawo tare. saida ya tabbatar babu wata matsala
tare da Bilkisun sannan yace su bata ruwan tasha.
Tunda ta kafa kai a babban goran ruwan da Batool ta saka mata a baki sai
da ta shanyesa tas sannan ta ɗauke kanta, dukansu kallon mamaki suke mata hatta da
Doctor ɗin kansa, sai dai babu wanda yace komai.
murya a sanyaye tace, “Mama zanyi sallah”.
Taimaka mata batool tai ta sakko a gadon, mama ta rakasu har toilet ɗin ta
sirkama bilkisu ruwan wanka da ruwan dake cikin flask, fita batool tai, mama ta
taimakama bilkisu tai waka da gasa jikinta dukda tana ta noƙewa saboda kunya. Itako
mama sai tayi kamarma bata gantaba. Bikisu taji daɗin wankan sosai, takumaji
karifin jikinta, sallolin dake kanta ta shiga ramawa harda sallar zuhur ɗin jiya
data tabbatar batayita cikin nutsuwaba.

★★★★★★

Zuwa 10:30am na safe dukkan mai alhakin tofa albarkacin baki akan
wannan matsalar ya hallara a gidan Dady, bisa umarnin Alhaji baba daya buƙaci
hakan, dan yanason jin gaskiyar magan akan abinda Jawaad ya faɗa masa gameda zancen
Azeema da yace sunsani. Jawaad yana jerin waɗanda sukazo a farko-farko dan tare
yake da Alhaji baba, hakan kuwa yaso bama kowa mamaki dan sunsan halinsa sarai da
iya ƙin zuwa wajen meeting akan lokaci saiya gama shanya jama'a, amma yau abin
mamaki sai gashi cikin masu sakkon zuwa.
Bayan isowar Imam da wasu daga cikin manyan massallacin da aka ɗaura
auren Salman da Qaseem daya rame sosai tamkar wanda ya kwana biyu yana jiyya suka
shigo suma, ya ƙara haske da tsayi abin tausayi, Jawaad dai baiko kalli inda Qaseem
yakeba, amma shi Qaseem sai binsa yake da wani irin mugun kallo tunda suka shigo.
Imam ne ya buɗe taro da addu'a, a kuma dai-dai lokacinne Shahudah da Mom da
suka taho daga asibiti bisa matsawar Shahudahn suka shigo suma, wajen zama suka
samu idon Shahudah akan Jawaad tana mai kwarar da hawaye, itama harta rame kwana
ɗaya kacal. Bayan imam ya kammala addu'oi ya ɗaura bayani da cewar, “Nasan kowa
dake nan yana neman amsar tambayarsane a gareni, wadda yinin jiya har zuwa dare na
ɓata lokacine wajen nemota nima amma har safiyar yau ban samo amsarba, narasa
wannan wane irin cuɗaɗɗen al'amarine mai sarƙaƙiya, a hasashena har junnu saida na
kawo dukda bani da tabbacin haka balle hujja, ban saniba shin ko a cikinku wani
nada amsar da nima nake cikin ruɗani da bulayin nemanta?”.
Shiru falon yayi babu wanda ya iyayin koda tari, sai shashshekar kukan
Shahudah kawai ke tashi. Uncle Nasir ne yay ƙarfin halin bama Shahudah umarni akan
ta tashi ta fita. kafaɗa ta maƙe alamar bazata tashinba, ta koma jikin Momy ta lafe
tana masa kallon harara dukda kasancewarsa wan uwarta. Babu wanda ya iya sake cewa
komai game da tashin Shahudah, dan kuwa anga iyayenta basu tankaba alamar basu da
damuwa da zaman nata su. Jawaad yay gyaran muryar da kowa ya maida hankali kansa,
batare da ya kalli kowaba yace, “Imam kayi haƙuri, babu ta inda zaka iya samo amsar
sarƙaƙiyar jiya kaida duk wanda keda alhakin sanin sirrin massallacin nan. Ni dasu
Momy mune kawai masu wannan amsar, dukda inada tabbaci da yaƙinin bayanmu wasu
sunsan komai koda ba duka ba”. kaf falon babu wanda bai sagade yana kallon Jawaad
ba, yayinda Momy ta miƙe zumbur tana nunashi, “Amma kai dai Jawaad anyi shaiɗanin
yaro, a gidan ubanwa nake da amsar? Ni dama tun jiya da akace an nemeka an rasa
nasan kaine shaiɗanin daya dace a nema dukka

n amsoshinnan a wajenka.......”
Murmushi Jay yayi, sai dai baice komaiba, hasalima kansa a duƙe yake bai
kalli kowaba har yanzun. Alhaji baba ne ya tsaida Momy jin tanata aibanta masa
jika, “A'ishatu, inaga mubashi dama muji ina maganganunsa suka dosa kafin mu yanke
hukunci koda na furucin bakine, mudukanmu nan a ƙage muke dason jin amsa, yakamata
muji yaya akai aka kwana a ragaya bayan munsan shirinmu a tandun mai ne”. Magana
Momy zata sakeyi Qaseem yace, “Momy Please ki zauna miji munafurcin dazai faɗa”.
Ƙwafa Momy tayi ta koma ta zauna saboda gargaɗin da Uncle Uwaisu yay mata da idanu.
Shirun da akaine ya saka Jawaad ɗagowa, yace, “Inaga kafin warware dukkan
sarƙaƙiyar massallaci yakama musan wacece Azeema da aka ɗaurama Qaseem aure da ita?
Domin wannan shine kawai zai zama mabuɗin buɗe mana gaskiyar abinda muke son sani
baki ɗaya”. Tsit falon yay saboda bugawar da zukatansu sukai a lokaci ɗaya babu
zato ko tsammani da zuwa furucin Jawaad ɗin a garesu. Alhaji baba ya katse shirun
da cewar, “Banda abunka Muhammad Jawaad muma ai duk amsar da muke nema kenan akan
Habib da Azeema?”.
Jawaad yace, “Hakane Alhaji baba, amma ina ganin karmu jata da nisa, domin
su Uncle duk sunsan wacece Azeema da Habib, idan ka cire Imam da jama'arsa, kai da
Uncle Sulaiman, Uncle Sadiq, Qaseem, kune kaɗai kuke neman ƙarin bayani”. Uncle
Sulaiman yace, “To mukam saiku amsa mana kunata sake dilmiyar damu a hasashe”.
Fuskar Uncle Nasir a matuƙar ɗaure cikin kafe Jawaad da idanu yace, “Mikake nufi da
waɗanan kalaman naka?”.
Jawaad yace, “Babu abinda nake nufi Uncle, kawai dai ina son kowa ya
fahimci daga ina matsalar take harshi Qaseem ɗin da aka ɗaurama aure.......”
Cike da masifa Momy ta sake katse Jawaad da faɗin, “Inma wani munafurci ka
ƙulla kai zai ƙaremawa, inace dai sokake kace mune muka haɗa auren Azeema da Qaseem
batare daya saniba, to ai mun isane, yarinyar da ya kawo yanason zai aura batai
manaba, tayaya idan shi baisan ciwon kansaba mu zamu biye masa duk muzama
mahaukatan?”.
Cikin ɓacin rai Jay yace, “Amma miyasa ni da nazo neman a bani na aura
kukace Qaseem shi zai aureta?”. Yanzukam tamkar Momy zata mari Jawaad ta bashi amsa
a matuƙar zafafe “Saboda Shahudah tafi ƙarfin yin kishi da ita, bandama rashin
mutunci da raini irin naka Jawaad, bakaji kunyar zuwa a gaban idanunmuba kace mu
haɗa maka ƴar cikinmu da wadda mukema alfarma mu aura maka”. Sosai zuciyar Jawaad
take sake hasala, sai dai ƙoƙarin dannewa yake dan koba komai Momy yayar mahaifinsa
ce ita, cikin ƙoƙarin danne fushinsa yace, “Amma Momy dan kawai baƙwa ɓuƙatar
marainiyar ALLAH ta jingini da jininku sai kuje ku biya wani kuɗi dan ya aureta
bayan kunsan shiɗin ba mutumin kirki baneba? Wai shin nawa ita wannan duniyar take
da har muke tunanin wanda muka tseramawa bazai taɓa taddomu ba? Baƙwason ta auri
ɗanku, baƙwason tayi kishi da ƴarku, tominene fa'idar biyan wani ya aureta? Saiku
barta ALLAH ya kawo mata wani mijin, shi kuma Qaseem ku sanar masa bakwason
alaƙarsa da ita bawai saikun cutar da itaba ta hanyar da batajiba bata
ganiba.......”
Qaseem ya miƙe a fusace zaiyi magana Uncle Sulaiman da baƙin ciki ya
lulluɓe yay saurin katseshi daga shi har Jawaad ɗin, yace “Kai Qaseem kaga zauna,
ku kuma Kunga kudaina mana magana a cuɗe daga kai har Humaira, shin minene ya
faru?”.
Sosai zuwa yanzu fushin Jawaad ya kasa dannuwa, cikin zafin zuciya da
kowa yasanshi da ita idan aka kaisa bango yace, “Wato Uncle yarinyace suke riƙo a
gidansu, har takai maganar aure ya shiga tsakaninta da Qaseem, kuma sune suka
amince masa, amma kuma sai suka koma ta bayan fage suka nema masa auren Azeemar
gwaggo Hajarah. Bayan kuma Alhaji baba yaje akan su bani auren yarinyar amma suka
nuna min cewar shi Qaseem ɗinne zai aureta. Abinda kuma zai baka mamaki ita kuma
yarinyar suka samu wani da sam ba mutumin kirki bane suka biyashi akan zasu aura
masa ita yarinyar batare datasan da shirinsu ba, kuma sun nuna masa duk badaƙalar
da za'ayi karya sake ya saketa, wannan shine dalilin dayasa na koma nima ta hanyar
da sukabi na canja nasu shirin

da nawa, tabbas nine na canja takardar da akaba Imam da tawa a lokacin da yake
ƙoƙarin shiga massallaci.. Bayan duk an kawomin bayanai akan shirin da sukai na
cutar da yarinyar saina shiga nazarin neman hanyar daya dace na hana faruwar
mummunan ƙudirinsu, a kaf hanyar danake gani zata zama yarinyar za'a sake cutarwa,
dan haka daga ƙarshe sai na yanke shawarar bin hanyar da suma sukabi, wato ta
ƙarƙashin ƙasa. Imam idan har baka mantaba bayan isowarka massallaci wani yazo ya
sameka akan batun wani aure, har ya roƙi afuwa akan rashin kawowa da wuri, kaikuma
ka amshi uzirinsa tare da bashi takardar list ɗin sunayen waɗanda za'a ɗaurama aure
a ranar kace ya rubuta sunayen waɗanda yazo dasu a gurin, to ba kowa bane face ni,
da wannan damar nai amfani na canja takardarma baki ɗaya bayan na kwafe sunayen
dake can nakuma canja namu a yanda naso”.
Salati manyan suka sanya da wannan al'amari, yayinda Cikin ƙaraji Qaseem
yace, “ Momy!!!, mikuke nufi da hakan da kukayi to? Minai muku da zafi haka kuka
zaɓi zalintata ni da Bilkisu?!, to wlhy, na rantse da ALLAH, ku kwana da
sanin...........” da sauri Momy ta rufe masa baki, sauran ƙarfinsa da wanda
ɓacinrai ya kawo masa yanzu ya tattara ya hankaɗe Momy gefe ta faɗi. Jawaad ne yay
saurin miƙewa yana faɗin, “Qaseem minene haka? Baka da hankaline?”.
“Eh bani dashi kaikuma? Idan kai haƙuri kaima ina tafe kanka, garama kayi
gaggawar sakarmin mata kafin kanema numfashinka a ƙirji ka rasa”.
Wani banzan kallo Jawaad yay masa, kafin ya bashi amsa Shahudah ta katsesu da
jehoma duk wanda ke falon tambaya cike da rashin kunya. “Kai broth kamaji munafukan
da suka ƙulla maka naka makircin, nikuma saiku faɗamin wanene Habib yake koma wane
oho muku, kaikuma Bb kai gaggawar sakin waccan ƴar iskar yarinyar tamaje ta auri
Uban Qaseem a yanzu wannan bai dameniba dan kaina kawai na sani, gwarama kowa yasan
abinda zanyi sai yafi naka ɗaga hankalin kowa dake gidanan wlhy”.
Jin komai ya warware Imam da tawagarsa suka miƙe domin tafiya, a ganinsu
wannan matsalace ta cikin gida, sukam tunda sun fita gara su kama gabansu. Godiya
su Alhaji baba sukai musu sannan suka fice.
A take falon ya kaure da hayaniya har babu maijin maganar ɗan uwansa,
Jawaad na shirin ficewarsa Shahudah dake kuka tana zubama mutane rashin kunya tai
saurin riƙoshi, “Wlhy bazaka fitaba saika saki tsinanniyarnan bb”. Bai tanka
mataba, sannan kuma bai juyoba, sai ƙoƙarin fisgar jikinsa da yay zai fice abinsa.
Ƙara Shahudah ta ƙwalla wadda ta dawo da duk hankalin ƴan falon kansu, sosai ran
Jawaad ke tafasa, ji yake badan wani daliliba da sai yayma Hudah dukan mutuwa yau,
saida kuma shi a tsarinsa babu bugun mace. Alhaji babane yace, “Jawaad dawo ka
zauna”. Umarnin Alhaji baba yabi, ya juyo tare da zubama Shahudah wani mugun kallo
daya sakata sakar masa riga ta durƙushe a wajen tana kuka, kota kanta baibi ba ya
koma inda ya taso ya zauna. Ran Alhaji baba a ɓace yace, “Wanene Habib ɗin to
dakasa ya aurar musu yarinya?”.
Shima Jawaad ɗin ran nasa a ɓace yake, amma dai sai ya danne cikin
ladabtaccen harshe ya bama kakan nasa amsa, “Alhaji baba shine wanda suka biya ya
auri yarinyar”.
Kuka Momy ta saka mai ƙarfima kuwa tana zagin Jawaad da ja masa ALLAH ya isa.
Cikin rawar baki Uncle Nasir ke faɗin, “Yanzu nan Jawaad ɗan fir'auna ka
aurama Shahudahr?.........”
Uncle Sadiq yace, “Wane irin sunane haka kuma Yayah?”. Kasa magana Uncle
Nasir.
Dad kam ai hawaye kawai yakeyi kashirɓan, saboda wani irin ruɗani da
wautarsa akan sakarma Momy ragamar gidansa yake hangowa. Falon yay tsit kowa na
jiran ƙarin bayani daga garesu, yayinda Shahudah dake jikin Momy keta ribzar kuka.
Qaseem kansa kawai ya dafe saboda tafasar da zuciyarsa ke masa da matsananciyar
ƙuna.
Kowa dai ya fahimci su Mom sune suka gina ramin mugunta wa marainiyar
ALLAH daga ƙarshe ya rufta dasu batare dasun fargaba, Alhaji baba ya katse shirun
da faɗin, “Bin ƙwaƙwƙwafin komai a yanda yake baida amfani, tunda su bamusan
manufarsu ba, a ganina yanzu mafita kawai ya dace mu nema kamardai....”
Qaseem ya

ɗago kai, cikin ɗacin rai yace, “Mafita itace wannan yaron ya sakarmin mata
tunkafin rayuka suyi ɓacin da yafi na yanzu”.
Miƙewa Jawaad yay cike da takun ƙasaita ya ƙarasa gaban Qaseem sunama juna
kalon kallo tamkar wasu zakuna, baki ya taɓe yana binsa da wani banzan kallo, cikin
kakkausan furuci yace, “Gurɓataccen tunani kenan Qaseem, domin kuwa wannan shine
abinda bazai taɓa faruwaba koda a cikin mafarki, kayi wani tunanin amma ba
wannanba” Yaƙare maganar da ɗan buga kafaɗar Qaseem ya raɓashi ya fice daga falon.

Babu wanda ya iya yunƙurin hana Jawaad ɗin fita har Alhaji baba, dan a
ganinsu garama ya tafi kar abin ya kuma ƙwaɓewa tsakaninsa da Qaseem. Asibiti
Jawaad ya nufa domin ganin yaya su Bilkisu suka tashi. Saida ya tsaya ya sai
abubuwa a hanya dukda yasan za'a kai abinci daga gidan Ummah, mintuna kaɗan ya
shigo asibitin, da Nabeelah yaci karo ta fito sayama Ummah kati, ta amshi kayan
hannunsa tana masa sannu da zuwa da gaishesa. Bai amsaba saboda waya yakeyi, hannu
kawai ya ɗaga mata yay gaba, tabi bayansa tana gulmarsa a zuciya batare daya
saniba, hardasu kwaikwayon tafiyarsa.
A ƙofar ɗakin ya tsaya yayma Nabeelah nuni akan ta shiga domin sanar
dasu. Da “to” ta amsa, shikuma ya cigaba da wayarsa a nutse, baifi minti biyu da
shigartaba tafito tace ya shigo.............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

✍🏻
[12/10/2020, 1:40 PM] HASNA : Billyn Abdul:
Page 25

.............Na daɗe banji irin wannan matsanancin bugun zuciyarba idan na samu
kusanci dashi.
Tunda Nabeelah ta sanar da shigowarsa duk sai na nema nutsuwata na rasa,
farfesun da Ummah ma ta tsareni naci sai naji ya fitarmin a rai, ƙasa-ƙasa nake
kallon ƙofar ta gefen ido harya shigo da sallama, Sanye yake cikin ƙananun kayan
nasa na fama, sai dai sun masa ƙyau kamar ko yaushe. Da hannu yake amsama kowa
sannun da yake masa saboda waya yakeyi. Ummah ta tura masa kujerar da take zaune a
kai ita kuma ta koma kusa dani a bakin gado.
Gaba ɗaya na kasa cigaba da shan farfesun har sai da Ummah taimin
magana, “Saifa kin cinye abincin nan tas dota, garama ki dage kafin nasa a
riƙeminke namiki ɗura”. Murmushi nai ina satar kallon boss da ƙamshin turarensa ya
addabi hancinanmu, kasancewar turaren maza yafi na mata ƙarfi duk sai ya danne
namu. A bazata muka haɗa ido, saurin janye nawa nayi dan banyi tunanin kallona
yakeba. Farfesun na cigaba da tsakura kaɗan-kaɗan, har yanzu inajin idanunsa na
yawo a kaina ko kunyar su Ummah bayaji.
Kusan mintuna biyar ya ɗauka kafin ya ajiye wayar yana faɗin, “Am sorry Ummana
nazo ina waya”. Murmushi Ummah tai masa, tace, “Babu komai Son”. Guntun murmushi
yayi yana mai risinar da kansa ya gaisheta ita da Mama, kafin ya ɗorama mama da
godiya. Mama tace, “Babu komai Jawaad, ai yima kaine, Bilkisu ta cancanci ai mata
abindama yafi haka dan yarinyar kirkice mai tarbiyya, mu saidai muce ALLAH ya sanya
alkairi a wannan al'amari ya kuma baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba”.
Gaba ɗaya ban fahimci kalaman mamaba, dan dama Nabeelah ta shigo ɗazu tana
cemin amaryar yayansu, kallonsa naɗan sata sai naga ya amsa da “Amin” akan
laɓɓansa. Tunanin ko da aunty Shahudah aka ɗaura masa aurene yasa naɗanji nutsuwa.
Ganin ya gama gaisawa da aunty Batool nima nace, “Ina kwana sir”.
Amsamin yay da “Lafiya, ya jikin naki?”. “Alhmdllh naji sauƙi”. Bai sake
cemin komaiba ya juya sukai magana da Ummah, sai naga sun miƙe sun fita. Numfashi
na sauke a hankali ina rumtse idona, dan fitar tasa yasa naji kamar an saukemin
kaya. Babu abinda nake buƙata a halin yanzu kamar ƙarin bayani akan abinda ya faru
jiya tsakanina da ƴan gidanmu, banga kowa a cikinsu ba kuma yau tunda na farka,
sannan kuma miya faru har aunty Shahudah ta nemi jimin ciwo su aunty Aamilah kuma
sukaimin wannan bugun da gashi ya kaini da kwana a asibiti?........
Ring ɗin wayatane da Ummie ta kawo ɗazun ya katsemin tunani, Nabeelah dake
kusa da wayar ta miƙomin tana ƴar dariya, “Matar Yayanmu waye kuma masarauta?”.
Wayar na amsa dan karta tsinke batare dana bata amsaba, bayan mun gaisa daga can
Amaturrahman ke tambayata a ɗakin da nake?. Mamaki ne ya kamani sosai, ta yaya akai
sukasan banda lafiya to? Kodai jiya sunzo ana wannan rikicin da bansan tshensa ba?
Tunanin ƙila Ummie ce ta sanar musu ya sakani amsa mata da cewar bara na turo a
shigo dasu. Da ga haka muka ajiye wayar, Nabeelah na kalla cikin marairaicewa nace,
“Sorry dear, dan ALLAH ki shigo da baƙi wai suna waje”. Cikin dariya tace, “Karki
damu matar yayanmu, girmankine ai”. Kasa haƙuri nayi nace mata, “Wai nikam wannan
sunan daga ina haka?”. Sosai ta kwashe da dariya tana nufar hanyar fita da faɗin,
“A wannan ba hurumina bane, yayanmu zai baki bayani”.
Aunty Batool ce tace, “Fitsararriya ALLAH yasa ya jiki dai”. “Ba amin ba” ta
faɗa tana ficewa fuska a kumbure.
Murmushi mukai ni da mama, danni taɓarar Nabeelah dariya take bani, na lura
gatane kawai yay mata yawa, ga uwa ga uba ga yayu ga dangi gata auta kuma. Mintuna
baifi goma ba sai ga Nabeelah ta shigo dasu Amaturrahman bakinta fal magana da
ganin jama'ar kamar jinin sarauta, dan tare suke da hadimai mata uku tare da wani
dattijo, sai hadimai maza suma guda biyu.
Tun a waje Jawaad da Ummah dake zaune suna magana akan yanda za'ai da bilkisu
kafin lokacin tarewar sukaga Nabeelah dasu Amaturrahman, cike da mamaki suka bisu
da kallo, ganin da gaske ɗakin da bily take suka shiga yasasu tasowa suka biyo
bayansu.
A waje suka iske hadiman su duka biyar, basuce dasu komaiba suka sh

iga.
Amaturrahman na zaune a bakin gadon da babu kowa a kai tare da aunty Batool,
Marwah tsaye kusa da mama dake a ɗayar farar kujerar ta wancan gadon. sai dattijon
kuma a kujerar da Jawaad ya tashi, , sai Safah data ɗane gadon kusa da bily tana
taɓa kumburin fuskarta kamar zatai kuka, Bilkisu dai murmushi take mata, dan har
cikin ranta takejin ƙaunar yarinyar da wannan shine haɗuwarsu ta biyu.
Jawaad ya ƙaraso suka gaisa da dattijon cikin mutuntawa, fuskar dattijo da
murmushi yace, “Ina fatan kaine mijin nata?”.
Wani irin muguwar bugawa ƙirjina yayi, babu shiri na zubama boss ido dan naji
amsar da zai bada, saiko naji yace, “Eh nine ranka ya daɗe”. Idanun mamaki na zaro
dan nama manta akwai mutane a ɗakin, wata ƴar harara naga ya zubamin ya ɗauke
kansa, yayinda shi kuma dattijon ke faɗin yazo zasuyi magana a waje. Binsa yay suka
fita. Cikin dawo dani hankalina Safah tace, “Aunty B mijinki mai ƙyau, zaki yarda
na zauna gidanku?”. Dariya duk ƴan ɗakin sukayi, bandani dana kasa koda motsi, sai
ɗan kaɗama Safah kai nayi kaɗan dan nikaɗai nasan a kalar ruɗanin da nake ciki.
Buɗe ƙofar da aka sakeyine yasa duk muka kalli can, shine ya leƙo yay kiran mama da
Ummah.
Suna fita naji hawaye sun silalomin, da sauri nai ƙoƙarin gogewa dan banason
kowa ya gani, sai dai na makaro dan Safah tarigada ta gani, da sauri tace, “Aunty B
miyasaki kuka?”. “Ba kuka nakeba Safah, abune ya shigarmin ido” nai maganar da
sauri. Tace, “Aunty B wai kema kina ɗaukata ƴar yarinyane? Nafasan kuka”. Tsawa
Amaturrahman ta daka mata da faɗin, “Safah wai miye haka? Ke duk inda kika zauna
saikin takurama mutane ne?........” Aunty Batool ce tai saurin katse Amaturrahman
ɗin da faɗin, “Minene abin takura anan ɗin? Ai kulawama take bata”.
Marwah datun ɗazun bayan gaisuwa bata sake maganaba ta harari Safah ɗin da
faɗin, “Aunty bakin yarinyarnan ne kamar bai gasuba”. Itama Safah ɗin harar Marwah
tayi, tace, “Halan tarene ba'a gasa manaba, manya na magana kina wani tsoma musu
baki mtsoww!”. Ƙwafa Marwah tai ta ɗauke kanta bata sake maganaba. Nai murmushi da
riƙo hanun Safah nace, “A'a banda faɗa to, Marwah kema zo”. Babu musu ta bufoni, na
kamo hanunta na zauna da ita ɗayan ɓangaren itama suka sakani tsakkiya.

A waje kuwa dattijo ya miƙama Jawaad takarda yana faɗin, “Saƙone daga
Sarauniyar gagara badau, tace na miƙa wannan takardar ga mijin Bilkisu Adam makaho,
ka karanta sannan ka bada amsar da za'a koma mata dashi”. Cike da mamaki Jawaad ya
amshi takardar dake nannaɗe an ɗaureta da zare ruwan gwal, yace, “Sarauniyar gagara
badau kuma? Ni kaina ya sake kullewa”. Dattijo dai baice komaiba sai murmushi da
yayi. Jawaad ya buɗe takarda tareda karantawa a fili domin Ummah da Mama suji
abinda ta ƙunsa.
Saida yakai har ƙarshe sannan suka shiga kallon-kallo, dan tayi bayanine a
taƙaice gameda sanin Bilkisu da sukai har zuwan su Amaturrahman jiya da sukai
tsozali da ruguntsumin da ya faru, a ƙarshe ta nuna buƙatar ganin shi Jawaad a yau
zuwa masarauta domin suyi magana.
Jawaad ya kasa cewa komai, sai kallon inda dattijon ya koma gefe danya basu
damar tattaunawa yayi, mamace ta katsesa da faɗin, “Jawaad nikam ina ganin kaje ɗin
sai kaji minene takeson ji ɗin”. A sanyaye Jawaad yace, “Shikenan Mama zanje, bara
na kira Alhaji babba shima na sanar masa”. “Hakan yayi” cewar mama, Ummah dai tama
kasa cewa komai dan mamaki, saida mama tace, “Hajiya Mariya bakice komaiba”.
Murmushi Ummah tayi, tace, “Abinne aini ya ɗauremin kai, daga tsintar Cards sai
kusanci har irin haka ya shigo? Lamarin manyan nanne baka musu gaggawa, amma nima
nagoyi bayan maganarki akan yajeɗin sai muji mitakeson su tattauna ɗin”. shidai
Jawaad gefe ya koma yayma Alhaji baba bayani ta waya, shi kansa saida ya jinjina
abin a ransa, kafin yace to Jawaad ɗin ya jirasa gasunan zuwa asibitin shi dasu Dad
zasu duba Bilkisu.
Ciki Ummah da mama suka koma akabar Jawaad tare da dattijo anan waje suna
tsumayen zuwansu Alhaji baba.

★★★★★★★

Kasancewar su Alhaji baba a hanya suke lokacin da Jay ya kira sai


gasu babu jimawa sun iso, gais

uwa sukai da dattijon da babu wanda yasan daga ina yake sai Alhaji baba, da ido
yayma Jawaad nuni dasu jirashi. Jawaad ya ɗaga kansa alamar amsawa. Shikuma yabi
bayansu Uncle Sulaiman ciki domin duba Bilkisu.
Dole su Ummah suka fito waje suka bama su Alhaji baba ɗakin dan yamusu kaɗan,
Safah da Marwah kaɗai aka bari tare da Bilkisu daketa faman gaishesu kanta a duƙe,
dan bata yarda ta kalli kowaba sai da Dad yake matsawa kusa da ita ya ɗago fuskarta
yana duba kumburin daya fara sauka da jera mata kalamun ban haƙuri tamkar zai ari
baki sannan ne ta ɗago tana ɗan murmushi. “Dan ALLAH Dad kabar damuwa, wlhy ni
kawai na ɗauki hakan matsayin ƙaddara da kuskure kawai, kuma nama yafe musu”. Babu
wanda bily bata birgeba da kalamanta, wata irin faɗuwar gabace ta riski Alhaji baba
lokacin da yay tozali da fuskar Bilkisu, ya kafeta da ido ko ƙyaftawa bayayi, dukda
kuwa a kumbure take kaɗan ta gefen haggu saboda duka hakan bai hanashi hango wani
abu tattare da itaba. Sam yama daina fahimtar sauran maganar data biyo baya
tsakanin Bily dasu Dad, haka kawai ya tafi wani bahagon tunani da shi kansa yasan
akwai kuskure a cikinsa. Saurin ture abin yay a ransa suka fito, saida ya kuma
waiwayawa ya kalli Bilkisu da batasan yanayiba sannan ya fice.
Dad wajen likita ya nufa dan yaji yaya ake ciki? Su Uncle Sulaiman kuma
suka fita domin tafiya gida, a wajen su Jawaad suka bar Alhaji baba shima.
Takardar Jay ya bama Alhaji baba, bayan ya karanta ya kalli dattijon,
“Ƙanina zance ko ɗana yaushene akesan ganin nasa?”. Dattijo yay murmuahi da faɗin,
“Baba yanzuma zamu iya tafiya, dan zanbar yaran anan muje mu dawo”. Kallon Jay baba
yayi, yace, “Shikenan kabisa Muhammad”. Jawaad ya kaɗa kansa da faɗin, “To baba,
amma zan koma gida na canja kaya tukunna”. Alhaji baba yace, “Ato ai maganinku
kenan, ƙiri-ƙiri kun ajiye suturar mutunci kun biyema ta yahudu, saboda irin haka
muke muku faɗa akan kuna tunawa da naku suturar kuma, dan sune kayan da zakuje
gaban ko wanene batare da kunji nauyin hakanba”. Shidai Jawaad baice komaiba, sai
dattijon masarautane keta murmushi da faɗin, “Wannan gaskiyane baba”.

★★★★★★

Sosai nake a cikin ruɗani da neman mai min ƙarin bayani akan wannan
rikiɗaɗɗen al'amari, ina Yah Qaseem ɗina ya shiga da har ake jinginani matsayin
matar boss?, shin wai mike faruwa hakane ni bilkisu? Mizaisa aitamin magana a
curkuɗe?, a rasa maimin bayanin dazan fahimta. Koda su Oga Hafiz ma sukazo dubani
harda matansu, matan sai faman yimin addu'ar fatan alkairi suke da faɗin, wai boss
ya dace da matar da suka dace da juna, hakama da Ummie ta dawo tare da ƴan gidansu
Momynta da Dady sunata min addu'ar ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, musamman ma
Daddyn Ummie danaga tsantsar farin cikin hakan a garesa har suka tafi. Amina ma da
Yayansu sunzo sunyi nasu kalar farin cikin, hakama Ummah ƙarama da naji suna faɗi
da yaranta da tazo, sai murna suke da kasancewata wai matar ɗan uwansu. ‘Oh ALLAH!
wannn wane irin ruɗanine haka?; Ina ƴan gidanmu suke? Dad kawai na gani, amma ko
Yah Qaseem ban ganiba, shin ina ya shigane??. Haka naita juya wannan tunanin a
raina, yawan jama'a da keta shiga da fici ya hanani sakat ɗin dazan samu na
tambaya. A gefe kuma inajin daɗin ganin nima ashe mai mutanece? Ashe inada gatan
dazan kwanta ciwo har mutane irin haka suyita tururuwar dubani?. ban sake ganin
boss ba har sai bayan sallar zuhur.

★★★★★★

A ɓangaren Jawaad kam kamar yanda ya roƙa alfarma ga dattijo saida


suka biya ta gida ya shiga ya sauya kayansa da ɗanyar shadda fara tas da tasha
ɗinkin zamani, yaukam hardasu hularsa zannah ainahin nutsatstsiyar saƙar barnawa ta
asali sai ƙyalli take, duk wanda ya gansa yaga sabon ango dukda bai shiga daga
cikiba😂, shi kansa dattijon tunda Jawaad yafito daga gate ɗin gidan kasa ɗauke ido
yay daga kallonsa, a fili ya furta ‘Masha ALLAH ’. Drivern dake jan motarma bai iya
ɗauke idanunsaba har Jawaad ya shigo.
Sun isa katafariyar masarauta mai daɗaɗɗen tarihi da gininta na
ɗaya daga cikin manyan gine-ginen da ake lissafasu a sahun farko na yankin masarau

tun afirika baki ɗaya saboda ƙawatuwarsa da gini mai nagarta data samu, gashi a
koda yaushe cikin sake fidda masa wasu tsare-tsaren akeyi masu matuƙar sake
ƙawatata. Wannan shine zuwa na biyu da Jawaad yayi cikinta, dan sun taɓa zuwa
gaisuwar salla wa sarki Sameer tare da tawagar Gwamna a shekaru uku kenan da suka
shuɗe. Sai dai a wannan karon sosai yaga sabbin tsare-tsare da tarin cigaban da
yafi na wancan lokacin, bayi sai zubewa suke suna gaisuwa a garesu saboda wanda
suke tare, shi kansa Jawaad ɗin kallon wani jinin sarauta suke masa saboda kama
yake dasu ta siffofi da dama.
Jawaad mutumne shi mai nutsuwa da aji, sanan yanada tsari, bai damu da
abinda babu ruwansaba komai ƙawarsa da abubuwan kallon cikinsa, wannan halin nasa
na yima abu kallon ko in kula yasa sam bai zama ya rikice wajen kalle-jalleba a
masarautar dukda ta cancanci a tsaya ƙare mata kallo harda son yin hotunama a
cikinta. Tafiyarsa yake kai tsaye tamkar ko yaushe a kuma ko ina ya tainci kansa,
bajinta, nutsuwa, da tarin ƙasaita kawai zaka hanga a takun nasa, waɗanda basu da
fahimta akan halayyarsa harma zasu iya haɗawa da Izza da girman kai, sai dai kuma
sam ba haka baneba, tun asali haka ALLAH yayisa tamkar wani jinin mulki wajen
girmama nutsuwa a dukkanin al'amuransa koda akwai ruɗarwa a cikinsu kuwa.
An saukesa a katafaren falo mai cike da abubuwan ƙawa da birgewa, cikin
mintuna ƙalilan aka cika masa gabansa da kayan ciye-ciye da har yake tsogumi a
ransa wai ‘Kamar wani mai cikin zani’ (😂kujifa daga abun arziƙi. Lol🤣)
Bai taɓa komaiba bayan ruwa a kayan da aka jibge masa, dan shi ba ko ina
yake sakin jiki yaci abuba (Yau naga mai irin halin babana a iya fulako😍, ALLAH ya
gafarta maka baba😥🙏🏻). Cikin nutsuwa yake ɗanbin falon da kallo da jinjina daular
dake ciki tamkar babu talaka mai buƙatar abinci da rigar sawa da kuɗin magani a
duniya, yaɗan taɓe baki yana gyara zamansa, sam shi fariyya bata birgesa, dukda
kasancewarsa mutum mai tarin dukiya bai taɓa sha'awar yin abinda ya fice hankaliba
a hidimar rayuwarsa, dai-dai da motar hawansa guda biyuce kacal a duniya, hakama
suturar sakawarsa akwai adadin da yake ajiyewa, ya gwammace duk sanda zai ɗinka
wasu kayan ko ya saya to ya fidda tsoffin ya bada kafin ya ajiye wasu, baya
sha'awar tsube sutura a drawer harya mance randa ya sake maimaita wata.........
Tunaninsane ya katse saboda sallamar da akayi a ƙofar falon, ya amsa yana
gyara zama da tsumewa cike da kame kai. Hadimai mata guda biyune suka shigo, cikin
girmama suka gaidashi kafin su sanar masa zai iya tasowa gimbiya ta fito.
Kansa kawai ya iya jinjina musu, ya miƙe tare da jefa wayarsa cikin aljihu
yabi bayansu. Ƙaramin falone madaidaici, sai daifa ya haɗu harma ya gaji da
haɗuwar, Hamshaƙiyar mace mai cike da tarin kamala da kwarjini da bazata gaza
shekaru arba'in da biyar ba a duniya tana zaune, sai ƙamshi da walwali take cikin
alƙyabbar da kallo ɗaya zakai mata kasan an sayeta da kuɗaɗe masu daraja. Gimbiya
Munaya Awwal fharok kenan, sarauniyar gagara badau mai lokaci da amfani da damarta
tana damawa yanda ya kamata, matar sarki Sameer saifudden Abubakar adalin sarki mai
mulkin dake tafiya da koyarwar addinin islama da zamani, cikakken sarki mai iko da
ƙasaita, adali mai tarin ilimin addini dana zamani, wanda yasha gwagwarmayar rayuwa
tunkan rayuwar tagama sanin shiɗin wanene.
Da hannu gimbiya munaya taima matashin saurayi Jawaad nuni da wajen zama,
bata haifi kamarsaba, amma kuma ta girmesa a shekarun haihuwa. Cike da nutsuwarsa
ya zauna, kafin ya risina cikin girmamawa ya shiga gaidata. Gimbiya munaya tai
murmushi mai ƙayatarwa dan Jawaad ya birgeta ainun, daganinsa zakasan yajiƙu da
tarbiyya tsaftatacciya. Cike da ƙasaita tace, “Kana lafiya?”.
Jawaad ya amsa da “Alhmdllh ranki ya daɗe”. Murmushin ta sakeyi, kafin ta
cigaba da faɗin, “Kana tare da Uwargidan Sakin gagara badau Sameer Saifudden, nasan
kana cikin ɗunbin mamakin kiran gaggawa da nai maka wanda ni kaina bansan dalilin
hakanba, kawai dai ina danganta lamarinne da tsantsar ƙaunar danaga gudan jinina
tanama wadda banmm

a taɓa ganiba mai suna Bilkisu da a jiya nake samun labarin an ɗaura maka aure da
ita, hakan kuma yazo da rikicin da ita Bilkisun ke buƙatar taimako”.
Jin tayi shiru Jawaad ya jinjina mata kai, cike da girmamawa yace, “Hakane
ranki ya daɗe”. “Idan ban shiga hurumin daba nawaba inasonjin wani abu koda zan iya
bada gudunmawa ta, dan a yanda yarana suka bani labarin abinda ya faru da Bilkisu
hakan ya matuƙar tsayamin a zuciya a daren jiya”.
Murmushi Jawaad yayi, dan haka kawai yaji ƙaunar gimbiya munaya har cikin
ransa, batare da tunanin komaiba ya buɗe mata cikinsa gameda abinda ya faru akan
auren nashi da Bilkisu. Shiru gimbiya munaya tai tana nazarin maganganun nasa kafin
ta sauke numfashi, cike da ƙasaitarta tace, “Jawaad!, a ɗan guntun hangena na
fahimci akwai matsala babba dai dake a ƙasa wadda kaima kanka kakeson bincikowa?
Hakan ya birgeni, dan inason jarumin namiji mara tsoro mai ƙwazo tamkar mai martaba
na, zan baka gudunmawa akan dukkanin shirinka ɗari bisa ɗari, dan bansan mi
UBANGIJI ke nufi da wannan haɗin namuba ta dalilin Safah da kullum bakinta bai
gajiyawa da ambaton Aunty B”.
“Godiya muke ranki ya daɗe da wannan karamci, ALLAH ya ƙara lafiya da nisan
kwana mai amfani”. Murmushi gimbaya Munaya tai tana maijin daɗin karamarwar Jawaad
a gareta, sannan ɗabi'unsa sunyi matuƙar birgeta, idan badan ya faɗaba babu yanda
za'ai kai tunanin yafitone daga tsatson tsohon shugaban ƙasa Marigayi Abdul-aziz
yusif tafida, adalin shugaba da su kansu masarautarsu tayi ƙyaƙyƙyawar alaƙa dashi
a lokacin mulkinsa na shekara huɗu a gwamna ɗaya a shugaban ƙasa, a yanzu haka kuma
dukkan kayan itatuwa da kaji dawasu abubuwan da suka shafi gona ana kawomusu shine
daga gidan gonarsa......... Kauda tunanin nata tai Tace, “Shikenan Jawaad, yanzu
mataki na farko da zamu farabi shine ina buƙatar Bilkisu ta dawo masarauta da zama,
dan komawarta gidansu bazai haifar da ɗa mai idoba kodan dalilin ita tsohuwar matar
taka da tsohon saurayinta da kuma mahaifiyarsu, zata zaunane na gajeran lokaci
daganan zuwa bayan sallar kamar yanda kuka tsaida tarewarta, dan itama tana buƙatar
ai mata auren gata tamkar kowane mace mai iyaye kodan hakan yazama izina ga masu
irin halin Gwaggonka dake tunanin su kaɗaine a sama babu mai taddosu, inason susan
babu wani bawa ƙasƙantacce sai wanda ya ƙasƙantar da kansa ga barin bautar ALLAH
saboda son zuciya..............✍

Ina godiya gareku akan addu'oin da akaita zubami harda masu kira da masu turo saƙo,
naji sauƙi Alhmdllh sai dai inajinran manyan ledojin kayan dubiya😆😋.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻


[12/11/2020, 3:18 PM] HASNA ✍🏻
: Bilyn Abdull :
*_WATTPAD:_* _BilynAbdull_

*_TELEGRAM:_* https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g

Page 26

BARKA DA JUMA'A
..............Jawaad da yay ɗan jim fuskarsa ɗauke da murmushi yana juya maganar
gimbiya ta ƙarshe a ransa, koba komai ya sakejin kimarta, domin ta nuna tanada
ƙyaƙyƙyawan tsari da tausayi akan talakawa. yace, “Shikenan ranki ya daɗe, ke
uwace, kinada damar yanke duk hukunci daya dace a kanmu koda babu saninmu, sai dai
ina neman alfarmar zuwa na sanarma kakana da kuma ƙannen mahaifiyata, zuwa gobe
insha ALLAH zan dawo na sanar miki yanda mukayi”.
“Wannan tunanin naka shine ƙyaƙyƙyawan tunani da yakamata ya fito daga
bakin jajirtaccen ɗa mai riƙo da tarbiyyar magabatansa, kaje ka sanar musu ɗin babu
damuwa, sai dai zan baka shawarar koda likita yace zai sallami bilkisu kace ya
jinkirta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, dan nafison da an sallameta kawai nan za'a
wuto da ita”.
Kansa ya jinjina mata. Ta ɗauki ɗaya daga cikin wayoyinta masu azabar ƙyau
ta miƙa masa, “Kasaka Number ka anan, saika ɗauki tawa yanda idan sun amince ɗin
zakai kirana ka sanarmin basai kayi wahalar zuwa ka koma kawomin bilkisu ba kuma”.
Tasowa jay yay ya amshi wayar, Number sa ta musamman da wanda ya yarda kawai
kuma yakeda kusanci dashi matuƙa kawaine ke da ita ya saka mata, sanan yay kira
yaga tata, saving yay mata da Jawaad A yusif ya maida mata yana godiya.

_______________________________

Tare Jawaad suka dawo da dattijon nan dan zai juya dasu Amaturrahman
masarauta.
Shi kaɗai ya shigo ɗakin da sallama ciki-ciki kamar yanda ɗabi'arsa take
ta rashin son hayaniya, babu kowa a ɗakin, Safah kaɗaice kwance tana barci a gadon
da Bilkisu ke jiyya, mamaki ya kamashi da tunanin ina suke har ita Bilyn?. kafin
yay yunƙurin yin wani abu aka buɗe ƙofar toilet, Bilkisu ce ta fito ɗaure da zani,
ta yafa ƙaramin towel a kafaɗarta da alama wanka tayo saboda yanda ruwa ke jiƙe da
fuskarta, duk tsefaffen gashinta ya kwanto goshinta da gefen kumatu.
Wani faɗuwa gabana yayi dan banyi tunanin iske kowaba tunda su Nabeelah
sunce zasuje sallah, Mama kuma tunda ta gasamin jiki ta fita akan zata ɗauraye
kwankikan da akaci abinci, bawani ƙwarin jikin nakejiba dama, dan dukan da sukaimin
yasa jikina yin tsami ko ina ciwo yakemin, wai danma Doctor ya bani maganin ciwon
jiki nasha. Nakasa koda ɗaga ƙafata da sunan juyawa baya, sai kawai na duƙe a wajen
inaji tamkar ƙasa ta tsage na shiga ciki dan matsananciyar kunyar data riskeni,
nice yau tsaye gaban boss babu riga? Dagani sai zani da ƙaramin towel ɗin dana yafo
a kafaɗa, kaina sanye da hular wanka, dukda nasan fuskata kawai zai iya gani da
hannayena zuwa gwiwa, sai ƙafafuna suma iya rabin ƙwairi dan zanin ya sauka min
ƙasa sosai duk da ɗaurin ƙirji nai dashi, hakan ba ƙaramin abun kunya bane a
gareni.
Ɗauke kai Jawaad yay daga kallon daya kafeta dashi yana mai lumshe idanu
a hankali da furzar da sassanyar iska daga bakinsa, baice da ita komaiba ya juya ya
fita zuciyarsa na gudu da sauri-sauri.
Hawaye nake kashirɓan da bansan dalilinsuba sam, dukda naji ƙarar buɗe
ƙofa da rufewa alamar ya fita na kasa miƙewa tsaye bare na tashi. “Bilkisu lafiya
kuwa? Ko jiri kike ganine?”. Muryar mama ta dawo dani hankalina. Saurin ɗago kaina
nai ina share hawayen da suka jiƙen fuska, ganin dagani sai ita a ɗakin yasani
sauke numfashi ina mai ɗaga mata kai alamar juwarce. Kwanikan hannunta ta ajiye
tazo ta taimakamin na tashi tsaye, da taimakonta muka ƙarisa bakin hadon dan a
gaske yanzun saima nakejin tamkar juwarce tazomin, ita ta taimakamin na shirya, ina
kammala shiryawa su Nabeelah da Amaturrahman da Marwah na shigowa. Sannu suka yimin
kafin Amaturrahman ta shiga tada Safah tana faɗin Su zasu wuce gida, jinai kamar
nace su zauna, amma banda wannan ikon, ga Safah ta sanya kukan shagwaɓa akan itafa
anan zata zauna tare dani. Ina mamakin wannan irin ƙauna da Safah ke nunamin.
Kafin kowa yace wani Abu boss ya shigo ɗakin da sallama. Nidai ƙasa nai da
kaina ban yarda nako saci kallonsaba, tambayar da yakema Safah akan mitakema kuka
kawai naji, Na

beelah ce ta bashi amsa da cewar tace bazata tafiba anan zata zauna wajena. Banji
ya bata amsaba, sai saukar hannunsa naji akan nawa dake riƙe dana Safah, a take
tsigar jikina ta tashi, gashi har yanzu akwai damshin ruwa jikina dama, ya cire
hannunta batare da yace uffan ba, binsu da kallo nai ta ƙasan ido har sukaje gab da
ƙofa. Ranƙwafawa yay yaymata maganar da duk bamujiba a cikin kunne, ta ƙyalƙyale da
dariya tana tsalle, shima wani shegen murmushi ya saki maiban mamaki, Safah tace,
“Amma Yayanmu (Yanda taji Nabeelah na faɗa) kafin goben zaka rama mata dukanta ko?
Inba hakaba saina saka Abbu ya turo sarkin tsabga na masarauta ya musu dukan mutuwa
da dorinarsa”.
Janyeta yay daga jikinsa da take neman shigewa yana lumshe idanu, a hankali
yace, “Karki damu zan rama mata da kaina”. Sosai ta shiga daka tsallen murna
Nabeelah da Mama na dariya harma da Amaturrahman, Marwah ce dai tai murmushi kawai
tana rakuɓewa a jikina, juyowa yay muka haɗa ido nai saurin janye nawa, da hannu ya
yafito Marwah alamar taje itama. Da sauri kam ta nufesa cike da ɗoki harda
murmushin daya bama kowa mamaki, dan tunda tazo taƙi sakin jiki da kowa. Hannunsu
ya kam suka fita, Amaturrahman taimin sallama tabi bayansu tare da Nabeelah da
zatai musu rakkiya, mama kuma ta bisu da kalaman godiya dana addu'a. Nima haka
godiyar nake musu har suka fice.

Bayan wucewar su Amaturrahman Jawaad bai koma cikiba, mota ya shiga


yabar asibitin. Kai tsaye gidan Alhaji baba ya nufa, harya zauna kusa da Alhaji
baba baisan ya shigoba, saida Jawaad ya kwanta tare da ɗora kansa a cinyar kakan
nasa sannan ya kawo numfashi. Cike da mamaki jay yace, “Tunanin mikake haka da
zurfi sofo?.”
Shafa kan Jawaad yay cikin ƙoƙarin danne damuwarsa yace, “Kaima zaka tsufan
wataran ai, ango mai rinton mata, yaya kukayi dasu a masarautan?”.
Dariya Jay ya ƙyalƙyale da ita yana faɗin, “Ashe dai ni jarumine tunda
gashi na ƙwace kuma dole a barmin. Ka fara gayamin damuwarka Baba sai na faɗa maka
nima”. Jay yay maganar cike da kulawa ga kakan nasa abin ƙaunarsa. Sosai Alhaji
babba ya sake danne halin da yake ciki ya nunama Jawaad bashi da wata damuwa, badan
Jawaad ya aminceba ya haƙura, sannan ya zayyane masa duk yanda sukai da gimbiya
Munaya. Alhaji babba yace, “Banƙi ta tataba, sai dai kuma kai kana ganin babu
damuwa?”.
Zaune Jawaad ya tashi sosai, yace, “Amincewarka ni itace kawai tawa baba, dan
kaine zaka hangomin abinda ya dace da wanda yake kuskure saboda kana gaba dani,
dalilan data kawo na komawarta gidan Dad abin dubawane, nikuma gashima ban shiryama
maganar tarewar tataba saboda akwai ayyukan da gidan da zan ajiyeta yake buƙata,
tunanin da nake dai bai wuce dama ta koma gidan Ummah babba ba, dan dama ni ban
tsara zata koma can gidanba saboda haɗarin dake tattare da hakan koda Qaseem da
Hudah da Momynsu.
Alhaji baba yace, “Lallai kayi tunani mai ƙyau, yanzu dai ka bata dama, dan
kowa yanama Uwargidan sarki ƙyaƙyƙyawan sheda akan adalci da shiga matsalar
talakawa da ƙarfinta da dukiyarta, to akanku wannan ba sabon abu bane, bakuma yauta
faraba, shiyyasa banajin wani ɗar balle tunanin akwai wani manufa a lamarinata”
Jawaad yace, “Shikenan Alhajin ALLAH zanyi yanda kace”. Daga haka hira
sukaɗan taɓa zuwa sallar la'asar, daga nan Jawaad yay masa sallama ya wuce gida,
dan a matuƙar gajiye yake, rabonsa daya huta tun daren alhamis ranar laraba kenan,
gabaɗaya bai hutaba, a hankali ya furta, ‘Dukta cinyemin lokaci ta gajiyar dani’ ya
ƙare maganar daɗan lumshe idanu ya buɗe akan titi.
iske gidan nasu yay kaca-kaca anata hayaniya, dai-dai sashensa yay
fakin inda ya saba, ya fito fuska ɗaure batare da ya kalli kowaba a cikinsu ya
shige abinsa, dan ya fahimci cecekucen maganar aurence suke har yanzu, shikam a
tsarinsa duk abinda ya gama da matsalarsa to yagama kenan baya sake waiwayensa sai
dai kuma sabo idan ya taso.
Yanda suka ganshi a tsume yasa aka rasa mai tunkararsa da magana dukda kuwa
shigowar tasa suke jira dama, Hatta da Momy da Shahudah duk suna gidan sunzo saboda
mama Atika data buƙaci ganin Momy, ga k

ukan da Shahudah keta dirja tunda Jawaad ya baro gidan. (Kaike musu yanda kaso ace
ɓarnar motace, inba kaiba saiwa ɗan Abdul'aziz😂, kaikeyi kayi kuma kamar bakaiba
dole a ganka a ƙyale🤣🤣).
Yana shiga falonsa ya dannama ƙofar key yana jan wani wawan tsaki, a
kwanakinnan ko shara sashen baya samu saboda yaraba hankalinsa biyu, ga matsalar
aiki ga matsalar cikin gida, duk ƙura ta kwanta bisa kayayyakin falon, haka ya
tsallake yanzunma ya haye sama, canɗinma dai yay ƙurar sosai, bai kulaba ya ƙarasa
bedroom, shi daɗan sauƙi saboda ana zama, gadonma a gyare yake, ga mayen ƙamshinsa
daya kama ɗakin na nan, kayan jikinsa kawai ya rage, dagashi sai boxer ya haye
gadonsa yana lullumshe idanu. Cikin ƙanƙanin lokaci barci mai nauyi yay awon gaba
dashi (Barcin bayan la'asar baida ƙyau Jay🤦🏻). A hankali numfashin Jawaad ya ƙara
nauyi alamar barcinsa yayi nisa, mafarki mai sarƙaƙiya, wanda a cikinsa aka sake
maimaita masa kalmar “(Ƙaddarar haɗuwar Jini a cikin jini da zai zama jini a yanzu
ta zama tabbatacciyar alaƙa da zata zama sanadin buɗe ma'anar jini a cikin jini,
takuma warware sirrin ɓoye, Kuzama masu addu'a, dan lokacin da ƙullalliyar
sarƙaƙiya mai cike dacin amana zai bayyana yayi, dolene maciya amana, amana tacisu
suma, dolene waɗanda sukai shuka su girbe abarsu dai-dai da abinda suka shukaɗin
tun a duniya kafin aje babbar kotu kowa ya amshi sakamakonsa, dolene gorar da
azzalumai suka fafe dan tafiya ta buɗe a yanzun da suke gab da kaiwa ƙarshen
tafiyar tasu, ɗan zaki ya girma, kaine jagoran fidda ƘWAI CIKIN ƘAYA, karkuyi wasa
da addu'a!! dan itace babban takobinku na yaƙar wata riundina ta azzalumai masu son
zuciya, gaggawarku zaizama sanadin tonuwar wasu jinane da aka kwarayar. wannan
itace ƙaddararku, ƙaddara mai sarƙaƙiyar data saƙa jini a cikin jini, karku manta!
Addu'a!! Karku manta!! Karku manta!!)”. Cike da firgici Jawaad ya farka, ya jiƙe
sharkaf da gumi dukda kasancewar yammace mai cike da ni'ima canjawar iskar farkon
damuna, ɗan zafi-zafin dake garin bashida gallazawar da zatakai mutum da irin
wannan zufar da yakeyi, gaba ɗaya jiyay ɗakin na juya masa tamkar hajijiya, ya dafe
kansa da hannu yana karanto addu'oin da duk sukazo masa kan harshe. Ya ɗauki tsahon
mintuna zaune kafin yaji ɗakin ya tsaya dai-dai, ya sauke hannunsa yana furzar da
iska zazzafa, idanunsa sunyi wani irin kaɗawa sunyi jazur, wannan wane irin
mafarkine haka? miyasa yaketa maimaita kansa garesa? Akan wa ake masa wannan
nunin?; ‘Ya ALLAH ka warwaremin abinda banida ilimin saninsa, ka haskamin abinda ya
kasance duhu a gareni, ka jagoranci tunanina akan abinda kakemin ishara dashi
acikin barcina’. Idanunsa ya sauke akan wayarsa dake haske, kamar zai share sai
kuma dai ya ɗauka, ashe yayi barci mai tsaho, ga magrib harta gabatoma, saƙon
da'aka turo masa ya buɗe, sanin muhimmancin wanda ya turo masa saƙonne yasashi
nutsuwa ya karanta abida ya rubuto.
“Oga na shirya faɗa maka komai a yanda yake, ina kuma buƙatar a bani
matata itama, amma akan farashin kuɗaɗe, kabani address ɗin inda zamu haɗu, sannan
kazo da naira miliyan hamsin, nikuma zan baka labari mai matuƙar tsada akan kai
kanka bayan nata itama”.
Naka ɗan fir'auna.
Ƙaramin tsaki Jawaad yaja yana mai dafe goshinsa da hannun damarsa tare da murzashi
da ƙarfi, da ace ya iya kuka akan komai da a yau zama zai kawai yayta kuka har sai
ya ƙoshi dan kansa yay shiru, to amma a tsarin wannan harƙallar kuka a garesa
kasawace. Miyasa ɗan fir'auna yace yanada labari a kansa? Kenan shima su.... Ya
haɗiye abunda ke neman toshe masa numfashi da sauri yana girgiza kai da faɗim,
‘No...’ bazai kasance hakaba. Komawa yay baya ya sake zubewa a gadon, ƴar ƙarar da
agogon ɗakin yayce ta sakashi miƙewa kuma zumbur. Toilet ya nufa, ya sakarma kansa
ruwa na tsahon lokaci kafin yay wanka ya fito ɗaure da alwala yay gaggawar shiryawa
ya fita.

_____________________________

Ganin mutane sun sassauta zuwa dagani sai Mama a ɗakin da Ummie yasa nai
dauriyar tattaro dukkan abinda ke raina ina mai kallonsu, “Mama!”. “Na'am Bilkisu
ya akai?”. Tafaɗa tana ɗago kanta ta kalleni, Ummi

e ma daina latsa wayar tai ta maido hankali kanmu. Cikin bama kaina ƙwarin gwiwa
nace, “Mama dan ALLAH mi yake faruwa? Gaba ɗaya tunanina ya kulle bana fahimtar
komai daga kalaman mutane wanzu daga safiyar yau har kawo yanzun?”.
Murmushi maman Amina tayi, sai kuma ta taso zuwa inda nake ta zauna a bakin
gadon, hannunta ta saka ta kamo nawa, har yanzu fuskarta da murmushi, “Bilkisu ya
kamata dama kisan miya farun kodan kiyaye girman nauyin dake kanki a halin yanzun,
danke ɗin matar aurece da haƙƙinta ya koma kan wani”. Banji komai dangane da
kalamantaba face wani mummunan faɗuwar gaba da harbawar zuciya, ta cigaba da
faɗin...................
Wani irin mazarin rawa jikina ya shigayi hawaye na rige-rigen sakkowa
akan kumatuna, cikin matuƙar rawar leɓe dana harshe nace, “Mama! Ki..k...kina
nu..fin ni aka ɗaurama aure da BOSSS!!!?”. Mama tace, “Bafa bos nace mikiba,
Jawaad! Nace”. “Innalillahi....” Na shiga ambata, yayinda Ummie ke ma mama ƙarin
bayanin cewar Boss ɗin ai Jawaad nake nufi nima, haka muke cemasa a wajen aiki.
Mama tace, “Ayyo, aiban fahimta bane ƴannan”.
Komai nama daina fahimta, wani irin zazzafan zazzaɓi nakeji yana saukarmin,
cikin lokaci ƙanƙani nafara rawar sanyi, tunani kalma ɗaya acikin abinda mama
taimin bayani na kasa nutsuwar yi, ni Bilkisu Adam makaho ce aka ɗaurama aure da
Boss ɗinmu, JAWAAD ABDUL-AZIZ YUSIF!!? dama na jima zuciyata na kokwanto akan
rashin damuwar da bangani a tattare da Momy ba akan aurena da Yah Qaseem, miyasa
Momy ta zaɓi rabani da masoyina wanda na ɗauka dukkan yardata na bashi? Bazan
ɓoyeba ina ƙaunar Yah Qaseem sosai, sannan ban tsani Boss ba dan yanada nagartar da
dukkan macen ƙwarai zataso mallakarsa matsayin mijin aurenta, to amma yaya zanyi da
aunty Shahudah da dukkanma ahalina? Wannan kuwa bai zama cin amanaba ga Dad da
halaccinsa a gareni?. ‘To ai bake kika ce a ɗaura miki aure da boss ɗinba ko’ wata
zuciya ta ayyana min daga can gefe kuma wata tace, ‘Bakuma kowa zai fahimci bakida
hannu a cikiba kamar yanda mama ta faɗa miki dangin Momy na ambata hatta da Yah
Qaseem dayasha gargaɗinki akan mu'amularki da Boss ɗin’. Sharr na matso wasu hawaye
masu zafi da suka cikan ido. A fili na furta, ‘Innata miyasa rayuwa takemin hakane?
Miyasa duk yanda naso ƙoƙarin raɓar duniya saita goce mani? Tunda na rasaki keda
Abba ban sake hawa dokin da yay daidai da cikar dukkan burukanaba, dana hau matakin
nasara sai ƙaddara ta sake zuwa ta datse zaren da nake tafiya da ƙwarin gwiwata a
kansa, kune kuka sanarmin duniya ba komai bace face wani filin gwagwarmaya na
ƙwanji da zuciya, kune kuka tabbatarmin jajircewa na iya zama babban ƙawance da
duniya koda duniyar bata buƙatar hakan, miyasa ni tawa jajircwwar a kullum
nisantani take da tawa duniyar, shin gaggawa nake a cikin al'amarina shiyyasa nake
durƙushewa kafin nakai kokuwa tawa ƙaddarar kenan kullum a curkuɗe?....”
“Wannan ai itace tabbatarciyar nasara kuwa Bilkisu, duk ɗan adam ɗin dakeji
a zuciyarsa shine kaɗai wane, shine kaɗai za'aita kira wane daga farkon ƙarni har
ƙarshensa to ya tabbata akwai ganganci da tarin wauta a al'amuransa, nasarar mai
nasara itace ƙalubale, kadingaji kamar baka kaiba, baka cancanci kaiwaba, bazaka ka
kaiba, sai kaga watarana ka kai harma ka wuce, lokacin da wani yake ganin ya rigaka
ɗauka baka da damar ƙwata babu zato saiya suɓuce masa wajen hura hanci da gadara
kai ka tsinta a ƙasa amatsayin shara kaci kai nagartar da har abadan bashi da damar
hangokama, wannan rubutacciyar ƙaddarace ga mafi yawan mutane marasa gata, duk
wanda ake ganin bai kaiba ko bazai kaiba shike wucewa wataran bilkisu, Jawaad shine
mijin da yafi cancanta da nasararki, UBANGIJI kuma yafiki sanin miyasa ya zaɓa miki
shiɗin, karki damu da adawa ko tunin kinci amana, a sannu duhun da kike ganin yana
binki zai yaye yazama haske, a sannu waɗanda suke ganin keɗin baki cancantaba zaki
zame musu hasken da zai mamaye rayukansu, ba'a cika baki da nasara, ba'a cika baki
da farawa, ba'a cika baki da iyawa, ba'a cika baki da cancanta, ba'a gadara da
abinda baka da ikon dawwamar dashi a hanunka tunda kaima a wajen wa

ni aka amsa aka baka, dagaske duniya rigar aro ce bilkisu, duk taƙamarka da ita da
alfahari wataran saika tuɓeta da mutunci koda ƙasƙanci, duk abinda kaga kayi a
duniya koka tsinci kanka kafin kai anyi dubunka masu ninkin banikin ɗinsa, bayanka
kuma wasune zasu amsa su dama ko kaƙi ko kaso. Dan haka ki godema ALLAH da ni'imar
da yay miki na mallakar miji mutumin kirki da bai ɗau duniya komaiba matsayin,
dukda tarin dukiya da ALLAH ya bashi tun yana ƙanƙaninsa, shiba duniyar bace a
gabansa, dan da itace bazai taɓa rabuwa da ƙyaƙyƙyawa irin Shahudah ba data haɗa
komai na gata da nasaba ya ɗaukeki a matsayin ƴar riƙo a gidansu, wadda suke kallo
ƙasƙantacciya a cikinsu. Akwai hikima mai yawa a al'amuran UBANGIJI bilkisu da
jahili baya ganinsu ta fuskar data dace kinji”.
Kaina na gyaɗa mata a hankali, dan kalamanta sun sakani jin sanyi a raina,
sai dai ina jinjina yanda zan rayu da mutum murɗaɗɗe mai wulaƙanci da ƙasaita irin
Boss, aɗan zaman danai dashi na fahimci abinda ba'a sakashiba sam baya burgesa
balle ya tsoma kansa. To miya kawosa cikin nawa lamarin ni kuma?.
Wannan itace tambayar data tsayamin a rai har dare.

_______________________________

Zaune yake a ɗaɗɗaure, an ɗaure masa idanu da jan ƙyalle,


bakinsa ma a liƙe yake, shi kansa baisan a ina yakeba, abinda kawai ya sani da zai
iya tunawa shine.
Ranar juma'ar da aka ɗaura auren su boss, lokacin da ake tsaka da wannan
dambarwa ta neman sanin wanda ya rikita tsarin auren, yabi sahun masu gani da ido
babu damar tofa albarkacin baki, har aka gama rikicin massallaci aka nufi gida,
baiga boss ɗinsaba, dama baisa ran ganin nasanba a wannan lokacin, ganin su dad sun
ɗunguma gida shima saiya hau napep domin komawa gidan ya ɗau jikkarsa ta tafiya
gida weekend kamar yanda ya saba, dama sunyi sallama da boss tun a daren jiya,
hakan yasa bai damu daya kirasaba koya jirasa. Shiru gidansu boss yake babu wata
hayaniya, dan duk suna gidansu Shahudah, Mama Atika da mama badiyya dake fama da
jiyyane kawai a gidan sai hadimai da samari waɗanda baza'a rasaba da suka dawo daga
wajen ɗaurin aure. Jikkar kayansa ya ɗauka ya fito bayan sunyi sallama da baba mai
gadi, cike yake da nishaɗi akan yanda auren ya kasance, Boss ya samu wadda yake
masa fata tun sanda ya fara ganinsa tare da ita, yana gab da barin layin wayarsa
tai ring, cirowa yay ya duba, gani mamansace yay murmushi tare da ɗagawa yana
waige-waige, saida ya tabbatar babu kowa ama kusa dashi balle yay tunanin za'a jisa
kafin ya fara maganarsa kai tsaye cikin zaurence kamar yanda suka sabayi. “Mamana
albishirinki?”..............✍

Karku rikice, muje zuwa page 27, danjin ina aka dosa, nasan dai dayanku sun fahimci
kowanene ma kafin akai ƙarshen zance😉🤫👌🏼.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, gamai buƙata zai iya
tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu. 09032345899 sai
kunzo😍😍😍😘.

Musha weekend lfy. Maybe kuma ku ganni lahadi koma gobe idan ALLAH ya kaimu😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭


✍🏻
[12/14/2020, 6:04 AM] HASNA : Billyn Abdul:
Page 27

.................Daga can akace “goro yaron alkairi”. Ya cigaba da faɗin, “Da


alamafa damunar bana zatai ɓarna, dan na hangi ɗakunan mutane da yawa sun buɗe ta
sama batare da sun fargaba, kuma lallai bular zata zubda yoyon ruwan da zai iya
haifar da ambaliya”. dariya ta tuntsure dashi daga can, tace, “Ɗan alkairi kana
nufin dai dara zataci gida kenan, ɗan zaki yafara buɗe idanunsa ga rundunar kuraye
masu gudun tseren neman abinci koda bai kasance halalinsu ba?”. “Ƙwaraima kuwa
mamana, bana sanar miki wani ƙwai dake cikin ƙaya ya bayyana ba kwanakin baya, kuma
duk haɗarin maciji ya gama shawaginsa ya barsa dan ya gagara haɗiya”. “ƙwaraima
kuwa ka sanar min da wannan, a farautar zaki yaci karo dashi kenan matsayin
abinci?”. “Hhhhh mamana kina birgeni da saurin ramfo zance, to wlhy ina mai
tabbatar miki da hakaɗinne ta kasance, tsagerun dawa na tunanin Zaki yafi ƙarfin
ruwan ƙwai sai gashi harma yana ƙoƙarin damƙosa cikin ƙayoyi”. “Kai ɗan alheri
karka sa farin ciki ya karni yau ɗinan ban kalmashe bakin buhun dana farama ɗureba,
yanzu dai ina fatan kana hanyar gidane?”. “Hasashenki baya zama kuskure mamana, mu
haɗu acan na baki sauran bayani, dan kuwa garin bita da ƙullin ƴaƴan kura sun rufta
damisa da ƴaƴan fadarta a ramin ɗan zaki, shiko ya afka musu ƙasa yasa ƙafa yatake
harma da share wajen kwanciya domin buƙatar hutu”. Wata irin dariya ta shigayi mai
cike da nuna tsantsar farincikinta data daɗe da mantawa da samunsa, yau ɗan nata ya
biyata da daddaɗan labari. tace, “Ɗan albarka wannan zinaran kalamai naka sunfi
ƙarfin saurare a salula, garzaya gida nima ina gab da iskoka, dan tun safe na nema
alfarma ga Uwargida sarautar mata akan zuwa na duba mai babban suna”.
“Babu damuwa mamana ina tsumayenki acan, alkairin ALLAH ya cigaba da
baibayeki tare da nasarar cigaba dayin haƙo a ramin azzalumai batare dasun fargaba
har sai kinkai musu wuya lokacin sungama shiga tarko”.
Murmushi tayi daga can tana faɗin “Amin ɗan albarka” kafin ta yanke wayar,
shima ya tura tasa a aljihun yana murmushi. Cigaba yay da tafiya harya fito titi,
napep ya tara takaisa inda motocin ƙauyensu ke tsayawa, duk da garinsu ba ƙauye
bane sosai dole muce dashi ƙauye, dan kuwa a ƙarƙashin wata ƙaramar hukuma yake,
saidai yamafi l.g ɗin dukkan abubuwan cigaba, gashi a bakin titi kuma babu nisa da
babban birin jiharsu. A mamakinsa ana saukesa falletsetsiyar mota na cin birki a
gabansa, baiyi mamakin hakanba, dan kasancewarsa drivern boss yanada alaƙa da sanin
mutane manya sosai ta fannoni da dama, lokaci-lokaci kuma yakanci karo da wasunsu
koda ace shi ya mantasu dan dama dalilin shige da ficin boss na aiki yake sanin
nasu. Wanda ke ciki ya sauke gilashi yana murmushi, sosai gimba ya zaro ido irin na
bazatar ganin wanda bai zatoba, “Lah Ɓaleru! Dama rai kanga rai? wane mai
gangancine yay kasadar baka idanunsa kaketa haska hanya dasu cike da ɗaukar faɗi?”.
Dariya na cikin motar yay har yana bugun sitiyari, yace, “Gimba kaidai baka rabo da
shaƙiyanci, kasan ɓalerun naka da shige-shige, ko iska ta shafamin lafiya. Daga ina
haka zuwa ina?”. Gimba yace, “Wlhy gida nai, zamuje hutun ƙarshen mako domin ganawa
da iyali”. Ɓaleru yay ƴar dariya da faɗin, “Mutumina baka wasa da gona, shiyyasa
kullum gatanan cikin yabanya take, banga laifinkaba, yi birgimarka ka more mata
sune jin daɗin duniyar ai dama. Shigo mu haura dan nima dai can na nufa ɗin”. Babu
musu Gimba ya shiga yana maida masa murtanin shaƙiyancinsa, saida suka ɗauki hanya
ɓaleru yace, “Nifa mamaki oganka ke bani, gashi jinin manya, ɗan tsohon shugaban
ƙasa mai tarin dukiya, shi kansa ƙwaron kansane dan ya tara bayan wanda aka tara
masa, amma abin mamaki kamar shima baya mora balleku ƴan muna jira ALLAH ya baka mu
samu”. Murmushi gimba yayi, cikin son kare boss ɗinsa yace, “Ai abin nagartace, sai
dai irinku ƴan ƙwanta ka mutu mu haye basa ganewa, komai boss yake da tsari a
cikinsa, shi bai ɗauki wannan dukiyar da ta tsolema kowa idanu wata tsiyaba, marasa
nasaba da itama amfanuwa suke da tagomashinta amma ta ƙyaƙyƙyawar hanya, bai yarda
da almubazzaranci ba, amma shi kogine maiba na kus

a harma dana nesa, alkairinsa dake jiƙe dani ALLAH kaɗai yasan iyakarsa, sai dai
ba'a iya ganinsa da idon gani saina zuciya”. Wata irin mahaukaciyar dariya ɓaleru
ya kece da ita wadda harta bama gimba mamaki, kafin yabi ba'asinta ɓaleru ya jefa
masa handkherchief a fuska, daga haka bai sake banbance fari ko baƙiba sai a washe
garin safiyar yau daya jisa a ɗaure, idanu a rufe, bakima a ɓame. A zuciyarsa ya
ayyana, ‘GADAR ZARE akaimin da wanda na sani kenan?’. Murmushi yay na takaici wanda
a zuciya ya kasance dan babu bakin yinsa. Da ƙarfin masifa aka fincike abinda aka
sa masa a baki, azaba ta sakashi sakin wani irin gurnani sai dai jarumta ta hanashi
nuna gazawa. Yace, “Suwanene ku? Miyasa kuka kawoni nan? Minai muku?”. Banza akai
masa babu amsa, yasan akwai mutum tare dashi, dan yana jin hucin numfashi
kasancewarsa mutum mai basira da wata ɓoyayyir baiwa. Yay ɗan yi murmushin ƙarfin
hali yana mai motsa jikinsa kaɗan, ɗauri akai masa bana wasaba, hakan yasa daƙyar
yake iya motsawa. Kusan minti biyir yana jiran tsammani kafin a saka masa abu akan
kunne.
Wata mahaukaciyar dariya aka sanya mai dogon zango daga cikin abinda
basirarsa ta ankarar dashi wayace, daƙyar mai dariyar ya tsagaita daga can, kafin
ya fara magana a kausashe. “Yaro ashe kaima tsagerane ban saniba, kai wanene daka
isa tono abinda ke ɓoye? Ƙaramin naman daji abincin karnuka dakai har kakejin kakai
zarra wajen yimana kutse a al'amuranmu? Banida lokacin doguwar magana dakai, yanzu
za'a sakeka kai gudun mutuwarka kafin jininka ya zama halattacce ga bakandamiyarmu,
wanda kakema aikinma bai isaba balle kai direbansa hhhhhhhhhhhhhh!!!!!”.
Wata dariya gimba ya kwashe da ita shima, a kausashe yace, “Faɗan
sunƙuru alamace tamai tsoro, idan kuncika maza kufito filin yaƙi mai nasara saiya
ɗauki kambu, boss kainuwane dashen ALLAH, zakine mai yagalgala mazan da suke kiran
kansu mazanma balle ku mata maza masu ɓuya a rumfar..........
Kafin Gimba yakai ƙarshen zancensa an cire wayar daga kunnensa, taune
leɓensa yay da ƙarfi. Kafin a maida masa baki a rufe, Bai sake jin motsin kowaba
har yammaci, yana nan ɗaure babuci babu sha tun safiyar jiya rabonsa da abinci,
garama ruwa yasha bayan fitowarsu massallacin juma'a, tun yana samun garkuwa daga
yawu har shima yay tifƙewar da harshe bai iya juyashi ya zama abun mai gudana,
ƙishirwa abune dake saurin illata mafi yawan halitta mai rai, balle irinshi mutum
mai matuƙar son ruwa. Alamun duhun magriba da hasashe ne nashi yaji ya sake ɗaure
garin, a wannan lokaci yaji an fara kuncesa, har aka gama tas bai motsaba bai
kumace ƙalaba. Jansa aka shigayi keeeyyyy har zuwa waje, bashi da ƙarfin kare kansa
dan haka ya salama bakinsa ɗauke da addu'a, tafiyar kusan mintuna uku kafin ai
wurgi dashi.
Numfarfashi ya shiga saukewa a gwame, yakai hannunsa da ƙyar ya janye ƙyallen
da aka ɗaura masa a fuska, baya ganin komai da ƙyau saboda idanunsa sun kwana sun
yini a rufe, ga duhun magriba, saidai ya fahimci dajine yake. Da sauri ya shiga
laluban wayarsa dake aljihu wadda suka gaza gani bisa kariyar ALLAH, ya kasance mai
saka waya silent saboda baison takurama Boss ɗinsa da shigowar kira, a hankali ya
saba da hakan har takai bayama buɗeta koda basa tare, tun ɗazun yakejin sautin
shigowar kira dama, daƙyar ya iya ganin Number boss saboda idanunsa basa gani sosai
sun masa nauyi ainun. Kai tsaye WhatsApp ya shiga, yay azamar danna recording ya
fara magana a galabaice.
“Boss banjin zankai labari, dan basu kamani dansu barniba, akwai babbar
ƙura a gabanka da bazan iya buɗe maka haske a kantaba yanzu saboda ƙarancin lokacin
daya ragemin a duya, itace musabbabin shigowata rayuwarka tun fil'azal ka gafarceni
da ɓoyewa, dama nabari ka fita daga wannan matsalar rikicin aurenne idan nadawo
muyi magana, saidai ALLAH bai ƙaddara hakanba, amma nagodema ALLAH da wadda zata
baka abinda yafi nawa tana raye, kai ƙoƙarin zuwa gidan Alh al..alhaji............
Ya kasa ƙarasawa saboda rawar da jikinsa ya fara na tunkarowar wata muguwar
halitta garesa maiban tsoro. Jifa yay da wayar bayan ya ɗaga ɗanyatsansa saƙon ya
tafi
kasancewar baya rufe data shi dama can. Baya ya fara jan jikinsa yana karanto duk
addu'ar data zo masa, yayinda shikuma wannan halitta ke biyosa danƙyas-danƙyas tana
buɗe baki da lashewa alamar dai taga abinci. Babu zato gimba yaji yay baya, ashe
wajen gaccine mai zurfin gaske dan akan tsauni suke. Wata irin wahalalliyar ƙara ya
saki data bada amsa kuwwa a dajin yay ƙasa.......
Wata irin mahaukaciyar dariya dahar saukarta ke kamar ƙasar dajin na girgiza
ce ta fara ratsa tsaunika, anyita da tsayi kusan na mintuna biyar kafin ta lafa
wani irin yare ya biyo baya da muryoyin mutane masu yawa. Duk wanda zai iya
nutsuwar saurarar yaren zai fahimci kalaman cikinsa shirkace kawai ake ambato.
(Wa'iyazubillah 😭ya ALLAH kasa mufi ƙarfin zukatanmu, ya rabbi ka saka duniya a
tafukan hannayenmu karka sata a zukatanmu, kaiconmu, kaicon burikanmu kaicon son
duniyarmu).

_________________________________

Ana sallar magriba su Momy suka koma gida akan su Uncle Nasir zasu
zauna da Jawaad domin yasa ɗan-fir'auna ya saki hudah.
Momy da Shahudah ciki suka shige sukabar Aamilah na waya a barandar shiga
falonsu.
Da mamaki Aamilah ke kallon akwatinan da aka jibge a harabar gidan
gaban motar Qaseem, ƙiyyy!! Sautin jawo abu ya karate kunnuwanta, kallon wajen da
ƙarar ke zuwa tayi, Qaseem ne jaye da jikkan gana must go irin ƙatuwarnan sabuwa
dal, amma tsabar yanda yasa ƙarfi wajen janta har hannu ɗaya ya fincike yana
lililo, duk dai ya ganta yiyai tamkar basan da zamantaba, baba maigadi dai tun
ɗazun yana hangen Qaseem ɗin daga ɗakinsa, tsabar baison yafito ya gansa ya sakashi
aikin tayashine ya sakashi maƙalewa cikin ɗakin yana leƙensa ta Window. Jikkar ya
dangwarar ya sake juyawa zuwa sashensu, daga shi sai gajeren wamdo da baƙar singlet
datai mugun fidda masa siffarsa ta ƙaƙƙarfan namijin dake cin ƙarfe. Saida taga ya
shige kafin ta juya da gudu gulma na cinta har saura kaɗan ta faɗi, ALLAH dai ya
ara mata damar dafe ƙarfen da aka ƙawata barandar ƙofar falon nasu dashi, ƙara
kwasa tai a gujen ta shiga tana ƙwala kiran Momy dake sama abin duniya ya isheta ga
Shahudah tsaye kanta tana ribzar kuka da mata fitsara. Sosai kiran da Aamilah ke
mata ya firgitata, ta miƙe zumbur ta fito tanabi matakalar benan da gudu-gudu.
“Haba auta wannan wane irin kirane haka kamar wata baƙauya, miya farune shin
kikemin kiran mafarauta?”. Baki Aamilah ta cuno bayan ta murguɗama Momy kamar wata
sa'arta, kafin cikin taɓara tace, “Kajimin Momyn nan, dama kika samu na taimakeki
na kawo miki labarin da ɗuminsa, toga ɗankican yana haɗa kaya da alama barin gidan
zaiyi”. Sosai gaban mom ya faɗi, batama tsaya saurararta wanne a cikiba ta fice
daga falon da sauri, dafa mata baya Aamila tayi tare da Shahudah data fito idanu a
kumbure.
Qaseem dake ta faman lodama ƙatuwar motarsa kayan yayma momy dake masa
magana kallo ɗaya ya ɗauke kai batare da yace da ita ko ci kanki ba. Muryarta har
zuga take na alamun ɓacin rai tace, “Qaseem wai badakai nake maganaba? Shin
mikukeson maidanine a gidannan kai da Shahudah? shin bazaka nutsu kai ka fahimci
uzirinmuba, Na shiga uku ni Aysha, wane irin mugun asiri wannan yarinyar ta haɗaku
da shine kaida yaronan Jawaad da kuke ɗaukar kowa ɗan iska akan lamarinta?”. Cikin
zafin murya Qaseem yace, “Nifa kin bala'in cikani da surutu hajiya, Please ki barni
nai aikin gabana Mtsooww!!”. Ya ƙare maganar dajan wani wawan tsaki yana ɗauke
kansa ya cigaba da loda kayansa a motar. Mutuwar tsaye kawai Momy tai tana
kallonsa, Aamilah ta kwashe da dariya tana kallonsu, “Faɗan Uwa da ɗa abin birgewa,
kucigaba da gashi guys”. Baki Shahudah ta taɓe tana mai juya manyan idanunta alamar
zubama Qaseem harara, tace, “Ɗan jaraba duk bakai kaja manaba, wani iyayi da ƙwala
kai a farantinne ya kaika nacema banzar yarinyarnan ƙazamiya mara gata, idan da
baka maƙale matanba ta gidan uwarwa aurena da naka zasu haɗu ballema har bb ya
aikata haka, asararre kawai mai baƙar zuciyar tsiy.....”
Jikake tasss!! Qaseem da babu wanda ya lura da isowarsa gaban Shahudah ya
sauke mata wani wawan mari, ƙasa ta zube tana garsheƙ

ar kuka daja masa ALLAH ya isa, to daman zuciyar ƴan mazan a kusa take, neman wanda
zai amayarwa yakeyi, gashi ya samu cikin sauƙi, dan haka ya shigar tamkar an
aikosa. Duk ihun da Aamilah keyi da Momy bai sauraresuba, sai ma tsarabar mari
Aamilah ta samu itama, Momy kuwa ya hankaɗeta. Qaseem yanada Masifaffiyar zuciya
irin wadda idan ta yunƙuro ɗinan sam bayajin bari, dan tamjar zugasama yake, sannan
shifa cinnakane baisan na gidaba. Wanna. mugun zuciyan da ALLAH ya basu shida
Jawaad itace ta hanasu zama ƙarƙashin inuwa ɗaya, dan kowa yanaji da kalar tasa,
kawai shi Qaseem yafi Jawaad saurin fushine, dan Jawaad na dannewa yay kawaici har
saika kaisa ƙarshe, amma ga Qaseem sam ba haka bane, sha yanzu magani yanzu, ga
kuma ɗanbanzan riƙo saikace dangin kutare🤦🏻.
Iya gwargwadon iko babu algus Shahudah ta daku harma da Aamilah daya koma
haɗawa daga ƙarshe, dama yanajin haushinsu akan abu biyu, dukan Bilkisu da jimata
ciwo, saikuma gudunmawar da suka bada akan ai masa aure da Azeema. Daƙyar da suɗin
goshi baba mai gadi da kuku suka amshi Shahudah da Aamilah a hannunsa, dan yay musu
kaca-kaca abinka da farar fata, Shahudah harda fasa mata baki akai jini sai ɗiga
yake. Yace, “ƙananun marasa kunya, daga yau idan harku kun cika tsagerune dan ALLAH
kusake shiga cikin al'amurana”. Kuka kawai suke daga su har Momy, babu wanda ya iya
tanka masa har kuku da baba mai gadi suka gama loda masa kayansa a motar, sashensu
ya koma ya ɗakko sauran tarkacensa ya shige mota ya fice batare da ya sakebi
takantaba.

Kai tsaye gidansa ya zarce, dama harya ajiye mai gadi tun jiya, kodaga
waje kasan gidan ya haɗu, ya mugun ƙawatuwa da shukoki masu ƙamshi da daɗi, ga
ƙamshin sabon fentima na tashi. Dakansa yayta shiga da kayan, da yake ALLAH yayisa
mutum mai hanzari da zafin nama sai gashi ya gama sakasu ciki tas.

★★★★★

Bayan barin Qaseem gidan babu jimawa Dad ya dawo, iske Momy yay zaune ta
zabga tagumi, Shahudah na kwance barcin wahala yay gaba da ita ta ɗora kanta a
cinyar momyn. sai Salman da Aamilah dake lido a d/table. duk sannu sukai masa, ya
amsa yana zama kusa da momy tare da kamo hannunta cikin nashi. “Humairah mike
faruwane?”. Muryarta na rawa tace, “Qaseem ne ya tafi?”. “Ya tafi? Ina ya tafi
to?”. “Muma bamu saniba, ya kwashe duk kayansa na gidannan”. Cikin taune leɓe Dad
yace, “Bari dai zamuyi magana, yanzu tare nake dasu Alhaji Nasir suna falon baƙi,
mun kira yaronan ne da aka ɗaura aurensa da mamana zaizo”. Zumbur Momy ta miƙe
jikinta har rawa yake ta ture kan Shahudah batare data tuna tana jikinta tana
barciba, tace, “Ya yarda ɗin zaizo Dadynsu?”. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Eh
ya amince, drivern Alhaji Nasir ma yaje ɗakkosa”.

________________________________

Bayan Jawaad ya dawo daga sallar magriba shiryawa yay ya amsa kiran da
Alhaji babba yay masa, kansa ciwo yake masa, amma bashi da ikon bijirema kiran
kakan nasa, ballema yaji muryarsa wani iri kamar yana tare da damuwa, tun da ranama
ya fahimci hakan, ya haƙurane kawai ya barsa da yace masa babu komai..
Fitowa yay yanata baza ƙamshi, sai dai fuskarnan a cinkushe babu walwala.
ya tsaya suka gaisa da mai-gadi har yake tambayarsa gimba bai shigo bane?. mai-gadi
yace, “Aiko bai isoba Oga, ni harma na fara tunanin ko lafiya? Dan tunda ya tafi
bamuyi wayaba kuma kaga har lokacin daya saba dawowa ya shige amma shiru”. Jimm
Jawaad yay alamar tunani, dan shima dai tunda gimba ya tafi basuyi wayarba kam, to
wannan hargitsicinne ya ɗauke masa hankali gaba ɗaya har bai ɗauki hakan komaiba.
Ya ɗan sauke numfashi yana kallon mai-gadin. baba bara dai naje na dawo, idan har
lokacin bai shigeba saina nemesa naji mike faruwa?”. Mai gadi yace, “To to ba laifi
oga, ALLAH ya maidoka lafiya”. “Amin” Jawaad ya faɗa yana ficewa, sai dai acan
ƙasan zuciyar tasa maganar gimba taƙi gushewa.

A ƙofar gida ya iske Alhaji babba zai shiga massallaci, dan haka yay
fakin anan waje ya fito suka shiga tare, bayan sun fito Alhaji baba yay sallama da
mutane maƙwaftansa da ragowar ƴan anguwa masu salla anan kamar yanda ya saba, kafin
ya kama

hannun Jawaad dake masa shagwaɓan shifa fura zaisha, Alhaji babba ya bada a siyo
masa. Alhaji babba dake murmushi ya tsaya yana dungure masa kai, “Kai miyasa idan
rikicinka ya motsa babu wanda ka raina saini? Kaje kaima su Mariya mana”. Fuska
Jawaad ya yatsine saboda ciwon da kansa ke masa yace, “Nidai ka daina sawa gaban
mamana na faɗuwa a darenan, kabama Tanimu ya sayo mani inba hakaba bazan sake zuwa
kwana gidanka ba”. Dariya Alhaji babba yay da jan hannunsa suka cigaba da tafiya,
yace, “Yoni ALLAH na tuba aina yayeka da zuwa kwanarmin gida, matarka ta jajiba
nima na huta da rigimarka hakanan”. Jawaad yace, “Basai na ɗakkota muke kwana anan
ɗin tareba”. “Bana gayya, ku zauna gidanku nima aure zanyo”. Ciki dauriya Jawaad ya
ƙyalƙyale da dariya, koba komai yarage nauyin da zuciyarsa tayi da tattaunawa da
kakan nasa, shi kansa Alhaji baba sai yaji damuwarsa ta sassauta.

Bayan sun zauna Alhaji baba ya zubama Jawaad fura mai ƙyau da daɗin gaske
da bai rabo da ita ya dubesa, cike da jin daɗi yake shan furan sanyinta na ratsa
masa zuciya da ƙirji. “Muhammad kasan miyasa na kiraka kuwa?”. Kallonsa Jay yayi ya
girgiza kansa batare da yace komaiba. Alhaji baba ya ɗan sauke numfashi, murya a
sanyaye yace, “Akan matarkane” Saida Jawaad ya haɗiye furan daya sha kafin yace,
“Matata kuma?”...............✍

Ƙyan alƙawari cikawa, sai dai wanda na ɗauka ni ya gagara cikar dalilin birkicewar
wattpad, harna fara canja page ɗinma sai ALLAH ya taimakeni ya dai-dai ta🤦🏻, page
ɗinnan kaɗai gareni babu nagobe saboda matsalar wattpad ɗinan ta ɗauki hankalina
banyi typing ba, ƴan telegram sunce a turo muku kawai, amma da wuya kujini gobe
idan ALLAH ya kaimu zan samu nayi typing ɗin jibi idan munada rabon kaiwa. Gaisuwa
ga kowa da fatan alkairi😍😍😘😘.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻


✍🏻
[12/15/2020, 2:54 PM] HASNA : Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
Page 28

................Alhaji babba ya gyaɗama Jawaad kai alamar eh ita. Cike da mamaki


Jay ya ajiye kofin hannunsa yana tsatstsare kakan nasa da idanunsa cike da sonjin
ƙarin bayani.
Murmushi Alhaji Babba yay masa tare da kamo hanunsa, “Daina tsareni da
waɗanan idanun naka ba wani abu bameba, kawai inason sanin dangin mahaifinta ne”.
Sassanyar ajiyar zuciya Jawaad ya ɗan sauke, kafin shima ya riƙe hanun Alhaji Babba
da ƙyau a cikin nashi, “Baba nima inason saninsu, sonake kawai wannan ƙurar ta lafa
itama ta sakejin sauƙine”. Alhaji babba yace, “Kayi tunani mai ƙyau, inason kayi
ƙoƙari ka bincika, sannan yaya maganarka da mutanen gidanku? Da kuma maganar shi
wanda kasa ya auri yarinyarnan ta wajen Ali?”.
Murmushi Jawaad ya ɗanyi ya ɗauki furarsa zai cigaba da sha, ganin zai basar
da zance Alhaji babba yace, “Nasanfa ka jini”. Ƴar dariya Jay yayi yakai kofin
bakinsa, “ALLAH ka iya rigima kaima tsohon nan, karka damu ina sane da komai”.
“Nasan kana sane da komai Muhammad, sai dai hankalina ya tashi matuƙa jin ba
mutumin kirki bane habibun, kajifa wani suna da Nasiru ya kirashi dashi ranar”.
Jay yay murmushi kawai batare da yace komaiba.

Sun cigaba da hirarsu har zuwa ƙarfe tara ya fita, yaso zuwa asibiti, amma
ganin dare yayi sai ya haƙura ya nufi gida abinsa. A gate ya tsaya ya tambayi mai-
gadi ko gimban ya dawo?. mai-gadi ya tabbatar masa da bai dawoba, ya kira wayarsa
kuma gashi tana ring amma ba'a ɗagaba.
Sosai abin ya ɗaurema Jawaad kai, daga baya kuma ya ajiye tunaninsa akan
inhar da safe bai dawoba zaisa abi bayansa garin nasu aga ko lafiya?. Da wannan
tunanin yay shirin barci ya kwanta.

_________________________________

Su Dady sun karɓi baƙuncin surikinsu habib, duk yanda Dad yaso su Momy
su zauna basai sunzo falon baƙiba hakan ya gagara, dole ya barsu sukabi bayansa, ba
ƙaramin tashin hankali Shahudah ta shigaba da ganin wanda ake kira wai matsayin
mijinta, daka gansa kaga cikakken tantiri marajin magana, cike da isa ya zauna a
kujerar da aka nuna masa sai wani cika yake da batsewa.
Ya kafe Aamilah da Shahudah da kallo yana wani lasar laɓɓa tamkar tsohon
maye, ko kunyar su Dad bayaji, dama daya shigo babu wanda ya gaida, bama su ishesa
kallon arziƙiba.
“Wace cikar tawa anan?” yay maganar cike da gadara. Babu wanda ya tanka masa
a cikinsu, sai Shahudah da Aamilah da suka zuba masa wata shegiyar harara. Ya bushe
da dariyarsa mara daɗin ji yana faɗin, “Dama ace ana auren yaya da ƙanwa wlhy da
duk haɗawa zanyi hhhhh! Dana kwashi gara aradu...” cike da tsiwa Aamilah da tafi
Shahudah jin hausa tace, “Uwarkane garan shege mai suffan aljanu.....” wata wuta
data gitta ta idanunta mai stars ce ta hanata kaiwa ƙarshe, lokaci ɗaya jinta da
ganinta ya ɗauke baki ɗaya ta zube a jikin Dad daya tarota. Babu wanda yaga sanda
Ɗan-fir'auna ya ƙarasa gaban Aamilah sai ƙarar maruka sukaji kawai.
A fusace Dad yace, “Kai ƙaramin ɗan tsagera, wanene ubanka da har zaka
mararmin yarinya a gabana?”. Kallon dad ɗan fir'auna yay ya watsar, kafin cike da
gadara yace, “Sanin ubana a gareka dattijo ai tamkar yankewar numfashinka ne, dama
kun kiranine domin kuci zarafina komi? kunga dalla malamai ku bani matata na wuce
na fasa zaman....” da sauri Uncle Uwaisu ya taresa cikin lallashi yana bashi
haƙuri, amma fir ƴaki sauraren kowa, Aamilah dai ta farfaɗo da ƙyar bayan an zuba
mata ruwa, Shahudah na rakuɓe lungun kujera sai tsiyayar da hawaye takeyi jiki na
rawa, harga ALLAH tsoronsa takeji, a ranta kuwa ayyanawa take ashe Bilkisu
baturiyace, dan ɗan-fir'auna ALLAH ya bashi baƙi, wanda daga gani kasan shaye-shaye
ya sake taka rawar gani wajen ƙara masa shi. Da ƙyar suka samu ɗan-fir'auna ya
zauna bayan an saka Shahudah da Aamilah sunbar falon, Salman kam yay laƙe kamar
baya falon (hege yaga maza🤣😜).
Duk yanda su Uncle Nasir sukaso lallaɓa ɗan-fir'auna akan ya saki
Shahudah yace shifa sam baisan wannan zanceba, dan yanzuma da shirin ɗaukar matarsa
yazo yana buƙatar abinsa, tunda yana zamansa aka kawo masa tallansu. Har ƙasa Momy
ta duƙa tana kuka da roƙonsa amm

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]


a sai dariyar wulaƙanci da cusa haushi yake musu.
“Kungafa kubar ɓata lokacinku akan roƙonama, tayaya kuke tunanin zanyi sake
da wannan babbar kaddarar ne haka, yo ko shugaban ƙasa ai nafishi hura hanci yanzu
akan wannan cikar tawa, ku manta kawai a saimin royal bed zan kama hayar gida aje
aimin jere gobe, babu damuwa idanma kunkai sati danshi shiri wuyane dashi, ko a
hotel mayi amarcin satin guda kafin ku kammala surukai..” ya ƙare maganar da miƙewa
yay salute nasu zai fice. Da sauri Dad yace, “Nawa kake buƙata a biyaka ka sakarmin
yarinya?”.
Tsayawa ɗan-fir'auna yayi, ya juyo yanama Dad wani matsiyacin kallo maiban
tsoro, sai kuma ya bushe da dariya tare da dawowa da baya. Yace, “Zan iya amsar
kuɗi na saketa pale, tunda yanzu na auri ƴarka ka zama pale ɗina nima, ammafa
kasani saina ɗanɗana kona sati ɗayane dan yawuna ya biya, a shiryata da safe nazo
na amshi kayata, nanda sati biyu saiku cakemin naira miliyan hansin na baku ƴarku,
idan haka bai mukuba kuma banida matsala, iyakaci inta mata ciki duk bayan wata
tara ta ringa juyen jajayen ƴan dugwi-dugwi irinta, koba komai na samu surukai masu
kuɗi nima nan gaba tunda naga jar fatar ake yayi yanzun” ya wani ɗage musu gira
cike da barikanci yay ficewarsa.
Babu wanda bai jiƙe da zufaba a falon, tun fitar ɗan-fir'auna babu wanda
ya iya magana sai kuka Momy dake tashi. Salman ya miƙe cikin raɗa-raɗa yace, “Wlhy
kuyi ƙoƙari ku biyashi, dan wannan dagani zai iya take mutum ya yanka tamkar ya
yanka kazar gidan gona, ku rufa mana asiri dad dan kuwa su momy sun kwaso mana
bala'i, wlhy barin ƙasarnan zanyi idan an gama watandarku na dawo zaman gaisuwa”.
Ya ƙare maganar da ɗai-ɗai yana kallon ƙofa, da gani kasan a tsorace yake (Kana
bani yaji Salman🤣, lusarin banza😠).

WASHE GARI.

Dad na zaune a harabar gidansa abin duniya ya taru ya masa yawa, tunda
ya dawo sallar asuba bai iya shiga cikiba, a daren jiya da ƙyar suka samu Shahudah
tai barci, dukta gama fita hayyacinta.
Baƙon da aka turo daga masarautane ya samu isowa, ya ƙwanƙwasa gate mai gadi
ya leƙa, sai da suka gaisa sannan yace, “Magatakarda ne daga masarautar gagara
badau, an aikoni domin isar da saƙo ga Alhaji Ali ko yana nan?”. Mai-gadi yace,
“Ƙwarai yana nan, sannu da zuwa bara a sanar masa”.
Sai da baba mai-gadi yay sallama sau kusan uku sannan Dad ya jisa, bai amsaba
sai zuba masa idanu da yayi. Baba mai-gadi yace, “Alhaji baƙone wai daga
masarauta”. “Masarauta kuma? Ni miya haɗani da masarauta malam Amiru?”. “To Alhaji
wlhy ban saniba, yadaice daga can yake”. Da hannu kawai Dad yay nuni alamar baƙon
ya shigo. Baba mai-gadi ya koma domin shigo dashi.
Sai da baƙo ya zauna a kujerar robar da baba maigadi shima ya ajiye masa
sannan suka gaisa da Dad, cikin nutsuwa magatakarda ya korama Dad bayani akan
gimbiya ta bada umarnin Bilkisu zata koma masarauta da zama har sai ranar tarewarta
gidan mijinta. rasa abinda ma zaice Dad yayi, sai tsurama magatakarda ido yay
kamar zai haɗiyeshi dasu. Har magatakarda yaymasa sallama ya tafi bai dawo
hayyacinsa ba, sai faman juya takardar hannunsa da magatakarda ya kawo yakeyi, shi
yanzu abin tambayarsa anan Bilkisu ce takai ƙararsa masarauta kokuwa Jawaad? Kai
yasan halin Jawaad da shegen taurin kai, bazai taɓa kai magana masarauta ba dan
tsaurin idonsa bazai barsa ganin ya gaza ba. To amma bai zaton Bilkisu nada irin
wannan wayon, kuma itada takema kwance a asibiti. Gaba ɗaya ransa ya kuma jagulewa,
cike da sassarfa ya tashi ya shige ciki.

★★★★★★

Jawaad kam koda ya gama shirinsa na office ya fito sai ya iske Gimba
bai dawo ba, mamaki ya kuma cikashi, dan jiya bayan ya dawo ya kira Number gimba
har sau biyu kafin ya kwanta amma ba'a ɗagaba, yanzu kam yafara tunanin babu
lafiya, akwai wani saurayi a gidan da aikinsa kawai kula da flowers ɗin gidanne,
garinsu kusada garinsu gimba yake, hakan yasa Jawaad ya kirashi yanama tsaka da
aikinsa na bayin fulawar. Durƙusawa yay yana gaida Jawaad, Jawaad ya amsa da masa
nuni ya tashi. “Banace ka dainamin irin wannan gaisuwarba Balarabe, kadaina min
wannan durƙuson kamar

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]


wani mai neman gafara kaji”. fuskar balarabe ɗauke da murmushi yace, “Alhaji nagode
sosai, amma nariga na sabane, koba aiki nake ƙarƙashin kuba aika girmeni nesa”.
Girgiza kai kawai Jawaad yayi, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙa masa 3k, “Balarabe
ajiye aikinnan naka zakai dan ALLAH kaje garinsu Gimba ka ganomin ko lafiya yake?
aikasan garin ko?”. Da sauri balarabe yace, “Eh Alhaji, ai daga garinsu zuwa namu
da ƙafama muke zuwa, kuma har gidansa na sani tunda naje sunan yaronsa da aka haifa
masa na ƙarshenan mai sunanka”. “Okey Alhmdllh, kayi ƙoƙari kaje yanda zaka dawo da
wuri, bani number ka na kira kaga tawa, daka isa kasan halin da yake ciki ka kirani
na sani kafin ka juyo”. Cike da girmamawa balarabe yake sauraren number da Jay yake
faɗo masa yana sakawa a wayarsa nokia, bayan ta cika ya kira shima jay yaga tashi.

Mota Jawaad ya shiga, yau da kansa yay driving, kai tsaye asibiti ya
nufa, sai da yaje suka gama magana da likita sannan ya nufo ɗakin da Bilkisu ke
jiyya. Sallama yay suka amsa, kafin ya tura ƙofar ya shiga.
Kasa ɗagowa nai in kallesa, dan wata matsananciyar kunyarsa nakeji a raina,
cikin girmamawa ya gaida mama, aunty Batool ma ta gaidashi da tsokanarsa,
gaisuwarta kawai ya amsa bai maida mata magana akan tsokanarsa da takeba, na ɗago
ido kaɗan nai masa kallo ɗaya na janye da faɗin, “Ina kwana”. shiru kamar bazai
amsaba, sai da ya ajiye kwalin maganina daya ɗauka yana dubawa sannan yace, “Lafiya
ya jikin?”. Ahankali nace, “Naji sauƙi”.
Jawaad ya ɗauke kansa daga Bilkisu ya maida ga mama, “Mama Doctor ya
sallameta, saiku haɗa kayanku, zanje office yanzu, nanda awa ɗaya zuwa biyu zan
dawo sannan ai kun kimtsa”. Mama tace, “To to Alhmdllh, ALLAH yasa haka shiyafi
alkairi, to amma kayanta fa? Kasan komai yana can gidan”. Ɗan jimm Jay yayi idonsa
akan Bilkisun, ya sauke numfashi kaɗan yana ɗauke idanunsa, “Inaga mu manta da
zancan zuwa gidansu yazu, bara naje na samo mata wasu kayan kawai”.
Jin abinda yake faɗama mama yasa na ɗago da mamaki na kallesa, hakan yay
dai-dai da shima ya juyo gareni, idanunmu ne suka shige cikin na juna, nai azamar
janye nawa da fargabar ina kuma zan koma? Badai gidan nasaba? yanzu har rashin
gatana yakai irin haka da.......
Katsemin tunani yay da cewar, “Dami-dami kike buƙata?”. Idanuna cike da ƙwalla
na ɗago na kallesa, ganin har yanzu ni yake kallo saina maida kaina ƙasa, muryata
cike da tahowar kukan da nake dannewa nace, “Miyasa bazan koma can ɗinba?”. Banza
yay bai amsa minba, hakan yasa hawaye masu zafi suka silalomin akan kumatu. Sautin
siririn tsakinsa kawai naji, cikin faɗa-faɗa yace, “Haka na gadama dole kuma hakan
za'ayi, idan kuma kika nema dagulan lissafi ALLAH yau ɗinan zaki tare”. Babu shiri
na ɗago kai da sauri, wata uwar harara ya zubamin. Dole na maida kaina ƙasa. Wata
ƴar ƙwafa yayi, sai takunsa ya biyo baya, kafin naji buɗe ƙofa da rufewa alamar ya
fice abinsa. Koda na ɗago sai naga ashe daga ni sai shine ma a ɗakin, sam banji
sanda su mama suka fitaba, dukda inajin motsin ruwa a bayi alamar ɗaya na ciki
ɗayane ya fita.
Gaba ɗaya zuciyar Jawaad a jagule take, sai dai jarumtarsa ta ɓoye hakan,
shi mutumne tamkar kowa, yana farin ciki yana baƙin ciki, yana shiga matsala yana
shiga tashin hankali, kawai dai ALLAH yayisa mai zuciyar dakiyane kamar yanda ALLAH
yay mafi yawan maza da juriya akan abu komin zafin da sukeji akan al'amari. Tafiyar
da bata wuce mintuna goma ba ya isa wani haɗaɗɗen boutique, yanda suka tarbesa zai
tabbatar maka da an masa farin sani a waje, sai gaidashi suke cike da girmamawa.
Wani mai tsananin kama da Jabeer ne ya fito daga wani lungu, ganin Jay ya sashi
faɗin, “Yah Jay barka da zuwa”. Kallonsa Jay yay daɗan murmushi yace, “Yauwa
Kabeer, ya kasuwar?”. “Alhmdllh Yayah, kanason wani abune?”. Kai kawai Jay ya kaɗa
masa kafin ya miƙe a kujerar da yake zaune. Yana gaba Kabeer na biye dashi har
wajen da kayan mata suke, tsala-tsalan jallabiya da ƙananun kaya harma da ɗinkakkun
atanfofi da shadda duk sunda. Ahankali yake binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, karon
farko a rayuwarsa da yazo saima ma

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]


ce kaya shi ɗaya, ko sanda suna tare da Shahudah hakan bai taɓa faruwaba, dan ita a
tsarinta bata sayen kaya anan saina ƙasashen ƙetare, hakan yasa koda yaga abu ya
burgesa baima taɓa wahal da kansa wajen saya matanba.
Ganin ya kasa ɗaukar komai kabeer yace, “Yah Jay aida ka kira ka faɗi duk
abinda kake buƙata bama saika zoba”. Guntun murmushi jay yay masa kawai daɗan taɓa
kafaɗarsa, kafin ya fara nuna masa duk abinda yay masa wanda ya ƙiyasta a ransa
zaiyi dai-dai da jikinta, saida ya ɗauka kaya kusan kala goma sha biyar, sannan ya
ɗauka takalma uku da hijjabai huɗu ya zaɓi akwatin da za'a zubasu. Yasan dolene ƴa
mace budurwa kamarta ta buƙaci kayan ciki, to amma shi ta ina zai fara tunda ba
sanin seize ɗinta yayba. Kallon sashen da kayan suke yay, gasunan kala-kala kuma
duk seize ɗin da kake buƙata zaka samesu, yaɗan yatsina fuska kafin ya nufi wajen,
amfani yay kawai da yanda yake hasasota cikin idanunsa ya ɗauka matasu aka haɗesu
da waɗancan. Card ɗinsa ya bama Kabeer, ganin kabeer na wani noƙewa akan baza amshi
kuɗinba dan harya kira Jabeer ya sanar masa ga Jawaad ɗin a wajen yace karsu amshi
kuɗi su rubuta su aje idan yazo zai biya. (Wajen na Jabeer ne, ƙaninsa kabeer ke
kula dashi sai sauran ma'aikata). Cikin sosa ƙeya Kabeer yace, “Yah Jabeer yace
karna amsa”. Sosai Jay ya kafesa da idanunsa da yau gaba ɗaya babu haske a cikinsu
saboda damuwa. “Kiransa kai ka faɗa masa nazo?”. Kasa cewa komai Kabeer yay sai
faman susar ƙeya yake, Jay yay gaba a binsa zuwa mazaunin kabeer ɗin da yake shine
mai amsar kuɗi. Ɗaya daga cikin yaran wajen ya kira ya duba masa kuɗaɗen duka kayan
aka zubasu a akwati, shikuma ya saka card ɗinsa ya cire adadin kuɗin yay ficewarsa
aka bisa da kayan.

★★★★★

Fitar jay babu jimawa a asibiti Qaseem yazo, cike da mamaki Bilkisu ke
kallonsa jikinta sai rawa yake dan tunda ta kwanta a asibitin nan sai yau ta gansa,
baiko kalli mama ba balle ta samu darajar gaisuwarsa ya finciki hannun Bilkisu dake
zaune bayan ta kimtsa suna jiran dawowar Jawaad, da sauri mama ta riƙe Bilkisun da
faɗin, “Lafiya kuwa Qaseem? Ina zaka kaita?”. Wani banzan kallo ya mata yana figar
bilkisu batare daya tankaba, itako kuka take iya ƙarfinta da roƙonsa ya sake mata
hannu karya jimata ciwo, amma sam yaƙi sauraren kowa. Tun suna ɗaukar abin wasa har
yanema fin ƙarfinsu, dan Doctor ma yazo ya basu sauran maganin bilkisun shima ta
ritata dashi. Rikici bana wasaba ake kwasa da Qaseem har ALLAH ya maido Jawaad
asibitin. Tunda ya gabato wajen yakejin hayaniya, cike da mamaki ya shiga dan ƙofar
a buɗema take. Idanun sane suka fara sauka akan hannun Qaseem dake riƙe dana
Bilkisu, tuni idon ƴan mazan ya rufe, a wata irin matsananciyar tsawa yace, “Qaseem
sake mata hannu!!”. shi Qaseem ma sai yanzu yaga Jawaad ɗin, shima a fusace yace,
“Anƙi a saki ɗin, koka saketa, koma karka saketa zan wuce da itane”. Saukar wani
bahagon bugu kawai Qaseem yaji akan damtsen hannunsa, ai baimasan ya saki hannun
Bilkisu ba saboda gaba ɗaya jijiyar hannunsa ta saki lokaci guda saboda azaba,
kafin ya gama dawowa hayyacinsa Jay yaja hannun Bilkisu dake kuka sun fice daga
ɗakin. Ganin haka yasa Doctor saurin rufe ƙofar ya kulle danya bama jay damar barin
asibitin gaba ɗaya.
Kuka bily take cin ƙarfinta har suka hau titi, jin ta cika masa kunne
yasashi taka wani wawan birki da batasan sanda tai tsale ta koma jikinsa ba. Sai
jinta kawai tayi zaune ɗare-ɗare bisa cinyarsa ta cusa kanta a ƙirjinsa tare da
ƙanƙamesa. ALLAH ne yaso Jawaad ya tsaida motar, da babu abinda zai hana su kife a
hanyarnan. Gaba ɗayama sai ya kasa cemata uffan, sai rumtse idanunsa da yay yana
mai cije leɓensa na ƙasa da masifar ƙarfi kamar zai hudashi.
Jin shiru mun tsaya ga ƙamshin turarensa yay mugun addabar hancina
haryazama shine iskar da nake shaƙa ya sani ɗagowa, sosai na zabura ganina a jikin
boss ɗare-ɗare, innalillahi.... Na shiga ambata ina rawar jikin sauka, harna koma
inda na baro bai motsaba, nikuma ban iya kallon fuskarsa ba saboda tashin hankali
da matsananciyar kunyar dana tsinta kaina a ciki. Jin tsahon mintuna biyar yaƙi
cewa komai yaƙ

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]


i kuma ya cigaba da tafiya yasani satar kallonsa ta gefen ido ina share hawayena da
sukaƙi tsayawa. A kife yake kan sitiyari bana ganin fuskarsa, tsorone ya sake
kamani, murya na rawa nace, “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy tsorata nayi”. A fusace ya
ɗago yana watsamin wani irin harara, yanda idanunsa sukai matuƙar jazur fiye da
farkone ya kuma ɗagamin hankali. A kausashe yace, “Idan baki rufemin bakiba saina
canja miki kamannin fuska! Saboda na raboki dashi kikemin wani kukan banza da
wofi?!!”. Da sauri na shiga girgiza masa kai ina mannewa da ƙofa, dan yanda yay
maganar tamkar zai haɗiyeni ɗanyane, ni tun lokacin da naga fushinsa nake tsoron
cigaba da ganin hakan. Yay ƙwafa da ƙara zubamin harara, “Share waɗanan banzayen
hawayen”. Saurin saka ƙasan hijjab ɗina nai na goge tas kamar yanda ya buƙata, sake
ɗauke kansa yay daga gareni Batare da yace komaiba ya tada motar da fusgarta muka
cigaba da tafiya.

Duk da hankalina a tashe yake da yanda yake zuba gudu a titi ban sake gigin
yin wani abuba, sai kaina dana tusa a cikin cinyoyina ina addu'ar ALLAH ya kaimu
lafiya dukma inda muka nufa.
A halin da yake ciki yanzu bazai iya shiga masarauta hakaba, hakan yasa yay
fakin daga waje, fita yay da waya a hannu, bayason kiran gimbiya dan haka ya maida
akalar kiransa ga dattijon nan, bugu biyu kuwa ya ɗaga suka gaisa, Jawaad yay masa
bayani a taƙaice. Dattijo ya amsa masa da sujirasa gashi nan zuwa. Babu jimawa kuwa
yazo tare da Amaturrahman data rikice da murnar ganin Bilkisu. Basu wani ja zanceba
ya basu Bilkisun batare da yace mata uffanba akan hakan, saida ya juya zai shiga
motarne ya dubeta sau ɗaya ya ɗauke kansa da faɗin, “Ki shirya gobe zaki koma aiki,
zan biyo na ɗaukeki” daga haka yay tafiyarsa. binsa tai da kallo har saida ya tada
motar yabar wajen itama suka shiga motar dasu Amaturrahman suka fito da ita.

__

Asibiti Jawaad yay niyar komawa dan yayma Qaseem dogon gargaɗi, sai dai
tunanin barinsa ya samesa har gida ya sakashi sharewa, juya kan motar yay zuwa
station zuciyarsa fal tunane-tunane, ga aiki jibge a gabansa da baisan iyakaba, ga
kuma matsaloli kala-kala da yarasa makamar dazai kama domin fara warwaresu. Saƙon
ɗan fi'auna ne yazo masa arai, har ya shiga office ɗinsa yana juya zancen a ransa,
‘Mi ɗan fir'aunan ya sani a kansa da haryake iƙirarin ya basa har naira miliyan
hamsin domin ya sanar masa? Shin waishi yaron nanma wanene shi? Kuma a ina su Momy
suka samosa?’. Wannan tunanin da yazo masa a raine ya sakashi dakatawa daga ƙoƙarin
kunna Computer gabansa da ya kai hannu zaiyi, komawa yay jikin kujera ya kwanta
yana lumshe idanunsa.
A haka Aliyu ya shigo ya samesa, sai da yay masa sallama har biyu sannan ya
farga da shi, ya buɗe idanunsa da tashi zaune sosai, tie ɗin wuyansa ya sassauto
ƙasa yana kallon Aliyu daya zauna. “Boss lafiya dai?”. Aliyu ya faɗa idonsa akan
Jawaad, sassanyan numfashi jay ya sauke da cewa, “Lafiya lau Aliy”. Badan Aliyu ya
yardaba ya ƙyalesa, saima takardun hanunsa ya miƙa masa yana masa bayani. Jawaad ya
amsa ya duba ya sake miƙama Aliyun, magana suka ɗanyi Aliyu ya tashi ya fita.
Koda Aliyu ya fita Jay kasa haƙuri yay ya ɗauka waya ya shiga neman ɗan-
Fir'auna, tana gab da katsewa aka ɗaga, daga can wanda ya ɗaga ɗin ko sallama
baiyiba balle batun gaisuwa yace, “Mai wayar yayi Accident yana asibiti”.
“...Accident?” jay ya maimaita da maɗaukakin mamaki tare da sake kiran wayar dan
har an katse.............✍

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]


iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻[12/16/2020, 2:27 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:


Page 29

...............Yanzunma dai saida taje gab da yankewar aka sake ɗagawa, sai dai
yanzu ba'ace komaiba, cikin ɗan zafi-zafi Jay yace, “A wane asibiti ne?”. Ɗan jimm
wancan yay, sai kuma cayay General”. Yanke wayar kawai Jay yayi batare da shima
yace komaiba, maida akalar kiran yay ga Jabeer, bigu biyu ya ɗauka, bayan sun gaisa
Jay yace ya fiyo zasu fita. Iyakar abinda yace kenan ya katse kiran ya miƙe, rigar
suit ɗinsa daya cire tun shigowarsa yay hanging a bayan kujerar zamansa ya ɗauka,
tare da ƙaramar bindiga ya tura a gefen ƙugunsa ya fice.
Tare suka fita shi da Hafiz da Jabeer, dan Aliyu akwai aikin da yakeyi. Koda
suka isa General hospital emergency suka nufa kai tsaye, tunda ance Accident can
tunaninsu ya fara basu su duba farko. Hafiz ne yay tambaya duk da basu da tabbas
ɗin cikakken sunan ɗan-Fir'auna bayan Habib, sudai ma'aikatan asibitin dake
Emergency ɗin basu ganeba, amma alamun da suka gani na cewar su hafiz jami'an
tsarone yasa doctor zagayawa dasu kaf gadajen dake cikin Emergency room ɗin suna
dubawa, babu ɗan-fir'auna anan ɗin. Doctor yace, “To akwai dai wani da aka kawo
tunda safe yayi accident, mun bashi ɗaki awa ɗaya data wuce, al'amarinsa akwai
ruɗarwa, daga baya ƴan uwansa sukazo suka ɗaukesa duk da yana cikin mawuyacin
hali”. Jabeer ne yace, “Suka ɗaukesa kamar ya? Baiji ciwo bane?”. “Yaji ciwo sosai
yallaɓai, dan ko farfaɗowa ma bai gamayiba mundai dubasa babu karaya sai raunika?”.
Kafin Jabeer ya sake magana Jay dake gefe yana latsa waya tamkar ba saurarensu
yakeba yace, “Miye sunansa?”. Yay maganarne ba tare da ya ɗagoba, dan yasan idan
har Dr Tayyeb ya gansa tsorata zai yaƙi faɗar komai.
Dr Tayyeb dai yasha jinin jikinsa akan Jay, sai dai da yake bai ganin
fuskarsa da ƙyau sai ya daure yace, “Kamar dai Habibu ƙaura suka bada a jikin
katin”. Jay baice komaiba dan ya fahimci dai ɗan fir'auna ne, sai kawai ya nufi
hanyar fita. Ganin haka yasa su Jabeer yima Doctor sallama suka biyoshi. Acikin
mota suka iskoshi, sai da suka shiga suma Hafiz yace, “Boss yanzu a ina zamu ganosa
kenan?”. Jawaad da har yanzu hankalinsa naga waya batare daya ɗagoba yace, “Anguwar
kuke”. Tada motar Jabeer yay sukabar asibitin batare da sun sake cewa komaiba, dan
sun lura akwai abinda yakeyi mai muhimmanci a wayar.
Sun shiga Anguwar Kuke, inda Jay ya sanar musu dai-dai inda zasu tsaya, a
tare suka fita a motar, Jawaad yay gaba suka bisa a baya har zuwa jikin jan gate,
gidan bawani gidane mai ƙyauba, dan irin ginin da ɗin nanne, sai dai a da ɗin
maishi ya kasance mai arziƙi, a rufe ƙofar take, hakan yasa Hafiz ƙwanƙwasawa.
Kusan mintina biyar suna tsaye kafin a buɗe a fusace, kodamar tambayarsu suwanene
su? wanda ya buɗe ɗin baisamuba Jay ya turashi gefe ya shige su Jabeer na biye
dashi. Duk tsagerancin tsagera idan yay gamo da wanda ya fisa tsageranci nutsuwa ya
keyi, hakan yasa saurayin bai iya cewa komaiba ya maida ƙofar ya rufe shima yabi
bayansu dan ya gane Jawaad.
Ɗunbin mamaki da al'ajab ne ya sakasu tsayawa cak a ƙofar falon, dan kuwa
gungun samarine da adadainsu zai iya kaiwa goma tsai-tsaye da candles kunne a
hannu sun zagaye katifar da Ɗan-Fir'auna ke kwance a tsakkiyar falon, dukansu
idanunsu a rufe suke babu mai magana bare motsi. Jabeer da Hafiz ne kawai sukai
magana tare da jan birki, Jawaad kam uffan baiceba sai kafawa matasan idanu da yay
a ransa yana nazarinsu. Hannu yasa da ƙarfi ya bugi ƙofar falon, a take duk suka
dawo hayyacinsu, suka juyo suduka suna kallonsa. Su Jabeer dai abin ya firgitasu,
amma a mamakinsu sai sukaga Jawaad ya danna kai cikin falon kamar baiga abinda yake
faruwaba. A baɗini shima kuma lamarin ya firgitashi, sai dai ya danne saboda shi
mutumne mai kasadar tunkarar abu kai tsaye, ko aiki suka fita duk haɗarin waje baya
shakkar shigewa gaba.
Cike da takun nutsuwa Jay ya ratsa ta tsakkiyarsu yana addu'a a ƙasan
ransa har zuwa gaban katifar da ɗan-fir'auna ke kwance samɓal jikinsa duk raunika
wasu ansa bandage, yay wani irin kukkumburewa a fuska saboda buguwar da yayi. Sai
da yay masa kallon mintuna uku kafin ya ɗago ya kalli samarin da suma

suka kafeshi da kallo tamkar zasu cinyesa ɗanye. Yi yay tamkar bai fahimci kallon
da suke masaba, cikin Kakkausan lafazi yace, “Dami yay Accident ɗin?”. Wanda yake
gaba gab da katifar sosai ne ya fara hure candle ɗinsa, sannan ya juya ga sauran
yay musu nuni dasu zauna. Babu musu duk suka zauna ƙasa suka tanƙwashe ƙafafunsu
hannayensu riƙe da candles ɗinsu har yanzu kuma a kunne. Sake maida dubansa yay ga
Jawaad yace, “Yakamata mu fara sanin baƙonmu ai”. Sake ɗaure fuska Jay yayi, kamar
bazai tankaba sai kuma ya gyara tsaiwa da faɗin “Nine na kira waya ɗazun”. Karon
farko saurayin da babu alamar mutunci tattare dashi yay murmushi da cema Jawaad,
“Hutawarka lafiya babba, haɗari yay da mashin yau da asuba, sai dai abin ya haɗa da
mabiya sahu”. Jawaad tsaf ya fahimci ma'anar kalamsa, amma sai yay kamar bai ganeba
yace, “Amma miyasa kuka ɗakkosa daga asibiti? Suwaye ke bibiyar sawun nasa?”. Gayen
yace, “Babba! wannan wasane tsakanin rindunar mafarauta guda biyu, suntaɓo inda
za'a maida gayya da gayyane, dolene tsakaninmu a fidda wanene sarki wanene bawa,
zasu biya diyyar jini da jini karka damu, koma gefe kawai kasha kallo dan muna
respecting ɗinka Babba, aishi sheri ɗan aikene maishi yake komawa, balle idan ka
haɗu da waɗanda suka fika iya sherin, zamu zuba dasu muga wazai kwashe, idan har
sukaci nasara a kanmu na rantse da jinin babata saina yanke kaina da hannuna da
takobin da aikinta kawai shine shan jini”. Kafin Jay ya ƙara magana Ɗan-fir'auna
yay wata irin mimmiƙewa da saki razananniyar ƙara data firgita su Hafiz dake a
farkon shihowa Falon basu ƙaraso ba, shi kansa Jawaad sai da ya toshe kunensa. Abin
mamaki sukam abokan ɗan-fir'auna ko gezau, saima sake miƙewa da sukai da candles
ɗinsu a hannu suka kuma zagayeshi.
Bayan wasu mintuna ɗan-Fir'auna yay shiru sai numfashi yake da sauri-sauri,
kafin kuma a hankali ya nutsu waje guda numfashin na komawa normal. Sake komawa
sauran sukai suka zauna, na ɗazun nan dai me ya sake magana, “Babba karka damufa,
nasan akwai harƙalla tsakaninka dashi, zai miƙe nanda kwanaki kaɗan tunda gashi ya
farfaɗo, alfarmar da muke nema gurinka kawai likitan dazai dinga zuwa gida kullum
yana duba masa waɗanan raunikan”. Cikin haushi Hafiz yace, “Kai kushiga hankalinku,
kufaɗa mana abinda ke faruwa?”. Kafin wancan yace wani abu Jay yay wani munafukin
murmushi da yima Hafiz magana da ido ya ɗauke kansa tare da nufar hanyar fita.
Hafiz ya sake kallon Ɗan-Fir'auna yana mai girgiza kansa, “Shikenan za'a kawo muku
likita”. Shima yana gama faɗa yabi bayan Jay ransa a ɓace. Jabeer da baice komaiba
sai nazarin kayan dake cikin falon shima yabi bayansu..
Kusan a tare suka fito, suna shiga mota Jabeer yace, “Boss miyasa za'a kawo
musu likitan da suka buƙata? Bayan dukkan alamun mutanen banza ya bayyana a
garesu”. Numfashi jawaad ya sauke a hankali yana kallonsu, “Wato Jabeer kowane aiki
akwai salon da yake zuwa da shi, waɗannan yaran da kake ganinsu duk a tafin hannuna
suke, dan duk wani binciken daya dace na kammala yinsa a kansu, mubisu a sannu
domin samun abinda muke buƙata yanda ya kamata”. Kai duk suka jinjina masa cike da
gamsuwa, dan sunsan bazai jefasu a hanyar da bazasu ɓille ba.
Sunbar anguwar Hafiz da Jabeer nata tattauna al'amarin, Jay kam dai yayi
shiru, dan kuwa shi kaɗai yasan mi yake tattaunawa da zuciyarsa. Jabeer yace,
“Wannan duniya nada abin mamaki da al'ajabi da bantsoro, rayuwar waɗannan mutane ta
ƙanƙanin lokaci kawai ka gani ta isa saka zuciyarka tsorata da sake tsarkake girman
ALLAH”. Cike da damuwa Hafiz yace, “Yaran nanfa kamar ba ainahin musulmai baneba
ma, sannan dagani kaga ƴan Cultism”. Jay dai duk dai yana saurarensu, har suka iso
station, office ya wuce ya cigaba da aiki biyu, na office dana zuciyarsa. Kalaman
abokin ɗan fir'auna yaketa harhaɗawa waje guda da nazarinsu.
Misalin biyar da wasu mintuna na yamma yaɗan fita wani waje, yanason zuwa
ainahin inda suka taɓa haɗuwa da ɗan-fir'auna a ranada Gimba ya kawo masa zancen
abinda ya gani. sai dai kuma hakan bata samuba saboda yana hanya kira ya shigo
wayarsa daga balarabe, a amsa kuwwa ya saka

wayar ya amsa masa sallama da gaisuwar da yake masa. “Ka isa garin nasu ne?” yay
tambayar wa balarabe. Daga can muryar balarabe cike da damuwa yace, “Ganima harna
dawo Alhaji, tun inacan naketa kiranka baka ɗagaba. sai dai baizo gidanba ma ashe,
kuma mamansa tace har waya sunyi lokacin dazai taso”. Babu shiri Jawaad ya taka
burki, yace, “Kana nufin canba gidaba tun ran juma'ar?”. “Eh wlhy Alhaji hakane”.
Mutuwar zaune Jawaad yay a cikin motar, gabansa sai wata irin mahaukacin faɗuwa
yake, cikin rawar jiki ya ɗauka wayar ya katse kiran balarabe ya fara laluben
Jabeer. Yana ɗagawa ko sallama bai masaba yace, “Jabeer maza dubamin daga ina Gimba
yake a halin yanzun?”. Daga can Jabeer yace, “Ƙila matarsa ta riƙesa bata gaji da
ganin kayantaba”. A tsawace Jawaad yace, “Jabeer kabar wasa mana!!, ka nemomin
yaron mutane Jabeer Please”. Ya ƙare maganar a hankali tamakar zai fashe da kuka.
Hankalin Jabeer ne yay matuƙar tashi, baƙaramin girgiza zuciyarsa tayiba da jin
yanda Jawaad yay magana da tsawa da sanyin murya kuma a ƙarshe. Jabeer yace “Yi
haƙuri, yanzu kana Office ne?”. “Gani nan zuwa” kawai ya iya cemasa ya yanke wayar.
Reverse yay tare ya figi motar da shegen gudu ya koma station.
A office ɗinsa ya iske Jabeer na jiransa, har wani jiri-jiri yakeji
saboda tashin hankali, sai da ya zauna sannan Jabeer yace, “Mike faruwa da
gimban?”.
“Jabeer nima ban saniba, ranar juma'a ya tafi weekend amma bai dawoba,
shinefa nasa a bisa aga ko yana lafiya, amma sai aka tararma baijeba”.
Cikin ɗaurewar kai Jabeer yace, “Ya salam to ina yaje shiko? Yanzu abinda
zamuyi bara mu bibiyi layin sa, ina fata kunyi waya dashi bayan tafiyar tasa?”. Kai
kawai Jawaad ya girgizama Jabeer, yana faɗin, “Na kirashi jiya amma bai ɗagaba”.
Jabeer yace, “Tunda dai kiran ya shiga zai taimaka mana”. Wayar kawai Jay ya miƙama
Jabeer baice komaiba. Gaba ɗaya Jay ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai faman zagaye
office ɗin yakeyi, Jabeer kuma nata ƙoƙarin ganin ya samo inda gimban yake, a haka
Aliyu da Hafiz suka shigo suka samesa harma da Rose da dawowarta kenan daga tafiya.
Haka suka duƙufa su huɗu suna taimakawa Jabeer. Inda alama ke nuna musu wayar gimba
na nan ɗinne ya tada musu hankali har suka kasa aminta suketa sake ninƙayar
bincike. Cikin girgiza kai Jabeer yace, “Kai abinnan akwai rikitarwa, mizai kaisa
wannan dajin mai haɗari? Inaga bara nai magana da kamfanin layinan dan muna buƙatar
bayanan da yafi haka”. Hafiz yace, “Hakan shine zai taimaka mana Jabeer, danni
kainama ya kulle gaba ɗaya”.
Jawaad dai yama kasa cewa komai, zaune yake kawai tamkar butunbutumi. Aliyu
ne yay kiran wanda yake musu aiki a kamfanin layin da gimba ke aiki dashi, bayan
sunyi magana ya ajiye wayar Jabeer ya tura musu Number gimba.
Ganin magriba tayi Aliyu yace, “;
Boss ka kwantar da hankalinka, ni ina ganin ko wasune suka Kidnapping ɗinsa bazasu
kaisa wannan jajejinba, kawai sunyi hakane domin rikita mana tunani, idan muka
kwantar da hankalinmu zamu fahimci komai cikin sauƙi, yanzu dai Ma'aruff ɗin yace
daganan zuwa safiya zai turo mana komai, inaga muje muyi salla da addu'ar ALLAH ya
kuɓutar dashi a duk inda yake, a kuma hannun duk wanda yake”.
A tare suka amsa da amin har Jawaad.
Koda suka fito daga salla Jawaad ya tafi gidane kawai cike da
matsananciyar damuwa, bai shiga gidaba sai da yay sallar isha'i.

A wannan dare idan har akace Jawaad yay barci to ɓarawone, kwana yay
miƙama UBANGIJI kukansa akan gimba da murɗaɗɗun al'amuran dake faruwa a tsakaninan,
roƙon ALLAH yake ya bashi ƙarfin zuciya dana jajircewa, ya kuma haskaka masa abinda
yake a duhu daya gaza fahimta. Mutuwar ɗan-fir'auna, ɓatan gimba, mafarkinsa,
dalilin aure da akaso yi tsakanin bilkisu da wanda ba mutumin kirkiba, damuwar da
yaga Alhaji babba jiya a ciki. Duk wanda ya roƙa UBANGIJI yana mai ƙasƙantar da kai
da fatan samu bai yanke ƙauna daga rahamarsaba ALLAH sai ya amince masa, ya kuma
dafama al'amarinsa ta inda bai zato ko tsammani ba.
Jawaad ya tashine da wata irin dakiyar zuciya, duk wani ɗigon tsoro da
fargaba daya haifarmasa da ruɗa

ni da kasala a daren jiya sai yaji sun gudu, ya tashi cike da yaƙinin son tunkarar
abinda ke tunkarosa. Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka
kashe ɗan fir'auna, miyasa suka kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-
fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda
ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba.
Ƙarfe bakwai na safe ya gama shirinsa yabar gidan, yau ko gadonsa bai
gyaraba, saƙo ya gani daga gimbiya Munaya akan zatasa akai Bilkisu wajen aiki
basaima ya wahal da kansaba, idan sun tashi sai ya dinga maidota da kansa.
Yaji daɗin hakan, dan dama yanata juya yanda zai dinga yawonan batare da
wataran yay lattiba shiɗinan gwani ayyuka da yawa. Station ya nufa cike da zumuɗin
son zuwa yaji ya ake ciki akan gimba.

________________________________

Tunda muka shiga cikin masarauta notin kaina ya nema kwancewa, karon
farko a tarihim rayuwata dana fara shigarta, ƴan uwa bansan yanda zan musalta muku
abinda na ganiba, abinda kawai zan iya ce muku masarautar gagara badau wani
katafaren garine kawai mai zaman kansa dake ɗauke da ɗumbin al'umma kala-kala masu
abubuwan kallo. Kaina bai sake kuncewa ba sai da muka shiga sashen da naji ance na
sarauniyane mahaifiyar su Amaturrahman, wato garin daɗi na nesa, angulu data leƙa
masai. Nidai bana cewa uffan, binsu kawai nake tamkar raƙumi da akala. Mun yada
zango a katafaren ɗakin Amaturrahman da Meenal sai Amatullah idan tazo daga Niger.
Amaturrahman ce ta tsaya kaina da hidima har saida nai wanka na canja kaya aka kawo
abinci ta takurani naci sannan ta barni na huta, muna zaune tana ɗan jana da hira
saƙon gimbiya ya iso garemu daga amintacciyar baiwarta akan tace na kwanta na huta,
kuma a bani dukkan kulawar data dace.
To lallai naga hidima mai ban mamaki da al'ajabi wadda har kuka sai da nayi,
ashe nima mutumce mai daraja irin haka? Ɗawainiyar da akeyi dani ta zabtare kaso
mafi yawa na damuwar da nake ciki akan abubuwa kashi-kashi da basu ƙirguwa, tunda
Safah kuma taji labarin nazo tadawo ɗakin su Amaturrahman ta tare tanata min hira.
Banga gimbiya ba har dare yay muka kwanta, da safe kuma na tashi da shirin fita
aiki kamar yanda boss ya tabbatarmin zasu zo ɗaukata, sunata barcinsu nai shirina
tsaf, na cika wayata da caji dan haka nai tunin tanan zai kirani, sai dai kusan 7:
00am saiga ɗaya daga cikin bayin gidan tazo isarmin saƙon kira, bin bayanta nai
muka fita, mun isa wajen Amintacciyar baiwar gambiya dake falon farko tana jiranmu,
na gaisheta da girmamawa saboda babbar mace ce, itama cike da fara'a ta amsa min
tana faɗin, “Sarauniyar gagara badau na gaisheki baƙuwar alkairi, baki samu ganinta
bane tunda kika iso saboda takawa yana mura, tana sashenshi tun jiya tana bashi
kulawa, akwai driver dake tsumayenki a waje ta bada umarnin a kaiki garesa”.
Fuskata ɗauke daɗan murmushi nace, “Nagode mama, ALLAH ya bama maimartaba lafiya
mai amfani da nisan kwana”. “Amin ya rabbi” ta amsamin damin nuni Abinci da aka
ɗora akan babban yire wai na breakfast ɗina, badan nasoba ta tsareni naci sannan
tayomin rakkiya waje.
Duk azatona gimba zan tarar, sai dai na iske saɓaninsa, da alama madai wannan
acikin masarautar yake shima, dalleliyar mota baƙa wulik yaymin nuni dana shiga
bayan mun gaisa, tamkar kazar da ƙwai ya fashema a ciki haka na shiga zuciyata
najin tarin ƙaunar waɗanan adalan mutane, ada nazata idan na rasa mafakar gidan Dad
bazan sake samun watantaba, sai gashi alkairai nata niye da rayuwata. Tafiya muke
ina tunani kala-kala a cikin raina ciki harda fargabar haɗuwata da mutum biyu, wato
Boss da Yah Qaseem, tayaya zanyi aiki cikin nutsuwa a tsakkiyar waɗanan zakunan?.

★★★★★

Jay da isowarsa kenan babu daɗewa yana zaune a kujerarsa ta office yana ɗan
taɓa aiki da tsumayen su Jabeer, baifi mintuna gomaba suka shigo a jere su huɗu har
Rose data dawo jiya, gaisuwa sukai cikin musabaha Rose kuma ta gaishesa kafin duk
su zauna, binsu kawai da kallo Jawaad yake. Jabeer ya nuna masa takardar dake
hanunsa yana faɗin, “Wannan sune bayanan da Ma'aruff ya kawo yanzun nan”. Jay

ya ɗago idonsa daga rubutun da yake yayma Jabeer kallo ɗaya ya ɗauke, “Ka buɗe
mugani” ya faɗa hankalinsa akan Computer ɗin gabansa, sai dai sam bama ya fahimtar
aikin da yakeyi ɗin.
Buɗe takardar Jabeer yayi, cikin nutsuwa yake bin komai da kallo daki-
daki, a firgice ya kalli Jay cikin rawar harshe yace, “Ka duba wayarka, alama ta
nuna kaine wanda ya turama saƙo na ƙarshe ta manhajar WhatsApp a ranar asabar da
ƙarfe shida da mintuna talatin da huɗu (6:34pm), sai kiran wayoyi barkatai da akai
masa amma babu wanda ya ɗaga a ciki, kuma wayardai tana a cikin jejin nan da muka
gani jiya, abin farin cikin kuma har yanzu layin yana kan waya yana aiki alamar
wayar tana a kunne”. Duk saurarensa suke, yayinda Jay keta ƙoƙarin duba saƙon
Gimba, tabbas kuwa ya tura masan, amma sam hankalinsa bai kaiba saboda hidimarsa
bata barima ya leƙa wata kafar yanar gizo ba a gaba ɗaya satinnan daya gabata. Babu
wanda hankalinsa bai tashiba a cikinsu da wannan voice note na gimba, tuni
jijiyoyin kan Jawaad duk sun miƙe ruɗu-ruɗu, muryarsa cike da damuwa yace, “Hafiz
kaima Sir Ahmad magana ina buƙatar helicopter”. Cikin matsanancin tsoro suke
kallonsa su duka, Aliyu yace, “Boss wannanfa dajine mai haɗarin gaske da ko soji
suna masa shiri na musamman kafin su shigesa, idanma sun shigan ƙalilanne a cikinsu
ke dawowa da ransu, baka tunanin ma wayar aka kai can dan a kauda mana hankali”.
Cikin rufewar ido Jawaad ya bugi tebir ɗin gabansa, “Aliy!! ya kakeso nayi ne shin?
Nabar yaron mutane mai mata da ƴaƴa har uku da uwa da ƙannen da suka dogara dashi a
hannun waɗanda suke azzalumai?. Aliy ta dalilinafa suka kamashi, wlhy kaji na
rantse maka sai ƙafata ta taka wannan jejin koda kuwa Gimba bayacan kokuwa nima
ajalina nacan!”.
Babu wanda bai firgita da alwashinsaba a cikinsu, sunaji suna gani ya fice
daga office ɗin, basu da zaɓin daya wuce goya masa baya dan wannan shine alƙawarin
da suka ɗaukama kawunansu duk rintsin da ɗayansu zai shiga suna tare dashi ɗari
bisa ɗari. Cikin mintuna ashirin suka samu amsar helicopter daga hukumar sojoji
tare da soji biyu da zasuyi musu rakkiya bisa tsayawar Sir Ahmad.
Office ɗin Jay ɗin dai suka koma suna tsare-tsaren yanda zasu tunkari Jejin.

A dai-dai wannan lokacin motar masarauta ta kawo bilkisu, godiya naima


drivern da ko sunansa ban saniba na fice, shi kuma ya juya inda ya fito.
Kaina tsaye office ɗinmu na nufa, a raina sai jina nake wani iri idan na
tuna waifa akwai aure a kaina yanzun, aurenma na Boss. kowa yazo sunata aiki,
shigowata yasa sukaimin caa da ido har gabana na faɗuwa da tunanin shikenan na mutu
kowa yasan komai. Ummie ta taso da gudu ta ɗaleni tana murna, “Babie ALLAH banyi
zaton ganinki ba yau a office”. Murmushi nai mata ina amsa gaisuwar sauran daketa
min yaya jiki, sai naji daɗi da Ummie bata sanar dasu komaiba sai rashin lafiya.
Na zauna a mazaunina idona akan Ummie da itama ta jawo kujerarta jikin
table ɗina ta zauna. “Yanzu angonki yazo ya gama haukatamu da masifa anan”. Ta ƙare
maganar da dariya. ɗan hararta nai na ɗauke kai bance komaiba, danni kam dama ta
ambatosa jinai gabana ya faɗi. na shiga duba aikin dana bari, Ummie kuwa na cigaba
da tsokanata dan na tanka amma na shareta kamar banajinta.
Dawood daya shigo yanzun ya ƙaraso gabana yana faɗin, “Bily Boss na kira”.
Babu shiri na ɗago ina kallonsa, shiko yay ƴar dariya yana zama a kujerarsa dake
kusa da tawa, “Kitafi da addu'a a baki dan wlhy yau a sama yake, yanzu naje office
ɗinsa jinai kamar nai fitsari a tsaye da yanda yaketa masifa”. Ban iya cewa
komaiba, Banida ikon kuma cewa bazanjeba, dan haka na miƙe cike da haushi na fita
har Ummie namin dariyar ALLAH yasa aiki za'a bani dan taga kwana biyunnan hutawa
kawai nake tunda bana zuwa office, ban kulataba na fice abina.
Ina fitowa na hangesu sun fito tamkar zakuna, kowa fuskarsa a ɗaure
musamman ma boss, gabana ya faɗi, a fili nace, ‘Ni balki ina kuma zamuje haka?’
bani da mai bani amsa na isa inda suke, babu wanda ya saurari gaisuwata ma a
cikinsu, Jabeer ya nunamin na shiga mota da boss yake, gaba na buɗe na shiga

, dai-dai da isowar Rose wajen, hararata tayi tana jan tsaki, ta buɗe indasu Aliyu
suke ta shiga, Hafiz kuma ya shiga kusa da Boss.
Mun fara tafiya Hafiz ya miƙomin bindiga, juyowa nayi zan amsa na samu damar
satar kallon boss, kansa a duƙe yake yana sakama bindiga alburusai, amsa nayi na
juya zamana nidai a raina ina addu'ar ALLAH ya maidomu lafiya...............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

[12/17/2020, 3:19 PM] HASNA ✍🏻


: Bilyn Abdull :
Page 30

................Daga station Barrack muka nufa, acan muka iske jirgi mai saukar
ungulu dake jiranmu.
Motar na tsayawa Jawaad da Hafiz suka fita, kafin bily tai yunƙurin fitowa
Hafiz dake kallon Jay yace, “Boss amma Mami jiya ta fito asibiti miyasa baza ai
mata afuwa da tafiyarnan ba?” Jay dake daƙilar waya ya ɗago yana kallon Hafiz, sai
kuma ya dafa kafaɗarsa da hannunsa da ya ciro aljihu, “Nasan tana buƙatar hutu
Hafiz, sai dai nima bansan miyasa nakejin kamar tafiya tare da ita yanada nasaba da
nasararmuba”. Hafiz ya jinjina kansa yana murmushi, shima Jay ɗin murmushi yayi ya
ɗauke kansa.
Ganin sun fita nima na fito, ido muka haɗa da boss dake ƙoƙarin saka waya a
kunne da alama kira yayi, duk yanda naso janye nawa na gaza, dan tamkar ya ƙulleni
ne da idanun nasa yayi. Murya ƙasa-ƙasa tamkar mai gudin wani ya jisa yace, “Koma
ciki ki jira”. Ƙasa nai da idona ina sauke ajiyar zuciya, na buɗe motar na koma
ciki ina kallonsu. Sojoji uku ne suka ƙaraso wajen, daga inda nake banajin mi suke
faɗa su da su Oga Jabeer, boss dai na gefe yana waya har yanzun.

Bayan Jawaad ya kammala waya da Alhaji babba akan a tayasu da addu'a shima
nufar inda su Aliyu suke tsaye tare da sojoji ukun nan yayi, cikin mutunta juna
suka gaisa, wanda ya kasance babba a cikinsu mai yawan shekaru kuma ya kalli Jay
yana faɗin, “Jejin nan jejine mai haɗari, Sojinmu sunsha wahala sosai a cikinsa
kafin ALLAH ya kawo mana ɗauki ya haɗamu da Ƙaura na bakin kadarko, a bakin jajenin
yake rayuwa shida iyalansa, sannan a cikin jajen yake farauta, sai dai wani babban
al'amari ya faru a shekaru biyu da suka wuce wasu azzalumai suka tashi gidansa
dukkan iyalansa babu wanda ya tsira sai shi, shima dai ya rasa hannunsa guda, daga
nan ne muka ɗakkosa mukazo dashi nan yay jiyya har ALLAH yasa ya warke, yaso komawa
jajenin saboda ya saba sosai dacan, yakan faɗa mana zama a cikin gari shi baya masa
daɗi, to adai taƙaice har zuwa yanzu da nake muku magana bamu barsa ya komaba, dan
yama tsufa kawai jarumtace irin ta mutan da da ALLAH ya azurta da sani.........”
isowar ƙaura da wani soji wajen ya saka Lieutenant General Mubarak Kambawa yin
shiru, ya zubama waje ɗaya ido. Duk juyawa su Jay sukai suma suna kallon inda yake
kallo, tsohone mai shekaru da yawa wanda basusan adadiba, babu wani gashi a jikinsa
da zaka iya gani baƙi sai wanda UBANGIJI ya ɓoye. Yana sanye cikin kayan fatu, ya
ɗaura fatar zaki a ƙasa yay riga data damisa wadda take tamkar ƴar shara, dan kai
kawai aka fitar sai gefe da gefe akai mata maɗauri, yana rataye da jikkar fatar
kura a wuyansa, sai dai bashi da hannu guda. Daka gansa kaga ƙauran kuwa. Yanda
sukaga lieut.. General na gaidashi cikin girmamawa yasa suma suka gaidashi da
girmamawa, dan koba komai ya wuce uba sai dai kaka. Dattijo ƙaura dake amsa musu
idanunsa kafe akan Jawaad ko ƙyaftawa bayayi, ya saki murmushi yana kauda idonsa
daga kallon Jay ɗin. babu wanda kallon bai bama mamakiba hatta lieut.. General, dan
haka yaja Ƙaura gefe guda.
“Baba nasan baƙwa kallon banza, akwai matsalane? Dan na lura ka kafe yaron
can da kallo har murmushin ka ya kasa ɓoyuwa” murmushin yanzuma Ƙaura ya sakeyi
tare da juyawa ya kalli Jay da Jabeer ke taimakawa yana saka bullet proof jacket a
jikinsa kafin ya sake maidowa ga lieut.. General yace, “Shima sojan kune
yallaɓai?”. Lieut... General yace, “A'a baba, sune nai maka bayani ai zakuyi
tafiyar”. “Oh na shafa'ane wlhy, kasan ƙwaƙwalwar yanzu sai a hankali takan manta
wasu abubuwan”. L. General dai murmushi yayi kawai, dan yasan wanene baba ƙaura,
yakuma tabbata akwai abinda ya gani tattare da Jawaad, amma tunda yake wani
kakkaucewa bayason ya sanine, dan haka ya ture maganar Jawaad gefe ya shiga masa
bayani akan taimakon da sukeso yayma su Jay saboda sanin sirrin jajen da yayi.
Sunɗan tattauna sannan suka dawo inda su Jay da suka gama shiryawa tsaf suke harda
Bilkisu data fito bisa umarnin Jawaad bayan yaje da kansa har cikin mota ya taimaka
mata ta saka bullet proof jacket ɗin itama suka dawo wajen tanata sinne kai saboda
kunya, yayinda Rose ta shaƙa tai fam da haushi tamkar zata f

ashe.
A bazata sukaji Ƙaura yace, “Yarinya yaya sunanki?”. Duk juyowa sukai su
duka suna kallonsa dason ganin dawa yake tsakanin bily da Rose?. Sai sukaga da
Bilkisu yake dan itace gab dashi kuma itace ta gaidashi tunda sai yanzu ta ganshi,
gashi ta kafeshi da idanu tamkar maison tuna inda ta sanshi. Tambayar da yaymatane
yasata dawowa hayyacinta, tace, “Bilkisu”. “Balqeesa! mai gadon zinari kenan” baba
ƙaura ya faɗa yana wani murmushi tamkar yanda yay ɗazun akan Jay. Jawaad zaiyi
magana L. General ya riƙe masa hannu yana girgiza kai alamar kar yace komai. Komawa
yay ya tsaya badan yasoba danshi al'amarin tsohon ya fara bashi haushi. Sarai ƙaura
yaga abinda Jawaad yayi, danta wutsiyar ido yake kallon duk miotsinsa, amma sai yay
kamar hankalinsa akan Bilkisun kawai yake. Har Lieut.. General ya basu Umarnin
shiga Jirgin Ƙaura ya sake jefama Bily tambaya. “Balqeesa! yaya sunan
mahaifinki?”. Yanzunkam ba Jawaad kaɗaiba kowama abin yazo masa wuya banda Rose,
ahaka zasuyi tafiyar da wannan mutumin mai shegen tambaya da bin ƙwaƙwƙwafin
mutum?. A miskile Bilkisu ta amsa masa da “Adam makaho”. Duk ido suka zubama Ƙaura
suji mizaice, amma sai ya ɗauke kansama gaba ɗaya kamar bashi yay tambayar aka bama
amsa ba.
Ganin yanda yay ɗin yasa L.. General cemusu su shiga. Haka duk suka fara shiga
suna ƙunƙuni da hararar baba ƙaura daketa murmushin da basusan inda ya dosaba. Jay
ya matsa ya kama hannun Bily dake tsaye tamkar wadda aka tsayar, ajiyar zuciya ta
sauke dan tayi nisane a tuno mafarkinta na daren jiya wanda ayanzu ta tuna acan
taga fuska wannan tsohon. Baba Ƙaura dake biye da bayansu ya ƙure hanunsu dake
cikin na juna da ido yana murmushinsa har yanzu, sai da suka taka ƙafarsu zasu hau
jirgin yace, “Sara da sassaƙa baya hana gamji tohowa”. Daga Jawaad har Bilkisu
sunji furucin baba ƙaura sarai, harma Jay ya juyo zaiyi magana sai kuma ya fasa.
“Karka damu yaro faɗi duk abinda ke ranka, nima nawa nake faɗa dan bana bari
a ciki ta kasheni. Ƙwai cikin ƙaya na gani ajiyar ALLAH”. Karan farko da kalaman
tsohon suka saka gaban Jawaad faɗuwa, kalmar Ƙwai cikin ƙaya idan bai mantaba ya
taɓa jinta a cikin mafarkinsa mai Sarauniyar da har yau basan inda ya dosaba. Har
suka zauna idonsa bai daina kallon baba ƙaura ba da yay biris da kowa tamkar bashi
ya gama takale-takalen maganaba yanzun.
Gaba ɗayansu duk da addu'a a bakinsu har jirgin ya ɗaga sararin subahana.

Duk da wannan shine karona na farko a hawa jirgi abin mamaki babu wani tsoro
ko ƙauyanci tattare dani, kodan helicopter ne oho, nasan dai lokacin da zamuyi sama
na riƙo hanun wanda bansan wanene ba sai da muka dai-daita na fahimci Rose ce, aiko
tacika tayi fam da haushi, har nai mamaki da bata turo hannunaba, sai daga baya na
fahimci Boss dake facing ɗinmu ne yaymata shamaki da hakan dan duk abinda zamuyi
zai iya gani.
Haka mukai ninƙaya a tafiya idanuna sun gaza daina kallon tsoho mai kayan
fatu, har jirginmu ya samu sauka. Jejine maiban mamaki da al'ajabi, bakajin komai
sai kukan tsuntsaye da mabanbanta sauti da zuciya bazata iya hasaso minene ba. Kowa
kagani hankalinsa a tashe yake da wannan jeji amma banda tsohon nan. Haka muka
firfito kowa na karanta addu'ar da tazo masa a baki, wani irin makeken ruwane
kwance ƙar-ƙar har haskensa na ɗaukar idanu a gabanmu, Oga Aliyu yace, “Ikon ALLAH,
amma a taswurar jejin nan bamuga wannan ruwanba sam, ko masu zanen taswirar basu
san da shi bane?”. “Wlhy Aliyu wannan shine abinda nake ayyanawa a raina yanzun”
Jabeer ya faɗa murya a harɗe.
Tsohon nan ya bimu da kallo ɗaya bayan ɗaya sai kuma ya girgiza kansa da
faɗin, “Wannan ruwa zuwayyene ba zaunanne ba”. “Kamar ya?”. Suka kusan haɗa baki
wajen tambaya.
Ƙin basu amsa yay, saima kallonsa daya maido gareni, “Ɗiyata Balqeesa
bismillah saka ƙafarki a ruwannan” sosai naji gabana ya faɗi, idanuna suka cika da
ƙwalla, ganin babu wanda yay magana a cikinsu yasa na ɗaga ƙafa zan nufi ruwan.
Caraf aka riƙomin hannu, basai na juyaba ƙamshinsa kawai ya bani amsar shine, murya
a kausashe yace, “Baba ya zaka turata shiga wannan ruwan maikama

da ruwan tsafi?”. Mu duka kallonsa mukai, Jawaad da shima maganar ta suɓuce masane
kawai babu shiri yay saurin dafe kai da faɗin, “Sorry, ina nufin ruwan daga gani
yanada ban al'ajab, tunda nake ban taɓa ganin ruwa mai ƙyawunsa ba da ɗaukar ido
irin haka”. Murmushi mai sauti mukaga Baba ƙaura yayi, cikin ɗauke kai daga garemu
yace, “Dole saimun ƙetarashi zamu kai inda muke hari, anmana katanga da shine domin
mu juya, kuma wlhy kunji na rantse wannan yarinyar kaɗaice zata ƙetarashi kafin mu
sami hanya, dan tanada taurari masu ƙarfin gaske”. A take duk suka zubamin ido, ni
kaina wata irin jarumta nakeji da dakiyar zuciya da bansan yaushe na sameta ba.
Hafiz yace, “Kana nufin har kai da akai iƙirarin kasan ciki da bai ɗin jejin?”.
“Yaro, baiwa kowa da irin tasa, wani har yabar duniya babu mai fahimtar tasa, wani
ko harmutsin duniya ke bayyana tasa, waniko nasarorinsane, wani ko hatsabibancinsa
ne, wannan idanun da kake gani ALLAH kaɗai yasan ajiyar da yay a cikinsu”.
Kai kawai duk muka shiga jinjina masa, boss yace, “Inhar zata ƙetara
ruwannan sai dai tare dani”. Murmushi baba ƙaura yay kawai ya nuna mana hanya.
Sai da mukaje gab da ruwan yace, “ku tabbatar a tare ƙafafunku suka sauka, kuma
da bismillah”. Umarninsa mukabi mukai yanda yace, ni dai harda ƙarama wata addu'ar
nayi, wani irin azabar sanyi ne mai keta fata da tsoka ya shiga cikin jijiyoyi ya
gauraye da jini ne ya riskemu lokacin da ƙafafunmu dake cikin takalma suka sauka
cikin ruwan, atake muka fara rawar ɗari dagani har boss, maimakon muyi ƙoƙarin
komawa baya sai naji ya fisgi hannuna mun sake saka ƙafafunmu na haggu suma, abin
mamaki sai gamu mun jiƙe da zufa sharkaf dalilin zafin daya riskemu kuma a yanzu
tamkar ana tafasamu a garwashi, zafin bashida maraba da wani zafi dana taɓaji
kwanakin baya da bazan tuna dalilin jinsa ba. Sake fusgata Boss yay muka cigaba da
tafiya dukda azabar dake ratsa jikkunanmu. Wani irin mahaukacin ihu ne mai ƙarfin
gaske ta karaɗe jejin, gaba ɗaya ruwan da muke tsakkiya ya koma jini, da farko na
tsorata, amma addu'ar da naji Boss ya kamo yanayi tuni nima na karɓa masa ina
mamuƙeshi. Ɗaf ruwan ya ɗauke lokaci ɗaya tare da kukan, sai ƙarar iskar guguwa mai
ƙarfin gaske da mukeji tana tinkaromu, a take muka daina ganin komai saboda guguwar
tai mana ruf. Wata muguwar shaƙa naji anmin a wuya, nai ƙoƙarin fincike hannuna
cikin na boss danna ƙwaci kaina amma hakan ya gagara, ashe shima shaƙesan akai, da
hannuna na haggu na shiga laluben abinda ya shaƙenin, dan idona a rufe yake saboda
guguwar data lulluɓemu. Ɗumbin mamaki ya kamani jin jikin mutumne da gaske, jikin
da ya taɓa riskata a cikin wasu darare da sam na mantasu a cikin ƙwaƙwalwata, cikin
amincin UBANGIJI Hannuna ya sauka a nasa wuyan shima, na damƙi sarƙar dake wuyan na
fincika da masifar ƙarfin dana san daga UBANGIJINA ne kawai. A take jejin yay wata
irin girgiza tare da wasu irin gigitattun ƙararraki ta mabanbanta muryoyi. Daga
haka ban sake sanin mike faruwa ba.

Yanda aka shaƙe bilkisu haka shima Jawaad aka shaƙesa, sai dai shi
saɓanin itane, maimakon ya samu nasarar fisgar sarƙar wuya sai yasamu nasarar ciran
wani abu dake hanun wanda ya shaƙesan, danshi hanunsa yay ƙoƙarin cirewa daga
wuyansa da aka shaƙe.
Da sauri yay azamar taro Bilkisu jikinsa ya rungumeta da ƙyau yana cigaba da
karanto addu'a, isakar data lulluɓesu ta fara washewa a hankali har suka bayyana
filin subahana, babu wancan ruwan da suka riska a farko, hasalima wajen tsaunine.
Su Hafiz da suka samu kariyar UBANGIJI daga wannan guguwa da basusan daga
ina ta ɓulloba duk suka miƙe daga rumfar da Baba ƙaura yay musu da jikinsa. Dan
ranƙwafe yake kansu ya baza hannayensa tamkar maison tattaro wani abu.
Gaba ɗayansu kansu Jay dake durƙushe a ƙasa kan Bily bisa cinyarsa yana
girgizata sukai, baba ƙaura yay murmushi yana mai ɗaga hannayensa sama da zuba
kirari wa UBANGIJIN AL'ARSHI, idanunsa na zubda hawaye, sai yanzune ya fahimci
ƙaddarar zamansa cikin gari na tsahon shekara biyu bayan halaka masa iyalinsa da
akai, UBANGIJI mai hikima, UBANGIJI mai rahama, sarkin da baya

zalinci ya kuma haramtashi a tsakaninmu, sai da ya kammala miƙa godiyarsa ga ALLAH


kafin ya nufi su Jay da duk suke kan Bilkisu kowa na ƙoƙarin faɗama Jawaad taimakon
da zai bata kozata farfaɗo, masu cewa ya murza hannu nayi, masu cewa ya murza ƙafa
nayi, masu jajen ina za'a samu ruwa a zuba mata nayi. Shikuma sai faman girgizata
yake yana faɗin ainahin sunanta na yanka wato BILKEESU!!.
Murmushi baba ƙaura yayi tare da katsesu baki ɗaya, “Bazata taɓa farfaɗowa a
hakaba ko zaku kwana kanta”. Gaba ɗayansu shi suka juyo suna kallo, sai dai babu
wanda ya iya cewa wani abu a cikinsu. Shima bai sake faɗar komanba, sai nuna musu
su koma gefe da yay da hannunsa, babu musu sukabi umarninsa aka barshi daga shi sai
su Jawaad ɗin. durƙusawa yay kusa da Jawaad murya ƙasa-ƙasa yace, “Iskar
numfashinka ce kawai zai taimaki nata dawowa gangar jikinta ɗan saurayi, ka ɗaura
bakinka kan nata ka zuƙo insha ALLAHU zata farfaɗo”.
A hankali Jawaad ya lumshe idanunsa tare da ranƙwafawa bisa fiskar Bilkisu
ya aza bakinsa saman tattausan lips ɗinta, numfashin dake fita ta hancinsa yana
sauka akan fuskarta, ya tura harshensa cikin bakinta dake ɗan buɗe kaɗan ya shiga
hura mata iska tare da shanye yawun bakinta babu ko ƙyankyami, wani irin numfashi
mai ƙarfi ta kawo tare da ƙanƙame hanunsa dake cikin nata ta damƙe laɓɓansa itama.
Da sauri Baba Ƙaura yace ta farfaɗo?”. Yay maganar da bubbuga bayan Jawaad ƙaɗan.
Jay ya janye bakinsa dake cikin na Bilkisu da ƙyar yana sauke numfargashi
da sauri-sauri, wani irin tsitstsinkewa jinin jikinsa keyi, baba ƙaura yay murmushi
tare da ɗora hanunsa akan na Jawaad da ƙofofin gashi duk suka buɗe. A hankali Jay
ya buɗe lumsassun idanunsa yana kallon Baba ƙaura kamar yanda itama Bilkisu ta buɗe
nata a hankali akan fuskar Jawaad. “Da bakajin sha'awarta a matsayin mata ko?”.
Gaban Jawaad ya faɗi yana mai al'ajabin ya akai tsohon ya sani?. Murmushi baba
ƙaura yay yana ɗauke kansa ya maida ga bilkisu, “Yanda bakajin sha'awarta itama
haka batajin komai game dakai dama kowane namiji a duniya, sai wanda sukaso yimata
wasa da hankali a kansa, ada ita kaɗaice da wannan matsalar, amma dalilin aurenku
kaima hakan ta shafeka, sun riga sinci buri mai tsanani a kanta, wanda hakan bamai
yuwuwa bane a garesu cikin sauki sai idan ALLAH ya ƙaddara hakan, akwai al'amari
mai sarƙaƙiyar gaske tsakaninku, sai dai inaji a jikina komai yana gab da warwarewa
dalilin abu uku wanda nima ALLAH bai bani ikon saniba, ka jajurce wajen tsananta
bincike zaka fahimci komai da yake komai dangane daku. Bazan ɓoye makaba, wanda
kukazo nema a wannan Jejin baya raye, sai dai jininsa shine jini mafi haɗari dazai
zamarma duk wanda tsiyayar dashi tauraruwa mai wutsiya, ki adana wannan tsintuwar
ta hannunki tamkar yanda kika adana ta farko, sai dai zasu cigaba da tsorataki
domin bibiyar kayansu dan kin raunanasu sosai, duk randa ta uku tazo gareki suka
zama huɗu dana hannun mijinki komai zai buɗe”. Baba ƙaura ya miƙe yana ɗan murmushi
da binsu da kallo tamkar yanda suma suke kallonsa har Bilkisu, ya sake cewa “ƘWI
CIKIN ƘAYA AJIYAR ALLAH”. ya juya ya barsu.
Da ƙyar Jawaad ya iya maida kallonsa ga Bilkisu, ya kamo hannunta dake
rumtse ya buɗe a cikin nashi, Wurine baƙi mai girma tamkar wanda ta taɓa tsinta a
ɗakinta. Zumbur ta tashi zaune jikinta har yana rawa, dan sai yanzu ta fargafa a
jikin boss take kwance. Wasu hawaye masu zafi suka fara zirara a kumatunta suna
sauka bisa fuskarta.
Shidai Jay kallonta kawai yakeyi, ɓullowar su baba ƙaura ya sashi faɗin.
“Shiii!!!” yana mai ɗora yatsansa akan bakinsa. Saurin kallon inda yake kallo tayi
itama, su Jabeer ne ɗau da mutum bisa buzu. Atare suka miƙe ita da Jay harsu Hafiz
suka iso inda suke suka ajiye gawar Gimba da duk fuskarsa tai kaca-kaca da raunuka
tamkar yakushi. Durƙushewa Jawaad ya koma yayi gaban gawar, hanunsa na rawa yakai
kan fuskar Gimba ya shafa, idanunsa sun sake kaɗawa sunyi masifar yin jazurr,
jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Su Hafiz sai sharar ƙwalla sukeyi suma.
Ɗagowa Jay yay yana kallonsu, dagani kasan shima kukan zuci yakeyi, ya maida
duba

nsa ga Baba ƙaura dake riƙe da farin ƙyalle a hannu. Baba ƙaura ya girgiza masa kai
da lumshe ido alamar ban haƙuri. Juyawa yay yana kallon Bilkisu dake kusa dashi
tsaye tana kuka iya ƙarfinta. Ya dafe goshinsa yana murzashi da ƙarfin gaske,
soyake yayi hawaye tamkar yanda suma sukeyi kozaiji daɗi, sai dai sunƙi fitowa, sai
zuciyarsa dake wani irin zafi mai azabartar da gangar jiki da ƙwaƙwalwa. Miƙewa yay
daga gaban gawar ya kamo Bilkisu dake tsaye. Jikinsa ta faɗa tare da sake fashewa
da kuka mai huda zuciyar mai sauraro.
Baba ƙaura sai basu baki yake da nuna musu muhimmancin ƙaddara da karɓarta
a duk yanda tazoma bawa, sannan mutuwa alƙawarin ALLAH ce ga kowane mai rai dake
doron ƙasa, shi da ya tafi ba gaggawa yayba, mu da muke raye bamuyi jinkiriba,
ALLAH yay alƙawarin kwanansa ya ƙare, waɗanda suka kashesha sanadi suka zama, da
sunyi haƙuri ma aranar zai bar musu duniyar dama. Da waɗan nan kalaman hikima Baba
ƙaura ya shawo kansu har suka ɗakko ledan da sojoji kan saka gawa kafin a kaita
inda ya dace idan har basu da damar binneta a wajen yaƙi. Haka aka saka gawar Gimba
da cikin hikimar UBANGIJI babu abinda tayi tamkar yanzune ya rasu.
Bily bata iya shiga cikin jirginba saida taimakon Jawaad, yanzunkam kusa
dashi ya zaunar da ita, dan shima yana buƙatar jin ɗuminta.
Dukda halin da ake ciki hakan ba ƙaramin zafi yayma Rose ba, har cewa Jay
take munafuki a cikin zuciya, a ganinta shida yake gudun taɓa macen daba matarsa ba
yau wane gulma ta kaisa mamuƙar wannan yarinyar kuma? Taja tsaki a cikin ranta tana
ɗauke kai, ta tsani yarinyarnan wlhy, kuma itama tana gab da salwantar mata da
rayuwa inhar bata fita rayuwar boss na, yarinya ƙarama sai baƙin karuwanci?.
Wannan zantuntuka sune Rose taita tattaunawa da zuciyarta har jirginsu mai
saukar angulu ya sauka a garin su gimba tamjar yanda Jawaad ya yanke shawarar suyi
kawai. Ya kuma kira Sir Ahmad ya sanar masa halin da ake ciki, hakama Alhaji Babba.

______________________

Tunda Jawaad ya kira Alhaji babba ya sanar masa inda zasuje da rokon a tayasu
addu'a sai ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka ya tara tsoffin anguwarsu sukai
shawara akan subi makarantu yanzunan a dasa saukar Alkur'ani mai girma, tare da
masallatai idan lokacin sallar zuhur yayi, ya kira Ummah babba da ƙarama ya
umarcesu da yin abincin sadaka su bada a fitar a rabama mabuƙata.
lokacin dasu Jawaad ke cikin wancan mawuyacin halin addu'oin bayin ALLAH ne
dana ƙananun yara keta riskarsu, tareda farin cikin mabuƙata da aketa rabama
lafiyayyen abinci harda abin sha.
(Duk wanda yace ALLAH ya tsira wlhy, bawa saki kowa ka kama ALLAH shine
shugaba mai kallon motsin kowa hatta da ƙwaron da idanu basa gani, mai bada kariya
ga kowa ta inda bakai zatoba, mubar zagin shugabanni na duniya da suka zama
wakilanmu akan san zuciyarmu, mubar ɗaukarsu matsayin waɗanda zasu bamu kariya ko
farin cikin duniya domin suma mutanene tamjarmu, basu isa sanin abinda yake ɓoyeba
sai wanda ALLAH yaso su sani, mu aje shirmen siyasa gefe muyima ƙasashenmu addu'a
da shuwagabanninmu wannan shine nasararmu).

________________________

Su Jawaad sun isa da gawar Gimba ƙauyensu, inda helicopter ɗin da suke
ciki ya sauka a filin makarantar primary ɗin dake gab da gidansu gimban, daga nanne
aka ƙarasa da gawar bayan su Baba ƙaura sun fara isa gidansu Gimba sun isar da saƙo
maiban tashin hankali.
Faɗa muku yanda abubuwa suka cabe a wannan lokaci abune mai wahala, dan
matarsama suma tayi saida aka zuba mata ruwa, haka ƴan anguwa da danginsa sunata
kuka dan gimba mutumne na mutane, sannan yanada son zuminci, duk alkairin da yake
samu ga Jawaad bai yarda yaci shi kaɗaiba hatta da wanda ba nasabama ci suke shima.

Gimba shi kaɗaine ɗa namiji wajen iyayensa, babansa ya rasu tun suna
yara, mahaifiyarsu itace taita ɗawainiya dasu har girma, sai ƙanwarta dake aure
birni da bata gajiyawa da taimakonta da marayun ƴaƴanta har suka girma, yayi
karatunsa har zuwa diploma saɓanin ƴan uwansa mata da ke tsayawa iyakar secondary
ake musu aure, shine ɗa na farko, sa

i ƙannensa shida duk mata, huɗu sunyi aure harda zuri'a sai biyu na nan suna
karatu, harma Jawaad ya ɗauka alƙawarin zuwa ya roƙa mahaifiyar su gimban dan suci
gaba da jami'a idan sun kammala sakandiri ɗin da suke aji shida yanzu, a lokacin
gimba yata murna dan dama burinsa kenan. Matar gimba ɗaya da yara uku duk maza,
yaronsa na ƙarshe sunan Jawaad ya saka masa yana kiransa da suna yayana. Adalilin
Hajiya Safara'u ƙanwar mahaifiyarsu dake zaune birni ya samu aiki a ƙarƙashin
Jawaad, (zuwa gaba lokaci zai fiddo mana wacece Hajiya Safara'u).

Mahaifiyar Gimba mace mai haƙuri da sam batai kukaba saina zuci itace tace
Jawaad ne zaima gimba wanka tare da ƙaninta mai suna Ibrahim wanda ya kasance
dattijo ne sosai.
Su Jawaad suna can suna ƙimtsa gawar Gimba su Alhaji Babba suka iso kusan
mota huɗu, harda jama'ar gidansu Jawaad wato kawunnansa.
Jawaad da kawu Ibrahim sun suturta gawar gimba tamkar yanda shari'a ta koyar,
kafin mahaifiyarsa da ƴaƴansa harma da ƙannensa su shiga suyi sallama da gawar,
daganan aka fito dashi domin miƙasa maƙwancinsa na gaskiya. Kuka sosai ya tashi a
gidan maiban tashin hankali har aka fice da gawar daga gidan zuwa ƙofar gida inda
su Alhaji babba da mutanen gari suka haɗu wajen sallatarta.
Masha ALLAH yayi jama'a kam har abin ya bama mutane mamaki, sai dai UBANGIJI
shiyasan ajiyar da yay a wannan waje. (ALLAH ya gafartama gimba da iyayenmu da
dukkan musulmai da suka rugamu tafiya😭🙏🏻).

Bayan an dawo daga kaisa su Jawaad basu tafiba, suna a cikin garin har
gabanin magriba ana amsar gaisuwa dasu shi dasu Hafiz, Jabeer, Aliyu, sai Bilkisu.
Sojojin da sukai musu rakkiya da Baba ƙaura sun wuce tun bayan da aka dawo daga
binnesa. Rose ma lokacin da su Sir Ahmad zasu tafi dasu Alhaji babba bayan sallar
la'asar Jay yace ta bisu. Bilkisu kuwa tana ciki tare da matar Gimba, batasan yaya
akai sukasan ita matar Jawaad baceba, sai kawai ganitai anata nunata da faɗin itace
matar ogan marigayi Gimba. Haka zasuyita jera mata addu'a da yabon halin Jawaad
bisa ɗawainiya da taimakon da ƙauyen yake samu daga Jawaad ɗin ta dalilin gimba.
Haka sukaita mata komai a girmame tamkar tafi kowa. Ita harma kunya ta komaji akan
yanda suke matan.
Wajen ƙarfe shida saƙo ya iso mata akan ta fito inji boss zasu wuce. Haka
ta tashi ta kimtsa jiki a saɓule dan ta amshi hijjab ɗin matar gimba ta saka tun
ɗazun saɓanin da da take da baby hijjab kawai. Sunata mata godiya da addu'a,
ƙannensa suka rakota har waje inda motar da zasu tafi take.
Sau ɗaya na kalli Boss na ɗauke idanuna saboda wani irin tausayi yake bani,
na ƙaraso inda yake tsaye na gaishesu tare da sake musu gaisuwa, murya cike da
damuwa ya amsa mani yana min nuni dana shiga motar daya buɗemin. Ni da shi da
Jabeer ne a baya, ina jikin ƙofa yana tsakkiya Jabeer kuma a ƙarshe, sai Aliyu da
zai ja motar Hafiz na gefensa. Haka muka wuce sunata mana addu'oin sauka gida
lafiya.
Sosai Aliyu ke sharara gudu kasancewar garin yay wani irin ɗaurewar
hadarin farkon damina mai cike da iska a ciki, babu mai magana a motar sai zancen
zuci, cikin awa ɗaya da mintunan da bazasu gaza ashirin da bakwaiba muka iso cikin
gari, zuwa lokacin garin ya sake yin duhu, gana hadari gana magriba, anata salloli
a masallatai. Nayi zaton masarauta zasu kaini, sai naga an nufi gidansu Boss, koda
mukazo gate sai yace basai Aliyu ya shiga da motarba bara mu sauka anan su wuce kar
hadarinan ya riskesu..................✍

(Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka kashe ɗan fir'auna,
miyasa suka kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa,
yanaji a jikinsa kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi?
Wannan ne bai saniba.)
dolene jiya kushiga ruɗani akan mutuwar ɗan fir'auna bayan farkon page na
nuna bai mutuba, nima sai a Comments ɗinku na fahimci kuskuren danayi na koma na
duba page ɗin, wlhy hankalina sam bai kaiba ko'a wajen editing, rayuwace abubuwa
sunma ƙwaƙwale yawa, kana gabas tunaninka na yamma, amin afuwa ɗan fir'auna bai
mutuba🤦🏻. anahin abinda naso sakawa a

wajen shine (Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka so
kashe ɗan fir'auna, miyasa sukaso kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-
fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa masu son kisan ɗan fir'auna nada nasaba
da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba).🤗🙏🏻

ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


✍🏻
[12/18/2020, 3:57 PM] HASNA : +234 909 304 4460:
Page 31

...............“Muje”. Ya faɗa a hankali. Babu shiri nai azamar ɗago idanuna na


kallesa, duk da ni yake kallo ban janyeba, cikin harɗewar harshe nace, “Anan zan...
zan kwana?”. Tamkar baiji abinda naceba ya ɗauke kansa, dubansa yakai ga sararin
samaniya daketa sake caƙuɗewa da duhu, batare da yace min uffanba ya raɓani ya nufi
gate. Hawayen da nake maƙalewa suka silalomin a kumatu, a fili nace, ‘Dan ALLAH kar
kaimin haka nidai’. Kamar yasan mi nake faɗe ya juyo yayinda ya buɗe ƙofar gate ɗin
zai shige, “Karki bari na dawo na sameki a nan gurin”. Yafaɗa yana nunoni da
ɗanyatsa alamar gargaɗi. Hannu nasa na share hawayen fuskar tawa kafin na taka nima
zuwa gate ɗin. Maigadine kawai ke bin jam'i a bakin gate ɗin da yake anaji daga
cikin gida. Ganin yayi tsaye yana kallon maigadin ne yasa nima naja na tsaya, sai
da aka sallame sallar da dama zaman tahiyar ƙarshe suke. Kamar jira, ana yin
sallama maigadi na miƙewa ya nufosa. Fuska a haɗe Jay ke kallon maigadi, baiko amsa
gaisuwar da yake masaba da sannu dazuwa yace, “Ka bautama UBANGIJI tamkar kana
ganinsa, dan idan kai baka ganinsa shi yana ganinka, MANZON ALLAH ya horemu da zuwa
masallaci muyi sallah cikin jam'i, miyasa kai kafi zaɓar yinta kai kaɗai a cikin
gida? Shin tsaron gate dan kar wani ya shigo yafi maka muhimmanci akan zuwa ka samo
cikakkiyar ladar da mahaliccinka kaɗai ke badata? Daga yau ina mai baka shawara a
kowanne lokacin salla ka kulle gate ɗin nan idan yazama dole saika zama mai tsaron
mutanen cikin gidan kaje kai sallah cikin jam'i”. Kan maigadi a ƙasa yace, “Nagode
sosai Alhaji, ALLAH ya saka da alkairi ya kareka kaima, ya ƙarin haƙuri?”. Cikin
lumshe ido Jay yace, “Alhmdllh, abokinku ya tafi ya barmu”. Hawayene suka ziraro a
fuskar maigadi, hakan yasa Jay yin gaba shima yana haɗiye abinda ya tokare
maƙoshinsa.
Jiki a saɓule nabi bayansa mukabar maigadi na kuka, sai naji nima hawayen
nawa na sake gangarowa, dukda bawani sanin gimba nai sosai ba mutuwarsa ta taɓani
ainun, mutum mai fara'a dason mutane.
Yana gama buɗe ƙofar da keys ɗin daya ciro a aljihu iskar na tasowa, hakan
yasa muka shige da sauri saboda irin mai ƙasarnan ce sosai, da sauri na maida ƙofar
na rufe na jingina jikinta ina sauke numfashi da share fuskata da hijjab ɗin gudun
kar wadda ta hau ta shigarmin ido.
Boss kam ya kunna fitilar falon saboda an kunna Gen..., a take haske ya
gauraye ko ina, baice dani komaiba ya nufi sama abinsa. Tafiyarsa kawai zaka kalla
zaka fuskanci yana cikin damuwa, dan a sanyaye yakeyinta. da kallo na bisa har
saida ya ɓacemin, na sauke ajiyar zuciya ina lumshe idanuna, a ƙasan raina addu'a
nake ALLAH yasa idan iskarnan ta lafa yace zai maidani Masarauta.
Tunda ya shiga bedroom ɗin sai ya shiga yatsina fuska, shaf yama manta
ko gadonsa bai samu arziƙin gyaraba yau, duk yanda yake jinsa a matuƙar gajiye haka
ya daure ya shiga kakkaɓe gadon, ya gyarashi tsaf kamar ba yanzu za'a kwanta a
kansaba, fitowa yay ɗaukar tsintsiya, duk da sarai yaga Bilkisu dake tsaye jikin
ƙofa har yanzu yay tamkar bai gantaba yaje ya ɗakko kwandon da kayan sharan ke ciki
yazo ya sake hayewa sama.

Da kallo na bisa, haka kawai sai naga kamar bai daceba, dan da alama
shara zaiyi da kansa, bayansa nabi jikina duk a saɓule, ga kaina namin wani irin
ciwo ƙasa-ƙasa, ga yunwa dan rabona da abincin kirki tun breakfast ɗin safe, a
garinsu marigayi fura kawai nasha rabin kofi itama sai da aka takuramin. Duk da
sallamar da nayi bai ɗago daga abinda yakeba, nasan salon amsa sallamarsa a ciki-
cikine hakan yasan ban damuba dan nasan dai ya amsani, nace, “Bara in share”. Kamar
bazai kulani ba, sai kuma ya miƙamin tsintsiyar ya fice.
Ajiyar zuciya na sauke na cigaba da sharan a sake ganin ya fita saini kaɗai.
Tsaf na kammala sannan na nufi toilet, shima dai yana buƙatar wankin dukda bawani
datti yayba na tashin hankali, tsaf na gyarashi cike da ƙarfin hali. Ina fitowa
daga bayin shima yana shigowa ɗakin, saurin ɗauke kaina nayi daga garesa saboda
ganinsa a tuɓe babu riga sai dogon wando kawai da farar singlet yana waya, ya zauna
a bakin gado

n yana cigaba da wayarsa, kusan mintuna biyu ya juyo inda nake tsaye, yatsunsa biyu
ya murza sukai ƙara, hakan yasa na ɗago kaina garesa, alamar nazo yaymin. Ahankali
na taka zuwa garesa, ya miƙamin wayar batare da yace komaiba ya bar wajen. Duk da
bansan ko waneneba haka nai sallama, muryar Ummah naji ta amsamin, hakan yasa na
gaisheta cike da girmamawa, itama daga can da kulawa ta amsamin tare da min
ta'aziyya. Nai mata godiya Nabeelah ma ta amsa muka gaisa, sai aunty Batool itama,
daga nan mukai sallama. Wayar na ajiye masa bakin gado na fita falo, Zama nai a
kujera ina jiran ya fito naji hanlin da nake ciki, harga ALLAH bana fatan kwana a
gidannan. Nai zurfi a tunani da jiran fitowarsa kira ya shigo wayata, gyara zama
nai na cirota a aljihu, Amaturrahman ce, dan haka na ɗaga muka gaisa, daga can
tace, “Mun jiki shirune, ca muke tun biyar zaki dawo?”. Ɗan murmushin ƙarfin hali
nayi, kafin nai mata bayanin yanda zata iya fahimta, nakuma nuna mata cewar bamu
dawoba muna ƙauyen su gimban sai dai gamu nan a hanyar dawowa” addu'ar isowa
lafiya tai mana kafin mu yanke wayar. Na faɗama Amaturrahman hakane da tunanin idan
boss ya fito zaiji tausayina ya maidani can a daren nan.

Jawaad daya samu yay wanka da ruwa mai ɗumi sosai sai yaɗanji daɗi da sauƙin
nauyin jikinsa sai dai na zuciya, yay alwala ya fito, ƴan dube-dube ya hauyi sai
dai babu ko alamarta a ɗakin, guntun tsaki yaja yana lumshe idanunsa, dan shi kaɗai
yasan ya yakeji, ga yunwa ga gajiya ga damuwa, dan shi babuma abinda ya sakama
cikin nasa bayan coffee da yasha a office sai ruwa da yayta sha a garin su Gimba.
ita kanta tausayinta yakeji gashi bawani ƙarfine da itaba ta tashi daga ciwo
shekaranjiya jiya. Wadrobe ɗinsa ya buɗe ya ɗauki jallabiya fara tas ya saka mata
turare sannan yasa a jiki, harya shinfiɗa abin salla sai kuma ya kalli ƙofa, koya
kirata bazai yuwu tajiba saboda iskar da ake a waje abun babu sauƙi, tamƙar zata
ɗauke rufin kwano, danma duk Windows ɗin sashen a rufe suke shiyyasa sukejinta da
sauƙi su.
“Ki taso kiyi wanka”. Ya faɗa kawai daga ƙofar ɗaki ya juya abinsa dan yasan
zata iya jinsa daga inda take. Ba ƙaramin wintsilawa kayan cikina sukaiba lokacin
da furucinsa ya isomin cikin dodon kunne, sai dai koda na ɗago tuni ya juya sai
ƙamshinsa daya barmin. Rasama wane tunani zanyi nai, mi yake nufi da nazo nai
wanka? ‘A toilet ɗinsa?’ na faɗa a fili kamar zanyi kuka. saukar ruwan sama babu
zato ya sakani miƙewa zumbur dan naji tsoro wlhy, gashi da ƙarfi ya sauka dukda
p.o.p hakan bai hanani jin ƙararsaba akan rufin, to nidai dama can akwai tsoro idan
ana ruwa, nafi buƙatar naga mutane a kusa dani hankalina yafi kwanciya, balle
wannan da ruwan ya kasance kaso biyu a cikin uku iskace ma, wani wal garin yayi na
walƙiya, labulen Window'n da ba'a sakiba sai glass ɗin kawai aka rufe yasa naga
tamkar inuwar mutum a wajen, jikina har rawa yake na tashi na nufi ɗakin boss da
ɗan gudu-gudu sauri-sauri har ina neman faɗuwa, wayatama anan na barta saman
kujera. Na maida ƙofar da ƙarfi na rufe ina rumtse idanu da sakin nishi mai ƙarfi,
har yanzu ƙirjina sai wani ɓal-ɓal yake badawa.
Shidai Jay salla yake, amm duk da haka ya jiyo yanda Bilkisu ta rufe ƙofa
da ƙarfi, koda ya idar bai juyi ya kalleta ba, ya miƙe domin kawo isha'i da yaga
lokacinta yayi. “Sallarce bazakiyi ba komi kike nufi?”. Da sauri na buɗe ido ina
kallon bayansa daya juyamin. Murya a raunane nace, “Ai idan naje gida duk zanyi
fa?”. Cikin takaici Jay yace, “Ainan ɗin jejine ko? Karki bari na ɓata miki rai a
darenan Miemaa, ƙyaƙy! tom”. Daga haka ya kabbara sallarsa.
Jin yanda yay maganar a kausashe na tabbar zai aikata duk abinda ya faɗa
ɗin, haka na nufi toilet ɗin ina ƙunƙuni a raina, wannan wane irin abune haka,
miyasa tunda anga hadarin baza'a kaini inda nakeba sai a wuto dani nan, nidai komai
dare saina bar gidanan ehe. Da wannan ƙunƙunan a cikin rai na shiga bayin, ruwa mai
zafi na haɗa dan jikina bala'in ciwo yakemin sosai, banga wani soso ba bayan nasa a
bayin, haka na ɗauka nai wankan da shi ina maijin daɗin ruwan, sai da na kammala
nai alwala sai kuma

naji ƙyanƙyamin maida kayan dana cire, to amma idan ba su ɗinba mizan saka? Nida
bazan fita da tawul ba gaskiya, to idanma na ɗaura tawul inada kayan dazan saka
ɗinne a ɗakin.........?
Wata irin ƙara na saki jikina na masifar rawa saboda ɗaga kan da zanyi
idanuna sukai tozali da wata iriyar mummunar halitta baƙa ƙirin da jajayen idanu,
jikinta dai zam maciji, amma kan bana maciji baneba...
A rikice Jawaad dake addu'a ya miƙe saboda jiyo ƙarar Bilkisu dake bayi,
ALLAH ya sosa bata kulle ƙofarba, ya tura da ƙarfi babu ko neman izini ya shige,
dai-dai bily tai baya zata faɗi saboda numfashinta daya ɗauke dan firgici,
tallafota yay ta faɗo jikinsa, yayinda idanunsa kebin halittar dake silalawa ta
Window zata fice da kallo. Sai da ta gama ficewa tsaf sannan ya maido kallonsa kan
Bilkisu, saurin kauda idanunsa yayi dan babu komai a jikinta, ya jawo tawul dake
ciƙin ƴar drawern glass na toilet ɗin ya yafa mata sanann ya ɗaukata cak batare da
yace komaiba ya fita da ita. Saman gadonsa ya shimfiɗeta, dukda ya yafa mata tawul
sai da ya sake jan bargo ya rufa mata har saman ƙirjinta, tsaye yay yana ƙarema
fuskarta kallo tamkar maison gano amsar tambayoyin zuciyarsa akan fuskartata,
tsahon mintuna kusan goma kafin yabar wajen ya koma toilet ɗin yana dube-dube, babu
komai kam, sannan a mamakinsa Windown kaɗan ya ɗaga, hanyar da yabi baikai faɗin da
halittarnan zata iya shiga da fitaba, ‘mikenan?’ ya tambayi kansa, dagacan gefen
zuciyarsa ta bashi amsa da (Aljanu). “Aljanu!” ya maimaita akan laɓɓansa har sau
biyu. “Hummm!” ya sake faɗa a fili yana ɗibar ruwa kaɗan a ƴar roba dake toilet ɗin
ya fita. Iskar hadarin ta fara lafawa, sai ruwa da ake yaf-yaf na farkon damuna,
dan daya fara da ƙarfi sai kuma ya koma ɗaf, sai kuma ɗan yaf-yaf, sai dai walƙiya
da aketa faman yi harda cida mai ƙarfi lokaci-lokaci. Zama yay a gefen gadon kusa
da cikin bilkisu tare da ajiye robar ruwan a ƙasa batare da ya shafa mataba ya faɗa
tunani. Abinda ya faru a jeji ɗazun, kalaman baba ƙaura, kalaman abokan ɗan
fir'auna, ainahin abinda Gimba ya gani har yazo ya faɗa masa a randa aka shirya
juya ɗaurin auren Qaseem da bilkisu zuwa Azeema da Qaseem bilkisu da ɗan fir'auna,
Accident ɗin ɗan-fir'auna, mafarkinsa, sai abinda ya gani yanzu wanda ya firgita
bily. Ya shiga saƙa waɗanan abubuwan dake gogayya da juna daki-daki a muhalli guda.
Yay murmushi mai ciwo saboda amsar data zo masa a zuciya lokaci ɗaya. Cikin zafin
nama ya miƙe, Ranƙwafawa yay kan bilkisu ya shafa mata ruwan daya dumtso a hannu, a
take ta kawo numfashi mai ƙarfi.
A hankali na buɗe idanuna, sai kawai a bazata naci karo da fuskar boss dake
ranƙwafe kaina daf da tawa, dan har inajin saukar numfashinsa akan tawa fuskar,
gabana ya faɗi, nai saurin fara waige-waige danson kauda fuskata. Saukar tattausan
tafin hannunsa naji saman fuskar ya sake juyo dani garesa. Duk yanda naso janye
idanuna da suka shige cikin nasa na kasa, kallon ido cikin ido mukema juna karon
farko, wani irin abu mai wuyar fassara ke fitowa daga ƙwayoyin idanunsa masu girma
da sirkin jaa suna shiga cikin nawa, atake naji tsigar jikina na tashi, ƙofofin
gashina na buɗewa gashin na miƙewa, jinina dukya tsinke lokaci guda yana wani irin
gudu a cikin jijiyoyi, sai kawai na saki kuka a hankali.
Jawaad da har yanzu idanunsa ke kafe a cikin na bilkisu yaɗan murza babban
yatsansa daga jikin hancinta har zuwa ƙasan idonta ya kwashe hawayen dake fitowar
ya maida yatsan baya jikin ƴan uwansa, dan har yanzun tafin hannunsa na tallafe da
kuncinta na haggu. Ahankali ya furta, “Tabbas ƙaddararki da tawa a haɗe take
Miemaa, zan bada ƙarfina da lokacina wajen binciko abinda ya ƙullemu ƙarƙashin
inuwa ɗaya insha ALLAH”. Yana gama faɗar hakan ya saka ɗayan hannunma a gefen
kumatuna na haggu ya ɗauke duk hawayen dake zuba a idanuna guda biyu, sannan yaja
baya tare da miƙewa tsaye yabar wajen.
Lumshe idanuna nai a hankali kalamansa namin kaikawo tsakanin zuciya da
ƙwaƙwalwa, a hankali nima kalaman baba ƙaura da abinda ya faru yau a jejin suka
shiga dawomin daki-daki. Jin an ruƙo hannuna nai saurin buɗe ida

nuna, boss ne riƙe da riga a hannu, batare da yayimin maganaba ya ɗaga kaina a
hankali ya ziramin wuyan, sannan ya kamo hannuna ya taimakamin na saka, ɗayanma
haka. Juyawa yay yana faɗin, “Ki tashi kiyi alwala ki sauke nauyin sallolin dake
kanki”. Daga haka ya fice a ɗakin. Dukda tsoron dake a raina haka na miƙe dan nima
rashin yin sallar cizon raina yake sosai, sauka nai daga gadon, rigarsa ce t-shirt
mai guntun hannu, dukda a ido bata da girma sai gashi takai min har kusan quarter
ɗin cinyata, na ɗauki wandon dana gani gefena, a raina nake raya ‘Ni balki, nice
kuma da saka kayan boss yau?’. Sauƙina wandon irin mai taushin nanne da roba acan
ƙasansa, sannan a sama ma robace harda zariya. zariyar naa ɗaure sannan a tsoro-
tsoro na nufi bayin ina addu'a a cikin raina, saida na leƙa na tabbatar babu komai
sannan na shiga batare dana rufeba na ɗauro alwalar na fito. Nayi namakin ganin
hijjab a ajiye, da alama tun ɗazunma ya ajiyeshi, haka na ɗauka na saka na fara
sallolin da suka shigemin.

Jawaad kam koda ya fita sashen Uncle Nasir ya nufa, a falo ya iske yaran
harda mamansu suna kallo, duk gaidashi suka shigayi da masa ta'aziyyar Gimba, ya
gaisa da Ammi ma, sannan ya zubama Ameera harara da faɗin, “Wannan banzar shigan
fa? Ko ɗan kwali babu kanki”. Cike da taoro Ameera ta miƙe tana faɗin, “Dan ALLAH
kayi haƙuri Yah Jay”. Bai sake tanka mataba, amma kallon da yake mata ya isheta
shiga uku, da gudu tai ɗakinsu domin suturta jikinta, dan dama ya hanasu shigar
banza tun yana zaune a sashen (karku manta bayan rasuwar mama Maryam Uncle Nasir
shine ya cigaba da riƙon Jay har yay aure). Baya musu wasa idan yaga kan mutum yana
rawa, shiyyasa suke masifar shakkarsa, gashi dama baya shiga shirgin ƴammatan gidan
saboda gudun raini, samarinma kansu ba kowa ke ganin fuska daga garesa ba sai
sa'anninsa dana sama dashi, suma ɗin bai maida kansa sakarai a garesuba ana dai
mutunta juna. Raihana da itama ta nutsu waje guda ya kalla, “Tashi ki samo min
abincin mutum biyu”. Tashi tai da sauri ta nufi kitchen, itadai Ammi batace
komaiba, dan macece mai mutunci da sanin ya kamata, yanda Jawaad ke tsaye kan
ƴaƴansu ita daɗi yake mata, dan shakkarsa na hanasu aikata abubuwa masu yawan
gaske, har ranta kuma ƙaunar Jay take dan ita dai halayyarsa birgeta yake sosai.
Suna ɗan taɓa hira da Ammi akan rasuwar gimba Raihana ta fito ɗauke da ƙaramin
basket na kaba mai ƙyau a hannu, tace, “Yah Jay gashi, ko nakai can?”. Batare da ya
bata amsaba ya miƙa mata hannu alamar ta bashi, kawo masa tayi tana godema ALLAH a
ranta, dan dama bason kaiwar takeba kar taje can ya sakata wani aikin kuma, dan
hankalinta nakan film ɗin da suke kallo. Yana amsa ya miƙe yayma Ammi sallama ya
fita.

Bayan na kammala sallolin sai kawai na ɗauki Alƙur'anin dana gani a ɗakin
na shiga karatu cikin sanyin murya da rauni, dan inayi hawaye na zirara tamkar an
buɗe fanfo.
Wani irin sanyi Jay yaji a ransa, ya ƙaraso cikin ɗakin sautin muryar
bilkisu na ratsa zuciyarsa, sai yaji wata nutsuwa mai daɗi na saukar masa har cikin
gaɓɓai. Bai dakatar da itaba ya ajiye basket ɗin ya fita, mintuna kaɗan ya dawo
ɗauke da kifuna biyu sunata turiri alamar tea ya haɗo musu. Motsinsa ya sani rufe
alkur'anin saboda nakai inda zan iya tsayawa, sonake na roƙesa ya maidani masarauta
tunda har yanzu da sauran dare, ƙarfe goma da mintuna Uku.
Ido muka haɗa dan shima kallona yake, na maida kaina ƙasa ina juya abinda
zan faɗaɗin da lanƙwasa yatsun hannuna madaidaita, “Dan ALLAH Yayah dare baiyiba,
tunda ruwan ya ɗauke ka kaini can koka kaini gidan Dad na kwana”. Jin shiru bai
tanka minba na saci kallonsa, shayinsa ma yake sha tamkar bai jiniba, kuma tsabar
wulaƙanci kallona yakeyi. Kusan mintuna uku yace, “Taso kici abinci”.
‘Yah ALLAH, wai da wane yare zan fahimtar dashi ya fahimtane?’. Na faɗa a
zuciya idanuna na cika da ƙwalla, Ban karaya ba dai, duk dan ya barni nafi nabi
umarninsa, babu musu na miƙe zuwa garesa, batare dana cire hijjab ɗinba nai
yunƙurin zama ƙasa. Gadon ya nunamin da hannu yana sake tamke fuska. Yanzunma dai
Umarni nabi na zauna dukda ba ha

ka nasoba, ya miƙomin kofin shayi kawai. Ƙananun kofunane dan basu wuci rabin kofi
ba, tea ɗin ma kuma bai cikaba, cikin dauriya da fatan maidani masarauta na hau
sha, sosai yayi daɗi abin mamaki, bansan na shanyeba balle dama yunwa nakeji.
Kofin da yasha nashi tea ɗin ya ajiye, ya buɗe kular dake cikin basket ɗin
ya ɗiba abinci dai-dai misali, nidai kallonsa nake ƙasa-ƙasa, tashi yay ɗauke da
filet ɗin a hannu ya koma saman kujerar ɗakin, “Ga abinci nan” yay maganar batare
da ya kalleniba. Duk da inajin kunyarsa yunwa nakeji sosai, idanma nace bazanciba
zan cutar da kaina matuƙa. Kofin na ajiye na ɗiba dai-dai misali. Koda wasa ban
ɗago kainaba harna kammala, na miƙe na tattare har filet ɗin daya gama shima na
fita dasu duk da a tsorace nake.
Jay ya bita da kallo harta fice, a ransa yake faɗin, ‘Ahaka sai ka ganta
kamar wata saliha, sai dai shegen taurin kaine da ita da tsoro ko farar kura ta
shafa mata lafiya’. (Jay a rage sa ido dai. Lol😂).

Babu jimawa na dawo ɗakin, zuciyata na sake tunzurani akan na sake


roƙonsa dai. Yana zaune inda na barsa ya baza takardu a table ɗin gaban kujerar
yanata rubutu, na ƙaraso bakina ɗauke da addu'ar neman nasara a kansa, jikin hannun
kujerar na duƙa ina mai narke murya dan yaji tausayina. “Amaturrahman ta kirani
akan sunga ban dawoba, ni kuma na sanar mata muna hanyar dawowa, kuma zan koma
masarauta, nasan sunacan suna jirana”. Aikin gabansa kawai yake kamar bai jiniba,
na kuma raunana murya da faɗin, “Boss Please, idan na kwana a gidannan da safe wace
amsa zanba mutanen gidan dasu Amaturrahman ɗin?”.
Karon farko Jawaad ya saki lallausan murmushin da har haƙoransa suka
bayyana, dukda yana cikin halin damuwa da alhinin rasuwar gimba sai ta bashi
dariya, fuskarsa ɗauke da murmushin har yanzun ya ɗago yana kallonta.
Wani irin daɗi naji ganin yana murmushi, a tunanina naci nasara, sai gani
nai ya ɗauke kansa ya maida ga abinda yakeyi batare da yace komaiba, “In faɗa miki
amsar da zaki basu idan sun ganki kin kwana anan da safe?”. Ya faɗa tamkar bashine
yay maganarba. Ganin bance komaiba ya ɗago yana kallona, “Ko bakiso na riƙe kayata?
Dan ƙyautace, idan ta ƙara wasu mintuna zata zama ta kuɗi”. Baki na tura masa dan
haushi, nace, “Inaso”.
Jay dake kallonta har yanzu yakai yatsansa dab da bakinta ya ɗallah yana
faɗin, “K kullum bazaki daina bani ciwon kaiba yarinyarnan?”.
Saurin ɗaura hannuna nai saman bakina dan zafi, idanuna har sun cika da ƙwalla,
saurin rufesu nayi dan karsu zubo, boss mugune yasin, ina tausayinsa ashe bama abin
tausayi baneba........
Ture takardun gabansa yay ya miƙe, a gaban bily dake durƙushe jikin kujerar
da yake zaune yaje yay wani ɗan dirƙuso da kowa yasan maza da iya salonsa, da
sauri-sauri zuciyarsa ke gudu, lumsassun idanunsa nakan fuskarta datai fayau saboda
ramar da taɗanyi.
Saukar numfashinsa a saman fuskata da mayen ƙamshin turarensa ya sakani ware
idanu dan mamaki, ko kaɗan ban san sanda yazo daf daniba, a take jikina ya fara
tsuma, ya saka hannunsa akan haɓata ya ɗago fuskata da ƙyau, saurin lumshe idanuna
na sakeyi ina ambatar sunan ALLAH a raina, dan wannan al'amari nasa yafi ƙarfina da
wayona. Cikin taushin muryar da bansan yanada itaba, yay magana a hankali “Na maida
amsata bakiso?”.
Da ƙyar na iya haɗiye yawu ina jinjina masa kaina alamar “eh” banason, dan
burina kawai ya tashi wlhy.
Jay da shima baisan mike damun kansaba ya kuma matsar da fuskarsa daf data
Bilkisu, a hankali ya busa mata iska saman idanunta dake rufe, mar-mar ta farayi da
idanun saboda iskar da yake busa matan.
hancinsa ya ɗora saman nata yana gogawa, cikin magana raɗa-raɗa da ko kana
kusa dasu da wahala ka jinsa yace, “Duk masu suna Bilkisu jarumaine, miyasa ke kike
matsoraciya?”..................✍

(😂😂Saura naji wani yace maganar Jay ba gashkiya bane, kowa yasan mu jarumawane masu
Suna Balkisu. Lol🚴🏼😜).

BARKANMU DA JUMA'A.

Kunata jira ko😑, ALLAH ina fara editing barci ya ɗaukeni, saida na tashi na tsinta
wayar a gehe🤣.

Asha weekend lahiya🚴🏼🚴🏼🚴🏼😍😍😍😍🤗

ZAAF
✍🏻
[12/19/2020, 3:04 PM] HASNA : +234 909 304 4460:
SURPRISE💁🏻

Wannan page sadaukarwa ne ga iyayen yaran da suka kuɓuta, gaskiya ina tayaku
murna matuƙa gaya, mungodema UBANGIJI daya maido mana dasu garemu da gaggawa cikin
ƙoshin lafiya kuma, ƴan uwa wannan yana sake nuna mana mu duƙufa addu'a wa ƙasarmu,
aikin bana shugabanni bane kaɗai, dan idanma munƙi addu'ar mune zamusha wahala,
shugabanninmu mutanene tamkarmu, suma basu isa tsaremu ba sai wanda ya haliccemu,
aduk yanda rayuwa tazo mana mu amsheta matsayin jarabawa mu godema ALLAH, UBANGIJI
yafi kowa sanin halin da muke ciki, muyi ƙoƙarin cinye jarabawa sai muzama masu
nasara, zage-zage marasa amfani nakasace irin ta zuciya, ALLAH yay mana ni'imomi
masu yawa miyasa bazamu gode masaba sai ƙoƙarin aibanta waɗanda suke mutane kamarmu
da hangen gazawarsu, sai dai taimakon addu'oinmu zamu samu tsaron da muke buƙata a
yankinmu, muyi haƙuri mu duƙufa wajen faɗama ALLAH kukanmu, mu gyara mu'amulanmu ga
junanmu mu kanmu, dan bazamu kasance azzaluman junaba sannan muce zamu samu
shugabanni adalai, mugyara sai ALLAH shima ya gyara mana danshi mai rahamane. ALLAH
ya kawo mana haske da kwanciyar hankali, ya dafama shugabanninmu suma akan ƙyawawan
ayyukansu, saɓanin haka ALLAH ka magance mana badan halinmu ba😭🙏🏻.

Page 32

.................Ganin yanda ta tsume sai ta bashi dariya da tausayi, ya dungure


mata kai yana miƙewa da faɗin, “Yarinyarnan ki rage tsoro”.
Ni kaina bansan na sauke wani kakkauran numfashiba tare da komawa na zauna
daɓar, nai azamar cusa kaina tsakanin cinyoyina ina mai godema ALLAH daya tashi. A
raina sai ayyana rashin kunya irin na maza nakeyi, suyi abu kuma su fuske abinsu
tamkar basuyiba.
Jay da tuni ya koma kan aikinsa yaɗan kalleta ya maida kansa ga rubutun
da yakeyi, haka kawai yanaso ya ganta a yanayin tsoro dan ƙyau take masa. Bai
sakebi takantaba ya cigaba da haɗa bayanai akan case ɗin mutuwar Gimba, ya ɗaukama
kansa alwashi sai yabi kadin jininsa, duk masu hannu a cikin wannan al'amarin kosu
ubanwaye saiya soya musu gyaɗa bisa tafin hannu. Ganin lokaci yaja sosai Bily na a
yanda take tun ɗazun ya sashi sake kallonta, muryarsa babu alamun wasa yace,
“Miemaa!”.
Gajiyar dake tattare dani tasa har barci ya saceni a haka ban fargaba, a
bazata naji ya kira sunana, na ɗago da sauri na kallesa, shima ni yake kallo, sai
dai fuskarsa babu walwala sam. “Tashi kije ki kwanta” ya faɗa yana nunamin gado da
idanu. Yanda ya tsuke fuska babu sauƙi yasa na miƙe babu musu dan nasan dai kwana
anan dole ya tabbata, zuwa nai na kwanta a bakin gadon sosai, naja bargon na rufama
jikina batare dana cire hijjab.
Jay daya kuma maida hankalinsa ga aikinsa yace, “Kicire wannan hijjabin
tunda ba cinyeki za'ai a ɗakinba”. ‘Boss matsala’ na ayyana a cikin raina ina zame
hijjab ɗin naja bargon har saman wuyana.
Duk da azabar ciwon kai da ya keji haka ya jure yana cigaba da haɗa
bayanan, sai kusan ƙarfe ɗaya saura ya miƙe, kallo ɗaya yayma sashin da Bilkisu
take kwance ya fahimci har yanzu idonta biyu, baice komaiba ya cire jallabiyar
jikinsa yasa t-shirt fara akan boxer ɗinsa ya haye gadon shima, sai dai ba kwanciya
yayba, zama yay ya jingina bayansa jikin fuskar gadon ya kashe fitilar ɗakin yabar
iya ta gefen gado. Bargon yaja ya lulluɓe iya ƙafafunsa zuwa cinya, ya lumshe
idanunsa yana maijin zafi da ƙirjinsa ke masa wanda yaketa ƙoƙarin dannewa,
tunɗazun dannewa kawai yake dan bayason ya ƙuntata zuciyar yarinyarnan da laifin
daba nataba, yana buƙatar jin wasu abubuwa daga garetane shiyyasa ya kawota nan
dama. Rayuwarsa da gimba ta shiga kokawar dawo masa cikin zuciya, yarone mai
mutunci da sanin mutuncin duk wanda zama ya haɗashi dashi, yasha saka Gimba manyan
ayyuka masu haɗari akan aikinsa kuma yay masasu cikin ƙwazo, gimba na ɗaukarsa
tamkar yayansa da suka fito ciki guda, tabbas yayi rashi wanda yasan bazai taɓa
maye gurbinsaba har abada, danshi tuni yabar ɗaukar gimba matsayin drivern sa kawai
jinsa yake a jininsa tamkar ɗan uwansa abokin farin ciki da baƙin ciki. Wata ƴar
ƙwalla ta taru mai akan fatar idanu kaɗan, hannu yasa ya shareta yana mai jero masa
addu'oin ne

man gafara a cikin zuciyarsa. Ya ɗau tsayin mintuna goma a haka kafin ya juya ya
kalli Bilkisu, ɗauke kansa yayi murya cike da ɗaci yace, “Miyasa kika dawo gidan su
Hudah da zama?”.
Banyi tunanin ya fahimci idona biyu ba har yanzun, na rumtse idanuna da
ƙarfi ina sauke ajiyar zuciya, batare dana motsaba nace, “Ƙaddarar maraici”.
Idanu Jay ya tsurama bayanta, tsawon sakanni ya ɗauka a haka kafin ya sake
ɗauke kansa daga gareta, “Ina dangin mahaifinki suke? Misa basa cikin rayuwarki?”.
Hawayene masu zafi suka silalomin, dan yau kan Boss ya taɓomin inda yafi
ko'ina ciwo a zuciyata, zaune na tashi na jingina da fuskar gadon nima, hawaye na
ƴar tseren fitowa na shiga bashi amsa kai tsaye, dan na fahimci so yake kawai yasan
wacece niɗin kafin zuwana gidan su aunty Shahudah, batare dana kallesaba nace, “Har
iyayena suka bar duniya su dukansu basu taɓa sanar dani wata matsala dake
tsakaninsu da duk danginsu ba, dukda nasha musu tambaya sai dai babu wanda ya taɓa
bani amsa ƙwaƙwƙwara a cikinsu, kullum amsarsu a gareni itace, (komai da lokacinsa,
idan lokacin yayi zan sani) tun ina damuwa da abun harma na ciresa a zuciya, dama
ba komai ke sakani kwaɗayin son jiba sai yanda nake ganin sauran yara ƴan uwana
sukan shirya a ranakun juma'a da Sallah suje gidajen danginsu, sai dai ni daga
gareni ba haka baneba, tunda na girma nai wayo a gidan haya mai ɗauke da ɗakuna
kusan arba'in na buɗi ido na ganmu, bara dai na maka gwari-gwari zakafi farimtata.
Ni dai sunana Bilkeesu ɗiya ga malam Ado makaho, ƙwarai mahafina
makahone da ko tafiya baya iya yi sai da ɗan jagora, Sai mahaifiyata Asiya.
A shekarun baya can mahaifina yana ɗan gani da ido ɗaya, amma da ga baya wahalhalun
rayuwa suka ida rufe ɗayan idon yazam gaba ɗaya, mahaifiyata ma tana da nakasar
ƙafa, dan kuwa gurguwace bata ma iya tafiya sai dai jan jiki. A matsayin da iyayena
suke kawai zai nuna muku ni ba kowan kowa bace ba, dan kuwa muɗin talakawane irin
tiɓis ɗinan da a kullum sai an nemo za'aci. Abin da zai matuƙar birgeka a rayuwar
iyayena shine sam mahaifina baya bara balle aje kan mahaifiyata, duk da baba baya
gani bai yarda zama maroƙi ba, dan a ganinsa UBANGIJI ya masa dukkan gata da ya
bashi rai da lafiya, idaniyar ganice kawai bashi da ita. Sana'ar mahaifina itace
sai da kayan ɗinki irinsu zare, allura, almakashi da dai sauran kayan nau'in ɗinki
tsiraru dai-dai arziƙinsa, a gaba ɗaya jarin idan zaka dinƙuleshi waje ɗaya bazai
wuce na naira dubu goma sha biyarba, wataƙil ma na zurma da yawa. Dalilin kamewarsa
na janye kansa da ga ƙasƙancin bara ne ya ja hankalin mafi yawan telolin anguwarmu
zuwa sayayyar kayan ɗinki a wajensa. Sai mahaifiyata da ke saida kayan kuka, kuɓewa
busashshe, kayan ƙamshi harda daddawa domin kare mana mutunci itama. Gidan da muke
gidan hayane mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in, dan irin dogon gidannan ne da akan
jeranta ɗakuna reras da ga farkon baranda zuwa ƙarshe tamkar gidan karuwai, ba wani
faɗine da gidan ba, amma kowa iyakar mu'amularsa a ƙofar ɗakinsa ne da bazata gaza
taku goma ba, babban kicinne guda ɗaya a gidanmu dake a farkon shigowa gidan wanda
ya gama cuɗewar baƙi saboda mafi yawancinmu girkin icce mukeyi, masu arziƙin
cikinmu ne keda lasisin dahuwar abinci saman gawayi, can da ga ƙarshen gidan kuwa
banɗakine guda biyu, na kashi da wanka, wanda suka ɗaine duk yawan mutanen gidan ke
shiga, shiyyasa mafi yawanmu zaki samu kowa da fo ɗinsa na kashi a ɗaki ko ƙaramin
botikin fenti, da safe idan bakai azamar tashi kai wanka ba to fa ka tabbata ƙila
sai dare ko goshin magriba zaka samu damar yinsa, shiyyasa da yawanmu mukan jera
kwana biyu babu wanka.
Tunda na taso a gidan na ganmu, hakama mafi yawan waɗanda suke gidan haka na tashi
na gansu, dan har takai mun wuce ƴan zaman haya sai dai ƴan uwa. mahaifina da
mahaifiyata duk haifaffun garinne, kuma dukkan danginsu suna ciki suna rayuwa,
hasalima akwai masu arziƙi a ciki. Sai dai kowa yasan halin zuciya irin ta wannan
zamanin, inhar baka da shi to kaida banza duk ɗaya kuke, kai tsaye ma ake mantawa
da kai a cikin dangi. To ballema irin iyayena da suka kasance n

akasassu, inhar za'a iya mantawa da mai ƙafafu da hannu da idanu saboda talauci ya
masa katutu ta yaya kake tunanin ba za'a manta da musakan iyayena da bayan rauni da
ALLAH ya jarabcesu da shi na halittar jiki harda talauci ba?. Ni kaɗai iyayena suka
haifa a duniya, nima an jima ba'a sameninba, sai da ga baya ALLAH ya azurtasu da
samuna matsayin ƴa ɗaya tilo a garesu, duk da talaucin iyayena da kasantuwarsu
nakasassu ni ƴar gatace, dan gwargwadon iko iyayena tsaye suke a kan bani tarbiya,
nakanje makarantar gwamnati kamar yanda sauran ƴaƴan gidanmu ke zuwa, hakama ina
zuwa islamiyya. Sai dai aduk lokacin da aka buƙaci wani abu da ga makaranta da yafi
ƙarfin ƙarfinmu hankalin iyayena kan tashi da ni kaina, wannan yasa da yawan lokuta
karatun nawa ke kwan gaba kwan baya, dan kuwa ƴan ajinmu sunsha tsallakewa gaba su
banni da maimaita aji saboda rashin kuɗin abu idan an buƙata tamkar ba makarantar
gwamnati ba. Badan bani da ƙoƙari bane, a wannan ɓangaren ma ina sahun farko na
gwarzayen yara masu ƙwaƙwalwar karatu da fahimtarsa, sai dai rashin kuɗi ke
daƙileni a kulum..........................

Tunda Bilkisu ta fara bama Jay labarin rayuwarta idanu kawai ya kafeta
dashi ko ƙyaftawa bayayi, ko sau ɗaya bai katseta ba har saida takai aya, fuskarta
shaɓe-shaɓe da haye ta juyo tana kallonsa. “Wannan itace asalin Bilkisu da take
gabanka, mai rawa da bazar Dad, badan shi ba babu mai sanin wannan BILKEESUN bare
ya bibiyi tarihinta, Yah Jawaad, bazan bijirema aurenkaba, dan har yanzun bansan
asalin ƙullashi ba, sai dai kasani rashin auren Yah Qaseem tamkar butulcine daga
alkairan Dad a gareni, ya ɗaukeni a lokacin da kowa ke ƙyamata, ya mini gata a
lokacinda masu gata ke gudun raɓata, ya tsaftace rayuwata a lokacin da datti mai
ciwo ke lulluɓe da ita, shin baka ganin ya cancanci fiye da auren jininsa a gareni
koda kuwa matarsa bata ƙaunata?”.
Jawaad dake kallonta idanu jazur ya ɗauke kansa daga gareta a karo na
farko, murya a dakushe yace, “Bazan musa miki cancantar Dad da abinda yafima haka
daga garekiba, sai dai ni Jawaad Abdul-Aziz Yusif nace bai cancanci samun
sadaukarwar komai daga gareki ba”.
Sosai nai masifar waro idanu ina ture bargon da naketa faman rufe jikina
dashi da, nama manta boss ne a gabana, dan haka cikin zafin rai nace, “Kai wanene
da kake tunin Dad bai cancantaba? Yaushe ka sanni harda zaka iya aza mizanin
cancantarsa da kalaman son sakamin shakku da baƙantasa a gareni, y.......”
“Yah isheki!!”. Ya faɗa cikin daka tsawa yana ɗaga hannu tamkar zai
makeni. Baya nai da sauri ina mai rumtse idanu dan nama sadaƙar mazgenu zaiyi.
Jawaad ya rintse hannun da yakai zai maketa yana lumshe idanunsa tare da
danne lip ɗinsa na ƙasa da haƙori tamkar zai hudashi, kusan sakan ashirin suna a
haka kafin shi ya fara buɗe nasa idon da hannun yaja goran ruwa dake bed side
drawer yasha, ahankali abinda ya tokare masa maƙoshi ya faɗa, ya maida jikinsa ya
jingina da gadon yana ƙoƙarin dai-daita nutsuwarsa.
Nima jin bai makeninba yasa na buɗe idanuna, karan farko a rayuwata da
nakejin zafinsa, miyasa yakeson aibantamin Dad ɗina bayan shine yaymin gatan da har
shiɗin ya shiga cikin jerin masu sanina....?
Jay daya ji ƴar nutsuwa tazo masa ya sauke numfashi daɗan ƙarfi, batare
da ya juyo ga bily ba yace, “Ina su Firdausi da iyayenta?”. Kamar bazan tanka
masaba sai dai nace, “Tun randa na baro gidan bayan kwaɗama Jazuga abu ban sake
waiwayarsa ba saboda inajin tsoro, Nima babban burina a yanzu sanin halin da suke
ciki, musamman dana yawaita mafarkinsu a kwanakinan”.
“Miya hanaki waiwayarsu bayan lafawar abubuwa?”.
Kallonsa nai da mamaki, nace, “Taya za'ai batun kisan kai ya iya lafawa?
Kasheshifa nayi da wannan hanun nawa”. Nai maganar ina mai fashewa da kuka da nuna
masa hanun nawa.
Murmushi naga yayi, dukda dagani kasan na takaicine hakan bai hanani jin
ciwoba. Ya juyo sosai yana kallon hannuna da nake nuna masa, sai kuma ya ɗauke
kansa. “Wace anguwa su Uwargida suke?”.
“Harna baro gidan bansan anguwarba nima”. Baice komaiba ya sauka daga gadon,

saurin ɗauke idona nai daga garesa ganin gajeren wandone a jikinsa wanda iyakarsa
rabin cinyarsa. Bai sake cemin komaiba tsahon lokaci yanata safa da marwa a ɗakin,
nidai gittawarsa kawai nake iya hangowa ban yarda na ɗago na sake kallonsa ba. Yazo
gabana ya tsaya, hakan yasani ɗagowa na kallesa a tsorace, “Wa bincikenki ya nuna
yayma Amina fyaɗe?”. Wani irin muguwar bugawa ƙirjina yayi akan wannan tambaya
batare da nasan dalilin hakanba, maimakon na bashi amsa sai kawai na fashe da kuka.
Tsura mata idanu kawai Jay yayi cike da mamaki? Yanzufa ta bashi labarin
komai tiryan-tiryan, amma ya mata tambaya ta saka masa kuka. A dake yace, “Qaseem
ne?”. Kasa bashi amsa nai saboda wani irin juyawa da kaina keyi tamkar ana bugamin
guduma, da sauri nakai hannu biyu na riƙesa ina faɗin, “Ya ALLAH kaina”.
Babu shiri Jawaad ya durƙusa a gaban gadon ya tarota ganin zata faɗi, saurin
kwantar da ita yay ya kama kan ya riƙe cikin hannunsa yana janye nata hannun,
addu'a ya shiga yimata jin kan ya ɗauki wani mugun zafi maiban mamaki, ga jikinta
ya ɗauki wani irin rawa. Cikin matuƙar sarƙewar halshe take faɗin, “Kamin addu'a,
kamin addu'a dan ALLAH, kaina zai fashe, wayyo kaina”.
Tsahon lokaci yana mata addu'a har tai shiru, jikinma ya daina rawar da
yakeyi, bai dainaba cigaba yay da mata har saida yaji zafin kan ya ragu sosai barci
ya ɗauketa kafin ya miƙe, alwala yaje ya ɗauro yazo ya saka dogon wando ya kabbara
salla.
Kusan ƙarfe uku da rabn ta farka, nama manta a ina nake sai dana gansa a
zaune da alkur'ani a hannu sannan na tuna. Yunƙurawa nai na tashi da ƙyar dan
jikinna kam ciwo yake min, nima alwalar na ɗauro nazo bayansa na saka wani abin
sallar na tada.
Jay duk yanajin motsinta, sai dai baiyi maganaba saboda karatun da yakeyi.

UBANGIJI mai rahama da jinƙai sai ya bama Bilkisu da Jawaad damar raya wannan
dare da ibada har akai kiran sallar asubahi.
★★★★★★★

Tunkafin ya dawo sallar asuba na gyara ɗakin na wanke har toilet, ina
cikin gyaran falon saman ya shigo, dauriya kawai nakeyi dan wani irin barci nakeji
fiye da zato, batare dana kallesa ba nace, “Ina kwana”. “Lafiya, waya saki wannan
aikin?”. Kaina a ƙasa har yanzu nace, “Babu kowa”. Gaba yay yana faɗin, “Ki barsa
iya nan kizo ki shirya na ajiyeki inada ayyuka da yawa yau”. ban iya cewa komaiba
harya shige, dubana na maida ga agogon falon, ƙarfe shida da minti talatin da huɗu.
Ƙarasa mopping ɗin nayi da sauri-sauri.

Yanda tai gyaran gadon sai ya kasa daina kallonsa, da ƙyar ya iya ɗauke
idanunsa, abu ya ɗauka ya fita daga sashen gaba ɗaya yana jaddadama Bilkisu tai
wanka kafin ya dawo.
Kayan sharan naje na ajiye na nufi ɗakin, a gaggauce nai wankan dan
banason yazo ya iskeni, babban tawul da yafi kowanne girma na ɗauro na maida
hijjabi jikina na fito, ina isa gaban mirror yana shigowa da sallama, ALLAH ya soni
ban cire hijjabinba, na amsa masa kaina a ƙasa. Ledar hannunsa kawai ya ajiye saman
gado ya nufi toilet yana faɗin, “Ga kayan da zaki sakanan”.

Sauri-sauri na shirya cikin doguwar rigar dake cikin ledar ruwan sararin
samaniya, sai sabon hijjab har ƙasa fari tamkar wata matar liman, na fita dan bana
fatan ya fito ya samini a ɗakin.

___________________

Misalin ƙarfe bakwai da mintuna arba'in Bilkisu da Jawaad suka fito


daga sashensa.
Addu'a naketayi a raina ALLAH yasa karmu haɗu da kowa, ALLAH kuwa ya amsa min
ma muna fitowa ashe motar da zamu fita na a kusa. Da kansa ya buɗemin na shiga,
sannan ya maida ya rufe ya zagaya mazaunin driver. Bazan ɓoye mukuba banason
tuƙinsa, dan na kula ya iya zuga gudun tsiya a hanya. To amma babu yanda na iya.
Haka muka tafi babu mai cema wani uffan a cikinmu, sai dai naji daɗi sosai
yanda naga mun nufi masarauta kai tsaye. Yauma kamar ranar a ƙofar farko ya tsaya,
waya ya ɗauka yay kira. bayan ya ajiye wayar ya juyo yana kallona.
“Ya sunan anguwar da kuka zauna?”. kaina a ƙasa nace, “Bankaura”. “Zaki
zauna a gida yau sai gobe idan ALLAH ya kaimu zaki koma aiki, ki dage da addu'a,
kina dai ganin duk abinda ke faruwa”.

Kaina na jinjina masa nace, “Insha ALLAH, amma dan ALLAH miyasa jiya kace ban
cancanci nai sadaukarwa ga Dad ba?”.
Shiru kamar bazai tankaba, kusan sakan biyar sannan ya juyo yana kallona,
“Lokaci zai nuna mana komai, babu abinda zaki iya fahimta a yanzu sai ruɗani, kije
idan lokaci yay zaki sani”. Kafin nace wani abu su Amaturrahman da Amintacciyar
baiwar gimbiya sun fito a mota. Gaishesa sukai cikin girmamawa, ya amsa shima fuska
aɗan sake yana faɗin, “Kucema Ummu ga amanarta nan ban ciba”. Dariya Amintacciyar
baiwar gimbiya tayi tana faɗin, “Jiya kam ai tayi faɗa tamkar ta ari baki anƙi
maido mata ƴarta”. Murmushi Jay yayi kawai yana ɗan kallon gefen da Bily take suna
magana da Amaturrahman kafin ya ɗauke kansa.
Sallama yay mana ya tafi, Muna shiga daga ni har Amaturrahman barci muka
kwanta dan shi nakeji fiye da komai a yanzun.

__________________________

Jay yana ajiye Bilkisu Office ya nufa, ayyukane fal kansa har baisan da
ina zai faraba, yana zama abinda ya farayi shine bige-bigen waya, a kiran farko
Umarni ya bada a nemo masa gidan da Bilkisu ta sanar masa sun zauna da iyayenta a
Anguwar Bankaura, tare da ainahin maigidan da halin da gidan yake ciki yanzun. Kira
na biyu kuwa Ainahin gidansu Baba makaho inda aka haufesa yasa a binciko masa
shikuma a Anguwar Tudin Jarƙasa.
Sunyi zaman awa biyu shida su Aliyu, duk da yaga ɗacin ran da Rose takeyi
baibi takanta ba, bayan sun kammala ta buƙaci yin magana dashi, ca yay mata bashi
da lokaci yanzun kam saita bari wani lokacin. Cike da takaici ta riga kowa fita.
Haka ya cigaba da rage akainin gabansa.
Misalin sha biyu yabar station zuwa Barrack ɗin sojoji da suka fara zuwa
jiya kafin su tai jejin nan, ya samu ganawa da Lieutenant General a tsaitsaye dan
ya iskesa yana shirin fita, ya sanarmasa wajen baba ƙaura yazo. Lieut G ya saka
wani soja yayma Jay rakkiya har gidan da baba ƙaura yake zaune a cikin Barrack ɗin.
Baba ƙaura ya tarbi Jay da murmushinsa mai tsayawa mutum a rai, bayan
sun gaisa ya sake yima Jawaad ta'aziyya. Jawaad yay masa godiya akan gudunmawar da
ya basu jiya. Fuska ɗauke da murmushi baba ƙaura yace, “Yaro bani nayiba ALLAH ne
yayi”. “Hakane baba” Jawaad ya faɗa cikin sake tabbatarwa. shiru suka ɗanyi na wasu
sakanni, baba ƙaura yace, “Mike tafe da kai?”. Ɗagowa Jay yay ya kallesa da ƙyau,
ya tsufa sosai sai dai yana tare da ƙarfinsa, bashi da tsaho sosai sannan shiba
wada bane, ya risinar da idanunsa yana faɗin, “Maganganunka na jiya baba na kwana
juyasu a rai, sai dai har safiyar yau ban iya samo amsar ko guda ba, baba mika sani
a kanmu?”. Murmushi baba ƙaura yay idonsa akan Jawaad, yace, “Yaro bansan komai a
kanku ba, hasalima jiya na fara ganinku a iya tsahon rayuwata, kowane irin mutum a
duniya yanada baiwarsa, ni tawa baiwar kenan, fahimtar wasu abubuwa daga mutane,
akwai mutane masu irin wannan baiwar tawa da yawa a duniya, sai dai mafi yawansu
sunfi zaɓar aikata saɓon ALLAH da tasu damar, sai kaga mutum ya zama ɗan tsubbu ko
naɗama kansa wani girman da zai halakar da mutane daga barin ALLAH, ko ya maida
baiwar tasa ga zalunci da neman duniya. wlhy kaji na rantse maka bansan komai daya
shafekuba face abinda UBANGIJI ya bama idanuna ikon gani tattare daku jiya.....”
Cikin jinjina al'amarin baba ƙaura Jay yace, “baba ko zamu iya sanin abinda
ka fahimta ɗin?”
Murmushi Baba yay da faɗin, “Yaro minene sunanka?”. Jay yace, “Jawaad”.
“Masha ALLAH, malam Jawaad bawani abune na gani a rayuwar kuba, domin kuwa ƙaddarar
da duk ke cikin rayuwar kowanne ɗan adam wannan ɓoyayyen sirrine daga taskar ALLAH,
abinda ALLAH ya bani ikon gani tattare daku kawai shine rayuwarku na ɗaure da wani
al'amari mai girma, sannan kunada taurari masu ƙarfin haske da suka hana duhun dake
zagaye daku tasiri, dan har na waccan yarinyar sunfi nakama haske, abinda nazarina
ya bani bayan faruwar abubuwa a dajin nan shine akwai sihiri mai ƙarfin gaske
jingine da jininku, su wanene sukai muku? Miye dalili? Saboda mi? Daga yaushe ne?
Shine ban saniba sai abunda ALLAH yasio sanar daku nan gaba”.

Cikin ɗaurewar kai Jawaad yace, “Amma miyasa kanema sanin sunan mahaifinta?”.
“Saboda duhun dana gani biye da bayanta yafi naka rintsi”. “Duhu kuma baba?”.
“Ƙwarai duhu ɗana, amma da sannu zai yaye insha ALLAHU bisa rahamar ALLAH, shawarar
dazan baku shine ku dage da addu'a da sadaka musamman a cikin wannan watan mai
albarka na Ramadhan da zamu shiga nanda kwanaki uku idan munada rabon kaiwa. Kunika
ciyar da bayin ALLAH fiye da yanda kukeyi a baya, ku saka dubunnan marayu farin
ciki fiye da yanda kukeyi a baya, ku kaima UBANGIJI kukanku fiye da yanda kukeyi a
baya, sannan a daren jiya naga wani haske dake nesa da kai na tunkaroka, sai dai
yana nesa dakaine, bansan tayaya zakaje garesaba koshi yazo gareka”. Da sauri Jay
ya kalli baba ƙaura, “Baba ko hakan nada nasaba da mafarkin da nake mai
sarƙaƙiya?”. “ALLAH kaɗai yasan gaibu Jawaad, amma tun yaushe ka fara mafarkin?”.
Jimmm Jay yay alamar tunanin, yace, “Baba idan har ban mantaba na farayinsa a daren
da muka dawo daga wata horaswa daga ƙasar America ne, shekara kusa ɗaya kenan, sai
da danayi sau ɗaya ban sakeba sai a watanan nan naketa maimaitawa, bayan ɗaurin
aurena da ita sai kuma ya canja salo”. “Ikon ALLAH,to shidai mafarki sirrine yaro,
sannan akwai abinda yake ishara daga UBANGIJI a cikinsa, akwai wanda shaiɗanu ke
jinginuwa a cikinsa, akwai wanda keda alaƙa da saka abu a rai, to amma kozan iya
jin wani abu daga mafarkinka?”. Babu musu Jay ya faɗa masa na farko da wanda yay a
ƙarshe washe garin ɗaurin aurensa da Bilkisu bayan sallar la'asar. Baba ƙaura ya
daɗe baice komaiba, yanata juya abun a ransa amma bai samu wani hasken da yake
buƙataba, ya ɗago ido ya zubama Jay na tsahon lokaci kafin ya janye, “Alƙar jini a
cikin jini yanada nasaba da kamar kun haɗa jini kenan nidai a nawa ɗan sanin da
UBANGIJI ya banifa, amma sanin gaibu sai ALLAH”. Sam Jawaad bai fahimci komai daga
kalaman baba ƙauraba, dan a iya saninsa babu ta inda yakeda dangantaka da Bilkisu
sai ta wajen su Hudah..... Baba ƙaura ya katse masa tunani da cewar, “Sarƙaƙiyar
dake ɗaure da rayuwarku tanada nasaba da wani zalincin mai tushe daga wasu jininku,
UBANGIJI shikaɗai yasan sirrin dake ɓoye dai, amma a mafarkinka mutum kake gani
yana sanar dakai kokuwa?”.
“Da farko dai bana ganin kowa, amma daga bayan nan mace nake gani, gashi na
santa a mafarkin, sai dai dana tashi fuskarta saita ɓacemin, duk iya hasashena bana
tunota”.
“To UBANGIJI shi kaɗai yasan dalilin sirranta maka ita a zahirin taswurar
zuciya, kuje kucigaba da addu'a, ALLAH bai manta da al'amarinku ba. Ga wannan
gadalin (maganin), karkaji komai sanine daga abinda ALLAH ya sanar dani nima,
saboda bibiyarta da ake ana tsoratar da ita dalilin abinda ke hannunta nasu ALLAH
bazai basu damaba insha ALLAH, a zubashi a Abu mai tsafta, a karanta Ayatul
kursiyyu (itace aya ta 255 a suratul baƙara), suratul Yunus aya ta 79~82, Suratul
Ɗaha aya ta 65~70, Suratul Kafirun, Al-Ikhlas, Al-Falaq, An-Nas, a tofa ciki, A
shafe jiki da shi akuma ringa sha safe da yamma, sannan ai turare da wannan. Insha
ALLAHU duk wani baƙin aljani da aka haɗata dashi zai gusa, zaku samu haske mai yawa
akan al'amarin cikin amincin ALLAH, sihirin dake jikinku zai warware da izinin
UBANGIJIN al'arshi.
Ada Jawaad ya tsani irin waɗanan abubuwan, amma jin baba ƙaura ya ambata
harda ayoyin ALLAH saiya amsa yay godiya, sunɗan ƙara tattaunawa yay masa sallama
ya tafi.
Daga Barrack ɗinan tasha ya nufa inda gimba ke hawa motar garinsu idan zaije
gida weekend.................✍

😉🤫👍🏻😘.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya

500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun
tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899


sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


✍🏻
[12/21/2020, 3:47 PM] HASNA : ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 33

...............A ɓangaren gidan Dad komai ya ƙara caƙuɗewa, yakasa barin ƙasar koda
kuwa zuwa Niger ne, komai Shahudah batayi yanzu banda aikin kuka da kiran Jawaad,
ta tabbatar musu indai basu rabata da Habib sun maidata gidan Jawaad ba saita kashe
kanta, kullum cikin lallaɓata suke da mata alƙawarin samun Jawaad duk rintsi kuma
har ƙarshen rayuwa, zakuma su rabashi da bily koda tsiya dan ita kaɗai ta
mallakesa, acewarsu tabari ya gama hayaƙin rashin mutuncinsa yanzun sunada hanyar
maganinsa ne.
Qaseem kan tun bayan barin Jay asibiti da Bilkisu ya shiga wankama Doctor mari akan
ya buɗe masa ƙofa, cikin gigitar azaba Doctor ya buɗemasa ƙofar ya fita, koda ya
fito sai bai iske su Jawaad ba, cike da mahaukacin gudu ya ɗauka motarsa ya fice
daga asibitin. Marukan da yayma Doctor ne yasaka sauran Doctors ɗin asibitin
alwashin ɗaukar mataki, atake suka kira police, ko jinin dake fita ta hancin Doctor
basu tsaida masaba saida ƴan-sandan sukazo suka gani.
Qaseem daya fita yana can yana bilayin neman su Jawaad titi-titi bayan yaje gidansu
ance Jay baizo nanba, ya nufi gidan Jay na A.Y street ne ƴan-sandan da aka tura
kamashi da yawun hukumar lafiya ta ƙasa sukai ram dashi, duk yanda yaso musu taurin
kai da nuna musu shiɗin wanene ɗan wanene sunƙi saurarensa. Dan kuwa dai shima
Doctor ɗin da ya mara ɗan wani ƙusane a ƙasar, gashi ma'aikaci a asibitin gwamnati,
shiyyasa kamun Qaseem ya taho tun daga sama.
Yau tsahon kwanakin Qaseem biyu kenan a police station batare dasu Dad sunma
saniba, su duk tunaninsu Qaseem na gidansa ne tunda fushi yake dasu bazasu ganshi a
yanzuba.
Salman ma dai daƙyar suka lallashesa ya haƙura da batun barin ƙasar, dan yacefa shi
lokacin mutuwarsa baiyiba da zai tsaya ɗan-fir'auna ya sakashi cikin jerin waɗanda
zai watandarsu kamar kajin salla, da farko Mom masifa ta fara masa, da dai taga
babu ci sai ta koma lallaɓashi har Dad ɗinma, da ƙyar ya haƙura akan shifa da yaga
wani motsi zai ware abinsa, da wannan ajandar tasa suka yarda, ba komai yasa
basason yay nesa dasuba sai sanin halinsa musamman akan shaye-shaye, shiyyasa
basason yay nesa dasu, ALLAH dai yasosu abin bai nisaba suka tsaya kansa ya haƙura.
Momy dake haɗama Dad tea takai dubanta garesa, yay shiru tamkar babushi a d/table
ɗin, gaba ɗaya rikicewar da gidan yayi yasa sun fita hayyacinsu daga ita harshi,
wani irin jin ƙarin tsanar Bilkisu tai a ranta, dan kuwa a ganinta duk itace
sanadin komai, shigowarta rayuwarsu ne ya tarwatsa musu gida, da Dad bai jajubo
musu itaba da yanzu suna zaune cikin kwanciyar hankalinsu, siririn tsaki taja tana
mai dangwarar masa da kofin tea ɗin gabansa. Kallonta yay da mamaki, yace, “Lafiya
kike tsaki? Bayan kinsan abinda nafi tsana kenan a rayuwata?”.
Momy ta kuma jan wani tsakin tana cigaba da zuba masa farfesun bindin sa ɗin da
takeyi, “Bakai nakema tsakiba nikan Dadynsu, sanadin tarwatsewar gidana na tuna,
lokacin da zaka ɗako yarinyarnan dana nuna ɓacin raina fushi kaitayi dani, ka ringa
nunamin batada maraba da ƴaƴanmu jininmu a wajenka, gashi kaga sakamakon daya biyo
baya ai, ka ɗakkota daga inuwa ita ta turamu rana, ranarma mafi munin zafi da ƙuna,
nikam dai wannan zuminci naku ai ALLAH ya tsine mar (Wa'iyazubillah, Mom zuminci ya
wuce tsinuwa, dan yana ɗaya daga cikin hanyoyin shiga aljannah🙄).
Dad yace, “Humm, wlhy kuma kingafa Aysha duk da wannan abun daya faru sai ban daina
jinta a rainaba, a ganina yarinyarnan bata da laifi akan rikicinan, daga gidanku
aka harɗa komai, kekuma gashi bakison laifin danginki sai nawane sakarkaru ko?!”.
Yanda yay maganar da zafi-zafi ya saka Momy kallonsa da mamaki fuska a yatsine
tace, “Ikon ALLAH, kaifa nagama sammun yarinyarnan yafi cinka fiye da kowa a
gidannan kai da wannan shashashan Qaseem, to wlhy inma ban ɗauki matakin ƙarshe
akan yarinyarnanba kuce ba sunana Aysha Humaira ba Mtsowww!!” ta ƙare maganar da
buge table ɗin ta tashi tabar wajen.
Duk wannan abu dake faruwafa tsakanin Dad da Mom Shahudah da Aamilah na zaune a
D/table ɗin suma, Aamilah dai earpiece ne a kunnenta tanajin waƙa, shiyyasa batasan
mi tsoffin nata je tattaunawa ba, Shahudah kam cikin damuwa take mai gusar da
hankali, zuciyarta gaba ɗaya tana ga Jawaad da tunanin ina Bilkisu?, dan a yanzu
dai wannan matsalar tafi cin zuciyarta fiye da komai, ɗan-fir'auna tasan ko kotune
Dad sai ya kaisa ya saketa, inmafa bai saketanba ita ahaka zatai aurenta tunda ai
bada soyayya tsakaninsu aka ɗauraba, a ganinta tunda babu soyayya ai auren bai
ɗauruba kenan (Hudah Kai a tukunya😖😂 lol).
Buga table ɗin da Mom tayine ya maido hankalinsu kansu, duk suka bita da kallo
kafin su kalli Dad da shima kallon Momyn nasu yake rai a matuƙar ɓace.
Aamilah dai baki ta taɓe ta cigaba da sauraren waƙarta dacin abinci, Shahudah ce
dai ta kalli Dad ɗin bayan ɓacewar Mom a idanunsu. “Dad wai faɗa kukeyi ne?”. Huda
tai maganar tana mai tsatstsare Dad da manyan idanunta da suka koma ƙanana a yanzun
saboda tsabar yawan kuka. Kansa ya girgiza mata yaja bowl ɗin data saka masa
farfesun ya fara shan romon kawai dan kauda hankalin Shahudah daga abinda take
zargin.

___________________________________
Jawaad kam daga wajen baba ƙaura tashar da Gimba ke shiga mota idan zai tafi gida
ya nufa. Wajen bawani babban tsasha baneba, dan motocin garin su Gimban ne kawai
sai masu ƙarisawa cikin ƙauyikan dake maƙwaftaka dasu. Kowa na sabgar gabansa daga
masu talla har matafiya da masu sauka, sai ƴan mashinan Napep dake ɗaukar masu
shiga cikin gari idan an saukesu a tashar. Sai da ya gama ƙarema wajen kallo daga
cikin motarsa kafin ya ɗauki glasess ɗinsa baƙi ya toshe idanunsa dashi, baya wani
cikin mood ɗin farin ciki, hakan yasa sam fuskar babu alamun sauƙi balle rangwame.
Tamkar zakin dake taƙama bayan yaci ya ƙoshi haka ya fito daga motar, dama tun
fakawarsa mafi yawan jama'ar dake kai kawo a wajen suka zubama motar ido da
tsumayen waye zai fito daga cikinta, dan kuwa dai taci ta ƙoshi ita kanta motar
balle kuma mamallakinta a ganinsu dole ya zama abin kallo. Yako zama abin kallon
dan shi kansa saida ya takura dajin yanda idanu ke yawo a kansa har jinin jikinsa
na tsitstsinkewa. Guntun tsaki yay yana sake ɗaure fuska, ya fara taku a hankali
yana tunkarosu kansa tsaye.
Tuni da masu kallon nasa da masu gulma suka nutsu, aka shiga gaishesa da tambayarsa
ko akwai abinda yake buƙata?. Ta cikin glasess ɗinsa yake ƙare musu kallo ɗai-ɗai,
sukam sam basa ganin idanun nasa, sai ƙyawun da glass ɗin yayma fuskarsa ba ƙaramin
ɗaukar hankalinsu yayba. Jawaad ya shiga ƙarema saurayin dake gabansa tamkar zai
duƙa kallo, nuni yay masa da hannu alamar ya miƙe da ƙyau. Babu musu kuwa ya miƙe.
“Inason ganin shugaban wajen nan naku ne”. Jay yay maganar yana maida hannunsa guda
cikin aljihun wandonsa. Kafinma saurayin yace wani abu wani dattijo da kallo ɗaya
zakai masa ka fahimci wahalace ba tsufaba ya ƙaraso wajen yana mai amsa maganar Jay
data shiga kunnensa. “Gani nan Alhaji, barka da zuwa, naɗan zagayane kama ruwa
shiyyasa”.
Shi dai jay kallonsa kawai yake harya dasa aya. Dattijon ya kuma faɗin, “Muje daga
cikin runfa Alhaji nan kaga rana na dukanka”. Babu musu Jay ya bisa suka shiga
rumfar da ƙuda keta faman bi saboda sanyinta, ga robobin abinci da sukaci harda na
fura duk ƙudan ya baibaye, gefe kuma masu saida abincinne ƴammata da yara ƙanana
abin gwanin ban tausayi. Shi kallonsu yake da tausayawa sukuma suna kallonsa da
birgewa da sha'awa. Duk da Jay yaji ƙyanƙyamin tebiran dake wajen matsayin abun
zama haka yay shirin zaunawa akai da farin wandonsa tas daketa ɗaukar ido. Da sauri
dattijon nan ya dakatar dashi, abin sallar dake can kan babbar tabarma shimfiɗe ya
ɗakko bayan ya bugata ƙura ta tashi, yazo ya saka masa kan bench ɗin. Jay baice
komaiba ya zauna duk da itama dai sallayan sai a hankali.
Dattijo yace, “Alhaji bara a kawo maka ruwa ko fura”. Da sauri Jay yace, “A'a
nagode karka damu, tambaya nazo yi”. Dattijo yace, “ALLAH yasa na sani to Alhaji.
Jay yaɗan gyara zamansa, idanunsa dake cikin glass kafe akan Dattijo, yace, “Akwai
wani yaro saurayi da bazai wuce shekaru talatin da ɗaya ba mai suna Gimba, duk
ƙarshen mako yake zuwa nan ya shiga mota ko kun sanshi?”. Cike da jimami Dattijo
yace, “Tabbas munsan Gimba, ai a wajenan kaf Alhaji babu wani driver da zai ce maka
baisan marigayiba, danshi mutum ne na mutane ga barkwanci ga alkairi”. Jay Cikin
nuna alamun kamar bai sani gimban ba yace, “Naji kace marigayi; kana nufin ya rasu
ne?”. Zama Dattijo ya gyara yana matsar ƴan ƙwalla, “Alhaji ashe bakasan ya rasuba?
Ai jiya-jiya akai zana'idarsa ma, muma yau labari yake zuwa mana akan duk yanda
abun ya faru, ance ogansa da yakema aikine yajasa cikin ƙungiyar asiri, dama anata
ƙananun magana akan yanda Gimban kema mutane ɓarin abin arziƙi a garin musamman a
irin wannan watan na Ramadhan dazai kama, to dai kasan mutanenmu da kwaɗayi, dukda
anajin tsoro dai haka ake amsa a lashe, sai ya gusa kaji anayi dashi, saifa
yanzunne da suka tsotse jinsa zance keta fitowa abubuwa gasu nandai barkatai babu
daɗin ji”. Tunda Dattijo ya fara magana jikin Jay ke wani yaamm na mamaki, haka
kuma aka maida zancen rasuwar gimban ahi baida labari?, kai ɗan adam sai dai ka
gansa ka barsa da halinsa kawai, baiji komai a ransaba tunda yasan ba hakan bane,
abinda kawai ya ɗauka jahilci ne ke aiki cikin ƙwaƙwalen kansu. Ya gyara zamansa
cike da ƙwarewa cikin salon aiki yace, “Ai nima akan batun mai gidan nasa nazo
daman, yanzu haka mun kamashi a hannu bincike mukeyi, idan ka bamu haɗinkai kaima
kanada naira dubu hamsin sabbi ƙar a takarda. Jimm Dattijo yayi yana ninƙaya a
nazari, mikuma ya tuna sai ya kalli Jay yace, “Nikuwa mina sani akan wannan zance
Alhaji?”. A karan farkio Jay yay murmushi, “Ba canai ka saniba daman ai, sonake dai
naji abinda ka sani ɗin, ranar juma'a Gimba yazo tashar nan taku?”. Dattijo yace,
“Eh to kamar dai yazo”. Jay daketa dannewa bayason ya tsoratashi yace, “Banason
ƙwana-ƙwana a magana, ka fitomin a mutum mu wanye lafiya”. Ya ƙare maganar da zare
glass ɗin idonsa sukai ido huɗu da Dattijo. Sosai kwarjinin Jawaad ya sake cikama
Dattijo idanu dama wajen baki ɗaya. kasa jurar kallon idon da Jay ke masa yayi ya
duƙar da kansa. Jawaad yay wani munafukin murmushi yana ɗauke kansa shima, “Yaya
zan samu amsar gaskiya?”. Kai Dattijo ya ɗaga batare da ya yarda ya sake kallon Jay
ɗinba. “Tabbas yazo nan ranar juma'a nayan an sakko masallaci”. “A motar wa ya tafi
gida?”. “Bai shiga motar kowaba ranar a tashar nan”. Cikin ƴar fusata Jay yace, “To
motar wa ya shiga?!”. “Ni...ni bansanshi ba Alhaji”. Murmushi Jay ya sakeyi irin na
zan lailaya kanka a titi ɗinan ya ɗaga jacket ɗinsa ƙaɗan yace, “Kalli nan”. Koda
Dattijo ya ɗago yauy arba da bindiga sai ya waro idanu waje, kafin kace kwabo zufa
ta gama jiƙesa. Jawaad yace, “Saika zaɓa, amsata ta gaskiya kokuma rasa numfashi?”.
“ALLAH ya baka haƙuri oga, wlhy inada iyali da ƙananun yara a gida, abinne wuya
garesa shiyyasa”. “Kai kake ganin wuyarsa”. Cewar Jay yana haɗe fuska fiye da
farko. Cikin kakkausan murya yasake faɗin, “A wace mota gimba ya tafi gida ranar
juma'a?”. “Tare da ɓaleru” Dattijo ya faɗa da sauri kamar zai haɗiye harshensa.
Jay ya sake zare glass ɗin idonsa a karo na biyu, sun sake kaɗawa sunyi ja da ɓacin
rai, “Wanene Ɓaleru?”. Ya faɗa yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya da harɗe hannayensa
saman ƙafar yanaɗan juya glasess ɗin hannunsa idanunsa kafe akan dattijon. Kan
Dattijo a ƙasa yace, “Shima ɗan garinmu ne, zanma a iya ce maka kamar abokai suke
da marigayi gimban, dan duk sa'anni ne kuma unguwarsu ma kusan ɗayane”. “Ina zan
samesa yanzun?”. “Wlhy oga ban saniba, kawai dai nasan yana anan birni shima yana
aikin drivernci a wani gida”. Miƙewa Jay yayi tsaye da cewar, “Koma ina yake ni zan
memosa, ba'a cin kuɗina a matsayin cin hanci, amma ina biya idan na saka aiki, zan
baka aiki nakuma biyaka yanzunan, ya rage naka kaimin da gaskiya kokaci amanata
idan anzo an biyaka abinda yafi nawa, biyoni”.
Jiki a saɓule dattijo yabi bayan Jay har zuwa isa inda ya faka motarsa. Jawaad ya
buɗe motar ya shiga ya zauna batare daya rufeba, ƙafafunsa duka a waje, takarda ya
ciro da pen ya kalli Dattijo dake tsaye, “Ka iya karatu ne?”. Da sauri Dattijo
yace, “Eh nayi sakandire Oga”. Jay baice komaiba ya maida kansa yay rubutu da hausa
a takardan sannan ya miƙa dattijon tare da kuɗi bandir ɗin ɗari biyar. “Wannan
aikin zakaimin, ga kuɗin aikinka nan”. Daga haka ya shige motar sosai ya rufe
abinsa yaymata key tare dayin reverse yabar wajen.
Ganin lokacin sallar zuhur yayi sai ya tsaya yay sallah kafin ya ƙarisa station,
tunkan ya shiga office ɗinsa ya samu kira daga sir Ahmad, fasa shiga nasa office
ɗin yay ya nufi na Sir Ahmad ɗin. Ba'a masa iso dan zai shiga office ɗin sir Ahmad,
knocking kawai yakeyi a bashi iznin shiga. Yanzunma kansa tsaye ya isa yay knocking
ɗin, daga ciki sir Ahmad ya bashi izinin shiga dan yana kallonsa.
Cikin girmama ya gaishesa, Sir Ahmad ya rufe file ɗin gabansa yana kallon Jay ɗin
dake zaune, “Ina ka shige hakane tun ɗazun nake aike a kiramin kai?”. “Am sorry sir
na fitane”. “Okey to ya ƙarin haƙuri?”. “Alhmdllh sir”. “To ALLAH ya gafarta masa,
ya raya abinda ya bari. Na kiraka ne dama akan Qaseem, wai yau kwana biyu yana
hannun police”. Cike da mamaki Jay yace, “Police kuma? Basusan shiɗin wanene ba?”.
Murmushi Sir Ahmad yayi yana kwantar da bayansa jikin kujera, “Sun sani sarai,
gabace da gabanta, ya mari wani Doctor ne a General hospital shekaranjiya lahadi
harya fidda masa jini, to Doctor ɗin ɗan Alhaji ɗan-iya warzu ne, shinefa yakai
maganar hukumar lafiya ta ƙasa baki ɗaya, sukuma suka saka aka kama Qaseem ɗin”.
Huci Jawaad ya furzar , shi shaf yama manta yabar Qaseem ranar a asibiti, yaso ya
koma amma sai aka samu akasi, ya tabbata dalilin abinda ya faru ranarne Qaseem ya
mazge Doctor, shi baisan yaushe Qaseem zai daina halin ƴan danbe ba ya rage baƙar
zuciya. Yace, “Yanzu miya faru to Sir?”. Sir Ahmad yace, “I.G ne ya kirani da safen
nan yake sanar min cewar shi Warzu yace sai anje kotu, shikuma yaga ɗaya daga cikin
yaranane shiyyasa ya kira ya sanarmin dan anrma lauya, kuma ko babansa ma bai
saniba”. Murmushi ne ya kufcema Jay, dan kuwa dai yasan lallai da Dad yaji da ba'a
zauna lafiyaba, dan inma ɓakin son ƴaƴane Dad yatake Warzun ya shanye. “Miya baka
dariya?” Sir Ahmad ya faɗa yana tsatstsare Jay da idanu. Kai Jawaad ya shafa yana
ƙara sakin wani murmushin, “Sir abinne nasu ne ai, ni nasan Dad da yasan Qaseem na
cell da yanzu garinan ya fara yawo a gajimare dan rikicinsa, kafaɗamin wane station
ne? zanje na fiddosa yanzun insha ALLAH”. “To aini banƙi in baka damar cirosanba,
kaima rikicin naka nake tsoro ai, dan baka da maraba da Dadyn naku, ta wani wajenma
ka fisa zama ɗan ƙunar baƙin wake, nikuma banason ka haɗa harƙalla da Warzu dan
shaiɗanin mutumne da kake ganinsa kullum cikin manyan kaya”. “Karka damu Sir salin
alin zamu dawo”. “To shikenan gashi, saika nema lauyan Qaseem ɗin kuje tare”.
Sallama Jay yaymasa ya fita.
Bai koma office ba ya sake ficewa, harga ALLAH bazai iya jurar tuƙiba, haka yake
shi baison tuƙi saita kama dole, dolene yasan mafita, to amma shikam ‘Wane driver
ne zai iya maye masa gurbin Ginbansa?’ yay maganar cikin rai zuciyarsa na masa
zafi. Office ɗin Jabeer ya shiga, babu jimawa suka fito tare. Jabeer ɗinne ya jasu,
sai da suka fara tafiya yaɗan dubi Jay ɗin daketa faman danne-danne a tab ya ɗauke
kansa ya maida ga titi “Na zatafa wajen rasuwarnan ka koma?”. Jay da bai ɗagoba bai
kuma fasa abinda yakeba yace, “A'a, dama sonake sai gobe idan ALLAH ya kaimu mu
koma mu duka”. “Okey ALLAH ya kaimu” cewar Jabeer yana maida hankalinsa ga tuƙin.
Asibiti suka fara zuwa wajen Doctor Ballo Warzu, cikin girmama ya tarisu yana
tambayar jikin Bilkisu?, mafi yawan amsarsa Jabeer ne ya bashi ita, sai da suka
gama gaishe-gaishensu sannan Jay yay masa magana akan abinda ya kawosu, da tambayar
miya faru bayan tafiyarsa?. Labarin komai Dr Bello ya basu, Jay ya dafe kai cikin
takaici.
Shi dai Dr Bello haka kawai komai Jay yayi ƙyau yake masa da burgesa, haka ALLAH ke
sakama bawa ƙaunar wani batare da wata manufa ba, yay murmushi yana kallonsa,
“Karka damu abokina na haƙura indai nine, bansan ɗan uwanka bane dana barsa tun a
ranarma baza'a kai hakaba saboda kai, naga rashin hankalin nasa ne yayi yawa
shiyyasa naga gara aɗau mataki, amma yanzu kam yaci darajar mai daraja”.
Fuskar Jay ɗauke da guntun murmushi yace, “Nagode Doctor ALLAH yabar zuminci”.
Shima Doctor godiya yaymusu, ya kuma rakosu har inda motarsu take, sai da yaga
fitarsu sannan ya koma office yana kiran babansa a waya.
★★★★★
Tunda suka shigo police station ɗin aketa basu girma, kai tsaye office ɗin d.p.o
suka nufa, inda acan ɗinma dai suka tarbi juna da girmamawa kafin a ɗaura da
gaisuwar mutunci. Jay da kansa yayma d.p.o bayanin abinda ya kawosa, ya kuma nuna
masa lawyer'n Qaseem ɗin da ya shigo a bayansu dan shi isowarsa kenan. A take anan
aka kashe magana babu zancen zuwa kotu sannan aka kawo musu Qaseem. Babu abinda
akai masa, dan ko hararsa babu wanda yayi tunda aka kawosa gurin saima girmamawa,
ko kayansa ba'a cire masaba, sannan ba'a haɗashi da kowaba a cell.
Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Jay, kowa ya ɗauke nasa fuska a tamke, Jay
ya fara miƙewa ya fice abinsa, hakan yasa Qaseem jan tsaki, rai a ɓace ya kalli
d.p.o yace su maidashi cikin cell ɗin. Duk kallon mamaki suke masa, Jabeer da yasan
wasan ya dafa Qaseem ɗin yana magana a hankali, kamar Qaseem ɗin bazai yardaba sai
kuma miya tuna oho masa ya nufi hanyar fita Jabeer da lawyer ɗinsa suka take masa
baya.
A jikin mota suka iske Jay tsaye yana magana da Engineer ɗin da zai masa gyaran
gidansa da Bilkisu zata zauna. Suna isowa yana ajiye wayar dan sungama. Sake ma
juna kallon ido cikin ido sukai shi da Qaseem, cikin ɗacin rai Qaseem yace, “Miyasa
ka cironi? Minene haɗina da kai?”. Murmushin rainin wayeo Jay yay masa yana lasar
lip ɗinsa na ƙasa, yaɗan ɗage gira cike da salo dukda idanunsa na cikin glass ne,
hannayensa duka cikin aljihun wandonsa suke, Yace, “Inada business da kaine
shiyyasa”. Wani kallon banza Qaseem yayma Jay shima, yace, “A kasuwa ka ganni?”.
Jay ya sake murmusawa tare da ciro hannunsa yaɗan sosa gefen girarsa da ɗan yatsa
yana karyar da wuya, “Karkai taurin kai, akwai tagomashi mai yawa da riba”. Qaseem
yaja tsaki ya motsa zaibar wajen yana faɗin, “Zanyi maganin tsagerancinka ne yaro
kwanan nan”. Cike da rainin hankali Jay yace, “Ai zuru batacin zuru, sai dai a haɗu
ai zuru-zuru. Nabaka nanda kwanaki bakwai kacal zaka nemeni da kuɗinka ma”. Qaseem
yay wata dariyar kai banzane ya wuce motar lawyer ɗinsa batare da yabama Jay
amsaba....
Jawaad yay wani lalataccen murmushi yana zare gilashin idonsa, sai da Qaseem ya
shiga motar sannan ya maida glasess ɗinsa yay salute ɗin motar da faɗin, “YANZUN
MUKA FARA”. (Bari na ƙarasa maka jikan Yusufa🤣. WASAN😉).
____________________________________
Ƙarfe sha biyu da wasu mintuna na farka, ni kaɗaice a ɗakin, na sauka daga gadon
ina addu'a da miƙa, naji daɗin jikina sosai gaskiya, rashin barci ai masifane.
Wanka na shigayi, amma abin mamaki sai nai karo da Jini, cikin mamaki nace, “Jini
kuma? To duka yaushe ma nai wankan tsarki? Kofa sati biyu banyiba”. Mamaki tamkar
zai kasheni nai wanka na fito. Ina shiri ina juya al'amarin cikin raina. Shigowar
Amaturrahman ne ya sakani juyawa na kalleta. Tai murmushi da faɗin, “Amarya saifa
wani Shining kikeyi miye sirrin ne?”. Murmushin yaƙe na mata kawai bance komaiba,
itama tai dariya kaɗan, “Kefa tuni na lura irin Marwah ce, muskilanci ya muku yawa,
idanma an zauna hira daku daga eh sai uhm sai a'a kuka ƙware yi, badai haka za'aje
anama Yayan namu dunɗun dunkum ba kamar hadarin maraice?”. Bansan sanda na
ƙyalƙyale da dariya ba babu shiri, dan harga ALLAH taban dariya musamman yanda tayi
da fuska sanda zatai maganar. Ta ɗagamin gira da cewar, “Ko kefa, gashi na sakaki
kin dara, ki shirya muje Ummu na jiranki, yau dai tace sai taga ƴarta”. Naji daɗi a
raina, sai dai ina ɗanjin tsoro-tsoro, nice yau zan gamu da Sarauniyar gagara badau
gaba ɗaya, ni Bilkisu ɗiyar baba makaho da Asiya gurguwa, ALLAH sarki duniya, duk
abinda kaga ba'a gani saboda ƙanƙantarsa wataran zai fito kowa ya gansa saboda
girmansa, wataran kuma sai tsufa ya sakayashi, a ƙarshe mutuwa ta ɓoyesa. Tsaf na
shirya da taimakon Amaturrahman cikin siket da riga na atanfa da sukaimin ɗas a
jiki, dukda dai basu kama jikina ba, duk yanda tasi hanani na saka gyale kasawa nai
saida na saka sannan muka fito.................✍
Barkanmu da dawowa, ina fatan kunyi weekend cikin ƙoshin lafiya😉😘😘😍😍😍😍.
Masu kira akan zasu sayi ƘWAI CIKIN ƘAYA!! bafa shi ake tallaba, muna tallar buks
ɗinmune guda goma na zafafa gasunan, duk wanda bai sayaba ya motso ya saya karya
bari romon daɗi ya wucesa🤗🤗🚴🏼

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
✍🏻
[12/22/2020, 6:53 PM] HASNA : ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 34
...................Katafaren falone daya amsa sunansa falo, komai yaji iyakar ji
fiye da tunanin mai hasashe, ga wani sassanyan ƙamshi mai kashe lakkar jiki da
tsaida gudun jini na tashi, lallai wannan baiwa ta isa a kirata sarauniya, ta haɗu
tama gaji da haɗuwar, ga kwarjini irin wanda kowa yasan masu mulki dashi. Tana
kishingiɗe ne amintacciyar baiwarta na gefenta da alama hira sukeyi, dan fuskokinsu
dukansu ɗauke suke da murmushi, sai bayi biyu kawai a falon, ɗaya na tausa mata
ƙafafu ɗaya na yanka mata tufa a ƙaramin filet. Sallamarmu ta sakata maido fararen
idanunta kanmu, da sauri Amaturrahman ta tareni tana faɗin, “Gaskiya Ummu sai kin
biya”. Murmushi Gimbiya Munaya tayi mai ƙayatarwa, cikin nutsatstsiyar muryarta
tace, “Amaturrahman kin maidani kakarki a gidannan, nakula kema auren kikeso”. Da
sauri Amaturrahman ta matsa gefe tana tura baki gaba da faɗin, “Ni ALLAH banason
aure ina tare dake da Abbu da Mommah”. Dariya hadiman sukayi, nima dai murmushi
nike, dan saita tunomin da Nabeelah. Gimbiya Munaya dake murmushi ta miƙomin
hannunta da yasha adon jan lalle, “Kinga ɗiyata manta da wannan zo naji ɗuminki
kinji”. Jikina har rawa yake saboda yanda tamin tamkar mahaifiya, na taka a sannu
cikin nutsuwa gareta, durƙusawa nai kaina a ƙasa, ina faɗin, “Barka da rana Ummu”.
Ina jiyo fitar sautin murmushinta, ta ɗora yatsunta saman haɓata ta ɗago kaina,
“Nagode da wannan girmama ɗiyata, ALLAH yay miki albarka kinji, kiyi haƙuri da
rashin ganina tun zuwanki”. Murmushi na mata ina ƙasa-ƙasa da idanu, dan bazan iya
kallonta kamar yanda take kallona ba, nace, “Babu komai Ummu”. Murmushi ta sake yi,
tare da zaunar dani sosai, ta sallami bayinta guda biyu, daga ni sai Amintacciyar
baiwarta da kuma Amaturrahman data koma can cikin kujera tana kumbura wai ance za'a
mata aure. itafa ta rantse bazatai aure tabar Ummu da Abbu ba. (Kujimin ƴa, to
itama munayar ai sunƙumota Galadima yay daga gabansu hajiya innaro😂).
Cikin nutsuwa da hikima Gimbiya Munaya kejan Bilkisu da hira, abin gwanin sha'awa,
babu wani nuna ƙyara ko izzar mulkin kasancewarta ƙasan ƙasa da ita, haka gimbiya
Munaya take, bata yarda ƙasƙantar da waniba a rayuwarta, tace tasan ciwon ƙasƙanci,
bazataso yima waniba, ita tasan wahalar da zuciyarta tasha lokacin da suke
ƙarƙashin mulkin mallakar Innaro a gidansu. (hajiya innaronmu ta mutumci
kwanciyarki lafiya cikin ƙasa matar Faruku😂🤗, karkimin fatalwa da daddare kuma
yasin😤).
Yanda Sarauniya ta iya hira har bansan sanda nake bata duk amsar data buƙata daga
gareni ba, har takai munyi zurfi sosai a hirar fiye dazaton mai hasashe, kiran
sallar zuhur ne ya tashemu, muka koma ɗakinmu domin yi, nidai banyi yunƙurin yiba
tunda naga jini a jikina dukda dai kaina a ƙulle yake.
Muna cin abinci kira ya shigo wayar Amaturrahman, ɗaukata cike da zumuɗi tana faɗin
“Meenal kun tahone?” bansan mi akace mata daga canba naji cike da murna ta sake
cewa, “Wlhy da gaske nake tana nan har sai lokacin tarewarta”. Daga inda nake ina
jiyo ihunsu, itama ta miƙe tana rawa da ihu. Nikam mamaki suke ban, Amaturrahman
irin tsagwaron izza da mulkinan na ƴaƴan sarakuna sam batayi, ko kiga tana
wulaƙanta bayi tana takasu yanda takeso, abinda kawai na fahimta tarbiyyace daga
iyayensu hakan, An nuna musu bayin gidansu mutanene tamkarsu masu daraja da
mutunci, shiyyasa sam basa tozartasu.
Ban tambayeta su wayeba muka cigaba da ƴar hirarmu, dukda nifa dauriya kawai nake
hankalina ya rabune kashi-kashi. Ba'afi mintuna talatinba saiga ƴammatan ranar da
muka taɓa haɗuwa a Saloon tare da su Amaturrahman ɗin, Meenal da Amatullah, ashe
tafiya sukayi shiyyasa ban gansuba tunda nazo. Suka rungumeni cike da murna, ni
harma mamaki suka bani, gasu suma da shegen kauɗi, aiko yinin yau dai kaina har
ciwo yake saboda surutunsu, amma zamana dasu ya ɗeben kewa sosai, sai nake ganinsu
kamar su Ummie. Muna tare Zuhrah ta kira waya, yanda sukaji muna waya da ita tana
tsokanata Amatullah ɗiyar Buzaye mai cike da sirrin ƙyau ta fige wayar ta saka a
hansfree kowa yanaji, a cewarta suma yanzu ai ƙawayen Zuhrah ne, duk ƙawayena sun
zama nasu suma.
Abin mamaki da daddare saina nema jini na rasa, baƙaramin ɗaure kaina al'amarin ya
sake yiba, ni a ƴan kwanakinnan sam bama na ganema kaina, daga wannan al'amari ya
wuce sai wannan, ALLAH na gode maka da wannan jarabawa, ya rabbi ka bani ikon
cinyeta, ka ƙaramin haƙuri da juriya.

(Amin Sakwara🚴🏼)
____________________________________
“Nifa wannan wasan naku dariya yake bani kaida Qaseem Boss, gashi yanzu Mami ta
sake tunzura komai ya ɗau zafi, shi bazai yarda da ƙaddara bane ba?”. Murmushi Jay
yayi baice komaiba, sai ƙoƙarin saka waya da yake a kunne. Daga can Abbati yay
sallama. Amsawa Jay yay suka gaisa. Yace, “Ina fatan yau zaka tashi aiki da wuri
dan inason ganinka, banason kuma a wuce yau saboda muhimmancin zaman”. Daga can
Abbati yace, “Babu damuwa, ai kama yanka akan gaɓa, dan inason na shigo namaka
ta'aziyya dama, zan shigo bayan magriba da safe sai na wuce”. Jay yace, “Kai malam
nifa yanzun ƙattai sun daina kwanarmin a gida inada iyali”. Ba Abbati ba hatta da
Jabeer dariya ya kwashe da ita harda ƙyaƙyƙyewa, Jay ya mangarema Jabeer kai tareda
ranƙwashi mai zafi, yace, “Kaima ɗan iska na wayar zan kamaka ne, masu zuwa lahira
da ido ɗai-ɗai”. Bai jira amsar abbati ba ya yanke wayarsa. Jabeer dake sosa inda
Jay ya ranƙwashesa yana tuƙi yace, “Oho dai, ai sa idon namu mai lasisi ne, ni nama
taɓa ganin munafukin soyayya irinka?, ALLAH zan cema sarauniya karta bar Mami ta
tare har sai kazo da kanka ka furta kana SO da hawaye”. Taɓe baki Jay yayi da
kwantar da kansa jikin sit ya lumshe idanunsa, a hankali yace, “Idan namata ciki a
waje saiku barta ta tare ɗin, koku bari saita haihu kukaita da ƴar ko ɗan”.
Jabeer dake ƙumshe dariya yace, “Ainasan kai waliyyine bazakai hakanba”.
Shiru Jay yay tamkar bazai tankaba. Sai kuma zuwa can ya zubama Jabeer ɗin harara
ya ɗauke kansa.
Kasa daurewa Jabeer yay ya kwashe da dariya yana dukan sitiyari. Jawaad yay guntun
tsaki da faɗin, “Kaifa wani lokacin baka da man kai, ka isheni fa”. Jabeer dake
dariya yace, “Baka da amsa yanzu, sai mun isa inda zan saida wannan jaridar
tukunna”. Banza Jay yay masa bai sake magana ba, saima kansa daya sake kwantarwa
jikin kujerar yay luf.
Gaba ɗaya a wannan yinin Jay yayisa cikin aiyuka, Baibar Office ba sai bayan sallar
isha'i, haka ya tashi a gajiye, gida ya wuce kai tsaye dan Abbati harya kirasa ya
sanar masa ya iso, ada idan zasu haɗu A.Y street suke haɗuwa, yakan daɗe bai kawo
aboki family house ɗinsuba sai idan ta kama dole, to a yanzu wancan gidan a
hargitse yake dan amma fidda komai na cikinsa aiki akeyi tuƙuru da sauya fasalin
abubuwa.
Tare suka shigo da Abbati dake ɗauke da jikkar Jay ɗin a hannu, basu zauna falon
ƙasaba saboda yay datti sosai, suka haye sama, anan yabar Abbati shikuma ya shige
bedroom dan yaɗan watsa ruwa. Ya sauke idanunsa akan gadonsa ya lumshesu yana
maijin wani iri, jiya iyanzu suna nan tare. Wasu abubuwan data dingayi ya tuna,
babu shiri murmushi ya suɓuce masa, aransa mamaki ma yake yanda take matsoraciya ya
akai ta shiga aikin nan? Bashi da mai bashi amsa dan haka ya nufi bayi, bai wani
jimaba saboda yanaso su tattauna da Abbati ya kwanta da wuri, yay shiri cikin kayan
barcinsa farare tas masu taushi wandon har ƙasa. Dama ya sayo musu abinda zasuci a
hanya, hakan yasa yana fitowa ƙasa ya sauka ya ɗakko filets ya dawo inda Abbati ke
zaune yana kallo. Sake gaisawa sukai, Abbati na juye kajin a filet Jay kuwa na daga
can wajen D/table yana haɗoma kansa Shayin da shansa ya zame masa jiki yanzun,
takai har idan baima shaba bayajin daɗi.
“Ni ina nawa shayin?” cewar Abbati. Hararsa Jay yayi ya ɗauke kansa ya maida ga tv,
“Sai kazauna tunda ni matarkane na kawo maka”. Abbati ya miƙe yana faɗin, “Kazama
matata aiban moreba Yasin, ina zani da gabjejen ƙato kamarka”. Murmushi kawai Jay
yayi ban sake tankawaba, saima shayinsa da yakesha hankali kwance har Abbati shima
ya dawo ɗauke da nasa.
Bayan sun sake gaisawa sukai jimamin rasuwar Gimba sosai sannan Jay ya ɗora da
faɗin, “Bana babu Gimba, dama shike tsaye akan rabon kayannan na azumi Abbati,
narasa wazan ɗauka yay aikinan, gashi ya kamata ace tun jiyama aka fara rabonsu
kamar yanda marigayi yakeyi”. Abbati yace, “ALLAH sarki rayuwa kenan, ALLAH ya
gafarta masa, lamarine na mutane sai addu'a, sam bama tsoron ALLAH, wanda ya bada
baiji ƙyashiba sai kaga masu rabawa sun zama azzalumai, amma kuma wai da an tashi
zagin shugabbani suma sunada bakin jefa nasu”. Jay yace, “Humm, ai Abbati ɗan adam
barshi yanda ka ganshi kaji, lokacin daka bashi zuma ya lasa zai sanar maka da daɗi
yama gode maka, amma da saɓanin hakan ya gitta kafi kowa muni a idonsa. Manta da
wannan maganar muyi wadda ta fita muhimmanci. Yanzu dai kafinma akai ga mahanar
fidda kayan, kayan abincinmu da zamu saida sunada yawane?”.
“ALLAH na tuba boss ai suma ɗin dai kamar ƙyautarne, tunda ana saida musu ne bisa
farashi mai matuƙar sauƙi, duka stores ɗinmu cike suke da kayan abinci kamar
kowacce shekara, idanma munada ƙarancin wani abu to manja ne gaskiya”.
“Karka damu, batun manja nayi magana da Jessica ɗazun, insha ALLAH zuwa jibi zai
iso, inason linka kayan da ake rabawarne, to da nayi tunanin sayen waɗanda muke
dasu a ƙasa, sai dai ɗazun kuma wani tunani yazo mani, gara mu saya hannun ƴan
kasuwa, shikuma namun mu saida musu akan farashin da aka saba ɗin bisa ƙaramar
riba”.
“Banƙi ta takaba Jay, amma kaima idan ka sayi namun ai zaka samu sauƙi, dan naga
wannan karon abubuwan sun taso da yawa, ga maganar gyaran gida naga ka saka,
hidimar aure ta wuce wasa ai”. Ɗan lumshe idanu Jay yay yace, “ALLAH zai rufa asiri
Abbati, muyi hakan kawai, inason zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu a kammala siyayyar,
dukda guri ya ƙure zuwa jibi sai a fidda kayan, kayanmu kuma da za'a saida yakamata
kuma ku fiddasu ai”.
“Eh dama munyi dasu Labaran gobe idan ALLAH ya kaimu za'ai baja koli, shiyyasama
nace zanzo na sameka yau ɗin, zan ɗauki hutun sati guda wajen aiki insha ALLAH muga
an raba kayan yanda ya kamata mabuƙata sun samu”.
“Nagode sosai Abbati, nayi magana da Alhaji Garba yadi, amma Jabeer ne zai tsaya
nan ɓangaren shi da su Aliyu dan aikin yamaku yawa kuma, inason wannan shekarar
insha ALLAH muhaɗa da tufafi wa ƙananun yara suma, ni kuma inason hankalina ya
tsaya wajen gyaran gidannan ne”.
Cikin jin daɗi Abbati yace, “ALLAH ya saka maka da alkairi ya ƙara buɗi, ALLAH yasa
baɗi iwar haka muna nan muna shagalin sunan babys ɗinmu. Murmushi kawai Jay yayi
baice komaiba. Sun cigaba da tattaunawa har kusan 12 sannan suka kwanta, Abbati a
ɗakin baƙi da Jay ya shiga ya taimaka masa suka gyara, shikuma ya koma ɗakinsa ya
kwanta.

WASHE GARI.
Washe gari Jay suka koma garin su Gimba, ta'azziya suka sakeyi, shima kuma aka sake
masa dukda wasu harda munafunci dan sun dasa ƙananun magana akan Jay ɗan ƙungiyar
asirine, shine yakai Gimba ma aka shanye nasa. Kasancewar shi mutumne mai saurin
fahimtar abu kafin su baro garin ya karanci abubuwa masu yawa daga mutane, ya kuma
saka an bincika masa inda ɓaleru yake ta hanyar iyayensa da basusan dawan garinba.
Zuwa Azhar suka baro garin.
Tunda suka dawo daga garin su gimba aiki yake babu hutu, kiran sallar la'asar ne
kawai ya tadashi, bayan an idar office ya dawo ya ɗora daga inda ya tsaya. Zamansa
baifi da mintuna goma ba Hafiz dake ɗauke da takardu a hannu ya shigo office ɗin da
sallama..
Batare da Jay ya ɗagoba ya amsa masa. Hafiz ya zauna a ɗaya daga kujerun gaban
tebirin yana faɗin, “Yauwa boss ga file ɗinan na gama tattare komai, abinda ya rage
mana kawai yanzun shine bin sawunsa kawai, kaga dai dukkan abinda muke buƙata mun
riga mun gama samunshi”.
Jawaad ya ɗago yana ɗan bubbuga pen ɗin hannunsa akan laɓɓa, takardun da Hafiz ya
ajiye ya ɗauka, sai da ya gama dubawa sannan ya sake ɗagowa ga Hafiz ɗin, “Kamar ba
komai ne anan ba ai Hafiz, Rose ta baka dukkan bayanan dake hannunta ne? akwai kuma
bayanan Restaurant ɗinan shima ban gansaba anan?”. Hafiz yace, “Oh sorry, wlhy nama
shafa'a sosai, na gidan cin abincin nan kamar suna hannun Mami ne fa, jiya naso
amsa, sai kuma na iske batazoba, bara na amsosu, saina haɗo dana hannun Rose ɗin”.
Dakatar dashi Jay yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. “Rose ta fita ita da Aliyu,
Miemaa Kirata ta kawo, nima akwai aikin dana sakata ma ita da Dawood shi ya kawo
nasa ita shiru kakeji”. Miƙewa Hafiz yay zuwa gaban landline ɗin office ɗin yana
faɗin, “Bara muji to kota kammala duka”. Jay baice komaiba ya cigaba da aikinsa,
yayinda Hafiz yay waya department ɗin su Bilkisun. Baifi mintuna goma da ajiye
wayarba akai knocking ƙofar.
★★★
Tunda nazo office ban gansaba, ban kuma je inda yakeba, ina namu office ɗin na
duƙufa dukkan ayyukan dake gabana, sai hirarmu da bata ƙarewa ni da Ummie.
Kasancewar jinin dana gani jiya tun a daren na nemesa na rasa yasa dukkan sallolina
yau nayisu batare dana sake ganinsa ba kuma. Mun fito sallar la'asar kowa ya koma
kan aikinsa. Nayi nisa sosai akan aikin da nakeyi saƙon kira daga office ɗin Boss
ya sameni. Dukda nasan dalilin kiran sai da gabana ya faɗi, dama tun ɗazun Dawood
ya sanarmin ya kai masa aikin daya sakamu tare saura ni yake jira. Miƙewa nai na
tattare files ɗin guda biyu na fita.
Da sallama na shiga office ɗin bayan nayi knocking an bani izinin shiga, naɗanji
sanyi ganin akwai Oga Hafiz a office ɗin, shinema ya amsan sallamata, dodon nawa
kam bai ko ɗagoba, gaba ɗaya hankalinsa nakan Computer, inama shigowa ƙarar danna
keyboard ɗinsa ce ta fara tarata, yanda yake dannawar da sauri-sauri yasa akejin
ƙararsu sosai. Da fara'a oga Hafiz ya tarbeni, na gaishesa ina miƙa masa file ɗaya
a cikin biyun dana shigo dashi tunda nasan dama shine wanda zan baiwa. Ɗayan kuma
na matsa tebirin boss na ajiye, murya a sanyaya nace, “Barka da yamma”. Batare daya
ɗagoba yace, “Barka” ya cigaba da aikinsa. Duk da yanda yaymin ɗin haka na sake
dannewa nace, “Gashi na kammala, sai dai result ɗin sayin hannun nasa ɗin bai
fitaba”. Dakatawa yay daga abinda yakeyi ya ɗago min manyan idanunsa da a yau suke
farare tas, sai dai sunɗan kumburo alamar cike suke da gajiya, sauri janye nawa nai
lokacin da sautin muryarsa ta fara isowa cikin kunnena. “Wakika kaimawa?”. Yay
maganar har yanzu idanunsa a kaina dan inajin yanda suke shiga ɓargona. Cikin
nutsuwa ta nace, “Sir danaje office ɗin Umar bayanan saina gamu da Hashim”. Cikin
kaushin murya yace, “Hashim! Kina nufin shi kika bamawa!?”. Yanda yay maganar ya
sani ɗagowa na dubesa da sauri. Dan masifa har fararen idanun nan dana gani yanzu
sun sirka da ɗan ja, na kula da yashiga ɓacinrai zakaga idanunsa sun sauya kala. A
ɗarare na ɗaga masa kai kawai. Uffan bai sake cewaba ya ɗauki wayar landline yay
kira.
Hafiz da duk yana zaune yana kallonsu ya kalli Bilkisu, “Mami garin yaya kika bama
Hashim bayan bashi akace ki bamawa ba?”. Kaina a ƙasa nace, “Wlhy ni bansan akwai
matsalaba ne, na fito shikuma zai shiga office ɗin shine yake tambayata ko lafiya?
Nikuma nace masa wajen Umar nazo, shine yace bara ya ajiye masa anjima saina dawo
na amsa, to kafin na koma ɗinne kuma mukai fitar ranar, jiya kuma banzo office ba,
ɗazun nakoma amsowa danna tattare komai shine Umar ɗin ya sanarmin bai bashiba,
amma ya fita idan ya dawo zai tambayesa koya mantane”
Hafiz ya ɗan girgiza kansa da faɗin, “Ki ringa kula kinji, duk wanda ba'ace kibama
abububa kidaina bashi, wannan aikin namu da kike gani kowa takansa yakeyi, shiyyasa
zakiga a komai ana taka tsantsan, bara ni naje wajen Hashim ɗin da kaina Boss”.
Jawaad ya dangwarar da kan wayar a ƙasa saboda yakasa samun Umar ɗinma, bai cema
Hafiz komaiba harya fice.
Kansa ya dafe cike da takaici, ya miƙe tare da tura kujerarsa baya da ɗan ƙarfi ni
harma na tsorata, yay taku ɗaya biyu kafin ya juyo yana kallona, yanda ya matso daf
dani yasani maida kaina ƙasa, yaɗan buga tebirin da faɗin, “Wai sai yaushene zaki
daina bani ciwon kai ne yarinyarnan? Wataran saina sauya miki kamannin fuskarnan
taki maikama data mage idan baki dawo hankalinki ba” yay maganar da yunƙurowa kamar
zai makeni. Baya nai da sauri, cikin zafin nama na tura kujerar na miƙe tsaye, dan
yanda ya fusato ɗinan nasan iya makeni zaiyi ɗin.
Jay da takaici yake neman shaƙema numfashi yace, “Zonan, idan kuma kika bari ni
nazo saina karya ƙasusuwanki”. Idanuna cike da ƙwalla na kallesa ina tura baki,
kafin na samu damar bashi haƙuri yace.
“Ni kike murguɗama baki?!”.
Saurin ɗagowa nai ina ƙwalalo idanu waje, kujimin sabon sharri, ni yaushe na
murguɗa baki dan ALLAH jama'a?. ganinfa da gaske ni yake nufowa fuska a ɗaure sai
na fara ja baya, bai fasa biyoni ba kamar yanda ban fasa tafiya da bayaba ina yarfe
hannu, jinai tamkar na saki fitsari, yayi bala'in ɗaure fuska yanda na tabbatar yau
idan ya kamani sai ya karyanin da yake faɗa. cikin sarƙewar harshe nace, “Ni wlhy
ban murguɗa maka baki ba fa Sir, kuma ALLAH bani da lafiya ma”. Nai maganar dai-dai
na dangane da bango, shikuma ya iso daf dani.
Ina rufe baki ana turo ƙofar, ido huɗu mukai da Rose, kafin bakina ya iya sake
furta wani abu naji an fisgoni na faɗo saman ƙirjin mutum.............✍

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻[12/23/2020, 2:52 PM] HASNA✍🏻: ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 35
.................Rintse idanuna nai da azabar ƙarfi, a duk lokacin da jikinsa ya
taɓa nawa nakanji tamkar na taɓa wuta, daga randa mukaje ɗakko gawar Gimba kuma sai
na rage jin hakan, sai dai sam banason yace zai taɓani, amma a mamakina yau sai
naji tamkar an azani bisa wutar. A take jikina ya fara karkarwa saboda azabar da
nakeji, cikin gangarowar hawaye bisa idanuna nace, “Boss dan ALLAH ka matsa, wlhy
jikinka tamkar wuta nake jinsa”.
Yanda ta ƙare maganar da fashewa da kuka tana neman silalewa ƙasa yasaka Jay ja
baya cikin ɓacin rai, dan shi kalamanta zafi sukai masa a zuciya, cikin kaushin
murya yace, “Qaseem ne kawai idan ya taɓaki baƙyajin zafi tunda shi kikeso?”.
Idanuna na shiga lumshewa ga zufa sai karyomin take a jiki saboda azabar da nakeji,
na shiga girgiza masa kawai, “Kaimin addu'a, fatar jikina jinake tamkar ana ɗayemin
itane”. Yanzu kam da mamaki yake kallonta, dan yanda jikinta ke wani irin karkarwa
da zufar da takeyi ta cancanci a fahimceta, kalaman baba ƙaurane suka faɗo masa
cikin rai, addu'ar ya shiga karantowa yana tofa mata, idanunsa harsun ƙaɗa sunyi
jazur saboda yanda yakeji a cikin ransa, gaba ɗaya yakan rasa wane tunani zaiyi
akan lamarinnan, idan ya zurfafa tunaninma sai kiji kansa ya fara matsanancin ciwo,
dole yake ajiye batun ya shiga wata sabgar badan kuma al'amarin baya cikin ransa
baneba. Ahankali Bilkisu ta shiga sauke numfashi, zufar na tsafewa sanyin ac na
ratsata, kusan mintuna goma suna a haka.
Rose da tunɗazun tai sumar tsaye tai Luuuu zata faɗi saboda wata hajijiya data rufe
ganinta. Da sauri Hafiz da isowarsa kenan dasu Jabeer ya tarota. tai ƙoƙarin
ƙwacewa jikinta na rawa zata sake danna kai cikin office ɗin idanunta na zubar
hawaye Hafiz yay saurin sake fusgota, cikin tsawa-tsawa yace, “Rose! Minene kikeyi
hakane?”. Wasu irin zafafan hawayene suka shiga rige-rigen sake gangaro mata saman
kumatu, ta tsare Hafiz da kallo, hannu na rawa ta nuna ƙofar office ɗin Jay, “Boss
fa rungume da yarinyar nan”. Cikin takaici Hafiz yace, “Idan ya rungumeta sai akai
me? Ba matarsa bace! matarsa ce ita halalinsa, ke kanki shedace akansa, inda Jay
yana harkar mata ke zai fara lalatawa ai” ya ƙare maganar da balla mata harara yaja
tsaki ya juya yabar wajen.
Da sauri Rose ta maida kallonta ga Jabeer da Aliyu. Tace, “Kunajinfa miyace, miyasa
Hafiz baya ƙaunata?”. Ɗan murmushi Jabeer yay yana girgiza kansa, “Hafiz ba
ƙaunarkine bayayi ba, gaskiya ya faɗa miki, Mami matar Jay ce yanzun”. Daɓar Rose
ta zauna ƙasa tana faɗin, “Jesus, shikenan na mutu Jabeer, yaushe akai musu
auren?”. Duƙawa Aliyu yay gabanta cikin taushin murya yace, “Baki mutuba Rose,
kisama ranki haƙuri dan ALLAH karki tada hankalinki kinji, ALLAH ya rubuta itace
matarsa, kema naki mijin nanan zuw.......” “Aliy daina faɗamin maganar banza kaji,
ni boss zai yaudara, dama tunda naga yarinyarnan na shige masa nasan zatai abinda
yafi haka, nasan asiri tai masa kawai”. Ƴar Dariya Jabeer yay shima ya duƙa
gabansu, “Rose na faɗa miki gaskiyar magana? Boss shike bin Mami ba ita ke binsa
ba, tunda muke da ita bata taɓa nuna wanima a cikinmu ya taɓa koda birgetaba, shi
kansa farautar soyayyarta yake amma sam taƙi bada ƙofar hakan, kullum ma nunawa
take ita batama taɓa fahimtarsa ba, itaɗin mace ce mai AJI!, shine babban maganin
asirinta akan zuciyar Boss, yakamata ki fahimci yana son mace mai suna mace, ma'ana
mai Ajiiii!!”. ya ƙare maganar cike da salon iskanci yana salute ɗinta, miƙewa yay
tare da mata nuni ta miƙe dan tayi sagafene tana kallonsa da fassara maganganunsa
sala-sala.
Sam Jay baiga Rose ba, Bily kanta data ganta halin data shiga yasa tama manta da
ganin nata, ruwa ya ɗakko ya bata, babu musu ta amsa, yanda tasha ruwan sosai har
mamaki ta bashi, ta miƙa masa kofin tana godiya, baice mata komaiba sai nuni da yay
mata data tashi takoma kan kujera.
Nima ina buƙatar hutawar, dan haka na tashi na koma saman kujerar na zauna tare da
lumshe idanuna.
Sosai nakeji a jikina kallona ake, ina buɗe idanu muka haɗa ido dashi, ɗauke kansa
yay tamkar baniɗin yake kallonba, nima na janye nawa a raina ina jinjina yanda ya
ƙware a iya kallon mutum.
Babu wanda ya sake shigowa office ɗin har aka kira sallar la'asar, shine ya fara
shiga ya ɗaura alwala sannan yace naje nayi nima, lokacin dana fito tsaye na gansa,
bance komaiba na nufi hanyar fita yana biye dani.
Daƙyar Aliyu ya lallaɓa rose suka bar ƙofar office ɗin Jay, kuka take rurus cin
ƙarfinta, a zuciyarta tana ayyana matakin gaggawa da zata ɗauka akan Bilkisu nan
bada jimawa ba, bazai yuwu tazo jiya-jiya ta samu abinda ita ta kashe shekaru masu
yawa tana bibiyaba, dolene kodai ita ta samu, kokima su rasa gaba ɗaya. Da wannan
ƙudirin tabar office yau.
Yau tare dashi mukabar office, a ƙasan raina cike nake da tuhumar ina Yah Qaseem ya
shiga? Sam bana ganinsa a office tunda na dawo, mike faruwa dashi ne? Inason
tambayar boss inajin tsoron buyaginsa. Munyi nisa a tafiya batare daya kalleniba
yace, “Jazuga bai mutuba”. Da wani irin matsanancin sauri na juyo na kallesa, harma
na manta dawa nake na kafesa da idanu ko ƙyaftawa banayi”. “Malama idanun nan
sunmin yawafa”. Kumbura fuska nai na ɗauke kaina jin abinda yace, sai kuma na kasa
haƙuri naɗan sake kallonsa na risinar da kaina, cikin zumuɗi nace, “Dan ALLAH da
gaske boss?”. yace, “Mun fara ƴar wasane dake?” kaina na girgiza masa dukda nasan
bani yake kalloba. Shiru bai sake cewa komaiba, har muka isa masarauta, dukda
inason jin ƙarin bayani haka na daure na danne a raina, idan taƙamarsa jan aji
gidan ya taras.
A cikin ran Jay wani irin haushine ke cinsa, mamaki da takaicin miskilancinta yake,
yayi shirune yaji kozata tambayesa cigaba labarin amma yanda yay shiru itama ta
tsuke baki, shikuma inhar ba ita tanema jin yanda akaiba bazai faɗa mataba. Babu
wanda ya sake yin magana tsakanina da shi har yasamu guri yay fakin gab da sashen
gimbiya, dan yanzu shi babu shamaki an bashi damar shigowa cikin masarauta a duk
sanda yaso. Yunƙurin buɗe motar nai ya riƙo hannuna. Daƙyar na iya danne abinda
nakeji na kallesa, ganin ni yake kallo sai nai ƙasa da kaina, sakarmin hannu yay
yana faɗin, “Saiki jira na gama tunda ba tauneki zanyi ba”. Nidai bance komaiba, ya
miƙa hannu sit ɗin baya ya ɗakko leda viva sabuwa. “ga wannan, duk yanda zakiyi
amfani dasu na rubuta miki, Karkiyi wasa Miemaa, dan ina buƙatar matata a kusa
dani” yay maganar ahankali yana kafeni da idanu, saurin sadda kaina nai dan naji
wata irin bahaguwar kunya ne. Jay dake kallonta yay wani lallausan murmushi da
cigaba da faɗin, “dolene ta hanyarki zan gano bakin zaren matsalarmu, hakan kuma
bazai yuwuba kai tsaye sai da taimakon UBANGIJI”. Kaina a ƙasa nace, “Insha ALLAHU
zanyi Sir”. “ALLAH ya tabbatar”. Ya faɗa batare da ya da ɗauke kansa daga gareni.
Nima saina fita a motar ɗauke da ledar da bag ɗina, ta sashensa na zagaya na sake
masa godiya sannan na shige, tuni an amshi kayan hannuna tun fitowata a motar.
Jay daya kafeta da kallo ta cikin mota yaɗan lumshe idanunsa yana sauke ajiyar
zuciya lokacin data shige. Shima fitowar yayi. Masallacin masarauta yay salla har
isha'i, kafin ya samu damar ganawa da gimbiya a tsaitsaye. Yamata bayanin abubuwa
da dama a gurguje, itama ta sanar masa ƴar firar da sukai da Bily da abinda ta
fahimta. Duk yanda taso yaci abinci ƙinci yay yauma yaymata sallama ya wuce.
__________________________
Tun daga wannan ranar gimbiya ta sake jan Bilkisu jikinta, riritata take tamkar uwa
da ƴa, gefe ɗaya tana koya mata dabarun rayuwar aure cikin hikima kamar yanda itama
Mommah tai mata gata, sannan a hankali take fahitar wasu abubuwa daga Bilkisu ta
cikin hira. Magungunan da Jay ya kawo mata Amintacciyar baiwar gambiya tsaye take
akan Bilkisu dan ganin tayisu kamar yanda ake buƙata, ga maganin sanyi shima da ake
bata acewar gimbiya shine matakin farko.
Kullum da safe driver zai kaita office da yamma idan an tashi Jawaad ya ɗakkota ya
maidota, dukda babu wata hirar arziƙi a ciki, yakuma daina raɓarta koda wasa, yanzu
sam basama haɗuwa sosai a station ɗin saboda baya zama aiki yaymasa yawa, su kansu
yana wajigasu da ayyukan sosai.
A haka aka shiga wata mai albarka na ramadhana, manya da ƙananun yara harma da
tsaffi kowa ya tashi da wannan ibada a baki cike da ɗoki da fatan kammalawa lafiya.
Yayinda Bilkisu ke kallon ikon ALLAH wajensu gambiya dangane da alkairin da ake
fita dashi domin talakawa. Abin sai ya birgeta, a cikin ranta tana fatan kwatantawa
taji idan zata iya watanara, sannan har yau da take nufar sati na biyu a masarautar
bata taɓa gamo da Sarki Sameer ba, Safah ta sanar mata yaje saudia hutawa shida
amaryarsa da suke kira Ammi, sai azumi yaje tsakkiya zai dawo sukuma su tafi Umarah
★★★★
Jay da muƙarrabansa sunyi busy matuƙa, ga aiki ga aikin sa kai gana hidimar bayin
ALLAH duk ya haɗama kansa, burinsa ya kammala abubuwa da yawa cikin watannan, baya
neman Bilkisu ne dan yana tausayinta sosai, ga azumi ga rana dan ruwa bai zaunaba
sosai, gani yay ta rame masa a kwanakinan sosai sai tai haske kuma.
Abin mamaki Rose kuma saita shiga ja baya dasu, har takai saida Jay yamata magana
da kasa, ranar kam dai yaga taɓara da iyayi, gashi yanaji da azuminsa. Shidai ya
lalaɓata kawai dan yana buƙatar nutsuwa baison hayaniya.
Tuni yasa ana bibiyar masa bayan Ɓaleru duk inda ya sanya ƙafa batare da shi ya
saniba, bayason kamasa a cikin watannan mai albarka shiyyasa yay tamkar ya manta da
al'amarinsa, ga jikin ɗan-fir'auna da har gidan su Shahudah suka ɗauka ya mutu na
nata sauƙi da warwarewa.
__________________________
Kwanci tashi babu wahala wajen UBANGIJI azumi yakai tsakkiya, a daren sha bakwai
sarki Sameer da Amaryarsa suka dawo, anyi murna da dawowar tasu sosai, dan ranar
kam kowa ya shaida hakan a masarautar gagara badau, ranar gimbiya da kanta taima
Takawa abincin buɗa baki a kicin ɗinta na sirri da babu mai shiga sai ita saiko
Amintacciyar baiwarta. Tunda ta tafi ɓangarensa su bily basu sake jin ɗuriyartaba
sai washe gari, sai a randa za'a ɗau azumi na sha takwas ne suka ganta, shima dan
tasaka a kira mata bily ne.
Cikin girmamawa na gaisheta kamar yanda na saba, fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa
min tare da kamo hannayena cikin nata. “Ɗiyata dama nasa a kiramin kene saboda zaku
wuce Umrah gobe idan ALLAH ya kaimu ke da su Amaturrahman, an kammala miki komai
insha ALLAH” Dama Boss ya sanarmin tun shekaranjiya, sai dai na nuna mata farin
cikina sosai akan hakan itama tamkar bansan da tafiyarba, nakuma mata godiya. Ta
cigaba da faɗin, “Naso ace tun farkon azumi kika tafi, sai dai mijinki ya sanarmin
hakan bazai yuwuba saboda aikinki, dan akwai wata auntyna matar yayan abokin Takawa
tanada makaranta ta musamman domin koyar da amare, ana gyaran jiki da komai a ciki,
koya girki da dukkan dabarun zaman aure, itama ƴar nan ƙasarmu ce, dalilin ƙaddara
ta shigo rayuwarmu, mun kaita domin neman magani sai yayan abokin Takawa yace shifa
yayi mata, wannan shine dalilin zamanta a can itama”. Fuskata ɗauke da murmushi
nace, “ALLAH sarki”. Itama murmushi tayi, “Yanzu dai yayi dukkan cuku-cukun daya
dace a wajen aikinku insha ALLAH keda nan sai saura kwana biyar tarewarki, inason
naga kin zama cikakkiyar mace mai amsa suna mace a fadar mijinta, mijinki babban
mutumne sannan yanada wasu sirrika dake kaɗai zaki fahimci kayanki anan gaba,
shiyyasa nakeso a gyaramin ke yanda ya kamata domin zukatan maƙiya su girgiza,
waɗanda suke ganin baki kaiba su fahimci kin musu zarrah ta har abada kinji”.
Hawayen dake ziraromin na share, bansan irin godiyar da zanma wannan baiwaba a
rayuwata, itaɗin ta musamman ce a cikin jerin abubuwa masu muhimmanci da suka shigo
rayuwata, ALLAH ya biyata da aljannarsa.
Washe garima naje wajen aiki, sai dai yau bashi ya maidoni ba sawa yay sabon
direbansa ya maidoni, gobe idan ALLAH ya kaimu kuma bazanje aikiba, dan ƙarfe huɗu
zamu wuce, share hawayen dake zubomin nake akan abinda ya faru tsakanina dashi
yanzu a office ɗinsa. Na roƙesane akan zanje gidan Dad nai masa sallama, dama tun
farkon azuminan naketa masa magiyar ya kaini na gaishesa, bai taɓa kulaniba sai yau
da yanema marina a office, yajamin dogon gargaɗi akan inhar na sake masa maganar
Dad ALLAH sai ya fasan baki. Sake share hawayen nai zuciyata namin zafi da
takaucinsa, ni bansan mi Dad yaymasaba haka da zafi shi da ahalinsa, inason ganin
koda mutum ɗayane a cikinsu amma abin ya gagara, sam yanzu bana ganin Yah Qaseem,
narasa ina ya shiga baya zuwa Office, mike damunsa? Minene matsalarsa? Haka kawai
bazai bar zuwa office ba ai?. Zafin boss yayi yawa, nikuma har zuwa yanzun ban taɓa
jin sonsa a rainaba, nasan dai zan iya haƙurin zaman aure dashi amma badan inajinsa
a raina da kalmar soyayya ba, bansan miyasa hakanba, har zuwa yanzu Yah Qaseem ne
kaɗai a zuciyata, shi nakeso, shi na fara so, sai dai shikuma banajin sha'awar zama
dashi matsayin miji, bansan miyasa hakanba shima. Ya ALLAH ka kawomin ɗauki bisa
ruɗaɗɗen tunanina daya banbanta dana sauran mutane a yanzu.
Har muka bar ƙasar bana cikin walwala sam, sai wata irin matsananciyar damuwa da na
tsinci zuciyata a ciki, wannan dalilin yasa har jirginma ya tashi ban tuna shine
hawana na farkoba, Safah na lafe a jikina tana barci har muka sauka. mun sami tarba
ta musamman daga wasu manyan mutane da bansan matsayinsu ba, sai dai ina tunanin
waɗanda Gimbiya taban taƙaitaccen labarinsu ne ranar, sai dai wannan nafi ƙyautata
zaton abokin takawane da iyalansa ba waccan mai makarantar bace da naji nafi ɗokin
gani. Ƴan uwa abu mafi ɗaure kaina shine, maimakon najini cikin farin ciki da zuwa
ƙasa mai tsarki a karo na farko a rayuwata sai saɓanin hakan ya biyo baya, kallonsu
nike kawai tamkar wata sakarai, ƙirjina na wani irin zafi, sai can ƙasan zuciyata
kuma nakejin wani irin sanyi dake kawomin sassauci a cikin ƙirjina kaɗan-kaɗan.
Darene sosai, dan haka makwanci kawai aka bamu da abinci, nikam bammaciba na
kwanta.
______________________________
Yau tunda ya tashi aiki wanka kawai yaje yay a gida ya kimtsa, sabon drivernsa mai
suna Sadiq ya ɗaukesa sai gidan Alhaji Babba dan acan yake buɗa baki yanzun kullum,
wataran kuma gidan Ummah babba, kokuma gidan Ummah ƙarama idan ta ishesa da ƙorafi.
Haka kawai yau yakejin tamkar wani abu dake nesa dashi yana tunkarosa, minene? A
ina yake? Itace amsar dakanzo masa akai-akai cikin shauƙinsa.
Shi dai Alhaji babba kallonsa kawai yake amma baice komaiba, sai da suka dawo salla
sukai zaman buɗa baki sannan, ya kai dubansa ga Jay da keta juya cokali cikin kofin
kuni yana ɗan murmushi. “Wai nikam gwauron nan yau miya saka farin ciki haka?”.
Kallonsa Jay yay fuskarsa ɗauke da murmushin har yanzun, yace, “Babu komai Baba,
kawai dai”. Murmushi shima Alhaji baban yayi, “Kawai dai haka ka tsinci kanka kaima
ko?”. Kai Jay ya jinjina masa yana lumshe ido. Alhaji babba yace, “Nima haka na
tashi da farin ciki, sai nakeji tamkar wani abu dana daɗe da rasawa zai dawo
gareni, sai nakeji kamar wani abuna mai muhimmanci ya haɗu da abuna mai muhimmanci,
sai nakeji kamar wani abun da na daɗe ina neman amsarsane lokacin sanin amsar yayi,
a daren jiya nayi mafarkin ƴaƴana guda biyu cikin farin ciki, tabbas Jawaad inaji a
raina wani abu mai daraja da haske na matsowa zuwa garemu”. Jawaad sauraren Alhaji
babba kawai yake yana murmushi irin wanda ya kasance mai tsada a garesa, ya ɗora
kansa a kafaɗar kakansa yana sake ƙawata murmushinsa, “Ya ALLAH ya tabbatar da
wannan hasashe naka ya zama alkairi kakana”. Shafa kansa Alhaji babba yay yana
murmushi da faɗin, “Amin ya rabbi jikallena, amma yakama ka dawo nan kwanaki goman
nan na ƙarshe muyisu tare cikin ƙololuwar ibada, ka ajiye duk wani aiki gefe”. Jay
ya tashi zaune sosai yana kallon kakan nasa, yace, “Nima nayi wannan tunanin, sai
dai banason takura maka da yawa”. Ranƙwashi Alhaji babba ya kai masa bisa kai, Jay
yay saurin kaucewa yana dariya da haɗe hannayensa waje guda alamar na tuba.
Bayan sun dawo daga salla suka iske Ummah babba da ƙarama sunzo, dama sunce yau
zasuzo. Jay ya zauna tsakkiyarsu yana dariya da faɗin, “Saini ɗan gatan ALLAH,
Ummahs ɗina duka tare dani”. Atare sukai dariya da riƙe hannayensa, Ummah babba
tace, “Ja'iri kamar ya wani damu damu?”. Karyar da kai Jay yayi ya ɗora saman
kafaɗarta, murya a sanyaye yace, “Idan ban damu da kuba dawa zan damu Ummah?, kuɗin
duniyatace, sannan haskena, aikine kawai ke hanani rawar gaban hantsi”. Guntuwar
dariya tayi da shafa kansa, ta sumbaci hannunsa tana mai saka masa albarka.
Kasancewar basu da ishashen lokaci suka fara tattaunawa akan maganar lefe da dama
shine ya kawosu. Da farko Jawaad yace su barsa zaiyi, amma sukace sam bazai yuwuba,
na farkoma dan an nuna musu fin ƙarfine Uncles ɗinsa sukace zasuyi, to wannan kam
suma sune zasuyi insha ALLAH.
Jawaad yay shiru yana murmushi dajin ƙaunarsu mai narkar da zuciya na ratsasa,
zamansa ya gyara a kujerar daya koma shi kaɗai yana kallonsu, “Nagode sosai
iyayena, kun sharemin hawayen maraici tuni, bani da abin biyanku sai dai naita muku
addu'oin gamawa da rauwa lafiya, idan na ganku saina manta bani da Uwa, idan kuka
kalleni sai nake ganin Mah-mah har yanzu tana tare dani, ida har tabar duniya ina
roƙon UBANGIJI yasa ana nuna mata dukkan alkairanku ga gudan jininta, idan tana
duniya ina fatan ganinta na bata labarin alkairanku ga gudan jininta, ku......” “Ya
isa haka kaji Muhammadu, insha ALLAH inaji a jikina BILKEESU tana raye, insha ALLAH
kafin nabar duniya saina ganta” Alhaji babba yay maganar yana share hawayen da suka
ɗan zubo masa. Ummah da Ummah ƙarama ma kuka suke, Jay gwanin dakiya babu hawayen
zahiri saina zuci kawai.

________________________________
Kasancewar nazo babu tsarki sai yau nake fatan samu lokacin da zamuyi sahur saina
duba, naji wani nishaɗi ganin ya ɗauke harda tsallena a bayi, wanka nayo da brush
na fito, cikin tsokana Meenal tace, “Gandiya halan yau kin musulunta ne? Naga wanka
da asubar fari”. Murmushi nai mata ina zama domin busar da kaina da hand drayer ɗin
dana gani saman mirror ɗakin, nace, “Oh da kafira kike kallona?”. Dariya sukayi ita
da Amaturrahman dake ƙoƙarin shiga yin brush itama, tace, “Ai kima godema ALLAH ke
kina zuwa yana ɗaukewa, ita tana shigowa yana zuwa”. Cikin ɗan zaro idanu na kalli
Meenal ɗin, sai kuma na langaɓe kai nace, “Kai harfa kin bani tausayi babie”. Filo
ta ɗauka ta jehomin ɗaya ta jefama Amaturrahman. Da gudu Amaturrahman ta shige bayi
tana dariya, nikuma na cafe wanda ta tillomin. “ALLAH karkiji wasa meenal tausayi
kika bani” nai maganar da ɗan mata gwalo. Ƙwafa tayi da faɗin, “Wlhy duk zan rama,
ke saurama ƙiris na raman ai, zaki gane kurankine”. Murmushi nai mata bance komaiba
na cigaba da busar da kaina.
Bayan munyi sahur salla mukai muka sake kwanciya barci, mune bamu tashiba sai sha
ɗaya, shima tadamu akazo akayi. shiri mukai a gaggauce na tafiya massallaci, nidai
Kasa daurewa nai na tambayi Amaturrahman Auntyn da Ummu tace tanada makaranta
gidansu kuma na kusa da inda zamu sauka?.
“Lah Bily ai yanzu bazakiga Umm-Anum ba, sun shiga ittifaqi, kinga gidansu nan, duk
Ramdhan idan mukazo bama ganinsu muma sai ranar sallah”. Da mamaki nace, “Basu da
yara?”. Tace, “Sunada yara biyu mana, mace da namiji, namijin ya girmemu da kusan
shekara biyar, sunansa Anwar, sai macen Anum, tare suke shiga ittifaqi. Tunkan na
gansu naji sun matuƙar burgeni har ina zumuɗin ganin nasu mai ban mamaki, dan tunda
Ummu taban labarin matar a taƙaice saita kasa barin zuciyata. Yanda na iso da
ƙuncin zuciya a yanzu sai ba hakaba, fes nakejin raina cike da nishaɗi da farin
ciki da shauƙin ganina a ƙasa mai tsarki, santin da banyi a daren jiyaba sai gashi
a yau inayinsa, dan har muka isa massallaci bakina bai hutaba, Safah kam bata
gajiya damin bayanin komai dalla-dalla. Lokacin dana ganni gaban ɗakin ka'aba sai
kawai nakejina tamkar wata sabuwar Bilkisu ce tsaye ba wadda tazo da ƙunci ba,
hawaye masu ɗumi na ziraromin bisa kumatu, abinda ban taɓa tunaniba koda a mafarki,
wani nauyin zuciya da ƙunci da damuwar da natsinci kaina a gaba ɗaya cikin
shekarunan sai naji tamkar an yayesu an zubar tare da ruwan wankan dana samu tsarki
ɗazun da asuba. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai ni'ima.
Muna zaune a wajen mutanen kirki, larabawan usul masu ƙyawawan zuciyoyi, bamu rasa
komaiba, ibada muke babu wasa dansu Amaturrahman sun horu sosai, sannan sunada
ilimin addini suna kuma aiki dashi, Umm-Aban koda yaushe cikin kulawa take damu
sosai, nasamu sauyi iri-iri da haske a rayuwata a cikin kwanakinan goma da mukai na
Umrah, babu abinda mukeyi banda ibada, duk wata shiririta mun ajiyeta gefe, a
kullum safiya bayan sahur muna waya da gimbiya, hakama su Ummie duk saina kirasu,
Boss kam ko filashin bai taɓa haɗamu ba, sannan dukkan numbers ɗin ƴan gidanmu bana
ganinsu a wayata yanzun, bansan yaya akai hakan ta kasanceba tunda nidai ban
gogeba.
Yau take salla, sosai massalacin ke cike, bayan an idar da sallah sai na dingajin
juwa, duk yanda naso dannewa hakan ya gagara, bandai sanarma su Amaturrahman ba dan
karsu tada hankalinsu, miƙewa nai da nufin na ɗan samu waje inda babu yawan mutane
na huta ko zanji nutsuwa sai kawai hajijiya ta kwasheni. Sama-sama na jiyo wata
nutsatstsiyar muryar ta ambaci “Yah ALLAH”. Sai jina nai a jikinta. Cikin ɗan
larabcin da nakeji kaɗan-kaɗan na tsinci tanama wani wanda bansan ko waneneba
magana akan ya bata ruwan zam-zam dake hannunsa. Gabana yay wata masifar faɗuwa jin
muryar data amsa mata, murya irin wadda wajan mutum ɗaya na santa, muryar dake
sakani bugun zuciya, muryar dake saka jinina gudu cikin jijiyoyi, da ƙyar nai
ƙoƙarin ɗaga idanuna dake neman rufewa na sauke a kansa dai-dai ya miƙo ƙaramar
goran ruwa wa matar da har yanzu nike a jikinta.............✍
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[12/25/2020, 10:03 AM] HASNA ✍🏻
: Bilyn Abdull :
Page 36

.................Tabbas muryar iri ɗayace, kamanin ma ɗayane, sai dai wannan farine
tas, shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na
sake lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar
goran ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a
gaibun mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi,
matashiyar budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta
duƙa gabana tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai
kuka, magana take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin
baki, na kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta
daban. Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai
sa'a itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake
buɗewa a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani
abu akan fuskata.
A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune
tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya
kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri
ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma
juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon
fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci
tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina.
Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar,
babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar
bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar
wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda
saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har
yanzun........
Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa
zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta,
“Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a
maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai
jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”. Cikin sauke
ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya
kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da
alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba
rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka
iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin
bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa
dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike
ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu
kamar bansan sunaiba.

A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin
ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai,
munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo
gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema
makwancinsa.
Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun
alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin
bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata
kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo,
dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake

zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin,
“Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar
dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.

★★★★★★★

Washe gari tunda safe saiga kira daga Ummu, bayan duk mun gaisa da ita
tace a bani wayar. Daga can tace, “Yauwa ɗiyata ki shirya komai naki danke yau
zaki koma wajen Aunty da zama, tun jiya da daddare ma taso shigowa ta ɗaukeki, ki
nutsu ki kwantarmin da hankalinki ki fahimci dukkan abinda akeson ki fahimta kinji,
kinga lokaci ya ƙure sosai, inason kidawo ƙasarnan da cikakken sunanki BILKEESU MAI
GADON ZINARI ba Bilkisu kawai ba kinji”. Cike da jin nauyinta nace, “Insha ALLAHU
Ummu zanyi duk yanda kikeso”. “Yauwa ƴar albarka ALLAH ya bada sa'a kinji, jibi su
Amaturrahman zasu taho su saboda makaranta, ranar litinin su Safah zasu koma hutu”.
Kamar zanyi kuka nace, “Wayyo Ummu ni kaɗai za'a bari anan kenan?”. Murmushi tayi
har ina jiyo sautinsa, tace, “Ohni Munaya, anya kuwa randa zan miƙaki gidan miji
baza'a sha daruba? Karki damu itama Anum ɗinta zakuyi sa'anni, nasan zata ɗauke
miki kewarsu, kuma kedama zaki maida hankali ga abinda za'ai miki ai baƙya
buƙatarsu Amaturrahman kusa dake, koma sun zauna na ganin juna zakuyiba, inason
suzo domin shirye-shiye, ki basu duka numbers ɗin ƙawayenki karki manta”. Godiya
nai mata mukai sallama.

Kamar yanda ta umarceni haka na shirya dukkan abinda yake nawa, duk ji
nake babu daɗi, banso ace batare zamu koma dasu Safah ba, to amma yaya zanyi tunda
haka Ummu ta tsara.
Atare muka fito cikin shiga ta kamala, Marwah jaye da ɗan ƙaramin
akwatina. Gida baifi huɗu bane a tsakaninsu, dan haka tafiyar mintuna ƙalilan muka
iso gidan, Aunty Mahfuzah tai knocking haɗaɗɗiyar ƙofar falon, babu jimawa akazo
aka buɗe mana, wani irin tsammm naji jikina ya bada saboda cin karo da fuskar
budurwar jiya. Ta rungume Aunty Mahfuzah tana magana cikin harshen larabci, kafin
ta saketa ta rungume Amaturrahman da Meenal cikin tsalle irin na nayi kewarku, sai
dariya suke da faɗin yanda sukai missing ɗin junansu. Ta sake rungume su Safah suma
kafin ta juyi gareni, idanu taɗan waro tana nunani da faɗin, “Lah kece?” murmushi
nai mata kawai dan nikaɗai nasan mi nakeji, rungumeni tayi nima, sannan muka ƙarasa
falon daya gama jin kayan more rayuwa, ga sanyin AC da wani ƙamshi mai kashe
zuciya, tuni ɗan gumin da mukai harya tsane, labarin haɗuwarmu ta jiya taketa
bamasu Amaturrahman saboda tambayar da sukai na ina muka san juna?.
Fitowar matar gidan ya sakasu Safah miƙewa gaba ɗayansu harsu Amaturrahman
sukai kanta suka rungume, ba kowa bace face matar jiya data taimakeni, bayan sun
zauna ta gaisa da aunty Mahfuzah cikin salon gaisuwar larabawa, nima gaidata nai
kamar yanda na iya a nawa al'adar da tarbiyyar, kallon mamaki tai min dan da'alama
sai yanzune ta lura dani ma, da turanci take tambayata wai dama tare muke dasu
Safah?. Amaturrahman ce ta bata amsar da take buƙata harma da ƙara mata wadda bata
tambayaba. Murmushi taita saki da ƙaremin kallon da kowa yaketa mamakinsa, tana ta
maimaita sunana tamkar karatu a bakinta, bansaniba daɗi yaymatane kokuwa yaya oho,
dan nasan suna Bilkisu dai sunane sananne da zaka iya jinsa a kowacce duniyar
musulmai balle tace yaune ta fara jinsa sabo.
Ranar dai anan muka yini, har yamma su Amaturrahman basu koma can
gidanba, danni dai an tabbatarmin da nazo kenan bazan koma canba, acewartama a
daren zata kaini can makarantar da Ummu ta faɗamin. Banga saurayin nanba sai yamma
lis ya shigo sanye da farar jallabiya sol da mayafi irin wanda larabawa kansa akai
su saka baƙin abunnan a sama tamkar gammo, fara'ar da bangansa da itaba jiya sai
gata yau a fuskarsa yanamasu Amaturrahman magana da kulawa kamar yanda suma suke
masa, shima dai sai da ya nuna mamakin sake ganin nawa anan, su Amaturrahman da
basa hutawa sukai masa bayani dai-dai fahimtarsa, shima dai murmushin yayta saki
kafin ya nufi ɗakinsa wai zaiyi wanka.

Ban tashi shiga damuwaba sai da su Amaturrahman zasu koma gidan aunty Mahfuzah
su barni anan, hakan kuma na

nufin munyi sallama kenan dasu, sai naji ƙwalla ta cikamin idanu, sabo kenan turken
wawa. Suma kansu na lura basuso hakanba, amma sai suketa dariyar ƙaramin ƙwarin
gwiwa da tsokana. Haka mukai musu rakkiya har gidan sannan muka sake dawowa ni da
Anwar da Anum mai shegen surutu, yanayin rawan kanta sai yakemin kamanceceniya da
Nabeelah, gata da saurin magana saina nutsu sosai nake fahimtar magana idan tayi,
dama dai maganar tamu sai da turanci. A falo muka sake zama, cikin son fidda abinda
kecin raina na tambayi Anum da Anuwar da naga shima ya saki jiki dani yanzu kosun
taɓa zuwa ƙasarmu?. Anuwar ne kaɗai yace ya taɓa zuwa shima sau ɗaya tare dasu
Abdur-rahman, sunzo hajji wata shekara zasu koma ya bisu sukaje tare, satinsa biyu
acan ya dawo daga nan bai sake komawaba har yanzun, amma yanada burin sake zuwa
saboda ƙasar tai masa daɗi sosai.
Murmushin jin daɗi nayi sai dai a ƙasan raina ina mamakin to Mamansu fa? Ita
bata taɓa kaisu wajen nata danginba kenan kokuwa?, da ƙyar na ture tunanin a raina
muka cigaba da hira har sanda Umm-Anum ta fito cikin shiri, sanin inda zamuje ya
saka duk muka miƙe, tana gaba muna biye da ita har inda Anuwar ya ajiye motar da
zamu fita. Ni da ita baya muka shiga, Anuwar da Anum na gaba, dukda darene garin
zirga-zirga aketayi tamkar rana, gashi ko'ina ƙwanyar da wuta abin birgewa.
Mun iso wani haɗaɗɗen gini babba da nake ƙyautata zaton makarantarce, Anuwar
yay fakin duk muka fito, jin kamar ana kallona yasa na ɗago, Anuwar na kama
idanunsa tsaye a kaina ƙyam, saida gabana ya faɗin dan wlhy sai naga tamkar Boss,
murmushi yaymin. ɗauke kaina nai batare dana maida masa murtani ba, Umm-Anum dana
fahimci tana kallonmu ta hararesa da kama hannuna mukai gaba. Ina jiyo dariyarsa
shi da Anum, sai dai banajin mi suke faɗa cikin harshen larabci. Gaskiya ina sake
jinjina wannan tsananin kama a cikin raina, kai gaskiya inason sanin wani abu
dangane da mutanen nan, wannan kamar ta wuce kama kawai, anya kuwa babu wata alaƙa
tsakanin...........
Shigarmu wajenne ya katsemin tunanina, Bansan yanda zan fasalta muku
haɗuwar wannan makarantaba da tsarinta, na bama kowa dama ya ƙiyasta a cikin ransa
kawai, dan idan nace zan lissafo komai shafin yau da gobe duk anan zamu ƙare. Tuni
na zama baƙauya wajen kallon abubuwan birgewa, to lallai da ace munada irin waɗanan
makarantun da mace-macen aure ya ragu muma a yankunanmu, da ansamu sauƙin rikin
aurarraki a gidajenmu. Sashe na musamman aka buɗe mana mai madaidaicin falo guda da
ɗakuna biyu a ciki.
Fuskar Umm-Anum ɗauke da murmushi ta kalleni, “Ɗiyata anan zaki zauna, dan da
kaina zan miki aikinnan saboda ƙurewar lokaci, ga mamanki ɗinan sotake ta ganki
tamkar zinare”. Murmushi nai mata kaina a ƙasa dan haka kawai nakejin nauyinta, nai
mata godiya tare da addu'ar fatan alkairi. Batace komaiba sai murmushinta dake
kasheni taketa sakarmin.
Ɗaya daga cikin ɗakunan muka shiga, kayayyakine ajiye da ban fahimci
kona mineneba, ta umarceni dana cire kayana gaba ɗaya na shiga wani madaidaicin
kwami dake cike da ruwa da bazamu kirashi normal ruwa ba, ita kuma ta fita.
Dukkanin yanda ta umarceni nayi haka nayi babu musu, inayi ina ɗan waige-waige
tamkar mai tsoron wani ya shigo, saida na cire komaina kafin na fara saka ƙafa
cikin kwamin, ajiyar zuciya na sauke a hankali saboda ɗan ɗumi-ɗumin ruwan mai
warware gajiyar jiki, na ida saka ɗayar ƙafar sannan na shige gaba ɗayana,
sihirtaccen ƙamshin da ruwan keyine ya sakani lumshe idanu ina karanto addu'ar
godiya ga ALLAH da ni'imominsa masu yalwata ta fuskoki da dama ga ɗan adam. Sai da
nai kusan mintuna uku da zama sannan ta shigo da sallama, ta canja kayanta da wata
doguwar riga mai kama da leda, hannayenta sanye da safar hannu ta leda itama,
murmushi taimin ta tako inda nake. Ɗan kwalina daban cireba ta zame daga kaina, ta
warware gashina da Alhmdllh yanzu ya cika sosai kuma yanada tsayi gwargwado saboda
kulawar da naita bashi bisa koyarwar su Ummie tun muna boarding, wani ɗumi mai daɗi
naji ya ratsa kan nawa, hakan yasani kallon madubin dake gabana da nake iya hango
kaina da ita kanta.

Tace, “A cikin ruwannan zaki kwana, babu abinda zai sameki insha ALLAH
karkiji tsoro, ruwane mai ɗauke da sirrika kala-kala da duk macen da aka gyara dasu
dolene mijinta yasan ta isa mace, sirrikane na ƙamshi masu daraja a jikin ƴa mace,
ƙa'idar makarantarmu watanni ukune domin mace ta samu damar koyon abubuwa masu
yawa, ba sirrin gyaran jiki bane kawai mace tafi buƙata a rayuwar aure ɗiyata,
zakiga wata macen komai ta iya ta kuma ƙware, amma idan batasan yanda zataima miji
maganaba kawai sai ya rusa mata komai, dan wani namijin shi abinda ke ƙololuwar
birgesa ga mace shine iya magana, wani kuma a kallo kawai zaki gama dashi, wani
tafiya, wani girki, wani ƙamshi, wani shagwaɓa, wani kwalliya, wani kwanciya. Karki
sakama ranki cewa tarayya da miji a gado shine kawai farin cikin aure ko shikaɗaine
auren, hakan kuskurene, wani namijin ƙanƙanin abun da kika raina shike sakashi
farin ciki. Karkiyi tunanin gyara kanki yana nufin kin mallaki namiji ya zama naki
ke kaɗaine, macen data isa mace bata shakkar zama da kishiya ɗiyata, dan wani
lokacin zama da kishiya nasake bayyana darajar macene a wajen mijinta. Karkuma kiyi
tunanin babu wata mace data isa raɓar mijinki dan yana sonki ko kin iya komai, wani
namijin badan baya sonki yake miki kishiyaba ko yake budurwa, a'a halayyar san mace
fiye da ɗaya a jinin maza yake, ko bazasu ƙara aureba saisun kalla. kizama mai
gyara aurenki ta kowanne ɓangare, idan nace kowane ɓangare ina nufin kowanne fanni
hatta da ƴan uwansa da duk abinda ya shafesa. Inason ki cire komai a cikin ranki ki
nutsu ki bani dukkanin hankalinki a kwanakinan goma sha biyu da zamuyi tare, sonake
komai na cikinsa ya zama tamkar rubutu bisa dutse a cikin ƙwaƙwalwarki, ki ɗaukeni
tamkar mahaifiyarki, kuma ƙawarki aminiya wadda zaki iya magana kowacce iri da ita
batare da kinji kunya ba, inhar kika riƙe duk abinda zaki koya a kwanakinan ina mai
tabbatar miki bazaki taɓa goguwa a zuciyat mijinki ba koda zai auri mata uku ku
zama huɗu bayan ke”.
Idona a risine na ɗaga mata kai alamar to, inajiyo sautun murmushinta
itama. Abu ta fara shafamin a fuska tana cigaba da min magana cikin nutsuwa, sosai
kunya ta lulluɓeni, dan abubuwane masu matuƙar nauyi a gareni take faɗa a buɗe, ta
haɗe fuska a yanzu babu wasa tattare da ita ko kaɗan. Saida ta gama tsaf sannan ta
fita suka sake dawowa da wata mata. Matar ta nunamin da faɗin, “zata zauna dake
anan, ni zan koma gida sai da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”. Kaina na jinjina
mata dan ta hanani magana tunda ta shafamin abin fuskarnan.

Duk yanda zan baku labarin abinda ya gudana a kwanakinan da wahala ku


iya fahimtata, abubuwan dana koya kam ba'a magana, sam Umm-Anum bata wasa dani idan
akazo ɓangaren abinda zan iya jin kunyarta balle naga fuskar yin sakaci da abinda
ake koyamin, tsaye take kaina ɗari bisa ɗari, komai buɗemin shi take babu hijjabi,
aduk lokacin da takemin bayani aka abinda yafi ƙarfin kaina tamke fuska take tamau
babu wasa, kai jama'a hatta da salon tafiya ba'a barniba sai da aka koyan, komai a
tsare yake. Matar da take bari ta kwana dani kasa haƙuri tayi ranar dai take
tambayata wai kodai ni ƴar uwar Umm-Anum ce? Dan ita yanda take ganin tanamin ya
ninka yanda takema ɗalibanta fiye da zato. An kawoni ɗaki na musamman, sannan komai
ba'a sakani cikin ɗalibai ni kaɗai ake koyamashi a nutse, daɗin daɗawa da kanta
take min komai bata yadda kowa yayminba sai abubuwan da ba'a rasaba, dan takance
kowa a rayuwa da irin basirar da ALLAH yay masa, abinda suma sauran malaman
makarantar suke koyamin zai amfanar dani ta fannoni da dama. Murmushi nayi nidai
bance komaiba, dan nikaɗai nasan mi nakeji game da matar nan, ita kanta lokuta da
dama nakan kamata ta shagala da kallona, kallo maiban mamaki, kallo irin na shagala
da zurfi ason tunano wani abu, idan tai irin wannan zurfin kuma zakaga daga ƙarshe
ta dafe kanta tamkar zata fita cikin hayyacinta. Akwai randa naga kallon har yaso
yimin yawa, sannan ni kaina yanda takemin ɗin nasan ba kamar yanda takema kowa
baneba, tana sakin jiki dani fiye da hasashen mai hasashe. Akwai randa tazo tana
koyamin

girki sai muke ɗan hira kaɗan-kaɗan, cikin dabara nake tambayarta ko zasuje ƙasarmu
nan kusa?. Shiru tai bata bani amsaba, na kasa daurewa dai na sake mata tambayar
cike da ladabi. Yanda ta juyo ta kalleni fuska a haɗe saida naso firgita. Kaina na
duƙar ƙasa ina faɗin, “Kiyi haƙuri dan ALLAH Ummu, bansan tambayar zata ɓata ranki
ba”. Sautin murmushinta na jiyo, hakan yasa na ɗan ɗago na kalleta, ta ajiye
cokalin hannunta tazo ta kama hannayena, murya a sanyaye tace, “Ɗiyata ba laifi
kikayiminba, ƙasar takuma ni ban taɓa zuwantaba ai, duk amintakar dakika gani
tsakanina da ƙanwata Gimbiya Munaya ban taɓa ziyartarta ba, sai dai ita idan tazo
nan mu haɗu, duk lokacin danai yunƙurin zuwa nakan tsinci kainane a wani mummunan
hali da baida fassara”. Tana gama faɗa ta saki hannuna ta juyamin baya, aikin da
mukeyi ta cigaba dayi batare da ta sake min maganarba.
Ajiyar zuciya na ɗan sauke hawaye na ziraromin, haka kawai yanda tayi maganar
sai naji abun daban, to amma ai Ummu ta sanarmin itaɗin ƴar ƙasarmu ce, sanadin
neman magani ya kawota nan hartai aure, itakuma gashi yanzun tace bama ta taɓa zuwa
canba, anya kuwa babu wani sirrin dake ɓoye?.......
Ajiyar zuciya na sauke da saurin kallonta jin ta taɓanu, tace, “Kinama
fahimtar abinda nakeyi kuwa?”. Da sauri na ɗaga mata kai alamar eh na tattara
hankalina gareta baki ɗaya.

____________________________

A ɓangaren Jawaad ma dai shirye-shirye sun kankama, an gama gyaran gida


tsaf, ya canja kamanni gaba ɗaya tamkar bashiba, amarya kawai yake jira ta shigo
cikinsa. Gaba ɗaya a tsakaninan a busy yake matuƙa, ga aiki ga shirye-shiryen biki
dasu Jabeer ketayi naban mamaki, dan gayya suke ta gaske da gayya tamkar wannan
shine auren farko da Jawaad ɗin zaiyi. Shidai ya zuba musu idone kawai yana kallon
ikon ALLAH, dan dayay magana ca sukai babu ruwansa, kawai dai yama shirya dan bai
isa cewa bazaije wajen abinda suke shiryawanba ehe. Bai sake musu maganarba kuwa ya
cigaba da nasa harkokin, maganar kayan da za'a saka a gidan kuwa gimbiya Munaya
tace Takawa yace zaiyi komai, kayan kicin kuwa itace zatayi. Da yay mata maganar
lefe tace masa ya dakata, zasu nema Dady suyi magana, sai ana saura kwana biyu
tarewar za'a kaisu can gidan Dad ɗin dan sune sukafi cancanta da amsar lefen,
koyayane zasu bashi matsayinsa na uba kodan ɗawainiyar da yay da Bilkisun. Jawaad
baice komaiba shi dai sai ALLAH ya kaimu.

A yau tunda safe Su Amaturrahman suka shirya yima Mami (Munubiya) rakkiya
gidan kamar yanda Gimbiya da Takawa suka buƙata, zataje su haɗu da kamfanin da zasu
shirya gidan. bayan sun duba saisu zaɓa mata kalar data dace a tsara komai yanda ya
dace..............✍

Bara dai na baku hakanan, inata ƙoƙarin typing ɗin bayan tafiyar baƙi amma kiraye-
kirayen waya ya hanani nutsuwar yi da yawa, takaima harna daina ɗaga wayoyin mutane
wlhy🤦🏻😑😓.Bilyn Abdull 📚:
Page 36

.................Tabbas muryar iri ɗayace, kamanin ma ɗayane, sai dai wannan farine
tas, shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na
sake lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar
goran ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a
gaibun mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi,
matashiyar budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta
duƙa gabana tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai
kuka, magana take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin
baki, na kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta
daban. Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai
sa'a itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake
buɗewa a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani
abu akan fuskata.
A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune
tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya
kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri
ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma
juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon
fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci
tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina.
Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar,
babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar
bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar
wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda
saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har
yanzun........
Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa
zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta,
“Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a
maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai
jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”. Cikin sauke
ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya
kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da
alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba
rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka
iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin
bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa
dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike
ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu
kamar bansan sunaiba.
A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin
ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai,
munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo
gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema
makwancinsa.
Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun
alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin
bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata
kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo,
dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake

zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin,
“Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar
dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.

★★★★★★★

Washe gari tunda safe saiga kira daga Ummu, bayan duk mun gaisa da ita
tace a bani wayar. Daga can tace, “Yauwa ɗiyata ki shirya komai naki danke yau
zaki koma wajen Aunty da zama, tun jiya da daddare ma taso shigowa ta ɗaukeki, ki
nutsu ki kwantarmin da hankalinki ki fahimci dukkan abinda akeson ki fahimta kinji,
kinga lokaci ya ƙure sosai, inason kidawo ƙasarnan da cikakken sunanki BILKEESU MAI
GADON ZINARI ba Bilkisu kawai ba kinji”. Cike da jin nauyinta nace, “Insha ALLAHU
Ummu zanyi duk yanda kikeso”. “Yauwa ƴar albarka ALLAH ya bada sa'a kinji, jibi su
Amaturrahman zasu taho su saboda makaranta, ranar litinin su Safah zasu koma hutu”.
Kamar zanyi kuka nace, “Wayyo Ummu ni kaɗai za'a bari anan kenan?”. Murmushi tayi
har ina jiyo sautinsa, tace, “Ohni Munaya, anya kuwa randa zan miƙaki gidan miji
baza'a sha daruba? Karki damu itama Anum ɗinta zakuyi sa'anni, nasan zata ɗauke
miki kewarsu, kuma kedama zaki maida hankali ga abinda za'ai miki ai baƙya
buƙatarsu Amaturrahman kusa dake, koma sun zauna na ganin juna zakuyiba, inason
suzo domin shirye-shiye, ki basu duka numbers ɗin ƙawayenki karki manta”. Godiya
nai mata mukai sallama.

Kamar yanda ta umarceni haka na shirya dukkan abinda yake nawa, duk ji
nake babu daɗi, banso ace batare zamu koma dasu Safah ba, to amma yaya zanyi tunda
haka Ummu ta tsara.
Atare muka fito cikin shiga ta kamala, Marwah jaye da ɗan ƙaramin
akwatina. Gida baifi huɗu bane a tsakaninsu, dan haka tafiyar mintuna ƙalilan muka
iso gidan, Aunty Mahfuzah tai knocking haɗaɗɗiyar ƙofar falon, babu jimawa akazo
aka buɗe mana, wani irin tsammm naji jikina ya bada saboda cin karo da fuskar
budurwar jiya. Ta rungume Aunty Mahfuzah tana magana cikin harshen larabci, kafin
ta saketa ta rungume Amaturrahman da Meenal cikin tsalle irin na nayi kewarku, sai
dariya suke da faɗin yanda sukai missing ɗin junansu. Ta sake rungume su Safah suma
kafin ta juyi gareni, idanu taɗan waro tana nunani da faɗin, “Lah kece?” murmushi
nai mata kawai dan nikaɗai nasan mi nakeji, rungumeni tayi nima, sannan muka ƙarasa
falon daya gama jin kayan more rayuwa, ga sanyin AC da wani ƙamshi mai kashe
zuciya, tuni ɗan gumin da mukai harya tsane, labarin haɗuwarmu ta jiya taketa
bamasu Amaturrahman saboda tambayar da sukai na ina muka san juna?.
Fitowar matar gidan ya sakasu Safah miƙewa gaba ɗayansu harsu Amaturrahman
sukai kanta suka rungume, ba kowa bace face matar jiya data taimakeni, bayan sun
zauna ta gaisa da aunty Mahfuzah cikin salon gaisuwar larabawa, nima gaidata nai
kamar yanda na iya a nawa al'adar da tarbiyyar, kallon mamaki tai min dan da'alama
sai yanzune ta lura dani ma, da turanci take tambayata wai dama tare muke dasu
Safah?. Amaturrahman ce ta bata amsar da take buƙata harma da ƙara mata wadda bata
tambayaba. Murmushi taita saki da ƙaremin kallon da kowa yaketa mamakinsa, tana ta
maimaita sunana tamkar karatu a bakinta, bansaniba daɗi yaymatane kokuwa yaya oho,
dan nasan suna Bilkisu dai sunane sananne da zaka iya jinsa a kowacce duniyar
musulmai balle tace yaune ta fara jinsa sabo.
Ranar dai anan muka yini, har yamma su Amaturrahman basu koma can
gidanba, danni dai an tabbatarmin da nazo kenan bazan koma canba, acewartama a
daren zata kaini can makarantar da Ummu ta faɗamin. Banga saurayin nanba sai yamma
lis ya shigo sanye da farar jallabiya sol da mayafi irin wanda larabawa kansa akai
su saka baƙin abunnan a sama tamkar gammo, fara'ar da bangansa da itaba jiya sai
gata yau a fuskarsa yanamasu Amaturrahman magana da kulawa kamar yanda suma suke
masa, shima dai sai da ya nuna mamakin sake ganin nawa anan, su Amaturrahman da
basa hutawa sukai masa bayani dai-dai fahimtarsa, shima dai murmushin yayta saki
kafin ya nufi ɗakinsa wai zaiyi wanka.

Ban tashi shiga damuwaba sai da su Amaturrahman zasu koma gidan aunty Mahfuzah
su barni anan, hakan kuma na

nufin munyi sallama kenan dasu, sai naji ƙwalla ta cikamin idanu, sabo kenan turken
wawa. Suma kansu na lura basuso hakanba, amma sai suketa dariyar ƙaramin ƙwarin
gwiwa da tsokana. Haka mukai musu rakkiya har gidan sannan muka sake dawowa ni da
Anwar da Anum mai shegen surutu, yanayin rawan kanta sai yakemin kamanceceniya da
Nabeelah, gata da saurin magana saina nutsu sosai nake fahimtar magana idan tayi,
dama dai maganar tamu sai da turanci. A falo muka sake zama, cikin son fidda abinda
kecin raina na tambayi Anum da Anuwar da naga shima ya saki jiki dani yanzu kosun
taɓa zuwa ƙasarmu?. Anuwar ne kaɗai yace ya taɓa zuwa shima sau ɗaya tare dasu
Abdur-rahman, sunzo hajji wata shekara zasu koma ya bisu sukaje tare, satinsa biyu
acan ya dawo daga nan bai sake komawaba har yanzun, amma yanada burin sake zuwa
saboda ƙasar tai masa daɗi sosai.
Murmushin jin daɗi nayi sai dai a ƙasan raina ina mamakin to Mamansu fa? Ita
bata taɓa kaisu wajen nata danginba kenan kokuwa?, da ƙyar na ture tunanin a raina
muka cigaba da hira har sanda Umm-Anum ta fito cikin shiri, sanin inda zamuje ya
saka duk muka miƙe, tana gaba muna biye da ita har inda Anuwar ya ajiye motar da
zamu fita. Ni da ita baya muka shiga, Anuwar da Anum na gaba, dukda darene garin
zirga-zirga aketayi tamkar rana, gashi ko'ina ƙwanyar da wuta abin birgewa.
Mun iso wani haɗaɗɗen gini babba da nake ƙyautata zaton makarantarce, Anuwar
yay fakin duk muka fito, jin kamar ana kallona yasa na ɗago, Anuwar na kama
idanunsa tsaye a kaina ƙyam, saida gabana ya faɗin dan wlhy sai naga tamkar Boss,
murmushi yaymin. ɗauke kaina nai batare dana maida masa murtani ba, Umm-Anum dana
fahimci tana kallonmu ta hararesa da kama hannuna mukai gaba. Ina jiyo dariyarsa
shi da Anum, sai dai banajin mi suke faɗa cikin harshen larabci. Gaskiya ina sake
jinjina wannan tsananin kama a cikin raina, kai gaskiya inason sanin wani abu
dangane da mutanen nan, wannan kamar ta wuce kama kawai, anya kuwa babu wata alaƙa
tsakanin...........
Shigarmu wajenne ya katsemin tunanina, Bansan yanda zan fasalta muku
haɗuwar wannan makarantaba da tsarinta, na bama kowa dama ya ƙiyasta a cikin ransa
kawai, dan idan nace zan lissafo komai shafin yau da gobe duk anan zamu ƙare. Tuni
na zama baƙauya wajen kallon abubuwan birgewa, to lallai da ace munada irin waɗanan
makarantun da mace-macen aure ya ragu muma a yankunanmu, da ansamu sauƙin rikin
aurarraki a gidajenmu. Sashe na musamman aka buɗe mana mai madaidaicin falo guda da
ɗakuna biyu a ciki.
Fuskar Umm-Anum ɗauke da murmushi ta kalleni, “Ɗiyata anan zaki zauna, dan da
kaina zan miki aikinnan saboda ƙurewar lokaci, ga mamanki ɗinan sotake ta ganki
tamkar zinare”. Murmushi nai mata kaina a ƙasa dan haka kawai nakejin nauyinta, nai
mata godiya tare da addu'ar fatan alkairi. Batace komaiba sai murmushinta dake
kasheni taketa sakarmin.
Ɗaya daga cikin ɗakunan muka shiga, kayayyakine ajiye da ban fahimci
kona mineneba, ta umarceni dana cire kayana gaba ɗaya na shiga wani madaidaicin
kwami dake cike da ruwa da bazamu kirashi normal ruwa ba, ita kuma ta fita.
Dukkanin yanda ta umarceni nayi haka nayi babu musu, inayi ina ɗan waige-waige
tamkar mai tsoron wani ya shigo, saida na cire komaina kafin na fara saka ƙafa
cikin kwamin, ajiyar zuciya na sauke a hankali saboda ɗan ɗumi-ɗumin ruwan mai
warware gajiyar jiki, na ida saka ɗayar ƙafar sannan na shige gaba ɗayana,
sihirtaccen ƙamshin da ruwan keyine ya sakani lumshe idanu ina karanto addu'ar
godiya ga ALLAH da ni'imominsa masu yalwata ta fuskoki da dama ga ɗan adam. Sai da
nai kusan mintuna uku da zama sannan ta shigo da sallama, ta canja kayanta da wata
doguwar riga mai kama da leda, hannayenta sanye da safar hannu ta leda itama,
murmushi taimin ta tako inda nake. Ɗan kwalina daban cireba ta zame daga kaina, ta
warware gashina da Alhmdllh yanzu ya cika sosai kuma yanada tsayi gwargwado saboda
kulawar da naita bashi bisa koyarwar su Ummie tun muna boarding, wani ɗumi mai daɗi
naji ya ratsa kan nawa, hakan yasani kallon madubin dake gabana da nake iya hango
kaina da ita kanta.

Tace, “A cikin ruwannan zaki kwana, babu abinda zai sameki insha ALLAH
karkiji tsoro, ruwane mai ɗauke da sirrika kala-kala da duk macen da aka gyara dasu
dolene mijinta yasan ta isa mace, sirrikane na ƙamshi masu daraja a jikin ƴa mace,
ƙa'idar makarantarmu watanni ukune domin mace ta samu damar koyon abubuwa masu
yawa, ba sirrin gyaran jiki bane kawai mace tafi buƙata a rayuwar aure ɗiyata,
zakiga wata macen komai ta iya ta kuma ƙware, amma idan batasan yanda zataima miji
maganaba kawai sai ya rusa mata komai, dan wani namijin shi abinda ke ƙololuwar
birgesa ga mace shine iya magana, wani kuma a kallo kawai zaki gama dashi, wani
tafiya, wani girki, wani ƙamshi, wani shagwaɓa, wani kwalliya, wani kwanciya. Karki
sakama ranki cewa tarayya da miji a gado shine kawai farin cikin aure ko shikaɗaine
auren, hakan kuskurene, wani namijin ƙanƙanin abun da kika raina shike sakashi
farin ciki. Karkiyi tunanin gyara kanki yana nufin kin mallaki namiji ya zama naki
ke kaɗaine, macen data isa mace bata shakkar zama da kishiya ɗiyata, dan wani
lokacin zama da kishiya nasake bayyana darajar macene a wajen mijinta. Karkuma kiyi
tunanin babu wata mace data isa raɓar mijinki dan yana sonki ko kin iya komai, wani
namijin badan baya sonki yake miki kishiyaba ko yake budurwa, a'a halayyar san mace
fiye da ɗaya a jinin maza yake, ko bazasu ƙara aureba saisun kalla. kizama mai
gyara aurenki ta kowanne ɓangare, idan nace kowane ɓangare ina nufin kowanne fanni
hatta da ƴan uwansa da duk abinda ya shafesa. Inason ki cire komai a cikin ranki ki
nutsu ki bani dukkanin hankalinki a kwanakinan goma sha biyu da zamuyi tare, sonake
komai na cikinsa ya zama tamkar rubutu bisa dutse a cikin ƙwaƙwalwarki, ki ɗaukeni
tamkar mahaifiyarki, kuma ƙawarki aminiya wadda zaki iya magana kowacce iri da ita
batare da kinji kunya ba, inhar kika riƙe duk abinda zaki koya a kwanakinan ina mai
tabbatar miki bazaki taɓa goguwa a zuciyat mijinki ba koda zai auri mata uku ku
zama huɗu bayan ke”.
Idona a risine na ɗaga mata kai alamar to, inajiyo sautun murmushinta
itama. Abu ta fara shafamin a fuska tana cigaba da min magana cikin nutsuwa, sosai
kunya ta lulluɓeni, dan abubuwane masu matuƙar nauyi a gareni take faɗa a buɗe, ta
haɗe fuska a yanzu babu wasa tattare da ita ko kaɗan. Saida ta gama tsaf sannan ta
fita suka sake dawowa da wata mata. Matar ta nunamin da faɗin, “zata zauna dake
anan, ni zan koma gida sai da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”. Kaina na jinjina
mata dan ta hanani magana tunda ta shafamin abin fuskarnan.

Duk yanda zan baku labarin abinda ya gudana a kwanakinan da wahala ku


iya fahimtata, abubuwan dana koya kam ba'a magana, sam Umm-Anum bata wasa dani idan
akazo ɓangaren abinda zan iya jin kunyarta balle naga fuskar yin sakaci da abinda
ake koyamin, tsaye take kaina ɗari bisa ɗari, komai buɗemin shi take babu hijjabi,
aduk lokacin da takemin bayani aka abinda yafi ƙarfin kaina tamke fuska take tamau
babu wasa, kai jama'a hatta da salon tafiya ba'a barniba sai da aka koyan, komai a
tsare yake. Matar da take bari ta kwana dani kasa haƙuri tayi ranar dai take
tambayata wai kodai ni ƴar uwar Umm-Anum ce? Dan ita yanda take ganin tanamin ya
ninka yanda takema ɗalibanta fiye da zato. An kawoni ɗaki na musamman, sannan komai
ba'a sakani cikin ɗalibai ni kaɗai ake koyamashi a nutse, daɗin daɗawa da kanta
take min komai bata yadda kowa yayminba sai abubuwan da ba'a rasaba, dan takance
kowa a rayuwa da irin basirar da ALLAH yay masa, abinda suma sauran malaman
makarantar suke koyamin zai amfanar dani ta fannoni da dama. Murmushi nayi nidai
bance komaiba, dan nikaɗai nasan mi nakeji game da matar nan, ita kanta lokuta da
dama nakan kamata ta shagala da kallona, kallo maiban mamaki, kallo irin na shagala
da zurfi ason tunano wani abu, idan tai irin wannan zurfin kuma zakaga daga ƙarshe
ta dafe kanta tamkar zata fita cikin hayyacinta. Akwai randa naga kallon har yaso
yimin yawa, sannan ni kaina yanda takemin ɗin nasan ba kamar yanda takema kowa
baneba, tana sakin jiki dani fiye da hasashen mai hasashe. Akwai randa tazo tana
koyamin

girki sai muke ɗan hira kaɗan-kaɗan, cikin dabara nake tambayarta ko zasuje ƙasarmu
nan kusa?. Shiru tai bata bani amsaba, na kasa daurewa dai na sake mata tambayar
cike da ladabi. Yanda ta juyo ta kalleni fuska a haɗe saida naso firgita. Kaina na
duƙar ƙasa ina faɗin, “Kiyi haƙuri dan ALLAH Ummu, bansan tambayar zata ɓata ranki
ba”. Sautin murmushinta na jiyo, hakan yasa na ɗan ɗago na kalleta, ta ajiye
cokalin hannunta tazo ta kama hannayena, murya a sanyaye tace, “Ɗiyata ba laifi
kikayiminba, ƙasar takuma ni ban taɓa zuwantaba ai, duk amintakar dakika gani
tsakanina da ƙanwata Gimbiya Munaya ban taɓa ziyartarta ba, sai dai ita idan tazo
nan mu haɗu, duk lokacin danai yunƙurin zuwa nakan tsinci kainane a wani mummunan
hali da baida fassara”. Tana gama faɗa ta saki hannuna ta juyamin baya, aikin da
mukeyi ta cigaba dayi batare da ta sake min maganarba.
Ajiyar zuciya na ɗan sauke hawaye na ziraromin, haka kawai yanda tayi maganar
sai naji abun daban, to amma ai Ummu ta sanarmin itaɗin ƴar ƙasarmu ce, sanadin
neman magani ya kawota nan hartai aure, itakuma gashi yanzun tace bama ta taɓa zuwa
canba, anya kuwa babu wani sirrin dake ɓoye?.......
Ajiyar zuciya na sauke da saurin kallonta jin ta taɓanu, tace, “Kinama
fahimtar abinda nakeyi kuwa?”. Da sauri na ɗaga mata kai alamar eh na tattara
hankalina gareta baki ɗaya.

____________________________

A ɓangaren Jawaad ma dai shirye-shirye sun kankama, an gama gyaran gida


tsaf, ya canja kamanni gaba ɗaya tamkar bashiba, amarya kawai yake jira ta shigo
cikinsa. Gaba ɗaya a tsakaninan a busy yake matuƙa, ga aiki ga shirye-shiryen biki
dasu Jabeer ketayi naban mamaki, dan gayya suke ta gaske da gayya tamkar wannan
shine auren farko da Jawaad ɗin zaiyi. Shidai ya zuba musu idone kawai yana kallon
ikon ALLAH, dan dayay magana ca sukai babu ruwansa, kawai dai yama shirya dan bai
isa cewa bazaije wajen abinda suke shiryawanba ehe. Bai sake musu maganarba kuwa ya
cigaba da nasa harkokin, maganar kayan da za'a saka a gidan kuwa gimbiya Munaya
tace Takawa yace zaiyi komai, kayan kicin kuwa itace zatayi. Da yay mata maganar
lefe tace masa ya dakata, zasu nema Dady suyi magana, sai ana saura kwana biyu
tarewar za'a kaisu can gidan Dad ɗin dan sune sukafi cancanta da amsar lefen,
koyayane zasu bashi matsayinsa na uba kodan ɗawainiyar da yay da Bilkisun. Jawaad
baice komaiba shi dai sai ALLAH ya kaimu.

A yau tunda safe Su Amaturrahman suka shirya yima Mami (Munubiya) rakkiya
gidan kamar yanda Gimbiya da Takawa suka buƙata, zataje su haɗu da kamfanin da zasu
shirya gidan. bayan sun duba saisu zaɓa mata kalar data dace a tsara komai yanda ya
dace..............✍

Bara dai na baku hakanan, inata ƙoƙarin typing ɗin bayan tafiyar baƙi amma kiraye-
kirayen waya ya hanani nutsuwar yi da yawa, takaima harna daina ɗaga wayoyin mutane
wlhy🤦🏻😑😓.
✍🏻
[12/25/2020, 6:15 PM] HASNA : Billyn Abdul:
BARKA DA JUMA'A

Page 37

..................Sosai su Amaturrahman ke santin gidan Jawaad na A.Y Street, badan


yafi kowane gidaba, bakuma dan an cikasa da ƙawa ba, ginine dai tamkar kowanne gini
da kowa yasani, sai dai yanda akai tsarin gyaran sai ya kuma fiddo da ƙyawun gidan
fiye da yanda yake a da, (masu karatu karku manta wannan shine gidan da aka haifa
Jawaad, a cikinsa iyayensa suka rayu, dan shine gidannan da turawannan suka bama
Abba Abdul-aziz, shine kuma sanadin wannan arziƙi daya tsolema mutane ido). Sai da
suka shiga ko'ina da ina dan babu komai cikinsa sai ƙamshin sabon fenti.
Suna tsaka da dubawa Jay ya iso gidan, zaune yake a bayan motar sai Sadiq
sabon drivern sa dake tuƙi cikin nutsuwa, dan shima dai baida matsala, amma hakan
bai hana Jay tuna Gimba ba a kowacce daƙiƙa ta rayuwarsa, yasan gimba bazai mantu a
zuciyarsa ba, dan yawuce duk tunanin mai hasashe a zuciyar tasa. Yauma kamar kullum
yana cikin gayunsa da ƙyamshi, sai dai ya ɗan rame, hakan yasakashi yin wani fayau
dashi, (bamu saniba azumin da aka shane kokuma ɗokin amaryarne. lol😂).
waya yakeyi, hakan yasa har Sadiq ya fito ya buɗe masa bai fitoba, sai
da yaja kusan mintuna huɗu sannan ya fito bayan ya ajiye wayar, Safah data dage sai
anzo da ita da gudu tayo kansa, fuskarsa ɗauke da murmushi harta iso garesa,
hannunsa ta kama tana gaishesa. Shidai kallonta yake kawai, dan sosai ƙiriniyarta
ke bashi mamaki, ko gajiya batayi, girma take amma abun tamkar ƙaruwar mata yakeyi.
(Hhhhh tunda Jinin Munaya na yawo a jikin Safah ai kaga abinda yafi hakama, sarki
Sameer ne zai baka labari dalla-dalla😂🤐). Cikin ɗoki tace, “Yayanmu gidanka kaida
aunty B ya haɗu sosai, nima harna zaɓi ɗakina dan kasanfa nan zan dawo. Murmushi
yay mata mai sanyi ya jinjina mata kai amma baice komaiba.
Sosai mamaki ya kama Jay lokacin da suka shiga ciki shi da Safah yay arba da
Munubiya, shi tunaninsa Gimbiyace da kanta, itama ɗindai kallon mamaki take masan
sai dai ita bamusan kona minene ba. Su Amaturrahman ne suka katse tunaninsa da
gaisuwar da suke masa, ya amsa musu da kulawa kafin shima ya gaida Munubiya cikin
girmamawa. Kasa haƙuri yay dai yace, “Ummu da kanki? Su Amaturrahman ma aisun isa
basai ke kinzoba”. Munubiya tai murmushinta mai kama dana Munaya, kafin ta bashi
amsa Safah tace, “Lah Yayanmu bafa Ummu bace, wannan Mami ce sweetheart ɗin Ummu”.
Cikin rashin fahimta yake kallon Safah amma baice komaiba. Amaturrahman tace,
“Yayanmu ai Ummu ƴan biyune, Mami itace hassanarta”. Ɗan waro idanu Jay yayi waje
sai kuma ya shafa kansa, “Sorry Mami ai wlhy ni duk ɗaukata Ummu ce, bansan ita ƴan
biyu baneba nasan dai tanada yaya mace”. “Karka damu ƙanina, Gida yay ƙyau masha
ALLAH, ALLAH yasa rai akaimawa, ALLAH yasa a cika manashi taf da ƴaƴa ko jikoki
zance”. Cikin murna su Safah suka shiga faɗin, “Amin”. Shidai a saman laɓɓa ya amsa
nasa amin ɗin.
Kasa jurewa Mami Munubiya tai ta koma gefe tai kiran Munaya, tana ɗagawa
tace, “Sweetheart kingako mina gani ga angon nan?”. Daga can murmushi gimbiya
Munaya tai tana gyara kanta a kafaɗar takawa, tace, “Nasan ina kika dosa
sweetheart, tun randa na fara ganinsa nima naga abinda kika gani, wannan ne dalilin
tura matarsa can ta ɗan zauna, sai dai bamu da tabbas, amma muna fatan ALLAH yasa
ta kasance hakanne”. “Kai to amin kuwa, al'amarin akwai ruɗarwa, amma gaskiya bana
tantamar alaƙa a tsakaninsa da Umm-Anum Sweetheart, nifa da farko na zata Anuwar ne
wlhy, sai da nai masa kallon nutsuwa na fahimci yafi Anuwar cikar zati, Anuwar kuma
ya fisa haske, hatta da maganarsu kumafa babu banbanci, bara sai dai mun dawo ma
tattauna”. Daga haka Mami Munubiya ta yanke wayar ta koma ciki dan baƙin da suke
jira har sun iso.
Sai da suka gama zagaye gidan tsaf kafin su basu hotunan kayan ɗakin da
zasu dace da tsarin gidan akan su zaɓa. Shi dai Jawaad bai saka musu bakiba, Mami
dai ta tambayesa kalar da yafi so, ya sanar musu, daga haka ya cigaba da danne-
dannen waya Safah na gefensa tana zuba masa surutu, shidai nasa saurarenta dayin
murmushi, sai jefi-jefi yake bata amsar wani abun koyay mata tamba

ya.
Kusan awa guda suka kammala komai dangane da zaɓin kayan, a take Mami ta
kira Ummu ta sanar mata kuɗin da suka cajesu. Kafin kuwa subar gidan har ƙuɗaɗensu
sun shiga accaunt. daga haka suka bar gidan akan sai zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu
zasu dawo suga yanda kamfanin suka shirya gidan. Jay yaymusu rakkiya har mota
yanama Mami godiya, sai da suka wuce sannan shima ya shiga mota suka bar gidan.

Office Jay ya koma domin cigaba da tarin ayyukan dake gabansa, dama
yana tsaka da aikinne Ummu ta kirasa akan yaje can gidan yanada baƙi, dole ya ajiye
ya tashi ya tafi. Fatansa ya rage ayyukan sosai, gashi yanason ɗaukar hutu kona
sati ɗayane, duk da dai Sir Ahmad yace bai isaba na sati biyu zai ɗauka shima yaje
yasha angwanci da ƙyau.
Zamansa baifi da mintuna talatinba baƙon da yake jira ya iso, sai da
akai masa iso sannan ya bada izinin a shigo dashi, ba kowa bane baƙon face Sulaiman
yayan Amina, Jay ya ɗago daga abinda yake fuskarsa a sake dukda dai ba murmushi
yake ba. hannu ya bashi suka gaisa kafin ya miƙe ya kawo masa abinsha baya. ya nuna
masa wajen zama, yah Sule yay godiya. Ɗan murmushi kawai Jay yayi baice komaiba.
Sai da ya ɗan sha ruwa sannan Jay yace, “Yaya ake ciki Sulaiman? ka gano ina
yake?”. Numfashi yaya sule ya sauke yana gyara zama, “Wato ni abin nasu yanzu ya
fara ruɗar dani oga, nama rasa wanene mara gaskiyar tsakanin Alhaji Alin da Hajiya
Humairan? A yanda bincikena ya nunafa Qaseem baya ƙasarnan”. “Baya ƙasar kuma?”
Jawaad ya faɗa yana tamke fuska cike da ɗunbin mamaki kuma. “Ƙwarai kuwa wannan
itace magana ta gaskiya, saura kwana ɗaya a ɗauki azumi ya tafi, kuma abinda na
fahimta lafiyarsa ƙalau ba kamar yanda ku anan office yace zaiyi zaman ganin likita
a gidaba”. Shiru Jay yayi yana juya al'amarin a ransa, tun randa ya fiddo Qaseem a
cell bai sake ganinsa ba, sai ana gobe za'a fara azumi, ya shigo station amma baifi
awa uku ba ya tafi, Jawaad bai kawo komai a ransaba sai da aka sake ɗaukar tsahon
sati ɗaya baiga yazo aikiba, shinefa yay bincike ya fahimci Qaseem ɗin hutu ya
ɗauka akan baida lafiya zaiyi zaman ganin likita a gida. Aranar bai ƙasa a gwiwa ba
ya nufi gidan Qaseem, amma sai ya iske bayanan daga bakin maigadinsa, yayi tunanin
yana gidansu ne, saiya saka a bincika masa can, nanma an tabbatar masa baya nan,
tunda yayma gidan yajin aiki ma bai sake waiwayensa ba. Shinefa yasa yaya Sule ya
bincika masa.
Huci mai zafi Jay ya furzar daga bakinsa yana danna ƙasan pen ɗin hannunsa
da ƙarfin gaske, ya ɗan kalli yaya Sule ya ɗauke kansa daɗan duka table ɗin,
“Tabbas yanzu na sake fahimtar akwai abinda suke ɓoyewa, in babu rami miya kawo
maganar rami? Sun fahimci ina bibiyar Qaseem shiyyasa suka turashi can, ammafa
sunyi abanza, sugama zagaye-zagayensu saina gano komai, da izinin ALLAH sai na
bankaɗo komai, idan nace ina nufin komaima Sulaiman!!”. Ya ƙare maganar cikin fushi
da dukan tebirin da masifar ƙarfi. Shidai Yaya Sule har sai da yaɗan rumtse ido.
Jay yace, “Wace ƙasa suka kaisa?”. Yaya Sule da yay ɗan shiru alamar tunani yace,
“Idan dai ban mantaba China naji”. Karan farko Jay ya saki murmushi mai ma'anoni da
dama, yaɗan ɗage kafaɗarsa da taɓe baki.

★★★★★

Da daddare bayan Jawaad ya koma gida ya samu kira daga su Uncle Nasir,
saida ya kammala shirin barcinsa sannan ya nufi sashen mama Atika inda suke
jiransa. Bai wani nuna mamakin ganinsuba gaba ɗaya ya gaishesu cikin girmamawa
kamar yanda ya saba.
Uncle Nasir yace, “Alhaji Ali ya kirani jiya akan ankirashi daga gidan sarki
za'a kai lefenka gidansa, Jawaad kana ganin kuwa wannan hanyar daka biyo mai
ɓillewace? Karfa ka manta a yanda kasa akai ɗaurin aurannan?”. Shidai Jay baice
komaiba kuma bai ɗago ya kallesa ba. Cikin fushi Uncle Uwaisu yace, “Wato ga ƴan
iska na magana kayi kunnen uwar shegu damu ko?” Murmushi Jawaad yayi yaɗan girgiza
kansa batare daya ɗago ɗinba, yace, “Uncle to nikam mi kukeso nace, idan maganar
yanda aure ta kasancene tun a wancan karon na bada amsar da duk ake buƙata, a
tunanina yanzun mun wuce wannan wajen, kai lefe kuwa daga can masarauta ne sukai t

unain akai lefen can saboda koba komai ubane shi ga yarinyar shine kuma mariƙinta
har a yanzun..........”
“A wannan ganganne Jawaad, Shine mariƙinta ko kai daka ɗauketa ka maida
gidan sarki saboda ka isa, karkuma a taɓa maka ƴar gwal?”. Uncle Bashir ne yay
maganar a fusace. Jawaad da har yanzu yaƙi kallon kowa a cikinsu yace, “Nidai duk
abinda kuke ganin na mukushi ba daidaiba akan wannan aure kuyi haƙuri ku kuma
gafarceni”. Uncle Sulaiman da tun ɗazun baice komaiba yace, “Nima dai a ganina
maimaita maganar baida amfani tunda abinda ya faru ya rigada ya faru, haka kuma
ALLAH ya tsara dama zata kasance, kunga kenan bamu isa canja wannan ƙaddarar ba.
Yanzu Jawaad ina zaka ajiye matarka? Dan bamuga kana ƙoƙarin gyara ɓangaren
nakaba”. Karon farko Jay ya ɗago daɗan murmushi ya kalli Uncle Sulaiman, “Uncle ba
anan zan ajiyeta ba, A.Y street zata zauna har an kammala gyaran”. Uncle Nasir
yace, “A.Y kuma? Saboda karmu cinyeta anan?”. Jay da keta ƙoƙarin danne fushinsa
yace, “Ba haka bane Uncle...........”
Da sauri Mama Atika ta ƙatseshi da faɗin, “Inma haka ɗinne kaidai ka
sani fitsararre mai shegen taurin kai da raini, hakan dakai ni bai dameniba, dan ko
kaƙi ko kaso dolene a maida aurenka da Sabira, dama shirin maka tsinannen mijin
daka aura mata muke a kotu, sai gashi ya matu kuɗinmu sun huta, to wlhy kama
tabbata aure kamar mun maidashi ne kai da Sabira”. Cikin fushi Jay ya kalleta zaiyi
magana Uncle Sulaiman ya girgiza masa kai. Shiru yay ya maida kansa ƙasa, har
sukaci jarabarsu suka tsire bai sake tankawaba, taron dai ya watse da sharaɗin sai
ya maida aurensa da Shahudah.
Shidai bai tanka musuba tunda yasan ɗan fir'auna bai mutuba.

______________________________

SAUDIA

Gaba ɗaya wannan yinin na yau Umm-Anum ta yisane cikin yimin nasihohi
da haɗamin kayan gyaran jiki da wasu littatafai masu muhimmanci kamar yanda tace,
sai faifan cds da tace na kasance cikin kallonsu duk randa nake da lokaci zasumin
amfani.
Gaba ɗaya raina a ɓace yake banason tafiya, basan yanda zan musalta muku yanda
nakejinta a rainaba, tunda tafiyarnan ta gabato har kuka nakeyi idan na tuna zan
tafi, baƙaramar shaƙuwace ta shiga tsakaninmu ba a kwanaki sha biyun nan, kodan ta
jani jikintane oho.

A ɓangaren Umm-Anum ma dai cike take da damuwa, haka kawai takejin batason
Bilkisu ta tafi, yinin yau komanta sukuku zaka gansa, da daddare tare suka dawo
gida da bilkisu, anan zata kwana yau gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce ita da
Aunty Mahfuzah da Anum sai Anuwar daya dage shima zaije, da farko Umm-Anum catai
bazaijeba, sai da Abie yasa baki sannan da ƙyar ta amince, dan haka kawai takeji
batason suje da ga shi har Anum ɗin.
Abie bai taɓa ganin bilkisu ba sai yau bayan sun dawo, itama kuma yauɗin ta
taɓa ganinsa, amma yanda ya karɓeta abin har mamaki ya bata, shikansa mamakin yanda
yarinyar ta shiga ransa yakeyi, sannan badan kar ace yay ƙaryaba wasu abubuwa nata
suna ɗan masa kama dana Umm-Anum ɗin, musamman tafiya da dai wasu ƙananun abubuwa
da saika nutsu sosai kake fahimtarsu.
Sai da su Bilkisu suka shige suka kwanta sannan ya fuskanci matarsa, dan
yanda take komai rai ɓace ne ya sakashi jinsa shima a damuwa. cike da kulawa yake
tambayarta mike damunta?. Hawayen da taketa riƙewane suka zubo mata. Sake rikicewa
yay ya jawota jikinsa, dan yanason wannan baiwar ALLAH shidai a rayuwarsa, dukda ba
ita kaɗaice matarsaba kuwa, amma yanda take ƙyautata masa yasa tazama tauraruwa a
garesa. Yanda yaketa jero mata tambaya wata kan watane ya sakata sakin murmushin
ƙarfin hali, idonta a kansa tace, “Bafa komai baneba, yarinyarnan banason ta tafi
wlhy, jinta nake cikin jinina fiye da yanda kake zato, ina mata ƙauna maiban mamaki
har a ƙarƙashin zuciya, sannan sunanta duk sanda na ambacesa ko wani ya ambata sai
naji matsananciyar faɗuwar gaba, bansan miya saba”. Abie dai kallonta ya keyi cike
da nazari, sai da tagama ya sauke ajiyar zuciya tare da sake rungumeta,
maganganunta na buƙatar ayi musu zama na musamman domin yin nazari, amma duk da
haka bara ya gwadata ya gani, ko lokacin da suke fata

ne yazo. “To kodai zamu shirya muma muje bikin nata ne?”. da sauri Umm-Anum ta
tashi daga jikin mijin nata tana girgiza kanta, fuskarta harta nuna ɓacin rai,
tace, “Babu inda zani Annur, badanma ka takuraba kosu Anum bazasu jeba”. Da kallo
shidai kawai yake binta, amma baice komaiba, baikuma sake cewa uffanba game da
tafiyar har gari ya waye su Bilkisu suka tashi da shiri.

★★★★
Yau ta kasance ranar da zan koma ƙasata ta haihuwa tare da tarin
alkairan Umm-Anum da mijinta da Aunty Mahfuzah, sai su Anum da nakejin ƙololuwar
farin cikin tafiya tare da su, gefe guda kuma na zuciyata najin ɗacin rabuwa da
Umm-Anum tare da matsananciyar kewa. Munfi awa uku zaune da ita tana sake tisamin
abubuwa masu dama, daga ƙarshe ta roƙeni akan karna manta da ita, zata kuma ringa
kirana akai-akai, idan kuma nasamu lokaci na daure muzo gareta wataran tare da
mijina, haka kawai takeji a ranta tanason ganin mijin ƴarta. Murmushi kawai na
iyayi ina share hawayena kaina a risine, ta rungumeni a jikinta tana jeromin
addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya a gidan aurena. Da ƙyar ta barni na fito,
tana kuka nima inayi tamkar zan shiɗe, da ƙyar Aunty Mahfuzah taja hannuna ita da
Anum.
Har jirginmu ya ɗaga ban daina kukan kewar Umm-Anum ba, ina ƙaunar matarnan
matuƙa a cikin jinina da tsokar zuciya harma da ruhi.
Kasancewar tafiyar yamma mukayo dukda ba time ɗinmu ɗaya da nanba munyi
saukar dare ne, inda mukaci karo dasu Amaturrahman ƴan tarba, sosai muke murnar
ganin juna, sai santi suke wai na canja matuƙa, sunata zubamin shaƙiyanci nadaiƙi
kulasu, dan bana cikin mood ɗin farin ciki sam.
Koda muka isa masarauta Ummu ma rungumeni tayi, sai taɓani take tana jerama
Umm-Anum addu'oi na musamman, ga daɗin da taji na barin su Anuwar da akai suka
biyomu. A ƙasan raina inata mamakin ganin yanda suketa shirye-shiryen bikin tamkar
zasu aurar da ƴarsu ne ta cikinsu ko ƴar uwa ta jini, kai waɗanan mutane sun
cancanci zama shugabbani, domin duk mai fuskantar al'umma da maida al'amarinsu nasa
to lallai shine shugaban da yafi cancantar zama shugaba.
Ɗaki guda aka waremin dan Ummu tace bazan zauna ɗakinsu Amaturrahman ba
wannan karon, akwaima sauran kayan gyara da Umm-Anum ta bayar a ƙarasa min a
kwanaki biyun da suka rage mana. Babu wanda yaymin maganar Boss nima kuma bamma
kowa ba, da yake darene bayan anɗan gaggaisa duk muka kwanta.

WASHE GARI.

A safiyar yau nakejin wai za'a kai lefena gidan Dad ne, haka kawai naji
gabana ya faɗi, amma sai na danne zuciyata na cigaba da addu'oi, har yanzu Yah
Qaseem na ƙasan raina, inason nasan halin da ya ke ciki shi da Dad fiye da kowa a
gidanmu, sai dai hakan ta gagara dan boss ya toshe ko ina da ina da zan iya jinsu.
Su Amaturrahman sunata shirin tafiya can gidan domin amsar lefen suma, sai a yau
naga sauran manyan ƴaƴan Ummu ƴan uwan tagwaicin Amaturrahman. Abdul-Raheem da
Abdur-rahman, sai Ameen ɗan uwan tagwaicin Meenal, sai Uncles ɗinsu huɗu, Sauban da
matarsa ƙyaƙyƙyawa mai kirki da yaransu huɗu masha ALLAH, sai Aryaan shima da
matarsa da yara biyu, Aiyaan ma matarsa da yarinyarsu ɗaya sai ciki ƙarami da
matarsa keda shi, sai Khalil shima da tasa matar da yara biyu, dukansu suma a jiya
suka iso daga India. Gida ya cika yanda akeso tamkar bikine daya shafesu na jini,
washe gari sai ga wadda naji suna kira Aunty Samha itama da nata ƴaƴan, sai kuma
babbar mace suna kiranta Aunty Mimi. Wlhy bansan sanda hawaye suka faramin gudu a
kumatuba, duk wani kewar ahali sun toshemin ita ta ko ina, sun mayemin gurbin
dangin da suka nisanceni.
A wajen Amaturrahman nakejin wai Boss yazo masarauta wajen Ummu yau da safe,
bai nemi inda nakeba har ya wuce, banji komai a rainaba game da hakan, sai daga
baya suke bani labarin Ummu ce tace an daina ganina har da shi kansa bazai ganniba.
Ni saida abinma yaso bani dariya amma na kanne.

_______________

A gidan Dad kam shirye-shiryen karɓar lefe suke, duk da dai ran Momy a
ɓace yake matuƙa tana dai ƙoƙarin dannewane, shi dai Dad baka gane yanayinsa, dan
yamafi maida hankali ga lallashin ƴar lelensa da suka cikama zuciya

da alƙawarin komawarta gidan Jay nan bada jimawaba.


Kusan sha biyun rana su Amaturrahman suka iso gidansu Hudah, Hudah dai bata
fitoba zamanta tai cikin ɗakinta, Aamilah kuma an fito ayi rainin wayo saita iske
waɗanan sunci uwarta aduk iskancin da take taƙamar ta tara kota iya. Dole fa ta
nutsu waje guda ta kama kanta, harta je ta ƙwanƙwasama Shahudah dake ɗaki gulma da
cewar lallai Bily ta shahara a asirin nata har ƴan gidan sarki taimawa. Cikin
takaici Shahudah tace, “Tsinanniya jikar matsafa, ai nayi alƙawarin randa na koma
gidan Bb wlhy bazata kwana a gidanba, shi kansa saina sakashi yin nadama wlhy, kuma
a banza zata shiga ta fito Hajiya (mama Atika) tamin alƙawarin ko hannunta bazai
riƙeba dan Uban da ya haifeta”. Dariya Aamilah ta sanya da sake tunzurata akan
hakan da zatai shine dai-dai, kuma taji daɗin matakin da mama Atika tace zata ɗauka
akan kar Bilkisu ta raɓu Jawaad, (dan sufa har iyanzu tunaninsu nakan asiri Bilkisu
taima Jay bawai sonta yakeba😂). “Mtsooww kamar kin manta da aikin matsafa kenan”
cewar Shahudah cike da takaici. Haka dai sukaita aikin zagin Bilkisu da Alhaji
Babba harda su Ummah basu tsiraba, kai gidan sarki ma saida suka samu rabonsu😂.

Oho su bama susan da zaman wata Hudah ba a duniya balle a cikin gidan, sun
ɓararraje abinsu sunata harkokinsu tamkar gidansu (😂Wani aiki saisu Samha)
hankalinsu kwancefa yake a gidan Dad dukda sunga cika da batsewar da Momy keyi basu
nuna ta damesuba.
Ƙarfe biyu da wasu mintuna na rana matan Uncles ɗin Jawaad dasu Ummah suka iso
da lefen Bilkisu. Kayane gwargwadon iko na gani na faɗa babu fariyya a ciki balle
nuna anfi kowa. Sai dai fa tsarin kayan da nagartarsu dolene ta girgiza zukatan
mahassada da masu ganin wadda akai dominta bata cancancesu ba. Inna zainabu sai
haɗiyar zuciya akeyi, hatta da Lawisa da ayanzun basa faɗa da bilkisun kuma itama
mijinta Alhmdllh sun sami sauyi saida taji ɗaci a ranta, hakama sauran dangin kowa
dai ta ciki na ciki, su kansu matan Uncles ɗin Jawaad da suka kawo kayan kowa dai
sai murmushin saman fuska tunda suma sai yaune suke ganin kayan tunda su Ummah ne
suka haɗa abinsu. To kowa dai ya danne an gama komai lafiya, an kuma bar kayan anan
sai Dad ya gani sai a kaisu masarauta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suma su Gimbiya
su gani.
Tukuyci mai tsoka ƴan masarauta suka saukema su Ummah, wanda ya girgiza
kowa hatta momy da take ganin wanda Dad ya bada a bayar yayi yawa da.

Aikam tunda su Safah suka koma masarauta babu abinda suke sai labarin lefe,
suka addabama Bilkisu da tsokana musamman su Amaturrahman da matansu Aryaan da suke
biye musu suma dayake mashiriritan ne. Sai da gimbiya ta fito da kanta ta korasu
daga kan Bilkisu sannan suka sama mata lafiya.

_____________

Gayya taban mamaki su Jabeer sukayo a wannan biki, al'amarin har


ba'a cewa komai, tun a yau baƙin nesa kuwa suka fara sauka, irin su Abbati ma duk
yau suka kawo matansu gidan Ummah babba, su kuma suka yada zango a masaukin da su
Hafiz suka tanada musu.
Ango kuwa yau alhamis yana zuwa office Sir Ahmad ya korosa akan ya tafi sun
bashi hutu, karya ƙara ganin ƙafarsa sai nan da sati biyu ciff, shidai murmushi
kawai yayi baice komaiba. Ƴan station ɗinsu ma dai zuwa yanzu sunsan boss ya auri
Bilkisu, masu gulmar dama soyayya yake da ita sai bakuna suka buɗe aka samu nayi,
yayinda masu goyama Rose baya suketa angizata da maganganun ɓatanci ga Bilkisu da
Jay ɗin kansa, masoyansu na ƙwarai kuwa murna suke tayasu da ganin sun dace da
juna.

MASARAUTA

Tunda garin ALLAH ya waye an tashine cikin shirye-shiryen kamu da aka


haɗashi da Hausa fulani day baki ɗaya, su Ummie, Nazifa, Zuhrah, Rebecca, Amina,
Nabeelah, duk suna can suma tare dasu Amaturrahman, abin birgewa kuma duk ƙawayensu
na Boarding skull sai da su Ummie suka gayyatosu suma duk sunata isowa masarauta a
safiyar yau, hakan saiya saka Bilkisu hawaye da tuno iyayenta, inama da ransu
wannan rana tazo mata, inama suna jingine da ita har zuwa yau ɗinta, ina firdausin
ta, ƙawar amana ko tace ƴar uwa rabin jiki, kullum addu'arta ALLAH ya

sadata da Firdausi da iyayenta kafin tabar duniya.

Tunda safe dama mai ƙunshi tazo muka shige cikin ɗaki daga ni sai ita ta shiga
zanamin na nutsuwa, zuwa azhar ya bushe yay shar kamar ka cinye dan baƙi da jaa aka
ɗaɗara mani, kasancewar fashin salla nike dama sai kawai aka shigamin gyaran kai a
nan gida dan Gimbiya nada dukkan kayan gyaran kai a gida da takema kanta, bayan an
kammala nai wanka lokacin ƙarfe kusan uku.
Kasancewar ba sallah zanyi ba sai ban damu da kwalliyar da ake shirin tsaramin
ba, ni kaina basai an faɗaba nasan ina tsaruwa dai-dai gwargwadon iko, duk da
ba'aimin kwalliyar dana canja kamanni baneba amma nayi ƙyau fiye da zato. Bayan an
kammala kwalliyar aka shiryani cikin atamfa lass ƴar ubansu datasha stones work ɗan
gaske, sket da riga akai da suka fidda ainahin tsarin jikina dukda basu matseni
tsam ba, sundai zaunamin a jiki ɗas har ni kaina ban gaji da kallon kaina ba. An
min naɗin ɗan kwali mai tsari aka ƙawata adon nawa da sauran kayan ƙawata kwalliya
irinsu sarƙa da sauransu. Ƙamshina kam ai har hawa kan mutane yakeyi, daka ganni
kaga cikakkaiyar bahaushiya jinin Fulani, tabbas a yau na sake yarda da babu
mummuna a duniya sai wanda ya munana kansa, idan har zaka tashi ka gyara kanka tofa
ka wuce a kiraka mai muni, dama can rashin gata da kulawane suka dadushe
sihirtaccen ƙyawuna mai cike da kwarjini.
Taron iya matane, dan acikin masarauta ma za'a yisa, su Ummah da danginsu duk
sun iso masarautar, hakama danginna na ɓangaren Uwa su Inna Zainabu dasu Momy harda
Aamilah, Aunty Shahudah dai ban gantaba, ƴan gidansu Boss ma kam inada tabbacin
ƙwai da kwarkwata ne a wajen nan. Babu abinda da dai za'a cema UBANGIJI sai godiya
a wannan al'amari, amma tabbas Bilkisu tazo da farin jini mai ban mamaki da tarin
alkairi. Iyayen ƙawayenta su Ummie, matansu Aliyu, abokan aikinsu ƴan station
ɗinsu, ƙawayenta na makaranta harma da waɗanda sukazo dalilin wane da wane duk suna
a wajen. Sai ƙarfe huɗu da rabi Gimbiya Sarauniyar gagara badau Munayatul-muna ta
fito riƙe da hannun amarya Bilkisu mai gadon zinari.
Ai a take wajen ya ɗauki ƙannan magana musamman ma ƴan gidansu Jawaad da ada
suke ɗaukar Bilkisu ba komaiba saboda yanda su Momy ke munanata da ƙasƙantar da ita
a garesu. Wasu sunɗan santa sama-sama wasuko sai a yau suke ganinta.
Ganin yanda ɗunbin mutane suka taru danni sai kawai naji hawaye sun zubomin
a kumatu, Zuhrah ce ta duƙa gabana inda ya kasance mazaunina ta shareminsu da
handkherchief tana murmushi, “Haba amarsu ai lokacin kuka baiyiba kinji, sai gobe
idan ALLAH ya kaimu kina kusa da Boss, da sun zubo ya lashe kayansa”. ta ƙare
maganar da kashemin ido. Hararta nayi ban iya cewa komaiba, sai dai fa maganar
datai sai da naji gabana yaɗan faɗi, dana tuna kuma ma ina period saina ɗanji sauƙi
a raina.
Ba'a ɓata lokaci wajen fara gudanar da abinda ya tara mutane ba, komai
kuma a nutse babu wata hayaniya, koda aka fara kiɗan ƙwarya ma a nutse ƴammata da
matan aurenma masu jini a jika keyin rawa, ina tsakkiya nikam anata zubamin liƙi,
Anum na liƙe dani wai tana gwagwaɗamin wai itama idan ta tashi aure zamuje Saudiyya
da masu kiɗan su mat. Murmushi kawai nayi mata dan ta bani dariya.
komai ya tafi cikin burgewa da kwanciyar hankali, kafin a koma yin hotuna
da kowa ke fatan yi da amarya da gimbiyar gagara badau. Zuwa magriba aka tashi.
Ni dai tunma kafin magriban muka bar wajen tare da Ummu da akoda yaushe tana
kusa dani idanunta akan kowa da zai iya raɓata. Dan tace itafa bata wani yarda da
kowa dake wajenba.

__________________

A ɓangaren su Jay suma sunacan suna nasu shagalin, sai dai su nasu sai bayan
sallar isha'i suka fara, suma iyasune maza zalla a wajen abokansa, su Aryaan duk
suna can dan kuwa dai sa'annine, sudai su Abdur-raheem, dasu Anuwar basu jeba
kasancewar su Jay yayunsune wannan shigar ba tasu bace, suna buƙatar sakewa kuma,
sunama can gidan Mami Munubiya suna shan shaftarsu hankali kwance.
Dauriya kawai Jay keyi, dan kansa ciwo yake masa matsanancin ciwo ma kuwa,
amma kasancewar yasan duk ɗunbin mutanennan dan shi

suka taru sai ya daure har zuwa goma na dare kafin ya gudu ɗakin da zai kwana a
hotel ɗin ya barsu, ko wanka baiyiba dan bai jima da yiba, kayansa kawai ya zame ya
faɗa saman gadon ya kwanta yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, cikin ransa ko
mamakin Bilkisu ya keyi, ƙaramar yarinya da ita sai shegen jan aji da miskilanci,
tunda ta tafi bata nemsaba, ta dawo ma haka. Wani ɓangare na zuciyarsa yace, ‘Kaida
haƙƙin sanin lafiyarta ke a kanka ka nemeta ne?’. Kansa ya dafe kawai da lumshe
idanu, kafin ya buɗe a hankali ya jawo wayarsa dan tunawa da saƙwanin da yasa a
turo masa.
Kasancewar datarsa a buɗe take duk sunma buɗe kansu da kansu, harda videos.
Ya sauki wani lallausan murmushi maiban mamaki daya sakani tunanin wai shin mi yake
kallo hakane?................✍

Jiya kun haɗan zafi yasin, waɗanda ban ɗaga kiransu ba suyi haƙuri man kaina ne ya
tsiyaye😂🚴🏼.

BARKA DA JUMA'A.

Musha weekend lafiya

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭😭🙏🏻.[12/25/2020, 6:15 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:


Page 38

.................Tinda su gimbiya munaya suka isa gidan,banda yabawa da tsari,da


kuma kokarin da jay yayi kan gidan,babu ajinda suke! sai dai wannan farine tas,
shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na sake
lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar goran
ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a gaibun
mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi, matashiyar
budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta duƙa gabana
tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai kuka, magana
take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin baki, na
kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta daban.
Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai sa'a
itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake buɗewa
a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani abu akan
fuskata.
A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune
tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya
kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri
ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma
juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon
fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci
tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina.
Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar,
babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar
bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar
wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda
saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har
yanzun........
Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa
zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta,
“Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a
maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai
jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”. Cikin sauke
ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya
kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da
alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba
rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka
iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin
bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa
dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike
ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu
kamar bansan sunaiba.

A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin
ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai,
munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo
gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema
makwancinsa.
Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun
alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin
bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata
kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo,
dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake

zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin,
“Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar
dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.

★★★★★★★

Washe gari tunda safe saiga kira daga Ummu, bayan duk mun gaisa da ita
tace a bani wayar. Daga can tace, “Yauwa ɗiyata ki shirya komai naki danke yau
zaki koma wajen Aunty da zama, tun jiya da daddare ma taso shigowa ta ɗaukeki, ki
nutsu ki kwantarmin da hankalinki ki fahimci dukkan abinda akeson ki fahimta kinji,
kinga lokaci ya ƙure sosai, inason kidawo ƙasarnan da cikakken sunanki BILKEESU MAI
GADON ZINARI ba Bilkisu kawai ba kinji”. Cike da jin nauyinta nace, “Insha ALLAHU
Ummu zanyi duk yanda kikeso”. “Yauwa ƴar albarka ALLAH ya bada sa'a kinji, jibi su
Amaturrahman zasu taho su saboda makaranta, ranar litinin su Safah zasu koma hutu”.
Kamar zanyi kuka nace, “Wayyo Ummu ni kaɗai za'a bari anan kenan?”. Murmushi tayi
har ina jiyo sautinsa, tace, “Ohni Munaya, anya kuwa randa zan miƙaki gidan miji
baza'a sha daruba? Karki damu itama Anum ɗinta zakuyi sa'anni, nasan zata ɗauke
miki kewarsu, kuma kedama zaki maida hankali ga abinda za'ai miki ai baƙya
buƙatarsu Amaturrahman kusa dake, koma sun zauna na ganin juna zakuyiba, inason
suzo domin shirye-shiye, ki basu duka numbers ɗin ƙawayenki karki manta”. Godiya
nai mata mukai sallama.

Kamar yanda ta umarceni haka na shirya dukkan abinda yake nawa, duk ji
nake babu daɗi, banso ace batare zamu koma dasu Safah ba, to amma yaya zanyi tunda
haka Ummu ta tsara.
Atare muka fito cikin shiga ta kamala, Marwah jaye da ɗan ƙaramin
akwatina. Gida baifi huɗu bane a tsakaninsu, dan haka tafiyar mintuna ƙalilan muka
iso gidan, Aunty Mahfuzah tai knocking haɗaɗɗiyar ƙofar falon, babu jimawa akazo
aka buɗe mana, wani irin tsammm naji jikina ya bada saboda cin karo da fuskar
budurwar jiya. Ta rungume Aunty Mahfuzah tana magana cikin harshen larabci, kafin
ta saketa ta rungume Amaturrahman da Meenal cikin tsalle irin na nayi kewarku, sai
dariya suke da faɗin yanda sukai missing ɗin junansu. Ta sake rungume su Safah suma
kafin ta juyi gareni, idanu taɗan waro tana nunani da faɗin, “Lah kece?” murmushi
nai mata kawai dan nikaɗai nasan mi nakeji, rungumeni tayi nima, sannan muka ƙarasa
falon daya gama jin kayan more rayuwa, ga sanyin AC da wani ƙamshi mai kashe
zuciya, tuni ɗan gumin da mukai harya tsane, labarin haɗuwarmu ta jiya taketa
bamasu Amaturrahman saboda tambayar da sukai na ina muka san juna?.
Fitowar matar gidan ya sakasu Safah miƙewa gaba ɗayansu harsu Amaturrahman
sukai kanta suka rungume, ba kowa bace face matar jiya data taimakeni, bayan sun
zauna ta gaisa da aunty Mahfuzah cikin salon gaisuwar larabawa, nima gaidata nai
kamar yanda na iya a nawa al'adar da tarbiyyar, kallon mamaki tai min dan da'alama
sai yanzune ta lura dani ma, da turanci take tambayata wai dama tare muke dasu
Safah?. Amaturrahman ce ta bata amsar da take buƙata harma da ƙara mata wadda bata
tambayaba. Murmushi taita saki da ƙaremin kallon da kowa yaketa mamakinsa, tana ta
maimaita sunana tamkar karatu a bakinta, bansaniba daɗi yaymatane kokuwa yaya oho,
dan nasan suna Bilkisu dai sunane sananne da zaka iya jinsa a kowacce duniyar
musulmai balle tace yaune ta fara jinsa sabo.
Ranar dai anan muka yini, har yamma su Amaturrahman basu koma can
gidanba, danni dai an tabbatarmin da nazo kenan bazan koma canba, acewartama a
daren zata kaini can makarantar da Ummu ta faɗamin. Banga saurayin nanba sai yamma
lis ya shigo sanye da farar jallabiya sol da mayafi irin wanda larabawa kansa akai
su saka baƙin abunnan a sama tamkar gammo, fara'ar da bangansa da itaba jiya sai
gata yau a fuskarsa yanamasu Amaturrahman magana da kulawa kamar yanda suma suke
masa, shima dai sai da ya nuna mamakin sake ganin nawa anan, su Amaturrahman da
basa hutawa sukai masa bayani dai-dai fahimtarsa, shima dai murmushin yayta saki
kafin ya nufi ɗakinsa wai zaiyi wanka.

Ban tashi shiga damuwaba sai da su Amaturrahman zasu koma gidan aunty Mahfuzah
su barni anan, hakan kuma na

nufin munyi sallama kenan dasu, sai naji ƙwalla ta cikamin idanu, sabo kenan turken
wawa. Suma kansu na lura basuso hakanba, amma sai suketa dariyar ƙaramin ƙwarin
gwiwa da tsokana. Haka mukai musu rakkiya har gidan sannan muka sake dawowa ni da
Anwar da Anum mai shegen surutu, yanayin rawan kanta sai yakemin kamanceceniya da
Nabeelah, gata da saurin magana saina nutsu sosai nake fahimtar magana idan tayi,
dama dai maganar tamu sai da turanci. A falo muka sake zama, cikin son fidda abinda
kecin raina na tambayi Anum da Anuwar da naga shima ya saki jiki dani yanzu kosun
taɓa zuwa ƙasarmu?. Anuwar ne kaɗai yace ya taɓa zuwa shima sau ɗaya tare dasu
Abdur-rahman, sunzo hajji wata shekara zasu koma ya bisu sukaje tare, satinsa biyu
acan ya dawo daga nan bai sake komawaba har yanzun, amma yanada burin sake zuwa
saboda ƙasar tai masa daɗi sosai.
Murmushin jin daɗi nayi sai dai a ƙasan raina ina mamakin to Mamansu fa? Ita
bata taɓa kaisu wajen nata danginba kenan kokuwa?, da ƙyar na ture tunanin a raina
muka cigaba da hira har sanda Umm-Anum ta fito cikin shiri, sanin inda zamuje ya
saka duk muka miƙe, tana gaba muna biye da ita har inda Anuwar ya ajiye motar da
zamu fita. Ni da ita baya muka shiga, Anuwar da Anum na gaba, dukda darene garin
zirga-zirga aketayi tamkar rana, gashi ko'ina ƙwanyar da wuta abin birgewa.
Mun iso wani haɗaɗɗen gini babba da nake ƙyautata zaton makarantarce, Anuwar
yay fakin duk muka fito, jin kamar ana kallona yasa na ɗago, Anuwar na kama
idanunsa tsaye a kaina ƙyam, saida gabana ya faɗin dan wlhy sai naga tamkar Boss,
murmushi yaymin. ɗauke kaina nai batare dana maida masa murtani ba, Umm-Anum dana
fahimci tana kallonmu ta hararesa da kama hannuna mukai gaba. Ina jiyo dariyarsa
shi da Anum, sai dai banajin mi suke faɗa cikin harshen larabci. Gaskiya ina sake
jinjina wannan tsananin kama a cikin raina, kai gaskiya inason sanin wani abu
dangane da mutanen nan, wannan kamar ta wuce kama kawai, anya kuwa babu wata alaƙa
tsakanin...........
Shigarmu wajenne ya katsemin tunanina, Bansan yanda zan fasalta muku
haɗuwar wannan makarantaba da tsarinta, na bama kowa dama ya ƙiyasta a cikin ransa
kawai, dan idan nace zan lissafo komai shafin yau da gobe duk anan zamu ƙare. Tuni
na zama baƙauya wajen kallon abubuwan birgewa, to lallai da ace munada irin waɗanan
makarantun da mace-macen aure ya ragu muma a yankunanmu, da ansamu sauƙin rikin
aurarraki a gidajenmu. Sashe na musamman aka buɗe mana mai madaidaicin falo guda da
ɗakuna biyu a ciki.
Fuskar Umm-Anum ɗauke da murmushi ta kalleni, “Ɗiyata anan zaki zauna, dan da
kaina zan miki aikinnan saboda ƙurewar lokaci, ga mamanki ɗinan sotake ta ganki
tamkar zinare”. Murmushi nai mata kaina a ƙasa dan haka kawai nakejin nauyinta, nai
mata godiya tare da addu'ar fatan alkairi. Batace komaiba sai murmushinta dake
kasheni taketa sakarmin.
Ɗaya daga cikin ɗakunan muka shiga, kayayyakine ajiye da ban fahimci
kona mineneba, ta umarceni dana cire kayana gaba ɗaya na shiga wani madaidaicin
kwami dake cike da ruwa da bazamu kirashi normal ruwa ba, ita kuma ta fita.
Dukkanin yanda ta umarceni nayi haka nayi babu musu, inayi ina ɗan waige-waige
tamkar mai tsoron wani ya shigo, saida na cire komaina kafin na fara saka ƙafa
cikin kwamin, ajiyar zuciya na sauke a hankali saboda ɗan ɗumi-ɗumin ruwan mai
warware gajiyar jiki, na ida saka ɗayar ƙafar sannan na shige gaba ɗayana,
sihirtaccen ƙamshin da ruwan keyine ya sakani lumshe idanu ina karanto addu'ar
godiya ga ALLAH da ni'imominsa masu yalwata ta fuskoki da dama ga ɗan adam. Sai da
nai kusan mintuna uku da zama sannan ta shigo da sallama, ta canja kayanta da wata
doguwar riga mai kama da leda, hannayenta sanye da safar hannu ta leda itama,
murmushi taimin ta tako inda nake. Ɗan kwalina daban cireba ta zame daga kaina, ta
warware gashina da Alhmdllh yanzu ya cika sosai kuma yanada tsayi gwargwado saboda
kulawar da naita bashi bisa koyarwar su Ummie tun muna boarding, wani ɗumi mai daɗi
naji ya ratsa kan nawa, hakan yasani kallon madubin dake gabana da nake iya hango
kaina da ita kanta.

Tace, “A cikin ruwannan zaki kwana, babu abinda zai sameki insha ALLAH
karkiji tsoro, ruwane mai ɗauke da sirrika kala-kala da duk macen da aka gyara dasu
dolene mijinta yasan ta isa mace, sirrikane na ƙamshi masu daraja a jikin ƴa mace,
ƙa'idar makarantarmu watanni ukune domin mace ta samu damar koyon abubuwa masu
yawa, ba sirrin gyaran jiki bane kawai mace tafi buƙata a rayuwar aure ɗiyata,
zakiga wata macen komai ta iya ta kuma ƙware, amma idan batasan yanda zataima miji
maganaba kawai sai ya rusa mata komai, dan wani namijin shi abinda ke ƙololuwar
birgesa ga mace shine iya magana, wani kuma a kallo kawai zaki gama dashi, wani
tafiya, wani girki, wani ƙamshi, wani shagwaɓa, wani kwalliya, wani kwanciya. Karki
sakama ranki cewa tarayya da miji a gado shine kawai farin cikin aure ko shikaɗaine
auren, hakan kuskurene, wani namijin ƙanƙanin abun da kika raina shike sakashi
farin ciki. Karkiyi tunanin gyara kanki yana nufin kin mallaki namiji ya zama naki
ke kaɗaine, macen data isa mace bata shakkar zama da kishiya ɗiyata, dan wani
lokacin zama da kishiya nasake bayyana darajar macene a wajen mijinta. Karkuma kiyi
tunanin babu wata mace data isa raɓar mijinki dan yana sonki ko kin iya komai, wani
namijin badan baya sonki yake miki kishiyaba ko yake budurwa, a'a halayyar san mace
fiye da ɗaya a jinin maza yake, ko bazasu ƙara aureba saisun kalla. kizama mai
gyara aurenki ta kowanne ɓangare, idan nace kowane ɓangare ina nufin kowanne fanni
hatta da ƴan uwansa da duk abinda ya shafesa. Inason ki cire komai a cikin ranki ki
nutsu ki bani dukkanin hankalinki a kwanakinan goma sha biyu da zamuyi tare, sonake
komai na cikinsa ya zama tamkar rubutu bisa dutse a cikin ƙwaƙwalwarki, ki ɗaukeni
tamkar mahaifiyarki, kuma ƙawarki aminiya wadda zaki iya magana kowacce iri da ita
batare da kinji kunya ba, inhar kika riƙe duk abinda zaki koya a kwanakinan ina mai
tabbatar miki bazaki taɓa goguwa a zuciyat mijinki ba koda zai auri mata uku ku
zama huɗu bayan ke”.
Idona a risine na ɗaga mata kai alamar to, inajiyo sautun murmushinta
itama. Abu ta fara shafamin a fuska tana cigaba da min magana cikin nutsuwa, sosai
kunya ta lulluɓeni, dan abubuwane masu matuƙar nauyi a gareni take faɗa a buɗe, ta
haɗe fuska a yanzu babu wasa tattare da ita ko kaɗan. Saida ta gama tsaf sannan ta
fita suka sake dawowa da wata mata. Matar ta nunamin da faɗin, “zata zauna dake
anan, ni zan koma gida sai da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”. Kaina na jinjina
mata dan ta hanani magana tunda ta shafamin abin fuskarnan.

Duk yanda zan baku labarin abinda ya gudana a kwanakinan da wahala ku


iya fahimtata, abubuwan dana koya kam ba'a magana, sam Umm-Anum bata wasa dani idan
akazo ɓangaren abinda zan iya jin kunyarta balle naga fuskar yin sakaci da abinda
ake koyamin, tsaye take kaina ɗari bisa ɗari, komai buɗemin shi take babu hijjabi,
aduk lokacin da takemin bayani aka abinda yafi ƙarfin kaina tamke fuska take tamau
babu wasa, kai jama'a hatta da salon tafiya ba'a barniba sai da aka koyan, komai a
tsare yake. Matar da take bari ta kwana dani kasa haƙuri tayi ranar dai take
tambayata wai kodai ni ƴar uwar Umm-Anum ce? Dan ita yanda take ganin tanamin ya
ninka yanda takema ɗalibanta fiye da zato. An kawoni ɗaki na musamman, sannan komai
ba'a sakani cikin ɗalibai ni kaɗai ake koyamashi a nutse, daɗin daɗawa da kanta
take min komai bata yadda kowa yayminba sai abubuwan da ba'a rasaba, dan takance
kowa a rayuwa da irin basirar da ALLAH yay masa, abinda suma sauran malaman
makarantar suke koyamin zai amfanar dani ta fannoni da dama. Murmushi nayi nidai
bance komaiba, dan nikaɗai nasan mi nakeji game da matar nan, ita kanta lokuta da
dama nakan kamata ta shagala da kallona, kallo maiban mamaki, kallo irin na shagala
da zurfi ason tunano wani abu, idan tai irin wannan zurfin kuma zakaga daga ƙarshe
ta dafe kanta tamkar zata fita cikin hayyacinta. Akwai randa naga kallon har yaso
yimin yawa, sannan ni kaina yanda takemin ɗin nasan ba kamar yanda takema kowa
baneba, tana sakin jiki dani fiye da hasashen mai hasashe. Akwai randa tazo tana
koyamin

girki sai muke ɗan hira kaɗan-kaɗan, cikin dabara nake tambayarta ko zasuje ƙasarmu
nan kusa?. Shiru tai bata bani amsaba, na kasa daurewa dai na sake mata tambayar
cike da ladabi. Yanda ta juyo ta kalleni fuska a haɗe saida naso firgita. Kaina na
duƙar ƙasa ina faɗin, “Kiyi haƙuri dan ALLAH Ummu, bansan tambayar zata ɓata ranki
ba”. Sautin murmushinta na jiyo, hakan yasa na ɗan ɗago na kalleta, ta ajiye
cokalin hannunta tazo ta kama hannayena, murya a sanyaye tace, “Ɗiyata ba laifi
kikayiminba, ƙasar takuma ni ban taɓa zuwantaba ai, duk amintakar dakika gani
tsakanina da ƙanwata Gimbiya Munaya ban taɓa ziyartarta ba, sai dai ita idan tazo
nan mu haɗu, duk lokacin danai yunƙurin zuwa nakan tsinci kainane a wani mummunan
hali da baida fassara”. Tana gama faɗa ta saki hannuna ta juyamin baya, aikin da
mukeyi ta cigaba dayi batare da ta sake min maganarba.
Ajiyar zuciya na ɗan sauke hawaye na ziraromin, haka kawai yanda tayi maganar
sai naji abun daban, to amma ai Ummu ta sanarmin itaɗin ƴar ƙasarmu ce, sanadin
neman magani ya kawota nan hartai aure, itakuma gashi yanzun tace bama ta taɓa zuwa
canba, anya kuwa babu wani sirrin dake ɓoye?.......
Ajiyar zuciya na sauke da saurin kallonta jin ta taɓanu, tace, “Kinama
fahimtar abinda nakeyi kuwa?”. Da sauri na ɗaga mata kai alamar eh na tattara
hankalina gareta baki ɗaya.

____________________________

A ɓangaren Jawaad ma dai shirye-shirye sun kankama, an gama gyaran gida


tsaf, ya canja kamanni gaba ɗaya tamkar bashiba, amarya kawai yake jira ta shigo
cikinsa. Gaba ɗaya a tsakaninan a busy yake matuƙa, ga aiki ga shirye-shiryen biki
dasu Jabeer ketayi naban mamaki, dan gayya suke ta gaske da gayya tamkar wannan
shine auren farko da Jawaad ɗin zaiyi. Shidai ya zuba musu idone kawai yana kallon
ikon ALLAH, dan dayay magana ca sukai babu ruwansa, kawai dai yama shirya dan bai
isa cewa bazaije wajen abinda suke shiryawanba ehe. Bai sake musu maganarba kuwa ya
cigaba da nasa harkokin, maganar kayan da za'a saka a gidan kuwa gimbiya Munaya
tace Takawa yace zaiyi komai, kayan kicin kuwa itace zatayi. Da yay mata maganar
lefe tace masa ya dakata, zasu nema Dady suyi magana, sai ana saura kwana biyu
tarewar za'a kaisu can gidan Dad ɗin dan sune sukafi cancanta da amsar lefen,
koyayane zasu bashi matsayinsa na uba kodan ɗawainiyar da yay da Bilkisun. Jawaad
baice komaiba shi dai sai ALLAH ya kaimu.

A yau tunda safe Su Amaturrahman suka shirya yima Mami (Munubiya) rakkiya
gidan kamar yanda Gimbiya da Takawa suka buƙata, zataje su haɗu da kamfanin da zasu
shirya gidan. bayan sun duba saisu zaɓa mata kalar data dace a tsara komai yanda ya
dace..............✍
Bara dai na baku hakanan, inata ƙoƙarin typing ɗin bayan tafiyar baƙi amma kiraye-
kirayen waya ya hanani nutsuwar yi da yawa, takaima harna daina ɗaga wayoyin mutane
wlhy🤦🏻😑😓.Bilyn Abdull 📚:
Page 36

.................Tabbas muryar iri ɗayace, kamanin ma ɗayane, sai dai wannan farine
tas, shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na
sake lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar
goran ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a
gaibun mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi,
matashiyar budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta
duƙa gabana tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai
kuka, magana take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin
baki, na kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta
daban. Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai
sa'a itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake
buɗewa a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani
abu akan fuskata.
A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune
tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya
kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri
ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma
juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon
fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci
tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina.
Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar,
babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar
bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar
wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda
saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har
yanzun........
Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa
zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta,
“Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a
maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai
jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”. Cikin sauke
ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya
kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da
alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba
rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka
iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin
bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa
dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike
ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu
kamar bansan sunaiba.

A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin
ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai,
munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo
gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema
makwancinsa.
Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun
alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin
bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata
kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo,
dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake

zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin,
“Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar
dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.

★★★★★★★

Washe gari tunda safe saiga kira daga Ummu, bayan duk mun gaisa da ita
tace a bani wayar. Daga can tace, “Yauwa ɗiyata ki shirya komai naki danke yau
zaki koma wajen Aunty da zama, tun jiya da daddare ma taso shigowa ta ɗaukeki, ki
nutsu ki kwantarmin da hankalinki ki fahimci dukkan abinda akeson ki fahimta kinji,
kinga lokaci ya ƙure sosai, inason kidawo ƙasarnan da cikakken sunanki BILKEESU MAI
GADON ZINARI ba Bilkisu kawai ba kinji”. Cike da jin nauyinta nace, “Insha ALLAHU
Ummu zanyi duk yanda kikeso”. “Yauwa ƴar albarka ALLAH ya bada sa'a kinji, jibi su
Amaturrahman zasu taho su saboda makaranta, ranar litinin su Safah zasu koma hutu”.
Kamar zanyi kuka nace, “Wayyo Ummu ni kaɗai za'a bari anan kenan?”. Murmushi tayi
har ina jiyo sautinsa, tace, “Ohni Munaya, anya kuwa randa zan miƙaki gidan miji
baza'a sha daruba? Karki damu itama Anum ɗinta zakuyi sa'anni, nasan zata ɗauke
miki kewarsu, kuma kedama zaki maida hankali ga abinda za'ai miki ai baƙya
buƙatarsu Amaturrahman kusa dake, koma sun zauna na ganin juna zakuyiba, inason
suzo domin shirye-shiye, ki basu duka numbers ɗin ƙawayenki karki manta”. Godiya
nai mata mukai sallama.

Kamar yanda ta umarceni haka na shirya dukkan abinda yake nawa, duk ji
nake babu daɗi, banso ace batare zamu koma dasu Safah ba, to amma yaya zanyi tunda
haka Ummu ta tsara.
Atare muka fito cikin shiga ta kamala, Marwah jaye da ɗan ƙaramin
akwatina. Gida baifi huɗu bane a tsakaninsu, dan haka tafiyar mintuna ƙalilan muka
iso gidan, Aunty Mahfuzah tai knocking haɗaɗɗiyar ƙofar falon, babu jimawa akazo
aka buɗe mana, wani irin tsammm naji jikina ya bada saboda cin karo da fuskar
budurwar jiya. Ta rungume Aunty Mahfuzah tana magana cikin harshen larabci, kafin
ta saketa ta rungume Amaturrahman da Meenal cikin tsalle irin na nayi kewarku, sai
dariya suke da faɗin yanda sukai missing ɗin junansu. Ta sake rungume su Safah suma
kafin ta juyi gareni, idanu taɗan waro tana nunani da faɗin, “Lah kece?” murmushi
nai mata kawai dan nikaɗai nasan mi nakeji, rungumeni tayi nima, sannan muka ƙarasa
falon daya gama jin kayan more rayuwa, ga sanyin AC da wani ƙamshi mai kashe
zuciya, tuni ɗan gumin da mukai harya tsane, labarin haɗuwarmu ta jiya taketa
bamasu Amaturrahman saboda tambayar da sukai na ina muka san juna?.
Fitowar matar gidan ya sakasu Safah miƙewa gaba ɗayansu harsu Amaturrahman
sukai kanta suka rungume, ba kowa bace face matar jiya data taimakeni, bayan sun
zauna ta gaisa da aunty Mahfuzah cikin salon gaisuwar larabawa, nima gaidata nai
kamar yanda na iya a nawa al'adar da tarbiyyar, kallon mamaki tai min dan da'alama
sai yanzune ta lura dani ma, da turanci take tambayata wai dama tare muke dasu
Safah?. Amaturrahman ce ta bata amsar da take buƙata harma da ƙara mata wadda bata
tambayaba. Murmushi taita saki da ƙaremin kallon da kowa yaketa mamakinsa, tana ta
maimaita sunana tamkar karatu a bakinta, bansaniba daɗi yaymatane kokuwa yaya oho,
dan nasan suna Bilkisu dai sunane sananne da zaka iya jinsa a kowacce duniyar
musulmai balle tace yaune ta fara jinsa sabo.
Ranar dai anan muka yini, har yamma su Amaturrahman basu koma can
gidanba, danni dai an tabbatarmin da nazo kenan bazan koma canba, acewartama a
daren zata kaini can makarantar da Ummu ta faɗamin. Banga saurayin nanba sai yamma
lis ya shigo sanye da farar jallabiya sol da mayafi irin wanda larabawa kansa akai
su saka baƙin abunnan a sama tamkar gammo, fara'ar da bangansa da itaba jiya sai
gata yau a fuskarsa yanamasu Amaturrahman magana da kulawa kamar yanda suma suke
masa, shima dai sai da ya nuna mamakin sake ganin nawa anan, su Amaturrahman da
basa hutawa sukai masa bayani dai-dai fahimtarsa, shima dai murmushin yayta saki
kafin ya nufi ɗakinsa wai zaiyi wanka.
Ban tashi shiga damuwaba sai da su Amaturrahman zasu koma gidan aunty Mahfuzah
su barni anan, hakan kuma na

nufin munyi sallama kenan dasu, sai naji ƙwalla ta cikamin idanu, sabo kenan turken
wawa. Suma kansu na lura basuso hakanba, amma sai suketa dariyar ƙaramin ƙwarin
gwiwa da tsokana. Haka mukai musu rakkiya har gidan sannan muka sake dawowa ni da
Anwar da Anum mai shegen surutu, yanayin rawan kanta sai yakemin kamanceceniya da
Nabeelah, gata da saurin magana saina nutsu sosai nake fahimtar magana idan tayi,
dama dai maganar tamu sai da turanci. A falo muka sake zama, cikin son fidda abinda
kecin raina na tambayi Anum da Anuwar da naga shima ya saki jiki dani yanzu kosun
taɓa zuwa ƙasarmu?. Anuwar ne kaɗai yace ya taɓa zuwa shima sau ɗaya tare dasu
Abdur-rahman, sunzo hajji wata shekara zasu koma ya bisu sukaje tare, satinsa biyu
acan ya dawo daga nan bai sake komawaba har yanzun, amma yanada burin sake zuwa
saboda ƙasar tai masa daɗi sosai.
Murmushin jin daɗi nayi sai dai a ƙasan raina ina mamakin to Mamansu fa? Ita
bata taɓa kaisu wajen nata danginba kenan kokuwa?, da ƙyar na ture tunanin a raina
muka cigaba da hira har sanda Umm-Anum ta fito cikin shiri, sanin inda zamuje ya
saka duk muka miƙe, tana gaba muna biye da ita har inda Anuwar ya ajiye motar da
zamu fita. Ni da ita baya muka shiga, Anuwar da Anum na gaba, dukda darene garin
zirga-zirga aketayi tamkar rana, gashi ko'ina ƙwanyar da wuta abin birgewa.
Mun iso wani haɗaɗɗen gini babba da nake ƙyautata zaton makarantarce, Anuwar
yay fakin duk muka fito, jin kamar ana kallona yasa na ɗago, Anuwar na kama
idanunsa tsaye a kaina ƙyam, saida gabana ya faɗin dan wlhy sai naga tamkar Boss,
murmushi yaymin. ɗauke kaina nai batare dana maida masa murtani ba, Umm-Anum dana
fahimci tana kallonmu ta hararesa da kama hannuna mukai gaba. Ina jiyo dariyarsa
shi da Anum, sai dai banajin mi suke faɗa cikin harshen larabci. Gaskiya ina sake
jinjina wannan tsananin kama a cikin raina, kai gaskiya inason sanin wani abu
dangane da mutanen nan, wannan kamar ta wuce kama kawai, anya kuwa babu wata alaƙa
tsakanin...........
Shigarmu wajenne ya katsemin tunanina, Bansan yanda zan fasalta muku
haɗuwar wannan makarantaba da tsarinta, na bama kowa dama ya ƙiyasta a cikin ransa
kawai, dan idan nace zan lissafo komai shafin yau da gobe duk anan zamu ƙare. Tuni
na zama baƙauya wajen kallon abubuwan birgewa, to lallai da ace munada irin waɗanan
makarantun da mace-macen aure ya ragu muma a yankunanmu, da ansamu sauƙin rikin
aurarraki a gidajenmu. Sashe na musamman aka buɗe mana mai madaidaicin falo guda da
ɗakuna biyu a ciki.
Fuskar Umm-Anum ɗauke da murmushi ta kalleni, “Ɗiyata anan zaki zauna, dan da
kaina zan miki aikinnan saboda ƙurewar lokaci, ga mamanki ɗinan sotake ta ganki
tamkar zinare”. Murmushi nai mata kaina a ƙasa dan haka kawai nakejin nauyinta, nai
mata godiya tare da addu'ar fatan alkairi. Batace komaiba sai murmushinta dake
kasheni taketa sakarmin.
Ɗaya daga cikin ɗakunan muka shiga, kayayyakine ajiye da ban fahimci
kona mineneba, ta umarceni dana cire kayana gaba ɗaya na shiga wani madaidaicin
kwami dake cike da ruwa da bazamu kirashi normal ruwa ba, ita kuma ta fita.
Dukkanin yanda ta umarceni nayi haka nayi babu musu, inayi ina ɗan waige-waige
tamkar mai tsoron wani ya shigo, saida na cire komaina kafin na fara saka ƙafa
cikin kwamin, ajiyar zuciya na sauke a hankali saboda ɗan ɗumi-ɗumin ruwan mai
warware gajiyar jiki, na ida saka ɗayar ƙafar sannan na shige gaba ɗayana,
sihirtaccen ƙamshin da ruwan keyine ya sakani lumshe idanu ina karanto addu'ar
godiya ga ALLAH da ni'imominsa masu yalwata ta fuskoki da dama ga ɗan adam. Sai da
nai kusan mintuna uku da zama sannan ta shigo da sallama, ta canja kayanta da wata
doguwar riga mai kama da leda, hannayenta sanye da safar hannu ta leda itama,
murmushi taimin ta tako inda nake. Ɗan kwalina daban cireba ta zame daga kaina, ta
warware gashina da Alhmdllh yanzu ya cika sosai kuma yanada tsayi gwargwado saboda
kulawar da naita bashi bisa koyarwar su Ummie tun muna boarding, wani ɗumi mai daɗi
naji ya ratsa kan nawa, hakan yasani kallon madubin dake gabana da nake iya hango
kaina da ita kanta.
Tace, “A cikin ruwannan zaki kwana, babu abinda zai sameki insha ALLAH
karkiji tsoro, ruwane mai ɗauke da sirrika kala-kala da duk macen da aka gyara dasu
dolene mijinta yasan ta isa mace, sirrikane na ƙamshi masu daraja a jikin ƴa mace,
ƙa'idar makarantarmu watanni ukune domin mace ta samu damar koyon abubuwa masu
yawa, ba sirrin gyaran jiki bane kawai mace tafi buƙata a rayuwar aure ɗiyata,
zakiga wata macen komai ta iya ta kuma ƙware, amma idan batasan yanda zataima miji
maganaba kawai sai ya rusa mata komai, dan wani namijin shi abinda ke ƙololuwar
birgesa ga mace shine iya magana, wani kuma a kallo kawai zaki gama dashi, wani
tafiya, wani girki, wani ƙamshi, wani shagwaɓa, wani kwalliya, wani kwanciya. Karki
sakama ranki cewa tarayya da miji a gado shine kawai farin cikin aure ko shikaɗaine
auren, hakan kuskurene, wani namijin ƙanƙanin abun da kika raina shike sakashi
farin ciki. Karkiyi tunanin gyara kanki yana nufin kin mallaki namiji ya zama naki
ke kaɗaine, macen data isa mace bata shakkar zama da kishiya ɗiyata, dan wani
lokacin zama da kishiya nasake bayyana darajar macene a wajen mijinta. Karkuma kiyi
tunanin babu wata mace data isa raɓar mijinki dan yana sonki ko kin iya komai, wani
namijin badan baya sonki yake miki kishiyaba ko yake budurwa, a'a halayyar san mace
fiye da ɗaya a jinin maza yake, ko bazasu ƙara aureba saisun kalla. kizama mai
gyara aurenki ta kowanne ɓangare, idan nace kowane ɓangare ina nufin kowanne fanni
hatta da ƴan uwansa da duk abinda ya shafesa. Inason ki cire komai a cikin ranki ki
nutsu ki bani dukkanin hankalinki a kwanakinan goma sha biyu da zamuyi tare, sonake
komai na cikinsa ya zama tamkar rubutu bisa dutse a cikin ƙwaƙwalwarki, ki ɗaukeni
tamkar mahaifiyarki, kuma ƙawarki aminiya wadda zaki iya magana kowacce iri da ita
batare da kinji kunya ba, inhar kika riƙe duk abinda zaki koya a kwanakinan ina mai
tabbatar miki bazaki taɓa goguwa a zuciyat mijinki ba koda zai auri mata uku ku
zama huɗu bayan ke”.
Idona a risine na ɗaga mata kai alamar to, inajiyo sautun murmushinta
itama. Abu ta fara shafamin a fuska tana cigaba da min magana cikin nutsuwa, sosai
kunya ta lulluɓeni, dan abubuwane masu matuƙar nauyi a gareni take faɗa a buɗe, ta
haɗe fuska a yanzu babu wasa tattare da ita ko kaɗan. Saida ta gama tsaf sannan ta
fita suka sake dawowa da wata mata. Matar ta nunamin da faɗin, “zata zauna dake
anan, ni zan koma gida sai da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”. Kaina na jinjina
mata dan ta hanani magana tunda ta shafamin abin fuskarnan.

Duk yanda zan baku labarin abinda ya gudana a kwanakinan da wahala ku


iya fahimtata, abubuwan dana koya kam ba'a magana, sam Umm-Anum bata wasa dani idan
akazo ɓangaren abinda zan iya jin kunyarta balle naga fuskar yin sakaci da abinda
ake koyamin, tsaye take kaina ɗari bisa ɗari, komai buɗemin shi take babu hijjabi,
aduk lokacin da takemin bayani aka abinda yafi ƙarfin kaina tamke fuska take tamau
babu wasa, kai jama'a hatta da salon tafiya ba'a barniba sai da aka koyan, komai a
tsare yake. Matar da take bari ta kwana dani kasa haƙuri tayi ranar dai take
tambayata wai kodai ni ƴar uwar Umm-Anum ce? Dan ita yanda take ganin tanamin ya
ninka yanda takema ɗalibanta fiye da zato. An kawoni ɗaki na musamman, sannan komai
ba'a sakani cikin ɗalibai ni kaɗai ake koyamashi a nutse, daɗin daɗawa da kanta
take min komai bata yadda kowa yayminba sai abubuwan da ba'a rasaba, dan takance
kowa a rayuwa da irin basirar da ALLAH yay masa, abinda suma sauran malaman
makarantar suke koyamin zai amfanar dani ta fannoni da dama. Murmushi nayi nidai
bance komaiba, dan nikaɗai nasan mi nakeji game da matar nan, ita kanta lokuta da
dama nakan kamata ta shagala da kallona, kallo maiban mamaki, kallo irin na shagala
da zurfi ason tunano wani abu, idan tai irin wannan zurfin kuma zakaga daga ƙarshe
ta dafe kanta tamkar zata fita cikin hayyacinta. Akwai randa naga kallon har yaso
yimin yawa, sannan ni kaina yanda takemin ɗin nasan ba kamar yanda takema kowa
baneba, tana sakin jiki dani fiye da hasashen mai hasashe. Akwai randa tazo tana
koyamin

girki sai muke ɗan hira kaɗan-kaɗan, cikin dabara nake tambayarta ko zasuje ƙasarmu
nan kusa?. Shiru tai bata bani amsaba, na kasa daurewa dai na sake mata tambayar
cike da ladabi. Yanda ta juyo ta kalleni fuska a haɗe saida naso firgita. Kaina na
duƙar ƙasa ina faɗin, “Kiyi haƙuri dan ALLAH Ummu, bansan tambayar zata ɓata ranki
ba”. Sautin murmushinta na jiyo, hakan yasa na ɗan ɗago na kalleta, ta ajiye
cokalin hannunta tazo ta kama hannayena, murya a sanyaye tace, “Ɗiyata ba laifi
kikayiminba, ƙasar takuma ni ban taɓa zuwantaba ai, duk amintakar dakika gani
tsakanina da ƙanwata Gimbiya Munaya ban taɓa ziyartarta ba, sai dai ita idan tazo
nan mu haɗu, duk lokacin danai yunƙurin zuwa nakan tsinci kainane a wani mummunan
hali da baida fassara”. Tana gama faɗa ta saki hannuna ta juyamin baya, aikin da
mukeyi ta cigaba dayi batare da ta sake min maganarba.
Ajiyar zuciya na ɗan sauke hawaye na ziraromin, haka kawai yanda tayi maganar
sai naji abun daban, to amma ai Ummu ta sanarmin itaɗin ƴar ƙasarmu ce, sanadin
neman magani ya kawota nan hartai aure, itakuma gashi yanzun tace bama ta taɓa zuwa
canba, anya kuwa babu wani sirrin dake ɓoye?.......
Ajiyar zuciya na sauke da saurin kallonta jin ta taɓanu, tace, “Kinama
fahimtar abinda nakeyi kuwa?”. Da sauri na ɗaga mata kai alamar eh na tattara
hankalina gareta baki ɗaya.

____________________________

A ɓangaren Jawaad ma dai shirye-shirye sun kankama, an gama gyaran gida


tsaf, ya canja kamanni gaba ɗaya tamkar bashiba, amarya kawai yake jira ta shigo
cikinsa. Gaba ɗaya a tsakaninan a busy yake matuƙa, ga aiki ga shirye-shiryen biki
dasu Jabeer ketayi naban mamaki, dan gayya suke ta gaske da gayya tamkar wannan
shine auren farko da Jawaad ɗin zaiyi. Shidai ya zuba musu idone kawai yana kallon
ikon ALLAH, dan dayay magana ca sukai babu ruwansa, kawai dai yama shirya dan bai
isa cewa bazaije wajen abinda suke shiryawanba ehe. Bai sake musu maganarba kuwa ya
cigaba da nasa harkokin, maganar kayan da za'a saka a gidan kuwa gimbiya Munaya
tace Takawa yace zaiyi komai, kayan kicin kuwa itace zatayi. Da yay mata maganar
lefe tace masa ya dakata, zasu nema Dady suyi magana, sai ana saura kwana biyu
tarewar za'a kaisu can gidan Dad ɗin dan sune sukafi cancanta da amsar lefen,
koyayane zasu bashi matsayinsa na uba kodan ɗawainiyar da yay da Bilkisun. Jawaad
baice komaiba shi dai sai ALLAH ya kaimu.

A yau tunda safe Su Amaturrahman suka shirya yima Mami (Munubiya) rakkiya
gidan kamar yanda Gimbiya da Takawa suka buƙata, zataje su haɗu da kamfanin da zasu
shirya gidan. bayan sun duba saisu zaɓa mata kalar data dace a tsara komai yanda ya
dace..............✍

Bara dai na baku hakanan, inata ƙoƙarin typing ɗin bayan tafiyar baƙi amma kiraye-
kirayen waya ya hanani nutsuwar yi da yawa, takaima harna daina ɗaga wayoyin mutane
wlhy🤦🏻😑😓.
[12/29/2020, 1:33 PM] HASNA ✍🏻
: Typing

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Bilyn Abdull 📚:
Page 38

..................Shagulgulan biki sun cigaba da gudana a washe gari tamkar yanda


aka tsara, su Ummah babba sunyi yinin biki suma matsayin iyayen ango, kafin zuwa
la'asar su ɗunguma zuwa masarauta domin halartar walima da gimbiya ta shirya itama.
Walima kam ta ƙayatar fiye da zato, amarya tasha ƙyau cikin shadda pink mai duhu.
Inda malamai magada annabawa suka gudanar da wa'azi mai kashe jiki da ɓargo,
bilkisu kam dai ansha kuka, idanu sun ƙara girma. Tun su Zuhrah dake zaune kusa da
ita suna mata dariya har dai suka koma lallashinta suma suna sharar hawayen dan
jikinsu duk sai yay sanyi ƙalau. An tashine gab da magriba, dan haka kowa yana yin
salla shirin tafiya dinner ya fara. Amarya ma wanka aka sakata ta shiga.
Gaba ɗaya jikina a sanyaye yake, tunani da fargaba duk sun cika
zuciyata, yau ni Bilkisu nice za'a ɗauka akai gidan boss matsayin matarsa ta aure,
aure ba yawo ba, idan naje shike nan natafi din din din, duk da nasan ba sonsa
nakeba, shima kuma bason nawa ya keba na ɗaura ɗammarar masa biyyayya insha ALLAH,
zanyi haƙuri tamkar yanda kowa ke faɗamin zaman aure haƙurine, zanyi biyayya a
garesa matsayinsa na mijina shugabana, zanyi aiki da dukkan dabarun Umm-Anum da
gambiya suka ɗorani akai domin samun zaman lafiya a gidana koda ace bazai soni ba.
tausayinsa nakeji har cikin raina yanzun, dan a daren jiya munyi zama na musamman
da Ummu inda muka tattauna game da kamanninsa da Anuwar harma da Umm-Anum ta
abubuwa da dama. Ta tabbatar min nice ya dace nai wannan aikin na bincikar abinda
ya shafesa ko tanan zasu iya fahimtar idan akwai alaƙar da duk muke zargi dan
kamannin sun wuce kama akwai dangantakar jini dole, bansan komai na abinda ya shafi
family nasa ba, sai ɗan abinda ba'a rasaba shima iyakarsa daga wajen su Mom ne da
da rashin jituwa tsakaninsa da Yah Qaseem, amma a raina nima tunda muka haɗu da
Umm-Anum nakeji abubuwa da dama nazomin a rai game da shi......... Da wannan
tunane-tunanen na tsaftace jikina na fito, kasancewar ba salla zanyiba zaman min
kwalliya akayi.
Tun ina jiyo hayaniyar ƙawayena dake ɗakin su Amaturrahman suna shiryawa har
naji tsit, alamar dai sun fice dan zuwa yanzu har anyi sallar isha'i. Basan yaya
zan musalta muku irin ƙyawun da nayiba yauma, amma na bama kowa damar ya hasasoni
cikin zuciyarsa, kwalliyata ta yau ta kasance harda alƙyabar da Mommah ta bani
matsayin ƙyautarta, basai an faɗaba, a gani da ido kaɗai ya isa amsa ga mai kallo
cewar an sayeta da kuɗaɗe masu nauyi da darajar gaske. Suna cikin gyaramin
alƙyabbar da santin ƙyawun da nayi aunty Samha ta shigo.
“Wow, masha ALLAH amaryar ƙamshi” ta faɗa tana rungumeni, ta ɗagoni tana
kallona da cigaba da faɗin, “Wannan ai saiki rikita angon yace an fasa dinner ɗin”.
Dariya waɗanda sukaimin kwalliyar sukayi, ni dai kaina a ƙasa ban yarda na kalleta
bama dan tasa naji kunya, gashi kukane keta ƙoƙarin tasomin ina dannewa. Itace ta
kama hannuna muka fice, ganin ba'a kaini wajen Ummu ba sai nayi tunanin za'a sake
dawo dani nan kenan, ƙilama sai gobe idan ALLAH ya kaimu. A take naji farin ciki ya
wani lulluɓeni. Ko ina ƙwanyar yake da haske a masarauta shiyyasa koda muka fito
dukda kaina a ƙasa yake ina kallon inda muka nufa.
Mun tsaya dai-dai motar da na hango Oga Jabeer jingine yana waya tun
fitowarmu, yana sanye da shadda ƴar ubansu ruwan madara. Yana ganin mun ƙaraso ya
ajiye wayar yana murmushi da faɗin, “Aunty Samha aini da har ina shirin bin
bayanku, dan naga baƙwa son bamu amaryarnan kamar”.
Murmushi tayi mai sauti tana gyaramin hular alƙyabar, “To gaskiya badan
munasoba zamu baku, dan bamu gaji da ɗiyarmu ba, amma yaya muka iya, wannan shine
girman”. Oga Jabeer na ƴar dariya ya buɗe ƙofar motar da cewa, “Aure yaƙin mata”.
Tace, “Har mazan ma”.
Daddaɗan ƙamshin turarensa da na sani daine ya fara tarbata da sallama, na
shaƙa na lumshe idanu ina ƙoƙarin dai-daita bugun zuciyata da kalato yawun da zan
jiƙa maƙoshina da ya bushe, sai da na zauna da ƙyau Mah-mah ta gyaramin alƙyabar
sannan na tsinkayi muryarsa yana gaisheta cike da mutun tawa, sai da suka gama
gaisuwar s

annan Oga Jabeer ya rufe motar ya shigo shima, itama motar da zasu tafi a ciki ta
nufa ta shiga.
“Ina yini?”. Na faɗa a hankali har banyi zaton zaima jini ba. Shiru banji
ya amsaba, kuma tabbas inaji a jikina idonsa a kaina suke, dan ina jinsu har cikin
ɓargona. kaɗan juya na kalli sashen da yake dan in tabbatar da bai jinin ba kokuwa
ƴan wulaƙancinne a kusa.....
Ina ɗagowa idanuna na shigewa cikin nasa, saurin maida kaina ƙasa nai ina
ɗan ƙunƙuni a cikin raina batare da nasan bakina naɗan motsawaba ashe, ‘mutum babu
abinda ya iya sai kallo, har sai an hango maka muni’.
Jawaad dake kallon yanda bakinta dake ta shining na ɗan lipstick ɗin da
aka sanya mata ya lumshe idanu a hankali yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, maida
kansa yay jikin sit ya kwantar yana maijin takaicin yarda da yay da zuwan wannan
dinner ɗin banzar, yanzufa kowa sai yaga wannan ƙyawun da tai ko?. Ware idanunsa ya
sakeyi a kanta yana binta da wani irin sassanyar kallo, gaba ɗaya ƙamshin turarenta
ya saukarma gaɓɓansa da kasala.........
“Ehhgy egeehhmm!”. Jabeer yay gyaran murya. Haɗe fuska jay yayi ya balla
masa harara tare da ɗauke kansa ya maida gefe bai dai ce komaiba. Jabeer ya haɗiye
dariyar dake cinsa daƙyar sannan ya tada motar suka fice.

Shiru motar tayi bakajin motsin komai sai na ac da ƙamshin turarukanmu,


tunda na gaida Oga Jabeer nima ban sake ko ɗaga kai na kalli inda sukeba, dodon
nawa kam tun gaisuwarsa da aunty Samha ban sakejin ya firta komai ba shima, anata
kiran wayarsama yayi kunnen uwar shegu tamkar ba yaji ana kiran. Mintuna ƙalilan
muka iso wajen taron, inda muka taras da abokansa dasu Ummie tsaitsaye alamar
isowarmu suke jira.
Jabeer da yay fakin ya juyo ya kalli Jay. “ku zama cikin shiri boss, bara
na musu magana”. Kai kawai ya ɗaga masa, shi kuma ya fice. Kusan sakanni ashirin da
fitar Oga Jabeer babu wanda ya motsa a cikinmu daga ni har shi, inata ɗan juya
zoben yatsana ne dan gaba ɗaya a takure nakejin zaman namu kusa da juna.
“Bana son rawa” na tsinkayi muryarsa ƙasa-ƙasa saitin kunnena, da sauri na
juya garesa dan a bazata maganar tazomin. A karo na biyu muka sake haɗa ido, sai
dai yanzun duk yanda naso janye nawa kamar ɗazun hakan ya gagara, kallo yakemin
irin na tsakkiyar idonnan tamkar zai haɗiyeni dasu, bazan iya jurewa ba, amma na
kasa janyewa dan tamkar yamin ɗaurin goro ne da mayun idanun nasa da a yau suke
farare tas babu sirkin ja alamar dai baya tattare da ɓacin rai. Da ƙyar na samu nai
ƙoƙarin yin ƙasa da kaina zuciyata na wani tsitstsinkewa tare da jinin jikina. Amma
a bazata saijin tattausan hannunsa nai ya taro haɓata ya sake ɗago fuskar, tuni
zuciyata ta sake wani zallo tamjar zata faso ƙirji ta fito, Farfar na farayi da
idanuna da suka cika taf da ƙwalla lokacin da ya matso da fuskarsa daf da tawa har
munajin saukar numfashin juna, lumshe idanun kawai nayi ganin bani da wata mafita
kuma, ya kawo bakinsa daf da nawa.
Yanda jikina ke tsuma zai tabbatar maka a matsanancin tsoro nake da
yanayin, tsigar jikina duk ta miƙe.
Jay dake kallon yanda bily ta rikice ya saki lallausan murmushi tare da
goga hancinsa kan nata, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Matsoraciya kawai, darajar
matata tafi ƙarfin nayi kissing ɗinta anan wajen yariya, hakan bazai taɓa yuwuba
sai a fadata insha ALLAH. badan girman alƙawari ba da bazan taɓa bari ki shiga
wajen nanba, ni kaɗai yafi cancanta na shaida wannan ƙyawu naki a cikin gidana. Ina
ƙara maimaita miki bana son rawa”. Ya ƙare maganar da ɗaura yatsansa babba saman
lips ɗina ya kwashe ɗan lipstick ɗin da aka samin.
Wata irin kunya naji ta lulluɓeni mai haɗe da tsoro da ɗan haushin gogen
lipstick da yayi, nai ƙasa da kaina ina ɗan kumbura da faɗin, “Toni nama iya rawan
ne ma.........”
Saukar ɗalli kawai naji a saman laɓɓana mai azabar zafin, na ɗago
idanuna da suka cika da ƙwalla a kansa. sassanyan murmushin mugunta ya sakarmin har
dimples ɗinsa duka biyu na loɓawa, ya ɗage kafaɗunsa yana ɗage gira ɗaya da taɓe
baki alamar ni naja.
Kafin wani ya ƙara magana a ciki

nmu akai knocking glass ɗin motar, sauke gilas ɗin yayi, oga Hafiz ne yay masa
magana akan mu fito. Banji amsar da ya bashiba, baice min komaiba nima ya fice, ina
ƙoƙarin gyara alƙyabata nima na fita naji an buɗe ƙofar ɓangarena, na ɗago dan
ganin wanene muka haɗa ido ashe shine ya zagayo tanan, hannunsa na dama ya miƙomin
yana wani ɓata fuska da kallona ƙasa-ƙasa, a kunyace na ɗora nawa ya taimakamin na
fita nima, hannunsa na haggu yasa yaja hular alƙyabar ya sake rufemin fuska da
ƙyau.
Ina jiyo wani cikin baƙin abokansa na faɗin, “Sarakin kishi muma ba kalla
zamuyiba ai bar wahalar rurrufe mata fuska”. banji ya bashi amsaba sai dariyar da
sauran sukayi. Inajin irin zafin da nakeji a duk lokacin da ya raɓu jikina, sai dai
yau kaɗan nakejinsa cikin amincin ALLAH, dan haka nai jarumtar daurewa tamkar
banajin komai ina addu'a cikin raina har muka shige abokansa da ƙawayena na biye
damu a baya cikin ƙyaƙyƙyawan tsari babu wata hayaniya.
Muna shiga da aunty Batool dake ƙofar tsaye tana jiranmu muka fara cin karo,
ta shiga feso mana wani farin abu mai ƙyalƙyali da ƙamshi, masu hotuna kuwa nata
ƙyalla mu.

Sauran mutanen duk suka miƙe idanun kowa na kan amarya da ango dake cike da
birgewa, yayinda ƴanmatan family ɗin su Jay sukejin zafi a zukatansu dajin takaicin
bilkisu da tazo daga sama tai musu wuf da shi, sai irinsu Rose da kallo ɗaya zakai
musu ka hango tsagwaron kishi da tsanar bilkisun a cikin idanunsu. MC kuwa na
zubama amarya da ango kirari. yayinda Ali jita ya sake gyara maƙogwaron nan nasa na
zinari ya fara baitocin girma ga amaryar ƙamshi bilkisu mai gadon zinari cikin
waƙarsa mai taken Bilkisu gimbiya.

(Bara naɗan raira muku kaɗan saura wani yace ban iyaba😣😚. lol)

🎸🎸🎶🎶BILKEESU zan faɗa dan ALLAH, mata ku bani dama duka.


bilkisu gimbiya.
BILKEESU mai gadon zinari waƙarki ta fita haka.🎸🎶🎶
BILKEESU sai gani sai nuni, kowa ya tabbata duka.🎸🎸🎸🎺🎺
BILKEESU gimbiya an baki, mata su dakata duka.🎸🎸🎺
BILKEESU sanya alƙyabar ki kaya mayalwata haka.🎸
Bilkisu gimbiya.
BILKEESU za'a yiwa fada, ai mata fifita haka. 🎸
Jita kaja muje nai waƙar Bilkisu masu girma haka.🎸
Mata ku rausaya Ali jita nine na baku dama haka🎸🎶🎶
Komai yanada rana a gane dama tanada dama haka, Bilkisu gimbiya.
Giwa ki rausaya BILKEESU ALLAH ya ƙara baiwa haka.🎸🎷🎷
Komai yaje ya dawo BILKEESU ku za'a tabbatarwa haka🎸
Ganga irin ta girma a miki waccan a mata garwa haka.🎸
BILKEESU za'a baiwa Number komai daren daɗewa duka
Bilkisu gimbiya
BILKEESU sannu mata irin na zamanin ɗebe kewa duka.🎸🎸
Kinsha aradu kinsha yasin, kin samu arziƙi duka.🎸🎷🎸🎷
Kin tsallakema tarkon maƙiya, ga ɗan abin biki haka.🎸
Kinzam sarauniya a cikin mata bar munafuka haka.
Bilkisu gimbiya🎸
Ga zamani da daɗi wannan al'amarinkine duka🎸🎸🎸
Tsarki na zuciya bilkisu ya baki ɗaukaka haka.
Kinsa kara a hanya BILKEESU wazata tsallakane🎸
Komai kina tunani Bilkisu baƙya abu daka haka🎸
Bilkisu gimbiya
Ga ilimi da halin girma, ALLAH ya ɗaukaka haka.........🎸🎷🎸🎷🎸🎺🎺🎺🎺

(Kunema sauran kuji na gaji😂😜)

“Mawaƙin nan dolene yaci ƙyautar mota”. Oga Aliyu dake bayanmu shida
matarsa ya faɗa yana ƴar dariya.
Murmushi naga boss yayi a hankali lokacin da yake kama kafaɗuna yana zaunar
da ni a ɗaya daga kujerar guda biyu da aka tanada danmu. Ni kaina waƙar tamin daɗi
sosai, hakan ya sakani sakin murmushi da banyi niyyaba. Jay yaɗan lumshe idanu ya
sake buɗewa a kanta sannan ya zauna a nashi mazaunin shima.

Babu ɓata lokaci aka fara gudanar da abinda ya tara mutane, an buɗe taro da
addu'a kafin ai kiran Ummie tazo ta bada tarihin amarya a taƙaice, Hafiz ma ya bada
tarihin ango tare da ɗorawa da shaƙiyancin randa suka fara gane Jawaad ya kamu da
son amaryar tasa. Yanda yake faɗar wajen dole ya saka mutane dariya, masu baƙin
ciki kuwa suka shiga zuba tsaki suna haɗiyar zuciya. Bily kanta sai da ta murmusa
dukda tasan ba haka bane tunda ita

dai bai taɓa ce mata yana son nata ba, ɗagowa tai da nufin satar kallonsa sai suka
haɗa ido, dan shima kallonta yake ƙasa-ƙasa idanu a narke.
Cike da salo ya wani ɗagemin girarsa ɗaya, maida kaina nai ƙasa zuciyata na
motsawa. Ban sake gigin kallon sashen da yakeba nima na maida hankalina ga kallon
mawaƙa da suketa baje fasaharsu cikin daɗaɗan waƙoƙi da duk an raira baitocinsune
da sunayenmu. Umar m shariff, Ado gwanja, Nura m inuwa, Naziru Ahmad, Hamisu
breaker, Isa ayagi, Abdul D one, kai abunfa ba'a magana, ƴan uwa da ƙawaye da
abokan ango nata casar rawa, duk yanda mc keta magiya da roƙon amarya da ango su
fito filin rawa ya hanani ko motsi, duk wanda ke buƙatar mana liƙi sai daifa yazo
nan inda muke zaune ya liƙa mana ɗin, amma ko sau ɗaya bamu shiga filin rawarba.
Lokacin da Anum da Nabeelah suka hawo domin yima su Jay liƙi ba ƙaramin
faɗuwa gabansa yayiba, itama ɗin dai sai da ta ɗora hannunta a ƙirji alamar gaban
nata faɗuwar ya keyi, dama tun sanda su bilkisu suka shigo saida gabanta ya faɗi,
jikinta a sanyaye ta liƙa masa kuɗin shi da bilyn suka sauka ko jin surutun da
Nabeelah keyi bataiba. Duk bilkisu na kula da yanayin da boss da Anum ɗin suka
shiga, dan harta sauka yana binta da kallone.
Tun ɗazun nake wuwwula idanu ko zanga Yah Anuwar, haka kawai nakeji a raina
bana son su haɗu da boss yanzu anan, to bammaga su Abdur-raheem bama. Da hannu na
yafito Anum, ta taso zuwa gareni. Cikin magana ƙasa-ƙasa nace, “Ina Yah Anuwar?”.
Tace, “Tab aishi bayason bidi'a, da wahala idan zaizo wajen nan, amma bakiga yanda
mijinki ke kama da Yah Anuwar ba? Nifa dana kallesa gabana sai ya faɗi wlhy
bilkisu”. Murmushi na mata da cewa, “Karki damu zamuyi magana amma ba anan ba”.
Kanta ta ɗagamin ta koma wajen zamanta. Ina kallon irin kallon tuhumar da boss
kemin nai kamar ban ganiba, dan rashin zuwar Anuwat ɗin yasa naji hankalina ya
kwanta.
An buƙaci mu fito domin yanka cake. Ganin bai motsaba nima nai zamana, Ina
jiyo fitar guntun tsakinsa alamar bayason yi, ni kaina bason nakeba, dan duk a
takure nake matuƙa. Sai da Jabeer yazo yayta roƙonsa da ƙyar ya amince muka miƙe
zuwa gaban cake ɗin da yay masifar ƙyau.
Mun yanka cake tamkar yanda tsarin yake, ni na fara cira ɗan guntu da zan
saka masa a baki cike da jin matsananciyar kunya, dan da ƙyar na iya control ɗin
tsumar da jikina keyi nakai hannuna bakinsa, hannun nawa ya riƙe shima muka saka
masa gaba ɗaya wanda na ciroɗin kasancewar ɗan ƙaramine a baki. Ina ƙoƙarin janye
hannun ya maidashi cikin bakinsa ya tsotse yatsun biyu dana ɗauki cake ɗin dasu
suka ɗan ɓaci kaɗan. tafi hall ɗin ya ɗauka. Jinai tamkar na nutse dan kunya.
Shi kam Maimakon ya ciro ya bani kamar yanda nai masa sai ya lakato ya
samin a saman hanci kawai dan wulaƙanci, ban gama fita daga takaicin salon nasaba
naji saukar numfashinsa kan fuskata, kafin na sami damar magana ya lashe wanda ya
lakatamin ɗin da bakinsa. tafin yanzun kam har yafi na ɗazu, dan yanzu harda waƙar
Ali jita aka sake saki ta Bilkisu gimbiya. Ƙasa nai niyyar duƙewa dan kunya yay
azamar riƙoni jikinsa, sai kawai na ɗora kaina saman ƙirjinsa ina sakin murmushin
jin kunya, shima ya ɗaura hannunsa ɗaya saman bayana yana ɗan bubbugawa.
Da ƙyar mc ya samu hayaniyar ta lafa, zamu koma wajen zamanmu aka dakatar
damu. Jabeer ya fara bayani kamar haka....
“To jama'a kowa sai ya buɗe idanu domin dai zamuga wasan manya ne, kunsan
daga amaryar har angon jarumaine a filin daga”. Ya nuna bindigu guda biyu dake
saman wani table duk an buɗesu, “Kuna dai ganin bindiga guda biyu ajiye ko? To
munason ango da amarya su haɗasu cikin minti ɗaya yanda suke, wanda ya fara gamawa
yana da ƙyauta ta musamman”.
Ni abinma dariya ya bani, hakan yasa naɗan murmusa, batare da tunanin zanyi
nasaraba muka ƙarasa, sai da oga Jabeer ya irga uku sannan duk muka fara ƙoƙarin
haɗawar cikin hanzari, ina kammalawa nai saurin ɗagowa na nunasa da bindigar
fuskata a ɗaure, dai-dai da shima ya nunani data hannunsa fusakarsa babu wasa. .
Wani irin ihu hall ɗin ya ɗauka da tafi. Murmushi ya saki tare da tanƙwa
ɓe hannuna bindigar tai ƙasa ya caɓe cikin hannunsa, nai ƙasa da kaina ina
murmushin nima dan naji kunya.
Duk da kusan tare muka gama ni aka bama ƙyautar dai dan nina fara nunasa
da bindigar, wajen zamanmu muka koma, muna zama mc ya fara sanar da babban saƙo
daga ƙannen ango na musamman Princes, sunce a basu wannan filin su kaɗai, dan ga
waƙa ta musamman daga garesu da suka tanada domin amarya da ango. tsit hall ɗin
yayi kowa ya buɗe kunne yaji ya kuma ga waɗanan ƙannen ango na musman da kowa ke
ƙyautata zaton ƴaƴane daga masarauta.
Matasan samari masu ji da jini a jika da wautar ƙuruciya, Abdul-Raheem,
Abdur-rahman, Ameen, suka miƙe, dan da gaske Anuwar bai zoba (su ustazu🤐 lol).
sunsha ƙyau harsun gaji cikin shadda kalar sararin samaniya, kansu tsaye mazaunin
ango da amarya suka nufa, yayinda Hamisu breaker ya miƙe ya fara raira musu
waƙar........
Ashe da rai yake sanki jaruma bada zuciyatai ba, komai ruwa da iska akanki jay
baza ya daina kewa ba, tunda dai ya samu zarrar samunki baza ya tanka kowaba, shi
baiga mai hararaba, balle ya waiwaya baya. Indai a kankine zaya jure wahalar zuwa
garin nisa, da an taɓaki ajirasa danko tilas yazo ya ɗau fansa..........

(Man kaina ya tsiyaye dole mukoma wajen breaker ya ƙarisa🚶🏻😫)

Breaker na fara raira waka sukuma suka farke ƴan dubu-dubu suka fara zubama
Jay da bily liƙi, gaba ɗaya hall ɗin ya yamutse da hayaniya, masu ɗaukar video nayi
a waya masu hotuna nayi, masu yima breaker liƙi nayi masu yima ango da amarya dasu
Abdur-raheem nayi. Daga hakafa aka tafi casun ƙarshe.
Alhmdllh taro ya tashi lafiya kowa cikin farin ciki, anci ansha kowa yayi
haniƙan banda amarya da ango, dan ko ruwa bily batasha a wajen nanba har aka tashi,
haka shima Jay ɗin.

★★★★★

Ana tashi aka fice dani daga wajen, ganin mun barsa acan ba'a mota ɗaya
zamu tafiba kuma farin ciki ya kamani, dan nazata dai masarauta za'a maidani. Sai
dai ana sakani mota naji suna faɗin daga nan gidan amarya za'a nufa, idan anje ana
kaita mutane su fito dan ba zama za'aiba dare yayi shabiyu saura.
A take zuciyata ta shiga tsitstsinkewa, hawaye suka fara gudu a kumatuna,
dan nama manta da wata kwalliyar fuskata, ALLAH bansan wannan shirin suka shirya
ba, duk zatona sai gobe idan ALLAH ya kaimu ganin bamuyi sallama da Ummu ba a
masarauta. Tun ina kuka a hankali har ya bayyana fili. Lallashina Mah-mah take tayi
da sakemin nasiha ƙasa-ƙasa har muka isa, dazan fita a motarma sai da ta sakani nai
addu'a, hakama da zan saka ƙafata a falon, kaina lulluɓe yake da alƙyabba banajin
komai sai ƙamshin fenta da ya haɗe dana turare dana sabon kaya ya bada yanayi na
musamman.

An miƙa amarya Bilkisu ɗakin mijinta, inda basu wani ɓata lokaciba dan
basufi mintuna ashirinba aka saka kowa ya fita ya shiga mota, dama wasu sun wuce
gida daga wajen dinner, acewarsu zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sazo suga gidan
amarya da ƙyau.
Cikin mintuna ƙalilan gidan yay tsit, motocin duk sun juya, Aunty
Batool kawai aka bari, itama zata ɗan zaunane kar abar Bilkisu ita kaɗai kafin Jay
ya shigo. Bayi ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi da turaruka masu ƙamshi tazo ta tada
bily da har yanzu take kuka. “Kukan ya isa haka amarsu, tashi ki daure ki watsa
ruwa dan wannan kukan naki nasan ya ɓata kwalliyar”. Ban musa mataba dan inada
buƙatar yin wankan kasancewar a yanayin da nake ciki. Alƙyabar ta taimakamin na
cire kawai ta fita ta barni, ban zauna jan jikiba dan tace nai sauri boss zai iya
shigowa koda yaushe, bai kuma dace ya iskeni a haka ba. Wanka na shiga nayo sauri-
sauri na kimtsa jikina na fito, harta kwashe kayan dana cire ta ajiye min riga da
zani na atanfa. Shiryawa nai a gurguje, ina kammala saka kayan tana shigowa. Tace,
“Yauwa kinga ai hakan yafi, bara aɗan gyara fuskar”. Bance komaiba nidai taɗan
shafamin fauda da lipsgloss a baki kaɗan sai turarurruka data fesheni dasu ta bani
babban gyale na yafa tare da sake feshe ɗakin da Air Fresheners masu daɗin ƙamshi.
Inda ta zaunar dani ta matso tana murmushi, “To Amarsu angonki ya shigo,
bara naje hasu Aliyu can na jirana zasu

saukeni a gida, mu kwana lafiya ALLAH ya huta gajiya”. Hawayen da suka ziraromin
na share, nace, “Aunty Batool dan ALLAH ki kwana anan mana, kingafa dare yayi”.
Murmushi tayi tana riƙe haɓa, “Inani ina kwana gidan amarya, kinga nayi nan”.
Hawaye masu ɗumi ne suka sake gangaromin, na zame na kwanta inayin kayana dan
jinake ma duk haushin kowa nakeji, ni banason auren a maidani gidan Dad kawai na
cigaba da zamana hankalina kwance.

__________________________

Lokacin da shagali ke gudana a gidan Dad tashin hankali suke


fuskanta, dan kuwa dai Salman ne ya gano hotunan biki na yawo a yanar gizo waɗanda
ke wajen dinner nata ɗorawa, kunsan mutane da waya a hannu tamkar abu na cizonsune
idan suka gani, tun fara dinner ɗin suketa ɗakar hotuna suna ɗorawa wasuma harda
videos. Aiko Salman yaci karo da su, shigowa gida yay ya kunna tv dan son ganin
wainar da ake toyawa a wajen kasancwwar babu wanda yaje a cikinsu Momy ta hana.
Yana zama Aamilah na fitowa, zama tayi suna kallo tare da zagin Bilkisu da Jawaad,
hayaniyarsu ta saka Shahudah dake kwance a ɗaki zazzaɓi ya rufe fitowa, aiko tai
mummunan gani, dan kuwa dai-dai wajen da Jay ya lashe cake ɗinan daya saka a hancin
Bilkisu taci karo dashi, idan ba kallon tsaf kaima wajenba zaka ɗauka kissing ɗin
Bilkisu ya keyi. Ƙara kawai ta ƙwalla ta yanke jiki ta faɗi.
Duk kanta sukayi da ihu har Momy Da Dad dake sakkowa daga sama. Girgizawar
duniya da sakama Shahudah ruwa taƙi koda motsi, a take hankalinsu ya ƙara kaiwa
ƙololuwar tashi suka kwasheta zuwa asibiti likitoci suka rufu a kanta. Har zuwa
yanzun dai babu wani bayanin farfaɗowarta kuma.............🤦🏻✍

Duk wanda suka kirani jiya ban ɗagaba suyi haƙuri, ngd sosai kuma da addu'oinku
gareni na samu lafiya🤦🏻.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭


✍🏻
[1/1, 9:21 PM] HASNA : Page 39

.................Tsaye kawai Jawaad daya shigo yay yana kallon Bilkisu da keta
faman shashashar kuka, ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana girgiza kansa. Sai ya tuna
da randa aka kai masa Shahudah, cikin kayan barci ya shiga ya sameta zaune
hankalinta a kwance tana buga game a waya, amma ita jiba duk da ba daga ainahin
iyayenta aka rabotaba ta kasa barin kuka. Idanunsa ya lumshe a hankali da ƙara
sauke ajiyar zuciya. Ya cire hular da babbar rigan, daga shi sai wando da ƴar cikin
da iyakarta rafin cinyarsa. Ƙarasawa yay gaban gadon ya zauna kusa da ita, dauriya
kawai yake dan kansa ciwo yake masa shima, hannunta ya kamo batare da yayi magana
ba.
Gaba na ne ya faɗi dan banji motsin shigowar kowa ba, gyalen dana rufe
har fuskata da shi nai saurin janyewa dan naji tsoro, ya murza hannuna dake cikin
nashi yana faɗin, “Tashi zaune, K baƙya gajiya da kukane?”. Yay maganar da kamoni
sosai ya miƙar. Koda na tashi zaunen ban yarda na kallesa ba, ya sake murza hannuna
da har yanzu yake a cikin nashin. Idanuna naɗan rumtse ina ƙoƙarin danne abinda
nakeji.
Jay dake kallonta ya girgiza kansa kawai tare da kai hannu ya janye
gyalen data rufe fuska “Jiba yanda wannan kukan ya saka miki zazzaɓi, amma bazaki
tausayima kankiba ki barsa haka, indai danni akeyi a ya isa haka na yafe”. Kamar
jira take yay magana wasu hawayen suka sake zubowa sharrr. Kai Jawaad ya dafe kawai
yana lumshe ido da sake buɗewa a kanta, shi kukan natama ya fara bashi dariya,
sudai mata a duniya suyi kuka shine jin daɗinsu, ya sauke numfashi kaɗan yana
ƙoƙarin danne dariyarsa. “Tashi muje kici abinci kisha magani sai mu dawo ki cigaba
da kukan kamar ƙyafi samun ruwan hawayen sosai ai”. Mamakin maganarsa yasa na ɗago
na kallesa. Yace, “To miye na kallon nawa? Ba daɗi kukan yake miki ba?”. Ɓata fuska
nayi nasa hannu na goge hawayen. Bai sake cewa komaiba ya miƙar dani tsaye, kunyace
ta kamani nai azamar ɗaukar gyalena daya zame zan maida, amma sai ya riƙe, yana
nunamin hanya alamar muje. Cikin rawar murya nai magana a karo na farko tun
shigiwarsa, “To ka bani gyalen”. Matsowa yay gab dani sosai, hakan yasa naja baya
idanuna na sake tara ƙwalla, Hannuna kawai ya kama batare da ya bani gyalenba bai
kuma cemin komaiba muka fito falo.
Dukda kaina a ƙasa yake nasan falon nan ya haɗu, ga wani ƙamshi mai kwantar
da zuciya na tashi a cikinsa. Cikin kujera ya zaunar dani shima ya zauna kusa dani,
ya buɗe filet ɗin dake akan centre table ɗin falon, ƙamshi mai daɗi ya daki
hancina, kajine guda biyu da suka sami gashi mai ƙyau da tsafta. Yace, “Kici abinci
kisha magani jikinki yayi zafi da yawa”. “Nifa na ƙoshi”. Na faɗa murya na rawa.
Banza yaymin ya ɗebo naman da hannunsa ya kawo min a baki. matsar da fuskata nai
ina girgiza kaina da sake faɗin, “ALLAH da gaske nake na ƙoshi”.
Shiru yay na wasu sakanni baice komaiba yana kallona, kafin ya ajiye wanda ya
ɗebo ɗin ya matsoni sosai, Hannunsa kawai naji saman haɓata ya ɗago fuskata,
muryarsa babu alamar wasa yace, “Iyayi zakimin danma kinga zan baki kazan ƙyauta,
ALLAH garama kici da arziƙi, bar ganin period kikeyi inada hanyoyin da zan sakaki
kukan da kike sha'awar yi mai dalili, idan kuma kinji ƙarya kar kici na nuna miki
ainahin kalata da baki saniba”. Tunda ya fara maganar idona ya cika da ƙwalla, na
fara ƙyaƙyƙyaftasu.
Fuska Jawaad ya haɗe sosai, dan ya kula sai ya buɗe mata wuta zasu dai-
daita, a ɗan kausashe yace, “Miemaa!”. Da sauri na ɗago na kallesa jin yanda ya
kira sunan a daƙile. Ya tsatstsareni da idanunsa dake tattare da ɗumbin gajiya, duk
yanda naso janye nawa ya hanani. “Na miki kama da abin wasanki?”. Kaina na girgiza
masa da sauri. “Inhar kika bari waɗanan hawayen suka zubo ALLAH saikin gane
kurenki”.
“Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy nima bada sona suke zubowa ba, wani irin
tsoro nakeji a raina, saina dinga ganin kamar gilmawar inuwa kuma idanuna, sannan a
ƙasan zuciyata wani irin zafi nakeji, kamin addu'a a cikin ruwa”. Kafeta yay kawai
da idanu na wasu sakanni, ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa yana jawota jikinsa ya
rungume. “Ki daure kinji, ki dinga ƙarfafa zuciy
[1/2, 1:07 PM] HASNA ✍🏻
: Typing

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 40
...............Sosai Nabeelah ta waro idanunta da suka cika da hawaye tana haɗe
hannayenta waje guda alamar roƙo, “ALLAH yayanmu ni babu abinda zan faɗa, dan ALLAH
kayi haƙuri”.
“Kinsan ALLAH idan kika bari harna miƙe kanki sai jikinki yay masifar yin tsami”.
Yay maganar muryarsa babu alamun wasa. A mamakina sai naga Nabeelah ta fashe da
kuka tana ɗanja baya, na kallesa da nufin bashi haƙuri duk da nima a tsoracen nake
sai na ga ya miƙe, ai kafinma nace wani abu sai hango Nabeelah nai ta kwasa da gudu
ta fice. Yanda yaja birki tare da riƙe ƙugu yana kallontane ya sakani kasa danne
dariyata, hannu nasaka na toshe bakina tare da saurin kauda idanuna ganin ya
kalloni.
Jawaad yay ƙwafa yanabin Bilkisu da kallo, “Ke kuma dariyan na miye to?”. Kallonsa
nai da sauri ina ƙoƙarin haɗiye kayata amma na kasan, dan fuskata kawai zaka kalla
kasan dariyar taƙi haɗiyu wa, harar daya ballo mince tasa nai niyyar barin masa
falon naje nai dariyata a ciki. Caraf naji an cafkomin hannu da faɗin, “Dariya ko?
To bara na huce a kanki”. Tsaf na haɗiye dariyar na koma zare idanu, cikin
marairaice fuska nace, “Nifa ba dariya nayiba”. “To mi kikayi?”. Yay maganar da
tsatstsareni da mayun idanunsa. Sosai kunya ta lulluɓeni nai ƙasa da kaina ina ɗan
waige-waige, nima na Nabeelah nake tsarawa na fece kawai. Kamar ya fahimci abinda
nake tsarawa a raina yace, “Kema guduwar zakiyi? Itama ɗin ba ƙyaleta naiba zan
sameta har gida sai naci ƙaniyarta na gasa mata baki tunda ita magananniyace”.
Murmushin da ban shiryaba ne ya suɓucemin, nace, “Yi haƙuri to niba baƙuwar zafi
bace wlhy”. Kafin yace wani abu wayarsa ta shiga ring, kallon wayar duk mukai da
mamaki, da alama ma anan ya mantata ta kwana ko?, hannuna dake cikin nasa na janye
na ɗakko masa wayar da rabinta ya shige ƙasan filon kujera. Ban tsaya kallon ko
wanene ba na kawo masa cikin.
Amsa yayi yana zama, ni kuma na juya na ɗauki basket ɗin da Nabeelah ta kawo wanda
ko ba'a faɗaba kasan breakfast ne a ciki. Harna nufi D/table naji ya kirayi sunana,
juyowa nai ina amsawa da “Na'am”. Dai-dai zai saka wayar a kunnensa alamar wancan
kiran ya katse shi ya sake kira. Yace, “Kawomin tea, karki saka suga da yawa”. Da
“to” na amsa kawai na ƙarisa na ajiye basket ɗin saman dani. Kicin ɗin na nufa ina
ɗan murmushi da yaba ƙoƙari da sadaukarwa irin ta waɗanan bayin ALLAH, babu dangin
iya babu na baba suka kashemin waɗanan kuɗin? Ba ƙaramin mutsuwar tsaye naiba da
ganin yanda kicin ɗinan yay mugu-mugun haɗuwa, ni balki ɗiyar baba makaho ce da
wannan gidan matsayin matar cikinsa? Sai kawai naji ƙwalla sun cikamin idanu, na
shiga maimaita kalomin Alhmdllh a zuciyata ina hawayen zuci. Fasalta muku yanda
kicin ɗinan yake ai ɓata lokacine, abin mamaki da al'ajab harda kayan abinci da
malam bahaushe ke kira da gara, dai-dai da magi wannan sakarai an ajiye min shi.
Sai dai kuma babu kayan tea ɗin da yace na haɗa masa, iya dubana banga koda lipton
ba sai kayan ƙamshi kawai da abinda ba a rasaba, komawa nai da niyyar faɗa masa ban
ganiba amma na iske yana waya da ransa a ɓace. “Uncle Please ka ƙyalesu ni babu
abinda zanzo na musu, ina ƙoƙarin danne duk abinda suke son takalata dashi kawai
amma na kula neman kaini maƙura sukeyi akan shirmensu”. Yaɗanyi shiru alamar
saurare, hakan yasa na juya zan koma dan na bashi damar gamawa amma sai naji
takunsa a bayana, baimin maganaba yazo ya wuceni, ganin hakan yasani bin bayansa,
drawer saitin fridge ya buɗe ya nunamin. Kaina na jinjina masa na ida shiga ciki
shi kuma ya fice yana cigaba da wayarsa. Bani da matsala da kayan ƙamshi dan duk
gasunan a robobi harma da ganyan shayi masu daɗi da Umm-Aban dama tace zata haɗa
min saboda ta lura inason shayi. Tukunya na ciro da dama an fiddata a kwalinta na
ɗauraye na zuba duk abinda zan buƙata na ɗora saman gas da dama an haɗashi shima.
Komawa nai na ɗauki plate da flask da kofi na ɗaurayesu tsaf, cikin mintuna ƙalilan
na kammala na fito da komai na ajiye a dani ɗin, sannan na koma na ɗakko tea ɗin
dana haɗa a kofi na ɗaura saman ƙaramin tire na kai masa falon dan har yanzu wayar
yakeyi. Yanda yake kallona harna ajiye tiren a centre table duk sai naji na takura,
nuni yaymin da in bashi, ɗauka nai na miƙa masa, ya ɗan lumshemin idanu alamar
“thanks”. Bance komaiba nabar wajen dan sonake nai wanka.
Saida na gyara gadon yay tsaf sannan na shiga wankan, wanka nai haɗe da wankan
tsarki dan mai jar motama ya ɗauke tunkan azhar ɗin da nake hasashen, zaton babu
mai shigominne ya sakani fitowa daga ni sai guntun towel ga gashi a jiƙe, sai dai
inata ƙoƙarin tsanesa da ƙaramin towel dake a hannuna. Ina ƙarasawa gaban mirror
yana shigowa da sallama ciki-ciki alamar ransa a ɓace yake har yanzun, saida naji
tamkar na ƙwala ihu, na ɗan wawwaiga banga wani abu dazan iya ja na rufe jikina da
shiba, haƙura nai kawai na ɗan ɗago na kallesa cikin dauriya ina faɗin, “Nazo na
baka abincin ɗinne?”. Shirun da naji yayi bai amsaba yasa na ɗago kaina na dubesa,
idanunsa nakan gashina ko ƙyaftawa bayayi. Sake maimaita masa tambayar nayi. Ya
janye idonun nasa da juyawa zai fita yana faɗin, “Ki gama nima zanyi wankan ne”.
Binsa kawai nayi da kallo dan na lura ransa a ɓace yake, ‘Komi akai masa kuma?’ na
faɗa a fili batare da inada mai bani amsata ba. Gudun karya sake shigomin yasa nai
shiri a gaggauce cikin sket da riga na shadda orange color. Ni kaina nasan sunyimin
ƙyau dan kamar an haliccesune a jikina sunmin ɗam dan telan ya iya ɗinki, kaina
nakeson busarwa amma abin haushi babu wuta, a haka na gyarashi bayan na tsanesa
sosai babu ruwa, ɗauresa nai da tunanin ƙila su kawo wutar anjima tunda naga
anguwar kamar suna samunta sosai. Bawata kwalliya nai da yawaba amma fuskata tayi
fayau, na saka ƙaramar sarka sannan na feshe jikina da turare sosai, kowa ya ganni
yaga amarya da gaske, farin gyale na ɗauka shima na saka turare sannan na yafa na
fito falon. Gidan tsaf yake babu wani datti, hakan yasa kawai na ɗauki fresheners
da turare mai ƙamshi haɗin gida na fesa iya falon nan kawai. Ina cikin fesawar ya
fito.
Jin Motsinsa a bayana ya sakani waigawa, kwalliyar tasa ta sakani shagala a
kallonsa batare dana fargaba, shaddace ƴar ubansu golden color ya saka, sai maiƙo
take da ɗaukar ido, ta samu nutsatstsen ɗinki na zamani da ya fiddo cikar zatinsa
mai tabbatar dashi jinin hausawan usul harda su hula......
Saukar iskar da naji a cikin idanuna da ƙamshi Mouth freshener ɗin da ya saka ya
sani dawowa hayyacina daga sakin layin da nayi, nai ƙasa da kaina dan naji kunya.
“Gulmammiya kinaso kina kaiwa kasuwa, na miki ƙyaune?”.
Ɗan kallonsa nai na juya ƙeya nace, “Kaɗan”. Murmushi ya saki har inajin sautinsa,
ya ɗaura hannunsa saman haɓata ya maido fuskata inda yake, “In har da gaske kike ki
kaleni cikin ido kice kaɗan nai ƙyau”. Hannu nasa na rufe fusa da sake juya masa
baya ina murmushi. “Baki da gaskiya kenan”. Yay maganar kusa da kunnena yana zame
gyalen dana yafa. “Malama niba surukinki bane ai, muje kiga gidanki”.
Shine yaymin rakkiya lungu da saƙo na cikin gidan har ɗakinsa da harabar gidan,
gaba ɗaya gidan ya canjamin tamkar ba wanda na taɓa zuwa ɗin nanba, an gyarashi
sosai ya canja kamanni. Sai da muka gama zagaye ko ina muka yada zango a wajen cin
abinci. Nidai kasa sakewa nai naci saboda yanda yay mugun tsatstsareni da idanu,
duk sanda zan ɗago sai naga idonsa a kaina. Da dai na gaji saina kumbura masa
fuska, “Nifa wlhy ba television bace ba”. Bakinsa ya taɓe baice dani komaiba bai
kuma bar kallon nawaba har muka gama. Ɗakinsa ya koma nikuma na tattarr wajen, na
fito masa da abincin maigadi da tunkan mu fara cin namu ya sakani na zuba shima ya
fito, agogonsa da links ya miƙomin tare da miƙamin hannunsa. Dukda inajin kunya
haka na saka masa links ɗin sannan na saka masa agogon. “Thanks” ya faɗa a hankali
yana ɗagemin gira ɗaya.
Kafin nace wani abu maigadi ya doka sallama a ƙofa, kallon ƙofar mukai gaba ɗaya
amma shi ya amsa masa, ya amshi kular hannuna tare da nufar ƙofar ya buɗe.
Maigadi ya gaidasa da faɗin, “Alhaji kanada baƙone”. Da ɗan mamaki Jawaad yace,
“baƙo kuma malam gambo?”. “Eh Alhaji, harzan masa ƙaryar baka tashiba saina fahimci
amatse yake da son ganinka gaskiya, kuma kamar baƙon mai muhimmanci ne”. “Okey, to
ga abincinka ina zuwa”. Amsar kular yay dayi godiya ya koma, Jay kuma ya maida
ƙofar ya rufe ya dawo inda yabar Bily tsaye tana kallonsu. Wuceta yay ya ɗauka key
ɗin motar dake kan centre table, “Bara naje na gaida Alhaji Babba daga nan na leƙa
asibi wai Hudah aka kwantar”. “Ya salam” na faɗa cikin damuwa, “Miya sameta kuma?
Dan ALLAH kaje dani”. Kaɗan ya kalleni ya ɗauke kansa, “Kimata addu'a daga nan ya
isa, kokin taɓa ganin amarya ta fita”. Cikin shagwaɓar da bansan inada itaba nace,
“Toni tsoro nakeji wlhy”. “Tsoro kuma?” ya faɗa yana kallona. kaina na ɗaga masa
batare dana yarda mun haɗa ido ba. Jin yaƙi magana yasa na sake kallonsa, sai naga
niɗin yake kallo ashe shima. “ALLAH na kula kinma rainani” yay maganar yana
matsoni, baya nai saurin ja, amma duk da haka saida ya riƙoni. Cikin magana raɗa-
raɗa yace, “Ke komai abin tsorone a wajenki halan?”. Nace, “To inason naje naga
aunty Shahudah ne”. “Uhhyim shine zakimin ƙarya? to babu inda zakije, ki jira
ƙawayenki na nan zuwa zan dawo bazan jimaba dan zanyi magana da ku”. Saurin
kallonsa nai da mamaki nace, “Su Ummie?”. Kansa ya ɗagamin. “Miya faru?”. “dan na
dawo zakiji ai, ana jirana yanzun”. Ya ƙare maganar da ɗaura bakinsa saman nawa
babu zato. ‘Ya salam’ na ambata a zuciyata tsigar jikina na tashi ga yanayin da
nakeji na neman tasomin dukda dai yanzuma da sauƙi sosai ba kamar da ba. Sai da
yaja kusan minti biyu kafin ya saki bakin ya sumbaci goshina. “Saina dawo”. Kaina
kawai na jinjina masa dan na kasa kallonsa. A hankali na furta, ”ALLAH ya tsare”.
Inajin yana murmushi. Nidai ban kallesanba har ya fice.
Sassanyar ajiyar zuciya na sauke tare zubewa a kujera daɓar na dafe kaina, wlhy
abun mamaki yake ban, boss fa! Kai rayuwa bata rabo da abubuwan al'ajabi. Naja
kusan mintuna biyar a haka kafin na miƙe naje ɗakinsa dan na gyara. Sosai ɗakin
yake ƙamshin turarensa daya fesa yanzun, tsaf na gyarashi na saka fresheners sannan
na koma kicin na ɗauraye kwankina da mukaci abinci shima naɗan gyara abinda bai
minba.
Koda Jawaad ya fito sai ya iske baƙonsa cikin rumfar bunun dake harabar gidan
maigadi ya kawosa, ƙarasawa yay yana faɗin, “Ai bammayi tunanin kai bane Munkaila”.
Baƙo mai suna Munkaila daya miƙe domin girmamawa ga Jay yay murmushi, “Nine wlhy
Oga barka da fitowa”. “Yauwa sannunka da zuwa” Jay ya faɗa yana zama tare da masa
nuni daya zauna shima. Cikin girmamawa Munkaila ya gaishe da Jay kasancewarsa
ogansa, file ɗin gabansa ya miƙa masa yana faɗin, “Oga dukkan abinda kake buƙata
gashi, harma da abinda bakaceba dukna haɗo maka”. Kai Jay ya jinjina masa da faɗi,
“Sannu da ƙoƙari” yana buɗe file ɗin. Da hotuna ya fara cin karo waɗanda sukai
masifar ɗaure kansa dan harda Alhaji baba tare da mata biyu wadda ɗaya a ciki
takasance kakarsace mahaifiyar su Ummah da shima a hoto ya santa, kallon Munkaila
yay kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida file ɗin ya rufe.
Munkaila yace, “Oga akwai matsala ne?”. Kai Jay ya girgiza masa, “Babu matsalan
komai, yaya maganar wancan aikin?”. “Shima ina gab da kammalawa oga, saboda naga ka
matsu da wannan ma shiyyasa na dakata da wancan”. “Shikenan kayi ƙoƙari shima ka
haɗamin shi a satin nan, ga wannan ka saka mai nima nayi aljihun nawa yay ƙasa”.
Godiya Munkaila yayi sosai sannan suka fito a rumfar. Jay ya shiga mota shikuma ya
fice dan mashin ɗinsa na daga waje bai shigo da shiba.
★★★★★
Fitar jawad babu jimawa su Ummie suka isa gidan amarya Bilkisu, Ummie, Zuhrah,
Rebecca, Nazifa. Duk da jiya suka rabu da juna tuni suka haukace da ihun murnar
ganin juna, suka saka bily tsakkiya da tsokana kala-kala, tun tana musu shiru dai
harta koma ramawa itama dan taga shirun nata bazai sa su barta ba.
_________________________
Asibiti yay niyyar fara zuwa saboda Uncle Sulaiman daya tilasta masa yaje, to amma
wannan bayanan da Munkaila ya kawo masa yanzun sun ruguza komai, burinsa kawai ya
dangane da gidan Alhaji Babba. A waje yay fakin motarsa ya shiga shi kaɗai, Alhaji
babba na zaune a falo hannunsa riƙe da Jarida Jay ya shiga da sallama. Ɗagowa yay
yana kallonsa fuska ɗauke da murmushi, cikin tsokana yace, “A lallai wannan angon
da gaske bahausa ya aura, ashe ba gidan jiya ya komaba”. Jay dake murmushi ya
girgiza kai kawai yana zama, “Wannan itace tarbar da zakamin ma na baro matata na
taho ganinka da farar safiyar nan”. Alhaji babba yay dariya irin tasu ta manya yana
faɗin, “Ja'iri kenan bakifa ya buɗe”. Gaidashi Jay yayi yana murmushin tsokanar da
kakan nasa ke masa. Sai da suka kammala gaisuwar da tambayar lafiyar juna da amarya
Bilkisu kafin jay ya buɗe file ɗin da Munkaila ya kawo masa, hotunan ciki ya fiddo
gaba ɗaya ya miƙama Alhaji Babba shi kuma ya maida hankali ga duba bayanan cikin
file ɗin.
“Sa'adatu! kuma?”. Alhaji babba ya faɗa da alamun bazata. Kallonsa Jay yayi amma
baice komaiba. Alhaji babba yace, “Jawaad kana nufin matarka nada alaƙa da wannan
ta hoton?”. Zama Jawaad ya gyara sosai yana maida dukkan hankalinsa ga kakan nasa,
“Baba abinda bincike ya nuna min kenan, sai dai nima kaina a kulle yake musamman da
ganin hotonka a tsakkiyar mata biyu bayan mata ɗaya nasan kanada ita kafin Mama
Maryam”. Shiru Alhaji babba yay na wasu mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya, yace,
“minene sunan mahaifin nata?”. “Adam makaho” Jay ya bashi amsa a taƙaice. Nanma
shiru Alhaji babba yay na wani ɗan lokaci yanata faman jinjina kai da murmushi a
fuskarsa kafin yace, “Abin akwai ɗaure kai da ban al'ajabi”. Jawaad yace, “Miyasa
zai ɗaure maka kai bayan na fahimci kasan wani abu”. Murmushi Alhaji babba yayi mai
ciwo da sake maida hankalinsa ga hotunan guda biyar, ɗaya shine da mata biyu a jiki
sai jaririn yaro da alamu suka nuna ranar sunansa aka ɗauki hoton ma ƙila, ɗaya
kuma matane da miji matar gurguwa sai mijin da alamu suka nuna makaho ne, sai hoto
na uku jaririyace nannaɗe cikin farin showal da gani kaga sabuwar haihuwa, hoto na
huɗu, mata da minjin nan ne da jaririyar, na ƙarshema dai mata da mijinne sai
bilkisu a tsakkiyarsu da bazata wuce shekaru goma sha biyarba. Ya ajiye hotunan
yana kallon Jawaad da ƙyau. “Akwai abinda ku baku saniba Jawaad, mahaifiyarka cema
kawai zata iya sanin wani abu itama ba duka ba dan a labari ta sani. Ba Amina da
Maryam kawai na taɓa aureba, na taɓa auren wata matar mai suna Sa'adatu. Kafin
aurena da Amina Sa'adatu itace yarinyar da naso aura dan itace muke soyayya amma
iyayena suka ƙi, bakomai ne ya sakasu ƙinba sai kasancewar Sa'adatu batajin magana,
duk da yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyarba a lokacin mutane kan jefeta
da kalmar ƙarancin tarbiyya, Sa'adatu ta tashi a gidansu bata da uwa a hannun
kakarta ta tashi, hakan yasa ta tashi sangartacciya da batajin ƙwaɓa, a dalilin ɗan
karatun da aka sakata na boko wanda a wancan lokacin iyakamu maza kawai keyinsa
yasa idanunta buɗewa dan ita kaɗaice mace a cikinmu, Sa'adatu ji take tafi kowa a
ƴammatan yankinmu dama gata ƴar gata kuma babanta shine maigari, ALLAH ya jarabceni
da sonta fiye da yanda kake tunani har takai naima iyayena maganar aurenta. Amma
sai mahaiyata tace sam batasan wannan zanceba tama rigada tamin mata Amina, na ɗaga
hankalina matuƙa a lokacin amma dole na haƙura muka rabu da Sa'a ina kuka tanayi.
Hakan ya zafi kakarta har tayi alwashin sai nayi nadamar yaudarar jikarta da nayi.
Babu wanda ya ɗauki alwashinta wani abu aka ɗauramin aure da Amina ta tare. Banason
Amina amma ita tana sona kuma mace ce mai haƙuri da kawaici, a zamanmu tasha wahala
kafin na ɗan fara fuskantarta, aurenmu da Amina yakai shekara shida amma bata taɓa
ko ɓariba, a wancan lokacin dan mace takai shekara goma ma bata haihuba babu mai
damuwa da hakan balle ya zama abin magana shiyyasa nima ban taɓa damuwaba. Zuwa
lokacin Sa'a itama tayi aure amma ba a wannan garin namu ba, wani ɗan uwanta mai
kuɗi aka aura mata, sai dai kuma hankalinta na kaina dan haka shekararta uku ta
kashe auren ta fito da yarinyarta guda safara'u, a lokacinfa na tsaya kai da fata
saina auri Sa'a dan sonta na nan daram a raina. Zakasha mamaki idan nace maka Amina
itace taita kai kawo ga iyayena har mahaifiyata ta amince na auri Sa'a. A farkon
shigowar Sa'a gidana ta kwantar da kanta tanama Amina biyayya kamar gaske, amma
tunda muka wayi gari ta samu ciki sai abubuwa suka fara canja salo, raini da
wulaƙanci babu wanda take ragewa bataima Amina shi ba a bayan idona, amma a gabana
babu abinda ya sauya na ladabin da take mata da. Sam ban fahimci zaman kisan
mummuƙen da akeyi a gidana ba dan Amina ko a fuska bata taɓa nunaminba har ALLAH ya
sauki Sa'a lafiya ta haifi ɗa namiji wanda yaci sunan kakana Adamu. Bayan haihuwar
Adamu ne na fara fuskantar akwai matsala a zaman nasu, dan wataran na shigo a
bazata na iske Sa'a nama Amina gorin haihuwa. Ranar nayi tamkar bansan Sa'a ba
saboda biji-biji nai mata tare da dogon gargaɗi na saki ɗaya. Kamar Sa'a ta nutsu
bayan wani lokaci saita dawo da halinta na rashin arziƙi har ƙawaye take kawowa
suna haɗuwa cin zarafin Amina. Cikin amincin ALLAH Sa'a bata yaye Adamu ba saiga
Amina da ciki. Munyi murna sosai fiye da zato, ganin Amina itama ta samu cikin da
ake mata gori sai Sa'a ta sake sabon salon iskanci, Amina dai bata kulata dan ta
bama banza ajiyartane. Cikin ikon ALLAH itama cikinta yakai haihuwa ta haifi mace
wadda taci suna Bilkisu (mamanka kenan) dariya Sa'a taitayi alokacin da faɗin ai
dai itace a sama tunda namiji gareta, Amina dai bata kulatan, bata yaye Bilkisu ba
sai ga wani ciki, Sa'a kuma shiru, hankalin Sa'a ya kuma tashi ainun da wannan ciki
na Amina harta sake haihuwa bata barta ta hutaba, a wannan haihuwarma dai mace ta
samu itace Wasila (Ummah babba). dukda Sa'a ta nuna bata damuba tunda Amina mace ta
sake haihuwa saita kasa daurewa, tashiga ƙananun magana Amina tai mata asiri
haihuwarta ta tsaya, tun ina tsawatarwa har al'amari yafi ƙarfina na saki Sa'a saki
biyu ya zama uku dan al'amarinta ya isheni. Wannan saki yama dangina daɗi yama nata
zafi dan dangina dama babu mai sonta sai ƙalilan a cikinsu. Nayi ƙoƙarin na amshi
Adamu amma kakar Sa'a tace ban isaba, duk hanyar data dace nabi suka hanani ɗana,
acewarsu kishiya bazata riƙe musu yaroba wataran ta kashesa. Rabuwarmu da Sa'a da
shekara guda Amina ta sake haihuwar mace dai again, wadda taci sunan Rahamah (ɗiyar
Alhaji babba wadda ta rasu) haihuwar Rahama babu jimawa kakar Sa'a ta rasu,
alokacinne na shirya amshe yarona dan banaso ya tashi da kalar tarbiyyar gidansu,
sai dai a randa naje nai magana da mahaifinta washe gari aka nema Sa'a aka rasa ta
gudu da Adamu. Neman duniya anyi babu wanda yaga Sa'a, munɗauki tsahon lokaci muna
nemanta amma babu Sa'a babu labarinta. Har kuma ALLAH yayma Amina rasuwa ta barni
da ƴaƴa huɗu duk mata ban sakejin ko labarin Sa'a ba balle yarona, kullum yana a
raina, dan harda Maryam mun taɓa yin labarinsa”.
Ajiyar zuciya Jawaad ya sauke yana mai jinjina al'amarin a ransa, yace, “to Amma
baba miya nisantaka da danginta harmu bamu taɓa saninsu ba ballema shi labarin
Uncle ɗin? Tunda gashi dai alamu sun nuna shi Uncle ɗin ya dawo gida har yay aurema
kenan ya haifi Miemaa”.
“Kasan na faɗa maka dama akwai damuwa tun hanani aurenta da akai a farko, sannan
koda mukai aure danginta sunajin zafin mahaifiyata dani kaina, badanma sunso Sa'a
ta dawo ta aureni ba, bayan guduwarta kuma sai abubuwa suka sake ƙwaɓewa suka ɗaura
laifin akan Amina ce tai mata kurciya tabar gari saboda ita ƴaƴanta matane Adamu
kuma namijine, dalilin wannan sheɗancin nasu nema yasa nayo nesa dasu na dawo nan
dan lokacin garin bai haɗe ya zama babba ba gaba ɗaya kamar yanzun, ahankali
abubuwa sukaita canjawa dangi makusanta sunata ƙarewa, shiyyasa kusancin namu ya
sake taɓarɓarewa ma baki ɗaya tunda wanda za'aiyi dominsa babu shi tare dasu”.
Kai kawai Jawaad ke iya jinjinawa amma ya kasa magana, Alhaji babba ya katse shirun
nasu da faɗin, “Duk da na daɗe banga Adamu ba tun yana yaro amma ƴarsa sai ta ɗakko
kamanin Rahamah sosai musamman tana yarinya fiye da nasa kamannin, dan ni randa na
farama ganinta a asibiti kamannin Rahamah na gani tattare da ita bana Adamu kawai
ba, hikimar UBANGIJI kenan mai tsara yanda yaso a lokacin da yaso, Jawaad yanzu
kenan Adamu baya raye?”. Cikin damuwa Jay ya jinjinama Alhaji babba kai, “Ta
faɗamin mahaifinta ya rasu bayan rasuwar mamanta kusan shekara bakwai kenan ana
cikin na takwas, kuma a yanda bayanai suka nunama kenan anan ɗin ya rasu, to amma
abinda yama ɗauremin kai sufa danginsa ma suna nuna tamkar bashi da wata alaƙa da
ɗiyar tasane fa, wannanne dalilin daya raunana zumincinsu ya dawo gefe yana
rayuwarsa shi da matarsa kawai da yarinyar, kuma ko bayan rasuwarsa abinda yasa
sukai watsi da ita kenan sai dai batasaniba ita”.
“Jawaad ban gane basu da alaƙa ba, duk wanda ya kalli matarka aiko yaga jinin Adamu
ai”. “Gaskiya ne Baba, a hoton dai kam daka gani kasan jinsa ce, nima inason zuwa
da kaina garesu naji miyasa suke nisantashi da abinda alamomi suka nuna nasa ne?”.
“Bakai kaɗai zakajeba Jawaad, tare zamuje ai, dan nima ina buƙatar amsoshi da yawa
a garesun”. Sun daɗe suna tattaunawa akan batun kafin jay yayma Alhaji babb sallama
ya tafi asibiti.
★★★★★★
Tunda ya shiga asibitin sukai masa caa da idanu, shiko ya fuske abinsa fuska a
ɗaure ya gaidasu da tambayar jikin Shahudah, kafin ya shiga ya dubata tana barci
har yanzun, dan data farka suke sake mata wata allurar barcin tunda taƙi kwantar da
hankalinta ta saurari kowa, ta dage sai an kira mata Jay.
fitowa yay daga ɗakin ya dawo wajensu da nufin yimusu sallama ya kama gabansa, amma
sai mama Atika ta dubesa cikin gadara fuska babu wasa tace, “Mun gama magana da
ƙannen ubanka yau bayan sallar azhar za'a maida aurenka da Sabira, kuma gobe idan
ALLAH ya kaimu zata tare koda ba'a sallameta daga asibitin ba”.
Wani lallausan murmushi Jay ya saki da ya bama kowa al'ajab da mamaki, dan ba
murmushin sukai tunanin gani daga garesa ba. Ya kalli mama Atika da ƙyau yana tura
hannayensa cikin aljihun wandon shaddarsa da gyara tsaiwa yace, “Shi kuma mijinta
yaya zakuyi dashi”. Yay maganar da maida kallonsa ga ƙofar shigowa.
Gaba ɗaya suka maida kallonsu ga ƙofar inda ɗan-fir'auna ke tsaye akan ƙafafunsa ya
warke sarai sai tabbunan raunikan da yaji waɗanda basu gama bajewa da
ƙyauba.............✍
(Kana basu pepe da ginger ɗan bilkisu da Abdul-Aziz mijin bilkisu🤣😂🚴🏼)

______________________
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[1/2, 11:31 AM] HASNA✍🏻: Billyn Abdul:


Page 41

.................A firgice Mama Atika, Dad, Mom, Uncle Nasir, Uncle Uwaisu,
Aamilah, Salman duk suka miƙe baki hangame. Uncle Sulaiman da Uncle Sadiq da
basusan komaiba illa cewar ɗan fir'auna ya mutu suka bisu da kallo dansu basusan
ɗan fir'aunan ba a zahiri har yanzun. Cikin tsananin firgici da suɓutar baki Mama
Atika tace, “Nasiru ba kunce sheɗanin nan ya mutu ba wai?”. Rasa mai bata amsa akai
a cikinsu.
Ƙyalƙyalewa da dariya ɗan-fir'auna yay irin ta asalin tsagerun nan da
suka gama gawurta a fitsara, ya nuna Mama Atika yana tsuke fuskar tamkar ba shine
ya gama dariyar ba, “Ke dai tsohuwarnan anyi ƴar buƙulu, to idanma na mutu ban
kwashi garaba ashe kanwa na kawo duniya, koda yake ashefa shirya kasheni akai ko?
To anyi tabanza dan shegen taurin raine dani zanyi dogon zamani fiye da naki, a
nunamin inda matata take malamai”. Jikin Aamilah na rawa tace, “Brother ga shi
nan”. Harara ya zabga mata, “K dan tsohuwarki waye Brother ɗin? Yayah zaki ringa
cemin dan gyatuminki hausa zakimin, kujimin faratun banza mai suffar yahudawan
farkon ƙarni”. “Kayi haƙuri dan ALLAH yaya bazan sakeba” tai magana tana komawa
bayan Jay da yay kunnen uwar shegu dasu kamar baisan wainar da ake toyawaba ta
maƙale, Jay wayama yake latsawa abinsa hankali kwance kamar baya wajen. Dariya ɗan-
fir'auna ya sake kecewa da ita yana faɗin, “Kaji bayani, da kikace ke tsagerace?
Hegiya nifa bar ganinki ƙanwar matata billahillazi jinake kamarfa nai miki eyane
dan zaki bada kala a garin maji daɗi. Amma kinci arziƙin musulunci ba'a wannan
haɗin. Oga bara na shige daga ciki duk da fa inajin nauyinka fuska kawai zanyi
aradun ALLAH na siɗaɗa”. Yay maganar da wani ɗora hannu ɗaya kan ɗaya irin salon
nan na gaisuwar gayu ga na gaba dasu. (ALLAH ya daidaita sahunka akan lokaci
habibullah😂🤣)
Jawaad da baiko ɗagoba ya jinjina masa kai kawai yana cigaba da aikin latsa
wayarsa. Sai da ɗan fir'auna ya shige ɗakin da Shahudah ke kwance sannan Jay ya
ɗago yana kallon Dad da yay sagade kamar wani gunkin hanya yana kallon ƙofar,
firgigit ya dawo hayyacinsa saboda bugo ƙofar da ɗan-fir'auna yayi da masifar
ƙarfi.
Inda Jay yake ya nufa da sauri-sauri yana baza babbar riga, Muryarsa da
zafi ya furta, “Inason muyi magana”. Kallonsa kawai Jay yayi baice komaiba, sai dai
fuskarsa shima a haɗen take, da ya kai maƙurar da ayanzu zai ɗauki matakin da bai
ɗaukaba ada akan kowa. Guntun Murmushi yay da miƙewa yana ɗan kallonsu Uncle Nasir
da suka zubo musu idanu. Rai a ɓace Dady yace, “Jawaad!!....” saurin ɗaga masa
hannu Jay yayi batare daya kallesa ba. “Karkai saurin harzuƙa, muje waje muyi
maganar”. Ɗauke kai Dady yayi kamar bazai sake tankawa ba sai kuma miya tuna oho ya
nufi ƙofar fita yana jiyo kukan Momy dake sukar masa zuciya. Tashi Jay yay shima ya
fice baiko kalli inda ƴan gidan nasu sukeba balle ya nuna yaji ihun kukan Momy dana
Mama Atika.
A can gefe inda babu mutane ya hango Dad nata kai kawo ransa a
ƙololuwar ɓace, Jay yay ɗan murmushi ya ƙarisa. Kallonsa Dad yay ya ɗauke kansa,
“Jawaad!! Tun muna ƴar kunyar juna ka saka wannan ɗan iskan yaron ya sakarmin
yarinya ta”. Murmushi Jay yayi da tura hannunsa ɗaya aljihu ɗaya kuma ya shafi
kumatunsa da gashin saje ke kwance kaɗan saboda yana askewa, “Miyasa kukai tunanin
kashesa ne zai baku mafita domin farin cikin ƴarku?. Irin wannan raɗaɗin da kakeji
a yanzun, ita kuka shiryama taji mafiyisa Dad, Miye dalilinku na janta jikinku
bayan baƙwa buƙatar ta raɓu jininku?........”
Dady ya kallesa da ɓacin rai sosai ya katsesa da faɗin, “Ya ina maka
magana akan Mamana kanamin wata banzar magana taka mara tushe?”. Haɗe fuska Jawaad
yayi da tura ɗayan hannunsa aljihu cikin ƙoƙarin danne nasa fushin yace, “Banason
mu bama juna wahala, dan inhar muka kai ga haka komaima zan bankaɗo babu ruwana,
dan haka mu tsaya iya haka ɗin kamar zaifi sauƙi. Batun Hudah na riga na gama da
wannan matsalar yanzu tsakanin kune ku da sirikinku. Lokaci yayi da zaku nuna
gajiyawar da baƙwaso a gareta na bakomai zaku iya bata ba, ALLAH shike bada komai
ga wanda yaso a lokacin da yaso ba mutum ma

i barci, mai mutuwa, mai mantuwa ba. Koda yake, wannan bashi bane matsalata. Minene
Ya kai Qaseem China kuma?!”.
“Kai Jawaad!! Tsagerancin naka da su Alhaji Nasiru ke faɗa har yazo kaina
nima kenan? Minene matsalarka ko alaƙarka kuma da barin Qaseem ƙasar nan?, Qaseem
fa ɗanane, babu kuma wanda ya isa ya sakani koya hanani a kansa, itama bilkisun ba
tsoro yasa na bar maka itaba dan inada ikon hanaka auren nata tunda ɗiyar ƴar uwa
tace, a hannuna kuma ka ganta. Niba sa'an yinka bane, ka kama kanka kajiki”. Ya
ƙare maganar da fara tafiya zai bar wajen.
Jay dake binsa da kallo yay murmushi, “Tabbas kanada iko da ita fiyema da
hakan, kuma har gobe ita kallon uba take maka dan ta baka dukkan yarda kai da
ahalinka, babu wani laifinku da take kallo laifi sai dai kuskure. Haka take komai
nata irin na masu ƙyaƙyƙyawar zuciya ne, tana ƙyautatama kowa zato musamman wanda
ya nuna tausayinta saboda a irin rayuwar data tsinci kanta ciki, Dady ka daina
tunanin har yanzu al'amarin a rufe yake, na tanadi hanyoyi masu yawa dazan bankaɗo
komai harda na Qaseem da kukai ƙoƙarin rufewa dan ina bibiyarsa kuka turasa China”.
Juyowa Dad yay daga tsayuwar da yay tun fara maganar Jay. Idanu suka
zubama juna na kusan mintuna biyu kafin Dady yay wani murmushi yana girgiza kansa.
Batare da yace komaiba ya juya ya tafi.
Da kallo kawai Jay ya bisa har ya shige, ya lumshe idanu da furzar da huci
mai zafi daga bakinsa, batare da yay ƙoƙarin sake komawa cikiba ya nufi motarsa ya
bar asibitin

A ciki kuwa tunda ɗan fir'auna ya shiga da maida ƙofar ya rufe babu
wanda ya sake jin ɗuriyarsa balle sanin mi yayi a ciki har saida Dad ya koma ciki
da kusan mintuna biyar sannan ya fito yana wani ɗan iskan washe baki kamar gonar
audiga. tsayuwa yay ya gama kallesu a ɗage sannan ya wuce batare da yacema kowa
komaiba, sai wani rangaji yake irin na tsageru tamkar wani bishiyar giginya.
Babu wanda ya iya cewa uffan dan har ransu tsoronsa sukeji, sai da ya kai
ƙofa sai kuma ya juyi da sauri, “Af kunga nayi mantuwa zan wuce, Surukina inafa da
magana da kai a ina zamu haɗu mu tattauna ta?”. Kafin Dad yay magana Uncle Sulaiman
yace, “Haba yarona, hakan duk bai kamataba kaji, koba k.......” Da sauri ɗan-
fir'auna ya katse Uncle Sulaiman cikin ɗaga masa hannu da faɗin, “Nifa ka ganninan
duk tsagerancina ina girmama masu mutunci, kai Uncle ɗin Ogane mai daraja babba,
dan ALLAH na roƙeka ka zama ɗan kallo, dan ko takalmin Oga bazan so na takaba balle
kai Uncle ɗinsa”. Uncle Sulaiman ya jinjina kansa kawai batare daya ƙarasa abinda
ya faroba, sai dai a ransa yana mamaki. Juyawa ɗan fir'auna yay yana faɗin, “Duk da
ni mutumne mai kunya da baya son yawan shiga gidan surukai Zanzo gida na sameka
surukina”.
Kallo kawai suka iya binsa dashi harya fice tamkar wasu wawaye babu wanda ya
iya sake tanka masa.

___________________________

Ɓangaren su Bilkisu kam sunsha firarsu cike da nishaɗi kasancewar


sun daɗe basu sami damar irin wannan haɗuwar ba, abincin da driver ya kawo daga
gidan Ummah babba suka ci, dan Nabeelah ƙin biyosa tayi dan tazata Jawaad na gidan.
Sai dai batasanma yana tafe zuwa gidan nasu ba, dan bayan sallar azhar can ya nufa.
Tana falo zaune tana kumburin fushin Ummah tace taje tai kitso yay sallama. Ai da
wani shegen gudu ta kwasa sai ɗakinta ta garƙame ƙofa. Hakan datai ya saka kowa
fahimtar laifi tai masa.
Zama yay suka gaisa da Ummah tare da musu godiyar hidima da gajiyar taro,
Aunty Batool ma ta gaidashi da tambayarsa bilkisu. Anan yaci abincin rana suka ɗan
tattauna da Ummah akan abinda ke faruwa, kuka rurus Ummah keyi na farin ciki da
al'ajabi, kai ita kanta tana mamakin irin yanda takejin Bilkisu har cikin jinin
jikinta da ɓargo, san nan tana hango abubuwa da yawa dake mata kamanceceniya da
jininta tattare da Bilkisun amma tarasa wacece?, wato jini ya wuce gaban wasa duk
inda yake. Tace, “Jawaad bazan iya haƙuri ba gobe idan ALLAH ya kaimu zaka ganni a
gidanku”. Murmushi Jay yayi, “To ai Ummah itama bata saniba, bamason ta san komai
yanzun har sai mun bincika sauran

abinda ke faruwar tukunna, dan kinga al'amarin yazo da ruɗani a ciki”. Shiru Ummah
tai na wasu sakanni, cikin sauke ajiyar zuciya tace, “Hakane kuma Jawaad, rashin
faɗa matan yanzu yanada amfani, dan ko ƴan gidanku karmu bari su sani yanzun sai
mun gama sanin komai mu kanmu”. Jay yace, “Insha ALLAHU Ummah bazasu sani ba”.
Baibar gidan Ummah ba sai kusan ƙarfe uku na rana. Daga nan gida Ummah
ƙarama yaje itama, itakam harma tafi Ummah Babba shiga ruɗani, saboda ita mutumce
mai ƙarancin juriya akan farin ciki ko ɓacin rai, duk wanda ta tsinci kanta a ciki
saika ganesa tattare da ita. itama dai ya jima anan suna tattaunawa, dan saida akai
sallar la'asar sannan ya baro gidan.
Gida ya nufa dan a gajiye yake ga barci yanaji sosai cikin idanunsa.
Dai-dai traffic light ta tsayar dashi idonsa ya hango masa ɓaleru cikin mota, wanda
ke a bayan motar ya kalla ya ɗauke kansa, sai kuma yay saurin sake kallon motar.
Abinda ya faɗo masa a raine ya sakashi saurin ɗaukar wayarsa ya shiga WhatsApp,
saƙon gimba da har yanzu yana nan ya kunna, ya maimaita dai-dai inda gimba yake
sanar masa sunan Alh...Alh..k......
Ganin an basu hanya ya harba motar gaba hankalinsa nakan motar su ɓalerun,
gefen titi ya gangara yabi motar da kallo harta ɓacema ganinsa, a fili ya furta
‘Tabbas Alhaji Kokino Gimba kake nufi’ yay maganar da ɗan dukan sitiyarin motar
yana cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi, kafin ya furzar da huci mai ƙarfi ya kife
kansa a sitiyarin na kusan tsahon mintuna bakwai. Tabbas inhar tunaninsa nakan dai-
dai matarnan ce, to minene alaƙarta da Gimba?. Bashi da mai bashi amsa, dan haka
wayarsa ya ɗauka yay kira, bugu biyu kuwa aka ɗaga daga can cike da girmamawa. Bai
tsaya sauraren gaisuwarba yace, “Hameed kana tare da ɓaleru ne yanzu haka?”. Daga
can aka amsa masa da, “Yes Sir, ai da naga ma irin sabuwar motarka a traffic yanzu
har na ɗauka kaine”. “Kaga manta da wannan, wa yake ja a motar?”. “Alhaji Sadi
Kokino ne sir” “Ka tabbata shine?”. “Wlhy shine Sir”. Shiru Jay yayi yana murza
goshinsa, ya sauke zazzafan numfashi da faɗin, “Amma kacemin Drivern Mr Gebrail ne
ai?”. “Wlhy Sir tunda na fara aikin nan tare da shi nake ganinsa, ni kaina yau da
naga ya ɗauki Alhaji Kokinon nasha mamaki, shiyyasa ban gazaba wajen bibiyarsu”.
Sitiyari Jay ya sake daka da ƙarfi, “Hameed akwai matsala, kodai sun shirya bada
ƙafane dama dankar a bibiyesu, kokuma sunada tabbacin akwai mai bibiyarsu, yanzu
haka suna ina?”. “To Sir nikam ka sakani a ruɗani, amma gamu a anguwar Sanni zasu
shiga wani gida mai farin gate”. “Maza kabar wajennan Hameed, kuma duk abinda ka
gani bai makaba ka tabbatar ka kirani, gobe idan ALLAH ya kaimu kazo ka sameni a
A.Y street”. Cikin mamakin da babu damar tambaya Hameed yace, “Okey Sire”. Yanke
wayar Jay yayi ya maida akalar kiran ga Jabeer, yana ɗagawa shima bai saurari
tsokanar da yake masaba ta ango ango yace, “Jabeer kuna Office ne?”. “Eh muna
Office, lafiya naji muryarka haka?”. “Jabeer inason yanzun nan ku bincikamin Number
da Gimba yay wayar ƙarshe da ita a randa aka ɗaukesa, a ina mai ita yake yanzu
haka? Sannan macece ko namiji?”. “Okey boss ina zuwa”. Yanke kiran Jawaad yayi ya
tada motarsa yabar wajen, kansa tsaye tashar da ake hawan motar garin su Gimba ya
nufa. Nesa da wajen yay fakin tare da kiran Dattijon nan a waya. Mintuna uku kuwa
basu cikaba sai gashi. Motar ya buɗe masa ya shiga sannan ya maida ya rufe. Saida
suka gaisa Jay yace, “Ka tabbatar yarinyarnan tana mana aikin da muke buƙata?”
“Sosai kuwa Alhaji, ai itama kanta batasan aiki take manaba a kansa, yanzu haka
ɗazun take sanarmin wai yau zasuje wani gidan dirama wani mawaƙi zaiyi wasa na
musamman akan soyayyarsu da ɓalerun”. Murmushi Jay dake ɗan wasa da yatsun hannunsa
saman sitiyari yayi, “Address ɗin wajen, sunan mawaƙin, time ɗin da zai shiga wajen
da tashinsa?”. Dattijo yay ƴar dariya da faɗin, “Ai Alhaji kamar dama nasan zaka
tambaya duk sai da na samo waɗanan amsoshin kaf, gasu a rubuce”. Amasar takardar
Jay yayi yana jinjina kai, ya ciro kuɗi ya miƙa masa yana faɗin, “Ga cikon kuɗin
aikinka nagode”. Baki a washe dattijo yac

e, “Nine da godiya ai Alhaji, ALLAH ya ƙara buɗi na alkairi, idan wani aikinma ya
taso wlhy a kawo zanyi”. Jawaad baice komaiba sai murmushi kawai.
Dattijo na fita kiran Jabeer na shigowa, ɗagawa yay yasa a kunne batare da
yayi magana ba. Daga can Jabeer yace, “Tabbas Boss mace ce, sunan da tai register
layin dashi shine Safara'u Hashimu, kakanta Bala, sunan mahaifiyarta Indo,
kakaninta na wajen uwa Hassan da Baraka, shekarunta sittin da huɗu a duniya,
asalinta ƴar garin Tsamiya ce, yanzu haka alama ta nuna ana amfani da layin a
anguwar Habbun.........” Jay ya katsesa da faɗin, “Habbun kuma? Ba garin nan bafa
kenan?”. “Kwarai hakane”. Baya Jay yay ya jingina da kujerar yana furzar da huci,
kafin yace, “Hasashena ba dai-dai bane kenan?”. Daga can Jabeer yace, “Kai minene
hasashen naka da?”. “Jabeer akwai wata mata lokacin case ɗin nan na Alhaji kokino
mun haɗu da ita a gidansa idan baka mantaba itace ta taimakemu sosai har muka ɗauke
mata yaro mai suna Yazeed, da ina zargin itace Gimba ke magana a gidan Alhajin nan
da bai ƙarisa faɗaba”. “Tabbas Boss hasashenka ba kuskure bane, tun a wancan
lokacin naso nace muku kodai Alhaji Kokino Gimba ke nufi, dan na taɓa ganinsa a
ƙofar gidan farkon fara maka aiki lokacin bikinmu da Surayya, kasan matar Alhaji
kokino ƙanwar maman tace, yanzu abinda za'ai shine kabani daga nan zuwa safiya
insha ALLAHU zan bincika komai”. “Okey babu damuwa, shima yaron nan yau insha
ALLAHU zan kamashi dan na kula akwai wani abu damu bamu saniba”. “A'a haba boss, ka
bari wani a cikinmu ya kamashi mana, karka shigarma Mami lokacinta, amma mika
hasaso mana”. “Da kaina zan kamashi Jabeer, dan akwai saƙon da nakeson bari a kamun
nasa, abinda na hasaso kuma sai mun haɗu zamu tattauna”. Ya kashe ƙittt batare da
ya jira amsar Jabeer ɗinba.
Wayar Bilkisu ya kira, sai da ta kusa tsinkewa ta ɗaga dan bata kawo a ranta
shi bane, ba Number data sani bace. Shiru tai taƙi magana, dan haka shi yay
sallama. Yanda ta amsa sallamar ne yasashi fahimtar ta gane wanene yanzun, zamansa
ya gyara da ƙoƙarin dai-daita muryarsa dake cike da ɓacin rai, “Am sorry kicema
ƙawayenki suje kawai zan haɗu dasu zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, wani uziri yane
ya riƙeni gaba ɗaya shiyyasa ban dawo ba”. Murya a sanyaye bily tace, “To zan faɗa
musu, amma bakaci abinciba fa, haka kake yawo da yunwa?”. Idanun Jawaad ya lumshe
yana murmushi, ji yay duk ɓacin ran da ya tarar masa a ƙirji yana guduwa, yace,
“Karki damu da anyi magriba zan dawo isha ALLAH, jin muryarki kawai tasa nama
ƙoshi, ke dai ki shirya amsar angonki kawai ƙanwar Jay.......” ƙittt ta yanke wayar
daga can.
Jawaad ya girgiza kansa yana murmushi har kumatunsa na loɓawa, motar ya
tada yay gaba har lokacin murmushi ya gaza barin fuskarsa.

___________________________

Tunda su Zuhrah suka wuce sai naji gidan duk babu daɗi, ga wani motse-
motse da naketa famanji amma narasa takamaimai a ina nake jinsan, nai jarumtar
dakewa dan bana son na ruɗar da kaina, sai kuma na koma ganin tamkar gittawar
inuwoyi ta jikin Windows, da farko dai naso fita na leƙa waje, sai kuma wata zuciya
ta gargaɗeni dayin hakan, yanda kaina ya farayin nauyine yasa na jawo wayata na
kunna karatun Al-Qur'ani mai girma, a hankali nutsuwa ta fara saukarmin, naji kaina
ya saki na koma normal, gidan kuma yay wani irin yin tsitt mai ban mamaki, babu
motsin nan sam, ko ƙarar na'urorin dake aiki da wutar dake a kwai duk bakajin
ƙararsu, ban ɗauki hakan komaiba na cigaba da zama a falon har aka fara kiraye-
kirayen sallar magriba, Miƙewa nai da shirin sake wanka, dan ɗazun lokacin sallar
azhar da zanyi salla ganin ɗingon jini yasa banyi ba, amma yanzu dana duba gab da
su Ummie zasu wuce kuma ya sake ɗaukewa, dama nasan ɗazun nayi gaggawar yin wanka
dan ƙa'idane sai bayan sallar azhar nake wanka ko la'asar duk da lokaci kan ɗan
canja min wani watan.
Wayar na ɗauka na shige bedroom, Kayan da zan saka na fara cirowa a drawer
na ajiye, dan waɗan nan dazan cire ɗin jini yaɗan ɗiga a sket ɗin kaɗan sai yanzu
na kula ma. Batare dana kashe karatunba nabar wayar a saman gado na cire

kayan na shiga bayin, ban jimaba na fito gudun kar lokacin salla ya ƙwace min.
Saida na farayin sallar magriba sannan. Saboda wutar dake akwai sai na jona hand
dryer a soket kawai, nai zaman fara busar da gashina.
Karatun Al-Qur'anin dana sakane yasa sam banji motsin shigowarsa ɗakin ba,
sai da yay sallama, da sauri na juyo dan banyi tunanin ganinsa ba.
Jay da tun ɗazun yaketa faman sallama ya ɗan tsura mata idanu, daya shigo
baiga kowa a falo ba, har yay tunanin nufar nasa ɗakin sai kuma ya nufo nan saboda
jiyo sautin karatu.
Towel ɗin dana tsane kai na ɗauka na ɗaura a kafaɗa ta ya ɗan rufemin ƙirji,
wanda na ɗaura ɗin kuma sai faman jansa nake ƙasa dan cinyoyina duk a waje suƙe.
Ganin ya ɗauke kansa tamkar baiga abinda nakeyinba ya sakani saurin cemasa, “Sannu
da zuwa”. “Yauwa sannunki kema”. Ya faɗa yana ƙarasowa cikin ɗakin sosai. Zama yay
a bakin gadon yana sauke numfashi alamar gajiya. Daurewa nai na tashi, na raɓa ta
gefensa na ɗauka kayana dake saman gadon zan nufi bayi dan na saka sannan na dawo
ɗauka masa ruwa da zaman busar da kan.
“Da miye na saurin yin wankan tunda kinsan bai tafiba?”. Maganarsa
tazomin a bazata. Cak na tsaya tare dayin ƙasa da kaina dan ni bansan wace amsa zan
bashi ba nikam, yaushe yasan nayi wankan to? Anya boss bai gani har hanji kuwa?.
Ganin yanda ta wani tsume waje guda ya sakashi miƙewa yana girgiza kansa,
zare rigarsa yayi ya raɓata ya wuce batare da ya sake cewa komai ba.
Ganin ya shige bayi nai azamar saka kayan sauri-sauri sannan na fita na
ɗaukko masa ruwa, zaman busar da kan na sakeyi yanzun kam hankalina kwance, saukar
laimar ruwa da naji a kan hannuna ya sakani saurin ɗagowa na kalli mirror'n, shine
tsaye a bayana, sakar masa hand dryern da yake ƙoƙarin amsa a hannuna nayi ina
rumtse idanu, dan wani irin masifaffen harbawa zuciyata tayi, karan farko da naga
namiji a tuɓe kamar haka a gabana bayan jazuga da baida wani fasalin kirki irin na
zaratan maza. a raina rayawa nake, ‘Wai miyasa maza sam basu da kunya ne? Daga shi
fa sai towel iya ƙugu zuwa gwiwa amma ya iya fitowa gabana ya tsaya’.
Jay da duk yana kallon yanda ta rikice ta cikin mirror'n yay guntun murmushi
kawai yana ƙarasa busar mata da kan, sai da ya gama tsaf ya ɗauki ribbon ɗin da
yaga ta ajiye ya ɗaure matashi tsaf fiyema da yanda zatayi, harda su mata wani ɗan
style da brush. Kujerar ya juya ya maido fuskarta inda yake kafin ya miƙar da ita
tsaye ya ɗaura duka hannayenta saman ƙirjinsa daketa raɓar ruwan wanka. “Buɗe
idonki” ya faɗa babu wasa.
Hannunta dake ɗan rawa tai ƙoƙarin zamewa tana maƙe kafaɗa alamar “Ah-
ah”. hannun nata ya maida da ƙyau, yana bin fuskarta da kallo. A bazata ya sumbaci
inda batai zatoba duk da akwai riga a jikinta. A take ta waro idanu waje da masifar
sauri tare da buɗe baki. Babu shiri Jay ya ƙyalƙyale da dariyar da bai niyyaba, dan
yaga tsoron nata fiyye da yanda yake son gani.
Bilkisu tai saurin duƙewa tana matse hannayenta duka biyu a ƙirjinta tare da
cusa kanta duka a cikin cinyoyinta tana murmushi, dan ita kanta tabama kanta
dariyar abinda tayin. Ga kunya mai tsanani akan abinda yayi ta lulluɓeta. Kafaɗunta
ya kama ya ɗagota yana murmushi, duk yanda yaso su haɗa ido taƙi, daga ƙarshema
saita ɗora kanta a ƙirjinsa ta ɓoye fuskar. Rungumeta yay da duka hannayensa yana
murmushi tare da shaƙar ƙamshin da gashinta keyi da jikinma nata ya lumshe idanu.
Kusan mintuna biyu suna a haka sannan ya zauna a bakin gadon ya ɗaurata saman
cinyarsa. Fuskarta ya ɗago yanda zata kallesa duk da dai tanata faman yin ƙasa da
idanu amma tana ganin fuskar tashi. Laɓɓansa ya nuna mata da ɗan yatsa yana wani
ƙanƙance idanunsa. Kafaɗa ta maƙe da sake maida kanta a ƙirjinsa.
“Ni ai sai nayi” yay maganar yana yin baya dasu a kan gadon ya birkiceta ta
koma ƙasa. A take idanun bily sukayo waje, hanata dukkannin dama yay ya shiga yin
yanda yaso da ita.
Kiran sallar isha'i ne ya ƙwaci Bilkisu a hannun Boss, shima da
ƙyar, dan daga kiss sai salon ya nema canjawa. Tunda ta samu ya barta ta cusa kanta
cikin filos. Baice da i
i buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an
kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

ta komaiba shima ya fice yana murmushi. Ɗakinsa ya nufa ya sake ɗaura alwala da
canja kayansa zuwa blue jeans da t-shirt itama Blue, ya saka turare kaɗan da ɗaukar
wata ƴar ƙaramar bindiga ya saka a gefen ƙugunsa sannan ya fito. Ɗakin Bilkisu ya
koma. isketa yay ta fito daga toilet fuska a jiƙe alamar alwala tayo. Ruwan data
ajiye masa ɗazun ya ɗauka yana sha idonsa a kanta. Kofin ya ajiye yana kallon
agogon hannunsa, “Bara naje za'a shiga salla, idan an idar zan ɗan ƙarasa wani waje
insha ALLAH kafin goma zan dawo.
Da sauri Bilkisu ta kallesa idanu cike da ƙwalla, “Dan ALLAH mu tafi tare,
nidai tsoro nakeji”. Yanda ta kumbura baki taso bashi dariya, amma sai ya danne
abinsa ya taka zuwa inda take tsaye, fuskarta data duƙar yasa hannu ya ɗago, acan
ƙasan maƙoshi yace, “Kin taɓa ganin amaryar kwana ɗaya a gidan miji ta fita?”. “To
ai babu wanda zaisan na fita tunda dare ne”. Fuskar tata ya saki yana ɗan ɗage
kafaɗa, “Okey, ki shirya kafin na dawo salla saimu je”. Cike da murna ta amsa masa
da to. Goshinta ya sumbata ya juya ya fice yana murmushi dan wayo kawai yay mata ba
dawowa zaiyi ba.

Ana idar da salla Jay ya fito daga massallaci, motarsa da dama ya bari a
waje bai shiga da ita gida ba ya shiga ya bar anguwar, kai tsaye address ɗin da
dattijon nan ya bashi ya nufa, anguwace irin sabuwar anguwarnan da uncompleted
building sukama fi yawa, sai dai inda gidan drama'n yake anɗan gaggama wasu gidajen
dan wajen harya fidda santa ɗoɗar, bakajin hayaniyar komai saina Genretor ɗin da
suka kunna da ƴar hayaniyarsu alamar basu gama zuwa ba, akwai ƙwayayen wuta a waje
da suka haska kusan rabin layin, sai mai Nama daketa faman haɗa wuta, gefensa mutum
biyune ɗaya mai ruwa ɗa kayan drinks, sai saurayi da budurwa dake can gefe suna
hira, sai kuma masu shiga da fita cikin gidan ɗai-ɗai dan yanzu suke kan zuwa. Waya
ya ɗauka yay kiran wani abokinsa da ya kasance ainahin police, saida suka gaisa ya
gama tsokanarsa da ango-ango, sannan Jay yace, “Auwal kuna garin nan amma tsageru
har suke da lasisin buɗe wuraren iskanci irin haka?”. Daga can Auwal yace, “Haba
dai Jay, kaima kasan hakan bazai kasanceba”. “Gashi kuwa na gani da idona, akwai
wani gidan Drama a sabuwar anguwar nan data kusa haɗewa da jan-ɓauna, inason ƙarfe
goma da rabi kuzo wajen kuyi kamen kan mai uwa da wabi”. Bai jira cewar Auwal ba
yace, “Mu kwana lafiya” ya yanke wayar. facemask ya ɗauka ya saka tare da facing
cap, kallon kasan yayi a madubi ya tabbatar komai yayi kafin ya fito bayan ya
kashe motar. Sai da ya tabbatar babu wanda yaga fitowarsa sannan ya nufi gidan.

★★★★★★

Ina idar da salla na koma bakin gado nai zaman jiransa, ganin shiru-shiru
sai kawai nahau yin game a waya, hamma na farayi ɗai-ɗai alamun inajin barci, nayi
guntun tsaki da kallon agogon ɗakin, tara saura minti ashirin, zamewa nai na kwanta
tare da jan filo na ɗaura kaina na cigaba da game ɗin, tun ina ƙoƙarin damƙe wayar
dake neman suɓuce min harna yaddata batare dana saniba.
A firgice na farka jikina na wani irin ƙyarma, ‘innalillahi wa'inna
ilaihirraji'un’ na shiga ambata ganin ɗakin dunɗum da duhu bayan kuma nasan fitilar
a kunne take, dariyar da aka tuntsure da ita ta sakani sake firgicewa nahau laluben
gadon.....
“Bilkisu! Kenan mai gadon zinari, wato ke amarya ko? Azatonki zaki iya
tsere minne? Ke da kina tunanin na barki? Wannan gurɓataccen tunanine bilkisa, na
rantse miki yau saina amshi abinda ya kasance cikar burina dan bazan rasa komai a
dalilinki ba wannan gangan ne hhhhhhhhhh!!!!!!!!.................✍

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gama
✍🏻
[1/4, 2:46 PM] HASNA : Page 42

..................Inda mai naman nan yake ya tsaya, batare da yayi magana ba ya


miƙama mai-naman 1k tare da nuna masa naman. Kallonsa yay a ƙufule, “Haba malam, ya
zakazo waje babu ko sallama ka miƙomin dubu wai na baka nama? An faɗa maka ni irin
sakarkarun masu saida naman nan ne da kuke rainama hankali, nibanma taɓa ganinka a
gidannan ba, kai wane?”. Jay ya danne takaicinsa cikin salon maganar kurame yay
masa nuni wai shi bebe ne”. Mai nama yace, “Oh to yanzu naji batu, kasan rainin
tsagerun gidannan ne bazan iya ɗaukaba shiyyasa kaima nai zaton kalarsu ne, na duka
kake so?”. Kai Jay ya jinjina masa. Mai nama ya fara yankowa yana sawa a takarda da
raira ƴar waƙarsa ta shata mai taken “Natsaya ga annabi Muhammadu.......” Jay dai
kallonsa yake da nazarin wajen harya kammala yanka masa, amsa yay da masa godiya ya
juya zai tafi, sai kuma ya juyo da sauri irin kamar yayi mantuwar nan. Ƴar takarda
ya ciro a aljihun wandonsa ya miƙama mai nama. Mai nama ya amsa da faɗin, “Miye
kuma wannan? Nifa kunsan ba wani boko nayiba amma kuyitamin wani lagude-laguden
jaraba. Kai Hamusu zo duba mi ya keso kuma?”. Wanda aka kira Hamisu dake gaban
lemuka ya amsa da “To baba”. Takardar ya amsa ya duba sannan ya kalli mai naman,
“Baba wai gidan Ɗan Alhaji ya keson a nuna masa”. Shiru mai naman yay yana kallon
Jawaad, mikuma ya tuna oho masa sai ya washe baki, “Af to inaga irin abokansa ne
daya ɗan gayyato, kasan yau zaiyi ajo”. Jinjina da hannu Jay yayma Mai nama irin ka
gane ɗinan. Mai-nama ya sake washe baki da nunama Jawaad wani gida dake can kusan
ƙarshen layin. Cikin alamar maganar kurame yayma Jay yay masa godiya da nufar inda
aka nuna masan.
Rufe gidan yake dan haka ya ƙwanƙwasa, sai da yay sau kusan baƙwai sannan
akazo aka ɓuɗe cike da masifa.
“Wai wane shegene yake bugama mutane gida haka? Sai kace ya bada ajiya ko an
ci masa bashi, idan akai haƙuri dai ai zan fito ba sai ansama lokacina ido b.....”
hankaɗa shin da Jawaad yay ya koma baya ya hanashi ƙarasa maganar, zai sake magana
Jay ya ɗaura hannunsa saman baki yace, “Shiiiiii”. yana ɗaga rigarsa bindiga ta
bayyana, jiki na rawa ɓaleru ya saka hannu ya toshe bakinsa yana faman zare idanu.
Ƙofar Jay ya maida ya kulle bayan yay wurgi da ledar naman daya shigo da ita, ya
sake kaima ɓaleru wani bahagon bugu tare da damƙo wuyan rigarsa ya miƙar dashi
tsaye. Batare da yay magana ba ya nuna masa hanyar cikin gidan. Jikin ɓaleru na
rawa ya shiga kaɗa kai tamkar wani ƙadangare.
Gidane madaidai ci yasha tiles har a jikin bango, ga hasken wutar Genretor da
alamu suka nuna na gidan drama ɗinne aka jawo masa har nan, ƙofar dake buɗe suka
shiga, budurwar dake kwance saman katifa tsirara ta miƙe da sauri zaune tana jan
bedsheet ɗin saman katifar ta ƙudundune kanta ciki zata zabga ihu.......
“Idan baki rufemin shegen bakin kiba saina ragargaza ƙasusuwanki wlhy!!”.
Jay yay magana cikin kaushin muryar da ta saka budurwar cusama bakinta bedsheet ɗin
tana zare idanu hawaye na ƙwarara, jikinta sai rawa yake.
Jawaad ya maida kallonsa ga ɓaleru da duk hankalinsa ke kan wayoyinsu dake
zube a ɗan table na glass ƙarami dake gefe. Ƙafa Jawaad yasa ya taɗesa ya faɗi ƙasa
tim, cikin zafin nama ya shiga sauke masa maruka a fuska da hannu bibbiyu. A take
ji da ganin ɓaleru suka gushe, gashi babu damar yin ihu yana tsoron bindiga. Sai da
Jay ya jigatashi da maruka ya tabbatar ya fita hayyacinsa sannan ya barshi.
Budurwar daketa gunjun kuka da faman ɓoye fuska ya kalla, “K zoki kashemin duk
wayoyin nan....”. Kafinma yakai ƙarshe harta miƙe zaram tana damƙe bedsheet ɗin da
ƙyau jikinta na rawa, wayoyin uku manya ta kashe sai ƙarama ɗaya. Yace, “Ina
taki?”. Nuna masa ɗaya daga cikin manyan tayi, ukun kuma tace, “N..na nashi ne
sauran”. Ɗauke kai Jay yay batare da ya sake cemata uffan ba, ya ɗauki Coc dake
ajiye yanata raɓar sanyi ya ɓalle murfin, saman fuskar ɓaleru daya suma ya juyeshi,
a take ɓaleru ya kawo numfashi. Wani marin Jay ya sake sauke masa a fuska. Take ya
dawo hayyacinsa ya fashe da kuka yana share jinin da yake fita daga hancinsa yana
sauka masa kan baki, “Dan ALLAH malam minai maka kake min irin wannan dukan? Idan
kuɗi kakeso ko nawane zan baka, nidai karka kasheni dan girman ALLAH, kag.....”
sake wanka masa wani marin Jawaad ya ƙarayi tare da ɗora ƙafarsa ɗaya kan katifar
ya ranƙwafo kansa da nuna masa fuskar wayarsa. “Wanene wannan?”. Ɓaleru da jikinsa
ke rawa ga jini nata fita masa ta hanci da gefen baki yace, “Ni...ni ban sanshi ba
wlhy”. “Baka sanshi ba! Kace baka sanshi ba?!!”. “Eh wlhy oga bamma taɓa ganinsa
ba”. “Yayi ƙyau” Jay ya faɗa yana miƙewa da tattare hannun rigarsa sosai yay sama.
Har Ɓaleru ya fara murna an barsa sai kawai ji yay Jay ya cakumo masa wuya ya miƙar
dashi tsaye da ƙyau. Mahaukacin duka ya shiga masa da babu algus, yanda yake bugun
nasa zai tabbatar maka zuciyar ƴan mazan a wuya take. Sam baya sauraren roƙon da
ɓaleru ke masa da kukan karuwarsa. Saida yay masa lilis sannan ya hankaɗashi ya
faɗa saman katifar kansa ya daki bango Ƙummm!!!!. Dafe kan Ɓaleru yay da sakin wata
wahalalliyar ƙara, saiga jini sharrrr. Jay ya sake cakumo wuyansa ya shaƙesa da
ƙyau da hannu guda, ɗayan kuma ya sake nuna masa hoton Gimba dake tare dashi da
suka ɗauka a gidan gonarsa wani zuwa da suka taɓayi tare. Yace, “Har yanzu dai baka
sanshin ba?!”. “Dan ALLAH ka tausayamin oga ka daina dukana karka halakani na
sanshi, Abokina ne sunanasa Gimba garinmu ɗaya”. Ɗauke fuskarsa Jay ya sakeyi da
mari yana faɗin, “Ɗan iska kake son maidanine da?”. “Na tuba dan ALLAH kayi haƙuri
bazan sake maka ƙarya ba”. Miƙewa Jay yay tsaye ya kaima Ɓaleru harbi a ƙafa da
tofa masa yawu, sai faman huci yake, jiyake tamkar ya kashe banzan nan ko zaiji
sauƙin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa.

________________________

Bilkisu! Kenan mai gadon zinari, wato ke amarya ko? Azatonki zaki iya
tsere min ne? Ke da kina tunanin na barki? Wannan gurɓataccen tunanine bilkisa, na
rantse miki yau saina amshi abinda ya kasance cikar burina dan bazan rasa komai a
dalilinki ba wannan gangan ne hhhhhhhhhh!!!!!!!!.
Hannu nasa na toshe kunnuwana domin nisanta jina daga shaiɗaniyar
dariyarsa, na fashe da kuka ina jan jikina baya, “Kaji tsoron ALLAH bawan ALLAH,
koda kai aljanine na tabbata kasan akwai hisabi tsakaninmu ƴan adam da ku, minai
maka ne kakeson ganin bayana? Ka tunafa ni matar aurrece yanzun, dan ALLAH na
roƙeka karka wulaƙantani, ka barni da mutuncina.............”
“Kima daina ɓata yawun bakinki madam, babu wani roƙonki dazan taɓa saurara,
keɗin kaddarace mai girma a gareni, makullin cikar dukkanin burkana. Kinsan illa
nawa kikaimin ne?!!” yay ƙare maganar a tsawace da cafke wuyana ya shaƙe. A take
jikina ya fara rawa na fara ƙoƙarin fisgo numfashi cikin kakari. Hankaɗani yay na
bigi fuskar gadon. Azaba ta sakani fashewa da kuka na riƙe wuyana da duka hannu
biyu. Wani irin matsanancin fushine ya tasomin jin dariyar da yake sake ɓaɓɓakawa
yanzu ma, nace, “Ƙarya kake azzalumi, idan ka isa ka daina ɓoyemin kanka,
matsoracin banza da wofi kawai, Bazan sake roƙoka ka barni ba koda hakan na nufin
zakai nasara a kaina ɗin, sai dai na ɗauki alwashin in ALLAH ya yarda, inhar
ƙazamin jikinka ya kasance shine ƙaddarata, nima nice zan zama ƙaddarar mutuwarka,
dan da hannuna zan kasheka a ɗakin nan, a wannan daren la'ananne ALLAH fasiƙi
kawai!!!”.
“Hhhhhhh!!” ya shiga sake ɓaɓɓaka dariyarsa mara daɗin ji da tafa
hannayensa. Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki sauti hakan yasa na kasa fahimtar taka maimai
inda yake. “Da ƙyau Bilkisu, da ƙyau!, ashe kema kin fara koyon jarumtar mijin
naki?, nine zaki kashe, ni ni ninan kikejin zaki iya ki kashe.....?!!!” naji an
sake damƙar wuyana an shaƙe.
A take jikina ya fara rawa, nasa hannu na daki cikinsa cikin gushewar
hankali, dukda alamu sun nuna yaji zafi bai sakeni ba, sai ma dannani da yay baya
ya maƙureni jikin fuskar gadon ya haye kaina. “Zanyi abinda ya kawonin, ada nayi
niyyar barinki a raye tamkar sauran kicigaba da rayuwa kema, to amma tunda kince ke
tsagerace saina shayar dake gidauniyar azabar mutuwa, k har wacece? Nawa kike? Da
zaki zamewa rayuwata matsala.......”
Yanda naima Jazuga ne ya shiga dawomin a rai, duk da shaƙar da yaymin cikin
rahamar UBANGIJI na samu damar lalubar bed side drawer da naji a kusa da hannuna,
kofin da boss yasha ruwa ban fiddaba yana a kai na jiyo, ALLAH ya bani sa'a fisgosa
na ɗaga hannuna dake rawa da ƙyar na maka masa a gefen kunnensa. A take ya sakarmin
wuya yana huci na shigar zafi..... Kafin ya dawo hayyacinsa na caka masa sauran
kofin dake riƙe a hannun nawa, sai dai bansa a inane ba dan a kwai duhu a ɗakin har
yanzun. ƙara ya saki yana sake kaimin wawura sai dai na zille harma na dire a
gadon. Cafkoni yay cikin zafin nama ya maidoni baya kan gadon har saida nai ƙara
dan azaba nima. Na gallama hannunsa cizo tare da halbinsa da ƙafa cikin salon
trianing ɗin da muka samu duk da ba ganinsa nake ba. kokawa ce ta kaure a tsakanina
da shi dukda yafi ƙarfina nesa ba kusaba. Amma kasancewar akwai taimakon UBANGIJI
da kuma kowa yasan mata ALLAH kan bamu ƙarfi a irin wannan yanayin koda ace bazamu
iya ƙwatar kanmuba kuwa. Kokawa muke bil haƙƙi da gaskiya dukda nice keshan wahala
ban yarda ya kaini ƙasa ba. Cikin sa'a na kama ɗan yatsan hannunsa da yake neman
sake kaiwa wuyana na murɗesa da azabar ƙarfi nai baya dashi. Jikake ƙaraƙassss
ƙasss ƙasss ƙashin na bada sauti. Wahalalliyar ƙarar daya saki yay baya ta bani
damar jan hannuna baya nima, sai na saɓulo da zoben dake jikin yatsan.
A take Ɗakin ya ɗauki sautin wata murya mai ban tsoro da saka firgici, aka
shiga faman faɗin, “Barmata shine kuskure mafi girma, ka karɓa maza ka fita karka
tsaya akwai matsala!!”.
Wani irin ɗagowa yay a zabure ya fisgoni muka tafi ƙasa tare ya murɗe
hannuna da zoben ke a ciki zai ƙwace. Hakan yasa na shiga ambaton,
‫َح ْسُبَنا اللُه َوِنْع َم اْلَو ِكيُل‬.
Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel.
(ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro).
‫َالَّلُهَّم اْك ِفِنيِه ْم ِبَم ا ِش ْئَت‬.
Allahummak finihim bima shi'ita.
(Ya ALLAH! Ka isar mini su da abin da Ka so).
‫َالَّلُهَّم َال َس ْهَل ِإَّال َم ا َجَع ْلَتُه َس ْهًال َو َأْنَت َتْج َع ُل اْلَح ْز َن ِإَذ ا ِش ْئَت َس ْهًال‬.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta
sahlan.
(Ya ALLAH! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai
sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki).
Ƙarar da aka ƙwallah ta sakashi Hankaɗani kaina ya daki gadon, ya fita da
gudu, na fasa wani irin gigitaccen ihu jikina na ɗaukar wani irin rawa, a take
komai yay min ɗifff.......
Fasa ƙarar Bilkisu tai dai-dai da ƙarasowar Jay jikin ƙofar falon zai buɗe
dan isowarsa gidan kenan bayan yakai Ɓaleru ya ajiye a wani ɓoyayyen waje. cikin
zafin nama ya faɗa falon batare da ya rufe ƙofar ba. Ledar dake hannunsa ma sakinta
yay a falon. A gigice ya danna makunnar fitilar ɗakin ta kawo haske. Ya daka wani
uban tsalle sai gashi gaban Bilkisu data sume. Da ƙarfi ya ƙwala kiran sunanta
jikinsa na rawa dan har yanzu yana tattare da fushin ɓaleru ne, yay saurin maidata
ya kwantar jin kamar gudun mutum ta bayan Windown ɗakin. Fita yay da gudu yana
ƙwalama maigadi kira cikin matsanancin hargagi akan ya rufe masa gate. sosai
maigadi dahar ya shiga ɗakinsa zai kwanta ya fito a gigice shima jin wannan
mafaraucin kira, baƙaramin tashin hankali ya shigaba ganin yanda Jawaad yake nufosa
tamkar mahaukacin zakin dake a yunwace. Ɗaukesa Jay yay da mahaukacin mari, “Waye
ya shigomin gida? Ka gayamin wa kabama damar ya shigomin gida!!?”.
Maigadi daya gama ruɗewa da marin da yasha yace, “Wlhy oga babu wanda ya
shigo gidannan tunda ka fita, narantse maka babu wanda ya shig........” bai gama
saurarensaba ya bar wajen, ta bayan Windows ɗinsu ya nufa kasancewar akwai wuta ko
ina da haske. Take masa baya mai gadi yay da sauri shima dan bai fahimci abinda ke
faruwa ba. Jay yaja wani mahaukacin birki yana kallon tsanin dake tsaye jikin
katanga alamar koma wanene tanan ya shigo, kuma tanan ya fita. Naushi ya kaima
bango da azabar ƙarfi yana faɗin, “Noooo!!”. Da sauri maigadi dake cikin tsoro ya
riƙe masa hannu, “Oga dan ALLAH karka jima kanka ciwo”. Fisge hannunsa yayi dayin
wani Uban tsalle ya ɗane katangar cikin ƙwarewar training da suka samu batare da ya
kalli inda tsanin ya keba. Dirarsa can baya kawai maigadin yaji. “Na shiga uku ni
gambo, mike faruwa a gidan wai?” mai gadi ya faɗa hankali tashe.
Babu abinda Jay ya gani sai sayin takalmi kawai da wani tsanin a baya, wajen
siririyar hanyace data fita ɗoɗar har babban titi, hanyar tana taimakawa ƴan
anguwarne wajen fita titi basai sunbi ta titin layinba dake da nisa da babban titi,
ya dafe kansa dake wani irin masifar sara masa. Halin daya bar bilkisu a cikine ya
faɗo masa a rai. Ya fiddo wayarsa a aljihu ya shiga haske-haske harya zagaya ta
ƙofar gate yay knocking. Koda aka buɗe baiko kalli maigadi dake neman ƙarin bayani
ba ya nufi cikin gidan.
Yanda ya barta haka ya Koma ya sameta babu alamar numfashi tattare da ita.
Tsugunnawa yay gabanta ya Rungumota da ƙarfi cikin ƙirjinsa jikinsa na wani irin
tsuma na tsananin ɓacin rai, “Ubanwaye ya shigomin gida? Miyay miki?”. Yay maganar
cikin raunin murya da ɗaci, jijiyoyin kansa na miƙewa ruɗu-ruɗu, zafafan hawayene
ke kwarara a cikin zuciyarsa, a zahiri kam babu ko ɗigonsu sai idonsa daya kaɗa yay
jazur. Ɗagata yay gaba ɗayanta ya ɗaura a kujerar dake ɗakin guda ɗaya ƴar doguwa,
sai da ya gama bin ɗakin da kallo tsaf, ɗigon jini har a kan gadon ya gani, sai
fasashen glass aƙasa zuwa gadon dake a yamutse alamar ansha dabbe a kansa. Kauda
kansa yay yana rumtse ido da danne abinda ke yinƙuro masa tamkar zai faso ƙirjinsa
ya fito mai alaƙa da Masifaffen kishi, sauran ruwan daya bari dake yashe a ƙasa ya
ɗauka, a hannu ya zuba ya shafa mata a fuska. A take ta kawo wani nannauyan
numfashi tare da miƙewa zumbur cikin zafin nama tana faɗin, “Saina kasheka, bazan
barkaba yau, kasheka zanyi wlhy......” Saurin riƙe hannunta da take ƙoƙarin kaiwa
wuyansa yayi da ƙarfi ya mannata jikinsa yana faɗin, “Kwantar da hankalinki ki
nutsu nine”.
Ƙamshin turarensa da naji ya sakani fashewa da kuka na ƙanƙamesa, “Boss
shine, wlhy shine ke bibiyata tun a gidan Dad wai sai yamin fyaɗe, ya ɗau alwashin
saiya ketamin mutuncina, yace nice cikar burinsa, saiya yimin yanda yayma su Amina,
na shiga y......” ɗagota yay da sauri jikinsa na kakkarwa ya manne bakinsa da nata,
sam baya buƙatar ji, bayason yaji komai a yanzu, zuciyarsa zata iya tarwatsewa idan
ta cigaba da faɗa bazai iya ɗauka ba, yanada kishi mai tsanani akan dukkan abunda
ya kasance nasa. hawayen da tun ɗazun yake fatan yinsu sunƙi suka shiga silalo masa
a kumatu yanzun, yanda yake matan kawai zai baka tabbacin ba'a hayyacinsa yake ba.
Yaja kusan mintuna biyar yana kissing ɗinta, tun tana ƙoƙarin son ƙwacewa harta
nutsu ta miƙa wuya, dan ta kula da fushi yake sumbatarta. hawayensu ne masu ɗumi ke
sauka bisa fuskokin juna. Saida yaga tayi laƙwasa sannan ya zare bakinsa cikin nata
da sake rungumeta yana haɗiyar zuciya tamkar numfashinsa zaibar ƙirjinsa. Yanda
ƙirjinsa ke sama da ƙasa sosai ya firgita Bilkisu, sai dai tai luf a jikinsa tana
kuka dan dukkan abinda ya faru a waɗancan ranakun a yanzu tsaf suke dawo mata
tamkar yanzune komai ke faruwa. Ɗaukarta yay gaba ɗayanta ya nufa ɗakinsa da ita,
kai tsaye bayi ya zarce. Tanason tai magana sai dai babu fuska, dan haka ta nutsu
shiru tanata share hawaye da sauke ajiyar zuciya. Ruwa ya haɗa mai ɗumi sosai ya
nuna mata alamar tai wanka ya fice.
Binsa nai da kallo harya fice sannan na maida idona ga hannuna dake a rumtse,
zobene mai azabar ƙyau da ɗaukar ido dana samu zamewa hannun tsinannen nan. Na
maida hannun na rumtse ina cigaba da zubar da hawayen, mamaki nake a raina miyasa
wancan zuwan da yaymin a gidan Dad ban taɓa tunawabama balle na sanarma wani? Nida
sam bani da mantuwa amma gashi wannan ban taɓa tunawaba sai yau? Ko yaya akai hakan
ta faru?. Da wannan zoben rumtse cikin hannuna nai wankan, da gasa jikina kawai
nayi da ruwan daya haɗamin kafin nai amfani da sosonsa sama-sama dan wani irin
ƙyanƙyami da takaicin raɓar jikina da la'anannen can yayi nakeji.
Jay Ɗakinta ya sake komawa. Bai taɓa komaiba bayan kayan barci daya ɗauka
mata ya kashe fitar ya rufo ɗakin. Ledar daya yasar a fali ya ɗauka ya koma
ɗakinsa.
ina kammala wankan yana shigowa, nai saurin komawa na duƙe dan bankai ga
ɗaura towel ba, bai fasa shigowa cikin toilet ɗinba, sai dai kuma bani yake kallo
ba, bathrobe dake ajiye ya ɗauka ya juyo inda nake, kafaɗuna kawai naji ya kamo ya
miƙar dani, nai azamar rumtse idanuna dake cika da ƙwalla hannuna na naɗe a ƙirjina
gaba ɗaya, ban buɗeba harya gama sakamin ya ɗaure igiyar sannan ya kama hannuna
daga cikin bathtub ɗin ya fitar dani. Muryarsa a dakushe yace, “Yi alwala”. Juyawa
nai naɗan kallesa, ganin shima ni yake kallo nai saurin maida kaina ƙasa tare da
miƙa masa hannuna dake a dunƙule rumtse da zoben. A hankali ya tako inda nake ya
kama hannun ya buɗe, jin bai ɗaukaba baikuma yi maganaba yasa na kallesa. Zoben ya
kafe da idanu tamkar mai nazari, hakan ya bani damar ƙarema fuskrsa kallo dake a
matuƙar ɗauren da ban taɓa ganiba nima. Ya ɗago jajayen idanunsa masu tsananin saka
firgici ya kalleni. “Nashi ne?”. Kaina na ɗaga masa. Bai sake cewa komaiba ya ɗauke
zoben yana sake nunamin nayi alwala. Nima ɗin bance komanba na barsa tsaye yana
jujjuya zoben a hannunsa. Ina alwalar ya fita, babu jimawa ya dawo lokacin na
kammala, fita nai na barsa, sai yanzuma nake tunawa banyi sallar isha'i ba ashe
balle shafa'i da wutiri. Riga da hijjab dana gani a saman gadon na ɗauka na saka,
na ɗauki abin salla dake ɗakin na shinfiɗa na tada sallar isha'i na miƙe nai
shafa'i, bayan na idar na miƙe zan sake kawo shafa'i da wutiri na tsinkayi muryarsa
yana dakatar dani. Dukda nayi mamaki haka nabi umarninsa, wani abin sallar ya
shimfiɗa a gabana. Munyi salla raka'a biyu sannan mukai shafa'i da wutir. Juyowa
yay ya dafa goshina bayan mun idar, a fili ya shiga karanto addu'arnan ga mai sabon
aure,
‫ َو َش ِّر َم ا َج َبْلَتَها َع َلْيِه‬،‫ َو َأُعوُذ ِبَك ِم ْن َشِّرَها‬،‫ َو َخْيَر َم ا َجَبْلَتَها َع َلْي ِه‬،‫َالَّلُهَّم ِإِّني َأْس َأُلَك َخْيَر َها‬.
Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min
sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh.
(Ya ALLAH ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a
kansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a
kansa).
Ya saki goshin nawa ya juya tare da ɗaga hannu yay doguwar addu'ar da
banaji, dan haka nima nai tawa tareda yima iyayena addu'a da sauran musulmai baki
ɗaya.
Batare da yace dani komaiba ya miƙe, ficewa yay, babu jimawa sai gashi da
kofi a hannu da filet, ina a inda ya barni zaune nidai banko motsaba, ledar ya buɗe
ya juye gasashen naman rago daketa tashin ƙamshi saboda yanda aka sarrafashi cikin
filet ɗin, kofin kuma ya saka fresh milk a ciki. “Taso kici abinci” ya faɗa yana
zama akan sofa. Duk da bazan cinba ban musaba na tashi zuwa garesa jikina duk babu
ƙwari ga ciwo yanamin ta ko ina saboda damben da mukaci da azzalumin can, ƙasa naso
zama amma sai ya riƙoni na zauna kusa da shi, murya a sanyaye nace, “Naƙoshi, da
yamma mukaci abincin da Ummah ta aiko dashi da rana”. Baice dani komaiba ya miƙamin
fresh milk ɗin cikin kofin, amsa nai ita na kafa kai na shanye gaba ɗaya badan
tanamin daɗiba sai dan buƙatar samun sanyi a cikin ƙirjina da yaymin nauyi. Jikina
ko ina ciwo yay tsamu ga barci dama inaji. Amsar kofin yayi ya sake zubawa ya
miƙomin, kaina na girgiza masa cikin marairaicewa dan kar yace saina shaɗin tilas.
shanyewa yay ya miƙe ɗauke da filet ɗin naman da kofin. “Ga kaya nan ki canja ki
kwanta”. Kaina a ƙasa nace, “To”. Juyawa yay ya fita, harna kammala saka kayan bai
dawoba, na zauna bakin gadon ina ƙara tariyo abinda ya faru awanni biyu da suka
shuɗe tamkar film ko mafarki. Gittawar da akai ta gabana ya sakani saurin ɗagowa,
ganin shine sai na sauke ajiyar zuciya a hankali. Kwantawa nai da sauri ganin zai
cire jallabiyar jikinsa na juya masa baya. Kusan mintuna goma sannan ya hawo gadon
shima ya kwanta bayan ya kashe fitilar yabar ta gefen gadon kawai. na lumshe
idanuna hawayen da suka taru min na silalowa, ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nakeji
a raina da ruɗanin abinda ya hanani tuna waɗancan kwanakin da wannan shaiɗanin
yazomin. saukar tattausan hannunsa akan kumatuna ya sakani buɗe ido a hankali
kansa, fuskarsa gab take da tawa har muna shaƙar numfashin juna, dan akan filon
danake kwance ya ɗora kansa shima, idanunsa dake kallon fuskata ya lumshe a hankali
cikin salon lallashi yana mai sharemin hawayen da hannunsa dake akan fuskar tawa,
cikin muryar raɗa yace. “Miyasa baƙya gajiya da kuka?”. Wasu hawayen ne suka sake
silalo min, nace, “Na tsaneshi ne fiye da yanda kowa zai iya tunani”. Murmushi naji
yayi mai sauti, hakan yasa na buɗe idanuna ina kallonsa, kallona yake shima,,
“Kinsan minene?” kaina na girgiza masa alamar a'a, yace, “Na fiki tsanarsa Miema”.
Murmushin da ban niyya bane ya suɓuce min a bazata. Gani nai shima yay murmushin
idanunsa da suka rine jaa na wani irin ƙyalli kamar hawaye ya taru a cikinsu. nai
ƙoƙarin jan fuskata baya dan kusancinmu yayi yawa, sai yay saurin maidoni gab
fiyema da farko, yace, “Faɗamin miya faru? Kozan sami nutsuwa”. Hawayen ne suka
sake silalowa, na maida idanuna na lumshe inajin yanda yake murza yatsansa babba
saman fuskata, sauran huɗun kuwa kan gashina daga ƙeyya zuwa gefen kunne “A wani
daren daya shuɗe, wanda tunani ko hasashe bai sake dawo dashi ba gareni, ranar da
ya fara zuwa gareni.........................”.
Na ƙare faɗa masa dukkan abinda ya faru har zuwa yau da fashewa da kuka mai
cin rai, da ƙarfi ya jawoni jikinsa ya rungumeni tsam, jikinsa na wani irin rawar
ɓacin rai, nima saina sake fashewa da kukan, dan koba komai na fahimci shima
yanajin irin zafin da nakeji a cikin raina, nace, “Na rasa miyasa ban taɓa tunawa
ba sai yau?, Inason nasan ko wanene shi? Miyasa duk waɗanan kalaman nasa a kaina?
saina kasheshi, da hannuna zan kasheshi azzalummi maƙiyin ALLAH, sainai gunduwa
gunduw.........”
Jawaad daya saki murmushin takaici mai ciwo ya ɗagota daga jikinsa,
babban ɗan yatsansa da yake share mata hawaye ya ɗaura akan laɓɓanta da faɗin,
“Shiiii!!. kisa a ranki zaki sanshi, bana buƙatar sake ganin kukanki, Ni Jawaad
Abdul-aziz yusif insha ALLAHU zan gurfanar miki da shi a gabanki kan gwiyoyinsa,
abinda yake bibiyar kuma zan tabbatar masa da yafi ƙarfinsa har abada a wannan
daren”. Ya ƙare maganar da manna bakinsa saman nata batare da ya sake bata damar
magana ba. Duk da yana tausayinta bazai iya barintaba, wani irin shauƙi da zumuɗin
kasancewa da ita yakeji, ji yake tamkar ana ingiza zuciyarsane akanta, jiyake idan
bai kasance da itaba a wannan daren kamar zai rasa komai ciki harda ita kanta, tun
yana sarrafata da tunanin iya ƙaramin wasa ya barta har hakan yaji bazai yuwuba,
zuciyarsa ingizashi kawai take na kaiwa ga ƙololuwar martabarta................✍

😜Saura kuma naji wani yay gulmar Jay ehe😣🤐🤣🚶🏻.

Barkanmu da dawowa.

A ranar asabar an samu kuskuren ɗakko page daga telegram zuwa WhatsApp, wadda tayo
copy ɗinsa daga can bata ɗauka a jereba kamar yanda page ɗin yake, shiyyasa tallan
zafafa goma ya koma tsakkiyar page, wasu sai sukai tunanin ƙwai cikin ƙaya ake
talla wai. To ba haka baneba, dan ranar kam masu sai da zafafa goma saida kuka
tsiyayar musu da man kansu tas🤦🏻😑 saboda kira. Waɗanan buks ɗin goma namu sune nake
talla gasu ga mai buƙata dan karku bari a baku labari inhar kasan baka karantanba
dan duk sunyi lagwadar daɗi aradu🚴🏼👇🏾 .

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[1/5, 7:05 PM] HASNA ✍🏻
: Bilyn Abdull :
*TELEGRAM LINK ƊINMU*
https://t.me/joinchat/SBu4bmWd8skN4Zfr

WATTPAD

https://my.w.tt/TiR6HMHUNcb

Page 43

.....................A take salon wasan ya canja, bily da batai tunanin hakan daga
garesaba a wannan daren duk da dai yau jinta take wani sakayau kamar an sauke mata
kaya tuni jikinta ya fara tsuma, zuciyarta da jininta na wani irin tsitstsinkewa,
gashi ya hanata dukkan damar da zatai ƙorafi ko magiya, juyata yake duk yanda yaso
da zafafan salonsa masu rikita ƙwanya da zuciyar duk macen data mallakesa matsayin
mahaɗin rayuwarta, ta rumtse idanunta da ƙarfi lokacin da yake karanto___
‫ َو َج ِّنِب الَّش ْيَطاَن َم ا َر َز ْقَتَنا‬، ‫ِبْس ِم اللِه الّلُهَّم َج ِّنْبَنا الَّش ْيَطاَن‬.
Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.
(Da sunan ALLAH. Ya ALLAH! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka
nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi).
Ƙanƙamesa tai da sauri jikinta na wani irin rawa cikin gigitar data risketa
batare datayi hasashe ko shiyaryama zuwan wannan daren ba.
Abinda yay matuƙar birge Jay da mamakin matar tasa shine Jarumtar da bai
zatoba daga gareta, ko sau ɗaya batai yunƙurin hanashi yin yanda yaso da ita ba, ta
miƙa masa dukkan ragama baki ɗaya cike da juriya da dauriya da sadaukarwa, sai
saukar ɗumin hawayenta kawai yake ji da ajiyar zuciyarta tamkar zata shiɗe. (Uhumm)
baiji daga garetaba dangane da ɗaga murya balle akai ga kwakwazon da duniya zata
fahimci ana dai-dai wajen. duk yanda yaso yin juriya wajen binta a hankali shima
dan nuna tausayinta hakan ya gagara, komai ya ƙwace masa a lissafi itaɗin kawai
yake gani abu mafi daraja da martaba a garesa a wannan daren dama cikin duniyar
baki ɗayanta. Ƙaunarta da tausayinta na ratsa dukannin tsoka da ɓargon jikinsa da
jijiyoyi yana gaurayewa da jininsa, bashi da bakin musaltawa, bashi da kalaman
kwatantawa, bashi da ƙarfin shelantawa, abinda kawai ya sani shine itaɗin
tadabance, idan yace tadaban yana nufin tadaban har ƙarƙashin ruhinsa. Nutsuwar da
ya daɗe yana hasashenta a zahiri da mafarkinsa daga gareta yama riski fiye da
hakan.......
A zahiri Bilkisu ta hana kanta kuka mai sauti, amma wahala iya wahala
shanta take a hannun Jay, yanda kawai take fitar da numfashi ɗai-ɗai zai baka
tabbacin baije da wasaba. Hawaye kam ai wasu basa direwa wasu ke gangarowa. shi
kansa bai fahimci ya tafka ɓarnaba sai da komai ya lafa, Sosai tausayinta ya sake
mamayesa, taimakon gaggawa ya shiga bata ta kowace hanya data dace. Yanda take kuka
sosai sai hankalinsa ya sake tashi, amma haka ya daure ya gasa mata jiki dan yasan
shine babban gatan dazai mata a yanzun. Sai da ya tabbatar ta samu ƴar nutsuwa
sannan ya barta ta ƙarisa gyara jikinta shi kuma ya fito ya cire bedsheet ɗin da
duk yaɗan ɓaci, tunani yake anya kuwa baiji mata ciwo ba?....... Da sauri ya waiga
bayansa jin kukanta, zanin gadon daya fara jawowa ya saki ya nufeta dan bai zaton
zata fito ba, tarota yay jikinsa yana magana a hankali dan shi kansa muryarsa gaba
ɗaya ta wani dadushe kamar mai mura, “Miyasa zaki fito kinsan bazaki iya tafiya
ba?” Yay maganar yana kwantar da ita akan sofa.
Hawayen dake ziraromin na share, dan ni kaɗai nasan azabar da nakeji, babu
inda kemin daɗi a dukan jikina, dai-dai da bakina ɗaci yakemin sam babu ɗanɗano,
tausayin dukkan matan da aka kusancesu ta ƙarfin fyaɗe ya kuma mamayemin zuciya,
shiyyasa Amina ta koma kamar wata ƙaramar mahaukaciya a lokacin.......
“Ya isa haka kukan mana uhmyim, kinga jikinki harya ɗauki zafin zazzaɓi, ina
cewa matar tawa jarumace ashe raguwace?”. Haushi maganarsa ta bani, dan haka nasa
hannayena biyu ina kai masa ƙananun duka a ƙirji. Hannayen nawa ya riƙe yana
ƙaramar dariya, “Oh to yi haƙuri jarumace, giwar mata, bara na duba wajen nagani
bakiji ciwo ba”. Ƙanƙamesa nai ina sake fashewa da kuka, nace, “Ni dai a'a, banji
wani ciwoba”.
Jay yay murmushi kawai yana girgiza kansa, miƙewa yay ya ƙarisa cire zanin
gadon ya shimfiɗa wani, rigarsa mai ɗan kauri data kai mata har cinya ya saka mata,
yasa towel ya tsane mata kanta sosai gudun kar mura ta kamata, dama ga

jikinta yay mugun ɗaukar zafin zazzaɓi, tausayinta duk ya gallabi ransa, cak ya
ɗauketa dan harta fara barci ya maidata saman gadon ya kwantar, so yake tasha
magani amma baison tadata, dan haka ya ɗakko man zafi kawai ya shafa mata a jiki
kozataji ƴar nutsuwa.
Gaba ɗaya a hidimar Bilkisu Jawaad ya kusa cinye wannan dare, sai da ya
tabbatar komai yayi masa yanda yake buƙata sannan ya samu shima ya kwanta, wani
irin zafi yaji jikinta ya ɗauka, sai sauke ajiyar zuciya take a jajjere cikin
barci, fuskarta ya ƙurama idanu yana kallon yanda ta ɓata fuska alamar dai bata jin
daɗi har a cikin barcin. Yaɗan lumshe udanunsa ya sake buɗewa akan fuskarta yana
wani ɗan murmushi, ƴar yarinyar nan itace ta nema zautar masa da tunani, “UBANGIJI
mai hikima, UBANGIJI mai rahama da jinƙan bayinsa” yay maganar a fili tare da
sumbatar goshinta da laɓɓanta da sukai jazur sosai saboda wahalar da sukasha a
hannunsa. ‘Yanda take mai sanyi haka komanta yake mai sanyi’ ya ayyana a ransa yana
rungumeta tsam cikin jikinsa har saida ta motsa sannan ya sassauta mata. A haka
shima barci ɓarawo yay awon gaba dashi.

★★★★★★

DARE MAIBAN MAMAKI.


Dolene mutane masu yawan gaske su kira wannan dare da sunan dare maiban
mamaki da ruɗani tare da tashin hankali ga wasuma maybe. Dan kuwa lokacin da Jawaad
ke angwancewa a lokacin wasu cikin matsanancin ruɗani suke, dan duk wani azzalumi
dake da alaƙa da wani ɓoyayyan sirri daya shafi waɗanan ma'aurata da hikimar
UBANGIJI ta dunƙule waje guda wannan shine mafarkin da suka tsinci kansu a ciki a
wannan dare.
(Ƙudirar UBANGIJI ta tabbata, rahamarsa ta yalwata, izzar mulkinsa ta
Ƙaddara haɗewar jini dake cikin jinin da kuka salwantar, azzalumai lokaci yayi,
UBANGIJI ya ƙulla rugujewar zaluncinku ta inda bakuyi zato ko tsammani ba, wannan
ruɗanin shine nai muku hasashe, kuma gashi ALLAH ya tabbatar dashi, dama na faɗa
muku wannan shukar saita fito da izinin UBANGIJI tai yaɗon da zata zamewa rayukanku
barazana, nakuma tabbatar muku kafin kubar duniya sai kun wulaƙanta, duk wanda yaci
amana dolene amana ta cisa shima, gashi kuwa ALLAH ya tabbatar da hakan, ku fara
gudu maƙiya ALLAH, na ce ku fara gudu tun yanzu.......”
Dukkanin wanda keda alaƙa da wannan mummunan kalamai a cikin mafarkin a
wannan dare hankalinsa a tashe ya wayi gari, domin dai wata shukace da suka binne a
wasu shuɗaɗɗun shekaru take nuni da tayi tsiro da yaɗo harta saki ƴaƴa, suwaye
ƴaƴan? A ina suke? Tayaya aka samesu bayan irin da suka shuka sunada tabbacin basu
bar ko fure ajikin itaciyarsa ba, itaciyar kanta saida suka busar da ita balle ai
tunani tayi yaɗon ɗa? Mike shirin faruwa dasune? A ina kuskuren yake? Ya akai mai
gidauniya bai taɓa gano musu hakanba? Shima bai gani bane? Kokuwa ya gani ya ɓoye
musu?.

Lokacine zai basu wannan amasar damu kanmu masu bibiyar labarin😵.

★★★★★★★

Rashin yin barci da wuri ya sakasu makara da asuba, dan sanda Jawaad
ya farka wasu masallatan ma harsun kusa idar da salla, akan fuskar bily ya sauke
idanunsa dake cike da barci, ya sauke siririyar ajiyar zuciya tare da tashi zaune
da ita a jikinsa, idanu itama ta buɗe a hankali, sai dai suna haɗa ido tai saurin
maidawa ta rufe tana ɓata fuska. Murmushin da bai niyyaba ne ya suɓuce masa, a
zuciyarsa yake ayyana ‘sai shagwaɓan tsiya’ A fili kuwa sumbatar laɓɓanta yay,
cikin raɗa-raɗa yace, “Good morning my Heartbeat”. Saurin cusa kanta tayi cikin
ƙirjinsa. Iska ya hura mata cikin kunnenta yana murmushi, “Ko a ɗan ƙarane” yay
maganar yana ƙoƙarin cusa hannaunsa cikin rigarta. kukan taɓara ta sakar masa da
sauri jan jikinta baya. “Matsoraciya” ya faɗa yana sauka daga gadon gaba ɗaya.
Lamo nayi kwance zuciyata na tariyomin dukkan abinda ya wanzu a
daren na jiya daya tara abubuwa masu yawa a cikinsa, darene da zuciya bazata iya
mantashiba ta kowacce irin siga, dan yazo da abubuwa kala-kala a cikinsa. Har yanzu
jikina akwai zazzɓi, ga ciwon kai da bala'in ciwon jiki, babu inda bayamin ciwo a
jikin nan nawa wlhy. Ina jin motsin fitowarsa amma nakasa motsawa, tunanima nake
tayaya zanyi t

afiya ni balki........? Cak aka ɗagani sama, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke
ina ɓoye kaina a ƙirjinsa dan banaso ko ido mu haɗa, wata irin matsananciyar
kunyarsa nakeji fiye da da. jina kawai nai cikin ruwan zafi, hakan yasa na
ƙanƙamesa sosai. A cikin kunnena yace, “Sorry daure, kaɗan za'ayi”. Kaina na ɗaga
masa ina haɗiye kukan dake neman tahomin. Yanda ruwan yaɗanyi zafi sosai sai naji
daɗi dan har jikina ya gasamin gaba ɗaya dukda inata noƙewa, har aka gama
hannayena suna naɗe a ƙirjina. Saida ya bani towel na ɗaura sannan na samu nutsuwa
duk da dai shima bawani babba bane amma yafi dai babu. Matsowa yay zai ɗaukeni
bayan na kammala alwala. kaina a ƙasa cikin dakusashiyar muryata nace, “Zan iya
tafiya da kaina”. Baice komaiba ya ɗan matsa baya ya bani hanya. Cikin dauriya na
fara tafiya a hankali ina matse idanu, dan zafin nakeji, sai dai ba sosai dazai
cutarba, bakamar na daren jiya dana ringajin tamkar ana yayyankani da wuƙa ba.
Kallonta Jawaad yake cike da nazari harta fice, yanda take tafiyan batason
haɗa ƙafafunta sosai ya sakashi jin dolene ya dubata kodai ya jimata ciwon da
gaske?. bayanta yabi shima. taimaka mata yay ta saka doguwar riga da hijjab shima
ya saka jallabiya ya jasu jam'i duk da garima harya waye.

Bayan sun idar fita yay daga ɗakin, babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke
da madaidaicin kofi daketa fidda turiri. Kwance ya sameta a inda tai sallar ta
ƙudundune da hijjab, tea ɗin ya ajiye ya ɗakko magunguna ya ajiye sannan ya ɗagota
jikinsa harma ta fara barci, “Sorry, tashi kisha tea da magani saiki kwanta”.
Duk yanda na marairaice masa akan na ƙoshi bai saurareniba, sai da ya
tabbatar nashaye tas sannan ya bani maganin nasha. Da taimakonsa na koma saman
gado, harna fara lumshe idanu naji yana buɗemin jiki, sauri buɗe ido nayi da riƙe
masa hannunsa ina ɓata fuska, dan nazata ƙarawar zaice zaiyi. “Na shiga uku, dan
ALLAH kayi haƙuri, wlhy ka maimaita mutuwa zanyi”.
Dukda ta bashi tausayi saida yaji dariya na neman kufce masa, ya dai daure ya
haɗiye kayansa yana wani binta da kallon ƙasan ido, harta fara hawaye. Ɗauke idonsa
yay daga fuskarta batare da yace komaiba ya maida inda yake son ganin.Ya kuwa ji
mata ciwon da yay hasashe, sai dai bamai ɗaga hankali bane, amma zaiso a dubata
gudun kuskure, tsabar son ya tsokane saiya ranƙwafo kanta kamar da gaske abinda
take gudun zaiyi. jiyay kawai ta fashe masa da kuka jikinta ya fara rawa kamar
wadda ta hango dodo. Dole ya danne dariyar da keson ƙwace masa ya rungumta. “Wasa
nake miki niba ƙarawa zanba yi haƙuri”. Da ƙyar ya samu tai shiru har barci yay
awon gaba da ita saboda maganin daya bata yana saka barci, ga kuma dama bawani
isashen barci sukaiba. Sai da ya tabbatar barcinta yay nisa sannan ya gyara mata
kwanciya ya sauka daga gadon bayan ya lulluɓeta da bargo. Dukda shima barcin yake
buƙatar yi bai kwanta ba, wayarsa dake a drowan gefen gadon ya ɗauka ya fita falo.

10:30am

Ring ɗin wayarsa ne ya sakashi farkawa daga barcin daya ɗaukesa anan
falon bisa doguwar kujera, kwance yake a rubda ciki, hakan ya sakashi miƙa hannu
bisa centre table ɗin dake gab dashi ya lalubi wayar batare da ya buɗe idanunsa ba,
guntun tsaki yayi sannan ya buɗe idonun da ƙyar ya kalli wayar. Ganin Jabeer ne ya
sakashi ɗagawa yasa wayar a kunne, cikin muryar barci ya amsa masa sallama suka
gaisa. Daga can Jabeer ya sanya dariyar shaƙiyanci, “A lallai boss Mamin mu batazo
da wasaba, ka kalli agogo kuwa? Kaine da barcin safe har goma da rabi?”. Idanu Jay
ya lumshe ya sake buɗewa akan agogon falon, kafin yace, “Kai ka sani dai ɗan sa
ido” yay maganar yana tashi zaune da ƙyar. Dariya Jabeer yayi daga can, “Bari
nakira anjima, dama akan maganar da mukai dakai jiya ne”. Jawaad ya ɗan sauke
numfashi a hankali, “Karka damu gani nan zuwa station ɗinma”. Kafin Jabeer yace
wani abu ya yanke wayar.
Ɗakinsa ya nufa inda ya tarar bily na barcinta har yanzu, sai da yaje gareta
ya taɓa goshinta, zazzaɓin yaɗan sauka amma ba duka ba. Baice komaiba ya ƙarisa
bayi domin yin wanka.
Shiri yayi cikin ƙananun kaya da sukai mas

a ƙyau, yana fesa turare ya jiyo ana knocking turaren ya ajiye ya fita, yasan bazai
wuce Nabeelah ba, dan ya kira Ummah yace ta turo masa ita, Ilai kuwa itace ɗin
tsaye a bakin ƙofar, Nabeelah da Ummah ta sakata zuwa akan dole kawo breakfast taja
baya ganin Yah Jay ne ya buɗe ƙofar yau da kansa, saurin durƙusawa tai ƙasa tana
faɗin, “Yayanmu dan ALLAH kayi haƙuri, na tuba wlhy bazan sakeba, ranarma suɓutar
bakine”. Shi dai baice mata komaiba ya bata hanya ta shigo, juyawa yay ya koma
ɗakinsa. Ta sauke ajiyar zuciya da ƙarisa takowa cikin falon sosai, basket ɗin
hannunta ta ajiye saman centre table ta zauna tana waige-waigen ta inda Bilkisu
zata fito, zamanta babu jimawa ya fito daga ɗakin yana waya, basket ɗi data ajiye
ya yaye ɗan ƙyallen da aka rufo a kansa, kulolin ya buɗe duka, baice komaiba ya
zauna a kujera da faɗin, “Tashi Ki haɗa min coffee”.
Nabeelah da aka nutsu kamar ba itaba tace, “to” tana miƙewa, tasan wannan
ƙyaletan da yay ba yana nufin ya bartaba, akwai abinda yake shiryawa, Ummah ce
dukta jamata, tayi alƙawarin bazata bari su sake haɗuwaba har sai bayan wata biyu,
amma aunty Batool ita da Ummah yau suka zuga Abbah yace itace zata kawo breakfast.
Ummah bata wasa wa yaranta akan aikin gida da girki, duk taɓarar Nabeelah da shegen
surutu komai ta iya na mata, sai dai son jikin jaraba, wani lokacin sai Ummah tai
mata wuju-wuju akan aiki take tashi tayisa. Kitchen ta nufa ta haɗa masa coffee mai
daɗi kamar yanda tasan yanaso sannan ta kawo masa. Har yanzu wayar yakeyi, dan haka
yaymata nuni da abincin da hannu. Komawa ta sakeyi ta ɗakko filet tazo ta haɗa masa
abincin shima ta koma gefe ta zauna, tana son tambayar Bilkisu tana tsoron sake yin
laifi a garesa.
Abincinsa ya cigaba da ci yana wayar har zuwa wani lokaci, kafin ya ajiye
ya maida hankali ga cin abinci kaɗai. Ita dai tana zaune ne tanata satar kallonsa
da gulmarsa a zuciya harya kammala ya miƙe yana goge baki da tissue, yay magana
batare da ya kalleta ba. “ki tabbatar kin gyara gidan nan, idan kin tashi karki
nutsu kiyi da ƙyau kinji, ki kuma tasheta da rawar kankin nan kiga yanda zan sauya
miki kamanni”. Fuska Nabeelah ta kumbura tana faɗin, “ALLAH kuwa yayanmu ni yanzu
na daina rawar kai”. Juyawa yay ya zuba mata harara ya nufi hanyar fita, harya kama
handle ɗin ƙofar kuma sai ya juyo, “Idan ta tashi ki kirani”. “To yayanmu”.

Sadiq da tun ɗazun yazo gidan saboda kiran da Jawaad yay masa akan yazo
zasu fita, ya taso daga wajen maigadi da yake zaune suna hira ganin Jawaad ya fito,
sai da suka gaisa sannan ya buɗe masa ƙofar ya shiga ya zauna. Zagayawa yay shima
ya tada motar suka fice a gidan bayan sun gaisa da maigadi daya buɗe musu gate.
Duk da ba aikine ya kawosa office ɗinba saida ya shiga suka gaisa da Sir
Ahmad da yayta tsokanarsa. Office ɗinya ya buɗe ya shiga, komai tsaf babu wani
datti sai ƴar ƙurar da ba'a rasaba. Yana zama babu jimawa su Aliyu na shigowa.
Yanda suke wani binsa da kallon shaƙiyanci ya sakashi haɗe fuska yana
harararsu. “Malamai miye namin wannan kallon ƙurullar?”. Dariya duk suka sanya masa
hatta Aliyu da bai cika tsokana ba. Jabeer yace, “Kuji kama kaifa jama'a, waya ce
da kai wani abu anan dan ALLAH?”. Jay ya sake zuba masa harara yana ɗauke kansa,
“Ai nasan zakuce ɗinne musamman ma kai da babu abinda ka iya sai shegen gulma ko
mace ta shafa maka lafiya”. Yanzunma dai dariyar suka sanya suna cigaba da masa
sherin wai ƙyallin angwaci yake kamar wata ɗan daren sha biyar.
Shiru yay musu sukai sherinsu suka gama sannan suka zauna.
Hafiz ya maida dubansa ga Jay dake duba file ɗin da Jabeer ya basa, “Boss
wai mike faruwane haka? Gaba ɗaya mun kasa banbance komai tun daga yinin jiya har
safiyar yau ɗin nan? Gashi kuma kazo office bayan munsan kana hutu?”.
Jawaad ya ajiye takardun yana sauke nannauyan numfashi, miƙewa yay ya
ɗakko wani file a drawer bayansa, yana daga tsaye ya ranƙwafo ya dafe tebirinsa da
duka hannayensa, dara-daran idanunsa da tun daren jiya haskensu bai gama dawowa ba
ya zubamasu Aliyun, cikin ɗacin murya yace,“Hafiz nima wannan amsar n

ake nema, nakasa fahimtar komai, komai sake ruɗar dani yake da dilmiyani a kogin
ruɗani..... a daren jiya wani ya shigar min gida domin cutar da Miemaa, lokacin
inacan wajen kama ɓaleru”.
A tare suka ɗago suna kallonsa fuska cike da tashin hankali. Har haɗa baki
suke wajen tambayar baidai cutar da itaba ko?.
Kansa ya girgiza musu yana miƙewa tsaye sasai, “Babu abinda yay mata, sai
itacema ta jijji masa ciwo, ta faɗamin a bubuwa da yawa masu kamanceceniya da yanda
akaima matar Jabeer fyaɗe.
Jabeer yace, “Boss da gaske?”. Kansa ya sake jinjinawa kawai yana mai datse
haƙwaransa waje guda saboda azabar zafin da zuciyarsa ke masa.
Su duka ukun tsaye suka miƙe, suma cikin zafin ran da akan daɗe ba'aga Jabeer
da shi ba yace, “Boss anya ba Qaseem bane?”.
Kafeshi da idanu Jay yayi kafin ya janye yana wani ɗan murmushi mai ƙona
zuciya, “Jabeer! Ba Qaseem bane, a yanzu bashi nake zargiba sam, tako wace siga na
auna Qaseem bai hau mizanin bincikena ba, Idan har wanda nake zargi ya zama
shiɗinne da gaske to lallai ƙungiyace dasu, dan adaren jiyan Miemaa ta samu nasarar
cirar zobe daga hanun wanda ya shigo gidannan, kuma zoben tabbas na taɓa ganinsa a
hannun kusan mutum huɗu, abinda ya kuma ɗauremin kai basuda wata alaƙar zahiri dake
a bayyane su duka huɗun kuma”.
Aliyu ne yay ƙarfin halin cewa, “To boss indai basu da alaƙar zahiri
tayaya zamuyi tunanin haɗasu a kamanceceniyar laifi?”.
“Ƙyaƙyƙyawar tambaya Aliy” Jawaad ya faɗa yana fuskantarsa da ƙyau,
hannayensa duka biyu ya zura cikin aljihun wandon sa ya zagayo ya sake zama a
kujerarsa. suma duk komawa sukai suka zauna.
Jay ya ɗauki coffee ɗin da Hafiz ya ajiye masa yakai baki yana faɗin, “Akwai
kamanceceniya mai yawa Aliy, musamman idan muka saka abubuwa da yawa da suka faru a
tsakanin nan a mizani guda, babu abinda yafi ɗaukar hankalina wajen kamantasu sai
maganar fyaɗen nan, dan haka zamuyi amfani da wannan damar mu canja salon
bincikenmu. Fyaɗen da akaima Amina, Matar Jabeer, Nazifa, yayar Ummie, da ƴar mai
aikin gidansu Nazifa daya faru kwanannan duk basu da banbanci, a tunani na hankali
da yazo a zahirance zai bama mai nazari wahala wajen fahimta musamman daya kasance
ba'a guri ɗaya al'amarin ya faruba, hasalima ba lokaci gudaba, idan har zamuyi aki
da hankali kuma amsar ƙarshe itace ba mutum ɗaya ke aikatawa ba kenan. Da akwai
aikin dana shirya dunƙule yaran suyi da, dan a jiya harma na sakasu zuwa gidana
zamuyi magana sai ban koma gida akan lokaciba, to yanzu zamuyi amfani da wannan
damarne, saboda su abin ya faru da wasunsu, sunsan zafi da raɗaɗin da akeji”.
Cikin farin ciki Hafiz yace, “Wannan tsarin yayi wlhy Boss, amma nima ga
tawa shawaran”. Gaba ɗayansu hankalinsu suka maida ga Hafiz ɗin, ya gyara zamansa
sosai yanda zai faɗi komai dalla-dalla. “Kunsan a yanzu bazai yuwu kai tsaye mu iya
binciko waɗanda akaima fyaɗe irin nasu ba, fitowarma fili zaisa masu aikatawar su
ɗauki mataki suma, haka bayyanar yaran kai tsaye zai dawo da hankalin masu
aikatawar kansu”.
“Ƙwarai kuwa hakane Hafiz”.
“Yauwa to mizai hana mu taimakama yaran su buɗe wata ƙungiya haka ta ƙarɓar ƙorafin
waɗanda akaima fyaɗen koma a wane yanayine, matanmu su zama sune masu ƙungiyar a
bayyane, mukuma mu koma ta bayan fage wajen tsayawa tsayin daka ga masu shari'a su
ringa yanke hukuncin daya dace cikin ƙanƙanin lokaci, na tabbata hakan zaisa mu
sami dukkan damar da muke buƙata kodan sakacinma da kotuna keyi akan wannan
matsalar, kunga mun jefi tsuntsu biyu da dutse guda, zamu sami abinda muke buƙata,
zakuma mu taimaki yaran da ake zalinta musamman waɗanda iyayensu basu da ƙarfi akan
tsaya masu bayan an cutar musu da ƴaƴansu”.
Tafama Hafiz suka shigayi dan shawarar tashi tamusu yanda suke buƙata. A
take kuma suka tsara komai yanda ya kamata. Suna cikin tattaunawar su Zuhrah suka
iso office ɗin kamar yanda Jay yay kirasu tunkan ya baro gida akan su samesa nan.
Ummie ce tai musu jagora har office ɗin na Jay, Sai da suka gaishesu duk
cikin girmamawa kafin su basu izinin zama. Shine ya fara magana cikin dakewar nan
tasa da

kowa ya sani musamman akan abinda ya shafi aiki, “Inason ku bani dukkan hankalinku
nan”. A take duk suka sake nutsuwa garesa fiye ma da yanda yake buƙata.
“Ku dukanku a yanzu zaku kasance wajen aiki ɗayane, ina mai gargaɗarku da
bama buƙatar wasa, daga yau zaku ajiye wani ƙawancenku gefe kuyi aiki tamkar
bakusan kankuba, zaku fito a ƙungiyance domin karɓar kukan iyayen da akaima ƴaƴansu
fyaɗe. Wannan itace hanya ta farko da zaku iya fahimtar dukkan abinda kukai buri.
Sunan ƙungiyarku, lauyoyin da zasu taimaka muku, harma da alƙalai mun tanada, ku
naku kawai sauraren duk waɗanda matsalar ta shafa. Baku kaɗai bane a ƙungiyar,
akwai matan su Jabeer, dan irin matsalar data faru da ke Nazifa da sister ɗin Ummie
data rasu da Amina itace irin hanyar da akabi akaima matar Jabeer fyaɗe kafin
aurensu da wasu ƙawayenta biyu data sani”.
Duk kallonsa sukai cike da ɗunbin mamaki, Nazifa dake sharar hawaye tace,
“Yaya kuma suma ba'a gane wanda yay musunba har yanzun?”.
Cikin tsananin takaici Jay yace, “Ba'a ganeba, hasalima daga ƙarshe a lalace
shari'ar ta ƙare tunda babu wasu hujjoji da zasu tabbatar da wanda ya aikata ɗin.
Abinda yasa mukai tunanin kufito a ƙungiyancan dan bazai yuwu mu iya gane waɗanda
akaima irin wannan kalar fyaɗen ba saita siyasa, suma waɗanda akayima ɗin ta wasu
hanyoyi wasu rashin gata ya sakasu sunyi shiru, wasu kuwa sakacin shari'a yasaka
zancen wucewa tamkar ba'ayiba. Ku jami'an tsarone shiyyasa muke fatan ƙungiyar da
zata fito daga ƙarƙashinku ta banbanta da sauran ƙungiyoyin, mukuma zamu tsaya a
bayanku mu baku dukkan gudunmawa ta ɓangaren shari'a dan acanne ake ruguza komi da
make ƙwarin gwiwar ƙungiyoyin dake faɗi tashi akan wannan matsalar. Dan haka
aikinku zai kasance da manufa biyu....”
Kasancewar hakan burinsune sai duk suka amsa cike da farin ciki da
zumuɗi.
A nutse Jay ya ƙarayi musu bayani suma su Aliyu suka ƙara musu da nasu.

★★★★★★★

Ring ɗin wayatane yasa na farka, na buɗe idanuna da ƙyar ina tashi
zaune, saman mirror ɗinsa na hango wayar, dan haka na sauka a kan gadon ina cije
baki, duk da Alhmdllh naji daɗin jikina bakamar a daren jiya ba da ɗazun da safe,
ganin Ummu ce da kanta tai kirana na ɗan zaro ido waje na ɗauki wayar da har ta
katse, ina ƙoƙarin kiranta kiran ya ƙara shigowa, cikin ladabi na ɗaga tamkar ina a
gabanta na gaisheta Ina hawaye.
Daga can gimbiya tai murmushi tana gyara kishingiɗar da tayi jikin mai
martaba, “Haba ɗiyata, miye kuma abin kukan, baki da lafiyane naji muryarki haka?
Ayi haƙuri to, shiyyasa naƙi kiranki ai sai yau, duk kuna lafiya ko?”. Kaina na
ɗaga tamkar ina gabanta nace, “Lafiya lau Ummu, barci na tashi ne, sai kaina dake
ciwo kaɗan, inasu Safah? Tun jiya naketa zuba idon zuwansu amma shiru”. “kisha
magani to, ALLAH ya ƙara sauƙi, Karki damu zasuzo insha ALLAHU, yanzuma na kirakine
akan zuwansu Anuwar anjima kaɗan dan zasu wuce gobe idan ALLAH ya kaimu”. Cikin jin
daɗi na share hawayena Ina faɗin, “ALLAH ya kawosu lafiya Ummu, to suzonan su kwana
dan ALLAH”. “A'a babu batun kwana ɗiyata, ai ba'a kwana gidan amarya, zasuzo dai
zuwa dare su dawo, ki tabbatar mijinki da Anuwar sun haɗu dan munyi waya dashi
ɗazun yace baya gida”. “Insha ALLAHU Ummu zanyi ƙoƙari”. “To shikenan, sai anjima
na kiraki kinji, kidage da shiga ruwan zafi karkiyi son jiki”. Kunyace ta kamani, a
raina ina tunanin kodai shine ya sanar mata..... “Kina jina” magarta ta maidoni
hankalina. “Eh Ummu”. “Bawai ina nufin ki shiga ruwan zafi idan babu abinda ya faru
ba, tunda nasan kina fashin salla, bakuma saina buɗe miki abinda nake nufiba, ayita
haƙuri danshi zaman aure haƙurine, allah yay miki albarka”. Hawayena na share nace,
“Amin Ummu nagode”.
Rashin ganinsa a ɗakin ya sakani jin daɗi bayan na ajiye wayar, cikin
dauriya na gyara ɗakin tsaf, na fito ɗaukar kayan shara naga Nabeelah, sosai naji
daɗin ganin nata, itace tace nabar sharar ita zatayi, ban musa mataba na shiga nai
wanka da sake gasa jikina sosai, hakan ba karamin nutsuwa ya ƙaraminba. Koda na
fito saina koma ɗakina nai shiri, ina cikin shirin Nabeel

ah ta kawomin abinci, dan tunda taga yanayina ta tambayeni lafiya nace mata banida
lafiya duk sai naga jikinta yayi sanyi. Yunwa nakeji sosai shiyyasa na zauna naci
abincin. ɗakinsa na sake komawa ɗaukar maganin dan naji daɗinsa, ina buɗe box ɗinne
Nabeelah ta shigo da sallama da waya a hannu, a kunne kawai ta sakamin batare da
tayi maganaba. Ɗagowa nai zan tambayeta wanene? Muryarsa ta shiga dodon kunnena.
Saida na lumshe idanu na buɗe sannan na amsa masa sallamar tasa,
“Amarsu kin tashi?”. Ya faɗa cikin zolaya.
Jinai tamkar na nutse dan kunya, dukda bana gabansa, nai saurin saka hannuna
na rufe fuskata ina murmushi da faɗin, “Nidai ALLAH a'a”. Ina jiyo sautin
murmushinsa shima, yace, “Nidai nasan amaryata amaryace ƴar gaske, yaya jikin
naki?”. Batare dana buɗe fuskarba nace, “Da sauƙi”. “Alhmdllh ai haka akeso, kinci
abinci ko?”.
“Uhm naci”.
“Tom kisha magani ki sake kwanciya ki huta karki biyema surutun Nabeelah, Gimbiya
ta kirani akan baƙi zasuzo kuyi sallama, zanyi ƙoƙari na dawo da wuri nima insha
ALLAH. ga Sadiq nan zai kawo cefane Nabeelah tayi girki”.
“ALLAH ya dawo dakai lafiya to”.
“To nagode, amma mizan ɗan samune Noor-Jahan?”. A marairaice nace, “Mi kake so?”.
yace, “Komai aka bani inaso mana”. Duk da ina tsananin jin kunya nace, “To rufe
idonka”. “Na rufe ruf Matar Jay”. Yay maganar cikin sanyin murya kamar ba shiba.
da saurin na yanke kiran ina dariya, ina gani ya sake kira naƙi ɗagawa, saima
maganin na ɗauka na fita falo wajen Nabeelah.
Babu jimawa da zamanmu Sadiq ya kawo cefanan da yace, karon farko da zan
fara girki a gidana dukda Nabeelah tace na barmata zatayi kar yazo ya gani yay
faɗa, ban sauraretaba dan nima inason ƙarfafa jikina ai. Tare mukai girkin cikin
nutsuwa da salon da Umm-Anum ta sake koyar dani, dan danan gidan ya kaure da
ƙamshi, muka kammala tsaf muka gyara kitchen ɗin sannan.
Kusan ƙarfe uku na rana saiga su Anum, Anuwar, Abdul-Rahman, Abdur-raheem,
Ameen, Meenal, Amaturrahman, Amatullah. Tuni muka rungume juna dasu Amaturrahman
kamar mun shekara da rabuwa, su dai su Abdur-raheem dariya suketa mana.............

Inacan ina muku dogon page, kunanan kuna ƙwalama sunana kira😣😫, ku baku ganeba ne,
duk randa nai posting da wuri to nayi typing ɗin dare ne ya kwana, idan kuma ban
samu damar yiba dole sai randa zan tura nakeyi, ga aikin gida ga uzurorin rayuwa🤦🏻
😓, gashi yanzu anzo gangara typing ɗin na buƙatar nutsuwata sosai, amma idan naga
wani Comments ɗin har mamakin mai rubutashi nakeyi wlhy. ALLAH dai ya dafa mana
kawai, duk ƙoƙarinka baka isa yima kowa yanda ya dace ba, ALLAH kaɗai ka iyama ɗan
adam da halinsa wlhy😂🚶🏻🚴🏼.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[1/6, 9:21 PM] HASNA ✍🏻
: Bilyn Abdull :
Page 44
Auntyn Alfindiki saƙonki ya iso gareni, alkairin ALLAH ya kai gareki a duk duniyar
da kike, kema ALLAH ya tabbatar da addu'arnan da kikaimin a gareki, yanda kika soni
domin ALLAH, kema ina roƙon ALLAH ya soki haka dear.
Godiya irin trillions dinan 😍😍😍😘😘😘😘

....................Duk yanda zan musalta muku kalar daɗin da naji na zuwansu


bazaku fahimtaba, irina da suke gararanbar rayuwane kawai zasu fahimci kalar jin
daɗin da mukanji idan mutane irin haka da baka haɗa komai da suba suna nuna maka
soyayyar da naka dangin basa nuna maka irinta, abinda ya ƙarama farin cikin nawa
armashi kuwa ganin harda matasan samarin ƴaƴan sarki masu zamani da lokacinsu a
cikin gidana, kuma sun sake dani tamkar jininsu kona rayu a cikinsu ne. Abdul-
raheem ne dai baida yawan fara'a da magana, amma shima bashi da wulaƙanci. Abincin
kuma da aka jera musu zama sukai sukaci sosai har ana santi, Abdur-Rahaman harda
cewa dama yunwarsa ya tara dan yazo yaci girkin amarya. Amaturrahman ta ɗauki filo
ta saka masa waiji wai santi yakeyi. Nan take faɗa ya kaure tsakaninsu, ni wlhy
dariyama suka bani, idan kana tare da triple ɗin Ummu dolene drama ɗinsu take baka
dariya, shi Abdul-raheem baya magana, amma idan ya mulmulo baƙar magana ɗaya sai
tayi kamar ta kar mutum dan takaici, shikuma Abdur-raham babu haƙuri saiya rama,
Amaturrahman kuma zuga. Gefe kuma Ameenullah da Meenal ma cashewa akeyi, hakama
Anum da Anuwar. Wannan caskalen nasu ne ya sake ƙara armashin hirar tamu da nishaɗi
sosai. Kiran sallar la'asar ya saka samarin fita salla, mukuma mukayi a gida.

★★★★★★

Ana idar da sallar la'asar Jawaad ya baro station, kai tsaye anguwar su
Hudah ya nufa, sadiq yay fakin dai-dai ƙofar gidansu Amina inda Jay ya bashi
umarnin tsayawa. Jay daketa rubuce-rubuce batare da ya ɗagoba yace, “Sadiq yimin
sallama a gidan nan”. “To Oga” Sadiq ya faɗa yana buɗe motar ya fita. Ƙofar gidan
su Amina ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama. Kusan mintuna uku Aminar ta fito sanye
da hijjab tana amsa masa. “Assalamu alikum. Malam lafiya kuwa?”. Amsa mata sallamar
Sadiq yayi, sannan ya nuna motar, “Dama oga ne yace aimasa sallama”. Cikin rashin
fahimta Amina tace, “Oga kuma? Wanene kuma oga?”. Batajira amsar Sadiq ba ta fito
zuwa motar, knocking glass ɗin tayi har sau uku, Jawaad da har yanzun hankalinsa na
akan rubuce-rubucensa ya saka hannu ya sauke glass ɗin batare da ya ɗagoba. Amina
taɗan zaro ido da ɗora hannunta saman baki, “Oh wlhy bansan kai bane Yaya Jawaad,
ina yini?”. Ɗagowa yay ya kalleta da amsa mata, duk da fuskar dai babu walwala bai
ɗaureta tamauba, “Mama na nan?”. Kanta ta jinjina masa, “Eh tana nan ka shigo”.
“Okey” ya faɗa yana maida kansa ga abinda yakeyi. Juyawa tayi ciki ita kuma domin
sanarma maman.
Sai da Jay yaja kusan mintuna huɗu sannan Sadiq ya buɗe masa motar ya fito.
yana fitowa Amina na leƙowa dan sunji shiru, itace tai masa iso har cikin gidan,
mama na zaune daga ƙofar ɗaki gefenta da tabarmar da aka shinfiɗa masa.
“Lale marhabin, yau angone a gidanmu?”. Ɗan murmushi Jawaad yay ya zauna a
tabarmar yana faɗin, “Ayi haƙuri Mama bamuzo mun muki ya gajiya ba”. “A'a nikam ku
riƙe ban gajiyar ku, dan an mana babban ya gajiya, ɗawainiya kan ɗawainiya Jawaad
baka gajiya? Anyi hidimar azumi akayi ta salla shekaranjiya kuma saiga saƙo, ALLAH
ya saka da alkairi ya jiƙan mahaifa kaji, ALLAH ya azurtaku da zuri'a tagari mai
albarka”. Kan Jay a ƙasa yana ɗan murmushi yace, ”Amin mama”. Amina ta ajiye masa
kunun ayar da sukayi ta sake gaishesa da tambayar Bilkisu.
Zama Jawaad ya gyara ya fuskanci mama sosai, “Mama wani taimako nazo
kimin Please”. “Inajinka Jawaad, ka faɗa kanka tsaye, inhar baifi ƙarfinaba zan
maka da izinin ALLAH”. “To nagode sosai Mama, nasan tun dawowar su Hudah ƙasarnan
kike aiki a gidansu bayan rasuwar mijinki, sannan kaf anguwarnan da ƴan gidan nan
suke mu'amularsu kawai, a zaman da kikai dasu nasan dolene zaki san abubuwa masu
yawa dangane dasu, musanman ma akan duk wani ma'aikaci da yake aiki a gidan”.
“Wannan gaskiyane Jawaad, dan mijina kansa kafin ya kwanta jiyyar ajali

Alhaji Ali ne ya koma masa kamar amini”. “Alhmdllh, inason sanin maigadin nan nasu
ke da shi waye ya riga wani fara aiki?”. “Ya rigani farawa, danshi tunma ana gina
gidan shine maigadinsa har aka gama suka tare”. “Okey, yanada mata ne?”. “Tunda
nake da shi ban taɓa ganin iyalinsa ba, sannan ban taɓa jin ance yau ya tafi ganin
gidaba, dan har tambayarsa nama taɓayi game da hakan lokacin inason bada wasu kaya
sai nake tuntuɓarsa ko yanada iyali na haɗasu ya kai musu?. Sai cayaymin ai suna
gida, daga wannan amsar ya shiriritar da zancenma gaba ɗaya. Nikuma ban sake
tuntuɓarsa game da suba gaskiya”. Shiru Jawaad yayi yana nazarin maganganun Mama,
kafin yaɗan huro iska da gyara zamansa. “Amma mama kin taɓa ganin wani abu dangane
dashi na rashin gaskiya haka”. “Gaskiya ban taɓa ganiba, saboda shifa mutumne ma da
baida yawan magana sam, kafin kaga firarsa da mutum tai tsawo akan daɗe, kodan ba
abokina hirar nawa bane oho”. “Kukun gidanfa, yakai shekara nawa shikuma yana aiki
dasu?”. “Shima tunda suka tare yake, a gidan na sanshi”. “Mai bayin fulawa fa?”.
“Eto shine dai kafin shi kusan mutum uku sukai aiki”. “Miyasa suka bari to? Ko ba'a
baku albashin daya dace ne?”. “Ai Jawaad idan ta yawan albashine babu wani mai aiki
da zaiso barin aiki gidan Alhaji Ali, zan iya rantse maka a cikin dubu irinsa dake
fita haƙƙin ma'aikacin gidansa da albashi mai tsoka sai an tona, sannan duk abinda
masu gida zasuci kaima mai aiki zakaci, wulaƙanci da rashin tarbiyyar ƴaƴansa ne
kawai matsalar ma'aikatan gidan, amma masu bayin fulawarnan da suka taɓa ajiye aiki
wlhy bansan dalilinsu ba, dan daina ganinsu kawai mukai mudai koma sallama basuyi
damuba”. “To amma baƙwa zaman mutuncine dasu har zasu ajiye aiki baku saniba?”.
“Sosai ake zaman mutunci wlhy, dan wanda na tararma a gidan idan kaga yanda ya
ɗaukeni tamkar uwa, amma daga zuwa ganin gida bamu sake ganinsaba sai wani mukaga
an kawo”. “Zan iya sanin garinsu su duka biyun?”. “To gaskiya anan gizo ke saƙar
dan na manta, amma zanyi ƙoƙari na tinano insha ALLAH”. “ALLAH ya bada iko to,
drivern su fa?”. “Shima basu taɓa canjawaba”. “Kafin ku wasu sun taɓa musu aiki
ne?”. “Akwai ƴammata biyu da suka fara musu aiki kafin mai gidana ya rasu mu fara”.
“Miyasa suka bari? Kodan an sameku?”. “Wannan bansaniba kam Jawaad, nidai kawai
nasan kafinmu wasu sunyi musu aiki, amma ai nasan kaima kasan duk waɗanan abubuwan
tunda kana zuwa gidan”. Murmushi Jawaad yayi, “Sanin dazan musu bazai kai na wanda
yake rayuwa dasu yini da kwana ba, Mama inason naji wani abu dangane da fyaɗen
Amina, tana ina?”. Mama tai ɗan murmushi, “Oh ni, yanzunan Bilkisu bazata haƙura da
maganarnanba? Abinda ya faru ya riga ya faru ai sai haƙuri kuma”. “Karki damu Mama,
binciken yanada amfani, dan inma ba'aiba haka za'a cigaba da wulaƙanta rayuwar yara
cike da zalunci, ita kanta Miemaa ɗin a zaman datai gidan anshayin farautar
rayuwarta akan hakan ai”. Cikin tsagwaron mamaki Mama tace, “Bilkisun?”. “Eh wlhy
Mama”. Mama tai sagade al'ajabi na neman kasheta, ta sauke nannauyan numfashi da
faɗin, “Bilkisu akwai zurfin cikin tsiya, koda wasa bata taɓa faɗiba wlhy. Saima
dagewa datai akan gano wanda yay ma Amina, to ALLAH ya ƙara tsarewa, tunda dai kuma
basuci galaba a kantaba ai Alhmdllh”. Ta ƙare maganar da ƙwala kiran Amina.
Amina ta fito daga ɗakin tana amsa mata. Gurin da Mama ta nuna mata ta zauna,
Jawaad ya kalleta da ƙyau. “Amina! Randa akai miki fyaɗe suwaye a cikin gidan
can?”. “Yaya daga maigadi sai kuku”. “Ina mutanen gidan sukaje?”. “Yah Qaseem da
Salman dai sun fita aiki, Momy kuma itada Aamilah ne suka fita, sannan Bilkisu tana
makaranta ita”. “Wanene ƙarshen fita a gidan?”. Shiru Amina tayi alamar nazari,
kafin tace, “Kamar Aamilah ce”. “Waye ya fara fita kuma?”. “Yah Qaseem”. “Waye ya
fara dawowa?”. “Momy da Aamilah nidai na farka na gani bayan na farfaɗo” “Toke dama
kina barcin rana a gidanne? Kokuwa a ranar kika fara?”. “Wani lokaci nakanyi idan
nasan Mama ta fita dan karna dawo gida ni kaɗai. Da yake akwai ɗakin masu aiki sai
nake shiga ciki na kwanta”. “Kafin ranar wani yataɓa miki maganar banza a gidan
ne?”. “A'a

babu wanda ya taɓa”. “Mikikaci ranar a gidan? Ina nufin Abinci ko abinsha?”. “Banci
komaiba bayan abincin safe, dana kammala aiki kuma saina zauna zanɗan huta, tunawa
da wani sauran lemo dana ganine lokacin da zan saka wasu a fridge yasa na miƙe na
ɗakkosa na shanye, daga haka ban sake sanin ina kaina yakeba sai farkawa nai na
ganni cikin mummunar ƙaddara ”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka. Shiru Jawaad
yay yana kallonta da nazarin maganarta. “Dama kina shan lemo a gidan kenan?”. “Eh
inasha Yaya, dan indai ɓangaren Abincine ba'ai mana shamaki da komai, abinda sukaci
muma shi mukeci babu hantara kuma ”. “Alamu sun nuna Dad baya gidan, lokacin
kwanakinsa nawa da tafiya?”. “Eh kamar dai zai kai kwana goma inaga”. “Da yaushe ya
dawo?”. “Kwana biyu dayin abun”. “Wane mataki ya ɗauka?”. “Da farko ya nuna
damuwarsa, har ya bada kuɗi a kaini asibiti, amma daga baya daya fahimci yaransa
ake zargi saima yayta faɗa ya kuma ja baya da al'amarin, yay mana korar kare da ƴan
sandan da Yaya Sule ya ɗakko dan bincike”. “ALLAH ya ƙyauta to, ai kinyi karatu
ko?”. “Eh nagama secondary school”. “Kin amshi result ɗinki? Kuma yayi ƙyau”. “Eh
Yaya, credit ɗina taƙwas”. “Masha ALLAH, ki shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Sadiq
zaizo ya kaiki wani waje, saiki tafi da takardun, jeki abinki”. Tashi amina tayi
tana masa godiya da addu'oin gamawa da rayuwa lafiya ta koma ɗaki.
Jay ya maida hankalinsa ga Mama, “Mama bara na wuce, zata iya yuwuwa kiga na
sake dawowa. nagode sosai”. “Babu komai wlhy Jawaad, ALLAH ya saka maka da alkairi,
bara kaga na ɗakko maka ɗanyar awara da nayi ɗazun da safe ka kaima ɗiyata dan tana
sonta sosai”. “To mama ALLAH ya saka da alkairi, ita Amina yaushe zataje mata ne?”.
Mama dake murmushi tace, “zuwa satin sama zatazo insha ALLAH, kusamu yanzu kuma ku
huce gajiya basai an dameku da hayaniya ba”. Murmushi kawai Jay yayi baice komaiba.

Koda Jay ya baro gidansu Amina family House ɗinsu ya nufa, yay ƙoƙarin
shishshiga ko ina ya gaishesu da musu godiyar hidima har wajen Mama Atika data
amsashi sama-sama, daga baya kuma ta koma lallashinsa akan ya saka ɗan-fir'auna ya
saki Shahudah kodan son da take masa ya maidata ɗakinta. Yana wannan murmushin nasa
na rainin hankali yace to zaiyi hakan tai musu addu'a. Daga haka ya baro sashen
nata ya leƙa yaga jikin Mama Badiyya da sai godiyar ALLAH kawai, zaman asibitin ne
anyi har angaji an maidota gida, amma kullum lkitanta na zuwa dubata, su Uncle
Sulaiman kuma tsaye suke akan al'amuranta basa wasa da ciwon mahaifiyar tasu da aka
rasa kansa. Daga nan ya shiga sashensa ya ɗauki wani akwati ya fito suka fice daga
gidan.
Hankalinsa kuma yay gida gaba ɗaya, duk da yaso zuwa ya duba ɓaleru sai
wani gefe na zuciyarsa yafi ƙwaɗaita masa wucewa gidan, koba komai yana da ƙyau
yaje yaga halin da ƴar mutane take ciki, ya kamatama ace yau a gidan ya yini ya
bata dukkan kulawa da tattali, amma muhimmancin aikin nan daya saka gaba dole ya
daure ya fito ɗin.
Bayan sun iso gidan Sadiq ne ya kwasar masa kayan ya bisa dasu a baya, suna
zuwa ƙofar falon ya amsa, duk da yasan suwaye sukazo gidan hakan bai hanashi jin
kishi ba saboda jin dariyar maza. Ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga falon da
sallama ciki-ciki. Su Abdul-Raheem duk suka amsa masa suna miƙewa tsaye domin
girmamawa a garesa, Ameen yazo ya amshi kayan hannunsa duk suna jera masa sannu da
zuwa banda Anuwar da tun shigowar Jay yay mutuwar tsaye, su kansu su Abdur-rahman
duk baki suka saki suna kallon Jawaad sai kuma su koma su kalli Anuwar dan yau suka
fara ganin Jay su. Jin yanda falon yay wani irin tsitt lokaci gudane ya saka Jawaad
da tun shigowarsa gabansa ke wata irin faɗuwa ɗagowa ya kallesu. Idonsa ƙyam ya
sauka akan Anuwar tamkar wanda magana ɗisu ya janyo. A take kansa ya shiga wata
irin juyawa tamkar mai ganin hajijiya. Amma kasancewarsa gwanin dakiya sai ya dake
ɗin ya kafe Anuwar kawai da kallo kamar zai haɗiyesa da idanun.
Anuwar da bazai iya jurewaba kansa ya riƙe da hannu biyu ya koma zaune
daɓar saman kujera. Cikin rawar jiki Anum ta ƙarasa gabansa tana faɗin, “Bana faɗa
makaba kace ƙ

arya nakeyi, kagani ko tamkar kai, Anuwar wlhy bari kaji yay bagana muryarku iri
ɗaya ne shima. Anuwar da ya kasa bama Anum amsa ya wani rinƙa fisgar numfashi da
ƙyar yana sake matse kansa cikin hannayensa yana jujjuyashi. “Anum kaina zai fashe,
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wash ALLAH kaina......”
Yanda yay maganar tamkar numfashinsa zai ɗauke baki ɗayane ya kuma
tadamana hankali mukai kansa mu duka. Duk yanda nake zumuɗin son ganin yanayin
dazasu shiga idan sun haɗu da juna sai hankalina ya tashi.
Ƙarar da Anum ta ƙwalla ce ta maido Jawaad da shima yake riƙe da kansa
hayacinsa yay kan Anuwar jiki na rawa. Karɓarsa yay daga cinyar Anum ya maidosa
jikinsa yana girgizashi. Sai dai ina numfashin Anuwar ya ɗauke ɗaf, Nabeelah da tun
zuwan su Anuwar ta shiga ruɗani hartai masa video cikin hikima batare da kowa ya
saniba ta matso tana faɗin, “Yayanmu a kawo ruwa ka zuba masa?”. Kansa kawai ya
jinjina mata yana cigaba da ɗan bubbuga fuskar Anuwar da girgizasa. Nabeelah na
kawo ruwar Abdul-raheem ya amsa, shine ya shafama Anuwar a fuska, wani irin
nannauyan numfashi ya sauke. Jawaad ma ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana lumshe
idanunsa ya buɗewa akan Anuwar da shima ya buɗe nasa a hankali, kallon juna suke
kallo irin na ruɗani da al'ajabi, basu da suke ganin kamainin nasu da junaba hatta
su Bilkisu al'amarin ya kuma ruɗar dasu, dan ita saima yanzun data gansu a waje
ɗaya ta sake tabbatar da hukuncin ubangiji, dai-dai da wani ɗan ɗigon baƙi dake gab
da kunnen Jay akwaishi a jikin Anuwar shima exactly yanda na Jawaad ɗin yake.......
Jawaad ya kwantar da Anuwar jikin Ameen a hankali ya miƙe yabar wajen dan
jikinsa wani irin tsuma yakeyi, idan kuma yay wasa shima hajijiyar zata iya
kwasarsa ne takai ƙasa kamar yanda taima Anuwar.

Ruwa na ɗauka da sauri nabi bayansa dan tafiya yake yana haɗa hanya, Zaune
na samesa a saman gado ya riƙe kansa da dukan hannayensa biyu, saurin ƙarasawa inda
yake nayi ina faɗin, “Boss lafiya?”. hannuna ya riƙo cikin nashi tare da fisgoni na
faɗa jikinsa, wata runguma data nema saka ƙirjina buɗewa yay min, ƙaramar ƙarar da
nai ta sakashi sassautamin, muduka muka shiga sauke numfashi, munkai tsahon mintuna
biyar a haka kafin ya miƙe dani zaune sosai a bakin gadon ya zauna tare da riƙo
hannuna ya zaunar dani a kusa da shi. “Wanene wannan Miemaa? A ina kika
sanshi?”. ƙasa nai da kaina dan gujema kallon daya kafeni da shi. saurin ɗago
fuskata yayi muna kallon juna sosai, “Please Miemaa ba batun kunya mukeba, ki
faɗamin wanene shi?”. “Bansan wanene shiba nima, sai dai nasan shiɗin ɗan Umm-Anum
dana zauna a wajen tane, mamarsa itace na zauna wajenta a saudiyya sati biyun nan”.
“Saudia?, kina nufin daga can yazo nan?”. “ƙwaraima kuwa harda ƙanwarsa ma Anum”.
Yace, “Innalillahi... mi hakan ke nufi? Wane irin kamannine wannan? Babu ta
indafa yaron nan baya kama dani Miemaa?”. “Irin wannan ruɗanin nima na shiga a
randa muka fara haɗuwa dasu, da yay magana wlhy nazata kaine, sai daga baya na iya
fahimtar ba haka baneba, amma boss kafin Mamah ta rasu bata haifa maka ƙani bane?”.
Yanda ya kafeni da idanunsa ya sakani yin ƙasa da nawa gabana na faɗuwa. Ya ɗora
duka hannayensa saman fuskata ya ɗago, “Bilkisu Mamata ba rasuwa tayiba”. Yay
maganar yana sakin fuskata ya miƙe zumbur yana girgiza kansa. saurin riƙo hannunsa
nayi nima ganin zai fita a ɗakin, “Miya faru?”. Saurin dawowa yay ya sake zama.
Muryarsa har sarƙewa take yace, “Inason ganin mamar yaran nan”. Bansan lokacin
danai wata zabura ba nima ina faɗin, “Ganinta ba matsala bane, amma dan ALLAH da
gaske kakeyi mama ba rasuwa tayi ba? To tana inane?”. Yanda nai masifar rikicewane
ya sakashi kamo hannuna ya maidani inda nake ya zaunar shima yana wani kafeni da
idanu fiye da ko yaushe, “Labarina mai tsahone, namiki alƙawarin a yau zakiji komai
daya shafi mijinki, dan kema a yanzu kin zama ɗaya daga cikin family na, kobabu
alaƙar jini a tsakaninmu ke matata ce, amma tabbas kamar yanda baba ƙaura ya faɗa
Ƙaddarata tana tare da taki”. Cike da mamakin kalamansa nake kallonsa, amma
fahimtar danai baya cikin hayyacin

sa, shiyyasa nai tunanin yana buƙatar yafara yin wanka yaci abinci sannan. nace,
“Kayi haƙuri to ka fara yin wanka kaci abinci sannan dan magriba na gab”. Baice
dani komaiba sai kallona da yakeyi har yanzun, hakan yasa na miƙe na shiga bayi.
Ruwan wanka na haɗa masa, inda na barsa anan nazo na sake samunsa. Sai dai yanzu
riƙe yake da kofi a hannu alamar yana shan ruwa. “Ga ruwan can?”. Idanunsa ya ɗago
ya kalleni da miƙomin hanunsa na haggu. Baya naja ina maƙe kafaɗa nace, “Kaje kayi
wanka bara na duba su Anuwar ɗin”. Muryarsa ƙasa-ƙasa yace, “Dama ɗazun kin
kashemin waya, yanzu kuma nace kizo zaki gudu, laifi biyu kenan nasan maganinki ai,
zaki biya bashinsune”.
Saida na kusa zuwa ƙofa sannan na juyo ina faɗin, “To nima idan na kiraka a
waya ka kashe shikenan ai ka rama ko?”. Miƙewa yay yana ɓalle maɓallan rigarsa, “Ai
nafi ƙarfin ramawa ta haka yarinya”. Tsayawa nai ina kallonsa fuskata a marairaice,
“To gani na dawo ai, amma dan ALLAH faɗamin ta yaya zaka rama? Nifa ɗazun wlhy
bansan mizan baka bane shiyyasa na kashe”. “Kin tabbatar?”. Kaina na ɗaga masa. Yay
murmushi kawai batare da ya sake cewa komaiba. Hakan yasa nace, “Naje dan ALLAH?
Kaga an barsu su kaɗai”. Kansa kawai ya ɗagamin. Nikam tuni nai waje. Mamakine ya
kamani ganin falon wayam, na leƙa ɗayan falon har zuwa ɗakina nanma babu kowa, a
rikice na fito harabar gidan saina iske babu motarsu, abinda ya sake ɗaure kaina
har Nabeelah babu itama. Dawowa nai ɗakinsa danna sanar masa saina iske harya shiga
wankan, da sauri na ɗauki wayarsa dan tawa babu kuɗi ciki na shiga laluben sunan
Ummu. Bugu biyu kuwa ta ɗaga tamkar dama jira take. Kafin tai magana nai sallama
dan karta ɗauka ko shine, ko gaisheta ban tsaya yiba nace, “Ummu.......” katseni
tai itama da faɗin nasan mizaki tambaya kwantar da hankalinki, Anuwar ne ya sake
suma shiyyasa nace su taho gida, yana da Asthma shiyyasa gashi basu taho dako
inhaler ɗinsa ba ma, sun faɗamin komai daya faru yanzu ina mijin naki shi?”. Ya
shiga wanka Ummu, ya kumace zai sanarmin da komai daya shafesa”. “Alhmdllh mu dama
wannan muke jira ai, saiki nutsu sosai ki fahimci komai yanda yake, ta hakane zamu
tabbatar da abinda yake gaskiya, sannan nasan zai iya cewa zai biyosu idan ya fito
yaji sun taho, karki faɗa masa Anuwar ɗin yana cikin wani haline, nafiso sai zuwa
da safe idan ALLAH ya kaimu inma zaizo ɗin kuzo tare”. “To Ummu insha ALLAHU zanyi
hakan, amma inaji a raina wlhy abinda muke zargin gaskiyane, dan yace mamarsa bata
rasuba”. “Da gaske?”. “Wlhy kuwa Ummu”. “To shikenan bara na barki karya fito”.
Ummu na yanke wayar kuwa na goge kiran na dawo ɗakin na ajiye masa wayarsa,
fita na sakeyi domin yin salla nima dan anata kira.

Koda Jawaad ya fito a gaggauce yay shiri ya fita massallaci, bai kawo komai a
ransa game da rashin ganinsuba a falon, yayi zaton sun tafi salla matan kuma sun
shige ciki, yanayin da yake ciki kuma ya saka bai kula da babu motarsu a harabar
gidanba.
Ana idar da salla gida ya nufo, dai-dai Bilkisu itama ta fito daga kicin tana
haɗa masa abinci a d/table. Tsayawa yay kawai yana kallonta daga cikin falon...
Jin idanu na yawo kaina ya sakani ɗagowa nima, cikin sanyin murya nace, “Ga
abinci”.
Ɗauke kansa yay daga gareni, ya tako zuwa dani ɗin yaja kujera ya zauna, “Su
suna ina?”. “Sun tafi”. Na faɗa ina ƙoƙarin zuba masa abincin, Da sauri ya ɗago ya
kalleni, “Bangane sun tafi ba, miyasa?”. “Takawane ya kira yace su koma gida
hakanan”.
“Aiko dolene na nabi bayansu dan zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason yima
yaronan tambayoyi”. Saurin zuwa nai gabansa murya a sanyaye nace, “Kayi haƙuri
zuwa safiya mana, nima akwai abubuwa da yawa dazan faɗa maka game dasu wanda tunda
naga kamaninka dasu naita samowa dama dan na kawosu gareka”. Murmushi yayi ya
jawoni kawai ya rungume a jikinsa batare da yace komaiba.............✍

Maganar gaskiya man kaina ya gama tsiyayewa antafi yajin aiki daga yau😓😫🚶🏻.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAF
✍🏻
[1/8, 9:27 AM] HASNA : Bilyn abdul ce
Page 45

Naga sakon ku da yawa akan jina shirun da kuka yi am very sorry hakan ta farune
saka makon wani uzuri nawa fatan zakuyi min hakuri na zaman jiran da na saka ku 🥰
Sun daukin wajen minti biyar a haka kafin a hankili ya raba jikin su yana jin wani
nutsuwa na daban yana sauka mishi a ilahirin jikinshi. Jan hannata ta yayi zuwa
dining zama yayi yana bude food plak din "me kyakkyawqn amaryar tawa ta tana da wa
boss din nata "? ya karashe maganar da sigar xolaya. Murmshi bily taye tare da
rufe fuskar ta da tafin hannun ta jin yanda yakira boss din da sigar yanda take
kira, "ai budewa zakayi kaga abin da ke ciki" ta fada a gajerce tare da tamke fuska
wa ita a dole zats kwaikwayi yanda yake magana, dariyar da beyi shirin yi bane ya
kubuce masa...

Nima ina nan ina tawa dariyar don nasan dole kun dage wai ku a dole kuna karanta
kwai cikin kaya to ku jira ita marubuciyar tazo ta muku ni nayi nan

Billyn abdul:
Page 44

Auntyn Alfindiki saƙonki ya iso gareni, alkairin ALLAH ya kai gareki a duk duniyar
da kike, kema ALLAH ya tabbatar da addu'arnan da kikaimin a gareki, yanda kika soni
domin ALLAH, kema ina roƙon ALLAH ya soki haka dear.
Godiya irin trillions dinan 😍😍😍😘😘😘😘

....................Duk yanda zan musalta muku kalar daɗin da naji na zuwansu


bazaku fahimtaba, irina da suke gararanbar rayuwane kawai zasu fahimci kalar jin
daɗin da mukanji idan mutane irin haka da baka haɗa komai da suba suna nuna maka
soyayyar da naka dangin basa nuna maka irinta, abinda ya ƙarama farin cikin nawa
armashi kuwa ganin harda matasan samarin ƴaƴan sarki masu zamani da lokacinsu a
cikin gidana, kuma sun sake dani tamkar jininsu kona rayu a cikinsu ne. Abdul-
raheem ne dai baida yawan fara'a da magana, amma shima bashi da wulaƙanci. Abincin
kuma da aka jera musu zama sukai sukaci sosai har ana santi, Abdur-Rahaman harda
cewa dama yunwarsa ya tara dan yazo yaci girkin amarya. Amaturrahman ta ɗauki filo
ta saka masa waiji wai santi yakeyi. Nan take faɗa ya kaure tsakaninsu, ni wlhy
dariyama suka bani, idan kana tare da triple ɗin Ummu dolene drama ɗinsu take baka
dariya, shi Abdul-raheem baya magana, amma idan ya mulmulo baƙar magana ɗaya sai
tayi kamar ta kar mutum dan takaici, shikuma Abdur-raham babu haƙuri saiya rama,
Amaturrahman kuma zuga. Gefe kuma Ameenullah da Meenal ma cashewa akeyi, hakama
Anum da Anuwar. Wannan caskalen nasu ne ya sake ƙara armashin hirar tamu da nishaɗi
sosai. Kiran sallar la'asar ya saka samarin fita salla, mukuma mukayi a gida.

★★★★★★

Ana idar da sallar la'asar Jawaad ya baro station, kai tsaye anguwar su
Hudah ya nufa, sadiq yay fakin dai-dai ƙofar gidansu Amina inda Jay ya bashi
umarnin tsayawa. Jay daketa rubuce-rubuce batare da ya ɗagoba yace, “Sadiq yimin
sallama a gidan nan”. “To Oga” Sadiq ya faɗa yana buɗe motar ya fita. Ƙofar gidan
su Amina ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama. Kusan mintuna uku Aminar ta fito sanye
da hijjab tana amsa masa. “Assalamu alikum. Malam lafiya kuwa?”. Amsa mata sallamar
Sadiq yayi, sannan ya nuna motar, “Dama oga ne yace aimasa sallama”. Cikin rashin
fahimta Amina tace, “Oga kuma? Wanene kuma oga?”. Batajira amsar Sadiq ba ta fito
zuwa motar, knocking glass ɗin tayi har sau uku, Jawaad da har yanzun hankalinsa na
akan rubuce-rubucensa ya saka hannu ya sauke glass ɗin batare da ya ɗagoba. Amina
taɗan zaro ido da ɗora hannunta saman baki, “Oh wlhy bansan kai bane Yaya Jawaad,
ina yini?”. Ɗagowa yay ya kalleta da amsa mata, duk da fuskar dai babu walwala bai
ɗaureta tamauba, “Mama na nan?”. Kanta ta jinjina masa, “Eh tana nan ka shigo”.
“Okey” ya faɗa yana maida kansa ga abinda yakeyi. Juyawa tayi ciki ita kuma domin
sanarma maman.
Sai da Jay yaja kusan mintuna huɗu sannan Sadiq ya buɗe masa motar ya fito.
yana fitowa Amina na leƙowa dan sunji shiru, itace tai masa iso har cikin gidan,
mama na zaune daga ƙofar ɗaki gefenta da tabarmar da aka shinfiɗa masa.
“Lale marhabin, yau angone a gidanmu?”. Ɗan murmushi Jawaad yay ya zauna a
tabarmar yana faɗin, “Ayi haƙuri Mama bamuzo mun muki ya gajiya ba”. “A'a nikam ku
riƙe ban gajiyar ku, dan an mana babban ya gajiya, ɗawainiya kan ɗawainiya Jawaad
baka gajiya? Anyi hidimar azumi akayi ta salla shekaranjiya kuma saiga saƙo, ALLAH
ya saka da alkairi ya jiƙan mahaifa kaji, ALLAH ya azurtaku da zuri'a tagari mai
albarka”. Kan Jay a ƙasa yana ɗan murmushi yace, ”Amin mama”. Amina ta ajiye masa
kunun ayar da sukayi ta sake gaishesa da tambayar Bilkisu.
Zama Jawaad ya gyara ya fuskanci mama sosai, “Mama wani taimako nazo
kimin Please”. “Inajinka Jawaad, ka faɗa kanka tsaye, inhar baifi ƙarfinaba zan
maka da izinin ALLAH”. “To nagode sosai Mama, nasan tun dawowar su Hudah ƙasarnan
kike aiki a gidansu bayan rasuwar mijinki, sannan kaf anguwarnan da ƴan gidan nan
suke mu'amularsu kawai, a zaman da kikai dasu nasan dolene zaki san abubuwa masu
yawa dangane dasu, musanman ma akan duk wani ma'aikaci da yake aiki a gidan”.
“Wannan gaskiyane Jawaad, dan mijina kansa kafin ya kwanta jiyyar ajali

Alhaji Ali ne ya koma masa kamar amini”. “Alhmdllh, inason sanin maigadin nan nasu
ke da shi waye ya riga wani fara aiki?”. “Ya rigani farawa, danshi tunma ana gina
gidan shine maigadinsa har aka gama suka tare”. “Okey, yanada mata ne?”. “Tunda
nake da shi ban taɓa ganin iyalinsa ba, sannan ban taɓa jin ance yau ya tafi ganin
gidaba, dan har tambayarsa nama taɓayi game da hakan lokacin inason bada wasu kaya
sai nake tuntuɓarsa ko yanada iyali na haɗasu ya kai musu?. Sai cayaymin ai suna
gida, daga wannan amsar ya shiriritar da zancenma gaba ɗaya. Nikuma ban sake
tuntuɓarsa game da suba gaskiya”. Shiru Jawaad yayi yana nazarin maganganun Mama,
kafin yaɗan huro iska da gyara zamansa. “Amma mama kin taɓa ganin wani abu dangane
dashi na rashin gaskiya haka”. “Gaskiya ban taɓa ganiba, saboda shifa mutumne ma da
baida yawan magana sam, kafin kaga firarsa da mutum tai tsawo akan daɗe, kodan ba
abokina hirar nawa bane oho”. “Kukun gidanfa, yakai shekara nawa shikuma yana aiki
dasu?”. “Shima tunda suka tare yake, a gidan na sanshi”. “Mai bayin fulawa fa?”.
“Eto shine dai kafin shi kusan mutum uku sukai aiki”. “Miyasa suka bari to? Ko ba'a
baku albashin daya dace ne?”. “Ai Jawaad idan ta yawan albashine babu wani mai aiki
da zaiso barin aiki gidan Alhaji Ali, zan iya rantse maka a cikin dubu irinsa dake
fita haƙƙin ma'aikacin gidansa da albashi mai tsoka sai an tona, sannan duk abinda
masu gida zasuci kaima mai aiki zakaci, wulaƙanci da rashin tarbiyyar ƴaƴansa ne
kawai matsalar ma'aikatan gidan, amma masu bayin fulawarnan da suka taɓa ajiye aiki
wlhy bansan dalilinsu ba, dan daina ganinsu kawai mukai mudai koma sallama basuyi
damuba”. “To amma baƙwa zaman mutuncine dasu har zasu ajiye aiki baku saniba?”.
“Sosai ake zaman mutunci wlhy, dan wanda na tararma a gidan idan kaga yanda ya
ɗaukeni tamkar uwa, amma daga zuwa ganin gida bamu sake ganinsaba sai wani mukaga
an kawo”. “Zan iya sanin garinsu su duka biyun?”. “To gaskiya anan gizo ke saƙar
dan na manta, amma zanyi ƙoƙari na tinano insha ALLAH”. “ALLAH ya bada iko to,
drivern su fa?”. “Shima basu taɓa canjawaba”. “Kafin ku wasu sun taɓa musu aiki
ne?”. “Akwai ƴammata biyu da suka fara musu aiki kafin mai gidana ya rasu mu fara”.
“Miyasa suka bari? Kodan an sameku?”. “Wannan bansaniba kam Jawaad, nidai kawai
nasan kafinmu wasu sunyi musu aiki, amma ai nasan kaima kasan duk waɗanan abubuwan
tunda kana zuwa gidan”. Murmushi Jawaad yayi, “Sanin dazan musu bazai kai na wanda
yake rayuwa dasu yini da kwana ba, Mama inason naji wani abu dangane da fyaɗen
Amina, tana ina?”. Mama tai ɗan murmushi, “Oh ni, yanzunan Bilkisu bazata haƙura da
maganarnanba? Abinda ya faru ya riga ya faru ai sai haƙuri kuma”. “Karki damu Mama,
binciken yanada amfani, dan inma ba'aiba haka za'a cigaba da wulaƙanta rayuwar yara
cike da zalunci, ita kanta Miemaa ɗin a zaman datai gidan anshayin farautar
rayuwarta akan hakan ai”. Cikin tsagwaron mamaki Mama tace, “Bilkisun?”. “Eh wlhy
Mama”. Mama tai sagade al'ajabi na neman kasheta, ta sauke nannauyan numfashi da
faɗin, “Bilkisu akwai zurfin cikin tsiya, koda wasa bata taɓa faɗiba wlhy. Saima
dagewa datai akan gano wanda yay ma Amina, to ALLAH ya ƙara tsarewa, tunda dai kuma
basuci galaba a kantaba ai Alhmdllh”. Ta ƙare maganar da ƙwala kiran Amina.
Amina ta fito daga ɗakin tana amsa mata. Gurin da Mama ta nuna mata ta zauna,
Jawaad ya kalleta da ƙyau. “Amina! Randa akai miki fyaɗe suwaye a cikin gidan
can?”. “Yaya daga maigadi sai kuku”. “Ina mutanen gidan sukaje?”. “Yah Qaseem da
Salman dai sun fita aiki, Momy kuma itada Aamilah ne suka fita, sannan Bilkisu tana
makaranta ita”. “Wanene ƙarshen fita a gidan?”. Shiru Amina tayi alamar nazari,
kafin tace, “Kamar Aamilah ce”. “Waye ya fara fita kuma?”. “Yah Qaseem”. “Waye ya
fara dawowa?”. “Momy da Aamilah nidai na farka na gani bayan na farfaɗo” “Toke dama
kina barcin rana a gidanne? Kokuwa a ranar kika fara?”. “Wani lokaci nakanyi idan
nasan Mama ta fita dan karna dawo gida ni kaɗai. Da yake akwai ɗakin masu aiki sai
nake shiga ciki na kwanta”. “Kafin ranar wani yataɓa miki maganar banza a gidan
ne?”. “A'a

babu wanda ya taɓa”. “Mikikaci ranar a gidan? Ina nufin Abinci ko abinsha?”. “Banci
komaiba bayan abincin safe, dana kammala aiki kuma saina zauna zanɗan huta, tunawa
da wani sauran lemo dana ganine lokacin da zan saka wasu a fridge yasa na miƙe na
ɗakkosa na shanye, daga haka ban sake sanin ina kaina yakeba sai farkawa nai na
ganni cikin mummunar ƙaddara ”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka. Shiru Jawaad
yay yana kallonta da nazarin maganarta. “Dama kina shan lemo a gidan kenan?”. “Eh
inasha Yaya, dan indai ɓangaren Abincine ba'ai mana shamaki da komai, abinda sukaci
muma shi mukeci babu hantara kuma ”. “Alamu sun nuna Dad baya gidan, lokacin
kwanakinsa nawa da tafiya?”. “Eh kamar dai zai kai kwana goma inaga”. “Da yaushe ya
dawo?”. “Kwana biyu dayin abun”. “Wane mataki ya ɗauka?”. “Da farko ya nuna
damuwarsa, har ya bada kuɗi a kaini asibiti, amma daga baya daya fahimci yaransa
ake zargi saima yayta faɗa ya kuma ja baya da al'amarin, yay mana korar kare da ƴan
sandan da Yaya Sule ya ɗakko dan bincike”. “ALLAH ya ƙyauta to, ai kinyi karatu
ko?”. “Eh nagama secondary school”. “Kin amshi result ɗinki? Kuma yayi ƙyau”. “Eh
Yaya, credit ɗina taƙwas”. “Masha ALLAH, ki shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Sadiq
zaizo ya kaiki wani waje, saiki tafi da takardun, jeki abinki”. Tashi amina tayi
tana masa godiya da addu'oin gamawa da rayuwa lafiya ta koma ɗaki.
Jay ya maida hankalinsa ga Mama, “Mama bara na wuce, zata iya yuwuwa kiga na
sake dawowa. nagode sosai”. “Babu komai wlhy Jawaad, ALLAH ya saka maka da alkairi,
bara kaga na ɗakko maka ɗanyar awara da nayi ɗazun da safe ka kaima ɗiyata dan tana
sonta sosai”. “To mama ALLAH ya saka da alkairi, ita Amina yaushe zataje mata ne?”.
Mama dake murmushi tace, “zuwa satin sama zatazo insha ALLAH, kusamu yanzu kuma ku
huce gajiya basai an dameku da hayaniya ba”. Murmushi kawai Jay yayi baice komaiba.

Koda Jay ya baro gidansu Amina family House ɗinsu ya nufa, yay ƙoƙarin
shishshiga ko ina ya gaishesu da musu godiyar hidima har wajen Mama Atika data
amsashi sama-sama, daga baya kuma ta koma lallashinsa akan ya saka ɗan-fir'auna ya
saki Shahudah kodan son da take masa ya maidata ɗakinta. Yana wannan murmushin nasa
na rainin hankali yace to zaiyi hakan tai musu addu'a. Daga haka ya baro sashen
nata ya leƙa yaga jikin Mama Badiyya da sai godiyar ALLAH kawai, zaman asibitin ne
anyi har angaji an maidota gida, amma kullum lkitanta na zuwa dubata, su Uncle
Sulaiman kuma tsaye suke akan al'amuranta basa wasa da ciwon mahaifiyar tasu da aka
rasa kansa. Daga nan ya shiga sashensa ya ɗauki wani akwati ya fito suka fice daga
gidan.
Hankalinsa kuma yay gida gaba ɗaya, duk da yaso zuwa ya duba ɓaleru sai
wani gefe na zuciyarsa yafi ƙwaɗaita masa wucewa gidan, koba komai yana da ƙyau
yaje yaga halin da ƴar mutane take ciki, ya kamatama ace yau a gidan ya yini ya
bata dukkan kulawa da tattali, amma muhimmancin aikin nan daya saka gaba dole ya
daure ya fito ɗin.
Bayan sun iso gidan Sadiq ne ya kwasar masa kayan ya bisa dasu a baya, suna
zuwa ƙofar falon ya amsa, duk da yasan suwaye sukazo gidan hakan bai hanashi jin
kishi ba saboda jin dariyar maza. Ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga falon da
sallama ciki-ciki. Su Abdul-Raheem duk suka amsa masa suna miƙewa tsaye domin
girmamawa a garesa, Ameen yazo ya amshi kayan hannunsa duk suna jera masa sannu da
zuwa banda Anuwar da tun shigowar Jay yay mutuwar tsaye, su kansu su Abdur-rahman
duk baki suka saki suna kallon Jawaad sai kuma su koma su kalli Anuwar dan yau suka
fara ganin Jay su. Jin yanda falon yay wani irin tsitt lokaci gudane ya saka Jawaad
da tun shigowarsa gabansa ke wata irin faɗuwa ɗagowa ya kallesu. Idonsa ƙyam ya
sauka akan Anuwar tamkar wanda magana ɗisu ya janyo. A take kansa ya shiga wata
irin juyawa tamkar mai ganin hajijiya. Amma kasancewarsa gwanin dakiya sai ya dake
ɗin ya kafe Anuwar kawai da kallo kamar zai haɗiyesa da idanun.
Anuwar da bazai iya jurewaba kansa ya riƙe da hannu biyu ya koma zaune
daɓar saman kujera. Cikin rawar jiki Anum ta ƙarasa gabansa tana faɗin, “Bana faɗa
makaba kace ƙ

arya nakeyi, kagani ko tamkar kai, Anuwar wlhy bari kaji yay bagana muryarku iri
ɗaya ne shima. Anuwar da ya kasa bama Anum amsa ya wani rinƙa fisgar numfashi da
ƙyar yana sake matse kansa cikin hannayensa yana jujjuyashi. “Anum kaina zai fashe,
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wash ALLAH kaina......”
Yanda yay maganar tamkar numfashinsa zai ɗauke baki ɗayane ya kuma
tadamana hankali mukai kansa mu duka. Duk yanda nake zumuɗin son ganin yanayin
dazasu shiga idan sun haɗu da juna sai hankalina ya tashi.
Ƙarar da Anum ta ƙwalla ce ta maido Jawaad da shima yake riƙe da kansa
hayacinsa yay kan Anuwar jiki na rawa. Karɓarsa yay daga cinyar Anum ya maidosa
jikinsa yana girgizashi. Sai dai ina numfashin Anuwar ya ɗauke ɗaf, Nabeelah da tun
zuwan su Anuwar ta shiga ruɗani hartai masa video cikin hikima batare da kowa ya
saniba ta matso tana faɗin, “Yayanmu a kawo ruwa ka zuba masa?”. Kansa kawai ya
jinjina mata yana cigaba da ɗan bubbuga fuskar Anuwar da girgizasa. Nabeelah na
kawo ruwar Abdul-raheem ya amsa, shine ya shafama Anuwar a fuska, wani irin
nannauyan numfashi ya sauke. Jawaad ma ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana lumshe
idanunsa ya buɗewa akan Anuwar da shima ya buɗe nasa a hankali, kallon juna suke
kallo irin na ruɗani da al'ajabi, basu da suke ganin kamainin nasu da junaba hatta
su Bilkisu al'amarin ya kuma ruɗar dasu, dan ita saima yanzun data gansu a waje
ɗaya ta sake tabbatar da hukuncin ubangiji, dai-dai da wani ɗan ɗigon baƙi dake gab
da kunnen Jay akwaishi a jikin Anuwar shima exactly yanda na Jawaad ɗin yake.......
Jawaad ya kwantar da Anuwar jikin Ameen a hankali ya miƙe yabar wajen dan
jikinsa wani irin tsuma yakeyi, idan kuma yay wasa shima hajijiyar zata iya
kwasarsa ne takai ƙasa kamar yanda taima Anuwar.

Ruwa na ɗauka da sauri nabi bayansa dan tafiya yake yana haɗa hanya, Zaune
na samesa a saman gado ya riƙe kansa da dukan hannayensa biyu, saurin ƙarasawa inda
yake nayi ina faɗin, “Boss lafiya?”. hannuna ya riƙo cikin nashi tare da fisgoni na
faɗa jikinsa, wata runguma data nema saka ƙirjina buɗewa yay min, ƙaramar ƙarar da
nai ta sakashi sassautamin, muduka muka shiga sauke numfashi, munkai tsahon mintuna
biyar a haka kafin ya miƙe dani zaune sosai a bakin gadon ya zauna tare da riƙo
hannuna ya zaunar dani a kusa da shi. “Wanene wannan Miemaa? A ina kika
sanshi?”. ƙasa nai da kaina dan gujema kallon daya kafeni da shi. saurin ɗago
fuskata yayi muna kallon juna sosai, “Please Miemaa ba batun kunya mukeba, ki
faɗamin wanene shi?”. “Bansan wanene shiba nima, sai dai nasan shiɗin ɗan Umm-Anum
dana zauna a wajen tane, mamarsa itace na zauna wajenta a saudiyya sati biyun nan”.
“Saudia?, kina nufin daga can yazo nan?”. “ƙwaraima kuwa harda ƙanwarsa ma Anum”.
Yace, “Innalillahi... mi hakan ke nufi? Wane irin kamannine wannan? Babu ta
indafa yaron nan baya kama dani Miemaa?”. “Irin wannan ruɗanin nima na shiga a
randa muka fara haɗuwa dasu, da yay magana wlhy nazata kaine, sai daga baya na iya
fahimtar ba haka baneba, amma boss kafin Mamah ta rasu bata haifa maka ƙani bane?”.
Yanda ya kafeni da idanunsa ya sakani yin ƙasa da nawa gabana na faɗuwa. Ya ɗora
duka hannayensa saman fuskata ya ɗago, “Bilkisu Mamata ba rasuwa tayiba”. Yay
maganar yana sakin fuskata ya miƙe zumbur yana girgiza kansa. saurin riƙo hannunsa
nayi nima ganin zai fita a ɗakin, “Miya faru?”. Saurin dawowa yay ya sake zama.
Muryarsa har sarƙewa take yace, “Inason ganin mamar yaran nan”. Bansan lokacin
danai wata zabura ba nima ina faɗin, “Ganinta ba matsala bane, amma dan ALLAH da
gaske kakeyi mama ba rasuwa tayi ba? To tana inane?”. Yanda nai masifar rikicewane
ya sakashi kamo hannuna ya maidani inda nake ya zaunar shima yana wani kafeni da
idanu fiye da ko yaushe, “Labarina mai tsahone, namiki alƙawarin a yau zakiji komai
daya shafi mijinki, dan kema a yanzu kin zama ɗaya daga cikin family na, kobabu
alaƙar jini a tsakaninmu ke matata ce, amma tabbas kamar yanda baba ƙaura ya faɗa
Ƙaddarata tana tare da taki”. Cike da mamakin kalamansa nake kallonsa, amma
fahimtar danai baya cikin hayyacin

sa, shiyyasa nai tunanin yana buƙatar yafara yin wanka yaci abinci sannan. nace,
“Kayi haƙuri to ka fara yin wanka kaci abinci sannan dan magriba na gab”. Baice
dani komaiba sai kallona da yakeyi har yanzun, hakan yasa na miƙe na shiga bayi.
Ruwan wanka na haɗa masa, inda na barsa anan nazo na sake samunsa. Sai dai yanzu
riƙe yake da kofi a hannu alamar yana shan ruwa. “Ga ruwan can?”. Idanunsa ya ɗago
ya kalleni da miƙomin hanunsa na haggu. Baya naja ina maƙe kafaɗa nace, “Kaje kayi
wanka bara na duba su Anuwar ɗin”. Muryarsa ƙasa-ƙasa yace, “Dama ɗazun kin
kashemin waya, yanzu kuma nace kizo zaki gudu, laifi biyu kenan nasan maganinki ai,
zaki biya bashinsune”.
Saida na kusa zuwa ƙofa sannan na juyo ina faɗin, “To nima idan na kiraka a
waya ka kashe shikenan ai ka rama ko?”. Miƙewa yay yana ɓalle maɓallan rigarsa, “Ai
nafi ƙarfin ramawa ta haka yarinya”. Tsayawa nai ina kallonsa fuskata a marairaice,
“To gani na dawo ai, amma dan ALLAH faɗamin ta yaya zaka rama? Nifa ɗazun wlhy
bansan mizan baka bane shiyyasa na kashe”. “Kin tabbatar?”. Kaina na ɗaga masa. Yay
murmushi kawai batare da ya sake cewa komaiba. Hakan yasa nace, “Naje dan ALLAH?
Kaga an barsu su kaɗai”. Kansa kawai ya ɗagamin. Nikam tuni nai waje. Mamakine ya
kamani ganin falon wayam, na leƙa ɗayan falon har zuwa ɗakina nanma babu kowa, a
rikice na fito harabar gidan saina iske babu motarsu, abinda ya sake ɗaure kaina
har Nabeelah babu itama. Dawowa nai ɗakinsa danna sanar masa saina iske harya shiga
wankan, da sauri na ɗauki wayarsa dan tawa babu kuɗi ciki na shiga laluben sunan
Ummu. Bugu biyu kuwa ta ɗaga tamkar dama jira take. Kafin tai magana nai sallama
dan karta ɗauka ko shine, ko gaisheta ban tsaya yiba nace, “Ummu.......” katseni
tai itama da faɗin nasan mizaki tambaya kwantar da hankalinki, Anuwar ne ya sake
suma shiyyasa nace su taho gida, yana da Asthma shiyyasa gashi basu taho dako
inhaler ɗinsa ba ma, sun faɗamin komai daya faru yanzu ina mijin naki shi?”. Ya
shiga wanka Ummu, ya kumace zai sanarmin da komai daya shafesa”. “Alhmdllh mu dama
wannan muke jira ai, saiki nutsu sosai ki fahimci komai yanda yake, ta hakane zamu
tabbatar da abinda yake gaskiya, sannan nasan zai iya cewa zai biyosu idan ya fito
yaji sun taho, karki faɗa masa Anuwar ɗin yana cikin wani haline, nafiso sai zuwa
da safe idan ALLAH ya kaimu inma zaizo ɗin kuzo tare”. “To Ummu insha ALLAHU zanyi
hakan, amma inaji a raina wlhy abinda muke zargin gaskiyane, dan yace mamarsa bata
rasuba”. “Da gaske?”. “Wlhy kuwa Ummu”. “To shikenan bara na barki karya fito”.
Ummu na yanke wayar kuwa na goge kiran na dawo ɗakin na ajiye masa wayarsa,
fita na sakeyi domin yin salla nima dan anata kira.

Koda Jawaad ya fito a gaggauce yay shiri ya fita massallaci, bai kawo komai a
ransa game da rashin ganinsuba a falon, yayi zaton sun tafi salla matan kuma sun
shige ciki, yanayin da yake ciki kuma ya saka bai kula da babu motarsu a harabar
gidanba.
Ana idar da salla gida ya nufo, dai-dai Bilkisu itama ta fito daga kicin tana
haɗa masa abinci a d/table. Tsayawa yay kawai yana kallonta daga cikin falon...
Jin idanu na yawo kaina ya sakani ɗagowa nima, cikin sanyin murya nace, “Ga
abinci”.
Ɗauke kansa yay daga gareni, ya tako zuwa dani ɗin yaja kujera ya zauna, “Su
suna ina?”. “Sun tafi”. Na faɗa ina ƙoƙarin zuba masa abincin, Da sauri ya ɗago ya
kalleni, “Bangane sun tafi ba, miyasa?”. “Takawane ya kira yace su koma gida
hakanan”.
“Aiko dolene na nabi bayansu dan zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason yima
yaronan tambayoyi”. Saurin zuwa nai gabansa murya a sanyaye nace, “Kayi haƙuri
zuwa safiya mana, nima akwai abubuwa da yawa dazan faɗa maka game dasu wanda tunda
naga kamaninka dasu naita samowa dama dan na kawosu gareka”. Murmushi yayi ya
jawoni kawai ya rungume a jikinsa batare da yace komaiba.............✍
Maganar gaskiya man kaina ya gama tsiyayewa antafi yajin aiki daga yau😓😫🚶🏻.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAF

SAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[1/11, 4:18 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:


Page 46

..................Tsaf muka kammala komai tare da shi, kiran sallar zuhur da


akayine ya sakashi fita ya barni ina ƙarasa sauran abubuwan. Nima a gurguje na
ƙarasa komai na fito yin sallar. Na idar kenan ina addu'a naji ana sallama, kafin
na miƙe na fita ganin wanene Nabeelah ta shigo ɗakin.
Murmushi mukaima juna, ta ƙaraso ta rungumeni tana faɗin “Amarsu ta ango mai
daɗin suna, bara na faɗa a hankali kar yauma nai suɓutar baki ya jini ya markaɗa”.
Dariya ta bani sosai, dan haka na shiga yi. “Hum ke dariyama abin ya baki, wlhy
kaɗan daga aikinsa yamin casar gyaɗa indai yayanmu ne. Ina fata baya nan?”. Toilet
na nuna mata da ahannu ina faɗin, “Yana ciki kuwa”. Sosai ta waro idanu waje da
faɗin, “Na shiga Uku dan ALLAH da gaske kikeyi?”. Yanda ta rikice ɗinne ya sakani
sakeyin murmushi, na ajiye abin sallar dana linke, “Wai ke kaɗai kikazo ne?”. “A'a
ni da su Ummah ne fa, suna falo”. Ban bata amsaba na fito batare dana cire hijjabin
ba.
Tunda na fito suka zubamin idanu har abin ya bani kunya, na ƙarasa inda suke
kaina a ƙasa, har ƙasa na durƙusa inai musu sannu da zuwa. Cikin fara'a suka
amsamin har suna haɗa baki wajan faɗin nazo garesu. A kunyace na kuma tashi naje
gabansu dab zan sake tsugunnawa Ummah babba ta riƙoni, tsakkiyarsu ta zaunar dani
tare da rungumeni jikinta tana sauke wani nannauyan numfashi daya bani mamaki
matuƙar gaya, itama Ummah ƙarama saita riƙo hannuna da faɗin, “ALLAH yaymiki
albarka kinji, lallai ƙaunar da muke miki da gaske ta wuce ta surukuta kawai”. Ban
fahimci zancen nataba nidai, na ɗago daɗan satar kallon Ummah babba da naga kamar
tana hawaye. Kaina na maida a ƙasa nace, “Bara na kawo muku ruwa”.
Ummah ƙarama da itama na ga tana share hawayen tace, “Bara mu fara yin salla
ɗiyata, dan ta riskemu a hanya saboda go-slow ɗin garin nan da baya ƙarewa”. Kaina
na jinjina musu tare da miƙewa nai musu jagora har cikin ɗakina. Sai da na saka
musu abin salla sannan na fito dan na basu waje suyi.
Kwance na iske Nabeelah na danna waya, na zauna kujerar dake kallonta,
“K bazakiyi sallarba madam?”. Wayar ta janye daga fuskarta tana tashi zaune, “Aini
shehi yamin”. Nace, “Okay to acigaba da gashi”. Dariya ta sanya tana ƙoƙarin komawa
ta kwanta, ni kuma na miƙe dan naje na shirya abincin a dining, harna miƙe na dawo
na sake zama. “Nabeelah niko kinga abinda na gani kuwa? Saifa naga kamar su Ummah
kuka sukai?”. Kallona tai tana murmushi, “Nima dai ba komai na saniba akai, amma
tabbas akwai wani abu da suka sani game dake wanda na lura shine dalilin kukan
nasu”. Babu shiri na koma na zauna a kujerar sosai ina faɗin, “Game dani kuma
Nabeelah?”. “Lah bafa wani abu mara ƙyau bane naga kamar kin ruɗe”. Ajiyar zuciya
naɗan sauke duk da bawai na gamsu da amsar tata bane, na sake miƙewa na nufi
kitchen. Abincin dana shirya a kuloli na fara fiddowa, ganin hakan Nabeelah ta taso
ta tayani muka shirya komai. Falon muka sake dawowa muka zauna, Nabeelah ta fara
zubamin surutu, nidai nawa murmushi ne, wani gurin kuma nakan jinjina wautarta
sosai. zamanmu baifi da mintuna goma ba su Ummah suka fito, miƙewa nai ina musu
sannu. Fuskokinsu ɗauke da murmushi suka amsamin suna zama. Ina fara zuba musu
ruwan dana ajiye ya shigo falon da sallama.
Tsokanarsa suka shigayi da faɗin ga ango ga ango. Yay murmushi mai
sauti cike da girmamawa yace, “Sannunku da zuwa Ummahs, har ina tunanin kiranku a
waya sai kuma na duba naga nama bar wayar a gida”.
Ummah ƙarama tace, “Wlhy Go-slow ne ya riƙemu Son, amma da tuni mun iso ai”.
Ledar hannunsa na amsa ina masa sannu murya ƙasa-ƙasa, ban jira amsarsaba ko
kallonsa nabar wajen.

Jay daya ɗan bita da kallo ya zauna yana amsa gaisuwar da Nabeelah ke masa,
kafin ya gaida iyayen nasa da keta tsokanarsa yayi ƙiba a kwana uku kacal. Shidai
murmushi kawai yake musu bai iya cewa komai.
Nabeelah data san halin kayanta kuwa tuni ta miƙe tabi bayan Bilkisu dake
kitchen tana wanke fruits ɗin daya shigo dashi. Tare suka ƙarasa suka fito.

Koda nazo na sanar musu cewar ga abinci sai Ummah babba ta hau faɗa akan
miyasa zan

fara girki, ai sai nayi sati biyu sannan. Murmushi nidai nakeyi kawai kaina a ƙasa,
shima dai banji yace wani abu ba. Sai da ta gama faɗanne sannan naji ya bata haƙuri
da cewar, “Ummah karki damu ai gara tayi, dan bazai yuwu muyita wahal dake ba”.
Ummah tace, “Minene wani abin wahala anan, aida nasan zatai girkin dana kira nace
karma ta fara”.
Shidai ya lallaɓasu akan suzo suci abinci, daga baya saita cigaba da
faɗan. Dariya Ummah ƙarama da Nabeelah sukayi jin furcinsa, nima dai saida na
murmusa. Ni da Nabeelah muka zuzzuba musu abincin yanda kowa yake buƙata, Nabeelah
ma ta zuba nata ta zauna, niko sai nai ƙoƙarin barin wajen, hannuna Ummah ta kamo
ta zaunar dani a kujerar kusa da ita, “Maza zauna kici abinci, kina nufin mu kaɗai
zakima wannan wahalar”. Kaina a ƙasa nace, “Ummah ai na ƙoshi, in ALLAH ya kaimu
anjima zanci”. Bata saurareni ba ta hau ɗiba da cokalinta ta fara bani, bazan iya
mata musu ba, dan haka dole na ringa amsa a kunyace, Nabeelah nata mana dariya
ƙasa-ƙasa dan tana tsoron yi yaci ƙaniyarta. Dana ɗago saina kamashi yana kallonmu,
hakan yasa na ƙara takura sosai. Ummah bata barniba saida ta tabbatar cikina yayi
ƙat da abincin nan, suma sukaci sosai suna santi da sakamin albarka da yaba ƙoƙari
na.
Bayan mun kammala Nabeelah ta tayani gyara wajen, shi kuma ya zagaya dasu
lungu da saƙo na gidan, inajin yanda suketa yaba gidan da jinjina halin girma irin
nasu Ummu, a yanda suka hidimtamin babu dangin iya babu na baba sun cancanci yabawa
mai girman gaske da ƙyaƙyƙyawar addu'a.

A falon Jawaad su Umma suka yada zango, inda suka shiga tattaunawa akan
batun Bilkisu da kuma kamannin Anuwar dana Jay. su Ummah sun dage akan cikin satin
nan zasuje saudia domin ganin Umm-Anum, dan sunce lallai sunaji a jikinsu kamaninsa
da Anuwar yafi ƙarfin kamanni, sunce zasu sanarma Alhaji babba dan su ɗunguma gaba
ɗaya su tafi.
Murmushi Jay yay yana gyara zama da fuskantar iyayen nasa. “Ummah banƙi ta
takuba kam, amma sai nake ganin kamar dai kubari na fara zuwa tukunna, dan kunga
bamu da tabbas hasashe kawai mukeyi, shima baba karmu sanar masa tukunna, yana a
shekarun da baya buƙatar irin wannan ruɗanin a halin yanzun, yanzu haka da kunga
yanda hankalinsa ke a tashe akan zancen Miemaa da zakusha mamaki, yana dannewane
kawai, to kunga abin zai haɗe masa biyu. Insha ALLAH zanje masarauta nima anjima
domin sakejin bayani dangane dasu yaran, duk da dai Miemaa tamin bayanin abubuwa da
dama game da mamansun”.
Duk sun gamsu da jawabinsa, sun kuma yi masa addu'ar fatan nasara, amma ita
Ummah babba ma tariga ta tabbatar musu da tanaji a ranta kamanin nan bazasu zama
kamanni na haka nanba, ita wlhy jima take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a saudia.
Shi dai Jay ya cigaba da lallaɓasu dan yanason abi komai a sannu kodan maganar
Bilkisu data sanar masa tana zargin akwai sihiri a cikin al'amarin.
Sun cigaba da tattanawa har zuwa la'asar, Jay ya fita salla su kuma sukai tasu
a gida. Ƙyaututtukan da duk suka kawoma Bilkisu duk suka bata, kafin suyi shirin
komawa.
Godiya naita musu dukda bansan mike a cikiba har sai da Ummah tace ya
isa haka nan, da ya dawo daga salla shima na sanar masa, shima dai godiyar yayi.
Har bakin mota nai musu rakkiya da bama fadila nima tsarabar dana haɗa
musu ta turaren wuta da fruits ɗin da basu sha ba sai kajin dana gasa guda uku na
naɗesu batare da shima ya sani ba. Sai da suka fice daga gidan sannan muka koma
cikin gida. Hannuna ya kama ya zaunar dani a kusa da shi yana faɗin, “Sannu da
ƙoƙari Miemaa, nagode sosai da yanda kika karrama ahalina”. Murmushi nai masa,
nace, “Nima ai ahalina ne yanzun, dan ƴan uwanka nawane, iyayena ne yazama dole a
gareni na girmamasu, dan haka ka dainamin godiya dan ALLAH”. Baice komaiba sai
jawoni da yay na haye saman jikinsa, ya sauke siririyar ajiyar zuciya yana lumshe
idanunsa. luf na kwanta nima ina shaƙar ƙamshinsa, gashi daman barci nakeji sosai,
ai tuni na fara lumshe idanu.
Ɗagoni yay yana kallon fuskata, ya saka hannunsa ya shafi kumatuna, “Badai
barciba ko?”. Buɗe idanun nawa nayi kaɗan na kallesa, g

anin ni yake kallo saina maidasu ƙasa da yunƙurin tashi daga jikin nasa, “ALLAH
barci nakeji”. Zamansa ya gyara sosai yana kallona, sai dai yaƙi cewa komai, jinai
idanun nasa sunmin yawa, dan haka nace, “Ko zaka ƙara cin abinci ne”. “Uhm, amma ba
wancan ba” ya faɗa yana nuna Dining. Da mamaki na kallesa sosai, “To wanne? Ko wani
za'a dafa maka?”. Hannuna ya kamo ya matso dani jikinsa sosai, a hankali kamar baya
son yin magana yace, “Zona faɗa miki wanda nake so”. Yay maganar yana ɗaura kansa
saman wuyana, yanda yake busan iskar numfashinsa a saman wuyan ya saka tsigar
jikina tashi, na cije bakina da haɗiye yawu da ƙyar, abinda ya gwargwaɗa min a
cikin kune ne ya sakani zabura naɗan kallesa, sai kawai na miƙe nabar wajen da ɗan
gudu.
Lumshe idanu Jay yay yana wani sassanyan murmushi, yabi hanyar falonta da
kallo yana sauke ajiyar zuciya, ganin idan ya cigaba da zama a gidan jikinsa zai
cigaba da mutuwa sai ya miƙe, ɗakinsa ya shiga, mintuna kusan goma ya fito ya nufi
nata.

Ina zaune a sofa ɗin dake ɗakin ina duba abinda su Ummah suka kawomin ya
shigo, ban yarda mun haɗa idoba nace, “Yayanmu kaga abinda su Ummah suka kawomin”.
Muryarsa a sanyaye yace, “Kin gode, ALLAH ya saka da alkairi”. Ɗagowa nai naɗan
kallesa na janye idanuna. “Baka da lafiya ne?”. “Mi kika gani?” ya faɗa yana ɗaukar
agogonsa dake kan mirror na. “Naji muryarka a sanyaye ne”.
Murmusa yayi ya miƙomin hannun da zaisa agogon, babu musu na fara ɗaura masa.
Harma na fidda rai ga samun amsa nikam, sai da na kammala ɗaura masanne ya ranƙwafo
tare da sumbatar laɓɓana, cikin ƙaramin sauti yace, “Bazaki ganeba Miemaa”. Idanuna
na ɗago na kallesa, ya ɗagemin gira ɗaya yana cije leɓensa na ƙasa. “Kimin addu'a
zan fita”. Duk da banason fitar haka na daure nai masa fatan alkairi da dawowa
lafiya, sake ranƙwafowa yay ya sumbaci laɓɓana da cewa “Amin” sannan ya fice.
Na sauke ajiyar zuciya da tattare kayan na maidasu inda suke sannan na miƙe,
gidan duk sai yamin babu daɗi, dan haka na saka silifas tare da hijjab na fito
harabar gidan dan inɗan rage kaɗaici, na ɗan zazzagaya ina tsinkar flowers ɗin da
aka ƙawata gidan dasu masu ƙamshi, sai gab da magriba na shige ciki, falonsa na
nufa kai tsaye domin tunawa da kofunan dasu Ummah sukasha lemo ban kwasosu ba, na
gama tattarewa zan fito idona ya sauka akan file daya ajiye a kan hannun kujera,
ajiye kofunan nai na ɗaukesa da nufin kaimasa ɗaki dan nasan mantashi yay anan.
Takardun dake ciki suka zubo ƙasa a mistake, ‘Ya salam’ na faɗa ina duƙawa na
tattaro su, ido na tsirama ɗaya daga cikin takardar domin ganin sunan Dad ɓaro-
ɓaro, mamaki yay matuƙar kamani, na koma na zauna a kujera ina dubawa daki-daki.
Kai nane ya nema kullewa, daga gefe kuma zuciyata najin wani irin takaicinsa,
waishi mutumin nan mi ya ke nufi da ƴan gidanmu ne? Na kula gaba ɗaya bayanan dake
a file ɗin akan ƴan gidanne, sunan Dad, mom da yah Qaseem yafi na kowa fitowa ma,
maidawa nai na dangwarar da file ɗin na ɗauka kofinan na fita ina ƙunƙuni, ko
wankesu ban tsaya yiba na ajiyesu a kicin ɗin na fito. Ɗakina na shiga raina duk
babu daɗi, Dad ya wuce duk yanda yake zato a gareni daga shi har zuri'arsa baki
ɗaya, Dad yaymin abinda sauran dangina suka gaza yimin, Dad ya tallafi maraicina a
lokacin da rayuwata ke walagigin ƙila wakala, ta sanadin gatan da Dad yay minne har
shiɗin ya sameni ya aura, lokaci yayi da yakamata nasan komai dangane da aurenmu da
shi da yanda akai na koma hannunsa ba Yah Qaseem ba, inason sanin ina Yah Qaseem
yake ne shin? Miya faru ne ranar ɗaurin aurenmu har aka ɗauramin aure da boss?’. da
wannan tunane-tunanen na shiga bayi, wanka nayo da alwala raina duk a dagule, na
shafa mai sama-sama tare da zira siket da riga marasa nauyi a jikina waɗanda sam
basu kamamin jiki ba. Hoda naɗan shafa kaɗan da lipsgloss na saka turare sannan na
tada salla, bayan an idar ban tashi daga saman abin sallar ba na ɗauka Al-Qurani
nahau karatu, har saida aka kira sallar isha'i sannan na tashi nayi har shafa'i da
wutiri dan yanda nakejin idanuna na bauri nasan kwanciyar wuri zanyi yau.

Koda na fito saina shiga k

icin na ɗauraye kofunan sannan nai zaman gyara masa fruit duk da raina a dagule
yake, na shirya tambayoyi fal ina jiran ya dawo na shiga yi masa su. Nayi nisa a
tunani har bansan ya shigo kicin ɗinba, ƙamshinsa da alamar mutum da najine ya
sakani ɗagowa da sauri. Ajiyar zuciya naɗan sauke dan baƙaramin tsorata naiba da
farko, nace, “Ni ALLAH kaban tsoro”.
“Ai ke komai abin tsorone a wajenki daman” ya faɗa yana juyawa ya fita a
kicin ɗin. Ɓata fuska nayi na cigaba da aikina, sai da na kammala tsaf na ɗoro akan
tray tare da ruwa da lemo sannan na fito. Ganin baya babban falo saina nufi parlorn
sa. Nanma baya nan, na ajiye tray ɗin na nema waje na zauna jiransa ya fito danna
amayar da abinda ke a raina, duk da tsoron da nakeji kuwa. Kusan zaman mintuna
talatin nayi sannan ya fito, ya canja kayansa zuwa wando da riga farare tas masu
taushi alamar yayi wanka. Yanda ya kalleni na kula baiyi tunanin ganina a nanba,
amma sai ya basar ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kamar wani saraki. “Bani
remote ɗin can”. Miƙewa nai na ɗakko masa. Inata dai danne abinda ke raina dan son
yin koyi da nasiha da dabarun da Umm-Anum ta koyamin. Sai da ya kunna television
ɗin sannan yace, “Sun wuce”.
Kallonsa nayi nace, “Su wanene?”. Kamar bazai tankaba ya maida hankalinsa ga
labaran, harma na fidda rai sai naji yace, “Daga masarauta nake”. Duk da na fahimci
waɗanda yake nufin sai nace, “Wai kana nufin su Anuwar?”. Kansa kawai ya ɗagamin.
Na fahimci ransa a jagule yake, amma duk da haka banji zan iya haƙuri ban masa
maganar su Dad ba. Ruwan dana tsiyaya na miƙa masa, ya amsa tare da haɗewa da
hannuna, ɗagowa nai mukaima juna kallon ido cikin ido, murya a sanyaye yace, “Jibi
idan ALLAH ya kaimu zan wuce saudia”. “Nidai dan ALLAH mu tafi tare, kuma ma ai ni
ta sani ba kaiba”. Karon farko datun shigowarsa naga yayi fra'a, ya ɗan murmusa da
zare kofin daga hannuna ya kai bakinsa, sai da yasha ruwan sosai ya ajiye kofin
sannan ya sake dubana, “Kinada kuɗin jirgine?”. Da sauri nace, “Eh” cikin karsashi
da ƙarfin gwiwa. Yace, “Yayi ƙyau hajjaju”. Yay maganar da buɗe plate ɗin dana rufe
fruit dana yayyanko a cikin bowl ɗin glass. Cokali mai yatsu dana haɗo da shi ya
ɗauka ya fara sha hankalin kwance kamar nace nasane🙄😒.
Shiru falon yayi sai tv daketa subaɗi, saida ya sha kusan quarter sannan
ya juyo ya kalleni, “Zo nan naji mike damunki ne?”. Mamaki ya kamani, ya akai ya
fahimta? Saurin gyara yanayina nai da cewa, “Babu abinda ke damuna sai barci”.
yaɗan tsuramin idanu sannan ya janye, “Tunda yau na fara saninki ko?. Taso nace”.
Tashi nai zuwa inda yake ina kumbura fuska, ya fisgoni da ƙarfi na faɗa saman
cinyarsa, ƴar ƙara na saki wadda ni kaina nasan ta shagwaɓace, “Shiiii” ya faɗa
yana saka kankana a baki, bakinsa ya ɗora kan nawa ya sakamin kankanar dake bakin
nasa cikin nawa. Na yamutse fuska kaɗan a raina ina faɗin ‘ƙazanta’. Ɗallar bakina
da yay ya sakani sake ɓata fuska dan naji zafi, ya ɗage gira ɗaya da faɗin, “Nasan
ai gulmata kikai a zuciyarki”. Saida na shanye sannan nace, “Nidai nasan banyiba
ai”. Bai tanka minba ya cigaba da bani fruit ɗin shima yana sha, saida nace masa na
ƙoshi sannan ya barni. Zameni yay na kwanta a kujerar kaina na saman cinyarsa,
wannan damar dana samuce ta bani damar faɗin, “boss wai dan ALLAH wane laifi Dad
yay makane?”. Kallona yay cikin ido ya watsar, ya maidama hankakinsa ga kallon
labaransa hankali kwance. Iya kaiwa ƙarshe nakai da haushi, hakan yasa na sake
maimaita tambayar kozai fusata ya bani amsa, amma nanma saiya shareni, aifa nakai
ƙarshen harzuƙa, na fashe masa da kuka, “Wai miye laifin Dad ne da Yah Qaseem a
gareka? Bayan tarin ƙauna da kulawa da suka nuna maka dagasu har Momy, ƴa fa suka
ɗauka sukutum suka baka ka aura, basu ji komaiba suka sake bakani duk da kuwa ɗansu
jininsune ya dace na aura, sannan ƴarsu da ke tsananin sonka ya dace ka aura kaima,
boss bai kamata ace ka maida alkairi ta wannan sigarba, suɗin ƴan uwanane fa
waɗanda sukaimin gatan da kowa ya gaza yimin, sune suka maidani mutum harna zama
abin sha'awa ga irink.......” ruf ya rufemin baki da nashi, ya ɗagan

i cak batare daya sakimin bakiba yay bedroom dani, duk ƙoƙarin son ƙwacewar da nake
ko gezau baiyi ba, dama ya kashe fitilar ɗakin sai na gefen gado kawai, dan haka
sai kawai jina nai bisa gado, babu wani ɓata lokaci ya shiga juyani da zafi-zafi
yanda yake so, gashi ya hana bakina damar neman ɗauki, yanda yake bi danine ya
tadamin hankali, dan sam babu wani bi a hankali kamar ranar, sai dai kuma hakan bai
hanashi kasancewa cikin nutsuwaba da min abinda zai gusarmin da hankali. Idan nace
muku na gurzu fiye da ranar farko to ku ɗauka gurzuwa nai irin ta ƙarshen nan da
faɗarta kawai takai a tausayamin, dan al'amarin ya zama kamar famine daga baƙar
azabar dana sha a daren shekaranjiya. Muryata harta dasashe saboda kuka, ya kuma ƙi
lallashina kosau ɗaya.
Kamar ranar yauma shine ya taimakamin na gyara jikina, ya kuma sakani a
ruwan zafi sosai sannan ya maidoni saman gadon ya kwantar batare da yace dani uffan
ba, yamayi tamkar baijin kukan nawa, komawa yay bayin yaje yayo wanka shima, har
lokacin ina shashshekar kuka na, muryarsa a dadushe kamar mai mura yace, “ALLAH
idan bakimin shiruba na hawo gadon nan saina sake banbance miki aya da tsakkuwa,
daga yau kuma dan ALLAH ki sake ahiga abinda babu ruwanki kinji ko”. Yana gama faɗa
ya ficewarsa a ɗakin.
Kukan na sake fashewa dashi ina danna kaina cikin filos dan karya ji, kusan
mintuna goma da fitarsa naji ya dawo ɗakin, haɗiye kukan nayi na koma sauke ajiyar
zuciya, bai tankaminba naji dai yanata kai kawonsa har na wasu mintuna kafin ya
hawo gadon. A jikinsa ya sakani ya rungume batare da yace ƙala ba, mintuna kaɗan
barci yay gaba dashi bayan yaymana addu'a, nima ajiyar zuciyata na cigaba da
saukewa har barcin yay awon gaba dani.

★★★★★
Da asuba shine ya tadani, kafinma na sakko a gadon yayi ficewarsa, na
rakasa da harara sannan na sakko da ƙyar, wani irin zafi naji ya ratsani a wajen,
sai ga hawaye shar, nasa hannuna na share ina jinjina muguntar maza a raina, idan
dai haka za'a dingaji to miye abin daɗi anan da har mata suke zuwa suyi iskanci dan
ALLAH?. Sai da na shiga ruwan zafi yanzunma sannan nai alwala na fito, naji daɗi
sosai yanzun kam harda nutsuwa, ficewa nai daga ɗakin na koma nawa, sai fitilar
waya na kunna dan sun ɗauke wutarsu. Ina idar da salla gado na haye nai kwanciyata
ko azkar banyiba, banason yazo ya iskeni zaune, barci yaɗan fara fisgata naji ya
buɗe ƙofar, ban motsaba balle yasan idanuna biyu, sai da ya maida ya rufe sannan
naɗan buɗe kaɗan naga bayanan, ajiyar zuciya na sauke na gyara kwanciya abina.

Taƙwas saura na farka, na sakko daga saman gadon ina matse fuska saboda
ciwon da jikina kemin ta ko ina, bama dole nai ciwon jikiba kodan muguntar da
akaimin, wanka nayi na fito nai shiri cikin wando da riga na parkistan da sukaimin
ƙyau, nai ƴar kwalliya dai-dai misali sannan nasa turare da yafa ɗan gyalen kamar
yanda sukeyi. Fitowa nai dan nema mana breakfast tunda ya roƙi Ummah akan a daina
kawo abinci, a bazata na iskesa a babban falo zaune yana aiki. ‘Agogo sarkin aiki’
na faɗa a zuciyata cike da gulma. Ɗagowa yay ya tsatstsareni da mayun idanunsa,
hakan yasa nai ƙasa da nawa, saida na rissina ina gaishesa sannan ya ɗauke kansa
daga kallona, amsamin yay da tambayata wai ya jiki. “Ni lafiyata lau”. Na faɗa ina
ɓata fuska “Haka akeso ai”. ya bani amsa a taƙaice. Miƙewa nai ina satar kallon
kofin dake a centre table ɗin alamar coffee ya haɗa da kansa yasha kenan? Bance
komaiba na nufi kicin, inaji a jikina kallona yake harna shige.
Idanunsa ya lumshe da sakin murmushi yana ɗauke kansa daga binta da kallo da
yayi, a fili ya furta, “Masu dangi, yauma ki ƙaramin maganarsu kiga yanda zamu
kwashe anan gidan sarkin son ƴan uwa”.
Gyaɗar dana jiƙa da farar shinkafa tun da daddare na wanke, na ɗakko
farar kwakwa da dama na fasa na yayyankata itama na haɗesu waje guda da citta ɗanya
da kayan ƙamshi dai-dai buƙatata na markaɗesu kasancewar akwai wutar da naita
addu'a da fatan su kawo tunda nai sallar asuba, sai da sukai laushi sosai sannan na
tace tsaf na ɗauraye tukunya na zuba, ban kunna gas ɗinba tukunna na ɗib

a wake gwangwani biyu da rabi shima nai zaman dakawa aɗan turmina, sai da yaymin
yanda nakeso sannan na cire na wanke shima nai markaɗan ƙosai, saida na tabbatar na
haɗa komai sannan na kunna gas, ban rufeba tukunyar kunun ba gudun karya taso ya
zube saboda gafin gyaɗa, na saka ludayi ina motsawa a hankali har yay zafi ya fara
kauri, cikin amincin ALLAH baiyi ƙurnu ba yay ƙyau abinsa sai ƙamshin gyaɗa da
kwakwa ke tashi, na sauke tukunyar a ƙasa danya ɗan huce kafin na saka madarar dana
dama. Suyar ƙosan na fara wanda dandanan na gama kasancewar bawani yawane da shiba,
na zuba madarar a kunun sannan na zuba ma maigadi muma na juye mana namu, saida na
gyara komai tsaf sannan na fito da namu a Dining na maigadi ma na fito dashi na
ajiye gefe. Baya a falon, dan haka naɗan gyara tunda babu wani datti na azo a gani
na saka turaren wuta. Ina kammalawa yana fitowa, yay tsaf cikin ƙananun kaya sai
baza ƙamshi yakeyi.
Baice dani komaiba ya ɗauki abincin maigadi ya fita, babu jimawa sai
gashi ya dawo, lokacin ina a Dining ɗin ina ƙoƙarin haɗa masa nasa, kujera yaja ya
zauna idonsa akan hannuna da har yanzu yake raɗam da ƙunshi.
“Duk a yaushe kikai wannan?” na tsinkayi muryarsa a bazata. Kallonsa nai na
janye idanuna, nace, “Yanzun”. “Kinyi ƙoƙari, ALLAH yay miki albarka”. Murmushin
daban niyyaba na saki sai naji duk fushin nawa yay ƙasa, a hankali nace, “Nagode”.
Shima murmusawa yayi kaɗan da ɗaukar ƙosan yakai bakinsa, ya lumshe idanu da faɗin,
“Uhhhmm”. Kallonsa nai dariya na cina, na ɗauki cokali nasa gefensa alamar waiji.
“Yarinya ai ba santi nakeba” ya faɗa yana jan kofin kunun dana ajiye masa a gabansa
sosai. “Nima ai bance santi kake ba”. “Kin taimaki kanki to”.
Murmushin na sakeyi ina ƙoƙarin haɗa nawa nima.
Nayi mamakin yanda yaci sosai, ya ɗauki tissue yana goge bakinsa damin almar
komai zamm da hannu👌🏼. “Nagode to” nafaɗa ina murmushi. Zagayowa yay ta bayan
kujerar da nake ya ranƙwafo ya sumbaci kumatuna duka biyu sannan yace, “Kin gama
mallake Jay da komansa Miemaa”.
Hannu nakai na shafi fuskarsa ina faɗaɗa murmushina, dan naji yanda ya
nuna jin daɗinsa da abincin.
ya zagayo ta gabana ya nunamin kuncinsa alamar na sumbata. Dukda inajin kunya
haka na daure na sumbacesan kamar yanda yake buƙata. Sassanyan numfashi ya sauke da
juyamin ɗayan, nanma dai yi nayi ina mamakin rashin kunyarsa. “Jazakhillah bi
jannah” ya faɗa yana kamo fuskata cikin tafukan hannayensa, kafin nace wani abu ya
manne bakinsa da nawa.
Yana saki na saka hannu na rufe fuska. yace, “Daga baya kenan. Bara naje
Alhaji Babba na jirana zamuje wani waje”.
Miƙewa nai tsaye nima, “To dan ALLAH ka kira Nabeelah tazo ta tayani zama,
ALLAH babu daɗi kaɗaicin”. “Baga wuta ba, kuma nima aiba daɗewa zanyiba”. Cikin
marairaicewa nace, “Idan suka ɗauke fa, kumafa ni tsoro nakeji”. “Jami'ar tsaro da
tsoro”. Ya faɗa yana jan hancina. Bai jira amsataba ya fice yana faɗin “Aimana
addu'a”.
Da “ALLAH ya tsare” na rakasa inajin duk babu daɗi...................✍

Jiya kam Wattpad yay muku buƙulu, nayi typing tun dare zan baku na nemesa na rasa,
wlhy sai sake wannan page ɗin nai cike da haushi, gashi dai sai dai kuyi maneji da
shi😥.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[1/12, 4:57 PM] HASNA ✍🏻
: Typing
ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 47

..................A harabar gidan suka iske Alhaji babba zaune alamar isowarsu
daman yake jira, kafin ma Sadiq ya fito ya buɗema Jay shi harya buɗe da kansa ya
fita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙarisa ga kakan nasa da tun shigowar motar
gidan ya ajiye jaridar dake hannunsa. Cike da zolaya Alhaji babba yace, “Kai angon
nanfa kamin wayo, gaskiya nima azo a nomin ƴar bana bakwai auren nan zanyi ko
kaurin wuya na ƙara da jar fata”. Sosai Jay ya ƙyalƙyale da dariya, ya zauna
akujerar robar dake gefen Alhaji babba yana faɗin, “Duk gasarka dai ba zaka samo
cancaɗeɗiya kamar tawaba Alhaji, domin tawa fa ta musamman ce”. “Ni dai banason
cika baki, kar nan da wata biyu inga ka faramin zarya a gida ehe”. “Ai bama zanyin
ba, sai dai kai ka ringa mana saboda zuwa cin tuwo”. Dariya suka sanya a tare, Jay
ya rissina ya gaidashi cikin girmamawa, kafin su miƙe cike da farin ciki. Sadiq da
shima tuni ya fito a motar ya rissina ya gaida Alhaji babba. Cike da kulawa ya amsa
masa tare da sanya masa albarka. Jawaad ya buɗema kakansa mota da kansa, sai da ya
shiga ya maida ya rufe sannan ya zagaya inda Sadiq shima ya buɗe masa. Kasancewar
tun fitowarsu Jay ya bama Sadiq address ɗin inda suka nufa sai kawai kaka da jika
suka cigaba da hirarsu, yayinda Sadiq keta aikin tuƙi abinsa.
Tun a farkon shigowa layin Sadiq yay tambayar gidan Malam ɗan inna. Kasancewar
sanannen gidane kuma anga mota mai ƙyau dan danan suka samu rakkiya har ƙofar
gidan. Gidane irin da ɗin nan, dan daga ƙofar gidan zaka iya kallon babban zaure
dake da ƙatan murfi ja wanda wahaka ta sakashi komawa mai roɗi-roɗin baƙi. Sadiq ne
kawai ya fita, cikin alnajiran dake zazzaune bisa dakalin gidan wasu na karatu wasu
na rubutu a alluna wasuma hirarsu sukeyi ya ƙarisa. Duk idanu suka zuro masa, ya
ɗaga musu hannu alamar sannu sannan yace, “Ƙannena dan ALLAH ko malam ɗan inna na
nan?”. Babban gardi dake karatu da sauri-sauri tamkar zai haɗiye harshensa ya
dakata yana kallon Sadiq ɗin. “Malam baya nan, amma ba nisa yayiba”. Sadiq dake
saurarensa yace, “To masha ALLAH, dama baƙine muke tare dasu gasu a mota, idan babu
damuwa ko za'a aika wani ya kira mana shi ne?”. Gardin baice komaiba ya gyara zaman
allonsa ya sakko daga dakalin, zauren gidan ya shiga, babu jimawa sai gashi ya
dawo. “Ku shigo” ya faɗa kawai yana kallon Sadiq. Sadiq baice komaiba ya juya ga
motar, a saitin Jay yay knocking glass ɗin, Jawaad da gaba ɗaya hankalinsa na'a
tattaunawa da Alhaji babba ya juyi tare da sauke gilashin motar. “Oga yaronsa yace
baya nan amma bai nisaba, yace kushiga ciki inaga zaije ya kirashi ne”. “Okay”
Jawaad ya faɗa a taƙaice yana maida kallonsa ga Alhaji babba dake saurarensu.
Kusan a tare suka fito, a take dukkan almajiran dake wajen suka zubo musu idanu,
sannu kawai suke musu babu batun gaisuwa, su dai suka shige cikin zauren dake ƙaton
gaske, sai dai ko'ina mulmule yake da suminti, sai alluna masu yawan gaske dake
jijjingine da kowacce kusurwa ta bangon zauren. Zama sukai a tabarmar da aka
shinfiɗa, Sadiq dai dama bai biyosu ba sai Gaddin nan kawai. Saida yaga sun zauna
sannan ya shige wata ƙofa alamar cikin gidanne, babu jimawa sai gashi ɗauke da
kofin silba babba. ya ajiye a gabansu sannan ya gaishesu. “Bara naje na kirashi
yana nan ƙasan layi suba wata mata mara lafiya”. Alhaji babba ne kawai ya amsa
masa, ahi Jay ma dai kallon Gaddin yake cike da nazari.
Kusan mintuna talatin da fitar gaddin nan sai gashi ya dawo tare da Dattijo, daka
gansa kasan akwai wahalar rayuwa tattare da shi, dan tsufan nasa yafi shekarun yawa
a zahiri. Tun shigowarsa Alhaji babba ya shaidashi tsaf, dan kamanninsa na ƙuruciya
duk suna a tare dashi, ya ɗan murmusa yana sake girmama buwayar UBANGIJI.
Sannu da zuwa shi dai malam ɗan inna keta zuba musu, ya zauna saman buzunsa dake
fuskantar su Jawaad, shima dai kallon sani yakema Alhaji babba, sai dai ya rasa a
ina yasan fuskar ne?. Hannu ya fara bama Alhaji babba suka far gaisawa, sannan ya
miƙama Jawaad shima suka gaisa. Cikin ɗan tsantseni yace, “Sai dai kuma ban gane
baƙin nawa ba duk da ina musu kallon sani sai dai na rasa a ina?”.
Murmushi Alhaji babba yayi yana gyara zamansa, yace, “To bazan musa makaba, sai dai
nasan ƙila kamanni kake gani kawai. Da farko dai sunana Nuhu. wannan jikanane
sunansa Jawaad, munzo neman wani bawan ALLAH ne mai suna Adamu”.
Malam ɗan inna ya kafe Alhaji babba da kallo, dan yanzukam ya gano ta inda ya kema
Alhaji babban kallon sani, to amma abin tambaya shi wanene? Haɗiye wannan tambayar
yayi a ransa, a fili yace, “To Adamu dai biyu ke garemu, ɗaya muna kiransa Ado,
yanzu haka yana can balaguro kudu damu, shiɗin babban ɗanane, yanada iyalinsa duk
suna man cikin gida tare damu, sai kuma ɗan ƴar uwata shima sunansa Adamu, amma ana
kiransa Adamu makaho, shikam dai ALLAH yay masa rasuwa shekara kusan ta takwas
kenan, matarsa ma ta rasu kafin shi”.
Su jay suna jira suji yace yana da ƴa sai sukaji yay shiru.
Alhaji babba daya haɗiye mamakinsa ya gyara zama yana faɗin, “Masha ALLAH, mu munzo
neman Adamu makahon ne, ashema ALLAH yay masa rasuwa?”. “Tabbas ya rasu dalilin
mota data bigesa”. Ƙwallar data cika idon Alhaji babba yasa bakin rigarsa ya share
yana ɗan murmushi, “ALLAH ya gafarta masa shi da matar tasa”. Amin ya rabbi, da
Alhaji ɗan inna suka faɗa a tare.
“Mahaifiyarsa fa ko ita tana raye? Sannan shi baibar zuri'a ba ne?”. Alhaji babba
ya faɗa cikin ƙarfin hali.
Alhaji ɗan inna ya jinjina kansa, “Mahaifiyarsa ta jima da rasuwa, dan dalilin
jinyane ma ya maidota gida saboda shekaru da dama ba'asan inda takeba ita da ɗan
nata, sai kawai rana tsaka muka ganta tare dashi, adalilin jinya ya matsa suka dawo
gida, dan shi makanta ta samesa ta idi ɗaya tun ƙuruciya dalilin ƙyanda, to ganin
inda suke babu mataimaki sai ALLAH ya matsa mata harta faɗa masa tushenta suka
dawo, kowa ƙin yarda ta raɓesa yay a cikin dangi, sai nine na bata masauki a
gidana, na kuma riƙe shi Adamun tamkar sauran ƴaƴana har nai masa aure, bayan
aurensa da shekara kusan huɗu ALLAH yay ma yaya Sa'a rasuwa. Shi adamun da anan
cikin gidan nawa suke zaune shi da matar tasa mai suna Asiya, itama tanada nakasar
ƙafa dan gurguwa ce. Daga baya kuma sai suka tashi”.
Kafin Alhaji babba yay magana Jay yay saurin faɗan, “Miye dalilin tashin nashi?
Sannan kuma basu da yarane? Naji baka amsa wannan tambayarba”.
Malam ɗan inna yaja fasali yana sake gyara zamansa a karo na babu adadi. “Mudai a
saninmu Adamu baida wasu ƴaƴa, amma kuma al'amarinsu dalilin wata ƴa ƙwallin ƙwal
yazo ma mutane da ruɗani musamman lokacin da tai girma kamanninta da nashi suka
fita. Tun aurensa da Asiya bata taɓa ko ɓatan wata ba a gidanan, danni da kaina nan
nasha basu taimako akan hakan ko za'a dace, amma har bayan rasuwa yaya Sa'a da
kusan shekaru uku babu wani bayani daga matarsa, hakanne ya saka muka fara masa
kwaɗayin kozai ƙara aure. Amma ya murje idonsa yace baisan wannan zanceba shi yana
son matarsa. Munta lallaɓashi akan inma kuɗin auren yakeji karya damu zamu haɗa
muyi masa, tunda dai maganar ciyarwa daga iyalina ake basu abincin dare da rana, na
safe kawai yake samowa da yake yana ƴar sana'arsa ta gyran tsummokara. Sam bai
saurari kowaba, dama yaga an takura masa da zancen sai kawai rana tsaka yazo mana
da maganar zai tashi ya samu ɗakin haya a wata anguwa dalilin abokinsa. Munsha
mamaki sosai da al'ajabi, dan bamuyi zaton gatan da muke masa har yakai abin zafin
da zaiyi tunanin yin nesa damu ba. Hakan ba ƙaramin sqkamu ɓacin rai yayiba ainun,
musamman ma ni da nake ganin na taimakesu shiga mahaifiyarsa a lokacin da kowa ya
gujesu. Cikin fushi nace yaje abinsa, amma karya sake tunawa dani matsayin ƙanan
mahaiyarsa tunda ya zaɓi mace sama damu. Suma sauran dangi duk sukai masa wannan
furucin.
Baiko nuna yaji ko ɗarba ya tattara matarsa daƴan komatsansu sukabarmu zuwa can
nesa damu sosai. Tunda suka tafi bamu sakejin ɗuriyarsu ba sai bayan shekara biyu
sukazo mana nan matar tasa da ciki ƙarami, da farko kowa yaƙi saurarensa, amma ni
saina sauraresa ganin abin farin cikin da matarsa ke tare dashi, shima ya nema
gafararmu dukda wasu a cikinmu basuce dashi sun yafe ɗin ba. Matarsa ta cigaba da
rainon ciki lokaci-lokaci sukanzo gaishemu, hakama yaranmu sukan ɗanje musu, idan
kuma sabga ta tashi matarsa na zuwa har cikinta ya shiga wata takwas. Rana tsaka
yazo ya sanar mana wai tana asibiti babu lafiya, likitoci sunce ɗan cikinta ya samu
matsala cireshi zasuyi dan rabin jikinsa a ruɓe yake, ma'ana dai bamashi da rai
kenan, suna buƙatar kuɗaɗen da za'ai mata tiyatar, shi kuma na wajensa basu kaiba
amma dan ALLAH mu ranta masa a hankali zai biyamu idan komai yay dai-dai. To mudai
bai samu ko sisiba daga garemu, dan bamu dashi saboda kuɗin sunda yawa gaskiya,
haka ya tafi. Mukuma anan mukai shiri domin zuwa mu duba matar tasa sai dai kuma
mun manta bamu tambayesa asibitinba. Haƙura mukai muka zauna zaman jiransa kozai
sauyo saiya kaimu. To adai ranar bai dawo ba sai washe gari mu mukaje can gidan da
yake hayar muka tambaya, daga can akai mana rakkiya asibitin, tun kuma kafin muje
an sanar mana ai anmata aikin an cire ɗan babu rai. Amma abin mamaki sai muka
isketa da jaririyar yarinya a hannu. Babu wanda ɗunbin mamaki bai kamaba a cikinmu,
har muka kasa haƙuri mukai magana tunda ita amma ce ɗa namiji aka cire mata kuma
baizo da raiba. Amma sai cewa sukai ai jaririyar dake wajenau itace ƴar tasu, yaran
ƴan biyu ne, ɗayane babu rai ɗaya da rai. Sam bamu yarda dasu ba, hakan yasa mukai
fushimuka bar musu asibitin, munta sauraren muga Adamu ya biyi bayanmu yay mana
cikakken bayani akan gaskiyar al'amari sai mukaji shiru, a haka har shekaru suka
shuɗa yarinya ta fara girma, kowa dai yasan tabbas ƴarnan ba ɗiyar Adamu bace akwai
abinda suka ɓoye dangane da samuwarta, amma kuma a zahiri ga wasu abu na kamanninsa
na bayyana ga yarinyar, sannan idan ka nutsu da kallon yarinyar lallai zakaga wasu
abubuwan na Asiya tattare da ita dukda sam batayo asalin fuskarta ta fulaniba dan
Asiya farace tas kuma ƙyaƙyƙyawar gaske, wahalhalun rayuwane kawai suka ɓoye kaso
mafi yawa daga ƙyawunta, wannan abu shine ya kawo mana ruɗani maiban mamaki wanda
har a yanzu da kuke a gabana bamu fita daga cikinsaba, kuma har Adamu ya rasu shida
matarsa basu taɓa faɗa mana komai daya shafi yarinyarba”.
Alhaji babba daketa sauke tagwayen ajiyar zuciya na tausayin gudan jinin nasa da
son zuciya ya saka mahaifiyarsa nisantasu ya share ƙwallarsa, muryarsa a raunane
yace, “Tabbas bakai dake bamu labarin nanba, hatta dani nan ka sake dulmiyani a
ruɗani, taya za'ai kuna zargin ba ƴarsu bace amma kuma take kamanni dasu ta wasu
abubuwan? Koni dana kalli hotonsa da yarinyar naga tabbataccen jini na haƙiƙa
tattare da junansu, na tabbatar koda kutu akaje wannan yarinya za'a iya tabbatar da
tasuce babu wani haufi a cikin hakan”. “Tabbas hakane Baba, sai dai mai warware
ainahin gaskiyar lamari sai ALLAH sai kuma su da suka kasance da yarinyar, gashi
kuma a yanzu duk basa a raye”.
Jawaad da baice ƙalaba, saima latsa waya da yakeyi, batare da ya ɗagoba yace,
“Yanzu Kunsan inda yarinyar take ku?”. Yanda yay maganar babu wasane ya saka Alhaji
babba da Malam ɗan inna kallonsa, dukda yasan kallon nasa suke bai ɗagoba, baikuma
gyara fuskarsa dake a ɗaureba. Malam ɗan inna da duk ya daburce yace, “E.. e eto
saurayi yarinyar dai tana gidan da ayka zauna”. Ɗago idanu Jay yay ya kallesa,
“Kenan babu wanda ya ɗauketa a cikinku bayan rasuwar mahaifinta saboda kunaji a ita
ba jininku bace bayan kuma UBANGIJI ya baku komai a bayyane tunda ya fidda kamanin
iyayenta a jikinta?”. “Saurayi ba haka bane ba”. “To yayane?”. Kasa cewa komai
malam ɗan inna yayi, sai zufa data jiƙe ta cikin babbar riga, shi dama tun
shigowarsa bai hangi sauƙi da ga yaron nanba sam.
Ajiye wayar Jawaad yayi yana fuskantarsa sosai, “Malam da farko dai yanzun bara na
fito maka a mutum, wannan da kake gani dai shine mahaifin Adamu makahon, mijin ƴar
uwarka Sa'a wanda ta gudar masa da ɗa bisa son zuciyarta, ina fatan ka gane”..
Sallalami malam ɗan inna ya kwaso daga samaniya ya dire bisa ƙasa yana zare idanu
jikinsa na ɓari, “Wai dan ALLAH da gaske kana nufin Mati ne? Dama kana raye? Adamu
yayta nemanka ruwa a jallo amma ko labarinka bai taɓa samuba daga wani, dangi da
duk muka sani a baya mun sakashi ya abi amma duk sun rasu bai samu ko guda ba a
ciki”.
“Hakane Hamza, kasan idan UBANGIJI nason saukar da wata aya ga bayi saiya datse
al'amarinsu ya ɓoyesa a rasa bakin zaren a dalilin ƙaddara, muduka ƙaddarace ta
ɓoyemu dukda muna a cikin gari ɗaya, nima nasha bibiyar ahalinku dalilin son ganin
ɗana ya dawo gareni, sai dai hakan bata kasanceba har gashi ƙasa ta rufe idanunsa,
hakan jarabawace, dan tabbas tun daga Zazzafar soyayyar danaima Sa'a har zuwa zaman
aurenmu da guduwarta da yarona duk jarabawace a garemu da wata hikima ta UBANGIJI,
naso ace na sake ganinsa, naso ace na kwatanta sauke haƙƙinsa dake kaina matsayin
mahaifi a garesa, naso ace shima ya tashi cikin ƴan uwansa da a yanzu sune suka
zamema rayuwata haske, ALLAH ne yaymin komai da kaini matsayin da nake a yanzu amma
ta dalilinsu ne, na yarda abinda kakeso bai zama lallai ya kasancema rayuwarka
alkairiba, wanda kake ganin yay kutse ma rayuwarka sai kaga shine alkairin, naso
Sa'a so mai tsanani, harnaso bijirema iyayena a kanta, sai dai itaɗin ashe ba itace
abinda nake ma hasashenba, wadda iyayena suka auramin ina baƙin ciki da takaici, na
ƙuntata rayuwarta a zamanmu sai tazama ashe itace abinda banyi zatonba, dan gashi
yanzun albarkacin zuri'arta nakeci ita bata raye, wannan aya ce ga masu ZUCIYA irin
tawa, ɗan adam shidai abinda akeso ya nema zaɓin ALLAH akan dukkan al'amarin sa ba
wai son zuciyarsa ba”.
Sosai Malam ɗan inna keta faman jinjina kansa, Jawaad dai yana saurarensu amma
bazaka taɓa fahintar yanayinsa ba sam, saida Alhaji babba ya gama share-sharen
hawayensa sannan Jawaad ya ɗago ya sake kallon Malam ɗan inna, “Na biyu kuma zamuje
da kai gidanda suka zauna danka nuna mana yarinyar, mu zamu ɗauketa mu riƙe, basai
munsan gaskiyar yanda suka sametanba”.
Sosai ruɗani ya bayyana ga Malam ɗan inna, ya shiga matsar hawaye yana bada haƙuri
da musu bayani akan suma basusan inda Bilkisu take zaune ba, amma kwanaki taɗan
zazzo gaishesu, sai dai maganar gaskiya ko tazo ɗin basu wani sake mata fuska,
danshi sau ɗayama ya taɓa ganinta, kusan shekara uku kenan ya kuma ja mata gargaɗi
akan karta sake zuwa masa gida tunda basu da alaƙa da ita, dan saida ya titsiyetama
yaji wanene ya nuna mata gidan kafin yaymata korar rashin arziƙi. to amma yaji
kwanaki iyalinsa suna gulma wai tana zuwa wajen Ramatu, kuma ma har tayi aure kwana
nannan ita Ramatun taje.
Kafesa kawai da kallo Jawaad yay ransa a matuƙar ɓace, ganin hakanne ya saka Alhaji
babba riƙe hannunsa yana murzawa alamar lallashi, hannunsa ya zame ya tashi ya fice
daga zauren.
Alhaji babba yay murmushi yana girgiza kansa, sannan ya maido kallonsa ga Malam ɗan
inna da shima yabi Jawaad ɗin da kallo, “Haka yake yana da matuƙar zuciya, sai dai
yanada kirki sosai, shine jikana na farko da ƙanwar Adamu mai suna Bilkisu ta wajen
Amina kenan ta haifa, ɗan tsohon shugaban ƙasa da ALLAH yayma rasuwa Alhaji
Abdul'aziz yusif tafida”. Idanu sosai malam ɗan inna ya zaro, cikin ɗan rawar baki
yace, “Dama yarinyar wajenka ce matar marigayi A.Y tafida?”. “Hakane, gama yaronsu
da ya bari nan”. “ALLAH maiyin yanda yaso, ALLAH mai hikima, lallai zaɓin ALLAH
shine zaɓi kam bawai son zuciya ba, wanene zai iya mantawa da tsohon shugaban ƙasa
Abdul-aziz Yusif Tafida a ƙasarnan ai saida azzalumi, adalin shugaba da har yanzu
ba'a ƙara samun makamancinsa ba ma”. Murmushi Alhaji Babba ya dingayi jin ba'a
manta da ɗan matarsa ba, surikinsa kuma uba ga babban jikansa. A take ya warwarema
Malam ɗan inna gaskiyar al'amari dan gane da bilkisu harma aurenta da jikansa
Jawaad, wanda a dalilin hakanne kuma yasaka su ma bincike har suka ganosu ta
dalilin kamannin bilkisu da Adomu daya gani, da kuma ƴarsa data rasu Rahmah, wanda
yake ganin bilkisu ta ɗakko kamanin Rahama ne saboda ƙarfin jini, to gashi sukuma
sunmace basu yarda ADamun ta haifi bilkisu ba, to shi ina zasu kama su fahimci
gaskiyar wannan ruɗanin ne. Al'ajabi ya sake kama Malam ɗan Inna har takaisa ga
sharar hawaye, yayta ban haƙuri da neman afuwa ga alhaji Babba tundaga laifin da
ƴar uwarsu ta zama sila har wanda suma suka tafka. Tarr syka fito har wajen mota
yana bama Jawad da yay kicin-kicin da fuska haƙuri shima. Hannu kawai ya ɗaga masa
da jinjina kansa, dan ransa a ɓace yake, kuma bayaso kosau ɗaya fushinsa yakaisa ga
aikata abinda bai daceba ga dattijon da zaiyi sa'a da mahaifinsa, gashi koba komai
akwai alaƙa.
Sun rabu akan zai faɗama sauran ƴan uwansa komai auzo kuma har gida su ƙara bada
haƙuri.

Lallashin Jawaad Alhaji babba yay tayi cikin hikima, tun yana baɓɓata fuska na
shagwaɓa harya sake yana masa murmushi, gida suka maida Alhaji babba, batare da sun
shigaba Sadiq yay reverse suka sake barin anguwar. Daga nan inda ya ajiye ɓaleru
suka nufa kuma.
Tun shigar Jay ɗakin da ɓaleru yake jikinsa ya fara ɓari, ya ajiye abincin da yake
ci gefe yana zazzare idanu, da hannu Jawaad yay masa nuni da abincin alamar ya
ɗauka ya cigaba da ci. Babu musu ɓaleru ya ɗauka teakaway ɗin yana cusawa kamar
yanacin maɗaci saɓanin yanda abincin ya fara masa daɗi da farko.
Ɗauke kai Jawaad yay daga garesa, saida ɓaleru ya cinye abincin tas ya ajiye batare
da yaci kifin cikiba, ”Shikuma wannan waka barwa?”. Jawaad ya faɗa yana
tsatstsaresa da idanu murya a kausashe. Ɗauka ɓaleru yay da sauri ya hau ci, ALLAH
dai ya taimakesa ƙaya bata maƙale masaba ya gama lafiya. Hannu yaje ya wanko ya
dawo, ya maƙure jikin bango hantar cikinsa na kaɗawar tsoro, dan har yanzu baibar
jin ciwon jikin dukan daya shaba ranar. Jawaad ya ajiye wayarsa yana kallon ɓaleru
da ƙyau. “Ka shirya faɗamin gaskiya ko sai mun sake kalar wasan ranar?”. “Wlhy duk
abinda kake buƙata inhar na sanshi zan faɗa maka oga”. “Tunani mai ƙyai” Jay ya
faɗa yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. “A gidan wa kake aiki?”. “Mr Gebrail”. “Waya
sakaka ka ɗauki Gimba a mota?”. Inda inda ɓaleru ya nema farawa Jay ya daka masa
tsawa, “Wlhy ko sau ɗaya kamin ƙarya saina karyaka a wajenan na ɗauraka”. Sanin Jay
zai iya aikatawa yasa ɓaleru haɗiyar yawu muƙutt, “Uh.. Uh... Uhmm ni dai kawai
wata safiya ne aka kirani da kwatanta mini shi, bammayi zaton shi bane saida naje
zan ɗaukesa”. “Waye ya kirakan?”. “Mr Gebrail ɗin”. “Ina ka kaishi?”. “Wlhy acan
titin ƙatshen gari ya tareni ya amshesa?”. “Kenan dama ka saba musu irin wannan
aikin? Koma shi kake musu?”. “Oga Wlhy.....” “Amsa kawai nake buƙata, duk abinda
yazo a saɓaninta kai kuka da kanka”. Kansa ya ɗaga da sauri yana karkarwa. “Shi da
waye suke sakaka? Kuma wanene ya kaika aiki gidansa?”. “Ɓaleru ya share hawayen da
suka cika masa idanu, “A anguwar da gidan drama ɗin nan yake yake gini, wataran
yazo wajen shine ya ganni”. “Sai kawai yace zoga aiki na baka?”. “A'a nine da kaina
naje na tambayesa saboda a lokacin aikin nake mema, to da yake ina ɗibo yashi daga
can wani rafin dake ƙasan anguwar ina kawoma masu gini na saya, lokacin ana aikin
gininsa kuma nine mai ɗebo musu yashin, sai naji yana tambayar Engineer ɗin ko
yasan wani driver? Dan yanason ɗaukar driver, drivernsa ya ajiye aiki saboda tsufa,
to ahinefa nace zanyi da yake na iya mota. Da farko yayi kamar bazai ɗaukeniba sai
kuma ya bani key yace na gwada ya gani, a take na amsa na shiga motarsa naɗan
zagaya wajen, a lokacinma bai amsa zai ɗaukeniba ya tafi, sai bayan kwanaki biyu
harma na fidda rai sannan yazo yace ya ɗaukeni”. “Daga nan sai ya maidaka kidnapper
ko? Har takai kuɗi ya rufe idonka aka haɗa baki dakai aka kashe abokinka ɗan
garinku?”. “Wlhy oga bada ni aka haɗa baki aka kashesa ba, hasalima nima mutuwarsa
kawai naji, wlhy tunda gimba ya rasu ban sake samun kwanciyar hankaliba, oga ina
tsaka mai wuya”. “Ai bama ka shigaba tukkunna indai tsaka mai wuya ce. Ya akai ka
tuƙa Alhaji Kokino ranar kuma?”. “Alhaji Kokino kuma? Wlhy ni bamma sanshi ba”.
“Humm kana wasa dani ko?”. “Wlhy oga da gaske nake maka”. Jay baice komaiba ya
ɗauka wayarsa, hoton da yay musu lokacin da traffic light ya tsaidasu ya nuna masa,
ɓaleru yace, “Aiho, ai yaje office ɗin Mr Gebrail ne sakan kasuwanci sai motarsa ta
samu matsa, shine drivernsa ya ɗauka ya kai wajen gyara, to bai dawo da wuriba shi
kuma ya gaji da jiransa shine yace na kaisa gida, wannan shine dalilin da yasa ka
ganmu tare”.
Kafesa da kallo Jay yayi cike da nazarin maganarsa, bai sake cewa komaiba ya miƙe,
fitowa yay abinsa. Ɓaleru ya bisa da kallo, daka ganshi kasan a tsorace yake.
Securitys ɗin dake kula da ɓaleru ya korama winning akan su kula dashi da ƙyau, duk
kuskuren da aka samu sune zai fara hukuntawa. Daga haka ya shiga mota suka bar
gidan.
Ganin lokacin sallar la'asar yayi saiya saka Sadiq tsayawa sukayi sannan suka
ƙarasa gida.
★★★★
Bily na zaune da ƴammatan maƙwafta da suka shigo mata dan a gaisa asan juna ya
shigo. Sannu da zuwa tai masa, suma suka shiga gaisheaa suna binsa da kallo tamkar
wasu mayu. Kallo ɗaya yay musu ya amsa Sau ɗaya yay shigewar, miƙewa nayi, dan haka
suma duk suka miƙe, sallama sukai man suka tafi, nai musu godiya nima sannan naje
kicin na ɗauki kunun ayar da nayi na nufi ɗakin nasa. A bakin gado na iskesa zaune
ya dafe kai, koda nai sallama bai ɗagoba yadai amsa mani. Naja ƙaramin table ɗin na
ajiye. “Su wanene waɗanan?”. Ya faɗa batare da ya ɗago ba. “Nima ban sansuba, basu
fi mintuna talatin da shigowaba, sunce min nan gidan maƙwaftan nan namu suke”.
Amsar kofin dana miƙa masan yayi, yaɗa lumshe idanu sannan yasaka a bakinsa ya
shanye gaba ɗaya alamar yanajin ƙishi sosai, kofin ya ajiye yana miƙewa, “Kidaiyi a
hankali”. Ya faɗa yana cire maɓallan rigarsa. “Insha ALLAH zan kiyaye”. Na faɗa ina
miƙewa.
Hannunsa ya miƙomin yana min nuni da rigar, dukda dai inajin nauyinsa haka na kama
na taimaka masa muka cire, dan na lura shifa komai yafison ai masa. Na juya zan
ajiye rigar naji kawai an kwasheni anyi sama dani, ina mamakin yanda ya ƙware da
iya ɗaukar mutum babu ko ɗar, shi ko nauyina bayaji ma.
Ganin ya nufihanyar bayi nai saurin cewa, “Bandaɗe da yin wankaba fa ALLAH”. “Ke
kika san wannan”. Ya shige toilet ɗin yana faɗa. Nidai balki naga ta kaina, inaji
ina gani dole akai wankan nan, ni gaba ɗayama ya fara busarmin ido da salonsa. Haka
mukai wankan muka fito, bayan mun kimtsa muka fita domin cin abinci.
★★★★★★★★
Yau kwanakinmu shida kenan da tarewa, zuwa yanzun bansan yanda zan lissafo muku
abubuwan da boss ya koya minba, gaba ɗaya ya fetsarar dani, duk da dau bana fiddo
zaƙewat dan akwai sauran lokaci, kunyarsa kuwa inajinta tamkar babu gobe, dan duk
abinda zai sakani na masa inayi ina rufe idanu, mu'amular gadoce fa na kasa sabawa,
dan duk sanda zaizo min babu fashi sai nayi kuka, har fargaba nake ya nuna
buƙatarsa, duk da hutun amarci da aka bamu hakan bai hana boss aiki tuƙuruba a
gida, ni kaina bai barni na hutaba, matan su Jabeer sunzo sun yinarmin, hakama su
Safah an kawosu, Amina ma tazo ta yini randa matan su Jabeer sukazo, da yamma sai
ga su Nazifa ma, maganar da muka tattauna ta sakani fahimtar sun shirya zuwanne
dama, nayi farinciki sosai ganin maganar ƙungiya ta kankama, komai an kammala na
shirye-shirye a satinan za'a fara fidda komi ta kafafen yaɗa labarai da yanar gizo
kamar yanda aka tsara, dan aomuke mu fito da zafinmu, ga bikin Nazifa nata matsowa
ita, dan ƙarshen wata mai kamawa ne.
Bayan tafiyarsu na gaji liɓis dan dan suma su Aliyun anan suka kusan yinar mana
tare da boss, sauƙina ma basu bar gidanba saida suka tayani na gama komai tsaf
gidan ya dawo normal, sanin ko nayi wanka idan ya dawo saina sake dole tare da shi
dan kullum tare muke wankan dare sai kawai naƙiyi na dafa masa shayi na gyara
fruit. Falonsa nakai komai sannan na shiga haɗa ruwan wanka, ina ciki kuwa ya
shigo, sai kawai jinai an ringumeni ta baya. Murmushi kawai nayi na juyo muna
kallon juna, murmushin shima yamin da kai hannu a.................✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


✍🏻
[1/13, 3:03 PM] HASNA : Page 48

..............Murmushi shima yaymin da kai hannu a ƙuguna ya kuma matsoni sosai


jikinsa, cikin raɗa yace, “Are you ready?”. Ɓata fuska nayi ƙwalla na cikamin ido
na girgiza masa kai dan nasan inda ya dosa. Wata shaƙiyyar dariya yayi dajan
hancina yace, “Kedai raguwa ce yarinyarnan”. “Ni dai wlhy naji koma miye ace ba
raguwaba, kai dan bakasan wahalar da ake sha bane ai”. Bakinsa ya ɗaura a saman
kunnena ya ɗan ciza yana dariya da faɗin, “Shiyyasa nake son maidaki jaruma”. Nai
saurin ƙanƙamesa saboda tsigar jikina dake tashi, da sauri na mintsini damtsan
hannunsa “Ai na fika jarumta”.
Saurin sakina yay da faɗin, “Ouch!. Ke dai muguwace wani lokacin”. Gwalo na
masa na shige cikin ruwan. biyoni yay ciki, “Yarinya kin taro match kuwa”. Saurin
ɗaukar soso nai dana haɗama kumfa na saka masa a fuska, yay ƙoƙarin riƙe hannuna
naƙi bashi dama, hakan yasa mukaita facal-facal da ruwan kamar wasu ƙananun yara.
Sai da muka gama shiriritarmu sannan muka fito. Zama nai a kujerar mirror ina
goge fuska yazo ta bayana ya tsaya yana miƙamin hannunsa.
Cike da mamaki na kalli hannun nasa, wani ɗan ƙyaƙyƙyawan akwatine mai kama
da diamond amma farine shi tas wannan, sai ɗaukar ido yake da ƙyalƙyali, ɗaga kai
nayi na kallesa ta cikin mirror ɗin ya ɗaga min kai da lumshe ido. Yawu na haɗiye
da ƙyar nasa hannu na ɗauki ɗan box ɗin inayi ina kallonsa, ganin idonsa a kaina
yake har sannan sai na nutsu waje guda, jiki a sanyaye na buɗesa. Na waro idanu
sosai waje da faɗin, “Woow!” dan ƴan kune ne masu ƙyau a ciki da zobe. Bansan sanda
na juya na daka tsale na ɗanesa bama ni, ya riƙeni da hannu biyu yana dariya muka
faɗa saman gadon, tattare kunya nai na ajiye gefe, cikin salonsa daya koyar dani na
shiga sumbatarsa fiye da yanda ya koyamin nasa karatun. A take ya rikicemin, nima
dai nasan na taro match ai dama, tunda a hannu yake, dan wannan boss ɗin da kuke
gani hummm, baisan wasaba ta wannan fannin.
Duk yanda na dawo kuma ina roƙo da magiya daga ƙarshe bai saurareni ba,
sai da ya samu abinda dama yakema ƙulafucin. Daga ƙarshe ya barni da kuka😒 (Kinada
matsala ɗiyarga🚴🏼. Lol)
“Haba my sweet Miemaa na Mai gadon zinarina, kukan ya isa haka Uhimyim,
kece kinzo da salon da ban taɓa zaton kin iyaba, ashe kina ɗaukar karatun dai-dai
gwargwado”. Cusa kaina nai jikinsa ina ɗan kai masa duka. Ya riƙe hannayen duka
yana sakin murmushi mai sauti, “To shikenan nama fasa zuwa dake ni kaɗai zan
tafiyata saudian gobe idan ALLAH ya kaimu”. Da sauri na ɗago na kallesa hawaye
shaɓe-shaɓe, “Dan ALLAH da gaske kake?”. Goshina ya sumbata yana murmushi, “Idan
kin barmin kuka ba”. Saurin share hawayena nayi, yaymin raɗa a cikin kunne. Zabura
nai da sauri inaja da baya, “Dan ALLAH ka tausayamin wlhy bazan iyaba”. Jawoni ya
sakeyi jikin nasa yana murmushi, ya sake min raɗa a acikin kunne, hakkane ya sakani
yin luff a jikin nasa ina sauke tagwayen ajiyar zuciya, shiko yana aikin shafa
bayana alamar lallashi.
Saida ya tabbatar nabar kukan sannan muka je muka sake wankan, shirin barci
mukai muka koma falo, gaba ɗaya ya sake rugurguzar dani da gajiya, ko iya zaman
shan fruit ɗin banyiba na kwanta da ɗora kaina a cinyarsa sai barci. Buɗe ido kawai
nai da asuba na gammu a kan gadon ɗakinsa.

Kamar yanda ya faɗa bayan dawowarsa sallar asuba ya sakani muka shirya
kaya akwati ɗaya kacal, da dukna ɗauka wasa yake wlhy, sai da naga dai da gaske
yake sannan na yarda. Da taimakonsa na gyara gidan, na killace duk abinda ya dace
da ya zam a kilkacen, abinda nasan zai iya lalacewa naci na tattaresa ya kaima
maigadi da Sadiq da yazo zai kaimu airport. Mamaki bai nema kasheniba sai da muka
fito zamu tafi, securitys ɗin hukumarmu na gani nata kaikawo, na kallesa amma sai
ya ɗauke kansa alamar baya buƙatar kowace iriyar tambaya, dole naja bakina na tsuke
dan a zauna lafiya tunda baya buƙata.
Wani gida muka fara zuwa, saida muka shiga naga dattijon tsoho da naita son
tunano inda na san fuskar amma na kasa hakan, ga kallon da ya kemin shima tsigar
jikina har tashi take. Har ƙasa na tsugunna na gaidashi cike da girmamawa.
Yanda ya amsamin da tsantsar kulawane ya sakani kallonsa, ya sakarmin
ƙyaƙyƙyawan murmushi wanda a wajen Mahaifina kawai nasan irinsa, gabana yay wata
irin yankewa ya faɗi har ina ɗan dafe ƙirji, “Babana”. Na faɗa a zuciya batare dana
san maganar ta fito fili ba. Daga Alhaji babba har Jay kallon Bilkisu sukai.
Nai saurin zama ƙasa danjin ƙafafuna suna neman gaza ɗaukata, wlhy da tsohon
nan yay murmushi sai naga kamar babana ne, sake ɗagowa nai na kalleaa sai naga duk
idanunsu a kaina suke. Boss yace “Yaya dai?”. Kai na girgiza masa da sauri alamar
babu komai ina sake satar kallon tsohon ta gefen ido.
“Tashi ki koma saman kujera”. Muryar tsohon ta daki dodon kunnena. “Nanma
Yayi Baba” na faɗa muryata naɗan rawa.
Murmushi yayi da har na iya jinsa daga inda nake, yace, “Amarya lallai kin iya
tuwo, naga wannan ɗan dokar ya washe harda kaurin wuya ya ƙara”. Murmushi nayi
kaina a ƙasa, sai boss naji yana basa amsa. “Idan yaji haushi gobe muje ɗaurin
aurensa Miemaa, idan ya auro matarsa shima saita ringa masa yayi kaurin wuyan”.
Dariya naji ya ƙyalƙyale da ita. Haka suka cigaba da tsokanar juna cike da birgewa,
kafin suɗan tattauna. Banji ya faɗa masa ainahin mi zamuje yiba, hakan sai ya bani
mamaki sosai. Kusan awar mu ɗaya da rabi a gidan sannan muka fito, daga nan sai
airport.
Farin cikine mara misali ya kamani lokacin da nai tozali da Ummu,
ashe tare da ita zamu tafi harda takawa, ta rungumeni a jikinta tana yaba yanda nai
ɓulɓul kamar yanda ta faɗa. Amintacciyar baiwarta nata mana dariya, banga takawa ba
saida zamu shiga jirgi, ‘Masha ALLAH’ na faɗa a raina dan ganin cikakken mutum mai
haiba da kwarjinin mulki, lallai sarauta ba ƙarya bace. Har ƙasa na tsugunna na
gaidashi, ya amsa min da kulawa tare da sakamin albarka.
Sai da suka fara shiga shi da boss da ya riƙema hannu da dogaransa biyu kacal
sannan muma muka shiga. Da yake waje na musamman aka bamu sai naji kamar mu kaɗaine
a jirgin, acan ƙasan raina cike nake da ɗoki da fatan dacewa akan abinda zamuje
dominsa.
____________________________________

Gaba ɗaya hankalin Momy a tashe yake da duk wanda yake cikin gidan
Dad a yau, ba komaine sanadin wannan tashin hankalinba kuwa sai zuwan ɗan fir'auna
gidan da far1ar safiya ya tafi da Shahudah. Kusan ƙarfe takwas yazo gidan,
lokacinma babu wanda ya tashi sai ma'aikatan gidan kawai, daga Shahudah harsu Momyn
ma babu wanda nake tunanin yayi sallar asubahi, sabuwar mai aikinsu na tsaka da
sharar falonsu ya shigo. Da ɓacin rai ta kallesa zatai magana, sai dai yanayinsa ya
sakata haɗiye abinta a cikin rai ta koma zare idanu. Ya zabga mata harara cike da
gadararsa yace, “K rakani ɗakin matata”. Cikin ƙarfin hali tace, “Matarka kuma?
Anan gidan?”. yay mata kallon tara saura kwata ya ɗauke kansa, “Baki da labari
kenan?”. Kafin ta bashi amsa sai ga Aamilah da muryar ɗan fir'auna ta sakata tashi
a firgice, dan sam shi baya magana a hankali.
Idanu ta zaro zata koma da gudu ya daka mata tsawa, “K dan tsohonki dawo
nan!!”. Bata da ikon jayayya, dan haka ta dawo ta tsaya tana rurrufe ƙirji da hannu
kasancewar rigar barcin jikinta bata kirki baceba. Yi yay kamar bai fahimci abinda
takeba, yace, “Ina matata?”. “T.. Tan tana barci a ciki”. tai maganar tana nuna
masa saman benen. “Kaini”. Yay maganar yana yin gaba. Binsa ta farayi a baya tana
hararsa, tai wata zabura daya juyo, baibi takanta ba yace, “Wuce gaba”. Kamar zata
fasa ihu haka taji, amma dole ta haɗiye abinta a rai tai masa rakkiya har ƙofar
ɗakin Shahudah.
Tana kwance ɗai-ɗai tana barcinta ac na kaɗata suka shiga. “Tasheta” ya faɗa
yana kallon Aamilah. Jikinta na rawa ta shiga tashin Shahudah, daƙyar ta tashi,
tana ganin Aamilah ta hau hararta, sai dai ganin ɗan fir'auna tsaye ya sakata
watsakkewa.
“Sannu da tashi ƴar hutu. Ke shirya mata kayanta”. Idanu Aamilah ta zaro,
ya daka mata wata mahaukaciyar tsawa da ta sakata fashewa da kuka tana bashi
haƙuri, a take ta buɗe Wadrobe ɗin Shahudah ta fara zuba kayanta a cikin a kwati,
shikuma yahau tattare kayan kwalliyar saman mirror. Ita dai Shahudah tayi mutuwar
zaune, dan binsu kawai take da kallo ko sau ɗaya ta kasa magana.
Momy da mai aikinsu taje ta kirawo tana fitowa falo ɗan-fir'auna na fitowa
daga ɗakin Shahudah riƙe da hannunta tana tirjewa da kuka tana kiran Dady da Momy,
Aamilah na biye dasu da akwati. “Kai wai wane irin mahaikacine ne? Gidan ubanwa
zaka kaimin yarinya? Sakarta dan ubanka!!”. Ko kallon Momy baiyiba yaja Shahudah
ƙeeyyy!! sukai waje, Aamilah na biye dasu tana hawaye. Binsu momy tayi takai hannu
zata riƙe Shahudah ya zaro bindiga a ƙugunsa, “Wlhy kina taɓata saina tsiyayar miki
da jinin hannu, inbanda rashin mutunci da raini, an ɗauramin aure amma kun maidani
ɗan iska kamar wani gwauro, ke lokacin da aka ɗaura aurenki da surukina ba ranar
aka kaiki kika tareba ya kwashi gararsa, saini dan an maidani wani sha ka tafi sai
safa da marwa nake tsakanin titi da gida, to daga yau ta ƙare, kwa biyota da sauran
kayanta, ga oga can an basa matarsa shi yanata watayawa ƙilama mun samu ɗa, amma ni
ambarni hagaga da baki kamar tsohon amalen raƙumi. Motsoow, aikin banza kawai. Ke
muje ƴar farata yau nima ango nake mai lokaci”.
Sunaji suna gani ɗan-fir'auna ya tura Shahudah a motar da yazo da ita bus, ya
shige abinsa ya tada yabar anguwar. Kuka momy da Aamilah keyi kamar ransu zai fita,
Salman yana daga jikin Window ɗakinsa duk abinda akeyi yana gani amma yaƙi fitowa,
saida ɗan fir'auna ya wuce da Shahudah sannan ya fito yana murza ido da tambayar
abinda ya faru shi a dole barci yake baiji komaiba.
Kuku ne ya masa bayani dan sun ɗauka da gasken barcin yake bai jiba.

Daƙyar momy ta iya samun Number Dad ta faɗa masa komai, hankalinsa yay
masifar tashi, yay kiran commissioner of police dan yayi report amma bai ɗauka ba,
ya kira I.G shima wayarsa switch up, duk ya rikice ya rasa wazai kira, daga ƙarshe
ya yanke shawarar kiran Jay, amma shima wayar tasa dai switch up. Tashin hankali
kenan wanda ba'a saka masa rana, karan farko da yaji nadamar barin Qaseem barin
ƙasarsa. Haka yayta bige-bige waya bai dace ba, wasu aƙi ɗauka, wasu suƙi shiga.
kansa gaba ɗaya ya kulle ya kasa fahimtar wannan ruɗaɗɗen al'amari, yama za'ai ace
shi kamarsa yana kiran wayoyin waɗanan mutanen amma babu mai wucewa, wasu kuma
sunƙi su ɗaga masa ma. ‘Mi hakan ke nufi?’.
Muma wannan amsar muke buƙatar ji Dad😥.

__________________________________

Mun sauka Saudia lafiya, inda akazo da zuƙa-zuƙan motoci akai mana tarba
ta girmamawa, Aunty Mahfuzah da mijinta da ƴaƴansu biyu. Nazata wannan karonma
gidansu Aunty Mahfuzah zamuje, sai naga an kaimu wani wajen daban.
Ba boss ba koni a ƙage nake da son ganin Umm-Anum wlhy, sai dai shi jarumin
naku ya dake kamar babu komai a ransa. Ni kaina ta yadda yake komai a sanyaye na
fahimci komai ya kwance masa, hatta da wanka da ƙyar na samu yayi sannan mukaci
abinci, kasancewarsa maicin abinci sosai sai gashi ya tsakura kaɗan ya tashi, nata
marairaice masa da lallashi akan ya ƙara amma ya girgiza min kai, daga ƙarshe ma
sai ya tashi ya shige bedroom ɗin ya barni a falon.
Raina gaba ɗaya sai ya sake jagulewa, na ajiye abincin nima na tashi na bisa
ciki, kwance na iskesa saman gado a rigingine yana kallon p.o.p ɗin da aka ƙawata
saman ɗakin dashi, ga fitulu masu ƙyau da ɗaukar hankaki, na daɗe tsaye a bakin
ƙofa amma baiko motsaba balle nasan yasan na shigo, kaina na girgiza inaji a raina
dolene nayi wani abu koyaya na dawo da kuzarinsa koda ba dukaba, dukda nasan ba
sauƙi zan samoba haka na cije na ƙarisa gaban gadon, kwanciya nayi a gefensa na
ɗaura kaina saman ƙirjinsa ina kallonsa, abin mamaki baiko motsaba fa, yatsana
manuniya na ɗaura saman lips ɗinsa na fara zagayawa a hankali. Ya sauke nannauyar
ajiyar zuciya da buɗe lumsassun idanunsa a kaina, gira na ɗage masa, na ɗan juya
ƙwayoyin idona alamar “Yaya dai?”.
Murmushi ya ɗanyi da gyara kwanciya ya juyo sosai muna fuskantar juna,
hannunsa ya ɗaura saman gefen fuskata muna kallon juna cikin ido, sai dai yaƙi cewa
komai, sai busamin numfashinsa kawai yake saman fuska kamar yanda nima nawa ke
sauka akan nasa.
“In baka wani labari”. Guntun murmushi ya ɗanyi, ya buɗe baki daƙyar yace,
“A kanki kawai”. Murmushi nayi har haƙwarana na fitowa, na ɗaura hannuna nima akan
fuskarsa ina ɗan murza gashin sajensa daya fito kaɗan da ƴan yatsun. “Bara na baka
labarin farkon girkina”. Kansa ya ɗagamin yana lumshe ido. Na gyara kwanciyata
sosai ina sake shigewa jikinsa, “Innata zataje anguwa sai ta barmin girki tace nayi
kafin ta dawo, amma komai zan zuba na tabatar Innar Firdausi na a wajen, dan bata
taɓa barina nayi girki ba, sai dai idan tanayi ta dinga sani na zuba abu harmu
gama. Ni sarkin rawan kai inason na bama Inna mamaki tasan na iya girkin nima, sai
kawai nahau hidima batare danama innar firdausi magana ba, da yake ita kuma tana
ɗaki sai batasan hidimar da nake ba. Shinkafa da wake aka barmin nayi, kasan mina
fara zubawa bayan na saka kayan miya, mai?”. Kansa ya girgizamin alamar a'a. Nai
ƴar dariya, “Karfa kace zakamin dariya to”. “Ɗan kaɗan zanyi” ya faɗa a hankali.
“Tab to na fasa gaskiya”. Da sauri yace, “Yi haƙuri wasa nake bazanyiba”. “Tam, in
gaya maka na tsaida ruwan abinci bayan nayi komai dai-dai ɓangaren soya mai, kayan
miya, da tsaida ruwa, na kawo magi da gishiri duk na zuba, saida ya tafasa saina
zuba shinkafa...” cikin ɗan zaro ido yace, “Waken fa?”. Ƙaramar dariya nayi, “Yo
waken sai da shinkafar tai rabin dahuwa sannan na wankesa na zuba na saka albasa na
rufe inata murmushi ni na kammala komai, har wani imagine yanda Inna da Babana zasu
kwashi girki nake a raina.
Kasa daurewa Jawaad yayi ya shiga ƙyalƙyala dariya sosai, dukda naji daɗin
ganin yana dariya saina saka hannuna kan bakinsa zan rufe ina kumbura fuska ni a
dole naji haushi. Hannuna ya riƙe zai janye naƙi, nai azamar hayewa kansa na danne
da ƙyau yanda bazai cireba, “Kafayi alƙawarin bazakayi dariya ba?”. Dagewa yay ya
cijemin hannun, nai saurin janyewa ina fashe masa da kukan taɓara duk da dai da
gaske naji zafin. “Ni ALLAH saina rama” na faɗa ina kai bakina kan hannunsa daya
riƙe ɗayan hannuna. Take muka fara kokawa, shi yana dariya ni kuma ina saina rama
da kukan da babu hawaye. Ba'akai dogon zangoba lissafin ya canja salo, duk kuma
yanda naso ƙwatar kaina a hannunsa sai hakan ta gagara, yayi yanda yakeso daga
ƙarshe ya koma lallashina kamar yanda ya saba.
“Wai har yanzu fushin ne?”. Ya faɗa yana jawoni jikinsa. Sake tura baki
nayi, nace, “Kuma indai mukaje gidan Umm-Anum bazan dawo nanba”. “Sai mu kwana tare
a can ai”. Yay maganar yana ɗauremin gashi na daya gama gyarawa. Ɗagowa nai na
kallesa, nace, “Dawa ɗin?”. Ya nuna kansa da ɗan yatsa. “Tab kayi ƙato da yawa
bazaka kwanar mata a gida ba”. Ranƙwashi ya bani a kai mai zafi. Na dafe wajen
idanuna na cika da ƙwalla. Ɗauke kansa yay tamkar baiganiba.

★★★★★★

Duk yanda muka kai da zumuɗin ganin Umm-Anum a ranar dai bata yuwu
ba, sai washe gari wajen goma na safe. Ni da Ummu da amintacciyar baiwarta muka
farayin gaba akan su boss sai daga baya zasu biyomu shi da Takawa da mijin aunty
Mahfuzah. Duk da bansan yaya manufar tsarin nasu yakeba hakan yamun.
Tarbar da akai mana kawai zai tabbatar maka da ansan da zuwanmu, sai dai
bawai da tunanin har dani ba, dan bayan Umm-Anum sun rungume juna da Ummu irin
gaisuwar larabawa tana ɗagowa ta ganni, baki ta saki da mamaki, “Amaryan kwana
takwas ne a saudia kuma?”. Kaina a ƙasa nidai ina murmushi ban iya bata amsaba, sai
Ummu ce ta bata amsa ƙasa-ƙasa, bansan mitace mataba naga dai sunyi dariya.
Yanda Anum ta rikice da ihun murna zai tabbatar maka itama batayi tunanin
dani a zuwan ba, ta rasa inda zata saka ranta dan daɗi, tabi dukta katantaneni da
labarai, ganin banga Anuwar ba nace mata, “Ina Yah Anuwar?”. Ɗakinsa ta nuna da
hannu. “Tunda muka dawo ai baida lafiya, dafa jiya zai kona ƙasarku wai yayi
mantuwa, shinefa Umm-Anum tace masa ai Ummu ma zatazo ya faɗa abinda ya manta ɗin
tazo masa da shi. Ni nasan bawani mantuwa da yayi, so yake yaje ya ƙara ganin
mijinki kawai Umm-Anum ta ɓata masa shiri, shinefa yaketa fushi da kowa a gidan tun
jiya, yau ko makaranta yaƙi yaje”. Tausayinsane ya kamani, sai dai bancema Anum
komaiba game da zuwan boss.
Munyi kusan zaman awa biyu sannan Anuwar ya fito, wani irin taka burki yayi
yana waro idanu waje. muryarsa har rawa take wajen faɗin, “Wai dama dake akazo?” ya
ƙare maganar yana murza idanunsa da hannu. Murmushi nai masa hakama Ummu, cikin
tsokana tace, “Dama kana gidan amma ko tarba babu Anuwar?”. Kafin yace wani abu
Umm-Anum tace, “Fushi yake dan ya shirya ƙaryan komawa ƙasanku na ganosa na hana”.
Kallonsa mukai da ga ni har Ummu, ya wani ɓata fuska da narketa a shagwaɓe. Dariya
nayi kaɗan ina ɗauke kaina. Ummu tace, “Kaga manta dasu Anuwar kaji, lokacin da
zamu rama yana zuwa ai”. “Yauwa Ummuna” ya faɗa yana zama kusa da ita ya gaisheta.
Nima gaishesa nayi. Cikin hikima yaketa tambayata ina mijina? Da tsokana nikuma
nake bashi amsar yana can mun baro. Da nace haka sai ya ɓata fuska ya ɗauke kai.
Har raina sai nakejin tausayinsa, dan bamusan mi ALLAH ya ɓoyeba a al'amarin nasu
da har suke masifar ƙulafucin juna irin haka.
Bayan sallar zuhur Abbun su Anum ɗin ya dawo gidan, sai da ya zauna suka
gaisa da Ummu sannan yake sanar da Umm-Anum gasu takawa nan a falon baƙi a shirya
musu abinci akai. Da yake dama tasan da zuwan nasu saita hau shirya komai yanda ya
dace, sai dai kallo guda zakai mata ka fahimci kamar a rikice take. Daga ƙarshe ma
saita zauna tana mai dafe kanta. Aunty Mahfuzah ce tai azamar ƙarisawa gareta ta
dafa ta, “Umm-Anum lafiya kuwa?. Kanta ta nuna mata da hannu alamar yana mata ciwo,
Ummu da Aunty Mahfuzah suka kalli juna dansu su Ummu sun sanar dasu komai dama.
Addu'a Aunty Mahfuzah tai mata sannan taɗanji ya sassauta mata, amma data miƙe sai
tace jiri take gani.
Anuwar ya fita salla bai dawoba, Anum da Bilkisu kuma suna ɗaki suma tunda
suka idar da sallar basu fitoba, dan haka basu san wainar da ake toyawaba su.

A falon baƙi Takawa ne zaune da mijin Aunty Mahfuzah abokinsa, sai


Jawaad dake zaune a wani irin yanayi mai wahalar fassara, idanunsa sun kaɗa sunyi
jazur, ya jingina da kujera saboda jin yanda ƙirjinsa ke wani irin mahaukacin bugu,
ga jinin jikinsa sai tsitstsinkewa yake. Takawa ya kafesa da idanu na wasu ƴan
mintuna cike da nazari kafin ya sauke gajeren numfashi yana maida dubansa ga Abu-
Siddiq, shima ɗin dai kallon Jay yakeyi tun ɗazun cike da nazari, dan tun haɗuwarsu
da Abunsu Anuwar gaba ɗaya yanayin Jawaad ɗin ya sake canjawa, shi kansa Abbun su
Anuwar ɗin rikicewa yay jikinsa ya hau rawa saboda ganin tsananin kamar Jawaad da
Anuwar ɗin, farine kawai Anuwar ya ɗara Jawaad. Duk da daman Takawa yay masa
bayanin komai tunma kan suzo ƙasar hakan bai hanashi shiga gigita da ruɗani ba, sai
dai baice komaiba bayan gaisuwar daya zauna sukayi, shine ya fita ya sanarma Umm-
Anum ɗin da zuwansu shi kuma ya sake dawowa.
Sam ya kasa haƙurin daina kallon Jawaad dake kwance cikin kujera idanunsa
rufe, ba barci yakeba amma sam tunaninsa da hankalinsa basa tare da duniyar mutane,
da za'a tambayesa wanene shi a wannan lokacin, bazai iya bada amsar komaiba. A
wannan yanayin Aunty Mahfuzah da ma'aikatan gidan suka shigo suka shirya abinci
gasu takawa.
Duk yanda sukaso Jawaad yaci abinci sam ya kasa, daga ƙarshema yace musu
kansa ke masa ciwo, kuma yana ganin jiri, wannan magana ta sake rikita Abbun su
Anuwar, dan a irin halin daya baro Umm-Anum kenan itama a cikin gida. Shine yayma
Jawaad addu'a, kafin ya sakashi dole cin abincin, gurasa ɗaya yaci da ƙyar ya tsame
hannunsa. basu sake tilasta masaba dan sun fahimci bayama cikin hayyacinsa
kamar.............✍

Ku lallaɓa da wannan, yau na tashi banajin garin dai-dai nima😩

Gaskiya a rage sakama Jay ido da yawafa ƴan Wattpad😂, dan kunfi kowa iya
gulmar Jay na kula, su ƴan Telegram ƴan blue House ne, Yah Qaseem ɗinmu sukafi sama
ido da Aunty Hudah🙄😣.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu
suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;


ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;


SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;


BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;


KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;


WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k
ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai
buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[1/14, 5:27 PM] HASNA ✍🏻
: Typing
ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 49
..............Kamar yanda Umm-Anum ta saba duk sanda takawa yazo Saudia ya kanzo
har gidan su gaisa, domin dai a halin da take ciki su kaɗai takema kallon ƴan uwa,
su kaɗai ta sani a yanzu sai mijinta sai ƴaƴan guda biyu, ta mance ita wacece? Ƴar
wacece? Daga ina take? Daga ina ta fito?. Wani lokaci hikimar UBANGIJI kan sakata
kawo wannan tunanin a zuciyarta, musamman ida tunaninta ya karaɗe ko ina a cikin
duniya ta ga babu wanda ta sani sai ƴan Masarautar gagara badau, sai mijinta da
danginsa dake anan, hakan kan ɗaure mata kai, sai dai duk yanda taso ta furta da
baki kota tambaya bata iyawa. Idan hakan ta kasance takan zauna tasha kukanta ta
share hawayenta.
Yauma kamar yanda ta saba ɗin haka ta ƙimtsa ta fito cikin shirin zuwa gaida
takawa, idan da Ummu yazo sukanje tare, idan kuma da amaryarsa ne tare itama suke
zuwa, sai idan shi kaɗaine yazo sai taje tare da Anum su gaida shi ko Aunty
Mahfuzah idan ta shigo. Yau kam sai suka ɗunguma gaba ɗaya, ita, Anum, Ummu,
Bilkisu, sai Anuwar daya shigo gidan babu jimawa shima, dan tunda ya fita salla sai
yanzu yake dawowa saboda baisan da Takawa sukazo ba balle yay tunanin harda Jawaad.
Sallama sukai a ƙofar ɗakin aka amsa musu da ga ciki, tare da basu izinin shiga,
jikin Umm-Anum sai tsuma yake tanata dai ƙoƙarin dannewa da karanto addu'a a
zuciyarta. Anum da Bilkisu ne suka fara shiga, sai Ummu sai Umm-Anum, sai Anuwar a
ƙarshe. Jay na kwance a kujera idanunsa a lumshe tamkar mai barci, sai dai
shigowarsu falon ya saka ƙirjinsa wani irin mahaukacin bugu irin wanda tunda yake a
rayuwarsa zai iya rantsuwa bai taɓa jiba, ya buɗe idanunsa a hankali zuciyarsa na
wani irin masifaffen tsitstsinkewa. Akan Bilkisu da Anum da suka zauna gefen Abbun
su Anuwar ya fara saukewa, ya maida kan Ummu da itama ta zauna a kujerar da takawa
yake zaune, sai Anuwar dake tsaye tamkar gunki idanu a ware yana kallon Jawaad, da
alama dai yayi sumar tsayene na bazata. Ya maida kallonsa ga dattijuwar mace data
juya masa baya suna gaisawa da takawa, tana sanye da baƙar abaya ta naɗe kanta irin
naɗin larabawa. Jiyay gaba ɗaya jinin jikinsa na wani bada zuuuu!! Zuuuu! Zuuuu,
bazai iya daurewa har saita juyo garesa ba, a matuƙar ɗokance yake da son ganinta
duk da cike yake da fargaba da tsoron kar hasashensu ya zama kuskurene kuma ba
itaɗin bace ba. Ya miƙe a hankali ƙafafunsa na harharɗewa, yayinda bugun zuciyarsa
da fitar numfarfashisa ke fita a matuƙar guje. Miƙewarsa tai daidai da miƙewar Umm-
Anum itama fuskarta ɗauke da murmushi sun gama gaisawa da takawa tanason komawa
kusa da mijinta ta zauna sai a ɗora firar, dauriya kawai take itama tana danne
halin da take ciki. Lokaci ɗaya sukai tsaiii! Suna kallon juna, kallo mai wahalar
fassara ga ma'abocin yinsa da wanda ke kallo, kallo mai saka razani da firgici da
ban mamaki, kallo mai ɗarsa tausayi ga duk wanda idanunsa zai iya sauka a kansu
shima.
Ƙafafun Jawaad sun kasa ɗaukar gangar jikinsa, Mahaifiya ta wuce gaban wasa, jini
ba ƙarya bane musamman irin na uwa da ƴaƴa, ko shekara dubu yay baigantaba saiya
gane, shekarun data barsa bazai yuwu ya iya manta fuskartaba musamman da ya zam
yana kallonta a hoto a koda yaushe, manyanta kawai da ƙiba da haske ta ƙara na
alamun girma da jin daɗi. Ƙasa ya zube bisa gwiwoyinsa jikinsa na rawa, kansa na
wani irin Masifaffen sara masa tamkar zai tsage gida biyu, cikin rawar harshe da
kwararowar hawaye bisa kumatunsa yace, “Ummuna!”.
Umm-Anum dake tsaye cikin mawuyacin hali da ruɗanin zuciya da gangar jiki idanunta
kafe akan Jawaad ko ƙyaftawa batayi ta ɗaga hannu da ƙyar tana mai nuna shi da
yatsanta manuniya jikinta na wani irin rawa, mai kama da Anuwar ɗinta! Wanene shi?
Da ga ina yake? Ya akai kamaninsa da Anuwar ɗinta?! Mutum ɗaya tasan duk duniya
yana kiranta da wannan sunan, sai dai wanene? A ina yake? A yaushe ne kuma?.
Bakinta rawa yake amma ta gaza furta komai, sai tai luuuu baya zata faɗi.
Wani irin wawan miƙewa Jawaad yayi ya tarota jikinsa, dai dai da zaburowar Anuwar
shima yana ƙoƙarin tarota, sai kawai hanunsu ya haɗe waje guda suka tallafota a
tare......
Zumbur suma ƴan falon duk suka miƙe tsaye, banda Takawa kawai da ya dake abinsa duk
da shima jikin nasa duk yay saƙwat. Da ga can Anum ta ƙwala kiran sunanta cikin
kukan da takeyi tun farkon durƙushewar Jay a gaban Umm-Anum. Bilkisu ma hawayen
takeyi.
Abin tausayi da tashin hankali daga Jawaad har Anuwar kuka suke suna faman girgiza
Umm-Anum da kiranta, Jay na faɗin, “Ummuna! Ummuna Please, Ummuna ki buɗe idanunki
ki ganni, nine Jay-p ɗinku ke da Abbah, karkice ba hakaba dan ALLAH, dan ALLAH
Ummuna zuciyata zata buga ki tashi ki ganni kicemin da gaske kece ba gizo idanuna
keyiba, ba mafarkin dana sabayi bane, ba tunain danake dulmiyawa bane, ki
tabbatarmin a zahirance kece tare dani Ummuna, kitashi kiga Jay-p ɗinku yazam Jay-p
ɗin gaskiya, Dan ALLAH Ummuna karkice baki ganeniba karkice baki sanibaaaaa”. Yaja
(a) ɗin ƙarshe da fashe da wanu irin kuka maiban tausayi da tsuma zuciya yana mai
kife fuskarsa saman tata.
Anuwar shima kukan yake yana faɗin, “Umm-Anum ki tashi da ALLAH, ki tashi ki
faɗamin shiɗin ɗan uwanmu ne da gaske, wlhy inajin ƙaunarsa mai zafi a raina irin
wadda ban taɓama wani mahaluki irinta ba, jinake tamkar zan iya rasa numfashina
sabida shi, Umm-Anum dan ALLAH kice shiɗin jininmu ne Ummu”.
Duk wanda yace baiyi hawayeba a parlorn nan ƙarya yake, hatta da Takawa saida yasa
handkherchief ya tsane hawaye, Abbun su Anuwar ya saka gefen mayafinsa da larabawa
ke sakawa saman kai ya share nasa hawayen, kafin ya taka a hankali shima ya durƙusa
a gabansu ya ɗago kawunansu ya rungume a ƙirjinsa yana shafa kansu, fuskarsa ɗauke
daɗan murmushi ga ƙwalla da suka sake cika idanunsa, a hankali yakai bakinsa saman
kan Jawaad ya sumbata, kafin ya maida akan Anuwar shima ya sumbata. Cikin harshen
turanci ya shiga lallashinsu da kalamai masu sanyi. Suna cikin haka Ambulance ɗin
da Abbu-Siddiq ya kira asibiti ta iso, mata ma'aikatan asibitine suka shigo su
huɗu, da taimakon su Jawaad da har yanzu jikinsa ke a sanyaye suka kamata aka ɗaura
a gadon gungura mara lafiya, ma'aikatan asibitinne suka fita da ita, Jawaad da
Anuwar suka take musu baya suma. Bilkisu da Anum ma miƙewa sukai da sauri sukabi
bayansu. Duk miƙewa suma sukai domin binsu, amma sai Abbun Anuwar yace Abu-Siddiq
ya maida su Takawa masauki su huta. Noƙewa Ummu tayi akan ita dai zatabi bayansu
itama. Takawa baice komaiba suka fito gaba ɗaya, su Jawaad harsun wuce, su Bilkisu
ma basu iskesu ba suna tsaye suna jiran fitowarsu Ummu, Ummu, Aunty Mahfuzah,
Bilkisu, Anum suka shiga mota ɗaya suka bisu. Abbunsu Anuwar kuma dasu Takawa suma
suka tafi a mota guda.

Da taimakon su Jay da suma suke a motar Ambulance ɗin aka fidda Umm-Anum zuwa cikin
asibitin, abinka da inda kasan darajar ɗan adam, dan danan likitoci sukai mata caa
da taimakon gaggawa, yayinda Anuwar da Jawaad ke tsaye aƙofar ɗakin da aka shiga da
ita kowanne cike da tsantsar damuwa, kaɗan-kaɗan saisu ɗago su kalli juna, sai dai
kowanne ya kasa magana ma ɗan uwansa ko sau ɗaya, dan harsunansu sun musu nauyi,
burinsu kawai suga farfaɗowar rabin numfashinsu masoyiyar zuciyarsu mahaifiyarsu
abin alfaharin kowa da tinƙaho.
A wannan halin su Bilkisu suka ƙariso suka iskesu, da ga ita har Anum idanunsu
sunyi luhu-luhu saboda kuka, Ummu duk tana riƙe da hannayensu. Idanu kawai Jay ya
zuba musu amma bai iya cewa komaiba, sai Anuwar ne ya bama Ummu amsar tambayar da
tayi akan ina Umm-Anum ɗin. Isowar su Abbu suma ya saka aka basu wajen zama, domin
su Abbu sun kasance zuri'a sananniya mai daraja a ƙasar saudia musamman cikin
birnin makka, nagartattun malamaine hafizan Al-Qur'ani mai girma, sunada manyan
makarantu na addini da cibiyoyin magunan musulunci da suke badawa da sunansu ya
zagaye lungu da saƙon birnin na makka da kewaye da saudia ke alfahari dasu a
ɓangarori da dama na ƙasar.
Anuwar da Jawaad dai sun kasa zama, sai da Abbu ya kamosu duk ya zaunar tare da
zama tsakkiyarsu. Jawaad shi kaɗai yasan irin matsanancin ciwon da kansa ke masa,
amma ya daure ya jure, sai dai ta jijiyar kansa data mimmiƙene kawai zaka iya
fahimtar yana cikin mawuyacin hali. Hannu Abbu ya ɗaura akan Jawaad ɗin daya
kwantar da bayansa jikin kujera ya lumshe idanunsa, hakan ya saka shi buɗe idanun
da suke jajur ainun, addu'a ya fara karantowa yana tofa masa a kan nasa, Jay ya
maida idanunsa ya lumshe jirin da yakeji na ƙara ƙarfi a cikin idanunsa. Luuuu ya
kwanto jikin Abbu alamar shima dai koya suman kokuma wani abun dai daban, saurin
ɗagosa Abbu yay yana girgizashi, amma ina numfashinsa yay ɗaf daga ƙirjinsa. Saurin
miƙewa Anuwar yay shima jiki na rawa, hakanne ya jawo hankalin sauran suka fahimci
abinda ke faruwa. Bilkisu ta cusa kanta cikin cinyoyinta ta sake fashewa da kuka
mai tsuma rai. Hakama Anum ƙanƙame Ummu tai ta fashe da kuka tana faɗin, “Ummu
shima yayi kamar na Umm-Anum”. Rungumesu Ummu tayi a jikinta daga ita har Bilkisu
itama tana ƙoƙarin haɗiye hawayenta, ‘wannan wane irin tashin hankaline haka?’. Ta
faɗa a ranta cike da tausayin wannan ahali.
A take shima Jawaad aka ɗaukesa zuwa ɗakin kusa da Umm-Anum aka shiga bashi
taimakon gaggawa domin ceto numfashinsa.
★★★★★★
Saida sukai zaman awanni biyu cikin kuka da tashin hankaki sannan suka sami labarin
farfaɗowar su, atake duk murmushi ya suɓuce musu, Bily ta saka gyalenta itama tana
share hawaye kamar yanda Anum keta faman yi. Ba'a basu damar shiga ba dan duk ance
suna buƙatar samun hutu musamman ma Umm-Anum da jikinta ya manyanta.
Da wannan albishir ɗin suka sami ƙwarin gwiwar tafiya yin sallar la'asar da
lokacinta yayi, kowa ya shiga miƙama UBANGIJIN al'arshi kukansa dan shine masanin
duk wani sirri dake a binne tare da rahama ga bayin da aka zalunta kuma suka jurema
jarabawar rayuwa batare da nuna ƙosawarsu ba. Sosai yin sallar ya ɗan basu ƙwarin
gwiwa suka dawo asibitin, Abbu ya roƙa takawa akan suje su huta haka nan tunda ance
sun farfaɗo ai. Daƙyar Ummu ta yarda, Bilkisu kam ƙasa tai da kai tana hawaye
alamar batason tafiya. Takawa yay murmushi da yima Ummu alamar a barta anan ɗin da
ido.
Hakan kuwa akayi, bayan sun shiga sun duba su Jawaad da Umm-Anum suka tafi akabar
Bilkisu da Anum da Anuwar anan, sai Aunty Mahfuzah, takawa kuma da Ummu da
Amintacciyar baiwar Ummu da Abu-Siddiq suka tafi, sai Anuwar da Abbu suma suna nan.
Suma dai bayan wucewar su takawan duk sai suka shiga suka dubasu suka sake fitowa
suka zauna zaman jiran farkawarsu da musu addu'oi.
Kasa haƙuri Abbun su Anuwar yayi yaɗan farama Bilkisu wasu tambayiyi game da Jawaad
da ita kanta, danshi tabbas yana kallon wasu abubuwan na Bilkisu masu mugun
kamanceceniya da Umm-Anum, tafiya, murmushi dama abubuwa da dama tun a wancan zuwan
nata, hakan sai yasa kansa ya ƙara kullewa ya shiga tambayarta ko auren zuminci
akai musu ita da Jawaad?. kanta a ƙasa ta bashi amsa da “A'a”. Ya tisa (a'a) ɗin
nan ta bilkisu a ransa yafi sau dubu, dan shidai gaskiya bai yardaba akwai abinda
ita Bilkisun bata saniba maybe, musamman yanda yake mata tambayoyin da amsoshin da
take bashi. Anuwar dai da Anum da Aunty Mahfuzah na binsu da kallone da saurarensu.
A haka lokacin sallar magriba yayi itama suka tashi suka gabarta, sun dawone suka
iske Jawaad ya tashi, Abbu ne yace Bilkisu kawai ce zata shiga, badan Anuwar da
Anum sunso ba suka haƙura.

Tunda na shigo ɗakin idanuna a kansa suke, shiko nasa a lumshe tamkar mai barci har
yanzun, yana kwance ne, amma yanzu an ɗago gadon sama ta wajen kanshi yanda
kwanciyar ta bada style kamar yana a zaune. Na cigaba da takawa a hankali na ƙarasa
garesa, Zama nayi dai-dai saitin fuskarsa tare da ranƙwafawa na sumbaci goshinsa,
hawayen da suka cikamin ido suka ziraro suka ɗiga akan fuskarsa. Buɗe idanun yayi a
hankali tare da riƙo hannuna cikin nashi, kallon cikin ido mukaima juna, wasu
hawayen suka sake silalo mani na tausayinsa, abinda ban taɓa gani daga garesaba sai
yau, (kuka) Boss ne gwanin dauriya da shanye abu yay kuka, kai mahaifiya dabance a
rayuwar kowanne ɗan adam, mahaifiya tafi gaban wasa, mahaifiya mutum mafi daraja
sama ga komai ga ƴaƴa. Na ayyana a raina ina matsawa jikinsa na kwantar da kaina a
ƙirjinsa ina fashewa da kuka, dan nima haka kawai sai naji ƙaunar tawa mahaifiyar
da kewarta, Innata gatana, innata abar alfaharina da tinƙahona harma da taƙama a
dukkan daƙiƙa ta rayuwata.
Jawaad da shima wasu zafafan hawayen da babu zato suka silalo masa ya ɗaura duka
hannayensa saman bayanta ya rungumeta a jikinsa. Sunkai tsahon lokaci Bilkisu na
kukan da shashsheka ta kasa ɓoyesa, Jawaad na kukan zuci da hawaye masu zafi da
raɗaɗi. Buɗe ƙofar da akaine ya saka Bilkisu saurin ɗagowa dan ta zata su Abbu ne,
shima babu musu ya saketa ta miƙe yana share hawayensa, itama nata ta shiga sharewa
da bakin mayafin jallabiyar. Nurse ɗin daya shigo ya nema afuwarsu, dan ya jima
yana sallama da knocking babu amsa, hakanne ya sakashi shigowa direct, dan tun daga
can waje ta cctv'n da suke amfani dashi na ganin duk wanda ke a sashen da suke kula
da shi ya gano ruwan da suka sakama Jay ya ƙare har jininsa ya fara zuƙa yana
komawa cikin robar ruwan, shikam sam baima luraba saida Nurse ɗin ya kama hannunsa
yana cirewa sannan suka gani shi da Bilkisu. Idanu taɗan ware waje na alamar
mamaki, shikam sai ya lumshe nasa idanun ya maida bayansa ya jinginar kamar yanda
yake da.
Nurse ya kammala komai sannan ya fita su Abbu suka shigo duba Jawaad ɗin. Sannu
sukaita jera masa da addu'oi, shi kuma yana amsa musu da kai dan harshensa ya masa
nauyi sosai har yanzu baijin zai iya furta wata kalma ga kowa idan ba Umm-Anun ba.
A rikice Nurse ɗin dake tare da Umm-Anun ta shigo tana sanar musu ta farka itama
amma bata cikin hayyacinta.
Rige-rigen fita aka dingayi a tsakaninsu, dan hatta da Jay ba'a barsa a baya ba
shima. Tashin hankali kenan, yanda Nurse kusan biyar ke riƙe da Umm-Anum zai baka
matuƙar tausayi, a take duk suka rufu a kanta banda Abbu dake tsaye kawai yana
kallon yanayin nata cike da nazari, ajiyar zuciya ya sauke kafin yayma Nurse ɗin
Umarni akan su sallamesu zasu koma gidan ciwon nata addu'a yake buƙata. Basu musaba
dan sunsan shiɗin babban likitane mai bada magungunan musulunci wanda akema ɗakko
marasa lafiya daga wata ƙasa mai nisa a kawo garesa balle matarsa kuma.
A take aka shirya musu maidata gida. Hankalin Jawaad yay matuƙar sake tashi ganin
mahaifiyarsa ta koma cikin asalin halin hauka kamar yanda tabar gida a wancan
lokacin, su kansu su Anuwar ɗin hankalinsu a tashe yake dan basu taɓa ganin Ummunsu
a wannan irin halinba, sundai san tanada wani rashin lafiya da takan fita
hayyacinta lokaci-lokaci amma basu taɓa sanin dalilin motsawar ciwon nataba suma,
da kuma Abbu ya dage kanta saita dawo normal kamilar mace. Anuwar yasha tambayar
Abbu amma bai taɓa sanar masa komaiba sai yace lokaci na zuwa da zai sani.
Da isarsu gida Abu-Siddiq da Abbu suka rufi kan Umm-Anum da karatun Al-Qur'ani mai
tsarki, hakanne ya ja hankali su Jawaad suma duk sai suka ɗaura al'awa suka zauna
sunayi su duka har Bilkisu da Anum, kai harma da ama'aikatan gidan da Aunty
Mahfuzah da yaranta itama dukda ƙanana ne ba'a barsu a baya ba. A hankali Umm-Anum
ta fara lafawa daga bige-bigen da takeyi, ta buɗe idanunta dake jajur tamkar
garwashin wutane a cikinsu tana binsu da kallo. Ba ƙaramin tsorata idanunta suka
basu ba, amma hakan baisa sun dakataba suka cigaba, maidawa tai ta sake lumshewa
tare da kwanciya jikinta na wani irin masifar rawa, sai kuma ta fashe da
matsanancin kuka. Turaren magani Abbu ya tashi ya kunna, hayaƙi ya fara fita yana
baje ɗakin. Wani irin gunjin kuka ta fara maiban tsoro tana magana cikin muryar da
dagaji kasan ba tata bace. “Ku daina ƙonamu, dan ko zaku shekara dubu kuna ƙonamu
bazamu bartaba, zamu gama jiyyane a jikinta batare da mun bar aikinmu ba,
alƙawarine rubutacce zamu kasance da ita har ƙarshen rayuwarta, dan haka kuma bar
wahalar da kanku babu inda zamuje, bazamu taɓa saɓama shugabanmu ba har abada dan
shima bai taɓa saɓa manaba bisa umarninmu...!!”. Sam su Abbu basu sauraresuba suka
cigaba da abinda sukeyi, hakama su Anuwar basu fasa nasu karatunba, yayinda Abbu ya
cigaba da zuba magani kala-kala na hayaƙi a cikin Burne. Tun suna ihu har suka koma
kuka da magiyar a daina ƙonasu kar'a halakasu suba laifinsu bane sakasu akayi. Zuwa
wani lokaci kuma sai tayi shiru sai uwar zufa take tamkar an jiƙeta da ruwan zafi.
Abbu bai dakata da abinda yakeba har saida yaji ta kirayi sunansa cikin sanyin
murya. Ajiye abinda ke hannunsa yayi ya ƙarasa gareta ya ɗago, faɗawa tai jikinsa
ta fashe da kuka mai ban tausayi. “Abu-Anuwar yau cikin mafarki naga wani abu
maiban mamaki da al'ajabi, naga mai kama da Anuwar wanda tabbas inada alaƙa dashi”.
Tashi Abu-Siddiq yay ya fita dan ya basu waje.
Abbu dake shafa bayan Umm-Anum yana murmushi yace, “Ba mafarki kikeba zahiri ne”.
Zumbur ta miƙe zaune tana kallonsa, sai kuma tai saurin dafe kanta da taji ya sara
mata. Kamata yay ya kwantar yana faɗin, “Kiyi haƙuri ki kwanta ki huta zuwa anjima
ko da safe idan ALLAH ya kaimu sai muyi magana, Alhmdllh nafahimci mun samu wani
haske saɓanin da da bama ki taɓa makamancin wannan maganarba”. Umm-Anum dai batace
komaiba hannunta na dafe da kanta, ahaka barci mai nauyi yay awon gaba da ita,
dukda anata kiraye-kirayen sallar magriba bai hanataba.
Sai da ya tabbatar barcin ya ɗauketa sosai sannan ya fito falo, Bilkisu da Anum
yace su shiga suyi salla a ɗakin dansu dinga kula da ita, shi kuma suka fita tare
da su Abu-Siddiq salla masallaci. Tunda suka fita salla Abbu ya fahimci Jawaad
bayajin daɗi, dan daya kama hannunsa sai yaji zafi alamar zazzaɓi na neman rufesa.
Baice komaiba sukai salla suka zauna har isha'i itama suka gabatar sannan suka koma
gida. Har lokacin Umm-Anum nata barci, su Bilkisu da suma suka idar da salla suna
zaune sun zuba mata idanu cike da damuwa.
Sashin baƙi Abbu yasa aka gyara, aka kaima su Jawaad abincinsu can, Abbu yace
Anuwar yaje ya raka Jawaad itama Bilkisu Anum zata rakota.

____________________________________
★★★★★★★★★★★★★★★★★★★
____________________________________
Duk wani masoyin su Momy hankalinsa a tashe yake akan ɗauke Shahudah da ɗan
fir'auna yayi, abin ɗaure kai da ban mamaki shine duk yanda ƴan sanda suka bazu
nemansa basu samu koda mai kama da shiba, dai-dai da wayarsa an kasa samunta ta
kowanne yanayi, dama ita Shahudah tata wayar na nan bai bari ta ɗauka ba, duk kuma
inda ake tunanin samun ɗan fir'auna anje babu shi babu abokansa.
Hankalin kowa ya ƙara tashi, Momy kuka take kawai tana zazzagama Dad masifa ta waya
akan ya dawo ita tashin hankalin nan yamata yawa, sannan ya saka Qaseem ya taho
shima. Shidai lallashinta kawai yakeyi dan shima hankalin nasa aiba a ƙwance
yakeba, yana matuƙar ƙaunar Shahudah fiye da zaton mai hasashe, shi da yake nesama
dasu ya fisu tashin hankalin. A ranar ya sanarma Qaseem ya shirya ya koma gida zuwa
gobe saboda halin da ake ciki. Qaseem dai ya amsa da “to” dan zuwa yanzun bai iyama
Dad musu akan komai, duk abinda yace yayi shi yakeyi koda bai masaba. Tun a daren
ya fara shirin komawa ƙasarsa ta haihuwa, dan dama hankalinsa bama a kwance yakeba
a China'r saboda wata cuta da aketa raɗe raɗin ta ɓillo a wani yanki na ƙasar chain
mai suna Corona virus, mutane duk a tsorace suke, daƙyar ya iya danne ransa yaje
yayo wata ƴar sayayya da yake buƙata ya dawo hotel ɗin da yake ya kimtsa kayansa,
insha ALLAH jirgin farko na gobe dashi zai tashi zuwa ƙasar Dubai cikin birin Abu-
dabi, daga nan zai hau jirgin da zai sadashi ƙasarsa.
Ɗan-fir'auna ka sakamu a cakwalkwali😣🙄😏😒😠🚶🏻.
______________________________________
((°•°))((•°•))((°•°))(())(())((°•°))((•°•))((°•°))
______________________________________
Iya ƙofar ɗaki Anum ta tsaya tai min saida safe, kaina kawai na iya ɗaga mata
batare da nace komaiba. Ƙofar na tura na shiga da sallama a bakina, falone
madaidaici da aka zuba komai cikinsa, sai ƙamshi mai daɗi ke tashi a ciki. Na sauke
kumburarrun idanuna akan boss dake kwance cikin doguwar kujera idanunsa rufe, nai
masa kusan kallon mintuna biyu kafin na ƙarasa inda yake, durƙusawa nai gaban
kujerar na ɗaura hannuna saman goshinsa, wani irin zafi naji zauu dan haka na
rimtse idanu da sauri. Jin ya ɗaura hannunsa saman nawa na buɗe idonuna, hannunma
akwai zafi shima, a rufe idanunsa suke har yanzu, “Yayanmu baka da lafiya ne?”.
Baice min komaiba sai idanunsa dake jajur ya buɗe yana kallona. Hawaye naji sun
cikamin idanu, yaɗan lumshe nasa idanun ya sake buɗewa a kaina da girgiza min kansa
alamar kar nayi kuka. ban ankaraba naji sun silalo kawai, hannunsa ya ɗaura saman
kumatuna ya shiga sharemin batare da yayi magana ba. Kusan mintuna biyar muna a
haka kafin ya buɗe baki da ƙyar yace, “Kukan ya isa mana, haɗamin ruwa maiɗan zafi
nayi wanka kozanji ƙarfin jikina”. Kaina na jinjina masa sannan na yunƙura na miƙe.
Ƙofar dana gani a falon ya sakani tunanin itace bedroom, can na nufa kaina tsaye,
koda na tura sai naga ƙaramin kicin ne, rufewa nai na nufi ɗayar ƙofar, itakam ina
buɗewa nai tozali da bedroom babba. Numfashi naɗan sauke na shiga, ban wani zauna
ɓata lokacin kalle-kalleba na shiga bathroom ɗin da shima ya kasance babba, komai
tsaf an gyarashi, sai ƙamshin fresheners masu daɗi. Dai-daita ɗumin ruwan nayi
yanda zai masa daɗi sannan na tara masa, komawa falon nayi na taimaka masa ya tashi
zaune, dan da gaske bayajin ƙarfin jikinsa, amma duk da haka yamin nauyi sosai,
haka dai na daure har muka isa bedroom ɗin, taimaka masa nayi ya cire kayan, ya
rage daga shi sai singlet da boxer kawai, a haka na sake taimaka masa zuwa bayin.
Duk yanda naso na zame na barsa yay wankan shi kaɗai bai yarda ba, yace na taimaka
masa jikinsa sam babu wani ƙarfi, gashi yanajin jiri. Dole na daure nai masa yanda
yakeso sannan na sake taimaka masa muka fito, har kayan barci an kawo mana dan haka
na taimaka masa ya kimtsa yasha shayi da magani ya kwanta, bargo naja masa na
rufesa na zauna gefen gadon ina kallonsa, shima dai idanunsa a kaina, bamu jima a
hakaba barci ya kwashesa, ajiyar zuciya na sauke a hankali ina share ƙwallar da
suka cikamin ido, duk wanda ya aikata al'amarin nan yacika baƙin azzalumi mai
busashshiyar zuciya. Nima shayin kawai nasha, na ɗauki abincin na maida sashensu
Umm-Anum sannan na dawo na shiga wankan nima. Gasa jikina nai sosai sannan na ɗauro
alwala na fito, nima nai shirin barcin na haye gadon na kwanta tare da shigewa
jikinsa da har yanzu yake zafi zau. Lumshe idanuna nayi ina sauraren yanda bugun
zuciyarsa ke harbawa, a haka nima barci ɓarawa ya saceni.

WASHE GARI

Bayan mun tashi daga barcin da muka koma na safe wanka mukai, muna cikin tunani da
zullumin kayan da zamu saka saiga sallamar Anuwar, boss ne ya amsa masa tare da
zira jallabiya ya fita falon, babu jimawa sai gashi ya shigo da akwatinmu. Kallonsa
nai da alamar tambaya, sai dai baice komaiba ya ɗora akwatin saman gadon tare da
buɗewa ya ɗauka kayansa nima ya fiddomin nawa. “Kitashi ki shirya suna jiranmu, su
Takawa ma sunzo” yay maganar cikin dasashshiyar muryarsa da tun jiya bata dawo dai-
dai ba. Kaina na ɗaga masa na miƙe.
Tsaf muka fito cikin shiga ta kamala munata zabga ƙamshi, mun iske Anum a fallon su
Umm-Anum zaune ita kaɗai da alama mu take jira, da girmamawa ta gaida Boss daketa
faman kallonta ko ƙyafta ido bayayi. Nima muka gaisa sannan ta sanar mana duk suna
falon baƙi mu ake jira.
Duk suna zaune an baje abinci kala-kala a tsakkiyar falon, yanda muka samu Umm-Anum
zaune cikin kamala ya sakamu sauke ajiyar zuciyar jin daɗi muka bisu ɗai-ɗai muka
gaisar.
Gaba ɗaya hankalin Jay akan Umm--Anum yake, kamar yanda itama nata hankalin na
agaresu shi da Bilkisu, sai dai batace komaiba dan an bari sai anci abinci sannan
ai zama akan hakan. Lafiyayyen breakfast ne da kowa ya tsinci kansa cikin jin daɗin
cinsa, sai dai boss tsakura kawai yakeyi. hakama Umm-Anum bata wani ci sai kallon
Jay take.
Bayan an kammala aka gyara wajen tsaf sannan kowa ya nutsu waje guda..............
✍😓
wayyo idona wayyo yatsuna😢🚶🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[1/16, 1:48 PM] HASNA ✍🏻
: Typing

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 50
.................Shiru kakeji falon ya ɗauka bakaji motsin komai saina ajiyar
zuciyoyi dana AC dake aiki. Sai da Abu-Siddiq yay doguwar addu'a kafin kowa ya sake
maida hankalinsa ga takawa da yay gyaran murya alamar zai fara magana. Wata gyaran
muryar ya sakeyi kafin yay sallama a garesu duk suka amsa, Cikin nutsuwa Takawa ya
sake gyara zamansa.
“Alhamdulillahi ala kulli halin, duk da dai bamu da tabbacin har yanzu Umm-Anum ta
gane Jawaad matsayin jininta ina ganin ya kamata na fara warware abinda mu muka
sani game da ita kafin muji abinda zai fito daga nata bakin yanzun”. Jinjina kai
kowa ya shigayi cikin gamsuwa da jawabinsa.
“Mun tsinci Umm-Anum a wasu shekaru da zan iya ƙiyastasu da kusan shekaru ashirin
da takwas idan ban mantaba, a lokacin nazo gida daga india domin halartar bikin
salla babba kamar yanda na saba a duk shekara, saukar dare nayi a ranar, dan sai
kusan tara na dare ma na iso, amma kamar ko yaushe na iske sarkin mota na jiran
isowata a airport ɗin. A gajiye nake matuƙa gaya dan haka bamu ɗau lokaciba muka
bar airport ɗin, tafiyar mu bata wuci ta mintuna goma ba akan titi sarkin mota yaja
wani wawan birki. Sosai gabana ya faɗi saboda ƙarar da aka ƙwalla mai nuna tabbacin
mun bige wani, daga ni har shi fita mukai cike da tashin hankali. hakama mutane
dake ɗan kai kawo a titin harsun fara taruwa a wajen. Ganin mace ce kuma cikin
shiga ta kamala duk da babu lulluɓi tare da ita sai muka fara bincikar mutane ko
akwai wani nata a wajen?, amma babu wani mai alaƙa da ita. Mun ɗauketa zuwa
asibiti, duk da gajiyar da nake ciki bamu bar asibitinnan ba sai da muka tabbatar
ta samu dukkan kulawar da ake buƙata a daren sannan muka wuce raina duk a dagule. A
dalilin bige baiwar ALLAHr nan gaba ɗaya bikin sallar nan baimin daɗi ba, dan tun
bayan farkowarta daga magagin ciwon bugetan da mukai sai muka fuskanci tanada taɓin
hankali ma, taɓin hankali irin mai ban tashin hankali, dan duk da cikin halin ciwo
da take ƙoƙarinta kawai ta gudu daga asibitin ita dai, dalilin hakan takai har sai
da aka saka mata hand corps a hannu da ƙafa sannan aka samu ɗan kwanciyar hankalin
ta, a hakanma fisge-fisge take ita kawai a barta ta tafi duk ta jima hannayenta
ciwo da ƙarfen ankwa dana gado. Doctor ɗin shine ya faɗamin gaskiya da tabbatar
mana cewar matarnan akwai wani babban al'amari tattare da ita, mizai hana mu haɗata
da malaman musulinci. Wannan shawara tasa itace ta zame mana haske a kanta, sai
kuwa na samu abokina Muftahu akan ya bincika min malamin da zamu kaita wajensa,
shine kawai ya bani shawarar mizai hana mukaita Saudia wajensu Abu-Siddiq. Na amshi
shawarsa da hannu biyu babu ɓata lokaci mukai duk wani ciku-ciku dagyar muka samu
damar fita da ita zuwa nan saudia. A ganin farko dasu Abu-Sufyan sukai mata suka
tabbatar mana akwai sihiri tattare da ita, dan kuwa tunda ta buɗe ido daga barcin
da take dan allurar barci a kai mata tun da ga can kafin mu taho saboda gudun
matsala, sai muka sameta a nutse babu wani bige-bige da takeyi sai dai alamar
rashin lafiya na haukan yana tare da ita, alamun hakan na nufin can ƙasarne ba'ason
ta zauna kenan ko wani abun daban da bamu da ilimi a kansa. Bayanin da mukaima Abu-
Sufyan akanta ne yasa yace mubarta a wajensa na wani lokaci zasu cigaba da kula da
ita. Nai masa godiya sosai bayan kwana biyu na koma india nabar Muftahu anan
saudia. shima kuma bayan wani lokaci saiya koma. A koda yaushe muna magana da Abu-
Sufyan ko Abu-Siddiq akanta da yanayin jikinta, sannan Muftahu nata ƙoƙarin bincike
game da ahalinta acan gida, sai dai babu wani haske da muka samu game da samunsu.
Bayan wani lokaci jikinta yay sauƙi sosai ta koma normal Alhmdllh, sai dai kuma ta
manta komai dangane da kanta, batasan ko itaɗin wacece ba, daga ina ta fito? duk ta
manta har sunanta, wannan shine ya ɗarsa tausayinta a zuciyar Abu-Sufyan yace
shikam zai aureta har ALLAH ya kawo iyakar komai ta gane ahalinta. Tunda yaymin
bayani sai ban musaba, dan uba nike kallonsa bawai yayan aboki kawai ba, na kuma
tabbata shine kawai zai iya riƙe amanar baiwar ALLAHr da bata da kowa tunda hatta
kanta da sunanta tama manta, ya bada gudunmawa sosai gameda jiyyar mahaifina shima,
har kawo yanzu kuma yana badawa a dukkanin al'amurana dana zuri'ata, babu abinda
zance a garesu sai addu'ar fatan gamawa da wannan rayuwar lafiya su samu sakamakon
aljanna a ranar sakamako”.
Tunda Takawa ya fara magana hawaye kawai kowa ke faman sharewa, Abbu yace, “Tabbas
duk abinda ya faɗa hakane, abinda kawai ya manta bai faɗaba shine ciki dake tare da
ita, sun kawota da ciki kwantacce da bamusan adadin wataninsa ba, kamar yanda ya
nuna, dan sai da muka dage da addu'oi da magani matuƙa sannan ya fara motsi alamar
abinda ke cikin yana raye, da alama dai akwai sharrin jinnu a al'amarin kokuma wata
hikimar UBANGIJI daya ɓoye game da cikin wadda zuwa yanzu munga ƙalilan daga ciki
shiyyasa ya ɓuya a jikinta, tashin da cikin yayi sai yazam watanninsa ya koma baya,
dan saiya koma wata uku, sai da tai wata shida sannan ta haihu Namiji, shine yaci
suna Muhammad Anuwar gashi nan, bayan haihuwarsa ne mukai aure da ita ta haifi Anum
kuma, ga tanan tana da shekaru ashirin da uku, daga ita dai bata sakeba har zuwa
yanzun”.
Cikin rawar jiki Anuwar ke kallon Jawaad, sai kuma ya kalli Abbu ya kalli Umm-Anum
da ke zaune shiru ta zabga tagumi tana hawaye, dan abubuwa da dama ne keta dawo
mata cikin rai tun a daren jiya, hatta da sunanta ta manta sai a daren jiya ta tuna
shi. Hannunta dake rawa ta miƙama Jay dake kallonta ko ƙyafta idanunsa bayayi, a
hankali ya miƙe ƙafafunsa tamkar an dokesu ya nufota, ta riƙe hannunsa ta zaunar da
shi kusa da ita tare da rungumesa ta fashe da kuka, shima Jawaad hawayen yakeyi. A
take falon ya ɗauki sabon koke-koke har saida Abbu ya fara musu nasiha akan hakan
sannan suka tsagaita. Anuwar ya taso shima ya zauna kusa da Ummu, kafin ya tashi ya
koma jikin Jay yana sharɓar kukansa, Jawaad ya rungumesa da ƙyau yana murmushin
farin cikin samun ƙanne. Tasowa itama Anum tayi tazo ta zauna ƙasa ta ɗaura kanta
saman ƙafar Jawaad, ya sake murmushi da shafa kanta yana lumshe idanunsa da kai
hannu ya share mata hawaye itama. Wata irin ƙaunarsu mai tsananice ke ratsa dukkan
ɓargonsa da jini, ji yake a duk duniya yau babu kamarsa a cikin masu nasara, jinsa
yake tamkarma su kaɗaine a cikin duniyar babu wani mahaluki mai numfashi da ya rage
bayansu ɗin, wani sanyi mai sanyaya kuzari na shiga cikin tsokar jikinsa tana ratsa
dukkan ɓargonsa da jijiya.
Cikin dasashshiyar murya Umm-Anum tace, “Tabbas niɗin na taɓa aure, bankuma taɓa
tuna hakanba sai a daren jiya, na auri wanda yake matsayin yayana a gidanmu dukda
ba iyayenmu ɗaya ba, matar babanmu ce da ya aura bayan rasuwar innarmu ce
mahaifiyarsa, itama kuma mijinta ya rasune, shine iyayenmu sukai aure, suka kuma
haɗemu suka riƙe tamkar tare suka haifemu, Auren soyayya mukayi da Abdul-aziz,
shiɗin mutumne mai himma wajen neman nakansa, sannan mutumne mara hayaniya da
damuwa da gudun ƙyale-ƙyalen duniya, mutum ne ma'abocin son noma da kiwo, mai
tsananin son ƴan uwa da zuminci, shine auta a gidansu kaf, shi kaɗai kuma mama
maryam ta haifa a gidan, baida wa baida ƙani dan haka yay mana gata sosai ni da
ƙannena lokacin da mahaifiyarsa ta dawo aure gidanmu. Bayan aurenmu mun samu
jarabawar rashin samun haihuwa na tsahon wasu shekaru harma dana abubuwan more
rayuwa, kafin na fara haihuwar kuma yaran su rasu, sai daga baya harma mun fidda
rai da wata haihuwar sannan ALLAH ya azurtamu da samunsa (ta nuna Jawaad) lokacin
da muka samesa Abdu-aziz ya bunƙasa, dan harkokinsa na noma da kiwo sun kaisa har
ƙasar turai dalilin zaman mutunci da wasu turawa da sukai aikin dam ɗin ƙauyen
garinsu, abinda kawai zan iya tunawa bayan wannan game da rayuwata shine, sunana
BILKEESU, sai mahaifina, sai ƙannena uku mata, Mariya, Rahmah, Wasila, sai Mama
maryam, saiko shi dana bari, sai Abbansa dana tabbatar ya rasu, wannan shine kaɗai
abinda zan iya tunawa game dani da rayuwata ta baya kafin gushewar komai”. Ta ƙare
maganar hawaye na ziraro mata.
Jawaad da shima ke hawayen ya saka hannu ya share mata yana girgiza mata kai alamar
ta bari, muryarsa a ɗashe yace, “Na godema ALLAH da yasa kika tunani Ummuna, na
kwana da tsananin fargabar kar kice baki tunani ba koma baki sanni ba gaba ɗaya, da
hakan ta kasance na tabbata sai dai ku binne gawata a yau Ummuna, na godema ALLAH
da yasa kina raye, na godema ALLAH da ya ƙaddara sake haɗuwarmu a duniyar nan, na
godema ALLAH daya jarabceni da son wadda ta silarta yau nake a jikinki Ummuna, (yay
maganar yana nuna Bilkisu) na godema ALLAH daya haɗa dangantakarta da zuri'ar
Takawa har nima nakai ga zuwa garesu, su ɗin shugabannine da adalcinsu yakai
kowanne yanki, kowacce ƙabila, suyi fatan zamowa masu mulkinsu Ummuna, mutanen nan
uku haskene babba a gareni da suka haskamin hanyata zuwa gareki”.
Share masa hawayen shima tayi tana miƙama Bilkisu dake kuka hannu alamar itama
tazo, da ƙyar BILKEESU ta miƙe zuwa garesu tana haɗa hanya, Umm-Anum ta sakata a
jikinta tana maijin ƙaunarta har ƙarƙashin ruhinta, “Ɗiyata ashe ƙaunar da nake
miki tun ganinki na farko bata wasa bace, ALLAH yay miki albarka kinji, ALLAH ya
ɗaukaka rayuwarki ya saka mata albarka ya baibaiyeki da alkairi da rahamarsa mai
tarin yawa”. Gaba ɗaya falon aka amsa da amin.
Ummu dake murmushi tace, “Haka rayuwa take, ƙanƙanin abu sai yazama silar warware
babba, kunga dai yanda aka ɗauki tsahon shekaru wajen addu'oi da neman ahalin Umm-
Anum, amma sai gashi cikin sauƙi Wallet ta zama silar komai......” Ta shiga bama su
Umm-Anum labarin komai game da haɗuwar Bilkisu da su Safah a Ladies mirror, da
dagewar Safah akan saita tafi da Wallet ɗin bilkisu masarauta, har silar komawarta
hannunsu...
Sosai al'ajabi ya kama su Umm-Anum sukaita sake jinjina al'amarin da girmama
hukuncin UBANGIJI mai shirya yanda yaso a lokacin da yaso ga wanda yaso cikin
hikimarsa.
Duk godiya suka shiga sake jera ma su takawa da addu'oin fatan alkairi, dasu Abbu
ma kansu suma har saida takawa da Abbu sukace ya isa haka sannan. Akwai sauran
magana sosai a bakin Takawa dan ya fahimci akwai wasu abubuwan da yawa dake a ɓoye
wanda Umm-Anum bata iya tunawa ba, shima kansa Jawaad dai akwai magana a bakinsa
musamman game da haukar mahaifiyarsa da abubuwa ma da dama, sai dai yayi shiru ya
barma ransa, so yake ya samu nutsuwar zama sake nazari da fashin baƙi akan komai,
su kuma keɓe da matarsa su tattauna kozai ƙara samun haske daga gareta dan kowa da
irin baiwarsa. To yanda duk tunaninsu yake hakama na Abbu da Abu-Siddiq yake, su
kuma sunason su keɓe ne da Jawaad sumasa tambayoyi game da family ɗinsa, dan sunji
Umm-Anum bata tambayi komaiba akan komai ma, alamomi da yawa kuma sun nuna akwai
abinda ke binne, bazasu fahimci hakanba sai sun sami sanin ainahin tarihin komai
tun daga tushe sannan.

Kiran sallar zuhur ne ya tashesu daga wannan zama, matan suka shige cikin gida
sukuma mazan suka fita massallaci.
Bayan an idar suka dawo akaci abincin rana, Jawaad dai tsakura yay tayi yanzun ma,
baici na kirki ba, hakama Bilkisu, Umm-Anum da take jinta sakayau yau tanata lura
dasu sai dai batace komaiba har aka kammala aka tashi.
Takawa, Abbu, Abu-Siddiq suka fice masaukin su takawa dan su masa rakkiya yaje ya
huta. Bilkisu kuma Umm-Anum ta tsareta ta kwanta barci, acewarta yanayin bily ya
nuna barci takeji, kasa mata musu tayi ta kwanta, itako ta ɗaura kan bily saman
cinyarta tana shafa mata kai har barcin mai nauyi kuwa yay awan gaba da Bilkisun,
Anum dake ta tsegumi Umm-Anum tabar yayinta itama tazo ta raɓa bayan Bilkisun ta
kwanta da yake a ɗakin Umm-Anum ɗinne. Ummu da Aunty Mahfuzah kuwa sun tafi can
gidan aunty Mahfuzah ɗin suma.
Anuwar da Jawaad kuwa suna can sashen baƙi suma, Anuwar ya tsare Jay akan ya bashi
labarin Abban su, sai shagwaɓa yake masa. Jawaad dake kwance cikin doguwar kujera
yay murmushi idanunsa akan Anuwar dake zaune a ƙasan darduma jikin kujerar da yake
a kwance hannunsu sarƙe dana juna. Cikin muryarsa dake a sanyaye yace, “Dear nima
bansan Abba ba sosai, abubuwan da zan iya tunawa game da shi basu da yawa, dan
banfi shekara bakwai ba ya rasu, sai dai kakanrmu mama maryam bata gusaba sai da ta
maidamin tarihinsa tamkar karatu, dan sai da na haddacesa a cikin kaina tsaf, daga
ni har kai da shi muke tsananin kama, musamman ma kai daka biyo har hasken sa,
abubuwa ƙalilanne muka ɗakko Ummuna. Inada videos da dama da akayi lokacin da yake
shugabancin ƙasarmu, ta hakane nakejin kamar na rayu da shi rayuwa mai
tsaho...........”
Da sauri Anuwar ya ƙara ƙanƙame hannun Jawaad dake a cikin nashi yana faɗin, “Suna
tare da kai yanzu?”. Murmushi Jawaad yayi ya kai hannu ya shafi kan Anuwar, “Da
ganinka ɗan karan gaggawa ne da kai da rashin haƙuri yaron nan”. Yanda yay maganar
da jan hancin Anuwar a ƙarshe ya saka Anuwar ɗin ƙyalƙyalewa da dariya, shima Jay
murmushin sa ya sake faɗaɗawa yana maijin daɗin ganin Anuwar ɗin cikin nishaɗi.
Wayarsa ya ɗauka ya lalubo folder da ta kasance duk hotunan Umm-Anum ne da Abban su
sai shi. Miƙama Anuwar yay, jikinsa har ɓari yake wajen son amsar wayar abin
tausayi, kallo ya shigayi yana hawaye sosai, hakan yasa Jawaad lumshe idonsa yana
haɗiye abinda ya tarar masa a ƙirji na tausayinsu musamman ma Anuwar ɗin. Saurin
buɗe idanu Jay yayi danjin yanda Anuwar ya fashe da kuka, ya kafesa da ido shima
yana ƙoƙarin danne tasa zuciyar, “Haba my sweet Darling kamar ba namiji ba, kukan
ya isa haka kaji lilly na”. Yay maganar da tashi zaune ya rungume Anuwar ɗin yana
mai shafa masa baya, har saida yaji yayi shiru ya koma sauke ajiyar zuciya sannan
ya barsa. Labarin ahalinsu da mahaifinsu ya cigaba da bashi cikin kulawa, wani
gurin Anuwar yay kuka wani gurin yay dariya, haka suka kasance har akai kiran
sallar la'asar, wanka Jawaad ya sakeyi da gaggawa suka fita massallaci.
Umm-Anum ma ta tada su Bilkisu sukayi tasu, bayan sun idarne ta saka mai aikinsu ta
kawo abinci, zaunar da Bilkisu tayi tana faɗin, “Zauna na baki abincin nan da
kaina, kwana biyu da zuwanku duk kun fara ramewa ke da mijin naki saboda rashin cin
abinci, ina dalili”. Murmushi nayi cike dajin kunyarta, yanda take ƙoƙarin yin
hausa sai abin keban dariya dan hausar kamar bata bahaushiya ba, wani wajenma
kakarewa take ta kasa faɗa.
Duk yanda nakejin kunyarta haka na ringa amsar abincin da take bani da hannunta,
sallamar su boss ta sakamu maida hankalinmu garesu, idanunsa a kaina dan haka nai
azamar ɗauke nawa na maida ƙasa. “Kaima zo ka zauna” Umm-Anum ta faɗa idanunta akan
Jawaad dake kallonsu cike da sha'awa dajin daɗi. Hannunsa ta riƙo ta zaunar ɗayan
gefenta, ta ɗiba abincin takai bakinsa, “Haa!” ta faɗa kamar yanda akema yara.
Ƙwallane suka cika idanun Jawaad ya buɗe bakinsa a hankali ta zuba masa, taunawa ya
shigayi yana kallon yanda take sakama Bilkisu itama, gabansu Anuwar yazo ya durƙusa
shima ya buɗe baki wai a basa. Umm-Anum ta zuba masa tare da dungure kansa. Anum ma
zuwa tai ta tsugunna tana faɗin, “ALLAH nima sai an bani to, anma manta dani kamar
banice autar ba”. Sosai abin ya bama Jawaad nishaɗi, su Bilkisu suka shiga yima
Anum dariyar tsokana.
Hannunsa Jay ya ɗauraye, shima ya ɗiba ya kai bakin Umm-Anum, amsa tai tana
murmushi ta shafa kansa da ƙoƙarin haɗiye hawayen da suke neman taho mata, murmushi
Jay yayi ya ɗiba ya bama Anuwar shima, sannan ya bama Bilkisu da kunya ta kusan
halakawa, Anum itace ƙarshe. Daka gansu kasan suna cikin farin ciki mai tsanani.
Haka suka ƙarasa wannan yini tare, har zuwa dare dan Abbu yau a gidan Uwargidansa
ma yake ba nanba, hakan ne ya ƙara bama Umm-Anum damar sakewa da ƴaƴanta har dare
ya farayi, daƙyar ta daure tace suje su kwanta haka nan gobe idan ALLAH ya kaimuma
ranace ai. Da wannan kowa ya nufi makwancinsa badan sun gaji da kasancewa tare ba.

Sai da muka gama shirin barci muka kwanta, ina jikinsa a lafe kamar wata mage yana
shafa bayana a hankali, fitar numfashinmu yana dai-daitane da sautin bugun
zuciyarmu, “Miema kinyi barci?” ya faɗa a hankali cikin kunne na. Kaina na girgiza
masa da ɗago fuskata dake cikin ƙirjinsa na kalli fuskarsa, shima kallona yakeyi.
Murmushi mukaima juna, ya ɗan sumbaci goshina kafin ya sake maida idanunsa cikin
nawa. Maida nawa nai na lumshe dan nakasa jurar cigaba da kallon cikin idanun nasa.
Baice komaiba sai sake turani da yay jikinsa ya rungume da ƙyau. A haka barci yay
awon gaba damu.
★★★★★★★
Mun cigaba da kasancewa a cikin Saudia tare dasu Umm-Anum cike da tsaftatacciyar
soyayya da tarin ƙauna mai daraja daga garesu, tattalinmu take tamkar wasu ƙananun
yara ni da boss, yayinda a koda yaushe ƙannensa ke nane da shi, yanayin waya sosai
dasu Oga Hafiz musamman akan aikin da a yanzu mukasa gaba na ƴan fyaɗe, a yanzu
haka dai su Jabeer suna ƙoƙarin miƙa wasu samari kusan goma sha uku kotu akan case
ɗin fyaɗen, sannan sunce sun samu case huɗu masu kamanceceniya da nasu Amina. Duk
da muna nan saudia muma aikin mukeyi musamman ma boss, danni wataranma A wajen Umm-
Anum nake yini komu tafi makarantarta. Har gidan Uwargidanta an kaimu, abin ya
birgeni sosai yanda aka tarbemu tamkar ba kishiyoyi ba, a raina nace ‘kaga inda ake
kishin ilimi, ba irin na ƴan ƙasarmu ba na hauka’.
Randa muka cika kwanaki bakwai a saudiya boss ya fara samun kira daga wajen aiki,
dan mun wuce ƙa'idar kwanakin da aka bamu na hutu, duk yanda yake da son aiki da
ƙwazo saina fahimci bayason komawa yanzun, nima dai bason komawar nakeba sam, amma
yaya zamuyi hakan tilasne a garemu kodan ɗunbin ayyukan da muka baro.
A ranar yayma Umm-Anum magana akan binmu, sai dai abin mamaki da al'ajabi a take ta
nuna ɓacin ranta akan bazataje ba, shiru mukai kawai duk muna kallonta, yayinda
fuskar Boss da Anuwar ta nuna tsantsar ɓacin rai akan hakan. Kafin suce wani abu
akan hakan Abbu yaja hannunsu suka fice daga gidanma gaba ɗaya.
Wannan al'amari ya tsaya min a zuciya, dan yinin ranar gaba ɗaya wuni Umm-Anum tai
cikin ɓacin rai, yayinda na yini nikuma cikin nazarin komai da fashin baƙi a kai.
★•°•★°•°★•°•★°•°★•°•★
A ɓangare su Jawaad suna fita daga nan wucewa Abbu yay dasu masaukin takawa,
tattaunawa suka shigayi game da abubuwa masu dama, Abbu yace, “kuyi haƙuri kubar
ɓacin rai kunji, itama ba laifinta bane, babu yanda za'ai taƙi son zuwa ƙasarta
kodan shekarun data ɗauka bata cikinta, al'amarin bai baku mamakiba yanda har yanzu
bata iya tambayar kowa daga ahalin nata ba, tunfa washe garin zuwanku har yanzu
bamu sake zaman tattauna komaiba, tama ƙi ƙara nuna tana buƙatar jin komai, hatta
da yanda ka rayuwu bayan barinta gida bata tambayeka ba Jawaad. Wannan babban
al'amarine daya dace ace an zauna anyi dogon nazari a kansa. Shi sihiri a jikin ɗan
adam abune mai wahalar yakicewa, musamman irin nata da ba'asan dalilinsa ba ma da
sarƙaƙiyar sa, shifa mai sihiri baya gajiyawa da ƙoƙarin ɗaura wani akan wani, dan
ya riga yayi imani da yin wannan shirkar itace ƙarfin ikonsa, har yanzu akwai
sihiri tattare da mahaifiyarku, wanda inaji a raina akwai wani abu da aka binne
wanda saimun tonosane komai dake jikinta zai iya warwarewa harmu fuskanci matsalar
gaba ɗaya, bakuma wai dan addu'oin da muke basa ƙarɓuwa bane, ita rahamar UBANGIJI
da kariyarsa bata taɓa gushewa ga wanda ya dogara da shi kuma yayi imani ya riƙe
gaskiya, gaskiyar ɗan adam bata taɓa ƙarewa sai dai ace ƙaryar wane ta ƙare, dan
haka mucigaba da bin komai mataki-mataki insha ALLAHU komai zai zama labari ne,
Jawaad idan babu damuwa ka bamu haske dangane da family ɗinku ko zamu samu wani
haske”.
Duk sun gamsu da maganar Abbu, dan haka Jay ya shiga basu tarihin rayuwar
mahaifinsa da Umm-Anum kamar yanda kakarsa mama maryam ta shaida masa komai bata
ɓoye masa ba. Ya cigaba da faɗin, “Ban taɓa zargin kowa a zuri'ata game da iyayena
ba, dan babu wani alamun cutarwa dana taɓaji ya shiga tsakaninsu da mahaifina harya
bar duniya, sai dai maganar gaskiya lalurar hauka da Ummuna ta gamu da shi a ranar
rasuwarsa abin tambaya ce, ada ban taɓa ɗaukar hakan komaiba sai kwanannan da
matata tai wata magana data kasa barin raina, na cewar a al'amarin Ummuna akwai
alamomin sihiri, dan mutuwar Abba bai kai ace ta kasa jure ƙaddara ba har ta kaita
da ciwon hauka, ciwo ma irin wanda mutum baison zaman gida, bayan duk musulmi yasan
mutuwa wajibine ga mai rai. Abinda kuma naji daga gareku a yau da wanda ya faru
ranar ya tabbatar min akwai abinda bamu saniba dake a ɓoye tabbas”.
Abbu ne ya sauke ajiyar zuciya yana gyara zamansa, yace, “Tabbas kamar yanda ka
faɗa Muhammad akwai ababen tambaya masu yawan gaske akan al'amarin, ko sunanta sai
a jiya na taɓaji, kai tsaye bamu da damar zarigin kowa akan wannan al'amarin,
musamman idan mukai dubu da marigayi yayi shugabanci na ƙasa, ƙasarma babba irin
taku, bazai yuwu ace baida maƙiyaba koda kuwa suna a kusa da shine. Sihiri
gaskiyane, hakama addu'a waraka ce, sai dai wani lokacin sai kaga kamar ka ɗauki
lokaci kana addu'ar babu biyan buƙata, ba haka bane, UBANGIJI maijin kukanmune a
koda yaushe, mai kuma magance mana damuwarmu ne a koda yaushe, wani lokacin ita
addu'a idan kayita takan jinkirta da ga abinda ka roƙo a kansa, saita zama kariyane
ga wani al'amarinka ɓoyayye da kai kanka baka san da shi ba, mahaifiyarku ta jima
cikin wani hali na jarabawa, mun kuma ɗauki lokaci muna gayama UBANGIJI, bamu
taɓajin mun ƙosa ba, domin mun tabbatar shi kaɗaine mai badawa, yana jinmu, kuma
yana ganinmu, yana kuma sane damu, jinkirtawar warwarewar komai ba yana nufin bai
karɓi kukanmu ba. a yanda kuma nakeji a raina addu'armu ta kasance da kai, kai
kanka, dan duk waɗanda suka iya tauyeta kaima abune mai sauƙi su ɓaddaka, inaga
damuwa akan saita biku ba shine ya kamata ba, bincike akan ainahin miya faru shine
ya dace domin mu samu bakin zaren, dan ko Anuwar bai kamata ya biku ba”.
Kallon Abbu Anuwar yayi cikin tsagwaron tashin hankali, kafin yace wani abu Takawa
yace, “Wannan tunanin shine a raina nima Abu-Sufyan, Anuwar kayi haƙuri kaji, indai
ƙasarmu ce zakaje ka rayu har saika gaji ma, amma ba a irin wannan lokacin ya dace
ba, dan abubuwa da yawan gaske na zuwarmin a zuciya game da al'amarin nan, sai dai
banason furta komai nafison matsayin Jawaad na jami'in tsaro shi yay wannan tunani,
zuwan Umm-Anum da Anuwar ba shine abu mai muhimmanci ba a yanzu ƙwarai da gaske,
dan komai ma zai iya faruwa inhar azzaluman da suka ƙulla al'amarin suna tare dasu
ne, kai koma nesa da su suke suna bibiyar al'amarin komai dan nima nayi makamancin
wannan rayuwar nasan sarƙaƙiyar cikinta, amma kai Jawaad minene a ranka?”.
Zama Jawaad ya gyara cike da kaifin basirar da ALLAH ya azurtashi da ita shima
yace, “Na gamsu da duk abinda kuka faɗa, dan nima a kwanakin nan sune suka zama
abin nazarina, rashin tambaya ta komai da Ummuna batai ba yafi komai tsayawa a
raina sosai, ni a yanzu shirina na farko shine lallaɓata naji waɗanda sukai rayuwa
dasu kamar ma'aikatan gidan da sauransu”.
“Tunani mai ƙyau” cewar Takawa da Abu-Siddiq. Jawaad ya cigaba da faɗin, “Sai
abokai makusanta da Abbah ya rayu da su kafin shigarsa siyasa da hawansa mulki, abu
na uku ne bamu da dama a kansa, dan a wajen Ummuna ne kawai zamu iya jin wasu
sirrika game da rayuwar Abba da ƴan uwansa a lokacin da yake mulki, dan haka wannan
na ajiyesa gefe zanyi anfani da waɗancan damar guda biyu mugani ko za'a dace, amma
nima na gamsu da basai sun bimu ɗinba kam yanzun”.
“ALLAH yay maka albarka” cewar Abbu yana dafa kafaɗar Jawaad dake a kusa da shi. A
tare suka amsa da amin. Abbu ya cigaba da faɗin, “Nima nanda sati guda zan biyo
bayanku dan inason ganawa da Abba (Alhaji Babba). Kai Jawaad ya jinjina masa yana
ɗan murmushi da faɗin, “ALLAH ya tabbatar Abbu”. Da Amin duk suka amsa..
Akan wannan shawarar taron ya tsashi, shi dai Anuwar badan yasoba ya haƙura akan
binsu Jawaad, dan yay masifar ƙwallafa ransa da zumuɗin son ganin ahalinsu.
★★★★★★★★
Cikin hikima Abbu ya samo sunayen ma'aikatan da su Umm-Anum sukai rayuwa dasu a
gidan gwamnati da kafin hakan, harma da sunayen abokan Abban Jawaad ɗin data iya
tunawa da ƙyar.
Sai kuma ta nema tada hankalinta akan komawar su Jawaad ɗin, ta kafe akan ita
bazata barsu su koma ko inaba sunzo kenan. Duk yanda Jawaad dake cikin damuwa shima
yake ƙoƙarin mata bayani akan aikinsu da buƙatarsu da akeyi taƙi fahimta, tamaƙi
sauraren komai, saima ta saka masa kuka daga ƙarshe. Wannan abu ya sake tada
hankalin Jawaad sosai, dama dauriya kawai yakeyi. Da ƙyar aka shawo kanta da
lallashi akan Jawaad da Bilkisu zasuje su ajiye aikinsu ne su dawo nan da zama gaba
ɗaya wajenta.
Wannan batu ya sakata yarda, amma sunsha gargaɗi akan karsu daɗe basu dawo ba, dan
da farko ma catai Jawaad yaje shi kaɗai yabar bilkisu ita anan, sai da Abbu ya sake
wata sabuwar dabarar ya lallaɓata sannan tadai barsu suje ɗin, sukuma dawo akan
lokaci kamar yanda ta faɗa, inba hakaba zata aika a ɗakkosu koda basu gama
shiryawaba.
Da wannan yarjejeniya daba tabbatacciya ba muka baro ƙasar saudia cike da kewa ni
da boss. su Ummu kam can muka barosu dansu sati biyu zasuyi.
Saukar yamma mukayi ƙasarmu ta haihuwa, inda muka iske Sadiq yazo tarbarmu, dan
shikaɗai yasan da dawowar tamu, dama tunda muka tafi boss bai yarda munyi waya da
kowaba bayan su oga Aliyu, su Ummah duk yaƙi yarda yay waya da su, dan baiso suji
komai da wuri harsu kasa daurewa su sanarma Alhaji babba, a yanzunma da muka dawo
bazai faɗa musu komaiba gudun matsala.............✍

Asha sauran weekend lafiya🤒😣🚶🏻🚴🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[1/17, 7:26 PM] HASNA✍🏻: Amina Wada:


ƘWAI cikin ƘAYA!! - 51 - Wattpad

Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta
muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine
mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo
wa...

*_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_*

*_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_*

*_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_*

*_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer


ta fannnin larabci?_*

*ALBISHIRINKU KANAWA*

*_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato


RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA
COMPUTER INSTITUTE(RACI)_*
_Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma
cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_

*ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don
baku darussa har cikin gida*

*sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)*

*kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya*

08033990209

*_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌🏽👌
🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽

..................Gidan duk ya ajiye ƙananun ƙura, duk da ko'ina a rufe yake, haka
na daure naɗan gyara ɗakinsa dan mu samu inda zamu kwanta, kafin a kira sallar
magriba na kammala, shikam wanka ma yayi ya fita tun fara aikin nawa. Bai dawo
gidanba har saida akai sallar isha'i, kusan tara sai gashi ya dawo mana da abinda
zamuci. Gaba ɗaya banajin daɗin yanayinsa, ya koma min Boss ɗin dana sani a office
mara walwala da yawan magana, komai nake sai dai yayta bina da ido kawai, abincinma
da ƙyar na samu yaɗan ci yace ya ishesa, nima cire hannuna nai a ciki na ɗauke
kaina gefe. “Miye hakan?”. Ya faɗa muryarsa can ƙasan maƙoshi. Ƙoƙarin miƙewa nai
tsaye nace, “Na ƙoshi nima...” kafinma na gama rufe bakina naji caraf ya cafko
hannuna ya maidoni ya zaunar, kallonsa nai ina kumbura fuska, ya zabgamin harara
tamakar idanunsa zasu faɗo ƙasa, “Ina wasa da ke ko?”. Ƙasa nai da kaina dan bazan
juri kallon nasaba, “ALLAH nima na ƙoshi to”. Banza yaymin bai tanka ba, ya ɗebo ya
kawo bakina, zan ɗauke kaina yay saurin faɗin, “Kinsan ALLAH idan baki shiga
hankalinki ba sai na sauya miki kamanin wannan fuskar taki, malama haa”. Idanuna
cike da ƙwala na buɗe bakin, ya ko zubamin yana sake zabgamin harara da yin ƙwafa,
inaji ina gani yaymin ɗurar dole, shiko yaƙi ya ci, sai yogurt yaɗan sha, hakanne
yasa naɗan samu kwanciyar hankali. Kasancewar a gajiye muke ga mai gayya mai aikin
baya tare da walwala, gashi zamu koma aiki gobe idan ALLAH ya kaimu sai mukai
kwanciyarmu da wuri.

WASHE GARI

Tun kiran sallar farko na tashi, cikin sanɗa na fita daga ɗakin nasa,
kasancewar barcin da muka kwanta da wuri sai na tashi jikina babu nauyi sosai, da
wannan damar na fara rage aiki. Koda ya fito zai tafi massallaci ya ga ina aikin
gyaran babban falo baice dani komaiba ya fice abinsa, ajiyewa nai nima na koma ɗaki
nai salla, ina idarwa ban hutaba na sake fitowa na cigaba, ana idar da salla shima
bayan wasu ƴan mintuna sai gashi ya dawo, bayan mun gaisa shima sai ya cire
jallabiyar jikinsa ya shiga tayani aikin. Duk da na roƙesa ya bari zan ƙarasa tunda
na kusa bai saurareni ba, sai da yaga ya rage bedroom ɗina kawai sannan ya barni na
ƙarasa.
Ƙurar dana gani tasa nake sharo har ƙarƙashin gado kamar yanda nayi a
ɗakinsa da ƙarƙashin kujerun falo ma, abu na sharo a ƙarƙashin gadon, wanda ya
sakani dakatawa da sharan nasaka hannu na ida jawosa dan naga minene, wallet ce ƴar
karama dan bata kai girman normal wallet dana sani ba, kamar zan buɗe sai kuma na
ajiye da tunanin ko tashice, saman mirror na ɗaurata na cigaba da sharan harna
kammala komai, ganin lokaci yaja na shiga bayi dan yin wanka sauri-sauri, ban wani
ɓata lokaciba na fito.

Idanuna ne suka sake sauka akan wallet ɗin nan, duk yanda naso na share a yanzun
sai na kasa hakan, na matsa gaban mirror ɗin ina goge fuskata da ƙaramin towel dake
a hannuna da hannun haggu, na damar kuma sai na fara ƙoƙarin buɗe wallet ɗin, ɗan
ƙaramin hoton dana fara cin karo da shine ya sakani shiga mamaki, na fara fiddo
abubuwan cikin wallet ɗin gaba ɗaya, ƙirjina sai wani irin mahaukacin bugawa ya
keyi, banma san lokacin dana saki towel ɗin hannun nawa ba jiki na rawa, harda zufa
ta fara tararmin a goshi, nagama zazzage komai a ciki, abubuwane masu muhimmanci da
daraja dana san maisu bazai taɓa sakaci dasu ba da har zan gansu anan, to wama ya
kawosu? Ni dai babu wanda ya taɓa zuwamin nan gidan a kaf mutanen gidan balle nace
a mistake wani yazo da su. A fili nace, “To kodai boss ne ya kawo?”. Wannan tambaya
na yitane badan zuciyata ta gamsu da ita ba, Duk da sallamarsa da naji a bayana ban
iya na waiga ba.
Ƙarasowa yay yana ɓata fuska ganin bama ta shirya ba, ya ajiye ƙaramin tiren
da ya ɗoro musu tea a saman table kafin ya ƙaraso inda take yana jan tsaki. Ganin
ko motsi bataiba har yanzu tanata juya abu a hannu sai kansa ya sake ɗaurewa, “Wai
kina kallon agogo kuwa Miemaa!?”. Ya faɗa a ƙausashe. Ɗagowa nai ina kallonsa,
cikin rawar baki da fargabar amsar dazan iya samu nace, “Dan ALLAH kaine ka kawo
wallet ɗin nan ɗakin nan?”.
Baice komaiba ya tako gabana tare da riƙo hannuna duka biyu yana kallon
abinda ke ciki, cards ne masu muhimmancin gaske, ga sunan maisu kuma ɓaro-ɓaro a
jiki da hotunan sa, “Ina kika ganta ke?”. Gado na nuna masa batare da nayi magana
ba, ya kafe hannayena da nake sake jujjuya cards ɗin ƙo ƙyaftawa bayayi, nikam
ƙirjina sake bugawa ya keyi da sauri-sauri, jira kawai nakeyi yace wani abu, amma
yaƙi cewar. Hawaye suka sulalomin ina mai fatan kar abinda keta zomin arai ya
kasance hakane, kai banama fatan hakan, sai dai idan anason min yawo da hankaline
dan a ɓata masa suna. Muryata na rawar kuka nace, “Kace wani abu dan ALLAH boss”.
Kansa kawai ya girgizamin yana mai cije leɓensa na ƙasa, ya saka hannu ya amshi
komai dake hannuna ya maida a wallet ɗin ya sakata aljihu, taimakamin yay na shirya
ina hawaye, wata gigitacciyar tsawa data nema haukatani ya dakamin, “Ke komai kuku!
kuka!! kuka!!!, komai abin kukane a gareki, ya isheni haka banason ji kuma, malama
ki sharemin waɗanan banzayen hawayen kafin nai miki bugun kayan wanki wlhy a gidan
nan!!!”. Na matuƙar tsorata da yanayinsa, na koma jikin madubi na maƙure ina
ƙoƙarin haɗiye kukan, gaba ɗaya kamanninsa sun masifar sauyawa, idanunsa sun kaɗa
sunyi jajur, baice dani komaiba ya juya ya fice daga ɗakin. Sake fashewa nai da
kuka ina faɗin, “Ya ALLAH ka bani haske akan wannan al'amarin”. ƙarar takunsa dana
jiyo ya sakani saurin goge hawayen na juya ina saurin ɗaukar soson hoda nahau
shafawa. Bayana yazo ya tsaya yace, “Agogon wanene wannan?”. Da sauri na juyo
gabana na faɗuwa na zubama hannunsa idanu, kusan mintuna biyu na ɗago na kallesa,
Kaina na girgiza masa alamar ban sani ba. “Kin tabbata?”. Na ƙara ɗaga masa kaina.
Bai sake cewa komai ba ya koma bakin gado ya zauna tare da ɗaukar kofin tea ɗaya ya
fara sha yana cigaba da kallon agogon kafin ya ajiyesa gefensa. Ganin ya kafeni da
idanu nai sourin ƙarasa kimtsawa zuciyata nata kaikawo da tunane-tunane kala-kala
waɗanda gaba ɗaya sake zurma zuciyata suke a firgici. Tea ɗin ya ɗauka ya miƙamin,
babu musu na amsa dan a yanda yake ɗinnan zai iya mammakeni idan nai masa gardama.
Ni nafara fita daga ɗakin nakai kofunan kicin na ɗauraye da sauri-sauri na fito, a
falo na iskesa jikkata na gefensa ajiye. Ɗauka nai tare da briefcase ɗinsa, baice
dani komaiba nai gaba ya bini a baya, shine ya kulle ƙofar sannan muka ƙarisa inda
Sadiq ya goge motar ƙal yana jiran fitowarmu shi da maigadi, mun gaisa dasu cike da
girmamawa, suka buɗe mana motar muka shiga bayan kowannenmu ya karanto addu'ar fita
daga gida.

Story continues below

Tunda muka fice daga gidan hankalinsa nakan wayarsa, yayin da ni kuma
na afka kogin ruɗaɗen tunanin da gaba ɗaya kwanyar kaina ta gaza ɗauka. Jinai kawai
an riƙo hannuna, na juyo na kallesa, baice dani komaiba ya matsoni jikinsa tare da
aza kaina bisa damtsen hannunsa yana shafa bayana. Shiru nai ina haɗiyar zuciya da
hawayen dake taho mani.
Tunda Sadiq ya tsaida motar muke ta yima station ɗin kallon mamaki, duk da
dai safiyace sosai baici ace babu mutane haka ba, sai securitys da keta kai kawo,
Sadiq ya buɗe masa ya fita, kafinma ya zagayo ta wajena nidai na buɗe da kaina. Na
ƙara ɗan wawwaigawa na kalli ko ina, station ɗin tsit kamar babu kowa a ciki.
Shima kansa kallon ko ina yake da mamaki, amma baice komaiba, ganin bai amsa
jikkarsa ba nasan so ya ke saina kai har office ɗinsa kenan? Tare muka jera, baya
bari ya tseremin da ko step ɗaya. Shine ya buɗe ƙofar, muna shiga kawai sai mukaji
abu kanmu ana mana wanka da shi. Saurin ƙoƙarin fara share fuskkokinmu mukayi, amma
abin yaƙi daina zubowa, sai ma ihun ma'aikatanmu da tafi daya karaɗe wajen. A
sannan ne abun ya daina zubowa, muka share na fuskarmu sannan muka kalli juna kafin
mu maida ga kallansu. A take kunya ta kamani kuma, dan gaba ɗayansu sukayo mana caa
a ka da kalmar “Muna tayaku murnar aure!”.
Murmushi Jawaad ya daure ya saki duk da iya fuskarsa ne, kafin ya maida
dubansa ga Bilkisu datai ƙas da kanta, ya kamo hannunta cikin nasa yana faɗin, “Mun
gode sosai, ALLAH yabar zuminci”. Ya ƙare maganar da kai hannun Bilkisu saitin
bakinsa ya sumbata. tafi aka sakeyi, sannan kowa ya nufosu da ƙyautar dake
hannunsa, tun jay na amsa har hannunsa ya cika bilkisu ma ta fara amsa, jabeer ne
ya matso ya taimaka musu aka tarasu waje guda ya sake musu godiya itama bilkisu tai
musu ranta fal mamaki.
Gaban ƙaton cake ɗin da akai da hotonsu aka jasu, daga bilkisu har jawaad
ɗin dai murmushine shinfiɗe a fuskarsu, bazaka taɓa gane sunada damuwa ba, bily ta
fara ɗaura hannun ta saman wuƙar kafin Jay ya ɗaura nasa saman nata suka yanka. Ita
ta fara cirar ɗan guntu ta saka masa a baki, yay mata murmushi mai sanyi ya ciro
kaɗan itama ya saka mata yana jawota jikinsa ya rungume, saboda ganin yanda Rose
take musu wani irin mugun kallo mai cike da tsana da takaici yay hakan, da farko
baiyi niyyar bama Bilkisu cake ɗinba, amma saboda Rose yayi dan yana lure da ita ko
kalma ɗaya bata togaba na tayasu murna, hakama wasu daga cikin matan gurin sai
baƙin rai suke da bankama bilkisu harara..
Nanma tafin akayi, kafin Sir Ahmad ya farayin jawabin taya murna a garesu
kasancewarsa head of department nasu, daga nan sauranma suka sake tayasu murna da
fatan alkairi da bama Jay hannu suna musabaha, matan kuwa Bilkisu suke bama hannu
itama suna mata, shikam Jay sai dai su ɗaga masa dan sunsan ƙa'idarsa ce baya hannu
da mace ko wacece ita a station ɗin nan ko tana a gaba da shi kuwa sai dai a
kuskure. Suma mazan duk da Bilkisu na ƙasansu hakan bai hanasu mata murna ba,
tanata amsawa a kunyace dan wasuma ko magana ita bai taɓa haɗata da suba sai yau.
Sai da aka gama ɗan kace nace sannan suka wuce office ɗinsa, ƙyaututtukan
da suka samu kuwa tuni Jabeer ya saka an kaisu ciki dama.
Jikkarsa na ajiye masa saman table ɗinsa na ɗan kallesa, ganin
hankalinsa nakan files ɗin saman table ɗin ya ɗauki ɗaya yana dubawa saina ce “Sai
anjima” kawai na juya zan fita. Caraf naji an riƙoni, kafinma na juyo ya maidoni
baya ya jingina da table ɗin, kallonsa nai da mamaki, ya ɗan harareni batare da
yace komaiba naji saukar laɓɓansa kawai saman nawa babu zato.
Idanuna na lumshe kawai ban masa wani musuba ko sau ɗaya, dan inhar zai huce
ta hakan to Alhmdllh, rabonsa dako kissing ɗina tun randa mukaje Saudia. Ganin da
gaske yake sai kawai na shiga bashi gunmawa, nidai fatana ya samu nutsuwa wannan
fushin da fusatar dana gani tattare dashi ya gushe.

lokacin da matsalarnan taku ta faru, saboda ina sonshi na haƙura na mance da komai
kamar bai faruba, yazo suka rabu da matansa muka tafi U.S ɗin nan, babu roƙon da
ban masaba muyi aure a lokacin tunda dai ai baida mata, amma ya dinga shareni da
zancen har muka dawo, yanzu duk ƙoƙarin nan da nai masa bai ganiba sai daga ƙarshe
ya auri wannan yarinyar da tazo jiya-jiya cikinmu, bakuga yanda ya yarfani a
gabanta ba yanzun, mi take da shi da har zai wulaƙantani a kanta?”.
Kasa magana duk sukai, dan wannan faɗan kam dai yafi ƙarfinsu, duk da sunsan
komai, amma ita rose banda haukarta ai ba lallaine ka SO a SOKA ba ko? Su shaida ne
boss bai taɓa cewa yana sonta ba, sannan bai taɓa wulaƙantata ba. Hafiz ya taɓe
baki cikin takaici yace, “Ikon ALLAH, so kike ya wulaƙanta matarsa a kanki kenan
komi? Mtsoww! Lallai aiki ya sameki, kuka kuwa yanzu kika fara s.....” hannunsa
Aliyu ya riƙe da sauri yana murmushi, yasan hafiz da iya yaɓowa mutum zafafan
magana, yanzu sai ya sake birkitata. Duk da hakan kuwa sai da Rose ta hayayyaƙo ma
Hafiz akan dama ta lura ita tuni ya tsaneta.
Da sauri Jay ya bugi tebirinsa, cikin tsananin ɓacin rai ya nuna mata ƙofa
yana faɗin, “Rose fitarmin a office!!”. Rose ta nuna kanta tana faɗin, “boss ni
ka.......” cikin ƙaraji ya katseta ta hanyar sake doka tebir ɗin, “Nace! Ki
fitarmin daga Office”. Yanda taga idanunsa sun masifar kaɗawa ya sakata firgita,
tasan shi tasan shiɗin wanene idan yay fushi, ta kuma san abinda zai iya aikatawa
bayan hakan, ta kalli su Jabeer ta sake kallonsa.
Tashi Jabeer yay ya kama hannunta ya fitar da ita dan ya tabbata wlhy idan har
ta sake wasu mintuna bata fitaba komai yazo masa rai zai aikata mata, sai da ya
kaita har waje sannan yace, “Rose miyasa kikai haka? Kinfa san wanene boss?”. Zatai
magana yace, “Kinga kije zanzo na sameki muyi magana, amma Please ki daina masa
haka babu ƙyau, wlhy na tabbatar yana ɗaga miki ƙafane darajar kina cikinmu, kinsan
fa yana gaba dake, sannan boss bayason raini, kije zanzo ni da Aliyu mu sameki”.
Badan taso ba ta tafi tana sharar hawaye da kissima irin tashin hankalin da
zata saka Bilkisu a station ɗin nan.

Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta
muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine
mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo
wa...

(🤔Rose mi kike ƙullawa kuma?).

★★★★★★★

Tana fita Jawaad ya daki kujerarsa daya tashi akai yana faɗin, “Wlhy
yarinyar can saita bar aiki a cikinmu, kai ama station ɗin nan gaba ɗayansa”. Da
sauri Aliyu ya taso yana faɗin, “Please Boss! calm down, don't waste your time for
her, ba yanzu ya kamata ai wannan ba”. Hafiz yace, “Gaskiyane maganar Aliyu boss,
micece rose da har haukarta zai dameka, nifa dama can bataimin ba, duk da tana da
ƙwazo tana da siffofin mutane masu bala'in son kansu, ka barta saita gama shagala
bazaka ɗauki matakin komai a kanta ba sannan ka ɗauka. Amma idan aka maida mata
murtani a yanzu anma damu da ita kenan, abinda kawai za'ai mata shine winning, ayi
bala'i bala'in winning ɗinta akan Mami, idan tace zata shigar mata hanci kacimin
ubanta iyakar iyawa”.
Ƴar dariya Jabeer da ya shigo yayi jin furucin Hafiz ɗin, ya zauna yana
faɗin, “ALLAH kai mugune Hafeez”. Zama duk sukayi suma, Hafiz yace, “ALLAH kuwa
jabeer haukar yarinyar baimin ba, haka ake so ne banda hauka?, ni dama ni tace tana
so ALLAH kuwa ko, hummm”. ya ƙare maganar da cije leɓe irin na tsantsar mugunta.
Basu Jabeer ba hatta Jay sai da ya murmusa yana mai girgiza kansa, dan yasan Hafiz
shegen kansane a iya mugunta.
Ya sauke ajiyar zuya da jan guntun tsaki. Aliyu yace, “Kayi haƙuri boss, mu
munzo musha labarin Honeymoon shashashar ta wargaza komai”. Harara ya balla musu,
dan haka suka kwashe da dariya suna tafawa. Jabeer yace, “Wlhy Jay kayi wani ɓul-
ɓul da kai fa, ka kuma ƙara haske”. “Kana baƙin ciki ne ɗan sa ido?”. Jay ya faɗa
yana jefa masa biron hannunsa. Dariya suka sake kwashewa da ita.

Burrum aka turo ƙofa babu ko neman izini, ƙoƙarin janye kaina nayi amma ya hanani
kowacce dama, saima sake turani jikinsa yayi sosai da sake sauya salon sumbatar,
ƙamshin turaren rose da naji ya sakani nima canja salo dan ta bani haushi ɗazun,
dan batamin magana ba sam, nakuma gaisheta taƙi amsamin. Jin ta fita da gudu tana
kuka ya janye kansa da ƙyar yana jan tsaki da harar ƙofar. Kallonsa ya maido gareni
yana hararata, hakan ya sakani sakin murmushi dan harga ALLAH dariya ya bani, to ni
miye laifina kuma?.
Kaina ya dunguremin da faɗin, “Idan kika cigaba da wannan noƙe-noƙen da sanyi
saita cigaba da raina miki ai, ki kwana da shirin cewar ke matar Jay ce a station
ɗin nan yanzun ba budurwarsa ba”. Ya ƙare maganar a hankali cikin kunnene kamar mai
raɗa. Lumshe idanuna nayi ina murmushi, bance komaiba na ɗauka jikkata nasa a
kafaɗa sannan na kallesa, shima kallona yake, murmushi na sake sakar masa da ɗaga
masa yatsun hannuna biyu alamar bye-bye. Kafin ya samu damar cewa wani abu harna
fice abina daga office ɗin.
A jikin ƙarfen lifter na iske Rose tsaye sai cika take da batsewa, kallo
ɗaya nai mata na ɗauke kaina, “K!!” ta faɗa a daƙile, banza nai mata tamkar banjiba
na haye lifter ɗin abuna, wani tsalle tayi zata cakumoni naji muryarsa a bazata
kanmu, “Koda kuskure karki sake wlhy hannunki ya taɓamin mata”. Ya faɗa a kausashe.
Murmushi nayi da ɗage masa gira na ɗauke kaina, banajin amsar da take bashi dan
nayi nisa da su, ina sauka kuma na sake ɗaga masa yatsun hannuna, shima ɗagomin
yay, nai gaba abina na barsu bansan yaya suka kwashe ba.

Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta
muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine
mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo
wa...

Bily na ɓacema ganinsa ya juya office batare da ya sake ko kallon inda rose
take ba, ta cika tayi fam da baƙin ciki tamkar zatai bindiga a wajen. Ganin zai
shige sai tabi bayansa a guje. Tana shiga office ɗin yana zama a kujerarsa, tsabar
wulaƙanci sai yay kamar baisan ta shigo ba ya fara ƙoƙarin haɗa Computer ɗin saman
table ɗinsa.
Kuka maicin rai Rose ta fashe da shi tana dafe tebirin da hannu biyu, “Boss!
Ni zaka wulaƙanta akan yarinyar da tazo station ɗin nan jiya-jiya? Ni zakaci amana
ka yaudara saboda waccan ƴar tatsitsiyar yarinyar da bata wuce ɗiyar cikinka ba?,
ko kunya bakaji kake iya nuna ƙaramar yarinya matsayin matarka wai?”.
Jawaad ya ɗan lumshe ido yana buɗewa akan Computer ɗin da ya kunna,
jikkarsa da bily ta ajiye masa ya ɗauka ya buɗe batare da yama rose ko kallo ɗaya
bama balle tai tunanin samun amsa.
Rose dake binsa da kallo ta sake fashewa da kuka tana faɗin, “Yanzu nan boss
ina maka magana kana sakemin wani wulaƙancin?”. Sake yimata banza yay yama fara
aikin gabansa. A wannan yanayin su Jabeer suka shigo office ɗin dan sunyi knocking
har kusan uku yanaji ya share, shigowar tasuma baisa ya ɗago ya kallesu ɗin ba, su
dai suka zauna a kujerun gaban tebirin suna kallonsa suna kallon Rose dake kuka.
Hafiz ya jawo kujerar dake can gefe shima ya zauna yana jan ƙaramin tsaki dan shifa
Rose takaici take bashi da halintan nan.
Ganin yamaƙi kallonsu Jabeer yace, “Boss wai mike faruwa ne?”. Bai tankaba
bai kuma kallesun ba yanzuma, dama cikin damuwa yake, ya fito gida da fushi, ita
kuma yanzu sake kunna zuciyarsa take tana cikowa saman ƙirji, idan kuma har ta bari
takai masa wuya to lallai zatayi nadamar biyosa office ɗinsa tana masa ihu a kai.
Jabeer zai sake magana Aliyu ya girgiza masa kai alamar kar yayi, Rose ɗin
ya kalla da take kallon Jay tamkar zata haɗiyesa, kuma har yanzu kukan take, “Rose
miya faru?”. Juyawa tai ta kalli Aliyu hawaye na sake ziraro mata, “Aliy na gaji
wlhy, na gaji da wulaƙancin da boss yake min, dan na soshi shine ya zama laifi?
Shekara nawa na ɗauka tare da ku, kuma ban gazaba wajen nuna masa ina sonsa tun
yana tare da wancan matar tasa, ya cemin shi bashi da ra'ayin yin mace fiye da
ɗaya, karka manta har suspension yasa aka bani

“Mtsoww, kufa wataran shashashancinku yawane da shi wlhy, ku ajiye


wannan shiriritan muyi abu mai muhimmanci, kosu sir Ahmad banje na gaida ba, so
nake mu gama sannan, dan na dawo da ayyuka masu yawan gaske, amma inason na fara
jin mike tafiya daga wajenku?”.
“Akwai nasarori masu yawa da zasu sakaka farin ciki kuwa, dama mun barsu
ne harka dawo muyi maka surprise”. Murmushi Jay yayi mai sanyi da jin duk ɓacin ran
daya toshe masa ƙofar zuciya yana faɗawa. Aliyu ya ajiye masa files ɗin hannunsa.
Ɗauka Jay yayi ya fara dubawa, a take fuskarsa ta bayyanar da annuri, sai da ya
gama dubasu duka sannan ya ɗago yana kallonsu, “Woow! Ina alfahari daku sosai da
sosai wlhy, gaskiya kunmin babban albishir mai darajar gaske, yanzu kuna nufin
waɗanan duk sunzo hannu? Kun gama mana da waɗan nan ayyukan?”. Jabeer yace, “Ƙwarai
ma kuwa, dan wanda yasa aka kashe jami'inmun ma yanzu haka gobe za'a miƙasa kotu”.
“Masha ALLAH, gaskiya naji daɗi wlhy, kuma nayi farin ciki sosai,
maganar yaran canfa?”. Jawaad ya faɗa yana miƙewa ya ɗakko wani file a drawer ɗin
bayansa.
Yanzunkam hafiz ne ya bashi amsa, “Ai boss maganar ƙungiya ta wuce duk yanda
mukai zatonta, lokaci kawai zamu samu ko zuwa anjima sai muje office ɗin nasu kaga
komai da idanunka zaifi, ko zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”.
“Hakan yayi Hafiz, mu barsa kawai zuwa gobe sai muje, kuma sannunku da
ƙoƙari, Jabeer maganar matar nan fa, har yau baka kammala ba ne?”. Na kammala
komai, sai dai abinda ba'a rasaba, shima akan binciken mitaje yi inda take ne,
inason binciko ƴan uwanta ne kokuwa? Gashi yanzu ma na daina samun wayarta gaba
ɗaya kuma”.
Saurin kallonsa Jay yayi “Bata aiki wayar kokuwa?”. “An kasheta dai kusan
kwana uku kenan, nafi kawoma raina matsalar caji ne”. Numfashi Jawaad ya ɗan sauke
da faɗin, “Okay to ALLAH ya dafa mana, yanzu dai bara na leƙa na gaida su sir
Ahmad, idan na fito zan ɗan fita wani waje, dana dawo saimu zauna akan wasu cases
ɗin da muke dasu a ƙasa tunda kun kammala waɗannan”.
Duk kai suka ɗaga masa, kafin duk su miƙe su fito, shi ya hau lifter yay
sama su kuma kowa ya nufi office.

Sai da ya shiga suka gaggaisa da oganninsa, office ɗin sir Ahmad ne ya


zama ƙarshe, bayan sun gaisa shima da tattauna abinda ya shafi aiki Sir Ahmad ke
cewa, “Nasan kasan Qaseem ya dawo ai?”. Da mamaki Jay yace, “Qaseem kuma sir!? Wlhy
ban sani ba. Yaushe ya dawo?”. “Ya dawo kwana uku kenan, sai dai kuma yanzu haka
sun killacesa, duk da shi ya dage akan shifa lafiyarsa ƙalau, shima Alhaji Ali ya
kirani akan maganar wai ya kamata muyi wani abu a sakar masa ɗa dan baida wata
corona”. Jawaad ya gyara zama yana ɗan murmushi da mamaki, yace, “To ALLAH ya
kiyaye, amma kunje ɗin ku?”. “To Jay mu zamu biye musu ne, wannan hurumine na
hukumar lafiya ai, kuma sunce nan da sati biyu idan bata basuga komai ba zasu
sakesa ai”. “To ALLAH ya kaimu lokacin”. “Amin” sir Ahmad ya faɗa sannan sukai
sallama ya fito.
Bai koma office ba ya nufi inda Sadiq ke jiransa, buɗe masa mota yay ya shiga
sannan suka fice.

★★★★

Cikin Barrack sukaje wajen baba ƙaura, baba ƙaura na zaune yanata fiƙar
tsinkayen iccen ƙwari Jawaad ya shiga da sallama shi da sojan da yay masa rakkiya.
Ɗagowa baba ƙaura yay yana amsa musu da musu sannu da zuwa, ya nunama Jawaad wajen
zama shi kuma wancan sojan ya fice. Sai da suka gaisa da tambayar ya kwana biyu
sannan baba ƙaura ya kalli Jay yay murmushi da ɗauke kai. “Malam Jawaad kenan, mi
kuma ya faru?”. Jawaad yaɗan murmusa yana kallon ƙwarin da baba ƙauran ya feƙe ya
zube gefe kusan ashirin, “Baba na zone akan wata magana daka faɗa ranar a dajin
nan”. “Tofa wace magana ce?”. Hannu Jay ya saka aljihun wandonsa ya ciro wuri da
gurun nan na hannu sai zobe ya ajiye gaban baba ƙaura”. Kallon kayan baba ƙaura yay
ya ɗauke kansa yana murmushi, “Kun sami huɗu kenan?”. Kai Jay ya jinjina masa.
Cigaba baba ƙaura yay da aikin gabansa kamar ba zaice komai ba, kusan mintuna biyu
sannan ya sake duban Jawaad ɗin da maida dukkan hankalinsa ga resa, “Yanzu ina
ɗayan yake?”.

“Bamu ɗakkosa ba, yana acan gidan data zauna ɗin”. Baba ƙaura ya ɗauki zoben ya
jujjuyashi sosai a hannunsa sannan ya ajiye, “Lallai kun samu damar amsar babban
makaminsu, amma yaya akai kuka iya samun zoben nan? dan abune mai daraja ga mai
shi”. Muryar Jay cike da ɗaci ya zayyane ma baba ƙaura komai da ya faru, harma da
maganar fyaɗen da aketa bibiyar Bilkisu da shi da sai a randa ta cire zoben ta iya
tunawa. Nannauyan numfashi baba ƙaura ya sauke, yace, “Ai dama na faɗa maka
yarinyar akwai duhu dake biye da ita, wannan yana ɗaya daga ciki, amma akwai wanda
ya fisa girma ma sai dai bansan minene ba, ku cigaba da gayama ALLAH shi mai komai
da kowa ne, ba ita kaɗai ba abubuwa da yawa zasu fito dalilin wannan zoben, dan duk
inda maishi yake hankalinsa baya a kwance yanzu, har dama duk wanda ke zagaye a
ƙungiyar shaiɗancin, ka turata gidan ta ɗakko wancan ɗayan wurin, idan har ta tarar
an hargitsa ɗakin data ajiye to lallai mai bibiyarta da wannan sheɗancin na fyaɗe
yana cikin wannan gidan, kuma shaiɗaninsu sun tabbatar masa wurin data cira a farko
yana a gidan, an basa damar ya nemosa gudun karku haɗasu kamar yanda muke buƙata,
dan inda tace maka ta ajiyesa babu wani shaiɗani da ya isa ɗaukarsa saboda darajar
Al-Qur'ani, shiyyasa shi akace ya ɗakko, inaji a raina kuma bazai gansaba insha
ALLAHU, dan daya gansa komaima zasu iya aikatawa a kanku domin halakaku baki ɗaya
musamman ma ita, suma kansu basusan taka mai mai inda ya keba bayan sanin yana
cikin ɗakin kawai”. Jay dake ta tauna lip ɗinsa na ƙasa sai jinjina kai kawai ya
keyi, ya furzar da huci mai zafi a bakinsa yana sake jinjina kansa. Baba ƙaura
yace, “Idan ta ɗakko ku yanka wannan gurun, ku zira zoben da wurin guda biyu cikin
gurin, zoben ya zama shine a tsakkiyar wurin, sai ku ƙulle gurun ku ajiye. wannan
ba tsafi bane, ba kuma wani shaiɗanci bane, zakuga abinda zai biyo baya insha
ALLAHU, dan cikin sauƙi zakuyita gano abubuwa masu ban mamaki da al'ajabi insha
ALLAH..............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[1/18, 4:58 PM] HASNA ✍🏻
: Typing

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 52
................Wata tarbar karramawar na sake iskewa wajen ƴan office ɗinmu nima,
suka baibayeni mazansu da matansu suna mai tayani murnar aure da samun boss
matsayin miji, su Ada iyayen gulma harda cewa na musu wayo nai wuf da boss. Ni
dariyama suka bani wlhy. Na musu godiya da fatan suma ALLAH ya basu nasu musha
biki. Fassara muku farin cikin dana tsinci kaina a ciki saboda dawowar su Nazifa
station ɗinmu ɓata lokacine, muka sake rungume junanmu daɗi na ratsamu, a karo na
uku mun sake kasancewa tare, ALLAH dai yasa muci amfanin wannan ƙawance har a gidan
aljanna. Gaba suka tasani da sheri wai nayi ɓul dani kodai an samar musu baby?.
Yinai kamar banjisu ba, da suka isheni sai nace suje su tambayo boss ɗin. Dariya
suka sanya kowa na miƙewa duk suka koma mazauninsu da aka basu suma a office ɗin
namu. Daga haka na samu lafiya daga iskancinsu.
Ban tarar da kowanne aikiba, Ummie ta sanarmin ai duk oga Jabeer ya bata ta ƙarasa
ayyukan dana bari, naji daɗin hakan sosai, saina miƙe ƙafa ina hutawata, da wannan
lokacin nai amfani wajen zurmawa duniyar tunane-tunane kala-kala, ciki harda neman
amsar yanda akai aurena da Yah Qaseem ya fasu aka maida shi kan boss, sai abinda na
gani yau a ɗakina da duk nama rasa wane tunani ya dace nayi akan hakan, dan duk
wanda nayi mai ƙyau sai naga bai zauna da al-amarin ba sam, sai marasa ƙyawunne
keyin dai-dai. Ban sakejin ɗuriyar boss ba har muka fita sallar zuhur, bayan an
idar mun fito su Nazifa ke faɗin ya kamata muje muci abinci, dan wasu a cikinsu ma
basu ko karya ba suka baro gida, nima ɗin sai yanzun na tuna ban karyaba, ruwan tea
ne kawai a cikin nan nawa. Shiru nai ina tunani, ni dai banda damar cewa zan bisu
wajen cin abincin nan boss bai saniba, ni kuma bana wani son zuwa Office ɗinsa....
Taɓanin da akai ne ya katse tunanina, na sauke numfashi da kallon Rebecca da
hannunta ke a kafaɗata, "Matar nan ina kika tafine? anata magana". Murmushi na mata
ina tura hannayena cikin aljihun wandona, "Ba komai, kinsan zuciya da tone-tone,
inaga kuje kawai banajin wani yinwa nikam". Har Ummie ta buɗe baki zatai magana sai
Zuhrah ta katseta, "Kai inagama fa bai kamata ta bimu ba mijinta bai saniba
gaskiya, tunda yana cikin station ɗin shima ta fara sanar masa, yanzufa ba da bace
da muka saba shirmen mu kai tsaye". "Hakane kuma gaskiya" cewar Nazifa tana komawa
kalar tausayi. Fahimtar inda ta dosa yasa muka kwashe da dariya mu dukanmu, dan
itama dai bai wuce nata auren da ya rage six weeks ta tuno ba. Office muka koma
bisa shawar Zuhrah, ita da Ummie kuma suka tafi sayo mana abincin..
★★★★★★
Tunda suka baro cikin Barrack ɗin Jay ke ƙullawa da kwancewa, lumsassun idanunsa da
launinsu ya gushe da ga farare zuwa ɗan jaa ya buɗe a hankali yana furzar da
nannauyan numfashin da har sadiq sai da ya saci kallonsa ta mirror. Wayarsa ya
ɗauka ya shiga daddanawa kafin ya saka a kunne dayin sallama, Munkaila na amsawa
bai tsaya bi takan gaisuwar da yake masaba yace, "Zan tura maka wasu sunaye guda
huɗu, inason daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu a nemomin inda suke,
sana'arsu ko aikinsu, abokan mu'amularsu na rayuwa dana kasuwanci". "Okay sir insha
ALLAHU zanyi ƙoƙari, akwai ma waɗan can ayyukan na wajena guda biyu suma duk na
kammala". "Saika haɗosu kawai". "Okay Sir" Munkaila ya faɗa cike da girmamawa.
Suna isowa cikin station ɗin baima jira Sadiq ya buɗe masaba ya buɗe da kansa ya
fita, sallamar Sadiq ɗin yay akan yaje zuwa biyar sai ya dawo, shi kuma kai tsaye
massallaci ya nufa saboda lokacin salla yayi.
Bayan an idarne ya fito zai koma office yaga su Bilkisu, sai dai su sam basu
ganshiba dan hankalinsu baya ta wajen, yazo zai ɗan gittasu yaji hirar da sukeyi,
ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yaba hankalinsu, yanda yake musu kallon yara ƙanana
bai zaton sunada zurfin tunani irin hakaba, dan daidai zai wucene maganar zuhura ke
shiga kunnensa akan bilkisu bai kamata ta bisuba mijinta bai saniba. Sai da ya
shiga office ya zauna sannan yay kiran gidan abincin da yaji su Ummie zasuje,
umarni ya bada akan a basu duk abinda suke buƙata kar kuma a amshi kuɗinsu shi zai
biya. Kasancewar sa babban Customer babu ɓata lokaci aka haɗa musu komai.
Su Ummi basu san wainar da ake toyawaba, sudai sukaga an haɗa musu abinci kala-kala
harma da wanda basuce ɗinba, amma dai-dai abinda zasu iya cinyewa ba almabazaranci
ba, sannan akaƙi amsar kuɗinsu, da suka matsa da tambaya aka basu amsa akan an
biya. Sosai sukaita mamakin da tambayar waye ya biya ɗin?, babu wani ɓoye-ɓoye aka
sanar musu.
Tunda suka dawo suka sanarmin yanda akai wajen sayen abincin sai naita mamaki akan
yaya akai yasan zasuje? Shin kodai idanu ma yasa a sakamin ne? Kai bana tunanin
hakan daga garesa, sai kace wanda bai yarda dani ba. waya na ɗauka na tura masa
saƙon godiya da fatan alkairi.

Jawaad na zaune ya duƙufa aiki saƙo ya shigo masa, kasancewar Number da kowa ya
sansa da itace ya zata akan wani aiki ne, dan ya kashe wayarsa da mutane masu
muhimmanci kaɗai ke ciki, gudun kar Alhaji babba kosu Ummah su kirashi susan ya
dawo, baiyi tunanin bily bace tunda bai saka Numbar ta anan ba, ɗauka yay ya duba,
a mamakinsa sai yaga itaɗin ce ashe, yay murmushi da ɗan lumshe idanu ganin abinda
ta rubuto, ajiye wayar yay kawai ya cigaba da aikin gabansa. Cak ya tsaya daga
abinda yakeyi yana mai ƙure takardar daya saka sunayen da suka samo wajen Umm-Anum
da ido, waya ya ɗauka da hanzari yay kiran Jabeer, yana ɗagawa yace, "Jabeer bama
wani ya kawo min file ɗin matarnan".
Daga can Jabeer ya amsa masa da "to". babu jimawa kuwa sai gashi ɗan aike daga
jabeer yay knocking, damar shigowa ya bashi.
Cikin girmamawa ya ƙame da sarama Jay kafin ya gaida shi, sannan ya ajiye file ɗin
hannunsa. Ɗaga masa hannu Jay yayi alamar ya tafi kawai. Yana fita ya ɗauki
takardar dake da sunayen bayan ya zagaye sunan macen dake a ƙarshe da jan biro,
sannan ya buɗe file ɗin wajen Jabeer. tsai Jay yayi a zaune yana ƙarema sunayen
kallo, sam babu wani banbanci hatta da sunan gari, waya ya ɗauka ya shiga dannawa.
Kira yayi, bugu biyu aka ɗauka, bayan sun gaisa yace, "Malam Rabo, yanzun nan
inason Ka binciko min Hajiya Safara'u a cikin ƙauyen nan naku, gashi nan zan turo
maka cikakken sunanta da sunan mahaifinta nasan zaka gane, banason ɓata lokaci,
yanzun nan nakeson kabar tasharnan ka tafi". "Insha ALLAHU kuwa oga yanzun nan
zanbi motar datai lodi kuwa, koma na amshi mashin ɗin Madu naje yanda zanfi sauri".
"Hakan yayi, ka zuba mai idan ka dawo sai a bashi wani abu shima". "To oga babu
damuwa, sai ka jini".
Jay na ajiye wayar ya maida dubansa ga file ɗin yana bin komai dalla-dalla, dogon
nazari ya shiga akan abinda ke cikin file ɗin da wanda ke a ƙwalwar kansa, 'Wato na
fahimci akwai wani kuskure da nayi ƙwarai da gaske' yay maganar a fili yana dafe
kansa, takarda ya ɗauka ya hau rubutu, sai kuma ya ajiye biron ya kwanta jikin
kujera da faɗawa duniyar tunani.
Rasuwar gimba ta rikitashi ainun har yama manta abubuwan da ya kamata ace ya
bibiyesu. Akwai Number ƙarshe da gimba yay waya da ita ya kamata yasan wanene ma?
da wuri, sannan matarnan da gimba ya ambata ta gidan Alhaji kokino tabbas da itane
suka taɓa haɗuwa a gidan Alhaji Kokinon, kuma itace tai aiki a gidansu kenan? Idan
binciken ya zama dai-dai. Yaya akai hakan ta faru bai taɓa fahimtaba kai tsaye,
kalamanta na wancan karon sun isa su bashi dukkanin amsar da yake buƙata. tabbas
wani baƙon al'amarine da bai taɓa sakashi a lissafisa bane ya shigo masa kai yanzun
nan musamman akan kashe Gimba da akayi yake tunanin da babu gaira babu dalili.
Abinda yake tunanin ya faru akan kisan gimba ba shi bane ashe. Alhaji kokino sunyi
abotar siyasa da Abba kamar yanda Ummuna ta faɗa, sun kumayi ta kasuwanci, indai
har matarnan tayi aiki a gidanmu mizaisa ta koma can gidan tana aiki? Lokacin da
aka sace Alhaji kokino itace ta bani dukkan sirrikan da nabi na samosa a hannun
ƙaninsa, maganar gimba a al'amarin, yace akwai dalilinsa na zuwa aiki ƙarƙashina,
na kuma nemeta zanji abubuwa masu muhimmanci. Idan har zan haɗa wannan maganar
tashi da maganganunta na waccan ranar da muka taɓayi to lallai tamin farin sani
kenan?. Miƙewa Jay yayi yana ɗan dukan tabirinsa da faɗin, "Yah ALLAH ". Ya
sassauta tie.. ɗinsa yay ƙasa da shi, saima ya fincikesa gaba ɗaya ya jefa saman
kujera ya shiga safa da marwa a office ɗin, duk da ac dake aiki hakan bai hanashi
haɗa gumi ba, tun randa yasan akwai alaƙa tsakanin Alhaji kokino da Mr Gebrail ya
saka ake bibiyar masa Mr Gebrail, ta hakane ya gano kuma alaƙar Mr Gebrail da ɗaya
a cikin Uncle ɗinsa, idan ya dunƙule maganar waje guda hakan na nufin, Uncle ɗinsa,
Mr Gebrail, Alhaji Kokino duk sunada a laƙa ta baɗini, dan a zahirance babu wannan
alaƙar kota gaisuwa a tsakaninsu sai a ɓoye. dolene a daren nan a sato masa wayoyin
Alhaji kokino, sai dai waye zai masa aikin? 'Dan dole ya kasance ɗan cikin gidanne
zaiyi hakan' ya ƙare maganar a fili yana dafe kansa da furzar da huci mai azabar
zafi.
Tunanin kiran bilkisu ne yazo masa a rai, dan kosu Hafiz bayason sakasu a wannan
case ɗin yanzu, saboda ya haɗa da family nashi, sannan yanada sarƙaƙiyar yarda da
wani, kai tsaye zai iya zama ganganci, bawai dan bai yarda dasu bane, dan su Jabeer
sun wuce duk hasashen mai karatu a garesa, amma ciki ba'a yisa dan abinciba kawai
ai. Bilkisu na ɗagawa yace, "Ina jiranki a office". Ya yanke wayar.
Kallon wayar kawai na tsaya yi da mamaki, to amma yanda naji muryarsa tamin kama da
ta mai damuwa, miƙewa nai na fice, inajin Nazifa na tambayata ina zuwa? Ban
sauraretaba na ɗaga mata hannu kawai. Koda nai knocking ba'a amsamin ba, dan haka
kawai na shiga kaina tsaye. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ganinsa ba yanda nai
zatoba, ya ɗago ido ya kalleni sannan ya maida ga abinda yakeyi. Takawa nai na
ƙarasa garesa, murya a sanyaye nace, "Wlhy nazata ko baka da lafiya, ya aikin?".
Baice dani komaiba ya nunamin wajen zama, shima zagayawa yay ya zauna a kujerarsa,
yanda ya tsatstsareni da idanu duk sai naji na takura, na risinar da nawa ƙasa ina
kallon yatsun hannuna. Numfashi naji ya sauke mai ƙarfin, kafin nace wani abu ya
fara min bayani akan kiran, ya ƙare maganar da faɗin, "Dole ne musami wayar a daren
nan, dan itace zata bamu haske akan komai da gaggawa, aikin nan kuma dole mu biyu
kawai zamuyisa ni da ke kawai, ko su Aliyu banason na saka sai na gama fahimtar
komai".
Naji daɗin karrawarsa gareni sosai, dan banyi zaton hakanba, na gyara zamana, "To
ina ganin mizai hana muyi amfani da cikin ƴaƴansa ko ma'aikatan gidan?". Shiru yay
yana kallona da goga ƙasan biro akan laɓɓansa, kusan sakan goma ya janye ya maida
kan takardar gabansa, ɗan rubutu yayi sannan ya sake ɗagowa ya kalleni, "Wannan
shawarar taki tayi, amma babu wani ƙarin bayani a kanta?". Tsai na ɗan ƙarayi na
tunani kafin nace, "Akwai, ya kamata wadda zamu saka ɗin cikin ƴaƴan nasa ta
kasance mace, sannan mu nuna mata za'a cutar da shine shiyyasa muke son wayoyin na
wasu awanni kawai za'a maido mata ta maida masa bayan mun saka matakan tsaro. Ko
baiyi ba?". "Ihum inajinki cigaba" ya faɗa cikin lumshe idanu. Naɗan sauke ajiyar
zuciya da cigaba da faɗin, "Idan muka amsa maimakon mu ajiye wayoyin a hannunmu
kawai muyi copy ɗin komai na ciki sai a maida mata ta maida masa zuwa safiya".
Lallausan murmushi ya saki yana ɗagemin gira ɗaya, "Ashe matar tawa ƙwaruwa ce?".
Yanda yay maganar cikin zolaya yasa na rufe idanuna da tafin hannu ina murmushi.
Yace, "Thanks Miemaa, da duk kaina ya kulle". Nace, "Haba dai, kaine kanka ke
kullewa?". "Oh ni ba mutum bane? Duk ma ba kece kika rabamin hankali biyu ba".
"Nidai babu ruwana". "Humm", ya faɗa kawai yana miƙewa. "Kinga tashi muje, da zafi-
zafi ake dukan ƙarfe".
Koda muka fito sai da ya shiga office ɗin Aliyu, babu jimawa ya fito riƙe da key
ɗin mota, da kansa ya buɗemin na shiga sannan shima ya zagaya ya shiga, nidai
addu'a nake a raina karyay gudu damu, yanda naci abincin nan na ƙoshi matsala za'a
samu ai. Kasa daurewa nai na roƙesa karyay gudu dan ALLAH, ƙin tankamin yayi, sai
ma waya daya ɗauka yay kira, kasancewar a Hans free ya sakata sai naji duk abinda
suke faɗa, na fahimci da wani ma'aikacin gidan Alhaji kokinon yay magana, dan ya
faɗa masa gamu mun taho ya fito mu haɗu a bayan layin. Dai-dai saitin wani shagon
saida kayan abinci dake farkon layin muka tsaya, wani dattijon tsoho ya fito daga
shahon, kallo ɗaya naga yayma motar ya ɗauke kansa, sai kuma naga ya buɗe ya shigo
baya. Motar boss ya harba gaba batare da yayi magana ba. Nidai mamaki nake tayi a
raina, wannan aikin namu gaskiya saida jajircewa da cire tsoro, sai kuma ka iya
kowanne irin salo na mutane masu wayo. Gaba ɗaya muka fita daga layin muka shiga
wani, shima muka fita muka shiga na gaba, yana tuƙin yana kallon mirror, na fahimci
dubawa yake yaga ko ana binmu, ganin babu wani mai bibiyarmu sai yay fakin gefen
babban titi da muka fito. Sai lokacin ne dattijon yay magana. "Na tabbata babu wani
mai binmu insha ALLAH". Kashe motar yayi ba tare da yace komaiba, ya ɗan kalleni
sannan ya juya yana kallon dattijon. "Wannan itace matata, sunanta Bilkisu". "Masha
ALLAH, kai ALLAH ya sanya albarka ya bada zuri'a tagari". "Amin" ya faɗa, ni kuma
na juya muka gaisa da shi yanata sakamin albarka.
"Baba wannan karonma aiki ya sake kawoni gidanku, kuma ina buƙatar taimakonka kamar
wancan karon". "Karka damu ɗana, zan baka dukkan taimakon da kake buƙata insha
ALLAHU". "Nagode baba, akwai dattijuwar mai aikin nan da naji kuna kira maman yara
ko tana gidan har yanzun?". Jimmm mai gadi yayi kafin ya sauke numfashi, "Gaskiya
bata nan, a ƙalla zata kai kusan wata biyu ma kenan bata gidan nan". "Aiki ta ajiye
kenan?". "A'a bata ajiyeba, mudai bamusan miya faruba, rana tsaka ɗanta yazo yana
nemanta wai kwana uku bai samunta a waya" kallonsa Jawaad yake cikin nazari, "Kana
nufin Yazeed?". "Ƙwarai shi kuwa, to dalilin zuwan nasane muka fahimci muma bata
gidan, ita dai Uwargida tace ta tambayeta zataje gida wajen rasuwar ɗan yayarta, to
nidai ALLAH shine shaida ranar data cika kwana uku da tafiya naganta da idanuna ta
dawo gidan lokacin ina sallar isha'i, to amma abin mamaki sai naji ana cigiyarta
bayan kwana biyu wai bata gidan". "Ban gane bata gidanba? Kai kuma bakaga fitarta
ba?". "Wlhy ban ganiba yarona, dan ita macece mai yawan barkwanci inhar zata fita a
gidan nan kota shiga saimun tsokani juna, to a randa ta dawo da yake salla nakeyi
sai ban kawo komai a rainaba, abinda ma ya ɗauremin kai da sukace su basu gantaba
randa ta dawo ɗin". Shiru boss yayi alamar tunani, dan haka nikuma nace, "To amma
baba a wannan daren kana tunanin zata iya fita?". "Gaskiya bazata iyaba ƴata, dan
maman yara ma tana da ciwon ƙafa bata cikason yawan kai kawoba". "Hakan na nufin
tana cikin gidan kenan kokuma an fita da ita a daren, ko kaine idonka bai nuna maka
dai-dai ba?". "Wlhy bana ko tantama itace ta dawo da mangaribar nan, to ƴata wazai
fita da ita kuma sai kace wata kaya batare da an gani ba?, shaiɗanin daya taɓa
kwatanta hakama mijinki yasa an kaisa gidan maza ai". Murmushi nayi kawai, na ɗan
juya na kalla boss ɗin dake saurarnmu sannan na maida ga baba, "Baba a wannan ranar
mota nawa ta shiga gidan ta kuma fita bayan dawowar maman yara?". "Babu wanda yazo
tunda Alhaji baya gari ma, sai wani yaro ɗan dogo baƙi mai dogon hanci da ya kanzo
lokaci-lokaci idan Alhaji na nan, to ni a ranarma da yazo ɗin saida na sanar masa
baya nan ai Alhaji, sai yace ai ya sani saƙo zai bama hajiya inji Alhajin. Daga
haka ban sake tofa komaiba na barshi ya shiga ni kuma na shige ɗakina, to baifi
mintuna goma sha biyar da shigaba ma naji yana horn nazo na buɗe masa ya fice".
"Kasan sunansa baba?" "A'a gaskiya ƴata, ban saniba wlhy".
Waya boss dake saurarenmu ya ɗauka ya shiga daddanawa, kafin ya miƙama baba wayar
yana faɗin, "Shine wannan?". Amsa baba yay ya kalli hoton, cikin jinjina kai da
murmushi yace, "Tabbas shine kuwa ɗana". "Baba ka tabbata?". "Babu tantama a
zancena". "Shikenan mun gode, bara mu maida kai, sai dai zamu iya dawowa gareka a
ko wane irin lokaci". "Babu damuwa wlhy ɗana duk sanda kake buƙatar wani abu ka
kirani". Godiya muka sake masa, ya tada motar yay reverse, a wani wajen muka
saukesa saɓanin inda muka ɗaukesa.
Jin yayi shiru sai na ɗan kallesa, "Hoton wanene ka nuna masa dan ALLAH?". "Zaki
gani yanzun" ya faɗa yana karya kan motar muka shiga wani layi. A ƙofar wani gida
madaidaici yay fakin, ganin zai fita nima sai na buɗe na fita. Mun gaisa da samari
uku da alama ta nuna suke tsaron gidan, yanda suke gaishemu cikin girmamawa nasan
lallai shine ya ajiyesu. Ɗakin farko dake a gidan muka shiga, inda muka iske
matashin saurayi zaune, shigowarmu ta sakashi miƙewa yana murmushi da mana sannu da
zuwa. Na buɗe baki zan amsa kawai naji tass!!!.
Idanu na zaro baki a hangame ina kallon boss da ya saukema saurayin mari, ban gama
fita a mamakinba naga ya hau dukansa. Dukansa yake ta ko ina, a take jikina ya fara
rawar tsoro, nasa hannu na rufe fuskata ina ambaton "innalillahi....." da sauri na
buɗe fuskata jin ƙarar ɗana kunamar bindiga, nai masifar sake zazzaro idanu waje
ina faɗin, "Boss badai kashesa zakai ba?". Harara ya balla min ya ɗauke kansa yana
huci.
A tare muka saki ƙara ni da saurayin saboda harbinsa da yay a ƙafa, zufa ta shiga
rige-rigen karyo masa, jikinsa na wani irin rawa, ko kallon inda nake baiba ya
ranƙwafa kan saurayin yana hure bakin bindigar dake ɗan hayaƙi da faɗin, "Kaga
bindigar nan cike take taf da alburusai, kuma idan zan ƙarar dasu tas a sassan
jikinka babu mai tambayata yaya nai da su?, wannan harbin danai maka na ƙaryar daka
mince, idan wata ta biyo bayanta yanzun kuma wlhy saina faffasa gaɓɓanka ɗaya bayan
ɗaya da alburusan nan kafin na aikaka lahira dan ubanka. Ina kakaita itama?". Jikin
ɓaleru na rawa ga jini na malala a ƙasa cikin hakkin kuka da azabar shigar harsashi
yace, "Bansan wacce kake maganaba oga, dan ALLAH karka kasheni, nayi kuskure a
farko amma wlhy bazan sake kwatantashi ba". "wani rainin hankalin zaka sakemin?" ya
faɗa a taƙaice yana sake ɗaure fuska da ɗana kunamar bindigarsa.
"A'a wlhy oga ba haka bane ba, na tuba dan ALLAH zan faɗa maka komai, bata a garin
nan". "Amma ranar ca kaimin baka da alaƙa da Alhaji kokino, bama ka sanshiba ko?"
ya faɗa yana ɗora masa bindigar a saman kai. a take jikin ɓaleru ya ƙara ƙarfin
mazari, harya jiƙe wandonsa da fitsari, "Oga kawa ALLAH da MANZONSA karka kasheni,
ka yafeni, komi kake buƙata yanzu wlhy zan makashi, harma abinda baka saniba zan
faɗa maka". Ƙafa Jay ya saka ya danna ƙafar ɓaleru daya harba. Ya sake sakin wata
wahalalliyar ƙara jikinsa na karkarwa.
Da sauri nazo na riƙe hannunsa ina hawaye. Janye ƙafar tasa yay ya juyo yana
kallona da wani murmushi irin na tsagwaron muguntarnan, ya lakacemin hanci da
faɗin, "Ki rage wannan tausayin malama". Rungumesa nai da sauri ina faɗin, "To dan
ALLAH kayi haƙuri ka barshi haka tunda yace zai faɗa mana".
"To na barsa" Jay ya faɗa yana ballama Ɓaleru da keta kukan wahala harara da shafa
bayan bily data lafe a jikinsa. Sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya ɗagota ya
share mata hawayen tas da sumbatar goshinta.
Jikkata ya amsa ya buɗe, ya fiddo biro da ɗan littafi dake ciki ya jefama ɓaleru,
duk da halin da yake ciki haka ya ɗauka ya rubuta masa address ɗin. Yana sharar
hawaye da sauke numfarfashi yace, "Oga gidan akwai matakan tsaro sosai, hanyar da
zaku iya fiddota cikin sauƙi itace kiran masu tsaronta da wayar Alhaji kokino".
Uffan baice masaba, saima waya daya kira, mintuna kaɗan saiga ɗaya daga cikin masu
tsaron gidan ya shigo. A daƙile yace, "A cire masa wannan bullet ɗin a tsaida
jinin". Da girmamawa ya amsa da "Yes Sir" hannuna ya kama kawai muka fice, sai
binsa nake da kallo da ɗunbin mamaki, ban taɓa zaton tsaurinsa ya kai hakaba, nikam
tsoroma yake ƙara bani yanzun.
Sai da muka fara tafiya sannan yay magana hankalinsa nakan tuƙi, "Tunaninmu na
samun wayar kokino yana a kan hanya, wannan tsoron da tausayin naki kuma dole ki
cireshi dan aikinmu baya buƙatarsa". Kallonsa nayi sai naga bani yake kallo ba,
yama fuske abinsa tamkar bashine yay maganarba. Nima bance komanba amma sai juya
lamarin nake a rai, 'sai kace a cikin film? kai anya kuwa ban sako kaina inda yafi
ƙarfina ba? Wani ƙarfin zuciyar ai sai maza dole'.
Da wannan tunanin a raina muka iso wani waje saɓanin station da nai tunanin zamu
koma. Fakin yay sannan ya ɗauka waya yay kira. Yanda ya kwantar da murya tamkar ba
shine ya gama hargagi yanzunba sai ya bani mamaki, jin kuma da mace yake maganar
dan a hans free yasa sai naji wani abu ya dunƙulemin a ƙirji na takaici. Ƙin
kallona yay ya cigaba da wayarsa, "Kiran da nai miki yanzu ai ya tabbatar miki ban
manta da ke ɗinba". Cike da yanga daga cikin wayar akace, "Kai dai kanason kare
kanka, shekara biyar ai ba kwana biyar bace". Baki naga ya wani taɓe da ɗauke kai
kamar yana a gabanta, a zahiri kuma sai ya sake kwantar da murya da faɗin, "Tom
nayi laifi, amma nima bana ƙasar ai, yanzu ma dai akwai wani taimako da zakimin
akan Dadynki". tace, "To yanzu na fahimci dalilin kiran, tunda ba taɓa kirana
kayiba, inma na kira baka ɗagawa" "Humm" ya faɗa batare da ya bata amsar zancen
nata ba, "Yanzu dai bazakimin taimakonba na nema wani?" "Ah haba, kaima kasan bazan
iyaba ai, ko karan gidanka ka aiko da buƙata ai zan biya masa balle kai ɗin da
kanka" "Yayi" ya faɗa a taƙaice, sannan ya cigaba da faɗin, "Wani ƙulli da ake
sonma Dadynki mukeson kwancewa batare da ya saniba, dan haka mukeson ki ɗebo mana
dukkan phones nashi a daren yau zuwa safiya insha ALLAH za'a dawo dasu ki maida
masa batare da ya saniba". Jimmm tai alamar tunani, kafin ta sauke numfashi da
faɗin, "Tab wannan aikin baiyi girmaba kuwa Jay, Dady fa ko Momy bai bari ta taɓa
masa waya balle mu, to ta inama zan fara hakan?". "Yanda za'ai ɗin ke ya kamata
kiyi tunani, inba hakaba komai zai iya faruwa da shi, idan kuma kin zaɓi komai ya
farun akan ki bada haɗin kai a taimakesa kafin ya farun to babu damuwa sai
anjima....." da sauri tace, "A'a tsaya-tsaya, ka bani lokaci zanje nayi tunani,
nanda magriba idan da yuwuwar hakan zan turo maka saƙo, dan matsalar shine kasan
shi business yake, komai dare kuma amsa waya yakeyi, to tayaya za'a ɗauka har sai
zuwa safiya a maido bai fahimta ba?". "Kidaiyi ƙoƙari mugani". "Shikenan sai ka
jini" ƙitt ya yanke wayar tare da juyowa ya kalleni. ɗauke kaina nai gefe batare da
nace komaiba. Shima ɗin baice min ɗinba, saima sallama da naji ya sakeyi alamar
wata wayar.
kiran oga Hafiz yay aka yayma su Jabeer magana su zo su samemu a office ɗin da aka
buɗe na karɓar cases ɗin masu fyaɗen nan, dan yanada buƙatar sanin komai a yau ya
fasa gobe, amma kafin sannan su fara turo su Ummie sannan, kafin su su biyo bayansu
nanda mintuna talatin.
Duk da abin ya bama Hafeez ɗunbin mamaki sai bai tambayi dalili ba ya amsa masa da
to kawai, dan yasan zai musu bayani. Wayar ya ajiye yana sauke numfashi, ya kamo
hannuna cikin nashi tare da saka ɗayan hannunsa ya juyo da fuskata garesa. "Na
matan ne ya motsa?". Yay maganar gab da fuskata yana wani ɗagemin gira. Fuska naɗan
ɓata nace, "Miye na mata?". "Kishi mana" ya bani amsa da lakacemin hanci. Bansan
sanda murmushi ya suɓucemin ba nace, "Nidai ai ban faɗaba". "Ai shi ba sai an
faɗaba, a fuska ake ganoku". Mintsininsa nai a hannun da yake murzamin cinya. Ya
ɗauke da sauri yana faɗin, "Ouch!, muguwa". Dariya na ƙyalƙyale da ita, dan yanda
yay da fuska kamar wani ƙaramin yaro.
Murmushi Jay yay yana kwantar da kansa a kafaɗarta da lumshe idanu dan dama soyake
yaga ta dawo cikin walwalarta.
Babu jimawa sai gasu Zuhrah sun iso, cayay na fita na samesu mu shiga wajen tare,
shi zai jira su Oga Aliyu.
"Anacan anashan soyayya an barmu" cewar Ummie sanda na iso inda suke. "Ya ranki
ne?" na faɗa ina mata gwalo. Dariya su Zuhrah suka sanya mana, Ummie kuma tace,
"Fari ƙal, muma ai tana tafe garemu, a lokacin wasu sun tsufa". "Ko kuma mun zama
gwanaye ba" na bata amsa ina mangare ƙeyarta.
Yanayin yanda aka tsara wajen ya birgeni sosai wlhy, ga matansu Oga Jabeer sunata
aiki tuƙuru, gaisuwa mukai cikin girmama juna suna tsokanata wai har mun dawo daga
Honeymoon ɗin. Dariya kawai nayi bance komaiba. Muka rungume juna da Amina ina
tambayarta ya mama da yaya sule?.
Babu jimawa da zamanmu su boss suma suka shigo, bayan anyi ɗan gaishe-gaishen juna
matar Jabeer data kasance shugaba ta fara mana jawabin cigaban da aka samu musamman
ma ni da Boss da bamusan yanda ake ciki ba.
"Ƙasarnan danƙare take da cases na matsalolin fyaɗe, wasu sunma kai kotun amma
rashin gata yasa an watsar da shari'oinsu, daga baya an saki waɗanda suka aikata
laifin, wasu ko tsoro yama hanasu fitowa su faɗa. A yanzu haka dai munada ƙararraki
kusan saba'in da uku a cikin kwanaki goma sha shidda kacal da shelanta ƙunyar, mun
gama bincike akan ashirin da ɗaya kamar yanda muka sanar maka, mun tabbatar da
gaskiyarsu kuma harma munsa an kama wasu daga cikin masu laifin, wasu kuma muna kan
fakonsu, sai cases Goma sha huɗu masu kamanceceniya da irin wanda muke nema".
Kai Jawaad keta jinjinawa yanajin daɗi da ƙaunar abokan nasa, ya ajiye file ɗin
hannun nasa da matar Hafiz ta bashi yana gyara zama, "Wace shawarace da ku yanzu
akan goma sha huɗun da muka samu? Dan kunga idan muka haɗa da baƙwai ɗin dake ƙasa
sun zama ashin da ɗaya kenan".
Aliyu yace, "Hakane, ni dai a nawa ganin shine mu fara bincike akan gidajen da duk
abin ya faru, dan abinda zai baka mamaki da ɗaure kai waɗanda abin ya faru dasu dak
ƴaƴan masu gidan ne, ko ƴaƴan ƴan uwa, kuma babu gidan talaka, ƴaƴan talakawan da
tsautsayin ya hau kansu duk masu aikine a gidajen".
"Shawararka tayi Aliyu, yanzu zamu rarraba yaranan cikin ofisoshin waɗanda abin ya
faru a gidansu a gobe idan ALLAH ya kaimu, kowacce zata lurar mana da abu biyu, na
farko zobe, na biyu sana'ar mutumin ko aikinsa".
Duk kai muka jinjina masa na gamsuwa, daga haka aka ƙara ɗan tattaunawa muka fito
bayan an damƙama kowa aikin da zaiyi.............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


✍🏻
[1/22, 9:04 AM] HASNA : Billyn abdul:
Page 54

................Kanmu duk muka ɗaga mata, da amsawa da “Insha ALLAHU mama zamuyi
ƙoƙari, a cigaba da tayamu dai”. rakkiya tai mana har soro. Ganin ya nufi mota na
dubesa cikin rawar murya nace, “Yayanmu gidan Dad ɗin fa?”. Bai tankaminba yaja
hannuna ya turani mota shima ya shiga, Sadiq ya tayar muka bar anguwar.
Kallonsa nake idanuna cike da ƙwalla, ya juyo shima ya kalleni fuska a
cinkushe. “Kinsan idan kika bari hawayen nan suka zubo sai ranki yay matuƙar ɓaci
wlhy!”. Ƙasa na maida kaina ina ƙoƙarin haɗiye kukan dake neman ƙwace mani, bai
sake kulaniba har mukaje gida, kowa ɗakinsa ya nufa zukatanmu duk babu daɗi, sai da
na rufe ƙofar sannan na saki kukan da ya hanani yi amota irin mai cin rai ɗin nan
kuwa. Harnai wanka na fito hawaye basu daina min gudu a kumatuba, a haka na saka
wando da riga marasa nauyi nai sallar magriba, ina idarwa na fita kitchen, banji
motsinsa ba harna kammala girka abinda zamuci, na ɗauki na maigadi zan fita na kai
masa mukaci karo a ƙofa zai shigo. Uffan baice mani ba ya miƙamin hannu alamar na
bashi. Bashi nayi na juya ciki shi kuma ya tafi kai masa. Ɗakina na nufa dan banyi
sallar isha'i ba, ina farawa ya shigo. Ganin ina salla sai ya juya yana faɗin,
“Idan kin idan ki sameni falon baƙi”.
Koda na idar ban cire hijjabin ba na fita, ruwa na ɗauka sannan na
nufi falon baƙin, nai sallama suka amsamin da bani izinin shiga. Dattijon tsohon
nanne da muka haɗu da shi ranar akan zancen maman yara, na ajiye ruwa na zuba musu
sannan na zauna muka gaisa. Miƙewa na sakeyi dan na kawo masa abinci, ban jimaba na
koma da abincin, sakamin albarka baba yay tayi, shi kansa boss na fahimci yaji
daɗin hakan da nayi. Abincin ya faraci, boss kuma yana cigaba da latsa wayarsa ta
fama, tashi nai zan barsu yace, “Dawo ki zauna, magana zamuyi da shi yanason komawa
da wuri”. Na amsa masa da “to” na koma na zauna. Cikin ƴan mintuna Baba ya kammala
cin abincinsa yana sake sanya mana albaka, sai da ya sha ruwa sannan ya maida
hankalinsa ga boss. “Yauwa ɗana ina saurarenka”. Ajiye wayar boss yay yana furzar
da huci. “Baba kamar yanda na fara maka bayani shine ta wace hanya kake gani zan
iya shiga gidan domin ɗakko abinda tace? Matsalar shine a ɗakinsa tace abin yake,
ɗakinma a tsakkiyar ƙarƙashin gado”. Baba ya jinjina kansa yana gyara zama, “Wato
ɗana, ba wai ɗaukar ko shigar bace matsala ma, dole al'amarin sai da lura, su
shaiɗanun mutane irin waɗan nan al'amarinsu baya buƙatar fuska da fuska, kamar
yanda suke ƴan yaƙin sunƙuru haka masu cinsu da yaƙi ya kamata su kasance suma”.
“Hakane baba”. “Yauwa to kagani ni a nawama tunanin wannan aikin kam da mace yafi
dacewa ta wani ɓangaren, wani ɓangaren kuma namijinne, ɗakinsa dai bazai shigu
gareka matsayin namijiba cikin sauƙi”.
“Baba to mizai hana ni kawai naje”. Na faɗa kaina tsaye babu ko ɗar a raina.
Shiru duk sukai suka zubamin ido. Cikin jinjina kai baba yace, “Shawararki kam abar
dubawace, sai dai kuma ai bazai yuwu kije kai tsaye ba, sai dai mu duba wasu ƴan
dabaru haka?”.
Kafin nayi magana boss yace, “Baba bazai yuwu taje ba, mudai sake wata
shawarar”. Murmushi naga baba yayi kawai, cikin rawar murya nace, “Miyasa to? Yanzu
idan bajeba wa zamuce zamu saka wannan aiki? Ni a ganina baba zai iya ya kaini
gidan matsayin jikarsa, insha ALLAHU ni kuma zan ƙarasa sauran aikin inhar na shiga
gidan dai da matsayin da zan iya shiga wasu ɓangarori shikenan”.
Shiru yay bai tankaba, baba yace, “ƴata idan mijinki baya so karki matsa,
dan gaskiya wannan aikine mai haɗarin gaske, inaga zanje na ƙara tunanin wata
hanyar, kuma sai ku sakeyi, yazam dai kafin safiya idan ALLAH ya kaimu ya muna da
abinda muka riƙe, dan na tabbata nan da kwana biyu zai dawo daga tafiyar da yayi
yau da safe. zan koma dan banason a farga da bani bane a gate ɗin”. Godiya mukai
masa ya tashi yay masa rakkiya, ni kuma na koma ciki ina ƙunƙuni, dan insha ALLAH
zanta lallaɓasa nikam harya amince naje nai wannan aikin da kaina. Ganin halin da
maman yara take ba ƙaramin zaburar da zuciyata yayiba, na fahimci al'ummata na
buƙatar jajurtattun mata irin su ma

man yara, wayasan shekarun data ɓata domin bibiyar wannan tukunyar? Amma gashi har
tana a cikin magagin wahalar da aka bata bataji ta gajiyaba da son cimma
ƙyaƙyƙyawar manufarta ba.
Jin an taɓani na sauke sassanyar ajiyar zuciya, kujera yaja ya zauna idonsa a
kaina har lokacin. Kallonsa nai cikin ido ko gezau babu a karo farko na tarihin
rayuwata, dukda bugun ɗari-ɗari da zuciyata keyi haka na daure na dake ban cire
idanuna ba, “Kar kace a'a, dan ALLAH, mune ya dace muyi aikin nan basai mun saka
kowa a ciki ba, sannan bamu da isashen lokacin zaman yin tunni ko binciken wanda
zaiyi mana ma. ɗiyarsa ta ɗakko mana wayoyi ba shine ke nufin zata ɗakko mana
wannan ba kuma”.
Gani kawai nai idanunsa na ƙyalli tamkar hawaye sun taru a ciki, ya
girgizamin kai a hankali yana kauda kansa, hannunsa nai saurin kamowa cikin nawa,
ya sake juyowa ya kalleni, nawa hawayen ne suka silalo a hankali saman kumatu,
“Please yayanmu karkace a'a, nima ka barni nai hidima ga Umm-Anum kamar yanda tayi
a gareni tun batasan wacece ni a gareta ba, har raina jin ahalinka nake a zuciyata
da ɓargo, idan ka hanani yin wannan aikin zanji matuƙar zafi a raina bakuma zan
daina jiba har na koma ga ALLAH, dan zanke ganin kamar ni ɗin dan ba ahalink.....”
Jawoni kawai yayi jikinsa ya rungumeni batare da ya barni na ƙarasa faɗa ba,
da sauri-sauri zuciyarsa ke harbawa a ƙirjinsa, kamar yanda nima tawa keyi, cikin
kuka na sake cewa, “Please Yah Jayyyy”.
Jawaad ya lumshe idanunsa a hankali yana wani cije lip ɗinsa na ƙasa da
ƙarfi, “Jay” sunane da mafi yawan mutane ke kiransa da shi, bai taɓajin ambatar
sunan da wani banbanci na daban ba ga mai faɗarsa sai yau a bakinta, musamman ma
data ja “y” ɗin ƙarshe sai yaji gaba ɗaya tsigar jikinsa ta tashi.
Ɗagoni yay a hankali na sake zama sosai a kujerar dining ɗin, ya riƙe fuskata
a cikin tafukan hannunsa yana sharemin hawayen da babban yatsansa, muryarsa a shaƙe
yace, “Miyasa kema kin iya rigima ne Miemaa?, aini Kin riga kin gamai min komai a
rayuwa tunda kika zama sanadin haɗuwata da mahaifiyata”. Sake ɓata fuska nai alamar
tahowar wani kukan, nace, “To dan ALLAH ka barni na cika ladana”. Murmushi ya ɗanyi
mai ciwo yana sake turani cikin jikinsa, “Shike nan bar kukan haka, zanyi tunani
daga nan zuwa safiyar da yace insha ALLAHU, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi
alkairi”. “Amin” na faɗa ina murmushi.
Yau shine ya bani abincin da kansa, bayan mun kammala ya taimaka min muka
tattare kwanikan zuwa kicin, ina wankewa yana ɗaurayewa har muka kammala sannan
muka fito bayan na kammala tanadar abinda zan haɗa mana breakfast insha ALLAHU da
safe. Yau kam bamuyi zaman wani aiki ba, brush kurum mukai da yin shirin barci muka
kwanta. Babu jimawa barci yay awon gaba damu kuwa. Kusan ƙarfe uku na dare ya
tadani, alwala mukai muka shiga yin nafilfili domin miƙa buƙatarmu wajen mahaliccin
kowa da komai, mai rahama da ƙari ga bayinsa. Bamu sake kwanciya ba sai da mukai
sallar asubahi, da yake a gida yayi shima muna idarwa ya jani muka haye gado, zanyi
magana yasa tafin hannunsa ya rufemin baki ruf. Dole na haƙura muka kwanta, barci
kuwa yay cak damu zuwa duniyarsa.

Bamu farkaba sai 8:11am, nice ma na fara farkawar, na waro idanu a waje dan
ganin makarar da nake gudu dai ta tabbata, jawoni yay zai maida ya sake kwantarwa
nace, “takwas fa ta wuce boss”. Buɗe idanunsa yayi yana ɓata fuska, da alama ba
haka ya soba. Da ƙyar ya iya tashi muka shiga wanka tare, a gaggauce mukai muka
fito, batare da mun tsaya neman abinci ba muka shirya, tea ɗin dana haɗa manama
cayay muje masha a mota, shi dai maigadi ya miƙa masa nasa tare da kuɗi akan ya
sayo bread mun makara yau. A motar kuwa muka sha tea ɗin abin dariya da tausayi
(lol😂😜). Aiko yau ina rakasa office na fito dan ban kammala aikin jiyaba nima, a
ƙofar office ɗin naci karo da rose, ko kallonta banyiba nai gaba abina, harna sauka
ƙasa ina jiyo idanunta dake yawo a jikina, nidai ban fasa neman tsarin ALLAH da ga
sharrinta ba harna ɓace abina.

Kusan sha biyu da wasu mintuna ya kirani akan idan anfito salla nazo na
samesa. Amsa masa

nai da to ana idarwa kuwa can na nufa, shi kaɗaine a office ɗin yanata ayyuka, duk
da da alama shima yanzu ya shigo ɗin, ban zaunaba har sai da ya bani izinin zama.
Tasowa yay daga kujerarsa ya dawo ɗayar dake kallon wadda na zauna, ya kamo
hannayena cikin nasa yana mai tsareni da idanunsa nan masu takurani. “Miemaa na
amince kije gidan Alhaji kokino, amma da sharaɗi”. Cike da ɗoki nace, “Minene
shaɗarin?”. “Sharaɗin shine kwana ɗaya kacal da yini biyu zakiyi, idan yayi
tsaurine kikai biyu, sannan tare zamuyi aikin dan bazan taɓa barinki ki shiga
wannan aikin mai haɗari ke kaɗai ba”. Rungumesa nai saboda jin daɗi, hannu biyu ya
amsheni yana murmushi, nace, “Na yarda da duka sharaɗin, ALLAH ya bamu sa'a da
nasara”. Yace, “Amin Beejay, yanzu zaki tashi Sadiq ya kaiki gida kiɗan shirya,
shine zai kaiki inda zaku haɗu da baba, sai ya ƙarasa da ke”. “Wow da wuri haka?,
insha ALLAHU zaka sameni fiye da yanda kai tunani, kaida kaitamin addu'a boss ɗinmu
abin alfaharinmu”. Ɓata fuska yay cikin wasa yace, “ke da wa?”. Ganin yanda yay da
fuska ya sakani ƙyaƙyƙyawa da dariya, “Ni kaɗai mana, sai su oga Jabeer ”. Hararata
yay, “K nifa kibarma kirana da wani boss na gaji da ji”. Kunya naji sosai, dan haka
na ɓoye fuskata a ƙirjinsa ina dariya.

★★★★

Duk yanda muka tsara hakance ta kasance, bayan sallar la'asar muka isa gidan
Alhaji kokino, cikin shiri nake irin na ainahin garorin yaran nan na ƙauye da ko
karatu basu taɓa samu ba, ga matarsa kam mun samu tarbar mutuntawa, ƴaƴan gidanne
dai sai a hankali, dan gaba ɗaya halayensu baimin ba, sai wani famar min kallon
banza suke, musamman mai son boss ɗin nan. Shiru nai na maƙure jikin kuje alamar
tsorata ta baƙunta. Baba mai gadi da suka gama gaisawa da hajiya ya juyo ya
kalleni, “K Larai! Baki iya gaisuwa bane? nifa banason wannan ɗabi'ar banzar kin
sani”. Muryata na rawa nace, “Ina wuni hajiya, mun sameku lahiya?”. Dariya yaran
suka bushe da ita duka falon, irin wai ƙauyancina ne ya basu dariyar. Ita dai
hajiyar Murmushi tayi tana cigaba da kallona, tace, “Lafiya lau Larai, yasu mamar
taku?”. “Lahiya lumi suke aradu hajiya, tace tana gaiheki”. Saboda dariya har ƙasa
suke faɗuwa daga saman kujerun. A raina nace, ‘Wawaye kawai’.
Baba ne da yake ɗan murmushi shima yace, “Hajiya dama tazo daga ƙauye ne can
anguwar tudun birji wajen ƴar uwar mahaifiyarta, to saita iske wai sunje suna ko
ina, kuma sai jibi zasu dawo, shine nace data koma kuma ai wahala goma da ashirin
tazo nan saita kwana idan suka dawo sai taje, ALLAH yasa dai ban wuce gona da
iriba?”. “A'a Malam baka wuceba kam, ai kaga anyi zuminci tunda dama kaƙi kawo mana
iyalanka shekara da shekaru, ni nagode sosai da wannan ziyara”. “Nima nagode
hajiya, bara na koma bakin aiki to ga tanan”.
Ganin zai fita nai ƙwalƙwal da idanuna alamar kuka, “Kaka anan zaka barni?”.
Juyowa yay da ɗan faɗa yana min daƙƙuwa, “Kinci gidanku Larai, nanɗin cin mutane
ake bare kice za'a cinyeki? To idan hakan bai mikiba tashi ki kama hanyar ƙauye
idan su Rakkiyar sun dawo sai ki dawo”. Baki na tura ina maƙe kafaɗa, “Ni alkur'an
a'a”. “Ke kuma kika sani ja'ira kawai” ya faɗa yana ƙarasa ficewarsa. Yana fita
suka fara jana da hira wai na basu labarin garinmu, nasan sosuke kawai su ringajin
yanda nake magana suna dariya. Abinci aka kawomin, inaci ina basu labari kamar wata
sakara, suko sai kwasar dariya sukeyi da zagina a kaikaice.
Haka na maida kaina ƴar cali-calin ƙarfi da yaji a gidan Alhaji
kokino, sannan aiki duk dana gani zan tashi nayi kamar bansan ciwon kaina ba,
bansan inajin kewar mijina ba sai da dare yayi nazo zan kwanta a tabarmar ɗakin
masu aiki, hakan bai dameni ba, dan wannan ba sabo bane a gareni, kewar tasace dai
kawai naji, sai tunani nake yanzu koshi mi yakeyi? Oho.

★★★★

Yanda Bily ke cikin kewa a gidan Alhaji kokino haka Jawaad yake a gidansa,
tun da ya dawo daga wajen aiki duk sai yaga gidan yay masa wani faɗi da baƙi, yay
zaune a babban falo yanata kallon sashenta, da ƙyar ya iya tashi yaje yay salla,
koda ya dawo yaga zuciyarsa na ƙara ƙuntata sai ya fice daga gidan zuwa gidansu A

mina, baisan yawan zuwa gidan dan kar a fahimci akwai wani abu duk da yasan Dad
baya a garin, sannan ma ƴan gidan hankalinsu baya aƙwance saboda rashin ganin
Shahudah, shiko akan hakan yamaƙi zuwa ko family house ɗinsu tunda suka dawo, ya
kuma kashe wayar da kowa zai iya samunsa.
A gidan su Amina ya ɗan rage kewa, maman yara tace ya kwantar da hankalinsa
tanaji a ranta insha ALLAH bilkisu zata iya, dan a zuwan da sukayi jiya ta fahimci
tana da hankali da wayo. Kai kawai Jawaad shi dai ya ɗaga, zuwa tara ya baro gidan,
rasa mizaiyi yayi, haka dai ya koma gidan ransa duk a jagule. Tea kawai yasha yay
shirin barci ya kwanta a ɗakinta, jin zuciyarsa ta sake ƙuntata ya ɗauki waya akan
bara ya kirata ko muryarta yaji, sai da yaji switch up sannan ya tuna cewar bama ta
tafi da waya ba. Tsaki ya buga yana jefar da wayar a kan gadon, waishi mima yasa ya
barta taje ne?. haka yayta takaicinsa hardai daga ƙarshe ya sake ɗaukar wayar,
Anuwar ya kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka cike da ɗoki. Wannan kiran Anuwar shine ya
rage masa kewar Bilkisu a ransa, sunsha hira sosai dai sai kusan ɗaya da rabi na
dare sukai sallama, sai kawai yayo alwala ya hau salloli ma. Sai kusan uku ya
kwanta sai barci.

WASHE GARI

Washe gari ma haka na tashi cikin ƴan aikin nan duk abinda sukeyi dani
akayisa, babu wanda yace nabari a gidan, saima faɗa suke wai nafi masu aikin iya
aiki. Nidai bance komaiba, sai lokacin da hajiya ke faɗa akan mai gyara mata ɗaki
batayi da ƙyau ba, idan bazata iyaba a canja da wata. Murmushi nayi domin wata
damace ni a gareni hakan, dan haka nai caraf nace ni bara na gyara mata yau. “A'a
Larai, daga zuwa sai kita aiki? Aiba haka akeyiba”. “Lah hajiya karki damu, yo mufa
mun saba alkur'an, dafa a ƙauyene da yanzu inacan ina sirhe, yo ni ina zan iya da
wanga lalaci naku na mutan burni hajiya, ke dai bani aiki kiga aikin mata aradun
ALLAH yanzu na ƙalƙale miki ɗaki ko fadar mai garin garinmu bata nuna masa fita
ba”. Sunata dariyarsu niko na fuske abuna.
Zagewa nai naima ɗakin gyara na sosai, sai gashi hajiya na santi ita da
yaran nata, aiko ranar na aikatu, dan ɗakunansu sukaita sakani na gyara musu suma
yaran, duk da na gaji haka na daure dan fatana nidai a ƙarshe a turani ɗakin mai
gidan, amma sai naji tsit. Washe gari babu wanda ya sakani wani aiki, har yamma,
abin duk ya dameni inata addu'a da fatan samun hanyar da zan shiga ɗakin, dan a
yinin da nai jiya na aiki nazarin gidan naitayi da hanyoyin cikinsa. Kusan ƙarfe
huɗu da rabi ina zaune a can baya ni da ɗaya daga masu aikin gidan sai ga hajiya ta
fito, sannu duk mukai mata da gaisheta dan duk yau ban gantaba bata yini a gida ba.
Tace, “Larai Please zoki min wani ɗan aiki nan na dawo a makare”. “To” nace ina
miƙewa, wani irin farin ciki ya kamani ganin mun nufi sama, inda nake da tabbacin
turakar mai gidance anan. Fasalta muku yanda tsarin yakema ɓata lokacine, kowa ta
ƙiyasta tsaruwarsa kawai. Kallona tai tana ɗan murmushi, “Larai nan zaki gyaramin,
babu wata mai aiki dake shigowa ni nake gyarawa, to naje saloon da gyaran jiki sai
yanzu na dawo gashi lokaci ya ƙure, kuma Alhaji nanda takwas na dare zai iso yayi
tafiyane, na yarda da kene saboda kinada nutsuwa, dan ALLAH ki gyara komai ƙal
kinji, ni kuma zanje mu ɗaura masa abinci”.
Farin cikin da ke cin raina na danne, na amsa mata da “Insha ALLAH hajiya
zaki samu fiye da yanda kikeso” “Yauwa ƴar albarka nakuwa gode, bara na turo miki
Laila ta tayaki. Ɗaf ɗokina ya gudu, kamar zanyi magana sai kuma nai shiru harta
fice. aikin na fara ina tunanin yanda abin zai kasance, dan insha ALLAHU bazan fita
daga ɗakin nanba yau sai da abun nan.
Laila ɗaya daga cikin yaran gidan ta shigo ko sallama babu, bataimin magana ba
ta nema waje ta kwanta a cikin kujera tana danna waya, nima bance da ita komaiba na
cigaba da aikin, tsaf na kammala falon na saka fresheners dana gani da turaren
wuta, sannan na nufi bedroom ɗin. Ƙaton gaske ne shima kuma ya haɗu, sai dai gadon
irin gajere ɗin nanne wanda babu yanda za'ai ka iya leƙa ƙarƙashin gado balle harka
jawo abu. Wucewa nai toilet ina ƙullawa da kwancewa a raina

, gabana sai faɗuwa yake amma inata addu'a. Bayan na gama sai na ɗan fito falon dan
naga mi laila keyi. Tsaye na taddata ta tashi, ta kalleni tana faɗin, “Nazo na baki
bedsheet ko?”. Kaina na ɗaga mata alamar eh. Tare muka koma cikin ɗakin, ta buɗe
haɗaɗiyar Wadrobe ɗin ta ciro zanin gado mai ƙyau ta ajiyemin a ledarsa. Murmushi
kawai nai mata, a raina ina addu'ar ALLAH yasa ta fita, sai kawai naga ta ɗane sofa
ta kwanta. Kaina na dafe ina cije leɓe, wannan itace damar da nake da ita ta
ƙarshe, gashi kuma tana neman kufcemin. Jiki a sanyaye na fara yaye zanin gadon
dake a gadon, na ajiyesa gefe suma filolin na fara cire rigarsu, harna gama na saka
na wanda ta fiddomin, na ɗauki zanin gadon na fara shimfiɗawa, ina gab da gamawa
akai kiran wayarta, gani nai ta tashi tana murmushi, ta kalle ni tana faɗin, “Larai
banda aikin mugunta fa, ki tabbatar komai tsaf bara na amsa waya”. Kaina na ɗaga
mata ina murmushi, ta zare keys ɗin duka drawer ɗin ɗakin ta fita da su, bakina na
taɓe dan inda take bama tsaron ni bashine abin harina ba. Wata ajiyar zuciya na
sauke mai ƙarfi jin ƙarar rufe ƙofa alamar tama fita daga falon. Ban ɓata lokaciba
na yaye zanin gadon gaba ɗaya jikina na rawa, katifar na kama na ɗaga, bana ganin
abinda ke ƙasan gadon saboda an saka kwali bisa katakon shimfiɗar gadon, maida
katifar nai na ɗan fito falo na sake lalleƙawa, ganin babu kowa nai azamar dawowa
na sake ɗagawa, shima kwalin ɗagashi nai, addu'a naketa yi a raina nidai, ina ɗaga
kwalin wani hayaƙi ya taso ya bulemin ido, tari na farayi kamar zan mutu, na saka
hannu na toshe bakina dan kar wani ya jiyoni, saurin maida katifar nai saboda jin
kamar motsin tafiya, na cigaba da ƙoƙarin gyara gadon kamar dama shi nakeyi,
hajiyace ta shigo, ɗagowa nai naimata murmushi, itama dai fuskarta da murmushin
take faɗin, “Kai sannu da ƙoƙari larai, falon yayi ƙyau kuwa, an wanko bayi ko?”.
“Eh na wanke hajiya, yanzu nan zan ƙarasa kawai”. “Yauwa to sannu da aiki kinji,
ina Lailan?”. “Yanzun nan tafita inaga abu zata ɗakko”. “Okay to bara naje mu
cigaba da namu aikin muma, dama dan naga yaya aikin ke tafiyane shiyyasa”.
Ficewa tai, ni kuma na sauke ajiyar zuciya da lumshe idanu na buɗe lokaci guda,
hannuna dafe da ƙirjina. Yanzu kam a fili na fara karatun alkur'ani mai girma cikin
suratul baƙara, na sake ɗaga katifar da kwalin, baƙin maciji na gani kwance
idanunsa jajur, sai tukunyar ƙasa a gefensa an ƙulle bakinta da jan ƙyale. UBANGIJI
mai rahama da ƙari, sai ya sakamin dakiyar zuciya da ganin nasa, nama cigaba da
karatuna ina sake danne al'ajabi na, baya ya ringa ja daga gaban tukunyar, ganin
haka sai na cigaba da karatun nima, sai kawai naga ya sulala ya shige wani rami a
jikin bangon wanda bansan tayaya aka ƙirƙiresa ba. Cikin rawar jiki na ɗauka
tukunyar na fiddo, ina cigaba da addu'a, sai dai ƙirjina wani irin mahaikacin
bugawa ya keyi tamakar zuciyata zata faso ta fito, maida kwalin da katifar nayi, na
fito falo da tukunyar jikina har yanzu rawa yake, sai da na leƙa falon ƙasa na
tabbatar babu kowa sai tv kawai dake magana sannan na fito cikin sanɗa, addu'a nake
jikina kuma na wani irin tsumar rawa, ina ficewa a falon naji muryar cikin masu
aikin na faɗin, “wanene ya fita?”. Innalillahi na faɗa ina ƙara sauri, baba maigadi
yana hangoni ya taso, na tsaya bayan wata mota inata waige-waige, isowa yayi gareni
cikin sassarfa, na miƙa masa tukunyar ina magana da rawar murya matuƙa, “Baba, ka
kirashi yazo ya amsa yanzun, bara naje na ƙarasa aikin da aka sani karsu fahimci
wani abu”. Kansa ya ɗagamin kawai, na juya da gudu na koma, nai saurin daidaita
yanayina lokacin dana shiga falon, hajiya na iske tsaye, ta zubamin ido cike da
kallon tuhuma. “Keda kike aiki a sama mi kuma ya sakko dake ƙasa larai?”. Da ƙyar
na iya ƙaƙalo yawu na haɗiye ina murmushin ƙarfin hali, “Hajiya wani yana na gani
ta tagan ɗakin (Window) shine fa na zagaya dan na share sai naga ashe da nisa ta
waje”. Dariya naga ta tuntsure dashi tana girgiza kanta, “Banda abinki larai ba a
sama kikeba? Ki barsa akwai yaron dake sharewa zaizo ya share ranar weekend”. Kaina
na ɗaga mata, ta juya kicin ɗi

n ni kuna na nufi saman benen ina godema ALLAH da ya rufamin asiri. Sai dai
jikinafa har yanzu wani irin tsuma yakeyi, ga Masifaffen ciwon kai da alokaci ɗaya
ya saukarmin. Haka na daure na koma ɗakin, canma na iske laila tsaye tana ƙarema
ɗakin kallo, da masifa ta hauni akan ina naje? Kenanma tana fita nima na fita tunda
ga shi nan ko gadon ban kammala gyarawa ba. Haƙuri na bata duk da zamuyi sa'anni da
ita, na faɗa mata kamar yanda naima hajiya bayanin share yana. Tsaki taja min tana
faɗin, “Malama kiyi sauri ki gama inada wajen zuwa”. Kaina na ɗaga mata kawai a
sanyaye na hau gyaran gadon, yanzunkam tsaye tayi a kaina harna kammala aikin,
hakan bai dameniba tunda naci nasara, na saka turaren wuta muka fito tare ina dafe
kai saboda ciwon da yakemin.

★★★★★

Jawaad na tsaka da aiki a office, sai dai rabin hankalinsa duk yana ga
Bilkisu, tunda ta tafi basuyi ko waya ba, sai dai baba na faɗa masa tana cikin
ƙoshin lafiya ya cigaba da mata addu'ar nasara. Wayarsa da tai ring ya duba, ganin
baba ne yay saurin ɗagawa babu ɓata lokaci. Ko gaisuwa baba bai jira sunyiba yace,
“Duk inda kake ka taho nan yanzun, yarinyarnan ƴar albarka tayi nasarar ɗakko
tukunyarnan gata a hannuna ma”. Zaram Jawaad ya miƙe tare da wancakalar da takardun
gabansa, bai saurari ɗaukar komaiba ya fice, key ɗin motar ya amsa a hannun Sadiq
yace ya zauna ya jirashi dan da kansa zai tuƙa motar.
Gudu yake na tashin hankali kamar titin nasane shi kaɗai, tsabar karya samu
cinkoso ma sai ya ringabi ta wasu hanyiyin daban yana ratsema duk titin da yasan
zai iske go-slow. Acan bayan layin suka haɗu da baba maigadi daya fito daga gidan
akan yaje salla, da yake anata kiraye-kirayen sallar magriba ne. Miƙa masa kawai
yayi batare da sun tsaya doguwar magana ba, “Maza kaje ka fasata Jawaad, karka
tsaya ɓata lokaci”. “To baba, amma matata fa?”. “Kaje itama zan fiddota yanzu dana
koma, dan tabbas akwai haɗari babba Alhaji ƙarfe takwas zai sauka ƙasarnan, duk
inda yake a halin yanzun kuma nasan yaji a jikinsa an ɗauka tukunyar
nan.............✍

ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻


✍🏻
[1/22, 9:04 AM] HASNA : Page 55

.................“Baba bazan iya barin anguwarnan ba sai da ita”. “Bazai yuwuba


Jawaad, kaje itama insha ALLAH lafiya zata fito, dana koma yanzu zan fiddotane
itama”. “Baba kaima fa bazai yuwu ka zaunaba, dan zamanka akwai haɗari Sadiq zaizo
ya ɗaukeku tare, kaje ka haɗa duk wani abunka mai muhimmanci”. “To shikenan ɗana,
ALLAH yay maka albarka sai ya zo”.

CIKIN JIRGI

Tun ɗaga gadon farko da Bilkisu tayi jikin Alhaji kokino ya bashi, to
amma yasan akwai mai tsaron wajen koma waye tsautsayi ya kaisa sai dai gawarsa. Sai
dai kuma ƙarfin gwiwarsa ta sare lokacin da yaga zoben dake a hannunsa yana canja
kala zuwa baƙi, gabansa yay matuƙar faɗuwa, gashi babu damar kiran waya, a take
komai nasa ya fara kwancewa lokacin da zobe tsafinsu ya shiga hasko masa abinda
bilkisu keyi, sai dai ALLAH ya hanashi ganin fuskarta sam sai duhun inuwarta kawai
yake gani harta ɗauki tukunyar data ɗauki tsawon shekaru a jiye babu wani mahaluki
da ko yatsansa ya taɓa taɓata, sai maman yara da idanunta suka gani itama kuma
saida ya sakata tai nadamar hakan, tanama can cikin nadamar ma (Masu karatu Alhaji
kokino fa baisan yanzu maman yara bata wajen yaransa ba, dan randa ƴarsa ta saka
masa maganin barci koda ya farka a washe gari har an maida masa wayoyinsa, babu
wata kuma alama da Jawaad ya bari dazai iya zarga, shikuma da yasan babu wani
mahaluki da zai iya masa makamancin haka sai bai kawo komai a ransaba, a washe
garin ya bar ƙasar batare da yayi waya da yaransa akan komaiba. ALLAH kuma ya hana
shaiɗanun dake taimaka musu fahimtar komai balle shugaban nasu na dodon tsafi damar
sanar masa.
Gaba ɗaya ya jiƙe da uwar zufa sharkaf kamar ana masa wanka da ruwan zafi,
jiyake tamkar ya rikito jirgin ƙasa dan tsabagen tashin hankalin da yake a ciki,
gashi sauransu kusan awa ɗaya da rabi kafin ma su sauka. Lallai wannan ko wanene a
cikin gidansa sai ya ƙarar da dukan ahalinsa bama shi kaɗaiba.
Jawaad kam kai tsaye gidan Alhaji babba ya nufa, sun fito masallaci kenan
sai ganin Jawaad ɗin yayi ya fito a mota, sai dai yanayinsa yay masifar ɗaga
hankalinsa. Tambayoyi ya shiga jera masa, Jay dai bai amsa masa ko gudaba a ciki
ba, “Baba wannan ba lokacin amsa tambayoyi bane”. Ya faɗa yana nufar cikin gidan da
tukunyar a hannunsa dan da duk a wajen gate suke inda Jawaad ɗin ya faka motarsa.
Alhaji babba da ciwon ƙafa ya matsamawa a kwanakin nan ga yawan mafarke-mafarke da
faɗuwar gaba da yake yawanyi yabi bayan Jawaad jiki a sanyaye, iskesa yay tsaye
tacan bayan ɗakunansu ya ɗaga tukunyar zai fasa bakinsa ɗauke da addu'a. “Kai wai
minene kake haka? sai kace wani matsafi?”. Jikake “Tassss!” Jawaad ya buga tukunya
da ƙasa.
Fashewarta tayi dai-dai da faruwar abu uku a zahiri, biyu a ɓoye.

Na farko shine saukar jirgin da alhaji kokino ke a ciki bisa ƙasa. Na biyu
mummunar faɗuwar gaba ga duk masu alaƙa da tukunyar, na uku faɗuwar Umm-Anum dake a
kicin tana dafama Abbu shayi da yake a gidanta yake yau. Na baɗinin kuwa daga can
fadar shaiɗancinsu ya faru.
Wasu irin mugayen layune manya-manya guda uku a ciki, sai ƙananun allurai
da wasu irin abubuwan surkulle da baisan minene ba shima, sai ruwan kuwa da suke
ciki na jini ne sai wani uban wari ya keyi maiban tashin hankali, Alhaji Babba ya
waro idanu waje jikinsa na rawa da toshe hancinsa da hannu yace, “Muhammad minene
wannan? A ina ka samoshi ni Nuhu?”. Taga-taga Jawaad yay zai faɗi idanunsa a
matuƙar jazur, Alhaji babba yay saurin riƙosa. Atare suka sauke ajiyar zuciya, da
sauri Jawaad ya zare hanunsa daga na Alhaji babba ya nufi cikin gidan, hankalin
Alhaji babba sake tashi yayi, ya kalli tukunyar da kayan ciki ya kalli hanyar da
Jawaad yabi, ya juya zai bishi sai gashi ya fito ɗauke da ashana da gallon ɗin
fetur na Genretor. Akan kayan ya zuba ya ƙyasta musu wuta. A take gidan ya ɗauki
wani irin mahaukacin ƙauri mara daɗin shaƙa, sai ƙananun motsi kamar ana guje-guje,
suka hau waige-waige suna dafe kunnuwansu da hannu da sauri, sai kuma aka fasa kuka
da wata irin murya mara daɗin saurare. Ana ƙwalla kiran sallar isha'i gidan kuma
yay tsitt dan masallacin idan aka kira salla kakanji tamkar a cikin gidan akeyi
tsabar kusancin da suke dashi. Jagwab Jawaad ya zauna a ɗan dakalin da aka shuka
fulawoyin gidan, ya dafe kansa yana karanto hasbinallahu wani'imal wakil. Sai kuma
ya miƙe zumbur saboda tunawa da bilkisu da baba, lallai duk inda Alhaji kokino yake
yanzu jirginsu ya isa sauka ƙasarnan. “Baba ina zuwa ya faɗa yana nufar gate cikin
zafin nama. Sake binsa da kallo Alhaji babba yayi harya fice.
Jay ya buɗe mota zai shiga saiga drivern gidan Ummah babba ya kawo Batool,
baiko kallesu ba duk da ɗaga masa hannu da takeyi ya buɗe motarsa ya shiga tare da
yin reverse yabar anguwar da mahaukacin gudu kamar zai tashi sama.

★★★★

Tun ina ɗaukar ciwon kai wasa har ya fara neman fin ƙarfina, dan idanuna
sun fara rufewa bana ganin abu da ƙyau, innalillahi wainna'ilairraji'un naketa
ambata da sauran addu'oi. A wannan halin lariya ta shigo ta sameni ɗaya daga masu
akin gidan. “Larai kije inji hajiya”. Gabana ne ya faɗi, dan a tunanina kodai ta
gane wani abune?.
A babban falo na iskesa tsuggune ita kuma tana daga tsaye da hijjab jikinta
alamar salla tayi, “Haba dai baba, ai bai kamata ace a darennan zata wuceba, gashi
bamu tanadar mata komai ba, kacema wanda yazo ɗaukar nata yayi haƙuri sai da safe
sai ya dawo su tafi”. Baba da gabansa ke faɗuwa yace, “To hajiya banƙi ta takiba,
amma da anyi haƙuri sun tafin dai babu damuwa, idan ta gama kwanakinta a can ɗin
saita dawo nan ta ƙara miki kwana ɗaya daga nan saita wuce”. Shiru tai kamar bazata
amsaba, sai kuma tace, “To shikenan na amince da wannan shawarar taka, bara na basu
ko kuɗin motane, amma dan ALLAH fa kartaƙi dawowa”. “Insha ALLAHU zata dawo
Hajiya”. Kallona tai da ɗan murmushi, “To larai kije ki ɗakko kayanki anzo
ɗaukarkine”. Kaina na ɗaga kamar banason tafiyar jikina a sanyaye, ta nufi sashenta
ni kuma na nufi ɗakin da aka saukeni na ƴan aiki, ƴar bakko ɗin kayana na ɗakko na
fito bayan nama sauran sallama, kaina ne kemin ciwo sosai, dauriya kawai nakeyi.
Dubu biyar hajiya ta bani, nai mata godiya da cewar ai zan dawo na sake mata
kwana biyu kafin na tafi, da haka mukai sallama. Muna fitowa daga cikin gidan ana
yin horn a ƙofar gate. Wani irin Masifaffen faɗuwa gabana yay, shi kansa baba mai
gadi a take ya diririce, saurin nunamin ɗakinsa yay yace na shiga ciki, shi kuma
yaje ya buɗe gate ɗin.
Drivern Alhaji kokino ya danno kan motar da sauri, kamar yanda baba ya saba
duk sanda ya shigo gidan zaije su gaisa kafin ya shige, yanzunma hakan yayi, sai
dai sama-sama Alhaji kokino ya amsama baba maigadi, yay ciki da masifar sauri
tamkar zai tashi sama. Drivern ya kalli Alhajin ya kalli baba maigadi yana faɗin,
“Anya kuwa lafiya gidan nan yake yau? Tunfa a filin jirgi yake azalzalata kamar
wanda akace gidansa naci da wuta”. Baba maigadi yace “kadai bisa da jikkar ka
dawo”. Yana ganin drivern shima ya shige yay saurin nufar ɗakinsa, jikkarsa daya
gama haɗawa Bilkisu ta haɗo da tata ta fiddo, ƙofa ya buɗe mata ta fice da sauri
shima ya rufa mata baya, suna fitowa Jay na isowa wajen, da sauri bily ta buɗe gaba
ta shiga baba kuma ya shiga baya, jan motar yay da gudu yabar anguwar.
Da gani har baba muka sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma naji
hawaye na gangaromin a fuska a hankali, kife kaina nayi saman jakunkunanmu dana
shigo dasu kawai na cigaba da kukana, babu wanda yay magana a cikin motar har muka
iso, sai sheshshekar kukana kawai.

___________________________________

Ɓangaren Alhaji kokino kam koda ya shigo falon sama yay cikin sassarfa,
sam bayama jin sannu da zuwan da ƴaƴansa suke masa harda ma matar tasa. Kaɗan ya
rage babbar rigarsa ta taɗesa ya faɗi a step na bakwai, yay azamar riƙe ƙarfen
ALLAH ya soshi bai faɗinba.
Matarsa da abin ya girmi kanta tuni ta take masa baya da hanzarinta, sai dai
tana zuwa ƙofar ɗakin sai ta jita a datse alamar ya kulle kansa. Duk da bayau ya
fara mata hakanba sai taji na yau yay mata zafi, ta shiga buga ƙofar tana ambatar
sunansa amma ko tari bataji yayi ba. Tana nan tsaye hankalinta a matuƙar tashe ya
buɗe ƙofar da ƙarfi ya fito, jikinsa sai ɓari yakeyi.
“Alhaji lafiya wai?”. Maimakon ya bata amsar tambayarta sai cayay, “Wanene
ya shigarmin ɗaki?”. “Alhaji ban gane wannan tambayarba, wanene zai shigar maka
ɗakin bayan ni?......” “K!! Bansan iskanci, uban wanene ya shigarmin ɗaki?!!”.
Yanda yay maganar tamkar zai haɗiyeta da mugun hargagi kuma sai duk ta firgice,
jikinta na rawa ta shiga girgiza masa kai, “Alhaji babu wanda ya shiga wlhy sai ni,
sai ko jikar baba maigadi da nasa ta gyara maka saboda aiki yamin yaw.....” wani
irin wawan mari ya ɗauke fuskarta dashi jikinsa na rawa. “Sau nawa zanmiki gargaɗi
akan saka wani yaymin gyaran ɗaki a gidan nan?!!”. Yanda jikinsa ke karkarwa dolene
ya bama mai kallo tsoro, tunda take da shi ko sanda yay auren amaryarsa yana mata
wulaƙanci saboda asirin waccan bai taɓa ɗaga hannu a kantaba ko murya irin haka,
gashi gaba ɗaya tama lura baya a cikin hayyacinsa, mike damun mijinta haka ne? Mi
Larai ta aikata masa a ɗakin da ita bata ganiba? dan yanzu ta shiga ta gama haɗa
masa ruwan wanka ta kuma ƙara Air Fresheners a ciki bayan ta shirya masa abinci a
dining....
Cikin wata gigitacciyar tsawar ya kuma cewa, “Ina yarinyar take?!!!”. Share
hawayenta tayi ta nufo ƙasa tana kiran larai, shima biye yake da ita yana baza
idanu da babbar riga yaga ta ina larai zata ɓillo?. Sai dai tun kafin su sakko
ƙasan ma ƴaƴansa da ma'aikatan gidan harsun bazu nemanta suma.
“Momy wlhy fa Larai bata gidan nan”. A rikice hajiya tace, “Ban gane bata
gidan nanba, yo ina zataje?”. Kafin wani cikinsu ya bata amsa Alhaji kokino yace,
“Wai ita laran ƴar gidan uban wacece? Da ga ina kuka samota?!!”. “Dady jikar baba
maigadi ce” laila ta bashi amsa a tsorace.
“Maigadi?!!” ya faɗa a wani irin zazzaro idanu, kafinma wani yace wani abu
tuni ya fice daga falon zuwa gate, driver kawai ya iske akan bench a zaune yana
ƙoƙarin zuba abincin da aka kawo musu daga cikin gidan. “Kai Mati ina maigadi?!”.
Yanda Alhaji yay maganar ne ya saka driver sakin plate ɗin abincin ƙasa a tsorace,
“Alhaji lafiya kuwa?”. “Ina tambayarka maigadi kana tambayata kafiya?!”. “Ayi
haƙuri Alhaji, yana bayi inaga, nima dana fito ban gansaba, nasan dai bazai wuce
banɗaki ya zagaya ba”. “Ƙwanƙwasa masa maza ya fito” tashi driver yay ya nufi cikin
ɗakin maigadi, sai dai yana taɓa ƙofar toilet ɗin da nufin bugawa sai kawai yaga
tama buɗe da kanta, ya leƙa babu alamar mutum, kai da ganima ba'ayi amfani da
ruwaba yanzun dan bayin a bushe yake ƙamas. fitowa yay da sauru yana faɗin, “Wlhy
bayanan ashe”. Shaƙosa Alhaji kokino yayi yana faɗin, “Idan baya nan dan ubanka ina
yaje?!” sosai hankalin kowa ya ƙara tashi, dan ya koma musu tamkar wani zararre.
Jikin driver sai rawa yake dan yaji shaƙa, Alhaji kokino ya wullar dashi gefe ya
shiga ɗakin da kansa. Hakan yasa Hajiya ta sake take masa baya duk da a tsorace
take. Abun mamaki duk kayan baba maigadi babu su, sai abinda ba'a rasaba waɗanda
sam basu da wani muhimmanci ga mai su. A yanzune hajiya ta fahimci lallai akwai abu
a ƙasa kenan. A fili tace “Mi hakan ke nufi to?”. Cikin tsananin tashin hankali
Alhaji kokino yace, “kezan tambaya Nafisa, shikenan kin kasheni Nafisa, taya za'ai
har wani ya kawo baƙon ido gidan nan kai tsaye ki yarda da shi harki bashi damar
shigarmin ɗaki?!!”. “Wlhy Alhaji ni....” hankaɗeta yay gefe batare da ya jira ta
ƙarasa faɗaba, ya fice da saurinsa yabar mata ɗakin, kuka mai tsuma rai ta fashe da
shi a ranta tana mamakin miyasa baba maigadi zaiyi haka? Shekaru nawa suka ɗauka
tare bai taɓa cutar da suba sai a yanzun? shin minene maigadi yasa Larai ta aikata
ne? Ta tuno fitarta ɗazun lokacin da take mata tambaya akan ina taje ita da aka
saka aiki? Tabbas ba cikin nutsuwa larai ta bata amsa da cewar yana ta fita sharewa
ba, amma da yake bata kawo komai a ranta ba sai bata zargeta ba.

SAUDIA

Hankali tashe Anum ta ƙwala kiran sunan Abbu da Anuwar dake falo suna
jiran shayi, har rige-rige. isowa suke cikin kicin ɗin, ganin Umm-Anun yashe a ƙasa
yay masifar ɗaga hankalinsu, Anuwar ya tallafo kanta ya aza bisa cinyarsa yana mai
fashewa da kuka, Abbu ne yay ƙarfin halin komawa ya ɗakko goran ruwan zam-zam ya
dawo, a hannu ya zuba ya shafa mata a fuska. Ta kawo wani irin nannauyan numfashi
da gurnani, ƙara ɗiba yay ya zuba mata a fuskar, nanma tagwayen ajiyar zuciya ta
sauke a jajjere. Matsawa yay sosai yana ambatar ainahin sunanta, BILKEESU!
BILKEESU!!, BILK...... Da sauri ta buɗe idanunta tana amsawa da “Na'am BAB......”
sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa ta kafe Abbu da ido, saurin janyewa tai ta
maida kan Anum, sai kuma ta kalli Anuwar da take a jikinsa. Cikin ɗan rawar baki
tace, “Jawaad!”. Abbu da Anuwar suka kalli juna, sai kuma suka kalleta, zaune ta
tashi tana raba idanu a kansu, sai kuma tai saurin dafe kanta tana faɗin, “Ya
ALLAH”. Riƙe mata kan Abbu yayi yana faɗin, “Sannu, kinga tashi muje ɗaki”. Bata
musaba ta yarda ya taimaka mata suka fita, sai faman lumshe idanu take saboda jiri.
Kwantar da ita yay a saman gado ya ɗaura kanta bisa cinyarsa, umarni ya bama
Anuwar ya ɗakko masa wani magani a ɗakinsa, babu jimawa Anuwar ya dawo, cayay ya
zubashi a abin turare, nan danan hayaƙi mai ƙamshi ya fara tashi a ɗakin, shi kuma
ya shiga karato addu'oi yana tofa mata. Cikin mintunan da basu gaza biyarba barci
yay awan gaba da ita. Duk ajiyar zuciya suka sauke, kafin Abbu ya gyara mata
kwanciya suka fito falo suka barta.
Cikin ɗaurewar kai Anuwar yace, “Abbu Yah Jawaad fa ta kira”. “Naji Anuwar,
amma lallai akwai wani abinda ya faru inaga, dan yanayinta yayi kama dana wadda ta
dawo hayyacinta gaba ɗaya, dan a farko sunan baba zata kira ganin nine yasa tai
shiru”. “Abbu to kona kira Yah Jawaad ɗin muji?” kansa ya ɗaga masa alamar eh.

★★★★★★★
Su Jawaad na zaune a falon Alhaji babba sun rufu kan bilkisu da keta juye-
juye a ƙasa da kukan kanta suna mata addu'a kira ya shigo wayarsa da Numbers ɗin
ƴan saudiyyane kawai a ciki, ɗagawa yay yana miƙewa, daga can Anuwar ya gaishesa,
sama-sama ya amsa masa da tambayar “ina Ummuna?”.
“Gata a kwance barci ya ɗauketa, dan tana kitchen zata haɗa mana shayi kawai
sai ta faɗi, ALLAH yasa Anum na tare da ita, sai dai abin mamaki ana saka mata ruwa
ta kawo numfashi saita fara ambatar Baba saboda Abbu da ya kira sunanta, ni kuma
tana kallona saita kirani da sunanka”. Lumshe idanu Jawaad yayi hawaye masu zafi
suka ziraro masa saman fuskarsa, kafin yace wani abu yaji maganar Alhaji babba a
bayansa. “Mi kuke ɓoyemani?”.
Duk da gabansa ya ɗan faɗi sai ya matsa ya rungume Alhaji babba ya saki wani
irin kuka mai tsuma zuciya wanda bai taɓa sanin ya iya irinsaba. Cikin matuƙar
tsorata Alhaji babba shima ya riƙesa hannu bibbiyu, “Muhammad karka rikitar dani,
minene ya faru dan ALLAH? Kai ne da kuka kuma?”. “Abubuwa da yawane suka faru baba,
sai dai dan ALLAH kaimin alfarmar yimaka bazata a kansu daga nan zuwa gobe idan
ALLAH ya kaimu”. “Namaka Jawaad, ALLAH yay maka albarka”. Ɗagowa Jay yayi yana
jinjina kai, Alhaji babba ya share masa hawayen, da ƴar tsokana yace, “Yau maza sun
koma mata kenan?”. Murmushin ƙarfin hali kawai Jay yay masa, amma bai iya cewa
komaiba.
Ciki suka koma inda suka samu Bilkisu taɗan samu barci, tana jikin Batool da
bata wuce gida ba. Kallonsu yay sannan ya kalli Bilkisun, “Baba bara mu wuce gida,
shi baba zai kwana nan gidan kafin zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu, kema Batool ki
tashi kije gida dare nayi, amma dan ALLAH karki gayama su Ummah komai sai zuwa gobe
idan ALLAH ya kaimu zakuji koma mike faruwa”. Kanta ta jinjina masa, tace “To ya ya
za'ai da mai sunan hajiya, bai kamata a tada taba tunda yanzu ta samu barcin”.
“Karki damu bara na ɗauketa kawai”.
Cak ya ɗauki bilkisu duk da yana jin nauyin su Alhaji babba, sai dai babu
yanda zaiyi idan ba haka ɗinba. Sallama yay musu ya fito, Batool dake biye da shi
ta buɗe masa baya ya kwantar da ita, sannan ya koma mazaunin driver ya zauna, ita
kuma ta nufi inda driver ke jiranta. Kusan tare suka bar anguwar. Sai da ya isa
gidane yama tuna da Sadiq da ya baro a office, hankalinsa a tashe ya ɗauka waya yay
kiransa, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, “Sadiq badai kana nan kana jiranaba har yanzun a
station?”. “Ina nan wlhy Oga, harma dasu oga Aliyu”. “Ya salam, kayi haƙuri kaji,
ka tafi gida kawai dare yayi, suma kace musu ina gida karsu damu”. Daga can Sadiq
yace, “To oga”.
Bayan ya ajiye wayar ya buɗe ya fito, sake ɗaukar Bilkisu yayi zuwa cikin
gidan, ya shinfiɗeta a gadon ɗakinsa sannan ya koma motar ya ɗauka wayoyinsa. Kiran
Anuwar ya sakeyi, ya tabbatar masa har yanzu Umm-Anum barci take, Abbu ya bama
wayar sukaɗan yi magana sannan ya kashe, ya zauna a bakin gadonsa ya tsirama
Bilkisu dake barci ido, gani yay harma taɗan rame masa a kwana biyun nan, wani
tausayinta ya kamashi, matarsa ta isa a kirata jaruma a ko ina, shi harma baisan
yanda zai musalta yaya ya keji a kanta ba, gadon ya hau ya rungumeta a jikinsa yana
sauke ajiyar zuciya a jajjere kamar wanda ya haɗiyi wuta.

DAREN ALKAIRI KO RUƊANI?.

Dolene mu ambaci wannan dare da sunaye masuma yawan da sukafi haka a


ɓangarorin mutane masu yawa. Jawaad, Alhaji babba, baba maigadi, Maman Amina, Yaya
sule, Abbu, Abu-Siddiq, Anuwar, Anum, aunty Mahfuzah, da wasu gungun mutane sun
ƙare wannan dare daga farkonshi har ƙarshensa wajen miƙama UBANGIJI godiyarsu da
kukansu, a tsakkiyarsa ALLAH ya bama bilkisu da Umm-Anum damar farkawa suma sukabi
ayarin masu bautar ALLAH da raya wannan dare da ƙiyamul laili.
A ɓangaren Alhaji kokino kuwa da duk mai alaƙa da wannan tunkuya wannan
dare ya kasance daren tashin hankali da ruɗani a garesu. Babban tashin hankalinma
shine kowa ya gaza fasalta kamannin bilkisu a gidan balle ai maganar samun hotonta,
sannan baba maigadi tunda suke dashi basu taɓa tambayarsa garinsu ba, abinda kawai
suka sani daga ƙauye yake, wane ƙauye? Shine basu saniba, bayan kuma ya kai kusan
shekara ashirin yana musu aiki, tsabar bashi bane a gabansu ba basu taɓa bibiyar
komai nashi ba a rayuwa, dan shi Alhaji kokino wani irin mutum ne da abinda ke
damuwarsa shine kawai mai muhimmanci a garesa. Bai taɓa takaicin wannan baƙar
halayyar tasaba sai a yau ɗin nan.
Tun a daren aka baza jami'an tsaro neman baba maigadi, sai dai shiru
kakeji, sudai sunce suna kan aikinsu. Daga can kuma tushen tsafinsu sam an kasa
ganin inda su Bilkisu suke, abinda kawai suka gani shine an fasa tukunya.
A daren duk wani mai alaƙa da wannan ƙungiya aka sanar masa gobe akwai mitin,
duk inda kake dolene ka dawo dan gagarumin mitin ne mai muhimmancin gaske.

SAUDIA

Tunda aka idar da sallar asubahi a ƙasar Abbu ya zaunar da Umm-Anum ya


zayyane mata komai da ya sani game da ita dan su gwada suga ko hankalinta ya dawo
jikinta sosai. Aiko a take ta shiga rairai masa kuka da roƙon Abbu akan ya kaita
wajen ƴan uwanta, tanason tagasu, ita ba zata sake kwana a saudia ba sai ta dangana
da ƙasar haihuwarta.
Da ƙyar suka lallasheta shi da Su Abu-Siddiq da su Anuwar. saboda gudun zuwan
irin wannan ranar a bazata yasa Abbu bai taɓa sakaci da duk wani abinda zai
taimakesa akan fita ƙasar ba idan Umm-Anum ta dawo hayyacinta, dan haka ya bata
haƙuri akan ta kwantar da hankalinta zasu tafi a yau ɗin nan komai dare insha
ALLAH.
Gari na ƙarasa wayewa suka fita shi da ɗan uwansa Abu-Siddiq, abinka da
manyan mutane cikin amincin ALLAH sai gashi cikin awa uku sun kammala dukkan wani
abinda ya dace, jirginsu zai tashi ƙarfe sha ɗaya na agogon ƙasar. cike da farin
ciki suka kirasu a waya tunkan su ƙarasa akan su fara shirin tafiya. Ai Umm-Anum da
Anum sunfi kowa ɗoki, Anuwar kam ai ba'a cewa komai, kayansa ya loda na fitar
hankali, a cewarsa saiya more ƙasarsa da ƙyau, ya kuma more ƴan uwansa da bai sani
ba. Sudai dariya sukaita masa kawai.

__________________________________

Da safe na tashi Alhmdllh, dan babu ciwon kan sam sai rashin jin ƙwarin
jiki, ganin gidan yay ƙura naɗan tashi na fara gyarawa, amma yana shigowa sai ya
hanani yace na barsa anjima Nabeelah zatazo ta gyara, yanzu muɗan sake kwanciya
zuwa goma saimu fita zuwa gidan Dad zan ɗakko ɗayan wuri ɗin nan da nace na taɓa
tsinta.
Haka kawai sai na samu kaina da faɗuwar gaba mai tsananin gaske, dan kuzarin
dana tashi da shi ya ida kakkaɓewa gaba ɗaya. Barcin da yaso muyi sai ya ƙauracema
idanuna, harma shi yayi nasa ni idona biyu inata saƙawa da kwancewa, ga mafarkin
danayi a daren jiya kafin na tashi naga yana salla nima nayo alwala sai dawomin
yake a cikin rai. Da tunane-tunane na cinye nawa lokacin barcin, harma goman tayi
ya farka. Kallon tuhuma yayta bina da shi akan banyi barciba, na dai fuske abina
bance da shi komaiba. Tare mukai wanka, hakama shiri da taimakonsa na shirya dan
duk bani da wani ƙarfin zuciya balle akai gana jiki kansa. Muna gama kimtsawa mun
fito sai ga Nabeelah da breakfast.
Zama mukai mukaci, koma nace yaymin ɗura, dan ko lauma ɗaya ban iya kaiwa
bakina ba, sai da taimakonsa, daga ƙarshema sai na ringayin yunƙurin amai, dole ya
ƙyaleni da iya abinda naɗanci muka fita muka bar Nabeelah a gidan akan bazamu
jimaba zamu dawo, dan dama ai yau juma'a ce..

Tunda muka bar gidan babu mai iya ƙwaƙwƙwaran motsi, nai shiru inata
kallon hanya da sauke ajiyar zuciya, shima haka yay shiru idanunsa a rufe.
Kai tsaye ya bama Sadiq umarnu akan yay horn a ƙofar gate ɗin, haka kuwa
akayi, Sadiq yayi horn, sai da baba maigadi ya leƙo, ganin mune sannan ya buɗe gate
ɗin.
Kasa fitowa nai sai da ya fita sannan ya zagayo ya fiddoni, jikina ya ƙarayin
sanyi, ga hawaye sun cikamin ido, narasa dalilin shiga irin wannan yanayin haka?.
Yah Salman da ya fito daga sashensu daga shi sai wando da singlet yay turus yana
kallonmu, boss yi yay tamkar baima gansa ba, sai nice nace, “Yah Salman!”. Da ɗan
rawar baki ya amsa saboda wata muguwar harara da boss ya zuba masa, kafin ya ƙara
da faɗin wani abu yaja hannuna muka shige falon da sallama.
Mom na zaune tayi wujiga-wujiga da waya a hannunta, da alama magana ta gamayi
a ciki, sai Aamilah a gefenta ta zabga tagumi. A tare duk suka kallemu da waro
idanu na maɗaukakin mamaki da al'ajabi. Bayan boss na koma na laɓe, shiko ko'a
kwalar rigarsa murmushi ma yaketa zubawa. Zama yayi ya kamo hannuna ya zaunar a
gefensa.
“Mom kun tashi lafiya?”. “Kuka ta fashe da shi kawai tana nunamu da hannu,
sai dai tama kasa magana gaba ɗaya. “Kinga kwantar da hankalinki Mom, ba wani abune
ya kawomu ba na tashin hankali, abu matata zata ɗauka mu tafi, “Miemaa tashi muje”.
Kasa tashi nai dan nima jikin nawa rawar yakeyi hawaye na gudu akan fuskata, ya
finciki hannuna yay ciki dani batare da ya saurari Mom ba, Aamilah dama bata iya
furta komaiba dan tsorata.

Tsaye Jawaad yay yana kallon ɗakin, dan an bala'in hargitsashi tamkar ɗan adam
bai rayu a cikinsa ba. Lallai maganar baba ƙaura ta tabbata. juyawa yay ya kalli
Bilkisu da itama tai kasare tana kallon ɗakin da mamaki na gaske. “Ina kika
ajiye?”. Hannu ta ɗaga da ƙyar ta nuna masa jakar islamiyyarta da ita kaɗaice zaune
a inada ta barta ba'ako motsata ba. Yana ɗora hannunsa akan jikkar Dad da basusan
yana garinba ya shigo ɗakin tamkar an jehosa..............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻


[2/12, 7:51 PM] Wasila: Bilyn Abdull 📚:
Page 56

................A yanda Dad ya faɗo mana ya sakani zabura nai baya zan faɗi, Cikin
sa'a boss ya taroni jikinsa, nannauyan ajiyar zuciya na sauke wadda tai dai-dai da
wadda shima Dad ɗin ya sauke yana dafe kansa. Sai kuma ya juya ya kalli bayansa da
faɗin, “Kai Humaira kedai lamarinki sai ke, wlhy na zata wani abunne ya faru da
yaran nan kikaimin wannan irin kira na ujila haka”.
Cikin tsananin ɓacin tai Mom dake kallon Dad tace, “Hakama zakace Alhaji?
Yanzu tsabar wulaƙanci yaran su shigo babu neman izini cikin gidannan har su wuto
nan kai tsaye tsabar raini amma kace hakan ba zama wani abuba?”.
“Haba Humaira, yanzu nan wanene baƙonki a cikinsu? Jawaad dai ɗanki ne,
tun bai kai hakaba yake shiga har ɗakin barcinki ma balle cikin gidanki, hakama
itama Bilkisun ɗiyarki ce, dan aure ya ɗauketa daga gidan sai kuma ya zama laifi
dan ta shigo, mtsoww, dan ALLAH kisan kin girma”. Dad ya ƙare maganar da raɓata ya
fice cikin ɓacin rai. Da kallo Mom ta bisa ranta na matuƙar suya, sai da ya ɓacema
idonta sannan ta juyo garemu. “K yanzu bakiji kunyar zuwa gidan nan ba butulu? Wlhy
nayi nadamar saninki a rayuwata, da nasan zaki zamarwa rayuwar zuri'ata tauraruwa
mai wutsiya da namiki addu'ar ƙare rayuwarki cikin masifa har abada, dan da bazan
taɓa amincewa kin raɓemu ba, amma ni da kaina zanyi maganinki. Kai kuma lusari
shasha, yarinya ƙarama ta gama tawaiwaye rayuwarka da tsafi ka kasa ganin kowa da
gashin arziƙi, inda Abdul-aziz ne ke raye ai da bakai masa hakanba, kaje ai
duniyace, wanda bai zoba ma jiransa take wlh Jawaad”. Tana gama faɗa ta fice abinta
tana huci tamkar wata kumurcin maciji.
Juyawa nai na kalli boss hawaye na zirara bisa kumatuna. Fuskarsa babu
wani alamar damuwa. Yama fiske abinsa tamkar ba'ai komai ba, ƙasa na sulale zan
durƙushe ya taroni jikinsa, rungumeni yay cikin ƙirjinsa yana ɗan bubbuga bayana,
kusan mintuna uku muna a haka, baice komaiba ni kuma inata zubar da hawaye masu
zafi da ƙunar zuciya saboda kalaman Mom. “Boss dan ALLAH ka faɗamin yanda akai
aurenmu ko nima zan daina tuhumar kaina da cin amana, ta yaya za'ai mijin yayata ya
koma mijina rana tsaka? Bana ganin laifin Mom dan kalamanta gaskiyane a gareni,
ni.......” Shiiiiii!!!!” ya faɗa yana ɗagoni da ɗan ranƙwafowa dan ya fini tsaho,
ya ɗaura hannunsa saman bakinsa. Ruf kuwa na rufe bakin nawa ina cigaba da kallonsa
tamkar idanuna zasu zubo ƙasa dan tashin hankali. Sassanyan Murmushi yay min da
kanne min ido ɗaya, yay zipping bakinsa alamar karna sake magana. Kaina na girgiza
masa hawaye na sake gangaro min saman kumatu, baki na buɗe zanyi magana ruf ya
rufemin shi da nashi batare da ya bari na ƙarasa faɗaba, wata irin sumbata mai cike
da sirrika masu wahalar fassara yake aikamin, tun muna tsaye bisa ƙafafunmu har
hakan ya nema gagararmu mukai baya zamu faɗi, saurin riƙe bango yay muka jingina
jikinsa. Ganin yana neman wuce gona da iri nai ƙoƙarin ƙwatar kaina dan na fahimci
yama manta nanɗin ba gidanmu bane. Da ƙyar na samu ya barni, muka ƙurama juna
idanu, tunda nake ban taɓa juriyar kallon tsakkiyar idanunsa a tsahon lokaci kamar
haka ba. Ya matso da fuskarsa dab da tawa har muna shaƙar numfashin juna, wani
munafukin murmushi da bai wuce laɓɓansa ba ya sakarmin, sai dai hakan bai hana
dimples ɗinsa da nake tsananin burgeni loɓawa ba, ya lumshe idanu a hankali sannan
ya buɗe yana ɗaura ɗan yatsansa saman laɓɓana da suka gama shan wajala a hannunsa
yanzu. Cikin magana raɗa-raɗa yace, “A wasu lokutan baki yana ƙarya, yana yaudara,
yana ha'inci. itako ZUCIYA abinda ke cikinta kawai take kuwwa a kansa, agaban kowa,
a kuma ko ina. k wacece a gareni bakina yayi ƙanƙantar lissafa miki, wani jinin sai
an tsaga ake ganesa a jini, karki zama mai gaggawa, karki zama mai wasiwasi, karki
zama mai sakaci, dan bakowa bane mai ZINARIYAR ZUCIYA irin taki”. Ya ƙare maganar
da ɗaura ɗan yatsansa saitin zuciyata. Kallon inda ya nuna ɗin nayi kafin na ɗago
shima na kallesa, ya ɗagamin gira ɗaya da ɗan ƙyaƙyƙyafta idanunsa da suka koma
sirkin jaa, “Ke ɗin ta dabance, idan nace tadaban ina nufin tadaban a kowanne
daƙiƙa na bugun zuc

iya da numfashina Bilkisu”.


Kamar wata sakarai haka na bisa da kallo harya fice a ɗakin. Gaba ɗaya ya
birkicemin tunanina, kalamansa suna dai-dai da tambayoyin jarabawa masu wahalar
gaske da ruɗani ga ɗaliban dake zana jarabawar ƙarshe ta barin makaranta. ‘Mike
nan?’ na faɗa a fili batare da tunanin mai bani amsarba........
Sanin hakan da nai ya sakani bin ɗakin da kallo tamkar baƙona, sai kuma na
juya jiki a sanyaye na fice daga cikinsa. Idanuna akan boss da ke zaune bisa kujera
ƙafa ɗaya kan ɗaya suka fara sauka, sai Dad da Mom dake zaune suma kusa da juna,
Yah Salman na daga can Dining zaune da waya a hannu, sai Aunty Aamilah dake jikin
ƙarfen bene ita kuma a tsaye. Takawa nai a hankali gaban Dad na durƙusa, hawayene
ke zarya a kumatuna masu zafi da saka ƙunar zuciya, “Dad ina kwana” ta faɗa
muryarta a ɗarare. Murmushi yayi yana gyara zamansa, “Ɗiyata yau da kanki a gidan
nan? Ko dai ɓatan kai kikayi?”. Hawayen da suka cikamin ido suka gangaro akan
kumatunna, na ɗago kaina ina kallon Mom da girgiza ma Dad kaina. “Kayi haƙuri Dad,
nasan ni ɗin mai tarin laifukace a gareku waɗanda a kullum nike cike da damuwa da
kunya a kansu, Dad wlhy banci amanarku ba, har yanzu bansan dalilin da yasa kuka
auramin shi ba a maimakon Yah Qaseem, Dad inajinka a rainane tamkar mahaifina,
banason nazama silar ɓacin ranka kona minti guda kai da Mom, banason ka ringa
kallona matsayin tauraruwa mai wutsiya, dan ALLAH kace ka yafemin, ka samin albarka
kuma, ka roƙamin gafara wajen Momy da ƴan uwana suma, ALLAH ne ya ƙaddara komai a
nasarata, sai dai ya sanyaka ka zama sila, ka nunamin hanya a lokacin da mafi yawan
al'umma suka rufemin tasu, ka haskamin rayuwa a lokacin da duhu ya lulluɓeta, ka
zamemin gata, a lokacin da nake ƙasƙantacciya, duk wanda zaiga bilkisu a yanzu
harta birgeshi kaine silar komai..........”
Dad da yaji ƙwalla sun cika masa ido yasa hannu ya ɗaukesu yana ɗan
murmushi da saurin dakatar da bilkisu, kafaɗarta ya kai hannu zai kamo sai kuma ya
fasa, murya a sanyaye yace, “Haba ɗiyata ni bakimin komaiba wlhy, duk abinda kikaga
ya faru a rayuwar ɗan Adam rubutaccene a littafinsa, ke yarinyar kirkice abin
alfaharin kowanne uba, inajinki har cikin raina nima Bilkisu, duk kuma abinda ya
faru kema ba laifinki bane namune, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci rayuwar
aurenku ya baku zaman lafiya kinji, aje aita haƙuri, karki sake yin kuka domin
hakan, ina fatan dai babu wata damuwa ko?”. Bilkisu tasa bakin gyalenta ta share
hawayen tana gyaɗama Dad kanta, “Ba komai Dad, shiɗin mutumin kirkine, kullum
ƙoƙarinsa yaga ya ƙyautatamin, zaɓin da kukaimin ƙyaƙyƙyawan zaɓine da nake
alfahari da shi, na kuma tabbata har ƙarshen rayuwata insha ALLAH bazanyi nadama
ba, nagode sosai da kulawarku a gareni”.
Kallon inda Jawaad ke zaune tamkar baya a falon Dad yayi, cikin ƙara
sanyaya murya yace, “Nagode sosai Jawaad, dama bana tsamanin saɓanin hakan daga
gareka, ALLAH ya ƙara muku zaman lafiya.
Jay ya ɗan ɗago idanunsa tare da tura wayarsa cikin aljihu. Kallon ido
cikin ido sukaima juna shi da Dad, irin kallon da kowa shi yasan ma'anar nasa.
Jawaad ya janye idanunsa yana wani shegen murmushi da sake ɗaura ƙafa ɗaya kan
ɗaya, kafin yace wani abu Mom taja wani wawan tsaki tana miƙewa tabar falon.
Duk muka bita da kallo banda boss da ya basa abinsa hankali kwance. sai
da ta gama hayewa benen Dad ya sauke nannauyan numfashi yana sake kallon Jay, “Tana
cikin fushine sosai akan damuwar ɓatan Mamana, duk inda muke tunanin samun yaron
nan an gaza samunsa Jawaad, dama koda bakuzo nanba ni da kaina zanje gidanku akan
maganar. Ka taimakemu dan ALLAH ”.
Kafin Jawaad yay magana Bilkisu dake share hawaye tace, “Dad wani abunne ya
faru da aunty Shahudah'n?”. Kansa ya jinjina mata cike da matsananciyar damuwa ya
labarta musu komai, shi dai Jay baice ko uffanba, sai Bilkisu da keta sharar ƙwalla
ita da Aamilah. Daga ƙarshe ma sai ya miƙe abinsa yana kallon bilyn, “Tashi mu
wuce” ya faɗa a daƙile. Kamar bily zata fasa kuka dan takaicinsa, ta buɗe baki
zatai magana ya zuba mata wata uwar harara..... Tsam ta mi

ƙe tana haɗiye sabon kukan dake neman taho mata, “Dad zamu wuce”. Kallon Jay Dad
yayi, “Jawaad bazaka bar mana ita ta yini ananba?”. Shiru yay kamar bazaice
komaiba, sai kuma ya kalli agogon hannunsa ba tare da ya kalli Dad ɗinba yace,
“Zamuje office ne”. “Shike nan to, kuɗan jirani”. Dad ya faɗa yana miƙewa.
Jakar islamiyyar ya ɗauka yay ficewarsa batare da yacema bily komaiba.
Da kallo kawai na iya binsa harya gama ficewa, naja numfashi ina danne
zafin da zuciyata kemin, bansan miyasa boss yake hakan gasu Dad ba? Yana ƙara
sakamin ruɗani da wasiwasine akan abinda naketa ƙoƙarin ƙaryatashi a zuciyata tun
randa nai gamo da wallet ɗin nan...... Dawowar Dad ta katsemin tunani na, ya
miƙamin leda babba mai ƙyau yana murmushi, “To ɗiyata ga tsarabarki nan, akwai
kuɗinki na kayan ɗaki danai niyya sai dai hakan bata faruba, insha ALLAHU kafin
kije gida zakiji alert, ALLAH ya ƙara zaman lafiya”. Hawayen da suka ziraromin na
share, na durƙusa har ƙasa ina masa godiya da addu'oin fatan alkairi. “Babu komai
Bilkisu. karki damu tashi kuje yana jiranki”. Jinjina masa kai nayi na miƙe, na
kalli inda Aunty Aamilah take zanyi magana, wata muguwar harara ta watsomin tana
jan tsaki da ɗauke kanta ta nufi ɗakinta. Duk da naji babu daɗi sai nai ɗan
murmushi kawai najuya ga Yah Salman. Shima koda nai masa magana bai amsamin ba,
haka na baro inda yake jiki a sanyaye naima Dad da duk abinda ke faruwa yana
kallonmu sallama na fice.
Fa kallo Dad yabi Bilkisu harta fice daga falon, ya sauke nannauyan
numfashi yana gyara babbar rigarsa, kallon Aamilah da keta cika da batsewa yay ya
ɗauke kansa, batare da yace mata komaiba ya haye sama abinsa. Ɗakinsa ya wuce, sai
da ya rufe ƙofar sannan ya ciro wayarsa daga aljihu yay kiran Qaseem. Bugu biyu
Qaseem ya ɗaga kuwa. Dad ya sauke numfashi yana cire hularsa ya zauna a bakin
gadonsa, “Qaseem gasu nan sun fito, dan ALLAH ka danne ranka karka bari rigimar da
kuka saba da yaron nan ta shiga tsakaninku, mu lallaɓasa musan inda Mamana take dan
nasan wlhy shi kaɗaine keda masaniyar hakan”. “Karka damu Dad, namaka alƙawarin a
daren yau sau Shahudah ta kwana gida, yanzun nan zan kirashi a waya nace masa yazo
ya sameni muyu magana”. Qaseem ya faɗa yana danne ɓacin ransa da mugun tsanar Jay
dake cimasa zuciya. Sallama sukai, Dad ya ajiye wayar yana sauke numfashi da haɗiye
tsantsar damuwarsa akan rashin abar ƙaunarsa mafi soyuwa acikin ƴaƴansa. Qaseem
kuwa daga can kiran Jay yayi duk da yana tunani da wahala ya ɗauka tunda bayin
wayar sukeba, a yanzunma sai da Dad ya turo masa number Jay ɗin dan bashi da ita
da.

A cikin mota na iske boss yana waya, bayan na shiga Sadiq ya rufe ƙofar
kamar yanda ya buɗemin na shiga. Har muka kusa isa gida yana waya, koda kuma ya
kammala bai kulani ba har muka ƙarasa gidan, a ƙofar gida yace Sadiq yay parking.
Batare da ya kalleni ba yace, “Kije ciki”. Kallonsa nai zanyi magana ya sake ɗaure
fuska. Haɗiye maganar nai kawai na ɗauki ledar da Dad ya bani zan fita ya riƙe
ledan. Sake kallonsa nai, sai kuma na sakar masa ledar batare da nace komaiba na
ƙarasa ficewa dan tsagwaron masifa na hango cikin ƙwayoyin idanunsa.
Duk yanda naso riƙe hawayena a yanzu kasawa nayi, haka na shiga cikin
gidan inayinsu duk da nasan Nabeelah tana a gidan kuwa. Kwance na isketa a babban
falo tana barci, dan haka na wuce bedroom ɗina kawai na faɗa saman gado ina fashewa
da wani kukan. Kusan mintuna biyar ina kukana kafin ƙarar shigowar saƙo ta sakani
dakatawa, ɗaukar wayar nayi ina share hawayen dan zatona ko boss ne, zumbur na miƙe
cike da firgicin ganin yawan kuɗin da Dad ya turo min. A fili nace, ‘Tashin
hankali, kodai Dad bai lura baneba?’. Bani da mai bani amsa dan haka nai saurin yin
dialing Number sa. Bugu biyu kuwa ya ɗaga, cikin rawar murya nace, “Dad a......”
“Banason kice komai ɗiyata, kin cancanci fiyema da haka daga gareni kinji, ke dai
ALLAH yay miki albarka”. “Nagode Dad, ALLAH ya ƙara buɗi na alkairi mai albarka”.
Na faɗa cikin kuka. Ina jiyo sautin murmushinsa daga can, ya sake kwantar da murya
yana lallashina cike da kulawa har sai da na

yi shiru sannan mukai sallama.


Jikina duk babu ƙwari na tashi na shiga bayi nai wanka da alwala, na idar
da salla ina ƙoƙarin tashi dan naje na tado Nabeelah sai gata tama shigo da
sallama. “Ai bansan kin shigoba, Sadiq ne da kulolin abinci inji Yayanmu”. “Abinci
kuma?”. Na faɗa ina ajiye sallayar. Tare muka fita, da mamaki nakebin manyan
kulolin da kallo, dan abincine na kusan mutane goma sha biyar ma. “Sadiq wannan
fa?”. “Oga ne yace na kawosu, amma inagafa baƙi za'ayi dan naji yana waya akan
nanda awa biyu da wasu mintuna ma zasu iso”. Bilkisu dake kallonsa kawai tace,
“Yana ina shi?”. “Da muka saukeki Barrack mukaje, bayan mun baro can kuma na
saukesa a General hospital sannan naje na amso wannan abincin, yanzu can zan koma
na ɗakkosa dan yace dubiya zaiyi”.
Sallama yay mana ya fita, ni da Nabeelah kuma muka kwashe kulolin muka
kaisu kicin inata tunanin baƙi kuma daga ina zasuzo haka to?. Bani da mai bani
amsa, dan haka na koma ɗaki danna gyara jikina, Nabeelah kuma tai alwala itama.

JAWAAD

Wayar da bily ta samu Jay nayi a mota wayace daga Qaseem dake a General
hospital a killace, ya buƙaci ganin Jay ɗin da gaggawa, duk da hakan ya bama Jay
mamaki baiyi ƙasa a gwiwa ba wajen amsawa, shiyyasa suka ajiye Bilkisu a gida ita.
Barrack suka fara zuwa wajen baba ƙaura da shima tun a safiyar yau ya saka aka
kirashi a waya akan yana buƙatar ganinsa. yaso suje tare da bily ne dama, to sai
kuma kiran da Qaseem yay masa ya shafe hakan. Kusan mintuna talatin ya ɗauka anan
sannan suka fito.
Likitoci basu bari Jawaad ya shiga wajen Qaseem ba kai tsaye sai da
matakan tsaro na kare kai, ko ina na jikinsa sai da ya kasance a rufe ruf sannan
aka kaisa inda Qaseem ya ke. Wajene na musamman.......

Babu wanda yasan mi suka tattauna har na tsahon mintuna hamsin da uku
sannan Jay ya fito, baka isa fahintar yanayinsa ba, dan kamilar fuskarsa ta shanye
komai, sai dai kumafa jijiyar kansa tai masifar miƙewa ruɗu-ruɗu, hakama idanunsa
jazur suke. Sadiq da tun da ya dawo yana zaune yana jiransa ya miƙe da sauri ya
buɗe masa mota ya shiga, yana zama wayarsa nayin ring, daba dan yasan kirane mai
muhimmanci ba bazai ɗaga ba, yay ƙoƙarin saisaita muryarsa suka gaisa da gambiya
Munaya. Bansan mi tace masa daga canba, ya ɗan dai murmusa yana gyara zamansa da
ƙyau. “Ina sake roƙon alfarma dai Ummu, Please a bani ƴar damarnan nima koda sau
ɗaya ne”. Idanu ya lumshe a hankali yana cigaba da saurarenta, ya sauke ajiyar
zuciya yana jinjina kansa kamar yana a gabanta, saida yay mata godiya sannan ya
sauke wayar daga kunnensa yana cika bakinsa da iska ya fesar.

Muna zaune a falo ni da Nabeelah ya shigo, sannu Nabeelah ta shiga


jera masa, bai amsa mataba, sai dai ya ɗaga mata hannu kawai ya wuce abinsa. Da
kallo muka bisa da gani har ita, na lumshe idanu da kwanciya jikin kujera ina sauke
numfashi. “Shi dai Yayanmu kamar mai jinnu haka yake, yanzu zaki gansa a mutum
anjima kaɗan ya koma dodo”. Nabeelah ce da wannan maganar cikin shagwaɓa, Bance da
ita komaiba na miƙe, ruwa na ɗauka da kofi nabi bayansa.
Ban samesa a faloba, hakan ya sakani binsa bedroom. A gaban mirror na
iskesa yana waya da cire boturan shirt ɗinsa, ido muka haɗa ta cikin mirror'n
kasancewar a bayansa na tsaya daf. Ni na fara janyewa, dan nikam banason ganinsa a
cikin yanayin nan tsoro nakeji, cigaba yay da yin wayarsa tamkarma bai ganni ba.
duk da hakan ya sosamin rai sai na nutsu ina saurarensa, mamaki ya kamani sosai dan
fahimtar wayar yana yinta ne akan Aunty Shahudah, cikin tsoro-tsoro nake kallonsa
lokacin daya ajiye wayar. “Boss wai kana nufin kasan inda aunty Shahudah take dama
kenan?”. Rigarsa da ya gama cirewa ya jefa saman sofa, ya fara ƙoƙarin zare belt
ɗin wandonsa batare da ya kalli sashenma da nakeba balle nai tunanin samun amsa.
Sai da ya gama zame komai daga shi sai boxer sannan ya raɓani ya wuce abinsa. A
take jikina ya fara rawa, na shiga ambaton innalillahi..... Ina kafe ƙofar bayin da
kallo kamar zai fitone ya bani amsar da nake buƙata. Bansan sanda na zube a bakin
gadonba na dafe kai, ts

ahon mintuna ina a haka wayarsa kuma nata faman ring a gefena amma banko kalleta
ba. A haka ya fito ya sameni, yanzun ma dai ban ishesa kalloba, ya shirya a
gaggauce cikin ƙananun kaya farin wando da farar riga, sai ya ɗaura baƙar jacket a
sama mara hannu. Koba'a faɗaba yayi ƙyau sosai, dan shi mutum ne da koyaya ya saka
sutura sai kaga ta zauna masa a jiki tsaf tamjar danshi akai. Tsabar wulaƙanci a
gabana ya sake ficewa a ɗakin bayan ya zauna ya saka takalma a ƙafarsa, bansan
sanda na fashe da kuka ba nai baya a saman gadon.

Gudu sosai Jawaad ya saka Sadiq shararawa dan jirgin su Umm-Anum


harya sauka bisa ƙasa, duk da gimbiya ta sanar masa Takawa ya aika motocin da zasu
tarosu hakan bai hanashi jin ɗokin son zuwa ya tarbo mahaifiyarsa da kansa ba, shi
kaɗai yasan a yanayin da wannan ranar tazo masa, tazo masa da abubuwa kashi-kashi
masu yawa, ruɗani daban al'ajabi da matsanancin farincikin dawowar mahaifiyarsa
duniyarsa cikin ƙasar haihuwarta.
Suna isowa su Umm-Anum na fitowa a jirgi Anuwar riƙe da hannunta. Da gudu
Anum ta ƙaraso gaban Jay da tun tana sakkowa ta hangosa, jikinsa ta faɗa ta
rungumesa. Duk da damuwar da yake ciki da yanayinsa na rashin son shiga harkar yara
bai gaza karɓar ƴar ƙanwar tasaba kamar yanda taso, ya shafa kanta yana ɗan
murmushi kafin ya janyeta a jikinsa ya nufi Umm-Anum. Haɗata yay ita da Anuwar ɗin
ya rungumesu gaba ɗa yana maijin a yau babu tamkarsa duk faɗin duniyar nan. Kasan
cewar yasan umm-Anum na fama da matsalar kafa bai tsaya ɓata lokaciba suka nufi
inda Sadiq ya faka motarsa kusa da motocin masarauta guda uku da sukazo tarbarsu.
“Ummuna Abbu fa?”. “Sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho suma insha ALLAHU,
nima dan bazan iya haƙurin kaiwa goben bane shiyyasa”. Murmushi ya saki mai sanyi
yana taimaka mata ta shiga motarsa da Sadig ya buɗe. Anuwar da Anum kuma suka shiga
motar masarauta ɗaya badan sun so hakanba.
Sai da ya tabbatar komai yayi dai-dai sannan ya zagaya inda Sadiq ya
buɗe masa kusa da Umm-Anum shima ya shiga, ya riƙo hannunta ya sumbata, “Amsiyatul
sa'iidah. Marhaban biki Ummuna”. Fuskarta ɗauke da murmushi da hawaye tace, “N:
Kaifa anta Jay-p na”. Idanu ya lumshe a hankali yana haɗiye nauyin da ƙirjinsa yay
masa da sake damƙe hannunta cikin nashi kamar mai gudun a ƙwace masa ita yace, “Ana
bikhairin Ummuna”. Ta shafa kansa tana murmushi da faɗin, “Alhamdulillahi ala kulli
halin Noorul Ayn”. Ɗagowa yay idanu jazur ya kalleta da sake sumbar hannunta ya
ɗaura kansa saman kafadanrta yana sake lumshe idanu. “Ummuna nayi kewarki”. “Nima
haka Muhammad Jawaad”. Ta faɗa tana sumbatar goshinsa.

Cikin nutsuwa motocin suka fice daga airport ɗin, ta Jay ce gaba shi da
Umm-Anum, sai kuma wadda su Anuwar ke ciki shi da Anum, sai ɗaya da babu kowa a
ciki, ta ƙarshe kuma dogaraine.

___________________

Daga kukan da ya barni inayi sai barci ya kwasheni, cikin barci naji
ana knocking ƙofar, na buɗe ido a hankali da tashi zaune dan nasan bazai wuci
Nabeelah bace, bayi na fara shiga na wanko fuskata da hawaye suka bushe, sannan na
fita. Nabeelah tai saurin riƙo hannuna tana faɗin, “Baƙinfa sun iso inaga, dan naji
ƙarar buɗe gate”. Bata jira amsata ba taja hannuna muka fito babban falo. Kiciɓis
mukai da Anum data fara shigowa. Ta daka wani uban tsalle ta ɗareni, tuni naji duk
wani ɓacin ran da Boss ya barni da shi ya gudu, na rungumeta nima cike da tsantsar
farin ciki.
Anuwar ne na biyun shigowa, ya fara sauke idanunsa akan Nabeelah da ke
tsaye tana kallon su bily da dariya, kafin ya maida ga su Bilkisun yana ɗan ɓata
fuska. “Lallaima Aunty, ni baki ganniba sai wannan yarinyar”. “Tuba nake Yah
Anuwar ” na faɗa ina sakin Anum.

A waje kam Jay ya taimakama Umm-Anum ta fito daga motar, ƙafafunta duk
sunyi fushi saboda zaman jirgi, ga kuma dama ƙafarta na mata ciwo. Wani irin kallo
take bin gidan da shi dan bazata taɓa mantawa da shi ba koda a magagin mutuwa take,
gidan da yazama tushen komai na maida mijinta wane, gidan da yazama harsashin ginin
ɗaukaka ga abin sonta, gidan da zata iya a

mbatonsa da komai a ɓangaren farin cikin rayuwar aurensu da akasinsa, gidan data
haifi gudan jininta bayan shafe shekaru tana kuka da fatan samu. kallon Jay tayi
hawaye cike da idanunta. A hankali ya kaɗa mata nasa kan yana ɗan murmushi. Ta sake
damƙe hannunsa cikin nashi tana haɗiye abubuwa masu yawan gaske dake yunƙuro mata
tun daga ƙasan zuciya har saman harshe. A hankali ya fara takawa da ita suka nufi
ƙofar da zata sadasu da cikin gidan, suna gab da isa ƙofar falon Bilkisu ta fito
cikin matsanancin hanzari.
Nai saurin ƙarasawa garesu batare dana tuna da wani matsayinta na surukata
ba, ni kallon uwa nake mata, uwa ɗinma mai muhimmancin gaske ga ɗa. sakin Jawaad
Umm-Anum tai itama da sauri ta buɗema bily hannayenta, aiko tazo ta shige jikinta.
A take hawayen da Umm-Anum ke maƙalewa suka gangaro mata saman kumatu. Kauda kai
Jay yayi daga kallonsu saboda ƙwallan da suka cika masa idanu, sai ya tura duka
hannayensa cikin aljihun farin wandonsa ya ɗaga kansa sama ya maida hawayen. Sai da
ya tabbatar hawayen sun koma sannan ya sauke fuskarsa a kansu. Yanzu kam Bilkisu ta
ɗago daga jikin Umm-Anum, sai dai su duka hawaye suke tana jeramata sannu da zuwa.
Umm-Anum ta shafa fuskar bilyn tana ƙare mata kallo sosai, wani sassanyan murmushi
ta sake saki da jawota jikinta ta sake rungumeta, dan ita kaɗai tasan mita gano.
“Ummuna kumuje ciki, sai ku cigaba da murnan”. Jay ya faɗa a hankali
kamar bashine yay maganarba. Kallonsa tai shima ta riƙo hannunsa suka sakata
tsakkiya shi da Bilkisu, a haka suka shiga falon inda Nabeelah da Anum ke zaune
surutu ya kaure tsakaninsu, Anuwar kuma ya tasasu a gaba yana kallon Nabeelah kamar
ya samu wani majigi.
Cak Umm-Anum ta tsaya tana kallon Nabeelah da itama tai mutuwar tsaye tana
kallon mai tsananin kama da Ummahn ta. Kallon Jawaad Umm-Anum tayi cikin wani
yanayi na alamar tambaya. Hannunta ya kama ya zaunar da ita yana ɗan murmushi, sai
da ya tabbar ta zauna sannan ya kalli Nabeelah da ke ƙoƙarin gaisheta. Hannun
Nabeelah ta kamo ta matso da ita jikinta, da ƴar rawar murya Umm-Anum tace, “Da ace
mutum baya ƙara shekaru da girma ni dai da nace wannan Mariya ta ce Jawaad, kamar
yanda nake kallon takwarata da kamannin Rahma”. duk da ba yaune karan farko da
akace Bilkisu na kama da aunty Mah-mah ba a gabansa sai da ya kalli Bilkisun da
tasha jinin jikinta, sai kuma ya ɗauke kansa yana zama kusa da Umm-Anum. “Ummuna ki
kwantar da hankalinki kinji, dukkan abinda kike buƙatar ji zaki samu fiyema da
hakan har sai kin gaji, yanzu dai kitashi a kaiki inda zakiyi wanka, kuci abinci ki
kwanta ki huta, sai komai ya biyo bayan hakan kinji”.
Kansa ta shafa da ja masa hanci tana faɗin, “Rigimammen Mama har yanzu dai
ana taɓawa kenan”. Dariya duk su Anuwar sukayi, shi kuma ya zuba musu harara da
kama hannun Umm-Anum ɗin ya miƙar da ita. Da kansa yay mata rakkiya har ɗakin bily,
itama da tabi bayansu tai saurin shiga bayi domin haɗa mata ruwan wanka.

Nabeelah na ganin Jay da bily sun shige da Umm-Anum tai saurin ɗaukar
wayarta ta turama Ummah babba saƙo.
Sai da suka tabbatar Umm-Anum ta shiga wanka sannan Jawaad ya fito, kayansu
da Sadiq tuni ya gama shigo musu da su ya saka Anum ta ɗauka na Umm-Anum ta kai
mata ɗakin Bilkisu, shi kuma ya kai Anuwar ɗakin baƙi inda zai zauna, Anum ma ɗakin
baƙin dake cikin falon bily zata zauna. Bilkisu da Nabeelah da keta ALLAH, ALLAH su
Ummah su iso sukai hidimar shirya abinci su kuma a tsakkiyar falon, dan yanda Umm-
Anum ta gaji bai kamata a sakata zaman Dining ba.
Tana son tabi Jay ɗakinsa dan ta nuna masa farin cikin data shiga na bazatar
da yay mata akan zuwan su Umm-Anum amma haushinsa da takeji ya hanata aikata hakan,
sai kawai ta sharesa ta cigaba da harkokin gabanta, dan farin cikin ganin su Umm-
Anum ya shafe mata duk wani damuwarta kuma.
A ɓangaren Jawaad shima tun shigowarsa ɗakin ya ke zuba idanu ya ga
bilkisu ta biyosa amma sai yaji tsit, duk da farin cikin ganin mahaifiyarsa da
ƙannensa ya shafe masa duk wani ɓacin ran da ya samo daga Qaseem da gidan Dad hakan
bai hana ransa sosuwa ba da ƙ

in shigowar Bilkisun, sai huci yake da jera tsagwayen ƙwafa, ayyanawa yake a ransa
sai yayi maganin miskilancin yarinyarnan a yau ɗin nan basai gobe ba, dan ya gama
lura gadon barcinsa da ta gama ganine yasa take neman fara kawoma rayuwarsa raini
(Ka manta wulaƙancin da kai mata kai ɗazun saraki🙄😜).
Tashi yay da ga kwancen da yake saboda jin an fara kiraye-kirayen sallar
Magriba. Alwala yayi sannan ya fito, a babban balo suka haɗu da Anuwar da shima ya
fito daga sashen baƙi da alamar shirin tafiya masallacin. Yayma abincin da aka
shirya a tsakkiyar falon kallo ɗaya ya ɗauke kansa batare da yace komaiba suka fice
shi da Anuwar dan falon babu kowa cikinsa.
Da taimakon Bilkisu Umm-Anum ta dawo falon bayan an idar da sallar
Magriba, suna zama Ummah babba da Ummah ƙarama da Batool nayin sallama, cikin
matsananciyar faɗuwar gaba Umm-Anum ta juya tana kallon ƙofar dan ko'a cikin
magagin barci waɗannan muryoyin sunfi gaban mantuwa a gareta balle ma a zahiri.
Kasancewar akwai hasken Genretor da aka kunna tas suke ganin junansu, da ga
Ummah ƙarama har Ummah babba jikinsu rawa yake da tsuma sosai, sun ƙurama Umm-Anum
idanu tamkar yanda itama ɗin kallonsu take bata ko ƙyaftawa. Su dai su Bilkisu
kallonsu kawai suke da son ganin yaya za'a kwashe. A haka Jawaad da Anuwar suka
shigo suka samosu. Jay ya kalli su Ummah da mamaki sai kuma ya kalli Nabeelah da ya
tabbatar itace da wannan aikin. Aiko sai tai ƙasa da kai gabanta na faɗuwa dan
tsoro ta koma bayan bily ta maƙale.
Ɗauke kansa yay daga gareta, ya ƙarasa gaban su Ummah ya tsaya a tsakkiyarsu,
hannayensu duka ya kama a cikin nasa, a take duk suka ɗago suna kallonsa hawaye na
gangaro musu saman fuskokinsu. Yanda laɓɓansu ke rawa zai baka tabbacin magana suke
son yi amma sun kasa saboda ruɗani. Jay yaɗan murmusa yana mai lumshe idanunsa ya
buɗe alamar tabbatar musu da wadda suke hasashen ce ba mafarki bane ko gizago.
Cikin ƙarfin hali Ummah Babba tace, “Yarona da gaske kake Yaya Bilkisu ce a gabanmu
ba mafarkin da muka sabayi bane?”. Yanzunma kansa ya jinjina musu, ya kuma ja
hannayensu har gaban Umm-Anum da alamu ya nuna suman zaune tayi. Hannayensu ya saka
a cikin nata yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi yaja jikinsa baya.
A gaban Umm-Anum Ummah ƙarama da Ummah babba suka zube suna fashewa da
kuka mai tsuma rai da cin zukata. Umm-Anum ta kawo nannauyan numfashi lokacin da
suka rungumeta su duka biyun a jikinsu.
Su Bilkisu dake kallonsu suma hawayen sukeyi, Jawaad kansa sai da ƙwalla ta
cika masa idanu, amma jarumta ta saka shi haɗiye kayansa ya koma cikin kujera ya
zauna yana jin wani irin matsanancin farin cikin da ƙirjinsa ma ke neman gaza
ɗauka. Su Ummah sunkai kusan mintuna huɗu zuwa biyar a jikin Umm-Anum suna raira
kuka kafin su saki juna, hannayenta ta ɗaura saman kumatunsu tana shafawa da
murmushi saman fuskarta ga kuma hawaye, suma dai murmushin sukeyi hannayensu duka
akan nata kumatun suna share mata nata hawayen. “Ashe Mariya ta da Wasila basu
girmaba har yanzun? Ashe shagwaɓar nan da akema Yaya tana nan ba'a fasaba”. Dariya
ta kwacema su Ummah lokaci guda da kuka, jikinta suka sake faɗawa ta rungumesu tana
dariya. Su ma ƴaƴansu dariyar sukeyi da hawaye banda Jay da murmushi ne kawai a
saman fuskar tasa.
Da sauri Umm-Anum ta sake ɗagosu tana faɗin, “Ina Rahmah take ita kuma? Ko
ba'a nan take aure ba?”. Duk ƙasa sukai da kawunansu hawaye masu zafi sosai na sake
rige-rigen fitowa daga idanunsu, Umm-Anum ta shiga girgiza kanta a hankali tana
kallonsu a tsorace, “Karku cemin na rasa Rahmah Mariya, kar kucemin rabuwa ta har
abada nayi da Rahmah dan ALLAH” “Sai dai haƙuri Yayah, Rahma ta jima da barinmu
gaba ɗaya, ta tafi tafiya mai nisan zango da babu iyakar sake ganin juna sai idan
ALLAH ya ƙaddara hakan a can wata rana”. Ummah babba ta faɗa zuciyarta na mata zogi
tamkar a yaune Rahmah tabar duniya. Yanzun kam Umm-Anum ce ta fashe da kuka mai
tsuma rai da cin zuciya, tana son Rahmah, tana ƙaunar Rahma sosai, dan tafi shaƙuwa
da ita a kaf cikin ƴan uwanta.
Ganin kukan nasu yana neman yin yawa gashi ha

r ana kiran sallar isha'i sai Jay yay gyaran murya. ɗagowa sukai duk suka kallesa.
Ya sakar musu murmushi da waro idanunsa waje kaɗan ya miƙa musu kwalin tissue da ya
ɗauka saman centre table. Babu musu suka amsa. “Yauwa Momys ɗina ababen alfaharina,
kukan ya isa haka nan kar ku ƙarar mana da hawayenku, lokacin kuka ya wuce yanzu
farin ciki ake buƙata da godiyar ALLAH da ya kawo ranar da ba'a taɓa tunani ko
tsamanin zuwanta ba, idan kuna kuka mu kuma mi zamuyi to?”. Cikin kaɗa kai Ummah
babba tace, “Hakane Jawaad, ALLAH yay maka albarka kaida sauran ƴan uwanka kaji, a
ina ka gano mana Zuciyarmu ne yaron albarka?”. “Ihhhmmm karku damu zan faɗa muku
komai sweet Ummahs ɗina, amma ba yanzu ba sai tsohon can shima yana gefena”.
Daƙƙuwa Ummah ƙarama tai masa tana faɗin, “Sai dai idan iyayenka ne tsoffi”. Dariya
ce ta nema kufcema su Bilkisu, suka saka hannaye duk suka kare bakunansu banda
Aunty Batool da tayi abunta sosai. Miƙewa yay ya dungurema Aunty Batool kai yay
ficewarsa domin yin sallar isha'i.
Bayan sallar isha'i natsuwa da ga UBANGIJI ta kuma saukar musu a zukata,
duk da su Ummah suna ƙage da sonjin wani abu daga yayar tasu, kamar yanda itama a
ƙagen take sai Jay ya hana, a cewarsa sai sunci sun ƙoshi sannan hakan zata
kasance. Babu yanda suka iya suka yarda da batunsa, dan suma sunsan ya cancanci
Umm-Anum taci abin ma ta kwanta ta huta, sai dai zukatansu bazasu iya jure hakanba.
Ummah babba da kanta ta bama Anuwar da Anum abinci a baki cike da so da
ƙauna, hakama Umm-Anum ta bama Aunty Batool da Nabeelah da Bilkisu, Jay kuma Ummah
ƙarama ta bashi. Cikin wani irin farin ciki mai wahalar misaltuwa sukaci abincin
suka ƙoshi, dan Umm-Anum har su Ummah ma sai da ta dinga basu a baki da kanta. Abin
dolene ya sakaka kuka ya kuma birgeka. Sai da sukai nak da girki suka godema
UBANGIJIN daya basu badan ƙarfinsu ba ba kuma dan sunfi kowa ba sannan su bily suka
tattare wajen tas. Da taimakon aunty Batool da Nabeelah da Anum suka wanke komai
tsaf. Yayinda a falo kuma Jawaad ke ta bama su Ummah labarin yanda komai ya kasance
game da ganin Umm-Anum ɗin duk da dama tun a wancan lokacin ya labarta musu a
sanadin Bilkisu ne. Wata iriyar ƙauna da soyayyar Bilkisu sai ta ƙara faɗaɗa da
daɗuwa a cikin zukatansu. Duk yanda mai hasashe zaiyi tunaninta a zukatansu tafi
gaban hakan ta wuce.
Sabon babin fira aka buɗe a cikin falon ba tare da sunma tuna darene ba
ranaba, babu mai kallon lokaci babu mai tunawa ma da shi. Ba suba ko Jay da baisan
yawan surutu yau sai yaji hakan bai gunduresa ba, wani wajen ayi kuka wani wajen
ayi dariya, wani wajen ayi tausayi da al'ajabi. Haka kawai bilkisu ta tsinci kanta
da yin matsanancin kuka akan labarin Aunty Mah-mah (Rahmah), haka kawai taji tana
ƙwaɗayin ganinta koda kuwa a hotone. Hakama Umm-Anum ta shiga matsanancin mamaki da
jin wai Bilkisu ba ɗiyar Rahmah bace ba. Yayinda shi kuma Jawaad al'amarin yay masa
tsaye cak a zuciya baisan dalili ba, kawai yanaji a ransa kamar akwai wani abu dake
a binne game da rayuwar bilkisun, musamman idan ya tuna da maganar baba ƙaura akan
duhun dake biye da Bilkisun, da kuma furucin baba ƙauran a jiya da yaje wajensa
saboda kiran da yay masa. ‘Kai anya kuwa babu wani abu........?’ ya faɗa a cikin
ransa yana kafe Bilkisu da idanu harta tsargu ta ɗan ɗago suka haɗa ido.
Barci ma da kansa yasan inda yake zuwa yay sata, dan kuwa idanun
waɗanan bayin ALLAH ko gyangyaɗi basaji balle ai maganar barci, suna zaune
dingangan har agogo ya nuna ƙarfe uku saura na dare. Jay ne ya katse firar tasu da
roƙonsu akan suje su kwanta haka da safe idan ALLAH ya kaimu saisu ɗora. Badan
sunso hakan ba suka miƙe dan suma susan Umm-Anum na buƙatar ace ta huta kodan
doguwar tafiyar da tayo wadda bata saba ba. Su mamaki ma abin ya basu dan basusan
lokaci yaja haka ba, jima suke tamkar daren bai wuce ƙarfe goma ba. Dole dai yau su
kwana gidan ɗansu.
Ummah babba Umm-Anum da Ummah ƙarama ɗakin bily aka kaisu su kwanta tare da
ƴar uwarsu, duk da dai ba kwanciyar sukaiba wani babin sabuwar hirar suka sake
buɗewa ma su. Batool da Anum da Nabeelah kuma ɗaki

n dake kusa dana Bilkisu, Anuwar yana a ɗakin baƙi. Jay ya nufi nasa ɗakin, Bilkisu
na shirin shigewa wajensu Nabeelah Ummah ƙarama ta korata ɗakin Jawaad.

Sosai kunya ta lulluɓeni har inaji kamar ƙasa ta tsage na shige, to amma
yaya na iya suɗin ba abin wasana bane balle nai tunanin musu gardama ma, haka na
nufi sashen nasa kamar na nutse dan kunya. Ina jiyo su Nabeelah namin dariya harda
Yah Anuwar. Sam banso hakanba, dan naso ace mun samu nisa da juna ni da shi koda na
kwanaki biyu ne dan ya fahimci inajin zafin abinda ke faruwa tsakaninsa da ƴan
uwana, ƙila ta hakan zan samu ya faɗamin abinda ke faruwar. Badan a ciwon kan da
nake ji ba da falo zanyi zamana na ƙarasa daren, haka dai na daure fuska a ciskule
na nufi bedroom ɗinsa, ciki ciki nai sallama na shiga, yana kwance a saman gado da
ga shi sai noxer kawai, idanunsa a rufe suke amma na tabbata ba barci yake ba, na
ɗauke kaina daga garesa na nufi bayi. Ban wani jimaba na fito dan fitsari kawai
nayi da abinda baza'a rasaba. Yanda na barsa haka na fito na samesa, bani da kaya a
ɗakin, sai naita tunanin mizan saka na kwanta dan bazan iya barci da kayan jikina
ba. Ganin lokaci na sake ja ga zazzaɓi nama neman saukarmin yasa na nufi Wadrobe
ɗinsa, cikin sa'a kuwa idanuna saka sauka akan t-shirt ɗinsa mara nauyi ruwan toka,
nasan indai na saka zata sakkomin dan babbace kuma girman ba ɗaya ba.
Zagayawa nai ta ɗayan gefen na kwanta can ƙarshen gado na juya masa
baya.....
“K har kin isa mu kwanta a gado ɗaya ki juyamin baya!”. Na tsinkayi saukar
muryarsa da furucinsa a fusace cikin kunnuwana. Ɗan rintse idanu nayi ina haɗiyar
yawu da ƙyar, zuciyata sai harbawa take da sauri-sauri na tsoro. A hankali na juyo
ina tura baki da sake ɓata fuska sosai, abin mamaki har yanzu yana a yanda yake. A
ƙasan ido naɗan hararesa naja bargo na rufe har fuskata ma.
Wani haushi ya sake kume zuciyar Jay, jiyake kamar yay mata filla-filla
ɗin da saita ƙarasa daren da kuka, sai dai yanata ƙoƙarin danne fushinsa kawai.
Ba ƙaramar razana naiba jin an fincike bargon, na waro idanuna dake cika da
ƙwalla a kansa, fisgoni yay na faɗa jikinsa ya matseni tsam-tsam, wani marayan kuka
na buɗe baki zan sakar masa sai dai kuma ya hana hakan ta hanyar baƙar muguntarsa
da ya ƙware a iyawa, nasan bani da wani ƙarfin ƙwatar kaina daga garesa musamman ma
a irin wannan lokacin da sam banajina ma garas. Ɓacin ransa baisa shi kasa bidani
cikin salon natsuwa da salo mai tsayawa a zuciya ba.............

....
..........✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻


[2/12, 7:51 PM] Wasila: Bilyn Abdull 📚:
Page 57

_______________________________
SHAHUDAH
_______________

Saukar su Umm-Anum ƙasar haihuwarta tayi dai-dai da komawar


Shahudah gida. Mom da Aamilah ne kawai a gidan, Dad ya fita tun bayan barin su Jay
gidan. Waya Mom keyi da Mama Atika. A take ta saki wayar ƙasa ta tarwashe bisa
tiles jikinta na tsananin tsuma.
Shahudah da ke cikin wani yanayi kamar ba'a hayyacintaba ta ƙaraso cikin
falon tana tangaɗi ta zube saman carpet. Da ga Mom har Aamilah zubewa sukai a
gabanta jikinsu na rawa, sai kuma Aamilah ta miƙe da sauri taje ta leƙa waje. Babu
kowa sai maigadi daya taimakama Shahudah ta shigo ya juya zai koma wajen gate.
Komawa falon Aamilah tayi bayan ta rufe ƙofar ruf ta garƙama mata key. Ta koma
wajen su Mom da gudu tana faɗin “Mom ita kaɗaice fa wlhy babu ɗan iskan”.
Mom tace, “Nashiga Uku ni Aysha, Shahudah daga ina kike haka? Miyayi miki
ne?”. Bata da mai amsa mata waɗanan tambayoyin dan Shahudah sai faman lumshe idanu
kawai take. Mom ta ƙanƙameta a jikinta ta fashe da kuka tana jama ɗan-fir'auna
mugayen addu'oi. Suna cikin haka akai knocking ƙofar, duk ɗagowa sukai suka zubama
ƙofar falon ido kawai, sai dai daga Mom ɗin har Aamilah babu wanda ya iya motsawa.
Shiru ba'a sake bugawar ba, hakan yasa suka share suka maida hankalinsu ga
Shahudah.
Salman dake buga ƙofa ganin ba'a buɗeba sai ya zagayo ta kitchen, shikansa
ba ƙaramin mamakin ganin Shahudah yay ba, jikinsa har rawa yake wajen ƙoƙarin kiran
Dad ya sanar masa Shahudah ta dawo.

Cikin mintuna ƙalilan sai ga Dad a hargitse kamar zai tashi sama, yanda
yake buga ƙofar kawai kasan babu lafiya, Aamilah ta buɗe masa tana matsawa ta bashi
hanya, da sauri ya shigo. A gaban Shahudah ya durƙushe tare da maido kanta jikinsa
idanunsa na kaɗawa lokaci guda dan ɓacin rai. “Shine ya kawota?”. Yay tambayar yana
kallon Mom. “Nima ban saniba Dadynsu, shigowarta kawai muka gani ita kaɗai. Leɓe
Dad ya taune da ƙarfi, ya kalli Salman dake tsaye cikin damuwa shima, “Kai Salman
kiramin Dr Tayyib, ke kuma Aamilah kiramin maigadi, ai bazai rasa sanin wanda ya
ajiyeta ba”.
Babu jimawa maigadi da Aamilah suka dawo falon, cikin girmamawa Maigadi ya
rusina yana gaida Mom. Bata amsa masaba, sai Dad ne ya jefa masa tambaya, “Yaya
akai Mamana ta dawo gidan nan?”. “Wlhy Alhaji ban saniba, kawai naji nishin mutumne
a jikin gate, shine na leƙa nama zata ko yaran nanne masu addabama mutane, sai naci
arba da ita kwance jikin gate ɗin, sai kuma ƙurar mota da nake zargin a ita aka
ajiyeta”. Ran Dad ya ƙara digunzuma sosai, yay ma maigadi nuni da hannu alamar ya
tafi kawai.
Maigadi na fita Dr Tayyeb na isowa gidan, bai zaman ɓata lokaciba ya shiga
bama Shahudah taimakon gaggawa bayan an kaita ɗakin Mom an kwantar a gado. Duk wani
taimakon da ake buƙata Dr Tayyeb ya bata, ya kuma tabbatar musu da cewar babu wata
matsala normal zata farka insha ALLAH, ruɗanine ya sakata shiga wannan halin kawai.
Hakanne ya basu ƴar nutsuwa, har suka kira su Mama Atika suka sanar musu dawowar
Shahudah ɗin.

Normal Shahudah ta farka a safiyar yau kamar yanda Dr Tayyeb ya sanar


musu, kasancewar ɗaki ɗaya, gado ɗaya ta kwana da Dad da Mom sai suka baibayeta da
tambayoyi akan abinda ya faru da ita?. Tsaf ta kwashe yanda akai ta sanar musu.
“Dad ashe shiɗin ba mijina bane, tunda ya tafi dani wani gida ya kaini
kawai ya ajiye bamma sake ganinsaba sai bayan kwana huɗu, ya sanarmin a randa aka
ɗaura mana aure a ranar Bb ya saka shi ya sakeni, yace dan kawai yana ganin
mutuncinsa yay hakan, amma badan Bb bane wlhy ko za'a kashesa bazai sakeni ba, kuma
koda ya sakeni badan na taɓa zama matar Bb ba da bazai ƙyaleniba sai ya ketamin
mutunci, wai Bb yana da kimar da bazai iya mu'amulantar abu shima yayi hakanba, Mom
wlhy Bb mutumin kirkine, dan ALLAH ku bashi haƙuri mu koma aurenmu kamar da, ALLAH
yanzu na amince zan haihu ko nawa yake so”.
Mom da Dad da mamaki ya cika suka kama hannayenta cikin nasu, cikin zafin rai
Mom tace, “Zaki koma gidan Jawaad kuwa Shahudah, zaki koma kodan shegiyar yarinyar
can tasan asirinta ai

kin banzane, namiki alƙawarin a yau ɗin nan basai gobe ba za'a maida aurenku da
Jawaad”. “Mom da gaske? Dad kaima kuma ka yarda da hakan?”. “Ɗari bisa ɗarima kuwa
mamana, duk abinda kikeso a duniyarnan saikin samesa ko minene shi, duk abinda
Momynku ta faɗa kisa a ranki ya gama tabbata”. Rungume Dad tayi tana fashewa da
kukan jin daɗi, suma suka rungumeta cike da so da ƙauna harma da tausayinta.
Gari na ƙarasa wayewa Mom ta ɗauki Shahudah suka tafi family house ɗinsu.

______________________________
BEEJAY
______________
Da ƙyar muka iya tashi sallar asuba, musamman ma ni da jikina ke ciwo ta
ko ina, idanuna sunmin nauyi sosai na rashin barci da kukan da na sha. To nidai
bansan randa zan zama jarumar ba, duk yanda zan fasaltama mai saurarona zai ga
kawai nacika rakine da ragwanta, amma ni kaɗai nasan sirrin al'amarin kawai.
Da taimakonsa mukaje bayi badan bazan iya tafiya da kaina bane, hakan kawai
shi yaso shiyyasa ya kamani muka shiga tare. Tare mukai wankan da bamu samu damar
yi ba saboda tsabar barcin da yaci ƙarfin idanunmu, muna fitowa ya fice daga ɗakin.
Tsaye nai ina tunanin ta'ina zan fara ne? Bani da wani kayan sakawa a ɗakinsa
sai abinda baza'a rasaba, tunanina ne ya katse jin motsin mutum da sallama ciki-
ciki, ya ajiye kayan dake hannunsa kusan kala bakwai, sai leda da alamu ya nuna
kayan barci dana cikine a ciki, ajiyar zuciya naɗan sauke, bai jira cewataba ya
sake ficewa.

Ana idar da sallar asuba ban zaunaba, ina ƙoƙarin tashi ya shigo ɗakin
da sallama, da alama ko azkar bai zauna yiba balle ai maganar motsa jiki,
jallabiyar jikinsa kawai ya zare ya ajiye ya haye gado, matsawa nai na gaishesa,
batare da ya amsa minba ya jawo hannuna na faɗo kansa, “Ouch” ya faɗa a hankali
alamar yaji zafi, ɗan kallonsa nai sai kuma na kumbura baki. Hancina yaja yana wani
lullumshe idanu, ya birkiceni na koma ƙasa fuskokinmu daf da juna muna shaƙar iskar
numfashin junanmu. Cikin yin mar-mar da idanu na tsoro nace, “Ina kwana?”. Shiru
yay kamar bazai amsaba yanzunma, yanata ƙarema fuskata kallo, ya sumbaci goshina
yana sake ɗagowa da ƙoƙarin saka idanunsa cikin nawa amma naƙi yarda da hakan.
Saima ɓata fuska nai ina faɗin, “Abinci zan ɗora fa”. “Da wane ƙarfin?”. Ya faɗa a
ƙasan maƙoshi, dan koni dake daf dashi badan ina kallon lips ɗinsa ba ba lallaine
na fahimtaba. “Da nawa mana” na bashi amsa nima ciki-ciki. Nauyinsa ya ɗan sake
sakemin yana faɗin, “Oh ni kika raina kikema raki dama kenan?”. Tuni idanuna sun
fara tara ƙwalla, “ALLAH zaka kasheni”. Nai maganar a rarrabe dan na fara sauke
numfashi da ƙyar. Yi yay kamar zai ƙarasa sakarmin nauyin sai kuma ya ɗagani yana
dunguremin kai. Nannauyan numfashi na sauke ina lumshe ido irin na ALLAH na gode
makan nan. Na yunƙura zan tashi ya maidani ya sake kwantarwa. “Barci” ya faɗa a
cikin kunnena. “Idan nayi barci sukuma mi zamu basu suci?”. “Shiiii!!” ya faɗa
batare da ya bani amsata ba. Shirun kuwa nayi ina masa kallon mamaki, yaja bargo ya
lulluɓemu da shi tare da sakani a cikin jikinsa, a hankali ya furta, “Thanks you
Miemaa”. Bansan dalilin godiyarba, dan haka na sake lafewa a jikinsa nace, “For
What?”. “For Everything Zinaran” Ya bani amsa da wani irin salon da yasa tsigar
jikina tashi. Sake lafe masa nai a jiki ina shaƙar mayataccen ƙamshin turarensa da
akwanakin nan yakemin daɗi fiye da komai. barcin mukeji, dan haka kafin wani dogon
lokaci yayi gaba da mu.

Barcin da su Umm-Anum suka gagara yinsa a daren jiya yau suna idar da
salla suka nema yinsa, koda Jay da Anuwar suka shiga gaishesu sama-sama suka amsa
musu, Jawaad da yasan za'a rina yaja hannun Anuwar suka fito. Dama yasan ai wannan
barcin sai sunyisa dan shi ba'a cin bashinsa daman.

Kasancewar na kwanta da maganar abincin a raina sai barcina baiyi tsahoba


na tashi, a hankali na zare jikina daga nasa na sauka a gadon, badan barcin ya
isheniba na tashi, zuciyatace kawai bata aminta dana kwantaba bayan gida cike da
baƙi. Ina fitowa babban falo naci karo da kulolin abinci, da mamaki na isa garesu
na bubbuɗe, lafiyayyen breakfast ne a ciki wa

nda ya fito shar kamar ka zauna ka cinye kai ɗaya. Mamaki ya kamani na inda ake
kawo wannan abincin? Sanin bani da mai bani amsa sai kawai na shiga kwashesu zuwa
kitchen, na dawo nahau gyaran falon zuwa falonsa da nawa da duk inda dai bazan
takurama masu barciba. Kafin su tashi na shirya abincin a falona na koma nayi wanka
na na shirya tsaf cikin zani da riga na atanfa da sukaimin ƙyau.
Jinai kamar ana kallona, na juyo da sauri na kalli gadon batare dana ƙarasa
ɗaurin ɗan kwalin ba. Boss dake kwance idanunsa a kaina ƙyam ya ɗan lumshesu ya
sake buɗewa a kaina cike da salo. “Dama ka tashi?”. Kansa ya jinjinamin kaɗan
batare da yace komaiba. Ɗan kwalinma sai naji na kasa cigaba da ɗaurasa saboda
idanunsa duk sun takurani, haka dai na daure na ƙarasa na miƙe har lokacin idanunsa
a kaina. Toilet naje na haɗa masa ruwa na fito, yanzu kam zaune na iskesa a bakin
gado da waya a hannu. “Ga ruwan wanka can”. Kansa kawai ya girgiza min, batare da
yace komaiba. “ba yanzu zakayi ba?”. ajiye wayar yay ya ɗago yana kallona, “Barshi
idan naci abinci zanyi, bara na duba saƙon nan da Jabeer ya turo min” yay maganar
yana miƙewa ya nufi Computer ɗin dake a ɗakin inda ya gyara a can gefe tamkar wani
ɗan office. Da kallo kawai na iya binsa, danni mamaki yake bani yanda sam bai
gajiya da aiki. Komai banceba na gyara gadon kawai na fice daga ɗakin.
A falo na iske Aunty Batool ta fito cikin shirin fita, na bita da
kallon mamaki da alamar tambaya. Murmushi tamin kaɗan tana gyara mayafinta, “Zanje
gida saboda abincin Alhaji babba, naga Ummah ganin ƴar uwarta yama mantar da ita”.
Murmushi nayi, “Ah haba aunty Batool itama nasan ba mantawa tayi ba, kawai dai tana
cikin yanayine mai wahalar fassara, to mizai hana ki ɗiba masa na nan? Idan kuma
wani ya keso daban ai saina girka masa yanzun nan insha ALLAH”. “A haba, wahalan ai
sai yayi yawa, bara kawai naje can ai zan dawo, koda yake nama san acan kuma yau
za'a yini ma”. “A'a dan ALLAH, muje kiga na nan ɗin dai aunty Batool, shima idan
yaji kin tafi can dan kawai dafa abincin baba ai bazaji daɗiba”. Nai maganar ina
marairaice mata.
Da ƙyar na samu ta amince mukaje kitchen ɗin, duk abinda tasan zai iya ci
shi ta ɗiba masa, ta zuba a kwando ta fice riƙe da key ɗin motar da sukazo a ciki.

Coffee na haɗa na koma kaima Boss, yanata aikinsa hankali kwance, na ajiye
ɗan tray ɗin dana ɗora ƙaramar butar shayi da kofinta sai cokali a gabansa,
tsiyayawa nai na miƙa masa, batare da ya kalleni ba ya amsa yana faɗin, “Waye ya
fita da mota?”. “Aunty Batool ce” na bashi amsa a taƙaice. Baice komaiba yakai
kofin bakinsa, ɗayan hannunsa kuma yana amfani da mouse.

★★★★★★

Zuwa goma da rabi duk mun hallara gaban abinci, bayan gaishe-gaishe da
tambayar lafiyar juna mukai zaman karyawa, kowa nacin abinci cikin salama bandani
da naketa tsakurarsa, badan rashin daɗiba kuma, haka kawai dai nakeji bana sonci
kuma yunwa nakeji.
Jay ya lura bily batacin abincin sam, sai dai kunyar iyayensa ta hanashi
cewa komai. Ummah babba ce ta lura da hakan, saita kira Bilkisu. Tashi nai na
nufeta dan nazata wani abun zata sakani, sai dai ina zuwa ta jani ta zaunar kusa da
ita, da kanta ta shiga ɗuramin abincin duk da nace mata na ƙoshine, ina kallon
sanda boss ya sauke ajiyar zuciya. Daurewa kawai nake ina amsar abincin.
Boss ne ya fara miƙewa alamar ya ƙoshi, yaɗan kalli iyayen nasa yana
faɗin, “Bara naje na watsa ruwa kafin time ya ƙure, jirgin su Abbu ƙarfe sha biyu
zai sauka”. Cikin kulawa Ummah babba da ƙarama suka amsa masa.
Shigewarsa babu jimawa muma duk muka kammala, da taimakon su Anum na gyara
wajen, gudun kar kwanikan su bushe sai mukai zaman wankesu, muna wanke-wanken ina
tunanin abinda ya kamata na dafa mana da rana, dan koma daga ina ake kawo wannan
abincin bana buƙatar a cigaba da kawosa, ya kamata nima in-lows ɗina suci girkina
ai....

★★★

Jay na fitowa daga wanka ya samu wayarsa na haske kasancewar a silent


take, matsawa yay gaban mirror ya shiga shafa mai batare da ya duba mai kiranba ma,
bayan ya kammala yana gaban Wadrobe zai ɗauka kayan d

a zai saka ya kuma hangar wayar tana haske, guntun tsaki yaja, ya ɗauka kayan da
yake bukata ya fara sakawa, sai da ya shirya tsaf sannan ya nufi wayar yana idasa
saka maɓallan rigarsa. Gabansa ne ya ɗan faɗi ganin Batool ce ta jera masa har
missed calls kusan talatin, sai kuma number sojan da sukanyi magana da baba ƙaura
idan hakan ta taso. tabbas wannan kiran bana lafiya bane, dan kaf cikin ƴan uwansa
babu wanda ya kai Batool iya zama da shi da halinsa, inhar tai masa kira ɗaya tai
na biyu taga bai ɗaukaba bazata sake kiransaba sai idan shine ya kirata. Yana
ƙoƙarin kiranta sai gashi ta sake kira, ɗagawa yay da sauri....
Daga can Batool ta sake fashewa da kuka jin an ɗaga, a cikin tsananin
ruɗani tace, “Yayanmu akwai matsala, wasu mutane sunzo har gida sun tafi da Alhaji
Babba da baƙon mutumin nan”.
Wani irin yankewa ƙirjin Jawaad yay ya faɗi, furicin Batool ya jisane
cikin kunnensa tamkar saukar guduma, cikin rawar baki yace, “Su su.. Su wanene?”.
“Ban sansuba Yayanmu, ina ɗakin Alhaji babba ina gyarawa suka shigo. fuskokinsu duk
a rufe suke da facemask, nima nasan da sun ganni bazasu barniba, tun shigowarsu
nake kiran wayarka amma baka ɗaukaba, ina tsoron na kira su Ummah su ruɗar da kansu
shiyyasa ban kiraba.....” Bai bata amsaba ya katse kiran, ƙirjinsa na wani irin
lugude tamkar ana gasar dakan fura a kansa. Da sauri ya fice daga ɗakin, harya nufi
sashen Bilkisu sai kuma ya jiyo dariyarsu a kitchen ita dasu Nabeelah, can ya juya
ya nufa......
Muna tsaka da yima Anum dariya boss ya faɗo kitchen ɗin, yanayinsa kawai
ya sakani faɗuwar gaba, Anum da Nabeelah kam duk ɗauke numfashi sukai dan tsoro,
baice komaiba yaja hannuna muka fice, har munje ƙofa ya juna yana watsama Nabeelah
kallon gargaɗi, “Kucigaba da aikinku, idan kuma ƙafar wani ta fita a kitchen ɗin
nan saina ɓallata”. Kai kawai suka jinjina masa, ya ja hannuna muka ƙarasa ficewa
zuwa bedroom ɗinsa.
“Boss lafiya kuwa?”. “Babu lafiya Miemaa, yanzu Batool ta kirani........
Akwai matsala ace su Ummuna susan wannan maganar, musamman ma ita da nasan yanzu
babu wanda ta ƙagu ta gani kamarsa, dan haka kiyi shiru da bakinki yanzu zan tafi
can, kosun tambaya kice nafita amma zan dawo yanzun k.......”. Da sauri na katsesa
da faɗin, “Boss tare zamu tafi, nima bazan zaunaba”. “Bazai yuwuba Miemaa, idan
muka fita mu duka zasu iya tunanin wani abu”. “Dan ALLAH kayi haƙuri mutafi tare,
koba komai nima zanyi wani amfanin ai, zamana anan zaisa na kasa jurewa na tona
asirin komai”. “Miemaa!....” “Please boss”. Nai azamar katsesa. Bakinsa ya cika da
isaka ya furzar da ƙarfi yana ɗaga wayarsa dake haske. Ban saurari amsarsa ba
nashiga ƙoƙarin canja kayana.

Ta kitchen muka fita, bayan boss ya jama Nabeelah dogon gargaɗi akan ta
kama bakinta wlhy, idan har sukace mun fita sai yay gutsi-gutsi da ƙasusuwanta
yanda babu mai iya shaida itace harma Anum ɗin kanta. Daga haka muka fice, Sadiq
baizoba, saboda weekend ce, dan haka boss da kansa zaiyi driving ɗin.
Mahaukacin gudu ya ke zubawa tamkar shi kaɗaine da titin, to dama yaya
lafiyar giwa balle....., dama can shi ɗin ɗan babu sauƙine wajen gudu da mota,
balle yanzu data zamto na ƙare numfashi. Ko gezau banyi da gudun nasaba yau, gani
nakema tamkar baya gudun, sai faman kaɗa yatsun hannuna nake jikinna na wani irin
tsuma. Yayinda boss kuma yana tuƙi yana waya da su Oga Hafiz.
Cikin mintuna ƙalilan muka iso gidan, mun iske tawagar su Jabeer a gidan harma
da ƴan sandan zahiri, sai wasu daga cikin ƴan anguwa da abin ya faru akan idanunsu
su Hafiz nata musu tambayoyi.
Aunty Batool ta iso garemu da gudu tana kuka, riƙo hannunta boss yayi
idanunsa na sake kaɗawa suna sake komawa jajur fiye da yanda muka fito gida.
Bayanin duk yanda yanda al'amarin ya faru ta shiga yimasa kamar yanda tayima su Sir
Ahmad ma. Kasa cewa komai yay, sai jikinsa dake wani irin rawar bala'i, ƙwanjinsa
da jijiyoyin kansa na sake buɗewa, yanda ƙirjinsa ke sama da ƙasa kawai zai
tabbatar maka zuciyarsa na gudu maiban tsoro dake neman fin ƙarfin gangangar jikin
nasa. ya saki hannunta ya nufi inda su oga A

liyu suke. Matsawa nai na rungumeta muna hawayen tare, sai dai ni saɓanin ita ina
ƙarfafa zuciyata yau ina lallashinta, sai da naga ta tsagaita da kukan sannan na
ɗagota na share mata hawayen. “Ki kwantar da hankalinki aunty Batool, insha ALLAHU
zasu dawo, kosu wanene ALLAH bazai basu dama akan ƙudirinsu ba”. “ALLAH yasa haka
mami” ta faɗa wasu hawayen na sake jiraro mata. kiran da oga Jabeer yaymin ne yasa
na taimaka mata ta zauna a cikin motar.

Tun a yanda Jawaad ɗin ya taka birki sanda suka iso gidan su Sir Ahmad
sukasan ransa a matuƙar ɓace yake fiyema da yanda sukai hasashen ganinsa. ganin
Batool ta nufesa sai duk suka dakata daga yunƙurin zuwa inda yaken, bayan yabar
wajen ya nufesu ne, Sir Ahmad yay saurin tararsa cikin zafin nama yana riƙe
hannunsa “Jay! Ka kwantar da hankalinka, insha ALLAHU zamu gano inda suke, koma su
wanene suka aikata hakan basuyi nisa damuba a halin yanzu tabbas, yanzu haka har su
Jabeer sun fara ƙoƙarin gano inda suke. Ka nutsu banason ka fusata kanka da yawa,
domin nutsuwarka ce abar buƙatarmu fiye da komai a yanzu. shin akwai wani da kake
zargi ne?”.
Jawaad dake tsaye kawai yana kallon yanda su Aliyu da sauran ƴan sandan
keta kai kawo akan al'amarin ya lumshe idanunsa yana busar da zazzafan numfashi,
“Sir! Kowama zan iya zarga a halin yanzun, sai dai hakan bazai saka na kasa fidda
ɗaya a cikin dubu ba”. “Nasani gwarzona”. Sir Ahmad ya faɗa yana ɗan bubbuga
kafaɗar Jay ɗin cike dajin ƙarin alfahari da ƙwazon yaron.
Jabeer ne ya ƙaraso wajen riƙe da tab.. A hannu, yay salute ɗin Sir Ahmad
sannan ya kalli Jay dake kallonsa shima. “Boss ƴan iskan mutanen nan basu bar wani
alama ko kaɗan da za'a iya bibiyarsu ba, bayanan dake hannunmu ma a yanzu haka ko
motar da sukazo a cikinta babu Number ma, abinda bayanan mutanen anguwa suke faɗa
mana kawai motar baƙa ce, suma mutanen kuma baƙaƙen kayane a jikinsu, fuskokinsu a
rufe”. Shiru yay yana kallon Jabeer cike da nazarin maganganunsa, kafin kuma ya
kallesa yana ɗan cije lip ɗinsa na ƙasa, “Dama bana tunanin zasu bar wata alama ta
zahiri, sai dai dolene za'a samu ta baɗini Jabeer. Zamanmu anan gidan baida wani
amfani, inaga mu wuce office kawai”.
Jabeer yace, “Okay nima nayi wannan tunanin, dama isowarka muke jira muji ta
bakinka, dan yanzu haka dai Number shi Alhaji Babba muketa ƙoƙarin bibiya saboda
Batool tace tana zaton da ita ya tafi a jikinsa batare da suma maharan sun sani ba.
a yanzu haka dai wayar na nuna tana titin gambari gab da babban titin ƴan robobi na
gabashiya. Jami'anmu suma suna gab da isa wajen harda Aliyu”. Amsar Tab ɗin Jay
yayi daga hannun Jabeer da sauri....
Hakan yay dai-dai da isowar Bilkisu da wani tunani yazo mata a zuciya inda
suke. Sai da tai Salute ɗin Sir Ahmad itama sannan taɗan matsa kusa da Jay da
hankalinsa kega Tab... ɗin da ya amsa a hannun Jabeer, amma yasan da zuwanta, dan
ƙamshin turarenta ma ya ishesa shaidar tana wajen. “Sir anya kuwa wannan aiken ba
daga gidancan bane?”. Da sauri Jay ya ɗago yana kallonta, “Wanne a ciki?” ya faɗa
cike da ƙaguwa. “Inda na dawo daga farauta shekaran jiya”. Kafeta yay da ido dan
maganarta na tafiya bisa ƙamshin gaskiya. Ta ƙara risinar da kanta cikin girmamawa
a garesu, cigaba tai da faɗin, “Bazai yuwu ace dama ya barmu ba, dolene zai
bibiyemu kodan maigadinsa, sai dai bamu da tabbas, hasashene kawai nayi Sir”.
Jawaad yay wani ɗan murmushi yana maida duka hannayensa biyu ya goya a bayansa,
taku ɗaya biyu yay sai kuma ya sake juyowa, hannunsa ɗaya ya sauke daga bayan ya
tura cikin aljihu, ɗayan dake riƙe da tab... Kuma ya ɗagosa yana goga tab... Ɗin
akan hancinsa. Daga Jabeer har Sir Ahmad da bilyn duk kallonsa sukeyi. Wani
murmushin ya sakeyi da tsayawa cak, bily ya nuna da tab... ɗin hannunsa yana faɗin,
“Maganarki akwai ƙamshin gaskiya, dolene a cikin biyu a samu ɗaya, idan kuma nai
wani nazari zan iya ɗaurasu a mizani guda ya zama aikin haɗaka ne”. Ya ƙare maganar
yana maida dubansa ga sir Ahmad da ke binsu da kallo kawai. Kafin yace wani abu
Hafiz ma ya iso riƙe da waya alamar magana ya gamayi. “Mutanen nanfa inaga sun
farga da

wayar jikin Alhaji babba, sam yanzu bama ganinsu alamar an kashe wayar”. Kallonsa
duk sukayi, Sir Ahmad yace, “Dai-dai ina kuka daina samunsu?”. “Sir a Roundabout
ɗin titin General hospital”. “General hospital?”. Jay ya faɗa cikin sigar tambaya.
“Ƙwarai kuwa boss, ka duba ma zaka gani anan”. Tab... Ɗin Jay ya sake buɗewa, dai-
dai inda Hafiz ya faɗa shima nan ya nuna masa, ya miƙama Jabeer tab... ɗin yana
faɗin, “Yanzunan inason a bincikamin inda Alhaji Kokino yake, a kuma bincikamin
inda Alhaji Ali da Qaseem suke, sai Mr Gebrail shima”. Yana maganarne yana daddana
wayarsa daya ciro a aljihun wandonsa. Da mamaki na kallesa jin ya sako Dad da Yah
Qaseem ciki, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska yasa na gaza cewa komai, sannan
ma bani da wannan damar dan a fagen aiki muke matsayinsa na ogana ba miji ba. Da to
muka amsa masa kawai, muna barin wajen.
Sir Ahmad dake kallon Jay yace, “Miyasa ka lissafo waɗanan mutanen? Kana
zarginsu da aikata hakanne?”. “Sosaima kuwa Sir”. Jay ya faɗa yana ɗaura wayar a
kunnensa jin an ɗaga. “Munkaila kana ina?”. Bansan amsar da aka bashiba daga can,
ya gyara tsaiwarsa idonsa a sashen da su Bilkisu ke magana ita dasu Jabeer yace,
“Ka ajiye wannan aikin, yanzun nan kaje gidan Alhaji Ali a ɗakkomin maigadin
gidansa da kuku”. Kansa ya gyaɗa da sauke wayar.
“Jay ka sake sakani a duhu, wai ba kana magana bane akan Alhaji Ali dana
sani baban Qaseem? Da shi Qassem ɗin kansa?”. Fuskar Jay cike da murmushin takaici
ya jinjina ma Sir Ahmad kai, “Shi nake nufi Sir”. “To amma miya haɗashi da Alhaji
kokino da har kake tunanin zasuyi aiki tare?”. “Hasashene kawai Sir”. Ya bama sir
Ahmad ɗin amsa a taƙaice. Badan bai yarda da shi bane, yanason tabbatarwa kasafin
ya buɗe aikin kowa ya sani........

__________________
BABA ƘAURA
______________

Tun a safiyar yau baba ƙaura ya sa ake nemar masa Number Jay sai dai
ba'a samu ba, iya ƙoƙari sojan dake taimakama baba ƙaura idan zaiyi waya da Jay
yayi amma wayoyin Jawaad ɗin duk sun ƙi shiga, sai kusan goma na safe da ƙyar ɗaya
ta shiga, sai dai kuma anƙi ɗagawa kusan kira goma.
Ganin lokaci na sake ƙwacewa baba ƙaura yace sojan idan yasan inda gidan
Jay yake ya kwatanta masa. Sojan shima bai saniba, dan haka yacema baba ƙaura bara
yaje ya bincika ko za'a dace. Tunda sojan ya fita baba ƙaura ya kasa zaune ya kasa
tsaye, ba komai ya kawo hakanba sai abinda ya jiyo a daren jiya, ga lokaci yanata
sake tafiya kuma.
A jiya gaba ɗaya zaman ya gunduresa, jiyay yana sha'awar zagaya jeji, dan
haka tun bayan sallar la'asar ya sulale yabar Barrack batare da sanin kowaba sai
sojan nan da General ya ɗaura alhakin kula da shi akansa, yanda yaron ke masane ya
sakashi ƙaunarsa harma yake masa wasu abubuwa na taimako, sannan baya ɓoye masa
wasu abubuwan da suka shafesa, hakan yasa a fitarsa ta jiya ma ya sanar masa. Yayi
ninƙaya cikin jejin sosai jiya bisa al'adarsa ta farauta da sanin sirrin jajejin da
ALLAH ya bashi badan zaiyi farautar ba, dan ko karnuka babuma a tare da shi. Tun
daga farkon dare har kusan ƙarshensa bai fitoba yana a dajin. sai da ya gama jin
sirri mai girma daga shaiɗanun da suka maida wani yankin jejin nasu sannan ya fito,
gab da asubahi ya shigo cikin gari, ana shiga salla masallaci yana isowa Barrack. A
gaggauce yay alwala ya shiga masallacin shima. bayan an idar da salla ya saka sojan
nan ya nemo masa Number Jawaad zaiyi magana da shi, sai dai sam an gaza samunsa, da
aka samesan kuma ma sai bai ɗaukaba.....
Dawowar sojan tasakashi tsayawa cak daga kai kawon da yake faman yi da tunanin
daren jiya, cikin ɗoki ya sanar masa an gano family house ɗin su Jawaad ɗin, kuma
yana ƙyautata zaton a ciki jay yake zaune da iyalinsa. Baba ƙaura yayi murna, sojan
nan yay masa rakkiya har bakin hanya ya sakashi a napep da faɗama mai napep ɗin
inda zai kai baba ƙaura. Kasancewar gidan su Jay sanan nan gidane sai akaci sa'a
mai napep ya sani.
Da ƙyar suka samu maigadin ya sauraresu, danshi tsoron baba ƙaura ne ya
kamashi ganinsa sanye cikin fatun namin jeji, gashi babu hannu guda. Sai da baba
ƙaura yayta m

asa magiya sannan ya sanar masa cewar Jawaad ba nan yake zauneba yanzu, yana
gidansa da ke a A.Y street. Nanma sunsha daga kafin ya basu address ɗin, mai napep
ɗin da yake yanada kirki shine ya sake ɗaukar baba ƙaura zuwa A.Y. sai dai suna
shiga layin, motar Jay na fita. A gidan Jay ɗinma sunsha daga da maigadi kafin ya
sanar musu Jawaad ɗin baya gida ya fita babu jimawa, suka roƙesa koya san inda ya
nufa yace shi bai saniba. Sosai hankalin baba ƙaura ya sake tashi, burinsa kawai
yaga Jawaad, harsun baro gidan ya roƙi mai napep ɗin suka sake komawa. Tambayar
maigadi yayi ko ina drivern Jawaad ɗin?. Maigadi ya amsawa baba ƙaura a daƙile
cewar yau Sadiq baizai zo aikiba yana gidansa. “Dan ALLAH ka faɗa mana inda gidan
nashi yake zamuje mu samesa?”. baba ƙaura ya faɗa yana kallon mai gadin. A fusace
mai gadi yace, “Kai malam kafa isheni, taya zan faɗa maka bayan bansan kaiɗin
wanene ba? Nama sani ko cutar da waninsu zakayi, indai ma ogane yafi ƙarfinka dan
shima wlhy aljanin kansane da kake ganinsa nan”. Murmushi baba ƙaura yayi, yace,
“Yaro nafika sanin hakan ai, ka daure dai ka faɗa mana kokuma ka kira mana shi
direban a waya idan ya gammu shi yasan manufarmu”. Kamar maigadi bazaiyi ba, sai
kuma miya tuna oho masa ya ɗauka waya yay kiran Sadiq.
Babu jimawa saiga Sadiq mai napep shima ya kasowa, yana ganin baba ƙaura
ya rikice, dan baiyi zaton shiɗin bane da gaske. Haƙuri yayta bashi akan abinda
maigadi yay masa, baba ƙaura yace babu damuwa, so yake yanzunan ya kaisa inda
Jawaad yake shidai. Maigadi dai jikinsa yayi sanyi ganin yanda Sadiq ya bama baba
ƙaura muhimmanci, a take ya shiga bashi haƙuri. Baba ƙaura yay murmushi kawai yace
karya damu........

___________________________

Anbar ƴan sanda zagaye da gidan Alhaji babba, su Jay kuma suka
kwasa zuwa station dan aikin zaifi yuwuwa acan cikin sauri.
Bilkisu dai duk ta kasa sukuni akan sako Qaseem da Dad da Jay yayi a waɗanda
yake zargi, zuwa yanzun kam tafara yarda da saƙe-saƙen zuciyaryarta, anya kuwa babu
wani abu a rufe da bata saniba? Haka kawai mijinta da Dad bazasu ringa takun saƙa
na kamar wasu maƙiya ba, a dafa surukinsa ne, sannan mijin yayar mahaifinsa ne. Ta
tuna kallon kallo da suka dinga yima juna jiya duk da shi Dad yanata nuna babu
komai.....
Da wannan tunanin a ranta suka isa station, babu mutane da yawa saboda weekend
ne. Ni da su oga hafiz muka nufi office ɗin boss, shi kuma suka nufi na sir Ahmad..

Bamufi mintuna goma ba shima sai gashi ya shigo office ɗin ɗauke da
takardu a hannu.
Kujerar zamansa ya nufa yana faɗin, “Miemaa taso kiyi wannan aikin”. Miƙewa
nai daga inda nake zaune ni kaɗai na nufesa. Kujerar zamansa ya nunamin, babu musu
na zauna shi kuma ya shiga ƙoƙarin dai-daita Computer ɗin.
Oga Jabeer da Hafiz dake can gaban Computers ɗin dake gefe guda biyu suka
juyo suna kallonmu, Hafiz ne yace, “Boss babu watafa alamar waya data shiga
tsakanin Alhaji kokino da Dadyn su Shahudah gaskiya, amma Dad yayi waya da Qaseem
awa ɗaya da mintuna hamsin da uku da suka wuce. Barin inda nake yay ya nufesu,
“Zamu iya samun maganar da sukayi?”. Jabeer da hankalinsa ke ga Computer gaba ɗaya
yace, “Bazai yuwuba gaskiya, dan inhar mukai hakan zai gane, kasan wayar Qaseem
tana da tsaro kamar yanda namu suke”. Jay yayi ɗan jimm na tunani. Numfashi ya
furzar mai zafi yana dafe kansa dake sara masa, sai kuma ya zabura kamar wanda ya
tuno wani abu. “Jabeer ina zuwa, bara na turo muku Numbers ɗin nan, dukansu inason
mu tabbatar idan suna aiki a halin yanzun”. Yay maganar yana sake nufo inda nake,
drawer ɗin jikin table ɗin ya jawo, flash ne da yawa a ciki, ya shiga ɗakkosu ɗaya
bayan ɗaya yana duba rubutun da yay a jiki, cikin sa'a ya samo wanda yake nema,
miƙamin yay yana faɗin, “Saka shi”. Yanda yake min magana babu wasa tattare da shi
yasaka jikina har tsuma yake, sai da na gama dai-daita komai abubuwan dake cikin
flash ɗin suka bayyana sannan ya ranƙwafo kaina, hannunsa ya ɗora bisa nawa dake a
dafe da mouse muka ringa control ɗin Computer tare.
A haka Sir Ahmad da wasu jami'a

nmu manya biyu suka shigo suka samemu. Nan take aikin ya sake ɗaukar zafi, ni dai
ta ɓangarena da taimakon boss nakeyi. Kusan minti goma sha biyar mun duƙufa,
hankalin kowa nakan abinda ke gabansa akai knocking ƙofar office ɗin, batare da
jiran izini ba oga Aliyu ya shigo da sallama. Inda muke ya nufo bayan yayi salute
ɗin su Sir Ahmad. Bansan miya gwargwaɗa ma Boss a kunne ba, na gadai shima boss ɗin
ya miƙe ya nufi Sir Ahmad cikin zafin nama. Sai kuma suka fice shi da Sir Ahmad ɗin
daga office ɗin.........

_________________
BABA ƘAURA
_______________

Cikin mintuna ƙalilan suka iso station ɗin bisa taimakon Sadiq, sai dai
kuma securitys sun hanasu shigowa musamman ganin yanayin baba ƙauran, sun musu
roƙon duniya amma sun hanasu, Sadiq ya kira wayar Jay amma bai ɗagaba, hakan yasa
suka koma gefe cike da damuwa, musamman ma baba ƙaura dake matuƙar matse da son
ganin Jay.
Suna a wajen tsaye su biyu Sadiq na cigaba da kiran Number Jay sai ga motar
su Aliyu, harma an buɗe musu gate zasu shige Aliyun ya hango baba ƙaura ta mirror.
Sauke gilashin motar yay ya saka ɗaya daga cikin securitys ɗin yay masa magana da
baba ƙaura. Ganin shi ɗinne dai kamar yanda yay hasashe sai ya bada umarnin barinsu
su shigo. Bayan ya shige da motar ya samu waje yay fakin ya fito shi da waɗanda
sukabi masu ƙwamushe Alhaji babba, gaisuwa kawai yay da baba ƙauran ya shiga ya
sanarma Jay.

Duk da Aliyu ya sanar masa baba ƙaura ne hakan nbai hanashi yin mamakin
ganinsa har station ɗinsu ba, ya ƙarasa fuskarsa babu walwala, dan duk yanda yaso
aro fara'a ya azama fuskar tasa kamar yanda ya saba idan yaje wajen baba ƙaura
hakan ya gagara. Cike da girmamawa suka gaishesa har Sir Ahmad.
Kallonsu baba ƙaura yay ya ɗauke kansa yana faɗin, “Kagani har a wajen
aikinka ko?”.
Ɗan murmushi Jay yayi da cewa, “Babu komai baba, ai nasan zuwan naka mai
muhimmanci ne”. “Hakane” baban ya faɗa yana sake maido hankalinsa garesu sosai.
Yace, “Tun da safe na saka a nemomin kai amma hakan ya gagara, ba'a samunka da
farko, daga baya kuma ta shiga ba'a ɗagawa”. Kai Jawaad ya dafe, “Dan ALLAH kayi
haƙuri baba, wlhy na tsinci kainane a yanayin da komaima bazan iyaba”. “Gudun
faruwar hakanne ya sakani yimaka neman gaggawa ai daman, tun bayan wucewarka na
tafi jeji ne, acan ma na kwana, dan sai gabannin asubahi na shigo gari, sanda na
iso nan har an shiga salla. Na saka a nema min kaine domin isar maka da saƙon
abinda idona ya ganomin jiya a cikin jajin nan. Muhammad Jawaad lallai akwai
matsala babba dake tunkaroku, da idona na gani, na kumaji da kunnena, gashi rashin
samunka akan lokaci ya nunamin alamomin fara faruwar matsalar dana guda ma a
yanzun”.
Hankalin Jawaad a tashe yace, “Baba hasashenka duk haka yake, yanzu haka
zancen da nake maka anje har gida an ɗauke kakana, akan binciken inda zamu samesa
muke”.
“Wannan shine shirinsu na farko dama. Na zauna nayi ƙyaƙyƙyawan nazari
mutanen nan ba haka nan suke bibiyarka ba, akwai wani abu aƙasa wanda akwai jininka
a ciki, ina nufin cikin zuri'arku akwai wanda ke tare da mutanen nan.....” cike da
mamaki Sir Ahmad da Jay suke kallon baba ƙaura. Ya jinjina kansa yana cigaba da
faɗin, “Kar kuyi mamaki, neman duniya babu wanda baya ɓatarwa, lallai kamar yanda
na faɗa akwai wani abu a ƙasa, dan babu rami miya kawo rami? Bayan abubuwan dana
sani ke a hannunku akwai wani abu da kuka ɗakko a wani gida ne?”. Sir Ahmad ya
kalli Jay, shima ya kalleshi, sai kuma ya maida dubansa ga baban yana jinjina masa
kai. “Akwai wani tukunya baba, wanda.........” ya labartama baba ƙaura da Sir Ahmad
komai.
Baba ƙaura da keta faman jinjina kai cike da nazarin maganganun Jawaad ya
sauke nannauyan numfashi. “UBANGIJI ya baku kariya sosai to akan wannan aikin, dan
suna cikin ruɗani mai girma akan son gano wanda ya ɗauki tukunyarnan, amma sun gaza
gano komai, inuwar wadda ta ɗauka ɗin kawai suke iya gani, sannan har yanzu tsafin
nasu kuma bai iya nuna musu mahaifiyarka ta shigo ƙasarnan ba. Wannan hikima ce da
rahama daga UBANGIJI, inaga iyakar suce tazo shiyyasa komai

ya keta ƙwace musu. A taron da sukai daren jiya sun tattauna abubuwa da dama wanda
zarge-zarge da yawa sun sami rinjaye a kai kanka, sai dai a yanda na fahimta na yau
sai sun fisu muhimmanci. Dan haka nakeso ku kasance a wajen kai da matarka idan zai
yuwu, sannan lallai matsayinku na jami'an tsaro wannan shaiɗancin ya kamata ma ace
ku kawo iyakarsa ma baki ɗaya. Dan tabbas kakanka yana tare da su, acanne kawai
zaku iya samosa a halin yanzun dama wasu mutanen da aka kai a wajen bisa zalunci da
son zuciya”.
Boss ya cika bakinsa da iska ya furzar yana taunar lip ɗinsa na ƙasa da
ƙarfi. Kallon Sir Ahmad dake fahimtar dukan maganganun nasu a baibai yayi. sai kuma
ya maida ga baba ƙaura yana faɗin “Babu damuwa baba, amma kana ganin ita zuwa da
ita bazai zama haɗari ba?”. Ƴar dariya baba ƙaura yay yana kallon Bilkisu data fito
da waya a hannu ta doso su, “Babu wani haɗari insha ALLAHU, matar nan taka akwai
sirrika tattare da ita waɗanda ALLAH kaɗai yasan tushensu, amma haka kawai nakeji a
raina kamar sunada nasaba da taka ƙaddarar. Amma ita ɗin ba jami'ar tsaro bace?”.
“Eh jami'ar tsaroce, irin aikinsu ɗaya”. Sir Ahmad ya bama Baba ƙaura amsarsa. Baba
ƙaura ya sake faɗaɗa murmushinsa “Ka barta itama ta nuna bajintarta a aikinta da
ƙwazon da ALLAH ya bata, ALLAH yana tare daku a dukkan al'amuranku insha ALLAHU.
kudai kuci gaba da gayama ALLAH”. A tare suka jinjina masa kawunansu da faɗin insha
ALLAHU baba. “Karkuji komai, wannan tafiyar tafi ta farko sauƙi insha ALLAHU, ta
wani ɓangaren kuma tafi waccan haɗari, dan haka runduna zaku haɗa mata da tafi ta
farko indai aikin zakuyi da gaske” ya ƙare maganar dai-dai da isowar Bilkisu wajen.
Rissinawa nai na gaida baba ƙaura da banyi tunanin ganiba anan, ya amsamin
cike da fara'a da kulawa. Cikin girmamawa na miƙama Sir Ahmad takardar hannuna da
aka aikoni na kawo masa. Amsa yay yana dubawa, ni kuma na maida dubana ga boss da
yanayinsa ya bani tsoro. Da ido nai masa alamar ‘Lafiya?’. Kansa yaɗan girgizamin
kaɗan yana lumshe idanunsa dake jajur.......
Sir Ahmad ne ya katse mu da faɗin, “Jay inaga yanzu haɗa rundunar da zamu
tunkaru jejin ne ya dace, bara na nema mana jirage masu saukar angulu yanzun nan,
sai ku haɗa kayan operation ko”. “Okay Sir” Jay ya faɗa cike da karsashi na jami'i
mai cikakkiyar lafiya da zafin nama..
Tare muka koma da baba ƙaura office ɗinsa inda su Jabeer keta aiki cike da
zafin nama da ƙwarewa. Boss ya ɗan bigi tebir da zafi-zafi yana faɗin, “Ayi shirin
fita operation mun gano inda suke insha ALLAHU”. Duk juyowa sukai suna kallonsa da
mamaki, harni kaina kallon nasa nake, amma sai ya ɗauke kai yana nufar telephone
ɗin dake saman table ɗinsa yana jero sunayen waɗanda za'a kira yanzun nan”.
Cike da bin umarni Aliyu ya fice zuwa office ɗinsa domin aiwatar da komai,
shima bayan yayi waya da wani da bansan ko wanene ba ya ajiye yana kallona da nufar
ƙofa yace na biyosa ni da Dawood da suka dawo da Oga Aliyu yanzun.
Store ɗin station ɗin muka nufa, inda acan muka iske Sir Ahmad da wani ogan
mu shima suna haɗa bindugu. Muma aikin haɗa wasu makaman aka sakamuyi. Mamaki ya
kuma cika zuciyata, duk yanda nake hasashen al'amarin da alama ya wuce nan, nasan
Boss mutum ne mai muhimmanci a hukumarnan tamu, ya cancanci a nuna masa kowanne
irin halacci akan taɓa ahalinsa, amma yanda ake shirin fita operation ɗin sai
nakeji a raina kamar ya zarce na maido kakansa kawai. Cikin mintunan da bazasu gaza
talatin ba duk wani shiri an kammalashi, duk jami'in da aka buƙaci gani ya amsa
kira, a mamakina harda su Ummie su dukansu, Rose harma dasu Ada, sai sauran jami'ai
na departments ɗin da ba namuba ma. Dukanmu mun kasance cikin Uniform ɗin aiki, dan
boss ma da yake sanye da kayan gida a da sai gashi ya fito cikin Uniform harsu oga
Jabeer da Sir Ahmad ɗin kansa. An bamu bullet proof jacket duk mun sassaka, kafin
oga Hafiz ya rarraba mana bindugu harda kibiya ga waɗanda suka samu horo na
musamman a kanta, wasu kuma wuƙaƙe naga an basu manyan takubba, sosai mamaki abin
yayta bamu mu baƙin shigowa hukumar, dan zan iya cewa wannan shine operation na

farko gagarumi da za'a fita damu..............✍

Da ace zan iya sai nabi wasunku da bulala goma-goma a ɗuwawu aradu🙄, wlhy nafiku
son naga na kammala buk ɗin nan🤦🏻. Uzirin daya riskeni ya wuce dukan tunanin mai
hasashe, yanzunma dauriyace kawai dason ganin na faranta muku, saɓanin wasunku da
bakunansu ke furta abinda bai daceba a gareni😢🚶🏻.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭


[2/12, 7:51 PM] Wasila: *_ƘWAI CIKIN ƘAYA!!_*

*_Bilyn Abdull ce🤗_*


_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR... INA KUKE NE? 🔊🔊KU
MARMATSO, DOMIN ZAMAN JIRA YA KARE, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKA HADA HAZAKA DA
KAIFIN TUNANI SUN SAKE ZAGE DAMTSE SUN ZO MU DA WASU SABBIN SALON RUBUTUN SU,
WADANDA ZASUWA’AZANTAR, SU NISHADANTAR, KANA SY DILMIYA KU A KOGIN KAUNA, BASU
TSAYA ANAN BA SALON RUBUTUN SU YA SAKE ZUWA DA SABBIN TSARE TSARE NA DARUSSA DABAN
DABAN, DA KUMA HANYOYIN GYARIN JIKI DA WAJE._

_KADA KU MANTA MARUBUTAN ZAFAFAN DAI SUNE WADANDA SUKA YO MUKU HAR KASHI BIYU A
SHEKARAR 2020 DATA GABATA,: WUTSIYAR RAKUMI DA GUDU DA WAIWAYE NA BILYN ABDULL. 2-
DAURIN BOYE DA ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA.3-BURI DAYA DA QAUNAR MU NA MAMUH
GEE-4- SAUYIN KADDARA DA DAURIN GORO NA HAFSAT RANO. SAI 5-KAI MIN HALACCI DA
IGIYAR ZATO NA MISS XOXO.._

_A WANNAN SABUWAR SHEKARAR TA 2021 MA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE DAWOWA DA WASU
SABBIN DA’DADAN LITTATTAFAN NASU:_

_1_

_* SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA DA ABADAN TAZO MUKU DA SABON


LITTAFIN TA MAI SUNA: *(SIRADIN RAYUWA)💜*_

_2_

_*HAFSAT RANO* MARUBUCIYAR GUGUWAR SO DA RUHI DAYA, TA ZO DA SALON NATA LITTAFIN


MAI SUNA: *(ABINDA KE CIKIN ZUCIYA..*)💘_

_3_

_* MAMUH GEE* MARUBUCIYAR TARAYYAH DA EZNAH, TAZO DA SABON ZUWA MAI SUNA: *(MIN
QALB).*_

_4_

_*MISS XOXO* MARUBUCIYAR NAUFAL DA SAIFUL-ISLAM, TA YUNKURO DA WANI MAI SUNA:


*(KIBIYAR AJALI)*💜_

_5_

_SAI MARUBUCIYA *BILLYN ABDUL* WADDA TAYO MUKU KWAI CIKIN KAYA, DA CIKI DA GASKIYA
TA YINKURO DA WANI MAI TAKEN: *(YANKAN BAYA)*💝_

_RIGIJI GABJI DUKKAN WADANNAN LAGWADAR DADADAN LITTAFAN BIYAR ZASU ZO MUKU NE INSHA
ALLAHU AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA;_

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*


ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Page 59

..................Motoci na alfarma aka aika daga masarauta domin tarbo su Abbu a


airport kamar yanda aka aika tarbar su Umm-Anum, sai dai su masarauta aka wuce
dasu, inda acan ɗinma suka sami tarba ta musamman da mutuntawa ga mai martaba sarki
Sameer Saifudden da iyalansa, harma da ƴan majalissar sarki baki ɗaya. A yanda
masarautar take yau ko ba'a faɗa makaba kasan anyi manyan baƙi a cikinta, waɗanda
suka isa suka bunƙasa. An baje musu abinci na alfarma na ƙasarmu masu daɗi da
daɗaɗa zuciya.

Tun kafin tafiya ɗakko su Abbu Gimbiya Munaya tasa Amaturrahman ta nema
Number Jawaad, amma taƙi shiga sam, ta kira ta Bilkisu kuma ba'a ɗagaba. Hakan ya
bata mamaki matuƙa, dan tasan dai ai su Jay ɗin sunsan da zuwansu Abbu, a yanda
suka tsara al'amarin kuma daga tarbo su Abbu a airport zasu wuce masarauta ne harsu
Umm-Anum ɗin, bayan su Abbu sunci abinci sun huta sai su ɗunguma baki ɗayansu gidan
Alhaji Babba, daga can idan dare bai rufaba zasu ƙarasa family house ɗin su Jay. To
amma gashi har lokaci ya shige babu Jawaad ɗin babu dalilinsa.

Basu ji halin da ƙasar take ciki ba sai sai kusan isowar su Abbu da awa
ɗaya da rabi sannan takawa ya samu kiran waya daga gwamna akan ya buɗe television
yaga tashin hankalin da a yanzu shima aka faɗa masa game da manyan mutane da ake
ganin mutuncinsu a ƙasar, babban abinda ya razana gwamna kuwa harda wasu a abokansa
masu manyan muƙamai kuma a gwamnatin tasa.
Al'ajabi daya kume sarki lokacin daya buɗe tv kasa ƙwaƙwaran motsi
yayi, dan shima ɗin ai akwai waɗanda suke matuƙar gaisawar zuminci a cikinsu
sosai..........

_________________
ASIBITI
____________

Hankalin su Mom a tashe suna jiran fitowar Dr Tayyeb daga ɗakin


da aka saka Mama Badiyya kira ya shigo wayarta daga mai aikinsu. Kamar bazata
ɗagaba sai kuma mita tuna oho mata ta ɗaga wayar.
A matuƙar ruɗe Talatuwa dake kuka ta zayyane mata abinda ya faru game da
zuwan wasu mutane da sukace su ƴan sandane har gida suka tafi da kuku da maigadi.
A tsawace Mom tace, “What!! K bansan shirme da hauka kinji, ubanmi suda suke
gida kullum zasu aikatama ƴan sanda harsuzo gida su kamasu?”. cikin kuka talatuwa
tace, “Wlhy hajiya da gaske nakeyi, yawwa gama wannan da kikacemin shine babban
yaronku nan yazo gidan”. Da mamaki Mom tace, “Waye? Kina nufin Qaseem?”.
“E...e...eh shi hajiya, wanda hotonsa ke a falo sanye da baƙaƙen kaya tare
da Alhaji”. Jikin Momy har rawa yake wajen ambaton, “Da gaske Qaseem, yaushe suka
barshi ya fito to? Kinga bashi wayar muyi magana nima gani nan zuwa gidan yanzun
nan”. “T..t...to hajiya, bara nakai masa”. Talatuwa ta faɗa tana ɗan gudu wajen bin
bayan Qaseem dako kallon inda take baiyiba ya haye sama ɗakin Dad direct. Yana kama
handle ɗin ƙofar tana ƙarasawa garesa, da rawar jikin tsoro ta miƙa masa wayar tana
faɗin, “Alhaji ƙarami sannu da zuwa, gashi inji hajiya zakuyi magana”. Wani
mummunan kallo daya kaɗa hanjin cikinta ya zuba mata, cikin daka tsawa yace,
“Ɓacemin da gani kona halakaki wlhy”. Zabura Talatuwa tayi da gudu tabar saman,
yayinda Momy kuma taji komai ta cikin wayar, ita kanta tsawar Qaseem sai da ta
sakata cire wayar daga kunnenta ma.

Bata iya cewa sauran ƴan uwanta komaiba ta nufi hanyar fita daga asibitin
da hanzari, duk faman tambayarta lafiya? da sukeyi bata juyoba balle ta amsa musu
harta fice. Da kanta taja motar tabar asibitin zuwa gida.
Akan hanyar momy na nufar gida ta fahimci garin babu lafiya, dan kuwa babu
abinda take gamo da shi a tituna sai matsanancin holdup. Mafi yawancin inda traffic
light suke an haɗa cinkoso a wajen sosai, ga jirage masu saukar angulu da keta yawo
na kaikawo a sararin samaniya, wasu ma daf da mutane suke. Ratse ta ringayi ta
cikin anguwanni tamkar yanda wasu motocin taga sunayi. Da ƙyar ta samu kanta a
anguwarsu, tai fakin motar a ƙofar gida batare data kasheba saboda wani bahagon
ruɗani da ta sake karo da shi kuma, ƙofar gate ɗinsu a buɗe take, ga jami'an tsaro
sun zagaye gidan, cikin sake shiga ruɗani ta afka cikin gidan da sassarfa tamkar
zaga kifa, ananma wasu jami'an tsaron ta sake cin karo dasu a cikin gidan, talatuwa
na durƙushe gefe tana kuka ita da mai bayin fulawa.
“Kai lafiya?”. Mom ta faɗa hajijiya na neman ƙwasarta zuwa ƙasa. Wani
cikin ƴan sandanne ya bata amsa da faɗin, “Hajjaju wannan gidan yana a hannun
hukumane a yanzun, akwai bincike da za'azo ayi a cikinsa daga yanzu zuwa kowanne
irin lokaci”. Cikin tsawa da hucin ɓacin rai, “Mom tace kuɗin ubanwa muka sata to?
Muba ƴan siyasaba ba ma'aikatan gwamnati ba, amma za'a turo mana jami'an tsaron
binciken almun dahana da dukiyar ƙasa?”.
“A'a hajiya, mu ba jami'an tsaron almun dahana bane ba, jami'an tsarone na
farin kaya, da kuma amincewar Sir Qaseem Ali muke anan bisa Umarnin Sir Jawaad
Abdul-aziz Yusuf”. “Qaseem! Da Jawaad kuma?”. “Hakane hajjaju” ya sake bata amsa
kansa tsaye.
Wata ashariya da momy ta manta tama iyata ta kwaso ta dire bisa ƙasa tanayin
wurgi da jikkar hannunta, ta shaƙo wuyan police ɗin tana huci, a take sauran suka
zagayeta da bindiga. Murmushi Munkaila yayi yana ɗaga musu hannu alamar su barta,
ya kalleta fuska babu wasa zaiyi magana ta tare numfashinsa. “Kai shashasha kasan
mi kake faɗa kuwa? Ina Jawaad da Qaseem ɗin suke?”. Ɗan murmushi yay mata yana zame
hannunta a wuyansa ya gyara rigarsa, “Sir Qaseem yanzu ya fita, Sir Jawaad kam yana
filin daga”. Sake rikicewa kanta ya nemayi, batare data nutsu wajen fahimtar inda
batunsa ya dosaba ta fice a gidan tamkar wata mahaukaciya.
Mota ta sake shiga tabar anguwar batare da tamasan kalar tunanin daya dace
ace tayiba, kanta tsaye station ɗin su Jawaad ta nufa, sai dai ɗan karen holdup ɗin
da take fuskanta a yanzun ya zarece na ɗazu data riska tsakanin asibiti zuwa
gida............

___________________
JAY-QAS
________________
Koda tawagar su Jawaad suka iso cikin gari cike suka iske station
ɗinsu da manyansu da ƴan jaridu, abu na farko da suka farayi shine gabatar da
sallolin azhar data riskesu a can da kuma la'asar da a yanzu aketa yinta.
Suna idar da sallar ƴan Jarida sukai musu caa aka, Jay dai bai saurari kowaba
daga shi har Sir Ahmad da sauran manyansu.
Cikin son ƙure mutane irin na ƴan jarida ɗaya a cikinsu ya juya ga masu
ɗaukar rahoton gidan tvn su yana magana a harzuƙe. “To jama'a kamar yanda kukai
hasashe dai hakanne ta kasance, dan kuwa munga alamar rufa-rufar da muka saba gani
ga jami'an tsaronmu idan laifi ya shafi manyan ƙasa yau gashi ta tabbata, to ta
yayama zasu yarda su buɗe komai wa duniya bayan daga kawunansu sai surukansu da
abokan iyayensu dama iyayen nasu. Haka za'a kifemu bayan kwana biyu muji shiru,
bayan kuma tarin gawarwaki da mutanen dake a cikin mawuyacin hali da aka amso a
hannun waɗan nan miyagu ƙuru-ƙuru duk mun gansu. ALLAH dai ya ƙyauta, dama ba sabon
abu bane irin wannan a ƙasarmu ta gado. idan kaga ana yayata mai laifi da cecekuce
da tada jijiyar wuya ga jami'an tsaro to talakane ya aikatashi, amma idan su masu
faɗa ajinne suka aikata sai a rufe komai ruf da sunan kare mutuncinsu ko maganar
shiga kotunsu bakaji balle musan an yanke musu hukunci. To kenan mu talakawa bamu
da suturar mutunci ne? shiyyasa ake ƙwance mana zannuwa a kasuwa?”.
A take wajen ya ɗauki ƙananun maganganun sauran ƴan jaridar, kowa na
ƙoƙarin ɗaukar zancen ɗan jaridar nan ya zama sinadarin zazzage tasa maganar dake
cin ransa.
Ganin abun na neman kawo hatsaniya har wasu cikin ƴan jaridar na fassara
abun da rufa-rufa Jay ya dawo garesu rai a ɓace. Ɗan jaridar da yay maganar Jawaad
ya kafe da kallo idanunsa na sake rinewa zuwa jajur, duk da azabar ciwo da kansa ke
masa haka bai hana maida masa murtaniba cikin tsananin ɗacin murya, “Kar kai
azarɓaɓi akan garin daka shigo cikinsa baƙo. Karka yankema littafi hukunci abisa
bangonsa, duk sharhin da zakayi batare daka buɗe rubutun cikinsaba kuskurene kawai
da son zuciya zai biyo baya. Alokacin da jami'in tsaro yake filin daga shi kaɗai
yasan wane irin kwazazzabo da ƙalubalene rayuwarsa ke fuskanta, da ace yanda ku ƴan
media kuka iya yayata al'amari haka kuke bama jami'an tsaro gudunmawa wajen kare
fituntunun da ƙasa ke a ciki da kowama ya zauna lafiya a duniya. Idan ƙoƙarinmu na
aiki da jajircewa wajen tsayawa mu tantance ke hantarar ra'ayinka akanmu, to kasani
sauyi ba namu bane, kai da irinkane zaku sauya. Duk lokacin da mukejin matsayinmu
ya girmama a duniya wajen jama'ar cikinta, tomu samu gazawa akan ƙoƙarinmu ta
ɓangaren aikinmu ko kasantuwar ɗaukakar tamu. Daga hakanne zamuga muɗin ba komai
bane wajen waɗan nan al'ummar dake ɗaga darajojinmu da girmanmu a bakunansu da
muryoyinsu. Daka zama mai ƙoƙarin ruruta wutar da bakasan tushentaba, mizai hana ka
ajiye aikinka ka koma gidanka ka ɗaura zani kawai, koba komai ƴaƴanka zasu samu
magirkan abinci biyu, shashasha kawai”.
Tsitt wajen. yayi tamkar ruwa yaci kowa, sai su Sir Ahmad kawai dake murmushi
da bin Jay ɗin da kallo tamkar yanda suma ƴan jaridar da sauran jami'an suka
rakashi da idanu harya shige.
Jabeer ne ya matsa garesu cikin ɓacin rai shima, ya sake kallon ɗan jaridar
nan da maganar Jawaad ta sakashi duƙar dakai dan yaji kunya sosai da ganin
kuskurensa akan kalamansa. “Aikin jarida ba neman kuɗi bane ko shiga rigar siyasa,
aikine mai daraja abin girmamawa ga maiyinsa, ita daraja da gaskiya ake samota bada
son a sani ba, kai da kayi waɗan nan kalaman kayisune bisa raɗin kanka kawai ko an
sakaka badan aikin jarida ya baka damar yin hakanba, kai tsaye kake anan domin
neman abinci wa iyalanka dake gida cikin kwanciyar hankali, shiko wannan da kakema
gugar zanar cewar akwai kawunsa da surukinsa shiyasa ake rufa-rufa, tare da nasa
iyalan ya shiga cikin jejin da baida tabbacin fitowa a raye. Atunaninka akwai
sadaukarwar data kai wannan girma kuwa? Ku daina zubarma aikin jarida mutunci dan
aikine na masu mutunci a kowanne lungu da saƙo na duniya, sai dai kaicon irinku
masu girmama fitina da riritata tai faɗin da zata buwayi wanda kuke tunanin kun
tozartar harta dawo ga iyalanku kuma cikin aikin jarida, baka dace da wannan
aikinba sam, ya kamata ka ajiyesa ka koma ka saka rigar siyasa, inaga kalamanka da
nuna iyawarka zatafi dacewa dacan ɗin”. Yay maganar da watsa musu harara shima
yabar wajen.
Sosai jikin duk ƴan jaridar ya sake yin sanyi, masu ƙara gishiri da magi akan
batun sai suka koma gyara harsunansu suna miƙa rahoto mai inganci dan an tunatar
dasu abinda suka manta domin kawai neman ɗaukaka da birgewa.

Duk jarumtar da Qaseem ke arowa yana ƙara ƙarfafa kansa da ita sai hakan
ya nema gagara, kalaman Jawaad dana ɗan jaridar nan sun bala'in taɓa ruhinsa da
zuciya, yabi bayan Jay hawaye na zurara saman fuskarsa batare da yayi tunanin
gogewaba. A jikin ƙarfen lifter Qaseem ya iske Jawaad ya kife kansa dake tsananin
sara masa, bai iya cewa dashi komaiba ya wuce zuwa office.
Ƙamshin turaren Qaseem ɗinne ya fargar da Jay zuwansa, ya ɗago a hankali
yabi bayan Qaseem dake kan lifter ɗin da kallo harya gama hayewa, harya maida kansa
zai sake duƙarwa sai kuma ya zabura cikin faɗuwar gaba, haka kawai zuciyarsa ta
ɗarsa masa wani abu dangane da Qaseem, yariga yasan yanda yake da zafin zuciya.
Cikin zafin nama ya haye lift... ɗin shima, ganima yake bata sauri gaba ɗaya, sai
faman kallon agogo yake dukda kuwa a mintuna biyu kacal take kaisu.
Da gudu ya ƙarasa office ɗin Qaseem ɗin, yana taɓa ƙofar ya jita a rufe,
hasashensa ya zama gaskiya kenan?, Qaseem ya shiga office domin aikata duk abinda
ransa ya raya masa, baya yay ya daki ƙofar office ɗin da masifar ƙarfi, sai dai
bata buɗeba amma ta girgiza. “Innalillahi...” ya faɗa yana bubbuga ƙofar da ƙwala
kiran sunan Qaseem, sai dai ko sau ɗaya Qaseem ɗin bai amsa masaba, rikicewa Jawaad
ya sakeyi, yabar wajen da gudu zuwa office ɗinsa dan ya tuna akwai key ɗin office
ɗin Qaseem ɗin a wajensa wanda Sir Ahmad ya bashi ranar domin ɗaukar wasu files a
ciki, da ƙyar ya iya gano keys ɗin saboda a rikice yake, yana ɗauka ya dawo da
gudu.

Jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar Qaseem daya samo bullets da ƙyar cikin office ɗin
nasa ya ƙara azama wajen ɗurasu cikin bindigar yana kuka shaɓe-shaɓe da hawaye.
yana gama zuba bullets ɗin cikin bindigar Jay na buɗe ƙofar ya shigo da gudu,
saurin ɗaurawa a kansa yay da rawar jiki yana ƙoƙarin saka ɗan yatsansa saman
kunamar bindigar jikinsa sai tsuma yake.
Da matsanancin ƙaraji Jay yace, “Qaseem!!! Karkayiii!!!!!” yay maganar cikin
wani irin doka mahaukacin tsalle ya dire gaban Qaseem ɗin da wawurar hannunsa yay
sama da shi harsashin da Qaseem ɗin ya harba ya samu p.o.p ɗin dake office ɗin.
Yanda Jay ya riƙe haka Qaseem ma yaƙi saki, sai da suka ƙarar da harsasan duk biyar
sannan Jawaad ya ɗauke fuskar Qaseem da mahaukacin mari cikin gushewar hankali.
Wannan harbi shine ya maido hankalin su Sir Ahmad wajen, yayinda ƴan jarida
da sauran mutane suka fara gudu sun zata hari aka kawo.
“Baka da hankali ne!!!? Wace riba kake tunanin samu a kashe kanka
da zakayi Qaseem? Kaifa musulmine! Taya zaka bari tunanin aƙidar yahudu da nasara
har takai mizanin tasirin zama a zuciyarka irin haka? kai ƙoƙarin salwantar da
rayuwarka da kanka!!! Kasan kuwa hukuncin wanda ya kashe kansa a addinin
musulunci?. To sunansa KAFURI!!! kuma wlhy WUTACE zata zama sakamakonsa!!!”. Jay ya
faɗa yana huci da nuna Qaseem ɗin da hannu.
A zabure Qaseem ya hankaɗa Jawaad yay baya yana faɗin, “Bani da hankali
Jawaad, wlhy da gaske na haukace, tabbas na haukace, minene amfanina idan na zauna
a raye a wannan duniyar da babu komai a cikinta sai ruɗani?!!” ya finciko rigar Jay
jikinsa na rawa, hawaye na zuba masa babu ƙaƙƙautawa, “Idan ka hanani kashe kaina
mi kakeso nayi Jawaad? Wacce irin amsace dani da zan bama duniya akan mahaifin da
nake kallo babu kamarsa a da? Matsayin suruki kawai ya taɓa amsawa a gareka amma
akai maka gugar zana da halayyarsa yanzun, to inaga ni da yake mahaifina!!, da wane
idanun kakeson na sake kallonsa Jawaad?! Dan ALLAH na roƙeka ka barni na kashe
kaina na huta!!”.... Ya ƙare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya da ya saka
jijiyoyin kan Jawaad sake mimmiƙewa shima hawayen na taruwar masa a idanu. Jawo
Qaseem yay ya rungume a jikinsa suka fashe da kuka a tare.....😭

(Kai jama'a, wlhy zuminci ya wuce gaban wasa komai lalacewarsa😭😭)

Dalilin go-slow da Mom ta riska a hanya yasa ta iso station ɗin a


wahale cikin dogon jinkiri, da kutsa-kutsar shiga cikin ƴan jarida ta samu shiga
ciki da ƙyar, inda shigar tata tai dai-dai da harbin harsasai biyar da Qaseem da
Jawaad sukayi. Da wannan ruɗanin da jama'a suka shiga ta samu damar bin ayarin su
Sir Ahmad zuwa office ɗin Qaseem dan ta sani, bata fahimci can su Sir Ahmad ɗin ke
yunƙurin zuwaba saida taga sun isa tare da su inda itama ta dosa.
Itace farkon shiga office ɗin, sai tai tsaye turus tana kallon Qaseem da
Jawaad dake rungume da juna da dauraren kalamansu.
“Qaseem hakan ba mafita bane ɓata ne, ba'a samun hutu da saɓon UBANGIJI
bisa ganganci, ka daina irin wannan tunanin”. “Dolene nayi Jawaad, ƙo Bilkisu da
tazo a ƙarshen ƙaddarar kunyarta nakeji balle kai da sauran mutane, nayi nadamar
kasancewata jininsa wlhy Jawaad”.

Da sauri Momy tazo ta fincike kafaɗar Qaseem ta matsar da shi baya daga
jikin Jawaad, batare da ta tsaya ta gama fahimtar matsalarba, jin sunan bilkisu
kawai da tai a bakin Qaseem ya sakata harzuƙa da fassara matsalar akan bilkisun ne
komai ke faruwa ma kawai, hawaye na zirar a kumatunta tace, “Qaseem wai mi kakeyi
hakane? akan tsintacciyar mage, kake wannan hanƙoron da tura mana ƴan sanda gida
saboda cin zarafinmu? Akan butulu da ya wulaƙanta ƴar uwarka har kake iƙirarin
mahaifinka ya shirya tarwatsaka? TSINTACCIYAR MAGE! YARINYAR DA MUKA ƊAKKO A
TSAKKIYAR RANA! YARIYAR DA......”

“Da haɗin bakinki kenan mijinki ke aikata komai!!” Qaseem ya faɗa cikin
matsanancin fushi tamkar zai haɗiye Mom, baya tai da sauri jikinta na rawa, cikin
rawar murya tace, “Qaseem anya kana cikin hankalinka kuwa? Miya samu kanka? Ko an
sauya mana kai ne?”.
“Komai ma ya sameni fiye da yanda tunaninki ke baki ke da shi. Tun bansan
kaina ba ke da shi kuketa nunamin banida wani maƙiyi a duniya sama da Jawaad, Why?.
Mom! Nace Why? Shiɗin baɗan ɗan uwanki bane?, shi ɗin ba mijin ƴarku bane? Miya
aikata mai zafine wai a gareku da har yau ban taɓa saninsa ba ni?......”
“Qaseem!!” Mom ta faɗa cikin tsawa tana fashewa da kuka.
Cikin ficewar hayyaci Qaseem yace, “Eh ki kira sunana koma sau dubune,
gaskiyace bazan taɓa fasa faɗaba, to idanma baki saniba yanzu zan sanar miki, idan
kuma kin sani bara na maimaita miki. Ita wannan tsintsiyar magen da kike magana
MIJIN naki ya tsintota daga ranar ne dan ya jefata cikin abinda yafi ranar zafi,
cikin wuta yay niyyar jefa mata rayuwa saboda cimma burinsa, mahaifinane shi amma
nasha zarginsa da aikata abubuwa marasa ƙyau a cikin gidan nan, amma da naso ɗaukar
mataki saina gaza hakan, na tabbata dukkan ƴan aikin da akai raping a gidannan
shine yay musu.....”
Tsawa Mom ta daka ma Qaseem jikinta na matuƙar rawa, “Qaseem!! Mahaifinka
zaka ƙullana sharri irin wannan saboda Jawaad da Bilkisu?”.
Da ƙarfi Qaseem ya daki tebir ɗinsa, kayan sama suka tarwatse, ya matsa gab
da Mom yana nunata da ɗan yatsa ƙirjinsa na sama da ƙasa na kumburar zuciya. Ya
cigaba da faɗin, “Tun kin nuna bakisan komaiba bara na faɗa miki to, tun lokacin da
akaima ƴar matarnan Amina fyaɗe a cikin gidanmu na gaskata hakan a cikin raina,
domin kuwa lemon da aka ajiye ta sha lemo ne da kaf gidan nan shi kaɗaine ke
shansa, hakanma yasa ba'a ajiyesa a fridge ɗin kitchen sai na falonsa kawai, ko a
falon ƙasa inhar baya ƙasar kwashewa kike ki maida masa sama, to tayaya akai ranar
yaje kitchen har yarinyar ta gani ta ɗauka ta sha bayan shi mai shan ma baya nan?
Abu na biyu sai da na ɗauki kwalin lemon a bola naje nai bincike akan ɗan sauran
cikinsa na gane magani ne mai ƙarfi aka saka a ciki kuma a ƙalla ya kai kwanaki
biyar da zubawa, abu na uku na zauna nayi dogon nazari da tunani harna gano ainahin
maganain da akai amfani da shi, sai kuma kwatsam na tunano na taɓa ganin maganin a
wajen Dad amma a wancan lokacin sai ya gayamin na ciwon bayane dan na gansa da
shine a bazata, da yake kuma ban kawo komai a rainaba sai ban amsa na karanta ba a
lokacin. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al'amuransa, sai dai abin mamaki
bana iya cewa komai akan dukan abinda zan gani. to bara nama faɗa miki abinda baki
saniba, a dukkan tafiye-tafiyensa cikin kashi uku biyu bayinsu yake ba, idan yace
yabar ƙasarnan tafiyar sati biyu to kwana huɗu ko sati guda ya keyi ya dawo, da
wannan makircin nasa yake amfani wajen aikata laifi a rasa wanene keyi a gidan, Mom
ya kamata kiyi tunani da hankalinki, a dukka masu aikinmu uku da akai Raping a
gidanmu duk sai baƙya nan ake aikatawa, kuma da anyi washe gari ko kwana biyu dayi
Dad yake dawowa.......”
Ƙasa Mom ta zube tana kallon Jawaad dake tsaye kawai yana kallon tamkar wani
gunki, tun fara maganarsu baice komaiba bai kuma motsa ba. hawayene ke kwarara a
idanun Mom tamkar an buɗe fanfo.
Qaseem ya nuna Jay da faɗin, “Kayi haƙuri Jay ka gafarceni, zan faɗi wani
abu a kan matarka duk da bata a wajen nan, tunda Bilkisu tazo gidanmu ban taɓa
jinta a zuciyata da sunan soyayya ba, sai dai ina sonta matsayin ƴar uwata kawai.
Amma tun randa na farka a barci naga Dad tsaye kaina a cikin ɗakina naji duk duniya
babu wadda nakeso sama da yarinyar nan, ga wata sha'awarta mai tsanani inaji wadda
inhar zata kasance kusa dani sai naji inason taɓa mata jiki, abin mamaki duk wannan
sha'awar tata da nakeji ban taɓa jin zan iya lalata mata rayuwaba, ni dai kawai
burina na taɓa jikinta ko nayi kissing ɗinta na rungumeta shike nan. Da ya ke kuma
yarinyace mai tarbiya ko hannunta bata yarda na taɓa sai ta nunamin ɓacin ranta.
Kuma saifa ina a kusa da itane nakejin hakan, amma da zarar bama tare da juna ni
mantawama nake da ita gaba ɗaya. A daren da Dad ya fara shigo mata ɗaki har aka
tsoratamu da ƙara a gidannan nine na fara fitowa, ni duk zatona mai gadine wani abu
ya sama, shiyyasa nai gate kai tsaye, ina isowa maigadi na buɗema Dad ƙofa ya fita
a gidan....”
Dafe kai Jawaad yayi da sauri zuciyarsa na wani irin matsanancin harbawa
da sauri-sauri, duk da Dad yake zargi dama hakan bai hanashi jin maganar tai masa
nauyiba a ƙwaƙwalwa da zuciya....
“Ƙwarai kuwa Dad” Qaseem ya bama ya sake maimaitawa yana kallon Mom cikin
ido, “A tunaninki mai aƙidar kar ƴan uwansa su raɓesa ne zai ɗakko budurwa kamar
bilkisu ya ajeta gidansa dan ya ƙyautata mata rayuwa kawai? Aini tun washe garin da
aka kawota gidannan na ganta kuma akai min bayanin zuwanta nasan akwai manufa a
zuciyarsa game da ita, sai dai narasa ta wace hanya zan kuɓutar da ita? Wannan
mijin naki da kike ji da gani ramin bushiyane daga shi sai ƴaƴansa, ke kuma matarsa
kura ce kema daga ke sai ƴaƴanki. Bara na sake maimaita miki shine keta bibiyar
rayuwar marainiyar ALLAH akan fyaɗe har cikin gidan aurenta, da yaga bazai cimma
burinsa cikin sauƙiba shine ya tafka mana asirin da har nai maganar shirya aurenta
duk da a zuciyata sam ba haka bane ba. A gaban duniya ya nuna cewa ya ƙyautata mata
rayuwa, zai kuma aurama ɗansa jininsa ita, amma sai ya zagaye ta bayan fage shi da
ɗan uwanki Uncle Nasir suka zurmaki a ciki da ɗauraki a dukkan hanyoyin da suka
gama tsarawa, ke kuma kika hau saboda baƙya son aurenmu bisa naki gurɓataccen
tunanin na jahilci da son zuciya. Kuka ɗakko hayar ɗan fir'auna akan ranar ɗaurin
aure za'a aura mishi ita, ni kuma zaɓinku, daga baya sai ace mistake aka samu, shi
kuma dama kunbiyasa akan karya sake ya saketa duk bala'in da za'ayi har sai ƙura ta
lafa an kaita gidansa. sai shi Dad yaje ya cika burinsa a kanta kawai batare da
kowa yasan hakanba har ke kanki. Sai dai UBANGIJI ba azzalumin sarki bane, sannan
shi yana dubi da ƙyawawan zuciyoyi masu tsoronsa da biyayya a garesa, ashe Jay ya
saka ana bibiyar dukkan al'amarinsu basu sani ba..........”
Zubewa Mom tai ƙasa kawai tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai
tare da riƙe kanta da ke juya mata. Jawaad yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa da
mai dawa kan Qassem. Murmushi mai ciwo da ƙunar zuciya Jay yay yana tura ɗayan
hannunsa cikin aljihu, ɗayan kuma ya dafa kafaɗar Qaseem sukaima juna murmushi.
Takawa ya sakeyi gaban Mom ya tsaya har lokacin fuskar tasa da murmushin, ya
durƙusa a gabanta yana haɗiye ɗacin daya tokare masa maƙoshi, “Har yanzu ke uwace a
gareni Mom, yayar mahaifina, duk da ina zargin kina cikin waɗanda suka tarwatsa
masa ahali”.
Da sauri Mom ta ɗago tana kallon Jay, ta shiga girgiza kanta tana hawaye,
“Jawaad dan ALLAH kar kaimin wannan mummunar zargin, mi Abdul-aziz zaimin niko a
duniyarnan da har zan tarwatsa masa a hali?......”
Miƙewa Jawaad yayi yana ɗage kafaɗa da taɓe baki, “Wannan amsar a gaban alƙali
zaki badata Mom ba ananba”.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Aysha wannan wace irin ranace”. Mom
ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka.
Qaseem da yakejin kamar ace yau ɗin ranar barinsa duniya ce yace, “Momy
wannan ranace ta tonon silili, ranace mafi muni da a garemu bisa ga son zuciyar
mijinki, rana ce da duniya suka san wanene shi? Mom Dad ya cutar da rayuwarmu,
kaicon dukiyar da zata kasance haramtacciya ga mai ita, ki kalla yanda ake nunasu
cikin ƙasƙanci dan ALLAH, wace riba sukaci? Wane alfahari suka barmana muyi? Wane
tunƙaho da taƙama ya rage mana kuma?”.
Mom da batasanma wainar da ake toyawaba game dasu Dad sai yanzu da Qaseem
ya nuna mata a tvn office ɗinsa a take ta ƙwalla ƙara ta zube yaraf a sume.
Jay daya fice ƙofar office ɗin ya tsaya dansu Sir Ahmad tuni suka bar wajen
ganin maganace data shafi family ya dafe kansa da rumtse idanunsa da masifar ƙarfi,
dan yaji dukkan abinda Qaseem ɗin ke faɗama Mom, ya kuma tabbatar ƙarar tata nada
nasaba da ganin abinda ya farun.

___________________________
Dr Tayyeb hospital
_______________________

Kamar yanda ƙarar kai kawon jirage ta ɗauki mafi yawan mutanen
dake cikin asibitin haka ta ɗauki tasu Anuwar dake zaune jigum-jigum suna jiran
farkawar Umm-Anum, dan Dr Tayyeb ya sake shiga ya dubata, ya kuma musu bayani akan
su kwantar da hankalinsu da ruwan da aka saka mata ya ƙare zata farka normal insha
ALLAH.
Aunty Batool ce ta fara miƙewa ta leƙa ta Window'n da suke a kusa da shi,
da ɗan mamaki ta juyi tana kallonsu Ummah da faɗin, “Anya kuwa yau garin nan lafiya
yake? Helicopters nefa na sojoji keta yawo wannan ƙarar da mukeji”.
“Helicopters kuma? To miya faru kuma?”. Ummah ƙarama ta faɗa tana miƙewa
itama ta leƙa. Tabbas kuwa zancen Batool gaskiyane, dan har wasuma dake cikin
asibitin sun fara fita waje. “Gaskiya garin nan babu lafiya kam”. Ummah ƙarama ta
sake faɗa tana nufar ƙofa.
Da sauri su Anum sukabi bayanta harda Batoul da Anuwar ma daya bisu a ƙarshe
shi da Ummah babba, sai dai Ummah babba na gabansa.
“Ya salam”. Anuwar ya faɗa da sauri saboda karo da sukaci da wani bawan
ALLAH dake ƙoƙarin shigowa shi kuma Anuwar ɗin yana yunƙurin fita. A kusan tare
suka buɗe baku zasu bama juna haƙuri sai hakan ya gagara kowa ya cak a tsaye baki
buɗe jiki na tsuma. Idanun Uncle Sulaiman tamkar zasu faɗo ƙasa dan ruɗani da
al'ajabi, cikin sarƙewar harshe yace, “Ja...waa...” sai kuma ya gaza ƙarasawa ya
girgiza kansa yana haɗiye yawu da ƙyar.
Shiko Anuwar wani irin yamutsawa jininsa keyi da kansa, ya kafe Uncle
Sulaiman da kallo tamkar ya samu television ɗin kallo. A haka Shahudah da sauran
ƴammatan family ɗin sa'anninta suka iso wajen suma zasu koma ciki. A take duk
sukaja wani wawan birki suna kallon Anuwar.
“Kai!!”
Shahudah ta faɗa daɗan ƙarfi tana matsawa gab da Anuwar da binsa da kallo daga sama
har ƙasa tana zagayashi. Nannauyan numfashi Anuwar ya sauke da ɗan lumshe idanu ya
kalato busashen yawun daya rage masa ya hadiye da ƙyar da raɓawa ta gefen Uncle
Sulaiman zai wuce. Caraf Shahudah ta riƙo hannunsa jikinta na rawa. “Kai dan ALLAH
wanene kai?”.
“Muhammad Anuwar Abdul-aziz yusif tafida”. Wata murya dake a bayansu ta
basu amsa saɓanin shi Anuwar ɗin da sukaima tambayar. Juyawa sukai da azabar sauri
har Uncle Yusif na neman zubewa ƙasa wajen rawar jiki.
“Hajiya Mariya, kinsan mi kika faɗa kuwa?”. Uncle Sulaiman ya faɗa yana
ware idanunsa akan Ummah babba data basu amsar.
Murmushi mai ciwo Ummah babba tayi tana kamo hannun Anuwar ɗin cikin nata,
“Alhaji Sulaiman ai ko baku sami wannan amsarba ya kamata kuyi tunanin hakan direct
tunda wanda ya mutu baya dawowa ai ko? Kuma koda ace yaya nada rai ai bazai zauna a
wannan ƙuruciyarba tunda har Jawaad daya bari matsayin ɗa ya wuceta”.
“Haj....h...ha..hajiya mariya kin sake sakani a ruɗani wlhy, a ina Abdul-
aziz ya samu ɗa bayan Jawaad kuma?”.
“Biyoni da zakayi shine kaɗai zai baka amsar dukkanin tambayoyinka”. Ummah
ta faɗa tana murmushi da kama hannun Anuwar suka nufi corridor ɗin da ɗakin da aka
kwantar da Umm-Anum yake.
Ba Uncle Sulaiman kawai ba, hatta su Shahudah bin bayansu sukai, yayinda wasu
a cikinsu kuma suka nufu kaima iyayensu rahoto.

Dr Tayyeb na ƙoƙarin fitowa daga ɗakin da Umm-Anum take dan ya sanarma


su Ummah su shiga an cire mata drip yaci karo da Ummahn dake riƙe da Anuwar.
Murmushi ya ɗanyi yana ja baya ya koma cikin ɗakin da juyawa ya kalli Umm-Anum dake
kallonsu da murmushi yace, “Yauwa hajiya, dama zan sanar muku ku shigo ta tashi
normal Alhmdllh, dan zama mu iya sallamarku kamar”.
Kafin Ummah tace wani abu Uncle Sulaiman dake a bayansu cikin tsananin kiɗima
yace, “Bilkisu!”. Da sauri Umm-Anum ta maida dubanta gareshi, sai kuma taɗan waro
idanu waje itama tace, “Yayah Sulaiman!”. Cikin matuƙar rawar jiki ya afka cikin
ɗakin, babbar rigarsa har tana neman taɗesa Dr Tayyeb yay azamar tarosa yana faɗin,
“Subahanalillhi, Alhaji yi a hankali”.
Duk da Umm-Anum batajin ƙwarin jikinta hakan bai hanata sakkowa daga saman
gadon ba. Sakkowar tata kuma tayi dai-dai da faɗowar Uncle Uwaisu da sauran ƴan
gidan su Jawaad ɗakin.
“Wlhy itace da gaske!!” Uncle Uwaisu ya faɗa yana jan birki da ɗaga hannaye
sama tamkar wani zararre.... Kafin wani a cikinsu ya samu damar sake tofa tashi
Nabeelah ta kutso tsakkiyarsu jikinta na rawa, “Ummah! Ummah!! Ummah!! Ku kalla
television, ku kalli abinda ya faru dasu Yayanmu a wajen ƙwato Alhaji babba,
m....m..matsafa Ummah, wlhy matsafa suka gano acan.....”
Uncle Sadiq ne yay azamar rarumar remote ɗin television ɗin ɗakin ya kulla,
anko haske dai-dai inada ake fiddo su Uncle Nasir daga cikin gidan daga su sai
jajayen ƙyallaye, Jawaad na rungume da Alhaji babba yana shafa masa ruwa a fuska
za'a sakashi cikin helicopter shi da wasu a cikin waɗanda aka ceto.
A take ɗakin ya ruguntsume da tsananin tashin hankali da ruɗani,
Umm-Anum ta fashewa da kuka tana dariya kuma, cikin wani ƙarfin zuciya ta
ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”.
A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi
mai wahalar fassara a fuskokinsu................✍

Nima dai kam na tsinci kaina a yanayin har takai alƙalamina da faɗuwa a ƙasa batare
da na shirya hakanba😳🚶.

Kuyi manegi babu editing yau🤒🚴🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻


[2/12, 7:51 PM] Wasila: ƘWAI CIKIN ƘAYA

BILYN ABDULL

*_FARIN WATA SHA KALLO🤓🤗_*

ZAFAFANKU SUN DAWO GAREKU A 2021😋😋😋😋🚴🏼🚴🏼


*_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥🔥🔥
*_SABUWAR SHEKARA_*
*_TAREDA SABON SALO_*👍

✔️
*_A DUNIYAR RUBUTUN HAUSA SU NA DABAN NE,_*
*_A DUNIYAR NISHADANTUWA DA KARATUN HAUSA SU DIN NA MUSAMMAN NE,_*
*_A DUNIYAR FADAKARWA DA QAYATARWA NA KARATU SU DIN NA FARKO NE,_*
*_A 'BANGAREN NISHADANTUWA DA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA MAI SHIGA RAI DA SANYA SHAUQI
DA NUTSUWA TO SU DIN ZA'BABBINE,_*
*_A 'BANGAREN SANYA NISHADI DA BARKWANCI TO SU DIN QWARARRINE,_*

*_Shin ko kunsan su ake kira da zafafa biyar masu tashe?_*


_*Idan kin/ka san kai maabocin karatun littafan HAUSA ne to tabbas karku Bari ayi
Babu ku*_
*_domin kuwa wannan karon sun dawo muku da wani sabon salon Wanda babusa a DUNIYAR
karatu,_*
*_cikinsu Babu wadda bataga jiyaba bataga yauba a fagen nishadantarwa._*

*_ZAFAFA BIYAR 2021_*🔥

_*YANKAN BAYA*_💚
_BILLYN ABDUL_
( _kwai cikin qaya_ )
( _raina kama_)
( _wutsiyar raqumi_ )

*_SIRADIN RAYUWA_*💛
_SAFIYYA HUGUMA_
( _alqawarin Allah_ )
( _daurin boye_ )
( _Dangantakar zuci_ )

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡


_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,


Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*


ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*09044191709*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Page 58

.................Muna tsaitsaye a inda aka bamu iznin tsayawa, Rose na mana bayani
akan abinda zamu tunkara. Cikin takunsa na zaratan jami'ai da sukasan aikinsu ya
fito Hafiz biye da shi da bullet proof jacket a hannunsa da alama ta boss ɗince, A
boss ɗinsa dana fara sani yake yau, kura ga tsoro gaban tsoro, zakin da babu abinda
ya sani face farauta a lokacin da yunwa ta ciyo cikinsa, gwarzon da baya alfarma ga
dukkan wanda baima kansa alfarmarba, ɗaya tamkar da dubu abin buƙatar kowacce ƙasa,
kowanne yanki, ko wacce zuri'a. Cike da izzarsa mai cike da tsantsar damuwa da
ɓacin rai yazo gabanmu ya tsaya yana ƙare mana kallo ɗaya bayan ɗaya. Ya furzar da
wani zazzafan huci daga bakinsa yana nunamu da yatsansa manuniya. “Kusa a ranku
aiki zaku fita bakin rai bakin fama, sakacinku na nufin sakaci da ƙasarku, sakaci
da yankinku, sakaci da garinku, sakaci da familys naku, idan kuka zama jajirtattu
kun fido da martabar ƙasarku ne, yankunan ku, garinku da familys naku dama
rayukanmu baki ɗaya da hukumarmu. Aikine mai cike da haɗari, ka kashe ko a kasheka
wannan duk hukuncin ALLAH ne, shawarar kawai itace addu'a, ina fatan kuna faimta
ta”.
“Yes Sir!!!” muka faɗa cikin haɗa bakuna tare da buga ƙafa ƙasa mukai salute
nashi. Juyawa yay ga Rose yay mata maganar da bamaji kafin ya kalli oga Hafiz
shima. Shima maganar sukai suka bar wajen kuma zuwa inda su Sir Ahmad ke tsaitsaye
tare da manyan jami'anmu da sojoji kusan goma sha biyar.
Mudai muna nan tsaitsaye muna jiran umarni, a haka oga Jabeer ya zo wajen ya
bamu damar zuwa mu shiga jirage masu saukar angulu (Helicopters) da za'ai tafiyar
dasu. Mu matan an haɗamu ne a guda ɗaya, drivern mu ma ta kasance mace ce yarinya
ƙarama da bazamu gaza sa'anni gudaba, sai baba ƙaura kaɗai daya kasance namiji a
cikinmu wanda ya wuce muce masa uba kawai sai dai kakanmu. A yau babu zancen fira
mu dasu Ummie, kowa addu'a ce ɗauke da bakinsa da fatan nasara, a can ƙarƙashin
zuciya kuma tsorone da kowa ke ƙoƙarin dannewa. Sai da muka hangi tashin wasu
jiragen kafin namu ya tashi, kusan duk sai da muka lumshe idanu kowa shi kaɗai
yasan abinda ke a cikin ransa.

Kamar a wancan karon tafiyace mukai da hasashe bazai iya ƙididdigar


iyakartaba, sai dai kawai muka tsinkayi saukar jirginmu a tsakkiyar jeji mai cike
da surƙuƙi da haɗarin gaske. Mun firfito kowa na ƙoƙarin kare ƙurar da fankokin
jirgin suka tayar da hannunsa domin samun damar ganin hanya da ƙyau, wasunmu da
basa son ƙura har ƴan ƙananun tari sukeyi da atishawa. Su boss suma duk sun firfito
a nasu. Sir Ahmad na ƙoƙarin buɗe taswurar jajenin da ya amsa a hannun oga Aliyu
baba ƙaura ya dakatar dashi. “Ranka ya daɗe bama buƙatar wata taswura, insha ALLAHU
komai zai kasance yanda muke fatansa, babu wani lungu ko kogo da zai layancemin a
wannan jajenin kaf ɗinsa, inda muke buƙatar zuwan zamu dosa kai tsaye babu ko
gargada a ciki”.
Sosai naga al'ajabi a saman fuskokin jami'anmu, muko da muka san wanene
baba ƙaura hakan bai zame mana sabon abuba, fatanmu kawai samun kariyar UBANGIJI da
nasara.
Tafiya muka farayi a cikin jejin, su oga Aliyu da boss da wasu a cikin
sojojin da baba ƙaura ne a gaba, sai su Sir Ahmad a bayanmu. Munyi tafiya mai nisa
kafin mu isa wani ƙyaƙyƙyawan tsuburi dake da ƙaramar ƙorama a gefensa, sai
tsuntsaye jefi-jefi dake shan ruwa. Da hannu boss ya tsayar damu kafin mu ƙarasa ga
ƙoramar, Oga Jabeer ya matsa kusa da boss, bullet proof jacket ɗin dake a hannunsa
ya shiga ƙoƙarin saka masa suna magana, nidai ina satar kallonsune da faɗin ‘Ɗan
gata rigarma sai an saka masa’. Ya juyo saitin da muke yana bama Jabeer bayansa
danya gyara masa can, ido muka haɗa nai azamar janye nawa, a bazata naji yace,
“Miemaa!”. Abinda ya tsargamin nai saurin haɗiyewa, yayi masifar iya ambatar
sunannan fiye da zaton mai tunani, kallonsa nayi na amsa da “Na'am”. Ya ɗauke
idanunsa daga kaina yana faɗin, “Ki gyara wannan jacket ɗin taki bata zauna da
ƙyauba”. Gaba ɗayansu suka zubamin ido banda su Sir Ahmad da hankalinsu ba wajanmu
yakeba. Kaina na jinjina masa ina haɗiye yawu da ƙyar dan yanda duk suka zubomin
ido sai naji na takura. Nazifa dake bayanace ta taimakamin na gyara, idonsa har
yanzu a kaina yace, “Matan nan ku kasance kusa da wani komai rintsi, sannan banda
harbi a kai, ciki, ƙirji, duk harbin da zakuyi karya wuce ƙafa ko hannu da inda
baza'a mutuba”. Kai muka jinjina masa da faɗin, “Okey Sir!!”.
Rose ta taɓe baki tana harar Bilkisu ta gefen ido, duk da tasan abinda
Jawaad ya faɗa musu dokace kasancewar a harbin da duk su bilkisu zasuyi babu kisa
sai ankai maƙurar da babu mafita taji zafi a ranta, dan a ganinta Jay ya faɗama
bilkisu ne ita kaɗai kawai cikin tsantsar nuna kulawa, tunda harda cewa ta gyara
jacket ɗinta. ‘Mtsossw’ taja ƙaramin tsaki a ƙasan maƙoshi da matsawa gaba.
Da ga inda muke tsaye muna hango gini maiban mamaki da tu'ajibi, dajine
sosai fa. amma sai ga gida a tsakkiyarsa, gida ginanne daya amsa sunansa gida da ko
a cikin gari ya cancanci kallo bawai sakaran gini ba ne. Babu wanda al'ajabi bai
sakashi kallon baba kaura ba. Cikin dattakonsa yay murmushi shima batare da ya
kalli kowa a cikinmuba. “Wannan gini ginine da ya ɗauki kusan shekaru ashirin da
bakwai a cikin jejin nan, magina aka kawo suka ginashi kamar yanda ake gina kowanne
irin gida, duk shekarar duniya kuma sai an sabunta masa fenti da abubuwan ƙawa.
Mabanbanta mutanene ke zuwa cikinsa ziyara, abinda suke aikatawa a cikinsa kuma,
sai munje idanunku zasu gane muku komai a yanzun, domin yau ranace da suka ware ta
musamman domin shaiɗancinsu, shiyyasama muke anan tsaye bisa ƙafafunmu batare da
sun farga da zuwan namu ba”. Kawuna kawai muke iya jijjigawa kamar wasu ƙadangaru,
shine yay mana nuni damu ƙarasa.
Ararrabe muka fara dosar ginin muna zagayesa kamar yanda commander'n
(boss) tafiyar ya bada umarni, ɗai-ɗai muka ringa shiga cikin dabara na salon aiki,
ina niyyar bin bayansu nima aka riƙo hannuna, waigowa nai da sauri dan bansan waye
da aikinba. Ya harareni damin alamar na dawo bayansa da idanu. Bani da zaɓin da ya
wuce bin umarninsa, na dawo ta bayansa yana gaba, duk da gani a baya sai ya raba
hankalinsa wajen kallon bayansa da gabansa, da haka muka shiga ciki muma kamar
yanda oga hafiz da Aliyu, Jabeer sukayi, sauran kuma suna daga waje su da su sir
Ahmad. Tafiya muke a sannu-sannu, babu wanda yay harbi dai a cikinmu kamar yanda
har yanzu nidai banji motsi na alamar akwai mutum a gidanba.
Cikin matuƙar zafin nama da ALLAH ya bama boss ya fisgoni tare da duƙar da
ni saboda tahowar wuƙa da aka wulwulo a bazata wadda sam hankalina baya wajen,
bakuma musan dga inda take ba, jikinsa na faɗa, shi kuma ya cafe wuƙar a hannunsa.
ɗagowa nai ƙoƙarin yi idanuna suka sauka akan ƙafa dake ta wani ɗan lingu, komawa
nai na duƙe har yanzun hannun hagguna na cikin na boss. Handkherchief ɗin aljihunsa
nasa hannu na ɗauka, tsayawa yay yana kallona yaga mizanyi, na zare hannuna daga
nasa na ƙarasa takawa inda ƙafar take cikin sanɗa, sai da naje gab sannan na miƙe
sosai cikin zafin nama na ratayo handkherchief ɗin a wuyan wanda ke tsayen, kafin
yay wani yunkuri na ɗaure masa wuya da ƙarfi yanda ko ƙara zaiyi babu maiji. Sukur-
sukur ɗin da mutumin keyine na neman ƙwatar kai ya saka boss kallona, fuskarsa
ɗauke da murmushin dana jima ban ganiba yaymin jinjina👍🏻. Nima sai nayi murmushin
dan ya bani dariya a salon da yay da idanu da murmushin harma da jinjinar. Zagayawa
yay ta ƴar ƙofar daya gani wajen wanda har yanzu nake ɗaure da wuyansa harya suma,
yaymin nuni dana cire handky ɗin, ya kamasa ya kwantar ƙasa nima na zagaya.
Jinjina ya sake min, cikin magana raɗa-raɗa yace, “Aikinki yayi ƙyau
Babie”. Ɗan murmushi nai masa sannan muka shige ta ƙofar da muka gani cikin sanɗa.
Saurin dakatawa yay yaɗan ja baya kaɗan muka koma jikin bango da ɗauke numfashi.
Baƙin mutumin da sam babu imani tattare da shi yazo ya wuce ta kusa da mu sai dai
bai kawo inda muke ba, har yay ɗan nisa sai kuma ya dawo baya yana waige-waige.
Yana zuwa gab damu boss ya jawo masa riga ta baya, cikin wani irin zafin nama ya
juyo sai kawai ya buga masa kansa yay baya, oga Hafiz daya ƙaraso wajen ya taresa
da saurin ɗora masa handkherchief ɗin hannunsa a hanci, da alama wani abun ya shaƙa
masa, dan a take jikinsa ya saki. Ƙasa ya kwantar da shi yana ɗagowa, ya matso kusa
damu sosai cikin magana raɗa yace, “Boss kuzo gasu tanan”. Binsa mukai cikin sanɗa
ta hanyar daya biyo boss nata faman murza goshinsa da yayma mutum can gware alamar
yana masa zafi wajen har yanzun.
Tsaye muka tadda su Jabeer cikin matsanancin ruɗani, ni da boss muka ƙarasa
jikin glass ɗin wajen da akayisa domin kwalliya kawai muka leƙa. A take tsigar
jikina ta tashi, ƙirjina yay wata irin dokawa nai saurin yo baya ina ambaton
‘Wa'iyazubillah’. Boss kam tsaye yake kyam akan ƙafafunsa ya dasama wajen ido baya
ko ƙyaftawa, sai dai jikinsa shi kansa tsuma yake, gashin duk sun mimmiƙe alamar
shima tsigar jikinsa tashi take. Duk mai imani dolene ganin wannan shaiɗancin ya
tada hankalinsa.
Shirka ƙuru-ƙuru ga waɗanan shaiɗanun mutane da a zahiri suke ambaton
kayinsu musulmai harsu shiga masallaci suyi salla cikin jam'i ma. Gaba ɗayansu
zindir suke sai wani ƙyale ja da suka ɗaura a ƙugu ɗan guntu da iya al'aurarsu
kawai ya rufe, sai wani ɗaure a kansu, durƙushe suke gaba ɗayansu sunyi Sujuda,
tsakkiyarsu ƙaton kaskon tukunyar ƙasa ne da aka kunna wuta a ciki tana ci, sai
babban shiɗaniyar tasu da kasancewarta tsirara yasa muka gane mace ce zaune bisa
kujera kanta a duƙe itama riƙe da sandar da maybe itama ta tsafin nasu ce. Hawaye
na gani suna sakkowa a kumatun boss, jin damshi a tawa fuskar ya tabbatar da nima
hawayen nakeyi ashe. Ganin zasu miƙe boss yay saurin maidoni baya muka koma jikin
bango, muna kallonsu ta haka. duk suka miƙe tsaye suna wani yare da su kaɗai
sukasan mi suke faɗa, da fuskar Alhajin da naje gidansa na ɗakko tukunyar nan na
fara cin karo, ganinsa da nai a hoto a gidansa yasa ananma na shaidashi, sai wanda
ke a kusa da shi daya kasance shima mutum mai tarin faɗa aji a ƙasar nan, zuciyata
wani irin luguden daka take kamar zata faso ƙirjina ta fito nakai dubana gana uku,
shidai ban sanshiba kam, sai na huɗu shima ban sanshi ba, a na biyarne kam ƙafafuna
suka nemi gaza ɗaukata, dan kuwa ba kowa bane face Uncle Nasir, bankai ga fita a
ruɗanin dana shigaba na ganin Uncle Nasir idanuna suka sake sauka akan Dadyn
Zuhrah, sai yayan Dadyn su Ummie dana taɓa gani a ranar bikin yayemu daga Jami'a. A
haka na cigaba da binsu da kallo, wasu na riga da na sansu a tv, wasu kuma ɗai-
ɗaiku a zahiri, wasu ko ban taɓa ganinsuba sai anan, nabi wanda ya juya mana baya
riƙe da ƙoƙo da kallon sani, sai dai bana ganin fuskarsa, amma hakan bai hanani jin
zuciyata raunana ba matuƙa akansa, so nake naga wanene amma ya juya baya.
Durƙusawa yay yayi sujuda (Wa'iyazubillah😭) ga wannan la'ananniyar tsohuwar
mata dake a kan kujera kamar basarakiya, sai kuma ya miƙe da ƙoƙon hannunsa yaje
gabanta kansa a rissine ya miƙa ƙoƙon. Ƙyalƙyalewa tai da wata irin mummunar dariya
da sam muryar tata bata kama data mata, sai kuma ta haɗe fuska tana faɗin,
“Jariri!! Kai mutum ne mai daraja a wannan Bakandamiyar tamu, kaine farkon fara
nasara ga dukkan matakai da tsare-tsarenmu da ƙa'idoji, kowane aikinka ka gudanar
da shi babu kuskure ko sau ɗaya, sai a na ƙarshe da ya zama cikamakin ayyukanka ya
gagareka?, ta dalilin yarinya ƙarama a cikamakin ayyukanka mun fuskanci asarori
masu yawa. Hhhhhhhh Mun baka dama tun a watan jiya Jariri amma ka kasa damawa,
munce ka nemo mana asalin yarinyar kace asalinta na farko daka kawo shine asalinta,
sai dai mu bamu amince da hakanba. Lallai Jariri wannan yarinya bincikenmu ya gano
mana akwai sirri mai nasaba da mafarkin mu na watan jiya dangane da ita. Jariri
wannan itace dama ta ƙarshe da zamu baka akan wannan yarinya, Bakandamiyar mu na
buƙatar jininta tunda budurcinta ya gagara, Jariri, idan ka gaza hakan daga nan
zuwa kwanaki biyu zaka fuskanci mummunan hukunci daga Bakandamiya, zakuma mu
saukeka daga shugabancin da kake kai. Sannan Jariri a yau ɗinnan ka tabbatar an
sake ɗaura igiyar aure tsakanin gudalliyarka da yaron nan, inba hakaba bazamu yafe
makaba a wannan karon dolene ka bamu jinin gudalliyarka........”
“Tuba nake uwargijiyarmu, tuba nake uwa maba da mama, tuba nake mai share
kukanmu, ina sake roƙon alfarmar a barni da gudalliyata dan itace zuciya ta, zan
iya yarda na rasa abubuwa da yawa amma banda gudalliyata ya shugata, nayi rantsuwa
da shugaban shaiɗanu a yau sai igiyar aure ta ƙullu tsakanin gudalliyata da
halattaccen jinin Bakandamiya. Ina mai sake rantsuwa da a gobe saina kawo jinin
wannan yarinya wa Bakandamiya shine zai zama abin kalacin mabiya Bakandamiya yake
abar bautarmu”. (wa'iyazubillah😭🙏🏻)
“Bakandamiya ta amsa maka, ta kuma baka damar ƙarshe ta dawowa da
martabarka tare da dukkan muhimman abubuwan ƙungiya dake a hannun yarancan da
jininsu ya halatta ga Bakandamiya. Kurakuranka zasu goge a dutsen rubuta laifuka
bayan ka cika alƙawuranka da jinin babban ɗanka Jariri kamar yanda yake a rubuce a
sharuɗan Bakandamiya”.
“Naji na karɓa yake mai biya mana dukan buƙatunmu”.
“Hhhhhhhhhhhhhhhhh!!!!!!!!!!!!!!” ta kece da wata mahaukaciyar dariyar da ta
saka duk saida muka toshe kunnuwanmu saboda yanda dajin gaba ɗaya yake amsawa bama
gidan kawai ba, tanayi tana tsiyaya masa wani abu mai kama da jini a cikin ƙoƙon
hannunsa. Da baya baya ya baro gabanta yana wasu surkulle da shi kaɗai yasan abinda
yake faɗi, sauran na amsa masa.
Mamaki, tsoro, al'ajab da ruɗani duk suka saukarmin lokaci guda ganin Dad a
inda tunanina ko tsammani bai taɓa raya minba, saurin ɗaura hannuna nai na rufe
bakinna jin kuka na neman kufce min. “D... Da...Daddy!!”. na faɗa cikin rawar murya
dana jiki ina mai matsawa jikin boss dake tsaye abinsa yana kallonsu Dad ɗin shi da
su Oga Hafiz.
Cikin matsanancin furgici Dad ya saki ƙoƙon hannunsa da kai dubansa inda
yaji muryar da bai zatoba ta ambaci sunansa. Ido huɗu sukai da bilkisu da jikinta
ke wani irin matsanancin tsuma.
A take Dad ya zazzaro idanu waje cikin tsananin firgici da ruɗani, jikinsa sai
wata iriyar tsuma ya keyi domin ganin wadda bai taɓa zato ko tsammani ba. duk da
glashi ya raba tsakaninsu, bai gaza gane bilkisu da Jawaad ba harma da jin
furucinta raɗam a kunnuwansa, dan basu da wani shamaki wajen iya jiyo maganar juna
duk da akwai hilashin daya rabasu.
Bansan sanda wani ƙarfi da zafin nama yazomin cikin jini da jiki ba na bigi
gilashin wajen da ƙafa jikina karkarwa saboda wata irin mummunar tsanar sa ce ta
saukarmin lokaci guda da ƙyamarsa.
Sauran abokan shaiɗancin nasa da tuni suma sun mike suna kallonmu a cikin
matsanancin firgici na alamun bazata a fuskokinsu suka shiga ƙoƙarin motsawa cikin
rawar jiki dan neman kariya.
Kafin suyi wani yunƙuri su Jabeer sun afko suma tare da su Ummie dake jiran
umarni a waje. Zagayesu akai da bindugu, hakan ya tabbatar musu basu da wata dama
kuma saina miƙa wuya........
“Ƙassaaa!!!!” Boss ya faɗa a iya ƙololuwar hasala jijiyoyin jikinsa na sake
mimmiƙewa. Durƙushewa sukai bisa gwiwoyinsu suna aza hannayensu bisa kawunansu
alamar yin surrender.
Ban samu dawowa hayyacina ba daga kallon al'ajabi da ruɗanin da nakema Dad
sai da Wani irin ihu shaiɗaniyar matarnan da tayi ya shiga dodon kunnena. miƙewa
tsaye tai da buga sandar hannunta ƙasa, a take ɗakin ya fara turniƙewa da hayaƙi,
sake bugawa tayi, sai jikinta ya fara canja launi harda su Dad ɗin suma. ta ɗaga
zata buga na uku nai wani wawan tsale na dire a gabanta na riƙe sandar. Bazan iya
fassara muku mawuyacin halin dana shiga ba a wannan lokacin, domin tsafi gaskiyar
maishi ne, abinda kawai nake iya jiyowa harmutsewar wajen da ƙarar harbe-harbe ta
waje alamar musayar wuta ta ɓarke tsakanin wasu a cikin jami'anmu da suke a waje
da yaransu masu tsaron gidan.......

Jawaad yay azamar nufar inda Bilkisu da matar nan ke riƙe da sandarnan,
jikin bilkisu wani irin rawa yake da karkarwa ga zufa, amma dan taurin zuciya taƙi
yarda ta sakar matar sandar. ta gama fuskantar buga sandar nan da take sonyi zai
iya zama kuskure ko halaka a garesu wajen baki ɗaya, kokuma wani siddabarun nasu
zasuyi don son ƙuɓuta.
Cikin tsawa Baba ƙaura ya dakatar da Jay da ya kai hannu domin bama bilkisu
taimakon. “Karka taɓata, barta da ita!!”. Ya faɗa a kausashe yana nufosu, Hankalin
Jay a tashe ya juyo yana kallon Baba ƙaura da girgiza kai, “Bazan iyaba bab....”
kafin ya gama rufe baki baba ƙaura ya riƙo hannunsa, hakan yayi dai-dai da hankaɗa
bilkisu baya da matar tayi, ta ɗaga sandar zata buga a ƙirjin bilkisun.

Da sauri nai wani irin juyi sandar ta caki ƙasa, nasa ƙafa na taɗo tata ƙafar
itama, baya tai, na bigi sandar da ƙafa itama tai sama na cafe cikin hannuna daga
kwancen da nake.

Wani irin mummunar amsa kuwwa ce ta karaɗe jejin lokaci guda, hakan ne ya
saka ruɗani gasu Jay kowa ya shiga ƙoƙarin toshe kunnensa banda baba ƙaura da yasa
ƙafa ya hankaɗa tukunyar kaskon wutar nan dake ci har yanzu ya kife a kujerar da
matarnan take zaune ɗazun. Tamkar an tsaida ihun sai dajin yay cak lokaci guda
kuma. Waige-waige su Jabeer suka fara dan su Dad gaba ɗaya basu a wajen sai matar
kawai dake a kwance ƙasa inda bilkisu ta zubar da ita, saboda take mata ƙafa da
Baba ƙaura yayi.
Hankalinsu duk tashi yayi suka shiga leƙe-leƙen lungu da saƙo na cikin gidan
hankulansu a tashe, sai dai abin mamaki babu ko ɗaya a cikinsu sai mutane da aka
ringa zaƙulowa a cikin ɗakunan cikin hardasu Alhaji Babba da ke a cikin mawuyacin
hali.
Baba ƙaura ya cire jikkarsa ta fatar damisa ya ajiye ƙasa, da hannunsa ɗaya
ya buɗeta ya ɗakko wani wani irin kibiya ta ƙarfe sai sheƙi take da walwali ya
shaƙo wuyan matarnan ya miƙar da ita tsaye, watsa mata wani mugun kallo yay yana
huci, a take ta ƙwalla kururuwa jikinta na rawa. “Barde kaga zan dawo dasu kaimin
rai karka kassarani mai babban suna, na tuba nabika”. “Bana buƙatar tubanki
shaiɗaniya, ai dama na faɗa miki nine ajalinki kokin manta na tuna mikii!!!!”.
“Cikin rawar jiki take girgiza masa kanta, ya fincike manyan layun dake a wuyanta
ya watsar ƙasa, a take ta zube a wajen tana fashewa da kuka. Cikin ƙwarewa da
sararafa hannunsa guda ɗaya da dungulmin ɗayan ya ɗana kibiyar nan ta ƙarfe a
kanta. Da sauri ta buga ƙasa da hannunta har sau uku sai gasu Dad dake can gefe
rufe da wani jan ƙyalle sun bayyana.
‘Innalillahi wa'ina ilaihirraji'un yau muna ganin tsantsar tashin hankali da
shaiɗanci, da a labaran tatsuniyoyi da fina-finai kawai muke jinsu. Koda ake cewa
akwai matsafa a duniya da yankunanmu ban taɓa yardaba, a nawa zaton labarine kawai
na ƴan shafawa labari shuni, ashe gaskene, ashe zan gani da idanuna, ashema harda
jinina a cikinsu wanda na ɗauka uwa uba ma. Hawaye nake masu zafi da ƙunar zuciya,
kaina juyamin yake gaba ɗaya dama duniyar kanta, tun ina fahimtar abinda ke faruwa
har jina da ganina suka ɓace ɓat daga duniyar mutane, daga haka ban sake sanin
abinda ke faruwaba kuma.

Cikin zafin nama Ada ta tare Bilkisu da juwa ta ɗiba, a tsorace take
kiran sunanta tana girgizata ganin batama numfashi gaba ɗaya. Aliyu ne yayo kansu
yana tambayar lafiya, dan Jay tunda aka fiddo su Alhaji Babba yabar nan zuwa
garesu.
Ba Bilkisu ce kaɗai ta sumaba, Zuhrah tun cin karo da idanunta sukai da
Abbanta ta sume, hakama Ummie ganin yayan mahaifinta tuni ta suma, sai cikin
mutanen da aka iske a wajen da yawansu basa cikin hayyacinsu harda su Alhaji babba
da basu wuci awanni da kawosu wajenba, dama ga tsufa kuma. Wasu daga cikin yaran su
Dad an harbesu, harma da waɗanda aka kashe.
Jejin ya hargitse sosai, bakajin komai sai ƙarar helicopters na sojoji dake
shigowa cikin jejin saboda wayoyi da su Sir Ahmad suketa faman yi da amsawa.
Dandanan sojoji da masu bada taimakon gaggawa harma da ƴan jarida dake cikin
jami'an tsaron da su Qaseem duk suma suka iso. Cikin ƙanƙanin lokaci jejin ya sake
harmutsewa da motsin mutane dana ababen hawa.
Su Dad na durƙushe cikin ƙasƙanci daga su sai jajayen ƙyallayen kawunansu
dana ƙugu da sukaɗan rufe jikinsu kaɗan, sai da jami'an tsaron da suka iso suka
sauka sannan bisa alfarmar da General ya buƙata aka basu mayafai suka rufa, amma da
Jawaad yace a haka za a fita jejin dasu har cikin gari domin sauran al'umma su
gansu.

Dajin fa kamar wasa sai gashi ya tara jama'a masu yawa kama daga manya-
manyan jami'an tsaro, zuwa shugabannin ƴan siyasa da ƴan jaridu, dan babu abinda ke
kai kawo sai helicopters da ƙananun jirage na yaƙi. Mutanen dake a cikin gari kansu
sun fahimci ƙasar babu lafiya yau, dan kai kawon da helicopters keyi kawai ya isa
amsa. yayinda kuma ƴan Jaridu suka fara nuna komai ta gidajen tv'n su live. Duk ta
yanda manyan ƙasar sukaso kar hakan ta kasance basuci nasaraba, dan kuwa ƴan jarida
sunada ƙarfin iko da ƴancinsu suma, balle kuma akan wannan al'amari mai tsananin
saka ruɗani da al'ajabi ga duk mai sauraro bama kallo kawai ba.
An shiga kwasar su bilkisu da suke a halin suma aka fara barin jejin dasu
domin miƙasu ga likitoci su samu taimakon gaggawa, sai waɗanda suka sami harbi da
gawawwaki da mutanen da aka samu an kawo harma da gawarwakin mutane da aka iske a
wani ɗaki cikin freezer irin wadda ake saka gawarwaki a asibiti, dan gidan suna
amfani da babban janareto dake basu wuta 24hours, duk wani abun more rayuwa kuma
akwaisa a gidan hatta da ruwa.
Su Jay ne keta kai kawo haɗa rahotanni har aka kammala kwashe mutane da
gawarwaki da wasu kayan sirrika da ke a cikin gidan tas, basu baro jejinba sai
bayan sallar la'asar, zuwa lokacin labari ya gama karaɗe lungu da saƙo na ƙasar
harma da ƙasashen ƙetare, to abinka da manyan mutane da ake ganin mutuncinsu acikin
manyan riguna da kuɗi suka saya musu.

__________________________

Su Ummah basu farga da rashin su Jawaad a gidanba sai da su Nabeelah


sukai kusan mintuna talatin da baro kitchen. Cikin ƙaguwa Umm-Anum ta kalli ƙannen
nata cikin hausarta da bata fita da ƙyau yanzun tana faɗin, “Mariya wai ina ɗanku
ya shige da matarsa ne? Nifa na ƙagu naga ubana, gara yazo ya kaimu ala bashshi sai
su ɗakko su Abbun Anuwar ɗin daga can idan sun iso”. Murmushi Ummah babba tayi, ta
kalli Nabeelah da suke kallon hotuna a wayarta da Anum. “K Nabeelah kiramin
yayanku”. Cikin ƴar ruɗewa Nabeelah tace, “N...n.....na'am Ummah mi kika ce?”.
“Ƙaniyarki nace dan gidanku” ta faɗa tana mata daƙƙuwa. “Kai Ummah ALLAH nifa banji
bane ba”. “ALLAH ya shiryeki to, canai kije ki kiramin yayanku”. Jimmm tai na
tunanin abinda zata faɗa, sai kuma dai ta miƙe ta fita, a babban falo ta tsaya
tanata kaikawo, tarasa wacce amsa zata koma ta bama Ummah ne, tsoro faɗar gaskiya
take kodan gargaɗin da Jay yay mata akan hakan”. Anuwar da ya shigo falon ya
lallaɓo ta bayanta yaja jelar gashinta. A firgice ta juya zata ƙwalla ƙara na
tsorata yay azamar rufe mata baki yana kallon sashen Bilkisu cikin ɗan zaro idanu.
Sai da ya tabbatar ta nutsu sannan ya saketa yana sauke ajiyar zuciya da murmushi
kan fuskarsa, “beauty ke matsoraciya ce gaskiya”. Cike da shagwaɓar data saba ta
tura masa baki, “Yoni tsoro naji ALLAH, nazata Yayanmu ne”. Murmushi Anuwar yayi
dake sake bayyana kamaninsa da Jawaad sosai yana ƙara narkar da idanunsa a kanta,
“Kiyi haƙuri tam, halan laifi kikaima Yayan kike tsoron ku haɗu?”. “A'a ba laifi
namasa ba, sai dai Ummah nason tajamin nayi masa yanzu”. ta ɗan wawwaiga kamar mai
tsoron Jay ɗin ya ganta sannan ta juyo ga Anuwar da shima ke tayata waigen, ƙasa
tai da murya cikin raɗa ta faɗa masa gargaɗin Jawaad. Sosai abin yaso bashi dariya,
shifa tun a bikin su Jay ya fahimci Nabeelah akwai wautan autanci tattare da ita,
“To ai kin kuma faɗamin yanzu, kenan bakiji gargaɗin nashi ba?”. Idanu ta waro waje
sosai tana ɗaura hannunta biyu aka zata fashe da kuka”. “Kinga wasa nake miki”
Anuwar ya faɗa da sauri ganin zata saka masa kuka. “To faɗamin mi zan cema su
Ummah?”. Kafin ya bata amsa Aunty Batool ta shigo, ganin ta wucesu tana kuka sukai
saurin bin bayanta.

Hankalin su Umm-Anum a matuƙar tashe suka tari Batool, kowa tambaya yake jeho
mata akan miya sameta?. Yanda duk suka rikice sai suka bata matuƙar tausayi, bata
ɓoye musu komaiba ta labarta musu halin da ake ciki har zuwan su Jawaad da
tafiyarsu office akan case ɗin.
Faɗuwar Umm-Anum kawai sukaji batare da kowa yaga sanda tai yunƙurin
faɗuwarba, hankalinsu a take ya sake tashi, basu wani tsaya maida yanda akayiba
suka kwasheta zuwa asibiti, dole Batool ce tai driving ɗin, dan Anuwar baisan
hanyaba.
Anum da Nabeelah nata kuka su Ummah na rarrashinsu. Saboda ta samu kulawar
gaggawa sai Batool ta nufi asibitin Dr Tayyeb da su, ai ko babu ɓata lokaci aka
karɓesu da bama Umm-Anum taimako akan lokaci..........

__________________________

A ɓangaren su Mom kuwa sun gama yanke hukuncin sake ƙulla auren
Jawaad da Shahudah batare da neman yardarsa ba, dan haka babu wani ɓata lokaci mama
Atika ta saka aka tattara mata su Uncle Sulaiman, sai dai kuma babu Uncle Nasir,
acewar matarsa yayi tafiya tun daren jiya.
Mom ta kira wayar Dad shima a kashe, hakan bai dameta ba, dan tasan shima
burinsa kenan ai, dan haka sukace Uncle Uwaisu ya wakilci Dad ɗin, Uncle Sulaiman
kuma Jawaad.
Duk yanda Uncle Sulaiman yaso fahimtar dasu kuskuren yin hakan sam Mama
Atika taƙi fahimta, saima rufesa da tayi da masifa tamkar zata cinyesa ɗanye.
Haƙuri ya bata, a take aka tattara samarin gidan da maƙwafta kasancewar weekend ne
aka sake ƙulla auren Jawaad Abdul-Aziz yusif da Sabeera Aliyu Fillo akan sadaki
naira dubu ɗari da Uncle Sulaiman ya biya.
Zo kuga farin ciki wajen Shahudah amarya dasu Mom da Mama Atika, dan a
wannan karon sun ɗauki alwashin babu abinda zai dakatar dasu daga cika burinsu akan
abinda suka jima sunama ƙwaɗayi. Ana cikin wannan murnarne ɗiyar Uncle Sulaiman
tazo sashen mama Atika da gudu tana kuka da faɗa musu cewar suzo mama Badiyya na
wani abu mara daɗin gani.
Gaba ɗayansu suka kwasa Uncle Sulaiman har gudu yake da tuntuɓe dan mahaifiya
tafi gaban wasa. Sosai hankalinsu ya tashi, murnar ɗaurin auren da sukeyi ta gushe
tabar fuskokinsu baki ɗaya. Cikin gaggawa aka ɗauki Mama Badiyya zuwa asibiti,
kasancewar kowa yasan matsalolin asibiticinmu na gwamnati sai Mom ta bada shawarar
a nufi asibitin Dr Tayyeb zatafi samun kulawar gaggawa. Da wannan shawarar sukai
amfani suka nufi can, sauranma suka shiga motoci suka dafa musu baya.
Da gaggawa aka amsheta, itama sauran likitoci suka rufu kanta dan Dr Tayyeb
yana wajen Umm-Anum a lokacin, sai da yaga numfashinta ya dawo jikinta, ma'ana ta
farfaɗo sannan ya saka mata ruwa ya fito dan amsa kiran da Mom keta masa a waya.
Sai a lokacinne shi yakejin cewar mama Badiyya suka kawo, bai tsaya bama su Ummah
gamsashshiyar amsar da suke buƙatar jiba ya basu haƙuri akan su jirashi ya nufi
ɗakin da aka kai Mama Badiyya..............✍

Hummmm koya zata kaya a asibiti kuma tsakanin waɗan nan familys guda biyu? Ga
tashin hankalin dake faruwa daga su Jawaad wanda duk ya shafi waɗanan ahali, kumuje
zuwa dan jin yanda zata kaya masoya, dan aski yazo gaban goshi insha ALLAHU, kuma
da gaske bily ta DAWO GARE KU🤗😍😍😘.
ALLAH Ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[2/12, 7:51 PM] Wasila: *_ƘWAI CIKIN ƘAYA!!_*

*_Bilyn Abdull ce🤗_*

_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR... INA KUKE NE? 🔊🔊KU
MARMATSO, DOMIN ZAMAN JIRA YA KARE, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKA HADA HAZAKA DA
KAIFIN TUNANI SUN SAKE ZAGE DAMTSE SUN ZO MU DA WASU SABBIN SALON RUBUTUN SU,
WADANDA ZASUWA’AZANTAR, SU NISHADANTAR, KANA SY DILMIYA KU A KOGIN KAUNA, BASU
TSAYA ANAN BA SALON RUBUTUN SU YA SAKE ZUWA DA SABBIN TSARE TSARE NA DARUSSA DABAN
DABAN, DA KUMA HANYOYIN GYARIN JIKI DA WAJE._

_KADA KU MANTA MARUBUTAN ZAFAFAN DAI SUNE WADANDA SUKA YO MUKU HAR KASHI BIYU A
SHEKARAR 2020 DATA GABATA,: WUTSIYAR RAKUMI DA GUDU DA WAIWAYE NA BILYN ABDULL. 2-
DAURIN BOYE DA ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA.3-BURI DAYA DA QAUNAR MU NA MAMUH
GEE-4- SAUYIN KADDARA DA DAURIN GORO NA HAFSAT RANO. SAI 5-KAI MIN HALACCI DA
IGIYAR ZATO NA MISS XOXO.._

_A WANNAN SABUWAR SHEKARAR TA 2021 MA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE DAWOWA DA WASU
SABBIN DA’DADAN LITTATTAFAN NASU:_

_1_

_* SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA DA ABADAN TAZO MUKU DA SABON


LITTAFIN TA MAI SUNA: *(SIRADIN RAYUWA)💜*_

_2_

_*HAFSAT RANO* MARUBUCIYAR GUGUWAR SO DA RUHI DAYA, TA ZO DA SALON NATA LITTAFIN


MAI SUNA: *(ABINDA KE CIKIN ZUCIYA..*)💘_

_3_

_* MAMUH GEE* MARUBUCIYAR TARAYYAH DA EZNAH, TAZO DA SABON ZUWA MAI SUNA: *(MIN
QALB).*_

_4_

_*MISS XOXO* MARUBUCIYAR NAUFAL DA SAIFUL-ISLAM, TA YUNKURO DA WANI MAI SUNA:


*(KIBIYAR AJALI)*💜_

_5_

_SAI MARUBUCIYA *BILLYN ABDUL* WADDA TAYO MUKU KWAI CIKIN KAYA, DA CIKI DA GASKIYA
TA YINKURO DA WANI MAI TAKEN: *(YANKAN BAYA)*💝_

_RIGIJI GABJI DUKKAN WADANNAN LAGWADAR DADADAN LITTAFAN BIYAR ZASU ZO MUKU NE INSHA
ALLAHU AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA;_

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,


Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*


ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Page 59

..................Motoci na alfarma aka aika daga masarauta domin tarbo su Abbu a


airport kamar yanda aka aika tarbar su Umm-Anum, sai dai su masarauta aka wuce
dasu, inda acan ɗinma suka sami tarba ta musamman da mutuntawa ga mai martaba sarki
Sameer Saifudden da iyalansa, harma da ƴan majalissar sarki baki ɗaya. A yanda
masarautar take yau ko ba'a faɗa makaba kasan anyi manyan baƙi a cikinta, waɗanda
suka isa suka bunƙasa. An baje musu abinci na alfarma na ƙasarmu masu daɗi da
daɗaɗa zuciya.

Tun kafin tafiya ɗakko su Abbu Gimbiya Munaya tasa Amaturrahman ta nema
Number Jawaad, amma taƙi shiga sam, ta kira ta Bilkisu kuma ba'a ɗagaba. Hakan ya
bata mamaki matuƙa, dan tasan dai ai su Jay ɗin sunsan da zuwansu Abbu, a yanda
suka tsara al'amarin kuma daga tarbo su Abbu a airport zasu wuce masarauta ne harsu
Umm-Anum ɗin, bayan su Abbu sunci abinci sun huta sai su ɗunguma baki ɗayansu gidan
Alhaji Babba, daga can idan dare bai rufaba zasu ƙarasa family house ɗin su Jay. To
amma gashi har lokaci ya shige babu Jawaad ɗin babu dalilinsa.

Basu ji halin da ƙasar take ciki ba sai sai kusan isowar su Abbu da awa
ɗaya da rabi sannan takawa ya samu kiran waya daga gwamna akan ya buɗe television
yaga tashin hankalin da a yanzu shima aka faɗa masa game da manyan mutane da ake
ganin mutuncinsu a ƙasar, babban abinda ya razana gwamna kuwa harda wasu a abokansa
masu manyan muƙamai kuma a gwamnatin tasa.
Al'ajabi daya kume sarki lokacin daya buɗe tv kasa ƙwaƙwaran motsi
yayi, dan shima ɗin ai akwai waɗanda suke matuƙar gaisawar zuminci a cikinsu
sosai..........
_________________
ASIBITI
____________

Hankalin su Mom a tashe suna jiran fitowar Dr Tayyeb daga ɗakin


da aka saka Mama Badiyya kira ya shigo wayarta daga mai aikinsu. Kamar bazata
ɗagaba sai kuma mita tuna oho mata ta ɗaga wayar.
A matuƙar ruɗe Talatuwa dake kuka ta zayyane mata abinda ya faru game da
zuwan wasu mutane da sukace su ƴan sandane har gida suka tafi da kuku da maigadi.
A tsawace Mom tace, “What!! K bansan shirme da hauka kinji, ubanmi suda suke
gida kullum zasu aikatama ƴan sanda harsuzo gida su kamasu?”. cikin kuka talatuwa
tace, “Wlhy hajiya da gaske nakeyi, yawwa gama wannan da kikacemin shine babban
yaronku nan yazo gidan”. Da mamaki Mom tace, “Waye? Kina nufin Qaseem?”.
“E...e...eh shi hajiya, wanda hotonsa ke a falo sanye da baƙaƙen kaya tare
da Alhaji”. Jikin Momy har rawa yake wajen ambaton, “Da gaske Qaseem, yaushe suka
barshi ya fito to? Kinga bashi wayar muyi magana nima gani nan zuwa gidan yanzun
nan”. “T..t...to hajiya, bara nakai masa”. Talatuwa ta faɗa tana ɗan gudu wajen bin
bayan Qaseem dako kallon inda take baiyiba ya haye sama ɗakin Dad direct. Yana kama
handle ɗin ƙofar tana ƙarasawa garesa, da rawar jikin tsoro ta miƙa masa wayar tana
faɗin, “Alhaji ƙarami sannu da zuwa, gashi inji hajiya zakuyi magana”. Wani
mummunan kallo daya kaɗa hanjin cikinta ya zuba mata, cikin daka tsawa yace,
“Ɓacemin da gani kona halakaki wlhy”. Zabura Talatuwa tayi da gudu tabar saman,
yayinda Momy kuma taji komai ta cikin wayar, ita kanta tsawar Qaseem sai da ta
sakata cire wayar daga kunnenta ma.

Bata iya cewa sauran ƴan uwanta komaiba ta nufi hanyar fita daga asibitin
da hanzari, duk faman tambayarta lafiya? da sukeyi bata juyoba balle ta amsa musu
harta fice. Da kanta taja motar tabar asibitin zuwa gida.
Akan hanyar momy na nufar gida ta fahimci garin babu lafiya, dan kuwa babu
abinda take gamo da shi a tituna sai matsanancin holdup. Mafi yawancin inda traffic
light suke an haɗa cinkoso a wajen sosai, ga jirage masu saukar angulu da keta yawo
na kaikawo a sararin samaniya, wasu ma daf da mutane suke. Ratse ta ringayi ta
cikin anguwanni tamkar yanda wasu motocin taga sunayi. Da ƙyar ta samu kanta a
anguwarsu, tai fakin motar a ƙofar gida batare data kasheba saboda wani bahagon
ruɗani da ta sake karo da shi kuma, ƙofar gate ɗinsu a buɗe take, ga jami'an tsaro
sun zagaye gidan, cikin sake shiga ruɗani ta afka cikin gidan da sassarfa tamkar
zaga kifa, ananma wasu jami'an tsaron ta sake cin karo dasu a cikin gidan, talatuwa
na durƙushe gefe tana kuka ita da mai bayin fulawa.
“Kai lafiya?”. Mom ta faɗa hajijiya na neman ƙwasarta zuwa ƙasa. Wani
cikin ƴan sandanne ya bata amsa da faɗin, “Hajjaju wannan gidan yana a hannun
hukumane a yanzun, akwai bincike da za'azo ayi a cikinsa daga yanzu zuwa kowanne
irin lokaci”. Cikin tsawa da hucin ɓacin rai, “Mom tace kuɗin ubanwa muka sata to?
Muba ƴan siyasaba ba ma'aikatan gwamnati ba, amma za'a turo mana jami'an tsaron
binciken almun dahana da dukiyar ƙasa?”.
“A'a hajiya, mu ba jami'an tsaron almun dahana bane ba, jami'an tsarone na
farin kaya, da kuma amincewar Sir Qaseem Ali muke anan bisa Umarnin Sir Jawaad
Abdul-aziz Yusuf”. “Qaseem! Da Jawaad kuma?”. “Hakane hajjaju” ya sake bata amsa
kansa tsaye.
Wata ashariya da momy ta manta tama iyata ta kwaso ta dire bisa ƙasa tanayin
wurgi da jikkar hannunta, ta shaƙo wuyan police ɗin tana huci, a take sauran suka
zagayeta da bindiga. Murmushi Munkaila yayi yana ɗaga musu hannu alamar su barta,
ya kalleta fuska babu wasa zaiyi magana ta tare numfashinsa. “Kai shashasha kasan
mi kake faɗa kuwa? Ina Jawaad da Qaseem ɗin suke?”. Ɗan murmushi yay mata yana zame
hannunta a wuyansa ya gyara rigarsa, “Sir Qaseem yanzu ya fita, Sir Jawaad kam yana
filin daga”. Sake rikicewa kanta ya nemayi, batare data nutsu wajen fahimtar inda
batunsa ya dosaba ta fice a gidan tamkar wata mahaukaciya.
Mota ta sake shiga tabar anguwar batare da tamasan kalar tunanin daya dace
ace tayiba, kanta tsaye station ɗin su Jawaad ta nufa, sai dai ɗan karen holdup ɗin
da take fuskanta a yanzun ya zarece na ɗazu data riska tsakanin asibiti zuwa
gida............

___________________
JAY-QAS
________________

Koda tawagar su Jawaad suka iso cikin gari cike suka iske station
ɗinsu da manyansu da ƴan jaridu, abu na farko da suka farayi shine gabatar da
sallolin azhar data riskesu a can da kuma la'asar da a yanzu aketa yinta.
Suna idar da sallar ƴan Jarida sukai musu caa aka, Jay dai bai saurari kowaba
daga shi har Sir Ahmad da sauran manyansu.
Cikin son ƙure mutane irin na ƴan jarida ɗaya a cikinsu ya juya ga masu
ɗaukar rahoton gidan tvn su yana magana a harzuƙe. “To jama'a kamar yanda kukai
hasashe dai hakanne ta kasance, dan kuwa munga alamar rufa-rufar da muka saba gani
ga jami'an tsaronmu idan laifi ya shafi manyan ƙasa yau gashi ta tabbata, to ta
yayama zasu yarda su buɗe komai wa duniya bayan daga kawunansu sai surukansu da
abokan iyayensu dama iyayen nasu. Haka za'a kifemu bayan kwana biyu muji shiru,
bayan kuma tarin gawarwaki da mutanen dake a cikin mawuyacin hali da aka amso a
hannun waɗan nan miyagu ƙuru-ƙuru duk mun gansu. ALLAH dai ya ƙyauta, dama ba sabon
abu bane irin wannan a ƙasarmu ta gado. idan kaga ana yayata mai laifi da cecekuce
da tada jijiyar wuya ga jami'an tsaro to talakane ya aikatashi, amma idan su masu
faɗa ajinne suka aikata sai a rufe komai ruf da sunan kare mutuncinsu ko maganar
shiga kotunsu bakaji balle musan an yanke musu hukunci. To kenan mu talakawa bamu
da suturar mutunci ne? shiyyasa ake ƙwance mana zannuwa a kasuwa?”.
A take wajen ya ɗauki ƙananun maganganun sauran ƴan jaridar, kowa na
ƙoƙarin ɗaukar zancen ɗan jaridar nan ya zama sinadarin zazzage tasa maganar dake
cin ransa.
Ganin abun na neman kawo hatsaniya har wasu cikin ƴan jaridar na fassara
abun da rufa-rufa Jay ya dawo garesu rai a ɓace. Ɗan jaridar da yay maganar Jawaad
ya kafe da kallo idanunsa na sake rinewa zuwa jajur, duk da azabar ciwo da kansa ke
masa haka bai hana maida masa murtaniba cikin tsananin ɗacin murya, “Kar kai
azarɓaɓi akan garin daka shigo cikinsa baƙo. Karka yankema littafi hukunci abisa
bangonsa, duk sharhin da zakayi batare daka buɗe rubutun cikinsaba kuskurene kawai
da son zuciya zai biyo baya. Alokacin da jami'in tsaro yake filin daga shi kaɗai
yasan wane irin kwazazzabo da ƙalubalene rayuwarsa ke fuskanta, da ace yanda ku ƴan
media kuka iya yayata al'amari haka kuke bama jami'an tsaro gudunmawa wajen kare
fituntunun da ƙasa ke a ciki da kowama ya zauna lafiya a duniya. Idan ƙoƙarinmu na
aiki da jajircewa wajen tsayawa mu tantance ke hantarar ra'ayinka akanmu, to kasani
sauyi ba namu bane, kai da irinkane zaku sauya. Duk lokacin da mukejin matsayinmu
ya girmama a duniya wajen jama'ar cikinta, tomu samu gazawa akan ƙoƙarinmu ta
ɓangaren aikinmu ko kasantuwar ɗaukakar tamu. Daga hakanne zamuga muɗin ba komai
bane wajen waɗan nan al'ummar dake ɗaga darajojinmu da girmanmu a bakunansu da
muryoyinsu. Daka zama mai ƙoƙarin ruruta wutar da bakasan tushentaba, mizai hana ka
ajiye aikinka ka koma gidanka ka ɗaura zani kawai, koba komai ƴaƴanka zasu samu
magirkan abinci biyu, shashasha kawai”.
Tsitt wajen. yayi tamkar ruwa yaci kowa, sai su Sir Ahmad kawai dake murmushi
da bin Jay ɗin da kallo tamkar yanda suma ƴan jaridar da sauran jami'an suka
rakashi da idanu harya shige.
Jabeer ne ya matsa garesu cikin ɓacin rai shima, ya sake kallon ɗan jaridar
nan da maganar Jawaad ta sakashi duƙar dakai dan yaji kunya sosai da ganin
kuskurensa akan kalamansa. “Aikin jarida ba neman kuɗi bane ko shiga rigar siyasa,
aikine mai daraja abin girmamawa ga maiyinsa, ita daraja da gaskiya ake samota bada
son a sani ba, kai da kayi waɗan nan kalaman kayisune bisa raɗin kanka kawai ko an
sakaka badan aikin jarida ya baka damar yin hakanba, kai tsaye kake anan domin
neman abinci wa iyalanka dake gida cikin kwanciyar hankali, shiko wannan da kakema
gugar zanar cewar akwai kawunsa da surukinsa shiyasa ake rufa-rufa, tare da nasa
iyalan ya shiga cikin jejin da baida tabbacin fitowa a raye. Atunaninka akwai
sadaukarwar data kai wannan girma kuwa? Ku daina zubarma aikin jarida mutunci dan
aikine na masu mutunci a kowanne lungu da saƙo na duniya, sai dai kaicon irinku
masu girmama fitina da riritata tai faɗin da zata buwayi wanda kuke tunanin kun
tozartar harta dawo ga iyalanku kuma cikin aikin jarida, baka dace da wannan
aikinba sam, ya kamata ka ajiyesa ka koma ka saka rigar siyasa, inaga kalamanka da
nuna iyawarka zatafi dacewa dacan ɗin”. Yay maganar da watsa musu harara shima
yabar wajen.
Sosai jikin duk ƴan jaridar ya sake yin sanyi, masu ƙara gishiri da magi akan
batun sai suka koma gyara harsunansu suna miƙa rahoto mai inganci dan an tunatar
dasu abinda suka manta domin kawai neman ɗaukaka da birgewa.

Duk jarumtar da Qaseem ke arowa yana ƙara ƙarfafa kansa da ita sai hakan
ya nema gagara, kalaman Jawaad dana ɗan jaridar nan sun bala'in taɓa ruhinsa da
zuciya, yabi bayan Jay hawaye na zurara saman fuskarsa batare da yayi tunanin
gogewaba. A jikin ƙarfen lifter Qaseem ya iske Jawaad ya kife kansa dake tsananin
sara masa, bai iya cewa dashi komaiba ya wuce zuwa office.
Ƙamshin turaren Qaseem ɗinne ya fargar da Jay zuwansa, ya ɗago a hankali
yabi bayan Qaseem dake kan lifter ɗin da kallo harya gama hayewa, harya maida kansa
zai sake duƙarwa sai kuma ya zabura cikin faɗuwar gaba, haka kawai zuciyarsa ta
ɗarsa masa wani abu dangane da Qaseem, yariga yasan yanda yake da zafin zuciya.
Cikin zafin nama ya haye lift... ɗin shima, ganima yake bata sauri gaba ɗaya, sai
faman kallon agogo yake dukda kuwa a mintuna biyu kacal take kaisu.
Da gudu ya ƙarasa office ɗin Qaseem ɗin, yana taɓa ƙofar ya jita a rufe,
hasashensa ya zama gaskiya kenan?, Qaseem ya shiga office domin aikata duk abinda
ransa ya raya masa, baya yay ya daki ƙofar office ɗin da masifar ƙarfi, sai dai
bata buɗeba amma ta girgiza. “Innalillahi...” ya faɗa yana bubbuga ƙofar da ƙwala
kiran sunan Qaseem, sai dai ko sau ɗaya Qaseem ɗin bai amsa masaba, rikicewa Jawaad
ya sakeyi, yabar wajen da gudu zuwa office ɗinsa dan ya tuna akwai key ɗin office
ɗin Qaseem ɗin a wajensa wanda Sir Ahmad ya bashi ranar domin ɗaukar wasu files a
ciki, da ƙyar ya iya gano keys ɗin saboda a rikice yake, yana ɗauka ya dawo da
gudu.

Jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar Qaseem daya samo bullets da ƙyar cikin office ɗin
nasa ya ƙara azama wajen ɗurasu cikin bindigar yana kuka shaɓe-shaɓe da hawaye.
yana gama zuba bullets ɗin cikin bindigar Jay na buɗe ƙofar ya shigo da gudu,
saurin ɗaurawa a kansa yay da rawar jiki yana ƙoƙarin saka ɗan yatsansa saman
kunamar bindigar jikinsa sai tsuma yake.
Da matsanancin ƙaraji Jay yace, “Qaseem!!! Karkayiii!!!!!” yay maganar cikin
wani irin doka mahaukacin tsalle ya dire gaban Qaseem ɗin da wawurar hannunsa yay
sama da shi harsashin da Qaseem ɗin ya harba ya samu p.o.p ɗin dake office ɗin.
Yanda Jay ya riƙe haka Qaseem ma yaƙi saki, sai da suka ƙarar da harsasan duk biyar
sannan Jawaad ya ɗauke fuskar Qaseem da mahaukacin mari cikin gushewar hankali.
Wannan harbi shine ya maido hankalin su Sir Ahmad wajen, yayinda ƴan jarida
da sauran mutane suka fara gudu sun zata hari aka kawo.
“Baka da hankali ne!!!? Wace riba kake tunanin samu a kashe kanka
da zakayi Qaseem? Kaifa musulmine! Taya zaka bari tunanin aƙidar yahudu da nasara
har takai mizanin tasirin zama a zuciyarka irin haka? kai ƙoƙarin salwantar da
rayuwarka da kanka!!! Kasan kuwa hukuncin wanda ya kashe kansa a addinin
musulunci?. To sunansa KAFURI!!! kuma wlhy WUTACE zata zama sakamakonsa!!!”. Jay ya
faɗa yana huci da nuna Qaseem ɗin da hannu.
A zabure Qaseem ya hankaɗa Jawaad yay baya yana faɗin, “Bani da hankali
Jawaad, wlhy da gaske na haukace, tabbas na haukace, minene amfanina idan na zauna
a raye a wannan duniyar da babu komai a cikinta sai ruɗani?!!” ya finciko rigar Jay
jikinsa na rawa, hawaye na zuba masa babu ƙaƙƙautawa, “Idan ka hanani kashe kaina
mi kakeso nayi Jawaad? Wacce irin amsace dani da zan bama duniya akan mahaifin da
nake kallo babu kamarsa a da? Matsayin suruki kawai ya taɓa amsawa a gareka amma
akai maka gugar zana da halayyarsa yanzun, to inaga ni da yake mahaifina!!, da wane
idanun kakeson na sake kallonsa Jawaad?! Dan ALLAH na roƙeka ka barni na kashe
kaina na huta!!”.... Ya ƙare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya da ya saka
jijiyoyin kan Jawaad sake mimmiƙewa shima hawayen na taruwar masa a idanu. Jawo
Qaseem yay ya rungume a jikinsa suka fashe da kuka a tare.....😭
(Kai jama'a, wlhy zuminci ya wuce gaban wasa komai lalacewarsa😭😭)

Dalilin go-slow da Mom ta riska a hanya yasa ta iso station ɗin a


wahale cikin dogon jinkiri, da kutsa-kutsar shiga cikin ƴan jarida ta samu shiga
ciki da ƙyar, inda shigar tata tai dai-dai da harbin harsasai biyar da Qaseem da
Jawaad sukayi. Da wannan ruɗanin da jama'a suka shiga ta samu damar bin ayarin su
Sir Ahmad zuwa office ɗin Qaseem dan ta sani, bata fahimci can su Sir Ahmad ɗin ke
yunƙurin zuwaba saida taga sun isa tare da su inda itama ta dosa.
Itace farkon shiga office ɗin, sai tai tsaye turus tana kallon Qaseem da
Jawaad dake rungume da juna da dauraren kalamansu.
“Qaseem hakan ba mafita bane ɓata ne, ba'a samun hutu da saɓon UBANGIJI
bisa ganganci, ka daina irin wannan tunanin”. “Dolene nayi Jawaad, ƙo Bilkisu da
tazo a ƙarshen ƙaddarar kunyarta nakeji balle kai da sauran mutane, nayi nadamar
kasancewata jininsa wlhy Jawaad”.

Da sauri Momy tazo ta fincike kafaɗar Qaseem ta matsar da shi baya daga
jikin Jawaad, batare da ta tsaya ta gama fahimtar matsalarba, jin sunan bilkisu
kawai da tai a bakin Qaseem ya sakata harzuƙa da fassara matsalar akan bilkisun ne
komai ke faruwa ma kawai, hawaye na zirar a kumatunta tace, “Qaseem wai mi kakeyi
hakane? akan tsintacciyar mage, kake wannan hanƙoron da tura mana ƴan sanda gida
saboda cin zarafinmu? Akan butulu da ya wulaƙanta ƴar uwarka har kake iƙirarin
mahaifinka ya shirya tarwatsaka? TSINTACCIYAR MAGE! YARINYAR DA MUKA ƊAKKO A
TSAKKIYAR RANA! YARIYAR DA......”

“Da haɗin bakinki kenan mijinki ke aikata komai!!” Qaseem ya faɗa cikin
matsanancin fushi tamkar zai haɗiye Mom, baya tai da sauri jikinta na rawa, cikin
rawar murya tace, “Qaseem anya kana cikin hankalinka kuwa? Miya samu kanka? Ko an
sauya mana kai ne?”.
“Komai ma ya sameni fiye da yanda tunaninki ke baki ke da shi. Tun bansan
kaina ba ke da shi kuketa nunamin banida wani maƙiyi a duniya sama da Jawaad, Why?.
Mom! Nace Why? Shiɗin baɗan ɗan uwanki bane?, shi ɗin ba mijin ƴarku bane? Miya
aikata mai zafine wai a gareku da har yau ban taɓa saninsa ba ni?......”
“Qaseem!!” Mom ta faɗa cikin tsawa tana fashewa da kuka.
Cikin ficewar hayyaci Qaseem yace, “Eh ki kira sunana koma sau dubune,
gaskiyace bazan taɓa fasa faɗaba, to idanma baki saniba yanzu zan sanar miki, idan
kuma kin sani bara na maimaita miki. Ita wannan tsintsiyar magen da kike magana
MIJIN naki ya tsintota daga ranar ne dan ya jefata cikin abinda yafi ranar zafi,
cikin wuta yay niyyar jefa mata rayuwa saboda cimma burinsa, mahaifinane shi amma
nasha zarginsa da aikata abubuwa marasa ƙyau a cikin gidan nan, amma da naso ɗaukar
mataki saina gaza hakan, na tabbata dukkan ƴan aikin da akai raping a gidannan
shine yay musu.....”
Tsawa Mom ta daka ma Qaseem jikinta na matuƙar rawa, “Qaseem!! Mahaifinka
zaka ƙullana sharri irin wannan saboda Jawaad da Bilkisu?”.
Da ƙarfi Qaseem ya daki tebir ɗinsa, kayan sama suka tarwatse, ya matsa gab
da Mom yana nunata da ɗan yatsa ƙirjinsa na sama da ƙasa na kumburar zuciya. Ya
cigaba da faɗin, “Tun kin nuna bakisan komaiba bara na faɗa miki to, tun lokacin da
akaima ƴar matarnan Amina fyaɗe a cikin gidanmu na gaskata hakan a cikin raina,
domin kuwa lemon da aka ajiye ta sha lemo ne da kaf gidan nan shi kaɗaine ke
shansa, hakanma yasa ba'a ajiyesa a fridge ɗin kitchen sai na falonsa kawai, ko a
falon ƙasa inhar baya ƙasar kwashewa kike ki maida masa sama, to tayaya akai ranar
yaje kitchen har yarinyar ta gani ta ɗauka ta sha bayan shi mai shan ma baya nan?
Abu na biyu sai da na ɗauki kwalin lemon a bola naje nai bincike akan ɗan sauran
cikinsa na gane magani ne mai ƙarfi aka saka a ciki kuma a ƙalla ya kai kwanaki
biyar da zubawa, abu na uku na zauna nayi dogon nazari da tunani harna gano ainahin
maganain da akai amfani da shi, sai kuma kwatsam na tunano na taɓa ganin maganin a
wajen Dad amma a wancan lokacin sai ya gayamin na ciwon bayane dan na gansa da
shine a bazata, da yake kuma ban kawo komai a rainaba sai ban amsa na karanta ba a
lokacin. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al'amuransa, sai dai abin mamaki
bana iya cewa komai akan dukan abinda zan gani. to bara nama faɗa miki abinda baki
saniba, a dukkan tafiye-tafiyensa cikin kashi uku biyu bayinsu yake ba, idan yace
yabar ƙasarnan tafiyar sati biyu to kwana huɗu ko sati guda ya keyi ya dawo, da
wannan makircin nasa yake amfani wajen aikata laifi a rasa wanene keyi a gidan, Mom
ya kamata kiyi tunani da hankalinki, a dukka masu aikinmu uku da akai Raping a
gidanmu duk sai baƙya nan ake aikatawa, kuma da anyi washe gari ko kwana biyu dayi
Dad yake dawowa.......”
Ƙasa Mom ta zube tana kallon Jawaad dake tsaye kawai yana kallon tamkar wani
gunki, tun fara maganarsu baice komaiba bai kuma motsa ba. hawayene ke kwarara a
idanun Mom tamkar an buɗe fanfo.
Qaseem ya nuna Jay da faɗin, “Kayi haƙuri Jay ka gafarceni, zan faɗi wani
abu a kan matarka duk da bata a wajen nan, tunda Bilkisu tazo gidanmu ban taɓa
jinta a zuciyata da sunan soyayya ba, sai dai ina sonta matsayin ƴar uwata kawai.
Amma tun randa na farka a barci naga Dad tsaye kaina a cikin ɗakina naji duk duniya
babu wadda nakeso sama da yarinyar nan, ga wata sha'awarta mai tsanani inaji wadda
inhar zata kasance kusa dani sai naji inason taɓa mata jiki, abin mamaki duk wannan
sha'awar tata da nakeji ban taɓa jin zan iya lalata mata rayuwaba, ni dai kawai
burina na taɓa jikinta ko nayi kissing ɗinta na rungumeta shike nan. Da ya ke kuma
yarinyace mai tarbiya ko hannunta bata yarda na taɓa sai ta nunamin ɓacin ranta.
Kuma saifa ina a kusa da itane nakejin hakan, amma da zarar bama tare da juna ni
mantawama nake da ita gaba ɗaya. A daren da Dad ya fara shigo mata ɗaki har aka
tsoratamu da ƙara a gidannan nine na fara fitowa, ni duk zatona mai gadine wani abu
ya sama, shiyyasa nai gate kai tsaye, ina isowa maigadi na buɗema Dad ƙofa ya fita
a gidan....”
Dafe kai Jawaad yayi da sauri zuciyarsa na wani irin matsanancin harbawa
da sauri-sauri, duk da Dad yake zargi dama hakan bai hanashi jin maganar tai masa
nauyiba a ƙwaƙwalwa da zuciya....
“Ƙwarai kuwa Dad” Qaseem ya bama ya sake maimaitawa yana kallon Mom cikin
ido, “A tunaninki mai aƙidar kar ƴan uwansa su raɓesa ne zai ɗakko budurwa kamar
bilkisu ya ajeta gidansa dan ya ƙyautata mata rayuwa kawai? Aini tun washe garin da
aka kawota gidannan na ganta kuma akai min bayanin zuwanta nasan akwai manufa a
zuciyarsa game da ita, sai dai narasa ta wace hanya zan kuɓutar da ita? Wannan
mijin naki da kike ji da gani ramin bushiyane daga shi sai ƴaƴansa, ke kuma matarsa
kura ce kema daga ke sai ƴaƴanki. Bara na sake maimaita miki shine keta bibiyar
rayuwar marainiyar ALLAH akan fyaɗe har cikin gidan aurenta, da yaga bazai cimma
burinsa cikin sauƙiba shine ya tafka mana asirin da har nai maganar shirya aurenta
duk da a zuciyata sam ba haka bane ba. A gaban duniya ya nuna cewa ya ƙyautata mata
rayuwa, zai kuma aurama ɗansa jininsa ita, amma sai ya zagaye ta bayan fage shi da
ɗan uwanki Uncle Nasir suka zurmaki a ciki da ɗauraki a dukkan hanyoyin da suka
gama tsarawa, ke kuma kika hau saboda baƙya son aurenmu bisa naki gurɓataccen
tunanin na jahilci da son zuciya. Kuka ɗakko hayar ɗan fir'auna akan ranar ɗaurin
aure za'a aura mishi ita, ni kuma zaɓinku, daga baya sai ace mistake aka samu, shi
kuma dama kunbiyasa akan karya sake ya saketa duk bala'in da za'ayi har sai ƙura ta
lafa an kaita gidansa. sai shi Dad yaje ya cika burinsa a kanta kawai batare da
kowa yasan hakanba har ke kanki. Sai dai UBANGIJI ba azzalumin sarki bane, sannan
shi yana dubi da ƙyawawan zuciyoyi masu tsoronsa da biyayya a garesa, ashe Jay ya
saka ana bibiyar dukkan al'amarinsu basu sani ba..........”
Zubewa Mom tai ƙasa kawai tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai
tare da riƙe kanta da ke juya mata. Jawaad yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa da
mai dawa kan Qassem. Murmushi mai ciwo da ƙunar zuciya Jay yay yana tura ɗayan
hannunsa cikin aljihu, ɗayan kuma ya dafa kafaɗar Qaseem sukaima juna murmushi.
Takawa ya sakeyi gaban Mom ya tsaya har lokacin fuskar tasa da murmushin, ya
durƙusa a gabanta yana haɗiye ɗacin daya tokare masa maƙoshi, “Har yanzu ke uwace a
gareni Mom, yayar mahaifina, duk da ina zargin kina cikin waɗanda suka tarwatsa
masa ahali”.
Da sauri Mom ta ɗago tana kallon Jay, ta shiga girgiza kanta tana hawaye,
“Jawaad dan ALLAH kar kaimin wannan mummunar zargin, mi Abdul-aziz zaimin niko a
duniyarnan da har zan tarwatsa masa a hali?......”
Miƙewa Jawaad yayi yana ɗage kafaɗa da taɓe baki, “Wannan amsar a gaban alƙali
zaki badata Mom ba ananba”.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Aysha wannan wace irin ranace”. Mom
ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka.
Qaseem da yakejin kamar ace yau ɗin ranar barinsa duniya ce yace, “Momy
wannan ranace ta tonon silili, ranace mafi muni da a garemu bisa ga son zuciyar
mijinki, rana ce da duniya suka san wanene shi? Mom Dad ya cutar da rayuwarmu,
kaicon dukiyar da zata kasance haramtacciya ga mai ita, ki kalla yanda ake nunasu
cikin ƙasƙanci dan ALLAH, wace riba sukaci? Wane alfahari suka barmana muyi? Wane
tunƙaho da taƙama ya rage mana kuma?”.
Mom da batasanma wainar da ake toyawaba game dasu Dad sai yanzu da Qaseem
ya nuna mata a tvn office ɗinsa a take ta ƙwalla ƙara ta zube yaraf a sume.
Jay daya fice ƙofar office ɗin ya tsaya dansu Sir Ahmad tuni suka bar wajen
ganin maganace data shafi family ya dafe kansa da rumtse idanunsa da masifar ƙarfi,
dan yaji dukkan abinda Qaseem ɗin ke faɗama Mom, ya kuma tabbatar ƙarar tata nada
nasaba da ganin abinda ya farun.

___________________________
Dr Tayyeb hospital
_______________________

Kamar yanda ƙarar kai kawon jirage ta ɗauki mafi yawan mutanen
dake cikin asibitin haka ta ɗauki tasu Anuwar dake zaune jigum-jigum suna jiran
farkawar Umm-Anum, dan Dr Tayyeb ya sake shiga ya dubata, ya kuma musu bayani akan
su kwantar da hankalinsu da ruwan da aka saka mata ya ƙare zata farka normal insha
ALLAH.
Aunty Batool ce ta fara miƙewa ta leƙa ta Window'n da suke a kusa da shi,
da ɗan mamaki ta juyi tana kallonsu Ummah da faɗin, “Anya kuwa yau garin nan lafiya
yake? Helicopters nefa na sojoji keta yawo wannan ƙarar da mukeji”.
“Helicopters kuma? To miya faru kuma?”. Ummah ƙarama ta faɗa tana miƙewa
itama ta leƙa. Tabbas kuwa zancen Batool gaskiyane, dan har wasuma dake cikin
asibitin sun fara fita waje. “Gaskiya garin nan babu lafiya kam”. Ummah ƙarama ta
sake faɗa tana nufar ƙofa.
Da sauri su Anum sukabi bayanta harda Batoul da Anuwar ma daya bisu a ƙarshe
shi da Ummah babba, sai dai Ummah babba na gabansa.
“Ya salam”. Anuwar ya faɗa da sauri saboda karo da sukaci da wani bawan
ALLAH dake ƙoƙarin shigowa shi kuma Anuwar ɗin yana yunƙurin fita. A kusan tare
suka buɗe baku zasu bama juna haƙuri sai hakan ya gagara kowa ya cak a tsaye baki
buɗe jiki na tsuma. Idanun Uncle Sulaiman tamkar zasu faɗo ƙasa dan ruɗani da
al'ajabi, cikin sarƙewar harshe yace, “Ja...waa...” sai kuma ya gaza ƙarasawa ya
girgiza kansa yana haɗiye yawu da ƙyar.
Shiko Anuwar wani irin yamutsawa jininsa keyi da kansa, ya kafe Uncle
Sulaiman da kallo tamkar ya samu television ɗin kallo. A haka Shahudah da sauran
ƴammatan family ɗin sa'anninta suka iso wajen suma zasu koma ciki. A take duk
sukaja wani wawan birki suna kallon Anuwar.
“Kai!!”
Shahudah ta faɗa daɗan ƙarfi tana matsawa gab da Anuwar da binsa da kallo daga sama
har ƙasa tana zagayashi. Nannauyan numfashi Anuwar ya sauke da ɗan lumshe idanu ya
kalato busashen yawun daya rage masa ya hadiye da ƙyar da raɓawa ta gefen Uncle
Sulaiman zai wuce. Caraf Shahudah ta riƙo hannunsa jikinta na rawa. “Kai dan ALLAH
wanene kai?”.
“Muhammad Anuwar Abdul-aziz yusif tafida”. Wata murya dake a bayansu ta
basu amsa saɓanin shi Anuwar ɗin da sukaima tambayar. Juyawa sukai da azabar sauri
har Uncle Yusif na neman zubewa ƙasa wajen rawar jiki.
“Hajiya Mariya, kinsan mi kika faɗa kuwa?”. Uncle Sulaiman ya faɗa yana
ware idanunsa akan Ummah babba data basu amsar.
Murmushi mai ciwo Ummah babba tayi tana kamo hannun Anuwar ɗin cikin nata,
“Alhaji Sulaiman ai ko baku sami wannan amsarba ya kamata kuyi tunanin hakan direct
tunda wanda ya mutu baya dawowa ai ko? Kuma koda ace yaya nada rai ai bazai zauna a
wannan ƙuruciyarba tunda har Jawaad daya bari matsayin ɗa ya wuceta”.
“Haj....h...ha..hajiya mariya kin sake sakani a ruɗani wlhy, a ina Abdul-
aziz ya samu ɗa bayan Jawaad kuma?”.
“Biyoni da zakayi shine kaɗai zai baka amsar dukkanin tambayoyinka”. Ummah
ta faɗa tana murmushi da kama hannun Anuwar suka nufi corridor ɗin da ɗakin da aka
kwantar da Umm-Anum yake.
Ba Uncle Sulaiman kawai ba, hatta su Shahudah bin bayansu sukai, yayinda wasu
a cikinsu kuma suka nufu kaima iyayensu rahoto.

Dr Tayyeb na ƙoƙarin fitowa daga ɗakin da Umm-Anum take dan ya sanarma


su Ummah su shiga an cire mata drip yaci karo da Ummahn dake riƙe da Anuwar.
Murmushi ya ɗanyi yana ja baya ya koma cikin ɗakin da juyawa ya kalli Umm-Anum dake
kallonsu da murmushi yace, “Yauwa hajiya, dama zan sanar muku ku shigo ta tashi
normal Alhmdllh, dan zama mu iya sallamarku kamar”.
Kafin Ummah tace wani abu Uncle Sulaiman dake a bayansu cikin tsananin kiɗima
yace, “Bilkisu!”. Da sauri Umm-Anum ta maida dubanta gareshi, sai kuma taɗan waro
idanu waje itama tace, “Yayah Sulaiman!”. Cikin matuƙar rawar jiki ya afka cikin
ɗakin, babbar rigarsa har tana neman taɗesa Dr Tayyeb yay azamar tarosa yana faɗin,
“Subahanalillhi, Alhaji yi a hankali”.
Duk da Umm-Anum batajin ƙwarin jikinta hakan bai hanata sakkowa daga saman
gadon ba. Sakkowar tata kuma tayi dai-dai da faɗowar Uncle Uwaisu da sauran ƴan
gidan su Jawaad ɗakin.
“Wlhy itace da gaske!!” Uncle Uwaisu ya faɗa yana jan birki da ɗaga hannaye
sama tamkar wani zararre.... Kafin wani a cikinsu ya samu damar sake tofa tashi
Nabeelah ta kutso tsakkiyarsu jikinta na rawa, “Ummah! Ummah!! Ummah!! Ku kalla
television, ku kalli abinda ya faru dasu Yayanmu a wajen ƙwato Alhaji babba,
m....m..matsafa Ummah, wlhy matsafa suka gano acan.....”
Uncle Sadiq ne yay azamar rarumar remote ɗin television ɗin ɗakin ya kulla,
anko haske dai-dai inada ake fiddo su Uncle Nasir daga cikin gidan daga su sai
jajayen ƙyallaye, Jawaad na rungume da Alhaji babba yana shafa masa ruwa a fuska
za'a sakashi cikin helicopter shi da wasu a cikin waɗanda aka ceto.
A take ɗakin ya ruguntsume da tsananin tashin hankali da ruɗani,
Umm-Anum ta fashewa da kuka tana dariya kuma, cikin wani ƙarfin zuciya ta
ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”.
A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi
mai wahalar fassara a fuskokinsu................✍

Nima dai kam na tsinci kaina a yanayin har takai alƙalamina da faɗuwa a ƙasa batare
da na shirya hakanba😳🚶.

Kuyi manegi babu editing yau🤒🚴🏼

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻


[2/12, 7:52 PM] Wasila: *_ƘWAI CIKIN ƘAYA!!_*

Bilyn Abdull ce

Page 60

_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR... INA KUKE NE? 🔊🔊KU
MARMATSO, DOMIN ZAMAN JIRA YA KARE, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKA HADA HAZAKA DA
KAIFIN TUNANI SUN SAKE ZAGE DAMTSE SUN ZO MU DA WASU SABBIN SALON RUBUTUN SU,
WADANDA ZASUWA’AZANTAR, SU NISHADANTAR, KANA SY DILMIYA KU A KOGIN KAUNA, BASU
TSAYA ANAN BA SALON RUBUTUN SU YA SAKE ZUWA DA SABBIN TSARE TSARE NA DARUSSA DABAN
DABAN, DA KUMA HANYOYIN GYARIN JIKI DA WAJE._

_KADA KU MANTA MARUBUTAN ZAFAFAN DAI SUNE WADANDA SUKA YO MUKU HAR KASHI BIYU A
SHEKARAR 2020 DATA GABATA,: WUTSIYAR RAKUMI DA GUDU DA WAIWAYE NA BILYN ABDULL. 2-
DAURIN BOYE DA ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA.3-BURI DAYA DA QAUNAR MU NA MAMUH
GEE-4- SAUYIN KADDARA DA DAURIN GORO NA HAFSAT RANO. SAI 5-KAI MIN HALACCI DA
IGIYAR ZATO NA MISS XOXO.._

_A WANNAN SABUWAR SHEKARAR TA 2021 MA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE DAWOWA DA WASU
SABBIN DA’DADAN LITTATTAFAN NASU:_

_1_

_* SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA DA ABADAN TAZO MUKU DA SABON


LITTAFIN TA MAI SUNA: *(SIRADIN RAYUWA)💜*_

_2_

_*HAFSAT RANO* MARUBUCIYAR GUGUWAR SO DA RUHI DAYA, TA ZO DA SALON NATA LITTAFIN


MAI SUNA: *(ABINDA KE CIKIN ZUCIYA..*)💘_

_3_

_* MAMUH GEE* MARUBUCIYAR TARAYYAH DA EZNAH, TAZO DA SABON ZUWA MAI SUNA: *(MIN
QALB).*_

_4_

_*MISS XOXO* MARUBUCIYAR NAUFAL DA SAIFUL-ISLAM, TA YUNKURO DA WANI MAI SUNA:


*(KIBIYAR AJALI)*💜_

_5_

_SAI MARUBUCIYA *BILLYN ABDUL* WADDA TAYO MUKU KWAI CIKIN KAYA, DA CIKI DA GASKIYA
TA YINKURO DA WANI MAI TAKEN: *(YANKAN BAYA)*💝_

_RIGIJI GABJI DUKKAN WADANNAN LAGWADAR DADADAN LITTAFAN BIYAR ZASU ZO MUKU NE INSHA
ALLAHU AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA;_

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*


ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Page 60

...............Umm-Anum na kuka tana dariya duk a lokaci ɗaya ta nuna tv'n da


yatsanta manuniya, cikin wani ƙarfin zuciya ta ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu
ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”.
A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi
mai wahalar fassara a fuskokinsu. Kowa ya gagara cewa komai sai kallonta kawai da
suke. Ta share hawayen da suka gama wanke mata fuska tana kallon Ummah babba.
“Mariya a kaini wajen baba”. Da ƙyar Ummah babba ta iya gyaɗa mata kai a hankali.
Bata ƙara cewa komaiba ta gyara mayafin jallabiyar ta data naɗa tamkar yanda
larabawan Saudia keyi, Batool ta ɗakko mata takalmanta zuwa gabanta, dafa Batool
ɗin tayi ta saka dan ƙafarta ciwo take mata kaɗan-kaɗan, tun jiya bata gama saki ba
har yanzun.
ta maida dubanta ga su Uncle Sulaiman dake tsaye tamkar sojoji, har yanzu
babu wanda ya iya gaskata ruɗani da al'ajabin da idanunsu ke gani a zahiri da
magiji. Hannayenta🙏🏻 ta haɗe waje guda tana ɗan murmushi, “Ku gafarceni, ganin
Mahaifina a yanzu gareni yanada matuƙar muhimmanci”. Bata jira amsarsu ba ta raɓasu
ta wuce abinta Batool da Anum da Nabeelah sukabi bayanta.

Da kallo suka bita tamkar wasu wawaye harta fice ita da zugarta.
Ummah ƙarama da babba suma sukai yunƙurin bin bayansu. Uncle Sulaiman ne ya sauke
nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin jiki da rawar murya yace, “Hajiya Mariya a
ina kuka samu Bilkisu? Tun tsahon wane lokaci kuma?”. Kanta ta girgiza masa tana
share guntun hawayenta itama, “Bani da ikon amsa waɗan nan tambayoyin Alhaji
Sulaiman, inaga mu bari har sai lokacin da Yayah taso hakan da kanta, na tabbata
zatazo ta sameku har gida insha ALLAHU. Mun barku lafiya”. Ta ƙare maganar da kama
hannun Ummah ƙarama suka fice suma.
“Uncle wacece ita ɗin wai?”. Shahudah da idanunta ke lullumshewa
saboda hajijiyar da take gani ta tsananin tashin hankali ta faɗa tana dafe bango.
Saurin ruƙota matar Uncle Sadiq tayi jikinta na rawa itama. “Shahudah!!” ta faɗa
daɗan ƙarfi ganin jikin Shahudah ya fara saki alamar neman suma takeyi itama.
Ruɗewa ɗakin ya ƙarayi, masu share hawaye suka ƙara ƙarfafa kukansu da sauti,
yayinda wasu suke zubewa ƙasa daɓar tsabar shiga ruɗani da abinda ake nunawa har
yanzu daga gidan tv.

__________________
STATION
_____________

Da taimakon Jawaad da Qaseem aka fita da Mom zuwa mota, Qaseem ya


shiga baya ya riƙeta yana kuka da kiran sunanta da roƙon karta tafi ta barsu, “Mom
Please ki tashi, dan ALLAH karki tafi ki barmu muna sonki, idan kika tafi abin zai
mana yawa Mom, idan kika tafi wa zamu kalla muji daɗi”. Ya ƙare maganar da kife
kansa bisa fuskarta yana cigaba da kuka, shi kansa bai taɓa sanin shi rago bane mai
rauni irin haka ba sai a yau, gani yake kaf duniya babu wanda ya kaisa shiga ruɗani
da tsananin tashin hankali.
Har Jawaad daya ja motar ya fice daga station ɗin Qaseem nata kuka rungume da
Mom. A haka suka isa General hospital, inda suka tadda ƴan jarida da jama'ar gari
cike anan ma, har takai da ƙyar ƴan sandan da aka zuba ke control ɗinsu. Burin kowa
yaga gawarwaki da mutanen da aka ƙwato wajen su Dad. A haka dai aka samu shiga da
Mom ciki da ƙyar. Darajar waɗanda suka kawotan yasa akai mata amsar gaggawa da
miƙata wani ɗaki.

Motar su Umm-Anum na shigowa asibitin ana shiga da Mom ciki, gurin a


cinkushe yake da mutane, hakan yasa suka rasa hanyar da zasubi su shiga balle susan
ta inda zasu fara. Aunty Batool ce tai tunanin kiran Jawaad, dan haka ta ciro
wayarta daga bag ta fara nemansa, harta tsinke bai ɗaga ba, bata gajiba ta sake
kira, nan ɗinma dai harta tsinken bai ɗagan ba. Kanta taɗan dafe zatai magana sai
idanunta suka sauka akan Jawaad dake magana da wasu police su uku da alama suna
masa bayani ne akan yanayin da asibitin yake ciki na cikar mutane da ƴan jarida.
“Alhmdllhi ga yayanmu ɗin canma ai”. Dukansu inda take kallo suka kalla, kafin
wani ya samu yin magana Anum da Nabeelah suka nufi inda yake, sai dai kafin su
ƙarasa aka dakatar dasu a tsawace. Bayani Nabeelah keson ma police ɗin daya
tsaidasun amma yaƙi saurarenta, hakan yasa ta fara masa magana da tsiwa dan sun
roƙesa amma yana neman cin zarafinsu ma. Hayaniyarsu ta jawo hankalin Jay ya juyo.
A bazata yaga ƙannensa, ya ɗan ɗaura hannunsa na dama saman goshinsa da keyi tamkar
zai tsage saboda azabar ciwon kai. Da sauri ya kalli police ɗin da suke tare yana
nunasu Anum ganin wancan ɗan sandan da suke tare ya ɗaga hannu zai mari Nabeelah
amma ta duƙe. “Kaga, cemasa ya barsu suzo”. Amsa masa yay da to, yana nufar inda su
Nabeelah suke, yay saurin riƙe hanun ɗan sandan daya sake ɗaga hannu zai mari
Nabeelah dan bakinta yaƙi mutuwa saboda haushin baƙar maganar daya faɗa musu dan
sunce su ƙannen Jay ne wajensa zasuje. A harzuƙe ɗan sandan ya juya zaiyi magana
sai yaga ogansu, saurin gyara yanayinsa yay zai masa bayanin abinda ya faru
tsakaninsa da yaran sai yaji ogan nasa yacema su Nabeelah suje wajen Jay ɗin. “Oga
kasan mi sukayimin kuwa?”. Murmushi yay masa da ɗan buga kafaɗarsa, “Komi sukai
maka kayi haƙuri. ƙanen yallaɓai Jay ne”.

Da kaushin murya Jawaad daya tsare su Nabeelah da rikitattun idanunsa


yace, “Miya kawoku nan?”. “Uh...Uhm Yayanmu bamu kaɗai bane, Ummu ce tace a kawota
wajen Alhaji babba”. Nabeelah ta bashi amsa tana laɓewa bayan Anum idanunta cike da
tsoro.
Da sauri Jay ya hau waige-waige, saiko idanunsa suka sauka akan Batool da
su Ummah da suma kallonsu sukeyi. Batare da ya sake cewa komaiba yabar wajen zuwa
inda su Batool ɗin suke.

Umm-Anum data rage a mota bata fitoba hango Jay ya nufosu ta fito da ƙyar
dan jikinta duk babu daɗi, kallo ɗaya zakaima idanunta kuma kasan tayi kuka sosai,
dan sun kumburi sun kumayi jaa.
Sauri riƙeta Jawaad daya ƙaraso yayi, ya taimaka mata ta tsaya akan
ƙafafunta sosai tana sauke ajiyar zuciya, “Ummuna miyasa kuka fito? Kallafa ƙafarki
ta kumbura?”. Maimakon ta bashi amsa sai tambaya ta jefa masa, “Ina Bilkisu?”.
“Amma Umm......” “Ni dai ina yarinyata nace maka?”. Numfashi ya sauke da ɗan ƙarfi
yana lumshe idanu sai kuma ya buɗe lokaci ɗaya, “Tana ciki Ummuna, sun saka mata
drip ne saboda ta suma acan, amma inama ganin ƙila ta farka yanzun dan tun ɗazun Dr
Bello ya sanarmin ta farfaɗo”. “Alhmdllh, babana fa”. Yanzu kam ɗan murmushi ya
mata da sumbatar hannunta, “Shiyyasa naga idanunki sun kumbura ko Ummuna, kinyi
kuka?”. Kansa ta dungure tana ƴar hararsa, yay murmushi da kama kunnuwansa alamar
na tuba.

★★★★

Sun fara shiga ɗakin da aka kwantar da Bilkisu, kamar yanda Jawaad yay
hasashe sun iske ta farka, tana zaune jingine da filo wata Nurse na bata abinci da
takeci da ƙyar dan warin asibitin yay masifar addabarta, farkawarta amanta biyu
saboda warin asibitin, yanzu ma Dr Bello ne da kansa yasa aka kawo mata abincin dan
taci tasha magani kafin Jay yazo ya ɗauketa kamar yanda ya sanar masa.
Gaba ɗaya tayi wani zuru-zuru, idanunta sunyi masifar kumbura da
ƙanƙancewa, sannan sunyi jajur a ciki. shigowar su Jay yayi dai-dai da zaburarta ta
sakko a gadon saboda tahowar amai, Nurse ɗin ta ajiye tray'n abincin da sauri tana
ƙoƙarin kamota amma tuni takai toilet. Duk rufa mata baya sukai cikin tashin
hankali, sai dai duk a ƙofar bayin sukaja birki, Jay da Nurse ɗin ce kawai suka
sami damar shiga. Sosai hankalin Jay ya tashi ganin yanda bily ke yunƙurin amai
tamkar zata amayo hanjin cikinta, Nurse ɗin na riƙe da ita tana jera mata sannu da
shafa bayanta. Matsowa yay kusa da ita shima ya ruƙo hannunta. Da ƙyar aman ya
tsagaita, ya taimaka mata da kansa ta wanke bakinta, sai numfashi take saukewa a
wahale, kwantar da ita yay a ƙirjinsa tausayinta mai tsanani yana ratsashi, a ƙasan
ransa kuma tunani yake ‘mi taci haka?’.
“Ka kaini gida, banason warin asibitin nan”. Ta faɗa murya can ƙasan
maƙoshi tana sake lafewa a jikinsa da shaƙar ƙamshin turarensa da yake ɗan dawo
mata da nutsuwarta. Ɗago kanta yay ya saka fuskarta cikin tafukan hannunsa suna
kallon juna, “Mi kikaci haka?”. Ya faɗa cikin tashi daskararriyar muryar yana raba
idanu akan fuskarta tamkar zai gano abinda ke damunta anan ɗin. Matsawa tai zata
sake kwanciya a jikinta tana faɗin, “Banci komaiba, warin asibitinne banaso nidai”.
“Jawaad yaya dai?”. Ummah ƙarama ta faɗa kafin ya samu damar sake
tambayar bily.

Da sauri naja baya daga jikinsa dan na manta bafa mu kaɗai bane, bango na
dafe saboda jikina babu ƙarfi. Ban iya fahimtar amsar daya bataba dan hankalina
baya a garesu, tadai riƙe hannuna ta kamani muka fita sunata jeramin sannu.

Jay da duk damuwa ta sake lulluɓesa ya fita domin son ganin Doctor dan yazo
ya duba Bilkisun ko akwai wata matsala data sakata aman ne.
A ƙofar ɗakin sukaci karo da Dr Bello da Nurse ɗin dake tare da bilyn, da
alama itace taje tai kiransa. Fuskar Dr Bello washe da murmushi ya miƙama Jay
hannu, “Dadyn baby ai bansan ka shigoba ma”. Duk da Jay bai fahimci sunan da yay
kiransa da shiba sai yaɗan saki fuska kaɗan amma ba murmushi yayi ba, yadai
sassauta ta daga cinkushen da take. Doctor bai gajiyaba ya sake faɗin, “Dama sister
ce ke sanarmin madam na amai, wannan babyn da alama soja ne, dan nakula zai wajiga
madam da yawa tun yana ɗan ficit”. Yanzunkam dai sosai Jay ya kallesa da alamar
tambaya, sai dai ya gaza cemasa komai. Lura da hakan da Dr Bello yayne ya sakashi
yin murmushi suka ƙarasa shiga ɗakin da Bily take, inda su Umm-Anum suka zagayeta
sunata jera mata sannu, kanta na'akan cinyar Ummah babba.
Sai da ya gaisa da su sannan yayma bilyn sannu, kanta taɗan ɗaga masa kawai
alamar amsawa, ya sake kallonta da murmushi ganin tanata faman rufe hannci, juyawa
yay ya sake kallon Jay dake tsaye hannayensa duka a aljihu shima yana kallon bilyn.
“Congratulations dear Friend, madam na ɗauke da babien mu ɗan sati shida. Ma'ana
tana ɗauke da ciki ɗan wata ɗaya da sati biyu”.
Babu shiri Bily ta janye hannunta daga saman hanci tana waro idanu waje,
ganin duk yanda suka zuba mata ido suna murmushi yasa taji kunya, saurin juya baya
tayi taja gyalen Ummah babba ta rufe fuskarta ƙirjinta na wata irin bugawa da
sauri-sauri.
Su Ummah kam fuskokinsu washe da murmushi sunata jerama UBANGIJI godiya da
kirari, gaba ɗaya sai damuwar da suka yini da ita ta ɓace ɓat. Ubangayya da tunda
aka fara cakwakiyar nan babu mai cewa yaga haƙorinsa a waje a take ya saki wani
lallausan murmushi yana mai lumshe idanu, duk wata damuwarsa sai yaji ta gudu,
farin ciki ya mamaye gurbinta. Dariyar su Ummah ce ta sakashi buɗe lumsassun
idanunsa dake jajur, yay murmushi a karo na biyu yana girgiza kansa ganin iya
shegen da Anuwar keyi shi da Anum da Nabeelah. Ya dage sai rawa yake yana waƙar
larabawa shi a dole yayi ɗa ko ƴa, yayinda Anum da Nabeelah ke tayashi.
Cikin dariya Ummah ƙarama tace, “Yarona dama haka kake da iya shege ina
ganinka wani ustazu?”. Umm-Anum dake murmushi tana kallon Bily da duk abin nan da
ake taƙi kallon kowa tace, “Kaɗanma kika gani indai Anuwar ne, dama can Ustaz ɗin
da babu Ustazai ne”. Dariya su Ummah da Batool da Dr Bello suka sanya, Jay dai
murmushine har yanzu a saman fuskarsa, kunyar iyayensa ta sakashi dakewa abinsa
yanata dai kallon bilyn ta ƙasan ido.
Aunty Batool tace, “Lallai ta maganar Doctor babyn nan namu soja ne, inba soja
ba wannan gumurzu da akashawo amma ko gezau baiyiba saima nuna kansa da yayi wa
duniya”. Sosai nanma suka sanya dariya, Dr Bello yace, “Gaskiyarki Sister kam,
ALLAH dai ya inganta, kema saiki daure kiyi aure ki samo mana namu”. Duk kallon
Doctor sukai banda Jay da Bilkisu dake ɓoye, Batool ta zuba masa harara. Shiko
murmushi yayi abinsa yana sosa ƙeya waishi yaji kunyar su Ummah. Cike da tsokana
Anuwar yace, “Su Aunty Batool kodai-kodai gidan Doctor zamu ɓulla ne?”. Duka takai
masa ya kauce yana dariya, Doctor Bello ya kama hannun Anuwar yana faɗin, “Yauwa
ɗan ƙanina tayani yaɗa manufa”. Yay maganar suna ficewa daga ɗakin.
“A to mukam wannan indai na ƙwaraine ai bashi zamuyi Batool”. Umm-Anum ta
faɗa tana kallon Batool ɗin. Ƙasa tai da kanta batace komaiba. Ummah ƙarama tace,
“Yayah wlhy bansan ko Dr Bello da wata matsalaba, mutum kirkine ɗan manyan mutane,
sai dai babansane ɗan rigima, amma shima bawai ta ashsha ba”. “Ato Alhmdllh, bara
nazo na fara shirin aurar da ɗiya kenan”. Murna Nabeelah da Anum suka fara, ita dai
Ummah babba batace komaiba, hakama Jay uffan baice ba, yayi kamarma baya a ɗakinne,
idonsa gaba ɗaya yana akan motsin matarsa.

★★★★★★★

Koda suka baro ɗakin da bily take da sallama daga Doctor gaba ɗaya
sai suka nufi ɗakin da aka kai Alhaji babba, daga shi sai baba maigadi a ɗakin,
jikin Umm-Anum har rawa yake, sai da Batool ta riƙeta, cike da sassarfa ta ƙarasa
gaban gadon da Alhaji babba ke a ƙwance an saka masa na'urar taimakon numfashi,
sosai jikinta ke ɓari, ta durƙushe ƙasa tana kamo hannunta cikin nasa da fashewa da
kuka tana kiran sunansa. “Baba kaine haka? ka tashi baba kaga BILKEESUN ka, nadawo
gareku baba, baba ka buɗe idanunka ka kalleni dan ALLAH kozanji sassauci babana
farin cikina” ta ƙare maganar da ɗaura kanta a gefen hannunsa tana kuka mai tsuma
rai. Suma su Ummah hawayen sukeyi har Bily, Batool da Nabeelah da Anum. Anuwar ma
hannu ya saka ya ɗauke nasa ƙananun hawayen tare da ƙarasawa ya durƙusa ta ɗayen
gefen kakan nasa daya fara gani a yau karan farko na rayuwarsa, Anum tazo kusa
dashi ta tsugunna itama tana ɗaura hannunta akan na Anuwar dake riƙe dana Alhaji
babba. Jawaad dai yana kallonsu, sai dai bazaka taɓa fahimtar yanayinsa ba, kamilar
fuskarsa ta shanye komai.
A hakanli Alhaji babba yaɗan motsa hannunsa dake riƙe a cikin na Umm-Anum,
saurin ɗagowa tai tana kallon hannun, ya sake motsashi a karo na biyu tare da
kansa. tsitt ɗakin yay duk suka zuba masa ido. Sake motsawa yay fiye dana farko,
sai kuma ya buɗe idanunsa a hankali ya sake maidawa ya rufe saboda nauyin da sukai
masa, sake buɗewar yayi a karo na biyu, dishi-dishi ya fara hango Jawaad dake tsaye
daga can ƙofar ɗakin yana facing nashi, ya ɗan kafesa da kallo tamkar dai yanason
gano wanene?. takowa Jay yay a hankali zuwa gaban gadon, ya tsaya kusa da Umm-Anum
tare da ɗan ranƙwafawa yanama Alhaji babba murmushi, hannu ya saka da kansa ya cire
masa na'urar da aka saka masa. cikin magana a hankali yace, “Tsoho mairan ƙarfe!”.
Karan farko Alhaji babba yay wani ɗan murmushi kaɗan da sake motsa hannunsa
sai ya jisu duka biyu an riƙe. “Babah!” Umm-Anum ta kira sunansa cikin sanyin
murya. Cikin wata irin faɗuwar gaba Alhaji babba ya juya saitin inda yaji muryar da
bazai taɓa mantawaba a rayuwarsa, to kodai mafarki yakeyine har yanzun? Ya ayyana a
ransa yana ware idanu akan Umm-Anum dake kallonsa tana murmushi da hawaye.
Ya mata kallon kusan minti ɗaya kafin ya sake juyowa ya kalli Jay, sai kuma
ya kalli Anuwar da Anum, ya sake maidawa ya kalli Ummah ƙarama da babba da Batool,
Bilkisu da Nabeelah, cike da ƙarfin hali ya yunƙura zai tashi zaune dan ba'a
ƙaramin ruɗani ya tsinci kansaba. Saurin riƙesa Jay yayi yana girgiza masa kai.
Alhaji babba ya kalesa cikin muryar dake nuna bashi da lafiya yace, “Jawaad
mafarkin dana sabane ko? Yo inba mafarkiba a ina nikam zanga mahaifiyarka ido da
ido irin haka? Dan ALLAH kaga karka tadani a barcin nan barni nayi tayi ko ALLAH
zaisa itama Rahmah da Maryam da Amina da Adamu zasuzo gareni duk mu haɗu anan”.
“Baba ba mafarki ka ke ba, Bilkisun ka ce a gaske gabanka, nice na dawo
gareku, ni ce ban mutuba baba”. Umm-Anum ta faɗa tana rushewa da kuka. Ai yanzunkam
babuma wanda yaga sanda Alhaji babba ya tashi dingangan zaune yana riƙo hannun Umm-
Anum cikin nasa duka, jikinsa sai rawa yakeyi, hannunsa ya ɗaura saman idonsa ya
murza, ya kai kuma kan fuskarta ya shafa. Tabbas ba mafarki yakeba Bilkisun sa ce a
gabansa, bilkisun daya rasa kusan shekaru ashirin dashida, bilkisun daya fidda rai
da gani a wannan duniyar dukda yana tsananin ƙwaɗayin hakan. “Bilkisu dama kina
raye?”. ya faɗa da tsananin rawar murya.
“Ina raye baba, ganima ALLAH ya ƙaddara sake haɗuwarmu, na godema
UBANGIJINA daya saka ka kasance mai tsahon ran da zan dawo na tadda, da ace na dawo
baka raye bazan taɓa daina yima mutanen nan munanan addu'oi ba har randa numfashina
zai yanke”. Fashewa Alhaji babba yay da kuka, ya kamo kan Umm-Anum ya ɗaura saman
cinyarsa ya rungume yana sake fashewa da kuka mai ban tausayi da tsuma rai.

Da ƙyar Jay da Doctor suka samu damar lallashin Umm-Anum da Alhaji


babba, harma dasu Ummah dasu Bilkisu, sai dai fa Alhaji babba ya tubure akan ya
warke a sallamesa ya tafi gida, anyi lallashin duniya yace sam baisan wannanba wlhy
shifa bazai kwana a asibitin nanba koma mi za'ayi.
Ganin ya rikice musu harda hawaye Jay yace Doctor ya basu sallama kawai, sai
su sami likitan dazai dinga zuwa gida yana dubashi babu damuwa. badan Doctor yasoba
ya basu sallama.
Jay da Anuwar ne suka kama Alhaji babba aka kaisa har mota, yayinda itama
Ummah ƙarama ke riƙe da Bilkisu da keta dauriya da ƙarfafa jikinta dukda batajin
daɗinsa sam, sai dai ƙasan ranta wani irin farin ciki takeyi da barin asibitin da
zasuyi. Motar ta musu kaɗan, dan haka suka shiga ta Aliyu da suka iso asibitin babu
jimawa suma dan an ƙaro jami'an tsaro cikin asibitin saboda mutane dake neman kawo
ruɗani, acewarsu sunason suga gawawwakin da waɗanda aka samo da rai ko akwai ƴan
uwansu a cikinsu.
Jay bai bisuba, cikin asibitin ya sake komawa inda Qaseem da Salman ke tare da
Mom wadda ta farfaɗo amma sun mata allurar barci mai ƙarfi dan jininta ya hau
sosai, Doctor ma yace badan ALLAH ya taƙaita mata wahalaba irin wannan faɗuwar da
tayi zai iya sakawa ta kamu da paralysis. Sai da suka ɗanyi magana da Qaseem da shi
kansa idan da za'a bashi gadon an taimakesa sannan Jay ya fito. Daya fito ɗinma
wajen su Jabeer ya tsaya sukai magana sannan ya amshi key ɗin mashin ɗin ɗaya daga
cikin jami'insu yabi bayan su Alhaji Babba.

_____________________
Dr Tayyeb Hospital
_________________________

Shahudah dai suma tai a wajen, sai da cikin ƴan matan family ɗin
wata tai ƙarfin halin shafa mata ruwa sannan ta kawo numfashi, hakama matar Uncle
Nasir ita sai dama aka bata gado, ƴaƴansa nata kuka maiban tausayi da saka zukatan
mai kallonsu rauni. Kosu Uncle Sulaiman sai da suka share hawaye dan tsananin
tashin hankali. A yanzun kam sun fahimci zaman asibitin sam bazai yuwu a garesuba,
dan haka suka tattara inasu-inasu suka nufi gida, dan anma hana kowa shiga wajen
Mama Badiyya dama, ba'ason ai mata wata hayaniya ko kaɗan.
Sun iso gida suka iske waɗanda suka bari anan cikin matsanancin tashin
hankali suma, ciki harda Mama Atika da tafi kowa shiga ruɗani ganin halin da babba
ɗanta yake a ciki da surukinta, tayi bala'in yin wujiga-wujiga da ita tamkar wata
taɓaɓɓiya, dan sai surutai take, fitsari kuwa ba'a magana, tayisa a zane sau babu
adadadi batare da tasan yanama zuba ba. Sai da ƴan asibiti suka isone suka fargar
da ita halin da take ciki.
Tabbas bayyana irin kalar ruɗanin da wannan ahali suke ciki ɓata lokacine,
sai dai na bama kowa gari ya ƙiyasta a ransa. Gashi an turo jami'an tsaro sun
zagaye sashen Uncle Nasir ɗin babu mai shiga kamar yanda akaima gidan Dad shima.

_______________________

Ba ahalinsu Jawaad ne kawai a cikin ruɗaniba, duk ahalin dake da


nasaba da waɗanan mutane yau hankalinsu baya tare da tunaninsu, anje kuma duk an
zagaye gidajensu da jami'an tsaron sintiri, babu mai shiga babu mai fita. Waɗanda
suka tsinci kansu a wani hali kuwa sai dai likitoci ake tura musu cikin gidajen
suna dubasu.
Sosai ƙasarma gaba ɗaya take a hargitse bawai jihar da abin ya faru kawaiba,
idan ka buɗe tv da redio babu wani magana saita wannan tashin hankali daya faru.
Masu jaje nayi masu ALLAH wadai nayi, waɗanda suka jima suna zarginsu kuwa suka
shiga maimaita ai dama a rina. Ƴan uwansu masu mu'amula dasu da suka rasa wasu
mutanensu da suka rasu ta wasu hanyoyin tuni suka fara yayibo hujjoji da zarge-
zarge suna ɗora musu (Kusan ɗan Adam kamar jira yake🤦🏻, abinda ma ba haka yakeba
sai ya maidasa hakan🙄🚶🏻😏).
Masu ƙara gishi da magi a teburan masu shayi da gidajen suna da biki
kuwa harda faɗin wai tukunya tukunya aka ringa fiddowa na farfesun mutane da
gasashshen nama daga gidan😂, jini kuwa drom-drom sai kace wani mangyaɗa🤣. Aifa nayi
ya samu a bakunan ƴan bani na iya, kowa burinsa ace shine ya fara kawo labarin🤒.

___________________________________
ƘARAMAR HUKUMAR GWANSU
_________________________________

Gidane madaidaici mai ƙyau, dan kuwa ko'ina na cikinsa mulmule yake
da suminti, sannan an shafesa da fenti ruwan madara da ganye mai haske, ƙal yake da
shara sai ƙyalli fasassun tiles ɗin da aka saka a tsakar gidan yake da ɗaukar ido.
Yarone da zai iya kaiwa shekara uku ke barci kwance a ƙaramar katifa ta yara a
tsakar gidan babu riga jikinsa saboda yanayin zafi, sai wani da bazai wuce shekara
shida ba tsaye jikin ƙofar fita daga soron gidan yanata kumburi alamar wani abun
akai masa.
Matashiyar mace da bazata gaza shekaru ashirin da huku ba ta fito daga
matsakaicin kicin ɗin dake tsakar gidan ɗauke da tukunya alamar abinci ta kwashe,
bayanta goye da jaririya ƙyaƙyƙyawa tanata barcinta hankali kwance. Tunkuyar ta
ajiye inda alamu suka nuna wajen wanke-wanke ne tana mai harar yaron dake laɓe
jikin ƙofar. “Wlhy kabari na kamaka a gidannan Fharhan sai na maka dukan da ko
ubanka ba ganeka zaiyiba, karkazo ka ɗauki abincin su Innata ka kakai musu tunda ni
na aikeka gidan su Musbahun har aka dakeka”.
Sake tura baki yayi gaba yana share ƴar ƙwallarsa, “To Umma ni kije ki amsomin
ball ɗina, inaba hakaba ni bazankai abincinba kuma”. “Karka kai dan ALLAH kaga
yanda zan kirɓa namanka a gidan nan mara mutunci..........”
“Yaya?! yaya?! dai”. Da gudu yaron da aka kira da Fharhan ya nufi mai
maganar daya shigo yana faɗin, “Oyoyo Abbanmu”. Buɗe masa hannayensa yay ya shige
jikinsa, ya ɗagashi sama yana dariya da faɗin, “Babana duk faɗan da nai maka akan
yima Umma laifi bakajiba ko?”. Yaron ya ɓata fuska yana kallon Umman tasa dake
tsaye tanama mijin nata kallon mamaki, yace mata wannan satin bazaizo weekend ba,
amma kuma sai gashi a bazata da yamma liƙis. “Abbamu buguna zatai fa”. “Laifi
kamata ai ko?”. Girgiza kai yaron yayi, kafin yayi magana ta matso inda suke ta
ɗauka leda viva daya ajiye ƙasa lokacin da zai ɗauki Fharhan. “Sannu da zuwa”.
Tafaɗa har yau da mamaki tattare da ita. Murmushi yay mata, yasa ɗayan hannunsa ya
shafa kan yarinyar dake goye a bayanta. “Mai gadon zinarina barci akeyi?”. “Ai
tunda naimata wanka ta ɓingire, irin wannan zuwan bazata haka”. Murmushi yayi
batare da ya bata amsaba ya ida shiga gidan yana faɗin, “Banga na hannun damar Inna
ba?”. “Gashi can yana barci”. Ta bashi amsa da nuna masa inda ɗayan yaron ke barci.
Sauke Fharhan yay ya kama hannunsa suka nufesa, saida ya shafa kan yaronsa sannan
ya zauna gefen tabarmar da aka ɗaura katifar. Itama ledar ta ajiye taje ta kawo
masa ruwan sha. Sai da ta ajiye sannan ta sake kallon Fharhan, “Kazo ka kaima su
Inna abinci karka bari na sake maimaita maka wlhy Fharhan ”. Baki ya tura zaiyi
magana Abbansa ya hararesa, “Kanason na ɓata maka rai ko?” da sauri yaron ya
girgiza masa kai, “Ɗauka abincin ka wuce, ka faɗama Inna muma muna nan zuwa gidan”.
Da mamaki ta kallesa, sai dai bata iya cewa komaiba har Fharhan ya ɗauka kular
abincin su inna ya fice daga gidan.
“Amma daga dawowarka kake.....” katseta yay da faɗin, “Firdausi babban
al'amarine ya kawoni gida, zo kiga abinda na gano”. Babu musu ta nufesa, ya ɗago
daga danna wayar da ya keyi ya miƙa mata wayar yana faɗin, “Ko zaki iya gane
wannan?”. Da saurinta ta amshi wayar, hoton da taci karo da shi ta tsatstsare da
idanu, kusan mintuna uku tana kallonsa cike da nazari ko ƙyaftawa batayi, da sauri
ta zabura tana zaro idanu waje da ɗora hannunta saman baki, “Abban Fharhan wlhy
kamar Bilkisu fa”. “Kama ko itace?” “Wlhy bana ko tantama Bilkisu ce wannan, ko
wane irin canjawa zatayi a rayuwa bazan gaza ganeta ba, dan ALLAH ina ka samo mana
Bilkisu? Bayan shekarun da muka ɗauka cikin nemanta babu ko labarinta”. Tai maganar
tana zama kusa da shi cike da zumuɗi. “Nima yau na ganta Firdausi, a media naci
karo da hoton yana yawo a dalilin abinda ya faru, tana cikin tawagar jami'an tsaron
da suka nuna bajinta wajen kamo miyagun mutanen nan yan cultism, kinganta anan tare
da mijinta ranar aurensu, shima jami'in tsarone”. “A...ab... Abban Fharhan wai kana
nufin Bilkisun ce ta zama jami'ar tsaro kuma tai aure?”. “Wlhy kuwa haka na gani,
auren nasu bai wuce wata huɗu ba akace, amma watanta kusan biyu kenan da tarewa,
shiyyasa nake faɗa miki ki ringa ɗan shiga yanar gizon nan amma kinƙi, koba komai
zaki san abubuwa da yawa da duniya ke ciki, yanzu hakama bakisan abinda ke faruwa a
ƙasarba yau ɗin?”. “A'a na sani, dan ɗazun su Luba sunzomin barka kasan sanda na
haihu tana Niger, to shine suke labarin, hakan yasa na buɗe redio anan naji komai”.
Murmushi yayi ya sake miƙa mata wayarsa dake ɗauke da hoton Bilkisu da Jawaad a
ranar dinner ɗinsu lokacin da suke wasan bindiga. Sosai Firdausi ta saku wani ihun
farin ciki, ta rungume mijinta tana mai fashewa da kuka, “Wlhy itace Abban Fharhan,
ashe zan sake ganin bily a duniyarnan. Abban Fharhan dan ALLAH muje gidan baba,
wlhy nasan zaifi kowa farin ciki a yau, bashi da wani buri daya wuce gamo da
Bilkisu, wannan shine burinsa, da fatansa a kullum”.
Babu musu ya amince, ta ɗakko mayafi da kayan da za'a sakama Abbas dake
barci, shibe ya amsa ya saka masa, ita kuma ta shiga da kayansa ɗaki ta kulle
ƙofar, ta kullo kicin da ɗakin da suke saka kayan abinci da tarkace, ɗaukar Abbas
daketa barcinsa yay a kafaɗa suka fice a gidan, saida ta kulle sannan suka ɗauki
hanyar gidan Baba a ƙafa da yake babu nisa sosai.

Sun iske Fharhan nata bama inna labarin abinda akai masa a gidan su
musbahu abokinsa kuma maƙwaftansu, tanata lallashinsa ita kuma. Sai dai shigowar su
firdausi yasata maida hankali a kansu, Abban Fharhan ya kwantar da Abbas a gefen
tabarmar da suke sannan suka zauna suna gaisheta.
“Wai dama kazo garin Muktar?”. “A'a inna, zuwana kenan”. “To, shine kuma
kuka taho nan? Lafiya dai ko?”. “Alhmdllh inna sai alkairi”. “To masha ALLAH, ai
haka akeson ji”.
Kamar yanda ya nunama firdausi hoto haka ya nunama Inna itama, kwatankwacin
ruɗanin da Firdausi ta shiga innama haka ta tsinci kanta a ciki, da sauri ta shiga
ƙwalama Baba dake ɗakinsa kira. Fitowa yay da ɗan hanzari dan dama bai jima da
shigaba wanka ya fito yake kimtsawa dan dawowarsa kenan daga kasuwar ƙauye da yake
zuwa yanzun yana sana'ar kayan miyarsa.
Shikam ai ganin Bilkisu sai ya rikice fiye da zatoma, musamman dayaga
hotunan waɗanda su Bilkisun suka kama, ya share ƙwallar data taru masa a cikin ido
yana faɗin, “ALLAH mai iko, ALLAH mai hikima buwayi gagara misali. Muktar kayi
haƙuri, dolene zuwa gobe mu koma birni tare da kai kuwa”.
“Baba har dani dan ALLAH”. Firdausi ta faɗa tana share ƙwalla. Inna tace,
“Wlhy nima kam ba'a barina baya, dolene naje ganin ɗiyata”. Itama muryarta da rauni
a ciki tai maganar.
A take babu wani ɓata lokaci suka yanke hukuncin tafiya birni gobe idan ALLAH
ya kaimu koda kuwa idan sunje Alhaji lado da Jazuga zasu salwantar da rayuwar tasu
kamar yanda suka faɗa musu a baya.

____________________________

Tunda muka baro asibitin saina samu ƴar nutsuwa, dan yanzu banajin
aman sam, sai dai kawai rashin ƙwarin jiki da damuwar dake cike taf da ƙirjina
harma da ruɗani, ganin duk abinda ya faru nake tamkar a mafarki zan farka zuwa
anjima naji ba hakaba.
Mun yada zango a gidan Alhaji babba, inda muka iskesa zagaye da jami'an
tsaro har yanzun, dan ba'a basu izinin barin gidanba. Aliyu na ajiyemu ya juya da
cewar zaije ya nemo mana abincin da zamuci.
Kasancewar magriba tayi ba zama mukayiba, da yake bayan ɗakin Alhaji
babba akwai isasun ɗakuna a gidan sai kowa ya samu wajen shiga a wadace, ni dai
sakani Ummah ƙarama tayi nai wanka da ruwa mai ɗumi, kamar yanda Anuwar ya
taimakama Alhaji babba shima yay wanka dan ya ƙara samun ƙwarin jikinsa.
Bani da wasu kaya a gidan dan haka na rasa yaya zanyi, saina maida na
jikina na fito, salloli ake bina tun daga zuhur har mgriba da akeyi yanzun, gashi
kayan jikina bana tunaninma zasuyi salla.
Ina cikin wannan hasashen Anum ta shigo ɗauke da leda, ajiyewa tai a saman
gadon tana murmushi, “Ga kaya yayanmu ya kawo miki”. Kallonta nai da sauri, mamaki
sosai a fuskata, “Yazo gidan ne?”. Kanta ta jinjina min, “Yazo yanzun nan shi da
abokan nan nasa na wajen bikinku, amma sun fita massallaci, Ummah tace ki saka kiyi
salla kizo kici abinci”. Kai kawai na iya jinjina mata, na miƙe nayi duk yanda
tace, ina saka kaya ina kallon cikina dake a shafe tamkar babu kayan ciki ma, amma
a haka ake maganar akwai ɗan mutum a ciki. Bansan murmushi ya suɓuce minba, na
ɗaura hannuna akan cikin naɗan shafa.

Lokacin dana kammala rama sallolin dake kaina anata kiran sallar
isha'i, dan haka na gabatar itama. ban fitaba, na kwanta a saman gadon ƙafafuna a
ƙasa fuskata na kallon silin ɗin ɗakin, idanuna a lumshe suke, yayinda hannayena
duka buyu ke cikin rigata ina shafa cikina, ni kaɗai nasan mi nakeji a lokacin, ina
farin cikin samun ƙaruwar da ALLAH kaɗai ke wadata bayinsa da ita, gefe kuma inajin
ɗacin tsintar wanda zuciyata take girmama da daratawa bayan iyayen firdausi fiye da
kowa a duniya cikin mummunan hali. Tabbas da ace wanine yazomin da wannan labarin
akan Dad bazan taɓa gaskatashiba koda kuwa ace Mijina ne, sai dai kash, nice da
idanuna na gansa, da kunnuwana na jisa, ba'a cikin mafarkiba ko magagin barci, ba'a
labari daga bakin wani ba. Haɗiye ɗacin daya tokare maƙoshina nayi daƙyar ina buɗe
lumsassun idanuna jin ƙamshin turaren dana fi ƙauna fiye da kowanne a duniya a
yanzun.
Jay daya jima da shigowa yana ƙare mata kallo harya gaji ya ƙaraso inda
take ya durƙusa a bakin gadon. A hankali ya kwantar da kansa saman cikinta bayan ya
janye hanayenta, ya lumshe idanunsa dake cike da nauyin damuwa dana gajiya.
“Kin bayyana a ranar da tarihi bazai taɓa mantawa da itaba Little
Beejay, rana mai cike da ruɗani kala-kala da ban al'ajab, ina roƙon ALLAH ya raya
mana ke cikin aminci, ALLAH yasa ki zama hasken idaniyarmu da al'ummar MANZON ALLAH
(S.A.W) baki ɗaya, kizama madubi mai haska addinin musulinci a kowace irin nahiya,
kizama jaruma irin Mamanki.....”
Murmushi ya suɓucemin babu shiri saboda jin sambatun da yakeyi, hannuna
nakai saman kansa na fara shafawa a hankali ina sake faɗaɗa murmushi na, shi kaɗai
ya ragemin yanzu a duniya sai gudan jininmu dake a cikin ciki, muryata da ɗan rawa
nace, “Nidai insha ALLAH Little Jay ne”.
“Tab, yarinya ban yardaba”. Ya faɗa yana ɗaga kansa da sauri da hawowa saman
gadon ya zauna, yunƙurawa nai zan tashi ya riƙeni, maidoni yay jikinsa ya kwantar
dani saman ƙirjinsa. Sai da na shaƙi ƙamshinsa na lumshe idanu sannan na buɗesu a
kan fuskarsa ma'abociya kamala da kamewa ina murmushi. Shima murmushi yay min kaɗan
yana kafeni da jajayen idanunsa, ya duƙo da fuskarsa dai-dai tawa ya sumbaci
goshina da laɓɓana. Sake lumshe idanu nayi da kai hannuna saman kumatunsa ina
shafawa a hankali har zuwa bayan kunnensa. “Thanks you Sweet Love” na faɗa a can
ƙasan maƙoshi batare dana san shauƙi ya kwasheniba nai suɓutar bakin. Idanu ya ɗan
waro alamar mamaki, cikin sarƙewar halshe yace, “Mi ki ka ce?!”. Cusa kaina nai a
ƙirjinsa wani masifan kunya na lulluɓeni, ya ɗago fuskata da sauri yana faɗin,
“Please Miemaa sake faɗa naji”. Ƙara ɓoye fuskar nayi da ƙyau. “Pleaseeeeeeee”. Ya
faɗa a wani irin yanayin daya saka tsigar jikina tashi na sake ƙanƙamesa. “Sweet
Love” na sake faɗa a hankali. “Oh my God, wannan rana ta musamman ce a gareni” ya
faɗa da sake ƙanƙameni yay baya muka faɗa saman gadon ina jikinsa. “Lilly kinzo da
tarin sauyi” ya sake faɗa yana shafa cikina da lalubar bakina ya haɗe da nasa.
Karan farko a rayuwata dana fara maida masa murtanin abinda ya kemin kaina
tsaye babu wani kunya kojin ɗar, a take ya haukacemin jikinsa sai tsuma yakeyi,
munyi nisan kiwo sosai dan da gaske neman kaiwa inda yafi ƙauna yake nemanyi, ALLAH
ya ceceni a bazata akai knocking ƙofar ɗakin.
Nice na fara ƙoƙarin zare jikina daga garesa a wale, amma duk da haka
ƙoƙarin maidoni ya keyi, na sake ja baya sosai ina sauke tagwayen numfashi da
sauri-sauri da gyara rigata, sake knocking ɗin akayi, sai dai narasa ta yanda zan
amsa, dan inhar nayi magana sai angane halin da nake a ciki, gashi kuma bansan
wanene ba. Juyawa nai na kallesa, yana kwance a yanda na barsa idanunsa a rumtse
yana sauke nasa numfashin shima, nasan tabbas yanajin buga ƙofar da akeyi, amma ya
share abinsa hankali kwance. Yunƙurawa nai zan miƙe naje na buɗe yay saurin riƙo
hannuna, sake juyawa nai na kallesa, yanzu kam ya tashi zaune, ya zaunar dani saman
cinyarsa sannan yay gyaran murya batare da ya kalleniba. Daga wajen Nabeelah tace,
“Yayanmu ance kufito aci abinci”. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, shikuma yace,
“Uhhum”. Daga haka bai sake maganaba, Nabeelah ma haka saita bar wajen kasancewar
tasan halin kayanta.
Kallon juna mukayi, yaɗan kaɗamin idanunsa da suka ƙanƙance yana cika bakinsa
da iska ya furzar. Bance komaiba na maida kaina na duƙar. Shima bai sake cewarba ya
ɗagani daga cinyar tasa bayan ya shafa cikina. Matsawa nayi gefe ganin na samu ya
sakeni, batare da yace dani komaiba ya nufi bayi.
Ƙarar ruwa kawai na jiyo alamar wankama ya keyi kenan, na ɗan dafe kaina ina
jinjina kaina, tunanin kar aga bamu fitoba ai zaton wani abunne ya sakani saka
hijjab ɗina na fita ni, idan ya fito ya iskeni a can.

Tunda na fito suketa jeramin sannu, Umm-Anum ta kamo hannuna ta zaunar a


kusa da ita. Ɗan kallon Alhaji babba dake gefenta nayi na gaishesa, ya amsamin da
kulawa tare da sakamin albarka da doguwar addu'a akan namijin ƙoƙarin da muka nuna
a jejin can dan a cewarsa yanzu ya ga komai a labaran dare da suke sake maimaitawa.
Kasa cewa komai nayi nidai, na juya na gaida Umm-Anum itama dasu Ummah babba, sai
Yaya Anuwar da Aunty Batool da Aunty Haneefa, Aunty Saudah da sukazo suma babu
jimawa, Anum da Nabeelah kuma na basu hannu mukai musabaha.
Babu wanda ya tambayeni boss har aka fara zuba abinci a babban faranti kamar
yanda Alhaji babba ya buƙata, muna shirin fara ci sai gashi ya fito sanye da kayan
daya haɗo cikin nawa da Anum ta kaimin ɗazun. Ɗan kallonsa nayi ya zubamin harara,
na ɗauke kaina ina haɗiye murmushin dake neman suɓucemin. Zama yay tsakkiyar Anuwar
da Ummah ƙarama, shima yay bismilla kamar kowa ya saka hannu.

Muna gab da kammala cin abincin wayarsa ta shiga vibration, da farko


kalla yay zai ɗauke kansa, sai kuma ya ɗauka wayar da ɗan zafin nama yana ja baya
daga gaban abincin, babu wanda yasan mi aka faɗa masa ya mike da ɗan hanzarinsa
yana faɗin, “Zanje office, na manta shaf munada meeting wlhy”.
“Meeting a daren nan Muhammad?”. Alhaji babba ya faɗa yana kallonsa.
“To ya zamuyi baba? Akan case ɗin mutanen nanne, kasan manyan ƙasar sunyi
caa akan batun, gefe kuma al'ummar ƙasar suma da zafi-zafi suke buƙatar suga
hukuncin da za'a yanke, gashi a kuma a dalilin faruwar al'amarin allura na neman
tono garma”.
Murmushi Alhaji babba yayi yana faɗin, “Garmuna ma, dan ta wuce guda ɗaya.
ALLAH ya bada nasarar ƙulla alkairi to, amma shiga ɗaki ka ɗakko magani kasha,
wannan kan naka daga gani ciwo yakeyi”.
Baiyi musu ba ya nufi ɗakin Alhaji babban ya ɗakko maganin, ruwa ya ɗauka a
inda muke yasha sannan yay mana sallama ya fice. Muka rakashi da addu'a mukuma.
Bayan kammala cin abincin zaman hira akai duk da gajiyar dake tattare da
kowa, Umm-Anum ta fara bamu labarin rayuwar da ta tsinci kanta bayan barinta gida.
Ma'ana sanda hankalinta ya dawo jikinta ta ganta a ƙasa mai tsarki, sai dai kuma ta
gagara tuna komai daya danganci rayuwarta ta baya, da inda ta fito, da ahalinta.
Kuka kowa ya keyi hawaye shaɓe-shaɓe, duk da nariga nasan duk wannan tunda mu
an faɗa mana sanda mukaje saudia nima saida nai kukan. Ummah babba ma ta labarta
mata yanda abubuwa suka faru bayan barinta gida. irin neman da akaita mata da
tashin hankalin da Mama maryam da Alhaji babba da Rahmah dasu kansu suka shiga,
harma da ƴan uwan mahaifin boss. Rasuwar Mama Maryam da Auran Rahma.
Sai dai bayan wasu shekaru kuma sai kowa ya haƙura aka cigaba da binta
da addu'a dansu tunaninsu koma ta rasune. Itama taci kuka, muma muka tayata.
Har kusan ƙarfe biyu na dare bamu kwanta ba. dan da ƙyar Anuwar dasu Aunty
Haneefa suka lallaɓa Alhaji babba ya yarda zai kwanta ya huta daboda jikinsa, gashi
Doctor yace ya samu isashen barci.
Muma duk tashi mukai mukaje muka kwanta kowa zuciya babu daɗi. cikin amincin
ALLAH ni dai inama kwanciya barci mai nauyi yay awan gaba dani.

___________________________
Tafida family house
______________________

Lokacin da labari ya isa kunnen mama Atika akan ganin Umm-Anum sai
tahau surutai tamkar wadda ta zare, tun su Uncle Uwaisu na ɗaukal al'amarin
matsayin ruɗani harya koma basu tsoro. Dan sosai neman fita take daga hayyacinta.
Sake ruguntsumewa gidan yayi da tashin hankali, babu mai iya fahimtar yaren
wani. Batun yunwa kuwa ai an manta da sunanta a wannan gida yau, dolefa aka
danƙarama Mama Atika allurar barci ta ɓingire, har dare basa tare da nutsuwarsu,
barema da Qaseem suka iso gidan Mom da itama take a jangwaɓe, ta tada hankalintane
akan a maidata gida batason kwanan asibitin shiyyasa Qaseem ya kawota nan dan can
gidan zamansa tashin hankali kawai zai ƙara mata.
Itama dai Mom maganar dawowar Umm-Anum ta nema maidata ruwa, dan ruɗani ta
sake komawa ciki fiye da tunani, al'amarin sai ya sake bama su Uncle Sulaiman da
basu san komaiba mamaki, a ganinsu dawowar Bilkisu cikin ƙoshin lafiya abin ayi
murnane bawai tashin hankaliba, amma yarasa miyasa abin ke neman zama wani iri ga
wasu daga cikin ahalin nasu?. Bashi da mai bashi amsa, dan haka yay gum da bakinsa
kawai.

Saboda meeting ɗin da za'ayi shima dai Qaseem baro musu gidan yayi, sai da
ya fara zuwa gidansa ya watsa ruwa yay sallar isha'i sannan ya nufi station batare
da yay tunanin neman abinciba ma, dan shi sam a yinin yau bama abinciba ko ruwa sai
ƙishirwa ta kaisa maƙura yake nemansa yasha.

______________
STATION
____________

Ɗakin meeting ɗin yay tsitt, tsumayen shigiwar oga kwata-kwata


(Director General) daya iso garin a yammacin yau kawai sukeyi, kusan mintuna goma
sai gashi ya fito tare da wasu manyansu. Duk miƙewa sukai tsaye domin girmamawa a
garesu, suka ƙame tare da sara musu.
Shima murtani ya maida musu sannan ya zauna da nuna musu alamar suma su
zauna. Zama duk su Jay sukayi, bawai matsayin rank ɗin Jawaad ya kai ai zaman
wannan meeting ɗin da shi bane, kawai ƙwazo da suka nuna akan aikin ya kai shi ga
shiga wannan tawagar, dan gaba ɗaya gurin manyansune nacan ƙololuwa, sai su Sir
Ahmad dasu Qaseem, sai dai shi Qaseem ma gaba ɗaya yama kasa shigowa ɗakin meeting
ɗin, koda yazo sai ya maƙale a office ɗinsa ransa duk a dagule.
An buɗe taron da addu'a a ɓangarorin addinan biyu, kafin D.G ya nuna
kujerar data rage babu kowa cikin alamar son sanin wanda ya kamata ya zaunata. Sir
Ahmad ne yay masa bayanin Qaseem, an ɗaga waya za'a kirasa Jawaad ya miƙe tsaye
yana ɗaga hannu, damar magana Oga kwata-kwata ya bashi. “Sir ina neman alfarma”.
“Muna saurarrnka”. “Sir Qaseem yana cikin tsananin ruɗani, inaga zamansa tare damu
a wajen nan kamar zai ƙara tunzura tunaninsane ga wani abu daban, a ɗazun har
mummunan hukunci yaso yankema kansa. mizai hana ai masa alfarmar barinsa kawai”.
Tsit ɗakin yay alamar jiran amsa daga bakin Oga. Sai da yaja kusan mintuna
biyu kafin ya jinjina kansa yana gyara abin maganar gabansa. “Maganar Cpt
gaskiyane, kasancewar abinda zamu tattauna ɗin yanada nasaba da mahaifinsa akwai
damuwa, kuma shi jami'inmu ne daya taka rawar gani a wannan hukumar, ya cancanci
koda sau ɗayane a nuna masa hallacin hakan”. Duk kawuna suka jinjina, inda wasu
kuma a cikinsu hakan bai musu daɗi ba, dan su kam basuƙi ama kori Qaseem ɗinba daga
hukumar gaba ɗaya.

Jawaad ne ya fara bayani akan matakan da sukabi dangane da kamasu akan


dukanin bayanan sirri da suka samu, sai abubuwan da suka samo a gidan kama daga
mutane zuwa wasu abubuwan daban, sai kuma adadin su Dad da suka kasance su 22 idan
aka haɗa da shugabarsu data kasance mace. Sai ayyukansu da muƙaman wasunsu a cikin
siyasa da kasuwancin wasunsu.
Bayan ya kammala ya miƙa takardar da dukkan bayanan suke ciki ga Sir Ahmad,
wanda shi kuma ya miƙama D.G.
Amsa yay ya duba na tsahon wasu mintuna kafin ya ɗago yana kallonsu. “To
duk kunji bayanai ga jami'inmu, mi zaku iya cewa ku?”. Hannu wani ya ɗaga aka bashi
iznin magana.
“Sir ina ganin kawai mu miƙasu kotu mana, dan dukkanin bayanan da Jay ya
bayar an samu mutanen nan dasu a zahiri kuma duniya duk ta gani, a ganina bama
buƙatar wasu hujjoji kuma”.
Jin jina kai D.G ya shigayi, amma baice komaiba. Wani ya sake ɗaga hannu
shima aka bashi izini.
“Ni kuma Sir a ganina kamar kaisu kotu ba mafita bace, dan za'a iya amfani
da siyasa wajen kuɓutar dasu, ƴan ƙasa kuma su cigaba da kallonmu da laifin daba
namuba, kawai mu riƙesu a wajenmu har iyakar rayuwarsu”. Nanma dai kawuna kawai
suketa jinjinawa, wanima ya sake miƙewa shima ya faɗi ra'ayinsa. Haka sukaita faɗar
ra'ayinsu ta kowanne fanni, inda maganganun su duk suna akan turbar gaskiya da kuma
muhimmanci mai ƙarfi, shi dai Jay baice komaiba ganin duk manyansane keta magana,
saida kowa ya lafa sannan D.G ya kallesa da kulawa. “Bakace komaiba Jawaad, bayan
kuma kaine jami'in dayasan sirrin case ɗin nan fiye da kowa a cikinmu”.
Iska Jay ya zuƙa ya fesar, kansa a ƙasa yace, “Sir ai kune iyayenmu, zaku hango
abinda mu sam bamu iya hangosa ba, duk hukuncin da kuka yanke muma zai zama dai-dai
a garemu”.
“Hakane Jawaad, amma kuma da kuke ƙasanmu zaku iya bada shawara mai amfani da
zatafi wadda mu zamu kawo, domin ku a yanzu kuke ganiyar ƙuruciyarku da kaifin
tunani, sannan kuke shiga lungu da saƙo akan kowacce matsala, kune kuke ganin komai
dangane da al'umma, kune kuke fita farautar masu laifi cikin kowanne irin runtsi da
ƙalubale, mu muna office zaune, idan kun bada shawara ai bazai zama kuskureba”.
“Hakane Sir. To nidai idan har shawarata bata sauka a layiba ina ganin kaisu
kotun shine babbar mafita, amma kafin hakan ya dace a faɗaɗa bincike dangane da
masana'antunsu, da wajejen ayyukansu, akwai business da wasu a cikinsu ke gudanarwa
a cikin ƙasa da wajen ƙasa, mizai hana musan mi suke fitarwa da shigowa ne? Masu
ayyuka a gwamnati musan wane irin aiki suke gudanarwa a ofisoshinsu suma, daga haka
mu basu damar neman lauyoyi muma mu samu namu ƙwararren lauyan. Hujjata anan itace
dukansu waɗanan mutanen akwai zargin fyaɗe akansu wanda sam bama asan adadinsaba,
sun lalata yara da yawa da mummunan aikinsu, ciki harda ƴaƴan ƴan uwansu. Duk yanda
muke tunanin kare kanmu ga al'umma bazamu fitaba sai anyi komai akan
idanunsu.........”
“Tayaya za'ai komai akan idanunsu?, fili kakeso a ɗiba a tara duka talakawa
ai zaman kotun a gabansu komi?”. Wani ya faɗa aɗan fusace yana kallon Jay ɗin.
Murmushi Jawaad yay yana mai girgiza kansa, “Ba haka nake nufiba yallaɓai,
abinda yasa na kawo wannan maganar ta al'ummah saboda idanma muna gudun manyan
ƙasar zasubi ta ƙarƙashin ƙasa wajen saye alƙalan da zasu gudanar da wannan shari'a
muryoyin ƴan ƙasa zai daƙile hakan, sannan suma manyan zasu tsorata domin inba
waɗan nan jama'ar ai babu su, musaman idan mukai dubi da mafi rinjaye a cikinsu
wannan shine hawa na farko da sukayi. sunason komawa na biyu, bazasu so sunansu ya
ɓaci ba ai kodan mulkin da suka ɗanɗana suke kuma ƙulafuci da ƙwaɗayin komawa”.
Sir Ahmad dake murmushi ya kalli D.G, “Sir Jay yazo da maganar hankali,
dominfa wannan faɗan sam ba namu baneba, faɗane tsakanin al'ummar ƙasa da waɗanan
mutane, idan kuma har mukai tunanin shiga ciki wajen kare mutuncinsu to lallai zamu
fuskanci ƙalubale harma a ringa zargin muma da namu dalilin mara ƙyau a ƙasa, amma
idan min fidda komai ga al'umma muka kuma nuna musu suma sunada ƙarfin iko akai su
kansu alƙalan zasu shiga hankalinsu sosai, sannan ƴan siyasa bazasuyi wani tasiriba
wajen yaɗa farfagandar da suka saba. Kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, mun
kuma ƙarama hukumarmu kima da daraja a duniya baki ɗayama ba wanan ƙasar kawai ba”.
“Wannan gaskiyane wlhy” wani ya faɗa cike da goyon baya akan zancen su Jawaad
da Sir Ahmad.

D.G yace, “Okay, inaga to zamu tsaya a wannan matsayar, zuwa gobe sai mu
yanke hukuncin daya dace ko ya kukace?”.
Duk kawuna suka jinjina masa cike da gamsuwa. Daga haka taron ya tashi.
lokacin ƙarfe kusan uku na dare.
Jay baibar station ɗinba saida yaje office ɗin Qaseem ya fiddosa, shine
da kansa ya kaisa har gida sannan ya wuce gidan Alhaji babba, ya iske duk sunyi
barci, dan haka ya wuce ɗakin da yake tunanin Bilkisu na a ciki. Kwance ya sameta
ita kaɗai a saman gado ta cure waje ɗaya kamar maijin sanyi, yay ɗan murmushi da
cire kayansa sannan ya raɓa ta gefenta ya kwanta tare da turata cikin jikinsa. A
take ta shaƙi ƙamshinsa, sai ta gyara kwanciya kawai ta lafe tana mai sauke
tagwayen ajiyar zuciya kamar wata mage.
Murmushi ya sake saki mai sanyi, ya sumbaci kanta yana sauke tasa ajiyar
zuciyar a jere.

________________
WASHE GARI
____________________

Washe gari ta kama Lahadi, tunda safe Jay ya samu kira daga Gimbiya
Munaya akan takawa da kansa zai yoma su Abbu rakkiya gidan Alhaji babba.
Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama Jawaad ba, dan haka ya sanarma dasu Alhaji
babba halin da ake ciki, su kansu sunyi mamaki, to amma idan akai dubi da matsayin
su Abbun a wajen Takawa hakan ba komai bane face girmamawa.

★★★★★

A family house ɗin su Jawaad ma sun wayi gari da shirin zuwa gidan Alhaji
babba wajen Umm-Anum kamar yanda Uncle Sulaiman ya bada shawara shi da wasu a cikin
sauran ƴan uwa.

★★★★★

Ɓangaren su Firdausi ma tun da farar safiya suka kammala nasu shirin na


nufowa birni, sai dai su saɓanin ƴan masaurata da familyn Jay ne, su gidan Jawaad
sukai shirin zuwa tamkar yanda Muktar mijin Firdausi yay ƙoƙarin sama musu adireshi
a daran jiya ta dalilin wani abokinsa ɗan sanda.

★★★★★★

Maman Amina ma sun tashi ne da shirin nufar gidan Alhaji Babba kamar
yanda Jay ya kirasu ya sanar musu suje dan Mama Safara'u ta gana da Umm-
Anum.............✍

“Hummmmmmm!!!!! Wannan shine ake kira da ga wuri ga waina, to masu karatu, idanfa
bakusan gariba to ku saurari daka, dan yanzu zamusan ma'anar ƘWAI CIKIN ƘAYA. su
wanen ƘAYOYIN? su wanene ƘWAYAYEN?. Amsoshinku na'a page 61, saiku shirya kuma
domin yin gangamin tafiya gidan ALHAJI BABBA mu gani wace wainar za'a toya
shinnnnnnn?🚴🏼🚶🏻😢.

Masoya ZAFAFA 2021 fa sunata gagarumin shiri da yafi rukunin farko dana biyu da
suka kawo muku a baya, mun shirya shiri na musamman domin ƙayatar daku da
nishaɗantar daku da daɗaɗan labaranmu a wannan karonma, naga baƙwa motsawa😪, bayan
kuma gagarumin shirin da muketa shiri dominku🤗.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭.[2/17, 9:22 AM] HASNA: Bilyn Abdull 📚:


Page 61

...............Cike da mamaki matuƙa Aamilah ke kallon Shahudah dake zaune gaban


mirror'n ɗakin Mama Atika tana tsara kwalliya, taci jan wando da farar top ƙal mai
ƙyau da akaima hoton zuciya a gaba, gefe kuma madaidaiciyar jikka ce mai azabar
ƙyau da aka ƙawata da zanen furrani na zuciya.....
“Sister! Wai mi kikeyi hakane?”.
Ɗago manyan idanunta tai da sukasha kwalli ta kalli Aamilah, sake maida fuskarta
tai ga mirror tana dai-daita janbakinta da yay mata ɗas a baki. “Harma tambayata
kike Aamilah? Kin manta yau Valentine day?. A duk irin wannan ranar kema shaidace
ai ina shiryama BB wani abu, sannan muɗan fita yawo koda dakene idan shi yace bai
zuwa. Tunda matsalolin nan suka fara kema kinsan hakan bata kasanceba, to amma
yanda aka maida auren nan namu ai wannan ranar ni tazomin a dai-dai, koba komai zan
sake tabbatar masa yana nan daram a raina, a shirye nake kuma nai waje da waccan
jakar baƙauya daga garesa da baƙin asirinta”. Cike da takaici ƙarara a saman fuskar
Aamilah ta girgiza kai ƙwalla na cika mata idanu, “Sister yanzu nan duk tashin
hankalin da muke a ciki keta soyayya ma kikeyi? Wlhy bantaɓa sanin akwai kunyaba a
duniya irin jiya, hatta da ƴan gidannan kunyar haɗa ido nake da wasu dalilin halin
da su Dad suka jefa kansu da mu, amma ke tun a daren jiya nagama kin ware kamar
komai bai faru ba, ga Mom can kwance yanzu haka zazzaɓi ne ma a jikinta, wlhy badan
su Uncle Sulaiman sun matsa fitar nanba nasan babu inda zataje. Duk shirmen Salman
jikinsa a sanyaye yake tun jiya ya kasa fita ko ina yana tare da Mom, amma
ke........”
Shahudah da kema Aamilah wani banzan kallo tunda ta fara maganar taja
gajeren tsaki tana ɗaukar sosan hoda da ƙara gyara fuskarta. “Aamilah kenan, harma
kece kike da bakin faɗamin ban damu ba? A kaf ɗinku nafi kowa shan kunya a
al'amarinnan, dannice kullum mai posting pictures ɗin Dad a kowanne shafina, kinsan
kuma yanda nake da ɗunbin fans. sannan a dukanin shafukansa hotunana yafi na kowa
yawa a cikinku, wlhy tsabar baƙinciki gaba ɗaya shafukana na rufesu, ke a jiya
saida na karya duka layikan na fasa wayar sannan na samu nutsuwa. Bayan wannan
mikikeso nayi? Na rasa Dad, nakuma rasa BB a karo na biyu? Impossible dear, dolene
na tsira da ɗaya, domin ina ƙaunar mijina. Nasan duk bayanin dazan miki ba fahinta
zakiyiba tunda ba auren kikayi ba, dan haka karki bari a jimu a gidan mutane”.
Baki a matuƙar hangame Aamilah da Mama Atika dake a kwance tana duk saurarensu
suke kallon Shahudah data jefa Cingam a baki tana ƙara gyara zaman gashin dokin
dake a kanta da siririn mayafin data yafa. Juyawa tai tana kallonsu kanta tsaye,
“Kumuje. dan nifa namafi son mu fara isa dan naga Maman BB sosai naga kuma kalar
tarbar da zatamin. Sannan naɗan faracin uban yarinyarcan kafin zuwa dare na tare”.
Uffan babu wanda yace mata a cikinsu, Aamilah ta taimakama mama Atika ta tashi
zaune dan dama tuni ta shirya, badan tasoba zata bisu, sai dai kawai waɗanda suka
bada shawarar zuwa gidan Alhaji babba a yau sunfi su da basa son zuwa rinjaye,
batason kuma tace bazataje ba a fassara al'amarin da wani abu daban, ko aga kamar
tana baƙin ciki da dawowar Bilkisu ne.
Sun iske mafi yawan jama'ar gidan suma duk sun fito harabar gidan, fitowarsu
ta saka kowa ya zubama Shahudah idanu, dan taci wani uban dogon takalmine bayan
ɗamewa datai cikin wando da riga. Uncle Sulaiman ya kalleta cikin ɓacin rai zaiyi
magana Uncle Sadiq yay saurin riƙe masa hannu yana girgiza masa kai alamar karya ce
mata komai, dan yasan yin maganar kan iya janyo wata fitina daban musamman ga mama
Atika da tun jiya taketa datsama mutane magana a gidan tamkar ba uwace a garesu ba.
Haɗiye maganarsa Uncle Sulaiman yayi, badan yaso hakanba. A sauranma babu
wanda yay yunƙurin cewa komai, sai dai sunata kallon Shahudah data toshe da baƙin
eyeglasess ga cingam a baki tanata tauna hankalinta a kwance.

______________
ZAFAFA 2021
___________

Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

Hafsat miss xoxo🥰


KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

__________________
Gidan Alhaji Babba
_____________________

Kasancewar mai martaba ya sanar da wuri zasuzo saboda yanada zaman


meeting da su manyan jihar zasuyi game da abinda ya faru akan su Dad, tun daga
sallar asuba bamu koma barci ba, aunty Batool da Boss suka fita suka haɗo
kayayyakin da za'a buƙata na haɗa abinci, kasancewar munada yawa dandanan muka
shiga hada-hadar haɗa breakfast. Koma nace dai sunayi, dan nikam bama wani aikin
kirki nakeba dan sam banajin daɗin jikina. Wasu na gyaran gida wasu na haɗa abinci
haka akai aikin, zuwa takwas na safe komai yayi tsaf kowa nata ƙoƙarin yin wanka.
Da yake boss ya ɗakko mana kaya ni da shi tun fitar da sukai da aunty Batool sai
banji damuwa da tunanin mizan sakaba, nai shirina tsaf cikin doguwar rigar lass ɗin
daya ɗakko mini, sai dai bayan fauda babu abinda na ƙara, turarema kaɗan na saka na
yafa mayafi na fito falo inda nake ɗanjin maganganun su Anum.
Zamana baifi da mintuna uku ba mukaji ƙarar buɗe gate, miƙewa duk mukayi,
Boss da Anuwar ma suka fito tare da Alhaji babba da suka sakko a tsakkiya, yasha
gayu cikin farar shadda ƙal harda babbar riga, fuskarsa fayau alamar gyaran fuska
yasha a ciki, sai baza ƙamshi suke su duka ukun. Ido muka haɗa da boss mukaima juna
murmushi.
Sune suka fara fita, mu kuma muna biye da su. Lokacin har motocin guda uku
zuƙa-zuƙa sun gama shigowa, sauran kuma duk sun tsaya a waje alamar bazasu samu
waje ba dan habar gidan batacin mota fiye da bakwai. Akwai kuma ta Batool, boss sai
na Alhaji babba guda biyu.
Abu-Siddiq ne ya fara fitowa, sai Abbu. Da gudu Anum ta nufi Abbu ta
maƙalƙalesa, shima ya tarba ɗiyarsa cike da ɗoki da kewa duk da shekaranjiya suka
rabu. Mota ta biyu, Gombiya munaya sai mai martaba Sarki Sameer Saifudden cike da
izzarnan tasa da kwarjinin girma da mulki, a take dogarai suka fara jera masa
kirari tare da lulluɓe gaban motar har saida ya fito. (ALLAH ya taimaki ɗan autan
jimina gagara ɗaukar shaho. Ɗawisu sarkin ado, hadari sa gabanka inda kakeso, kaga
dutsen cikin ruwa bakasan ana rana ba, kainuwa dashen ALLAH. Ɗan sarki, jikan
sarki, baban sarki kuma insha ALLAHU). Duk da sarauta da mulki na wannan sarki yana
girmama duk abinda ya kasance a gabansa, ma'ana wanda yasan ya girmesa a shekaru,
dan haka koda Alhaji babba da su jay suka ƙarasa gabansa ƙasa ya rissinar da kai
alamar girmama ga Alhaji babba. Dan ya tabbata a haife zai haifesa.
Sosai Alhaji babba yaji daɗin wannan girmamawa har fuskarsa ta bayyana.
Ba'a ɓata lokaci ba akai musu jagora zuwa babban falon baƙi na Alhaji babba
da yasha gyara da ƙamshi, an kuma shirya musu abincin karin kumallo.
Gambiya na riƙe dani sai faman taɓa jikina take da tambayata mike damuna.
Nidai kaina a ƙasa nake faɗa mata babu komai, kawai gajiyace, da yake ita bata bi
su takawaba muna tare da itane sai Ummah ƙarama ke faɗa mata ai ta samu jikane. A
take Ummu ta rikice da murna ta rungumeni a jikinta kai kace niɗin jininta ce da
gaske. Hakan ya ƙara saka kimarta da mutuncinta gasu Umm-Anum dama duk wanda yake a
wajen.

Daga haka mukai zaman yin breakfast, inda Ummu ta saki jikinta sosai kodan
dama can ta riga ta saba da Umm-Anum ne oho. Sai dai kowa yaci ya ƙoshi Alhmdllh
sannan su Nabeelah suka gyara wajen, bandani da Umm-Anum ta hanani tashi, a cewarta
na zauna na huta haka nan.

★★★★

Acan falon baƙi kam Abbu kasa sakewa yay yaci abinci saboda nauyin Alhaji babba
da yakeji, hakama takawa da ƙyar yasha haɗaɗɗen shayin da Umm-Anum taima dahu na
musamman saboda tasan shi da Abbu suna matuƙar son shayin, dan idan takawa yaje can
sosai yake shansa, sai farfesun kan rago da shima yana matuƙar sonsa.
Alhaji babba babu ruwansa, mutum ne mai sakewa da jama'a dajan na ƙasa da shi
a jiki, dan haka yayta jansu da hira hardai suka saki jiki da shi, musamman Abbu
daya fahimci shine surukin nashi kodan nannoƙewar da yaketa famanyi.

__________

Bayan kammala cin abinci dukanmu muka ɗunguma falon baƙi inda su takawa
suke kamar yanda Alhaji babba ya bada umarni, muna gama zama sai ga kira ya shigo
wayar boss, tashi yay ya fita, mintuna baifi uku ba ya dawo ya sanar da cewar su
Uncle Sulaiman ne. damar shigo da su Alhaji babba ya bada.
Tunda suka shigo falon idona ya sauka akan aunty Shahudah sai kaina ya
ɗaure, bawai alamunta na nuna bata tatare da damuwa bane, bakuma shigartace ta bani
mamaki ba dan dama nasaba ganin abinda ma yafi hakan, yanda take ta faman shigewa
jikin Boss da shi hankalinsama baya kantane ya bani mamaki, inajin lokacin da take
faɗa masa wai tanason magana da shi. Banji ya bata amsaba, baima kalleta ba naga
yabar inda take ya nufi kusa da Alhaji babba ya zauna.
Harara ta watsomin tare da jan tsaki ta koma kusa da kakarsu ta zauna dan
tsallakawa inda boss yake dai babu dama na sani. ɗauke kaina nayi tamkarma ban
gantaba, dan ni bata gabana wlhy.
Sai da aka fara buɗe taro da addu'a kamar yanda addini ya koyar, kafin kowa
ya fara magana Umm-Anum ta kalli Alhaji babba, cikin girmamawa ta roƙesa dan ALLAH
tanason idan da hali a kawo Dad da Uncle Nasir da Alhaji kokino gidan kafin ita dai
tace komai, dan tanason ta maimaita dukkan abinda ta sani a gabansu gudun karma ace
ta musu ƙazafi.
Kowa kallon Boss yayi, dan ansan dai wannan aikinsane. Kansa ya girgiza yana
gyara zamasa, “Bani da wannan damar, domin case ɗinsu babbane, sai dai........” sai
kuma yay shiru yana ɗan kallon sashin da Takawa yake. Murmushi sarki Sameer daya
fahimci inda ya nufa yayi, baice komaiba ya ɗauka wayarsa ɗaya a cikin wayoyinsa,
ɗan danne-danne yay kafin ya ajiye, da alama dai text message ya tura. Babu jimawa
kuwa wayarsa tai ƴar ƙara alamun shigowar saƙo. ɗauka yay ya duba, sai kuma ya
ajiye yana kallon Boss, shima kallonsa ya keyi, Takawa ya jinjina kai alamar an
gama. Murmushi Boss yay yana rissinar da kansa akamar girmamawa da jinjina.
Da ɗan lokacin jira ne Gimbiya tai amfani wajen basu labarin yanda akai su
Takawa suka tsinci Umm-Anum, har kaita asibiti da maidata saudia, da maganin da aka
nema mata, bata kai ƙarsheba aka iso dasu Dad kowanne a cikin ankwa. Gaba ɗayansu
kansu a duƙe sun kasa kallon kowa dake falon saboda kunya, jami'an tsaronma dake a
tare dasu basu bada damar kowa ya raɓi inda suke ba, dan cikin kuka Aamilah ta nufi
Dad amma sai suka daga mata tsawa, hakama yaron Uncle Nasir autansa hanashi taɓa
Abbansa akai, dole ya koma jikin mamansa yana kuka itama tanayi.
Gyaran murya takawa yay, a take falon yay tsitt, sai ƙarar ac kawai data
taimakawa cinkushewar falon kakeji, dan falon yay matuƙar cika sosai. Hakan ya saka
Jay miƙewa ya tada yaran da ƴammatan yace su koma falon cikin gida. badan sunso ba
duk suka miƙe har bily. sai dai kuma Alhaji babba ya buƙaci Bilkisu ta dawo. a
cewarsa zaman yanada nasaba da ita ita da Anum.
Dawo mukai muka zauna, dama a raina naji haushi ganin banda Shahudah aka kora
sai mu, dan ƙin tashi tayi ita, duk da kuma harda ita ya nuna ɗin.
“Inaga kuka bashi bane ya dace ace munyi a wannan lokacin, haƙuri dayin
amfani da lokacin zamuyi domin warware matsalolin dake a tsakkiya”. Takawa ya faɗa
a hankali yana kallon kowa dake falon. Hakan yasa kowa ya sake nutsuwa aka sake
maida hankali ga Gimbiya data cigaba da bada labarin Umm-Anum, bayyanar cikinta da
kuma aurenta da Abbu da haihuwar Anum. Sai a yanzu Dad, Uncle Nasir, Alhaji Kokino
sukama fahimci halin da ake ciki. Gaba ɗaya ganin Umm-Anum dajin ƙarin baya

ni game da ita daga bakin Matar sarki ya sakasu diriricewa, sai kallonta suke
hawaye na kwarara bisa fuskokinsu. Uncle Nasir ne cikin kuka yace tabbas BA FARKON
BA ƘARSHEN, da ace nasan da zuwan wannan rana da ban biyema yaudara ta azzalumai
irinku ba Alhaji Sadi, yau gashi babu Abdul-aziz a duniya amma ina cikin tsananin
kunya mai muni dako ƙaramin ɗana banason duba, mama kin bada gudunmawa, kema....”
yay maganar yana kallon Mama Atika data duƙar da kai ƙasa tana hawaye. “Da baki
zama mai hassada da ƙyashi ba da ban tsinta kaina a wannan halinba, da baki zama
maison tafi kowaba da ban tsinci kaina a hakaba, tabbas ke uwace mahaifiya a
gareni, amma tun daga jiya na farajin nadamar hakan, kaicon rayuwar da take ƙarewa
da dana sani da ruɗani. kaicon jin daɗi da arziƙin da sakamakonsa yake zama wuta,
inama nine Abdul-aziz...........”
“Bashi bane kai, bakuma zaka taɓa zama shiba azzalumi, mai maida hallaci
da butulci”. Umm-Anum ta faɗa a harzuƙe idanunta sun kaɗa sunyi jazur da ɓacin rai.
Numfashi takawa ya sauke yana gyara alƙyabbarsa, yace, “Inaga mai makon
wannan kace nace ɗin, mizai hana mutafi kai tsaye akan abinda ya taramu nan. Umm-
Anum, mike faruwa?”.
Cikin soyewar zuciya Umm-Anum ta kalli Takawa da yay mata maganar tana
haɗiye zafin da takeji a ƙirjinta, kafin ta maida dubanta ga jama'ar falon baki
ɗaya. “Basai na maimaita ba kowa yasan wacece ni, ɗiyar wacece, sannan wanene ya
kasance mijina a shekarun baya, gwagwarmayar da akasha kafin zamansa wani abu harma
ya zama wani abun. Abdul-aziz mutum ne mai matuƙar son ƴan uwansa, bai haɗa sonsu
da kowaba hatta ɗan da ya haifa, yanda yake ƙaunarsu al'amarin har tsoro yake bani,
dan nidai nasan suɗin da wahala ace suna sonsa kamar haka. Sai dai kuma ban taɓa
magana ba, dan hakan ba hurumina baneba. Halayyarsa ta samo asaline kuma da yanda
mahaifiyarsa tai masa tarbiyya akan ƙyaunar ƴan uwansa da zuciya ɗaya. Abdul-aziz
yanada abokai tunkan yazama wani abu, sai dai babu wanda yafi shaƙuwa da shi kamar
Sadi Kokino duk da kuwa ya girmesa da shekaru masu ɗan tazara. tare sukai karatu
tamkar yanda ya faɗa min, sannan kuma aminine a garesa bawai aboki kawai ba. Sadi
ya taka matuƙar rawa a bikinmu dan a lokacin yafi Abdul-aziz abin hannu, saboda shi
yana juya dukiyar da mahaifinsa ya rasu ya bar masane shi da ƙaninsa. Bayan aurenmu
nasha zuwa gidansa wajen matarsa, hakama matarsa tana zuwa wajena sosai, a haka
muka zama aminai sosai har ALLAH ya ɗaga darajar Abdul-aziz ya zama gwamna, wanda
Sadi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka tsaya tsayin daka akan hakan har Abdul-aziz
ya amince duk da baya buƙata. Harga ALLAH siyasar da Abdul-aziz ya shiga bata taɓa
kwantamin a rai ba, sai dai nayi shiru ne saboda su Mama maryam da Baba duk sun
amince masa, kuma shima naga ya karɓa, Alhaji kokino yana ɗaya daga cikin waɗanda
sukaita nunamin muhimmancin mutane irin Abdul-aziz a cikin masu mulkin ƙasarnan,
tun ina ganin suna tunzurashine kawai harna yarda dasu na shiga jerin masu masa
addu'a. A haka ya kammala shekara huɗun farko a gwamna aka tsaidashi takarar
shugaban ƙasa a bazata. Yaso ya bijire a lokacin kam, amma muka tsaya kai da fata
ni da Sadi da Nasir da wasu a ƴan uwansu wajen roƙonsa ya tsaya tunda jama'ane suke
buƙatar hakan. Haka ya haƙura dan darajar roƙon da mukai masa. An shiga hidimar
kamfen da sauransu har dai gwamnati ta tsaya, Abdul-aziz ya zama shugaban ƙasa.
Harkokin mulki sun fara zama da ƙafafunsu yanada watani huɗu, dan anyi naɗe-naɗe ga
waɗanda ya dace, ciki harda Sadi wanda ya samu muƙami mai tsokar gaske, hakama
Alhaji Ali. cikin amincin ALLAH suka fara fiddo ayyuka na cigaban ƙasa wanda ina
ɗaya daga mashawartan na cikin gida. Ƴan ƙasa nata murna da nuna jin daɗinsu, sai
dai kuma ga Abdul-aziz abubuwa sun fara canjawa, walwalarsa da kuzari duk sun fara
raguwa, idan ya zauna sai kagansa zugum tamkar wani wanda abin duniya ya addaba.
Abotarsa da Sadi kokino kamar ta fara ja baya, dan yawan zuwa da ya keyi gidan sai
naga ya rage daga shi har Ali. A koda yaushe ya dawo gida yana manne da Jawaad
kamar wani wanda za'a ƙwace masa shi. Idan na tam

bayesa mike damunsa kuma sai yace dani babu komai, ko yace, “Harka mulkin ƙasarnan
sai addu'a Bilkisu, babu komai cikinsa sai baƙin tashin hankali, a zahiri kawai
shugaban ƙasa yake amsa sunansa, amma a baɗini ɗaure yake tamau agun waɗanda ke
zagaye da shi”. Nakan nema fashin baƙi akan wannan magana a duk sanda ya yita, amma
sai dai yay murmushi kawai baya cewa komai. Tun ina ƙoƙarin tambayarsa ma harna
daina, sai dai inata masa addu'a. Yana wata na goma da hawa mulki nakasa haƙuri nai
masa tambaya akan Sadi da Ali, amsar daya bani itace kawai babu komai. Hakan yasa
naji babu daɗi gaskiya. dan harna nuna masa. Mutum ne shi mai matuƙar sauƙin kai ga
iyalansa. sai ya zauna ya dinga bani haƙuri damin nasiha akan wani abun barinsa a
yanda yake yafi muhimmanci fiye da tonasa. Nanma dai haƙura nai na barsa badan naso
hakanba, sai daga bayane na samu Mama maryam da maganar dan abin ya kasa barin
zuciyata. A ranar yazo nan gidan, sai dai bansan mi suka tattauna ba, da ya koma
gida kuma ban tambayesa komaiba”. Umm-Anum ta sauke numfashi da share hawayen dake
gangaro mata, wanda su Bilkisu ma kukan suke a hankali. Ƙafarta mai ciwo taɗan miƙe
da cigaba da faɗin,

“A daren wata juma'a dake dai-dai da cikar Abdul-aziz shekara ɗaya da


wata ɗaya akan kujerar mulki sai yay baƙi bayan sallar isha'i, tunda naga har ya
yarda zaiga baƙin na tabbata masu muhimmanci ne, dan a ƙa'ida shugaban ƙasa baya
irin wannan zaman musamman ma da daddare, kuma a cikin gida, gidanma a falonsa.
Inason tashi na bisa naga wanene Jawaad dake fama da zazzaɓi ya hanani tashi dan
yanata faman kuka, haka na haƙura nai amfani da telephone nai kiran su Wasila dake
ɗakinsu, dan suna a tare damune kowa ya sani. Rahma ce ta ɗaga wayan, a cewarta
Wasila tayi barci. Umarni na bata akan tasaka akaima baƙin Abdul-aziz abin sha,
idan kuma suna buƙatar wani abu sai a haɗa da shi. Ta amsamin da to na katse kiran.
Kusan mintuna arba'in da yin haka harma na manta ina jiran shigowarsa ne kawai sai
ga Rahma ta shigomin a wani iri. Faɗa na fara mata, dan basa shigowa ɗakinsa inba
da wani babban daliliba. Cikin rudin da take ciki tace, Kiyi haƙuri Yayah, wlhy
wani abune ya sakani a ruɗani, zomuje ɗakinki kiji dan ALLAH kada Yah Abdul ya
shigo. Ban musa mataba nabi bayanta muka fita, ina goye da Jawaad da yay barci a
bayana”.
(Yayah wai dan ALLAH mi su Alhaji Sadi keson Yah Abdull yayi ne yaƙi?). Ban
ganemba Rahmah miya faru?. (Ruwan da kikace na saka a kaimusu saina iske ma'aikatan
sunata faman aiki, kinsan kuma Yaya bason kowa yay masa aiki yake ba wani lokacin,
shinefa na ɗauka da kaina nakai ruwan, to saina iske Yaya Nasir, Alhaji Ali da
Alhaji Kokino tare da shi, sai dai kafin nai sallama naji wani furuci na Yaya Nasir
daya saka bayan na gaishesu na ajiye ruwan na sake laɓewa, dan tundafa na shiga
falon kan Yah Abdull a ƙasa alamun ransa a ɓace yake. Kinsan minaji kuwa?) kaina na
jinjina mata a lokacin. (Ta cigaba da faɗin Yaya Nasir naji yana faɗin, “Amma dai
Abdul-aziz kasan baka isa sanin sirrinmu ba sannan ka bijire mana, bafa wai dan
bama sonka bane muke jawoka jikinmu, duk yanda kake tunanin mulkin ƙasarnan yafi
ƙarfinka saika ɗaura ɗammarar da muke nuna maka, dan mulkin ƙasarnar baya buƙatar
GASKIYARKA ko ƘWAZONKA balle son TALAKAWANKA”. Murmushi Yaya Abdull yayi yana
girgiza kansa, cike da ladabi yace, “Yaya dan ALLAH mu ajiye maganarnan, indai nine
kusa a ranku abinda naji na gani a can wajen na barsa wlhy, kuma har abada bazan
taɓa furtashi ga waniba koda kuwa ace Bilkisu ce ko Mama ko Jawaad. Amma hakan
bawai yana nufin zan barku kucigaba da zama akan wannan hakalarba, kuji tsoron
ALLAH, karku.........” da sauri Yaya Nasir ya ɗaga masa hannu, “Bama buƙatar ji”.
Murmushi Yaya Abdull yay kawai yaɗan girgiza kansa, “Shikenan Yaya na bari, ALLAH
ya ganar daku gaskiya idan kunada rabonta. Sai dai gaskiya koda zan haɗe wannan
maganar a cikina bazan iya barin Sadi ya cigaba da sarrafa mugan ƙwayoyi ana cutar
talakawa naba, dolene kodai ka rufe kamfaninka na sararafa magunguna, kokuma ni
nasaka kwamitin bincike a kansa ƙarƙashin hukumar lafiya.......”

a fusace Alhaji Ali (Dad) yace, “Mi kake nufi Abdul!? Kenan zaka iya mana SARAN
ƁOYE (littafina na zafafa 2021🤗😋) kenan bayan kasan mu duka nan munada hannun jari
a wannan kamfanin hatta da kai kanka ka sakama ɗanka hannun jari zaka aikata hakan
kuma?”. “Babu wani maganar Saran Ɓoye Alhaji Ali, inda Saran Ɓoye zan muku da bazan
fito na faɗa muku ba ai, sannan da kake maganar na sakama Jay hanun Jari a ciki
ALLAH shine shaidata bansan abinda kukeyi a ɓoyeba kenan ai, nidai ABINDA KE CIKIN
ZUCIYA ta (Littafin Rano a Zafafa 2021🤗😋) na fito na faɗa muku, dan ALLAH ya
kukeson nayi? Ku kune garkuwata, a wannan tafiyar, amma kundawo kuna meman sakani
cikin SIRAƊIN RAYUWA (Littafin Huguma a zafafa 2021🤗😋) kuma? Dama kun dafamin
bayane domin kuyi amfani dani wajen cimma burinku ko mi? To wlhy! Wlhy! Wlhy!!
Kunji sau uku, bazan taɓa cutar da talakawana danna faranta mukuba, bakuma zan taɓa
nisanta kaina da UBANGIJINA saboda ku ba, sirrinku kuwa zan riƙe, domin wanda ya
halicceku na kallonku, nayi imani da KIBIYAR AJALI.....(Littafin Miss Xoxo na
zafafa 2021🤗😋) sulke baya tareta saita gitta wataran, duk abinda yay farko zaiyi
ƙarshe. Karku sake zuwamin gida akan wanan maganar daga yau na rufeta, kuma har
gaban abada bazata sake tashiba insha ALLAH”. Kallon tsoro suke masa sosai, Alhaji
Kokino zaiyi magana Alhaji Ali ya hanashi, shinefa na taho ganin Yaya zai fito).
Ajiyar zuciya na sauke da cigaba da kallon Rahmah tamkar a jikinta zan samu
amsoshina, fassara maganganunta nake amma babu wadda na iya samawa fassarar data
dace, haka na haƙura na barta ta tafi ɗakinsu saboda farkawar da Jawaad yayi baban
yaji kukansa ya shigo. Ban tambayesaba a ranar sai bayan sati kusan ɗaya, sai dai
ko uffan baice daniba balle na samu amsa, haka na cigaba da masa naci daga ƙarshe
yace karna sake damunsa akan abinda bai shafeniba. Ranar haka muka yini ran kowa a
ɓace ni da shi”.
Ta sake share hawayenta tana shaƙar numfashi da ƙyar, saida Gambiya ta bata
ruwa tasha sannan ta cigaba.
Tun daga wannan lokacin na fahinci abubuwa sun ɗauki zafi tsakanin Abdul-
aziz da su Sadi, sai dai yaƙi faɗa min komai duk yanda naso ji, kamar yanda yay
alƙawari ya saka kwamitin bincike akan kamfanin magunguna na Sadi, wanda abin bai
nisaba aka ƙwace kamfanin batare da am bayyanama duniya mi aka gano a cikiba, sai
dai abin mamaki ko sati biyu ba'ai da amsarba aka maida masa abinsa. daga wannan
lokacin kuma yanayin yanda Abdul-aziz ke gudanar da mulki ya fara canja taku, baya
iyayin komai sai abinda su Sadi sukace, ikon ALLAH dai talakawan ƙasa basu fahimci
hakanba sai mu dake a kusa da shi sosai. Hankalina ya tashi sosai, dan ko shawara
na bashi akan abu ko Baba da Mama maryam suka bashi sai yace ba hakaba, ga abinda
Sadi da Ali sukace, ma'ana dai yafi yarda da nasu. Cikin wata guda duk ya susuce
komansa ya koma ƙarƙashin ikonsu, mulkinma dai tamkar sune suke yinsa bashi ba, dan
komai akan ikonsu yake gudana, sai sunce yayi yakeyi, wanda kuma sukace kar yayi
komai muhimmancin abun bazai yisaba. Tun yana ciwo a tsaitsaye harta kaisa ga
kwanciya, da ƙyar ya amince Doctor yazo ya dubashi a wata ranar laraba, a gwajin
farko aka gano ciwon hawan jini tattare da shi, sannan zuciyarsa na barazanar
kamuwa da ciwo kuma. Hankalina ya tashi, na dinga masa kuka da roƙon ya sanarmin
abinda ke damunsa ko shawara na bashi, amma yaƙi. Bayan kwana biyu ya cigaba da ƴan
harkokinsa yana nunamin ya warke, amma ni nasan akwai wata a ƙasa tunda nasha
ritsashi yana hawaye, sannan idan ya zauna shi kaɗai zaka samesa yayi jigum yana
tunani. Sai kuma rama da ya ketayi a tsaye wadda Baba da Mama maryam suka kasa
haƙuri suma sai da suka tambayeni ko lafiya?. gudun karsu tashi hankalinsu nace
babu komai kai kawone kawai irin na shugabanci da kuma ɗan zazzaɓi da yay na kwana
biyu. Sun masa addu'a daga haka muka bar maganar.
Bayan kamar sati shida da tashinsa daga wannan ciwo sai ya ƙara kwanciya,
wannan itace kwanciyar data zama ajalinsa, a ranar bai fita office ba duk da
kasancewar ranar aikice, yanama da meeting da gwamnoni, amma hakan ya gagara. Wajen
yamma sai ga Sa

di Kokino da Ali sunzo sun dubashi, ban kawo komai a rainaba na barsu daga su sai
shi, ina ɗakina inama Jawaad shirin islamiyya sai ga Rahma da gudunta, sai dai tama
kasa magana, hannuna kawai taja muka fito zuwa ɗakin da Abdul-aziz yake kwance. Sai
dai muna kawo ƙofar ɗakin su Sadi na fitowa. Kallon Rahmah suka dingayi cikin wani
yanayi daya sakani faɗin, “Lafiya kuwa? Miya faru?”. Cikin shashantar da zancen
suka shiga gaisheni da tambayar jikinsa, tare da ɗorawa da faɗin ya kamata a sanar
dan a fita dashi ƙasar U.S yaga likitan daya san aikinsa. Ban musa musu hakanba,
dan nima ina buƙatar lafiyar mijina, na raɓasu na shige ɗakin sai na tadda Abdul-
aziz a lulluɓe har fuskarsa, nai saurin matsawa na janye bargon. Ajiyar zuciya na
sauke ganin idanunsa biyu, sai dai da alama hawaye yakeyi, amma jin motsina yay
saurin sharewa ya maye fuskarsa da murmushi. Zama nai kusa dashi ina jera masa
sannu, na shiga karanto addu'a kuma ina tofa masa kamar yanda ya buƙata, dan ya
faɗamin jikinsa na masa zafi kamar ana hura wuta.
Indai taƙaice muku a wanan dare bamuyi barciba sam, washe gari muka wayi
gari jikinsa ya rikice, da yayi tari sai jini, tun yanayi a ɓoye harna farga da
hakan, sai dai ya hanani na faɗama kowa, a cewarsa zasu tafi asibiti gobe idan
ALLAH ya kaimu zai samu sauƙi insha ALLAH. Badan hankalina ya kwantaba na yarda.
Zuwa bayan sallar la'asar baba yaje gida ƴaɗan watsa ruwa dan tare damu ya
yini sai ga Alhaji Ali (Dad) Alhaji Sadi Kokino, Alhaji Nasir (Uncle Nasir) da wasu
mutane biyu daban saniba sunzo dubashi wai. Da yake muna falon ɗakin da yake kwance
sai nace su shiga yana ciki, caraf Rahma ta riƙemin hannu tan girgizamin kai hawaye
cike da idanunta amma ban fahimtaba, duk zatona damuwar ciwon nasane kawai, dan ita
da Wasila tunda gari ya waye suke kuka, amma da yake Rahma tafi Wasila wayo a
lokacin sai nata yafi yawa. Suna shigewa ta miƙe zaram ta kama hannuna tana nunamin
ɗakin, mamaki abin ya bani na hau mata faɗa akan bata da bakine?. Har sannan bata
tankaminba, kanta dai taketa faman jujjuyamin da fusgar hannuna muka zagaya ta
Window.
Ban taɓa ganin tashin hankali mai muni irin na wannan ranaba, dan kuwa
zagaye muka hangi su Alhaji Kokino akan Abdul-aziz, sun lulluɓa masa wani jan
ƙyalle suna wani kalar yare da su kaɗai suka san mi suke faɗa, duk yanda naso ɗaga
ƙafa naje cikin ɗakin dagani har Rahma mun gagara hakan, a gaban idanunmu Nasir ya
shiga zubama Abdul-aziz wani ruwa yana surkulle, sannan ya hau kansa yay....ya
ya...yay fasiƙanci mafi muni da shi”. Umm-Anum ta ƙare maganar da fashewa da wani
irin matsanancin kuka mai cin rai da zuciya, numfashin ta sai sama da ƙasa yake
tamkar zata shiɗe.
Tsitt falon yayi babu maiyin koda ƙwaƙwaran motsi, da alama dukansu sunyi
suman zaune ne.
Umm-Anum dake kuka tamkar ranta zai fita ta cigaba da faɗin, “Yana kuka da
roƙonsa karya aikata masa wannan aiki maimuni, ga aman jini yanayi amma sam Nasir
bai sauraresaba, sai da ya biya buƙatar zuciyarsa Ali ma yayi, Kokino ma Yayi. Duk
muna kallonsu ni da Rahma, sai dai ko motsin kirki mun gazayi balle wani yunƙuri
har suka fito suna kuka. Fitowarsu tayi dai-dai da dawowar baba tare da Mama
Maryam. Sai ji kawai mukai suna faɗin Abdul-aziz ya rasu. Iya abinda naji kenan ban
sake sanin mi nake cikiba sai a Saudia, shima ban tuna komaiba makamancin hakan sai
shekaran jiya dana farka tamkar mai barci naga Anuwar da Abbunsu tare
dani............✍

______________
ZAFAFA 2021
___________

Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

Hafsat miss xoxo🥰


KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS

BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Kwace wannan kodai itama su Dad sun ƙwamusheta ne🤣, na barku a gidan Alhaji babba
kunata jira, yo sakawa sukai nimafa akai kidnapping ɗina, da ƙyar na fito a inda
suka ɓoyeni😪🚶🏻🚴🏼.

Ku fara da waɗanan kafin na ƙara editing sauran na turo muku da safe idan ALLAH ya
kaimu💃🏻. Yanzu kam mankaina ya tsiyaye sai an ɗura wani😣😪😫🚶🏻🚶🏻.
[2/17, 9:22 AM] HASNA: Page 63

....................Su Jawaad basu san wainar da ake toyawaba a gari, sai iface-
iface suka dingaji da tashin hayaniya, sai kuma hayaƙi daketa turnuƙe sararin
samaniya a hankali. Sai sukaga kuma mutane nata fita daga asibitin.
Gaban Jay ya faɗi, ya zaro waya daga aljihu yay kiran Jabeer dan yaji ko
lafiya?. “Boss wlhy akwai matsala, an fito da mutanen nan daga prison za'a kaisu
kotu jama'ar gari sun tare motar sun banka mata fetur sun saka wuta. Wlhy duk yanda
jami'an tsaro sukaso tsaidawa al'amarin ya gagara, harma an raunata mana ɗan sanda
guda daketa ƙoƙarin basu kariya da roƙon mutane su kwantar da hankalinsu kotu za'a
kaisu, kuma a yau za'a yanke musu hukunci. Amma sam basu sauraresaba, saima suka
nema haɗawa dashi shima, dan acewarua shima nasune”. Innalillahi Jawaad keta ambata
zufa na keto masa a duka sassan jikinsa. Dole yabar asibitin ya nufi inda al'amarin
ke faruwa..

Wuta taci su Alhaji kokino sosai kafin ƴan kwana-kwana suzo da masu bada
taimakon gaggawa na jami'an tsaro, da ƙyar aka iya samun hanyama motar ta ƙarasa,
police kuma suka fara jefa barkonon tsohuwa, da wannan damar aka samu mutane suka
fara darewa har aka ƙarasa gasu Dad aka basu taimakon, sai dai kuma ina komai ya
gama ƙurewa, dan wutar ta cisu sosai, sunta ihu da neman taimako basu samuba.
Waɗanda basu mutunba ma da wahala ace zasu rayu, dan su Dad ko iya gane
fuskokinsuma ba'ayi sam. A haka dai aka kwasosu zuwa General hospital inda su
Bilkisu suke.
Faruwar hakan yasa aka baza jami'an tsaron sintiri a kowane titi, tare
da kafa dokar hana shiga da fita gaba ɗaya, kasuwanni da kowacce ma'aikata an
rufesu ruf an kora mutane gidajensu. Garin yayi tsit, sai gidajen redio dana tv
kawai ke aiki, anan mutane kejin halin da ake ciki.
Kafin a ƙarasa dasu Dad asibiti wasunsu suka sake mutuwa, ciki harda Uncle
Nasir kuwa. Suma dai an shiga da sune kawai, amma likitoci sunma rasa ta ina ya
kamata su fara basu taimakon daya dace, gaba ɗaya jikinsu ya sale tas, yay jazur
tamkar naman dake kusa da wuta ana masa gashi😭.
Ba ƙaramin tashin hankali su Umm-Anum suka sake shigaba da ganin su Dad, duk
da zalincin da sukaima rayuwarsu har hawaye sukai musu. Bama suba duk mai hankali
yaga wannan bahagon al'amari dolene ya shiga ruɗani mai tsanani, ya kumaji tsoron
wannan mummunar rayuwa da waɗanan mutane suka ƙirƙirar ma kawunansu. Gadai duniyar
an tara, kuɗi, mulki, zuri'a, da komai amma an ƙare da tafiya a barsu cikin tozarci
da wulaƙanci. Basu karesu daga faruwar kowanne irin bala'iba ko masifa ba, abinda
suka tara da wanda suka shuka bai hanasu mutuwaba, bai hana ƙarshensu muniba,
wannan shinefa ake kira da BA FARKON BA ƘARSHEN, yakai ɗan uwa bari murna akan
aikata mummunan aiki kuma babu abinda ya sameka, bari tinƙaho da taƙama akan kai
haƙƙin wani bai sakaka komai sai ƙiba da kwanciyar hankali, bari farin ciki kaine
sama dakowa saboda kasancewarka azzalumi, bari taƙama da tinƙahon ka tara kai babu
yanda aka iya da kai. Rage buri da hangen haramun domin kawai burge duniya ko
morarta dayin bishasha a cikinta. Daure ka nema halak komai wahalarta da ƙaracinta,
nisanta kanka daga haramun komai sauƙinta da zaƙinta. Ji tsoron UBANGIJI koda ace
baka ganinsa to shifa yana kallonka. Kiyaye ruɗin duniya dana abokan banza ka kama
ALLAH da abokan ƙwarai masu nuna maka muhimmancin tsoronsa. Ya ALLAH ka gafarta
mana, kasa muyi ƙyaƙyƙyawan ƙarshe. ya rabbi ka ɗauki rayukanmu muna masu cike da
ɗunbin tsoronka da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W)🙏🏻😭.

__________________________________

Al'amura sun sake ƙwaɓewa, a gaba ɗaya kwanakin satin da suka biyo baya,
babu wani farin ciki daga jama'ama balle su Jawaad da iyalan waɗanan mutane. An
samo gawar Aunty Mah-Mah (Rahmah) a gidan Dad cikin wani akwatin tsafinsu, ashe
lokacin da suka halakata wata gawar daban suka kawo a zuwan itace, shiyyasa Dad ya
hana kowa yimata wanka shine yay mata a lokacin. To ashema ba gawarta baceba,
gawarta na nan cikin ɗakin sirrinsa da ko Mom ta rantse bai taɓa barinta ta
shigaba, ita kuma duk tunaninta bai taɓa kaiwa ga hakanba.
Abin sha'awa da tsarkake sunan UBANGIJI gawar Rahma fes aka sameta dukda
sheɗancin da Dad ya ɗauki tsahon shekaru yanayi da ita. Fuskarta fayau tamkar a
yaune ALLAH ya ɗauki ranta. Bilkisu ta rungume gawar tana kuka abin tausayi. Da
ƙyar Jawaad ya ɗagata akan gawar shima yana nasa hawayen da baisan suna zirarowaba.
Alhaji babba kam yayi dauriya matuƙa, sai dai haɗiyar zuciya kawai yakeyi da kukan
zuci. Umm-Anum tai mata wanka aka suturtata. Ɗunbin al'umma daga ɓangarori da dama
suka sake sallatar gawar Rahama a karo na biyu, ta kuma samu rakkiyar ɗunbin jama'a
zuwa makwancinta na gaskiya.
An samo zunzurutun kuɗaɗe da kayan tsafi kala-kala da wasu abubuwan a gidan
Dad, hakama Uncle Nasir da sauran abokan sheɗancinsu irinsu Kokino. Kamfanoninsu ma
an samo abubuwa masu yawan gaske masu matuƙar tada hankali, ciki harda kayan shaye-
shaye kala-kala da tabar wuwu buhu-buhu da adadinsa ya tasarma dubu goma. Sai wasu
gurɓatattun abubuwan da bama zasu lissafuba gamai sauraro.
Ƙasa tayi tsitt, manyan dake huɗar kasuwanci dasu data abokantaka sun fito
sunata ALLAH wadai da nisanta kansu da ɓoyayyun ayyukan su Dad ɗin, komai dai ya
fito fili, anyi walƙiya ijiya taga kowa da komai. Inda aka bar iyalansu da waɗanda
aka zalunta irinsu Jay da jiyyar zukata.
Idan kaga Bilkisu a irin wannan lokacin dole ka tausaya mata, ga laulayin ciki
ga tashin hankali da damuwa, sauƙintama ƴan uwanta da mijinta kowa tattalinta yake
da burin ganin farin cikinta. Takanyi kukan jin daɗi da ganin ƴan uwanta zagaye da
ita, waɗanda ada ta rasa samu.

★★★★★★

Ɓangaren Shahudah kam ba'a cewa komai, ita babban kukanta da tashin
hankali bawai ya ta'allaƙa da halin da Dad yake ciki na halin rayuwa da mutuwa
bane, babban tashin hankalinta shine ance babu aure tsakaninta da Jay sai dai idan
sakin Bilkisu yayi kota mutu, amma bazai yuwu suyi zaman aure a ƙarƙashin miji guda
ba ita da ƴar uwarta da suke Uban ɗaya.
Hakan ba ƙaramin tada hankalinta yayiba, babu kunya babu tsoron ALLAH ta
dinga tsinema Dad da jera masa ALLAH ya isa cikin hausarta da koma fitar kirki
batayi. Ƙiri-ƙiri ta nema haukata kanta. Mom ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi
itama, da abinda ya dameta zataji kokuwa da haukar Shahudah, ko ciwon mama atika,
ko kuma nisantarsu da Qaseem yayi?. Dan tun bayan lafawar komai Qaseem ya ajiye
aiki yabar ƙasar gaba ɗaya batare da kowa ya saniba sai daga baya sukeji ta hanyar
saƙon daya bar musu.

A yanzu kam kowa burinsa Jawaad da mahaifiyarsa da ɗan uwansa su yafe musu a
wannan family, musamman ma waɗanda sukasan sun muzguna masa bisa jagorancin
makircin mama Atika da ƴaƴanta.
Dan samun lafiyar Mama Badiyya ta sake bayyana abinda ta gani Uncle
Nasir nayi a wani dare bayan ɗakunansu shinefa ya banka mata baƙin asiri itama ya
tauye rayuwarta ta koma ita ba'a duniyaba ba kuma a lahira ba😪.
Jay dai bai samu zaman sauraren kowaba, dan shi a yanzu ta matarsa ma yakeyi
da fatan samun nutsuwarta da abinda ke cikinta.

★★★★★

A kwanakin da aka cika kwana goma da sakama su Dad wuta shima ya mutu da
safe yana ihu da kururuwa kamar yanda su Uncle Nasir sukayi lokacin da suma zasu
mutu, ga wani irin kakari maiban tashin hankali, jikinsa kuma ya koma fari fat
tamkar babu jini a jiki, gashi dama wuta ta gama ɗaye fatar gaba ɗaya. Da yamma
Alhaji Kokino yabi bayansa da Abban Zuhrah, kamar yanda aka binne su Uncle Nasir
babu wanka saboda ƙunar jikinsu haka shima Dad dasu Abban Zuhrah aka haɗasu akai
musu salla aka biznesu da halinsu. Wata shari'ar dai kam lallai tafi ƙarfin alƙalan
duniya, sai dai a jiraceta daga sarkin alƙalai kuma😭🙏🏻.

Haka rayuwa take su Dad sun tafi tamkar ba'ayusuba a duniyar dagasu har
ayyukan da suka shuka, a hankali hankulan jama'a sun fara dawowa jikinsu daga
abinda ya faru, sai kuma labarai da maida yanda akayi da har yanzun sun gaza
ƙarewa. Yayinda akebin gidajen da suka bari ɗaya bayan ɗaya ana rushewa, wanda suke
ciki kuwa ana barinma iyalansu dan su sami matsugunnin rufama kansu asiri. Masu
ƙarfin imani a cikinsu kuwa sun tsame kansu daga komai na dukiyar acewarsu basa
buƙata, dan dukiyace ta tsafi, sun gwammaci su ƙare rayuwarsu a talauci da su zauna
a ƙarƙashin ikon dukiyar jinin al'umma.

BAYAN WATANNI BIYAR.

Abubuwa sun sake lafawa, harma wasu da yawa sun faffaru, ciki kuwa harda
komawar Umm-Anum Saudia tare da ƴan uwanta suka sauke faralin miƙama ALLAH godiya
daya kawo musu ƙarshen komai cikin rahamarsa da hikimarsa. Bayan kammala aikin
hajji su suka dawo ita kuma aka barta a can tare da mijinta da Anum, Anuwar dai kam
yayi uwa yayi maɗaukiya a ƙasarsa ta haihuwa, harma an ware masa ɗaki guda a gidan
Jawaad yana zaune tare dasu.

Ansha bikin Nazifa da Ummie, harma da Zuhrah da wani ɗan uwansu da yake
bala'in sonta dama abbanta ya ƙi bashi, yanzu bayan lafawar komai ya dawo, acewarsa
ai ita yakeso, kuma ba ita ta aikata abinda ya faruba babantane, a yanzukam bashi a
duniya, dukiyar daya barima sun ajiyeta ita da mahaifiyarta da ƴan uwanta.

An kumasha bikin Amina da Yah Qaseem wanda Jawaad yaje yayo biko har ƙasar da
yake, tare da zaunar dashi yay masa nasiha mai ratsa jiki, tare da bashi shawarar
ya tallafi ƴan uwansa a yanzu da mahaifiyarsu dan shine uba, ya kuma nema musu
malamin addini su koma islamiyya musamman ma Shahudah da har yanzu hankalinta bai
gama kwanciyaba dan tana masifar son Jay. Lokacin da taga cikin Bilkisu da yanda
Jawaad ke riritata ita da cikin ba ƙaramin shiga ruɗani ta sakeyiba, tasha kuka
ranar harda shiɗewa kuwa.

Batool ma ansha bikinta da Dr Bello daya dage akan shifa da gaske yanaso babu
wasa. Ganin tsakani da ALLAH yake sonta ta bashi dama ya kawo kuɗi aka gwangwaje.
Alhaji babba ma bisa takurawar Jay suka ɗaura masa aure da Maman su Amina,
da da Maman yara za'a haɗa masa ita ta roƙa arziƙi akan a barta dan ba isashshiyar
lafiyace da itaba har lokacin, tana dai lallaɓawane bisa taimakon da kulawar da
Jawaad ke bata.

Ƙungiyar su Bilkisu nata ƙara haɓaka da faɗaɗa akan daƙile fyaɗe da hukunta
duk waɗanda aka samu akan laifin. hukunci kuma mai tsananin gaske. Inda manyan
mutane da shugabanni suma suka ƙara basu goyon baya domin fata da samun damar
daƙile matsalar kodan addabar da taima al'umma.

Mama Atika bayan wahalar jinya da tasha na kusan wata huɗu itama ALLAH yay
mata rasuwa, su Mom da su Shahudah ansha kuka. Komai nasu sai ya daɗa yin sanyi
kuma, musamman ma ita da duk ƙwalisarnan yanzu babu ita, babu Dad babu dukiyar da
ake taƙama da ita.

A ɓangaren rose kam ta buga ta buga taga babu ci, mai shiga tsakanin
soyayyar Jawaad da Bilkisu sai dai ALLAH. Babu kalar ƙulle-ƙulle da munafurcin da
bataima bily ba a station ɗin sai dai babu tasiri, daga ƙarshema da Jawaad ya
ganota sai yasa akai mata transfer waje mai nisa a tsakaninsu. Wannan abu ya sakata
jin takaici harda kukanta kuwa, ballema randa taji anƙarama su bily girma da
ƙyaututtuka susucewa tayi duk da itama harda ita, a ganinta bily batakai ta
kamotaba, amma ya ta iya da abinda yafi ƙarfin wuta inji kishiyar ƙonanniya. tana
kewar jawaad ainun. dan koba komai idan tana ganinsa kusa da ita tana ɗanjin
sassauci.

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

Hafsat miss xoxo🥰


KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

★★★★

A gidan Iyayen gayya kuwa ai ba'a cewa komai, cikin Bilkisu da har yanzu gata
nanneda ya fito sosai, dan yana cikin wata na bakwai. Tattali sosai take samu a
wajan Jawaad da duk ahalinsuma baki ɗaya, inda aka maido mata Nabeelah gidan tana
tayata zama, gefe kuma tana shan soyayyarta da masoyinta Anuwar.
Faruwar wannan al'amari ya sake maida bily miskilar gaske, dan ko Jawaad
ɗin idan bata gadamaba saita yini batai masa maganar data zarta gomaba. Ta ƙara
ƙwazo akan aikinta fiye da zaton mai hasashe, musamman ma da bayan lafawar abubuwa
suka samu ƙarin girma itada duk jami'an da sukaje wannan aiki a waccan rana. Saboda
cikinta dai bata fita operation, sai dai tayi ayyukan cikin gida kawai daga office.
A gefe kuma tana sake samun ƙwazo da horo a wajen mijinta, wanda a kullum cikin
sake nuna mata ƙauna da soyayya mai tsanani yake. Sam baison yaga tashin hankalinta
ko damuwarta balle fushinta. Shidai fatansa ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo masa
little Beejay kamar yanda yake faɗa a kullum.

Cikin Bilkisu nada watanni taƙwas Jawaad ya sakata ɗaukar hutun dole,
acewarsa saita haihu ƴarsa tayi ƙwari sanan. Aranar da hakan ta faru harda kukanta,
amma sai yaƙi kulatama yay kamar bai jitaba, sai Anuwar dake mata dariya shi da
Nabeelah suka koma lallashinta da lallaɓata.
Tana shiga watan haihuwa Ummah babba tace zata maidata can gidanta, dan
bazai yuwu a barta ta zauna nan babu babba tare da ita ba. Babu kunya Jawaad ya
murje idanu yace shifa bai yardaba, idan dan babbane ya amince asamo wata tsohuwar
ta zauna da ita, amma shi bai yarda matarsa tai nesa da shiba gaskiya.
Ranar Bily ta tasashi gaba ta dinga kwasar dariyar mugunta, dan kawai ta rama
abinda yay mata na sakata ɗaukar hutu a office saita shiya kaya kusan akwai huɗu na
tafiya gidan Ummah babba, aiko ya murje ido ya balbaleta da masifa kamar zai
cinyeta ɗanya jagab🤣.
Aifa ganin yanda ya harzuƙa dole Ummah babba ta janye ƙudirinta, aka samo
wata dattijuwa zata zauna dasu, ga kuma Nabeelah da Anuwar tare dasu. Ummah ƙarama
da babba kusan kullum saisunje ganinta. Hakama maman Amina, dan cikin na shiga wata
tara sai ya ƙara girma kamar wadda zata haifa ƴan biyu.

★★★★★★

A wannan ɗan tsakanin akasha bikin su Amaturrahman suma, inda Bilkisu ko sau ɗaya
bata samu leƙawaba saboda cikinta, Jay yace idan ta haihu taje taima Ummu ALLAH ya
sanya alkairi.
Bayan anyi biki an shashshare Umm-Anum da itama ta halarta da Aunty
Mahfuzah sukazo nan dansu gaisa da Alhaji babba. Randa suka cika kwana uku gidan
Alhaji babban sai sukazo nan gidan Jay duba bily, danshi kullum yana zuwa can ya
gaidasu, itako saita waya tunda bata fita sam.
Ta taresu da tsantsar farin ciki, inda sukuma suketajin tausayinta da mata
fatan sauka lafiya. Su Anuwar ne dai ke amsawa, itako kanta na a ƙasa dan kunya.
Anuwar ya kumbura fuska yana kallon Umm-Anum daketa mammatsa ma bily hannunta
daya kumbura. “Umm-Anum gaskiya nimafa amin aure, so kuke sai little tazo duniya
taga Abbanta tuzuru”.
Dariya duk suka sanya ƴan falon, banda Jay dake zaune gefen Umm-Anum yana
latsa waya, yadai ɗan ɗago ya kalli Anuwar ɗin ya zuba masa harara ya ɗauke kansa.
Sai da suka gama dariyarsu sannan ya sake kallonsa fuska babu wasa. “Kai baka da
kunya ko......?” “A'a yayanmu nifa wlhy gaskiya na faɗa, yanzu dan ALLAH little
zataji daɗine idan aka haifota ta iskeni babu aure, ita dai ai nasan tanason iske
kawunta a dattijonsa ko”. Kai kawai Jay ya girgiza ya sake ɗauke kansa, dan indai
shaƙiyancine akazo wajen Anuwar kowa ya shafama kansa lafiya, duk masifarsa kuresa
yake shima har yagaza cewa komai.
Umm-Anum da itama ke dariya yanzun tace, “To ni miye nawa, aiga mai maka auren
nan a gabanka” tai maganar tana nuna Jay. Tasowa yay ya tsuguna a gaban Jay ɗin
yana wani marairaice fuska. “Yayanmu dan ALLAH ka aurar dani kar a haifi little ina
a ƙasa” yay maganar cikin harshen nasara da haɗawa da ƴar hausar daya fara kowa
wajen Nabeelah”. Kunnensa Jay ya kama ya murɗa da ƙarfi, aiko a take yahau roƙo
daban haƙuri. su Bily kuma namasa dariya.
Cak ta tsaya daga dariyar tata jin bayanta ya riƙe, ta shiga yamutsa fuska
tanason fiskewa amma hakan ya gagara, kamar wasa saiga ƙaramar magana ta zama
babba, dan kuwa kafin wani dogon lokaci naƙuda ta tashi gadan-gadan, dama a gaba
ɗaya kwanakinan naƙudar tsaye takeyi.
Cike da rikicewa Jay ya sugunmeta daga ita har cikin sai mota, Anuwar ya
jasu sai asibiti.

BAYAN AWA BIYAR.

Bayan gumurzu da wahalar da bily tasha a ɗakin haihuwa ta sunkuto ɗiyarta


mai kama da ubanta sak, dan yarinyafa tun bata gama hucewaba kamanin Jawaad ɓaro-
ɓaro a fuskarta, sai dai kalar fatarta tazo daɗan duhu saɓanin yanda ake haihuwar
jarirai farare tas.
Ai murna wajen wannan ahali ba'a magana, a take Jay ya tauna dabino ya zuba
mata a baki tare da miƙama Anuwar yay mata huɗiba da suna BILKEESU MAI GADON
ZINARI, Alƙawarin ALLAH ya cika, Jawaad Abdul-aziz yousif ya zama Ɗan BILKEESU,
mijin BILKEESU, baban BILKEESU, saura kakan BILKEESU🙄😜🤣lol.

A ranar aka sallami mai jego da jinjirarta dan suna cikin ƙoshin lafiya,
bakin Jay ya kasa rufuwa, ya murje idanu sai kulawa yakebama matarsa da ƴarsa a
gaban kowa.
Washe gari ƴan barka suka fara ɓarkowa ta ko ina, ciki kuwa harda Shahudah
dataita kuka dan damuwa, yayinda takejin zafi da tsanar bily har cikin ranta.
(Shiriyar wanifa sai ALLAH yaso, bashi yuwuwa lokacin damu mukaso😫).
Yah Qaseem ma ya kawo ƴar Aminatunsa, hakama matan su Jabeer dasu Ummie da
abokan aikinsu harma da ƙawayen makaranta. Bily kam tayi goshi, kaga ƴar gatan
dangi. Baba ƙaura ma daya koma daji abinsa tuni sai gashi yazo, dan yace yafi son
zaman can, alkairan da manyan ƙasa sukai masa dasu Jawaad duk tattarawa yay ya bada
gidan marayu, acewarsa sun fishi buƙata, sai dai ya riƙe waya suna gaisawa da
abokan arziki irinsu jay, tananma ya sanar masa da haihuwar anayinta.

Su Umm-Anum basu komaba har saida akai suna, inda kowa dai yasan sunan
jinjira BILKEESU. Su Firdausi duk sunzo sun taka rawar gani, hakama abokansa su
Abbati na ƙauyensu, inda ɗunbin jama'a sukai masa alkairi da dama wanda shi wasuma
bai sansuba.
Amaryar jego tasha gayu harta gaji, koni dai ta gama burgeni aradu🤗, balle
kuma ubangayya Jay. Ansha hotuna inda naita hango fans cikin ƴan taron suna🤗.
(Kunyima Jay halacci gaskiya😘😘😍🤣, dan yau Ƴan Team Beejay da team Qaseem da team
Shahudah duk sun dunƙule waje ɗaya😋☺😉💃🏻.

★★★★★

Ansha hidimar suna kowa ya gaji, wasuma har sunyi barci. Da ƙyar na iya
miƙewa na shiga bayi dan na samu na watsa ruwan da Anum ta haɗamin. ita kuma na
barta tare da Little Bee. Ban wani jimaba, da dai na samu jikin ya saki na fito.
Tsaye nai a ƙofar bayin ina kallon wanda banyi zaton ganiba, shima juyowa
yay yana kallona fuskarsa ɗauke da murmushin nan nasa mai tsada dasai ya gadama
yake yinsa. “Umm-Bee ƙaraso mana”. Murmushi nayi na cigaba da takawa a hankali zuwa
garesu, hannuna dake da damshin ruwa ya kama ya zaunar dani gefensa. Na ɗan sauke
ajiyar zuciya ina kwantar da kaina gefen kafaɗarsa. “Sweet Love bakayi barciba
daman?”. Fuskata ya shafa yana sake rungumoni jikinsa sosai. “Nakasa barcin
Miemaa”. Idanuna na ɗaga da sauri ina kallonsa, “Miyasa hakan Dear?”. “Saboda MIN
QALB (Littafin Mamu gee na zafafa 2021) ɗina mana”. Na ɗan lumshe idanu na sake
buɗewa a kansa, cikin sake sanyaya murya nace, “Minene shi?”. Nunani yay tare da
ƴarsa yana murmushi. Nai ƴar dariya da komawa jikinsa na kwanta ina shafa kan baby
bee daketa barcinta hankali kwance, dan tasha wankane wajen inna tsohuwa yanzu babu
jimawa.
“Wai kinsan miya faru?”. Kaina na girgiza masa ina cigaba da shafa mata kai.
“Ummuna tafa dage tare zaku tafi, nifa gaskiya gaskiya.......” kallonsa na sakeyi
da sauri cikin ɗan zaro ido, sai ya fasa faɗa ya ɓata fuska kuma. Ƙyalƙyalewa nai
da dariya da sumbatar kumatunsa ina faɗin, “Boss na Miemaa”. Ya ranƙwashi kaina
yana hararata, “Oh hakama zakice ko? To nama fasa babu inda zaki, gara ki zauna
nanda wata biyun ki sake ɗaukar wani cikin”. Idanu na zaro ina buga ƙirji, “Dan
ALLAH rufamin asiri sweet Luv daina min wannan fatar kaji”. Dariya sosai ya sanya,
ya kwantar da Little Bee tare da jawoni jikinsa muka faɗa saman gadon yay min runfa
da jikinsa. Kallon juna muke cike da shauƙi babu mai ko ƙiftawa, sai da naji
bakinsa cikin nawa na dawo hayyacina da sauke nannauyar ajiyar zuciya, son tureaa
nake amma yaƙi bada damar hakan, na rinƙa dukan bayansa amma bai barniba saida yayi
san ransa sannan ya sakeni ya miƙe yana dariya damin gwalo. “Dama abinda ya kawoka
kenan ai” na faɗa iana ɓata fuska kamar zanyi kuka. Gwalo yaymin dai-dai zai fita
yace, “Eh naji ɗin”.
Fariya sosai nayi ina girgiza kai, na jawo ɗiyata na rungume ina sumbatarta
dajin kamar na haɗiyeta na huta dan ɗunbin son da nake mata.

BAYAN WASU SHEKARU.

Yarane kusan uku keta wasan basket ball a madaidaicin filin wasa dake
a cikin wani ƙaton gida mai ɓangarori kusan huɗu. ina tsaye a wajen kusan mintuna
huɗu saiga mata da miji sun fito daga ɗayan ɓangare na gidan, ba kowa bane face
Anuwar da Nabeelah, suma suna sanye ga j.c. ihu yaran suka fara, biyu na kiran
Abbah! Abbah! Abbah. Biyu na kiran Mamma! Mamma! Mamma!! Cikin ɗaga hannu irin na
jinjina da ɗokin isowar abokin wasa. Anuwar yaja ƴan team ɗinsa, Little Bee, da
ƙaninta na biyu Abdul-aziz suna kiransa (Awwab). Nabeelah kuma taja nata ƴan team,
ƙanwar Little bee mai bimata Maryam suna kiranta (Khairiyya) sai yaron su Anuwar
ɗin mai sunan Jawaad, suna kiransa (Khalifa). Wasansu suka fara cike da nishaɗi,
basufi mintuna talatin da farawarba sukaji horn. Maigadi dake kallonsu daga gate
yay saurin zuwa ya buɗe. Farar mota tas ta shigo gidan wadda Bily ke mazaunin
driver cikin kayan aiki, Jay na gefenta shima sanye da suit yanata faman danne-
danne a laptop.
Da gudu yaran suka nufi motar suna faɗin, Abie! Miemaa! oyoyo. Bily dake
murmushi ta kalli Jay shima ya kalleta, kafin su maida idanunsu ga yaran nasu dake
tunkarosu. Awwab da Khairiyya suka nufi sashen da bily take suka buɗe mata, Little
Bee da Khalifa kuma Jay suka buɗemawa. A tare suka fito fuskarsu ɗauke da murmushi.
Jay ya ɗaga khalifa tare da sumbatar kumatumsa, shima yaron ya sumbaci Jay ɗin yana
dariya da faɗin, “Abie i love you”. “I love you too second Jawaad” ya faɗa yana
lakace masa hanci, kafin ya duƙa ya sumbaci Little bee ƴar kimanin shekaru goma
itama. “Little BeeJay ɗina”. Fuskarta washe da murmushi sak irin na Bily tace,
“Sweet Abie na i love you” tai maganar da sumbatar hannunsa itama. Ta matsa jikinsa
ya rungumeta ta gefen hannun damarsa, na haggun kuma yana ɗauke da khalifa.
Acanma dai Awwab da khairiyya suna maƙale da Bily, saida suka gama ɗokin
ganinta sannan suka dawo wajen Abie, ya sumbacesu suma a kumatu kamar yanda yayma
su Khalifa. Kafin su Anuwar su ƙaraso suna musu barka da dawowa.
Cikin tsokana bily tace, “Iyayen da basa girma da shiriritar ƴaƴansu”. Dariya
Anuwar da Nabeelah sukayi, Jay dake murmushi shima yace, “Karki ja mana yanda muka
dawo a gajiyanen yanzu su tara mana ciwon kai suda ƴaƴansu, zomu gudu muje mu
hutama ranmu princess”. Cikin dariya Anuwar yace, “Idanma kun gudu binku zamuyi,
dan yau a falonka aka haɗa dinner. Idanu Jay ya zaro sosai. sai kuma ya ɓata fuska
yana kallon Bily cike da langaɓe kai. “Miemaa kinajifa, nidai ALLAH ban yardaba
hutawa zanyi”. Kafin bily ta bada amsa yaran suka shiga ihu da tsalle suna faɗin
suma basu yardaba a falon Abie zasuyi dinner yau”.
Ƙwafa Jay yay yana kallon Nabeelah, “Auta kece kika haɗamin wannan aikin ko,
maganar gaskiya ayi hutu na tarkataku ku tafi Saudia wajen Ummuna muma muɗan huce
gajiya da matata a gidanga. A waje dambe da ɓarayi a gida dambe da iyayen yara da
yaransu”.
Sosai Nabeelah da Anuwar ke dariya, Nabeelah tace, “ALLAH babu ruwana, Abban
Little ne”. “Kai ko?”. Jay ya faɗa yana kama kunnensa. “ALLAH da zafi Yayanmu”
Anuwar ya faɗa cikin marairaicewa yana riƙe hannun Jay. Yaran suma duk sai suka
marairaice suna faɗin, “Sorry Abie Abbanmu yanajin zafi sosai”.
Dariya Bily takeyi. Jay dake murmushi ma ya saki kunnen Anuwar ya kama hannun
matarsa suka shige dan anfara kiran sallar magrba. Kayansu yaran suka kwasa daga
mota tare da tsarabar da aka yo musu sukabi bayansu. Anuwar da Nabeelah ma suka
nufi ɓangarensu dansu watsa ruwa tu fito.✍😭🙏🏻

ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN.

Na godema UBANGIJIN al'arshi daya bani ikon kammala wannan littafi daya jani dogon
zango, kuskure. dana tafka a cikinsa ALLAH ka yafeni, abinda nayi dai-dai ALLAH ya
haɗamu a ladan daku masoya da mukai tafiyar tare.

Nagode, nagode, nagode irin trillions trillions trillions ɗinan da haɗin kai da
ɗunbin soyayyar da kuka nunamin akan wannan littafi. Alkairin ALLAH da rahamarsa su
tabbata a gareku a duk inda kuke.

Duk wanda na ɓatama rai a yayin rubuta wannan Littafin ya gafarceni dan ALLAH, nima
kuma na yafema duk wanda ya ɓatamin😭🙏🏻😍😍😍😘😘.

inajin kewarku tun yanzu, sai dai kuma nasan insha ALLAH zamu haɗu a ZAFAFA 2021🤗.

Masoya na Telegram, Wattpad, Facebook, WhatsApp dama duk wata manhaja da wannan
littafi ya leƙa ina muku fatan alkairi da sake miƙa godiya a gareku.

Zakuga ba'a sake kawo maganar Jazuga da gidan ƴan lesbians ba. Haka rayuwa take,
wani yakan shigo rayuwarkane bisa ZAREN ƘADDARA bawai sai kaga wani abu daga
gareaaba daga baya, mutane da yawa sukan shigo rayuwarmu su taka rawa, walau
alkairi ko sharri, daga baya kuma saisu ɓace mana ɓat komu mu ɓace musu. Alka
gafarta mana😭🙏🏻.

Sai mun haɗu a ZAFAFA BIYAR 2021, karku bari a baku labari, dan aumafa sunzo da
ɗunbin sabon salo mai birgewa ta musamman, bazance muku komaiba akai sai mun fara
sakin ɗanɗanon free pages😋 zaku tabbatar da hakan. Masoya ku garzaya kar a baku
labari, dan idan babuku muma babu mu ai😪🚶🏻.

Taku Bilyn Abdull ce🤗.

Insha ALLAH bayan sallah sannan an gama zafafa zamu sake dasa free book mai daɗi😉💃
🏻😍😍😍
Ina fatan yanzu kowa ya fahimci ƙaddarar jini a cikin jini da zai zama jini🤗.

Shahudah, Bilkisu, sun haɗu akan son abu guda, Jawaad, wanda kuma ya kasance
jininsune su duka. Ga kuma

Ya rabbi ka gafartama iyayenmu damu baki ɗaya🙏🏻😭

[2/17, 9:22 AM] HASNA: __________________


ZAFAFA 2021
_______________

Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

Hafsat miss xoxo🥰


KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
Page 62

....................Wani irin tsuma jikin Jay ya keyi irin wanda kowama bai taɓa
ganiba, idanunsa sunyi masifar rinewa abun tsoro, duk wata gaɓa ta jikinsa ta sake
buɗewa, ƙwanjinsa ya kumbura hakama jijiyoyin kansa dana dukkan sassan jikin nasa.
Da sauri Alhaji babba daya fahimci komai zai iya faruwa a wajen dan yasan wanene
jikansa da zafin zuciyarsa. yay azamar riƙo Jay ya rungume a jikinsa, duk da neman
ƙwacewa da ya keyi bai sakesaba. sai ma taimaka ma Alhaji babba da Uncle Sulaiman
yay suka danne Jawaad ɗin yanda bazai iya tashiba duk yanda yaso hakan. Kuka kawai
ya fashe dashi dan zuciyarsa tai masifar kaiwa maƙura, Alhaji babba ma kuka ya
keyi. ya kalli su Dad yana faɗin, “Amma Ali ka cuceni, yanzu kunsan da wannan
zaluncin da kuka aikata amma harka iya zuwa neman auren Rahmah a wajena?”.
Cike da tashin hankali da tsoron Jawaad dake a cikin idanunsu ƙarara Dad
yace, “Munyi hakane domin rufe sirrinmu, dan bayan mun gama aikata abinda
bokanyarmu tace ga Abdul-aziz sai kawai mukaci karo da Rahama da Bilkisu a bazata
duk suna kallonmu ashe, duk da munsan asirin dake tattare damu bazai bari su iya
komaiba a kanmu hakan bai hana hankalinmu mummunan tashi ba, a take muka aika ɗan
aike wajen bokanya, mukuma mukabi ayarin masu kukan mutuwa da jimami. Kafin a gama
kammala haɗa gawar Abdul-aziz muka sake samun ɗan saƙo daga bokanya akan bilkisu da
Rahmah. andai rufe bakin Rahmah kamar yanda bokanya ta faɗa har abada bazata sake
tuna abindama ta ganiba balle wani ma yaji daga gareta, Bilkisu kuwa babu yanda
za'ai bakinta ya rufu sai dai ta haukace, hakan kuma bazai tabbata ba sai idan data
farka za'a bata ruwan tsafin da bokanya ta aiko dashi. Musan mu bazai yuwu muyi
hakaba, dan haka Nasir ya kawo dabarar zuwa ga Humaira (Mom) da Mama (Mama Atika)
dan ya sakasu suyi mana wannan aikin ta hanyar daya dace tunda suma akwai nasu
burin akan dukiyar Abdul-aziz........”
Kuka mama atika da Mom suka fashe dashi. mama Atika tace, “Wlhy ALLAH ne
shaidarmu baku sanar mana akan hakan zakuyima Bilkisu asiri ba, Nasir ya samemu
lokacin da aketa shirin fita da gawar Abdul-aziz, mukuma isowarmu kenanma babu
jimawa. Yace muyi ƙoƙarin bama bilkisu ruwan maganin, ta hakane kawai zamu sami
damar mallake duka dukiyar da Abdul-aziz ya tar.......” sai kuma ta kasa ƙarasawa
ta fashe da matsanancin kuka. Uncle Nasir ya kalleta shima yana kukan,
“Ki ƙarasa mana mama, ai duk kece silar komai, kece kike mana huɗuba akan
karmu yarda kowa ya fimu a ƴaƴan baba, kece kika saka ƙiyayyar Abdul-aziz a ranmu,
a cewarki an auro uwarsa a bayan baya amma ɗanta yazo yafi kowa arziƙi a gidan
harda ƴaƴanki, bayan kuma mune ya dace muyi wannan arziƙin saboda kece matar baba
ta farko, mukuma mune ƴaƴan farko a gidan. A dalilin wannan huɗubar taki na jefa
kaina a halaka, tun bana ɗaukar huɗubar Alhaji Ali da Alhaji Sadi har suka fara
tasiri a raina, nidai burina kullum na wuce Abdul-aziz arziƙi dan na faranta miki
rai. hakan yasa duk muguntar dasu Alhaji Sadi suka kawo shawarar a aikatama Abdul-
aziz na dinga biye musu, har takai sunyi ƙokarin jawo Abdul-aziz cikin tafiyarmu,
dan har wajen bokanya an kaisa da yaudarar zata bashi maganin sammune saboda
magautan siyasa. Ko'a hakanma saida ya tirje, nine naita lallaɓarsa harya amince ya
bimu, koda yaje yaga abinda muke nufin ɗorasa a take ya bijire mana ya kuma nuna
ɓacin ransa mai tsanani akan hakan. Sai dai zukatanmu sun rigada sun bushe a
lokacin. gani muke kamar zai tona mana asirine. dan haka muka gaza ƙyale rayuwarsa
ta huta, duk wani burinsa na aikata alkairi ga talakawansa mun daƙilesa ta hanyar
asiri da muzgunama rayuwarsa, kowane aiki munyi bake-bake a kansa tare da handame
dukiyar da aka keɓe danyin ayyukan, daga ƙarshema bokanya ta bamu tabbacin jinin
Abdul-aziz zai taimaki tafiyarmu, dan haka muyi amfani dashi, kafin hakan kuma
dolene muyi fasiƙanci dashi. Jinin Abdul-aziz shine jini na farko da muka fara
salwantarwa, dan da duk abinda zamuyi na tsafi da jinin dabbobi mukeyi. Amma
nasarar da muka samu da jinin Abdul-aziz yasa burikanmu sake faɗaɗa, muka fara
sadaukar da makusantanmu. Mama da humaira sune suka ɗurama Bilkisu maganin da
bokanya ta bamu bisa taimakon Uwaisu, mukuma lokacin mun tafi bizne gawar Abdul-
aziz.
Sanda muka dawo mun iske bilkisu cikin hauka tuburan, hakan ba ƙaramin
daɗi yay manaba kuwa, dan asirinmu kam dai munsan ya rufu kenan. Ni na bada babbar
ƴata kamar yanda bokanya ta sharɗanta mana, na kuma bada na Mama (Mama Atika) sai
dai bokanya tace ba'a lokacin take buƙatar Mama ba, dan tana hango zatai mana
amfani sosai a tafiyarmu, haka na musanya jinin Mama dana Mama Suwaiba da Mama
Maryam, na kuma haɗa da matata ta farko. Shima Alhaji Ali aka buƙaci ya kawo, shi a
take ya bada na Mamansa da ƙanwarsa, da ɗansa na biyu, sai dai kuma nace bai isa ya
bada na ƴar uwataba (Mom), wannan dalilin yasa ƙungiya tai masa lamuni akace ya
bada na wata matar idan yanada ita, kokuma ya ƙara aure, sai kuma jinin ƴarsa babba
mace shima. Hankalinsa ya tashi dan yana tsananin son Shahudah, a lokacinma batafi
shekara huɗu da wata bakwai da haihuwaba, yayta roƙo da neman alfarma akan zai
canja da wani. Da farko Bokanya bata amince ba, sai bayan kusan kwana biyu dayin
hakan ta bashi umarni akan ya auri Rahmah, hakan shine kawai zai kawo sake rufuwar
asirinmu, sannan idan Shahudah ta girma yay ƙoƙarin haɗata aure da Jawaad, nanma
zamuci moriyar hakan, indai ya aikata haka ƴarsa zata tsira da matarsa, idan Rahmah
da ta haihu sai ya bada duk abinda ta haifa madadin Shahudah. Da wannan shawara da
umarni yay amfani, na shige masa gaba ya samu auren Rahma ta wajen mahaifinta, dan
lokacin Mama Maryam ta rasu. Tabbas badan baƙin asirin da mukaima Rahma ba bazata
taba yarda ta auri Ali ba, duk da kuwa abinda ya faru kusan shekara bakwai a
lokacin, amma bata da wani zaɓi, dan ta ko'ina mun gama ƙulleta.
Kafin auren Rahma da Ali ya tattara su Humaira ya bar ƙasar dasu, wannan duk
yana cikin dabarun karta tada hankalintane akan za'ai mata kishiya, shi kuma Ali
yana matuƙar sonta bayason tashin hankalinta. Sai da ya maidasu da kusan wata biyar
sannan akai bikin, lokacin Bilkisu ta gudu daga gida saboda asirin da muka kuma
tafka mata aka kai gidan Alhaji Kokino, burinmu haukanta ya nisan tata da gida har
abada koda ƙasar waje ne ma taje. Badan Ali nason Rahma ya aura ba. bayan bikinsa
da Rahmah itama ya ɗauketa daga ƙasar ya maidata Ghana da zama duk a cikin
shirinmu, sai dai kuma acan ɗin saita gamu da wata ƙawa data tsaya tsayin daka
wajen taimakonta da addu'oi ganin kamar batama cikin hayyacinta a rayuwar aurenta
da Ali. ba komai yaja hakanba sai ganin yanda Ali ke gallaza mata, bata taɓa
yunƙurin barinsa ba ko faɗama ƴan uwanta, sai dai tai kukanta ta share hawaye.
gashi tana zuwa ta samu ciki kuma. Ganin matarnan zata buɗe mana aiki ya sake
ɗakkota ya maido ta nan ƙasar, inda mukai zaman dakon haihuwarta....” Kuka ya sarƙe
Uncle Nasir ya kasa cigaba, sai Dad da shima ke kukanne ya cigaba da faɗin,

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

Hafsat miss xoxo🥰


KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

________________

“Tabbas na zalinci Rahama, dan a zamana da ita bata taɓa jin daɗiba
koda na awa ɗaya, daga hantara sai ƙyara da gallazawa a tsakanina da ita. Bantaɓa
bata ƴanci na matar aure ba. Abincima nakan batane tamkar wata dabbar da nake
turka, kullum cikin roƙona take daban haƙuri amma ban taɓa saurarentaba, tunda
cikinta ya cika watanni bakwai ta fahimci manufata a kansa sai hankalinta ya sake
tashi, zuciyarta ta bushe, ta daina kuka akan dukkan gallazawar da nake mata, ta
maida hankalinta wajen addu'oi akan ALLAH yakare mata cikinta, ƴan uwanta duk wanda
yazo wajenta ko ƴan uwana roƙonta shine su tayata addu'a ta haihu lafiya. Daga
randa na fahimci haka saina hana kowa shigowa gidan har ƴan uwana, na saka maigadin
da babu wanda yake bari ya shiga saida izini na. Hakan ya ƙara saka Rahma a ƙunci
da damuwa, nikam ko'a jikina ban taɓa jin tausayintaba, burina kawai ta haihu na
samu cikar burina. A wannan halin cikinta ya cika watanni tara da wasu kwanaki,
haihuwa kawai muke saurare, bana yarda nai tafiya mai nisa dan karta haihu bana
nan, dama gashi na hana kowa shigowa gidan, na kuma ƙulle bakunansu da asiri har
mahaifinta da ƴan uwanta. A wani dare ta farka da naƙuda, babu ko tausayi nazo
kanta na tsaya, duk taimakon data buƙata naƙi yimata shi, haka taita wahala har
wayewar gari bata haihunba, tunanin kar abinda zata haifamin ya mutu nayi asara ya
sani shiryawa na nufi wajen bokanya ni da Nasiru, ko zamu samo wani taimakon da
zamu bata ta haihu. Lokacin da muka dawo sai muka isketa ta haihu, sai dai babu ɗan
sai ita kaɗai. Hankalinmu ya tashi, muka shiga mata tambaya sai tahau dariya da
faɗin, “UBANGIJI baya zalinci ga kowa sai dai bawa ya zalunci kansa, jinin jinina
yafi ƙarfinku azzalumai, ALLAH ya cire ƙwai a cikin ƙaya sai dai ku mutu, a yau
kuma ALLAH ya tunatar dani duk abinda kuka binne akan yah Abdull, babu shakka kuma
saina tona muku asiri, sai duniya tasan kuɗin su wanen........”
Wani wawan mari na ɗauke fuskarta da shi tare da buga kanta a bango har
saida ta suma, kafin na shureta da ƙafa ta farfaɗo, a hakanma bakinta bai mutuba,
gaya mana duk maganar da tazo bakinta takeyi, hakanne ya harzuƙamu muka kwasheta
zuwa wajen bokanya. A can ɗinma bakinta bai mutunba, ta dinga faɗa mana jininta
shine jini mafi tashin hankali da zamu salwantar, “Daga wannan ranar bazaku sake
samun kwanciyar hankaliba azzalumai, insha ALLAHU wataran sai Ƙaddara ta haɗa Jini
da jini sun addabi jininku, Jawaad da ɗiyar dana haifa da izinin UBANGIJIN al'arshi
sune zasu zamewa rayuwarku barazana da tashin hankali tun anan duniya, kuma in
ALLAH ya yarda sune sanadin tonuwar asirinku a duniya, waɗanan kwayayen guda biyu
sai sun kunna wuta bisa kanku ku ƙayoyi kun ƙone ƙurmus kafin kuje ga UBANGIJI
shima yay muku nasa hukuncin. Sai kun tuna wannan ranar da wannan furucin da izinin
ALLAH. Daga yanzu ku zauna zaman saurare da cikar lokacin da ƘWAI zai fita a cikin
ƘAYA ta inda bakuyi zato ko tsammani ba. Domin biyune zasu ɗau fansa tare da ɗunbin
al'ummah”.
Wannan shine furucin Rahma na ƙarshe a garemu, muka aikata mata mummunan aiki
tamkar yanda mukaima duk wanda muka salwantar. Duk da kuwa maganganunta sun
shigemu, kuma tabbas sunyi tasiri a zukatanmu. Iya bincike bokanya tayi ko zata
samo inda abinda Rahama ta haifa yake amma hakan ya gagara, abindama take gani
jaririyar ta mutu, tun zukatanmu na rawa akan hakan har muka cire abin a ranmu muka
cigaba da harkokin gabanmu, ciki harda aƙidar fyaɗe wa ƙananan yara domin amsar
budurcinsu kawai kamar yanda bokanya ta sharɗanta mana. Rayuwa ta shuɗa, duniya ta
samu a garemu, dan kuwa dukiya ta zauna ga kowanmu, duk abinda bokanya ta sharɗanta
mana bi mukeyi, musamman ma ni da bana tsallake komai duk dan gudun kar bokanya
tace na bada jinin mamana (Shahudah), haka kawai ALLAH ya jarabceni da matsanancin
sonta fiye da suran ƴaƴana. gashi kuma bokanya tace min akwai nasarata tattare da
ita, dama ƙungiya baki ɗaya, amma hakan bazai tabbata ba sai anyi aurensu da
Jawaad. Da wannan damar mukai amfani wajen jan Jawaad jikinmu, duk da ita Humaira
dai batasan ai nahin manufar ba, hankalinmu bai kwantaba har saida akai aurensu,
sai dai kuma baiyi nisaba komai ya lalace, a lokacin mu kaɗai mukasan a irin tashin
hankalin da muka tsinta kanmu, duk da daga baya bokanya tace mubarsu zatai wani
aiki a kansu, amma a aura masa wata matar cikin ƴaƴan family ɗinsu, hakanma zai
taimaka mana, sai dai sam Jawaad yaƙi hakan, mun buga ta kowanne fanni babu nasara,
tun daga wannan lokacin komai na ƙungiyarmu ya ringa samun tangarɗa da ruɗani, ciki
harda shigowar wani maharbi rayuwarmu, sai dai daga baya shi munyi maganinsa ta
hanyar salwantar da rayuwar duka iyalansa dashi kansa. Ƙwatsam muna a wannan
ruɗanin kuma sai ga Bilkisu ta shigo rayuwata a bazata, inda naci karo da ita a
gidan ƴar uwata. Banyi sakaciba na ɗakkota, a washe gari kuma nakai sunanta ga
bokanya kamar yanda mukeyi akan budurwar da duk muke buƙatar budurcinta, sai dai
kuma Bilkisu sai tazo da banbanci ga sauran, dan bokanya tamin alƙawarin inhar na
mallaki budurcin Bilkisu na cika dukkan sharuɗan ƙungiya, dukiyata zata sake
haɓaka, zan kuma samu nutsuwa akan komaina. Tamin alƙawura da dama game da
yarinyar, sai dai kuma komai bai yuwuba, dan yarinyar tana tattare da wasu sirruka
da muka gaza ganewa har zuwa yau, ta zama sanadin rushewar abubuwa masu yawa a
garemu ciki harda aurenta da Jawaad, tashin hankalin da muka fahimci yana tunkaromu
a dalilinta yasa muka sadaukar da jininta ita da Jawaad.........”

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

Hafsat miss xoxo🥰


KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

________________

“Babban sirrin dake tattare da ita shine amincewar UBANGIJI game da furicin
mahaifiyarta game daku”.
Wata murya ta bada amsa ga Dad a bazata. Gaba ɗaya falon suka juya suna
kallon mai maganar cike da mamaki da al'ajabi. A bazata Bilkisu ta miƙe zaram tana
share hawayenta, jikinta na wani irin tsuma da rawa tace, “Inna! Baba! Firdausi da
gaske kune? Kodai gizon da kuka saba yiminne?”.
Fuskar Baba cike da murmushi yace, “Mune ƴata ba gizo muke miki ba, mune tsaye
a gabanki bayan rabuwar ƙaddara ta tsahon shekaru, na godema UBANGIJI daya sake
haɗamu Bilkisu, na godema ALLAH daya kawoni wannan ranar dazan sauke nauyin da ɗan
uwana abokina ya ɗauramin tsahon shekaru”.
Da gudu Bilkisu ta nufesu ta rungume Inna da firdausi tana mai fashewa da
matsanancin kuka, suma kuka suka sanya harda Baba. Mai martaba ne yay gyaran muryar
da ta sakasu yin tsuru lokaci guda, cikin nutsuwa yace, “Su wanene ku? Mi kuma ya
kawoku nan?”. Kafin a cikinsu wani ya samu damar bada amsa Jabeer dake bayansu
tsaye yace, “Ranka ya daɗe suna tare da magana mai muhimmanci, tun da sassafe suke
a gidan Jay suna jira dan suga matarsa, duk korar da maigadi yaymusu basu tafiba.
Kasan yanayin da ake ciki, shinefa drivern sa ya kirani ya sanarmin, da naje
bayanin da sukaiminne yasa na gamsu na kawosu nan”.
Umarnin ƙarasawa ciki aka basu, sai da suka zauna da mika gaisuwa Bilkisu na
maƙale da inna sannan takawa ya bama baba damar yin bayani akan abinda ke tafe da
su. Baba ya sauke nannauyan numfashi yana mai duban Bilkisu da Inna ke sharema
hawaye, sai kuma ya duƙar da kansa ƙasa ya fara magana da rawar murya. “Sunana
Abdullahi, babban amini ga malam Adamu makaho. Abotarmu ta farane tun lokacin daya
kama haya a gidan da nake, tun muna iya gaisawa da mutunci sama-sama tsakanin
iyalanmu har muka zama aminai, matanmu ma haka. Kamar yanda na daɗe ban samu
haihuwa ba Adamu ma hakane, cikin hikimar ALLAH sai ga ciki a jikin matanmu kusan
lokaci guda ni da shi. Matata itace ta fara haihuwar ɗiya mace, ga tanan (ya nuna
Firdausi) dan dama ta riga matar Adamu samun ciki da kusan watanni biyu zuwa uku.
Kamar yanda al'adarmu take matata ta tafi wankan jego ƙauye, bayan tafiyarta da
kusan wata ɗaya matar Adamu ta wayi gari da naƙuda, hankalinmu ya tashi dan ba
watan haihuwarta bane, a haka muka ɗauketa zuwa asibiti, ƴan kuɗin sana'arsa ya
ƙundume ya miƙa akai mata duk abinda ya dace, sai dai daga ƙarshe likita yace sai
an mata aiki, dan ɗan dake cikinta ya ruɓe, ma'ana yadai mutu ma, barinsa itama zai
zamarwa tata rayuwar barazana. Hakan ba ƙaramin tada mana hankali ya sake yi ba,
gashi ƴan kuɗaɗen hannunmu sun ƙare, kuma suna buƙatar kuɗi kafin su mata aiki.
Adamu ya barni a asibiti ya hau acaɓa ya kaisa can anguwarsu gidan iyayensa dana
sani, dukda dai ya sanarmin mahaifiyarsa aka haifa a gidan (Alokacin Adamu na gani
da ido ɗaya fa) sai dai kuma bai wuce awa biyuba sai gashi ya dawo rai a ɓace
alamar bai samo komaiba. A gabana ya labartama Asiya komai, dukda halin ciwo da
take ciki saita kwantar masa da hankali, tace yaje wajen yayanta Alhaji Ali (Dad)
tasan zai taimaka musu. Baiyi musubu ya jani muka tafi tare, gidane katafaren gaske
mai ƙyau da gate, a lokacinma duk gidan da kaga gate to lallai maishi ya tara,
munta ƙwanƙwasawa amma ba'a buɗe mana ba, Adamu ya tura ƙofar cikin haushi sai gata
ta buɗe a bazata, sai da muka lalleƙa babu kowa sannan muka shige cikin gidan
batare da tunanin komaiba. Munta sallama a ƙofa nanma dai bamuji motsin kowaba, sai
wani irin nishi da gurnanin kuka. Babu tunanin komai Adamu ya nema cusa kansa, na
riƙesa ina girgiza masa kai akan karya aikata haka, tunda ba gidanmu baneba, kuma
akwai mace a ciki. Hankalinsa dake a tashe na halin da asiya ke a ciki yasa bai
saurareniba, ya fisge hanunsa ya shige ciki babu ko sallama. Duk da a tsorace nake
banida zaɓin daya wuce bin bayansa nima. Sanda muka shigo cikin falon sai mukaji
kukan ya yawaita, gashi ana kukan ne da addu'ar fatan neman ɗauki daga ALLAH, Adamu
ya kalleni na kallesa, sai kuma duk muka kalli ƙofar da muke jiyo kukan. Kukan
jinjiri ya sakamu dawowa a hayyacinmu batare da mun shiryaba, Adamu ya matsa jikin
ƙofar da sauri yana magana. Daga ciki aka amsa da faɗin “ko wanene ya shigo dan
ALLAH” kamar bazai shigaba sai kuma ya afka kansa tsaye, duk kiransa da nake
famanyi bai saurareniba. Haka nabisa na leƙa sai dai ban shigaba, daga ƙofa na
hango mace durƙushe tana naɗe jariri dake cikin jinin hauhuwa a zane, ita kanta
inda take durƙushen duk jinine. Adamu na tsaye hankalinsa a tashe yana kallonta.
Ɗagowa tai ta miƙa masa jinjirar jikinta na rawa, sai kuma tai cak tana kallonsa,
kallo irin na kamar na sanka kokuma ina nasanka? Da rawar baki tace, “Mai kama da
Baba!”. Sai kuma ta girgiza kai da sauri tana hawaye. “Wannan ba lokacin tunanin
hakan baneba, bawan ALLAH koma miya kawoka gidannan nasan UBANGIJI ne ya aikomin
kai danka taimaki wannan baiwa da batasan komai ba sai iskar duniya data shaƙa a
yanzun. Dan ALLAH ka ɗauketa, ka nisantata da gidannan, itaɗin ɗiyatace, mijina ke
neman kasheta saboda matsafine, kaimin alfarmar saka mata suna BILKEESU, karka taɓa
faɗa mata bakai ka haifetaba dan girman ALLAH har sai takai shekaru ashirin a
duniya, ka binciki ɗan gidan tsohon shugaban ƙasa daya rasu, JAWAAD ABDUL-AZIZ ka
haɗata dashi, ka sanar masa suɗin ƴan uwan junane, ɗiyar Rahama ƙanwar mahaifiyarsa
Bilkisu ce. Suyi ƙoƙari su haɗa hannu wajen binciken mai gidannan da duk abokan da
yake mu'amula dasu, babu isashen lokacin dazan maka bayani aka kaina da abinda ya
faru, amma nasan komin daren daɗewa lokaci zai fiddo komai dan sharri baya ɓoyuwa a
duniya. Ka ɗauki wancan akwatin akwai kuɗi da kayanta a ciki na baka halak malak,
dan ALLAH ka bata tarbiyya irin ta addini, karka bar rayuwarta ta tarwatse da
ruɗanin duniya, ka faɗa mata ina tsananin ƙaunarta fiye da komai dana mallaka a
duniyarnan. Kai maza ka fita, suna gab da dawowa, idan suka iskoka zasu halaka ka
da ita da ni baki ɗaya, ni kuma bana fatan hakan”. Ta ƙare maganar da wani irin
kuka mai cin rai da zuciya. Motsin buɗe gate da mukaji ya sakamu fita da gudu,
kafin mukai ƙofa mukaji ana shirin buɗewa, wani ɗaki muka shige da gudu muka ɓuya
muna leƙen masu shigowar ta taga, a gaban idanmu Wannan (Uncle Nasir) da wannan
(Dad) suka shiga ɗakin da matarnan take, duk maganganun da sukai ita dasu muna
saurarensu, har lokacin da suka fita da ita daga gidan. Da ga ni har Adamu kuka
muke rurus, sai dai bamu da wani ƙarfin ikon sakawa ko hanawa, sannan muna son cika
mata alƙawarin fita da ƴarta daga gidan cikin aminci. Sai da muka tabbatar motarsu
ta fice a gidan sannan muka fito muma muka fice da gudu, cikin amincin ALLAH mai
gadin gidan yanzunma bai ganmuba ya shige cikin ɗakinsa kamar ɗazun da muka shigo
yana ciki.
Da kuɗin da matarnan ta bama Adamu akaima Asiya aiki, aka cire ɗanta mara rai,
bayan an kamala mata aiki aka kaita ɗakin hutu. Adamu yakai jaririya da ya roƙa
wata nos ta gyara ya kwantar kusa da Asiya. Bayan ta farfaɗo cikin dare bai ɓoye
mata komai game da bilkisu ba, ita kuma saita amsa da daraja ta rungume tana kuka,
dan koba komai ai ɗiyar ɗan uwantane. Abinda kawai Adamu ya ɓoye ga Asiya shine ɗan
uwanta matsafine, bai faɗa mata wannanba, ya kuma roƙeni na ɓoye wannan sirrin dan
ALLAH har sai lokacin da jaririya Bilkisu takai mizanin shekarun da mahaifiyarta ta
roƙa kafin mu bayyana komai ga kowa. Na masa alƙawari da karɓar amanarsa, na rufe
wannan zance a raina tamkar yanda shima ya rufesa ga kowa nasa suka cigaba da
rainon bilkisu, har ALLAH yasa takai shekarun girma, sai dai kafin lokacin da Adamu
ya cika alƙawarin sanar mata ita wacece ALLAH yay masa rasuwa sakamakon bigesa da
mota tayi, itama kuma Asiya ALLAH yay mata rasuwa kafin shi. Musan ƴan uwan Adamu
bazasu ɗauki Bilkisu ba, dan sun saka wasiwasi a ransu game da ita tun tana
jinjira. Na ɗauki Bilkisu na cigaba da kulawa da ita kamar yanda Adamu yayta roƙona
gab da numfashinsa zaibar jikinsa. Sai dai kuma na gaza cika alƙawarin lokacin da
taƙadin yaron mai gidanmu ya shigo rayuwar gidan............” ya ƙarashe labarinsa
da zaman Jazuga a gidansu, har faruwar komai na abinda bilkisu tai musu, da maidasu
ƙauyensu da Alhaji Lado yayi, tare da gargaɗi da baza abokan Jazuga a ƙauyen suyi
gadinsu. Doguwar jiyyar Firdausi da sukasha wadda tai kamar bazata rayuba har
tsahon shekara kusan guda kafin ta warke ayi bikinta da ɗan uwanta, gashi a yanzu
sunada yara uku, Musa (Fharhan), Abbas, sai bilkisu da firdausi taima bily takwara
saboda ƙauna da soyayya haɗe da ɗunbin bege a gareta.

Jin wannan labari daga bakin Baba ya saka falon sake ruɗewa da koke-koke,
Bilkisu kuwa data gigice tamkar wadda ciwon hauka ya sama lokaci guda ta miƙe zaram
tana nuna Dad jikinta na wani bala'in karkarwa. “Baba kana nufin shine Mahaifina?”.

“Tabbas Bilkisu shine mahaifinki?”. Ai ganin Bilkisu kawai akai ƙasa wanwar
ta sume. Dad kuma ya fashe da wani irin gigitaccen kuka da ƙwalla ƙara, ya shiga
buga kansa jikin bango yana ihu maiban tashin hankali da faɗin “Tabbas Rahmah
maganar ki ta zama gaskiya, Alaƙar ƙaddarar jiji dake cikin jini ta tabbata.....”.
Ƙoƙarin riƙesa ƴansanda sukeyi, yayinda can kuma aka rufu kan Bilkisu ciki harda
Jawaad daya ƙwace daga riƙon da Alhaji Babba yay masa.

Bayyana muku tashin hankalin da waɗanan mutane ke a ciki a wannan lokaci


zaici tsahon lokaci bamu gamaba, komai ya sake hargitsewa da ruɗewa, dole ƴan-
sandan dake a waje suka shigo cikin gidan tare da dogarawan sarki wanda shi yama
rasa abin faɗa tsabar mamaki, a da gani yake babu wata ruɗaɗɗiyar rayuwa irin tasa,
sai a yau yaga wadda tafi tasa muni da tashin hankali.
Da ƙyar aka iya fita dasu Dad daga gidan, suna kuka da roƙon a yafe
musu amma babu wanda ya sauraresu, sai ma tsinuwa da sukesha daga bakin kowa harda
ƴaƴansu kansu da matansu. An shiga ƙoƙarin yayyafama waɗanda suka suma ruwa harda
Shahudah da Bilkisu, da Mama Atika. Wadda itakam da alama ma dai faɗuwar da tayi
tazo da sakamakon paralysis, dan ta gaza motsa komai nata sai ido takebin mutane da
shi kawai tana kuka.
______________

Komai fa ya sake rikicewa, gari ya ɗauki magana da ba'asan tayaya ta fita


daga gidan Alhaji babba ba, sai daga baya aka fahimci camera aka saka jikin su Dad
da ba'asan wanene ya sakaba, ta naɗe komai daya faru a gidan Alhaji babba, lokacin
da aka maidasu office kuma a take aka fidda komai ta kafafen yaɗa labarai.
Lokacin da takawa ya baro gidan Alhaji babba zuwa inda ake jiransa zasuyi
meeting da ƙyar suka kai saboda hargitsewar da garin yayi, matasa ta ko'ina sun
fara fitowa zanga-zanga da makamai akan sufa sai an basu su Dad sun kashe. Kamar
wasafa saiga zanga-zanga ta fara faɗaɗa, dan harda ƴammata da zawarawa a cewarsu
suma sunabin kadin haƙƙin ƴan uwansu dasu Dad suka lalatama rayuwa ta hanyar fyaɗe.
Idan ba'a basu su Uncle Nasir ba zasu bankama station ɗin da aka ajiyesu wuta.
Sai kuma rukunin magidanta da tasu zanga-zangar ta ɗauki manufa akan kisan
tsohon shugabanƙasa Abdul-aziz Yousif Tafida, a cewarsu sumafa sai sunbi kadin
jinin adalin shugabansu. Tofa jama'a sun fusata ainun, kowane titi ka zagaya mutane
ke tittiɗowa zuwa station ɗinsu Jawaad da aka ajiye su Alhaji Kokino, tun jami'an
tsaro na ƙoƙarin kwantar da tarzomar dake nemans harfa al'amarin ya nema gagararsu
sai da aka kawo wasu jami'an tsaron kala-kala. Amma duk da haka al'amarin ya
gagara. daga ƙarshema sai suka zagaye hall ɗin dasu Takawa sukai zaman meeting,
acewarsu su fito su bada damar a fiddo musu dasu Kokino kokuma su haɗa dasu. Dan
bazasu taɓa yarda sai ankai su Dad Kotu ba, su duk duniya basuga alƙalin da zai iya
yima su Dad shari'a ba sam. Gara kawai su kashesu a haɗu a kotun UBANGIJI kawai.

★★★★★★★

Har dare gari yaƙi lafiya, tamkarma ƙara ƴan zanga-zangar akeyi. Jawaad na
gida tare da ƴan uwansa dake cike da ruɗani da tashin hankali wannan al'amari har
yanzu kira ya samesa daga office. Duk yanda yaso ƙin fitar Alhaji babba sai da ya
takurashi, acewarsa babufa yanda zasuyi, wannan al'amarin su barma ALLAH kawai
shine zaiyi maganin waɗannan mutanen bawai ƙarfinsuba ko dabararsu. Haka ya fita
jikinsa duk babu wani daɗi, ya sumbaci goshin bilkisu daketa barci yana haɗiye
hawayen da suka cika masa ido, tausayin kansu yakeji daga shi har ita, musamman ma
ita da nata al'amarin yazo a yanda basuyi zato ko tsammaniba, kenan Shahudah da
Bilkisu ubansu ɗaya fa kenan? Bilkisu jininsa ce, jini mafi kusanci da muhimmanci a
garesu, jinin wadda take da daraja a garesa, wadda ta yarda ta rasa ranta da farin
cikinta a dalilin salwantar da mahaifinsa.
Bai iya jan motarba sai Hafiz ne yazo har gida ya ɗaukesa, shi kansa halin
da yaga garin yake ciki ba ƙaramin sake tada masa da hankali al'amarin yayiba, dare
harya rufa amma mutane basu da niyya komawa gidajensu. Da ƙyar motarsu ta samu
hanyar shiga station ɗinsu.
Sun sami su Sir Ahmad cikin tsananin tashin hankali da damuwa, sune
sukaimasa bayanin yanda akai komai ya fita har jama'a sukayo wannan gangamin na
farautar rayukan su Dad. Ajiyar zuciya kawai Jawaad keta saukewa, tausayin su
Qaseem da sauran iyalan waɗanan mutane kawai yakeji, dan haka ya bada shawarar a
fita dasu Dad ta ɓarauniyar hanya abar station ɗin dasu zuwa cikin prison dasu ko
hakan zaisa a samu sassaucin da hankulan mutane.
Da wannan shawara ta Jawaad akai amfani, sannan D.G da kansa ya fita yayma
jama'a bayani daban haƙuri akan su bari suga idan ba'a yankema su Dad hukuncin daya
daceba sai su ɗauki matakin da duk sukai niyya, amma dan ALLAH yanzu su kwantar da
hankulansu kodan dare.
Da ƙyar suka amince akan safiyar gobe su farka da batun shigar su Kokino
kotu, kokuma su su ɗauki doka a hannunsu game dasu. Garin baiyi lafiyaba sai da aka
sake baza jami'an tsaro, duk yanda su Jay sukaso kwana a gidajensu yau kam ta
gagaresu, sunata kai kawo akan mutane har garin ALLAH ya waye.

_________________

Tunda na farka kallon kowa kawai nake, jinake tamkar an kwashemin


ƙwaƙwalwa da zuciya an jefar gefe, kukan zuci zanyi kona zahiri? Wane kalar tunani
zanyi akan wannan juyayyen al'amari ruɗaɗɗe? Iyayen dana tashi na gani ƙaddara ta
juyasu sun zama ba nawa ba, waɗanda ban taɓa kawowa a tunanin hankali da ƙwaƙwalwa
ba sune suka zama iyaye na gaskiya. Dad fa? Jama'a kuji wani batu tamkar a
tatsuniyiyi da hikayoyin marubuta. Ashe shiyyasa nakejinsa a raina tun lokacin dana
fara tozali dashi matsayin yayan innata? Shin murna ya kamata nayi shin kokuwa
kuka? Baƙinciki kokuwa takaicin kasancewarsa Ubana ni jininsa? Wane hukunci ya dace
dashi game da mahaifiyata da sauran al'ummar da suka cutar suka zalinta saboda son
zuciya da ƙwaɗayi da burin duniya da kayan cikinta? Anya badan kalmomin bakina
sunyi nauyin da zasu iya zama tuntuɓen harshe wajen aikata zunubiba da ban
zazzagesu ga azzalumin uba irin nawaba kodan duniya taji tasan na tsanesa. Inama
gaskiya bata fitaba na ciga da kallonsa matsayin yayan inna ba Mahaifina ba, inama
ace banga wannan ranarba Mamana ta bari yayi tsafin dani nima. Inama.... Inama.....
Inama.....?
Bilkisu ta faɗa a fili tana rushewa da matsanancin kuka mai cin zuciya.
Rungumeta Umm-Anum tayi suka cigaba da rerawa a tare. Kowa ka gani a gidan idanunsa
a kumbure babu ko ƙyan gani, su Uncle Sulaiman tun a daren jiya duk sun koma
gidansu, anan su kaɗaine zuri'ar Alhaji babba sai su firdausi kuma da Maman Yara da
tun jiya tana nan, ganinta ba ƙaramin daɗi yayma Umm-Anum ba, inda itama a wajen
maida yanda akayi ta sake buɗe komai dangane da abinda ta sani game dasu Dad ɗin da
zamanta gidan Alhaji Kokino na tsahon shekaru dan kawai ta samu damar ɗaukar
tukunyar tsafin da akaima Umm-Anum. Ganota da Alhaji Kokino yayi gameda taimakon da
suke bama Jawaad ita da ɗan ƴar uwarta Gimba, kashesa da sukayi da kamatan da
sukayi sukaita azabartarwa, harma da wasu manya-manyan sirrikansu da taji.
Nanma dai ansha kuka mai ban tausayi, tare da jera ɗunbin godiya a gareta da
addu'oin fatan alkairi. Duk yanda sukaso ganin kwanciyar hankalin bilkisu hakan ya
gagara, daga ƙarshema saita fara bleeding, a matuƙar tashin hankali aka kwasheta
zuwa asibiti, inda ta samu taimakon gaggawa a wajen Dr Bello. Jawaad baisan mike
faruwa ba saida Nabeelah ta kirasa ta sanar masa, hankali tashe kuwa ya iso
asibitin.
To cikin dai ikon ALLAH an samu damar tsaida jinin, inda Doctor yay musu
albishir da cewar cikinta na nan bai zubeba, sai dai tana buƙatar samun hutu dan
gaskiya ƙwaƙwalwarta da zuciyarta suna cikin tsagwaron ruɗani, har jininta yama
hau, idan da bama suyi gaggawar kawota asibiti ba da ba cikin kawai za'a rasaba ita
kanta zasu iyama rasatan. To amma Alhmdllh yanzu kam komai ya dai-daita, sai kawai
a jira farkowarta kuma aga abinda ALLAH zaiyi..................✍

Ku dakaceni da sauran zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu idan na kammala editing😊😍😍😘🚴
🏼.

ALLAH ka gafartama iyayenmu[2/17, 3:01 AM] +234 703 966 0069: Page 63

....................Su Jawaad basu san wainar da ake toyawaba a gari, sai iface-
iface suka dingaji da tashin hayaniya, sai kuma hayaƙi daketa turnuƙe sararin
samaniya a hankali. Sai sukaga kuma mutane nata fita daga asibitin.
Gaban Jay ya faɗi, ya zaro waya daga aljihu yay kiran Jabeer dan yaji ko
lafiya?. “Boss wlhy akwai matsala, an fito da mutanen nan daga prison za'a kaisu
kotu jama'ar gari sun tare motar sun banka mata fetur sun saka wuta. Wlhy duk yanda
jami'an tsaro sukaso tsaidawa al'amarin ya gagara, harma an raunata mana ɗan sanda
guda daketa ƙoƙarin basu kariya da roƙon mutane su kwantar da hankalinsu kotu za'a
kaisu, kuma a yau za'a yanke musu hukunci. Amma sam basu sauraresaba, saima suka
nema haɗawa dashi shima, dan acewarua shima nasune”. Innalillahi Jawaad keta ambata
zufa na keto masa a duka sassan jikinsa. Dole yabar asibitin ya nufi inda al'amarin
ke faruwa..

Wuta taci su Alhaji kokino sosai kafin ƴan kwana-kwana suzo da masu bada
taimakon gaggawa na jami'an tsaro, da ƙyar aka iya samun hanyama motar ta ƙarasa,
police kuma suka fara jefa barkonon tsohuwa, da wannan damar aka samu mutane suka
fara darewa har aka ƙarasa gasu Dad aka basu taimakon, sai dai kuma ina komai ya
gama ƙurewa, dan wutar ta cisu sosai, sunta ihu da neman taimako basu samuba.
Waɗanda basu mutunba ma da wahala ace zasu rayu, dan su Dad ko iya gane
fuskokinsuma ba'ayi sam. A haka dai aka kwasosu zuwa General hospital inda su
Bilkisu suke.
Faruwar hakan yasa aka baza jami'an tsaron sintiri a kowane titi, tare
da kafa dokar hana shiga da fita gaba ɗaya, kasuwanni da kowacce ma'aikata an
rufesu ruf an kora mutane gidajensu. Garin yayi tsit, sai gidajen redio dana tv
kawai ke aiki, anan mutane kejin halin da ake ciki.
Kafin a ƙarasa dasu Dad asibiti wasunsu suka sake mutuwa, ciki harda Uncle
Nasir kuwa. Suma dai an shiga da sune kawai, amma likitoci sunma rasa ta ina ya
kamata su fara basu taimakon daya dace, gaba ɗaya jikinsu ya sale tas, yay jazur
tamkar naman dake kusa da wuta ana masa gashi😭.
Ba ƙaramin tashin hankali su Umm-Anum suka sake shigaba da ganin su Dad, duk
da zalincin da sukaima rayuwarsu har hawaye sukai musu. Bama suba duk mai hankali
yaga wannan bahagon al'amari dolene ya shiga ruɗani mai tsanani, ya kumaji tsoron
wannan mummunar rayuwa da waɗanan mutane suka ƙirƙirar ma kawunansu. Gadai duniyar
an tara, kuɗi, mulki, zuri'a, da komai amma an ƙare da tafiya a barsu cikin tozarci
da wulaƙanci. Basu karesu daga faruwar kowanne irin bala'iba ko masifa ba, abinda
suka tara da wanda suka shuka bai hanasu mutuwaba, bai hana ƙarshensu muniba,
wannan shinefa ake kira da BA FARKON BA ƘARSHEN, yakai ɗan uwa bari murna akan
aikata mummunan aiki kuma babu abinda ya sameka, bari tinƙaho da taƙama akan kai
haƙƙin wani bai sakaka komai sai ƙiba da kwanciyar hankali, bari farin ciki kaine
sama dakowa saboda kasancewarka azzalumi, bari taƙama da tinƙahon ka tara kai babu
yanda aka iya da kai. Rage buri da hangen haramun domin kawai burge duniya ko
morarta dayin bishasha a cikinta. Daure ka nema halak komai wahalarta da ƙaracinta,
nisanta kanka daga haramun komai sauƙinta da zaƙinta. Ji tsoron UBANGIJI koda ace
baka ganinsa to shifa yana kallonka. Kiyaye ruɗin duniya dana abokan banza ka kama
ALLAH da abokan ƙwarai masu nuna maka muhimmancin tsoronsa. Ya ALLAH ka gafarta
mana, kasa muyi ƙyaƙyƙyawan ƙarshe. ya rabbi ka ɗauki rayukanmu muna masu cike da
ɗunbin tsoronka da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W)🙏🏻😭.

______________________________

Al'amura sun sake ƙwaɓewa, a gaba ɗaya kwanakin satin da suka biyo baya,
babu wani farin ciki daga jama'ama balle su Jawaad da iyalan waɗanan mutane. An
samo gawar Aunty Mah-Mah (Rahmah) a gidan Dad cikin wani akwatin tsafinsu, ashe
lokacin da suka halakata wata gawar daban suka kawo a zuwan itace, shiyyasa Dad ya
hana kowa yimata wanka shine yay mata a lokacin. To ashema ba gawarta baceba,
gawarta na nan cikin ɗakin sirrinsa da ko Mom ta rantse bai taɓa barinta ta
shigaba, ita kuma duk tunaninta bai taɓa kaiwa ga hakanba.
Abin sha'a
[2/17, 3:01 AM] +234 703 966 0069: wa da tsarkake sunan UBANGIJI gawar Rahma fes
aka sameta dukda sheɗancin da Dad ya ɗauki tsahon shekaru yanayi da ita. Fuskarta
fayau tamkar a yaune ALLAH ya ɗauki ranta. Bilkisu ta rungume gawar tana kuka abin
tausayi. Da ƙyar Jawaad ya ɗagata akan gawar shima yana nasa hawayen da baisan suna
zirarowaba. Alhaji babba kam yayi dauriya matuƙa, sai dai haɗiyar zuciya kawai
yakeyi da kukan zuci. Umm-Anum tai mata wanka aka suturtata. Ɗunbin al'umma daga
ɓangarori da dama suka sake sallatar gawar Rahama a karo na biyu, ta kuma samu
rakkiyar ɗunbin jama'a zuwa makwancinta na gaskiya.
An samo zunzurutun kuɗaɗe da kayan tsafi kala-kala da wasu abubuwan a gidan
Dad, hakama Uncle Nasir da sauran abokan sheɗancinsu irinsu Kokino. Kamfanoninsu ma
an samo abubuwa masu yawan gaske masu matuƙar tada hankali, ciki harda kayan shaye-
shaye kala-kala da tabar wuwu buhu-buhu da adadinsa ya tasarma dubu goma. Sai wasu
gurɓatattun abubuwan da bama zasu lissafuba gamai sauraro.
Ƙasa tayi tsitt, manyan dake huɗar kasuwanci dasu data abokantaka sun fito
sunata ALLAH wadai da nisanta kansu da ɓoyayyun ayyukan su Dad ɗin, komai dai ya
fito fili, anyi walƙiya ijiya taga kowa da komai. Inda aka bar iyalansu da waɗanda
aka zalunta irinsu Jay da jiyyar zukata.
Idan kaga Bilkisu a irin wannan lokacin dole ka tausaya mata, ga laulayin ciki
ga tashin hankali da damuwa, sauƙintama ƴan uwanta da mijinta kowa tattalinta yake
da burin ganin farin cikinta. Takanyi kukan jin daɗi da ganin ƴan uwanta zagaye da
ita, waɗanda ada ta rasa samu.

★★★★★★

Ɓangaren Shahudah kam ba'a cewa komai, ita babban kukanta da tashin
hankali bawai ya ta'allaƙa da halin da Dad yake ciki na halin rayuwa da mutuwa
bane, babban tashin hankalinta shine ance babu aure tsakaninta da Jay sai dai idan
sakin Bilkisu yayi kota mutu, amma bazai yuwu suyi zaman aure a ƙarƙashin miji guda
ba ita da ƴar uwarta da suke Uban ɗaya.
Hakan ba ƙaramin tada hankalinta yayiba, babu kunya babu tsoron ALLAH ta
dinga tsinema Dad da jera masa ALLAH ya isa cikin hausarta da koma fitar kirki
batayi. Ƙiri-ƙiri ta nema haukata kanta. Mom ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi
itama, da abinda ya dameta zataji kokuwa da haukar Shahudah, ko ciwon mama atika,
ko kuma nisantarsu da Qaseem yayi?. Dan tun bayan lafawar komai Qaseem ya ajiye
aiki yabar ƙasar gaba ɗaya batare da kowa ya saniba sai daga baya sukeji ta hanyar
saƙon daya bar musu.

A yanzu kam kowa burinsa Jawaad da mahaifiyarsa da ɗan uwansa su yafe musu a
wannan family, musamman ma waɗanda sukasan sun muzguna masa bisa jagorancin
makircin mama Atika da ƴaƴanta.
Dan samun lafiyar Mama Badiyya ta sake bayyana abinda ta gani Uncle
Nasir nayi a wani dare bayan ɗakunansu shinefa ya banka mata baƙin asiri itama ya
tauye rayuwarta ta koma ita ba'a duniyaba ba kuma a lahira ba😪.
Jay dai bai samu zaman sauraren kowaba, dan shi a yanzu ta matarsa ma yakeyi
da fatan samun nutsuwarta da abinda ke cikinta.

★★★★★

A kwanakin da aka cika kwana goma da sakama su Dad wuta shima ya mutu da
safe yana ihu da kururuwa kamar yanda su Uncle Nasir sukayi lokacin da suma zasu
mutu, ga wani irin kakari maiban tashin hankali, jikinsa kuma ya koma fari fat
tamkar babu jini a jiki, gashi dama wuta ta gama ɗaye fatar gaba ɗaya. Da yamma
Alhaji Kokino yabi bayansa da Abban Zuhrah, kamar yanda aka binne su Uncle Nasir
babu wanka saboda ƙunar jikinsu haka shima Dad dasu Abban Zuhrah aka haɗasu akai
musu salla aka biznesu da halinsu. Wata shari'ar dai kam lallai tafi ƙarfin alƙalan
duniya, sai dai a jiraceta daga sarkin alƙalai kuma😭🙏🏻.

Haka rayuwa take su Dad sun tafi tamkar ba'ayusuba a duniyar dagasu har
ayyukan da suka shuka, a hankali hankulan jama'a sun fara dawowa jikinsu daga
abinda ya faru, sai kuma labarai da maida yanda akayi da har yanzun sun gaza
ƙarewa. Yayinda akebin gidajen da suka bari ɗaya bayan ɗaya ana rushewa, wanda suke
ciki kuwa ana barinma iyalansu dan su sami matsugunnin rufama kansu asiri. Masu
ƙarfin imani a cikinsu kuwa sun tsame kansu daga komai na dukiyar acewarsu basa
buƙata
[2/17, 3:01 AM] +234 703 966 0069: , dan dukiyace ta tsafi, sun gwammaci su ƙare
rayuwarsu a talauci da su zauna a ƙarƙashin ikon dukiyar jinin al'umma.

BAYAN WATANNI BIYAR.

Abubuwa sun sake lafawa, harma wasu da yawa sun faffaru, ciki kuwa harda
komawar Umm-Anum Saudia tare da ƴan uwanta suka sauke faralin miƙama ALLAH godiya
daya kawo musu ƙarshen komai cikin rahamarsa da hikimarsa. Bayan kammala aikin
hajji su suka dawo ita kuma aka barta a can tare da mijinta da Anum, Anuwar dai kam
yayi uwa yayi maɗaukiya a ƙasarsa ta haihuwa, harma an ware masa ɗaki guda a gidan
Jawaad yana zaune tare dasu.

Ansha bikin Nazifa da Ummie, harma da Zuhrah da wani ɗan uwansu da yake
bala'in sonta dama abbanta ya ƙi bashi, yanzu bayan lafawar komai ya dawo, acewarsa
ai ita yakeso, kuma ba ita ta aikata abinda ya faruba babantane, a yanzukam bashi a
duniya, dukiyar daya barima sun ajiyeta ita da mahaifiyarta da ƴan uwanta.

An kumasha bikin Amina da Yah Qaseem wanda Jawaad yaje yayo biko har ƙasar da
yake, tare da zaunar dashi yay masa nasiha mai ratsa jiki, tare da bashi shawarar
ya tallafi ƴan uwansa a yanzu da mahaifiyarsu dan shine uba, ya kuma nema musu
malamin addini su koma islamiyya musamman ma Shahudah da har yanzu hankalinta bai
gama kwanciyaba dan tana masifar son Jay. Lokacin da taga cikin Bilkisu da yanda
Jawaad ke riritata ita da cikin ba ƙaramin shiga ruɗani ta sakeyiba, tasha kuka
ranar harda shiɗewa kuwa.

Batool ma ansha bikinta da Dr Bello daya dage akan shifa da gaske yanaso babu
wasa. Ganin tsakani da ALLAH yake sonta ta bashi dama ya kawo kuɗi aka gwangwaje.

Alhaji babba ma bisa takurawar Jay suka ɗaura masa aure da Maman su Amina,
da da Maman yara za'a haɗa masa ita ta roƙa arziƙi akan a barta dan ba isashshiyar
lafiyace da itaba har lokacin, tana dai lallaɓawane bisa taimakon da kulawar da
Jawaad ke bata.

Ƙungiyar su Bilkisu nata ƙara haɓaka da faɗaɗa akan daƙile fyaɗe da hukunta
duk waɗanda aka samu akan laifin. hukunci kuma mai tsananin gaske. Inda manyan
mutane da shugabanni suma suka ƙara basu goyon baya domin fata da samun damar
daƙile matsalar kodan addabar da taima al'umma.

Mama Atika bayan wahalar jinya da tasha na kusan wata huɗu itama ALLAH yay
mata rasuwa, su Mom da su Shahudah ansha kuka. Komai nasu sai ya daɗa yin sanyi
kuma, musamman ma ita da duk ƙwalisarnan yanzu babu ita, babu Dad babu dukiyar da
ake taƙama da ita.

A ɓangaren rose kam ta buga ta buga taga babu ci, mai shiga tsakanin
soyayyar Jawaad da Bilkisu sai dai ALLAH. Babu kalar ƙulle-ƙulle da munafurcin da
bataima bily ba a station ɗin sai dai babu tasiri, daga ƙarshema da Jawaad ya
ganota sai yasa akai mata transfer waje mai nisa a tsakaninsu. Wannan abu ya sakata
jin takaici harda kukanta kuwa, ballema randa taji anƙarama su bily girma da
ƙyaututtuka susucewa tayi duk da itama harda ita, a ganinta bily batakai ta
kamotaba, amma ya ta iya da abinda yafi ƙarfin wuta inji kishiyar ƙonanniya. tana
kewar jawaad ainun. dan koba komai idan tana ganinsa kusa da ita tana ɗanjin
sassauci.

______________
ZAFAFA 2021
___________

Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

Hafsat miss xoxo🥰


KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne


SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

★★★★

A gidan Iyayen gayya kuwa ai ba'a cewa komai, cikin Bilkisu da har yanzu gata
nanneda
[2/17, 3:01 AM] +234 703 966 0069: ya fito sosai, dan yana cikin wata na bakwai.
Tattali sosai take samu a wajan Jawaad da duk ahalinsuma baki ɗaya, inda aka maido
mata Nabeelah gidan tana tayata zama, gefe kuma tana shan soyayyarta da masoyinta
Anuwar.
Faruwar wannan al'amari ya sake maida bily miskilar gaske, dan ko Jawaad
ɗin idan bata gadamaba saita yini batai masa maganar data zarta gomaba. Ta ƙara
ƙwazo akan aikinta fiye da zaton mai hasashe, musamman ma da bayan lafawar abubuwa
suka samu ƙarin girma itada duk jami'an da sukaje wannan aiki a waccan rana. Saboda
cikinta dai bata fita operation, sai dai tayi ayyukan cikin gida kawai daga office.
A gefe kuma tana sake samun ƙwazo da horo a wajen mijinta, wanda a kullum cikin
sake nuna mata ƙauna da soyayya mai tsanani yake. Sam baison yaga tashin hankalinta
ko damuwarta balle fushinta. Shidai fatansa ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo masa
little Beejay kamar yanda yake faɗa a kullum.

Cikin Bilkisu nada watanni taƙwas Jawaad ya sakata ɗaukar hutun dole,
acewarsa saita haihu ƴarsa tayi ƙwari sanan. Aranar da hakan ta faru harda kukanta,
amma sai yaƙi kulatama yay kamar bai jitaba, sai Anuwar dake mata dariya shi da
Nabeelah suka koma lallashinta da lallaɓata.
Tana shiga watan haihuwa Ummah babba tace zata maidata can gidanta, dan
bazai yuwu a barta ta zauna nan babu babba tare da ita ba. Babu kunya Jawaad ya
murje idanu yace shifa bai yardaba, idan dan babbane ya amince asamo wata tsohuwar
ta zauna da ita, amma shi bai yarda matarsa tai nesa da shiba gaskiya.
Ranar Bily ta tasashi gaba ta dinga kwasar dariyar mugunta, dan kawai ta rama
abinda yay mata na sakata ɗaukar hutu a office saita shiya kaya kusan akwai huɗu na
tafiya gidan Ummah babba, aiko ya murje ido ya balbaleta da masifa kamar zai
cinyeta ɗanya jagab🤣.
Aifa ganin yanda ya harzuƙa dole Ummah babba ta janye ƙudirinta, aka samo
wata dattijuwa zata zauna dasu, ga kuma Nabeelah da Anuwar tare dasu. Ummah ƙarama
da babba kusan kullum saisunje ganinta. Hakama maman Amina, dan cikin na shiga wata
tara sai ya ƙara girma kamar wadda zata haifa ƴan biyu.

★★★★★★

A wannan ɗan tsakanin akasha bikin su Amaturrahman suma, inda Bilkisu ko sau ɗaya
bata samu leƙawaba saboda cikinta, Jay yace idan ta haihu taje taima Ummu ALLAH ya
sanya alkairi.
Bayan anyi biki an shashshare Umm-Anum da itama ta halarta da Aunty
Mahfuzah sukazo nan dansu gaisa da Alhaji babba. Randa suka cika kwana uku gidan
Alhaji babban sai sukazo nan gidan Jay duba bily, danshi kullum yana zuwa can ya
gaidasu, itako saita waya tunda bata fita sam.
Ta taresu da tsantsar farin ciki, inda sukuma suketajin tausayinta da mata
fatan sauka lafiya. Su Anuwar ne dai ke amsawa, itako kanta na a ƙasa dan kunya.
Anuwar ya kumbura fuska yana kallon Umm-Anum daketa mammatsa ma bily hannunta
daya kumbura. “Umm-Anum gaskiya nimafa amin aure, so kuke sai little tazo duniya
taga Abbanta tuzuru”.
Dariya duk suka sanya ƴan falon, banda Jay dake zaune gefen Umm-Anum yana
latsa waya, yadai ɗan ɗago ya kalli Anuwar ɗin ya zuba masa harara ya ɗauke kansa.
Sai da suka gama dariyarsu sannan ya sake kallonsa fuska babu wasa. “Kai baka da
kunya ko......?” “A'a yayanmu nifa wlhy gaskiya na faɗa, yanzu dan ALLAH little
zataji daɗine idan aka haifota ta iskeni babu aure, ita dai ai nasan tanason iske
kawunta a dattijonsa ko”. Kai kawai Jay ya girgiza ya sake ɗauke kansa, dan indai
shaƙiyancine akazo wajen Anuwar kowa ya shafama kansa lafiya, duk masifarsa kuresa
yake shima har yagaza cewa komai.
Umm-Anum da itama ke dariya yanzun tace, “To ni miye nawa, aiga mai maka auren
nan a gabanka” tai maganar tana nuna Jay. Tasowa yay ya tsuguna a gaban Jay ɗin
yana wani marairaice fuska. “Yayanmu dan ALLAH ka aurar dani kar a haifi little ina
a ƙasa” yay maganar cikin harshen nasara da haɗawa da ƴar hausar daya fara kowa
wajen Nabeelah”. Kunnensa Jay ya kama ya murɗa da ƙarfi, aiko a take yahau roƙo
daban haƙuri. su Bily kuma namasa dariya.
Cak ta tsaya daga dariyar tata jin bayanta ya riƙe, ta shiga yamutsa fuska
tanason fiskewa amma haka
[2/17, 3:01 AM] +234 703 966 0069: sa. Kallon juna muke cike da shauƙi babu mai ko
ƙiftawa, sai da naji bakinsa cikin nawa na dawo hayyacina da sauke nannauyar ajiyar
zuciya, son tureaa nake amma yaƙi bada damar hakan, na rinƙa dukan bayansa amma bai
barniba saida yayi san ransa sannan ya sakeni ya miƙe yana dariya damin gwalo.
“Dama abinda ya kawoka kenan ai” na faɗa iana ɓata fuska kamar zanyi kuka. Gwalo
yaymin dai-dai zai fita yace, “Eh naji ɗin”.
Fariya sosai nayi ina girgiza kai, na jawo ɗiyata na rungume ina sumbatarta
dajin kamar na haɗiyeta na huta dan ɗunbin son da nake mata.

BAYAN WASU SHEKARU.

Yarane kusan uku keta wasan basket ball a madaidaicin filin wasa dake
a cikin wani ƙaton gida mai ɓangarori kusan huɗu. ina tsaye a wajen kusan mintuna
huɗu saiga mata da miji sun fito daga ɗayan ɓangare na gidan, ba kowa bane face
Anuwar da Nabeelah, suma suna sanye ga j.c. ihu yaran suka fara, biyu na kiran
Abbah! Abbah! Abbah. Biyu na kiran Mamma! Mamma! Mamma!! Cikin ɗaga hannu irin na
jinjina da ɗokin isowar abokin wasa. Anuwar yaja ƴan team ɗinsa, Little Bee, da
ƙaninta na biyu Abdul-aziz suna kiransa (Awwab). Nabeelah kuma taja nata ƴan team,
ƙanwar Little bee mai bimata Maryam suna kiranta (Khairiyya) sai yaron su Anuwar
ɗin mai sunan Jawaad, suna kiransa (Khalifa). Wasansu suka fara cike da nishaɗi,
basufi mintuna talatin da farawarba sukaji horn. Maigadi dake kallonsu daga gate
yay saurin zuwa ya buɗe. Farar mota tas ta shigo gidan wadda Bily ke mazaunin
driver cikin kayan aiki, Jay na gefenta shima sanye da suit yanata faman danne-
danne a laptop.
Da gudu yaran suka nufi motar suna faɗin, Abie! Miemaa! oyoyo. Bily dake
murmushi ta kalli Jay shima ya kalleta, kafin su maida idanunsu ga yaran nasu dake
tunkarosu. Awwab da Khairiyya suka nufi sashen da bily take suka buɗe mata, Little
Bee da Khalifa kuma Jay suka buɗemawa. A tare suka fito fuskarsu ɗauke da murmushi.
Jay ya ɗaga khalifa tare da sumbatar kumatumsa, shima yaron ya sumbaci Jay ɗin yana
dariya da faɗin, “Abie i love you”. “I love you too second Jawaad” ya faɗa yana
lakace masa hanci, kafin ya duƙa ya sumbaci Little bee ƴar kimanin shekaru goma
itama. “Little BeeJay ɗina”. Fuskarta washe da murmushi sak irin na Bily tace,
“Sweet Abie na i love you” tai maganar da sumbatar hannunsa itama. Ta matsa jikinsa
ya rungumeta ta gefen hannun damarsa, na haggun kuma yana ɗauke da khalifa.
Acanma dai Awwab da khairiyya suna maƙale da Bily, saida suka gama ɗokin
ganinta sannan suka dawo wajen Abie, ya sumbacesu suma a kumatu kamar yanda yayma
su Khalifa. Kafin su Anuwar su ƙaraso suna musu barka da dawowa.
Cikin tsokana bily tace, “Iyayen da basa girma da shiriritar ƴaƴansu”. Dariya
Anuwar da Nabeelah sukayi, Jay dake murmushi shima yace, “Karki ja mana yanda muka
dawo a gajiyanen yanzu su tara mana ciwon kai suda ƴaƴansu, zomu gudu muje mu
hutama ranmu princess”. Cikin dariya Anuwar yace, “Idanma kun gudu binku zamuyi,
dan yau a falonka aka haɗa dinner. Idanu Jay ya zaro sosai. sai kuma ya ɓata fuska
yana kallon Bily cike da langaɓe kai. “Miemaa kinajifa, nidai ALLAH ban yardaba
hutawa zanyi”. Kafin bily ta bada amsa yaran suka shiga ihu da tsalle suna faɗin
suma basu yardaba a falon Abie zasuyi dinner yau”.
Ƙwafa Jay yay yana kallon Nabeelah, “Auta kece kika haɗamin wannan aikin ko,
maganar gaskiya ayi hutu na tarkataku ku tafi Saudia wajen Ummuna muma muɗan huce
gajiya da matata a gidanga. A waje dambe da ɓarayi a gida dambe da iyayen yara da
yaransu”.
Sosai Nabeelah da Anuwar ke dariya, Nabeelah tace, “ALLAH babu ruwana, Abban
Little ne”. “Kai ko?”. Jay ya faɗa yana kama kunnensa. “ALLAH da zafi Yayanmu”
Anuwar ya faɗa cikin marairaicewa yana riƙe hannun Jay. Yaran suma duk sai suka
marairaice suna faɗin, “Sorry Abie Abbanmu yanajin zafi sosai”.
Dariya Bily takeyi. Jay dake murmushi ma ya saki kunnen Anuwar ya kama hannun
matarsa suka shige dan anfara kiran sallar magrba. Kayansu yaran suka kwasa daga
mota tare da tsarabar da aka yo musu sukabi bayansu. Anuwar da Nabeelah ma suka
nufi ɓangarensu dansu watsa ruwa tu fito.✍😭🙏🏻

ALHAMDU
[2/17, 3:02 AM] +234 703 966 0069: LILLAHI ALA KULLI HALIN.

Na godema UBANGIJIN al'arshi daya bani ikon kammala wannan littafi daya jani dogon
zango, kuskure. dana tafka a cikinsa ALLAH ka yafeni, abinda nayi dai-dai ALLAH ya
haɗamu a ladan daku masoya da mukai tafiyar tare.

Nagode, nagode, nagode irin trillions trillions trillions ɗinan da haɗin kai da
ɗunbin soyayyar da kuka nunamin akan wannan littafi. Alkairin ALLAH da rahamarsa su
tabbata a gareku a duk inda kuke.

Duk wanda na ɓatama rai a yayin rubuta wannan Littafin ya gafarceni dan ALLAH, nima
kuma na yafema duk wanda ya ɓatamin😭🙏🏻😍😍😍😘😘.

inajin kewarku tun yanzu, sai dai kuma nasan insha ALLAH zamu haɗu a ZAFAFA 2021🤗.

Masoya na Telegram, Wattpad, Facebook, WhatsApp dama duk wata manhaja da wannan
littafi ya leƙa ina muku fatan alkairi da sake miƙa godiya a gareku.

Zakuga ba'a sake kawo maganar Jazuga da gidan ƴan lesbians ba. Haka rayuwa take,
wani yakan shigo rayuwarkane bisa ZAREN ƘADDARA bawai sai kaga wani abu daga
gareaaba daga baya, mutane da yawa sukan shigo rayuwarmu su taka rawa, walau
alkairi ko sharri, daga baya kuma saisu ɓace mana ɓat komu mu ɓace musu. Alka
gafarta mana😭🙏🏻.

Sai mun haɗu a ZAFAFA BIYAR 2021, karku bari a baku labari, dan aumafa sunzo da
ɗunbin sabon salo mai birgewa ta musamman, bazance muku komaiba akai sai mun fara
sakin ɗanɗanon free pages😋 zaku tabbatar da hakan. Masoya ku garzaya kar a baku
labari, dan idan babuku muma babu mu ai😪🚶🏻.

Taku Bilyn Abdull ce🤗.

Insha ALLAH bayan sallah sannan an gama zafafa zamu sake dasa free book mai daɗi😉💃
🏻😍😍😍
Ina fatan yanzu kowa ya fahimci ƙaddarar jini a cikin jini da zai zama jini🤗.

Shahudah, Bilkisu, sun haɗu akan son abu guda, Jawaad, wanda kuma ya kasance
jininsune su duka. Ga kuma

Ya rabbi ka gafartama iyayenmu damu baki ɗaya🙏🏻😭

You might also like

pFad - Phonifier reborn

Pfad - The Proxy pFad of © 2024 Garber Painting. All rights reserved.

Note: This service is not intended for secure transactions such as banking, social media, email, or purchasing. Use at your own risk. We assume no liability whatsoever for broken pages.


Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy