Maraba Da Ramadan !!!

Download as pdf or txt
Download as pdf or txt
You are on page 1of 34

MARABA DA WATAN RAMADAN

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.


Godiya ta tabbata ga ALLAH (SWT) mai kowa mai komai wanda cikin
ikonsa da yardarsa da amincewarsa na samu damar yin wannan rubutu
wanda ya shafi bayani akan Azumin Ramadan da hukunce-hukuncensa, Yabo
da salati su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (sallallahu
Alaihi Wasallam) da alayensa da sahabban sa da wadanda suka yi imani da
kyautatawa har izuwa ranar tashin alkiyama.

KWADAITARWA AKAN AZUMIN WATAN RAMADAN !!!

Hakika shari'ar musulunci ta karfafa kwadaitarwa akan azumtar watan


Ramadan tare da bayyana falalarsa da kuma daukakar darajarsa. Da ace mai
Azumi zai kasance yana da zunubai (kanana) kuma ace yawansu ya cika
sama da qasa to za a gafarta masa wannan zunubai don Albarkar wannan
ibada ta Azumi. Saboda haka zamu takaita wannan bayani akan abubuwa
guda uku domin Kwadaitarwa akan azumi, kamar haka:

1.GAFARTA ZUNUBAI: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam)


Yace:"Dukkan wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da ALLAH
kuma yana mai Neman lada, to an gafarta masa ayyukan da ya gabatar na
zunubansa" [Bukhary 4/99, Muslim Hadith No.759]

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace:" Salloli biyar da jumma'a


zuwa wata jumma'a da watan Ramadan zuwa Ramadan suna kankare
zunuban dake tsakanin su, matuqar an nisanci kaba'ira (manyan zunubai).
[Muslim 233]

2.KARBAR ADDU'A DA 'YANTARWA DAGA WUTA: Ana karbar addu'ar bayi a


watan Ramadan cikin ko wani lokaci na watan Ramadan.

Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace:"Lallai ALLAH (SWT) yana


da bayi abin 'yantawa daga wuta ko wani yini da dare na watan Ramadan,
kuma ko wani musulmi da ya roqi ALLAH yana da wata addu'a da idan yayi
ana kar6a masa" [Ahmad 2/25]
3.MAI AZUMI YANA CIKIN MASU GASKIA DA SHAHIDAI: Wani Mutum yazo
wurin Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) sai Yace: Ya Manzon
ALLAH shin ko kana ganin idan na shaida babu abun bautawa da gaskia sai
ALLAH, kuma na shaida kai Manzon ALLAH ne, kuma nayi salloli biyar na
bada zakkah kuma nayi azumin watan Ramadan kuma nayi tsayuwarsa, cikin
wani Matsayi nake? Sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace:"
cikin masu gaskiya da shahidai) [Ibn Hibban Hadith No. 19]

WAJABCIN AZUMIN WATAN RAMADAN !!!


ALLAH (SWT) Ya wajabtawa musulmi azumin watan Ramadan kamar yadda
ya wajabtawa al'ummomin da suka gabata.... [Surah ta 2 aya ta 183]

Amma farkon wajabta azumin watan Ramadan ya kasance akan zabi ne tare
da kwadaitarwa akan yinsa, saboda yin azumi abu ne mai wahala ga wadansu
sahabbai (RA) saboda haka sai aka bada za6in cewa wanda bazai yi azumi ba
to yayi (Fidya) wato duk ranar da bazai yi azumi ba ya cigar da mabuqaci
daya.

ALLAH (SWT) Yace:" kuma akan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansar
ciyar da matalauci (miskini),sai dai wanda ya qara alheri, to shine nafi alkhayri
agare shi, kuma kuyi azumi da (wahalar) shine mafi alkhayri agareku idan kun
kasance masu sani" [Surah ta 2 aya ta 184]

Amma an shafe wannan sauqin saboda ayar data zo bayanta, sahabbai biyu
wato Abdullahi dan Umar da Salmatu dan Ak'wa'u (RA) sun bada labarin cewa
ayar data zo bayan zuwan wannan aya ta shafeta. Ayar data shafeta farkon
itace:

Fadar ALLAH (SWT): "Watan Ramadana ne wanda aka sauqar da alqur'ani


acikinsa wanda ya kasance mazaunin gida daga cikinku acikin watannan to
lallai ya azumce shi" [Surah ta 2 aya ta 185]

Da fadarsa ALLAH (SWT):" Yaku wadanda suka bada gaskiya ga ALLAH da


Manzonsa an wajabta azumi akanku kamar yadda aka wajabta ma wadanda
me gabanninku, Ko zaku ji tsoron ALLAH?" [Surah ta 2 aya ta 183]

Dangane da bayanan da suka gabata na ayoyi da hadithan Manzon ALLAH


(SAW) zamu fahimci lallai azumin watan Ramadan wajibi ne akan musulmi
maza da mata baligai sai dai idan an samu wani uzuri Wanda shari'a ta yarda
da Barin azumin dominsa.
MA'ANAR AZUMI DA KUMA LOKACINSA:
AZUMI: ibada ce daga cikin cika-cikan musulunci guda biyar.

AZUMI: shine barin ci da sha da saduwa da iyali da kuma Barin dukkan


abubuwan ci, tun daga 6ullowar alfijir har Zuwa faduwar rana acikin dukkan
kwanakin watan Ramadan.

Wannan bayani yana nuna iyakancewar yinin mai azumi tun farkon yinin har
qarshensa, wato daga 6ullowar alfijir har zuwa faduwar rana da fuskantowar
dare da kuma boyuwar kaskon rana acikin shamaki. Wannan shine cikakken
lokacin fara azumi da kuma Kare sa.

ALLAH (SWT) Yace: "An halatta muku saduwa da iyalinku acikin dararen
watan Ramadana, su (iyalanku) sutura ne agare ku kuma sutura ne agare su"

Har zuwa fadansa (SWT) "kuci kuma Ku sha har sai farin silale ya bayyanar
muku daga bakin silale na alfijir, sannan Ku cika azumi zuwa dare". [Surah ta
2 aya ta 15]

Hadith yazo daga Umar ya tabbatar da iyakancewar lokacin azumi Inda Yace:
Manzon ALLAH (SAW) Yace: "idan dare ya fuskanto daga nan yini ya bada
baya daga can kuma rana ta fadi to lokacin buda baki yayi ga mai Azumi"
[Bukhary 4/671, Muslim 1101]

NIYYAR AZUMI !!!


Niyya ita ce qudurta wani abu a zuciya, wato Mutum yayi qudurin ko wani irin
aiki na ibada a zuciyarsa, domin ko wani aikin ibada baya inganta sai da
Niyya.

Manzon ALLAH (SAW) Yace: " dukkan ayyuka basa inganta sai da niyya, kuma
ana sakawa kowane Mutum da abunda yayi niyya" [Bukhary da Muslim suka
ruwaito shi Umar (RA)]

YADDA AKE YIN NIYYAR AZUMIN WATAN RAMADAN:

Bayanin malamai ya tabbatar da cewa: wajibi ne kwana da niyya a axumin


farilla na (Ramadan) wato tun kafin 6ullowar alfijir idan an tabbatar da ganin
watan Ramadan daga adilan mutane ko shugaba, ko kuma lokacin da
kwanakin watan sha'aban suka cika talatin.

A wannan lokaci ya wajaba akan duk musulmi baligi namiji ko mace suyi
niyyar azumin watan ramadan cikin dare kafin 6ullowar alfijir. Kamar Yadda
Annabi (SAW) Yace: "Wanda duk bai wayi gari da (Niyyar) azumi ba kafin alfijir
to bayi da azumi" [Nasa'i 4/196]

Da kuma fadarsa (SAW) cewa: "Wanda bai kwana da niyyar azumi ba tun da
dare to babu azuminsa' [(Tirmizi 730]

Malamai sun ce " Zuciya ita ce wurin niyya, Amma yin furuci da ita bidi'ah ne
koda kuwa mutane na ganin yin haka abu ne mai kyau. Saboda Manzon
ALLAH (SAW) da sahabbansa basu ta6a yin furuci da Niyya ba" Domin karin
bayani duba: [siffatu saumin Nabiy (SAW) shafi na 30]

GANIN WATA DA HUKUNCE- HUKUNCENSA.

Hakika ALLAH (SWT) ya sanya rana ta zama ma'auni ga bayinsa don su san
lokutan wasu ibadodi kamar Sallah. To haka kuma ya sanya Wata a matsayin
alama ta sanin lokutan wasu ibadodi na bauta masa kamar Azumi da kuma
Hajji.

ALLAH (SWT) Yace: "Suna tambayarka game da jinjirin wata kace musu, an
sanya su don mutane su San lokuta da kuma aikin Hajji" [Suratul Baqara aya
ta 189]

ALLAH (SWT) ya Sanya watanni guda 12 acikin shekara kamar Yadda Yace:
"Hakika kididdigar watan ni a wurin ALLAH guda 12 ne acikin littafin
ALLAH....." [Suratul Taubah aya ta 36]

Kuma ALLAH (SWT) daga cikin watanni 12 ya ke6ance wasu ibadodi na


musamman da ake aikatawa acikinsu. Kamar yadda Yace: "shi aikin Hajji
yana da watanni sanannu...." [Suratul Baqara aya ta 197]

Kuma ALLAH (SWT) ya fada game da Ramadan (Azumi) cewa: "Watan


Ramadana shine watan da aka sauqar da Alqur'a ni acikinsa domin shiriya ga
mutane da hujjoji da shiriya da kuma rarrabewa tsakanin gaskiya da qarya
saboda haka Kowa ya shaida anga wata daga cikin ku to ya azumce shi...."
[Suratul Baqara aya ta 185]

BAYANIN GANIN WATA DAGA MANZON ALLAH (SAW) !!!

Hakika Annabi (SAW) yayi mana bayani mai gamsarwa acikin Hadithai daban
daban kamar haka:
Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Abdullahi dan Umar (R.A) Yace: Annabi
(SAW) Yace: "Wata kamar haka yake da kuma haka" wato yana nuni da yatsun
tafin hannunshi biyu sau 3 yana nufin kwana 30. Sannan yace da kuma haka"
yana nufin kwana 29.

Yana nufin wani lokaci Wata kwana 30 ne wani lokaci kuma kwana 29.
Malaman Hadith sunyi muwafaqa akan ingancinsa.

Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Abu Hurairata (R.A) Yace: Annabi (SAW)
Yace: " kuyi Azumi idan kunga wata kuma Ku ajiye Azumi kuyi sallah idan
kunga wata, idan an kare muku ganin wata saboda wasu giragizai to sai Ku
cika qirgar sha'aban kwana 30"

ABUBUWA GUDA 2 DAKE TABBATAR DA WATAN RAMADAN !!!

1• Ganin jinjirin watan idan sama ta kasance tangaram ba abin sake hana a
ganshi na giragizai ko qura da makamantansu.

2• cika qirgan sha'aban kwana 30 idan ba a samu ganin watan ba ranar 29,
wannan yana daga cikin dalilin Hadith da ya gabata.

GAME DA GANIN WATA A WASU KASASHE !!!

Idan ganin wata ya tabbata ga wani yanki na wata qasa to ya wajaba sauran
yankuna su dauki Azumi idan sanarwa tazo musu ta hanyar da zata wajabta
musu daukar Azumi, ba' a lura da banbancin sabanin mafitar wata.

Wannan shine ra'ayin Mazhabobi guda 3 wato: Imam Abu-hanifa, Imam


Maleek da Imam Ahmad.

Amma a wajen Imam Shafi'ee sun inganta wannan hukunci ga makusanta


wannan gari kawai, idan akwai nisa tsakaninsu da inda aka ga Wata to
kowace qasa zata yi aiki da ganin watanta.

JAN HANKALI GAME DA GANIN WATA !!!

Ganin Wata ba wani Girma bane ko daraja bare ace sai sheikh ko malam
wane zasu fara ganin shi ko kuma sai qasa mai tsarki ta ganshi kafin wata
qasa ta ganshi ba, ba haka abun yake ba.

Ana iya ganin wata a America ko Isra'eela amma Saudia basu Ganshi ba.

Kafiri yana iya ganin wata, musulmi bai Ganshi ba illa dai ba'a amsar shedun
ganin wata saiga Musulmai Adilai kawai.

Domin a zamanin Annabi (SAW) an samu wani Baqauye yazo daga garinsu
yacewa: Manzon ALLAH (SAW) sunga wata da zaran Manzon ALLAH (SAW)
ya gamsu da shaidarsa a matsayinsa na musulmi sai kawai Yace Bilal (R.A)
ya bada sanarwar daukar Azumi ko kuma ajiye shi.

Saboda haka a kula musulunci Addini ne mai sauqi ga wanda ALLAH ya


sauqaqewa.

FALALAR WATAN RAMADAN MAI ALBARKA !!!


ALLAH mai girma da daukaka yace: "Waccan wata falala ce ta ALLAH yana
bayar da ita ga wanda yaso, kuma ALLAH ma'abocin daukakar falala ne mai
girma" [surah ta 62 aya ta 4]

Yana daga cikin abunda babu sa6ani a tsakanin malamai game da shi cewa
lallai watan Ramadan watane mai alkhayri da albarka wanda ALLAH ya
ke6ance shi da falala mai yawa, kamar yadda wannan bincike zai bayyana.

ALLAH mai girma da buwaya ya sauqar da littafinsa a matsayin shiriya ga


mutane da waraka ga muminai da hujjoji bayyanannu daga shiriya da kuma
rabewa (tsakanin qarya da gaskia). Yana shiryarwa zuwa ga hujja mafi qarfi
kuma da yana bayyana tafarkin shiriya. An sauqar dashi ne a daren LAILATUL
QADRI daren daraja acikin watan Ramadan mai alkhairai.

ALLAH (SWT) yana cewa: "Watan Ramadan ne wanda ALLAH ya sauqar da


Alqur'ani a cikinsa yana shiriya da rarrabewar (gaskia da qarya) to wanda ya
halarci watan daga cikin ku sai ya azumce sa....[surah ta 2 aya ta 185]

Sauqar da alqur'ani a wannan watan yana nuni ne akan falalar watan. Daure
shaidanu da rufe qofifin wuta da bude qofofin aljanna wata dalala ce da ta
ke6anci watan Ramadan.

Manzon ALLAH (SAW) Yace: "idan Ramadan tazo ana bude qofofin aljannah
kuma ana rufe qofofin wuta kuma ana daure shaidanu" [Tirmizi 682, Ibn
majah 1642 daga Abu-hurairah]
kuma duk wannan aiki ana yin sane a farkon daren watan Ramadan

Annabi (SAW) yace: "idan farkon daren watan Ramadan yazo ana daure
shaidanu da kangararrun aljanu.

Kuma ana bude qofofin Aljannah ana rufe qofofin wuta ba a bude ko wace
qofa daga cikinta, kuma ana bude qofofin aljannah ba a rufe ko wace qofa a
cikinta, sannan sai wani mai qira yayi qira (cewa): "Ya kai mai neman alkhairi
fuskanci aukin alkhayri kuma Ya kai mai neman aikata sharri ka taqaita (bari)
kar ka aikata! Kar ka aikata" kuma ko wani dare ALLAH yana 'yanta wadansu
bayi daga wuta" [Bukhary 4/97, Muslim 1079]

Haka kuma samun daren LAILATUL QADRI a watan Ramadan wata falala ce
wadda wannan watan kadai keda ita.

ALLAH (SWT) Yace:"Lallai ne mun sauqar dashi (Alqur'ani) acikin daren


LAILATUL QADRI (daren daraja). To me ya sanar da kai abunda ake cewa
LAILATUL QADRI ? Mala'iku da ruhi suna sauqa acikinsa, da izinin Ubangijinsu
saboda ko wani umurni, aminci ne shi daren har fitar alfijir" [surah ta 97 aya ta
1 zuwa ta 5]

FA'IDODIN AZUMI MAI ALBARKA !!!


in Alqur'ani da Hadithan Manzon ALLAH (SAW) sun bayyana Fa'idar Azumi da
kuma Falalarsa, kamar haka:

→SAMUN GAFARA DA LADA MAI GIRMA GA MASU AZUMI MAZA DA MATA:

ALLAH mai Girma da daukaka Yace:" lallai musulmai maza da musulmai


mata, da muminai maza da muminai mata, da masu gaskiya maza da masu
gaskiya mata, da masu haquri maza da masu haquri mata, da masu tsoron
ALLAH maza da masu tsoron ALLAH mata, da masu sadaqa maza da masu
sadaqa mata, da masu azumi maza da masu azumi mata da masu tsare farji
su maza da masu tsare farjinsu mata da masu ambaton ALLAH maza da
masu ambaton ALLAH mata,ALLAH yayi musu tattalin gafara da sakamako
mai girma" [surah ta 33 aya ta 35]

Kunga a wannan ayar azumi tazo acikinta.

→AZUMI GARKUWA NE DAGA WUTA KUMA KARIYA CE DAGA SHA'AWA:

Kamar yadda fiyayyen halitta Annabi (SAW) Yace: " ya ku taron samari wanda
duk ya samu hali daga cikinku to yayi aure, domin shine mafi runtsewa ga ido
kuma mafi kiyayewa ga farji, wanda kuma bai zamu iko ba to sai yayi Azumi
domin shi Azumi kariya ne agareshi" [Bukhary 4/109, Muslim 1400 daga Ibn
Mas'ud R.A]

Kuma Manzon ALLAH (SAW) Yace: " Babu wani Bawa da zai azumci wani yini
saboda ALLAH, face sai ALLAH ya juyar da fuskarsa daga barin wuta da
Nisan shekara saba'in" [Bukhary 6/35, Muslim Hadith mai lamba 1153]

A wani fadin nasa kuma: "Azumi garkuwa ne wanda Bawa ke kariya da ita
daga wuta" [Ahmad 3/241]

→HAKA KUMA AZUMI NA ZAMA DALILIN SHIGA ALJANNAH GA MAI YINSA:

Tunda mun San cewa azumi yana nisantar da mai yinsa daga wuta to lallai
kuma yana kusantar da mai yinsa zuwa ga aljannah.

Hadithin Abu Umamah Al-bahiliy ya tabbatar da haka yayin da Yace" sai nace
Ya Manzon ALLAH (SAW) ka shiryar dani ga wani aiki wanda zai shigar dani
aljannah, sai Manzon ALLAH (SAW) Yace na umurceka da Azumi babu tamka
agare sa" [Bukhary 4/95, Muslim 1156]

→ALLAH (SWT) YANA CIKAWA MASU AZUMI LADAR SU BA TARE DA


IYAKANCEWA BA:

Wannan wata falala ce da fa'ida mai girma wadda ta cancanci masu azumi.
Duba ga wannan hadith din:

Abu-hurayrah RA) Yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: "dukkan kyakykyawan


aiki da dan Adam yayi ana ninja masa ladar aikin har zuwa ninki goma ko
zuwa ninki 700, amma sai ALLAH (SWT) Yace: shi Azumi nawa ne kuma Ni
me sakawa a kansa"

Wannan Hadith yana tabbatar mana da cewar ALLAH ne kadai yasan yawan
ladar da mai yin azumi yake samu.

→AZUMI YANA CETON MAI YINSA A RANAR ALQIYAMA:

"Azumi da Alqur'ani suna ceton Bawa a ranar alqiyama, Azumi zai ce: Ya
Ubangijina na hana bawanka cin abinci da kuma sha'awarsa domin haka ka
bani cetonsa, Alqur'ani shima zai ce: nima na hana masa barci da dare yana
karanta ni, domin haka ka bani cetonsa, sai ALLAH ya basu ceto sai su ceci
wannan Bawa. [Ahmad 6626, Hakim 1/554]
→ALLAH (SWT) YA KEBANCE WATA KOFA DAGA KOFOFIN ALJANNAH:

Hakika ALLAH (SWT) ya ke6ance wata qofa daga cikin qofofin aljannah ga
masu azumi kuma ya ambace ta da suna "RAYYAN"

Manzon ALLAH (SAW) Yace:"lallai acikin Aljannah akwai wata qofa ana
ambatonta da Suna Rayyan, a ranar qiyama masu azumi suna Shiga ta cikinta
babu mai Shiga ta cikinta sai su, idan suka qare Shiga sai a rufe qofar, kuma
duk wanda ya Shiga ta wannan qofar za'a shayar dashi abin sha wanda bazai
sake qishin ruwa ba har'abada" [Bukhary 4/95]

→AZUMI YANA ZAMA KAFFARA: daga cikin falalar da Azumi ya kebantu


dashi ALLAH (SWT) ya Sanya shi a matsayin kaffara ne ga wasu laifuffuka.

BUDA BAKI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA

Hakika buda baki yana daga cikin Sunnar Annabi (SAW).

BUDA BAKI: shine mai Azumi ya buda baki (Yaci wani abu) idan rana ta fadi,
yini ya bada baya dare kuma ya gabato, daga wannan lokacin buda baki yayi
ga mai Azumi.

GAGGAUTA BUDA BAKI: Gaggauta buda baki yana kawo wa al'ummar


musulmi alkhayri, saboda Hadithin Sahal dan Sa'ad (RA) ya tabbatar cewa:

Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Mutane ba zasu gushe tare da alkhayri ba


matuqar suna gaggauta buda baki" [Bukhari 4/173, Muslim 1093]

Idan al'ummar Musulmi suna gaggauta buda baki to haqiqa sun wanzar da
Sunnar Annabi (SAW), Yazo a hadithin Sahal dan Sa'ad (RA) cewa: Manzon
ALLAH (SAW) Yace: "Al'ummata ba zata gushe a kan sunnata ba matuqar
bata jiran 6ullowar taurari, a wajen buda bakinta ba" [Ibn Hibban 891 ya
ruwaito shi da ingantaccen isnadi]

kuma an ruwaito Hadith daga Abu Hurayrah (RA) cewa: Manzon ALLAH
(SAW) Yace: "Addinin Musulunci ba zai gushe ba rinjayayyen addini matuqar
musulmi suna gaggauta buda baki lokacin Azumi. Saboda yahudu da nasara
suna jinqirta buda baki" [Abu-dawud 891 ya ruwaito shi da ingantaccen
isnadi]
ABUNDA YA KAMATA A BUDA BAKI DASHI:

Hakika Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana kwadaitar da al'ummarsa


akan su buda baki dabino kamar yadda yazo a Hadithin Ans dan Malik (RA)
Yace: Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana buda baki da danyen dabino
kafin yayi sallah, idan bai samu ba sai yayi da busashshe, idan bai samu ba
sai ya kamfaci ruwa, saboda shi mai tsarki mai tsarkakewa ne" [Mutane 5
suka ruwaito shi, Ibn Khuzaimah, Ibn Hibban, Hakeem sun inganta shi]

ADDU'A A WAJEN BUDA BAKI:

Ya 'Yan uwana hakika Addu'armu a wajen buda baki kar6e66iya ce, saboda
haka muyi addu'o'i muna masu sakankacewar an kar6a mana. Amma mu sani
cewa ALLAH baya kar6ar addu'ar wanda zuciyarsa rabkananniya ce mai wasa
daga ambaton ALLAH.

Abu-Hurayrah (RA) ya ruwaito Hadith cewa: Manzon ALLAH (SAW) Yace:


"Addu'o'i 3 abin kar6awa ne: Addu'ar mai Azumi, Addu'ar wanda aka zalunta,
Addu'ar matafiyi, wannan sune addu'ar da ba a mayar wa.

A wani Hadith kuma Abu-Hurayrah (RA) Yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: "
Addu'o'i 3 ba'a mayar dasu ko kuma mutum 3 ba a komar da addu'arsu:
Addu'ar mai Azumi lokacin buda baki, Addu'ar shugaba mai adalci, Addu'ar
wanda aka zalunta"

MAFIFICIYAR ADDU'A A WAJEN BUDA BAKI:

Hakika an samo daga Hadith cewa Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance duk
lokacin da zai buda baki yana cewa: "ZHABAZ ZAMA'U WABTALATIL URUQU
WA THABATAL AJRU INSHAA ALLAH"

Ma'ana "Kishirwa ta tafi, jijiyoyi sun sanyaya, ladar (ALLAH) ta tabbata in


ALLAH yaso" [Abu-dawud 2/306, Baihaqi 4/239, Hakeem 1/422]

SAHUR DA HUKUNCE HUKUNCENSA

SAHUR: Shine abincin da Musulmi ke ci a qarshen rabin kashin daren Azumi,


kafin bullowar alfijir.

Annabi (SAW) yayi umurni da sahur domin bambantawa tsakanin Azuminmu


da Azumin ma'abota littafi (Yahudu da Nasara)
Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Banbancin Azuminmu dana ma'abota littafi
(Yahudu da Nasara) shine cin abincin Sahur" (Dabarani 6127)

FALALAR YIN SAHUR:


Akwai albarka cikin yin sahur, wannan kuma yazo a hadith masu yawa, daga
cikinsu akwai Hadithin Salman (RA) Yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Ana
sanya albarka acikin abubuwa guda 3:- daga cikinsu akwai sahur" (Dabarani
6127)

Da kuma Hadithin Abu-Hurayrah (RA) Yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace:


"Lallai ALLAH (SWT) Ya sanya albarka acikin sahur"

wani Sahabin Annabi (SAW) Yace: Na shiga wurin Manzon ALLAH (SAW) a
lokacin yana sahur, sai yace: "Lallai (shi sahur) albarka ce wanda ALLAH
(SWT) Ya baku ita, kada kuyi wasa da ita" (Nasa'i 4/145, Ahmad 5/970).

Malamai sun tabbatar da cewa an so a jinqirta yin sahur sai kusan 6ullowar
alfijir, saboda Manzon ALLAH (SAW) da Zaid Bin Thabit (RA) sunyi sahur
lokacin da suka qare, sai Annabi (SAW) ya tashi zuwa sallar asuba yayi sallah.

Anas dan Malik ya ruwaito daga Zaid Bin Thabit (RA) yace: "Mun yi sahur da
Manzon ALLAH (sAW) sannan ya tashi zuwa sallah, Anas Yacewa Zaid Ibn
Thabit, daga qiran sallah zuwa sahur wani lokaci ne ke tsakaninsu? Sai Yace:
Gwargodon (Tsawon) karanta aya 50 (Hamsin)" [Bukhari 4/118, Muslim 1097]

HIKIMAR YIN SAHUR:

1•Bambanta tsakanin Azumin Musulmi dana Yahudu da Nasara.

2•Yin kyakykyawan shiri domin fuskantar Azumi da rana.

3•Sahur sunnah ce mai qarfi kamar yadda ya tabbata a Hadithai ingantattu.

HUKUNCIN YIN SAHUR: Acikin hukuncin yin sahur akwai magana kashi biyu:

1•Sashen Malamai sun tafi akan cewa Sahur Mustahabbi ne (Abin so a


shari'a) saboda Hadithai sun nuna haka:

Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Wanda duk zai yi azumi to idan yaso yayi sahur,
da wani abu" (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi)
2•Wasu Malamai sun ce Sahur Sunnah ce mai karfi, saboda Annabi (SAW) ya
fada a wani hadith cewa: "ALLAH ne da kansa ya baku shi (Sahur) kada ku
barshi" (Nasa'i 4/145, Ahmad 5/270)

Magana mafi rinjaye ita ce: Sahur Sunnar Annabi (SAW) ce mai karfi.

ABUBUWANDA AKA HALATTAWA MAI AZUMI !!!

Haqiqa saboda tausayin ALLAH (SWT) ga bayinsa, yana nufinsu da sauqi,


baya nufin ya tsananta musu, saboda haka ne ya halatta wa mai Azumi wasu
al'amura, kuma ya dauke masa laifi idan ya aikata su, ga wasu daga ciki:-

1• YIN ASWAKI GA MAI AZUMI: Aswaki yana cikin sunnar Annabawa, wanda
Annabi (SAW) yayi umurni da ita kamar yadda yace:

"Badon kar na tsanantawa al'ummata ba dana umurce su da yin Aswaki acikin


alwala" (Bukhari 2/311, Muslim 202)

Abunda wannan hadith ke nunwa shine Manzon ALLAH (SAW) bai ke6ance
mai azumi ba daga waninsa ba domin haka mai azumi da maras azumi duk
zasu iya yin aswaki a kowace alwala.

2• WAYEWAR GARIN MAI AZUMI DA JANABA: Ya kasance Annabi (SAW)


Alfijir na riskarsa alhali yana da janaba daga iyalinsa, sai yayi wanka bayan
bullowar alfijir ya cigaba da azuminsa.

Hadisin Aisha (RA) ya tabbatar da haka da kuma Hadisin Ummu Salma (RA)
sunce: "Lallai Manzon ALLAH (SAW) Alfijir yana riskarsa alhali yana mai
janaba daga iyalinsa, sannan yayi wanka, ya cigaba da azumi" (Bukhari 4/123,
Muslim 1109)

3• KURKURAN BAKI DA SHAKA RUWA: Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance


yana kurkuran bakinsa, kuma yakan shaqa ruwa yana mai azumi, sai dai yayi
hani ga mai azumi ya kai matuqa wajen wannan, saboda ya umurci wani
mutum cewa: "Ka shaqa ruwa sosai a wajen alwala sai dai, idan azumi kak yi"
(Tirmizi 3/146, Abu-dawud 2/308, Ahmad 4/32)

wannan yana tabbatar mana da cewa kada mai azumi ya kai matuka.

4• ZUBA RUWA MAI SANYI A JIKI DOMIN SANYAYA KISHIRWA: Imam Bukhari
(ALLAH Ya jiqansa) Yace acikin littafinsa:
Babi mai magana akan wankan mai Azumi, Yace: "Ibn Umar (RA) ya jiqa
tufafinsa da ruwa, sannan ya sanyasu a jikinsa yana mai azumi" (Fat-hul Bari
4/153)

Haka kuma sha'abiy ya shaiga gurin wanka yana mai azumi, kuma Hassan
(RA) yace: Babu laifi ga kurkurar baki da yin wanka ga mai Azumi.

Kuma Manzon ALLAH (SAW) Yana zubawa kansa ruwa yana mai azumi
saboda Qishirwa da tsananin zafi. (Abu-dawud 2365, Ahmad 5/376)

5• YIN KAHO: daga farko yin kaho yana cikin abubuwan da ke 6ata azumi, sai
daga baya aka shafe wannan hukunci, saboda ya tabbata daga Annabi (SAW)
cewa yayi kaho yana azumi.

Abdullahi dan Abbas (RA) Ya ruwaito cewa Lallai Manzon ALLAH (SAW) Yayi
kaho yana mai azumi. (Bukhari 4/155)

6• DANDANON ABINCI GA MAI GIRKI: wannan babu laifi a kansa ga mai


azumi sai dai da sharadin kada dandanon ya zarce cikin maqoshi. Saboda
abin da aka samo daga Abdullahi dan Abbas (RA) yace: "Babu laifi ga mai
azumi ya dandani wani abincin da ake dafawa kamar kunu ko wani abu,
matuqar dandanonsa ba zai zarce zuwa maqoshinsa ba" (Bukhari 4/154)

ABUBUWAN DA KE BATA AZUMI:


Hakika akwai abubuwa da suka wajaba dole mai azumi ya sani cewa suna
6ata Azumi. Ga wasu daga cikinsu a takaice:
.
1• CI KO SHA DA GANGAN BA TARE DA WANI UZURI BA: ALLAH (SWT) Yace:
"Kuci ku sha har sai silale fari ya bayyana gare ku da silale baqi na alfijir
sannan ku cika azumi zuwa dare..."

wannan aya tana tabbatar mana da cewa Azumi shine kamewa daga barin ci
da sha acikin lokaci kayyadadde. Da zarar mai azumi yaci ko yasha a tsakanin
6ullowar alfijir da faduwar rana, to azuminsa bata inganta ba, amma wannan
hukunci ya ke6anci ci da sha bisa ganganci.

Idan mai Azumi yaci ko yasha da mantuwa ko kuskure ko halin tilastawa to


babu komai akansa, Dalili akan haka:

Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Idan mutum yaci ko yasha da mantuwa ya


cigaba da azuminsa, ALLAH ne ya ciyar dashi" [Bukhari 4/135, Muslim 1155]
Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Lallai ALLAH Ya yafewa al'ummata kuskure da
abunda suka aikata da mantuwa da abunda aka tilasta su akai" [Hakeem
2/198]

2• GANGANCIN FITAR DA AMAI: Ma'abota Ilimi sun hadu akan cewa wanda
amai ya rinjaye shi babu komai a kansa, sai fa idan yayi shi da gangan ko
kuma yayi dalilin fitarsa, to wannan lokaci zai rama azumi, domin:

Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Duk wanda amai ya rinjaya to babu komai
akansa amma wanda ya jawo amai da kansa to zai rama azumi" [Abu-dawud
2/310, Tirmizi 3/79 daga Abu Hurairah RA]

3• JININ HAILA DA NIFAS (BIKI): idan jinin Haila yazowa mace ko jinin biki
(Nifas) acikin wani yanki na yinin Ramadan ko qarshensa, to sai taci abinci
wato tabar azumi, amma zata rama azumi bayan Ramadan, idan kuma tayi
azumi a hakan bazai amfaneta da komai ba.

Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Shin ashe ba idan mace tana haila bata sallah
kuma bata azumi ba? Muka ce eh Ya Manzon ALLAH! Sai yace: "Wannan
shine tawayar addininta"

A wata Ruwayar cewa yayi "Zata zauna kwanaki bata sallah kuma taci abinci
cikin watan azumi, wannan shine tawayar addininta" [Muslim 79/80 ya
ruwaito shi daga Ibn Umar da kuma Abu Hurayrah R.A]

4• ALLURAR DRIP WATER: wannan yana 6ata azumi wato sanyawa maras
lafiya abinci ko abinsha ta hanyar wannan allurar har ya isa zuwa uwar
hazanyarsa.

To lallai irin wannan allurar na 6ata azumi domin shigar da wani abu ne acikin
uwar hazanya ko ciki. Haka kuma allurar dake saduwa da jini tana 6ata azumi,
idan dai tana matsayin abinci ko abinsha.

(Domin karin bayani duba Hakikatus siyaam na Ibn Taymiyyah)

5• SADUWA DA IYALI (JIMA'I): Babu sa6ani a tsakanin malamai akan cewa


Jima'i yana 6ata azumi idan ya faru da ganganci, amma idan akayisa da
mantuwa, to haqiqa sashin malamai sun riskar masa da hukuncin ci da sha
da mantuwa.

Duk wanda ya 6ata azuminsa ta hanyar jima'i to lallai akwai ramako da


kaffara akansa, dalilin wannan shine:
•Abu-Hurayrah (RA) ya ruwaito cewa wani mutum yazo wurin Manzon ALLAH
(SAW) sai yace: "Ya Manzon ALLAH na halaka! Sai Manzon ALLAH (SAW)
YACE: me ya halakar da kai? Sai yace: "Na aukawa matata ne da rana a watan
Ramadan. Sai Manzon ALLAH (SAW1 yace masa ko kana iya 'Yanta baiwa?
Yace a'a, sai Manzon ALLAH (SAW) yace masa ko kana iya yin azumin wata 2
a jere? Sai yace a'a, sai MANZON Allah (saw) Yace: masa kana da abunda
zaka ciyar da matalauta 60? Sai yace a'a, sai aka zowa Manzon ALLAH (SAW)
da wani buhu acikinsa akwai dabino yace masa kaje kayi sadaka da shi, sai
mutumin yacewa Manzon ALLAH (SAW) Wanda yafi mu talauci zan baiwa? Ai
duk a fadin madina babu wanda yafi mu tsananin talauci da tsananin buqata.
Sai Manzon ALLAH (SAW) Yayi dariya har sai da haqoransa suka bayyana, sai
yace to tafi ka ciyar da iyalanka da shi" [Bukhari 11/516, Muslim 1111]

ABUBUWAN DA SUKA WAJABA MAI AZUMI YA NISANTA.

Hakika dole ne mu sani mai azumi na gaskia shine wanda dukkan ga66ansa
suke azumi tare dashi, wajen barin sa6on ALLAH, kuma ya hana cikinsa daga
dangogin abinsha da abinci, ya kare farjinsa daga jima'i kuma idan yayi
magana bazai yi wadda zata 6ata masa azuminsa ba, sai maganarsa ta zamo
mai kyau, ayyukansa su zamo kyawawa. Wannan shine azumi na haqiqa na
shari'ah.

Hakika Manzon ALLAH (SAW) Ya kwadaitar da mai azumi ga siffantuwa da


halaye nagari da kyawawan dabi'u, ya nisanci munanan halaye, da alfasha da
surutan banza, duk da kasancewar miyagun halaye an umurci musulmi ya
nisance su a kowane lokaci na rayuwarsa, sai dai hani a kansu da nisantarsu
acikin wannan wata mai Alfarma lokacin ibadar Azumi yafi tsanani domin
haka ne yake wajaba ga musulmi mai azumi ya nisanci, al'amura guda uku ya
barsu gaba daya, wadannan abubuwa basa haduwa da azumi a lokaci daya,
sune kamar haka:-

1• FADAN KARYA: wannan yana lalata azumi, kuma yana yanke ladar mai
azumi, qarshe ma, ya maida Azumi, tamkar ba ayi ba. Saboda Hadisin
Abu-Huraira (RA) Yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Duk wanda bai daina
qiran qarya ba a lokacin azumi to ALLAH (SWT) ba yi da buqatar azuminsa, ko
yaci abincinsa ko yasha abun shansa duk daya ne a wurin ALLAH (SWT).
[Bukhari 4/99]

2• MAGANAR BANZA: wannan ma ya wajaba ga dukkan musulmi, ya bar


wannan domin ya zama cikin muminai wadanda ALLAH (SWT) Ya yabe su
acikin littafinsa.

"Su Muminai idan suka shude inda ake wadannan maganganun banza
yasassu, to suna shudewa ne acikin mutuncim basa tsayawa bare har su
saurara" [Surah ta 25 aya ta 82)]

Kuma Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Ba wai manufar Azumi kamewa daga
barin cin abinci ko shan abunsha bane kawai, a'a Azumi yana nufin kamewa
daga wadancan da kuma kamewa daga maganar banza da jima'i da sauran
duk abinda zai bata shi.

Haka nan yazo cikin Hadith cewa: Idan wani ya zageka to sai kace dashi, Ni
mai Azumi ne, Ni mai Azumi ne. [Ibn khuzaimah 1996, Hakeem 1/430]

3• YIN JIMA'I ko yin abubuwa da zasu iya kaiwa ga yin jima'i kamar kallon
mace da sha'awa ko wasa da ita ko yin magana da ita mai kashe jiki (ta jin
dadi) da sauransu, duk wannan lallai ne mai azumi ya nisancesu saboda
Hadisin Abu-Hurairah (RA) da ya gabata.

SALLAR TARAWIHI (Asham)


Hakika wannan sallar sunnah ce daga cikin sunnonin Annabi (SAW), kuma an
shar'anta sallar Tarawihi acikin jama'a saboda Hadithin Aisha (RA) da tace:
"Lallai Manzon ALLAH (SAW) Ya fito wata rana a tsakiyar dare, yayi sallah a
masallaci, sai wasu mazaje suka yi koyi da sallarsa, washe gari magana ta
yadu, a wani daren sai jama'a suka taru sosai, sai Manzon ALLAH (SAW) Yayi
sallah, suka yi sallah tare dashi, washe gari kuma labari ya qara yaduwa akan
haka, a dare na uku kuma aka cika masallaci, sai Manzon ALLAH (SAW) yayi
sallarsa suka yi sallah bayansa, a dare na hudu masallaci ya kasa daukar
jama'a, Manzon ALLAH (SAW) bai fito ba sai a lokacin sallar asuba, bayan ya
qare sallar asuba tare da su sai ya fuskance su Yace: "Ban rena qoqarinku ko
matsayinku ba, amma ina jin tsoron a farlanta ta agareku ku kasa aiwatar da
ita. Al'amarin sallar Tarawihi bai gushe ba akan haka har Manzon ALLAH
(SAW) Ya rasu" [Bukhari 3/220, Muslim 761]

Manzon ALLAH (SAW) bayan tabbatar da shari'ah kuma tsoron da Annabi


yake yiwa al'ummarsa kada a wajabta musu sallar tarawihi ya gushe, domin
haka damar cigaba da tarawihi acikin jam'i ta tabbata.

Sayyidina Umar dan Khattab (RA) ya rayar da wannan sunnah kamar yadda
Abdurrahman dan Abdullah Al-kari yace: "Na fito tare da Umar Dan Khattab
(RA) zuwa masallaci a wani dare cikin Ramadan, sai g mutane warwatse
kowa yana sallah shi kadai, sai ga wasu jama'a suna sallah bayan wani
mutum, sai Umar (RA) yace: "Ina ganin cewa na hada mutanen nan ga
makaranci daya ya jagorance su sallah yafi, sannan yayi niyya sai ya hada su
da Ubayyu dan Ka'ab domin ya jaqorance su a sallar Tarawihi"

Abdurrahman Yace: "sannan na fito tare da umar a wani daren, sai ga mutane
suna sallah da sallar makarancinsu, sai Umar (RA) yace: " Madallah da
wannan aikin mai kyau wanda na qirqiro"

Sai dai yin sallar Tarawihi bayan an kwanta (tsakiyar dare) to yafi lada daga
yinta a farkon dare. Sai mutane suka kasance suna tsayuwar sallar Tarawihi a
farkon dare" .
[Bukhari 4/218,]

ADADIN RAKA'O'IN SALLAR TARAWIHI

Malamai sun yi sa6ani a adadin raka'o'in wannan sallah, amma zance mafi
dacewa da shiriyar Manzon ALLAH (SAW) shine: Lallai sallar Tarawihi Raka'a
Takwas ce ba tare da shafa'i ko wutiri ba, Abunda ke tabbatar da haka shine
Hadithin Nana Aisha (RA) tace: "Manzon ALLAH (SAW) bai kasance yana qari
a kan raka'a goma sha daya ba, a sallar sa ta dare cikin Ramadan ko waninsa"
[Bukhari 3/16, Muslim 736]

Ra'ayin Jabir Dan Abdullah (RA) yayi daidai da bayanin Aisha (RA) yayin da
yace: "Lallai Manzon ALLAH (SAW) yayi sallah raka'a takwas lokacin da ya
rayar da dare tare da mutane sannan sai yayi witiri" [Ibn Hibban 920,
Dabarani 108]

Kuma lokacin da Umar Dan Khattab (RA) ya rayar da wannan sunnah


TARAWIHI ya hada mutane da limaminsu akan raka'o'i goma sha daya (11) ne
daidai da abunda ya tabbata a sunnah ingantacce.

Imam maleek ya ruwaito da isnadi mai kyau yace: Ankar6o daga Muhammad
Dan Yusuf daga Sa'ib Dan Yazid, lallai yace: " Umar dan Khattab ya umurci
Ubayyu Dan Ka'ab da Tamimu Addaariy, suyi qiyamullaili (sallar dare) tare da
jama'a raka'a goma sha daya (11). [Muwatta maleek 1/115]

Akwai ruwayoyi da yawa ma banbanta da suka zo akan bayanin adadin sallar


tarawihi, amma dukkan wata ruwaya data zo akan sa6anin ruwayar Aisha da
Jabir (RA) ruwayoyi ne masu rauni kwarai wadanda suka sa6awa ruwayoyi
ingantattu.

A Lura cewa riko da abunda ya inganta daga Manzon ALLAH (SAW) shine
mafifici abun koyi ga al'ummah. ALLAH shine mafi sani.

FALALAR CIYAR DA MAI AZUMI !!!


Hakika ayoyin alqur'ani mai girma sun zo da kwadaitar da Musulmi akan
ciyarwa saboda ALLAH a lokacin Azumi da lokacin da bana Azumi ba, da
taimakawa matalauta da mabuqata domin yaqar talauci a tsakanin al'ummar
musulmai, kuma yin haka na qara tabbatar da 'yan uwantakar musulunci a
tsakanin musulmai. Daga cikin wadannan ayoyi akwai fadar ALLAH (SWT)
cewa:

"wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana , 6oye da bayyane, suna da


sakamakon lada a wurin Ubangijinsu kuma basu tare da kowane irin tsoro ko
baqin ciki (a ranar alqiyama) [Surah ta 2 aya ta 274]

"(Ku ciyar) daga Abunda muka fitar muku na (tsirrai) daga qasa, kada ku nufi
maras kyau acikinsa kuna ciyar dashi, alhali ku baku kar6arsa, sai in (kun
daure) kun runtse ido, ku sani ALLAH (SWT) mawadaci ne ga abinda duk zaku
ciyar kuma wanda ya cancanci yabo ne acikin ko wani hali" [Surah ta 2 aya
ta 267]

"Ba zaku samu cikakkiyar lada, har sai kun ciyar da abunda kuke so, abunda
duk kuka ciyar na alkhayri, to ALLAH Masani ne game dashi" [Surah ta 3 aya
ta 92]

"Misalin masu ciyar da dukiyoyinsu saboda ALLAH, kamar qwayar hatsi ce


wadda ta fitar da zangarniya bakwai, acikin kowace zangarniya akwai qwaya
dari, kuma ALLAH yana lullunkawa ga wanda yaso, ALLAH Mayalwaci ne,
kuma mai sani akan duk abunda kuka ciyar" [Surah ta 2 aya ta 261]

Wadannan ayoyi duk suna nuni akan falalar ciyarwa saboda ALLAH acikin
dukkan yanayi da lokuta. Ciyarwa saboda ALLAH bata ke6anta ga wani lokaci
ba, sai dai ciyarwa a wannan mafificiyar watan yafi falala.

Kamar yadda ayoyi suka gabata suna kwadaitarwa akan ciyarwa a lokacin
azumi da lokacin da bana azumi ba. Haka ma Hadithan Manzon ALLAH
(SAW) sunzo da yawa suna kwadaitarwa akan haka, daga cikinsu akwai
wadanda suka zo akan siffar ciyarwa gaba daya, akwai kuma wadanda suka
ke6anta ga watan Ramadan kawai, wanda shine muke magana a halin yanzu.

Manzon ALLAH (SAW) Yace:" Duk wanda ya ciyar da mai azumi ga budin baki,
yana da kwatankwacin ladarsa, ba tare da an tauye wani abu ba daga ladar
mai Azumin ba" [Ahmad 4/114, Tirmizi, Ibn Majah 1746]
WASU DAGA CIKIN ADDU'O'IN WANDA AKA CIYAR GA WANDA YA CIYAR
DASHI !!!

Yana da kyau ga wanda aka ciyar yayi Addu'a ga wanda ya ciyar dashi bayan
qare cin abincin, kamar yadda yazo daga Manzon ALLAH (SAW) Addu'o'in
suna da yawa amma ga kadan daga ciki:

“AFDARA INDAKUM SA’IMUNA WA AKALA DA’AMAKUMUL ABRARU,


WASALAT ALAIKUMUL MALA’IKATU.”

Ma'ana: "ALLAH Yasa masu azumi sunyi buda baki a wajenku, kuma ALLAH
Yasa nagartattun bayi sunci abincinku, kuma ALLAH yasa Mala'iku sunyi
muku addu'a"

[Abu-dawud 3/367 da Ibn Majah 1/556, da Nasa'i a cikin Amalul Yaum wal
Laila Hadith na 296-298. Albani ya inganta shi acikin Sahih Abu-dawud 2/730]

"ALLAHUMMA AD’IM MAN AD’AMNI WASKI MAN SAKANI”

Ma'ana: "Ya ALLAH! ka ciyar da wanda ya ciyar dani, ka shayar da wanda ya


shayar dani" [Muslim 3/1626]

"ALLAHUMMA BARIK LAHUM FIMA RAZAKTUHUM, WAGHFIRLAHUM


WARHAMHUM”

Ma'ana: "Ya ALLAH! Ka albarkace su acikin abunda ka azurta su dashi, kuma


ka gafarta musu, kaji kansu" [Muslim 3/1615]

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) Yace: "Aiki wanda yafi falala shine ka
shigar da murna acikin (zuciyar) dan uwanka mumini ko ka biya masa bashi
ko kaciyar dashi " [Silsilatus sahiha 1494]

A LURA CEWA: Annabi (sallallahu alaihi wasallam) Yace: "kada ku ciyar da


talakawa daga abunda Ku Baku cinsa" [Sisilatus sahiha 2426]

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) Yace: "lallai Bawa ya tabe kuma yayi
hasara idan ALLAH (SWT) bai saka masa tausayin yan Adam acikin zuciyarsa
ba" [Silsilatus sahiha 456]

AZUMIN MATAFIYI !!!


MATAFIYI: shine wanda zai tashi daga wani gari zuwa wani gari, amma a
zamanin Annabi (SAW) Matafiya suna kama hanyar tafiya ne da qafa ko akan
wata dabba, amma a wannan Zamanin Matafiya suna tafiya ne a Mota ko a
Jirgi wata motar ma hada AC.

ALLAH (SWT) Yace: "duk wanda ya kasance daga cikinku a halin rashin lafiya
ko halin tafiya to sai ya qirga kwanakin da yasha Azumi domin ya rama daga
baya, saboda ALLAH yana son sauqi gareku baya son ku da wahala ko
tsanani" [Surah ta 2 aya ta 185]

ZABI GA MATAFIYI:

Hakika Hadithai ingantattu sunzo da dama akan za6i ga matafiyi, ko yayi


azumi ko yasha bayan Ramadan ya biya.

Hamza Dan Amr Al-Aslamiyya (RA) ya kasance mai yawan azumi ne, sai ya
tambayi Manzon ALLAH (SAW) Cewa: "Shin ko ina iya yin azumi acikin halin
tafiya? Sai Manzon ALLAH (SAW) Yace masa: "Kayi Azumi idan kaga dama;
kuma ka ajiye idan kaga dama" [Bukhari 4/156, Muslim 1121]

Anas Dan Maalik ya ruwaito cewa: "Nayi tafiya tare da Manzon ALLAH (SAW)
acikin watan Ramadan, daga cikinmu akwai masu Azumi Akwai wadanda
basa azumi, kuma Manzon ALLAH (SAW) bai aibanta mai azumi akan wanda
baya azumi ba, ko wanda baya azumi akan wanda yake yi ba" [Bukhari
4/163-164, Muslim 118]

Wadannan Hadithai duk suna nuni ne akan za6i ba fifiko ba, sai dai mafi
yawan Hadithai sun nuna fifita ajiye azumi alokacin tafiya, saboda cewar da
Manzon ALLAH (SAW) Yayi: "Lallai ALLAH (SWT) yana son ayi aiki da
rangwamenSa kamar yadda yake qyamar a aikata sabonSa [Ahmad 2/108,
Ibn Hibban 2742 An kar6o daga Dan Umar R.A]

Malaman Hadith sun ruwaito cewa: Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Ba ya daga
cikin aiki mai nagarta yin azumi a lokacin tafiya" [Bukhari 4/161, Muslim
1115 An kar6o daga Jabir R.A]

Abunda Malamai suka rairaye daga Hadithan da suka gabata shine, cewa
idan Azumi zai wahalar lokacin tafiya to yinsa baya cikin nagarta, a wannan
lokacin barinsa shi yafi a wurin ALLAH da ManzonSa kamar yadda yazo a
Hadithin da ya gabata.

Idan kuma Mutum Yana iya yin Azumi ba tare da wata wahala ba, kamar
yadda Hadithin Hamza Dan Amr da Hadithin Anas Dan Maleek suka tabbatar
to babu laifi yayi azumi. ALLAH shine mafi Sani.
AZUMIN MARAR LAFIYA, MATA MASU HAILA DA MASU JININ BIKI (NIFAS),
TSOFFI, MAI CIKI DA MAI SHAYARWA A WATAN RAMADAN !!!

MARAR LAFIYA
Marar lafiya shine wanda ya kasance cikin wani yanayi na rashin lafiya wanda
ya kai bazai iya azumtar azumi ba.

Hakika ALLAH (SWT) Ya halatta wa marar lafiya ya ajiye azumi domin


tausayawa da sauqaqa ga lamarinsa, sai dai rashin lafiyar dake sa ajiye
azumi shine wanda yake cutar da maras lafiya a jikinsa, ko kuwa yin azumin
agare shi zai qara masa wata rashin lafiya ta daban ko jinqirin warkewa.

HUKUNCINSA: ALLAH (SWT) Yace: "Duk wanda ya kasance maras lafiya daga
cikinku,ko a halin tafiya to sai ya rama kwanakin da yasha azumin" [Surah ta 2
aya ta 185]

Zai ajiye azumin ya rinqa irga abunda yasha, idan ALLAH Ya bashi lafiya zai
rama bayan Ramadan, idan kuma rashin lafiya ne wanda bazai iya yin azumi
ba koda bayan Ramadan ne to zai ciyar da miskini a kowace rana. ALLAH
shine mafi sani.

MACE MAI HAILA DA JININ BIKI (NIFAS)


Ma'abota ilimi akan addini sun hadu akan cewa mai Haila da Mai Jinin Biqi
(Nifas) baya halatta agaresu su dauki azumi, sai dai su cigaba da cin
abincinsu, kuma zasu rama azumin da suka sha bayan Ramadan, sannan idan
jinin ya dauke zasu yi wankan tsarki su cigaba da sallah da Azumi.

Domin qarin bayani a koma ga littafan fiqhu akan bayanin hukunce-hukuncen


Jinin Haila da Jinin Biqi (Nifas).

TSOFFI: Tsoffi sune wadanda shekarunsu yaja ma'ana suka manyanta wanda
har yakai baza su iya azumtar azumi ba.

Abdullahi Dan Abbas (RA) Yana cewa: Tsoho da Tsohuwa wadanda basa iya
yin azumi to sai suci abincinsu a lokacin azumi, amma su rinqa ciyar da
abincin miskini kullum" [Bukhari 4505, Fat-hul Bari 8/180]

Anas Dan Maleek (RA) yace: Wata shekara ya kasa yin Azumi (domin tsufa),
domin haka sai ya tanadi daro daya na abinci, ya ciyar da miskinai 30"
[Darul-quduni 2/207 ya ruwaito shi da isnadi ingantacce]

MACE MAI CIKI DA MACE MAI SHAYARWA


Yana daga rahamar ALLAH (SWT) babba akan bayinsa masu Karfi da
raunana, rangwamen da yayi na cewa su ajiye azumi lokacin Ramadan idan
akwai wani uzuri a tare da bayinsa.

Daga cikinsu akwai mace mai ciki da mai shayarwa, kamar yadda ma'abota
ilimi suka ambata.

Alka'abi ya ruwaito Hadith cewa: "Dawakin Manzon ALLAH (SAW) sun kai
farmaki (hari) akan mu, sai nazo wurin Manzon ALLAH (SAW) na same shi
yana cin abincin rana, sai yace mani matso kaci abinci, sai nace masa azumi
nake yi, Yace to matso na baka labari akan Azumi, Lallai ALLAH (SWT) Ya
daukewa matafiya rabin sallah, ya daukewa mace mai ciki da mai shayarwa
azumi" [Tirmizi 715, Nasa'i 4/180]

HUKUNCINSU: mace mai ciki da mai shayarwa ya halatta ta ajiye azumi sai ta
ciyar, ko kuma ta rama azumin data sha bayan gushewar larurarta. ALLAH
shine mafi sani.

FIDIYA/FANSA (CIYARWA)
FIDIYA: Shine ciyar da abincin mabuqaci matalauci a kowani wuni na
Ramadan saboda rashin samun damar yin azumin ko kasa yinsa saboda
girman shekaru da sauran uzurorin shari'ah.

Asalin wannan mas'ala shine fadar ALLAH (SWT) da Yace: "Akan wadanda
basa iya yin azumi, azumi yana basu wahala, to sai suyi Fidiya (ciyarwa) wato
fansar kai, ciyar da abincin miskini daya a kullum" [Surah ta 2 aya ta 184]

Ma'abota ilimi sun samu sabani a game da wannan ayar, wasu suna ganin
shafaffiya ce, wasu kuma suna ganin ba shafaffiya bace

Dan Abbas (RA) Yace: "wannan ayah ba a shafeta ba, ta sauqa ne akan
tsofaffi masu shakaru da yawa wadanda basa iya yin azumi, sai su ciyar da
abincin miskini guda daya a kullum" [Bukhari 8/135]

Wadanda suka tafi akan cewa ayar shafaffiya ce sun kafa hujja da cewa:
akwai ayar da ta shafe ta inda ALLAH (SWT) Yace: "Duk wanda ya kasance
mazaunin gida acikin watan daga cikinku to ya azumce shi" [Surah ta 2 aya ta
185]

Imam Bukhari acikin littafinsa, Sahih Al-Bukhari a babin KITAB ATTAFSIR yabi
ra'ayin Abdullahi Dan Abbas (RA) ne wajen kawar da cewa an shafe wannan
ayar.

Magana mafi rinjaye wannan ayah an shafeta ga ma'ana: Hukuncinta dai ya


tabbata akan tsofaffi masu manyan shekaru, idan baza su iya yin azumi ba,
da kuma mata masu ciki da masu shayarwa, idan suka ji tsoro akan 'ya'yansu
sai suci abinci, kuma su ciyar da abincin miskini a kullum. [Ibn Jarud 381,
Baihaqi 4/230, Abu-dawud 2318]

WADANDA CIYARWA KO RAMAKON AZUMI YA WAJABA AKANSU:

1• Matafiyi.
2• Marar lafiya.
3• Tsoffi.
4• Mace mai ciki ko mai shayarwa.

Mu lura cewa matukar mutum zai iya rama azumin to ramawar shi yafi
alkhayri agare sa. Shi ciyarwa idan mutum bazai iya yin azumi bane aka masa
rangwame da ya ciyar. ALLAH shine mafi sani.

FALALAR KWANA GOMA (10) NA KARSHEN WATAN RAMADAN !!!

Kwanakin watan Ramadan dukkansu akwai falala acikinsu, sai dai mafi
falalarsu sune kwanaki 10 na qarshe. Saboda ayoyin Alqur'ani da Hadithai
ingantattu sun zo da bayanin falalarsu. Daga cikin falalar wadannan kwanaki
akwai:-

1• Acikinsu ne ake dacewa da daren Lailatul Qadr, ba a nemansa acikin


sauran kwanaki face acikin kwana 10 na qarshen Ramadan, saboda Hadithin
Aisha (RA) tace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Ku nemi Lailatul Qadr acikin
marar kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan" [Bukhari 4/225, Muslim
1169]

2• Lallai Manzon ALLAH (SAW) Ya himmantu kuma ya kula sosai da


wadannan kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan, saboda idan suka zo
Manzon ALLAH (SAW) Yana daura gyautonsa (damara) ya dage da ibada ya
nisanci iyalansa, yayi ta ayyukan alkhayri da Da'a zuwa ga Ubangijinsa a
Masallacinsa.

Aisha (RA) tace: "Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana yawaita qoqarin
ibada a kwanaki 10 na qarshen Ramadan, irin qoqarin da baya yin irinsa a
kwanakin da ba wadannan ba" [Muslim 1174]

3• Yana daga Falalarsa cewa duk wanda ALLAH (SWT) Ya azurta da tsayuwa
acikinsa, wato sallolin dare da raya daren ta hanyar bautar ALLAH dayi masa
Da'a, to ALLAH Ya yafe masa duk abunda ya gabatar na zunubansa da ya
aikata, kamar yadda yazo a Hadith:
Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Wanda duk yayi tsayuwar daren Lailatul Qadr
yana mai imani da ALLAH da kuma neman ladar Ubangiji to an gafarta masa
abunda ya gabatar na zunubai" [Bukhari 4/217, Muslim 759]

4• Yana daga falalar wadannan Kwanaki 10 cewa i'itikafi baya kasancewa sai
acikinsu, kamar Yadda Hadithin Aisha (RA) yazo, tace: "Lallai Manzon ALLAH
(SAW) Ya kasance yana yin i'itikafi a kwanaki 10 na qarshen watan Ramadan,
kuma haka Manzon ALLAH (SAW) Yake yi har ALLAH Ya kar6i rayuwarsa
[Bukhari 4/226, Muslim 1173]

Ya ALLAH ka bamu dacewa ka sanya mu daga cikin salihan bayinka masu


tsayuwa akan bautarka da addininka (Ameen)

I'ITIKAFI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA

I'ITIKAFI: malamai sunyi bayanin ma'anar i'itikafi cewa shine tsayuwa akan
wani abu, ta wannan ma'anar ne ake cewa wanda ya zauna masallaci yana
ibada acikinsa, wanda ya ke6e domin bautar ALLAH (SWT).

HIKIMAR YIN I'ITIKAFI: Hakika ALLAH (SWT) Ya shar'antawa bayinsa yin


i'itikafi, wanda manufar hakan ita ce komawar zuciya ga ALLAH (SWT) domin
neman kusanci da neman yardarSa, Kuma ALLAH ne ke debewa mai i'itikafi
kewa a lokacin da ya nisanci mutanen dake debe masa kewa domin zai
ke6antu ne da ambaton ALLAH, kuma haqiqa ALLAH yana son masu
ambatonsa.

ZAMAN I'ITIKAFI: ALLAH (SWT) Yace: "Kada ku yi mubashara (hada jiki) da


mata alhali kuna masu yin i'itikafi a masallatai" [Surah ta 2 aya ta 187]

I'itikafi abun so ne, wato (Mustahabbi ne) a watan Ramadan da wanin watan
Ramadan. Domin ya tabbata cewa: Manzon ALLAH (SAW) Yayi i'itikafin
kwanaki 10 na qarshen watan Shawwal" [Bukhari 4/226, Muslim 1173]

Kuma Ya tabbata cewa Umar Dan Khattab (RA) yace wa Manzon ALLAH
(SAW): "Ya Manzon ALLAH (SAW) lallai ni a lokacin jahiliyya nayi alwashin yin
i'itikafin dare daya acikin masallacin makkah. Sai Manzon ALLAH (SAW) yace
wa Umar (RA) to sai ka cika alwashin da kayi, domin haka sai Umar (RA) yaje
Makkah yayi i'itikafin dare daya a masallaci mai alfarma .[Bukhari 4/237,
Muslim 1656]

Amma mafificiyar i'itikafi shine i'itikafin watan Ramadan, saboda Hadithin


Abu-Hurayrah (RA) da yace: Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana yin
i'itikafi na kwanaki 10 acikin ko wane watan Ramadan, amma yayi i'itikafi na
kwana 20 a shekararsa ta qarshe wanda ALLAH (SWT) Ya kar6i rayuwarsa
acikinta" [Bukhari 4/225]

Aisha (RA) tace: Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana i'itikafi a kwanaki 10
na qarshen watan Ramadan har ALLAH Ya kar6i rayuwarsa" [Bukhari 4/226,
Muslim 1173]

SHARUDAN I'ITIKAFI

1. MASALLATAI: Yin i'itikafi baya inganta sai acikin masallatai. Saboda ALLAH
(SWT) Yace: "Kada ku yi mubashara da mata alhali kuna masu i'itikafi acikin
masallatai"[surah ta 2 aya ta 187]

Amma ba kowane masallaci ake i'itikafi acikinsa ba, domin yazo acikin Hadith
cewa: "Babu i'itikafi (cikakke) sai a masallatai uku" wato Masallacin Makkah,
Masallacin Qudus da Masallacin Madina" [Hadith ne ingantacce malamai sun
inganta shi]

Amma wannan Hadith ba yana kore yin i'itikafi bane acikin wanin wadannan
masallatai bane, sai dai yana kore cikar ladar i'itikafi a wani masallacin na
daban.

2. MUSULUNCI: sharadi ne mai i'itikafi ya kasance musulmi domin ba'a


kar6an i'itikafin Kafiri.

3. HANKALI: Dole ne mai i'itikafi ya zamo mai hankali domin ba a kar6ar


ibadar Mahaukaci.

4.BALAGA: Wanda zai yi i'itikafi ya zamanto mutum ne wanda


hukunce-hukuncen addinin musulunci ke gudana akansa, kuma masani akan
addini kuma masani akan i'itikafi da mas'alolinsa.

5. NIYYA: Dole ne mai i'itikafi zai tsarkake Niyyarsa domin ALLAH (SWT) Ya
zamanto ba domin Riya ba.

ABUBUWANDA SUKA HALATTA GA MAI I'ITIKAFI


1• Ya halatta ga mai 'i'itikafi ya fita daga masallaci saboda wata buqata ta
shari'ah. Saboda Aisha (RA) tace: "Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana
shigar da kansa gare ni yana i'itikafi a masallaci ina cikin dakina, na taje masa
shi, a wata Riwayar kuma "In wanke masa kansa" kuma ya kasance a lokacin
i'itikafi baya shiga cikin gida sai domin wata buqata ta dan adam" [Bukhari
1/342, Muslim 297]

2• Ya Halatta ga mai i'itikafi yayi alwala a masallaci amma alwala sassauqa,


amma yin hakan ya zama baya kawo qazanta a masallaci ko cutarwa ga
jama'a. Hadith Yazo cewa: "Manzon ALLAH (SAW) Yayi alwala sassauqa a
masallaci" [Ahmad 5/364]

3• Mai i'itikafi yana da damar sanya shimfidarsa a masallaci, dominan samu


daga Hadith, Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance idan zai shiga i'itikafi ana kai
masa shimfidarsa a masallaci, a bayan wani ginshiqi daga cikin ginshiqan
masallaci" [Ibn Majah 642]

4• Fita daga cikin Masallaci zuwa wurin wanka amma idan babu wurin wanka
a masallacin, to mai i'itikafi yana da damar zuwa duk yake domin yin wanka
saboda lalura ce. Saboda Hadithin Aisha (RA) tace: "Manzon ALLAH (SAW) Ya
kasance baya zuwa gida idan yana i'itikafi sai domin wata buqatar dan adam"
[Bukhari 1/342, Muslim 297]

ABUBUWANDA BAYA HALATTA GA MAI I'ITIKAFI


1• JIMA'I: Yin jima'i da sumbatar mace da wasa da ita baya halatta ga mai
i'itikafi da dare ko da rana, idan kuma har hakan ya faru to i'itikafin ya 6aci,
saboda hani akan wannan yazo cikin alqur'ani mai girma, ALLAH (SWT) Yana
cewa: "kada kuyi mubashara da mata alhali kuna masu i'itikafi acikin
masallatai" [Surah ta 2 aya ta 187]

2• FITA DOMIN GANIN MARAR LAFIYA: Ba ya halatta ga mai i'itikafi ya fita


zuwa ganin marar lafiya a gida ko a asibiti.

3• JANA'IZA: Ba ya halatta ga mai i'itikafi ya halarci sallar gawa sai dai idan
sallar gawar ta kasance acikin masallacin da yake i'itikafi ne to zai iya yin
sallar gawar tare da Liman. Kar ya fita sai fitar da bata da makawa, saboda
Aisha (RA) tace: "Abunda yake sunnah ga mai i'itikafi kar ya gaida marar
lafiya, kar ya halarci jana'iza (sallar gawa) kar yayi jima'i da mace, kuma kar ya
shafeta shafar jin dadi" [Abu-dawud ya fitar dashi]

4• YASASHSHIYAR MAGANA: Baya halatta ga mai i'itikafi ya shagaltu da


wasa da yasassun maganganu a lokacin ibadarsa da ko wane lokaci, saboda
Nassin AlQur'ani yayi hani akan wadannan abubuwa, kuma babu fa'ida ta
duniya ko ta lahira acikinsu.

5• GIBA DA ANNAMIMANCI: Yin giba da yawo da Annamimanci da sauransu


basa halatta ga mai i'itikafi, saboda Giba da Annamimanci Dabi'u ne wadanda
ALLAH (SWT) da Manzon ALLAH (SAW) suka haramta, kamar yadda yazo
acikin alqur'ani: [Surah ta 49 aya ta 12 da kuma Surah ta 68 aya ta 10 zuwa ta
11]

LOKUTAN YIN I'ITIKAFI

Malamai sunyi sa6ani game da mafi qarancin lokacin yin i'itikafi. Amma Mafi
Yawan malamai sun tafi akan cewa mafi qarancin i'itikafi shine dare da yini,
dalilinsu shine Hadithin Umar (RA) wanda ya gabata.

JAN HANKALI
Mutanen mu na wannan zamanin basa bawa i'itikafi muhimmanci da yawa
daga cikinsu suna tafiya masallatai da sunan i'itikafi amma sai suje suyita
qiran mutanen su a wayoyi alhali suna ikirarin suna i'itikafi wannan ba daidai
bane yin hakan wulaqanta bautar ALLAH (SWT) ne. Da wannan nake jan
hankali al'ummar musulmai idan zasu yi i'itikafi su tsarkake Niyyar su, su
gabatar dashi domin ALLAH ba tare da sanya wasa acikinsa ba..

LAILATUL QADR
LAILATUL QADR: shine Qaddararren dare, dare mai daraja mai girma, daren
alkhayri, dare mai albarka, dare ne wanda misali bazai gama rarrabe abunda
wannan dare ya qunsa ba face ALLAH (SWT) shine masani.

FALALAR DAREN LAILATUL QADR


Falalar wannan dare mai girma ce domin an shedar da sauqar al'qur'ani
acikinsa, kuma ALLAH (SWT) Ya ambace sa acikin LittafinSa a wurare
daban-daban, daga cikinsu akwai fadar ALLAH (SWT): "lallai mu muka sauqar
da shi (Alqur'ani) acikin daren Lailatul Qadr, me ya sanar da kai abunda ake
qira Lailatul Qadr, Daren Lailatul qadr yafi daraja akan wata dubu, saboda
mala'iku suna sauqa acikinsa tare da ruhu (jibril) da izinin Ubangijinsu ga
kowane al'amari, Amincin ALLAH ne wannan daren (da abinda ke cikinsa) har
6ullowar alfijir" [Surah ta 97 aya ta 1 zuwa 5]

Hakika daukakar daraja ta isa ga wannan dare na Lailatul Qadr acikin


wadannan ayoyi cewa yafi watanni dubu, Haka kuma sauqar mala'iku acikinsa
har da Mala'ika Jibrilu (AS) wata falala ce ta wannan daren. Kuma lalla akwai
daga falalar wannan dare cewa acikinsa ne ake rarrabe dukkanin al'amura
abin hukuntawa.

ALLAH (SWT) Yace: "Lallai ne mu mun sauqar da alqur'ani a cikin dare mai
albarka, lallai Mu masu gargadi ne, acikinsa ne ake rarraba dukkanin al0ura
abin hukuntawa" [Surah ta 44 aya ta 3 zuwa 6]

LOKUTAN DA AKE SAMUN DAREN LAILATUL QADR

Annabi (SAW) yace: shi wannan dare, ana samunsa a daren 21, da daren 23,
da daren 25, da daren 27 da daren 29 da daren qarshe na watan Ramadan.

Dan Umar (RA) Yace: wasu mutane daga sahabban Annabi (SAW) an nuna
musu daren Lailatul Qadar acikin barci, acikin kwana bakwai na qarshen
watan Ramadan, sai Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Ina zaton cewa mafarkinku
ta dace da kwana bakwan qarshe, saboda haka wanda ya kasance zai nemi ta
to ya neme ta acikin kwana bakwai na qarshen watan Ramadan" [Muttafaqun
Alaihi]

Mu'awiyya Dan Abu-sufyan (RA) Yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: acikin
(Lokacin ganin) Lailatul Qadari: "Daren 27 ne" Abu-Dawud ya ruwaito shi,
kuma zance mafi rinjaye Hadith ne mauqufi. Kuma lallai (Malamai) sunyi
sa6ani acikin ayyana takamammen daren a bisa zantuka arba'in.

Aisha (RA) tace: "Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana maqwabtakar


masallaci a kwana goma na qarshen Watan Ramadan, Yana cewa ku nemi
daren Lailatul Qadr a kwana Goma na qarshen watan Ramadan " [Bukhari 4
/225, Muslim 1169]

Ibn Hajar Yace: Bayan jeranta bayani akanta (Lailatul Qadr) mafi rinjayen
zance shine tana cikin marra ta Goman qarshe, kuma ita tana cancanjawa ne.
To wadannan sune Lokutan da ake samun Daren Lailatul Qadr.

ALAMAR DAREN LAILATUL QADR


Manzon ALLAH (SAW) Ya siffanta daren Lailatul Qadr cikin abunda Dan
Abbas (RA) Ya ruwaito cewa: Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Daren Lailatul
Qadr dare ne mai sauqi wanda yake a sake, ba mai zafi bane kuma ba mai
sanyi ba ne, rana tana wayuwar gari tana mai rauni (Marar zafi) mai launin ja"
[Ibn Khuzaimah 3/231]

NEMAN DACEWA DA "DAREN LAILATUL QADR"


Musulmi yana neman dacewa da wannan Dare mai albarka ta hanyoyi kamar
haka:

1• Tsayuwa da Da'a ga ALLAH yana mai imani da kuma kwadayin ladar


Ubangijinsa.
Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Wanda duk yayi tsayuwar daren Lailatul Qadr
yana mai imani da ALLAH da kuma neman ladar Ubangiji to an gafarta masa
abunda ya gabatar na zunubai" [Bukhari 4/217, Muslim 759]

2• Musulmi kan iya neman dacewa da wannan dare ta hanyar yawaita addu'a.
Aisha (RA) tace: "Ya Manzon ALLAH shin ko kana ganin idan na gane wani
dare ne Lailatu Qadr me zance acikinsa? Sai yace kice: .
ALLAHUMMA INNAKA AFUWWUN TUHIBBUL AFWA FA'AFU ANNIY"

Ma'ana: "Ya ALLAH Lallai Kai mai yafewa ne kuma kana son yafewa to ina
roqonka ka yafe min" [Tirmizi 3760, Ibn Majah 3850]

3• Raya kwana 10 na qarshen Watan Ramadan da ibada, da kuma nisantar


abubuwan sha'awa da yawaita ayyukan Da'a zuwa ga ALLAH (SWT).

Aisha (RA) tace: Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana yawaita qoqarin
ibada a kwana 10 na qarshen Watan Ramadan, irin qoqarin da baya yin irinsa
a kwanakin da ba wadannan ba" [Muslim 1174]

4• Yawaita ambaton ALLAH irin wanda aka samo daga Manzon ALLAH
(SAW) da kuma yawaita karatun Alqur'ani mai Girma da Haddarsa, da kuma
qiran mutane zuwa ga ayyukan alkhayri, dayi musu hani akan mummuna.

ZAKKAR FIDDA KAI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA !!!

ZAKKAR FIDDA KAI farilla ce, Manzon ALLAH (SAW) Ya farlanta ta akan
al'ummar musulmai baki daya, Maza da Mata babba da qarami kamar yadda
ya tabbata a Hadithin Abdullahi Dan Abbas da Kuma Hadithin Dan Umar (RA)
sunce: "Manzon ALLAH (SAW) Ya farlanta zakkar fidda kai a watan Ramadan
akan mutane" [Bukhari 3/291, Muslim 984]

WAJABCIN ZAKKAR FIDDA KAI: Zakkar fidda kai yana wajaba akan Maza da
Mata da 'ya'ya da Bayi daga cikin musulmai.

ABUNDA AKE ZAKKAR FIDDA KAI DA SHI DA ABUNDA AKE FITARWA A


ZAKKAR FIDDA KAI

Abdullahi Dan Abbas (RA) Yace: Ana fitar da wannan zakkah daga dangogin
sha'ir ko dabino ko cukui ko zabibi ko sulti"

Abu Sa'id Alkhudri (RA) Yace: "Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai
sa'i daya daga abinci, ko sa'i daya daga sha'ir, ko sa'i daya daga Dabino ko sa'i
daya daga cukui ko sa'i daya daga Zabibi" [Bukhari da Muslim suka ruwaito
shi]

Musulmi zai fitar da zakkar fidda kai ga kansa da Iyalansa, da duk wanda
ciyar dashi yake kansa. Sa'i daya ne daga galibin abincin da mutanen gari ke
amfani dashi. Ko daya daga cikin dangogin da aka ambata a baya.

Manzon ALLAH (SAW) Yace: "Ku bayar da zakkar fidda kai, sa'i daya daga
abinci mai qwaya ko alkama ko dabino ko sha'ir " [Ahmad 5/422]

WADANDA AKE BAWA ZAKKAR FIDDA KAI

Ba a bada zakkar fidda kai sai ga wadanda suka cancanta, wato Talakawa
sune kadai ake bawa zakkar saboda Hadithin Abdullahi Dan Abbas yace:
"Manzon ALLAH (SAW) Ya farlanta zakkar fidda kai domin tsarkake mai
azumi daga dattin zunubai, kuma domin ciyarwa ga miskinai (talakawa)
Wannan shine zabin Sheikhul Islam Ibn Taymiyya da Ibn Qayyim Al-jauzy.
(Domin qarin bayani a koma ga Majmu'ul fatawa na Ibn Taymiyya 25/27-78)

LOKACIN DA AKE FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAI

Ana fitar da zakkar fidda kai kafin fitar mutane zuwa masallacin Idi, ba ya
halatta a jinqirta har zuwa bayan sallar idi, kuma baya halatta a gaggauta
bayar da ita kafin lokacinta, sai dai idan sallar idi ta rage da kwana daya ko
biyu, to ya halatta a fitar da ita a wadannan kwanaki.

Hadith Yazo cewa Abdullahi Dan Umar (RA) yana fitar da ita kafin sallar idi da
kwana daya ko biyu. (Domin qarin bayani a koma ga Majmu'ul Fatawa na Ibn
Taymiyya 25/71-78)

SALLAR IDI DA HUKUNCE-HUKUNCENSA !!!

SALLAR IDI: Sunnah ce mai qarfi akan wanda sallar jumma'a ke wajaba
akansa wato mace ko namiji baligi, mai hankali, lafiyayye daga dukkanin
cututtuka ko uzurori masu hana shi halartar sallar idi.

LOKACIN SALLAR IDI: Lokacin sallar idi yana farawa ne a lokacin da rana ta
6ullo tayi sama, gorgodon tsawon mashi daya ko biyu, kuma yana qarewa
kafin rana ta karkata daga tsakiyar sama wato kafin lokacin sallar azahar.
WAJEN DA YAKAMATA AYI SALLAR IDI
Yana daga Sunnah musulmai suyi sallar idi awajen gari (wato bayan gari) idan
har hakan zai yuwu ba tare da wata Matsala ba. Manzon ALLAH (SAW) Ya
kasance yana barin masallacinsa ya fita zuwa daji tare da mutane yayi sallar
idi tare dasu. Duk da kasancewar masallacinsa yafi ko ina falala a garin
madina.

Abu-sa'id Alkhudri yace: "Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana fita bakin
daji a sahara ranar Idul Fidr da Idul Adhaa zuwa masallaci, sallah ita ce farkon
abunda yake fara yi" [Bukhari da Muslim @kitabus siyaam]

ABUBUWAN DA SUKA KEBANTU GA SALLAR IDI

1• ADADIN RAKA'O'IN SALLAR IDI DA KABBARORINTA: Sallar idi raka'ah biyu


ce , za'ayi kabbara bakwai kafin fara karatun liman a raka'ah ta farko, a
raka'ah ta biyu kuma za'ayi kabbarori biyar bayan kabbarar tsayuwa.

Saboda abunda yazo daga Dan Umar (RA) yace: " Na halarci sallar idul fidr da
idul Adha tare da Abu-hurayrah (RA) sai yayi kabbarori bakwai a raka'a ta
farko kafin ya fara karatu, a raka'a ta biyu kuma sai yayi kabbarori biyar kafin
ya fara karatu"

2• KIRAN SALLAH KO TADA IQAMAH A SALLAR IDI: sallar idi bata da qiran
sallah ko iqamah, Ijma'in malamai ya tabbatar da wannan. Saboda fadar
Abdullahi Dan Abbas da Jabir Dan Abdullahi (RA) sunce: Manzon ALLAH
(SAW) bai ta6a yin qiran sallah ko iqamah ba a sallilin idi" [Bukhari da Muslim
daga Hadithin Dan Abbas]

3• KARATUN SALLAR IDI: Bayan karatun Fatiha liman yana da damar ya


karanta abinda yake so na Alqur'ani a sallar idi bisa ijma'in malamai. Saboda
ALLAH (SWT) Yace: "ku karanta abunda ya sauqaqa agare ku daga cikin
alqur'ani" [Surah 73:20]

Hadith yazo daga Manzon ALLAH (SAW) Ya kasance yana karanta suratul
A'ala a raka'a ta farko, a raka'a ta biyu kuma suratul Ghashiyah" kuma ya
inganta cewa wani lokaci yana karanta suratul Qaaf a raka'a ta farko, a raka'a
ta biyu kuma suratul qamar. [Ahmad, Dabarani da Muslim sun ruwaito shi
daga Hamza Dan jundubi]

4• HUDUBAR SALLAR IDI: Yin huduba a sallar idi Sunnah ce haka sauraron
hudubar ma Sunnah ce, ana yinta ne bayan an idar da sallar. Kamar yadda
hadisin Abu sa'id Alkhdri ya tabbatar cewa:..... "_sannan bayan sallah mutane
na Zaune a sahu sai Manzon ALLAH (SAW) Ya juyo ya fuskance su yayi musu
wa'azi da wasiyya sannan yayi musu umurni da alkhayri da hani ga miyagun
ayyuka"
Hakanan ba a kayyade hudubar sallar idi ba liman yana da damar yayi huduba
yadda ta sauwaqa.

5• KABBARORI A RANAR SALLAR IDI: kabbaori a ranar sallar ana fara sune
daga bayan sallar asubah ta ranar farko ga watan Shawwal har zuwa lokacin
sallar idi.

Lafazin kabbarorin shine: "ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA'ILAHA


ILLALLAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WALILLAHIL HAMDU"

Ya tabbata sahabbai suna yi a ranar daya ga watan Shawwal da kwanaki uku


bayan sallah.

6• ZUWA SALLAR IDI DA DAWOWA DAGA IDI: shine mai zuwa sallar idi ya
dawo daga idi bata hanyar da yabi yaje ba, hadith ya tabbata daga Jabir Dan
Abdullah (R.A)

ABUBUWAN DA AKE BUKATA KAFIN ZUWA SALLAR IDI

*Ana son ayi wanka a Sanya turare kuma ayi ado da sabbin tufafi kafin zuwa
sallar idi.
* Ana so aci abinci asha abunsha kafin a fita zuwa sallar idi.
*Ana son ayi gaggawa wajen fitar da zakkar fidda kai kafin ayi sallar idi.
*Ana so a tafi zuwa idi da qafa bada abun hawa ba sai dai idan da wani uzuri,
kuma ana son a tafi zuwa idi cikin nutsuwa.

BAN KWANA DA WATAN RAMADAN !!!


*Watan Gafara.
*Watan Yantawa.
*Watan Falala.
*Watan Tuba.
*Watan Ibadah.
*Watan Alkhayri... d.s

Hakika Magabata sun kasance a yayin da watan Ramadan ya kusanto qarewa


sukan kasance cikin Damuwa da zulumi da tsoro da jajircewa da Neman
Yardar ALLAH, badon komai ba sai domin tunanin shin ALLAH Ya amshi
ibadun su ya gafarta musu ko kuwa? domin ALLAH (SWT) shine masani ga
dukkan ayyukanmu.

Saboda haka sai mu yawaita ambaton wannan addu’ar: “ALLAHIUMMA


TAKABBAL MINNA INNAKA ANTAS SAMI’UL ALIM”
Ma'ana: "Ya Ubangijinmu ka karba daga gare mu domin kai mai ji ne masani".
[Q:2:127]

Asara ta tabbata ga Wanda Ya riski watan Ramadan kuma ya kasance daga


cikin wadannan:

*Wanda ya riski wannan watan amma ya gagara yin wani aiki na alkhayri
Wanda zai samu rabo a wajen ALLAH. kamar yadda yazo daga Manzo ALLAH
(Sallallahu alaihi wasallam).

*Wanda ya zamanto Mai Bautawa watan Ramadan ba ALLAH ba, shine


Wanda idan watan Ramadan yazo sai ya kange daga aikata ayyukan zunubi,
yayin da Ramadan kuma ya wuce sai ya koma gidan jiya Tir da wannan hali.

*Wanda ya riski Ramadan kuma ya raya baqoncinta da ayyuka mai yawa


amma ba domin ALLAH ba.

Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam) Yace: "Lallai ALLAH baya karba
daga aiki sai wanda ya kasance anyi shi don ALLAH (da ikhlasi) kuma aka nufi
fuskar ALLAH da shi" [Nasa'i: 2/25].

Watan Ramadan ne ALLAH (SWT) Ya farlanta akan bayinsa kamar yadda


bayanai suka gabata acikin wannan rubutu mai taken MARABA DA WATAN
RAMADAN, Sai dai akwai Azumi Wanda Masoyin mu Annabi Muhammad
(Sallallahu alaihi wasallam) Ya kwadaitar mana su domin samun lada. Daga
cikinsu akwai azumtar kwanaki shida (6) a bayan Ramadan wanda shine
zamu fuskanta inshaa ALLAH.

AZUMIN SITTU SHAWWAL


Imam Muslim ya fitar da hadith ingantacce daga Abu Ayyub Al'ansari daga
Manzon ALLAH (Sallallahu alaihi wasallam): "Wanda ya Azumci Ramadhan
sannan ya bishi da Azumi shida acikin watan Shawwal Ya kasance kamar
Wanda ya Azumci shekara"

Mafi yawan rinjayen maluma sun tafi akan cewa Azumtar kwana shida (6) na
watan Shawwal Mustahabbi ne, wasu malaman kuma sun karhanta shi
(Makaruhi) ne domin jin tsoron kada a dauka cewa shima Farilla ne kamar
Ramadan.

MU AZUMCI KWANA (6) DAGA WATAN SHAWWAL YADDA MUKA SO BISA


ZANTUKAN MALAMAI:
Ana iya yin azumin a jere guda (6) a farkon watan. Ana iya yinsa a rarrabe, Ana
iya yinsa a tsakiyar Watan ko a karshenta.

FALALAR AZUMTAR SITTU SHAWWAL:

• Azumtar kwana (6) na watan Shawwal tana cika Ladan azumin shekara.
• Azumtar kwana (6) na watan Shawwal tana tsaftace Azumin da aka gabatar
na watan Ramadan.

ALLAH Ya bamu ikon yi, ALLAH shine mafi sani.

ALHAMDULILLAH, wannan shine abunda ALLAH (SWT) ya bani ikon rubutawa


bayan nayi nazari acikin littafai da dama wadanda suka yi Magana akan
Azumi da Hukunce-Hukuncensa kuma nayi tambaya ga malamaina bisa
abubuwan da ban sani ba, sannan na rubuta wannan maudu’in a social media
inda na ringa rubuta shi sannu a hankali har zuwa rubutu sama da 30, wanda
a yanzu kuma naga dacewar tattara shi awaje guda bisa shawarwarin da na
samu daga ‘yan uwa masu girma ALLAH Ya saka musu da alkhairi, ALLAH
Yasa ayyukanmu kar6a66u ne ALLAH Yasa muna daga cikin bayinsa
wandanda ya Yanta a wannan watan (Ameen)

Ina rokon ALLAH abunda na rubuta daidai ALLAH Ya hadamu a ladar baki
daya, abunda na rubuta bisa kuskure ALLAH Ya gafarta min, Malamaina da
iyayena ALLAH Ya saka musu da alkhairi bisa kokarin da suka yi na
tarbiyantar dani da ilimi har izuwa wannan lokacin. Kofa a bude take ga duk
wanda yaga kuskure na ko kuma shawara da zai bayar gare ni ina Marhaban.

YAR’UWARKU A MUSULUNCI:

Faridah Bintu Salis


(Bintus~sunnah)

You might also like

pFad - Phonifier reborn

Pfad - The Proxy pFad of © 2024 Garber Painting. All rights reserved.

Note: This service is not intended for secure transactions such as banking, social media, email, or purchasing. Use at your own risk. We assume no liability whatsoever for broken pages.


Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy