ZAGON ƘASA by Khadeeja Candy - 1

Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1of 636

http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zago-asa01.

html

BISMILAHI RAHAMANIN RAHIM

*GABATARWA*
Wani ɓangare na labarin nan ya faru ɗa gaske, sai dai an ƙara da wasu abubuwan dan
ilmantarwa da nishaɗi. Labarin na iyalai uku three family.

NAMRA FAMILY.
DR. HILAL FAMILY.
KALSOOM FAMILY.

Sunan Novel ɗin *ZAGON ƘASA*


Green snake under green grass, people with two colors. A tension, Schemed Novel of
slut.
Witness to regret.
Witness to love.
Witness to tears.
Witness to drunken.
Witness to revenge

*MEANING OF THE NAMES*


NAMRA - Delicious water
UZAIR - Name of a prophet
HILAL - Crescent
KALSOOM - Name of Prophet Muhammad (pbuh) daughter
EZZAH - A person who give the honor, respect
RASHIDA - Intelligent sober
IFHAN - Respectful, nice, precious
RAFEEK - Friend
YASMEEN - Flower
ABDULLAHI - Servant of Allah
ASIM - Person who keep away from sins.

*SADAUKARWA*
Na sadaukarda wannan littafin ga (Daughter) RASHIDA ABDULLAHI KARDAM kin cancanci
fiye da haka a gareni

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandycom.ng for your updated.

FIRST FAMILY...

*1.......* Ƙarfe biyar da minti arba'in da takwas na yamma, ta faka Motarta a


parking space, ajiyar zuciya ta sauke ya fi sau uku, sannan ta kalli takardun da
ke gefenta kamar mai tunani, daga bisani ta kai hannu ta ɗauka, ta buɗe motar ta
fito.
Jiki a sanyaye ta nufi harabar gidan, gurin da Mahaifinta yake zaune yana shan
iska, daman a al'adarsa ya kan zauna a habarar gidan da yamma, wani sa'in ya kan
duba jaridu wani lokacin kuma ya leƙa yanar gizo, dan sanin me duniya take ciki.
Da kamar fargaba Namra ta doshi gurin da yake, zuciyarta na raya mata abubuwa da
dama.

talkamin ƙafarta ta fara cirewa tun kamin ta ƙasara kusa da carpet ɗin da aka saba
shimfaɗa masa, sallama ce ta fito bakinta kanta na ƙasa kamar mai jin nauyin
kallonsa.

“Assalamu Alaikum”

Bai amsa sallamar ba, sai dai ko kaɗan hakan bai bata mamaki ba, daman bata
tsammaci zai amsa mata ba, sai kawai ta ɗora da gaisuwa.

“Abban sannu da hutawa ya aikin?”

Ya yi jinkirin amsa mata na daƙiƙon da zai kai ashiri zuwa ashirin da biyar, sannan
ya amsa mata can ƙasan maƙoshinsa

“Al-hamdulillah”

Bata yarda wata kalmar ta ƙara fito daga bakinta ba, sai kawai ta tashi jiki ba
ƙwari ta saka takalminta, ta nufi hanyar da zata sadata da part ɗin Mahaifiyarta.
Sai da ta share hawayen da suka zubo mata kamin ta kai hannu ta murɗa ƙofar falon
ta shiga. Babu kowa a parlor sai air conditioner dake ta aikinsa, Kai tsaye ɗakinta
ta wuce zuciyarta cike da rauni.
Saman gadonta ta zauna ta lumshe ido tana sauraren bugun zuciyarta, kalaman da
Mahaifinta ya yi mata ɗazu da safe suƙa riƙa dawo mata, irin yadda ya riƙa aibanta
ta, yasa ta ta yi saurin dafe kanta, sai kuma ta fashe da kuka tana murza zoben
dake hannunta.

Haka ta zauna a ɗakin bata fito ba har sai da aka yi sallah Magariba, bayan ta yi
sallar ta fito ta nufo parlor fuskarta babu yabo babu fallasa.
Duk ƙannenta suna zaune parlor suna kallon Dadin kowa, babu wanda ya lura da
fitowarta sai Mahaifiyarta. can nesa da Mahaifiyarta ta zauna tana gaisheta.

“Anty barka da dare”

Bata amsa mata ba, sai kallonta take tana karantar irin halin da ƴarta take ciki.

“Tunda kika dawo daga makaranta Namra kina cikin ɗakin, so kike yi damuwa ta yi
miki yawa ko? Yau ranar girkina ce amman saboda ke Abbanku bai leƙo nan ba, na
shiga sashensa na rasa gane kansa, so kike ki kashe min aure ko Namra? kin fi son
ki rayu da son zuciyarki fiye da farincikin iyayenki? bana ƙin zaɓin ki Namra,
amman tun da mahaifinki ba ya so barin shi ya fi alheri”

Matsewa ta yi cikin kujerar tana wani irin kuka da ba zata iya fitarwa ba.
Sai yaushe Abbah ta zai fahimci halin da take ciki ne, sai yaushe zai tausayawa
rayuwarta? ji take idan har ta yarda ta rabu da Asim zata iya mutuwa, bata jin zata
iya rayuwa da wani Namji da ba Asim ba, kuma idan har bata aureshi ba, ta san Allah
ba zai yafe mata ba, mutane zasu masa dariya, daman an daɗe ana masa kirarin ita
ɗin ba sa'arsa bace, ta san irin son da Asim yake mata, ta ya zata iya sanar da shi
ba zata aurensa ba? Yayyu ta Mata da Maza Tara Mahaifinta ya aurar, duk kuma a
cikinsu babu wanda ya yi ma zaɓin miji ko matar aure sai ita.

Sallamar Barrister Yasmin da Mijinta ne, ya ankarar da ita ta yi saurin share


hawayenta, tana gyara fuskarta dan kar su gane ta yi kuka.
Anty Amarya ce ta amsa musu fuska a sake kamar yadda ta saba tarbonsu.

“Maraba maraba da Lauyoyi, cikin daren nan ake tafe”

Yasmin ta zauna a kujerar da Anty Amarya take zaune, yayin da Uzair ya zauna a
kujerar da ke kusa da ƙofa, idonsa na kan Namra wace ta banye ɗaurin ɗankwalinta
tana ƙoƙarin magana da matarsa.
“Anty Barrister ina Afnan?”

“Yanzu na biyo uban daren nan na miƙe hanya ki rasa wanda zaki tambaya sai Afnan?
amman yarinyar nan akwai ki da rainin hamkali”

Kusa da ita Namra ta dawo ta zauna tana faɗin

“Kaji Anty da wata magana, toh ai ita ce Ƴata dan haka ni ita zan tambaya”

“Idan kina son ganinta kawai ki je gidan Gwaggo ki ganta, amman indai tambaya zaki
yi, ki riƙa cewa ya na ke ni da Mijina”

“O'oh masu miji manya, toh ni ban ga mijin na ki ba ai”

“Ni ai na ganki”

Uzair ya amsa daga inda yake zaune yana kallon ƙugunta zuwa saman ƙirjinta.

“Jar uban nan, ka ji min wata magana! saboda ke fa muka biyo ta nan amman zaki wani
ce baki ganshi ba”

Duk suka sa dariya Maryam ta ce

“Toh mijin na ki ai tsoron mutane yake shiyasa ya maƙure gurin kamar wani ɗan
fashi”

Anty Amarya ta kai mata dudu

“Wai dan kun ga baya magana shiyasa kuka raina shi ko?”

Dariyar suka sake yi, sannan Anty Amarya ta shiga tambayar Barrister ya aiki. Namra
kuma ta nufi hanyar kitchen dan ta ɗauko musu ruwa, tun da ta tashi Uzair ya bi
bayanta da kallo har ta shige kitchen ɗin.

Bayan sun sha ruwan ne Barrister ta ce

“Anty Mun zo aron Namra ne, Uzair zai yi ɓaƙi daga Abunja,kuma yana son ayi musu
wainar kaza kinsan Namra ce ta iya shiyasa muka zo mu faɗa miki”

“Aa ni ba ruwana ga ku ga Namra”

Cewar Anty Amarya tana kallon Namra da ta ɗan ɓata fuska kaɗan, dan sam yanzu bata
son zuwa gidan Yasmin, Hakan kuma ya samo asali ne tun lokacin da Uzair ya soma
nuna mata maitarsa a fili.

“Kai gaskiya na so nayi tilawar haddata, dan Saturday nan ne walimar mu fa”

Yasmin ta ɗan zungureta

“Ke uwar kuiya, just for one day ne fa zaki mana, ai yau Wednesday, zaki iya yi
Friday”

“Haba kije mana idan kin gama musu da wuri ma ai zaki iya dawowa”

Anty Amarya tasa baki. Yasmin ta ce

“Kuma ni kin ga fita zan yi ba gida zan wuni ba, ina da cases har huɗu ƙila sai
yamma zan dawo balle ki ce zan dame ki da surutu, Uzair kuma sai biyar yake dawowa,
ke kaɗai ma za'a bari a gidan”
Ta amince ba dan ta so ba, sai dan babu yadda zata yi, indan har ta ce ba zata je
ba, Yasmin zata zargeta, Anty Amarya kuma zata mata faɗa, sa'arta ɗaya gobe ba su
da lacca.
ba su wani daɗe sosai ba, suka yi ma Anty Amarya sallama suka fice. Har gurin Mota
Namra ta rakasu, Yasmin na laƙame da kafaɗarta tana mata tambihi game da haƙuri,
dan ta fi ƙowa sanin halin da Namra take ciki, kasancewar shaƙuwarsu, Namra bata
ɓoye mata ƙomai.

Bayan sun wuce ne ta dawo jiki a sanyaye ta shigo parlor.

“Ni wallahi bana son zuwa gidan Anty Yasmin”

Ta faɗa tana ƙoƙarin zaunawa saman kujera. Maryam ta kalleta ta ce

“Saboda me?”

Kamar zata ce wani abu sai kuma ta yi shiru ta kalli tv.

“Tashi kije ki ci abinci”

“Bana jin yunwa”

“Ai gaki nan, duk kin bi ki koɗe sai fama kike da rama kamar wata marar lafiya”

“Wallahi Allah bana jin yunwa Anty”

“Ta ya zaki ji yunwa kin ɗauki damuwa kin sawa ranki, Allah ya sauwaƙe miki wannan
rayuwa”

Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, dan ta dan duk yadda zata yi ma mahaifiyarta
bayani, ba ganewa zata yi ba.
Annur ne ya shigo ya tsaya daga bakin ƙofa hannunsa riƙe da lemu ya ce

“AntyAmarya wai Abbah ya ce ki zo tare da Anty Namra”

Gabamsu ya faɗi dukansu, bama kamar Namra data ja wani dogon numfashi ta sauke,
kamin ta kalli Mahaifiyarta. Ba tare da ɓata lokaci ba suka tashi suka nufi part
ɗinsa, kishingiɗe suka tararda shi, kofin tea na gefensa yana sanye da madubi
fuskarsa babu annuri yana duba wasu documents.
Namra ta zauna ƙasa cikin ladabi, Anty Amarya kuma ta zauna saman kujera tana
faɗin

“Annur ya ce kana kiran mu!”

Bai ce uffan ba, har sai da ya ƙare duba takardun da yake sannan ya cire gilashin
idonsa, ya kalli Namra babu alamun wasa a tare da shi ya ce

“Kin san Alhaji Madu Sanusi?”

“Eh”

Ta amsa ƙasa-ƙasa gabanta na ɗan faɗuwa, aikan ta san Alhaji Madu akan farin sani,
mutumen da kwana biyu, uku yana gidansu, aminin mahaifinta.

“Shekaran jiya ya yi min magana akan ki, saboda yana son ƙara aure dan ki zame masa
first lady tunda sauran matansa basa jin turanci, kuma a takarar da yake akwai
buƙatar ya auri mace ƴar boko, mun gama magana da shi gobe da dare zai zo ku gaisa”
Tun da ya soma maganar hawaye ke zuba a idonta har ya ƙare, daker ta iya amsawa da

“Allah ya kai mu”

Anty Amarya ta amsa da “Amin” Tana sauke ajiyar zuciya, sam bata jindaɗin yadda
Abbah yake yi ma ƴarta sai dai babu yadda zata yi, ko magana ta yi cewa yake ita ke
ɗaure mata gindi tana yadda take so.

Cikin sauri Namra ta taso, ta baro falon zuciyarta cike da zulumi, tana tsaron
abunda zai je ya dawo, ta rasa ƙwaƙwaran dalilin da ya saka Mahaifinta ba ya son
tarayyarta da Asim.
Har ta shigo ɗakinta kalmar Alhaji Madu ce take mata yawo a kunne, saman gado ta
kwanta hawaye na bin fuskarta, sai ta kai hannu ta janyo wayarta, gallery ta shiga
ta kamo hoton Asim tana kallo.

“Miyasa Ƙaddarata zata min haka? kin san ba zaki barni na yi soyayyah da shi cikin
kwanciyar hankali ba kuma kika haɗa mu? kinsan ba zan auresa kuma kika sa na sansa,
Allah kayi min mafita karka ka bar ni da kaina”

Rumgume wayarta ta yi sosai tana kuka da tuna kalaman daya faɗa mata yau a
makaranta.

‘Ina son ki sosai Namra duk da jikina yana bani lallai ba zaki aure ni, saboda ni
da ke ba ɗaya ba Namra, ga shi mahaifinki baya son na, Mahaifiyata tana yawan faɗa
min wai zaki ɓata min lokaci ne kawai ba zaki aure ni ba, Namra ina gudun ranar da
zan wayi gari kin zama matar wani magauta suyi min dariya...’

Kuka take sosai har da karkarwa, tana matsar idonta da buga ƙafafunta.

**********

Manjo Usman Zamau tsohon soja ne, mai mata biyu Hajiya Barau wanda ake kira da
Mama da kuma Hajiya Larai wanda ake kira da Anty Amarya. Gidan Alhaji Usman babban
gida ne mai ɗauke da part uku, part ɗin uwargidan sa da kuma na Amaryarsa sai nasa.
Uwargidansa na da ƴaƴa tara hudu mata biyar maza kuma dukansu sun yi aure, wasu
suna tare da ita wasu kuma aure ya kai su nesa, a yanzu bata da ɗa ko ɗaya a gidan
sai jikoki da ƴaƴan ƴan'uwa.

Anty Amarya ce aka auro daga baya, ita ce mai yara huɗu dukansu mata, Namra ce
babba sai Maryam dake binta da kuma Hindatu da Aisha. cikakkancen sunan Namra shine
Khadija mahaifiyarta ta kan mata Alkunya da Namra ne kasancewarta ita ta fari
gareta. Namra na 100l a jami'ah ta haɗu da Asin, suka ƙula soyayyar da babu wanda
ya sani har suka kai 300l, sai a yanzu ne abun ya zame musu matsala kasancewar Asim
ba ɗan kowa bane face talaka mai neman abunda zai sa a bakinsa.

Ita kuma ƴar masu arziki ce musamman yanzu da Mahaifinta yake takarar Senator,
daman can mutun ne mai abun hannunsa dan yana da kamfanoni da dama ciki da wajen
ƙasar nan.
A duk familynsu da shi suke tinƙaho dan Allah ya yi masa rufin asiri ta ko ina.
Gashi shi ƙaɗai mahaifiyarsa ta haifa a duniya, a duk familynsu ya fi shaƙuwa da
Mahaifiyar Yasmin da Kuma Mahaifiyar Uzair kasancewar kakanninsu guda, kuma yana
ganinsu mata, yana tausayinsu sosai.

WANNAN KENAN

*********

SECOND FAMILY...
Tun da ta dawo daga aiki take cikin damuwa, abun duniya ya fara isarta komai ya
taru ya yi mata katutu a rai, kullum ta fita ta dawo sai anyi da ita a unguwa,
ƙawayenta su zolayeta familynsu ayi ta tambaya, kamar ita ta ɗorawa kanta rashin
aure.

Kallon kanta take ta madubi tana hawaye, ta ko'ina Allah ya yi mata sura, mace ce
abunda ake cewa mace, amman babu mai neman aurenta sai mutanen banza, duk acikin
manemanta babu na ƙwarai da zata ware da sunan wanda zata aura, duk wanda ta yi ma
maganar aure ba zai sake dawowa ba, sai dai su nuna suna son jikinta.
Sa'aninta duk sun yi aure, sun barta sai kace wanda ta zagi maza, tun tana sa ran
idan ta gama karatu ta samu wanda zata aura yanzu ga shi har ta gama ta samu aiki
amman ba shiru, ada abun ba ya damun iyayenta amman yanzu ya zame tunaninsu, suna
addu'ah amman kamar basa yi, sun aurar da ƙannenta biyu mata ita shiru, babu
mashinsshini balle malashi.
Faɗi tashi na neman magani babu irin wanda bata yi ba ita da iyayenta, amman ba
wani labari. Yanzu kan har ta fara fidda rai daga samun mijin aure.

Kallon kanta take sosai da sosai a gaban madubi tana mamakin yadda take ƙokarin
kare kanta daga zina da alfasha, tana ƙokarin sallah dare da sadaka, amman ta kasa
samun mijin da zai aureta.
Hawaye ne suka zubo mata tana tuna irin yawan ƙawayenta, amman babu ko ɗaya duk
sun yi aure sun barta.
Ƙarar da wayarta ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, sai ta
kalli Screen ɗin wayar Salma ce rubuce a fuskar wayar, cikin sauri ta share
hawayenta ta ɗauki wayar ta kara a kunne.

“Hello Salma”

“Na'am Kalsoom ya kike?”

“Lafiya ƙalau, ya Ahmad?”

“Lafiyarsa ƙalau, idan kina da time gobe ki shigo da wuri zamuje wani guri”

Da toh kawai ta amsa mata ta aje wayar, ta san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi,
ko bata faɗa ba ta san ba zai wuce ta kai ta gurin wani Malamin ba, dan duk cikin
ƙawayenta ita ce ta fi kowa damuwa da rashin aurenta, ita ce take ta faɗi tashi
akan taga ta yi aure.

Kiran da ta ji ana mata downstairs ne yasa ta motsa ta tashi ta nufi ƙofar fita.
Karo suka yi da Momy sai ta ja baya da sauri tana faɗin

“Kirana kike yi?”

“Eh yanzu mijin Zainab ya kira wai bata da lafiya tun shekaranjiya”

“Subhannallah miye same ta?”

“Wai maleria ce, amman dai na san ba zai wuce ciki ba, shine nace ki shirya gobe
kije can ki yi mata ko da kwana uku ne idan ta ɗan sarara sai ki dawo”

“Haba Momy ni kuma? miyasa Saleena ba zata je ba ni fa yayarta ce kuma ace na koma
can na zauna”

“Toh miye a ciki? ai ansan lalura ce ta kai ki, Saleena Exam za su fara gobe kinga
ba zai yiyu ta je can ba, amman ke tunda aiki ne ai idan kin dawo sai ki ɗan taya
ta aikin gidan da dafa musu abinci”
“Amman Momy ai yana da ƙanne mata kuma za a iya ɗauka mata ƴar aiki”

“Ya san da ƙannensa amman ya zo nan ya faɗa mana, idan mutum yana mutunta ya kamata
kai ma ka mutun tasa, kwana uku kawai zaki yi ki dawo kin ji?”

Ta ɗaga mata kai alamar toh, zuciyarta cike da damuwa.

“Allah ya yi miki albarka”

“Amin”

Daga haka Momy ta juya ta sauka ta barta a gurin tsaye. Jinginawa Kalsoom ta yi
jikin ƙofar tana addu'ah

“Ya Allah idan mijina yana nesa da ni Allah ka kusan to dashi a gare ni, idan yana
kusa da ni Allah ka haɗa mu”

Juyawa tayi ta shiga ɗakinta tana cika ma bakinta iska.

***********

THERD FAMILY....

A-hankali ya ke shafa lallausar fatar jikinta da hannunsa, idonshi a lumshe yana


hura mata iska a kunne, daga bisani ya fara tsosar kunnen nata hannunsa ɗaya yana
saman ƙirjinta. A take ta lumshe ido tana maida numfashi, tana ƙoƙarin mayar masa
da martani, hannayenta tasa cikin gashin kansa kamin ta juyo ta soma masa kiss a
ƙirji, ɗayan hannunta na cikin cibiyarsa, da sauri ya kwantar da ita ya zare tawul
ɗin jikinta ya soma murza fatarta bakinsa cikin nata suna maida numfashi. Ringing
ɗin wayarta ne yasa ta walƙato shi cikin dabara ta dawo saman ta, sai ta yi saurin
sauka tana dariya

“Am sorry Sweetheart na yi latti, ka ga har an fara kira na”

Daker ya iya ɗaga jajayen idanunsa ya kalleta yana haɗiye yawu

“No Please karki min haka Ammyn Rafiq, i need you”

Tawul ɗinta ta ɗauka ta ɗaura tana faɗin

“I need you too Babe, but there's nothing i can do, you know how my work is”

Babu abunda zai ce mata, haka take masa time to time, ta kan hana sa haƙƙinsa
saboda aikinta, idan ta dawo da dare ta ce ta gaji bachi idan kuma da safe ne ta ce
zata yi latti, babu kuma yadda zai yi ya hanata aikin tun da mahaifinta ya tsaya
kai da fata akan lallai sai ƴarsa ta yi aikin banki.
Yana kwance a gurin har ta yi wanka ta shirya yana kallonta, sai daf da zata
fita sannan ta zo daidai kunnensa ta yi masa kiss

“Take care of yourself okay, idan Rafiq ya tashi ka shirya shi idan zaka je aiki ka
aje shi kurin Hajiya, zan ɗauko shi idan na dawo, idan kuma su Ulfah sun dawo
abincin su na nan a flask, love you my hubby my Doctor”

Daga haka ta fice tana murmushi, da kallon ya bita har ta fice, sannan ya ɗauke
kansa yaja bargo ya lulluɓe ya soma sana'arsa.

_______________________________
Hello my beautiful people, ina fatar kuna lafiya kuma ina fatar wannan tafiyar zata
muku daɗi zaku kuma bani haɗin kai kamar ko yaushe.
Wannan tafiyar ba irin wacan bace ce, ba zan baku kunya ba In'shallahu, iyana
gayyartar ku a sabon shafina wanda zan riƙa zuɓa duka littafaina a can, zan riga
yin update a can sama da ko'ina zaku iya samun shafuka na akan kari Just click the
for your updated.

www.khadeejacandy.com.ng

Zan cigaba idan na ji ra'ayoyinku 08036126660 na gode ☺

Best regards 💖
Khadeeja Candy🌺
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa03.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 2*

NAMRA POV.

Yadda Namra ta ga rana haka ta ga dare, dan kwana ta yi kuka da tunanin Asim, da
safe ma bata fito ba sai da ta yi shirin fita, sannan ta leƙa ɗakin Anty Amarya dan
gaishe ta, daga bakin ƙofa ta tsaya tana miƙa mata gaisuwar tana ɗan kare
fuskarta.

“Anty Ina kwana?”

Yanayin muryarta kaɗai ya isa ya karantar Anty Amarya halin da ƴarta take ciki,
daman ta san za'a rina, ko babu dalili Namra ta kan yi kuka balle yanzu da kuka ya
zame mata jiki.

“Ba zan hana ki kuka ba Namra, dan kina da dalilin yinsa, amman nasan kin sauke
Alƙur'ane kuma kin haddace hizo arba'in daga cikin Alƙur'ane, ashe ko ya kamata
a'ce idan kin shiga damuwa ki riƙa faɗawa Allah buƙatarki kina kai kukan ki a
gareshi”

Daga inda take tsaye ta amsa da

“Na gode sosai Anty In'shallahu zan yi, zan je gidan su Anty Yasmin”

“Allah ya kiyaye hanya, amman ki tabbatar kin ci abinci ka min ki je”

“Toh”

Bayan ta amsa da to ne ta juya ta fice, dinning ta nufa ta haɗa tea kaɗan ta sha,
dan bata jin cin komai, ta daɗe a gurin zaune sannan ta ɗauki handbag ɗinta ta
rataya ta fice daga palour, direct ta nufi gurin da Motar ta take.

Bayan ta yi addu'o'in data saba, sannan ta yi ma Motar key ta yi horn Mai gadi ya
buɗe mata ta fice.
Tuƙi take kamar marar lakka, gashi zuciya ba ƙwari, sai tunane-tunane take.
Hannu ta ga ana mata gefen hanya alamar ta tsaya, tana ganin Asim ta yi saurin taka
burƙi ta yi ribas ta dawo dai-dai inda ya ke ta faka, buɗe Motar tayi ta fito jiki
na rawa ta ga masoyinta.

Matsowa ya yi kusa da ita yana murmushi

“Namra”

“Asim”

Haɗa baki suka yi gurin kiran sunan, sai ko wannensu ya yi shiru yana kallon
ɗan'uwansa.
Da sauri Namra ta kawarda fuskarta saboda hawayen da suka cika mata ido. Hankali
Asim ya tashi sosai ganin hawaye a idon Sahibarsa.

“Jiya na kira ki ya fi a ƙirga amman baki ɗaga ba, yanzu kuma ga hawaye a idonki,
hakan ya tabbatar min da akwai abunda yake damunki”

Ta share hawayen da suka zubo mata.

“Babu komai, ba abunda ya ke damuna”

“Kina ɓoye min wani abu Namra, kina son tunani ya yi min yawa ko, ina tunanin halin
da muke ciki, ga halin talaucin da nake ciki ga rashin aikin yi da ke damuna, Namra
da wanne zan ji?”

“Faɗa maka bashi da amfani Asim, zai ƙara maka damuwa ne kawai”

“Saboda ba zan iya miki maganinsa ba ko Namra?”

“Ba haka bane, Asim zan baka wasu kuɗaɗe da zaka ja jari da su...”

Hannu ya ɗaga mata

“Tun yaushe nake faɗa miki ba dukiyar ki nake so ba Namra, ke nake so ba abunda
yake cikin gidan ku, ko abunda kika mallaka, kawai ina son ki yi min alƙawari duk
rintsi duk wuya ba zaki rabu da ni ba, ki min alƙawarin zaki aure ni Namra shi
kawai nake so”

Kai ta girgiza masa tana wasu irin zafafan hawayen

“Ba zan iya ba Asim, ka gafarce ni ba zan iya ba...”

Dammm! Ya ji kamar an jefa masa dutse a zuciya, a take idonsa suka rine suka cika
da ƙwallah, sai ya yi saurin sadda kansa ƙasa yana zauke ajiyar zuciya.

“Ashe gaskiya Umma take faɗa min, ashe yaudara ta kike ba zaki aure ni ba, amman
kin ban mamaki Namra, ban tsammaci haka daga gareki ba”

Ta yi saurin kama hannunsa tana kuka

“Ba laifi na bane Asim, iyaye ne...”

Ya katsa mata tsawa

“Iyaye? Ni bana da iyayen ne Namra? Mahaifiyata bata son tarayyata da ke amman na


tsaya kai da fata akan sai na aure ki, sai ke? kin fi ni sanin darajar iyayen ne ko
me?”
Kasa cewa komai tayi, daman ta san ba zai fahimce ta ba, ba zai mata uzuri ba, zai
zargera da da cin amana, ita kam ta san bata kyauta masa ba, sai dai babu yadda
zata yi.
Hannunta ya ture, ya share hawayen da suka zubo masa ya juya a fuce ya kama hanya.

“Asim!Asim!! Asim!!!”

Haka ta bishi da kira tana kuka, amman ko waigowa bai yi ba balle ya amsa mata.
Zubewa ta yi a gurin tana kuka, kukan tausayawa kanta da zuciyarta, dan ita ma
kanta ta san tana son Asim, zata yaudari zuciyarta ne kawai idan har ta ce zata iya
rayuwa da wani namijin da ba Asim ba.
Ta kusan minti goma shabiyar a gurin tana kuka, sannan ta buɗe Motarta ta shiga.
Hanyar da zata sadata da gidansu ƙawarta Amira ta ɗauka tana wani irin gudu na
fitar hankali.

Cikin ƴan mintuna ta isa gidansu Amira, daga wajen gidan ta faka motar ta dan ba
zata iya jira mai gadi ya buɗe mata ba, sai ta fito ta taka da ƙafa ta shiga cikin
gidan still tana kuka.
Mahaifiyar Amira ta yi mamakin ganin ta haka, sai tambayarta take lafiya, ita
dai bata yarda ta faɗa mata komai ba, ta wuce ɗakin Amira kasancewar gidan ba
baƙonta bane.

“Ke lafiya miya same ki?”

Amira ta tambaya cike da tashin hankali tana girgiza Namra. Bata ɓoye mata komai
ba, tun daga yadda suka yi da Abbah, har abunda ya faru tsakaninta da Asim a yau.
Wani dogon tsaki Amira taja ta ɗauke hannunta daga jikinta

“Ke dan Allah duk kin tayar min da hankali, ni na ɗauka ma wani abun ne”

Kallon rashin fahimta Namra ta yi mata da idanunta da suka rine saboda kuka.

“Ban gane ba, Amira ko baki fahimci abunda na faɗa miki bane?”

“Na fahimta sarai, ai da hausa kike magana, naga dai babu wani abun tada hankali a
ciki, tunda kina da mafita”

Namra ta ƙara kallonta

“Wace irin mafita? Ai nima mafitar nake nema”

“Kawai ki bishi ku gudu kuje can wani guri a ɗaura muku aure, daga baya iyayenki
zasu yafe min idan suka fahimci irin son da ke tsakanin ku”

“Wannan ba mafita bace Amira, ni ba zan iya wannan ba, duk son da nakewa Asim bai
kai wanda nake yi ma iyayena ba, ko wanne muhallinsa daban”

Amira ta taɓe baki

“Ashe ko ba son ƙwarai kike masa ba, tun da har ba zaki iya sadaukar da kan ki a
gare shi ba”

Shiru Namra ta yi kamar mai tunani, sai kawai ta share hawayenta ta ɗauki jakarta
ta rataya tana faɗin

“Bari na wuce akwai inda zanje, sai mun yi waya”

“Toh, Allah ya kiyaye hanya”


Lokuta da dama haka Amira take nata yaɓen maganar duk data zo bakinta, ta kan bata
shawara tsaɓanin tunaninta, sai dai babu wanda zata faɗawa damuwarta kamar ita da
Anty Yasmin.
Da wani mugun kallo Amira ta bita tana harararta, can kuma ta taɓe baki.

“Wahalalliya, ashe ƙaryar so kike tun da ba zaki iya barin iyayenki ba”

Wayarta ta jawo ta soma danne-danne, kamin ta tashi ta nufi ɗakin mahaifiyarta dan
labarta mata abunda ya faru.

Har Namra ta fito daga gidan nazarin kalaman Amira take, sam bata ganin dacewa
akanta guje iyayenta, saboda saurayin da zai iya barinta ya ɗauki wata, taya zata
iya gudu mutanen da suka shekara ashirin da biyu suna bata gudummawa, akan saurayin
da haɗuwarsu bata wuce shekara uku ba, idan har ta yi hakan ta yi babban butulci
wanda ta cancanci ko wane irin sakamako. Sai dai wani ɓangare na zuciyarta, yana
karantar da ita akan abunda Amira ta faɗa mata shine mafita, dan idan ba haka ba
mahaifinta ba zai taɓa bari ta auri Asim ba.

Har ta isa gidan Barrister Yasmin wannan tunanin take, tana hangowa kanta illa da
kuma alfanun da ke tare da ita idan har ta zaɓi guduwa ta bar iyayenta.
Ta daɗe a cikin motar tana kiran wayar Asim, amman yaƙi picking at the end ma sai
ya kashe wayar gaba ɗaya, cikin rashin kuzari ta buɗe motar ta fito tana kallon
balcony ɗin ƙofar Yasmin, sai a lokacin ta lura da Motoci uku da aka faka a gurin.

‘Waɗannan ba Motocin Ya Uzair bane, kar dai ace baƙin har sun iso, ko da yake abuja
ba nesa bace idan sun shigo jirgi’

Shine abunda take rayawa a zuciyarta tana ƙoƙarin duba agogon hannunta, 11:23am ya
bata hakan yasa ta saki jiki ta nufi ƙofar, tana isa ta kai hannu ta murɗa ƙofar.
Abunda ta yi arba da shi yasa ta mutuwar tsaye, zaro ido ta yi ta rufe bakinta da
sauri taja baya.

Cikin sauri Uzair ya ture Mutumen da ke samansa ya tashi ya nufi inda take, har ya
iso kusa da ita jikinta rawa yake, gashi be da riga daga shi sai gudun wando. Shima
hankalinsa ya tashi sosai bai tsammaci a buɗe ya bar ƙofar ba, mamakin kansa yake
ma yadda bai ji buɗe gate ɗin gidan ba da fakawar Motar ta.

Da hannu ta nuna shi, sai kuma ta kasa magana. Cikin zafin hannu ya kai hannu ya
cafko hannunta ya jefa ta cikin parlor.
Baya-baya tayi tana neman mafita sai kawai ta shige kitchen da samawa kanta makami,
tana shiga ta nufi inda wuƙa take ta kai hannu ta ɗauka. Shi kuma ya kunno kai
cikin Kitchen ɗin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.

“Ba zan miki komai ba Namra, matukar kika rufa min asiri, wallahi kuskure ne ba a
son raina bane cilas ta ni suka yi”

Nuna shi ta yi da wuƙar da ke hannunta tana girgiza kai

“Ba zan rufa maka asiri ba Ya Uzair, tun da ba rufin asirin kake so ba, tun ba yau
ba na taɓa ganin wani video a wayarka, Namiji na kissing ɗin Namiji ɗan'uwansa sai
kace min sabon Memori ne ka siye baka san da video ba, yanzu kuma na kama ka da ido
na.

Kai wane irin Namiji ne dan Allah? Matarka ta yarda da kai ta baka amana amman kana
cutar, cutar ma bata tsaya akan ka har sai ka neme ni! Kuma miye abun son ga Namiji
ɗan'uwanka? Tirrr da kai Ya Uzair, na yi baƙinciki da ka kasance mijin Anty Yasmi,
sam bata cancanci zama matarka ba”
Murmushi ya yi ya jawo ƙofar Kitchen ɗin ya rufe.

“Na nemeki ne saboda naga abunda nake so a jikinki, lokacin da nace na aureki ai
cewa kikayi kina da wanda kike so, daman nima ban shirya zama da mata biyu ba,
shiyasa na nemi yin sex da ke.

Amman yanzu bari kiji na faɗa miki, duk kika kuskura kika bari maganar nan ta fita,
kika faɗawa duniya cewar ni ɗan homo ne sai na tarwatsa rayuwarki, ki rubuta ki
aje”

Ya faɗa mata haka fuska a ɗauri babu alamar wasa a lamarinsa, sannan ya buɗe ƙofar
kitchen ɗin

“Zo ki fice, amman ki rubuta ki aje duk kika kuskura fitar da wannan maganar sai na
salwanta rayuwarki”

Daga haka ya fita ya bar mata kitchen ɗin.


Ita kam bata yarda ta fito ta nan ba, sai ta buɗe ƙofar baya ta kitchen ɗin ta fita
gabanta na mugun faɗuwa, har ta shiga Motarta jikinta rawa yake, zuciyarta na raya
mata karta ɓoyewa ƴar'uwarta kuma aminiyarta abunda mijinta keyi, gani take idan
har tayi haka bata yi mata adalci ba.
Tana fita daga gidan ta faka gefen ti-ti ta dannawa Yasmin kira, three miss
call tayi mata amman bata ɗaga ba, ta san ba zai wuce tana cikin kotu ba, sai kawai
ta yanke shawarar tura mata saƙo.

Ko da ta isa gida Anty Amarya bata nan, part ɗin kuma babu kowa, ƙannenta duk suna
makaranta, hakan ya bata damar shiga ɗakinta ta baja kolin hajar tunaninta.

UZAIR POV.

Lokacin da Uzair ya ga Namra ta fita sai ya gargada ƴan iskan friends ɗinsa, ya
gyara gidan tas kamar komai bai faru ba. Ba ayi minti Arba'in ba, sai ga Yasmin ta
dawo gidan, cikin sauri ta shigo parlor tana dube-dube.
Uzair na zaune saman kujera yana kallonta, hankalinsa kwance kamar ba komai, sam
be yarda ya nuna akwai wani abun a fuskarsa ba, tashi yayi ya tare ta, tare da
rumgumeta yana kissing

“Lafiya wife?”

Ta sakar masa jikinta sosai

“Wallahi miss call ɗin Namra na gani da text ɗin ta, wai na yi sauri na zo gidana,
shine duk hankalina ya tashi”

Dariya yayi sosai a zuciyarsa yana jinjina ƙarfin hali irin na Namra.

“Haba dai sai kace baki san Namra ba? Zata iya disgaki fa ai ba yau ta saba ba,
karki tashi hankalinki”

Juyowa tayi sukayi kissing ɗin junansu sannan ta ce

“Ta katse min aiki na, ina fatar dai tayi maka kosan kazar?”

Hancinta ya laƙata

“Namra bata ma zo nan gidan ba, friends ɗina kuma har son kama hanyar Abuja daman
ɗaurin aure suka zo”

Da haka ya shammace ta ya cigaba da kissing ɗinta.


NAMRA POV.

Duk yadda ta so ta labartawa Anty Amarya abunda ke cikin ranta na game da Uzair sai
ta kasa, haka ta wuni tana tunanin abunda ya faru tsakaninsu da Asim, da kuma
shawarar da Amira ta bata, a ɗayan ɓangaren kuma ƙwaƙwalwarta na ɗauke da hoton
abunda taga Ya Uzair yayi.
Har bayan Sallah Isha'i tana kiran wayar Asim amman ya ƙi ya ɗaga, ta tura masa
massage no reply, abun duniya duk ya bi ya dame ta.

Shigowar Anty Amarya ne yasa ta tsaita natsuwarta, har tana ƙoƙarin gyara zamanta.

“Abbanki yace na faɗa miki baƙonki ba zai samu zuwa ba”

Anty Amarya ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zaunawa saman gadon kusa da ita. Namra ta
ɗan kalleta kaɗan

“Miyasa?”

“Nima ban sani ba, amman na naji a waya yana cewa wai kin masa ƙarama, kuma yana
jin nauyinki”

Namra ta ɗan yi murmushi ƙaɗan ta kwanta jikin Anty Amarya.

“Shima dai yasan ni ba sa'arsa bace”

Anty Amarya ta shafa kan ƴarta.

“Allah dai yayi miki zaɓin da yafi alheri, ya yaye miki damuwarki”

“Amin Mamana”

KALSOOM POV.

Around eight thirty Kalsoom ta fito ɗakinta, a lokacin Saleena har ta wuce
makaranta. Ita ta haɗa musu breakfast bayan ta gama, ta zuba ma Dad da Momy nasu ta
ɗauka ta nufi part ɗinsu.
Bayan ta gaishe su, ta aje musu abincin tana ƙoƙarin rasowa Momy tayi mata tuni da
zuwa gidan ƙanwarta Zainab.

“Ban manta ba Momy, yanzu idan na shirya can zan fara zuwa na aje kayana sannan na
wuce aiki”

“Hakan yayi Allah ya kawo miki naki mijin”

Sai da ta amsa sannan ta tashi ta fice. Kala biyar ta ɗauka a maimakon uku, dan
tasan sai ta fi kwana uku a can, cikin ƙaramin akwati ta saka su, sannan ta shirya
kanta ta fice.
Kamar yadda ta tsara sai da ta fara biyawa gidan ta aje kayanta sannan ta wuce
gurin aiki. Biyu da rabi ta tashi daga aikin direct gidansu ƙawarta Salma ta wuce.

Ta taki sa'ah, tana shiga mijinta na fita. Sai da tayi Sallah Salma ta ɗebo mata
abinci ta ƙoshi sannan ta ɗauko mata zance.

“Kalsoom wani gari ne nake son muje tare da Ruƙayyah ita zata kai mu, ance malamin
yana aiki sosai dan mutane da dama suna dacewa”

Kalsoom ta sauke ajiyar zuciya


“Ni wallahi har na gaji da irin wannan shige-shigen, kullum ana abu kamar ba'ayi,
wani gurin ace aljanu ne wani su kuma su ce sihiri ne, na rasa gane kan matsalar
nan, Wani lokacin har ji nake kamar na kashe kai na”

Salma ta dafata

“Subhanallahi, haba Kalsoom ki daina wannan maganar mana, Allah ya baki aikin da
zaki iya taimakon kanki, Allah ya rufa miki asiri aure ne kawai Allah bai kawo miki
ba, shine kuma kike ƙoƙarin butulce masa, kina wannan maganar sai kace ba musulma
ba?”

Kalsoom ta lumshe ido ta buɗe ta kalli Salma cike da damuwa ta ce

“Salma duk abunda Allah ya ban da wanda zai ban bai kai kamar aure ba, aure shine
cikar mutuncin ko wace ƴa mace, ni fa ba dotse bace Salma ina da sha'awa ina tsoron
abunda zai kai ni ga halaka”

Salma ta riƙata tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali.

“Roƙon Allah baya faɗuwa ƙasa Kalsoom, komai zai zo ya wuce kamar ba'ayi ba, kuma
ba asan inda rabo take ba wata ƙila mu dace”

“Ni dai ba zan sake zuwa ko ina ba, na haƙura ballantana kinsan Ruƙayya ba a sirri
da ita, kuma ko munje ba wani dacewa za muyi ba, tun da babu wanda zai iya matso
maka da nesa kusa, babu wanda zai iya goge abunda Allah ya rubuta maka, sai dai
kawai su ci kuɗinka, na fawwalawa Allah komai daman da shi na dogara”

Duk yadda Salma ta so ta lallaɓa Kalsoom su je, sai taƙi dan ita yanzu ta riga ta
sadaƙar. Sai da Yamma Kalsoom ta bar gidan Salma.

__________________________________

How about dis journey?

#threefamily
# Vote
#Comment
#TeamNamra
#TeamKalsoom
#TeamHilal
#Candy
#Blog

Always check my website for more.

BEST REGARDS💖
Khadeeja Candy 🌺

www.khadeejacandy.com.ng
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


*PAGE - 3*

DOCTOR HILAL POV.

Bayan ya gama abunda yake ya shiga ya yi wanka, sannan ya fito falo ya yayi
breakfast, sai kuma ya sake dawowa ya tashi Rafiq ya shiya sannan ya fice.

Kamar yadda ya saba gidan Hajiya ya nufa dan kai Rafiq ɗin, kasancewar Hajiya na da
ƴan aiki da yawa masu kula da shi, wani lokacin ya kan aje shi a falo yace a shiga
dashi gudun kwankwamin Hajiya, ko kuma ya aje mata shi ya yayi saurin barin gidan.
Sai dai yau bai yi sa'ah dan yana shiga ya ci karo da ita cikin falon tana karyawa,
sun-sun-sun yayi ya gaisheta.

“Hajiya Barka da tashi”

“Barka dai mijin Hajiya, har ta tafi aikin ko? Bari dai kaji na faɗa maka na kusa
barin rainon ɗan ku”

Maganar tayi masa zafi, sai dai babu yadda ya iya tun da mahaifiyarsa ce, kuma idan
sabo ya saba da irin waɗannan kalaman daga bakin Hajiya da Alhaji, Murmushi yayi ya
shafa kan sa.

“Hajiya haƙuri dai za'ayi, kisan ƴan rainon nan ba tsoron Allah suke ba”

“Kai ai kana tsoron Allah, tun da har kakr barin Matarka tana shiga cikin maza tana
gogaiya, ace mace idan ta fita takwas na safe ba zata dawo ba sai cikin dare? Bata
da lokacin mijinta balle na ƴaƴanta”

“Hajiya kin san aikin banki ne, kuma ita ce Manager ta banki dole ne ta riƙa bada
lokacin can”

“Toh ta bar aiki mana dole ne? Amman ace mace ta bar Yaro ƙarami mai shan nono dan
kawai ta je aiki”

Murmushi kawai yayi ya tashi yana shafa kai yana faɗin

“Bari na wuce”

Har ya kai ƙofa bai ji tace masa komai ba, sai ya juyo yana murmushi yace

“Hajiya ni fa bana son fushin nan da kike da ni”

Wani kallo ta watsa masa

“Yaushe na ce ina fushi da kai?”

“Toh ai ban ji kince Allah ya tsare ba”

“Ko ban ce ba ai Allah tsare ka zai yi”

Wata irin dariya yayi, ya dawo yayi mata side hug

“Allah ya bar mana ke Hajiya, i love you”

Dariya tayi tana faɗin

“Jeka ka aikinka kamin Alhaji ya fito, kasan nashi faɗan babba ne”
Ficewa yayi yana dariya, zuciyarsa cike da shauƙin son mahaifiyarsa.
Uku da ƴan mintuna ya tashi aiki, sai da ya biya ya ɗauko Yaransa daga makaranta
sannan ya dawo gida, sai da suka yi sallah sannan ya zuba musu abinci suka ci, wani
lokacin lokacin ta kan tashi da wuri ta dafa musu abinci, wani lokacin kuma sai dai
yayi musu takeaway. Bayan sun gama ci suka shirya suka tafi Islamiya.

Haka Doctor Hilal yake fama da irin wannan kaɗaicin kamar marar mata, gashi shi ba
mutun ba ne mai son yawa fita, indai ba gurin aiki ba kullum zaka tararda shi a
gida.
Matarsa kuma ota da gidan sai dare, babu yadda ya iya tunda babanta ya tsaya kai
da fata akan lallai sai tayi aikin banki kasancewarta babbar ƴarsa, tana da ƙanne
maza amman ya tsaya akanta dan kawai yaga ya kashe mata aure, tun asali ba Doctor
Hilal ya so ta aura ba, shiyasa baya ƙaunar surikin nasa ko kaɗan, shi kuma baya
jin zai iya rabuwa da ita saboda yana son matarsa ita kuma tana sonsa.

Ulfah da Ezzah na dawowa daga makarantar islamiya, suka ɗauko Homework ɗin su
Doctor Hilal ya yi musu.
Gimbiyar tasa kan bata dawo gida ba sai bayan Isha'i. Da sallama ta shigo amman ko
inda take bai kalla ba balle har ya amsa mata sallamar, sai ta kwanto jikinta tana
masa shagwaɓa

“Yanzu zan yi sallah ka kasa amsa min haba Dear”

“Yaran ki har sun gaji sun yi bachi, yau kwatakwata Rafiq bai sha nono ba, idan ni
ina iya haƙuri na su kuma ba? Rashin ba su lokacin ki da kike shi zai sa ki kasa
karantar wane hali ƴaranki suke ciki”

Bata yi mamakin kalamansa ba, daman yakan yi fushi da ita wani lokacin, kuma ta
lura da hakan tun daga lokacin da samu promotion. Yana tashi tayi saurin sakin
handbag ɗinta ta riƙo shi, sai ya ture hannunta

“Zaki iya fushi da ni?”

“A'a ni Wallahi ba zan iya”

Ta faɗa a marairaice

“Toh ki koya daga yanzu, ta yadda za mu iya yin sati ba muyi magana da junan mu ba”

Rumgume shi tayi tana kukan shagwaɓa.

KALSOOM POV.

Ko da ta isa, Zainab na kwance falo tana bachi. Mayafinta ta aje ta ɗauki hijabi ta
saka, ta bi gidan gyara tass, sannan ta ɗora musu girki.
Haka ta kwana huɗu tana musu aiki, cikin rashin sakewa dan gani take kamar
Zainab ɗin da Mijinta zasu raina ta, ta kan abuɓda bai dace ba amman bata magana,
sai dai kwallafawa zuciyarta idan har ta je gidan sai ta faɗawa Mony irin zaman
auren da Zainab keyi. A kwananta na huɗun ne Momy tayi ma Mijin Zainab magana ya
kawo ƙanwarsa dan ta taya Zainab zama, Ranar da zata dawo ranar ce Zainab ta fara
awo cikin, dan haka dole ita ce ta rakata bata je aiki ba a ranar, asibitin ta je
aka yi ma Zainab komai, sannan suka dawo gida tare, da zimmar ita Zainab ɗin zata
koma gidanta da yamma.
Bayan sun gama cin abinci rana ne, Kalsoom ta ɗauko labarin dan Momy ta ja mata
kunne.

“Gaskiya Momy ayi ma Zainab faɗa, ya kamata ace ta canja rayuwa ta riƙa lurar da
mijinta abunda ya dace da wanda bai dace ba, kinsan mijinki fa kece makarantarsa ta
farko, gareki zai fara ɗaukar darasi”

Momy tace

“Mi akayi?”

“Sam sam sam mijinta baya son alheri kuma baya son yan'uwansa suna zuwa gidan,
sannan idan za ayi girki sai dai komai yaje ya siyo ƙire-ƙire kamar ba mai kuɗi ba,
idan fa kika saba masa da wannan rayuwar ita zai riƙa miki ko can gaba”

Zainab ɗin ta haɗe rai sosai irin bata ji daɗin maganar ba.

“Nifa gaskiya bana son haka, daga zuwa jinya sai kuma kizo kina faɗar sirrin gida
na”

“Ba ina faɗar sirrin gidanki bane, gaskiya nake faɗa miki”

“Toh ya kike son nayi masa? Ai halinsa ne idan yaga dama zai canja, Anty Kalsoom
kefa ba auren nan kikayi ba balle kice kinsan yadda abun yake, ki bari har kiyi
auren sannan ki faɗa min abunda da zan yi da wanda ba zan yi ba”

Saleena tayi farat tace

“Haba Anty Zainab daga an faɗa miki gaskiya”

Zainab ɗin ta yatsene fuska.

“Wane irin gaskiya, so take na masa bala'i ne ya sake ni nazo na zauna tare da ku”

Momy ta kalli Kalsoom tace

“Ki daina irin haka ba kyau, koma minene ki kyale ta can ita ta sani, ba kyau kana
faɗin sirrin ɗan'uwanka, ita fa rayuwar aure sai da haƙuri kuma ke baki yi ba balle
ki gane haka, ku daina wannan maganar bana so”

Duk maganar nan da Momy take kan Kalsoom na ƙasa saboda idonta daya cika da ƙwalla,
daga bisani ta tashi ta nufi ɗakinta tana hawaye. Saleena ma ta tashi ta bar musu
gurin tana harar Anty Zainab.

NAMRA POV.

Ranar Assabar aka yi walimar kamar yadda aka tsara, Namra na cikin ɗalibai talatin
da uku da suka haddace wani ɓangare na Alƙur'ane, da ban aka ware su aka karramasu,
aka kira manyan mutane suka yi musu kyauta.
Maryam na cikin Ɗaliban da suka sauka bana, bayan walimar makaranta sai da Anty
Amarya ta shirya nata walimar a gidan dan karrama ƴarta.
Ƴan'uwa da abokan arziki da dama sun samu halarta, cikin har da Anty Yasmin da
Ya Uzair. Anci ansha nama kam kamar mayankansa, ga uban takeaway da Anty Amarya ta
shurya gwanin ban sha'awa.
Ana sallah la'asar Ya Uzair ya tashi zai wuce dan Yasmin tace ita kam sai dare.
Anty Amarya ta ɗauko masa takeaway, ƙin karɓa yayi sai yace a bawa Namra ta kai
masa. Ba dan ta so ba ta karɓa ta nufi gurin Motarta fuskarta babu annuri. Shi ko
yana cikin motar ya hakince yana kallonta.

“Ba nace karki faɗa Yasmin ba? Shine har da buga mata waya ko?”

Ya faɗa bayan ya kai hannu ya karɓa.


“An faɗa mata ba, amman zan faɗa mata very soon dan ba zan bar ta ta cutu da kai
ba, ba zai yiyu ka laƙa mata cutar HIV ba ina zaune ina kallo”

“Wai miyasa idonki ya buɗe haka? Alaƙar dake tsakanin ki da Yasmin ita ce tsakani
ɓa da ke, kuma Yasmin matata ce babu ruwanki da lamarin mu”

“Idona ya buɗe ne tun daga lokacin dana fahimci kai fasiƙi ne, kuma wallahi sai na
tona maka asiri, har nema da kayi sai na faɗa”

Wani dogon tsaki taja, ta juya ta nufi hanyar falo.


Da wani irin kallo ya bita yana jin kamar ya kamo ta ya shaƙure, ƙwafa yayi ya rufe
motarsa.

Sai bayan sallah isha'i kowa ya watse, a lokacin ne Maryam da Namra suka samu damar
duba kyaututukan da suka samu, Ba wanda suka fi murna kamar na Abbah da yayi musu
kyautar Zinari, ihu suka riƙa yi kamar zasu tashi gidan dan murna, ba ma kamar
Marya data daɗe tana roƙon Abbah ya sai mata zinari.
A tare suka nufi part ɗinsa dan yi masa godiya, sai suka tararda shi zaune tare da
Hajiya barau fuskokinsu shimfiɗe da murmushi.
Guri suka samu suka zauna suna masa godiya, sai ya amsa da far'ah kamar ba shine
yake fushi da Namra ba, ita kanta abun ya bata mamaki sai dai kuma ta jidaɗin
hakan.
Daf da zasu tashi ne Abbah ya kira sunan Namra

“Khadija”

“Na'am”

Da faɗuwar gaba ta amsa, ta dawo ta zauna tana jiran ta ji abunda zai ce. Sai da
yayi gyaran murya sannan ya ce

“Kisan yadda nake da Uzair ko?”

“Na sani Abbah”

“Toh ya aiko Hajiya gata nan zaune ne yace yana son ƙara aure kuma ke yake so ya
aura idan na amince masa”

Dakan shida-shida gabanta yayi saɓanin uku-uku dana kowa ke yi, da sauri ta kalli
Abbah sai kuma ta sadda kanta ƙasa kamar wanda bata gane abunda suke faɗa ba.
Can ƙasa-ƙasa ta tsinkayo muryar Hajiya tana cewa

“Uzair kam ko wani gurin yaje neman aure ai mu zamu shige masa gaba, balle yace
yana son ƴar mu”

Abbah yayi murmushin jindaɗi yace

“Sosai kan, wallahi yaron nan yana da tarbiya, ga hankali”

“Kuma ina fatar Khadija ba zaki bamu kunya ba, zamu yi matuƙar farinciki idan har
kika amince da wannan auren”

Cewar Hajiya Barau. Abbah ya kalli Namra fuskarsa babu alamun wasa yace

“Zan baki kwana uku kije kiyi shawara, but lemme remind and warning you for the
last time, kar damar dana baki na shawar ki zo ki ce min ba ki amince da Uzair ba”

Bata iya cewa komai ba har na tsawon lokaci, sai kawai ta tashi tayi baya-baya ta
ƙara baya baya tana dafa kai kamar wanda zata faɗi, har sai da Maryam ta riƙa ta
suka fita.

____________________________________

Yauwan Comments din ku yawan typing dina, comments din ku gwarin guiwa ne a gare
ni.

#DOCTOR HILAL TEAM


#NAMRA TEAM
#KALSOOM TEAM
#UZAIR TEAM

#Comment
#Share
#Vote
#Blog
#Threefamily

BEST REGARDS 💖
Khadeeja Candy 🌺
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa04.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 4*

NAMRA POV.

Da kuka Namra ta shiga part ɗin Anty Amarya, sai ta zube ƙasa, ta jefar da sarƙar
da ke hannunta cikin parlor.
Hindatu da Aisha duk suka kalleta, Anty Amarya kuma ta nufo ta da sauri tana
tambayar ba'asi. Maryam ce ta faɗa musu abunda ya faru, dan Namra kuka kawai take
kamar wacce za'a cirewa, zaunawa Anty Amarya tayi kusa da ita, ta kai hannu ta riƙa
fuskar Namra idonta cike da ƙwallah ta soma magana

“Namra mi yake damun ki ne? Saboda Uzair yace yana son ki shi ne kike wannan kuka?
Ni kike sakawa a damuwa, ni kike son jama matsala, duk rashin biyayyar da zaki yi
ma mahaifinki laifin a kaina yake, ƙaurin suna zaki yi Namra, matuƙar kika ce ba ki
son Uzair, kuma ni za'a zaga, miyasa a duk lokacin da za'a miki maganar wani Namiji
sai kiyi kamar ki kashe kan ki? Namra mi yake damunki? Ke ce babba a gareni ke ya
kamata ace kina nunawa ƙannenki dai-dai da rashinsa, haba Namra haba, haba, haba”

A take ta ji kukanta ya yanke, sai ta share hawayenta ta unƙura ta tashi, ta nufi


ɗakinta.
Saman kujera ta zauna tana tunanin dalilin Uzair na faɗawa Abbah cewar yana son
ya aure ta.

‘Miyasa yaje ya faɗa Abbah? Ko ma ya aure ba auren Allah da Annabi bane zai min,
baya tunanin zumuncin mu da Anty Yasmin zai iya lalacewa? Ko dai wani abun ya ke
nufi da ni ne?’

Tashi tayi ta nufi gurin gadonta tana cigaba da tunani

‘Tabbas idan har na ƙi yarda da auren shi ni za'a zaga, Abbah zai iya ɓatawa da ni,
zan saka Umma cikin damuwa,

Wata ƙila yayi hakan ne dan na rufa masa asiri, ta yadda babu wanda zai san abunda
yake aikatawa’

Saman gado ta zauna tana murmushin takaici

“Idan kasan wata, baka san wata ba Uzair, kaine zaka zanje maganar auren ka da kan
ka, ko kuma na tona maka asiri Wallahi, ba zaka ci riba biyu a kai na ba”

Wayarta ta jayo ta shiga contact ɗinta ta nemo number Ya Uzair ta danna masa kira,
ringing tayi har ta katse bai ɗauka ba, haka ta jera masa kira kusan tara amman be
yi picking ba at the end sai mai ya kashe wayarsa.
Jin wayar a kashe ya matuƙar harzuƙa Namra sai kawai ta yanke shawarar kiran wayar
Yasmin, dan tana tunanin ko saƙo ta tura masa ba zai karanta ba.

Yasmin na kwance jikin Mijin mijinta wayarta ta yi ƙara, sai da tayi kamar ba zata
tashi sai kuma ta tashi a kasale ta nufi gun da wayar take.
Da far'ah tayi picking tana mata zolayar data saba mata a duk lokacin data kira
ta

“Ke miyasa zaki kira ni yanzu, mijina baya son wayar dare fa”

Namra bata jin wasar, sai kawai ta ce

“Anty Yasmin Ya Uzair na kusa da ke?”

“Yana nan manne da ni mana, ya akayi?”

“Ba shi wayar zanyi masa magana ne”

“Okay”

Ba tare da kwan-kwanton komai ba, ta nufi inda yake ta miƙa masa wayar.

“Gashi Namra na son magana da kai”

Gabansa ya faɗi, ya kusan five seconds yana kallon wayar kamin ya karɓa ya kara a
kunne

“Ina jin ki”

Cikin fusata Namra ta soma magana

“Ai daman so nake ka ji ni kuma ka maida hankali akan abunda zan faɗa maka. Uzair
ina jan kunnen akan kayi saurin janye maganar aure na, ko kuma na tona maka asiri,
ka je ka faɗawa Abbah cewar ka janye zancen aure na ko kuma ni naje na faɗawa Abbah
waye kai.
Uzair zan iya kiran family meeting dan kawai na tona maka asiri, kaga har Anty
Yasmin sai ta gujeka, kuma ka kunyata a idon duniya”

Murmushi yayi mai sauti


“Amman mi yasa ba zaki iya haƙuri na kunna wayana ba Namra? Wannan wane irin
matsuwa ne haka? Be kamata kina min haka ba, sai ki bari har komai ya kama sannan
kowa ya sani”

Be tsaya jiran abunda zata ƙara cewa ba ya kashe wayar yana girgiza kai, sai ya kai
hannu ya janyo Yasmin ta faɗo jikinsa ya shiga mammatsa breast ɗinta yana hura mata
iska a kunne.

“Bloody me Namra tace maka ne?”

Sai da ya kai hannunsa saman wandonta na bachi sannan yace

“Idan na faɗa miki zaki fahimta? Zaki min Uzuri?”

“Uhm”

“Bloody Son Namra nake kuma yanzu haka har na yi ma Abbah magana akan hakan, sai
dai ita tana jin kunyar ki”

Ɗauke wuta tayi na ƴan daƙiƙu, sannan ta zare hannunsa daga jikinta ta juyo ta
kalleshi

“Kasa a duniya babu wasan dana tsana irin wannan, dan Allah ka daina bana so”

Dariya yayi ya gyara zamansa ta yadda zata iya fahimtar zancensa

“Wallahi kin ji na rantse miki ko? Abunda na fada miki gaskiya ne, ƙara aure zan yi
kuma Namra zan aura”

Tashi tayi ta matsa baya tana masa wani kallo kamar ta ga dodo

“Karka haukata ni Uzair, karka raba min hankali gida biyu”

“Ai na rantse miki, kuma idan har baki yarda ba ki kira Hajiya Barau ki ji, dan ita
na aika ta faɗawa Abbah”

Kasa magana tayi, sai kawai ta rufe bakinta tana kallon wani gurin kamar mai
tunani, zuwa can kuma ta jiya ta bar ɗakin, shi kansa Uzair ɗin bata nata yake ba,
kalaman Namra yake tunani da nemawa kansa mafita.
A falo Yasmin ta dawo ta zauna, tana tunanin kalaman Uzair da son tantance
gaskiyarsa

‘Idan har ba da gaske yake ba, mi zai sa yayi min wannan furucin? Ni kaina ina
zargin irin yadda Namra take kula Uzair’

Bitar kalaman zuciyarta kawai take, wani ɓangaren tana ganin kamar Namra ba zata
iya mata haka ban, bayan ma ta san babu wanda Namra take so kamar Asim, ko kuma dai
tana yaudarar take dan ta karkatar mata da hankali?
Har garin Allah ya waye Yasmin bata iya tsayar da ƙwaƙwaran dalilin da zai sa
Namra ta iya cin amanar ta ba, kuma ta kasa gasgata cewar Uzair ba da gaske yake
ba.
Tun da tayi sallah asuba, ta koma saman gado ba dan bachin ba, sai dai kanta da
ta ji yana sarawa, kuma bata jin haɗa ma Bloody ɗinta breakfast a yau, dan tun jiya
ta warewa kanta ɗaki daban ta bar masa wacan ɗakin dan zuciyarta ta soma ɗasuwa da
ƙiyayyarsa.
Shi kuma be bi sawunta, dan yasan she need a space, ta yadda zata gasgata
kalamansa kuma ta san da gaske yake, shi kanshi da ace ya biyeta da be samuwa kansa
mafita ba.
Tun bakwai na safe yayi shirinsa na zuwa office, be damu da breakfast ba ya fito ya
nufi ɗakin da Yasmin take, yana taɓa ƙofar ya ji ta kulle, be tsaya komai ba ya
sauko downstairs ya buɗe Fridge ya ɗauko ruwa ya sha, sannan ya fice.

Ba tare da fargabar komai ba ya nufo gidan Abbah, tun da yayi parking ya sauya
yanayinsa zuwa na damuwa da ɓacin ciki.
Part ɗin Hajiya Barau ya fara shiga har wani sauke ajiyar zuciya yake. Murya ƙasa-
ƙasa yayi sallama, Jikokinta suka amsa masa. Be yarda ya zauna ba dan be ga alamun
Hajiya a falon ba.

“Ina Hajiya?”

Sai duk suka haɗa bakin gurin amsa masa

“Tana part ɗin Abbah”

Be tsaya komai ba ya juya ya nufi part ɗin Abbah yana ƙoƙarin ƙirƙiro ƙwalla.
Ƙwanƙwasa ƙofar ya fara yi sai da aka amsa masa daga can ciki sannan ya tura ƙofar
ya shiga da sallama.

Guri ya samu ya zauna ya natsu, yana sauko da kalaman da suke ƙwaƙwalwarsa zuwa
bakinsa.
Ya kusan minti biyar zaune sannan Hajiya Barau ta fito, tayi mamakin ganin Uzair
da wannan safiyar, a zatonta ma ko cikin yaran gida ne suka zo karɓa wani abu
hannun Abbah, zaunawa tayi tana kallon yadda damuwa ke shimfiɗe a fuskarsa ƙarara.

“Uzair lafiya kuwa?”

“Hajiya lafiya ba ƙalau ba”

“Toh mi ya faru?”

“Abbah yana nan?”

“Yana nan”

“Dan Allah ki kira min wata magana nake son mu yi”

Ba musu Hajiya ta tashi ta nufi ɗakin Abbah. Bata ɗauki wani dogon lokaci ba sai
gata ta fito tare da shi. Guri Abbah ya samu ya zauna yana amsa gaisuwar da Uzair
yake masa

“Lafiya ƙalau, lafiya dai kayi mana sammakon nan?”

Jimmm yayi kamin ya ɗago kai ya kalle Abbah ya ce

“Abbah ka gafarce ni, kuma ka fahimci dan Allah”

“Mi ya faru?”

“Abbah...”

Sai kuma yayi shiru, kamar mai jin nauyin furta, har sai da Abbah ya ce

“Am... Uzair ni mahaifinka ne, kuma ina tunanin kasan da hakan, so ka faɗa min
damuwarka kawai let your voice out”

“Abbah akan maganar dana aiko Hajiya ne na neman auren Namra, shine nake son a
yanje...”

Wani kallo Abbah yayi masa yana karantar yanayinsa.

“Daman kace kana son ta dan ka dawo daga baya kace ka janye?”

“Ko kaɗan babu hakan a raina Abbah, kawai na lura kamar bata so nane kamar akwai
wanda take so”

Abbah ya kalli Hajiya.

“Ke kika faɗa masa akwai wanda take so?”

“A'a Wallahi mi zai sa nayi haka?”

Cewar Hajiya tana ƙoƙarin kare kanta. Sai Abbah ya kalli Uzair ya ce

“Waya faɗa maka haka?”

“Abbah jiya ta kira ni da dare, gaban Yasmin tana min kalamai da basu dace ba, babu
irin zagin da bata min ba, sannan tayi min barazanar ɓata min suna matuƙar ban
janye maganar aurena da ita ba, tace min Asim take so kuma shi zata aura”

Abbah yayi murmushi yana gingina kai.

“Kurciya ho, ai Khadija ba ita zata aurar da kanta ta ba, kar wannan ya ɗaga naka
hankali, sai dai ina son ka tabbatar min da zancen ka, shin har yanzu kana nan akan
kuɗirinka na aurenta?”

Ɗagowa yayi ya kalli Abbah ido cikin ido.

“Abbah da bana son ta babu abunda zai sa na nemi aurenta, idan har zata amince da
aure zan fi kowa farinciki, sai dai idan bata so kar a cilastata gudun abunda zai
je ya dawo”

Abbah ya tashi tsaye yana faɗin

“Kar ka damu Uzair, kawai kaje ka fara shawarar date ɗin da kake so a saka musu na
aure”

Murmushi Uzair yayi ya sauka ɗaga kan kujera ya ɗuka yana yima Abbah godiya.

“Abbah na gode sosai Allah ya ƙara rufa asiri yaja nisan kwana”

Sannan ya kalli Hajiya yana faɗin

“Hajiya a taya ni godiya”

“Ba komai Uzair, ai kai ɗan mu ne”

Cewar Hajiya. Cikin farinciki yayi ma Abbah sallama. Uzair na ficewa Hajiya ta
kalli Abbah tace

“Amman ita kam Namra mi yasa tayi hakaɓ”

Abbah be ce mata komai ba ya kaɓe rigarsa ya nufi part ɗin Anty Amarya a fuce.
Haka ya shiga falo babu ko sallama sai sunan Namra yake kira iya ƙarfinsa. Duk
fitowa suka yi har Hindatu dake kitchen da Maryam da Aisha, Anty Amarya ta nufo
shi tana tambayar lafiya.
Wata harara ya watsa ma Namra sai da ta haɗe yawu da ƙarfi tayi ƙasa da kanta.

“Ni zaki watsawa ƙasa a ido? Ni zaki tozarta? Ɗan ƴar'uwata zaki kira ki ciwa
mutunci dan kawai yace yana son ki?”

Kasa magana tayi sai kawai ta fara kuka. Anty Amarya ta girgiza ta

“Namra kin kira shi ne?”

Kai ta ɗaga. Anty Amarya ta shiga salati. Cikin kuka Namra tace

“Wallahi bana son sa ne, na zan iya auren sa ba, haba Abbah da wane ido zan kalli
Anty Yasmin idan na aure shi”

“Da idon da kika kalle ni kika ce min kina son Asim”

Abbah ya faɗa a fusace yana zare mata ido. Anty Amarya tace

“Amman Namra ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, Uzair ɗin ne kike faɗin ba
zaki iya aurensa ba? Da me kika fishi toh?”

Karkato fuskarta tayi ta kalli Anty Amarya tana kuka

“Wallahi Uzair ba mutumen kirki bane, yace yana so na ne da wata manufa”

Anty Amarya ta nuna ta da yatsa

“Ke ai mutuniyar kirkice tun da Mahaifinki ya shimfiɗa miki tabarma, kika naɗe kika
jefar”

“Wallahi Uzair ɗan homo ne Abbah, maza ya ke nema ƴan'uwansa”

Lokaci ɗaya ta ji ɗaukewar wutar cikin kanta, wanda hakan ya haddasa mata ganin
waɗansu ƙananan taurari sakamakon wani irin mari da Abbah yayi mata, bata ankaro ba
ya ƙara mata wani, be tsaya komai ba ya sake marinta, kamin kace kwabo sai ga jini
ya gangaro ta hancinta kamar mai haɓo.

____________________

#Blog
#Comment
#Share
#Three-family
#Three-Team

http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa05.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


*PAGE - 5*

NAMRA POV.

Cikin takaici da jin haushi, Abbah ya nuna ta da tsaya.

“Ke baki isa kisa nayi magana ta tashi ba, a duk cikin ƴaƴana babu tsagerarra irin
ki, bari kuma kiji na faɗa miki weather you like or not sai kin auri Uzair, idan
kin haihu ranar da aka ɗaura miki aure da Uzair ki kashe kan ki”

A fusace ya juya ya fice. Anty Amarya ban da hawaye babu abunda take, sam bata ga
laifin Abbah ba, dan tana ganin duk abunda yayi mata ita taja, ita ma kanta
kwatankwacin abunda zata iya yi mata kenan, dan bata ga dalilin aibanta Uzair ba
dan kawai bata son sa, kasa cewa komai ta yi ta juya cike da baƙinciki ta nufi
ɗakinta.
Namra kan na risine gurin tana kuka, Maryam da Aisha na bata haƙuri.

Babu wanda zai fahimce ta saboda babu wanda yaga abunda ta gani, kuma bata da wata
sheda da zata nuna.
Hajiya Barau ce ta ɗauki zancen tana yayatawa, wai Namra ta yi ma Uzair ƙazafi dan
kawai bata son ta aure shi. Cikin sati maganar ta zagaye familyn su. Wasu kan sun
yarda duba da irin kuɗin da suka taso masa lokaci ɗaya, sai dai kyakkyawan halinsa
da mutane ke gani ya shafe wacan baƙin fentin da wasu suke ganin Namra ta shafa
masa.
Hakan da Namra tayi ba ƙaramin sosa ran Uzair yayi ba, ko ba komai ta ɓata masa
suna ta wani ɓangare, ga kuma rashin jutuwa daya samu da Matarsa Yasmin.
A ƴan kwana kin nan sai shiga cikin dangi yayi masa wuya, gani yake kamar sun
yarda da abunda Namra ta faɗa, a waya wasu ke kiransa suna nuna masa abunda Namra
ta yi bata kyauta ba, wasu har da yi mata Allah ya isa. Amman ita kan Yasmin ko a
jikinta, sai ma sha'aninta take kamar abun be dame ta ba.

Babu irin faɗan da mahaifiyarsa bata masa akan ya janye maganar auren nan, amman ya
ƙi saboda Abbah yaƙi bashi damar hakan.

“Uzairu ka janye zancen auren nan, ka faɗa maka, duk fa mutumin da yayi maka haka
toh ko kashe ka zai iya yi, wannan ƙazafin data maka zai iya shafar har aikinka, ni
ban taɓa ganin maƙiyiyi kamar Namra ba, ace ɗan'uwanka,
Aiko kama da gaske ne ka rufa masa asiri”

“Babu komai Umma Allah zai saka min, sai ta ga abunta inshallah”

“Allah dai ya isar maka, amman abun nan ya ɓata min rai matuƙa Wallahi, kai ma dai
da hange-hange kake mi Namra take da shi daya fi na Yasmin har kake son aurenta”

“Wallahi Umma tun lokacin dana auri Yasmin ina jin son Namra, kuma wannan walimar
da akayi na haddatan ƙur'ane kin san har da ita ciki, shiyasa naji na kwaɗaitu da
zama mijinta dan na samu mai bawa ƴaƴana tarbiya, tun da ni da Yasmin ba wani dogon
ilmin Islama ne da mu ba, sam ban tsammaci abun zai zama haka ba”

“Toh ai ko ilminta ya zama na banza tun da har ta iya yi ma ɗan'uwanta wannan


ƙazafin”

Haka dai suka yi ta hirar Namra Hajiya Binta na tsine mata har aka kira Azahar.
A masallacin gidan yayi sallah, sannan ya koma ciki yayi ma mahaifiyarsa sallama
ya fice. Babu abunda yake ji a ransa sai tsanar Namra, ji yake ko kashe ta yayi ba
zai huce abunda tayi masa ba.

A dai-dai gate ɗin gidan su Amira yayi parking, sai ya fita ya taka da ƙafa, ya
ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin. Mai gadi ne ya leƙo yana tambayar.
“Wanene?”

“Dan Allah Amira na ciki?”

“Eh tana ciki”

“Dan Allah yi min sallama da ita”

“Toh wa zan ce mata?”

“Ce mata manager ne”

Daga haka ya juyo ya dawo gurin motarsa, ya ciro wayarsa yana ƴan danne-danne. Ba a
ɗauki dogon lokaci ba sai ga Mai gadin ya dawo yana faɗin

“Wai tace tana zuwa”

Tsayuwarsa ya gyara, yana kallon ƙofar gidan har ta fito.


Cikin rangwaɗa da isa take tafiya har ta ƙaraso kusa da shi da sallama.

“Maraba da sarauniyar kyau, gimbiyar mata, kuma adon mata, nasan ba ki san ni ba
amman ni na san ki”

“Na sanka mana, ba kai bane Cousin ɗin Namra”

“I'm glad you remember”

“So what brought you here?”

“Ke ai ba sai kin tambaya ba, mace kyakkyawa irin ki mai hankalin da tarbiya, ai
dole ne ta riƙa samun masu ziyartar ta a duk lokaci, son ki ne ya kawo ni, zuciyata
ta kasa haƙura da ke na kasa haɗeye yawuna a kan ki, shiyasa kika gan ni a ƙofar
gidan ku”

Cikin salon jan hankali yake maganar yana murmushi. Ita kuma sai wani yauƙi take
abun ka da mata.

“Na ji matashin darasin ne kawai amman ban fahimcin karatun da yake cikinsa ba”

“Zan miki bita, na kuma fassara miki inda baki gane ba idan har mafaraucin zai
samun ganin Gimbiya anjima?”

Shiru tayi tana fari da ido.

“Sai ka shigo, kuma idan ka zo karka tsaya a waje ka shiga harabar gidan, kar ka
wuce ƙarfe tara”

“Consider it done my lady”

Buɗe motarsa yayi ya ɗauko bandur ɗin 1k ya miƙa mata.

“Ki shiga da wannan, zan yi farinciki”

A yadda ya karanceta be yi zaton zata karɓa ba, a take murmushi ya bayyana a


fuskarta, tasa hannun biyu ta karɓa tana masa godiya

“Na gode sosai”


“Never mention it again, my regards to mom please”

Fari ta ƙara masa da ido

“Sure”

Ta juya ta shige. Wani shu'umin murmushi yayi ya buɗe motarsa ya shiga.

KALSOOM POV.

SIX MONTHS LATER.... Tun da ta dawo daga Seminar take bachin gajiya, ta taje aiki
ta dawo sai bachi. Ga kuma ɓacin ran dake tare da ita, da tunani, dan ko ranar da
zata tafi seminar ɗin sai da Dad yayi mata jan kunne akan ta kame kanta, ya sake
maimata mata irin zagin da ake masa na yaƙi aurar da ita ya barta tana aiki sai
yawa take gare gare, Babu kuma yadda zai hana ƴarsa aiki, dan da shi take yima
kanta wasu laluraron ba dan kuma ya kasa ɗaukar nauyinta ba, sai dan rashin auren
da bata tayi ba, idan har yace zai hanata aiki sai yaga kamar be mata adalci ba,
kuma zai tauye mata haƙƙi damuwa zata mata yawa.
Sai dai burin iyaye ne suga sun aurar da ƴarsu sai idan hakan be samu ba, yadda
zamani ya lalace komai girman ɗan ka dole ne kasa mishi ido gudun kar ɓata gari su
lalata maka shi, musamman ƴa mace.
Ita kanta wani lokancin ba son zuwa seminer take ba, sai dai babu yadda ta iya tun
da haka kamfamin MTN ya tsarawa ma'aikatansa.
A ɗayan ɓangare kuma tana ganin kamar iyayenta ba su yarda da ita bane,
shiyasa suke takura mata da da yawan tambihi a duk lokacin da zata nisanta da su.
Tana ji a ranta har yanzu iyayenta ba su gama karantar ta bane, dan ta ɗaukarwa
kanta alƙwarin duk irin sha'awar dake damunta da son auren da take ba zata taɓa
aikata zina ba.

Da yamma ta tashi bachi, bayan ta ci abinci ta koma ɗakinta ta buɗe system tana
duba wasu abubuwan. A ɗakin Momy ta same ta tana labarta mata hukuncin da
mahaifinta ya yankena haɗata aure da Cousin ɗin ta Abubakar.

Gabanta ya faɗi, duk yadda take son aure bata jin zata iya auren Abubakar, mutumen
da duk a familynsu an buga masa tambarin neman matan banza, neman mata kawai yasa
ma gaba shiyasa auren ma kwata-kwata baya gabansa gashi yanzu har ya girmi tazurai,
ba dan kuma ya rasa matar aure ba.
A cikin yanayin damuwa ta kalli Momy tace

“Amman Momy mi yasa ba'a nemi shawara na ba, kamin ku yanke wannan hukuncin?”

“Yayi hakan ne dan yasan ba zaki bashi kunya ba, kuma ba mahaifinki bane yayi masa
magana, mahaifinsa na yayi ma Abbanki magana da amincewar Abubakar ɗin”

Girgiza kai tayi

“Gaskiya ni ba zan iya aurensa ba”

Wannan maganar da Kalsoom tayi ta fusata Momy har tasa ta canja fuska.

“Haba Kalsoom ana son a samu kiyi aure sai kuma kice ba zaki iya aurensa ba? Toh
idan ba shi ba kina da wani wanda zaki iya fitarwa a yanzu ne? Ba zaki bar ruwan
idon nan ba ko?”

Hannu biyu tasa ta dafe kanta. Sai yaushe Momy zata fahimcin matsalarta ne? Kullum
cewa take tana ruwan ido, taƙi ta tsayar da miji, alhalin ba ruwan ido bane, duk
mazajen babu na aure ko wanne da tasa matsalar.
Dagowa tayi ta kalli Momy tace

“Yanzu dan kawai ina son aure sai ace duk wanda ya zo min sai na aura? Abunda nake
it not calling ruwan ido it calling carefully planning for the future”

Momy ta taɓe baki

“Yanzu dai idan kunya zaki bawa mahaifinki sai kiyi, naji ma yana faɗar baya son
aja abun da nisa ina jin ba zaki wuce wata biyu a gida ba idan har kin yarda, kuma
ni ban san Abubakar da wani mugun hali ba, yana da rufi asiri yana da kyau kuma
baya shaye-shaye, neman mata ne kawai shi ma kuma bamu tabbatar ba tun da bamu taɓa
kama shi yana yi ba,
Kuma yanzu ai da wahala ace maza basu san mace ba, ko kuma basu taɓa aikata zina
ba, wata ƙila ma idan ya aure ki zai daina”

Idon Kalsoom ya cika da ƙwallah, ganin yadda Momy take gyara Abubakar dan kawai ta
aure shi.

“Idan kuma be daina ba, ƴarki zata cutu, Momy kisa wannan a zuciyarki”

Momy ta dafata

“Kiyi auren dan ibada Kalsoom, kuma ki auri Abubakar da zuciya ɗaya”

Tashi Momy tayi ta fice, ta bar Kalsoom cikin tunani da neman zaɓin Allah.

____________________________

Masu karantawa a blogger ina ganin ku fa, amman baku comments, sometimes zan samu
mutum 200+ sun leƙa website ɗin amman ba ku comments. Yadda kuka ga Wattpad haka
Blogger yake zai nuna masu karantawa, amman babu Comments, ina fatar zaku gyara.
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa06.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

Ƴan Taskar Khadeeja Candy wannan shafi na ku ne. Ina jindaɗin Comments ɗin ku keep
it up.🌺

*PAGE - 6*

NAMRA POV.

Har yanzu Asim baya ɗaukar wayarta, ta masa text ya fi a ƙirga, amman ba reply,
kuma tun ranar da suka samu matsala bata sake saka shi a idonta ba, scul ma ya
daina zuwa.
Hakan yasa ta yanke shawarar jan ƙawarta Amira su je gidan iyayensa, dan dubasa.
Haka kuwa akayi bayan an gama lacca, sun fito ita da classmates ɗin su, sai ta riƙa
hannun Amira ta nufi hanyar library da ita.
Amira biye kawai take da ita, amman hankalinta na can wani gurin, sai tunani take.
Saman balcony suka zauna, kamin Namra ta yi magana sai Amira ta fara yi mata
tambayar da ke cikin ranta.
“Namra kin ce da Uzair aka sa muku rana ko? Kuma kin ce baki son sa right?”

“Uhm”

“Ba taimakon ki zai yi ba?”

Namra ta yi mata kallon rashin fahimta

“Taimako kamar ya?”

“Haka dai na ji ana faɗa wai taimakon ki zai yi, dan Abbah ya bari ki auri wanda
kike so”

“Kowa ya faɗa miki haka ƙarya ne, idan har zan nemi taimakon wani toh ke ce zaki
riga kowa sani”

“Amman miyasa baki son sa?”

Shiru tayi, tana tunanin faɗa mata gaskiyar lamarin, sai dai tana jin har yanzu
Amira bata kai matsayi da zata san sirrin gidan su ba, wannan matsalar ta cikin
gida ce kawai, kuma ba komai bane zaka faɗawa ƙawa, dan ba kowa bane zai iya riƙe
maka sirrinka, wani kuma zai yi kallon ka da abun ne, duk kuwa da amincin da ke
tsakaninku.

“Amira so na ke ki raka ni gidan su Asim”

Ta ɗauko mata zancen ne, dan samun damar kawarda wancan tambayar da tayi mata.
Ajiyar zuciya Amira ta sauke, har yanzu kan ta kulle yake ta rasa dalilin da yasa
Uzair ya yi mata ƙaryar yana son ta, kuma ya ƙulla alƙawarin zai aureta, lalai
akwai wani abu a ƙasa.

“Zan raka ki mana, kwana biyu ya daina zuwa makaranta, nima ina tunani ko lafiya?”

Ta faɗa lokacin da Namra ta girgiza tana maimaita mata zancen.

“Tashi muje kamin four ta yi”

Namra taja hannunta suka tashi. Har suka isa gidan, Amira tunanin maganar Namra
take, wani ɓangare na zuciyar na nuna mata lallai Uzair so yake ya yaudareta.
Namra nayin parking ta dafa Amira, ganin tun ɗazu hankalinta baya jikinta.

“Wai lafiya kike kuwa?”

Saurin buɗe motar ta yi, gudun kar Namra ta samu damar zargin wani abu.

“Lafiya ƙalau, fito muje”

Fitowa Namra ta yi gabanta na faɗuwa, a bakin ƙofar gidan ta tsaya tana tunanin
abunda zata ce musu idan ta shiga.
Amira ce ta yi sallama taja hannun Namra suka kunna kai cikin gidan.

Ƙannen Asim ne suka amsa mata, mahaifiyarsa na haɗa ido da Namra, ta sauke kai ta
cigaba da ƙullin zoɓonta kamar bata gansu ba.
Har ƙasa Namra ta risina ta gaisheta, yayinda Amira ta gaisheta a tsaye. Can
ƙasan maƙoshinta ta amsa musu, fuska a haɗe kamar ta ga mutuwarta. Kasa magana
Namra tayi, har sai da Amira ta ce

“Umma ko Asim na nan?”


Ɗago kai ta yi tana musu wani ƙazamin kallo.

“Ai ku zan tambaya, dan yau kusan sati uku kenan, ban saka Ibrahim a ido ba, tun
ranar da ya zo nan yana hawaye yace kin cuceshi, ban sake ganinsa ba, ni kaina
nemansa nake”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Namra ta faɗa idonta na ƙoƙarin cika da ƙwalla.

“Wani Innalillahi zaki yi? Ashe kin san Allah? Babu irin roƙon da ban miki ba akan
ki rabu da Ibrahim amman kika ƙi, duk irin maganar da na masa a banza saboda idon
sa, ya rufe akan ki”

Amira ta yi saurin saka bakinta.

“Wallahi Umma ba haka ba ne, ita kanta Namra tana son Asim, laifin mahaifinta ne”

“Ni ban tambaye ku laifin kowa ba, dan Allah ku fitar min daga gida, kuma wallahi
sai Allah ya saka masa”

Har suka fito kuka Namra take, kasa tuƙa motar ta yi, sai Amira ce tayi driving
ɗinsu.

“Yanzu ina Asim ya tafi? Duk abunda ya same shi ni ce sila, ba zan yafewa kai na
ba”

“Namra ki daina kukan nan indai ba so kike muje gida a riƙa tambayar ki me ya faru
ba. Ke ni fa ban ma yarda da zancen ta ba, ta ya za'a ce namiji kamar Asim ya bar
gidan iyayensa dan kawai ya rabu da ke? Ai wannan fashion ɗin ya wuce”

“Zai iya saboda gudun waɗanda za su masa dariya, kuma ɓacin rai babu abunda ba ya
sawa Amira”

“Amman ke dan Allah rabuwa da shi be fi miki alheri ba? Saboda shi kika ɓata da duk
samarin ki, kuma mahaifinki ya ɓata da ke, shiyasa ma yanzu yake ƙoƙarin miki auren
dole, abunda aka bar yayi tun kakanni”

Shiru Namra bata ƙara cewa komai ba har Amira ta yi parking a bakin gate ɗin
gidansu Namra, dan bata jin shiga cikin gidan, ita ma kanta tana da nata damuwar.

“Ni dai zan wuce, idan kin gama kukan sai ki shiga da motar ciki”

Bata jira abunda zata ce ba, ta buɗe motar ta fice. Sai da Namra tayi kusan minti
talatin a gurin sannan ta buɗe motar ta fito ta dawo mazaunin direba ta yi ma motar
key tare da horn.
Mai gadin na buɗe mata gate, ta shiga da gudu har sai da tayi kaura da wata motar
dake gabanta fake.
Buɗewa tayi ta fito, tana cigaba da kukan ta nufi part ɗinsu.

Anty Amarya na tsaye jikin window tana kallon abunda Namra ta yi, tasan Namra da
zafin zuciya nan gaba har kanta zata iya jima ciwo da motar, ranta ya ɓace sosai,
ita kanta ta damu da halin da ƴarta take ciki, sai dai babu abunda zata iya yi tun
da ita ta jawo kanta haka tun farko.
Namra na shigowa Anty Amarya ta miƙa mata hannu.

“Bani makulin motar?”


Ba musu ta miƙa mata, tana share hawayenta, bayan Anty Amarya tace ta karɓi key ɗin
tace

“ATM ɗin Abbanki yana nan na aje miki, shi ya aiko yace a baki yace ki ciri ko nawa
kike so ki yi lalurarki, kuma yace ki samu ƙawayen ki ku rubuta events ɗin da zaku
yi, on Wednesday za'a kawo lefen ki da IV”

Wani irin abu ta ji ya ratsa zuciyarta, idonta cike da ƙwalla ta kalli Anty Amarya.

“A tunani na uwa ce zata fi kowa fahimtar halin da ɗan ta yake ciki. Ke kika haife
ni, ke kika raine ni har na kawo yanzu, ashe be isa yasa ki karance wacece ni ba?
Ashe za'a iya zuwa a'ce miki nayi kisan kai kuma ki yarda? ”

Anty Amarya ta sauke ajiyar zuciya.

“Namra kin yi furucin ne a idan ba zan iya goge zanen rubutun ba, ba zan iya musu
da Baban ki ba, idan har na goya miki baya wajen butulce masa duniya zata zage mu,
shi kuma ayi masa dariya ace ƴar waje na tafi ƙarfin sa. Ban san dalilinki ba,
amman nasan na za ki yi ma Uzair irin wannan sheirin ba haka kawai ba, amman ni da
ke duk babu abunda za mi iya yi”

“Na gode da kika fahimta, na gode da zuciyarki ta raya miki ba ƙazafi na yi ma


Uzair ba, Allah ya fahimtar da Abbah”

Anty Amarya tace

“Namra ina nan ina miki addu'ah, idan auren ki da Uzair ba alheri ba ne kada Allah
ya bari ayi shi”

Da kuka ta rumgune Anty Amarya

“Na gode”

Anty Amarya ta riƙa hannunta suka zauna, ta soma tambayarta taya ta ga Uzair yana
aikata wannan mummunan aiki na luwaɗi, kuma miye hujjarta.

Babu abunda Namra ta ɓoye Anty Amarya, tun daga lokacin daya fara nemanta, har
zuwa lokacin data kamashi da friends ɗinsa da irin gargaɗin da ya yi mata.
Anty Amarya taja wani dogon numfashi ta sauke tana jinjina lamarin.

“Lallai Uzair ya cika tantiri, shine kuma ya zagayo ya zo neman aurenki?”

“Ina tunanin yayi hakan ne dan Anty Namra ta rufa masa asiri, tun da mijinta ne ai
ba zata tona masa asiri ba, kuma kin ga yanzu data faɗa sai ta zama ita ce mai
laifi”

Cewar Maryam tana riƙe ƙoƙarin zama kusa da Namra.

“Amman miyasa baki faɗa min ba tun farko? Miyasa kika kirashi a waya kika masa cin
mutunci? da wannan ne ya zagayo yazo ya ɗaure ki a gurin Abbanki, miyasa ba ku
shawara idan zaku yi abu?”

Namra ta share hawayenta.

“Ban zaci abun zai zame min haka ba, nayi tunanin zai ji tsoro ya janye maganar
auren ne”

“A ƙasashen yahudawa Uzair yayi karatu, ya fiki iya makirci, kuma mai son abun ka
ya fi ka dabara”
Maryam ta kalli Anty Amarya

“Yanzu meye abun yi?”

“Abun yi kawai mu duƙufa da addu'ah, daga ke har ita, kuma In'shallahu wannan aure
Allah ba zai bari a yi shi ba, tun da akwai zalumci a ciki”

Sun daɗe zaune a falo suna firar, sannan Namra ta tashi ta nufi ɗakinta zuciyarta
cike da sassauci. Daf da zata shige Maryam ta kira ta

“Anty Namra”

Juyowa ta yi, ta amsa murya a daƙishe

“Na'am”

“Ki sawa zuciyarki sanyi, Mama na tare da ke, nima ina tare da ke, Allah ma yana
tare dake, kuma zai kawo miki mafita”

Daga inda take tsaye ta ɗan murmusa

“Na gode Maryam”

Ko ba komai ƴar hirar da suka yi, da goyan bayan da suka nuna mata, yasa ta samu
kanta da ɗan sakewa, tsaɓanin baya da take ganin kamar ita kaɗai ce a cikin
matsalar.
Daman komai na duniya yana son tattaunawa, ta haka ne zaka fahimci wasu, wasu kuma
su fahimce ka, matuƙar kace zaka kulle sirrinka a zuciyarka, shine mataki na farko
wajen gurɓata tunaninka, da jawa kanka ciwo.

Sai dai duk da haka maganar da Mahaifiyar Asim ta yi mata ɗazu ta tsaya mata a rai,
cewar Allah sai ya saka masa, yasa jikinta sanyi, da kuma zancen bata san inda
ɗanta yake ba.

“Ina ka shiga Asim? Miyasa zaka yi haka? Zaka lalata karatun ka, ka guji iyayenka
saboda ni Asim?”

Rumgume filo ta yi, tana tuna ranar da yake labarta mata irin rayuwar da suka taso
ta maraici shi da ƙannensa, da kuma irin wahalar daya sha kamin ya samu kuɗin
registration, wanda shi ya hana shi shiga makaranta da wuri.

Lumshe ido tayi, tana buga kanta da hannunta. Wayarta ta sake ɗauka ta kira layinsa
still switch off, sai kawai ta aika masa da sako.
Sannan ta kira Amira ta labarta mata yadda suka yi da Anty Amarya, da kuma goyon
bayanta da suka yi a yanzu.

************
ONE WEEK LATER...

Wednesday tun da sanyi safiya Anty Amarya da Maryam suka fara shirya abunda za
su tarbi masu kawo lefe dashi, snacks da meatballs da sauran abubuwa Hajiya Barau
ce tace zata yi, dan ɓangarenta za'a kai lefen.

Tun safe Namra ta bar gidan, kasancewar ba su da lacca sai kawai ta yanke shawarar
zuwa gidan su Amira. A can ta wuni tana aikin kuka, tun Amira na iya rarrashinta
har ta gaji ta zuba mata ido.
Sai bayan sallah Azahar Amira take labarta Namra wai jiya taga Asim. Da sauri
Namra ta kalleta.
“A ina kika gan shi?”

“Shi ya zo nan gidan, ya kara ni a waya na fito, kuma yace karka faɗa miki”

“Haba Amira? Baki faɗa masa halin da nake ciki bane? Wai da gaske kike ko wasa?”

“Na saba miki irin wannan wasan ne? Babu abunda ban faɗa masa ba akan halin da kike
ciki, kuma nayi-nayi ya faɗa min inda yake zaune ya ƙi, Namra karki so ganin Asim
duk ya koma wani iri”

Namra ta dafe kanta

“Wayyo Allah na. Da wace number ya kira ki?”

“Wata baƙuwar Number ce”

Ta ɗauko wayarta tana nuna mata number. Cikin rawar jiki Namra ta kofe number tasa
a wayarta ta soma kiransa. Ƙasa-ƙasa Amira take kallonta har kiran ya katse ba'a
ɗaga ba. Daga bisani sai aka kashe wayar gaba ɗaya.

Har aka yi Magariba Namra nata trying ɗin Number amman kashe.

“Ki haƙura da kiran nan Namra, idan ya ga dama zai kira ki tun da kin tura masa
saƙo”

“Baki fahimci yadda nake ji bane Amira, ni kaɗai na san halin da nake ciki”

“Yanzu dai kin ga anyi magariba, ya kamata a'ce kin koma gida, nima kuma ina son na
biki dan naga lefen, zaki ci abinci ko na haɗa miki tea?”

“Tea zai fi dan bana jin cin wani abu”

Tashi tayi ta fice daga ɗakin, sai gata ta dawo riƙe da kofin tea, yaji Lipton da
ginger da lemun tsami sosai har ya canja kala.
Ta daɗe riƙe da kofin kamin ta miƙa ma Namra.

“Ki daure ki shanye, tun da baki ci komai ba, nasan kina jin yunwa zai taimaka
miki”

Ba musu Namra ta karɓa, tayi bismillah ta riƙa kuɓa tea har ta shanye. Sannan ta
tashi sukayi Sallah, sai Amira ta ɗauko Hijabinta ta saka suka fito.

Napep suka tsaida, dan Namra yanzu bata da Mota tun lokacin da Anty Amarya ta amshi
key ɗin bata mayar mata ba, ita kuma Amira daman ba Mota ne da ita ba.
Magana suka masa yace zai kai su ɗari biyu, sannan suka shiga.
Be aje su ko'ina ba sai ƙofar gidan su Namra, Amira ce ta biya kuɗin, sannan suka
fito suka shiga cikin gidan.

A falon Anty Amarya suka tararda ƙannenta biyu, Hajiya Lariya, da Mama Zainab.
Cikin ladabi Namra ta gaishe su, suka amsa suna mata fatan alheri, sai yaba lefen
suke suna shi masa albarka.
Ita dai bata ce komai ba, idonta dai cike da ƙwalla, sai Amira ce take amsawa da

“Amin”

Fitowar Anty Amarya ne yasa Namra tashi tsaye, ta kalleta.

“Kin dawo?”
Nan ma Amira ce ta amsa

“Eh, Anty ina wuni?”

Anty Amarya ta lura da hawayen da suka idon Namra, kuma bata son ta yi kuka har
ƙannenta su fahimcin halin da take ciki, sai ta yi saurin cewa Amira.

“Lafiya Ƙalau, Amira ku shiga ɗaki”

Hannun Namra, Amira ta riƙa suka nufi ɗakinta.


Saman gado suka zauna, sai Namra ta kwanta jikin Amira tana kuka, jikinta duk ya
mace kamar marar lakka.
Amira ta ciro wayarta dake cikin pose, tayi ƴan danne-danne sannan ta mayarda
wayar, ta cigaba da rarrashin Namra tana bata Haƙuri.

Ba'ayi minti ashirin ba, sai ga kira ya shigo wayar Namra, da number da Amira ta
bata tace mata number Asim ce.
Cikin rawar jiki Namra tayi picking ta kara akunne tana.

“Asim! Asim!! Asim!!! Dan Allah kayi magana”

Shiru ba a amsa mata ba, daga bisani sai aka kashe wayar. Kira ta riƙa aika ma
number amman ba'ayi picking ba, bayan kamar minti biyar sai ga sako ya shigo
wayarta.

‘Namra ki fito yanzu, ina son na yi wata muhimmiyar magana da ke, ina nan bayan
layin ku ta gurin gidan Alhaji Sani’

Tana gama karantawa ta nunawa Amira, sai Amira ta riƙe ta

“Namra karki je...”

Sai kuma ta yi shiru kamar wacce ta tuno wani abu, sai ta kalli Namra da ke
kallonta tace

“Amman idan ba wannan ba, ba ki da wata dama ta ganinshi, kuma idan ba kije ba zai
iya fushi da ke”

Namra ta sauke ajiyar zuciya

“Zaki raka ni?”

“A'a ni ba zan je ba, kar a shigo ɗakin ba kowa, kuma idan mun fita tare za'a zarge
mu, wata ƙila ma Asim ya kasa yin magana da ke idan yaga muna tare, amman me zaki
ce wa Anty idan ta gan ki?”

“Nima ban sani ba, kuma idan har na faɗa mata ba zata bar ni naje ba”

“Toh karki faɗa mata, kibi ta ƙofar kitchen ki fita, zan jira ki a nan har ki dawo”

Ba tare da fargabar komai ba, Namra ta tashi ta nufi ƙofar fita.


Sai da ta fice sannan Amira ta ɗauki wayarta ta kira number, ana ɗauka ta ce

“Gata nan zata fito yanzu”

Namra na fitowa taga Anty Amarya na zaune falo tare da ƙannenta suna hira. Da
faɗuwar gaba Namra ta nufi kitchen ɗin, tayi sa'ah babu kowa a ciki.
Hakan ya bata damar buɗe ƙofar a hankali ta fice. Da wage-wage ta isa gate, nan ma
a hankali ta soma buɗe ƙofar, sai ga mai gadi ya taso ya nufo ta yana tambayar
lafiya.
Dan ya san indai ba dolen-dole ba babu abunda ke fitar da su da zarar anyi sallah
magariba, dan Abbah baya son fitar dare.

“Lafiya ƙalau, saƙo zan karɓo nan baya, yanzu zan dawo”

“Toh Allah ya tsare”

Sai ya maida ƙofar ya kulle. Sauri-sauri take tafiya tana wage, sai kiran wayar
take amman anƙi picking.
Sai data kai ƙarshen layin, sannan ta karya kwana ta nufi gurin daya kwatanta
mata, jiki babu ƙarfi sai jin take kamar ta faɗi, dan ƙafafunta basa iya ɗaukarta.
Kamin ta ƙarasa taji kamar ana binta a baya da mota, ta ɗan ji tsoro daman da
fargaba ta fito gida, kasancewar unguwarsu ba kasafai zaka ga mutane ba ko da rana
balle da dare, ga kuma fargabar kar wani ya ganta yaje ya faɗa a gida. Tsayawa tayi
tana kallon ƙatuwar Bus ɗin mai baƙin gilashi.

Wasu maza ne guda huɗu suka fito ɗaga ciki Bus ɗin suka nufo ta ciki har da Uzair,
ganin Uzair ne ya hana ta gudu daman can bata jin ƙarfin gudun, sai ta tsaya tana
masa kallon mamaki da tunanin me ya kawo shi nan.

‘Daman yana biye da ni kenan? So yake ya tona min asiri yace ya gan ni na gana da
Asim da dare ko me?’

Kiran daya shigo wayarta ne ya ankarar da ita daga tunanin da take. Number ce wanda
aka turo mata saƙo da ita da sunan Asim ne. Da sauri ta kalli Uzair daya ƙaraso
kusa da ita

“Uzair daman kai ne? Ko kuma wayarsa ka karɓa?”

Ta tambaya a kasale, jiri na ƙoƙarin ɗaukarta.


Murmushi kawai ya yi mata, ya kai hannu ya riƙo ta iya ƙarfinsa.
A nan Allah ya bata ikon yin ihu da dukan muryarta. Cikin sauri mutumen dake tare
da Uzair ya fitar da wani ƙyalle ya danne mata hanci dashi, daga nan bata sake
sanin inda take ba, sai numfashinta ya ɗauke dif.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa07.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

NOT EDITED⚠

*PAGE - 7*

A hannunsa ta suma, sai ya ɗauke ta ya miƙawa mazan da yake tare da su yana faɗin

“Ku shiga da ita, kuma ku tabbatar bata farka ba, har sai na dawo”

“Yes Boss”

Cikin girmamawa suka amsa, suka saka ta cikin Bus ɗin. Sai da Uzair ya ga sun bar
gurin sannan ya nufi ƙofar gidan Alhaji Sani inda yayi parking ɗin Motarsa.
Bude Motar yayi ya shiga, ya ɗauko wani turare ya fesa, sannan yayi ma Motar key.
Ribas yayi ya dawo ta bayan layin sai gashi a bakin gate ɗin gidan su Namra.
Horn yayi mai gadin ya buɗe masa yana gaisheshi. Guri ya samu a harabar gidan ya
yi parking.
Sai ya fita ya taka da ƙafa ya isa part ɗin Abbah, dan yaga motarsa a waje,
alamar yana nan kenan.
Hankalinsa kwance ya shiga falo, Abbah na kishimgiɗe yana duba jarida, Uzair ya
shigo sai yayi saurin zubewa ƙasa yana kwasar gaisuwa.

Da far'ah Abbah ya amsa, yana nuna masa gurin zaman, bayan sun gama gaisawa, sai
Uzair yayi shiru be ce komai ba har sai da Abbah ya kalle shi ya ce

“Uzair kana da wata magana ne?”

Abbah ya tambaya, yana mai jin son Uzair ɗin a cikin ransa, kusan ma ya fi kowa
jindaɗin wannan haɗin, dan Allah ya sa masa son Uzair shiyasa komai na harkar
kasuwancinsa sai ya saka shi, duk kuwa da cewar shima yana da ƴaƴa maza.

Sun-sun ya yi da kai

“A'a Abbah, akan maganar IV ne na mata, har yanzu Namra bata rubuta ba, kuma lokaci
na tafiya, shine Hajiya tace na zo, na mata magana, shine nace bari na gaishe ka”

Abbah ya yi murmushi irin nasu na manya, sannan ya yi gyaran murya yace.

“Uzair sai ka yi haƙuri da lamarin Khadija, har yanzu akwai ƙurciya a tare da ita,
kuma ita ba zata gane alfanun wannan auren ba har sai anyi, haƙiƙa ina son Khadija
matuƙa sai dai tayi tsalle ne da ɓata rawarta tun daga lokacin data tsaya kai da
fata akan lalle ita sai wannan yaron,
na bata dama na fitar da wani ta ƙyale wannan yaron amman sai ta buga min ƙafa a
ƙasa ita sai Asim, shiyasa kaga na fita lamarin ta, saboda so da yawa zaka abunda
mu iyaye muke hangowa ba shi ƴaƴa ke hangowa ba, a tunanin ta na yi mata hakan ne
dan na cutar da ita, tun da ta nuna bata so.
Nasan anbar auren dole a yanzu, amman duk abunda na yi ma Namra ita ta jawa kanta”

Abbah ya ɗaga kai ya sake kallon Uzair da kyau yana mai nuna masa abunda yake faɗi
a bakinsa shine a zuciyarsa.

“Uzairu ina fatar zaka riƙa Khadija da amana, kuma zaka nuna mata so da kulawa,
irin son da zata san lallai ta yi dacen mahaifinta be mata mugun zaɓi ba, ina son
ka sani duk abunda ya samu Namra ni ya sama, kuma zai taɓa mahaifiyarta, ina addu'a
wannan aure Allah ya sa masa albarka, ya baku haƙuri zama da junanku”

Jikin Uzair yayi san yi sosai da kalaman da Abbah yayi masa, sai yake jin kamar
Abbah ya san abunda yake son aikatawa.
Cikin rashin kuzari ya yi ma Abbah sallama, ya tashi ya fice.

Har ya iso gurin motarsa tunanin kalaman Abbah yake.

‘Abunda duk ya sami Khadija ni ya sama’

Same shi ya fi tsaya masa a rai, tunani yake what if Abbah ya gane gaskiyar
dalilinsa na neman aurenta? Shi kuma baya jin yana da wata mafita ta rufa ma kansa
asiri bayan wannan, tun shi dai ba zai ce zai kashe Namra ba, gashi ta ce sai ta
tona masa asiri.

Ya kwashe minti arba'in a gurin yana tunani, ba tare da ya sani ba. Can sai ya nufi
gurin Mai gadin yayi masa magana kan ya shiga yayi masa sallama da Namra.
Cikin girmamawa mai gadin ya nufi part ɗin Anty Amarya, shi kuma ya dawo gurin
Motarsa ya tsaya ransa a jagule.

In few minute Mai gadin ya dawo ya shaida masa ance gata nan zuwa. Chanji ya fiddo
a aljihunsa ya miƙawa Mai gadin, sannan ya gyara tsayuwarsa yana jiran fitowarta.

Lokacin da Mai gadin ya shigo falon, Anty Amarya, na zaune tare da ƙannensa suna
cin abinci, sai tace da Mai gadin yace tana zuwa, sannan ta tashi Maryam ta ce taje
ta kirata ɗakinta.

Maryam ta aje littafin dake hannunta ta tashi ta nufi ɗakinta. Tana yin sallama
Amira ta zabura kamar marar gaskiya.

“Anty Amira, ina Anty Namra?”

Shiru tayi tana dube-dube kamar mai neman abu, can kuma ta kalli Maryam tace

“Maryam idan na faɗa miki wani abu zaki fahimta ai ko?”

“Uhmm minene?”

“Namra ta fita ɗazu, Asim ne yayi mata texs wai yana son ta zo suyi sallama, shine
ta fita tun ɗazu”

Gaban Maryam ya faɗi

“Amman kika barta taje ita kaɗai? Idan wani abun ya same ta fa?”

Shiru tayi tana tunanin ƙaryar da zata ƙaƙaro

“Ba yadda ban yi ba, amman tace ba zan bita ba, wai na tsaya kar a zo nemanta ba'a
ga kowa ba, amman bari na kirata”

Cikin sauri ta shiga kiran wayar. Maryam bata tsaya ba, ta juya ta fita.
Daga bakin ƙofa ta tsaya tana kiran Anty Amarya. Daker ta taso saboda abincin da
suke ci da kuma firar da suke da ƴan'uwanta.
A tunaninta Maryam zata ce mata Namra taƙi zuwa ne, sai kawai taji wani labari
banbaragwai. A take Anty Amarya ta ɗauko wayarta ta shiga kira amman ba a picking.

Sai duk hankalinsu ta tashi, Anty Amarya ta koma ɗakin Namra ta samu Amira zaune
tana faman kiran waya.

Anty Amarya ta katsa mata tsawa.

“Ina tace miki zata?”

Jiki na rawa ta amsa ma Anty Amarya dan ta ga ranta ya ɓace sosai.

“Tace min nan bayan layi”

“Amman dai Anty Amira kin yi wawanci Wallahi, shine kika bar ta taje? Maimaiko ki
hanata ko ki faɗawa Anty, kuma kika ƙi binta kuje tare”

Maryam ta faɗa tana hararar Amira. Anty Amarya tace

“Ita ma Namra ai da wayon ta”

“Ko da wayonta ai wani abun sai an nuna mata, tun da kinsan yadda Anty Namra take
ko ni sai na fita wayo, waya sani ma ko da ke ya haɗa kai kika lallaɓa masa ita ta
tafi”
Amira ta kalleta

“Haba Maryam wane irin magana kike haka ne? Kina tunanin ni zan iya cutar da
Namra?”

“Waya sani abu a duhu, ƙawayen yanzu ai ba abun yarda bane, kuma Wallahi duk abunda
ya samu Namra ki ƙaddara ke ya sama dan ba zan taɓa yafe miki ba”

Amaimakon Amira tayi magana sai kawai ta fashe da kuka, ta tashi ta ɗauki pose
ɗinta ta fice tana kuka.
Anty Amarya sai ta hau Maryam da faɗa

“Wai Maryam ba zaki bar fitsarar nan ba ko? Kullum ina miki magana kan shegen bakin
nan naki amman baki ji, yanzu miye na wannan furucin fisabillahi? Ita Namra ƙaramar
yarinya ce da Amira zata ɗorata a layi ta hau?”

Maryam ta tunzure baki.

“Wallahi zata iya ɗora ta a layi wannan Amirar da kike gani shegen wayo ne da ita,
kuma Wallahi tun ba yau na lura kamar tana hassadar Anty Namra, wani fa sam baya
son yaga cigaba a gareka sai ci baya, kuma wani maƙiyi na ɓoye ba gane shi ake ba”

Anty Amarya ta katsa mata tsawa

“Zaki je kiyi magana da Uzair, ko tsayawa zaki yi, kina ƙara min ɓacin rai”

Juyawa tayi ta fita tana faɗin

“Wallahi duk wani abu ya samu Anty Namra Amira zan zarga”

Ɗakinta ta shiga ta ɗauki Hijabinta ta saka, sannan ta fito ta nufi harabar gidan
gurin da Uzair yake, tana harararsa.

“Bata jindaɗi ba zata iya fitowa ba”

Ta faɗa ba tare data masa sallama ba, kuma bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta
juya tayi tafiyarta.

Wani kallo ya bita dashi, daman duk cikin Family Abbah Maryam tafi uban kowa
tsageranci. Buɗe Motarsa ya yi ya shiga zuciyarsa cike da tunane-tunane, hannu yasa
ya shafa kansa, sai ya ciro wayarsa ya nemo wata number ya danna mata kira.
Ana yin picking ya ce

“Tahir kana ina?”

Ban ji me aka ce masa ba, sai kawai yace

“Ok gani nan zuwa yanzu”

Daga haka ya kashe wayar, ya ƙarama gudu. Can kaɗai ne yake jin zai iya tafiya ya
fayyace sirrinsa, tun da duk akan layi ɗaya suke.
Sai da ya yi tafiya mai nisa, sannan ya isa bakin wani ƙaton gate.
Horn yayi mai gaɗin ya buɗe masa sannan ya kunna kai cikin ƙaton guesthouse ɗin.
Parking ya yi, ya fito ya nufi hanyar shiga gurin. Zazzaune ya tararda su, Tahir da
Najeeb. Tun daga ganin yanayin shigowarsa sun san akwai wani abu a ƙasa. Tahir ne
ya fara magana

“Lafiya kake Uzair?”


Bakinsa ya cika ma iska ya busar

“Wallahi ina cikin matsala”

“Matsalar me?”

Najeeb ya tambaya, cike da son sanin abunda ke damun amininsa.


Uzair be ɓoye aminansa komai ba, tun daga ganin da Namra tayi ma friends ɗinsa na
Abuja har zuwa nemanta da yayi, kuma kalaman da Abbah yayi masa yanzu, sannan ya
ɗora da sace ta da yayi.
Tahir ya girgiza kai

“Uzair you Fuck up, ai yin wannan abun da kanka matsala ne, mun riga mun san junan
mu toh miye na ɓoyewa kasa kanka a matsala? Yanzu ka sace yarinyar mutane kana
ganin asirinka ba ze tunu ba?”

“Nayi tunanin zan iya solved ɗin matsalar ne, da nayi nufin na riƙe ta ne har kwana
biyu ta yadda za a yi tunanin ta gudu da bi saurayinta ne. Ga Yasmin ta juya min
baya na rasa gane kanta, kuma yanzu idan ta dawo zata iya faɗa asirina ya tonu kuma
kasan komai ze iya faruwa, family ni za a zaga kuma.mahaifinta ba zai ƙyale ni ba”

Tahir ya dawo kusa da shi ya dafa shi.

“Ka kwantar da hankalinka, irin wannan yarinyar ta dabara bata musu, kuma irin
wannan sirrin ba a sake da shi”

Najeeb yace

“Lallai kam, irin wannan yarinyar malamai za a shiga da ita, fiussss an gama da
ita”

Tahir yace

“Shine kawai, yanzu kaje kayi abunda zaka yi da ita, kasa a maida ita gida kamin
asuba, zan rubuta maka wani magani ka bata tasha zata manta abunda ya faru, idan
Jafar ya dawo zamu zauna mutattauna”

Murmushi jindaɗi yayi, yajin ya samu mafita gurin abokansa.


Cikin kuzari ya tashi bayan Doctor Tahir ya rubuta masa maganin a takarda, ya yi
musu sallama ya fice.

__________________________
LOVE YOU ALL FISABILLIAH 😘
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 8*
Yana cikin mota yana driving zuwa guesthouse ɗinsa, kiran Najeeb ta shigo wayarsa.
Picking yayi ya kara a kunne sai ya mai da tuƙin da hannu ɗaya.

“Hello”

“Uzair kana ina? Ka isa gidan ne?”

“A'a gani dai kan hanyar zuwa siyen maganin”

“Karka siyo ka wuce gidan kawai, idan ka isa ka jira ni gani nan zuwa, kuma ka
tabbatar bata farka ba, idan kuma ta riga ta farka, karka bari ta gan ka, ina ka
aje ta?”

“A guesthouse ɗina”

Sai ya kashe wayar, ya ƙara ma Motarsa gudu. Yana isa, Najeeb na isa. Sai duk suka
yi saurin fitowa Motar. Najeeb ya nufi shi yana faɗin

“Yanzu ya kamata mu mai da ita gida”

“Taya?”

Najeeb ya kalli ko ina na gurin, sannan yace

“Ni zan kaita, faɗa min inda ka ɗauke ta, zanje can na maidata, zamu saka mai gadin
nan naka ya je a inda take ya riƙa ihu da neman taimako har mutane su taru su, su
nuna masa gidansu, zai bamu haɗin kai dai ko?”

“Me zai hana indai an bashi kuɗi”

Uzair ya faɗa.

“Okay zan tsara masa yadda zai yi, miye sunan Saurayin nata?”

“Asim sunan shi Ibrahim, amman anfi saninsa da Asim”

“Good yanzu kira ɗaya daga cikin masu tsaronta ya duba mana idan bata farka ba”

A take Uzair ya ciro wayarsa. Najeeb kuma ya nufi gurin mai gadin.
Ɗaya daga cikin yaran ne suka shaida masa har yanzu bata farka ba. Shi kuma ya
nufi Najeeb ɗin ya faɗa masa.
Sai da Najeeb ya gama tsarama mai gadi yadda zai yi, sannan ya juyo gurin Uzair.

“Good yanzu kasa su ɗauko ta, su saka ta a mota na, sai ka shiga taka motar ka nuna
mana daidai inda ka ɗauke ta”

“Baba Audu zaka iya ko?”

“Ƙwarai Zan iya ranka ya daɗe ai wannan abu ne mai sauki, kuma taimako ne”

Baba Audu ya faɗa da kansa. Sai Najeeb yayi murmushi.

“Zamu baka dubu ɗari idan aiki yayi kyau, zamu baka wasu dubu ɗari na rufar sirri,
ka tabbata dai ba'a samu matsala ba”

Har ƙasa Baba Audu ya risina yana godiya baki har kunne.

“Allah Ubangiji ya saka da alheri, ai ni ko baka bani komai ba, zan iya maka fiye
da wannan”
Najeeb ya nuna masa Mota.

“Kaga Mota can je ka shiga gidan gaban”

Sai kuma ya kalli Uzair

“A fito da ita yanzu”

Cikin sauri Uzair ya nufi gurin, be daɗe ba ya fito, wani namiji na ɗauke da ita.
Ita kuma ta langwaɓe kamar wacce ta mutu.
Najeeb da kansa ya bude Motar suka saka ta gidan baya. Sannan Najeeb ya shiga
driver seat, Baba Audu ya shiga front seat, Uzair kuma ya shiga Motarsa, sai ya
shiga gabansu dan nuna musu hanya.

Cikin mintuna suka isa gurin. Can nesa da gurin suka faka, sai Najeeb ya buɗe motar
ya fito da ita. Uzair ya nuna dai-dai inda ya ɗauketa sai Najeeb ya ajeta a gurin,
yasa car key ɗinsa ya ɓarke mata Hijabi, ya yagashi, ya barƙa rigar afamfar dake
jikinta, har rabin breast ɗinta ya fito.
Sanna ya ɗago ya kalli Uzair

“Ta fito da waya?”

“Yes ga wayar ta nan hannu na”

Ya faɗa yana ƙoƙarin cirota daga aljihunsa. Najeeb ya miƙa masa hannu

“Wani wayar zan taka ta da mota, kuma ka bani layin da ka kira ta da shi”

“Why?”

Najeeb yayi masa wani kallo

“Haba Uzair ya kake abu kamar ba wayaye ba? Baka san za'a iya amfanin da wayar a
gano sawon hannunka ba? Za a iya gano ka idan kana amfani da layi, kuma yanzu ai
amfanin layin ya ƙare”

Kamin Uzair yayi magana, kiran Amira ya shigo wayarsa. Da sauri Najeeb ya tambaya.

“Who's calling?”

“Her Best friend”

“Did she know?”

“Yes tare da ita muka haɗa komai”

“Karka yi picking call ɗin nan it risk, let's go kar wani ya gan mu”

“Da wahala wani ya gan mu, baka ga yanayin gurin ba? Ko da rana ba a cika wucewa ba
balle yanzu pass 11 fa”

Najeeb yayi murmushi, irin na har yau baka waye ba Uzair. Sai kuma ya kalli Baba
Audu

“Da ka daina hango hasken Motar mu, zaka fara ihun”

“Toh ranka ya daɗe”


Cikin sauri suka nufi motocin su, Najeeb sai wage-wage yake kamar mai neman wani.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa09.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 9*

A lokacin da Baba Audu ya daina hango su, sai ya buɗe dukanin muryarsa ya kwarara
uban ihu yana neman taimako.

“Wayyo Allah jama'ah a taimaka mana, a ceto rai, jama'ah ku kawo agaji”

A yanayin gurin, ba kowa bane zai iya saurin fita, saboda yanayi na tsoro da ake
ciki, gashi ta bayan layin unguwar ne ba mutane sosai.
Cikin ƙarfi hali da bugawar zuciya, Baba Audu yake ta kwarara ihun yana wage-wagen
jiran wanda zai fito.
Tsinta-tsinta aka fara fitowa ana nufar gurinsa, sai tambayarsa suke lafiya. A nan
ya soma ƙirƙiro hawayen ƙarfin hali yana faɗa musu abunda Najeeb ya tsara masa.

“Wallahi wasu mutane yanzu suka jefo da wannan yarinyar daga mota, kuma suka zo
suna ƙoƙarin taɓa mata mutunci”

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Shine abunda kowa yake faɗa, dan makamacin
wannan be taɓa faruwa a unguwar ba. Wani dattijo ya kai hannu ya gyara mata
Hijabinta, ta yadda zai suturta mata breast ɗinta dake buɗe.
Waɗanda suka santa sun gane ta, sai dai kowa mamaki yake, yana tunanin suye ne
suka mata haka? kuma a ina ta haɗu da su haka.
Wani saurayi ne ya kawo ruwa aka zuba mata, amman shiru bata farka ba, haka akayi
ta zuba mata ruwan but still bata motsi. Anan mutane suka ce a ɗauke ta a kaita
gidansu

*** *** *** ***


Babu irin kiran wayar da Anty Amarya bata yi ma Namra ba, tun tana ringing har aka
kai ga kashe wayar.
A lokacin hankalinta ya tashi sosai, ita da Maryam har Aisha da Hindatu sai da
hankalinsu ya tashi.
A take Anty Amarya ta fara kuka, tana tunanin abunda ze samu ƴarta, kuma tana
tsoron kar Abbah yaji, sai duk tabi ta rikice ita da Maryam. Aisha da Hindatu suka
ce zasu je bayan layi su duba ko Allah yasa zasu same ta.

Anty Amarya ta share hawayenta.

“Babu inda zaku je cikin daren nan, bayan layi da yake da duhu idan wani abun ya
same ku fa, ban san abunda yasa Namra ta raina ni ba, ta ya zata saka ƙafa ta fita
ba tare data faɗa min ba? Duk abunda ya same ta ita tajawa kanta”

Maryam ta ɓata fuska.

“Gaskiya Anty Namra bata kyauta ba, amman da kin bari munje mun duba ko zamu ganta”

“Babu inda za ku je, idan Abbah ku ya gani kuce masa me?”

“Abbah ba ze gani ba, tun da yana part ɗinsa, kuma ba daɗewa zamu yi ba, dubowa
kawai zamu yi mu dawo”

“Babu inda za ku je yanzu goma ta wuce, inda har kuna jin magana ta, toh karku je
ko ina nemanta, ai ita ta kai kanta, ina zaune falo tabi ta ƙofar kicin ta fita, ba
dai-dai bane tasa ƙafa ta fita ba tare da sani ba”

Anty Amarya na gama faɗar hakan, ta tashi ta nufi falo tana hawaye. Yanzu kan babu
abun ɓoyewa dole ta faɗa ma ƙannenta abunda yake faruwa, su kansu basu jidaɗi ba,
sai laifin Namra suke gani, wai taya zatayi haka kamar wata ƙaramar yarinya.

Haka suka yi zaune jugum, kowa sai addu'ah yake, babu irin roƙon da Mama Zainab
bata yi ma Anty Amarya ba akan ta bari suje su dubota, amman ta hana.
Har kusan shaɗaya babu wani labari, sai shabiyu saura kwata, suka soma jin hayaniya
a habarar gidan, sai doko musu sallama ake da muryar maza.

Wani irin faɗuwa gaban Anty Amarya yayi, har sai da ta dafa zuciyarta ta lumshe
ido. Mama Zainab da Hajiya Raliya ne suka riga fita, Aisha da Hindatu suka rufa
musu baya.
Maryam kuma ta tsaya kusa da mahaifiyarta ganin halin da take ciki. Cikin ƙarfin
hali Anty Amarya ta tashi, Maryam ta ɗauko mata hijabinta ta saka sannan suka nufi
ƙofar fita.

Ko da suka fito har Hajiya Barau ta isa gurin, Abbah kuma ya fito daga part ɗinsa
ya nufi gurin da mutane suke tsaye, riƙe da Hannun jikan Imam jikan Hajiya, da
alama shi ya je ya faɗawa Abbah.
Cike da kasala Anty Amarya ta ƙasara gurin ita da Maryam. Tana ganin halin da Namra
take cike gabanta ya ƙara faɗuwa, a take kasala ta sauki mata. A nan Maryam ta fara
kuka ganin Namra kwance kamar matatta ga Hijabinta a yage.
Abbah ya kalli mutanen cikin tashin hankali.

“Miya faru? Ina kuka ɗauko Khadija?”

Kowa sai ya nuna Baba Audu yana faɗin shi ne san abunda ya faru, tun da yace musu a
gaban idonsa akayi. Tun kamin Abbah ya tambaye shi ya shiga yi masa bayani.

“Na fito ne gidan ƙanena can baya, sai na hango wata ƙatuwar mota mai kamar ta ƴan
makaranta ta tsaya, a gefen gurin sai aka jefo wannan yarinyar , sai kuma suka fito
su huɗu suna ƙoƙarin cire mata tufafi, shine fa sai na fara musu ihu suka gudu suka
shige motar, bayan sun wuce ne, na ƙarasa inda take ina neman taimakon jama'ah
ganin halin da take ciki, da jama'ah suka fito sai suka ce sun santa a nan gidan
take, dan ni ba ɗan unguwar nan ba ne ban san ta ba Wallahi”

Wani irin abu ne ya taso ma Abbah, tun daga kan ɗan yatsan ƙafarsa zuwa ƙasan
zuciyarsa, a take kalar idanunsa suka canja, wata jijiyar ɓacin rai ta taso masa,
ta ratsa gefen wuyansa zuwa kansa, a hankaɗe ya kalli Anty Amarya.

“Yaushe ta fita?”

“Wallahi... Ban ...san ...ta fita ..ba ...”

Anty Amarya ta amsa murya na rawa. Abbah ya katsa mata tsawa

“Baki san ta fita ba kamar ya? Taya zata fita ba tare da kin sani ba?”

Kamin Anty Amarya ta ƙara bashi amsa, sai mama Zainab ta yi ɓaranɓarama, a ƙoƙarin
kare Anty Amarya.

“Wallahi duk muna falo ta fita, babu wanda ya san da ita, ta hanyar kitchen ta bi,
wai zata yi sallama da saurayinta”

Anty Amarya jin tayi kamar ta matse bakin Mama Zainab amman ba dama.

“Junaidu!”

Hajiya Barau ta ƙwalawa mai gadin kira. Da sauri ya amsa dan yana kusa da ita,
yana kallon Namra dake kwance cike da mamaki.

“Ya aka yi Namra ta fita? Ba dokar gidan nan bace idan anyi magariba ba wanda ze
fita?”

Jikinsa ya hau ɓari, yana ƙoƙarin ƙare kansa.

“Wallahi sai da na yi mata magana, sai tace wai saƙo zata karɓo nan kusa, ni sam na
manta ma da bata dawo ba sai yanzu”

Abbah ya kalli Baba Audu

“Kasan mutanen ne? Zaka iya gane su?”

Baba Audu ya yi shiru kamar mai nazari.

“Gaskiya ba zan iya gane su ba, amman dai na ji suna faɗin Aasimu ko Ƙasimu, suna
ce masa ya yi sauri su tafi”

“Asim..!”

Abbah ya amsa da ƙarfi. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya, ya kalli mutanen.

“Na gode sosai, Allah ya saka ma kowa da alheri”

Sai da suka masa Allah ya kyauta, sannan suka fita kowa bakinsa ƙunce da magana,
wasu kuma mamakin fitar da ta yi suke, ga kuma ɓarin zancen da Mama Zainab ta yi.

Maryam ta nufe ta tana faɗin

“Abbah akai ta asibiti, duba fa bata motsi”

Juyawa Abbah ya yi ya nufi part ɗinsa rai a ɓace. Hajiya Barau ta ce

“Daga ta zan ɗauko mota akai ta, ai kisan halin Abban ku sai dai ta mutu a nan”

Hajiya Barau ce taja mota, da taimakon Hindatu da Mama Zainab suka sa Namra a mota,
suka nufi asibitin dake kusa da su.
Suka bar Anty Amarya da Maryam suna aikin kuka, Hajiya Raliya na bata haƙuri, sai
kawai Aisha ta yanke jiki ta faɗa iskokanta suka taso.

*** *** ***

Suna shiga Uduth, aka wuce da ita emergency, da sauri Nurses suka karɓe ta, aka
ɗorata akan gado, suka shiga da ita wani ɗaki, taimakon gaggawa suka shiga bata
kamin Likitoci su iso.

Ba a fi minti biyar ba, Doctor Hilal ya shigo cikin manyan kaya, hannayensa zube a
aljihu, tare da wani likita, hankalin kwance ya ƙarasa inda take kamar ba marar
lafiya ze duba ba.
Duk natsuwa Nurses ɗin suka yi suka ja da baya suka bashi guri. Hannu ya kai ya
taɓa gefen wuyanta, yana kallon agogonsa hannunsa, sannan ya kalli drip ɗin da aka
ɗora mata.

“Ku cire mata drip ɗin nan sai numfashinta ya dawo, ku kira Doctor Adamu ko wani
likitan, da wannan ba aikin Likita ɗaya ba ne”

Yana kaiwa nan ya juya, sai Likitan da suka shigo tare ya yi saurin cewa.

“I'm sorry Doctor, Doctor Adamu is not around, that's why i call you”

Juyowa ya yi ya kallesa

“Wannan ba aiki na ba ne, and you know it, tiyata kawai na zo yi garin nan, ba kuma
zan ɓata lokaci na akan abunda ba aiki na ba, jirgi zan bi na koma kaduna a can ma
ina da aiki”

Yana kai wa nan ya fice. Da sauri wasu Nurses suka fita dan kiran wani likitan, shi
kuma wannan likitan ya shiga bata taimako.

KALSOOM POV.

Tana tashi daga aiki, ta wuce gidan ƙawarta Salam dan labarta mata halin da take
ciki.
Bayan Salma ta kawo mata abinci ta ci tayi sallah, sai take bata labarin abunda ya
faru.
A maimakon ta ga ɓacin rai a fuskar Salma na taya ta baƙinciki irin
mijin da zata aura, sai ta ga Salma na murmushi da yima Allah godiya

“Alhamdullah Allah mun gode maka, haba Kalsoom ko dan daɗewar nan da kika yi ba
aure, be isa yasa kiyi haƙuri ki auri wannan ɗan'uwan naki a haka ba? Kina ji fa na
faɗin da babbar budurwa ƙara ƙaramar bazawara, ƙannenki biyu a ɗaki ke kina nan,
haba Kalsoom ki yi tunani mana”

“Ba auren ne bana so ba Salma, halin Sadiq ɗin ne na ke tsoro, ina gudun abunda ze
je ya dawo, tun kamin tafi ake shawara ba sai an dawo ba, Wallahi na tsani mutum ne
neman mata”

“Dan Allah ki daina faɗar wannan maganar, kar wani ya jiki ya san sirrinki, nema
mata yanzu ya zamo ruwan dare, da wahala ki samu namiji me aure ko marar aure da
baya neman mata, ko wace mace da kika gani a gidan mijinta tana da nata matsalar,
no married friend of yours will ever tell you her marital problems,no woman will
tell you her husband's fault amma karya take tace he is perfect,because no one is,
dan Allah kiyi auren ki Kalsoom ke kaɗai ce a cikin kawayen mu kika rage baki yi
aure ba”

Wani kallo Kalsoom ta yi mata, tana mamakin yadda ta kasa fahimtar ta.

“I have never blame myself for being single, i know I'm pretty, i'm well behaved,
i'm Godly,and yet still single. Salma thats just how nature works, that is how
Allah has designed it.
Idan duk a cikin ƙawaye na ni kaɗaice ban yi aure ba so what? Ni nayi kai na? Allah
who created me differently and created them differently, surely made you destinies
different. Komai lokaci ne Salma i don't want to rush into marriage with just any
guy just because i want to be married, babu mai son ya je ya yi aure ya fito”

Salma ta dafa ta

“Haba Kalsoom zaki yi auren ne da niyar ki fito? Your idea is inside you Kalsoom,
kiyi tunani me kyau, amman aure nan shi ya fi, kawai ki bawa Allah zaɓi”

Hawayen da suka zubo mata ta share ta ɗauki jakarta ta rataya.

“Na gode Salma zan yi tunani akai”

Har bakin gate Salma ta rakota, suka yi sallama sannan ta koma. Tafiya Kalsoom take
tana tunani, sai taji ana mata horn, juyowar da zata yi sai taga wata hadaɗɗiyar
mota mai kyau, tana binta a baya. sayawa tayi sai mai motar ya zo dai-dai ita ya
tsaya, yana sauke gilashin motar.
Dattijo ne mai yalwatacciyar fuska da cikar kamala ta mai kuɗi.

“Shigo mana”

Ya faɗa yana buɗe mata front seat. Bata kawo komai a ranta ba, sai kawai ta buɗe
motar ta shiga. Driving yake kaɗan-kaɗan yana gaisawa da ita.

“Ya kike ya gida?”

“Lafiya ƙalau”

“Ina zaki je ne haka?”

“Gida”

“Kuma kike tafiya a rana haka, kar fa rana ta taɓa min ke”

Ɗan murmushi tayi ta gyara yafin gyalenta.


Ba ko kunya ya kai hannu ya yaye mata gyalen

“Haba ke kuwa ya kiƙe ƙoƙarin rufe min kyau nan naki...”

Be karasa ba ta buge masa hannu tana masa wani kallo

“Sauke ni Malam, ni ba irin waɗannan matan bane”

“Haba kyakkawa daga magan...”

“Ka sauke ni nace!”

Ta faɗa a tsawace. Ba shiri ya ya faka motar ta buɗe ta fita tana tsaki.

“Ku ba za ku ce kuna son mace da aure ba sai lalata, duk Namijin da ka haɗu da shi
abunda kawai yake ƙoƙari ya kai ga jikinka, ƴan iska kawai marar mutunci”

Haka tayi ta zaginsa, shi dai be bi ta kanta ba ya ƙaɗa motarsa yayi gaba.

_______________________________

Share it please, and drop your opinion. 🙌

Best regards 💖
Khadeeja Candy 🌺
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa10.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺


_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 10*

UZAIR POV.

A guesthouse ɗin suka koma. Bayan Najeeb ya fito motarsa sai Uzair ya fito, suka
nufi bayan motacin da suke gurin.
Ta inda suka san ba za'a gansu ba suka tsaya. Sai Najeeb ya kalle Uzair ya ce

“Uzair zaka janye maganar auren nan gobe gobe ba sai jibi ba, ka ce ka fahimcin
tana da wanda take so, dan haka kai ka haƙura.
Sai idan ka yanje maganar ne sannan za mu je da kai gurin Malam gobe da nisa, dan
ba za a yi mata magani kana auren ta ba”

“Amman idan mahaifinta yaƙi yarda fa?”

Najeeb ya yi masa wani kallo

“Ta ya zai ƙi yarda ? Shi ze aure ta ne? Ya kake abu Uzair kamar ba ɗan duniya ba?
Sai wani ɓoye-ɓoye kake ai gashi nan ka jawa kan ka”

“Babu babbar matsala kamar ganin da tayi min, yanzu idan ta faɗa dame zan kare
kaina”

“Sai kace ai ta saba maka ƙazafi, kai ma ai kasan kayi kuskure na bari ta ganka,
kamata ya yi kasa a ɗauko maka ita”

Uzair ya yi shiru yana nazari, tashin hankali bayyane a fuskarsa. Kiran Amira tana
ta shigo masa a waya amman yaƙi ɗagawa.
Ƙarfe ɗaya da rabi na dare kiran Baba Audu ya shigo wayar Najeeb. Cikin sauri ya
ɗauka yasa hands-free.

“Hello Baba Audu ya ake ciki?”

Daga ɗayan ɓangaren Baba Audu ya amsa

“Na gama komai, na fito ina babban ti-ti, dai-dai inda kace na tsaya”

“Ina fatar anyi nasara?”

“Komai ya tafi yadda kake so”

“Toh ka jira ni, zan zo nan gurin na ɗauke ka”

Daga haka ya kashe wayar, ya kalli Uzair.

“Yanzu ka wuce gida kawai, ni zanje na ɗauko shi, idan ka taso aiki gobe mu haɗu a
guesthouse ɗin Jafar, kuma ka tabbatar da ka sallami waɗannan mutane da suka ɗauko
ta in case of”

Be jira abunda Uzair zai ce ba, ya nufi motarsa. Sai bayan ya fice sannan Uzair ya
nufi cikin guesthouse. Be daɗe ba ya fito ya buɗe motarsa ya shiga, ya ɗauki hanyar
da zata kai shi gidansa.
Tun kamin yana yin parking ya kashe wayarsa, sannan ya fito ya nufi hanyar falon.
Yasmin na zaune falo tana duba wasu takardu da system Uzair ya shigo da sallama.
Sai dai bata amsa masa sallamarba ma balle har ta ɗaga kai ta kalle. Kamar hakan be
dame shi ba, sai kawai yazo ya zauna kusa da ita ya rufe system ɗin dake gabanta.
Yana ganin ta unƙurin zata tashi, sai yayi saurin riƙe ta ya zaunar, ya danneta da
dukan ƙirjinsa ya ɗora mata nauyinsa, yana ƙoƙarin saka mata hannu ciki riga.

“Haba Bloody miyasa kike min haka ne? Dan kawai zan ƙara aure sai na zama
maƙiyinki? Ai badan bana son ki zan ƙaro wata ba, sai dan rufin asirin mu”

A kaɗan-ƙaɗan ya raɗa mata haka, cikin wani irin siga na son tada mata hankali, sai
numfashi yake sakar mata a kunne.
Ƙoƙarin ƙwatar kanta take amman ta kasa, ta ƙara haɗe rai sosai.

“Sake ni mana, Uzair bana son haka”

“Zan sake ki, amman sai kin faɗa min idan kin daina fushi da ni, idan kuma baki
daina ba toh zan janye maganar auren”

“Maganar auren ka be dame ni ba, babu ruwana da lamarin auren ku, dan haka ka daina
saka ni a ciki”

“Babu ruwanki da lamarin aure na kuma kike fushi da ni?”

“Amman dan zaka yi aure sai ka rasa wadda zaka aura sai Aminiyata, kuma ƴar'uwa
ta”

“Nima ai ƴar'uwata ce, kuma naga kamar zaku fi zaman lafiya”

Wani dogon tsaki taja, tasa guiwar hannunta ta buge masa ciki. Ba shiri ya sake ta
ya dafe cikin.

“Yasmin kashe ni zaki yi?”

Tsaki ta sake masa ta wuce ɗakinta, tana cika da batsewa. Da kallo Uzair ya bita
yana murmushi, sai da ta shige ɗakinta sannan ya tashi ya nufi ɗakinsa.

Tun da asubar fari Hajiya Barau ta bugo masa waya ta faɗa masa abunda ya faru. Yi
yayi kamar be sam komai ba, duk ya firgice yana nuna damuwa, sai tambayoyi yake
zubo mata, yana nuna mata tashin hankalinsa kamar ance masa gata nan gabansa.

“Ban san miyasa Namra ta tsane ni har haka ba, ban san abunda na tsare mata ba, na
rasa gane kanta”

“Uzair, inda har ba Allah yayi auren nan naku ba, bana jin zata zauna gidanka ko da
ka aureta, kuma Wallahi a yadda zuciyar Namra take ko kashe ka zata iya yi ko kuma
tayi maka wata illar, tun da bata son ka”

“Daman abunda Hajiyata take ta faɗa kenan, ni ina ganin gaskiya haƙura zan yi, ƙara
taje ta auri wanda take so kawai”

“Da kam yafi maka, dan wannan auren ba zai yi ƙarƙo ba, sannan bana jin wannan
yaron daya ɗauke ta ze barta haka nan, kar ayi maka kwashe-kashe”

“Barin ze fi tun da har zuciyarta wani take so, kuma duk macen da zata iya bin
saurayinta kinsan ta girma”

“Ashe kai ma kana da tunani, fasa auren akam zai fiye maka”
Daga haka suka yi sallama. shi kuma ya sauka saman gadon ya nufi bathroom.
Sai tara da ƴan mintuna ya shirya, be damu da breakfast ya fito ya nufi parking
space. Lokacin Yasmin har ta daɗe da barin gidan. Direct gidan Mahaifiyarsa ya nufa
Hajiya Binta. A can ya yi breakfast yana labarta mata abunda ya faru, sai tace masa
ai Hajiya Barau ta kira ta ta faɗa mata komai. Ta ji daɗin maganar da yayi ta basa
auren Namra, ita daman zuciyarta bata natsu da aurensa da Namra ba, tun lokacin da
tayi masa ƙazafi.

NAMRA POV.

Cikin ikon Allah numfashinta ya dawo, sai aka ɗaura mata drip,
Sai dai bata farka ba sai kusan Asuba, a lokacin Mama Zainab ce kawai a ɗakin, dan
Hajiya da Hindatu tun cikin dare suka koma gida.
Kuma har garin Allah ya waye babu wanda ya leƙosu sai Amira, ita ma sai goma har da
rabi sannan ta iso.

Namra na zaune jugummm tana tunani hawaye na bin fuskarta. Amira na shiga ta je da
gudu ta rumgume Namra tana kuka.

“Wallahi da ba'a ganki ba Namra, da kashe kai na zan yi”

Namra ta share hawayenta, ta kalli Amira.

“Amira ina Asim yake?”

Gabanta ya faɗi, har sai da ta haɗiye yawun bakinta ta.

“Ina Asim yake Amira? Taya Asim ya zo gidan ku har ya baki wannan number?”

Nan ma kasa amsawa ta yi sai kukan munafurci take, zuciyarta na tsara mata irin
ƙaryar da zata yi Namra dan kare kanta. kamin ta amkaro har Namra ta ƙara mata wata
tambayar.

“Amira ki amsa min mana, ina Asim? Amira number da kika ba ni bata Asim ba ce,
lokacin dana je ba Asim na gani ba Uzair na gani, faɗa min ta ya haka ya faru?”

Har lokacin Amira shiru take, bakinta sai rawa yake ta kasa magana. Hakan ya
tabbatar ma Namra abunda take zargi.

“Uzair ya haɗa kai da ke an cuce ni”

Dam! Dam!! Dam!!! Zuciyar Amira take bugawa har cikin ƙwaƙwalwarta, ja ta yi da
baya tana girgiza ma Namra kai hawaye na fita a idonta.

“Ki zargi kowa da cin amanarki, amman ban da ni, har a bada Amira ba zata taɓa cin
amanar Namra ba”

Namra ta ɗaga mata kai tana hawaye.

“Asim ma ba zai iya cin amana ta ba, karki yaudari kanki wajen nuna min Asim yana
so ya cuce ni. Amman ke Uzair zai iya siyen ki ya biya ki dan ya cimma burinshi,
babu wanda ze fahimci ni, na ɓata ran kowa, ban san hali da Mahaifana suke ciki ba,
sanadin ke da Uzair”

“Namra karki yanke hukuncin abunda baki sani ba, zan iya dafa miki qur'ane Namra,
ban haɗa kai da Uzair ba dan na cuce ki.
Namra ta ya zan haɗa kai da wani ya wulaƙanta ki a titi? Har sai jama'ar unguwarku
sun ɗaiko ki su kawo gidanku, Kuma su bada shaidar sun ji muryar Asim kuma sun ji
an kira sunansa.

Namra tun da na bar gidan ku, ban rumtsa ba saboda tunanin da kukan rashin sanin
halin da kike ciki, kina fita Maryam ta shigo ni ta ɗaurawa laifi tace ni ce silar
komai, na yi tunani ke zaki bada shaida akaina ashe na yi kuskure.

Namra ki faɗa min dalili ɗaya, da zai sa na cuce ki, faɗa min Namra? Kinsan a iya
zamantakewar mu da ke duk wanda ya ci amanar wani Allah sai ya fitar masa da
haƙƙinsa”

Da wani irin kuka ta ƙarasa maganar kamar ta sheɗe. Kalamata sun sa jikin Namra
sanyi, sai zargin da take mata ya soma raguwa, sai dai har yanzu bata ji zuciyarta
ta natsu da Amira ba.
Kan ta ya kulle, ita dai tasan ba mafarki tayi ba, tabbas ta yi ido huɗu da Uzair
kuma ya riƙa ta, sai dai bayan nan bata san wani abunda ya faru ba.

‘Taya Uzair yazo gurin? Miye dalilin da zai sa Uzair ya yi min haka? Taya Amira
zata cu ni ta’

Sune tambayoyin da suka tsaya mata a rai, kuma suke ƙoƙari riƙita mata ƙwaƙwalwa.
Jin Amira ta dafa ta ya dawo da ita daga dogon tunanin da take.

“Namra kin fi kowa sanin ni wace ce...”

Bata ƙarasa Namra ta kai hannu ta riƙa hannunta.

“Ki yi haƙuri, kaina a kulle yake, a yanzu bana iya banbance gaskiya da ƙarya, bana
iya tantance komai na rasa gane abunda yake faruwa da ni...”

Da kuka ta ƙarasa maganar, sai Amira ta rumgume ta suna kukan tare.


Shigowar Mama Zainab ne yasa suka tsagaita kukan, suka share hawayensu.

“Kuka fa ba zai muku ba, abunda ya faru ya riga ya faru sai dai a tari gaba.
Likitan ya rubuta miki wani magani?”

Ta tambaya dan ɗazu Likitan daya shigo ne yasa ta fita, ta basu guri. Namra ta
ɗauki takardar dake gefenta ta miƙa mata.

“Bai rubuta min komai ba, ya dai bani takardar sallama, yace bayan sati biyu na
dawo”

Mama Zainab ta karɓa tana faɗin

“Masha Allah, sai ki tashi muyi harama, dan yanzu Hajiya Raliya ta kira ni wai tana
son ta zo Mamanki ta hanata, kuma ƙara mu koma gida kar a fara mana taro, tun da
babu wanda yaji abunda ya faru sai ƴan gida”

Namra ta lumshe ido ta jin wani abu daya tsaya mata a zuciya.
Amira ce taje ta biya komai da komai sannan ta zo ta riƙa Namra suka fita tare.

HILAL POV.

A gajiye ya fito asibitin, daker yake driving saboda gajiya, dan wuni yayi yana
aiki, har jin yake kamar fever na son rufe shi.
Yau kan baya iya bin gosulon nan na government house, saboda taron da ake.
Sai kawai ya hanka ta cikin estate dan samawa kansa sauƙi sai dai tafiyar zata masa
nisa sosai tun da ya biyo doguwar hanya.
“Subhanallah”

Ya faɗa lokacin da idanuwansa sukayi arba da wata kyakkyawar fuska, dake takowa
izuwa hanyar daya fito. Sai ya rage gudun da yake, ya mai cigaba da kallonta.
Tana da kyau sosai mai jan hakali da saka natsuwar zuci, sai dai fuskarta kawai
yake iya gani, domin jikinta rufe yake da ƙaton hijabi. Hakan kuma ba ƙaramin
burgeshi yayi ba, ganinta cikin kamala ga tafiyarta a natse.
Kamin ta ƙaraso kusa da shi ya faka gefen ti-ti yana ƙare mata kallo.
Tana da tsayi da dogon hanci ga idonta dara-dara, farin fuskarta fes, sai dai a iya
yadda ya fahimta kamar bata da jiki sosai.
Dai-dai lokacin data kawo kusa da shi sai ya sauke gilashin motarsa yana miƙa mata
sallama.

“Assalamu alaikum Malama”

“Wa'alaikassalam”

Ta amsa mishi da zazzaƙar muryarta sai dai hakan be sa ta tsaya ba, sai ta cigaba
da tafiyarta kamar ba ita ta amsa masa sallamar ba.
Da sauri Doctor Hilal ya buɗe motar ya fito ya biyo ta da ƙafa.

“Dan Allah ɗan tsaya na tambaye ki wani abu”

Allah daya haɗa ta dashi yasa ta tsaya, da badan haka ba babu abunda ze sa ta tsaya
dan iya yanzu ta sallama a lamarin maza.

“Dan Allah ke matar aure ce?”

“A'a”

“Dan Allah ya sunan ki, kuma ina ne gidan ku?”

Sai a lokacin ta kalleshi, wani faɗuwa gabanta yayi lokacin da idonta suka sauka
cikin nasa, kyausa yayi mata kwargiji, wanda yasa tayi saurin sauke idonta ƙasa,
tana sauraren bugun zuciyarta.

“Miyasa ka tambaya?”

“I ask you first”

Ba amfanin yin ƙarya, dole ta faɗa masa gaskiya.

“Sunana Ummul-Kalsoom amman ana kira da Kalsoom, gidan mu yana ta nan gaba number 5
gidan Alhaji Faruk Kafinta”

“Toh na gode”

Bata sake ce masa komai ba, ta cigaba da tafiyarta. Shi kuma ya bita da kallo har
sai da yaga inda ta shiga, sannan ya shiga motar yana murmushi, a take ya ji duk
gajiyar da take tare dashi ta wartsake, cikin farinciki da annashuwa ya kunna motar
ya hau ti-ti.

__________________________

What do you expect next?


http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa11.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺


_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 11*

NAMRA POV.

Keke Napep Amira ta tare musu ta faɗa masa inda ze kai su, sannan suka shiga.
Be sauke su ko'ina ba sai Ƙofar gidan, Amira ta biya shi sannan ta riƙa hannu Namra
suka shiga cikin gidan.
Kamar mai nauyin ƙafa haka Namra take tafiya tana hawaye, gaban na bugawa da ƙarfi.
Da wane ido zata kalli Anty Amarya? Idan Abbah ya kalleta me zata ce masa.
Mama Zainab ce gaba da sallama sannan Namra, sai Amira ta biyo baya. Hajiya Raliya
ta amsa musu sallamar, Anty Amarya kam yi tayi kamar ma bata gansu ba, ta tashi
tayi ta nufi kitchin.
Saman Kujera Amira ta zaunar da Namra, sai ta zauna kusa da ita tana amsa ya jikin
da Hajiya Raliya take mata.

“Da sauki har an sallamota”

“Wallahi babu yadda ba mu yi ba ni da Aisha da Hindu muje ganin ki amman Larai ta


hana, sai gashi Abbanki ya zo shi yace kar wanda ya fita da sunan ganin ki a gidan
nan, toh kar ma ya kuskura ya dawo”

Fashewa ta yi da kuka, ta kwantar da kanta jikin Amira dake hawaye.


Shigowar Hajiya Barau ne yasa ta noke kanta, Amira da Mama Zainab suka amsa mata.
Idonta kar kan Namra sai kallon jikinta take.

“Namra kin dawo? Wallahi Alhaji ne ya hana mu zuwa ganin ki, ya jikin?”

“Alhamdulillahi”

Mama Zainab ta amsa. Zaunawa tayi kusa da Amira.

“Ince dai babu abunda ya same ki ko?”

“A'a ba komai likita ya bincika yace babu abunda yake damunta”

Cewar Amira

“To Alhamdulillahi, Allah ya tsare gaba”

Sai ta tashi sun-sun-sun ta fice. Hajiya Raliya ta kalli Namra cikin damuwa ta ce

“Haba Namra haka kike so maƙiya su yi ta miki dariya? Ansa ranar aurenki kije ki
gana da wani? Haka aka kawo mana ke shame-shame mazan unguwar nan zagaye da ke, shi
haka shine daɗi?”

Amira ya share hawayenta

“Dan Allah ku daina wannan maganar, zaku ɗaga mata hankali ne kawai, ita kan ta
ba'a son ran ta hakan ya faru ba, kusan babu yadda Namra zata kai kanta ga halaka
ko kuma inda ta san mutuncin ta ze zube”
Namra kan kuka kawai take, tana jin wani irin ƙololon baƙin ciki ya riƙe mata
zuciya. Kamar daga sama sai ga Abbah ya shigo falon fuska babu annuri.

A take cikin Namra ya ɗauki ƙugi, ko Amira sai da ta razana da yanayinsa, yana
katsawa Namra tsawa jikinta ya hau rawa.

“Khadija ki tashi ki koma can gurin saurayin na ki bana son ganin ki a cikin gidan
nan!”

Cikin baƙar zuciya Anty Amarya ta fito daga kitchen ta nufo inda Abbah yake tsaye
tana faɗin

“Babu inda Namra zata je, ko kisan kai ta aikata idan ta shigo nan gidan ta samu
mafaka, dan gidan ubanta ne ciki da waje, komai Namra ta aikata sai ance ƴar Alhaji
Usaman ce ko da bata duniya, duk inda aka ga sunan Namra sai anga naka kuma dole
ace ƴar ka ce”

Abbah ya nuna Anty Amarya

“Ai daman ke kike goya mata baya take duk abunda take”

Anty Amarya ta nuna kanta tana hawaye.

“Ƙwarai, nina goya mata baya nace ta fita cikin dare taje taga Asim, kuma idan taje
ta faɗi ta suma jama'a su ɗauko ta su kawo maka cikin gida ni nace....”

Mama Zainab ta rufe mata baki, tana ba Abbah haƙuri. Da ƙarfi Anty Amarya ta buge
mata hannu ta matsa tana faɗin

“Ki ban ni ina faɗi ciwon bakin na, wannan ƙurjin ya daɗe yana min ƙaiƙayi a cikin
rai, duk abunda Namra ta aikata gare ni yake dawowa, ni nake tura ta, faɗa min wace
uwa ce zata so abunda ya faru da Namra ya faru da ƴarta, amman ni yake ɗorawa
laifi”

Shiru Abbah yayi yana kallon Anty Amarya data cika falon da ruwan bala'i tana
zazzaga masa rashin mutuncin har yata gama be sake cewa uffan ba.
Hajiya Raliya ce keta bashi haƙuri tana cewa kar ya tanka mata, shi ma daman be
da niyar sake ce mata komai, dan yasan Anty Amarya bata iya faɗa ba, idan ta
birkice masa babu mai iya tare ta sai Allah, haka take wani lokacin kamar mai
aljannu, shiyasa Hajiya Barau ta sallama ma lamarinta.

Tsaye Anty Amarya ta yi masa ƙyam, tana jira ya ce mata kulle ta ce masa chas, dan
idonta yanzu a murje yake, zuciyarta kuma ta kawo. Abbah be yarda ya sake ce mata
ƙomai ba, ya juya ya fice.
Sannan Anty Amarya ta kalli Amira a tsawace tace

»“Ke Amira tashi ki je gida”

Da sauri Amira ta ɗauki jakarta ta rayata, ko sai ajima bata ce ba, ta fice jikinta
na rawa.
Tasss! Tasss!! Tasss!!! Anty Amarya ta sauke ma Namra mari har sau uku, sannan ta
nuna mata ƙofar ɗakinta

“Tashi ki wuce ɗakin ki, kin samu farinciki kin jidaɗi”

Zubewa Namra ta yi ƙasa daga kan kujera tana kuka, ta riƙe ƙafafun Anty Amarya.
Riƙo fuskar Namra Anty Amarya ta yi ta sake sakar mata wani marin sannan ta tureta
ta fisge ƙafarta, ta wuce ɗakinta cike da ɓacin rai.
Daga Hajiya Raliya har Mama Zainab tsaye suka yi basu yi unƙurin yin wani abu ba,
dan sunsan halin ƴar'uwarsu kan akwai haƙuri amman idan ta hasala bata da daɗi.

Sai daNamra tayi kukanta mai isarta sannan ta tashi ta nufi ɗakinta. Saman gadonta
ta faɗa ta sake fashewa da sabon kuka.
Har La'asar bata fito daga ɗakin ba, kuma babu wanda ya shiga inda take inba Aisha
ba, itama tun da ta fita tayi shirin islamiya babu wanda ya leƙo ɗakin.
Tasan dole ne Maryam tayi fushi da ita, dan Maryam tafi kowa ɗaukar zafi idan wani
abu ya faru. Sai da dare Aisha ta shigo ta aje mata abinci ta fita.

UZAIR POV.

Yana tasowa daga gurin aiki kai tsaye ya wuce guesthouse ɗin Jafar, daman tun yana
gurin aikin suka sha masa kai da kira, wai duk sun hallara shi kawai suke jira.
Yana shiga ruwa kawai ya sha Najeeb ya tambaye shi.

“Ya Labarin yarinyar?”

“Wai asibiti ta kwana, Kishiyar mamarta take faɗa min ɗazu da safe, sai na nuna
mata kamar ban ji ba”

“Amman kaje ka ganta?”

Jafar ya tambaya. Sai ya girgiza masa kai

“A'a na dai je gurin Hajiyata na faɗa mata maganar janye auren tace zata je ta
faɗawa Abbah”

Najeeb yace

“Amman ai da kaje ka ganta Uzair sai ka nuna kasan abunda ya faru, anyway muje ciki
malamin yana ciki tun ɗazu ya iso”

Uzair yayi sauri haɗiye ruwan bakinsa.

“What? Na ɗauka zuwa zamu yi gurin shi”

“No Ba zamu iya shiga dajin nan ba, sai na aika direba ya ɗauko shi, kasan su kuɗi
kawai suke so da sun ga ƙuɗi komai zasu iya”

Cewar Najeeb. Tahir ya aje wayar dake hannunsa saman tebur ya miƙe tsaye.

“Muje ayi abunda za'ayi akwai inda nake son naje”

Sai duk suka ɗugunzuma suka nufi wani ƙaramin falo, da ba kasafai suke zama cikin
shi ba.
Dattijo ne sanye da babbar rigarsa, kansa ya sha uban rawani, haƙorasan duk goro,
ga wani ƙaton faifai dake gabansa, mai cike da jar ƙasa. Idan ka kalleshi sai kayi
masa ɗaukar mutumin kirki, a fuskarsa ba zakayi zaton zai iya aikata wani mugun abu
ba.

Duk guri suka samu suka zauna, bayan sun gaisa, Jafar ya kora masa da bayani

“Am daman na faɗa maka tun ɗazu, abokin mu ne yake ciki wata ƴar matsala, wata
ƴar'uwarsa ce take ƙoƙarin masa zagon ƙasa, saboda ta kamashi yana aikata luwaɗi,
shine take son tona masa asiri, babu yadda be lallaɓata ba amman ta ƙi yanzu haka
so take ta rabashi da matarsa, da kowa nasa”
Lokacin da Jafar ya kai aya sai ya zumguri kafaɗar Uzair alamar yayi magana, sai
shi kuma ya ɗora.

“Yanzu haka ta ɓata min suna a cikin familyn mu kuma yanzu haka tana nan akan
bakanta na cewar ta faɗawa duniya da ƙwaƙwarar hujjah”

Malamin yayi murmushi yana gyara zamansa.

“Yanzu me kake son ayi mana, shin kana son a kulle mata baki ne ko kuma ayi mata
kurciya ta bar garin gaba ɗaya?”

Kallo-kallo suka riƙayi, kowa na tunanin abun cewa, can sai Najeeb yace

“A ɗaure mata bakin kawai ta yadda komai ta gani ba zata iya faɗa ba”

“Ko kuma ayi mata kuciya ta bar garin gaba ɗaya”

Cewar Jafar. Uzair ya girgiza kai

“Idan muka mata haka ba muyi mata adalci ba, why not dai ayi mata na rufar bakin”

Najeeb yaja tsaki

“Ita ba naka sunan ta ɓata ba? Idan aka mata kuciyar ta bar gari kana tunanin wani
zai zargeka ne? Sai dai ace ai halinta ne, kuma wannan shine kawai mafita”

Uzair yayi shiru yana nazari. Sai Malamin yace

“Minene sunan ta? Sai mu duba muga irin aiki daya dace ayi mata, dan aikin da ke
yima wani bashi ke ma wani ba”

“Sunanta Khadija, amman Namra ake kiranta”

A take Malamin ya gyara ƙasar ya shiga bincike, yana wasu tsiface-tsiface.


Ya ɗauki tsawon lokaci yana bincike amman be gano komai ba, can ya ɗago kai ya
kallesu yana jinjina kai yace

“Lallai wannan aikin ze ci ƙuɗi da yawa, kuma magana ta gaskiya wannan yarinya
akwai tsari tare da ita na musamman, ba lallai bane ko wane irin aiki ya kamata sai
dace”

Duk sun cika da mamaki, bama kamar Tahir daya kasa haƙura har sai da ya tambaya

“Saboda me?”

“Ban san dalili ba amman lallai akwai tsari mai ƙarfi a tare da ita, kasan ni bana
aiki da munafurci kuma idan har abu baya yi zan fito fili na faɗa maka gaskiya”

Uzair ya sauke ajiyar zuciya

“Yanzu ba wata mafita kenan?”

Lailaya ƙasar yayi

“Bari mu bincika mu gani”

Sai ya koma bincike yana watsa wani farin miski a jikin ƙasar.
Zuwa can ya ɗago ya kalli Uzair yace
“Ta ƙi bayyana a binciken mu, sai dai an samu mafita, za a iya samun sa'arta ne
kawai da asuba ko kuma lokacin da take haila”

Lokacin asuba lokacin ne mala'ikun da suke tsare bawa idan yayi addu'ar bachi suke
tashi, Idan be yi saurin tashi yayi sallah ba, a lokacin har sheɗan yake samun
sa'arsa ya saka masa kasala, da ƙuiyar yin sallah har sai rana ta fito.
Lokacin Haila kuma lokaci ne da ba ko wace mace ba ce take tsare yin addu'ah a
wannaɓ lokacin ba, saboda ganin tana al'ada, bayan kuma duk kan addu'o'i an yarda
mai haila ta karanta sallah ce kawai aka ɗauke mata, da ɗaukar cikakken ƙur'ane, da
kuma ɗawafi.
Dan haka yan'uwa mu kiyaye addu'ah a wannan lokacin, kuma mu kiyaye Sallah asuba a
cikin lokaci, tana da muhimmanci sosai.

Najeeb yace

“Amman kana ganin idan har anyi aikin zai ci kuwa?”

“Zai ci dan wannan aikin ba za a yi shi ace ba a ga nasara ba, sai dai ya zamo
wanda ake son ya sama ɗin be same shi ba”

“Kamar ya?”

Tahir ya tambaya da sauri.

“Zamu yanka baƙin bunsuru guda biyu, da rago, sai a samo mana tunfafiya da kurciya
da su zamuyi aikin, sai a rubutu wasu abubuwan da jinin bunsurun a watsa a riga ko
zane da zata ɗaura sai a bata ta saka, inda har ba wanda ya bata ɗin nan bane yayi
kuskure toh lallai babu tantama aikin zai kamata, amman fa a lokacin da take Haila
ko kuma kamin sallah asuba”

Jafar ya riƙe baki

“Babbar magana, dole sai ta wannan hanyar kawai?”

“Ba dole sai ita ba, amman ita ce tafi ko wace sauƙi”

Tahir ya kalli Uzair

“Toh kai kana da mak maka wannan aikin ne?”

“Akwai wata ƙawarta ina jin kamar zata iya, amman what if ba ayi nasara ba?”

Tahir ya dafa shi.

“Ka yarda kawai za'ayi nasara, karka sawa kanka wannan”

Kai ya girgiza

“Ni dai ko na haƙura kawai na ƙyaleta”

Ganin yadda Uzair ya tsorata yasa Malamin shiga kwantar masa da hankalin

“Za'ayi nasara, karka damu, ka haɗani da wadda zata kai mata rigar na san yadda zan
tsara mata komai”

Shiru Uzair be ce komai ba, shi dai sai tunani yake. Ganin hakan yasa Najeeb yace
da Malamin
“Shikenan a fara aikin kawai, zan turo maka dubu ɗari a account ina tunanin zasu
isa? Idan ma da wani abu sai ka kira a waya”

“Zasu isa inshallah, amman za a kawo rigar da taɓa sawa, dan da ita zamuyi aiki,
kuma ina son ganin yarinyar”

“Ba matsala zuwa gobe duk yadda muka yi zaka ji ni”

Daga haka suka yi sallama, Najeeb yasa direba ya maida malamin. Sannan suka ya dawo
falo suka shiga tattauna maganar.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa12.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 12*

HILAL POV.

Wanka yayi ya shirya cikin wata gizna, maroon color, sannan ya ɗauki hulla mai kyau
ya saka, ya ɗauki agogon hannu ya saka ya feshe jikinshi da turare, sannan ya buɗe
wardrobe ya ɗauko sababin kuɗi ya saka a aljihu, sannan ya dawo gaban madubi ya
sake kallon kansa, ya tabbatar da kwaliyarsa ta fito, sannan ya ɗauki keys ɗinsa ya
saka baƙaƙen takalmi, ya fice.

Ko da ya fito falo, Rashida na gaban dinning tana shirya musu dinner, su Ulfah
zagayeta suna nuna mata assignment ɗinsu.
Kusa da ita ya ƙarasa yana leƙon abincin da take zubawa.

“Pyar a zubawa yara nasu nawa sai na dawo mu ci”

“Ina zaka je?”

“Ango zamu je rakawa ba zan daɗe ba”

Juyowa tayi ta kalleshi daga sama har ƙasa, yadda kyau nan nasa ya fito ya bata
tsoro. Shi kuma sai yayi kamar be ga kallon da take masa ba sai ya kalli agogon
hannunsa.

“Bari naje kar nayi latti, ni kawai suke jira”

Hannu yasa ya rufe idon Ulfah sannan yayi mata kiss a baki, sannan ya nufi ƙofa sai
ƙanshi turare yake.

“Allah ya tsare min kai ni dai”

Ta faɗa lokacin da zai fice. Murmushi kawai yayi ya saka kai ya fice.
Motarsa ya shiga yayi horn mai gadi ya buɗe masa, ya hau ti-ti zuciyarsa cike da
nishaɗi.
Cikin ƴan mintuna ya isa estate ɗin su Kalsoom. Numbers ɗin gidaje ya riƙa dubawa
har ya kai ga number.
Dai-dai gate ɗin ya tsaya yayi horn yayi mai gadin gidan ya leƙo sannan ya buɗe
masa, sannan ya shiga harabar gidan yayi parking. Sai ya fito ya nufo mai gadi ya
bashi hannu suka gaisa sannan yace

“Dan Allah ko nan ne gidan Alhaji Faruk Kafinta?”

“Eh nan ne”

“Dan Allah mai gidan yana ciki?”

“Eh yana ciki”

“Dan Allah kayi min sallama da shi”

“To wa za'ace masa?”

“Ce masa Doctor Hilal ne”

Da sauri mai gadin ya nufi cikin gidan. Doctor Hilal kuma ya dawo gurin motarsa ya
tsaya yana ƙarema gidan kallo.
Hilal ya kusan minti goma tsaye a gurin sannan Abban Kalsoom ya fito, yana ganin
Doctor Hilal ya washe baki.

“Maraba da bokan turai, yau likita a gidana na”

Da sauri Hilal ya miƙa masa hannu suka gaisa, har da ɗan risina masa yana murmushi.

“Wai daman nan ne gidan ka?”

“Nan ne kasan abu ga talaka”

Ya faɗa yana dariya, yasan Doctor Hilal sosai dan shine likitan da yake dubashi a
duk lokacin daya je asibiti, sai dai Doctor Hilal be waye shi sosai ba, sai yanzu.

“Shigo ciki mana”

A falonsa ya shiga da Hilal ya ɗauko masa lemu da kansa, zai zuba masa Hilal yayi
saurin karɓa ya zuba da kansa.

“Ya fama da jama'ah”

Daddy ya faɗa yayin da ya zauna saman kujera.

“Al-hamdulillah da fatar dai na same ku lafiya”

“Lafiya ƙalau, yau dai sai ga likita gidana, ina ji dai hanya ce ta biyo da kai, ni
dai nasan Likita be san gidan ba”

Doctor yayi dariya.

“Yanzu ma dalili ne ya kawo ni, akwai wacce na gani naga ta shigo nan gidan”

“To, kuma bata faɗa maka sunanta ba? Ta yiyu ma ƴar maƙota ce”

“A dai yadda nake tunani ƴar nan gidan ce, sunan ta Kalsoom wata doguwa haka”

Daddy yayi murmushi.

“Kalsoom ai ƙanwar ka ce Likita”


Hilal yayi ƙasa da kanshi

“Ina fatar ba'ayi mata miji ba?”

“Ba'a mata ba, amman akwai manema”

“Ina fatar shiga cikin su, amman idan kayi min izini, dan ni da gaske nake yi idan
Allah ya yarda”

“Ba ni da matsala Likita, inda har kun dai-dai ta kanku, ni da Kalsoom ai duk
mallakin ka ne, tun da ni Patient ɗin ka ne”

Ƙasa Hilal yayi da kansa cike da jindaɗin maganar Daddy, be ɗago ba har sai da
Daddy ya tashi yana faɗin

“Bari na kira maka ita”

Daddy na ficewa ya miƙe tsaye ya ƙara karkaɗe shaddarsa, sannan ya zauna a natse
yana kallon ƙofa. Sai gata ta fito cikin hijabi tana tafiya a hankali, sallama ta
fara masa sannan ta nemi guri ta zauna, tana gaishe shi.

“Lafiya ƙalau, ina fatar Gimbiyar tana nan lafiya”

“Al-Hamdulillah”

“Mashallah, na zo mun gaisa da Daddy ki sai yace ze kira min ke mu gaisa, ina fatar
ban takura ki ba, kuma in babu matsala zan so ki gabatar min da kan ki”

“Sunana Kalsoom ni budurwace ina aiki a MTN Service, nan ne gidan mu kuma ina
ƙarƙashin kulawar iyaye na ”

Gabansa ya faɗi, jin tana aiki, shi da yake son ƙara aure saboda aikin da matarsa
take sai kuma ya sake karo da wata ma'aikaciyar. Sai dai be nuna mata ba, sai kawai
yayi murmushi yace

“Mashallah, ni kuma sunan Doctor Hilal Abubakar Mai-lafiya, ina aiki a American
Hospital dake nan Kaduna, ina da mata ɗaya da yara uku, ina fatar zan samu karɓuwa,
duk da kasancewar na san muna da yawa”

Murmushi kawai tayi masa, ta shiga murza hannunta.

“Ba zan cikaki da surutu ba, dan na fahimci kamar Gimbiyar tawa bata son yawan
magana, ni kuma gani kamar wazirin aku, zan nemi alfarma ɗaya zuwa biyu”

“Allah yasa zan iya”

Ta faɗa da murmushi.

“Ina farko ina son ki bani damar zuwa muna gaisawa, bace kullum ba gudun kar na
takura miki, amman zan riƙa kwatantawa, sannan ina son ki samin number wayarki”

A take ta karanto masa number, sai da yasa yayi saving sannan ya kalle ta

“Amman fa ni bana son na kira naji User busy, dan ni ina da kishi sosai, ba kamar
sauran samarin ki bane”

Nan ma murmushi tayi, sai ya tashi tsaye yana faɗin


“Bari na zo na tafi, kar Daddy yace zan sace masa ƴa”

Sai a lokacin tace

“Ai Daddy ya san be kawo ɓarawo gidansa ba”

“Kar kiyi saurin yanke hukunci, Wallahi sata na zo nayi masa”

A kaikaice ta kalleshi zuciyarta na raya mata abunda ze fito bakinsa.

“Zuwa nayi na sace zuciyar ƴarsa, daga nan sai na sake sace gangar jikinta, na
kaita gidana na aje”

Fuskarta da murmushi ta lumshe ido yana girgiza kai. Yau kam Allah ya haɗa ta da
Mutum me son raha.

“Ba dan kar na takurawa Sarauniyar ba, dana nemi izinin a rakani ”

Lumshe ido tayi ta buɗe

“Ai duk umarnin da sarki ya bada, da shi baiwa zata yi amfani”

Hannunsa ɗaya yasa aljihu sai ya nuna mata ƙofa da ɗayan.

“Zan so Sarauniya ta wuce gaba, gudun kar bafade yayi mata ba dai-dai ba”

“Amman ai ko a fagen yaƙi, Yarima ne yake sharewa Gimbiya hanya”

Wani irin murmushi Hilal yayi murmushin daya ƙara fito da kyaunsa. Sai kawai ya
shiga gaba ta rufa masa baya.
A tare suka isa gurin motar sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro sabbin kuɗi ya miƙa
mata.

“Nasan wannan ba ze siye kalamai da kuma tsadadden murmushin ki ba, amman zai iya
zama tukuici ga rakiyar da kika min”

Naɗe hannayenta tayi

“Ai wanda ya cika da yaƙi, ya mallake ka duka kai da iyalan ka”

Yasan me take nufi sai kawai yayi murmushi yace

“Zan yi farin ciki idan kika karɓa”

“Ni kuma zan fika farin ciki idan baka cilastani na karɓa ɗin ba, kuma nasan
farincikin na naka ne”

Mayarda kuɗin yayi aljihu.

“Na gode da wannan karramawar Kalsoom, ni zan tafi ki kula min da kanki”

“Ni kuma ka kula min da Anty na da duk yarana, kuma ka miƙa min kyakkyawar gaisuwa
na a gare su”

Ya buɗe baki

“Baki ce min na kula da kai na ba”

Murmushi tayi masa as respond ta juya ta shige cikin falon, tana mai jin sonsa a
zuciyarta.
Shima murmushi yayi ya buɗe motarsa ya shiga.

Ko da ya isa gida, Rashida na zaune falo tana jiransa, duk ta haɗe rai sai kallon
agogo take, jikinta na bata ba gurin kai ango yaje ba, gurin wata yaje.
Yana yin sallama ta amsa masa

“Wa'alaikassalam, amman pyar ba gurin kai Amarya kaje ba ko? Gaskiya wannan fitar
daga gani gurin wata kaje”

Kusa da ita ya zauna yana murmushi.

“Na gode Allah daya sa matana ta iya karantar mijinta har haka, inda zuciyarki ta
raya miki can naje kinsan ba zan iya ɓoye miki ba, ɗa zun ma dan bani da tabbacin
zan karɓu ne shiyasa ban faɗa miki inda zanje ba”

Ta masa wani kallo

“Ka karɓu kenan?”

“Sosai ma har da tukuici”

Nan da nan idonta ya cika da hawaye.

“Doctor wasa dai kake”

“Banker da gaske nake, ba tuni nake miki waƙen zan yi aure ba kika ganin kamar wasa
nake ba”

“Wallahi baka isa ba, ba a gidan nan ba”

“Toh ai sai ki hana idan gidan ki ne, ni dai tashi ki zubo mana abinci yunwa nake
ji”

“Ba zan zubo ba, sai ka koma can kaje ta baka abinci”

“Toh ai ba'a ɗaura mana aure ba, amman dai idan na aure ta zaki ga soyayyah ba ni
ba har ke sai tayi feeding ɗin ki”

“May God forbid ,kuma Allah ya tsine mata albarka”

Ta tashi ta nufi ɗakinta da kuka, shi kuma ya bita da murmushi yana jin son matar
tasa har cikin ranshi.

UZAIR POV.

A mota ɗaya suke zaune shi da Najeeb, suna jiran fitowar Amira.
Sai ta ɓata musu lokaci, sannan ta fito sanye da abaya, tazo tayi musu tsaye
tana hararar Uzair.

“Me ya kawo ka gidan mu?”

“Shiga mota zamu yi magana”

Ba musu ta buɗe motar ta shiga gidan baya ta zauna. Sai da ya gabatar mata da
Najeeb sannan ya faɗa mata abunda ya kawo su.

“Lallai Uzair ban zaci zaka iya zuwa da wata buƙatar a gare ba, kira nawa nayi maka
amman baka ji ba, yanzu ka haɗa ni da ƙawata har ta fara zargina”

Najeeb yayi murmushi mai sauti.

“Wannan ita kaɗaice mafita a gareki a gare mu kuma gaba ɗaya, kin ga idan mun
aikata haka har ke asirinki zai rufu, amman idan asirinki ya tonu zaki fi kowa
shiga cikin matsala”

Shiru tayi tana tunani.

“Amman nawa zaka biya ni?”

Uzair yayi murmushi.

“Zan baki 100k yanzu idan aiki ya yi zan baki 300k har abunda ya yi sama, amman ki
tabbatar ta saka rigar”

“Taya zan iya tabbatar wa tun da ba tsare ta zan yi ba?”

“Ko ya ya zakiyi a kin sani tun da ke mace ce kuma Aminiyarta, idan ta kama sai ki
kwana a gidan, yanzu dai kije ki karɓo mana rigar da dare zamu zo mu karɓa”

Cewar Najeeb.

“Naji amman ni ba zanje gurin wani Malami ba, kuje ku yanke min kai”

Duk dariya sukayi, sai Uzair yace

“Mun ji amman dai ki tabbatar rigar data taɓa sakawa ce, zan miki transfer 100k an
jima”

Uzair be yarda ya faɗa mata abun ze iya dawawa idan be kamata ba, sai kawai ya
ƙaleta har ta buɗe motar tayi ta fita.
Su kuma suka yi kwana suka wuce, daman baki gate suka tsaya basu shiga ciki ba.
Cikin gidan ta koma, a tsakar gida ta samu Ammy da Yayanta a tsaye suna magana, sai
ta wuce ciki ta ɗauko handbag ɗinta sannan ta cewa Ammy zata je ta duba Namra.

“Kice ina gaishe ta dan Allah”

Cewar Ammy, sai ta fice tana faɗin

“Toh zan faɗa mata”

Waje ta fito ta tari mai napep ta shiga. Lokacin data shiga falon Anty Amarya ce
kawai a zaune, su Maryam da Hindatu duk sun tafi makaranta, Mama Zainab kuma tun
jiya da yamma suka kama hanya.
Har ƙasa ta risina ta gaishe da Anty Amarya sannan ta tambayi Namra, Anty Amarya
tace mata tana ɗakinki sai ta tashi sun-sun ta nufi ɗakin.

Namra na kwance saman gadonta tana hawaye.


Kusa da ita ta zauna ta kai hannu ta riƙa hannunta.

“Haba Namra yanzu kina ganin kukan naki maganin ne?”

Tasowa Namra tayi ta rumgume Amira.

“Amira kowa fushi yake da ni, ina jin tsoro Amira”

“Tsoron me?”
“Ina tsoron kar ace sun taɓa min mutunci”

Amira ta fara hawaye.

“Nima ina wannan tunani Namra, kuma idan har haka ta tabbata kika yi ciki kin gama
wulaƙanta a rayuwarki ta duniya”

Ƙara fashewa Namra tayi da kuka.

“Wallahi duk na gano wanda yayi min wannan abu sai na kashe ki, sai na masa
wulakacin mafi ƙasƙanci a duniya”

Gaban Amira ya faɗi, ji take kamar da ita Namra take.

“Mafita ɗaya ce Namra, ki gwada shan magani da haila zata zo miki, kin ga ko da
kina da cikin sai ya zube, tun ba daɗe ba”

Namra ta ɗago ta kalleta

“Amman ba ni da tabbaci”

“Shiyasa nace ki sha ɗin, kin ga idan ma anyi ko ba'ayi ba ke dai kin san babu ciki
a tare da ke”

“Ina zan samu maganin?”

“Zan nemo miki, zan bincika na siyo miki”

“Na gode sosai Amira Allah ya bar zumunci, amman har yanzu baki da labarin Asim”

“Wallahi har yanzu, amman ki kwantar da hankalinki na san zai dawo komai daren
daɗewa”

“Allah yasa”

“Amin, ni bari na tashi na tafi, daman gurin ɗinki zanje sai nace bari na biyo na
duba ki, daga nan na ari rigarki ta atamfa”

“Gashi can je ki duba wanda kike so”

“Na jikin ki zaki ara min, dan bana son ɗinki mai hayaniya”

Ba tare da tunanin komai ba, Namra ta tashi ta cire rigar ta miƙa mata tare da zane
sai ta saka wata gown.

“Ai dama kin bar Zanen tun da ba shida wani style, rigar kawai nake so”

Mayarda zanen Namra tayi ta aje, ta ɗauko mata jaka ta saka rigar, sannan ta tashi
tana faɗin.

“Bari na je kar Ammy ta ga na daɗe tace na gaishe ki”

“Ina amsawa yaushe zako dawo?”

“Da na siyo maganin zan zo na kawo miki, amman ki kwantar da hankalin ki kinji?”

Kai kawai Namra ta ɗaga mata.Sai Amira tayi mata sallama ta fice.
Bayan fitar Amira Anty Amarya ta shigo ɗakin. Ɗaga bakin ƙofa ta tsaya tace

“Uzair ya janye zancen Auren shi dake yace shi ya haƙura, Abbah ki yace shi ba zai
sake miki zaɓi ba ki kawo Asim ɗin zai ɗaura miki aure da shi”

Anty Amarya na kaiwa nan ta juya ta fice. A maimakon ta ji farinciki, sai kawai ta
ji wani kalar abu ya baibaye ta, shi ba farinciki ba kuma ba baƙinciki ba. Sai
kawai ta rushe da kuka.

Amira na fita gidan ta kira Uzair ta faɗa nasa yadda sukayi da Namra, ya jidaɗin
abunda Amira tayi tun da yana ganin ta nan zasu samu mafita. Da dare yazo ya karɓi
rigar, yace mata jibi ze kawo mata tare da maganin.

RASHIDA POV.

Tun da safe tayi shirin office, wace ke fita takwas ko takwas da rabi yau tun shida
ta bar masa gidan, tun jiya da dare kuma ta ƙi sake masa sai fushi take dashi.
Kai tsaye gidan su ta nufa, Mahaifiyarta tayi mamakin ganin ta tun da sanyin
safiya, ga fuska duk hawaye.

“Ke lafiya?”

Sai kawai ta faɗa jikinta tana kuka. Sai duk ta rikita mahaifiyarta a zatonta ma ko
sun yi faɗa da Hilal ne ko kuma wani ne ya mutu. Sai da tayi kukanta mai isarta
sannan ta faɗa mata abunda ya faru.

“Mom wai Hilal aure ze ƙara”

“Amman shine kika zo kika ta da mun hankali na ɗauka ko wani abun ne ma? Toh dan ze
yi aure hana shi zakiyi ko me? Ke kaɗai aka ce masa ya aura?”

“Mom kishiya fa ze min ko baki gane ba”

“Na gane mana, ba'a aure ke aka aureki? Tun yaushe yake miki zancen ƙarin aure?”

“Mom wannan karon da gaske yake”

“Toh idan da gaske yake sai me? Hana shi auren zaki yi? Ke idan mai hankali ce ai
da kanki ma kyace masa yaje yayi aure, duk irin haƙurin da yake da ke, idan ma yayi
auren ai sai ki samu me riƙa miki yaranki”

Ɗaukar gyalenta tayi ta yafa ta ɗauki jakarta

“Ai daman nasan ba zaki goya min baya ba”

“Oh so kike na goya miki baya ki yima mijinki rashin mutunci ko? Shine kika wani
ɗauko gyale kika zo gida ko kunya baki ji, kuma Wallahi bari jiki na faɗa miki kar
ki biye son zuciyarki kije ki kawa kanki, kar naji wata matsala ta shiga tsakanin
ki da mijinki akan auren nan”

Ficewa tayi tana hawaye tana faɗin

“Ba zan sake zuwa gidan nan ba”

Mom taja tsaki ta tashi ta nufi bathroom.

NAMRA POV.
Haka Anty Amarya ta kwashe kusan kwana huɗu babu ruwanta da Namra, ita kuma tana
cikin ɗaki ta kasa fitowa kullum sai kuka take da ƙaratun Ƙur'ane, abun duniya duk
ya isheta ji take kamar ta kashe kanta ta huta.
Bayan sauko Sallah Jumma'ah Namra ta tashi ta shiga banɗaki tayi alkwala ta fito
ta gabatar da Sallah Azahar, bayan ta ƙare ta ɗauko Ƙur'ane tana karantawa.
Ta tsagaita karatun ne lokacin data ji sallamar Amira, sai da bata tsaya ba sai da
ta kai ƙarshen aya, sannan tayi addu'ah ta rufe Ƙur'ane, ta juyo ta kalli Amira.

“Amira”

“Na'am”

A kasale Amira ta amsa mata, dan jikinta ya gama mutuwa tun ɗazu, gashi ko ɗazu sai
da Uzair ya jaddada mata baya son a samu matsala.

Sai da Namra ta kai Ƙur'ane mazauninsa ta aje sannan tazo ta zauna kusa da Amira.

“Amira tun ranar ban ganki ba, gashi bana da waya balle na kira ki”

“Wallahi ban samu zama bane kinsan ga makaranta, wai miyasa kika daina zuwa ne
mutane sai tambayarki suke”

“Amira kunyar shiga makaranta nake yanzu, a gida ma na kasa sakewa balle makaranta”

“Amman da kin daure ai tun da gani, zai riƙa cire miki kewa, kin ga yanzu fa kina
ajin ƙarshe idan kika ce ba zakije ba duk wacan karatun naki zai tafi a banza fa”

Namra ta sauke ajiyar zuciya.

“Ni dai ba wannan ba, kin kawo min magani?”

“Na kawo miki gashi a jaka na, amman ban zan baki ba har sai kin min alƙawarin zaki
saka atamfar nan mu fita tare da ke, dan zaman nan ke kaɗai shi ke ƙara miki
tunani”

Ta ƙarasa ta ciro rigara daga jaka.

“Ba zan iya ba Amira bana iya fita ko ina yanzu”

“Ni dai ko cikin gida ne”

“Naji yanzu ina maganin?”

“Gashi nan”

Ta ciro ta miƙa mata.

“Gashi amman yace idan kina son yayi sauri zo miki toh ki sha huɗu, kuma yace idan
kin sha ki ɗan yawata”

A take Namra ta karɓa ta ɓare huɗu ta shiga bathroom ta sha. Tana fitowa Amira ta
miƙa mata rigar.

“Tun jiya na wanke miki ita, ɗinkin nan yaɓa fitar dake ke, je ki saka sai mu fita
ko garden ne mu zagaya”

Bata zaton da wata manufar Amira take son ta saka rigar, dan ko a mafarki bata
zaton Amira zata iya cutar ta ko kuma a haɗa kai da ita a cuce ta. Sai kawai ta kai
hannu ta karɓa, a gaban Amira ta ɗaura zanen rigar kuma da zata saka sai da tayi
Bismillah, hakan kuma ba ƙaramin tsoro ya bawa Amira ba, sai dai bata yarda ta nuna
ba, har suka fito tare suka nufi garden ɗin.
Wayarta ta ciro ta aika ma Uzair da text.

‘Ta saka yanzu, amman Haila be zo mata ba, na san dai ze zo mata tana sanye da ita’

Ƙarkashin bishiyar mangoro Namra ta zauna, kasancewar ta riga Amira isa gurin,
kamin ta zauna taji wayarta tayi ƙara alamar saƙo, sai kawai ta fasa zaman sai ta
koma gefen tana ƙoƙarin buɗe saƙon.

‘Amira you fuck up’

Ba shiri ta zaro ido ganin irin reply ɗin da yayi mata.


http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa12_28.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 13*

Hankalinta ya tashi sosai, har ta kasa jin kiran da Namra take mata, sai da ta yi
mata kiran kusan sau huɗu sannan ta amsa kamar a firgice ta juyo ta kalleta.

“Lafiya?”

Namra ta tambaya ganin yanayinta duk ya canja.


Ƙasarowa tayi kusa da ita ta dafa ta tana faɗin.

“Ba komai, Yaya ne yayi min text ina jin Ammy ba lafiya bari naje gida”

“Ko na raka ki?”

“A'a No yi zamanki da sauƙi ai”

Bata tsaya jiran abunda Namra zata ƙara cewa ba, ta nufu hanyar fita da sauri.
Hankalin Namra sai duk ya tashi tana jin kamar mahaifiyarta ta ce, har ta unƙura
zata tashi sai kuma ta koma ta zauna hango Maryam da tayi tafe ta doso inda take.
Kusa da ita ta zauna ta aje hangout ɗinta gabanta tana ƙoƙarin cire hijabinta.

“Anty Namra yanzu shikenan kin yi watsi da karatun ki ko?”

Namra ta sauke ajiyar zuciya.

“Haba Maryam kina min wannan maganar kamar ba kisan halin da nake ciki ba?”

“Allah ya kyauta! Amman ai ke kika jawa kan ki, ya dai kamata ace kin fara yima kan
ki karatun ta natsu, ba wai azo a zuga ki kawai ki hau kan layi ba”

“Maryam babu wanda ya zuga ni, kawai kisan bawa baya wuce kaɗɗararsa, dan Allah ki
daina ganin laifin Amira”

“Ba laifi ta nake gani ba, amman dai ina tunatar da ke kiyi hankali da yarinyar
nan, jikina yana bari babu alheri a abotar nan taku, dan ni tun ba yau na lura da
irin shigo-shigo ba zurfi da Amira take miki, dan tana kishin ki”

“Amira bata da wannan Maryam baki fahimce bana”

“Bata da wannan, take kishin ki? Yai Amira tana baƙinciki ta ga kin ɗinka sabon
kaya ita ata ɗinka ba, Amira tana baƙincikin ace kin fita zarra a jarabawa, Amira
bata ƙaunar a tare ki a hanya ita ba'a tare ta ba, in yau kika saye sabon takalmi
sai Amira ta siye, idan aBun farin ciki ya same ki a take Amira take canja fuska,
idan wani abu kika samu sai tasan yadda ta shiga ta fita kika hallakarda da shi
sannan hankalinta ya kwanta, ke duk baki lura da hakan ba?
Anty Namra ƙarshen duniya muke fa, kuma Annabi da kansa ya faɗa a cikin alamomin
ƙarshen duniya akwai rashin amana da cin amana da rashin yarda, Wallahi kiyi
hankalin da mutane.
In ma wani sirrin ki ne karki ƙara faɗawa Amira, dan daga lokacin da ke da kanki
kika kasa ɓoye sirrinki a cikin cikinki, har kika faɗawa Amira Wallahi kamar kin
faɗawa duniya ne”

Namra tayi shiru tana kallon yadda Maryam take tsire baki tana faɗin maganganun,
zuciyarta na nazarin kalamanta. Ita kanta a yanzu tana zargin Amira tun daga abunda
ya faru da ita, sai dai yadda Amira take nuna mata akwai Aminci a tsakanin su ya
kan rikita zarginta.

“Forget about Amira, yanzu dai Abbah yace ki kawo Asim ze aura miki shi how do you
feel?”

“I don't know, amman ina jin kamar ban kyautawa Abbah ba, kuma ba zai fahimce ni
ba, idan kuma na kawo wani wanda ba Asim na aura Asim zai cigaba da kallo a
matsayin mayaudariya, ban san yadda zan yi ba”

“Yanzu dai Uzair ya fasa auren ki, dan haka duk wanda zaki aura babu ruwan Abbah ba
kuma ze karɓi wani excuse daga gare ki ba, kinga ƙara ma ki auri Asim ɗin, in yaso
sai kiji da Abbah”

“Maryam ban san inda Asim yake ba, Mahaifiyarsa ma tace min bata san inda yake ba,
saboda ni ya bar garin nan”

“Ƙarya take tace bata san inda yake ba, shi Asim ɗin yaro ne da zai gudu be faɗawa
mahaifiyarsa ba? Baya gari ya akayi Amira ta ganshi?”

“Nima ban sani ba, tace min kiranta yayi a waya”

“Kin gani ko? Wannan Amirar munafukace. Ni zan taya ki nemansa, har gurin uwarsa
zanje idan kuma tayi min maganar banza na ci mata mutunci”

“A'a ni dai dan Allah karki mata rashin mutunci, ki bita da lalama”

“Ke fa Anty Namra kina da matsala, mutanen duniya in ka sake sai su ci maka tuwo a
ka, kawai idan mutum ya maka zuma sai ka masa wuta, idan kuma ya maka yayyafi sai
ka masa ruwa”

“Nidai na ji amman ban da rashin mutunci kinji?”

Ta tsire baki gefe.

“Naji tashi mu shiga ciki, ni yunwa ma nake ji ganin Amirar yasa na shigo nan”

Miƙewar da Namra zatayi sai taji abu ya gangaro mata a ƙafa, tana ɗaga zagen taga
jini. Lumshe ido tayi ta buɗe ta kalli Maryam dake kallonta sannan ta riƙa hannunta
suka shiga ciki.
Suna shiga Maryam ta nufi kitchen, Namra kuma ta nufi ɗakinta, ta cire kayan
jikinta ta gyara jikinta ta saka pad sannan ta saka wasu tufafin.

UZAIR POV.

Sai safa da marwa yake, hankalinsa ya kasa kwanciya, tun lokacin da Amira ta masa
text ɗin shirmen data aikata. What if aikin ya dawo gareshi? Tun da malamin yace
indai akayi aikin dole ne ya ci.
Najeeb ya dafa shi

“Uzair ka kwantar da hankalin ka mana”

“Haba Najeeb wane irin kwantar da hankali kamar baka san yadda abun nan yake ba,
kuma kana ganin taje ta aika mana shirme, ban san abunda yake damun ƴar iskar
yarinyar nan ba”

“Ka natsu mana sai mu kira malamin mu faɗa masa abunda yake faruwa”

Sai a lokacin ya zauna, tashin hankali ƙarara a fuskarsa. Kira biyu Malamin ya
ɗauka, sai Najeeb yayi masa bayanin komai. Malamin ya daɗe yana jimamin abun sai
tambayar yadda akayi suka yi wannan kwaɓar yake.

“Yanzu dai mu saurara nan da kwana biyu mu gani”

“Yanzu Malam babu wani abu da za'a iya yi, babu wata mafita?”

“Mafita ɗaya ce, a nemo kurciyar nan acire layar da aka laƙa mata, kasan kuma mun
riga mun saki kurciyar kamunta yanzu ba abu ne mai yiyu ba, sai dai kasan ai da
sunan ita yarinyar mukayi dan haka ku ɗan dakata tukuna mai yiyuwa ya iya kamata”

“Ko asa ta cire rigar?”

“A'a duk ta cire rigar ba tare da aikin ya shiga jikinta ba, zai iya dawowa, kasan
lamarin iska”

“Okay toh mun gode”

Najeeb na kashe wayar Uzair ya miƙe tsaye yana faɗin

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,


Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah ka cece ni Allah”

Jafar ya aje wayar hannunsa ya kalli Uzair yace

“Haba be a Man mana, ai ko aiki zai dawo ba akanka zai koma ba akan Amirar zai
koma”

Uzair ya kalleshi

“Amman ai ba ita tayi aikin ba”

“Easy Man ai ita tayi kuskuren, kirata muji yadda tayi wannan banzan shirmen”

Jafar na gama maganar, Uzair ya ciro wayarsa ya danna mata kira.

AMIRA POV.

Kuka take sosai, tun da ta baro gidan su Namra take kuka har ta iso gida. Bata bari
Ammy taga shigowarta ba, sai kawai ta shige ɗakinta ta hau kuka baji ba gani. Ita
kanta idan za'a tambayeta bata san dalilin kukan ba, ita dai tana jin kuka yana zo
mata kawai.

Ganin Number Uzair ce yasa ta ɗauka ta kara a kunne.

“Amira taya kika yi wannan shirmen? Ban faɗa miki ba a son a samu matsala ba?”

“Ai tasa rigar”

“Toh Uban wa yace ki bari tasa ba tare da haila yazo mata ba? Wace irin mahaukaciya
ce ke?”

“Yanzu idan ba a yi dai-dai ba me zai faru?”

“Ban sani ba”

Sai ya kashe wayar. A take zuciyarta ta soma raya mata Namra haukacewa zatayi. Kuma
ita za a zarga tun da anga shigarta gidan gashi Maryam ta haɗu da ita, hakan yasa
ta fashe da kuka zuciyarta na raya mata lallai asirinta na daf da tonuwa.
Haka ta wuni ta kwana da tunanin abunda ze samu Namra, gashi kukan yaƙi ya tsaya
mata, ta takure kanta a ɗaki, a ɗayan ɓangaren kuma tana tunanin inda zata samawa
kanta mafita, dan ji take kamar wani zai faru da Namra, tun da batayi dai-dai ba,
kuma ba makawa ita za a zarga. Ji take duk ta tsani kanta, zuciyarta na raya mata
ta gudu kawai kamin asirinta ya tonu.

MARYAM POV.

Daga Makaranta ta wuce gidan iyayen Asim. Cikin ladabi tayi sallama ta shiga. Sai
Mahaifiyarsa ta amsa mata dan ita kaɗaice yau a gidan. Har ƙasa Maryam ta risina ta
gaishe ta. Ta ta ɗan kawarda fuskarta dan ta gane ƙanwar Namra ce tun da sun taɓa
zuwa tare da ita.

“Lafiya ƙalau”

“Dan Allah ko Asim na nan?”

“Baya nan yayarki ta zo nan na faɗa mata baya nan, ni ma ban san inda yake ba”

Daga nan sai Maryam ta canja salo.

“Kin san inda yake kam, dan babu yadda za'ayi ace uwa kamar ki bata san inda ɗanta
yake ba, shi Asim ɗin yaro ne da zai bar gida yaje nesa ba tare daya faɗa miki ba”

“Au toh ko ƙarya zan miki, macuta maciya amana, bayan kun gama cin moriyar ɗana
sannan zaku watsa masa ƙasa a ido, yanzu dan munafurci ne za ku wani zo nemansa
kamar ya ci bashin ku?”

“Bashin mu yaci mana, yaje ya ɗaukewa ƴar'uwata hankali ta haukace tace shi take
so, yace ta kawo shi a aura mata, shine kuma dan rainin hankali zaki ce baki san
inda yake ba, Wallahi sai kin nemo shi duk inda yake ko kuma naje na faɗawa Abbah
yasa a kulle ku dake da danginki har sai Asim ɗin ya dawo, dan ba zaku sa muna
ƴar'uwa a matsala ba”

“Eh ai zamu iya, tun da ku ƴan siyasa ne ku keda gwannati, amman bari kiji na faɗa
miki ni ɗana ba zai aure ƴar marasa mutucin ba”

Maryam ta matso kusa da ita tana zare ido.


“Ooo.... Uwata ce marar mutunci ko?”

“Ni ban ce ba, salon kije ki ƙulla min ƙullaliya, Toh ta Allah ba taki ba”

“Ni dai na faɗa Wallahi ko ki nemo inda ɗanki yake ko kuma duk abunda ya faru dake
ke kika ja”

Mahaifiyar Asim ta nuna Maryam da yatsa.

“Ke wannan da ganin ki ba zaki gama lafiya ba”

Maryam ta tuma ta dire.

“Ƙwarai ba zan gama lafiya saboda da kika hallice ni ai baki yi dan na gama lafiya
ba, ta yadda idan an je lahira zaki jidaɗin ƙoneni a wuta ko? Ai ke cw ba zaki gama
lafiya ba tsohuwa dake kina ƙarya baki san inda ɗan ki yake ba ko kunya baki ji ba”

Ta daki ƙirji.

“Ke ni kike faɗawa wannan maganar?”

“An faɗa ɗin, biri ai a hannun malami ya kan yi guɗa, a hannun bamaguje sai kuka,
kuma Wallahi ko ki nemo ɗanƙi ko ki shiga a matsala”

A nan Maryam ta tofar mata da yawu ta wuce, tana bankaɗar mutanen da suka fara cika
gidan gurin kallon faɗa.

_____________________________________

Me kuke tunanin ze faru a shafi na gaba?

Anya Asim zai dawo? Da gaske Mahaifiyar Asim bata san inda yake ba?
Ya rayuwar Amira da Uzair akan kuskuren da sukayi? Me zai faru da Namra?

Masu ziyarta shafina, a ƙasan blog ɗin zaku ga gurin subscribe, a nan zaku saka
email address ɗin ku ta yadda da nayi sabon updated zaku samu notification, na kan
fara sauke post ɗina a can kamin na kawo shi whatsapp.

Ina son ku duka fisabilliah 😘


Best regards 💖
Khadeeja Candy 🌺
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa-14.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

*PAGE - 14*

Sai da aka kwana biyu sannan Maryam ta labarta ma Anty Amarya da Namra yadda suka
yi da Maman Asim.
Ran Anty Amarya ya ɓace sosai, daga ita har Namra basu jidaɗin abunda Maryam tayi
ba.
“Ke ke Maryam ba wata ba, Allah ya sauwaƙe miki bakin mutane, kullum ana miki
magana amman kamar ba'a yi, rashin kunya an faɗa miki abun ƙwarai ne? Ai gashi nan
baki mutane akan ki Wallahi Allah ya sauwaƙe miki wannan rayuwa”

Maryam ta ɓata rai sosai, daman tasan za'a rina dan tasan sai Anty Amarya tayi mata
faɗa, tun da bata taɓa yaba ma masifar ta ba.
Anty Amarya kam sai harararta take tana jin kamar ta dake ta.

“Aure dai zakiyi kuma mace kike Wallahi ki canja rayuwa dan baki san inda zaki faɗa
ba”

“Naji Anty yi haƙuri kin san ni yarinya ce har yanzu”

Namra tayi mata wani kallo

“Kece yarinyar?”

Sai kawai tasa dariya ita da Aisha. Anty Amarya ta ɗauke kai tana amsa sallamar da
Ammy tayi.
Cikin tashin hankali ta doso inda Anty Amarya take gyalenta ma a bai-bai ta
yafashi.

“Hajiya Amina lafiya na ganki haka?”

Ta zauna saman kujera tana kuka.

“Wallahi ba lafiya ba, Amira ce tun jiya ba mu ganta ba, ba musan inda take ba”

Gaban Namra da Anty Amarya ya faɗi. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Shine
abunda yake fitowa a bakin su. Namra tace

“Amman an bincika ko ina? Kuma bata ga inda zata ba?”

“Bata ce ba, tun ranar data fita tace min nan zata zo inda kike ban sake sata a ido
ba sai da safe, ko na na shiga ta tarar tana ta kuka wai kanta ke mata ciwo, sai ce
min take tana jin tsoro, na bata magani ta sha sai tayi bachi, ko da na sake leƙawa
ɗakin na dubata sai naga bata ciki, na duba ban ga jakarta ba da wayarta, sai na
ɗauka ko tazo nan ne, har dare shiru, sai da Abbah ta ya dawo muka yi ta nemanta ba
mu ganta ba idan an kira wayarta kuma kashe, haka muka kwana cikin tashin hankali”

Da kuka sosai ta ƙarasa maganar. Sai hawaye suka silalo daga idon Namra a take ta
fasa kuka. Anty Amarya tace

“Wallahi rabonta da gidan nan tun shekaran jiya ranar laraba, ban sake sata a ido
ba, Allah ya a gaji wannan yarinya ko ina ta shiga?”

Namra ta share hawayen idonta

“Ammy baku mata komai ba? Ba faɗa tayi da wani ba? Kuma babu wanda yayi mata
sallama ko da a waje?”

“Wallahi bamu mata komai ba, kuma ni dai ban san wani yayi mata sallama ba, amman
dai Babanta ya kai ma ƴan sanda report ko Allah ze sa a gane inda take, amman ke
Namra baki san inda Amira zata iya zuwa ba?”

“Wallahi ban sani ba, ranar ma data bar gidan nan naga kamar anyi mata saƙo sai
tace min wai kece ba kida lafiya bari tafi gida, washen garin ranar ne ma nace
Maryam taje ta duba ki, sai tace min ai sun haɗu da Amira tace mata kin ji sauki”
“Wallahi ni ban yi wani ciwo ba lafiya ta ƙalau, na shiga uku yau ina Amira ta
shiga?”

Da kuka ta tashi ta nufi ƙofa. Anty Amarya na bata haƙura har gurin har gurin gate.
Lokacin data dawo ne Hajiya Barau ta tare ta tana tambayar lafiya. Itama salati
tasa lokacin tada ji abunda ya faru, suna cikin maganar sai ga Namra ta fito sanye
Hijab tana hawaye.
Tana ƙarasowa kusa da su Anty Amarya tace

“Namra ina zaki ?”

“Anty zama be gan ni ba, tun da Amira ta ɓata”

Hajiya Barau ta riƙota

“Wallahi babu inda zaki, kije nemanta kema a ɗauke ki, ko kin manta abunda ya faru
ne? Allah dai yasa ba Asim ɗin ne ya sace ba itama”

Namra tayi saurin girgiza kai.

“Wallahi Hajiya ba shi bane, Asim ba ze haka ba, Asim ma baya garin nan gaba ɗaya”

“Uhmm Aifa sai kiyi kuma, irin abunda aka miki ne za a mata, Inshallah mutun ɗaya
ne yake muku wannan abun”

“Wallahi ba wanda zuciyarki take zargi bane, Asim baya garin nan”

“Toh a ina yake?”

Hajiya ta tambaya tana mata wani makirin kallo.

“Nima ban sani ba, amman dai ba shi bane”

Anty Amarya ta kasa mata tsawa

“Ai sai ki tsaya nan kina gardama da uwarki akan abunda baki da tabbaci, wuce ki
koma ciki babu inda zaki je”

Ba dan taso ba, ta juya ta koma ciki tana kuka. Anty Amarya ta rufa mata baya tana
ta mata faɗa wai tana gardama da Hajiya kamar ma uwarta.

Hajiya Barau ta tsire baki ta shige part ɗinta zuciyarta na raya mata Namra ta san
inda Amira take.
Bedroom ɗinta ta shige ta ɗauki waya ta kira Uzair tana labarta masa abunda ya
faru. Ya kaɗu matuƙa shi kansa ya kwana biyu yana kiran wayar Amira amman baya
samu. Sai dai wani ɓangaren hankalinshi ya kwanta ganin kamar asirin kan Amira ya
koma ba kansa ba.
Bayan ya gama waya da Hajiya ya kira Najeeb ya labarta masa ɓatan Amira.

“Kaga abunda nake faɗa maka ko? Ai daman nacw maka aikin ba akan ka ze dawo ba akan
Amira ze koma”

“Ban sani ba ko nawa na nan tafe Najeeb, amman ina cikin tashin hankali”

“Ka kwantar da hankalinka babu abunda ze faru, amman kuma ka rufe wannan maganar”

“Ya za'ayi ma an faɗa, Allah dai ya sauwaƙe, Ni wallahi ba zan sake irin wannan
abun ba”
Najeeb yasa dariya.

“Uzair ka cika tsoro da yawa, shiyasa ka yi sake har waɗannan abubuwan suka faru”

“Ni dai naji”

Daga haka ya kashe wayar, ya nufi ɗakin matarsa.

Hajiya na gama waya da Uzair sai ta kira wata ƙawarta wace take taubashiyar Ammy.
Bugu ɗaya zuwa huɗu ta ɗauka.

“Assalamu Alaikum”

“Wa'alaikissalam Hajiya yanzu nake labarin ki, nace ko kina da labarin abun da ya
faru?”

“Wallahi bani da labari sai yanzu nake jin abunda ya faru, shima fa dan Ammy tazo
da kanta ne dan Wallahi sam ni Amarya bata faɗa min ba”

“Au kina nufin sai yanzu kika ji?”

“Wallahi sai yanzu shiyasa ma nakira ki, Namra ta ɗaki ƙasa ta rantse ita ba Asim
bane ya sace Amira”

“Wanene Asim kuma?”

“Ina wani tsohon Saurayin Namra wanda na taɓa baki labari nace miki mahaifinta ya
mata miji amman tacw bata so sai shi ko kin manta?”

“A'a na tuna ɗan makarantar su ko?”

“Allah ya bar ki, shi ne fa, toh ai kinsan shine ya sace Namra kwanakin baya har
shiyasa ma mijin da zai aureta yace ya fasa”

“Ke ya sace fa kika ce?”

“Wallahi ya sace ko kuma ta bishi ba, kuma kinga ita Amira ta faɗa tace shine yazo
ya tafi da Namra ɗin kuma duk nan mutane unguwa sun shedi haka dan sunce sunji
lokacin da yake magana, har fa iskanci yayi da ita”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un toh wai ko sha ya sace Amirar?”

“Nima dai shi nake zargi, kuma magana ta gaskiya Namra tasan inda Amira take saboda
tasan inda shi Asim ɗin yake, saboda ɗazu take take ƙoƙarin kare shi wai baya garin
nan me me magana babu kai babu gindi”

“Amman wannan magana ai bata kyalewa bace, indai har haka ne dole ne a nemi Namra
ɗin kuma ita da kanta Ammy tace min Namra ce mutum na ƙarshe da Amira ta gani”

“Ai ke dai bari ƙawayen zamani ai sai a hankali, Allah dai ya bayyana ta”

“Amin bari na kira Ammy yanzu”

Hajiya Barau tayi saurin cewa.

“Dan Allah karki ce gare ni kika ji, kinsan halin Alhaji balle kuma baka kake iko
da gida ba, sai ace kayi ma ɗan kishi shaeri”

“Haba dai Hajiya sai kace wata ƙaramar yarinya da zanje nace ke kika faɗa? Ai babu
wannan tsakanin mu”

“Toh na gode sai na jiki”

Daga haka ta kashe wayar.

KALSOOM POV.

Kwata-kwata Hilal be yi zuwa huɗu ba Daddy yace ya turo iyayensa. Shi kuma daman
haka yake son yaji, satin daya zagawo iyayen Hilal suka neman auren Kalsoom, farin
ciki gurin mahaifiyar Hilal kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha.
Iyayen basu bar gurin ba har sai da Daddy da ƴan'uwansa suka yanka musu sadakinta
dubu saba'in suka biya sai Daddy yasa musu rana dan ba so yake aja abun da nisa ba,
shirin da biyar ga watan huɗu. Cikin farinciki da jindaɗi suka bar gidan.

A ranar Rashida bata yi bachi ba saboda baƙinciki, kwana tayi kuka Hilal na
rarrashinta. Washen garin ranar da akayi abun Kalsoom taje aiki sai suka riƙa taya
ta murna suna ce mata amarya. Tayi mamakin inda suka samu labarin tun dai ita ban
da ƙawarta Salma bata san ta faɗawa kowa ba, da Momy tace mata ƙara kawai mutane
suji za'a ɗaura mata aure.

Sai daga baya suka faɗa mata ai Asma'u ce ta faɗa musu. Kalsoom ta kalli Asma'u
tana dariya

“Asmee ina kika ji?”

“Abun sheri ma be ɓoyu ba balle na alheri”

“Ni ina mamakin ta ina kika ji”

“Ai tuni ni na sani dan har a wayar mijin naga hoton ki, ido na sa miki dan naga
indan zaki faɗa”

Sai duk suka sa dariya. Suka mata barka da Allah yasa alheri.
Bayan ta wuce office ɗin ta Asmee ta bita tana zolayarta

“Amaryar mu amarya mu”

Kalsoom ta ɗora jakarta saman tebur tana dariya.

“Wai daman Hilal ɗan'uwan ku ne?”

“A'a unkuwar mu ɗaya dai da shi, kuma mijina abokin shi ne”

“Allah sarki ke haka unguwarku daya ba”

“Amman Wallahi kin yi dacen miji, gaskiya Hilal yana da mutunci sosai, gashi bawon
mata sai yadda kika yi dashi, matarsa ma ba daɗinta yake ji ba amman sai juya shi
take”

“Kin san matarsa kenan?”

“Sosai ma, amman wallahi ƴar banza ce sai kin shirya zama da ita hmmm amman aje
aikinki zakiyi ko?”

“Haka yace wai baya son aiki”

“Ai saboda aikin matarsa zai ƙara aure dan ya son ya hanata aiki amman ba dama”
“Saboda me?”

“Ai ma'aikaciyar banki ce ƴar gidan su Dr. Ayuba matsayi, kin san ai ƴaƴan gidan ba
daga baya ba, haka ake cewa wai aba a musu kishiya, uwarsu ma duk masifar Uban sai
tun da ya aure mui”

Ta ƙarasa tana shafa baki. Ganin yadda Kalsoom ke kallonta yasa ta tsargu sai ta
tashi daga saman kujerar da take zaune tana dariya tace

“Bari na koma gurin zamana kar MD ya tararda ni a nan ina tsiyaya”

Nan ma Kalsoom murmushi kawai tayi. Sai ta nufi ƙofa tana faɗin

“Mu dai ayi auren nan da wuri aje ayi mana rainon ƴan ɗiyan mu, Allah ya sanya
alheri”

Da Amin Kalsoom ta amsa ta bita da kallo tana nazarin maganganunta.

NAMRA POV.

Wuni Namra tayi addu'ah tana ba Allah cigiyar inda Amira take. Duk hankalinta ya
tashi ji take kamar ita ce ta ɓata, abu ɗaya zuciyarta ke ayyana mata wato Uzair,
sai dai ta kan tambayi kanta da kanta ma zai haɗa alaƙa tsakanin Uzair da Amira.

Kiran da taji Maryam tana mata yasa ta tashi daga saman sallayar da take ta nufi
falo.
Tsatsaye ta tararda su Anty Amarya da wasu police biyu mata tsaye a falo. Gaban
Namra ya faɗi, da sauri ta ƙaraso kusa da su.

“Lafiya?”

Sai ɗaya daga cikin ƴan sandar ta nuna mata id cart ɗinta.

“From Marna Police station, Muna zargin da a hannu gurin kidnapping ɗin Amira,
abokan aikin mu suna waje, zamu je da ke a station”

Ba shiri Namra ta daki ƙirgi tana nuna kanta.

“Ni....?”

Da sauri Maryam ta nufi part ɗin Abbah tana kuka. Anty Amarya ma kuka take ita da
Aisha. Kamar an jefo Hajiya Barau sai gata cikin ɗakin tana salati da sallami.

____________________________________

THERE WORDS FOR THIS CHAPTER...!


WHAT DO YOU EXPECT NEXT?
LOVE YOU ALL FISABILLIAH 😘
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa12.html

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 15*

Suna fitowa waje Abbah na kawowa. Sai ya tsayar da ƴan sanda yana tambayarsu.

“Miya faru haka?”

“Sir muna tuhumar Namra ne da sa hannu a gurin sace Amira”

Abbah yayi ma Namra wani kallo. Sannan ya kalli ƴan sanda yace

“Ɗaya daga cikin ku zata biyo ni muje cikin motana”

Ba su musa masa ba, ɗaya daga cikin police ɗin ta bi Abbah suka shiga mota ita da
Namra baya, Anty Amarya a front seat.
In banda kuka babu abunda Namra take har aka isa station ɗin. Sannan Abbah ya fita
suka shiga cikin station ɗin. Ammy da ƙanwarta na tsaye a gurin idonta A kumbure.
A take wani police ya karanto masa abunda ake zargin Namra da shi, sannan yayi musu
jaga zuwa office ɗin dpo. Sai da ya gama da wasu cases sannan ya su Namra suka iso
gurin ya gaisa da Abbah cikin mutumci yana girmama shi.

“Ranka ya daɗe Ashe kai ne”

“Nine Wallahi ya aiki ya kwana biyu”

Abbah ya faɗa ba dan ya waye shi, sai dai shi ɗin yasan Abbah kasancewarshi
sanannen ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa.

Bayan Abbah ya zauna, Namra ta zauna a kujera dake kusa da Abbah, sai Ammy ta zauna
a kujarar dake gefen Namra ita da ƙanwarta.
DPO ya kalli ya dubi takarda take gabansa ya kalli Namra yace

“Amm Namra Usman ana zargin ki dasa hannu gurin ɓatan ƙawarki Amira...”

Kasa magana Namra tayi sai kuka take. Abbah ya katsa mata tsawa.

“Ki buɗe baki kiyi magana mana”

Sai kawai ta ƙara rushewa da kuka kamar zata tsuƙe. Anty Amarya tace

“Taya zata iya magana? Bayan irin ƙazafin da aka mata, a rasa wanda za'a zarga sai
ita, lokacin da Namra ta ɓata miyasa bamu zargi Amira ba, ko ita Namra ba ƴa bace?
Ko kuma ni ban san zafin ta ba? Faɗa min ɗa ya fi ɗa ne? Wallahi Allah sai ya saka
mata shikenan dan anga yarinya bata magana komai aka kwaso sai a dire a kanta, dan
kin rikice akan neman ƴarki sai ki ɗauka ki ɗorawa wani, me kuke da shi da har
Namra zata sa a ɗauke Amira, wallahi ke kinsan Namra ta fi ƙarfin Amira nesa ba
kusa ba...”

Dpo ya miƙe tsaye yana ɗaga ma Anty Amarya hannu.

“Dan Allah Hajiya ki saurara, an zo nan dan a sasanta ba dan faɗa ba”

Bayan ya zauna ya kalli Namra yace

“Ki kwantar da hankalin ki ba wani za'a miki ba, nan guri ne na...”

Ƙwanƙwasa ƙofar da akayi ne ya hana Dpo ƙarasa maganarsa.


“Yes come in”

Wani ɗan sanda ne ya shigo ya sare masa sannan yace

“Sir Alhaji Haruna is here to see you”

“Let him in”

“Yes Sir”

Ya sake sare masa sannan ya juya ya fice. Sai ga Abbah Amira ya shigo cikin ɓacin
rai, idonsa be sauka ko ina ba sai akan Ammy, nunata yayi da yatsa.

“Amman Wallahi Asiya baki jin magana, yanzu duk maganar da na miki baki ji ba, sai
da kika aikata? Yanzu miye amfanin haka? Ki zubar da kanki mutuncin kawai”

Ya ƙarasa yana miƙawa dpo hannu suka gaisa.

“Wannan maganar bata ma kamata ta fito bakin ki ba, dpo ban kawo maka rahoton ɓatan
yarinyar nan ba? Babu inda ban kai rahoton nan ba”

Dpo ya ɗaga masa kai yana murmushi. Abban Amira ya miƙa Abbah hannu suka gaisa

“Alhaji Usman, yau dai mun yi zumunci dole, mata sun haɗa mu”

Abbah yayi dariya.

“Kasan sha'anin mata sai haƙuri, ba tunani suke ba idan zasu yi abu”

“Wallahi basa tunani yanzu miye amfanin wannan abun? Yanzu haka sai da aka kira ni
daga gwuiwa station aka ce min ance anga Amira a tashar mota amman basu san motar
data shiga ba”

Ammy ta fashe da kuka.

“Wallahi babu abunda ze sa Amira ta gudu tun da ba wani abu muka mata ba”

“Toh aljana ce aka gani kenan? Ko kuma ƙarya suke, tashi ki wuce gida bana son
maganganun banza”

Cewar Alhaji Haruna Abban Amira. Abbah yace

“Karka ga laifin ta duk haka muke fama dasu inda mata ne sai haƙuri”

“Magana ce da bata da toshe balle makama ban san inda ma wannan maganar ta fito ba”

Cikim kuka tace Ammy tace.

“Hajiya Barau ce ta faɗa kuma ai ba zata yi ƙarya ba”

Abban Amira ya nuna ta da hannu yana kallon Abbah.

“Kaji ko? Jita-jita ne kawai”

Abbah yayi shiru yana motsa baki alamar nazari. Alhaji Haruna ya kalli Ammy da
Ƙanwarta yace

“Ku tashi muke gida”


Da kuka Ammy ta tashi ta fice, sannan ya kalli dpo ya ciro wasu ƴan kudaɗe a
aljihunsa ya aje gaban teburin dpo

“Dan Allah aka kashe maganar nan dpo, matsala ta cikin gida ayi haƙuri”

“Ba matsala, muma ai mun fi son haka”

Tare da Abbah suka fito. Anty Amarya na riƙe da Namra har suka fito harabar station
ɗin. Sun ɗan daɗe suna fira da Alhaji Haruna sannan sukayi sallama cikin mutunci ya
wuce Abbah kuma ya nufi Motarsa.
Har Abbah ya iso gida Anty Amarya masifa take, tana kiran Hajiya Barau da munafuka.

“Ai itama ta haifi ƴaƴa mata, zata jidaɗi idan aka mata haka? Me Namra ta tare mata
ne? Ai Wallahi duk mace data ɗuka ta haifi mace tace wata macen ba zata jidaɗi ba
sai Allah ya gwada mata akan ƴaƴanta”

Sai da Abbah yayi parking sannan ya kalli Anty Amarya yace

“Bana son ƙananan maganganu, ki wuce part ɗin ki ki bar ni da ita kawai”

Bata sake cewa komai ba, dan tasan halin Abbah zai iya juyarda faɗan akanta. Sai
kawai ta buɗe ta fita ita da Namra suka nufi part ɗinta Abbah kuma ya nufi part ɗin
Hajiya Barau.

Tana ganin Abbah hankalinta yayi mugun tashin, kamar tasan asirinta ya tono, ko da
yake ta karanci yanayinsa shiyasa zuciyarta ta ayyana mata lallai akwai laifin da
tayi masa.

Abbah be kula jikokinta da suke falon ba ya hauta da faɗa, daman haka yake idan ya
tashi matsifa babu ruwanshi da wanda yake zaune. Ta inda Hajiya barau take shiga
bata nan take fita ba, tun tana ƙoƙarin kare kanta har ta kai ga fasa kuka tana
faɗin

“Ni Wallahi ba da wata niya nayi ba, kuma tun da daɗewa mukayi wannan maganar fa”

“Ni dai na faɗa miki, ki iya bakin ki ko kuma duk abunda ya same ki ke kika ja,
Namra dai kin kusa jikanya da ita, dan haka ba dai-dai bane ki zauna kina faɗan
mugaye kalamai akan ƴarki”

Kuka take sosai tana faɗar wai ƙazafi aka mata, har jikokinta suka dafata suna bata
haƙuri. Sannan Abbah ya tashi ya nufi part ɗinsa.

Namra na kwance jikin Anty Amarya tana sauke ajiyar zuciya Maryam tace

“Wallahi Allah sai ya saka miki daga Ammy har tsohuwar makirar can Hajiya”

Anty Amarya ta katsa mata tsawa.

“Ke matar uwanki zaki cewa makira ko dan darajar tsufanta kya ce mata haka, balle
tana auren uban? Kin gani ina ja miki kunne akan rashin kunyar nan kina ƙarawa ko?
Wallahi kika kai ni ƙul sai na ɓata miki rai”

Miƙewa tayi tsaye cikin fushi ta miƙawa Namra takardar dake hannunta.

“Ke ni dai karɓi, Asim ya zo baki nan yace a baki”

Da sauri Namra ta ɗago ta kai hannu ta karɓi takardar, sai ta share hawayenta ta
tashi ta nufi ɗakinta, zuciyarta cike da zazzanar son sanin abunda takardar ta
ƙumsa.

__________________________

Wannan shafi na ƴan TASKAR KHADEEJA CANDY ne, da CLASSIC LADIES, tare da NAMRA FANS
GROUP. I really appreciate your comments 💖💖💖
https://chat.whatsapp.com/LHd6gwdQQWZKNeHU9z4qf0

Masu tambayan grp ga link nan. Amman ban da maza ❌

🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 16*

Natsuwa tayi sosai ta tattara dukan hankalinta ta mai da gurin takardar, sannan ta
buɗe ta soma karantawa.

_SALAM_
MY DEAR NAMRA.

Na zo gidan ku ance min baki nan, na kira wayarki ban samu ba, mahaifiyata kuma ta
shaida min kina nema ma, ban san ta yadda zan iya ganin ki ba amman ga sabon number
waya na ki kira ni dan Allah.

Urs ASIM.

Wani dogon ajiyar zuciya ta sauke, ta rumgume takardar a ƙirjinta ta lumshe ido,
tana sauraren bugun zuciyarta.
Ta ɗauki daƙiƙa goma zuwa shabiyar kamin ta buɗe idon, ta tashi ta nufi ɗakin
Maryam.
Dariya ta tararda Maryam na ƙyalƙyala kamar wata sabuwar mahaukaciya, har ta zauna
kusa da ita bata san ta zauna ba, tana taɓa ta ta zabura.

“Wayyo Allah na”

“Ke lafiyan ki?”

“Wallahi wani littafi ne nake karantawa mai shegen dariya”

“Littafi kuma ai ke Allah be raba ki da karatun littafai ba”

“Wallahi Anty Namra yayi daɗi kamar me, da zaki karanta kema da kin sha dariya”

“Idan na samu time zan karanta, meye sunan littafin?”

“Noor na Khadeeja Candy”

“Okay ni dai ara min wayarki wani abu”

“Ke dai ce zaki kira Asim ba wai kiyi wani abu ba”
“Naji ni dai bani”

Sai da tayi saving ɗin page ɗin, sannan ta miƙa mata wayar tana zolayarta. Namra
dai bata ce mata komai ba ta tashi ta fice tana faɗin.

“Ina fatar da Akwai kuɗi a ciki”

“Kai kaji ki da wata magana, manyan Babe's irin zasu zauna waya ba kati, taf mune
tare da manyan samarin garin nan fa, kin san ko dan karya dole a saka mana manyan
kati ”

Da dariya Namra ta fice, ta koma ɗakinta. Takardar ta ɗauko ta saka Number ta danna
kira. Ringing biyu zuwa uku yayi picking da sallama.
Sai da ta lumshe ido ta buɗe da murmushi sannan ta amsa masa.

“Wa'alaikassalam. Asim”

“Namra...”

Daga cikin wayar tana jin lokacin daya sauke ajiyar zuciya, sannan yace

“Namra wai Abban ki ya yarda na aure ki?”

Kai ta ɗaga masa kamar yana gabanta, hawaye suka silalo mata.

“Ya yarda Asim, shiyasa na neme ka”

“Alhamdulillah”

“Ina kaje Asim? Ashe zaka iya tafiya wani guri ka bar ni?”

“Namra idan mun haɗu zamu yi magana”

“Yaushe zaka zo?”

“Ba zan iya zuwa gidan ku da sunan hira ba, sai dai mu haɗa ta layin su Azeema”

“Okay gobe da ƙarfe tara dan Allah”

“Allah ya kai mu I Love You”

“I Love You More”

Daga haka ya kashe wayar. Sai ta rumgume phone ɗin tana murmushi tare da hawaye.

KALSOOM POV.

Kusan kullum sai Doc. Hilal ya kirata a waya sun gaisa, sai dai fira ce be cika
zuwa ba sai jefi-jefi. Sau biyu ya taɓa kawo mata ƴaƴansa suka gaisheta ita kuma
tayi musu goma na arziki.
Ana sauran sati biyu biki Doc. Hilal ya nemi ta bashi list ɗin abubuwan da zata yi
na biki. Bata rubuta wasu abubuwa masu yawa ba, bayan abubuwan da al'ada ta tana
da.

Batayi wata hidima ba duk da kasancewar ƙannenta sun so tayi, amman bata biye musu
ba, wai ita ta girmi wannan yanzu.
Kala kusan arba'in da huɗu yayi mata, duk masu kyau da ɗaukar hankali, kowa ya gani
sai ya yaba, wasu na faɗin haƙurin da tayi yanzu zata ci riba.
Ranar laraba aka saka amarya lalle a daren ranar akayi wankin amarya, washegari
alhamis akayi ƙunshi da kitso, friday akayi walima, Assabar aka ɗaura aure Kalsoom
da Doc Hilal.
Daddy yayi mata nasiha mai ratsa jiki, gwaggwanin suka mata jan kunne akan rayuwar
gidan aure kamin Momy ta ɗora da nata. Kuka sosai Kalsoom tayi a lokacin da aka
fito da ita za a saka ta mota zuwa gidan mijinta. Duk wanda ya gani zai yi zaton
bata son auren ne.

Da ƙafar dama ta shiga gidan aurenta tana ƙorar shedan kamar yadda Momy ta faɗa
mata. Sai da aka zaunar da ita a saman gadon aurenta sannan ta tsagaita kukan.
Batayi zaman minti ashirin ba abokan ango suka shigo tare da ango, sai zolayarsa
suke, anyi siyen baki da wasu abubuwa da al'ada ta tanada sannan suka yi musu
addu'ar zama lafiya.
Har gurin ƙofa Hilal ya raka abokansa, yayi ma ƴan'uwan amarya da wasu daga
abokanta sallama sannan ya rufe ƙofar.

A maimakon ya koma ɗakin Kalsoom, sai ya nufi ɗakin Rashida dan duba halin da take
ciki.
Zaune ya tararda ita ƙasan carpet tana wani irin kuka kamar ranta ze cire, wata
cousin ɗinta na kusa da ita tana bata haƙuri.

“Habiba ɗan bamu waje”

Ya ƙarasa faɗar yayinda yake zaunawa kusa da ita, janta yayi izuwa ƙirjinsa ya
rumgume ta sosai.

“Shiiiiiiiii. Wannan hawayen ban ga dalilin zubar da su ba Ammyn Rafiq, kin san ba
ɗan bana son ki bane yasa nayi aure sai dan sauwaƙe miki wasu abubuwan, a maimakon
kiyi farin ciki sai kuma kiyi kuka?”

“Ina son Hilal ina kishin naga wata a tare da kai, zan iya mutuwa Hilal”

Ta faɗa tana ƙara narke masa a jiki. Saman kanta ya shafa ya sumbanci shi sannan
yace

“Allah ya sassauta miki wannan kishin Pyar, I Love You so much amman ina son ki so
abunda nake so”

Kuka tayi sosai har sai da maƙoshinta ya bushe sannan ta sassautama kanta, har kuma
lokacin Hilal na rumgume da ita yana rarrashinta.

“Pyar”

Ta ɗago kai ta kalleshi da kumburarin idanuwanta.

“Karki sa damuwa a ranki kin ji? Mijinki yana son ki matuƙa, kuma baya da niyar
cutar da ke”

Ta ɗaga daga jikinsa.

“Tashi kaje kar na shiga mata haƙƙi”

“Zanje amman sai kin yi min alƙawarin zakiyi bachi!”

“Zan yi”

Babbar rigarsa ya cire, da ita ya gyara mata fuskarta, ya goge majinar data ɓata
mata gaban riga sannan ya kai bakinsa cikin nata yana kiss.
Ya ɗauki lokaci mai tsawo yana kiss ɗinta da shafa wani ɓangare na jikinta, har sai
da ya tabbatar ya kashe mata jiki, sannan ya ɗaga ya kalleta.

“Good night Pyar”

“Good night”

Sai ya sumbaci goshinta.

“Dream me i love you”

Ɗan murmushi ta sakar masa kaɗan. Sannan ta sake shi ya tashi, ya baro mata ɗakin
zuciyarsa cike da zumuɗin zuwa gurin Amaryarshi.

Da sallama ya shiga ɗakin yana murmushi, sai ya zauna kusa da ita ya kai hannu ya
yaye lulluɓin dake kanta.

“Wannan Amaryan bakinta da tsada yake, har ta kasa amsa sallamar angonta”

Hawayen daya gani a fuskarta ya tada hankalinsa. Dan be yi zaton macen data kai
kamar Kalsoom idan anyi mata aure a zamanin nan zatayi kuka ba.

“Wannan hawayen na minene My Queen? Ashe yau ba ranar farincikin mu bace? Ai kamata
yayi mu gode Allah ko?”

Ita kanta bata san hawayen minene take ba, na farincikin yau Allah ya gwada mata
aurenta, ko kuma na yanayin da take ciki na baƙincikin rabuwa da iyayenta.
Matsawa yayi daf da ita sai ya kai tattausan hannunsa ya share mata hawayen, ya
kwantar da ita jikinasa, yasa babban yatsansa da mai bi mata yana mata saƙa a jiki.

“Ranar yau ba ranar kuka bace ranar murna ne, ranace da zaki gode Allah kuma ki
shirya karɓar angonki da kyakkyawar tarba”

Notse kanta tayi cikin ƙirjinsa, jikinta na amsa saƙon da ƴan yatsunsa suke kai
mata. Tana jin wasan ya canja salo sai ta zame jikinta, idonta cike da nauyin
kallonsa.

Murmushi yayi yana wani lumshe ido yana buɗe, sannan ya janyo ledar dake gefensu ya
buɗe ya ɓalle lemun dake cikin kwali ya ɗauko cup ya zuba mata. Duk yadda taso ta
ci da kanta ƙin yarda yayi a dole ta haƙura yayi feeding ɗinta, ba dan tana
jindaɗin yadda yake bata ba, abun ka da wanda be saba ba.

Bayan sun gama, ya riƙa hannun tana mursa lallen dake hannu tare da yaba.

“Amman wanda tayi miki lallen nan ta iya lalle gaskiya, yayi kyau sosai”

Yadda yake taɓa hannun nata yasa tsigar jikinta tashi. Duka hannayensa yasa yana
luddar hannun nata, a ɗan space ɗin dake tsakanin fingers ɗinta yasa one finger
ɗinsa yana mata tafiyar tsusa, sai kallon yanayinta yake, gaba ɗaya idonsa sun koma
kamar ba nashi ba.

Janye hannunta tayi ta miƙe tsaye.

“Bari mu tashi mu yi sallah”

Murmushi yayi ya dantsi bakinsa, sannan ya tashi ya nufi bathroom ɗin.


Tun da sunayi sallah godiya be yarda ya kai hannunshi ya sake taɓa jikinta ba, in
banda kayan bachi daya ciro a closet ya miƙa mata sai shima ya saka nasa. Sannan ya
hau saman gadon ya kwanta ya bata baya, be juyo ba sai asuba.

Bayan sun yi Sallah, ta hau gado ta kwanta, shi kuma ya fita dan duba uwargidansa.
A kitchen yaji motsinta, hakan ba ƙaramin bashi mamaki yayi ba, da sauri ya nufi
kitchen ɗin ba dan zuciyarsa ta yarda da ita ɗince a kitchen ba.

“Wow Pyar me kike yi?”

Ta juyo ta kalleshi da murmushi, fuskarta acan-acan da kwalliya kamar ita ce


amaryar.

“Breakfast nake haɗa muku”

Ya zagaye ƙugunta da hannayensa, zuciyarta cike da jindaɗi.

“Seriously Pyar? Amman gaskiya kin kyau mana, so faɗa min jiya kin yi bachi?”

“Nayi bachi mana, ai nasawa rai na zan iya ne”

“Good girl”

Yaja hancinta, wanda hakan yasa ta dariya.

“Amman ni dai Doc Ina jin tsoro, kar yarinyar nan ta amshe min kai, wasu ba aure
Allah suke ba burinsu kawai su fitar da matar gida su maye gidan da ƴaƴanta”

“No no no, wannan yarinyar ba irinta na auro miki ba, tana da tarbiya fiye da
tunanin ki”

“Allah yasa”

“Amin”

Sai ta ɗago kai ta miƙa masa bakinta sukayi kiss, sannan ya rumgume ta a kafaɗa
kamar wani ƙaramin yaro.
Har ta gama soya dankalin rumgune yake da ita ta baya, sai da ta fara jera kayan
abincin sannan ya sake ta da nufin zuwa ya tashi Kalsoom.

Har lokacin bachi take hankalinta kwance. Da murmushi ya ƙarasa kusa da ita, zanen
bachinta ya fara yayewa, yasa hannunshi ta ƙasan wandon bachinta ya soma shafa
ƙafarta zuwa cinya.

Wani yarrr taji, sai tayi saurin buɗe ido ta tashi tana kallonsa. Murmushi yayi ya
hau saman gadon ya ɗora kansa saman wuyanta.

“Good morning Queen ina fatar kin tashi lafiya?”

Kamin ta amsa ya zira halshensa yana lasar wuyanta, ya kai hannunshi saman
ƙirjinta, ya soma murza breast ɗinta a hankali, lumshe ido tayi zuciyarta cike da
ƙyamar abunda yake mata. Tana jin ya fara ƙoƙarin ɓalle bottom ɗin rigar bachinta
tayi saurin riƙe hannunsa, ta buɗe ido ta tashi.

Sai shima ya miƙe tsaye yana murmushi.

“Je kiyi brush zamu ci abinci”

Bata tace komai sai kawai tayi murmushi, ta nufi bathroom, shi kuma ya fice ya nufi
nashi ɗakin dan wanke bakinsa.
Bayan ta fito ta ɗauki mayafinta na jiya ta rufa a jikinta sannan ta nufi falon. A
lokacin Hilal har ya hallara a dinning yana riƙe da hannun uwar gidansa.
Yadda taji abu ya soki zuciyarta sai taji kamar karta ƙarasa kusa da dinning ɗin,
sai dai tayi ƙarfin halin ƙirƙirar murmushi ta ƙarasa tana gaisawa da Rashida.

Rashida da kanta ta zuba ma Hilal abinci sannan ta zuba ma Kalsoom, sai ta zuba ma
kanta.

“Ina Ezzah?”

Ƙalsoom ta tambaya. Sai Rashida tayi murmushi tace

“Suna bachi around tara da rabi zasu je islamiya, idan na tashe su yanzu zasu dame
mu ne kawai”

Ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin zaunawa, zamanta keda wuya sai hawaye ya gangaro ta
idonta ya wanke mata fuska, da sauri ta tashi.

“Am sorry”

Sai ta nufi ɗakinta. Sai Hilal yayi saurin tashi ya rufa mata baya. A take yanayin
Kalsoon ya canja har ta haɗiye wasu yawu da ƙarfi, ta sauke ajiyar zuciya tana
kallon yadda abincin ya fita ranta.

NAMRA POV.

Tara saura mintuna Namra ta saci jiki, ta nufi gidansu Azeema. Sai da ta kusa
ƙarasa sannan wani tunanin yazo mata.
Sai ta yanke tafiyar ta dawo gida, a lokacin an buɗewa Abban gate zai fita, taji
kunyar ganinsa sosai sai dai sa'arta ɗaya dawowa ne tayi ba fita ba da fita ne da
me zata ce masa?

Lokacin data kawo kusa da shi ya zuƙe gilashin motarsa yana mata wani kallo.

“Daga Ina mike?”

Ta ɗanyi jikiri gurin bashi amsa saboda tunanin ƙaryar da zata masa.

“Az- Azeema ce bata da lafiya shine yaje na dubata”

“Da izinin wa?”

“Anty”

“To kar na sake ganin kin fita ke kaɗai”

Be jira amsar ba ta ya ɗagarda gilashin motarsa, direba ya jashi yayi suka yi gaba.
Ta hanyar kitchen ta biyo ta shigo falo, sai rabon ido take idan wani be ganta ba.
Al-hamdulillah falon ba kowa hakan ya sata jindaɗi, cikin natsuwa ta nufi ɗakin
Anty Amarya.

“Wa'alaikissalam”

Ta amsa sallamar Namra a yayinda ta aje kofin tea dake hannunta saman bedside
drawer.
Kusa da ita Namra ta zauna tana tauna maganar da zata mata.

“Anty kin ga jiya ai Maryam ta bani wasiƙa ko?”


“Uhm”

“Asim ne ya bar min ita wai yazo be same ni ba, shine ya rubuta min number wayarsa,
sai na kira da wayar Maryam, yace min mu haɗu a gefen gidansu Azeema”

Anty Amarya ta girgiza mata kai

“A'a ke yanzu girman ki ne a ganki a ƙofar gidan wa su kina fira? Yazo gidan ku
mana, sai kace wani baƙo”

“Wai shi yana jin ba daɗi idan yazo nan gidan”

“Cinye shi zamuyi? Ai ko yanka namansa ake dole ne yazo nan indai yana son ki”

Shiru Namra tayi tana nazari. Anty Amarya ta mire baki.

“Uhm- Allah dai yasa kina son Asim ɗin nan yana son ki kamar yadda kike son sa”

Murmushi kawai Namra tayi, ta kai hannu ta ɗauki wayar Anty Amarya dake gefenta.

“Bari na kira shi”

Sai ta tashi ta fita. Ɗakinta ta dawo ta sake ɗauko takardar ta saka number ta
kira. Ringing tayi har ta katse be ɗauka ba, sai da ta ƙara kiransa sannan yayi
picking.
Tana yin sallama ya gane ta.

“Namra gani a gurin ban gan ki ba”

“Ina gida Anty tace ba sai dai kazo gida”

“Namra ina jin tsoro, bana son zuwa gidan nan naku kallon wulaƙanci ake min”

“Kazo mana babu koma ma, Hajiya tana part ɗinta, Maryam da Hindatu sun tafi
makaranta, Abbah ma ya fita”

“To gani nan zuwa”

“Gidan ka shigo kaje gurin Garden”

Daga haka ta kashe wayar, ta mayarwa Anty Amarya.

“Anty ga wayarki na gode”

“Ke kin hallaka taki wayar ko?”

Murmushi tayi, ta juya ta fice. Firjin ta buɗe ta ɗauki lemu da kofuna, sannan ta
nufi garden zuciyarta cike da zumuɗin son ganin masoyinta.

A-ƙalla ya ɗauki mintuna goma shabiyar, sannan ya iso, da faɗuwar gaba ya buga
ƙofar gate ɗin. Sai mai gaɗinsu ya buɗe masa yana tambayar wanene.

“Nine ko Namra na ciki?”

“Eh tana ciki”

Mai gadin ya buɗe masa ƙofa, yana mamakin ganinsa.


Gidan ba baƙonsa bane, dan haka be sha wahala ba gurin ɗaukar hanyar da zata
sadashi da garden ɗin. Namra na hango shi ta miƙe tsaye ta rumgume tana murmushi,
ta hannayenta, idonta ya cika da ƙwallah.
Shima murmushin yayi yana kallon yadda ta rame tayi baƙi kamar ba ita ba.

“Namra ashe zan ƙara ganin ki?”

Bata bashi amsa ba sai kawai ta nuna masa kujerar dake facing ɗin nata. Bayan ya
zauna sai ta zauna tana share hawayenta.

“Asim ina ka tafi?”

“Katsina naje gurin wani Ƙanen Mahaifina ina riƙa masa aikin jima da yake yi”

“Haba Asim shi kenan sai ka gudu ka bar ni kana ganin kamin adalci kenan?”

“Namra idan kika aure wani ba niba, mutane zasu min dariya, ban san da wane ido zan
ɗaga kai na kalli mutane ba”

“Matuƙar kace zaka biye ma dariyar mutane ba zaka iya aikata komai ba Asim. Nima
dana biye dariyar mutane da ban yarda na aure ka ba, yanzu ka watsar da karatun ka,
abunda nake da yaƙinin shine zai taimaki rayuwarka”

“Ba karatu ne a gaba ba yanzu, faɗa min da gaske mahaifinki ya yarda muyi aure?”

“Ya yarda shiyasa yace na nemo ka, kuma ina jin ba zai sa mana date da nisa ba”

“Al-hamdulillah Allah mun gode maka, amman Namra kina ganin zaki iya zama da ni?”

“Ba zan iya zama da kai ba na amince zan aure ka? Ya kake wannan maganar kamar ba
Namra ce a gaban ka ba?”

“Ina ganin kamar yanayi na da naki ba ɗaya bane”

“Ba mu da banbanci ai duk mutane ne. Asim Amira ta ɓata”

“Haka naji kuma ni ake zargi da sace ta ko? Kamar yadda aka zarge ni da sace ki”

Ta share hawayenta.

“Waya faɗa maka?”

“Ai abun duniya baya ɓoyuwa Namra, kuma kin san akwai munafukai da yawa a duniyar
nan. Shiyasa na yanke shawarar barin garin gaba ɗaya, ko da mun yi aure a Katsina
zamu zauna tun da ban da gurin aje ki a nan, amman can family house ne akwai ɗakuna
da yawa, sai dai na ƙasa ne”

“Amman Asim kana ganin zaman mu a can zai yiyu? Karatun ka fa?”

“Na riga na yafe karatu Namra. Kuma zaman mua can zai fi, saboda har ga Allah nan
bana da gurin aje ki, kuma kin ga nan idan mun ci za'a gani, idan ba mu ci ba ma
za'a gani, kuma abu kaɗan za a zo gidan ku a faɗa, can kuma babu wanda ya san ki,
kuma kin ga ɗan zuwan nan da nayi, ina kama masa aikin jima nima ina samun nawa,
kin ga ko dashi zamu iya cin abinci kamin Allah yayi mana wata hanyar”

“Amman Asim shi yace zai baka gida a can? Ni dai zan fi jindaɗi mu zauna nan”

A take ya canja fuska.

“Ko be yarda ba ni zan roƙe shi ya bamu gurin zama, kuma ni a tunani na Namra ko a
ciki wuta nace ki zauna zaki iya zama in har kina so na”
“Ina son ka Asim, kuma zan zauna a duk inda ka aje ni, yanzu kaje ka samu magabatan
ka suzo su ga Abba”

Murmushi yayi ya sauke ajiyar zuciya.

“Zan yi haka Inshallahu, na gode sosai”

Ba suyi wata doguwar hira ba suka yi sallama, ko lemun da ta kawo masa be sha ba.
Cikin rashin jindaɗi ta nufi shiga falo, har ta nufi kitchen ta aje lemu na ɗauke
da kalaman da Asim yayi mata. Idan tace ba zata iya zama a can ba zai zargeta, sai
dai har ga Allah bata jin zamanta acan ɗin zai fi.
Bata yarda ta labarta ma Anty Amarya komai ba, sai kawai ta shige ɗakinta tana
shawarta zucuciyarta, da nema musu mafita.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa17.html

🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺

Wattpad @
KHADEEJA CANDY

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

Wannan shafin sadaukarwa ce ga SANAH S MATAZU. Namra da Kalsoom sun ce a gaishe


ki😘

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 17*

KALSOOM POV.

Sun ɗauki dogon lokaci kamin su fito. Ko da suka fito har Kalsoom tayi nisa da cin
abincinta.

“Sorry mun bar ki kina cin abinci ke kaɗai”

Rashida ta faɗa tana ƙoƙarin zama. Kallonta kawai Kalsoom tayi ta cigaba da cin
abincinta. Hilal ya lura da yadda yanayin Kalsoom ya canja hakan yasa ya zauna a
kujerar dake daf da ita ya ɗauki abincin ya mai da agurin.

Sosai da sosai hakan ya sosa ran Rashida, for the first time in history jikin
mijinta yana gugar jikin wata mace. Wasa da riƙayi da abinci ta kasa ci. Hilal ya
lura da yanayinta amman be kulata ba har ya gama cin abinci tare da Rashida. Tashi
Rashida tayi zata kwashe kwanukan sai ya riƙe mata hannu.

“Bar su kawai je ki shirya kan ki zan kwashe kayan, nima na iya aikin ai, amman
kamin nan zauna zamu yi wata magana”

Ba musu ta koma ta zauna. Sai da yaja dogon numfashi sannan yace

“Rashida Kalsoom ina son ku bani aron hankalinku, Ban auri Kalsoom ba dan na
wulaƙanta Rashida, kuma ban auri Kalsoom ba dan bana son Rashida ba, yanzu nauyin
ku duk ya hau kai na, dan haka ina fatar zaku taya ni sauke nauyin da Allah ya ɗora
min, ba wai ku tada min hankaliba, zan fu kowa jindaɗi idan kuka haɗa kanku.

Zan iya zama abun kwatance idan kuka kwantar min da hankali, ba zan iya gane wace
tafi so na ba sai ta sai ta hanyar kwantar min da hankali da kuma kyautatawa. Bana
son wani rashin jituwa ya shiga tsakanin ku, kuma ban da ɗauka anyi ance duk wanda
take ganin ba ayi mata dai-dai ba zata iya magana”

Kalsoom ce ta fara magana bayan ya kai aya.

“Inshallah zaka same me mai biyayyah, ni ɗai indai gefe na inshallah ba za a taɓa
samun matsala ba, kuma ina fatar wasu abubuwan da zanyi a cikin rashin sani Ammyn
Rafiq zata tunatar da ni”

“Inshallah ina fatar nima zaki tunatar da ni Allah ya bamu haƙuri zama da juna, sai
dai sai kin yi haƙuri dasu Ezzah saboda basa jin magana”

Rashida ta faɗa tana mai jin sassauti a zuciyarta.

“Ba komai Ai yara na kowa ne, yaran ki ai nawa ne”

Hilal ya jidaɗin yadda yaga sun ɗan sake da juna, yasan nan gaba komai ze wuce
kishi ne kawai wanda ba a rasa ba.

Bayan sun ɗan yi fira ta tashi ta nufi ɗakinta, Rashida kuma ta nufi ɗakin yaranta,
dan ta tashesu.
Shigar da tayi a ɗakin ya bata damar kallon irin dukiyar da mahaifinta ya zuba
mata, ta jidaɗi matuƙa sai da ta ƙare ma ɗakin kallo sannan ta ɗaga hannu sama tayi
ma Allah godiya. Sannan ta nufi bathroom ɗinta tayi wanka, cikin koriyar atamfa ta
shirya ta tsaɓa ado. Sannan ta ɗauki wayarta ta kira Momy da Daddy ta gaishe su.

Guraren biyu da rabi Salma tazo gidan, aiko Kalsoom kamar ta haɗeye ta, sai duk
taji kamar ta daɗe bata ganta ba.
Ɗakinta ta kaita ta kawo mata abinci da abun sha. Sai da Salma ta ci ta ƙoshi
sannan ta kalli Kalsoom tana dariya tace.

“Komai mai lokaci, yau dai gashi na ci abincin gidan Kalsoom”

Kalsoom tayi dariya. Salma tace

“Ya dai zaman ku babu wani matsala dai ko?”

“Eh toh babu matsala zuwa yanzu, ban sani ba dai ko gaba. Amman a yadda na lura
kamar yana son matarsa da yawa”

Salma ta saki baki.

“Kalsoom kenan ke kin fi son ki auri mijin da zai riƙa wulaƙanta uwargidansa? Irin
wannan mijin ai ba mijin aure bane, idan ya gama da ita akan ki zai yo.
Kuma Hilal ai dole ya so matarsa tun da matarsa ta gina masa sonta a zuciyarsa,
kema ki gina naki mana, yana son matarsa cikin bata bashi lokacinta bata kula da
gidanta a yadda ya dace, me kike tunani idan ke kika masa duk abunda yake so?

Aure ba abun wasa bane Kalsoom sai kin kai zuciyarki nesa, babu ruwanki da sashenta
indai ba har ta kama bane, wani abu da gangan zata yi dan ki gani amman ki riƙa
kauda idonki dan samawa kanki masalaha.
Ban da nuna masa ke maki son matarsa, wallahi komai take miki karki nuna masa baki
son matarsa balle kuma ƴaƴansa, sai dai idan tayi miki wani abun na laifi ki nuna
ɓace ranki ki yi magana dan ƙwatar yancin ki. Karki kuskura zagin matarsa gaban
idonsa, kina ida kina haka ko da ita ta nuna masa bata son ki ita zai riƙe da abun
a zuciya ba ke ba

Kuma ki kama ƴaƴansa ki riƙe kamar naki, babu ruwanki da ƴan anyi ance, ban da
ɗaukar zancen maƙota, ban da biye son zuciya, duk wani kishi da zaki ji ki danneshi
ki sawa ran ki sassauci, ban da faɗin sirrin miji, musamman na al'amarin auratayya.
A duk lokacin daya buƙace ke ki nuna masa kin fisa buƙatarsa, ki sake jikinki ki
yiwa mijinki duk abunda yake so. Ke ai baki da matsala da wannan matar tun da bata
da lokacin kanta ma, yara kuma kullum suna islamiya da boko kin ga ai gidan ma
kusan naki ne ke ɗaya

Ƴan uwansa ki kama ki riƙe ki maida su kamar naki, ki girmama mahaifansa, ki


girmama abokansa, ki tarbi kowa da far'ah idan kina da abun basu ki basu, ki zama
mai yawan alheri, gidan ki ya kasance mai ƙamshi da tsafta, abincin ki ko yaushe a
ready.
Kin ga waɗannan abubuwan da na faɗa miki? Sune mallaka na musamman wanda mu mata
basu san da ita ba, idan kina wannan wata mace ba zata iya gane kan mijinki ba, sai
dai kiji ana ta mallake shi ai baya da magana sai nata”

Kalsoom tayi dariya tana mamakin yadda Salma take jero mata waɗannan bayanan kamar
wata tsohuwar mace.

“Salma.yaushe kika ɗauki wannan karatun?”

“To ai ke sabuwace mu kuwa mun tsufa a lamarin, ke bari na baki wani sirrin, idan
zaki bawa mijinki abinci ki laɓe a inda ba zai ganki ba ki riƙa karanta masa
Bismillah kafa shirin da tara ko sha tara, ki tofa masa a ruwa ko wani abu kamar
alawa haka ko dabino, a lemu ma zaki iya amman idan kin ƙanƙare, sannan ki karanta
masa Hal'ata alal insanu har zuwa samin'an basira, sai maimaita sami'an basira sau
bakwai ki tofa masa a abinci, ki yawaita lalle idan mijinki mai son lalle ne, ko
kuma ki karanta ayatul kursiyo ki tufa masa a ruwa, kuma ko yawaita cin fruits da
tsarki da ruwan ɗumi, ki riƙa masa shagwaɓa dan zama suna son shagwaɓa sosai, hmmm
ƙawata sauran soyayyar ki nemeta gurin Allah kawai, amman sai kin ba labari”

Taɓawa sukayi, Salma ta ɗora

“Ai shiyasa bana da shakku akan mijina, nasan ko aure yayi ba dai wata ta ɗauke
masa hankaƙi ba, sai dai ma ta rasa gane kansa”

Salma ta daɗe tana yi ma Kalsoom lacca har aka kira la'asar, bayan tayi sallah suka
je tare a ɗakin Rashida Kalsoom ta gabatar mata da Salma sannan ta fito, har gurin
gate Kalsoom ta raka ta.

NAMRA POV.

Washe garin ranar da sukayi maganar da Namra, Asim ya sanar mata a wayar Maryam
cewa iyayensa zasu zo ganin Abbah ya saka musu rana. Ita kuma sai ta faɗawa Anty
Amarya tayi masa magana, ya saka musu ranar lahadi.
Ranar lahadin na zuwa suka zo, Abbah yayi musu tarba daidai gwargwado, sai dai
basu ga annurin fuskarsa ba ko kaɗan.
Dubu Hansi yayi musu sadakinta, yasa musu date 23 ga wata mai biwa wanda zai shigo,
su kuma suka tafi akan sai sun yi shawara.

A Ranar Namra kuka tayi kamar zata mutu, sai dai bata yarda ta faɗa ma Anty Amarya
ba, balle Maryam, a ɗayan ɓangaren kuma tana tunanin ƙawarta Amira.
Sai da dare Asim ya kirata a wayar Maryam, a lokacin tana zaune falo sai ta
tashi ta shige ɗakinta, sannan ta amsa wayar.

“Assalamu alaikum”

“Asim ya kake?”

“Lafiya ƙalau Dear, yau dai kin ga kamar mafarki an yanka min sadakin ki”
“Daman inda haƙuri ai komai mai faruwa ne”

“Haka ne Allah ya bani ikon biya”

“Ameen, amman Asim nace kana ganin zaman a can zai yiyu ko dai haya zamu kama”

“Haya kuma? Haba Namra ina naga kuɗin kama haya a yanzu, ni da nake tunanin sadakin
ki da lefe kuma?”

“Ni zan biya kuɗin hayar, kuma zan taimaka maka da kuɗin da zaka haɗa lefe, amman
Asim bana son kabar karatun ka”

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke.

“Amman gaskiya Namra ba zan bari kiyi gaka ba, ni ban aure dan kiyi min haka ba”

“Ban maka hakan dan wani abun ba, sai dan nema maka mutunci da girma”

“Zan yi tunani a kai, amman gaskiya wannan shawarar bata yi ba”

“Kayi tunani Asim, matuƙat Abbah yaga inda zaka aje ni ba zai bari na aure ka ba”

“Allah yayi mana mafita”

“Amin”

Daga haka suka yi sallama. Sai ta tashi ta nufi falo dan mayarwa da Maryam wayarta.
A lokacin ne Anty Amarya tace mata

“Namra wai ya maganar karatun ki? Kin san kwanan ki nawa baki je makaranta ba
kuwa?”

Tsaye tayi cak kamar hoto tana kallon fuskar Anty Amarya.

A waje Asim yayi waya da Namra, ya daɗe a gurin zaune yana nazari sannan ya tashi
ya shiga cikin gida. Aiko Mahaifiyarsa kamar jira take ta hau shi da masifa.

“Ai sai kaje ka samu kuɗin biyan sadakin kuma, dan babu wanda zai taimaka maka da
komai, tun da kai kacw kaji ka gani”

Zaunawa yayi saman tabarma cike da damuwa.

“Haba Mama ai maimakon ki ƙarfafan gwuiwa sai kuma ki riƙa min faɗa?”

“Na ƙarfafa maka gwuiwa kaje ka aure wannan yarinyar? Ai ba da ni ba Wallahi,


yarinya data gudu ta bi wani saurayi yayi mata abunda zai yi, mijin da zai aureta
ma cewa yayi ya fasa sai aka ɗauko aka ƙaƙaba maka, kai kuma da kake sakare kace
kaji ka gani, gudun jin kunyar mutane ko? Waya sani ma ko wani abun aka ganta da
shi”

“Subhanallahi irin wannan kalaman sam basu kamata ba Mama”

Tsaki tayi ta tashi ta shige ɗakinta, tana cigaba da nanata maganar.


🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

I dedicated this chapter to.


Angel
M Mimi
Mum Khady
Sarwee
Khady U Dome
Husaina daughter.
And all members of ZAGON K'ASA FAN'S grp. And KHADEEJA CANDY NOVELS 💖

I changed my phone so if your massage are still pending please PC me now.

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 18*

Kalsoom na fita tare da Salma, Rashida taja tsaki.

“Aifa an auro min iyani, ina ruwana da wata ƙawarki can”

Wayarta ta jawo ta danna ta nemu number Asmee ta danna mata kira.

“Ke ƴar gari ya akayi?”

“Toh gani nan dai, kin san yau ba'a zuwa aiki”

“Haka ne nima ina gida ai. Ina Amaryarki ance jiya an kawo miki amarya?”

“Tana nan yanzu ta fita raƙa ƙawarta”

“Hmm wai kisan yarinyar nan da taurin kai, babu irin zugar da da ban mata ba amman
Wallahi ta tsaya kai da fata ita sai ta aure shi”

“Ai dole ta aure shi mana, babu mace da zata ga Hilal bata so shi ba balle har shi
da kan sa yace yana son ta, kuma ance fa kwantai tayi babu mijin aure ba dole ta
laƙe masa ba”

“Aiko dai ce ni na faɗa miki gurin aikin mu ɗaya da ita Wallahi, ƙanenta duk sun yi
aure ita tana nan, Allah ya agaje ki dai kar tace zata fitar dake a gidan”

“Idan kuma bata fitar da ni ba ta karɓe min gida ba, dan naga yana ta wani rawar
kai akanta”

“Ke ma ai kin sani duk mace data daɗe bata yi aure ba idan zata shiga a gidan ai
sai ta shirya, kuma irin su ne suke ƙwace maza su tiyar da matar gida”

“Shiyasa fa nake tsoron auren nan na zamani”

“To ai laifin ki ne Rashida, shi kenan dan kana aiki sai miji yaje ya ɗauko maka
wata banza da hujjar wai baka bashi lokacin ka! Ai wannan zancen banza ne, ni ɓa
gani ina aikin ba amman mijina shiru kake ji ko ƙorafi bayayi”

Rashida tayi dariya tana mire baki

“Asmee kenan ke ai mijin ki be isa yace ze ƙara aure ba, wanda ko kallo mata ba
yayi. Ke nima fa da nake matar abokinsa, sai da wani ƙwaƙƙwaran dalili yake min
magana balle kuma har ya shiga office ɗina”

Asmee tayi dariyar jindaɗi, daman haka take son ji, kuma Rashida ta kan yawaita
faɗa mata mijinta babu ruwanshi da mata, kasancewar gurin su ɗaya da Rashida.

“Kema ai idan kin tashi sai ki zo aka kama miki kan shi, wallahi ba dai wata ta
gane kan gidan ki ba, dan kin san ba'a shedun Namiji anjima kaɗan zai canja miki,
ballantana kin ga wannan Uwar tasa ba son ki take ba”

“Toh yanzu ya zamu yi kin san ai ba nida lokacin zama ma balle na fita”

“Ba ki da matsala da wannan, indai kin yarda kuɗin ki kawai zaki bada, ba sai kinje
ba”

“Haka zai yi, amman ta san muna abota dake ?”

“Bata sani ba ai ban taɓa nuna mata ba, ce mata nayi mijinta ne abokin mijina kuma
ni maƙociyarki ce, na nuna mata sam bana ma shiri dake”

“Hakan yayi kyau sai kiyi ta bugun cikinta”

Ƙyaƙyalewa Asmee tayi da dariya. Rashida tace

“Kin ga suna min warning wai kuɗina ya ƙare, ki shigo gobe ganin amaryar mu daman
gobe monday bana gida”

“Toh Allah ya kai mu, na gode sai anjima”

Tana kashe wayar ta tashi ta nufi kitchen daɓ ɗora girkin rana.

DOC. HILAL POV

Tun da ya fita be dawo ba sai dare, da ledodi ya shigo gidan, sai da ya fara biyawa
part ɗin Rashida ya kai mata nata, sannan ya shiga ɗakin Kalsoom. A bakin ƙofa ya
tsaya ya ware mata hannyensa yana murmushi.

“Taso ki tarbe ni mana”

“Ka ƙaraso dai kawai tun da ka riga ka shigo”

Ta ƙarasa da murmushi tana mai sauke idonta daga gareshi. Ba dan yaso ba ya ƙarasa
kusa da ita ya zauna, ya aje ledar gefe ya jata jikinsa ya rumgume yana shinshinar
ƙamshin turarenta yana wani lumshe ido.

“Wannan ƙamshin na nawa ne?”

Hannunsa ya saka mata a riga, unƙurin tashi tayi sai yayi saurin walƙatowa ya
danne ta, a kunne ya raɗa mata.

“Kin fa san daren yau nawa ne, jiya ma dan nasan kin gaji ne shiyasa na ƙyale ki”

Dariya tayi, cikin dabara ta zame jikinta daga nashi ta tashi tana faɗin.

“Bari na haɗa maka ruwan wanka”

Kai kawai ya ɗaga mata ya bi bayanta da kallo a zuciyarsa yana ayyana lalai yau sai
ya shiga gonarsa.
Fita tayi daga ɗakinta ta shiga ɗakinsa ta haɗa masa ruwan wanka, sannan ta fito ta
dawo ɗakinta ta same shi still yadda ta bar shi.

“Ga ruwan can na haɗa maka”

Kwantawa yayi saman gadon, yana wani nuna jikinsa ya mutu.

“Ni da zaki taimaka min ki ɗauke ni ki kai ni bathroom ɗin kiyi min wanka da na
gode Wallahi”

Dariya ta suɓuce mata, sai tayi ƙoƙarin rufe bakinta.

“Na ɗauke ka kuma?”

“Yes wannan ɗan jikin da kike gani ba wani nauyi da ni ba, kina ɗagawa zaki ji nayi
sama suuuu”

Kai ta girgiza still tana murmushi.

“Baka tashi wanka ba, bari na ɗauko maka abinci”

“Wait...”

Sai ta tsaya, har ya taso ya ƙaraso kusa da ita ta yadda zasu iya shaƙar numfashin
junansu, ya kama hannayenta, yana kallon tsakiyar idonta yace

“Kalsoom I love you with all my heart, ina fatar auren ki ya zame min alheri kuma
farinciki”

“Inshallah”

Ta faɗa tana kawar da fuskarta daga kiss ɗin da yake ƙoƙarin aika mata.
Hancinsa ya goga saman nata yana murmushi mai sauti.

“Wannan kunyar ta ki tana burge ni My Queen, shi yake nuna min lallai ke mace ce”

Ya tsunsa yasa cikin nata, sai ta zame jikinta tana dariya.

“Ruwanka yana hucewa”

Cikin sauri ya janyota, ya walƙato da ita cikinsa, ya riƙe ƙugunta kanshi saman
wuyanta, ya tura ta.

“Aya muje ki taya ni”

Ƙofar ɗakinta ta riƙe suka riƙa ja-in-ja, shi yana son ta bishi ɗakinshi, ita kuma
tana jin kunya, taya zata iya taya shi wanka, daga kawo ta jiya-jiya. Ganin ta kafe
masa yasa yace

“Kema kije kiyi wanka yanzu, or else na taya ki idan na fito”

“Nayi wanka fa tun ɗazu”

“Wannan be min ba, a sake wani”

Kai ta ɗaga masa. Sannan ya saketa ya nufi ɗakinsa.


Wanka yayi ya feshe jikinsa da turare ya saka kayan bachi, sannan ya fito falo ya
kashe kayan kallo ya nufi ɗakinta.

Zaune ya tararda ita tana cin naman daya shigo da shigo dashi.
“Kai....!”

Ba shiri ta zabura tana masa kallon tsoro. Ya ƙarasa shiga ɗakin.

“Waya ce ki min nama?”

“Ba ni na siyo ma ba?”

“Dana kawo na aje cewa nayi gashi na siyo miki? Aiko dai yau sai kin biya ni”

Dariya tayi ta ƙara ɗaukar wata ciɓyar kazar ta kai baki.

“Anƙi a biya ka ɗin sai kace wani yaro”

Kusa da ita ya zauna ya buɗe mata bakinshi.

“Toh ɗan sammin na ci, amman fa sai kin biya ni gaskiya”

Ledar kazar ta tura masa, sai ya girgiza mata kai

“Na bakin ki zaki ba ni”

Sai tayi saurin haɗewa tana zare ido. Fuskar shanu yayi ya riƙa kunnenta ya murɗa
har sai da tayi ƴar ƙara

“Oh ouch that hurt”

“To dan nace ki sammin shine zaki cinye?”

“Ɗauko min abinci ne na ci, ba zan ma ci kazar ba”

Bayan sun gama cin abincin, sukayi shirin kwanciya, sai ya rigata hawa saman gadon
ya kwanta yana kallon yadda take ƙoƙarin canja kayan jikinta zuwa na bachi. Ita
kuma duk ta tsargu ganin yadda ya sakar mata, tasan jira yake tayi kuskuren saki
wani ɓangare na jikinta ta kallah, hakan yasa ta nufi bathroom, sai kawai ta ji an
riƙe ta.

“Wallahi ba zaki je bathroom saboda canja kaya ba, ni dodon ki ne hala?”

“To ka sakar min ido kana ta kallo na”

“An kalle ki, ke ya kika yi kika ga ina kallon ki?”

Ta ɓata rai kamar zata masa kuka

“Haba Doc”

“Haba Mrs Doc”

Zata ƙara magana, ya saka mata yatsunsa biyu na dama cikin baki immediately ya soma
wasa da halshenta, ɗayan hannunsa kuma a jikinta yana murza fatarta. Ba yadda ta
iya daman tasan ƙarshen wasan kenan, a dole ta lumshe ido yana karɓar saƙwannin da
yake aika mata.

Da haka yayi nasarar kwantar da ita saman gado, ya ƙarasa cire mata kayan, sai ga
komai nata bayyane, wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da haɗe yawun, ya shiga
aikama mata da saƙwannin cikin salo na musamman. A take jikinta ya mutu sai dai duk
abunda yake mata jikinta rawa yake abun ka da wace bata saba ba, daker ta iya buɗe
idonta karaf ta sauke su cikin nasa, yadda taga launin idonsa ya riƙiɗe yasa
gabanta faɗuwa, gashi kuma ta ganshi a yanayin da take ganin be kamata ta kalle shi
a haka ba, sai tayi saurin maida idon nata ta kulle gam.
Hakan ya bashi damar riƙe kanta yana karanto addu'ar da Annabi ya koyar
da mu kamin sexual intercourse.

“‫ َوَجِّنِب الَّشْيَطاَن َما َرَزْقـَتَنا‬،‫ الَّلُهَّم َجِّنْبَنا الَّشْيَطاَن‬،‫“ِبْسِمالَّلِه‬

Bismillaah. Allaahumma jannibnash-Shaytaana, wa jannibish-Shaytaana maa razaqtanaa”

*** *** ***

Tun da asuba ya tashi ya haɗa ruwan wanka yayi sannan ya tashe ta, duk yadda yaso
ya taimaka mata tayi wanka ƙin yarda tayi a dole ya ƙyaleta tayi da kanta sai
zolayarta yake, wai jiya duk ta hajiyar da shi.
Ita kam kunyarsa ma take ji, ta gasa kanta sosai gurin wanka saboda yadda ƙasanta
yake mata zafi da raɗaɗi, a tare suka yi sallah. Ita kam bata tsaya komai ba suna
sallamewa ta hau gado sai bachi.
Bata farka ba sai tara har da tabi, a lokacin Hilal har ya gama haɗa musu breakfast
dan yau Rashida da wuri ta fita ko gaisa bata bari suka yi ba, shi ya kai yara
makaranta, sannan ya shigo ɗakin ya tashe ta.

NAMRA POV.

Ta daɗe a gurin tsaye tana tunanin abunda zata cewa Anty Amarya, ita kanta tana
buƙatar karatun dan tana da yaƙinin zai taimaki rayuwarta, sai dai tana ganin hakan
kamar ba me yiyu bane, tun da Asim yana nuna mata alamun baya son ta cigaba da
karatun, gashi ma yace ba nan zasu zauna ba.

“Anty naga zan yi aure shiyasa na bar zancen karatu”

Duk kallonta suka yi suna mamakin irin sakarcin da take ƙoƙarin aikatawa.

“Namra kenan, ai karatu baya hana aure kuma aure baya hana karatu, karki yarda ki
bar karatun ki”

“Anty yace ba a nan zamu zauna ba, a katsina zamu zauna”

“Katsina kuma?”

Maryam ta amsa, sai ta taso ta dawo kusa da Namta ta zauna.

“Dan Allah, karki yi haka Anty Namra taya zaki bishi zuwa katsina? Kibar karatun
ki? Idan shi be san darajar nashi karatun ba ke ya kamata ace kin san naki, yanzu
kina son ki zubar da duk shekarun da kikayi ki zubar da su?”

Anty Amarya ta riƙa hannunta.

“Namra karki yi ma kanki zaɓen tumun dare dan Allah, kar kije kiyi abunda zaki yi
nadama”

Fashewa tayi da kuka

“Anty idan nace na zan aure shi zai ce naci amanarsa kuma kin ga yanzu har an yanka
masa sadaki taya zan ce na fasa? Bayan kuma Abbah ya bani dama, baya da gurin aje
ni a nan sai can, ɗan zuwan nan yayi ya samu aiki da zai iya taimakawa kansa da
shi”
Anty Amarya ta dafe kanta tana sauke ajiyar zuciya. Zuwa can ta ɗago ta kalli Namra

“Ki masa magana idan ya aminta zan baku gidan da zaku zauna a nan garin, in yaso
sai ku cigaba da karatun ku muga abunda Allah ze yi kuma”

Namra ta jidaɗin abunda Anty take ƙoƙarin mata, cikin murna ta share hawayenta tana
mata godiya.

“Na gode sosai Anty, zan masa magana anjima inshallah”

“Ba komai Allah ya sanya alheri”

Daga haka Anty Amarya ta tashi ta nufi ɗakinta. Sai da ta shige sannan Namra ta
kalli Maryam tace

“Dan Allah Maryam ina son na nemi taimakon ki”

“Na me?”

“Abu nake son ki ara min dan Allah”

“Minene faɗa min mana, kina abu kamar mai jin kunya na”

Sai da ta sosa gefen wuyanta, cikin jin nauyi da kunya tace

“Kuɗi naƙe son ki ara min, zan yi wani abu ne, kuma kuɗin da yake account ɗina be
wuce dubu ɗari takwas ba”

“Kamar nawa kike so?”

“Zan samu 1.5 million?”

“Zaki samu kan, ai kin san budurwar Sadiq ba za'a rasa kuɗi a account ɗin ta ba,
kullum Sadiq samin kuɗi yake min Wallahi”

Namra ta harareta

“Dan kuma nace ki ara min kuɗi ai ban ce ki min gori ba, muma na mu lokacin yana
zuwa ”

Dariya Maryam tayi ta kai ma Namra dudu a baya.

“Dole nayi miki dariya mana, duk manyan garin nan wasu-wasu ne kawai basu nemi
aurenki ba, amman kika ƙi kula kowa ke sai Asim, Allah yasa dai ba auren jari zai
yi dake ba”

“Dan Allah ki daina zargin Asim mana haba, ni dai kiyi min transfer kuɗin gobe”

Tashi tayi ta bar mata falon cikin jin zafin furucin Maryam.

*** *** ***

Sai da aka kwana biyu sannan Asim ya samu damar zuwa gurin Namra, duk kuwa da
damuwarsa da take da waya, sai yace mata wai neman kuɗi yake.
Guraren takwas da rabi na dare ya shigo gidan, bata ɗauki lokaci ba ta fito cikin
hijabi. Sai da suka gaisa sannan ta koro masa da bayanin da gidan da Anty Amarya
tace zata basu su zauna.
A maimakon ta ga jindaɗi a fuskarsa sai kawai ta ga ya canja fuska kamar ransa be
so ba.

“Har yanzu ƴan gidan ku basu yarda dani ba Namra, har yanzu basa son aure na dake,
a tunani zaki iya zama a duk inda zan aje ki, kwata-kwata bana da ra'ayin zama
garin nan, a can nake da sana'ah”

“Idan mun zauna a nan zamu iya cigaba da karatun mu, kuma a nan ɗin ma ba zaka rasa
sana'ar yi ba”

Miƙewa yayi tsaye irin ya fusata ɗin nan sosai.

“Ba zan zauna a nan ba, Katsina nake son zama, idan kuma baki da ra'ayin aure na
kawai ki faɗa min”

Ita miƙewa tayi tsaye tana girgiza masa kai

“Abun be kai ga haka ba Asim, magana ce ta fahimtar juna, bana nufin ƙin aurenka ko
kaɗan a cikin rai na”

Takardar dake hannunta ta miƙa masa tare da zinarin da Abbah ya bata ranar da aka
musu walima.

“Kaje ka cire wannan kuɗin miliyan biyu ne da dubu ɗari uku, nasan ze isa kayi
komai, na mai ƙaramin ƙarfi, ba sai kayi lefe mai yawa ba kala ashirin ma ya isa
amman kasa me ɗan tsada dan Allah”

Kawar da kai yayi yaƙi karɓar kuɗin.

“Ni bana buƙatar wannan kuɗin Namra”

“Idan baka amsa ba kana da wata mafitar ne? Wallahi ba zan faɗawa kowa kai na ba
ba, dan Allah ka karɓa Asim”

Sai da tayi ta masa magajiya har da kukanta sannan ya karɓa. A fuska yake nuna mata
baya son karɓa amman a ransa farinciki ne fess shi da be taɓa mallakar dubu ɗari
biyar nasa na kansa ba yau gashi ta miƙa masa million biyu har da wani abu.

Bayan sun yi sallama ta samu Anty Amarya a ɗakinta ta faɗa mata yadda suka yi da
Asim, akan ƙin amincewar da yayi na zama garin, sai ta nuna mata wai har ƙanen
Babansa ya bashi gida a can, kuma sana'ar da yake acan mai ƙarfi ce wai a ƙarƙashin
kamfanin Dangote ya samu suka ɗauke shi.
Bayan Allah ya kyauta babu abunda Anty Amarya tace mata, sai ta taso jiki ba ƙwari
ta dawo ɗakinta, zuciyarta a cunkushe, tunaninta a kulle, ya rasa abunda yake mata
daɗi har wani jiri take jin yana ɗaukarta.

_____________________________________

WHO CAN'T WAIT FOR THE NEXT CHAPTER?


COMMENT LINE BY LINE!
LOVE YOU ALL FISABILLIAH 💖💖💖
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa19.html

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 19*

Baki har kunne Asim ya isa gida da kuɗin, tun daga yanayin sallamarsa Mama ta gani
yana cikin farinciki. A ƙuryar ɗaki ya same ta tana zaune saman sallaya ya zauna
kusa da ita yana murmushi.

Wani kallo tayi masa ta ɗauke kai, dan ita yanzu wani haushi ma yake bata ji take
kamar tayi ta dukansa. Takardar kuɗin dake aljihunsa ya ciro ya aje mata gaban
sallaya tare da zinarin da Namra ta bashi.
Ba a ɓoye zinari yake ba, ko yanzu ka tashi daga bachi aka nuna maka shi zaka iya
gane shi, musamman irin wannan na Namra da aka siya daga Dubai. Gabanta ya faɗi,
sai ta kalli sarƙar ta kalleshi kusan sau huɗu sannan ta ce

“Ina ka samo wannan sarƙar Ibrahim?”

Da dariya ya amsa mata

“Nawa ne”

“Na ka? Sata ka fara ne? Kamar fa zinari nake gani”

“Ba kama bace zinari ne, wannan kuma takardar kuɗi ce na miliyan biyu da dubu ɗari
uku”

Ta daki ƙirji ta da ƙarfi.

“Miliyan biyu Ibrahim? Ina ka samo wannan kuɗi?”

Yanayin yadda tayi masa tambayar da ƙarfi, yasa ƙanensa shigowa ɗakin da gudu suna
tambayar miya faru.

“Kuɗi na samo mana miliyan biyu da dubu ɗari uku, ga kuma sarƙar zinari”

Ƙanensa ya zauna kusa da shi da mugun mamaki.

“Ya Asim taya ka ɗauko?”

“Ba ɗaukowa nayi ba, Namra ta bani tace nayi hidima da su”

Duk tsalle suka saka suna murnar Yayansu ya samo kuɗi, sai Mama tayi saurin riƙe so

“Dan Allah ku rufa mana asiri, kar aji a dirar mana cikin daren nan”

Sai da suka natsu sannan ta kalli Asim

“Da gaske ita ta baka Ibrahim?”

“Wallahi ita ta bani yanzu nan, sai da ma nayi kamar ba zan karɓa ba, sannan na
karɓa kuma tace ba zata faɗawa kowa ba”

Hannu Mama ta ɗaga sama.

“Al-hamdulillah Allah mun gode maka”


Ƙanensa yayi dariya yana faɗin

“Mama ke da baki son ta”

“Ai suma ba dan Allah zasu aura masa ita ba, kai kana ganin masu kuɗi kamar Alhaji
Usman zai yarda Ƴarsa tayi aure irin gidan nan idan ba da wani dalilin ba”

Asim ya sauke ajiyar zuciya kana yace

“Wallahi haka kowa ke faɗa, ni kwata-kwata ma ta fitar min a rai, kawai dai zan
aure ta saboda na fita kunyar masu ganin kamar ɓa zata iya auren mutun iri na ba”

Mama ta mere baki

“Wallahi ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba, da abun nan be faru ba ba zasu taɓa
yarda kmsu barta ta aure ka ba, Amman wannan shi ake cewa gobarar ti-ti ko ba komai
dole dai a kira ka da surukin Alhaji Usman kuma ko yaƙi ko ya so dole ne ya samo
maka wata hanyar, kuma Allah kaɗai yasan ribar da zaka ci akan wannan auren”

“Haka abokaina ke faɗa, wai wata hanyar ce Allah yayi min”

“Sosai tun dai baka ci amanarta ita ta nemi ta ci taka ai dole Allah ya saka maka”

“Yanzu wannan kuɗin tace min aje a haɗa lefe dasu kuma da su zan kama gidan hayan
da zamu zauna a katsina”

“Amman Ibrahim zaman ka a nan be fi ba? Karatun ka fa?”

“Can ɗin zai fi Mama, kin ga zan samu sana'ah mai ƙwari, kuma ƴan'uwanta basa zasu
sa mana ido a zamantakewar mu ba, idan muna da shi aci idan babu a haƙura, babu
wanda yasan mun ci ko ba mu ci ba”

“Haka ne, sana'ah ma yafi, kuma nan kan sai sun sa maka ido har dai wata yarinya na
nan marar mutunci kai yarinyar nan bata da kunya kaga yadda ta riga min fitsara sai
da ta tara min jama'ah a gida kamar nayi sata! A nan ma saurin kashe auren zasu yi”

“Ai Maryam bata da mutunci ni kaina ina haƙe da ita Wallahi”

Ƙanwarsa ta risino.

“Amman Ya zaka gyara mana gidan nan ko?”

“Gyara gida ai dole ne yanzu kan, bari dai na ciro kuɗin kawai komai ma za'ayi da
yardar Allah”

Duk tsalle suka hau yi. Mama na musu dariya zuciyarta ta cike da farinciki.

*** *** ***

Shi da kansa yasa ta faɗawa Abbah cewar ƴan'uwan babansa zasu zo su kawo sadaki da
aka yanka tare da lefe.
Sai da Abbah ya sake sa musu rana sannan Anty Amarya ta faɗaata ita kuma ta faɗa
masa.
Da daren ranar ne Aisha take faɗawa Anty Amarya irin maganganun da ake tayi a
makarantar ta islamiya.

Namra na zaune parlour tana jinsu, har suka yi maganganunsu suka gama bata ce uffan
ba, shiru kawai take tana saurarensu ƙwaƙwalwarta na juyawa.
“Amman gaskiya Anty Namra karki bar karatun ki, idan har ba zai iya bari ki ƙare
makarantar ba kawai ya haƙura da auren ki, ai ba akanki aka fara cin amanar ba,
kuma wallahi duk mai maka son gaskiya dole ne yaso cigaban ka, amman gani nake
kamar cin amanarki kawai zai yi”

Maganar Hindatu ce ta ɗago da hankalin Namra har tasa ta kalleta, sai dai bata iya
tace musu komai ba ban da ruwan hawaye daya fito daga idonta.
Maryam ta tsire baki

“Ke dai kika sani, tun da baki da ra'ayin kan ki sai na Miji, kuma wallahi kina daf
da yin nadama dan duk mace da bata da ra'ayin kanta wahala tana tare da ita, ina
tunanin wani abu ne ya ƙire kuma sauran kaɗan ya faɗa miki, ko kuma a ɗaga auren
har sai kin ƙarasa karatun ki”

Hannu Namra tasa ta share hawayenta ta tashi jiki ba ƙwari ta nufi ɗakinta tana
wata tafiya kamar marar lakka.
Sai a lokacin Anty Amarya ta kalli Maryam tace

“Kar na sake jin kun mata wata magana akan auren nan, kuyi mata fatar alheri kawai,
wannan maganganun ba zai haifar mata da komai ba sai baƙinciki, idan kuna mata
wannan maganar damuwa zata mata yawa.

Gani nake yi abun kamar zai taɓa ƙwaƙwalwarta, dan Allah karku sake mata magana
nan, ita kan ta a yanzu bata iya banbance fari da baƙi, bata daɗe da fita lamarin
Uzair yanzu kuma ta faɗo wannan, ko wane ɗan'adam baya wuce ƙaddararsa, no matter
how you try baka iya tsallake ƙaddararka,
Kuma ba musan alherin da yake cikin wannan auren ba”

Maryam ta tsire baki.

“Wallahi babu wani alheri a ciki, daga gani ma amanarta zai ci shiyasa yake son
yaje can nesa da ita, kuma ya hanata karatun ta tun da shi be san muhimmancin
karatun ba”

“Babu alheri a ciki kin san gaibu ne? Idan ma amanarta zai ci ai ita ba yarinya ba
ce, idan bata iya karatun duniya ba ai sai duniyar ta karantar da ita, ai kowa ya
ƙona rumbunsa, ya san inda toka ke kuɗi”

Daga haka Anty Amarya ta tashi ta nufi ɗakin Namra, zaune ta tararda ita tana aikin
kuka. Kusa da ita Anty Amarya ta zauna ta jata jikinta tana rarrashinta.

“Ki riƙa sauraren zuciyarki Namra, Allah yasa wannan auren ya zame miki alheri,
kada Allah ya bar ki da kanki Allah ya dafa miki lamarin ki”

Rumgume Anty Amarya Namra tayi sosai tana wani irin kuka mai taɓa zuciya. Anty
Amarya bata san lokacin da nata hawayen suka zubo ba.

*** *** ***

Ranar Assabar suka kawo lefen, tarba ta musamman akayi musu, tun daga kan drinks
har zuwa abubuwan ciye-ciye, Hajiya Barau ta soya musu kaji da wasu abubuwan. Sai
dai wannan karon ba'a tara mutane kamar wacan ba, iya su ƴan gida ne kawai suka
tarbi lefen.

Su basu ga wani abun a'zo a gani ba, a lefen tun da abun masu hannu da shuni idan
ba an saka tufafin dubu ɗari, ɗari biyu ba su ba ƙimarsa suke gani ba. Sai dai Anty
Amarya bata bari sun yi magana a gaban idonta ba, sai dai idan bata nan, a fuska
kuma sai tasa suka nuna mata ai yayi ƙoƙari. Ita kanta tasan yaba mata ne kawai
suke dan su ƙarfafa mata gwuiwa, amman ba dan sun ga darajar kayan ba.
Tun daga ranar da aka kawo mata lefen Namra tayi sallama da abinci, duk yadda aka
tursasata sai tacw bata iya ci, sam bata ma jin sha'awar abincin balle ta ci.
Iyakarta abu mai ruwa, ko kuma tea, gashi ta yi baƙi sosai kamar ba farar mace ba,
ta rame kamar marar lafiya.
Ita kaɗai tasan abunda yake cin ta a zuciya, tana jin son Asim, wani ɓangaren
kuma tana jin kamar ta fasa auren amman babu dama, ta kasa samawa kanta mafita.
Haka take wuni a ɗaki kamar wata marainiya, duk wata hidima da ake na zuwa siyen
kayan aurenta ba da ita ake yinsa ba.

Da dare Maryam ta samu Namra ɗakinta tana nuna mata pictures ɗin gadaje wato
furniture ɗin da za a zuba mata.

“Kin ga wannan miliyan ɗaya da rabi, wannan kuma miliyan ɗaya da ɗari bakwai Abbah
yace ki zaɓi wanda kike so”

Kasa zaɓa tayi, ita sam zuciyarta bata mata daɗi.

“Kawai ki zaɓa min wanda duk kika ga yayi miki”

“Amman Anty zaki yi event ko?”

“ Babu abunda zan yi Maryam wanda ya wuce walima”

Kallonta Maryam tayi kamar tace wani abu sai kuma wani tunanin ya zo mata, sai
kawai tayi shiru ta shiga nuna mata kujeru.
Sai da suka kai ƙarshe sannan Namra ta riƙa hannunta cikin rashin kuzari tace

“Maryam dan Allah kar ku yi fushi da ni dan na aure Asim, ku yi miki kyakkyawar
fahimta dan Allah”

“Babu wanda yake fushi dake, kuma kin yi ma Asim halacci iya halacci Allah yasa kar
ya zamo butulu, ya riƙe ki Amana”

“Amin na gode”

Daga haka Maryam ta tashi ta bar mata ɗakin. Ita kuma ta gincira tana sauke ajiyar
zuciya.

KALSOOM POV.

Yanzu kam ƙofar farinciki ta buɗe mata dai-dai gwargwado bata da wata matsala a
gidan mijinta.
Tun da safe zata tashi ta haɗa yara breakfast, tayi musu shirin makaranta, sannan
ta tashi Doc. Sai dai yanzu kusan wata ɗaya kenan, Rashida babu ruwanta da Kalsoom
duk kuwa da kasancewar yaranta ne take yima hidima, da ranar girkinta da ba girkin
ta ba duk Kalsoom ce take girki, sai dai da dare ne zaka banbance ba ita ke da
girki ba, kasancewar kwana biyu-biyu yake musu.
Doc. Hilal kam ji yake kamar ya ɗauki Kalsoom ya haɗeye, saboda yadda take masa
komai daki-daki a gidansa, yana jindaɗin yadda take tashi tun da asuba tayi aiki,
daman maza basa son raguwar mace. Gashi tana nunawa yaransa so hakan ba ƙaramin
daɗi yake masa ba. Sai dai a ɗayan ɓangaren yadda Rashida taƙi ta sake Kalsoom abun
na sosa masa rai, dan duk wahalar da zatayi da yaran Rashida ba zata iya ce nata
sannu ba, balle na gode, ko kuma ta nuna mata jindaɗinta a kansu.

Yau ma kamar kullum bayan ta gama sallamar yara, sun karya sai ta raka shi bathroom
suka yi wanka tare.
Ita ta shafa mishi mai ta murza masa turare, jaka yazo ya zauna ta saka mishi
tufafi ko kunya. Har ta ɗora masa hula akai bakinta yake kallon.

“Perfect everything clear”

Ta faɗa tana ƙara gyara masa girarsa. Bakinsa ya miƙa mata.

“Na siye wannan lips ɗin”

“Yau ba za'a sai da maka ba”

Lumshe mata ido yayi, ya langaɓar da kai

“Haba Ma'am... Pity me”

Sai taja kumatunsa.

“No Toy”

Miƙewa tayi tsaye. Ganin da gaske ba zata masa kiss ɗin ba yasa yayi hanzarin
fisgota ya jefar saman gado.

“Idan ban samu kiss ba toh zan nemi abunda ya fi kiss ɗin”

Hannu ta ɗaga masa

“Tsaya Wallahi zan baka, amman kiss kawai”

“Naji kiss kawai aya tashi”

Ya faɗa yana nuna mata bakinshi. Kamin ta miƙe tsaye ya buɗe durowa ya ɗauki sweet
candy yasa bakinsa. Riƙe ta yayi gam kamar wanda zata tsire masa sai da ta tsosar
masa bakin da kyau da kyau sannan ya sake ta bayan ya mayar mata da sweet ɗin cikin
bakinta.
Sai ya zaunar da ita.

“It my turn”

Mai ya ɗauka ya fara shafa mata, sannan ya shafa mata hoda, sai janbaki. Sannan ya
ɗauki underwears ya saka mata, ya ɗora mata da gown, haka ya mundula mata ɗankwali
saman kai sai dariya yake.
Bayan sun gama, ta rako shi har gurin mota, sai da yayi mata side hug sannan ya
shiga motar tana masa addu'ah.

“Allah ya haɗa ka da halak komai ƙanƙantar ta, ya nisanta ka da haram komai


yawanta”

“Amin I Love You Dude”

“I love you more”

Bayan ya wuce ta dawo falon ta ƙarasa gyarasa. Guraren goma da rabi Rafiq ya tashi,
sai tayi masa wanka ta bashi abincin sannan ta ɗauko shi suka dawo falon suka
zauna.
Ƙonƙosa ƙofar data ji anyi ne ya ɗago da ita ɗaga kallon MBC2 da take.

“Waye?”

Daga inda take zaune ta tambaya.


“Nice Amarya”

Jin muryar Asmee yasa ta tashi ta buɗe mata ƙofar fuskarta a sake.

“Amarya gida sai ƙamshi yake”

Ta faɗa bayan ta zauna. Kalsoom tayi dariya

“Daman gidan mace a gidan ƙamshi ne, ya aikin ya kwana biyu?”

“Lafiya ƙalau, kina nan kina fama da rainon yara ko?”

Murmushi Kalsoom tayi.

“Asmee ke nan, ai yara na kowa ne, kuma ƴaƴan Hilal ai ƴaƴana”

Asmee ta wani gyara zama tana tsire baki.

“Ke ni dan Allah raba ni da abun haushi, ke kika zama ni nake miki kishi”

“Asmee kenan nikan na so naga kishiyarki”

Kalsoom ta faɗa tana dariya. Da sauri Asmee ta matsa

“A'a Wallahi mugun abin ki ya biki, ke daman Allah be raba bakin ki da tsaɓo ba,
bari ma na bar miki gidan daman wani haki ne na siya nace bari na sam miki”

Ta faɗa tana fiddo wani baƙin abu a ƴar ƙaramar roba.

“Kin ganshi ɗan matse ne mai kyau Wallahi, sai kin ban labari, nasan ai kayan
amarcin ki sun ƙare yanzu ai”

“Wallahi sun ƙare, duk na kyautar da su ni ba son irin abubuwan nan nake ba, nafi
son masu zaƙi ko kuma ƴan fruits haka, kin san suma suna gyara jiki”

“Amman gaskiya kiyi amfani da wannan dan Wallahi yana da kyau sosai”

“To na gode zan gwada”

Bata daɗe ba ta tashi ta fita, har gurin gate Kalsoom ta rakata, sannan ta dawo
gida.

Tun kamin Asmee ta isa gida ta buga Rashida tana labarta mata cewar saƙonta ya
samu isa yadda ake so. Daga ɗayan ɓangare Rashida tayi murmushi tayi mata godiya
sannan suka yi sallama.

Tana aje wayar ta tsire baki. Mutumen dake zaune saman wata huge chair ya kalle a
ƙasaice yace

“Wacece?”

“Matar ka ce”

Yayi saurin ɗagowa

“Miya kai ta gidan ki? Bayan baki nan?”

“Ai abokiyar zama na nan, gurinta taje”


Ɗan murmushi yayi

“Mata Allah be raba ku da kicihiba”

Dariya tayi ta ɗauki documents ɗin da suke saman teburinsa, ta nufi ƙofa.

“Ki kai min waɗancan documents ɗin a guesthouse”

Ya faɗa yana kallon mazaunanta dake cikin suit.

“Gaskiya yau ba zan samu shiga ba da wuri zan koma gida”

Daf da zata fice ta amsa masa, sannan ta fice.

___________________________________________

Assalamu alaikum Habibaties💖. To all those that are asking about Amira and Uzair
labarinsu zai zo nan gaba, so please wait patiently. And masu cewa kaza ya kamata
ayi ba kaza ba, blah blah blah, yen yen yen, this and that, na gode duka amman
please ku bar tafiyar nan ta tafi a yadda na tsara ta. Ba ku san dalilin da yasa
Yasmeen ta fito a Barrister ba, ba ku san miyasa asiri ya koma kam Amira ba instead
of Uzair, so please judge less.

Na gode Sosai Jazakallahu Khairan 🌺

I Love You All Fisabilliah 😘


https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa20.html

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 20*

Ba'ayi wasu events ba, bayan salalle da wanki a Amarya, sai Walima da akayi ranar
Jumma'ah. Bikin yayi mutane sosai musamman ta ɓangaren Anty, kasancewar Anty Amarya
yanzu ne ta fara aurarwa. Har Ƴaƴan Hajiya Barau da suke nesa sai da suka zo.
Kaɗan daga cikin ƙawayen Namra ne suka samu halartar walimar, kasancewar bata yi
gayyatar mutane ba, wasu ma ta hanyar Maryam suka ji.
A babban masallacin Jumma'ah akayi ɗauren aurenta, manyan mutane da dama sun
tafi ta dalilin Abbah.

Yadda Asim.yake far'ah da nuna jindaɗinsa kamar ya zuba ruwa ƙasa ya sha. Takeaway
na Manyan mutane Abbah yasa aka shirya masa ya rabawa abokansa. Asim kan shimkafa
da miya yasa aka shirya masa a gidan wani abokinsa, sai ya tare da Abokansa a can
bayana ɗaurin auren sukayi liyafar cin abinci.

Namra na zaune ɗakinta tare da wasu cousins ɗinta, Maryam ta shigo da guɗa.

“Ayyyyyyy Yau an ɗaura auren Namra da Asim”

Wani irin faɗuwa gaban Namra yayi, a maimakon tayi murna sai kawai idonta ya cika
da ƙwallah. A take ta soma ganin kamar mafarki take. Farinciki da baƙinciki sai
suka taru suka mata tsaye a guri ɗaya.

Yadda ƴan'uwan nata suka riƙa zolayarta yasa ta fito da kukan nata a fili, su kuma
suka cigaba da zolayarta. Daker wata Gwaggonta ta lallaɓata ta tashi, tayi wanka
lalle ta shirya cikin jar atamfa, mai makeup ta zo ta gyara mata fuskarta.
Sai suka fito da ita harabar gidan inda ake ta kiɗin ƙwarya.
Tsaye tayi a tsakiyar filin riƙe da hannun wata jikar Hajiya, ƴan'uwan Abbah da
Hajiya Barau suka riƙa mata ruwan kuɗi suna cashewa, ƴan'uwan Anty Amarya ma sun
watsa mata kuɗi sosai. Bata daɗe sosai ba a filin aka dawo da ita dan ta canja wasu
kayan, saboda tafiyar da zasu yi, dan tuni motocin da za su ɗauki Amarya zuwa
katsina suka iso.

Lokacin da Gwaggwaninta suka fara mata huɗuba akan zamatakewar aure da haƙuri, sai
ta riƙa kuka kamar ranta zai fita. Tana faɗuwa tana tashi a aka riƙota aka shiga
part ɗin Abbah da ita.

Duk fita suka yi suka barta daga ita sai Abbah, sai Maryam dake riƙe da gefenta
itama tana hawayen rabuwa da ƴar'uwarta.

“Maryam tashi ki bamu guri”

Ya faɗa lokacin daya sauke idonsa kar kam Namra dake aikin kuka. Tashi Maryam tayi
ta fita. Sai Abbah ya tattara duk kan natsuwarsa ya maida kan Namra.

“Haƙiƙa Khadija ke ƴata ce, kuma ina farinciki da Allah ya gwada min yau na aurar
da ke, farinciki ko wane uba ne ya aurarda ƴarsa da ransa kuma ga wanda take so.
Khadija yau igiyar aure ta shiga tsakanin ki da wanda kike so, ina jan kunnenki
akan haƙuri zaman aure, duk abunda yayi miki na daɗi ko akasin hakan kiyi haƙuri ki
zauna da shi a haka, kar wani tsaɓani ya shiga tsakanin ki da mijinki ki kin tunawa
cewa kina da uba! Na ɗaira miki aure da wanda kike so a yau, kuma na sallama masa
ke har abada!

Karki kuskura wanke ƙafarki ki zo gidan nan da sunan yaji ko saki. Nayi miki iya
abunda ya kamata uba yayi ma ƴarsa na abunda al'ada ta tanada, sai dai kiyi haƙuri
ba zan miki gara ba, ba kuma zan ɗora masa kuɗi ba, ke dai yake so kuma ga ki nan
na bashi, Allah yayi miki albarka ya baku zama lafiya”

Tun da Abbah yake maganar kan Namra na ƙasa tana wani irin kuka kamar ranta zai
fita, duk yadda taso ta tausa muryarta tayi ma Abbah magana sai ta kasa saboda
kuka.
Har Abbah ya gaji da sauraren kukanta, ya kira Maryam ta fita da ita. Ko da aka
koma da ita part ɗin Anty Amarya numfashinta har rawa yake. Nan ma barinta akayi
daga ita sai Anty Amarya. Amman Anty Amarya ta kasa mata magana saboda kukan da
take na rabuwa da ƴarta.

Har lokacin da aka bata ya ci ya cinye, Anty Amarya bata iya cewa Namra komai ba,
daga ita har Namra suke. Sai da su Mama Zainab da Hajiya Barau suka shigo zasu fita
da Namra sannan Anty Amarya ta iya furta

“Na yafe miki Namra Allah yayi miki albarka”

Juyowa Namra tayi ta rumgume Anty Amarya iya ƙarfinta. Har Hajiya Barau da Mama
Zainab sai da idonsu ya cika da ƙwallah. Daker suka ɓanɓareta daga jikin Anty
Amarya saboda yadda ta rumgumeta.
Yadda Namra take kuka yasa duk wanda yake falon sai da yayi hawaye. Ƙanen Asim
da wasu ƴan'uwansa suna tsaye gefe suna kallo.
Muta ɗaya suka shiga da Maryam da Mama Zainab da Hajiya Barau. Ɗayar motar kuma
ƴan'uwan Asim suka shiga daman ciki suka zo. Biyun wasu ƴan'uwan Abbah suka shiga,
sai ta su Maryam da Aisha da Hindatu da wasu Cousins ɗin su. Ƙarfe uku da ƴan
mintuna suka kama hanyar Katsina.

KALSOOM POV.

Yanayin yadda Doc. Hilal ya shiga yau, ya bata tsoro, sai dai bata damu sosai ba,
dan tasan haka rayuwa take yau daɗi gobe ba daɗi. Ballantana ma yau ba ɗakinta bane
wata ƙila ma uwargidan tasa ce ta ɓata masa rai.

Sai dai hakan be sa tayi ƙasa a gwuiwa ba, wajen zuwa tayi masa kyakkyawar tarba.
Sai ta aje Rafiq a falo ta tashi ta nufi ɗakinsa, tana faɗaɗa murmushinta.
Kwance ta kararda shi saman gado ya lumshe ido yana, hannunsa ɗaya dafe da kansa.

Kusa da shi ta zauna, ta kai hannunta ta shafi gefen fuskarsa.

“Ya Omri lafiya kake kuwa?”

Shiru be amsa ta kamar ba zai yi murmushi ba, can kuma ya buɗe ido ya kalleta, sam
baya jindaɗin ransa, amman a haka yayi ƙarfin hali ya ƙirƙiro murmushi ya kai hannu
ya shafa bayanta.

“Matar Doc. Yau jina nake sai a hankali Wallahi?”

Duk sai taji babu daɗi, daman tasan ba banza tun da taga ya shigo babu ko sallama,
kuma be kulata ba ya shigo ɗakinsa.

“Wani abun ne yake maka ciwo?”

“No”

Ya sake lumshe ido.

“Kawai bana jindaɗin rai nane, shiyasa na baro office ɗin”

“Ko wani ne ya ɓata maka rai?”

Idonshi a lumshe ya girgiza mata kai.

“No haka kawai Wallahi”

“Toh Allah ya sauwaƙe ammn idan irin hakan ya same ka, ka riƙa karanta Innalillahi
wa'inna ilaihi raji'un, zaka ji sassauci”

Tashi yayi zaune, ya sakar mata ido kamar yau ya fara ganinta, sai kuma yaja ta
jikinsa ya rumgume gam-gam, yana maida numfashi.

________________________________________

Yan Katsina ga Amanar Namra nan mun kawo muku 😢

Anya Hilal lafiya yake kuwa?🤔

#Comment
#Share
#Blogger
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa21.html

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

NOT EDITED ⚠️

*PAGE - 21*

Ana kiran Sallah magariba suka isa Katsina. Kai tsaye suka wuce unguwar Nasarawa.
Sun yi mamakin ganin gidan da aka sauke su da sunan gidan da Namra zata zauna.
Ba dan komai ba sai dan sanin Asim ɗin ba shida halin da zai iya kama hayar irin
wannan gidan balle kuma har ya siye. Daman tun lokacin da aka zo jere an labartawa
Hajiya Barau irin tsarin gidan. Gida ne plate mai kyau da shike-shike, ga farin
fentin daya ƙawata gidan. A can ciki an ware dinning area da kitchen a gefe sai two
bedrooms da babban falo, ga manyan kujerun da Abbah yasa aka zuba mata kamar ƴar
wani shugaban ƙasa, duk bedrooms ɗin an saka mata furniture masu kyau da tsada.
A ƙaramin ɗaki ta tare ita da ƙannenta, su Hajiya kuma suka fito falo sukayi
sallah, bayan sun gama direba ya kawo musu takeaway data aika a siyo musu, sai da
suka ci abinci suka ƙoshi sannan Hajiya Barau ta shiga ɗakin da Namra take tana
mata sallama, wai zata je gidan wata ƴar'uwarta ita da sauran waɗanda suka zo tare,
su Maryam kuma sai idan Ango ya shigo sannan za su je.

Ko da Hajiya Barau ta bar gidan ana kiran sallah I'sha'i. Sai a lokacin Namra ta
tashi ta shirya cikin wasu tufafin duk da kasancewar fuskarta a kumbure, ta koma
babban ɗakin. Tara da rabi ango ya shigo tare da abokansa, ba a wani yi siyen baki
ba, bayan addu'ah da fatan alheri da suka musu. Maryam dai sai ta watsawa abokan
nasa wani mugun kallo take, tana Allah-Allah wani yace yana son ta cikin su tayi
masa wankin babban bargo.

Tare suka fita da abokan angon, ɗayan yana ƙoƙarin magana da Hindatu dan itace mai
ɗan dama a cikin su, sai wata cousin ɗin su Sameera. Lokacin da Namra taji ɗakin
yayi tsit sai sabon kuka ya dawo mata, sai dai wannan karon hawaye ne kawai ba
kamar na ɗazu ba.

Bayan ya rufe ƙofar gidan ya shigo ya rufe ƙofar falo, sannan ya nufi ɗakin da take
da Sallama, bata iya amsa masa ba saboda kukan daya cika zuciyarta, sai shaƙar
majina take tana haɗeye yawu da jimmar dannen kuka daya kasa ɓoyuwa.

Kusa da ita ya zauna, ya yaye mayafinta fuskarsa ɗauke da murmushi.

“Namra kukan me kike kuma? Bayan Allah ya cika mana burin mu”

Ɗagowa tayi ta kalle shi, kamar tace wani abu sai hawaye suka silala daga idonta
zuwa kumatun ta.
Shi kansa baya buƙatar da faɗa masa dalilinta na kuka tun da yasan iyayenta
basa son sa, gashi ya rabo ta da garin su. Shi kan ta ɓangarensa yau take sallah,
tun da ya cika burinsa na aurenta ya fita kunya, ga uban dukiyar da aka zuba masa,
ga kuma wanda yake jira a matsayin gara a kawo masa.

Jin kawai ta yi ya rumgume ta yana rarrashinta.

“Na san ban kyauta miki ba, dana nesanta ki da iyayenki, amman ni a nawa tunanin
hakan shine zai fi mana, Namra a can abubuwa da dama zasu iya faruwa idan muna tare
da iyayenki, amman a nan ba komai zasu ji ba, kuma a nan zamu tabbata ba zaman na
ɗan wani lokaci ne kawai idan muka ga abunda Allah yayi sai mu koma can, kiyi
haƙuri kinji?”
A yanayin da take bata iya magana, sai kawai ta ɗaga masa kai tana sauke ajiyar
zuciya, tasa hannayenta ta rumgumeshi.
Har kusan shaɗaya dare suna zaune a gurin, daker ya lallaɓata ta tashi suka yi
sallah nafila, kazar ma shi kaɗai ya ci ita kan lemu kawai ta sha ta hau gado ta
kwanta. Washe gari guraren takwas na safe ya fita ya siyo musu kayan haɗa tea, ya
shiga kitchen ya dafa ruwan zafi a electric, sannan ya dawo ɗakin ya haɗa ya zuba
mata nata ya zuba nasa. Nan ma tea kawai ta sha bata ci birede ba, tsakanin jiya
zuwa yau ta rame sosai kamar ba ita ba.

Shi kuma be yi matsa mata akan sai ta ci ba, tun da dai ita ba yarinya bace taya
zai yi forced ɗinta akan cin abinci, shi duk ma ta cika sa dan yayi hating kuka for
no reason, ita kanta ta san babu abunda ya tsana kamar kuka. Daman zuciyarsa ta
faɗa masa, dan a rufa mata asiri ne aka yarda aka aura nasa ita, dan yasan babu
dalilin da zai sa Abbah ya yarda ya aureta har ya baro garin da ita ya kuma hanata
karatunta haka kawai ba tare da wani abu ba.

Sai dai hakan be dame shi, tun da ko ba komai ya taka first step of success, tun da
ya auri ƴar masu hannu da shuni, kuma zama da kutuwar uwa dole, a dole dai Abbah ya
kyautata masa tun da ya zama surikinsa.

Tashi yayi ya kwashe kofunan ya kai kitchen, sannan ya dawo kusa da ita ya zauna.
Sai ya kai hannu ya shafa bayanta, dan tana daga kwance ne.

“Namra ko kina buƙatar wani abun ne? Naga baki ci komai ba”

Tashi tayi zaune hawaye cike a idonta, ta riƙa hannunsa tasa cikin nata, ta kalli
ƙwayar idonsa tace

“Asim ka min alƙawarin ba zaka ci amana ta ba, ka min alƙawarin ba zaka taɓa rabuwa
da ni ba, ka min alƙawarin ba zaka wulaƙanta ni ba, ka min alƙawarin zaka zauna da
ni a duk halin da muka samu kan mu”

Gabansa ya faɗi sosai, a take ya ɗauke idonsa ɗ


Daga kallon da take nasa, yaja jikinsa ya rumgume.

“Taya kika wannan maganar kamar baki san waye Asim ba? Namra bakin ki ya daina
furta irin waɗannan kalaman Asim ne naki har abada”

Sallamar su Hajiya Barau da Maryam ne, yasa shu saurin sakinta ya tashi ya fita
yana amsa musu, a falo suka yi karo, sai ya kai har ƙasa yana gaida Hajiya Barau,
ba laifi Maryam ma ta ɗan sakar masa fuska sun gaisa kamar daman can shiri suke.

Ko da suka shiga ɗakin Namra na gyara fuskarta da hoda, sai ta juyo ta kalli Maryam
da murmushi a fuskarta.

“Hajiya Maryam an samu isowa”

“Toh ba dole ba, Hajiya ta sha kai muzo mu kawo miki abinci muyi sallama dake da
wuri zamu koma”

Ta faɗa tana dire kular abinci a gaban Namra. Saman gado Namra ta dawo ta zauna
tana ɗan ɓata fuska.

“Yanzu tafiya za kuyi ku bar ni?”

“Ahaf to ba aure kika zo yi ba”

Cewar Sameera tana mata kallon zolaya. Zata ƙara cewa wani abu Hajiya Barau ta
shigo bakinta ƙumshe da sallama. Duk haɗa baki sukayi gurin amsa mata, Namra ta
saukar da kai tana gaishe ta.

“Lafiya ƙalau, Amarya ya tashin ku?”

“Alhamdulillah, ya gajiya”

“Gajiya ta bi lafiya, muna ta sauri a kawo muku breakfast, sai angon yake ce min ai
kun karya”

“Eh da safe ne ya haɗa mana tea”

“Toh ai yayi kyau”

Juyawa tayi ta koma falo, Sameera ta bita tana nuna mata abu a wayarta. Sai ya rage
daga ita sai Maryam da Aisha. Maryam ta ciro waya a jakarta sabuwa ta miƙawa Namra.

“Gashi inji Anty tace na baki, akwai layi a ciki”

Da murna Namra ta karɓa

“Wayyo Mamana ta kai na”

Cikin zumuɗi ta buɗe kwalin kwayar iPhone 6+ ce golden color yayi kyau sosai.
Rumgume Maryam Namra tayi tana rawa.

Sai kusan azahar sannan su Hindatu da sauran mutanen suka ƙaraso. A lokacin ne
Hajiya ta shigo ɗakin tayi ma Namra jan kunne akan zamantaewar aure da haƙuri, nan
ma kuka Namra tasa mata, bama kamar lokacin da suka fito za su kama hanya. Tayi
kuka sosai kamar ranta zai cire, a take taji kewarsu ta kama ta, sai duk taji kamar
ta bisu. Tana tsaye bakin gate tana kallon motarsu har sai da ta daina hangota
sannan ta dawo cikin gidan da sabon kuka.

Asim kan be dawo ba sai yamma, ya shigo tare da wasu dangin Babansa da suke Bakori,
kallo kan kallo suke sun daga kan gidan zuwa kayan da suke cikin gidan.
Da far'ah Namra ta tarbe su, ta zuba musu abincin da Hajiya ta kawo mata ɗazu,
waina ce da miya sai doya da ƙwai, sannan ta kawo musu ruwa. Sai daf da magariba
suka tafi, ƴar fitar da Asim yayi ya rakasu ya dawo duk tsoro ya kamata tun da bata
saba zama ita kaɗai ba a gida.

Ko da ya dawo tana tsaye bakin ƙofar falon tana jiransa, da murmushi ya riƙa
hannunta, ya lago ɗayan hannunsa a ƙogunta suka koma cikin falon. A tare suka zauna
saman kujera maƙalle da juna

“Aiko.kina da aiki duk kika sakawa ran ki tsoro dan ke kaɗai zaki riƙa rayuwa a
cikin gidan nan ƙara ma tun wuri ki cire tsoro a ranki”

Maganar yake yana kallon ƙirginta, rigar lace ce a jikinta, kuma kalar ɗinkin da
aka mata ya bayyana breast ɗinta. Ita kanta ta lura da yadda yanayinsa ya canja,
hakan yasa ta tashi ta nufi da jimmar shiga ɗaki. Sai yayi sauri riƙe hannunta.

“Ina zaki je?”

“Ɗa... Ɗaki”

“Okay”

Sai ya tashi tsaye yayi mata side hug suka nufi ɗakin tare, har suka isa ɗakin
mazaunanta yake shafawa, tana zaunawa sai ya kwanto mata saman jikin ta yadda
breast ɗinta zasu shafi ƙirjinsa, ya kai ɗayan hannunsa yana shafa ta.

Lumshe ido tayi ta buɗe tana murmushi, sai ta haɗe bakinta da nashi, duk yadda tayi
ƙoƙarin abandoned na ƙin yarda sauri yarda da shi sai ta kasa, saboda yadda ya
kashe mata jiki, ga kuma irin kayan mata data sha tun jiya suke damunta, a take ta
shiga mayar masa da martanin irin saƙon da yake aiko mata.
Basu samu kansu ba sai kusan asuba. Basu yi bachi daya kai minti ashiriba aka
kira sallah asuba, shi ne ya riga ta tashi ya shiga bathroom yayi wanka tsarki
sannan ya zuba wasu ruwan yayi alwala. Sai da ya canja ya saka jallabiya sannan ya
tashe ta dan tayi sallah.

Daker ta unƙura ta tashi zaune, har ta samu ta ɗauki zanenta ta ɗaura sannan ta
tashi tana wata tafiya kamar wanda aka ɓarewa kafafu ta nufi banɗaki.

Shi dai da kallo ya bita zuciyarsa cike da zarge zarge, sam shi be ga alamun
budurci a tare da itaba, jinin da aka ce ana ganin idan anyi sex da virgin shi be
gan shi ba, an faɗa musu wasu har kasa tafiya suke amman ita gashi har ta kai kanta
banɗaki.
Kuma the way da take mayar masa da kiss da yadda take romance ɗinsa ya nuna ta
taɓa sanin wani namiji kamin shi, daman yasan za'a rina, zargin mahaifiyarsa ya
zama gaskiya.

A take wani ƙololon baƙinciki ya taso masa, yana ayyana irin cin amanar da Namra
tayi masa, zuciyarsa na nuna masa tayi masa zagon ƙasa, shi take son ta yaudara.
Har sukayi sallah suka gama be kalli inda take ba, har sai da ta gama
addu'o'inta sannan ta gaishe shi cikin kunya. Duk wani abu da yake ji a zuciyarsa
sai ya dannesa ya ƙirƙiro far'ah da murmushi ya yaɓa a fuskarsa.

“Lafiya ƙalau Amarya, ya gajiyar jiya?”

Tayi saurin sauke kanta, tana mai jin kunya, shi kuma ya watsa mata wani kallo
ƙasa-ƙasa, zuciyarsa na ayyana masa abubuwa ƙala-ƙala.
Tashi yayi ya je ya siyo musu kayan tea, ita kuma ta hau gadon ta kwanta saboda ta
gaji da yawa. Shi ya haɗa musu tea kamar jiya, har yayi ya gama tana bachi abunta.

Bayan ya kawo kayan tea falo wayarsa tayi ringing, ganin number mahaifiyarsa yasa
ta fita daga harabar falo gaba ɗaya, ya nufi can bayan kitchen sannan ya ɗaga
wayar.

“Mama ina kwana”

“Lafiya ƙalau Ibrahim ya gida?”

“Lafiya ƙalau”

“Kina lafiya dai ko?”

“Lafiya ƙalau muke, ina su Amma?”

“Kowa lafiya ƙalau, nace ba a aiko da komai ba ko?”

“Eh kin san ai yau kwana biyu da auren a ɗan jira tukuna kuma ko zasu aiko a nan
gida zasu kawo sai ku aiko mana ko?”

“Eh toh haka ne, kasan dashen da aka shiga ne jiya ta aiko mana”

“A ɗan jira dai Mama na san suna kan hanya”

“Toh Allah ya taimaka, amman dai karka yi wasa da kuɗin nan ana kawo su ka samu
wata sana'ah babba ka riƙa”

“Haka zan yi ai, ko abokaina haka suke cewa”

“Toh Allah ya taimaka, ina Namra ɗin take ne?”

“Bachi take”

“Toh idan ta tashi a gaishe ta”

Daga haka suka yi sallama, sai ya dawo falon ya cigaba da haɗa tea, sannan ya shiga
ya tashe ta.
Sai da tayi brush shima yayi sannan suka dawo falo suka karya. Bayan sun gama ya
kwashe kayan ya kai kitchen, ita kuma ta shiga kiran wayar Anty Amarya suka gaisa.
Kowa dai da ta kira a gida har Hajiya Barau, sannan ta kira Abbah, kira biyu tayi
masa be ɗauka ba saboda sabon layi ne, sai a na uku yayi picking, be wani sake
sosai ba sama sama suka gaisa, sannan ta kashe wayar.

Duk tsawon lokacin data ɗauka tana gaisawa da ƴan'gidan su Asim na kusa da ita yana
lalabenta, tana aje wayar ya shiga saka mata hannu ƙasanta. Sanin abunda yake nufi
da ita yasa ta unƙura ta tana tureshi, cikin yanayin damuwa take masa magana tana
son ya fahimceta

“Asim, not now please, Wallahi na gaji kuma har yanzu zafi nake ji”

Kallonta kawai yayi ba dan yana da niyar fasa abunda yake yi ba, idonsa sun rikiɗe
sun canja sosai, sai wani numfashi yake.
Ita kanta tasan a yanzu ko da wane yare tayi masa magana ba ganewa zai yi ba, a
dole ta ƙyaleshi ya riƙa wasa da ɓangare jikinta, kamin ya jata su koma ɗaki.

Har yayi abunda zai yi gama, be ji ya gamsu ba, ita kuma duk ta ƙosa ya fita ma ya
bata ɗakin, da ita kaɗai tasan irin azabar da take ji. Daker ta samu ya rabu da
ita, ta tashi a wahale tayi wanka dan ta karanta ta gani kuma ta sha ji a wa'azi
ana faɗar cewa ba kyau ka kwanta bachi da janaba a jikinka, ko yaya ne ƙara dai
kayi wankan. Ta gasa jikinta sosai da sosai sannan ta fito kamar da rarrafe ta dawo
bedroom ɗin. Ko tufafi bata tsaya sawa ba ta hau saman gado, sai bachi.

KALSOOM POV.

A cikin ƴan kwanakin nan kwata-kwata ta rasa gane kan mijinta, duk yabi ya birkice
mata kamar ba shi ba, abu kaɗan sai ya hauta da faɗa, ko kuma yayi ta haɗe mata
fuska yana nuna baya son tana zama kusa da shi. Sai dai a ɗayan ɓangaren ta samu
sassauci gurin Rashida yanzu kan zamansu babu laifi tana ɗan sakewa da ita, har ma
tayi mata godiya a wani lokacin.

Yau ta kama weekend Rashida bata da aiki, kuma Doc yau a ɗakinta yake. Sai ta tashi
tun da asuba ta haɗa musu breakfast, sai ta gama shirya komai sannan yaje ta
tasheshi, ta shiga ɗakin Kalsoom ita ta taso ta.

Da gangan Rashida ta ɗauki dinner set mai plantain da kuma mai kifi ta aza gaban
kujerar Kalsoom.
Sannan ta shiga haɗa masa tea dan tuni ya iso gurin yana duba chat ɗinsa na
whatsapp. Har Kalsoom ta iso gurin ta zauna be kalli inda take ba, gaisuwar da tayi
masa ma can ciki ya amsa mata still be kalle shi ba.

Rashida na lure da yanayin Kalsoom da Hilal zuciyarta cike da shauƙi, sai dai a
zahiri sai tayi kamar bata gani ba, ta hidimar haɗa masa tea kawai take.
“Maman Rafiq miƙo masa plantain gata nan a gabanki”

Ta faɗa tana dire masa tea ɗin a gabansa. Ba tare da tunanin komai ba Kalsoom ta
ɗauki kwanon ta dire masa a gabansa. Ta miƙa masa birede, sai a lokacin ya samu
damar aje wayar har ya kalleta, sannan ya miƙa hannu ya karɓa. Yana buɗe kwanon
yaga kifi sai yaja wani dogon tsaki ya kalleta.

“Ace ki miƙo min plantai sai ki bani kifi kifi kika san ina ci ne?”

Bata iya cewa komai ba, sai Rashida ce tayi magana.

“Haba Doc toh ai kwanukan biyu ne bata san wannenen a ciki ba”

Kallonta kawai yayi ya tashi a hasale ya nufi ɗakinsa. Daman haka ya koma mata abu
kaɗan yasa shi zuciya indai ita ce tayi masa abu. Rashida taja wani dogon numfashi
tana kallon Kalsoom da idonta ke ƙasa

“Tashi ki bi mijinki mana, haka halinsa yake sai kin yi haƙuri, nima fama nake da
shi”

Murmushi Kalsoom tayi ta nuna mata kamar ba komai.

“Fushi fa yake da ni, dan nace masa ina buƙatar hutu, shine tun ranar yaƙi ya
sauƙo”

Ta faɗa tare da tashi ta nufi ɗakin nasa. Hakan da tace ya ɓata ran Rashida kuma ya
dagula mata lissafi.
Kwance ta tarrada da shi ya lumshe ido yana dafe da kai.

“Doc...”

Buɗe ido yayi ya kalleta, sai ya tashi zaune ya zaunar da ita.

“Sorry for what i did earlier, i just that... ”

Sai kuma yayi shiru. Hannunsa ta riƙa tasa yatsunta cikin nasa.

“Doc idan akwai abunda nayi maka kayi haƙuri kasan ɗan'adam ajizi ne, amman be
kamata ace kullum kana fushi da ni ba, a zamantakewa kullum tattauna ake so da
fahimtar juna, idan har wani abun nake maga kamata yayi ka faɗa min zan gyara
inshaAllah”

Rumgumota yayi jikinsa.

“Baki min komai ba, kawai ina abu ne a ciki na mai ƙarfi, irin ii can't control
myself when I'm angry at you, I'm sorry too”

Lafewa tayi jikinsa kamar wata mussa, sai toshe hanci take, dan warin turarensa
yana son sata a mai. Duk yadda tayi ƙoƙarin daurewa sai ta kasa saboda aman daya ci
ƙarfinta, da gudu ta tashi ta nufi bathroom ɗinsa. Sai ya rufa mata baya da sauri
yana tambayar lafiya.

Amai ta riƙa kwararawa ba ji ga gani kamar zata amaye hanjinta, gashi komai bata ci
ba da safen nan. Har tayi aman ta gama yana riƙe da da ita yana shafa bayanta.

Sai da ta gama ya wanke mata bakinta, sannan ya riƙota suka fito yana mata sannu.
__________________________________________

Share it please I'm busy 🙌

Best regards 💖
Khadeeja Candy 🌺
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 22*

NOT EDITED ⚠️

Yau kusan two weeks kenan, babu gara babu labarinta. Sosai da sosai hakan ya dami
Asim, sai dai ya ɓoye maitarsa, be yarda ya nuna mata komai ba. Ya kan yi ƙoƙarin
siyo duk wani abu na buƙata wanda za'aci ko ayi amfani da shi a gidan. Sai dai duk
tsawon wannan satin biyu Namra a wahale tayi su dan kullum yana manne da ita, bata
da wani dogon hutu indai yana gida.

Bayan sun gama cin abinci ya aje Spoon ɗin hannunsa yana sauke ajiyar zuciya.
Kallonsa tayi dan ta lura da yadda yanayinsa ya canja.

“Lafiya dai?”

Ya ɗan kalleta kaɗan ya ɗauke kai yana ɗan murmushi, fuskarsa na nuna alamun
damuwa.

“Ba komai”

“Haba Hubby ai ni da kai yanzu mun zama ɗaya, ya kamata ace damuwarka ta zama nawa,
babu wani ɓoye-ɓoye”

“Wato bana son nayi maganar ne kiyi mata wani ɗauka, wata ƙila ba zaki fahimce ni
ba”

“Idan ban fahimce ka, wa kake tunanin zai fahimce ka? A tunanin ka idan ka ɓoye min
damuwarka zan jidaɗi ne?”

Tashi yayi daga ginciren da yake ya gyara zamansa yana tsara kalamanta, ta yadda
zasu zaunu a ƙwaƙwalwarta.

“Namra ina gudun ki shiga cikin irin rayuwar ta ne, kin min abubuwa da yawa,
zuciyana bata da muradi illah na kyautata miki. A kullum tunani ina zan zam sama
mana mafita muyi rayuwar jindaɗi, sai dai gaskiya I'm scared”

Sai yayi shiru be ƙarasa ba yana auna yadda kalamansa zasu kamata.
Ita kuma sai ta tambaya zuciyarta cike da shauƙin kalaman nasa.

“Scared of what?”

“Namra ba ni da wani aiki ko sana'ah mai ƙwari da zan iya riƙe ki da ita, ƴan kuɗi
dana ke tunanin zasu ishe ni na kama sana'ah da su na kama hanayar gidan nan
50,0000 per year dan kawai na burge ƴan'uwanki da ke kan ki, nasan ke kika bada
kuɗin amman naso nayi saving ɗin su dan mu samu wata madafa, sauran da suka rage
min kuma gasu muna cin abinci da su kamin Abbah ya yi mana aike”
Ta ɗan ji babu daɗi da kalmar ta fito daga bakinsa, kusan kullum da tunanin take
kwana take tashi, na rashin garar da Abbah yayi mata, a tunaninta hakan da Abbah
yayi mata ya mata ne dan ta auri Asim, tun da ba haka yake ma sauran ƴaƴansa ba,
ita kam ya kasa sai mata girma.

Can ƙasa-ƙasa ta fara magana, zuciyarta cike da rauni.

“Abbah ba zai aiko mana komai ba, da zai aiko da yanzu ya kawo mana ai, sai dai mu
yi tunanin wata mafitar”

Sosai da sosai gabansa ya faɗi, kalamanta sun haddasa masa ciwon kai, har zufa na
ƙoƙarin karyo masa. Janta yayi jikinsa ya rumgume.

“Toh Allah yayi mana mafita, ai Abbah ya gama mana komai tun da ya yarda na aure
ki, Allah dai ya ƙara masa nisan kwana da ƙyaƙƙyawar rayuwa”

“Ameen”

Ta faɗa tana shafa rigarsa.

“Amman yanzu wace sana'ah kake gani yafi? Nifa da zaka bi shawarana da ka koma
makaranta, ka cigaba da karatun ka”

“Bana son karatun nan a yanzu kwata-kwata ya fita rai na, na fi son sana'ar da zata
riƙa kawo min ƙuɗi sosai ta yadda zan riƙa kyautatawa matana”

“Wace sana'ah zaka yi?”

“Wai da naso na kama wani shago dake nan Uguru Plaza na zuba atamfa haka da lace da
shaddodi na gwada na gani, na ma yi maganar shagon dan akwai wani abokina daya ce
babansa yana ba da rancen kuɗi ko nawa kake so kayi sana'ah kuna raba riba, toh
shine nake son na masa magana”

Ɗagowa tayi ta kalleshi, damuwa ƙarara a fuskarta.

“Kamar nawa zaka kashe?”

“Zai kai 1.5 million, har kuɗin hayar shagon, indai ana son a saka kaya masu kyau”

“Tau me zai hana na siyar da motana sai na...”

Bata ƙarasa ba yaja wani dogon tsaki, ya tureta daga jikinsa ya tashi ya nufi
ɗakin. Da sauri ta rufa masa baya tana karantar yadda ransa ya ɓace nan take.

“Kuɗin ba zasu iya ba ne?”

Ta tambaya lokacin data kunna kai cikin ɗakin. Sai ya juyo kamar a fusace yace

“Ban taɓa sanin baki da wayo da hankali ba Namra sai yau, da badan na sanki ba da
sai nace shaye-shaye kike yi, taya zaki ce a siyar da motarki saboda na kama
sana'ah? So kike zargin da mutane suke min ya tabbata gaskiya ko? Daman ance na
auri ki ne dan dukiyarki, dan Allah dan Annabi ki taimaka wajen shanye raɗa da riƙe
amanarki”

Sai yanzu hankalinta ya kwanta, data ji dalilin fushi nasa. Murmushi tayi tasa
hannyenta ta laƙamo wuyansa tana kallon hawayen da suka cika masa ido.

“Bana nufi komai sai alheri, kai kan ka yanzu ai abun kunya ne kaje wani guri neman
rance bayan ni ina da hanyar samo maka wannan kuɗin. Zai zame kama abun magana ace
kana angonka kaje wani guri rancen kuɗin da zaka yi sana'ah, kuma ni Wallahi ba zan
faɗawa kowa ba.

Nasan motar zata yi 2.5 ko ma 2 million, kaga idan ka kama sana'ah sauran sai mu
siye abinci da sauran kayan gida, ni kai na ina buƙatar ƙuɗi a yanzu”

Kai ya girgiza mata ya cire hannayenta daga wuyansa.

“A'a kima daina wannan maganar dan Allah, kin san ko kuɗin da kika bani na haɗa
lefe sai da nayi baƙinciki karɓar su? Nayi nadama sosai da zuciyata ta yaudareni na
karɓi kuɗin”

“Amman ai baka da wata mafita Asim, idan ban baka kuɗin ba a ina zaka samo? Wannan
ma ai dole ka karɓa”

“Da baki bani ba, da dole zan nemo mafita a duk inda take, ko wane hali zan iya
shiga dan na samo kuɗin aurenki”

“Wannan ma ni zan taimaka maka da yardar Allah, kawai ka amince da buƙatata dan
Allah, ba ma acan za'a siyar ba, kawai zan yi ma Anty waya nace zaka zo ka karɓa
min motana, idan an zo nan sai a siyar Asiri rufe”

Kai ya girgiza mata, irin shi fa sam ba zai karɓa ba, ya nufi ƙofa yana wani huci
kamar gaske.
Da kallo ta bishi tana murmushi har ya fice, zuciyarta cike da shauƙin son Asim,
tana jin lallai tayi dacen miji.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa22_13.html

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 23*

NOT EDITED ⚠️

Haka ta cika gidan da ihu sai kuka take duk ta bi ta rikice, zuciyarta na nasaltama
Asim ya tafi ya bar. Yarinyar da suke tare ne taje da gudu ta faɗawa Mahaifiyarta,
sai gata ta zo da gudu cikin gidan tare da Babbar ƴarta.

Dafa Namra tayi tana girgiza ta.

“Haba ke kuwa sai kace ba musulma ba? Cewa akayi ya mutu ne?”

Cikin kukan Namra ta amsa mata.

“Ban sani ba, sun ce yana asibitin Funtua”

“Yanzu ba kuka ya kamace ki ba, tashi ki wanke fuskarki Mardiya ta raka ki, kuje
Asibitin”

Da sauri ta tashi ta shiga ta wanke fuskarta ta ɗauko Hijabinta ta saka, keys ɗin
gidan ma sai da Mardiya ta karɓa ta rufe mata gidan, sannan ta koma gida ta shirya
sannan ta suka kama hanya Mahaifiyarsu na mata Allah ya tsare.
Keke Napep suka hau ta kai du tasha, sannan suka shiga motar Funtua.
Tun cikin Motar Namra take kuka, har suka isa Funtua, kowa sai tambayar yake
lafiya, Mardiya ce kawai take iya amsawa, Namra kan ji take kamar ta yi tsalle ɗaya
ta ganta gaban Asim, sam zuciyarta ta kasa aminta da be mutu ba.
Suna isa cikin asibitin suka tambaya, sai a nuna musu emergency ward. Hankali a
tashe ta shiga gurin, sai rabon ido take, akwai mutane da yawa a gurin ga kuma
ɗakunan bata san wanda zata shiga ba.
Daga gefe ta tsaya ta kira wayar Asim, ringing biyu aka ɗauka.

“Ga mu cikin Asibitin yana ina?”

“Yana ciki suna duba shi, bari na fito yanzu”

Ba a ɗauki dogon lokaci ba, sai gashi ya iso gurin sanye da uniform ɗin road
safety. Sai ya miƙa mata wayar hannunsa yana faɗin

“Hajiya ki kwantar da hankalin ki be mutu ba, sai dai ɗan abunda ba za'a rasa ba,
ba shi kaɗai yayi haɗarin ba tare da wata babbar mota da kuma ƙananan motaci uku,
duk babu wanda be ji ciwo ba, motar ma da yake ciki duk ta ƙone”

Wani sabon kuka ne ya dawo ma Namra.

“Dan Allah da gaske yana da rai?”

“Ko da muka kawo shi nan yana da rai, mutun biyu ne kawai suka rasa rai ciki, amman
shi yana da rai”

“Na gode...”

“Ba komai, amman ki kwantar da hankalin ki babu abunda zai faru”

Hawayen idonta ta share, ta fidda wayarta ta saka number Anty Amarya ta kira ta,
sai da kiran ya katse bata ɗauka ba, sai ta sake kiranta, sai a uku ta ɗaga.

“Assalamu Alaikum, Namra kin kira ina sallah”

“Anty Asim yayi haɗarin mota yanzu haka muna asibiti”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Da sauki dai ko?”

“Eh sun ce be mutu ba, amman har yanzu likitoci suna kansa”

“Wace Asibitin?”

“Specialist dake Funtua”

“Toh ki kwantar da hankalin ki kin ji? Kin san abunda Allah ya ƙaddara ma bawa baya
wuce shi ko? Ki daina kuka ke ma malama ce Namra, ki fawwalawa Allah komai”

“Toh Anty”

“Kin kira mahaifiyarsa?”

“A'a”

“Toh ki kira ta yanzu ki faɗa mata, Allah ya bashi lafiya, gobe zamu zo inshallahu”

“Tau Anty”

Daga haka ta kashe wayar. Ta ɗauki tasa wayar ta kira number Mahaifiyarsa. Ringing
ɗaya ta ɗauka tana faɗin.
“Yanzu nake cewa a sawo min kati na kira ka, na ji ko ka isa lafiya”

“Mama ba shi bane Namra ce, yayi haɗari ne a hanyarsa ta dawowa, yanzu haka muna
asibitin Funtua”

“Wayyo ni Allah na shiga uku, ya mutu ne? In ya mutu ki faɗa min Namratu”

“Be mutu ba yana da rai”

“Ba shi waya muyi magana”

“Likitoci suna duba shi yanzu, ba zai yiyu ki yi magana da shi ba”

“Kice min kawai ya mutu, wayyo Allah ni Halimatu, na shiga uku na lalace”

Kuka take sosai cikin wayar, Namra na amsa mata da nata kukan. Daga bisani ta kashe
wayar, ta risina a gurin tana kuka.

“Haba Namra, ki gode Allah mana da ba mutuwa yayi ba, ki tashi muje muyi Sallah”

Cewar Mardiya tana goge ma Namra hawayenta. Tashi tayi suka nufi wani ɓangare na
asibitin suka siye pure water suka yi alwala Mardiya ta shinfiɗa ɗankwalinta tayi
Sallah, sannan Namra ta yi.

Ta daɗe tana yi ma Asim addu'ah kamin ta tashi su koma cikin emergency ɗin. Sai
kusan goman dare likitoci suka fito da shi tare da wasu mutane maza da mata kusan
mutum shida.
Wani ɗakin aka kai shi, irin ɗakin da ake aje majinyata, aka ware masa gado ɗaya,
suka saka masa jini. Kusa da shi ta zauna tana kallon fuskarsa. Idonsa a rufe,
gefen kansa an saka masa bandeji, an ɗaure ƙafarsa ɗaya, da cinyar hannunsa.

Wani irin tausayinsa take ji, ji take kamar ta cire ciwon ta maida a kanta. Sam
bata ji maganar da likitan yake mata ba har sai da Nurse ɗin dake tare da shi ta
taɓa ta.

“Kece Matarsa?”

Kai ta ɗaga mata, dan bata jin zata iya magana a yanzu, saboda bakinta kumshe yake
da kuka.

“Ki zo likita yana son ganinki”

Tashi tayi tabi bayan Nurse ɗin dan likitan tuni ya tafi duba wasu masara lafiyar.
A kusa da wani marar lafiya likitan yake tsaye yana masa tambayoyi, sai da ya
ƙare dashi sannan ya kalle ta ya miƙa mata wata takarda take cikin file ɗin dake
hannunsa.

“Ki siyo masa wanɗannan magungunan yanzu, kuma ki siyo masa ɗan ƙaramin wando da
riga a saka masa, kin ga yanzu zane kawai aka rufa masa”

Hannu biyu tasa ta karɓa, sai ta koma gurin da Asim yake, Mardiya na zaune a
kujerar dake kusa da shi. Namra ta dafa ta.

“Zan je na siyo magani yanzu na dawo”

“Amman kin san guri?”

“Zan tambaya”
“Toh Allah ya tsare”

“Amin”

Haka ta sa kai ta fice ba dan tasan inda zata ba, bata ma jin kuɗin da yake jakarta
zai isa ta siye duka maganin. Da tambaya ta isa pharmacy dake cikin asibitin, suka
duba magungunan suka ce mata babu irinsu a cikin asibitin sai ta fita waje.

Bata bar gurin ba sai da ya kwatanta mata inda zata samu, can unguwar dake kusa da
asibitin. A harabar Asibitin ta hau Napep ta faɗa nasa inda zai kaita. Be direta ko
ina ba sai bakin pharmacy ɗin. Sai ta ciro naira ɗari ta miƙa masa. Ta taka da ƙafa
ta shiga pharmacy ɗin, sai da aka gama da wasu mutanen sannan ta miƙa musu takarɗar
maganin.

Dubawa mutumen yayi ya rubuta kuɗin ko wanne a jikin rubutun.

“Duka dubu shida da dari takwas da naira arba'in”

Gabanta ya faɗi, kwata-kwata kuɗin da yake jakarta be wuce dubu ɗaya da wani abu
ba. Wayarta ta ciro ta miƙa masa.

“Dan Allah ka riƙe wayar idan na kawo maka ƙuɗin gobe sai ka bani wayana, mijina ba
lafiya kuma bani da kuɗin yanzu, amman nasan gobe Mamana zata zo”

Ba musu ya karɓi wayar, ya miƙawa ɗayan

“Duba mana wannan ba fake ba ce?”

Sai da ya duba gabanta da bayanta, ya ce ta cire mishi password ya duba komai,


sannan suka bata maganin.

Tana fitowa cikin pharmacy ɗin, wani ƙaton mutum ya sha gabanta.

“Malama ana magana da ke a can”

Ya nuna mata wata shegiyar Mota mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Ɗauke kai tayi
kamar bata ji shi ta cigaba da tafiyar tana kallon ti-ti ko zata samu Napep.

Jin tayi ana binta a baya, kuma ba takun mutum ɗaya ba, juyowar da zata yi sai
ƙamshin wani daddaɗan turare ya daki hancinta.

Tsayawa tayi cak tana masa kallin jin dalilin binta da yake shi da bodyguards
ɗinsa. Shi kuma ya tsaya a gurin yana mata wani kallo mai wuyar fassara.

Mashallah kyakkyawa ajin farko kuma ajin ƙarshen a kyau. Manyan idanuwansa, su suka
fi komai kyau a halinta dake fuskarsa, manya ne sosai farin yayi fari, baƙin kuma
kamar an shafa masa kwalli, hancinsa ya zauna a tsakiyar fuskarsa kamar anja masa
layi, a ƙasan hancin an yanka masa wani hot lip pink color, shape ɗin fuskarsa mai
faɗi kamar ƙirginsa. Robe ce a jikinsa mai kyau da ɗaukar hankali.

Ganin be ce mata komai ba, yasa ta juya da nufin cigaba da tafiyarta. Sai kawai
yayi kuskuren kai hannunsa ya riƙa hijabinta, da nufin juwo da ita.

Tassssssss. Ta sauke masa lafiyayyen mari a fuska. Da sauri Bodyguards ɗinsa suka
zaburo za su kai mata duka, sai yayi saurin ɗaga musu hannu.

“Baka da hankaline da zaka kai hannunka ka taɓa min Hijabi? An faɗa maka kowa wace
mace ce ƴar iska? Kasan muhimmancin hijabi da zaka saka wulaƙantacen hannunka ka
taɓa min Hijabi? Ni matar aure ce dan haka ka shiga hankalin ka”
Duk balbalin bala'in da take masa, kallonta yake fuskarsa da murmushi, har yanzu
sanyin da laushin hannunta yake ji a gefen fuskarsa.

“Nima Mijin aure ne”

Ya faɗa lokacin daya ga tana ƙoƙarin juyawa. Awww Mashallah his voice was soft and
sweet, such a nice voice irin ta larabawan nan masu ƙalƙala, wandanda baka gajiya
da jin muryar su.

Wani dogon tsaki taja dai-dai lokacin data tsayar da mai Napep ta shiga tayi
tafiyarta.
Har cikin ransa yake jin tsakin nata, yana yawo a ƙwaƙwalwarsa kamar wani blood.

“Abdul”

Da sauri wanda ya kira da Abdul ɗin ya matsa kusa dashi yana tsare masa.

“Sir”

“Rubuta Number Mai Napep ɗin can. 771A97K Funtua”

“Yes Sir”

Da sauri ya juya ta nufi gurin da suka yi parking ɗin motocinsu. Shi kam sai da ya
daina hango Napep ɗin sannan hankalinsa ya dawo kansa.

‘For the first time in history wata mace ta ɗaga hannu ta mari Abdullah Ahmad Mai-
doki’

A zuciyarsa yayi furucin yana mamakin kansa.

“Unique one”

Ya furta a fili. Sannan ya ce su zo da motocin ya shiga suka kama hanya.

Tana isa cikin asibitin ta kai ma likitan maganin yace ta bawa Nurse. Haka suka
kwana a kansa ita da Mardiya, ko wanne ya shimfiɗa ɗankwalinsa ya kwanta. Sai dai
Mardiya ce kawai tayi bachi Namra kam har safe idonta biyu.
Da safe ita ta bawa Mardiya kuɗi tta siyo abinci a ƙofar asibitin ta karya, ita kam
jasa cin komai tayi har likita ya shigo.

Bayan ya gama duba shi ya sake sa masa drip, a cikin drip ɗin yayi masa alluran da
aka siyo sannan ya miƙa mata wasu magungunan yace idan ya farka ta bashi.

“Amman likita har yanzu be buɗe ido ba”

“Zai buɗe yana da rai fa, kawai yaji jiki ne, mai yiyu juwa anjima ya buɗe idon,
amman inda hali ku kai shi babbar asibitin Katsina dan akwai yiyuwar sai an masa
aiki a ƙafarsa, saboda kashinsa na cinya ya shige ciki”

“Innalillahi wa'inna ilaihi”

Ta faɗa tana faɗuwa zaune saman kujerar roba dake gurin.

“Allah ya bashi lafiya”

Wucewa ya yi gurin wasu marar lafiyar ya barta tana aikin kuka. Likitan be yi minti
talatin da barin gurin ba, Sai ga Mama ta iso da kukanta. Aiko hankalinta ya tashi
sosai da taga yadda fuskar ɗanta ya kumbuɗe kamar an busashi, gaba ɗaya halittarsa
ta canja.
Yadda take rusa kuka sai yasa hankalin duk wanda yake gurin ya koma kanta, ƙanwar
Asim sai haƙuri take bata tana kuka.

Guraren shaɗaya da rabi Anty Amarya ta iso tare da direban su da Aisha. Namra na
ganinta ta fashe ta sabon kuka ta kwantar da kanta jikin Anty Amarya.
Anty Amarya ta danne kukanta, tana lallasar Namra.

“Ki yi haƙuri, Namra ki kwantar da hankalin ki, duk abunda ya kamata ayi masa za'a
masa kinji? Idan ma waje ya kamata a fitar da shi za'a fitar, amman ki kwantar da
hankalin ki”

Karaf Mama ta tsuma baki, tana mai jin zafin yadda Anty Amarya take lallarsar Namra
ita ga ɗanta kwance.

“Ta kwantar da hankali kamar yaya? Ga mijinta kwance ki ce ta kwantar da


hankalinta, ta nata ma kike ba ta Ibrahim ba, daman ai nasan ba son ƙwarai kuke
masa ba, ni wannan aure bai zo da komai ba sai abun baƙinciki, gashi nan daga
shigowarki gidansa ya koma da ƙafa ɗaya”

Da kuka ta ƙarasa maganar. Kallonta kawai Anty Amarya tayi ta ɗauke kai, tana mai
jin zafin kalamanta. Bata wani daɗe ba ta tashi ta fito harabar asibitin tare da
Namra.

“Allah ya sauwaƙe Namra mu kan za mu koma”

Da sauri Namra ta kalleta

“Yanzu Anty?”

“Eh daman Abbah ki yace min kar na kwana, ƙara mu kama hanya yanzu kin san tafiyar
dare bata da kyau, Maryam tace tana gaishe ki”

Nan da nan sai tasa kuka, a zatonta Anty Amarya zata kwana ne. Har suka ƙarasa
gurin mota Namra kuka take, daker Anty Amarya ta lallaɓata tayi shiru.

“Anty ba mu da kuɗin biyan Hospital bill, kuma ba ni da ko naira yanzu a hannuna”

Ta faɗa tana ƙara share hawayenta.

“Ai ga mahaifiyarsa can sai ta biya masa”

Anty Amarya ta faɗa tana shirin zama cikin mota. Namra bata ƙara cewa koma, sai
idonta dake zubar da ƙwallah.
Sai da Anty Amarya ta rufe motar ta zuƙe gilashin sannan ta ce.

“Zan miki transfer 100k Allah ya bashi lafiya”

“Amin na gode Allah ya kai ku lafiya”

A haka suka yi sallama. Namra ta bi motar tasu da kallo har suka bar asibitin.

____________________________________
Share it please.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa24.html

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 24*

NOT EDITED ⚠️

Har Anty Amarya ta koma gida tana jin zafin kalaman da Mama ta yi a gabanta. Sai
yanzu take jin zafin rashin mayar mata da magana da bata yi ba.

Bayan Sallah Magariba Hajiya Barau ta shigo ɗakin, tana tambayar Anty Amarya ya mai
jikin, a lokacin Maryam da Hindatu har Aisha suna ɗaki suna maganar.

“Jiki da sauki sosai, yaji ciwo a ƙafa da hannu, sai gefen fuska”

“Toh Allah ya ƙara sauki ya tsare gaba, mu kam sai an kwana biyu sannan muje mu
ganshi”

“Ai ba komai da sauki ma sosai, ƙaddarori ne kawai idan Allah ya kawo”

“Allah ya sauwaƙe ya ɗauke Wahala”

“Ameen”

Ta tashi ta nufi ƙofa tana faɗin

“Maryam ki zo ki karɓo dambu ɗazu Hajiya Hadiza ta aiko min da shi”

Tashi Aisha ta yi, ta bita suka fita tare. Maryam ta yi ƙwafa tana maimaita maganar
ɗazu.

“Amman Wallahi matar nan bata da kirki sam, kuma ta ci sa'ah ba da ni aka je
Wallahi da sai nayi mata tasss”

“Hmmm kin san wasu ba su iya yarda da ƙaddara ba, idan abu ya same su sai riƙa
ganin kamar wani yayi musu ba Allah ba”

Cewar Anty Amarya, tana gyara zamanta. Hindatu tace

“Ni fa gani nake daman can kamar ba son auren take ba, shiyasa ma ya siye gida can
su zauna”

Maryam ta ƙara tsire baki

“Ai mune ma ya dace muce haka ba su ba, dan yanzu na san ita za a bari ɗmda wahala,
kuma wannan gidan ba siyen shi yayi ba, sai dai idan haya ya kama, idan ma siye
yayi Wallahi Anty Namra ce ta bashi kuɗi, dan ta rance 1.5 million gare ni tace kar
na faɗa”

Daga Anty Amarya har Hindatu da Aisha data shigo yanzu kallon Maryam suka yi da
mamaki.

“Dan Allah da gaske?”


Hindatu ta amsa da ƙarfi. Maryam ta watsa mata harara

“Haka kawai zan ƙirƙiri ƙarya na faɗa, kuma nasan Wallahi shine ya zuga ta yace ta
bashi wai kuma fa ta ƙara masa nata masu yawa, idan ba haka ba taya zai yi wannan
lefen har ya samu gidan kai ta”

“Ko Motar nan waya sani ko sai dawa zasu yi ta bashi kuɗin, Wallahi Anty Namra bata
da wayo sam”

Cewar Aisha tana ɗire wainar gaban Anty Amarya. Gaba ɗaya yanayin Anty Amarya ya
canja, sai ta kawar da fuskarta wani gurin tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta, babu abunda
take tunani sai lamarin Namra.

NAMRA POV.

Asim be farka ba sai washe garin ranar da la'asar, har lokacin Namra bata sa komai
a cikinta ba, dan bata jin yunwa ma a tare da ita.
Daker ya buɗe idonsa kumburarrin idonsa sai kuma ya mayar da sauri ya rufe,
saboda zafin da yaji suna masa. Hannunsa ɗaya ta kama, idonta cike da ƙwalla.

“Sannu Asim”

Sai ta tashi da sauri taje ta kira likita. Abun ka da Nigeria sai da likitan ya
kusan minti ashiri sannan ya iso tare da abun awonsa.
Sama-sama ya duba sa, ya kira sunan sa kusan sau uku, amman be amsa ba, sai motsa
ido yake yana jin abunda yake ji.
Likitan ya kalli Namra yace

“Gaskiya bawan Allah nan yana buƙatar kulawar gaggawa, idan hali zan muku transfer
zuwa babbar Asibitin Katsina dan ya samu kyakkyawar kulawa indai kuna buƙatar
ransa”

A dai-dai lokacin ne Mama ta iso, sai kawai tasa kuka tana faɗin ta bani ta lalace.
Nurse ɗin dake tare da Likitan ta katsa mata tsawa

“Haba Inna muna da wasu majiyanta fa, kukan ki zai iya takura musu”

Namra ta share hawayen idonta tana in'inna tace

“Likita a yi mana”

A take ya karɓi file ɗin dake hannun Nurse ɗin ya fiddo wata doguwar takarda, yayi
rubuce-rubuce ya miƙa Nurse ɗin yana faɗin.

“Ki basu takardar biyan hospital bill kuma ki faɗa musu inda zasu je su biya”

Daga haka ya wuce, ya bar Nurse ɗin tana duba adadin abunda aka kashe musu, sai ta
ware wata takardar ta daban ta rubuta mata kuɗin ta miƙa mata.

“Idan kin wuce pharmacy zaki ga gurin da ake biya, idan kin biya sai ki zo na baki
transfer”

Daga haka ta wuce ta bar Namra da Mama tsaye suna hawaye. Zaunawa Mama tayi a
kujerar roba da take gurin. Namra kuma ta fito ita da Mardiya tana duba jakarta.
Kwata-kwata kuɗin da yake ciki be wuce ɗari bakwai ba, saboda abincin data siya ma
Mama da Mardiya da kuma ƙanwarsa.

“Amman yanzu kina da kuɗin biya kuwa”


Mardiya ta tambaya tana kallon yadda idon Namra ke zubar da ƙwalla.

“Muje ki raka ni na karɓo waya na”

Shine kawai abunda Namra ta faɗa, taja hannun Mardiya suka nufi gate. Napep suka
tare suka shiga, ta sauke su dai-dai bakin pharmacy. Namra ta bashi ɗari biyu
sannan suka shiga cikin Pharmacy.
Bata sha wahala gurin su gane ta ba, saboda kayan jiya ne a jikinta. Bayan sun
gaisa tace

“Ka gane ni?”

“Eh ba kece ta jiya mai waya ba? Ana ta kiran wayar ta tun jiya”

“Dan Allah wayar zaka bani na kira”

“Tau kin zo da kuɗin ko?”

“A'a waya zan kira naji ko an turo”

“Toh sai dai idan nan a zakiyi kiran”

“Eh a nan zan yi”

Sai da suka yi kamar kar su bata sai kuma ɗayan ya ɗauko ya miƙa mata. Number Anty
Amarya ta fara kira, daman ta ga missed call nata a calls list. Ringing biyu Anty
Amarya ta ɗauka da sallama.

“Anty ina wuni ya hanya?”

“Alhamdulillah ya jikin Asim ɗin?”

“Ba sauƙi Anty yanzu haka likitan ya tura mu


zuwa babbar asibitin Katsina, kuma ba ni kuɗi”

“Allah ya sauwake, nima kuɗin da nace zan aiko miki ban samu ba, daman ina jiran
Abbah ku ya bani kuɗin da nake binsa ne sai na aiko miki”

Wani irin abu Namra ta ji ya daki tsakiyar kanta zuwa cikin ƙafafunta. Ta san da
gangan Anty Amarya tayi mata haka ba dan bata da kuɗin ba. Da na gode ta amsa mata
ta kashe wayar, tana hawaye.

Number Maryam ta lalabo ta danna mata kira, tana yin pincking sai Namra tasa mata
kuka.

“Maryam dan Allah taimako nake nema a gareki”

“Taimakon me?”

“Dan Allah kuɗi nake son ki ara min ko nawa ne dan Allah, Wallahi zan biya ki har
da waɗancan ma”

“Anty Namra ban taɓa ara miki kuɗi dan ki biyani ba, duk abunda na baki a kyauta
nake baki shi, gaskiya yanzu bana da kuɗi hannu na, amman ki tambayi Anty ba za'a
rasa ba”

Namra bata ƙara cewa komai ba, sai kawai ta kashe wayar, ta fashe da wani irin kuka
mai taɓa zuciya. Mardiya duk sai ta tsargu ta duƙa a gurin tana bata haƙuri.
Wata Hajiya dake kusa da ita ta kalle tana tambayar lafiya. Sai masu pharmacy suka
mata bayani, cike da tausayawa ta kalli Namra tace

“Tashi Bawai Allah zan biya miki, Allah ya bashi lafiya”

Gyalenta Namra ta riƙa tana mata godiya.

“Allah ya saka miki da Alheri, na gode sosai”

Sai ta kalli Mutumen.

“Dan Allah ina ka san za'a iya siyen wayar nan?”

“Gaskiya sai kasuwar Ƴan wayoyi, dan wannan wayar mai tsada ce can ne kawai zasu
iya siyen ta”

Yana faɗar hakan Mardiya ta zaro ido tana ƙara kallon wayar dake hannun Namra.
Hajiyar ta kalleta.

“Haba ke kuwa kar ki siyar da wayar ki mana”

“Dole ne na siyar kuɗin asibiti zan biya”

Namra ta faɗa cikin kuka. Tun daga sama har ƙasa Hajiyar ta kalli Namra sannan tace

“Nawa ne kuɗin?”

“Dubu ashirin da shida da ɗari bakwai”

Hajiyar ta kalli yaron pharmacy

“Nawa ne kuɗin ka har nata?”

“Ya kama dubu takwas da ɗari huɗu”

Dubu tara ra ƙirgo ta miƙa masa, bata tsaya karɓar canja ba, ta kalli Namra.

“Muje cikin Mota na muga marar lafiyar”

Da sauri Namra ta fita ita da Mardiya, har suka riga Hajiyar isa gurin motar. Sai
da ta buɗe ta shiga sannan ta buɗe musu tace su shigo.
Namra ce a front seat Mardiya a baya. Hajiyar tana yi tana satar kallon Namra. Ita
kuma natsuwarta bata tare da ita, tambayar da take mata ma sama-sama take amsa
mata.

“A nan garin kuke?”

“A'a Katsina nake zama, shine ma suka mana transfer zuwa can”

“Allah sarki wane unguwa a katsina, nima a katsina nake”

“Nasarawa”

Ta amsa mata dai'-dai lokacin data tayi parking, a harabar asibitin. Sai da taje ta
duba Asim tayi ma mahaifiyarsa sannu ta suka je tare da Namra ta biya mata kuɗin
Asibiti. Aiko Namra da dingi mata godiya kamar wanda tayi mata kyautar rai.

“Ba komai Wallahi, ai yi ma kai ne. Muje ki kai musu takardar su baki wacan sai
muje katsina ɗin, dan nima yanzu can zan wuce”

Komawa suka yi, Namra taje ta kai ma Nurse ɗin takardar ta bata ta transfer ɗin,
sannan ta dawo ta kawo ma Hajiyar. Ita ta ciri kuɗi a jakarta ta miƙawa Mardiya
tace taje ta siyo masa shorts da ƴar riga a saka masa. Sannan taje ta biya dubu
biyu aka basu ambulance, wanda za'a kai Asima ciki.

Mama da Hajaru (ƙanwar Asim) ne suka shiga ambulance ɗin tare da Asim. Namra da
Mardiya kuma suka shiga motar Hajiyar, Tun kamin motar ta tashi Mardiya ta karɓi
jakar Namra wai ta kawo ta riƙa mata. Ba musu Namra ta miƙa mata daman jakar ta yi
mata nauyi.

Yadda take tuƙa motar kamar wata fitacciyar direba, dan da ita da ambulance ɗin
ba zaka iya gane wanda yafi gudu ba.
Daf da Magariba suka isa Katsina, kai tsaye Babbar Asibitin suka suka wuce.
Emergency Motar ta shiga Hajiyar na binta a baya. Suna shiga aka karɓe shi aka wuce
da shi Anas room wato ɗakunan da aka tana na marar lafiya shi kaɗai dan bashi
kulawa na musamman. Sai da Hajiyar ta biya dubu goma sha shida na ɗakin sannan aka
aje shi, nan take suka soma bashi kulawar gaggawa abunka da babbar asibiti.

Godiya sosai Namra tayi ma mata har ta rasa yadda zata nuna mata jindaɗinta.

“Babu komai Allah ya bashi lafiya, ni yanzu zan wuce gida idan wani abun ya taso ki
neme ni a wannan address ɗin”

Hajiyar ta faɗa tana murmushi tare da miƙa mata katin ta. Da hannu biyu Namra ta
karɓa, ta raka ta har gurin motar ta, sannan ta dawo.

A Dai-dai lokacin ne likitan ya fito daga ɗakin da Asim yake ya nufo Mama yana
magana da ita.

“Za'ayi masa gyara a cinyar ƙafarsa, sai kuje ku biya kuɗin, kuma za a siye masa
jiki kamar na gora uku, kuje kuma ku biya kuɗin magani”

Ya ƙarasa faɗar yana miƙawa Mama takardun hannunsa guda uku. Da muguwar damuwa Mama
ta karɓi takardar irin bani da madafa ɗin nan. Sai Namra tasa hannu ta karɓa, tana
kallon likitan

“Idan ya kai gobe ba komai?”

“Ba matsala, amman dai ku ƙoƙarta kar ya wuce goben”

“Tau mun gode”

Bayan likitan ya wuce Namra ta shiga kwantar ma Mama hankali

“Mama ki shiga ki zauna da shi, ni zan je gida naga ko akwai abunda zan samo”

“Tau”

Ta faɗa da muryar kuka sannan ta shiga ɗaki. Namra ta juya ita da Mardiya suka nufi
gida.

Mai Napep na sauke su Mardiya ta miƙawa Namra jakarta, ta nufi gidansu. Cikin
kasalar jiki Namra ta buɗe ƙofar gate ɗin ta shiga. Ta daɗe a tsaye jikin ƙofar
falon tana kuka, sannan ta buɗe ta shiga.

Wanka ne abunda ta fara yi, ta saka wasu tufafin sannan ta shiga kitchen ta ɗora
indomie, a gaggauce ta dafa ta zuba a kula, ta haɗa ma kanta tea kaɗan ta sha,
sannan ta dawo ta fito da tabarma da filo da bargo guda biyu, ta aje falo ta ɗauko
plates huɗu da spoons da kofuna ta saka a basket, ta aje a falo. Duk abunda take
Asim ne a ranta, tunani take inda zata samo kuɗin da za'ayi masa aiki, har kuma ta
gama bata samarwa kanta wata mafita ta bayan ta siyar da wayarta.

Mayafinta ta ɗauka ya saka ta fita ta nufi gidansu Mardiya. Da sallamarta ta shiga,


mataɓ gidan suka amsa mata, suna mata ya mai jiki. Sai da ta gama gaisawa da su
sannan ta wuce ɓangaren su Mardiya, kasancewar gudan irin tsohon gidan nan ne da
ake na dangi mai ɗakuna da yawa.

Bata tararda Mamarta ba, sai Mardiya dake sallah. Zaunawa tayi saman simintin ɗakin
tana jira ta gama. Bayan ta sallame ta juyo ta kalli Namra.

“Namra har kin yi wanka?”

“Tun ɗazu, dan Allah so nake ki kai ma Mama abinci da wasu abubuwan da za su
buƙata, kuma dan Allah idan kin san inda ake fansar da waya ki kai ni ina son siyar
da wayar ne”

“Kai yanzu kam sun tashi kin ga har tara ta gota fa, sai dai gobe, sai na rakaki ki
kai”

“Abincin fa?”

“Muje na kai musu”

Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi. Tare suka fito gidan. Tun da suka fito Mardiya take abu
kamar mai jin kunya, har suka shiga cikin gidan. Namra ta bata kayan ta ɗauko
sauran canjin dake jakarta ta miƙa mata wai tayi na okada da su.

Bayan ta wuce, Namra ta sake buɗe jakarta ta ɗauko waya, sai taga wayam, babu waya
babu alamunta, a nan fa hankalinta ya tashi, sai ta zazzage jakar gaba ɗaya, bata
ga wayar ba.
Jikinta be bata ta jefar da wayar a cikin gidan ba, amman haka tabi ta yamutse
gidan tana neman wayar.

Har Mardiya ta dawo bata ganta ba, idonta duk ya rine tana jin kamar tayi kuka ba
hawaye.
Ita kanta ta lura da yadda Namra ta ƙara firgicewa.

“Na kai musu, tace wai na faɗa miki likita ya sake zuwa”

Hannu Namra ta ɗora saman kai ta fashe da kuka

“Kai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kin ga wayar ma da nake son saidawa ban
ganta ba, ko kin ga inda na jefar”

Wani irin dakan ƙirji Mardiya tayi

“Baki gani ba? Wallahi ban ga inda kika jefar ba, kuma tun da na karɓi jakarki ban
ma buɗeta ba, yau ko na shiga uku, da wayar mutane”

A take tasa kuka. Sai Namra ta share hawayenta tana faɗin

“Ƙila ko na jefar a motar matar nan ne ban sani ba”

“Lallai ba zai wuce can ba, amman ni ban ɗaukar miki waya ba Wallahi, sai idan kuma
a asibiti kika jefar”
“Bana zargin ki Mardiya, da zan samu rancen kuɗi da sai naje gida ta yanzu, dan
hankalina ba a kwance yake ba”

“Amman yanzu dare ne, da kin haƙura har da safe, kin ga ma baki san gidanta ba”

“Ai ta bani addireshinta, dan Allah ki ara min ko ɗari biyu ne naje na duba, kin ga
halin da mijina yake ciki”

“Ina da wasu ɗari takwas da aka bani ajiya sai idan sun zan aro miki”

“Aro min dan Allah”

“Bari na ɗauko miki ɗari biyar”

Tashi tayi ta fita, bata daɗe ba ta dawo, ta kawo mata kuɗin. Sai Namra ta ɗauki
Hijabita ta saka.

“Dan Allah Mardiya ki zauna nan har na dawo, ina son ki taya ni kwana”

“Tau ba komai Allah ya tsare”

Ta ɗauki katin ta fice, hankalita a tashe. Napep ta tara ta shiga. Su kusan


tafiyar rabin awa sannan suka isa unguwar GRA ring.
Gidajen gurin duk masu kyau ne da ɗaukar hankali, abun ka da wanda hankali ba
kwance ba haka suka kai ƙarshen unguwar bata gane gidan ba, dan numbobin gidajen
sun ɓace mata. Har sai da suka yi tambaya, saɓnan aka nuna musu gidan Hajiya
Saratu.

Sai ta da buga ƙofaɗ gate ɗin mai gadin ya buɗe mata, ta tambaya yace mata gidan
nan sannan ta sallami mai napep ɗin, shi ma ɗaker ya karɓi ɗari biyu da hansin.

A bakin gate ɗin ta tsaya sai da mai gadin yaje ya faɗawa Hajiyar sannan yayi mata
iso.
Tana saka ƙafarta cikin falon ƙashin turare ya fara mata marhabun.
Haka tayi ta doka sallama amman ba a amsa mata ba, sai ta samu guri ta zauna,
zuciyarta sam bata natsu da gidan ba.

ta ɗauki tsowon lokaci sannan matar ta fito cikin wata rigar yadi mai shara-shara,
kusan ana ganin underwears ɗinta.
Tun da Namra ta kalleta sau ɗaya ta sadda kai bata sake kallonta ba, duk gaisuwar
da suka yi idon Namra na ƙasa.

Cikin wani irin karairaiya taje ta ɗauko ma Namra lemu da snack ta kawo mata. Namra
bata ci dan basu ne a gabanta ba, kuma ta kasa ɗaga ido ta kalli Matar. Ganin hakan
yasa matar ya taso ta dawo kusa da Namra ta zauna, ta kai hannunta dafa Namra tana
shafa bayanta duk da kasancewar Namra na cikin Hijabi ne.

“Ki kwantar da hankalin ki miji zai samu sauƙi nayi miki alƙawarin duk abunda tmya
dace ayi masa za a masa, dan ya samu lafiya, yanzu me likitocin suka ce ne? Dan
daga ganin ki akwai wani a ƙasa”

“Na gode sosai, yanzu sun ce sai an biya kuɗin aiki dana magani, kuma suna buƙatar
jini gora uku, shine naso na siyar da wayana na duba ban gani ba, nace ko na manta
a motar ki ne”

Wani ƙasaitattacen murmushi tayi, ta girgiza mata kai.

“Baki jefar da komai a mota na ba, amman bari na baki keys ki duba, saboda cire
kwankwanto”
Bata jira komai ba, ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗauko mata keys ɗin ta miƙa mata.

“Muje ki duba, amman na faɗa miki ba dole sai kin siyar da wayarki zaki iya
taimakon mijinki ba”

Namra ta karɓi keys ɗin tana faɗin

“Ba ni da wata mafitar ne sai wannan”

“Kina da mafitoci ba ma ɗaya ba”

Ta faɗa yayinda suke fitowa daga cikin falon suka nufi gurin motocin da suke gidan.
Ita da kanta ta nuna mata motar da suka shigo, cikin rawar jiki Namra ta nufi motar
ta buɗe tana dubawa. Zuwa Hajiyar tayi bayan Namra ta tsaya tana shafa mata duwawu,
tare da faɗin

“Duba da kyau ki gani, amman ni bana tunanin kin bar wani abu a gurin”

Da sauri Namra ta juyo ta fito da jikinta cikin motar tana yima matar wani mugun
kallo.

“Miye haka? Ya zaki riƙa taɓa min jiki kamar wata karuwa, ko an faɗa miki ni irin
waɗannan mata nan”

Murmushi Hajiyar tayi kamar bata ji zafin kalaman Namra ba.

“Ɓana nufi komai da ke sai Alheri, kina da kyau da duk mace data kalle ki sai tayi
sha'awarki, balle kuma namiji, dan haka kiyi amfani da damarki ki taimaki kan ki”

“Ke kuma haka kike? Tirrr da ke daman taimakon da kika min ba dan Allah kika min
ba? Saboda wani mugu nufi naki? Toh Allah ya fiki, jikina bana mata irin ki bane,
ba kuma na wasu mazan bane, na mijina ne shi kaɗai halalina”

“Hmmm kije kiyi tunani Namra, matuƙar kika amince da buƙata zan miki duk abunda
kike so a duniyar nan, idan ma waje ya dace a fitar da mijinki zan sa a fitar da
shi”

Namra ta girgiza mata kai.

“Dukiyarki bata burge ni, arzikin gidan mu ya ninka naki sau dubu, ƴan'uwana ne
suka juya min baya shiyasa kika ganin a halin da kika tsince ni”

Hawayen ya gangaro daga idon Namra. Hajiyar ta matsa kusa da Namra tana ƙoƙarin
dafata.

“Kaicon ki, haƙiƙa ina tausayin rayuwarki, wallahi wata mace bata taɓa burge ni ba
kamar ki”

“Ba nice a abun tausayi ba, kece a abar tausayi a ranar da zaki yi nadamar da bata
da amfani”

Namra ta buge mata hannu ta juya ta fice daga gidan tana hawaye. Ta daɗe tana
tafiya a estates ɗin kamin ta samu Napep. Har ta iso gida hawaye take zuciyarta a
cakushe.

Ɗari biyun da hasin da suka yi saura ta miƙawa mai Napep ɗin, ya so yayi magana,
sai dai hawayen daya gani a idonta yasa shi tausayinta, ya kaɗa napep ɗinsa yayi
gaba.
Mardiya na gani hawaye a fuskar Namra, hankalinta ya tashi, da sauri ta riƙa ta
suka zauna saman kujera.

“Lafiya ? Ba acan kika jefar da wayar ba?”

Sai kawai Namra ta fashe da kuka tana riƙe Mardiya kamar ta shige cikin jikinta.

*** *** ***

Ganin dare ya lula Namra bata dawo ba, yasa Mama har zuƙa sosai, a ganinta abun
kamar be damu Namra ba. Tun da tana da hanyoyin da zata iya biyan wannan kuɗin. Ita
ganin take kamar ma da haɗin kai aka yi masa wani abu yayi haɗari motar, so that
idan ya mutu sai ta auri wanda take so.

“Mama ko kuɗin adashe zamu karɓo a biya ina ganin fa kamar bata da kuɗin nan”

Cewar Hajaru, Mama ta kai mata wani mugun zungura

“Duk naji bakin ki yayi maganar adashen nan sai na kusa halaka ki, taya zata ba mu
kuɗi bayan mun riga mun zuba, kina ganin kullum zogaron kuɗin zubi take mana. Ai
ita ta fimu sanin hanyoyin samo kuɗi, ta nemo ta biya a itace silar komai tun da
tasan be wani iya mota ba, tasa ya jawo ta tun daga sokoto har katsina dan kawai su
ga bayan shi.
Ni Wallahi ɗana ko mutuwa yayi sai nayi ƙararsu”

Hajaru dai tayi shiru bata sake cewa komai ba, Mama kam sai cika take tana barsewa,
ita mai ɗa.

KALSOOM POV.

Babu abunda ta ɓoye Salma na zamantakewar auren da suke yanzu da Hilal.


Ita tafi raja'a akan Hilal baya son haihuwa, daman Asmee takan nuna mata alamun
hakan tun lokacin data shigo cikin gidan. Sai dai tunaninta ya sha banban lokacin
da Salma take nusar da ita akan wasu abubuwan data manta.

“Haba Kalsoom ke kan ki yanzu ba zaki iya gane wani abu a tare da shi ba? Taya za
ace dan kin yi ciki sai ya sauya miki? Baya son haihuwa zai bar matarsa ta haifi
yara uku kuma tana aiki?Sherin kishiya yana da yawa Kalsoom musamman na zamanin
nan”

“Naga sauyi a ɓangarenta dan duk wani kishi data ɗauka yanzu ta aje shi, bana da
matsala da ita”

“Wannan ma kaɗai ya isa ya nuna miki akwai abun da tayi, ki bita a sannu kuma ki yi
taka tsantsan da ita. Sannan a duk lokacin da mijinki yake fushi yana hawa sama
karki tanka shi, kisa mishi ido, saboda maganar zai iya zama miki illah.

Cigaba da addu'ah, idan zaki iya kiyi alwala a zama ɗaya ki karanta Yasin ƙafa goma
sha biyar, ki roƙi Allah, ko kuma ki karanta ayatul kursiyu ɗari uku da sha uku
Wallahi duk kika roƙi Allah sai ya amsa miki, ki daure kiyi na tsawon sati acikin
kwana uku Allah zai biya miki buƙarta ki.

Sannan ki samu ruwa mai kyau ki watsa a saman rufin ɗaki, idan ya gangaro ki tara
abu ya zuba a ciki, ki taceshi ki sha ki wanke kanki, Wallahi indan Asirine akayi
miki sai ya karya kuma sai Allah ya nuna miki wanda yayi miki haka a bachin ki,
maƙukar kika yi har sau uku”
“Na gode sosai Salma, Allah ya bar zumunci”

“Amin Allah ya baku zama lafiya”

Daga haka ta aje wayar, ta jingina da gadonta tana sauke ajiyar zuciya.

“Kai kayi auren baka huta ba, idan kuma baka yi baka huta ba, da wannen zaka ji”

Yadda ya turo ƙofar ɗakin ya shigo ne yasa ta zabura ta tashi zaune, tana kallon
yanayinsa.

“Ina kuɗina dake cikin closet?”

Wani kallon mamaki tayi masa.

“Kuɗi kuma? Ni ban ɗauki kuɗin ka Doc, ban ma san ka aje kuɗi a gurin ba”

“Babu wanda zai ɗaukar min kuɗi bayan ke, dan ke kaɗai kike goge gurin”

“Amman ai ba ni kaɗai bace a gidan nan”

“Mata ta bata taɓa min sata ba, ƴara na kuma basu ɗaukar min kuɗi, sannan basa da
wayon da zasu iya ɗaukar dubu ɗari uku da hansi”

Hawaye ya silala a idonta. Ta nuna kanta

“Ni kake zargi kenan, ni na ɗaukar maka kuɗin ko? Haba Doc taya zan ɗaukar maka
kuɗi abunda ban taɓa yi ba”

Ƙara haɗe fuska yayi kamar an aiko masa da mutuwa, ya ɗaki mirror ta yana ƙara
jadadda mata.

“Bari kiji na faɗa miki, ko ki nemo dubu ɗari uku da hansi ko kuma a bakin auren
ki!”

Bata san lokacin data kwantar da kanta gefe tana masa kallon da ita kanta bata san
tana masa ba, ta kasa tantancewa shi ne ko ba shine ba.? Fuuuu ya bar ɗakin kamar
walƙiya yana wani irin huci.

________________________________

I need more and more comments. 🙌


Bari na ga suwa suke son nayi long chapter gobe 🤔

BEST REGARDS 💖
Khadeeja Candy 😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

Masu Tambayar Labarin Uzair da Amira zai zo muku a gaba, tare da nasu Zagon ƙasa.
Just keep moving komai zai zo daki-daki.
*PAGE - 25*

NOT EDITED ⚠️

KALSOOM POV.
Ta daɗe a gurin tsaye duniyarta na juya mata, kunnuwanta sun kas ɗaukar abunda
suka ji Hilal ya faɗa mata, idonuwanta kuma sun kasa yarda da ba mafarki take ba.
Makomar aurenta take tunani, yadda zamanta a gidan zai kasance yake mata yawo a
ƙwaƙwalwa, taya zata biya abunda bata ɗauka ba? Akan me zai nuna dubu ɗari uku sun
fi aurenta daraja a gareshi? Dan me idonsa zai rufe har yayi mata wannan furucin?

Ta kasa zaɓa tsakanin igiyar aurenta da kuɗin da idan har ta bashi zai iya tabbatar
masa da lallai ita ɗin ce ta ɗauka.
Hawayen dake idonta ta share, ta tashi ta ɗauko akwati ta buɗe wardrobe ta ɗauko
tufafinta ta saka aciki, ta ɗauki jakarta ta saka wayarta da duk wasu abubuwa da
tasan zatayi saurin buƙata, ta zari mayafin ta yafa ta jayo akwati ta fito. A
lokacin Hilal yana zaune falon ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya.

“Ina zaki je?”

“Gidan mu, ba kace na kawo kuɗi ba ko kuma a bakin aure na? Ni ba zan iya biyan
abunda nasan ban ɗauka ba, amman Allah yana nan baya bachi baya angaje zai bayyana
gaskiya, amman ni ba ɓarauniya bace”

Tasowa yayi ya ƙaraso kusa da ita.

“Look Kalsoom ...”

Sai kuma yayi shiru ya kasa magana, ya kuma kasa kallonta. Ganin hakan yasa t share
hawayenta ta cigaba da jan akwatin. Sai ya riƙe ya kai hannu ya riƙota, kuma ya
kasa mata magana, shi dai ji yake babu daɗi ya rasa abunda ke damunsa, sai yanzu
yake jin nadamar furucin da yayi mata, mamakin yake yadda ya alaƙanta sakinta da
kuɗin da basu taka kara sun karya ba a gurinsa, bayan kuma baya da tabbacin ita ɗin
ce ta ɗauka.

“Ban aureka dan dukiyarka ba, balle har ya kai ni ga yi maka sata, nayi tunanin
kasan darajar aure, ashe na yi kuskure, daman an faɗa min baka son haihuwa kana son
kayi amfani da wannan damar ne ka wulaƙanta ni ko? Zan bar maka gidan ka sai ka
zauna da wanɗanda ba ɓarayi ba!”

Kalamanta sun harzuƙa shi matuƙa, sai kawai y saki hannun nata.

“Kije duk inda zaki je, amman bari na faɗa miki duk wani abu ya samu cikin nan na
ki, Wallahi sai kin yabawa aya zaƙinta”

Cikin wani irin ɓacin rai ya nufi ɗakinsa, ita kuma ta bishi da wani kallo na
takaici na baƙinciki, kamin ta saka kai ta fice.

Ɗakinsa ya koma ya zauna, rasa yayi abund ke masa daɗi, dawowar da yayi ɗaukar kuɗi
sai ya kasa komawa. Ba shi ya fito ɗakin ba sai da lokacin ɗauko yaransa daga
makaranta yayi har ya gota, sannan ya fito daga ɗakin.
Kukan Rafiq yaji da yaji yasa shi ya nufi ɗakin Kalsoom dan shi sam ya manta da
Fariq na bachi.

Ɗaukarsa yayi ya ɗora a kafaɗa yana jijjigashi, ya fito ya buɗe motarsa ya saka shi
gidan gaban, sannan ya zagaya ya shiga ya tashi motar.
Ko da ya isa ɗaukarsu duk sun ƙosa, ga Rafiq sai kuka yake masa, har suka dawo
gida.
Da gudu suka shiga falon, sai suka tsaya a gurin da Kalsoom ta saba nuna musu su
aje safunan su suka aje sannan suka nufi ɗakinta suna rigangan.
Ganin bata ɗakin yasa suka fito suka nufo kitchen da gudu, nan ma basu ganta ba,
sai suka nufo dinning gurin da Hilal yake tsaye yana haɗawa Rafiq madara.

“Daddy ina Anty?”

Yi yayi kamar be ji su ba, har sai da suka ƙara tambaya sannan ya kalli Ezzah
kasancewar ita ce babba.

“Anty ku taje unguwa”

“Yaushe zata dawo?”

Ulfah ta tambaya. Sai da ya sawa Rafiq madara a baki sannan ya amsa musu.

“Ni ma bata faɗa min ba”

“Daddy ta dafa mana abinci?”

“A'a bari Rafiq ya gama zan muku takeaway yanzu”

“Anty tace mu daina cin takeaway sai abincin gida”

Kallonta Ezzah yayi da kyau.

“Amman yau Anty ki bata nan na ce zaku ci takeaway”

“Daddy ka dafa mana Indomie”

Ulfah dake ƙoƙarin cire uniform ɗinta ta turo baki tace

“Ba za mu ci indomie ba ai da safe Indomie muka ci, Daddy ayi mana takeaway”

Ezzah ta nufo a fusace tana faɗin

“Allah kuwa duk Anty ta dawo sai na faɗ mata nace kin ci takeaway”

Ita kuma sai ta taɓa hannayenta alamar ma shiryawa masifar.

“Nima na faɗa mata na ce kin yi faɗa da wata a makaranta, ai ta ce ki daina faɗa a


makaranta”

Hannu Ezzah ta kai zata daketa sai Hilal ya katsa mata tsawa.

“Ezzah karki dake ta, zan dafa miki indomie, ke kuma zan miki takeaway is that
okay?”

Duk suka haɗa baki gurin amsa masa.

“Yes Daddy”

“Come and take your brother”

Ezzah ce taje ta karɓe shi, sannan ya nufi ɗakinsa kansa na masa wani mugun zafi.

NAMRA POV.
Tare suk kwana a gidan ita da Mardiya. Sai dai ita batayi bachi ba, har safe Asim
take tunani da halin da yake ciki.
Tasan ita kaɗaice a duniyar nan zata iya taimakonsa, idan kuma har bata masa ba
waye zai masa, tun da mahaifiyarsa bata da hali.

Babu abunda ya fi ɓata mata rai kamar abunda Anty Amarya da Maryam suka mata, kuma
bayan su bata tunanin akwai inda zata iya zuwa ta kai kukanta.
Tun da tayi sallah asuba ta shiga kitchen ta haɗ ma Mama abun kari, sannan ta shigo
ɗakin da suka kwana da Mardiya ta tasheta.

Tashi tayi zaune tana murtsikar ido.

“Ina kwana har kin tashi?”

“Ba dole na tashi ba, har na haɗa muku abun karyawa,dan Allah shiga ki wanke bakin
ki ki karya, idan kin san gidan wat dillaliya ki kai ni ko kuma ki kira min ita ta
zo ta siye gadona”

Mardiya ta daki ƙirji

“Gadon ki kuma? Haba Namra karki siyar da gadon ki mana”

“Idan ban siyar da shi ba, kai na kike son na siyar ? Ko sata zan yi? Ba ki ga hali
da mijina yake ciki ba”

“Amman ba ku da ƴan'uwan ne da za su iya taimaka muku?”

“Ƴan'uwana sun juya min baya, shi kuma ƴan'uwansa ba wani hali ne dasu sosai ba,
nasan ko da za a samu ba zai wuce ayi karo karo ba, kuma kin ji abunda likita yace
kar ya wuce kwana biyu ba'ayi masa aikin ba”

Sosai Mardiya ta ɓata rai tana nuna mata rashin jindaɗinta akan siyar da Gadon da
Namra zata yi.

“Gaskiya ni ban jidaɗin haka ba”

“Ba komai Allah zai bani wani, tashi ki shirya ai kin san wata mai siye ko?”

“Eh akwai wata a nan unguwar mai siye sosai”

“Dan Allah ki min magana da ita yanzu kar rana yayi, kuma ina son kije ki kai musu
abincin su”

“To bari na tashi”

Ƙoƙarin tashi take tana wani kare-karen zane, kar sarƙar dake jikinta ta faɗo. Ita
kam Namra bata ma kula ba sai ta tashi ta bar mata ɗakin.

A haɓar zanenta ta ƙulle sarƙar sannan ta shiga banɗakin, ta wanke fuskarta, koda
ta fito har Namra ta kawo mata taliya a plate da ruwan sanyi ta aje mata.
Haka ta riƙa aika abincin kamar wata tsohuwar mayunwaciya, nan da nan ta ƙare ada
plate ɗin, ta sha ruwa sannan ta fito falon tana faɗin

“Bari naje na kira miki ita”

“Toh dan Allah ki yi sauri”

Namra ta faɗa tana shan tea ɗin dake hannunta, idonta duk sun wani zurun-zurun
kamar ita ce marar lafiyar.
Mardiya bata ɗauki dogon lokaci ba ta dawo tare da matar, sai da suka gaisada Namra
sannan Namra ta ta shiga da ita cikin ɗakin ta nuna mata gadon. Tana ganinsa tasan
sabo ne, amman duk da haka sai da ta gama duba ko ins nasa sannan ta kalli Namra
tace

“To nawa aka masa kuɗi?”

“Babu wanda ya taya, ki siya kawai”

“Toh ai ba siyen ba, kin san irin wannan manyan kayan ba ko wace mai keya ke siyen
su ba, sai su daɗe baka sai da ba amman ke nawa kika ga zaki iya sai da su?”

“Ni dai miliyan ɗaya har da wani abu Abbah ya siya min su, ke kuma sai ki kwatanta”

“Kai kai aiko an daki hancinsa, dan wannan kayan yanzu wasu ma sun daina yayinsu,
ai sun faɗi sosai. Sabin ma ba zasu wuce ɗari bakwai ba”

“Tau ki bayar da haka ɗin”

Tayi ma Namra wani kallo tana taunar goron dake bakinta.

“Ni ko ai ba zan ci riba ba, magana ta gaskiya zamu yi, dan ni bana son nakkasa
mutum, ƙara ayi ciniki babu cuta babu cutarwa, indai zaki iya bari ɗari, shima dai
ƙoƙartawa zan yi dan ba duk dillaliya ke zuba kuɗi da yawa ta siye kayan data san
ko ta sai da ko karta sai da ba”

“Haba baiwar Allah, Wallahi lalura ce tasa zai sai da abu na, ba kiga sabo ba ne”

“Na gani amman ai kin san duk abunda aka riga aka fitar indai kuɗi kake so sai ka
faɗi, amman yanzu zan yi miki magana ɗaya idan yayi miki na siye ɗari uku da
ashiri”

Kallon gadon Namra tayi ta sake kallonsa ta kalleshi sannan ta kalli Matar tace

“Kawo kuɗin”

“Amman fa sai naga mai gidan ki, dan wani lokacin ana siyen kaya sai kuma miji ya
zo yace shi ba za'a siyar da kayan matarsa ba”

“Mijina ba shi da lafiya kuɗin magani nake nema shiyasa zan siyar da wannan gadon,
yanzu haka yana asibiti aiki za a masa”

“Allah sarki, Allah ya sauwaƙe, amman duk da haka zan zo da ɗana sai yayi mana
takarda guda biyu saboda gudun matsala”

“Ba matsala, kuɗin fa?”

“Kuɗi gaskiya sai zuwa gobe na kawo miki sai na ɗauki gadon, dan yanzu ƙuɗin da
suke hannuna ba su wuce ɗari biyu ba”

“Bani haka gobe sai ki kawo min sauran ki ɗauki gadon”

“To ba matsala amman sai kin biyo ni gida na baki ga ban ƴan gidan mu saboda shedu”

Sai da Namra ta bawa Mardiya abincin da za a kai ma Mama sannan ta saka hijabinta
ta kulle gidan suka fita tare.
Gida matar suka shiga, ta ƙirgo kuɗin gaban mutanen da suke gidan ta bawa Namra
bayan ta faɗa musu yadda suka yi, da Namra tun a gida. Sannan tasa ɗanta ya ɗauko
takarda yayi shedu guda biyu ya bata ɗaya ya bawa Namra ɗaya.

Tare da Mardiya Namra ta fito gidan, suka tare napep ta kai su Asibiti. Mardiya ce
ta wuce kai musu abincin Namra ta nufi gurin biyan kuɗin magani. Dubu ɗari da
talati ta biya na aikin, sannan ta biya na magani suka zo suka ɗibi jininsa suka
auna sannan suka tura ta lab gurin siyen jini, tayi sa'ah an samu irin wanda ake
so, gora uku ta siyo sannan ta dawo ta kawo musu.

Cikin dubu ɗari biyu, kuɗin daya rage be wuce dubu bakwai da ƴan canji ba. A kasale
ta shiga ɗakin da yake, sai ta tararda shi cike ƴan'uwan Asim na Sokoto da Bakori
sun zo dubiya.

Cikin far'ah da ƙarfin hali ta gaisa da su, sannan tayi ma Mama ina kwana. Sai
kusan azahar wasu suka koma aka bar mutum biyu su wai ba yau zasu ba.
Ganin azahar tayi yasa Namra ta ba Mardiya makulli taje ta girka mata abincin rana,
ita kuma ta dawo kusa da Asim ta zauna, ta zuba masa ido kamar ba gobe. Daker ya
ɗaga ido ya kalleta ya sake rufewa ji yake kamar ba duniya yake ba.

Ita kuma wani irin tausayinsa take ji take ciwon kamar a jikinta yake.
Uku dai-dai nurses suka shigo suka fita da shi zuwa ɗakin da za'ayi masa aikin.

ABDOOL POV.

Hannu ya kai ya kunna air conditioner dake ɗakin sannan, ya rage tufafin jikinsa,
ya buɗe freezer ya ɗauko power horse ya sha.
Sai ya dawo saman sofa ya zauna, yana kallon window. Gaba ɗaya ya tattara
hankalinsa ya miƙa gurin windowdake garden yana sauraren birds singing.

Yana jindaɗin saurarensu sosai da sosai, hakan yasa lokuta da dama idan ba shi da
wani aikin ya kan tare a garden dan kawai sauraren sautin na su.
Hannayensa ya zuba a aljihu ya tashi yana wani irin taku na sarauta da ƙasaita
ya nufi window, Peacock ɗin dake ƙarƙashin apple tree yana sha'aninsa ya tsurawa
ido. Kamar wanda ya tuno wani abu sai kawai yayi wani ƙayataccen murmushi ya wanda
ya sanya dimples ɗinsa fitowa, lumshe ido yayi yana shafa fuskarsa.

“Because of her, half the time I don't even know that I'm smiling, she insult me
but i still need to see, who's she?”

Abund ya furta kenan a fili sai kuma ya bawa kansa amsa.

“The Unique one”

Murmushi yayi mai sauti, ya rumgume hannayensa yana ƙara saita tunaninsa.

Taya akayi ya zure haka? Mema ya kai shi kula wata har yayi ƙoƙarin mata magana,
shi da bay da lokacin wasu mata. Hannu yasa a aljihun wandonsa na Army, ya ɗauko
wayarsa ya kira wata number, bugu ɗaya ya ɗauka.

“Ali ya ake ciki?”

“Naje har gurin shugaban masu Napep ɗin na bincika, sai aka kawo min mutumen yace
shi be santa ba kuma a bakin babbar asibitin funtua ya sauke ta, wai yana ganin
jinya take”

“So what's the solution?”


“Sir want i think is better mu shiga cikin asibitin mu bincika”

“No”

Ya girgiza kai alamar shawarar bata masa ba, ya ɗan ɗauki dogon lokaci, be ce masa
komai ba, ba dan kuma baya da abun cewar ba, sai dan isa da izza.

“Ka cire kuɗin da zai isa, a shirya takeaway da five thousand sai muje mu raba ma
Patients ko Allah zai sa mu samu ganinta”

“Okay but Sir Akwai meeting da zaka je gobe Abuja, kuma the next day akwai meeting
ɗin Mr President ya shirya za ku yi akan matsalar tsaron nan na Maiduguri da
Zamfara”

Lumshe ido yayi ya buɗe.

“I know that, nasan end of this month ina da free days, a cikin wannan rana ku zamu
je, sai ka saka mana date”

“Alright Sir zan duba the most expensive free day na ka”

“Good of you”

Sai kawai ya kashe wayar, ya mayar aljihu. Da ƙarfi aka banko ƙofar ɗakinsa, sai
kawai yayi murmushi.

“Hey Dude”

Wanda ya kira da sunan ta fito daga cikin labule tana dariya, yarinya matashi wanda
ba zata wuce fourteen to sixteen years.

“Yarima Ummi na kiran ka”

Ta faɗa tana taɓa hannayenta. Hannayen nata ya riƙa yana murmushi.

“Dude Yarima has finally found his princess”

Ta zaro ido

“Wow, when? How? Who?”

“At funtua i don't know who's she”

“Is she really cute?”

Wa wara manyan idanuwansa.

“Yeah she's so pretty, she had that diamond eyes, her lips is so cute, i like her
face, she's tall, she wearing Hijab and she's black, Dude you know how i love black
girls huh?”

“Yes Dude so how are we going to meet her?”

“I don't know, she slap me Dude”

Ya wani ɓata fuska kamar ƙaramin yaro. Itama ta ɓata fuska kamar tayi kuka.

“So heart touching”


“Don't worry i will slap her heart when i have a chance, but i still feel her soft
fingers on my cheek”

“ I will be the first one to tell Ummi”

Ta faɗa tana dariya. Sai yayi saurin rufe mata baki

“No Dude wannan sirrin mu ne, no one will ever know”

“Yes I won't tell”

Ta faɗa tana ɗaga hannu sama alamar tayi alƙawari.

“So tell me why Ummi take son gani na?”

“She want you to go and meet Cute Eysha, daughter of Hajiya Saratu”

“What? Please tell her I'm sick”

Har ta buɗe baki sai kuma ta rufe ta saki hannunsa ta fita. Batayi minti biyar da
fitar ba yaji alamun shigowar Ummi.
Da sauri ya haye saman gado yaja bedsheet ya lulluɓe ya makore kamar da gaske ba
shida lafiya.

“Ai dole ka riƙa ciwo, kullum baka da hutu kai ne agogo sarkin aiki, idan an maka
maganar aure kamar ance ka faɗi ka mutu, duk yaran garin nan kace basu maka ba, ko
so kake ni da Mai martana mu mutu ba muga auren ka ba?”

Ɗan ɗagowa yayi kaɗan yana pretending like he's really sick.

“Ummi yanzu kuma miye nawa? ”

“Ƴar wajen Hajiya Saratu nace kaje ka gani, tace min jiya ta dawo daga Kaduna”

“Ummi ko na yi aure babu wanda zata zauna da ni, saboda ina da lalura ta rashin
lafiya yanzu haka Dr Alex ya ɗora ni akan magani”

Ya faɗa yana ƙoƙarin mayarda ƙaryarsa ta zama gaskiya. Ita kuma sai ta amsa da
ƙarfi.

“What?”

Sai kuma ta kalli ƙanwarsa.

“Afrah go and watch your favorite channel”

Sai da suka yi ido biyu da yayan nata sannan ta fice.

ANTY AMARYA POV.

Ji take bata kyautawa Namra ba, idan har bata mata ba babu wanda zai mata sai
Allah, soyayya irin ta ƴa da uwa ta hana Anty Amarya ƙyale Namra har sai da tasa
Maryam ta tura mata dubu ɗari da Hansi.

A gajiye Maryam ta shigo falon ta zauna kusa da Anty Amarya tana miƙa mata atm ɗin
ta.
“Kai yau nasha wahala Wallahi, sai kusan 4 muka tashi lacca, naje back kuma na
tararda layi”

“Kin tura mata?”

“Eh but her phone is still switch off ”

“Maybe ta siyar ita ma”

“Kai why not su dawo nan garin? Zama acan zai mata wuya”

“Leave here ita ta so ai, sai taje tayi abunda take ganin yafi mata”

“Amman Anty Namra zata sha wahala tun da tana gudun zuciyar mutane”

Ajiyar zuciya Anty Amarya ta sauke, tana wani nazarin na daban.

_________________________________________

Five words for this chapter... 😻


Waiting for your comments... 😘
Best regards to you all... 💖

CANDY🌺
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

This page is for Birthday Girl Salwees. Happy Birthday Dear 💖

*PAGE - 26*

NOT EDITED ⚠️

Hankalin Namra be kwanta ba har sai da aka fito da shi daga ɗakin da aka masa
aikin.
Sai suka dawo da shi, ɗakin da yake, anyi aiki cikin nasara da taimakon Allah.

Sai da yamma Mama ta je gidan Namra ita da Hajara dan yin wanka ta kuma ɗan huta,
Mardiya Namra ta bawa keys ɗin gidan dan ta taba musu abinci kuma ta taya su zama.
Ita kuma ta kwana da Asim a asibitin.

Babu irin inda Mama bata shiga ba a gidan, sai baya kyau gidan take da girmansa.
Mardiyace ta faɗa mata Namra ta siyar da gadon har an bata wani abu daga ciki.
Babu irin tsinuwar da Mama bata yi ma iyayen Namra ba, a zatonta sune suka turo
mata da kuɗin aiki dana magani, a nan ne Mardiya ta ƙara fayyace mata matar data
taimaka ta kawo Asim asibiti ba yar'uwarsu bace, nan ma Mama ta cika da mamaki, dan
a zatonta ita yar'uwarsu.

“Kai tirr da wasu mutune Wallahi, wato su babu ruwansu da lamarin mijinta tun da ba
ita bace ko? Hmmm ni ban taɓa ganin iyaye irin nata ba, daman ba son auren su ke”

Taja wani godon tsaki sannan ta fito daga ɗakin, ta shiga kitchen ta fito ta shiga
ɗayan ɗakin. Mardiya dai na biye da ita har ta gama duba gidan. Shikafa da miya
Mardiya ta dafa tare da Hajara.
Washe gari ma wani abincin Mardiya ta sake dafa musu, bayan sun ci ta zuba wanda
zasu tafi dashi a asibiti, sannan suka wanka suna cikin shiri Dillaliyar ta zo
Mardiya tace mata bata nan, sannan ta rufe gidan suka nufi asibitin.

Namra suka tarar zaune a kujerar dake ɗakin tana bawa Asim tea. Ba laifi alamun
sauƙi ya bayyana a yanayinsa, wanda a ada ma idan ya ɗaga ido sai yayi saurin
rufewa yanzu kuma gashi har yana shan tea.
Farinciki gurin Mama ba'a magana, sai ta zauna saman gadon kusa da shi, tana
murmushi

“Mashallah Ibrahim, Allah ya ƙara maka lafiya”

Ɗan murmushi yayi kaɗan irin yana jin zafin ciwon nan yana ƙarfin hali. Mama ta
kalli Namra

“Yaushe ya farka?”

“Tun da asuba, har likita ya duba shi ya bada wata takardar ta gani yace allura ce
za a masa guda bakwai, kullum ɗaya saboda jinin daya bugu a kansa”

“Allah yasa dai babu tsada”

“ Pharmacy asibiti sun ce duk ɗaya, dubu tara ne, ga kuma maganin da suka rubuta
shima sai yaci dubu biyar”

Mama ta rafka uban tagumi.

“Tau ai fa kaji matsalar babbar asibiti, yanzu ina za a samu wannan kuɗin kuma? O
Allah”

Namra ta saci kallon Mardiya da idonta ke kansu, tace

“Mardiya kuje waje ke da Hajara”

Tashi tayi ta fice ita da Hajarar. Sannan Namra ta kalli Mama tace

“Akwai kuɗin da zan siya da su, amman da abinci naso mu siya dan abincin mu ya
ƙare”

Kai Mama ta girgiza

“Wai Namra iyayenki haka zasu zura miki ido, babu wani taimako? Naga dai suna da
shi, amman ko ɗan abincin nan ai sa taimaka muku da shi, amman ace kayi ta sai de
sai de anya haka yayi?”

Wani kallo Namra tayi mata.

“Iyayena sun yi iya ƙoƙarinsu duk kan abuɓda zasu min a yanzu kyautatawa ce, amman
ba dole ba, balle kuma mijina ”

“Haka ne, daman can ai ba son auren su suke ba, sun fi son ku yi ta wahala kamar ba
ƴarsu ba”

“Mama ya kamata ki kina tauna magana kamin furta ta, iyayena, iyayena kuma sun min
komai tun da har suka bar ni na auri Asim”

“Amman idan ga mutunci ai da ke da shi kun zama ɗaya, ki duba kiga ko dubiya har
yanzu babu wanda ya sake leƙowa daga danginku, Kuma wallahi inda wani guri ne dole
ne su ɗauki nauyi naganinsa tun da da motar gidan yayi haɗari, amman sun ɗauki
ƙiyayyar duniya sun ɗora masa akan auren ki kamar wanda ya kashe musu wani abu”

Zuciyar Namra ta kawo sosai, a take idonta ya cika da ƙwalla.

“Asim yayi haɗari da motar gidan mu saboda an rubuto zai yi haɗarin, wai Mama mi na
tare miki ne? Miyasa kike abu kamar wanda bata yarda da ƙaddara ba, miyasa zaki
ɗauki laifin haɗarin motar da Asim yayi ki ɗora min?

Kin manta da ni matarsa ce wace mace ce zata so mijinta ya kasance a halin da Asim
yake? Duk abunda na masa baki gani ba? Mahaifiyarsa ce ke amman sisi ban tambaye ki
na siyer da kayan ɗakina na biya masa kuɗin magani, amman duk wannan be isa a goge
laifina ba? Kin kira aure na da ƙaddara kina tunanin hakan yayi min daɗi? Me kike
son na masa ne? Rai na kike son na cire na bashi ko kuma ciwon kike son na maida
jikina?

Haba Mama ku bar ni na ɗaya mana, da matsalar iyayena zan ji ko da ta mijina, ko


kuma wanda kike ƙoƙarin sani, ke uwace wata maganar be kamata tana fitowa daga
bakin ki”

Mama ta cika da mamakin jin furucin da Namra tayi mata, wani dogon numfashi taja ta
sauke tana taɓe baki.

“Kin goge ladarki Namra, daman kin masa duk abunda kika masa ne dan ki faɗa kin
masa, ai kaji tsiyar taraiya da mai arziki, so kike ace ɗana ya cinye miki komai
ko? A ƙaƙaba masa, kamar yadda aka masa na satar ki ko? Ni da zuciya ɗaya na bar
ɗana ya aure ki ba da wata manufar ba”

Ta ƙarasa maganar da kuka har da hawaye. Uffan Namra bata ƙara cewa ba, sai kawai
ta ɗauki jakarta ta fice.
Sai da ta biya gurin da su Mardiya suke ta karɓi keys sai Mardiya ta biyo ta suka
yi gida tare. Tun a Napep Namra ta soma yi ma Mardiya faɗa.

“Dan me zaki faɗawa Mama na siyar da gado na ? Ina ruwanki da rayuwata tana mijina?
Jaka zaki tallata ni a unguwa? Ko akai na farau? Abunda ya shafi mijina da
mahaifiyata nawa ne babu ruwanki a ciki, dan haka ki iya bakin ki”

Ta ƙarasa dai-dai lokacin da mai Napep ɗin ya sauke su ƙofar gida, Namra ta miƙa
masa kuɗinsa ta nufi gate ɗin ta buɗe ta wuce cikin gidan a fusace. Mardiya ta rufa
mata bayana tana ƙoƙarin wanke kanta.

_______________________________________

Yau yayi kaɗan ko? Bana son na bar ku babu post ne. Idan Allah ya bani iko zan yi
dogon page gobe.
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 27*

NOT EDITED ⚠️

Namra na saka ƙafarta cikin falon Mardiya ta saka nata, ta zauna kusa da Namra ta
marairaice tana ta ƙoƙarin kare kanta.

“Dan Allah ki tsaya ki saurare ni, Wallahi Dillaliya ce ta shigo lokacin da zamu
fita da su, nace mata baki nan shine tace ga cikon kuɗin ki kuma tana son ta ɗauki
gadon, shiyasa har ta ji, idan ma baki yarda ba zan iya zuwa na kira Dillaliyar ki
tambaye ta ki ji”

Namra ta sauke ajiyar zuciya tana son danne fushinta.

“Na ɗauka ke kika faɗa, da nace baki min amana ba”

“Haba Namra nikam miye ruwana da sha'aninku tsakanin ki da miji da yan'uwansa babu
ruwana a ciki. Dama tazo nan babu irin maganar da bata yi ba a kan iyayenki amman
uffan ban ce mata ba, ke ma kuma ban faɗa miki ba”

Wani ɗogon numfashi Namra taja ta sauke, tayi shiru kamar mai nazari.
Mardiya ta tashi tana kaɗe jiki.

“Ni kam na tafi sai wata rana kuma”

Namra ta yi saurin riƙe mata hijabi.

“Haba Mardiya ki yi haƙuri mana, rashin fahimta ne kin ga ai ko kece ba zaki jidaɗi
ba”

“Haka ne amman kin ga zama da rashin aminta da mutum ba daɗi, matsalar mijinki ma
kawai ta isashe ki”

“Shine abunda ya fi damu na, yanzu ma wani maganin suka rubuta min, ina ganin sarƙa
na zan siyar na haɗa da kuɗin da suke hannun dillaliya na siya masa maganin abunda
ya rage mu siye abincin”

Gaban Mardiya yayi dakan uku-uku jin Namra ta ambaci zancen sarƙarta, take taji
natsuwar dake tare da ita ta tafi. Sai ta tashi tana karkaɗe jiki

“Bari naje gida, daga can zan yi ma dillaliya magana nace kin dawo”

“Yauwa dan Allah ki faɗa mata, ai kin san inda ake sai da zinari ko?”

“Gaskiya ban sani ba, amman zan bincika miki”

“Yauwa na gode kin ci abinci ai ko?”

“Eh na ci, sai an jima”

Kamar walƙiya haka ta fice daga falon, zuciyarta kamar zata fito daga ƙirjinta
saboda tsoron kar Namra ta nemi sarƙar ta, bata gani ba, kuma tasan ita kaɗai zata
zarga tun da ita ta saba shigar mata ɗaki.

Bayan fitar Mardiya Namra ta tashi a gajiye ta shiga ɗakinta, tufafin jikinta ta
cire ta ɗauki tawul ta ɗaura ta shiga wanka.
Ta daɗe tana wankan sannan ta fito cike da jindaɗin jikinta, ta buɗe lalulayen
ɗakin kasancewar babu nepa, ta kwanta saman godon ba tare data saka wasu tufafin
ba, saboda gajiya da kuma bachin dake cikin idonta. Nan da nan bachi yayi gaba da
ita.

ANTY AMARYA POV.

“Nifa na damu da rashin kiran Namra, idan an kira ba a samu ita kuma bata kira,
Allah dai yasa lafiya”

“Lafiya ƙalau Inshallah, kin san halin da Asim yake maybe ta siyar da wayar”
Cewar Hindatu tana dannar wayar dake hannunta.

“Amman kin san ba mu kyauta ba? Rashin sake zuwa duba shi da kuma kira a ji ya
jikinsa? Ko a kan Namra ya kamata mu yi haka”

“Toh ai matsalan ba a samun wayarta”

“Ki je gidan su Asim gobe ko anjima ki karɓo min line sa, ko shi mu kira sai muyi
magana da Namra ɗin”

“Amman ba Mamarsa taje Katsina ba?”

“Eh amman ai ba a rasa mai number ba a gidan”

“Zan je anjima inshallah”

Maryam dai na jinsu amman uffan bata ce ba, sai karatun ta take.

NAMRA POV.

Da ƙarfi taji tsawar mota a harabar gidan. Da gudu ta fito daga kitchen ta nufi
gurin da motar take tsaye. Ga mamakinta sai ta ga Asim ya fito daga motar jikinsa
ƙam kamar be taɓa ciwo ba, wani irin tsale ta daka ta dire saboda murna, tana
shirin gudu izuwa gareshi sai kawai wasu karnuka suka taso ta bayansa suka yi
cikinta suna ƙoƙarin cizonta.
Hakan be hana ta gudu da isa gare shi ba, ta rumgume shi, sai kawai taji ya
ƙyalƙyale da dariya ya luma mata wata ƙatuwar wuƙa dake hannunsa. Wani irin ihu ta
saka ihun da bata san har a fili tana yinsa ba. Kirgigi ta farka daga bachin tana
wani irin haƙi da ambatar sunan mahallincinta.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, A'uzubillahi”

Har yanzu jikinta rawa yake, kanta sai rasawa yake, saboda mummunan mafarkin da
tayi. Ta daɗe a haka sannan ta yi unƙurin tashi tana kallon agogon ɗakinta. Har
biyu da rabi ta gota tana bachi bata yi Sallah.
Da sauri ta nufi banɗakin dan yin alwala, kamin ta ƙarasa ta tsaya cak, saboda
abunda ta ji yana zubo mata daga ƙasanta zuwa ƙafafunta, dubarwa da zata yi sai ta
ga jini sare-sare yana zuba kamar an tunkuɗo shi.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un”

Shi ne abunda ta furta da ƙarfi tana mai jin tsoron halin da take ciki, kamin ta
ankaro ta soma jin wani irin mugun ciwon mara marar misaltuwa, a gurin ta zube tada
dafe ƙasan marar nata dake mata wani irin mugun zugi.
Mulmula ta fara yi tana kuka, tawul ɗin dake jikinta ya kwance amman bata kula ba
sai neman ceto take gashi gidan babu kowa.

Sai kusan biyar na yamma hankalinta ya dawo jikinta, har ta gane inda take kwance,
gurin duk ya bace da jini, sai dai har yanzu mararta na mata ciwo da zuji ga wani
uban nauyi da take jin cikinta yayi.
Daker ta unƙura ta shiga banɗakin, nan ma zubewa tayi ƙasa saboda rashin ƙarfin
jiki, haka sare-saren jini ya riƙa fita daga cikinta tana kuka. Bata samu sassauci
ba sai gaf da magariba, sannan ta samu ta tashi ta wanke jikinta ta gyara gurin
cikin rashin kuzari ta dawo ɗakinta ta kwanta ƙasa idonta har wani lumshi suke.

Daker ta iya amsa sallamar da Mardiya da Dillaliya suke, sai dai bata iya tashi ba
har Mardiya ta samu meta a gurin.
Yanayin yadda ta ga Namra yayi matuƙar ɗaga mata hankali, da sauri ta ƙarasa kusa
da ita ta tashe ta zaune.
“Subhanallah, Namra me ya same ki?”

Cikin dauriya da ƙarfin hali Namra tayi mata magana.

“Jini ne yayi min zuba, kuma marana ciwo take sosai”

“Ko ki tashi muje asibiti?”

“Ba zan iya tafiya ba”

“Zan riƙa ki, tashi ki saka tufafin ki muje, kuma dillaliya tana falo tana jiran
ki”

“Ki ce mata ta shigo”

Ta faɗa tana wani irin dantsar baki. Mardiya taje ta shigo da ita. A tsatsaye suka
gaisa da ita ta miƙawa Namra kuɗin tana mata sannu.

“Allah ya sauwaƙe amman gara kuje asibiti, daman nace bari na kawo miki cikon kuɗin
ne, inya so gobe sai na zo na kwashe kayan”

Kai kawai Namra ta iya ɗaga mata, ta juya ta fita tana mata Allah koro sauƙi.
Ƙyar idon Mardiya kan kuɗin da Dilalliyar ta bawa Namra. Namra ma bata kuɗin take
ba ta lafiyar ta take.

“Ki tashi ki shirya bari naje na kira mai Napep”

“Amman za a same su da daren nan? Kin ga magariba tayi kar muje asibitin ba kowa”

“A'a Asibitin Malam Yakubu zamu nan kusa take kuma shi ko yaushe yana karɓar marar
lafiya, musamman irin wannan”

Ta kai Hannu ta ɗauki kuɗin da suke gefen Namra ta saka cikin bed side drawer.

“Bari a aje kuɗin nan har mu dawo”

Bata tsaya jiran abunda Namra zata ƙara cewa ba, ta juya ta fita da sauri. Cikin
ƙarfin hali Namra ta tashi ta saka pad ta zura doguwar riga, ta saka Hijabi ta fito
falo ta zauna, yana sauraren yadda kanta ke tsarawa ga jikinta duk yayi mata babu
daɗi.

Tana haka Mardiya ta dawo.

“Tashi muje gashi can ƙofar gida”

Ta riƙa suka fita tana mata sannu, a hankalin Namra take takawa kamar mai koyon
tafiya har suka isa bakin gate ɗin, da taimakon Mardiya ta shiga Napep ɗin. Sannan
Mardiya ta kalleta tace

“Ina Keys ɗin a rufe gidan?”

“Na manta shi yana can gefen dinning, dan Allah ki ɗauko min jaka na, ki ɗauko dubu
biyar cikin kuɗin nan da Dillaliya ta kawo”

Da Tau ta amsa ta koma cikin gidan zuciyarta cike da saƙe-saƙe. Lokacin data shiga
Kitchen ta fara shiga ta ɗauki ashana, sannan ta shiga ɗakin ta ɗauko jakar data
san Namra na saka atm ɗinta, kuɗi da kuma wasu abubuwan a cikin sannan ta bude
dorowar ta ɗauko kuɗin ta ciri kubu biyar ta saka a jakar Namra, sannan ta ɗauki
sauran ta saka wata ƴar ƙaramar jaka dake jikinta mai kamar pose ɗin tsofi, sai ta
warware zagenta ta ɗaga pant ɗinta sa saka jakar cikin pant ɗinta sannan ta ɗauki
ɗankwalin Namra ta ƙyasta ashanar ta liƙa masa ta jefa saman gadonta.

Sai ta fito da sauri ta ɗauƙi keys ɗin ta rufe falo, sannan ta nufi gate gabanta na
mugun faɗuwa ƙirjinta kamar zai fito.
Nan ma sai da ta tsaya ta rufe gate ɗin, sannan ta shiga Napep ɗin tana miƙawa
Namra jakarta. Har mai Napep ɗin ta tashi Napep ya fara tafiya idon Mardiya yana
kan gidan, zuciyarta cike da wasi-wasi. Namra kam idonta a lumshe yake ta jinginar
da kanta jikin Mardiya tana yadda Mararta ke mata zugi.

KALSOOM POV.

Har ta isa gida tana tunanin abunda zata faɗawa iyayenta, taya zata iya faɗa musu
dalilinta na dawowa gida? Bata samu mafita wata ƙarya da zata musu ba, hakan yasa
taja bakinta tayi shiru duk juyin duniyar nan da Momi tayi akan Kalsoom ta faɗa
mata dalilin na dawowa gida sai taƙi, bata ce shi yace ta dawo gida ba, kuma bata
musu wata ƙaryar ba.

“Bari Dady kun ya dawo idan ni baki faɗa min ba, shi ai kya faɗa masa, haka kawai
ki ɗauko akwati ziƙi-ziƙi ko kunya ki tafo gida, auren an samu daker anyi yanzu
shine kike son ki kashe ko? Tau baki isa ba Wallahi”

Duk irin faɗan da Momi tayi Kalsoom bata yarda ta faɗa mata abunda ya faru ba,
hakan yasa Momi kira Dad a waya ta labarta masa abunda yake faruwa. Cikin ƴan
mintuna ya baro office ya dawo gida. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ya
rufe Kalsoom da faɗa akan ta faɗa masa dalilinta na dawowa gida amman ta ƙi.
Da kansa ya ɗaga waya ya kira Hilal yace yana nemansa, a lokacin Hilal yana tsakar
aiki ne hakan yasa ya nemi Dad yayi masa lamani har zuwa dare.
Daren na yi sai gashi ya zo gidan, a nan ma yayi sallah isha'i, sai fira yake da
Dad kamar Abbansa. Har suka shigo cikin falo sannan Dad yake tambayarsa ko akwai
abunda ya shiga tsakanin su da Namra. Murmushi Hilal yayi ya wayance sosai kamar ba
shi ba.

“Dad ni ai nayi mamakin da kace min Kalsoom ta zo gida ɗazu, dan gaskiya ni ban san
wani rashin jituwa daya shiga tsakanin mu ba, sai dai ɗan abunda ba a rasa ba na
kishi tsakanin ta da abokiyar zamanta, amman kasan rai ajizine ban sani ba ko nayi
mata wani abun da ba zata iya faɗa min ba shiyasa ta kawo ƙarana”

Dad yaja tsaki yana girgiza kai irin nasu na manya.

“Kai sha'anin mata sai haƙuri, ni Wallahi na ɗauka wani abun akayi ma, babu yadda
ba muyi ba amman yarinyar nan taƙi tayi magana”

Dad ya tashi ya shiga ciki gurin kiran Kalsoom. Hakan yasa Hilal gyara zamansa yana
mai jindaɗin da Kalsoom bata faɗi abunda ya faru ba. Dad be daɗe ba sai gashi ya
dawo falon tare da Kalsoom da Momi.
A kujera ɗaya ya zauna da Momi Kalsoom kuma ta zauna ƙasa kusa da Momi.

“Tau gashi nan shi dai yace be san wani abu ya shiga tsakanin su ba, ke sai ki faɗa
idan akwai abunda yayi miki wanda be sani ba, ko kuma yayi miki shi cikin kuskure”

Ɗagowa tayi ta kalleshi, shi ma sai ya tsare ta da manyan idonsa, har sai da taji
ba zata iya ɗaukat kallonsa ba, ta kawair da nata idon. A hankali ta kira sunan ta.

“Kalsoom, Dan Allah kiyi haƙuri ki yafe min, idan har akwai abunda nayi miki a
cikin rashin sani ko da kuskure, koma da gangan kin san ɗan'adam aziji ne”

Ji tayi kamar yasa sarƙa ya ɗaure dukanin ilahirin jikinta, sai ta kasa sake ɗaga
ido ta kalleshi, kuma ta kasa furta komai. Har Dad ya gama faɗansa da yake mata
akan zamantakewar aure da haƙuri. Momi ma ta ɗora da nata sannan suka tashi suka
basu guri.
Tasowa yayi daga inda yake zaune ya zauna ƙasa kusa da ita jikinsa na gogar nata,
yasa hannunsa ya riƙe nata, fuskarsa kuma daf da nata ta yadda suna iya shaƙar
numfashin juna.

“Babe tashi muje gida, na gode sosai da baki faɗawa Dad abunda ya faru”

“Ba zan iya bin ka gida ba, saboda ka riga ka furta duk ban biya ka ba, a bakin
igiyar aurena”

“Kuskure na, na san nayi amman dan Allah ki yi, ba zan sake ba”

“Ni ba zan zauna ba, ai ka riga ka nuna kuɗin sun fi rayuwar aurena daraja”

“Shiiiiiiiiiii”

Ta ɗora lips ɗinsa saman nata, yana goga mata hancinsa.

“Ba haka nake nufi ba, zuciya na ne ya kawo har nayi wannan furucin kuma yanzu ina
nadama”

Kawarda fuskarta tayi ta unƙura zata tashi, sai ya danneta da dukan ƙarfinsa.

“Don't try me, ba ki da wannan karfin bana son Dad da Mom su san halin da muke
ciki, dan Allah Kalsoom kiyi haƙuri idan ma zuciyarki bata natsu ba, idan mun koma
zaki iya biyana”

Be sake ta ba har sai da yawun bakinsu sukayi taraiya. Sannan ta tashi ta koma
ciki, shi kuma ya fito waje yayi ma Dad sallama. Ita kuma ta ɗauko akwatinta ya
karɓa ya saka a mota sannan suka tafi.
Tun da suka kamo hanya ta kalli inda take yake ba, idonta na kam gefen gilashin
motar gurin ti-ti. Murmushi yayi ya kai hannu ya shafi fuskarta.

“Na san abunda na yi ban kyauta ba, amman dan Allah kiyi haƙuri, i love you so
much”

Uffan bata ce masa ba, bata kuma sakar masa fuska ba, har suka isa gida. Shi kuma
duk ya damu, wani irin sha'awarta yake jin tana masa yawo a jiki ga shi be ga
alamun sauƙi a tare da ita ba.
Suna shiga cikin falon ta wuce ɗakin. Yayi kamar ya bita sai kuma wata zuciyar ta
hana shi, sai kawai ya nufi ɗakin yaransa inda yake jin ihunsu. Da gudu suka zo
suka rumgune shi.

“Eyyyy Daddy welcome”

Ɗaya bayan ɗaya ta riƙa shafa kansu, daga bisani ya kai hannu ya ɗauki Rafiq ya
rumgume.

“Daddy Ammyn Rafiq ta fita wai gurin aikinta suna nemanta, tace mu zauna har ka
dawo”

Ezzah ta faɗa tana wasa da ribon ɗin dake hannunta.

“Kuma tace idan ka tambaya mu faɗa maka ita ce ta ɗauki kuɗin dake cikin closet na
ka”

Wani irin abun ɓacin rai ya taso yayi matsa tsaye a zuciya, yana auna irin rainin
da Rashida tayi masa, taya zata fara yi masa abunda bata saba ba har tasa ya zargi
Kalsoom.
Rufe ido yayi saboda wani mugun ɓaci rai da yaji ya rufe shi,

“Daddy are you okay?”

Yayi murmushin ƙarfin hali yana kallon Ezzah.

“I'm fine, Kuje ɗakin Anty ku ta dawo”

Da gudu suka nufi ɗakin suna ihu da murna.


Kamar zasu ɓalla ɗakin haka suka tura ƙofar ɗakin Kalsoom suka shiga suna mata
sannu da zuwa. Yanayin yadda suka ga Kalsoom tayi musu da fuska yasa suka yi tsaye
cirko-cirko suna kallonta.
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

Meaning of POV. Point of view: used especially in describing a method of shooting


a scene or film that expresses the attitude of the director or writer toward the
material or of a character in a scene.

*PAGE - 28*

NOT EDITED ⚠️

“Bana ce ku daina shiga ɗaki da gudu ba? Ban hana ku ban kar ƙofa ba? Sai kace
ball”

Duk kama kunnensu suka yi kamar yadda ta koya musu.

“Auntie we sorry”

“Sorry for yourselves, aya kowa ya riƙe ƙafarsa ɗaya”

Duk dariya suka saka suka rumgume.

“Allah kuwa ba zamu sake ba, Auntie da baki nan Ulfah tace Dady ya siyo mata
takeaway”

Ezzah ta faɗa tana zare idon, sai murƙususu take kamar ta shige jikin Kalsoom.

“Ke kuma kika yi faɗa da wata a School”

“Eyye 2+2 kowa taje ta kama ƙafarta na ce”

“A'a ai kince ba zaki sake mana horon dare ba, yau mun yi missing ɗin ki Auntie ina
kika je?”

“Wani guri na je”

Ta faɗa tana jan hancin Ulfah, har ga Allah tana son yaran, haka take jin su kamar
itace ta haifi su, sam basa sakewa da Mamarsu kamar yadda suke sakewa da ita,
saboda ta kan basu lokacin ta.

“Aje a kwanta gobe akwai makaranta, kar a makara”

“Okay Auntie”
Duk kiss suka mata a gefen fuska sannan ta shafa kan su.

“Idan za a kwanta a yi alwalah, Ezzah ki yi addu'ah sai kiyi ma Ulfah, ke kuma


Ulfah kiyi ma Rafiq, kuma zan shigo na ga wanda ya kwanta ba dai-dai gobe akwai
kama ƙafa”

Ulfah ta tsuke baki ta girgiza kai

“A'a bana so yawunta be da tsarki”

Dariyar Hilal ce ta ɗago ta duka hankalinsu izuwa garesu, ashe yana tsaye jikin
ƙofa yana kallon su.
Kalsoom ta ɗan sha masa mur, irin har yanzu fa fushi nake kai, ta kalli yaranta.

“Good night sweethearts”

“Good night Sweet Auntie”

“Ku saka kayan bachi, sauran ku watsar da wannan kayan idan kun cire”

Dariya kawai suka yi, suka je suka ma Daddyn u sai da safe suka fice. Shi kuma ya
mai da ƙofar ɗakin ya rufe ya nufo ta yana murmushi.

“Yanzu shi kenan, daga fitar su sai kuma ki ɗaure min fuska, ni da su waya fi
cancanta da far'ar nan naki?”

“Su kasan ana canja miji ba a canja ƴaƴa ba”

Dariya yayi ya rumgumota.

“Haba ni da nazo miki da albishir kuma”

Ta tsire baki tana ƙoƙarin zamewa daga jikinsa.

“Wallahi da gaske na ke, nayi shawara zan fara baki 50k duk month, tun da ita
Rashida aiki take, ina ganin kamar ban yi adalci ba idan na bar ki haka”

“Dan Allah da gaske”

Ta tambaya cikin murna da jindaɗi, sai kawai ta saki jiki ta rumgume shi.

“Yauwa yanzu da kika ji maganar kuɗi sai na samu rumguma ko? Ko kunya baki ji ba”

Ta rufe kanta cikin ƙirjinsa tana dariya.


Duk wannan maganar da Hilal yake Rashida ya tsaye jikin ƙofa tana jinsa, wani
ƙashin baƙinciki ne ya taso ya zo yayi mata tsaye a wuya, har ta kasa jurar tsayi a
gurin ta wuce ɗakinta.
Har ta cire tufafin da suke jikinta, tsanar Kalsoom sai ƙaruwa yake a ranta, gani
take duk ta zo cikin gida ta hana ta tsukuni ta ƙauce mata miji. Tawul ta ɗauka ta
shiga bathdroom tayi wankan tsarki sannan tayi na sabulu ta ɗora da alwalah ta
fito. Ta rama sallah magariba sannan ta yi na Isha'i.

Sai kusan goma saura Hilal ya leƙa ɗakinta. Ƙiri-ƙiri tayi kamar bata ganshi ba, ta
cigaba da chatin ɗin da take a waya. Shi kuma ya tsaya a kanta.

“Bayan kin dawo aiki sai kika sake fita baki faɗa min”

“Amman ai kasan idan ba aiki ba, babu abunda zai sake fitar da ni ko? Kuma na ga
kai ka bani damar nayi aikin, ita wacan da yake ƴar gatan ka ce ai sai ka hanka
mata albashi tana zaune a gida ko?”

Murmushi yayi mai sauti.

“Kalsoom bata nufin komai dake sai alheri, ki duba kiga yadda take kula da yaran
nan, ke kanki baki kula da su haka, a ganin ki kema kan ki be ci ace kin yanka mata
albashi ba, naga ke kina aikin ai”

“Ƙwarai aikin kam yanzu na fara saboda abunda mahaifina ya koya min kenan, be nuna
min na zauna a nema a bani ba nima na san Freedom ɗina”

“Good of you, amman idan har aikin yana da rana a gare ki be kamata ki saka hannu
ki ɗaukar min dubu ɗari uku ba ba tare da sani ba, bayan kuma babu nauyin da ban
ɗauke ba na cikin gidan nan, kin san iya abunda na aikata a rashin ganin kuɗin
nan?”

Cikinsa tayi da masifa tana kuka.

“Ka yi min duk abunda zaka yi Hilal, ka kira ni da ko wane irin suna ka siffanta ni
da duk sunan da yayi maka a duniyar nan, saboda kayi amarya, daman haka halin ku
yake a duk lokacin da kuka aure mune abun wulaƙantawa, mune banza mune wofi”

Kallonta yake har ta gama faɗan ta koma gefen gado ta zauna tana cigaba da kuka.
Sai ya sassauta zuciyarsa, duk wani abu da yake ji sai ya aje shi gefe, ya zauna
kusa da ita ya jata ya rumgume.

“Bana da niyar wulaƙanta ki dan na yi aure Rashida, i love you so much”

Ƙara narkewa tayi.

“Hilal ina kishin ka, ina kishin ka kwana da wata Mace ba ni ba, Hilal i can't deny
it and i can't take it, please divorce her Hilal”

“I can't and won't, ita amana iyayenta suka bani, son da nake miki ba zai sa na
rabu da ita ba a kan ki, ke ma kuma ba zan miki haka ba, so karki yaudari kan ki”

Ganin ba zata daina kukan ba, yasa ya ɗaga ta ɗaga jikinsa, ya tashi cikin rashin
daɗin rai ya nufi ɗakin Kalsoom.

NAMRA POV.

Sun yi sa'ar samun likitan har ya duba ta, ya sanar mata ciki ne amman ta samu
miscarriage, ya rubuta mata gani da allurai sannan ya bata gado. Sai bata yarda ya
kwanta ba sai tace mishi sai taje ya faɗawa mijinta. A cikin asibitin ta siye wasu
maganin nikan.
A bakin gate ɗin suka samu Napep, Namra kamar jira take, suna shiga ta fara kuka.
Ita sam bata jidaɗin ɓarewar cikin ba, gashi har yanzu zugi mararta take mata.

Ba karamin ƙarfin hali Mardiya tayi ba, wajen bata haƙuri dan ita gaba ɗaya
hankalinta ya tattara ya koma gida, zuciyarta sai yaye yaye take mata. Ita kanta
tana jin bata kyauta ba idan har gidan Namra ya ƙone, sai dai bata da mafita sai
wannan.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ”

Ta furta a razane lokacin da mai Napep ya sauke su cikin jama'ar da suke gurin. Da
sauri Namra ta buɗe idonta dake rufe ta fito daga Napep ɗin ta nufi gida a ruɗe.
Mardiya ce ta sallami mai Napep ɗin ta rufa mata baya, tana ta innalillahi. Haka
Namra ta ƙira kusa mutane da suke tsastsaye suna kallon wutar, har ta shiga cikin
gidan. Da sauri wani daga cikin yan fire service ya tare ta sai matan unguwar suka
zo da gudu suka riƙe ta.
Wani irin fisge-fisge take take tana son ta kuɓuce ta shiga cikin wuta, sai ɗakinta
take nuna musu tana wani irin kuka mai ban tausayi.

Wani irin tuma take tana direwa ƙasa, kamar sabuwar mahaukaciya. Sai kuma ta koma
can gefe ta rumgume kanta, jikinta sai rawa yake kamar mai sabon fever.

“Allah na gode maka Allah, mijina ya kare, cikina ya ɓare yanzu kuma gidana ya
ƙone, Allah ka sassauta min haka nan Allah, Allah ka yafe min na san ni mai yawan
zunubi ce mai yawan saɓa maka Allah”

Wani irin ajiyar zuciya ta sauke sai jiri ya kwasheta, ta soma ganin mutane biyu-
biyu sai ta jinginar da kanta, tana numfashi a hankali. Mardiya na can gefe tana
kuka sosai, kamar gidan nata ne ya ƙone, idonta har ya kumbura ya daina hawaye.
Haka wutar ta ci ta cinye, ba a samu nasarar kasheta ba, sai da ta ƙone ilahirin
gidan gaba ɗaya, ya rage saura BQ kawai. Har kuma lokacin Namra sama-sama take
ganin mutane, komai ya zame mata kamar mafarki, yanzu kam bata da gabas bata da
yamma, bata da madafa, bata da mafita sai ta Allah. Gashi babu abunda ya fita nata
sai tufafin da suke jikinta.
A tunaninta kuɗin da Dillaliya ta kawo mata ya ƙone, ga sarƙarta ga tufafinta kayan
ɗakinta da kayan kallo freezer da sauran kayan kitchen, yanzu bata da komai sai
rai, gashi lafiyar jikinta ma bata isheta ba.

Mutane sun yi ta bata haƙuri suna nuna mata yarda da ƙaddara, da mata fatan Allah
mai da alheri, a gidansu Mardiya ta kwana, ba kuma dan kwanan bachi ba, dan a zaune
ta kwana, tana jinjina lamarin Ubangiji.
Da safe Mahaifiyar Mardiya ta siyo mata koko da ƙosai, Namra ta kasa sha, ta aika
a siyo mata tea shima ta kasa sha. Sai tayi zaune jigum, tunani ya taru yayi mata
tsaye a rai.

Tunanin yadda zatayi da Dillaliya, da kuma yadda zata faɗawa Asim gidansu ya ƙone,
bata tunanin faɗawa Anty Amarya, saboda a ganinta sun juya mata baya, ita kuma ta
ɗauki alƙawrin ba zata sake nuna musu tana buƙatar wani abu ba.

Sallamar Dillaliya sata ta razana sosai, kamar ance mata ga baƙon mutuwa. Sumi-sumi
Dillaliya ta shigo ɗakin fuskarta ɗauke da damuwa da kuma tausayi.

“Allah sarki Baiwar Allah, haka Allah ka kawo miki wannan ƙaddarar ke kuma?”

Ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zaunawa. Idon Namra ya cika da ƙwallah.

“Kin dai gani, duk abunda Allah ya kawo ba a iya guje mishi, Wallahi komai ya ƙone”

“Haka na ji ƴar nan, ai ni jikina duk yayi sanyi na haɗa ɗan jarin na miƙa miki har
da kuɗin mutane gashi komai ya ƙone”

Ta fara hawaye. Dubu biyar ma Dillaliya jin su take kamar ranta balle har dubu ɗari
uku da hansin.

“Ni ko yau ina zan samu wannan kuɗi, ba kaya ba kuɗi mutane ba haƙuri ne da su ba,
yanzu wanda na karɓar wa kuɗin nan ba yafewa zata yi ba, nima ɗan jari masu son
ganin baya na yau burinsu ya cika, na shiga uku na lalace”

Namra tayi mata wani kallo wanda ita ka ɗai ta san fassararsa.

“Allah satki Dillaliya, ke dubu ɗari uku kawai kika rasa, ni ko mijina ya karye
cikina ya zube yanzu kuma gidan ya ƙone gaba ɗaya komai be fita ba, kuma yanzu ki
zo kina min wannan maganar, ba sai kin yi lunƙe-lunƙe ba, ki kwantar da hankalin ki
zan biya ki, sisinki ba zata yi ciwon kai ba Inshallah”

Namra ta ƙarasa maganar da kuka. Wani daɗi da Kunya ya lulluɓe Dillaliya a lokaci
ɗaya, daman ita tana ganin alamu tasan Namra ƴar masu kuɗi ce, kuma haka da Namra
tace ya ƙara tabbatar mata da zancenta. Sumi-sumi ta tashi tana share hawaye.

“Ba haka bane ƴar nan, Allah dai ya sassauta miki amman ba shine nufi na ba”

Tana ficewa Namra ta rafka uban tagumi tana tunanin rayuwarta. Babu wanda ta faɗo
mata a rai sai Hajiya Saratu matar data taimaketa lokacin da Asim be da lafiya, sai
dai zuciyarta bata yarda da zata taimaketa dan Allah ba. A ɗayan ɓangare na
zuciyarta kuma Anty Amarya take tunani, su biyu nan sune kawai mafitar ta a rayuwa.

KALSOOM POV.

Kwana biyu nan ta miƙa lamarinta ga Ubangiji, nafila dare da Karatun suratul yaseen
da Salma ta faɗa mata shi kawai ta sawa gaba.

Yau ma da wuri ta tashi ta shirya musu komai na karya. Amman Rashida bata tsaya
karyawa ta fice, yara kuma tasa musu nasu a kula suka tafi makaranta.

Sai da ta sawa Hilal ruwan wanka yayi wanka sannan suka fito dinning sai tsokanarta
yake.

“Ni duk gajiyar da ni, sai fama nake, Allah dai yasa ina da juriya ba zan iya zama
da ke ba”

Ya kashe mata ido ɗaya, yana ƙoƙarin zaunawa saman kujera. Ita kam ido ta sakar
masa tana kallon ikon Allah, daman yasan abunda zata faɗa ne shine ya rigata faɗa.

“Kai dai Allah be raba ka da abun magana ba”

“Ba wani magana sai gaskiya kema ai kin san ina ƙoƙari in ba haka ba ai sai abun
yayi min yawa”

Dariya kawai tayi ta cigaba da haɗa masa tea. Shi kuma ya kwantar da kai yana
kallon rigar bachinta dake buɗe.
Tana gama haɗa masa tea aka buga ƙofar falo, saurin miƙewa yayi yana faɗin bari na
duba, dan nasan ki da shegen salo zaki iya cewa bari ki duba, har wani yaga
halalina.

Kai kawai ta girgiza tana dariya, shima dariyar yake har ya isa gaban ƙofar ya
buɗe.
Mai Gadi ne jikin ƙofar riƙe da wani farin abu kamar wasiƙa, ya miƙawa Hilal.

“Alhaji, gashi aka ce a bawa Auntie su Ulfah”

“Waya kawo?”

Doc. Ya karɓa yana tambaya.

“Wani ne a mota har ya tafi ma”

“Okay”

Ya mai da ƙofar ya rufe. Sannan ya juyo ya nufo dinning inda take Kalsoom take
zaune yana faɗin.
“Ga saƙo aka ce a baki”

“Saƙon me?”

“Oho sai kin buɗe”

Sai da ya zauna sannan ya miƙa mata. Ita kuma ta karɓa da hannu biyu, ba tare da
fargabar komai ba ta yage takardar.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Da sauri ta miƙe tsaye tana zaro ido, sai hotuna suka faɗo tare da kofin tea dake
gabanta.

“Subhanallah”

Hilal ya faɗa lokacin da idonsa ya sauka kan hotunan.

____________________________________________

#Share
#Comment
#Candy
#Blog
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 29*

NOT EDITED ⚠️

Shiru-shiru Mama bata aga an kawo musu karin safe ba, gashi har rana tayi kuma babu
wani labari, ga yunwa tana ji ita da Asim.
Dan yauzu sauki ya fara zo masa yana son abinci sosai har fira ya kan yi sama-
sama.

“Hajara tashi na baki kuɗin achaɓa ke je ki karɓa mana abinci wata ƙila na yanzu
zata zo ba,marar lafiya kuma sai da abinci, wannan zunzunzun ba amo ba labari,
Ko tana nufin ba zata ake zuwa asibitin bane dan nayi magana?”

Ta ciro naira hansi ta miƙawa ƴarta Hajara.

“Ungo idan kin je ta baki na dawowa”

Da kallo Asim.ya bi ƙanwar tasa, sai da ta fice sannan ya kalli Mama yace

“Wallahi ko maƙiyinka ya faɗa a hali dana shiga sai an tausaya masa, ki duba ki
gani ace ina sirikin su amman har yanzu ba su sake zuwa duba ni ba, ai ko wani na
kashe musu sa duba ni tun da ƴar su nake aure”

“Hmmm ai Wallahi mutane nan basa son ka da alheri, su fa basu ƙi ka mutu ba, nifa
ina zargin kamar ma da sa hannunsu a haɗarin nan da kayi”

“Nima haka nake tunani saboda lokacin dana je karɓar motar sai da suka sa Direban
su, ya duba motar gaba da baya sannan aka ba ni key ɗin, sannan idan har ba plan ba
taya daga haɗari mota zata kama da wuta haka kawai”

“Ato nifa na faɗa maka ba su ƙi ka mutu ba, sai ƴarsu ta auri wanda take so, daman
can ba a banza aka baka ita ba”

“Amman Namra sai naga kamar tsakani da Allah take so na”

“Hmm ai wannan hidumar da tayi maka, saboda itace silar komai shiyasa tayi maka,
kuma yanzu kaga ta kama kayan ɗakinta ta sai da dan ace kai ƙa canye komai sai a
fara cewa ta sai da komai dalilinka, ai ba zata rasa kuɗin da za'a maka komai a
bankinta ba amman ta zaɓi ta siyar da kayan ɗakinta ai kasan da walakin goro a
miya”

“Kayan ɗakinta ta siyar?”

Ya tambaya a wahale dan ciwon kan ya fara dawo masa.

“Eh ba shine ka ji jiya ina magana ba, har kake ganin laifina”

Shiru yayi be sake magana ba, sai ciwon kan yake saurare.

NAMRA POV.

Ta ci kuka sosai har sai da ta goɗe Allah, ba tare da ta bari kowa ya gani ba, dan
wuni tayi a ɗakin su Mardiya, duk wanda ya zo mata tanzanko sai yayi mata a cikin
ɗakin ko kuma daga bakin ƙofar.

Guraren Uku da rabi Hajara ta shigo ɗakin da sallama, Namra ta amsa mata murya can
ƙasa-ƙasa.

“Wa'alaikissalam Hajara”

“Na'am Anty naje gidan naga duk ya ƙone aka ce min kina nan”

“Wallahi jiya ne muna dawowa daga asibiti muka tarar ana kashe wutar”

“O'o wannan abun be yi daɗi ba, nima Mamace tace na zo na karɓo abinci tun safe
bata gan ki ba shiru, ashe abunda ya faru kenan, Wallahi ba mu sani ba”

Ta faɗa cike da tausayawa.

“Ina Asim ɗin yaji sauƙi?”

“Ya samu sauƙi sosai ɗazu ma har fira muke yi da shi, har shi ma yace na zo na
karɓa abincin”

“Bari na baki ƙuɗi ki siya masa na hanya”

Ta tashi cikin rashin kuzari, suka fita a tare daga cikin ɗakin. Kular Maman
Mardiya ta ara tana cikin wanke wa, wata maƙociyar su ta shigo tace kiran Namra.

“Kin yi baki masu gida sun zo su duba gidan su”

A take ta aje wankin kular da take ta gyara tsayin Hijabinta ta fita. Manyan motoci
ne fake a ƙofar gidan.
Cikin faɗuwar gaba ta nitsa ta shiga cikin gidan tana musu sallama.
“Wa'alaikissalam ke ce matar gidan?”

Hajiyar ta tambaya tana cire gilashin dake zaune a idonta.

“Eh Nice ance masu gida sun zo”

“Eh ina mai gidan na ki?”

“Yana asibiti ba shi da lafiya ne”

“Ayyah so sorry, amman kin san musabbabin tashin wutar ne?”

“A'a wallahi nima asibiti naje ko da na dawo na tarar wuta na ci”

“Allah sarki Allah ya maida alheri, daman mun zo ne mu duba ance muna anyi wuta”

Ta faɗa tana picking ɗin wayar dake hannunta.

“I'm my way Abdool, har na ga gidan ma”

Sai kuma tayi dariya, ta kashe wayar. Tasa hannu a jaka ta ɗauko kuɗi masu ɗan dama
ta miƙawa Namra.

“Ga wannan Allah ya tsare gaba”

Har ƙasa Namra ta ɗuka mata.

“Na gode Allah saka miki da alheri”

Murmushi farar Hajiyar tayi

“Ba komai”

Har gaban mota Namra ta raƙa ta ta shiga motar ta wuce, sannan Namra ta koma gidan
ta ɗauki kular da plates da cibi, suka fito ita da Hajara.

A bakin titi ta siya musu shinkafa da miya da nama na 1k. Sannan suka tari Napep
suka hau.
Daga ita har Hajara sululu suka shiga ɗakin, kama kamar ita dake ta sun-sun da kai
bata son a ga kumburin dake fuskarta.

Sai da ta gaisa da Mama sannan ta nufi gurin da Asim yake ta zauna, yana kallonta.

“Ya jikin ka?”

“Alhamdulillah”

“Likitan ya duba...”

Jin abunda Hajara take faɗa yasa ta kasa ƙarasawa. Mama ta ɗora hannu a ka, tana
faɗin

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Asim kuma ya kalli Namra cike da tashin hankali. Ita kuma babu abunda take sai
kuka.

“We lost everything Asim, i lost my baby, shine naje asibiti ko da na dawo na tarar
gidan ya ƙone”

Rumtse ido Asim yayi, zuciyaraa ɗauke da abubuwa biyu, jindaɗin ɓarin da tayi, da
kuma baƙincikin ƙonewar da gidan yayi.
Ringing ɗin wayar Asim dake hannun Mama ne yasa ta share munafukan hawayenta ta
danna picking tana kara wayar a kunne.

“Wa'alaikissalam.
Lafiya ƙalau
Alhamdulillah”

Shiru ta ɗan yi kamin tace

“Allah sarki. Namra karɓi ga Maman ki”

Hannu Namra ta kai ta karɓa sai ta fice daga ɗakin. Mama ta kalli Asim cikin ruɗu
tace

“Ibrahim idan kaji sauƙi ka rabu da yarinyar nan, ina ganin babu alheri a zaman
auren ku, wannan irin bala'i haka”

Shi dai be ce mata komai ba, shi ta kansa yake abunda duk yake tunanin zai zame
masa alheri yana ƙoƙarin koma masa sheri.
Yanzu da wannen zai ji ciwon jikinsa ko wannan rashin da suka yi?

“Kuma ina ganin abunda yafi kawai ku koma gida, a can ma dole ta samu wani abu
saboda a gaban iyayenta take”

Har lokacin be ce komai ba, Hajara tace

“Ni Wallahi duk ta bani tausayi”

“Ai ba itace abun tausayi ba, Yayanki ne shi da ba shi da kowa sai Allah ita kau
har iyayenta suna da abun hannun su”

“Ita ai da tausayi Wallahi”

“Hmmm Allah dai ya kyauta kawai”

Namra na fita ta ƙara wayar a kunne tana dda ƙoƙarin gyara muryarta kar Anty Amarya
ta gane tana cikin damuwa.

“Anty”

“Na'am Namra y jikin mijin na ki”

“Ya ji sauƙi”

“Allah ƙara lafiya Wallahi Abbah kin ya hana na dawo duba shi, ko jiya sai da nayi
masa magana sai ma masifa ya riga min, Abban ki ya kira ki?”

“Ba komai ai yaji sauƙi, be kira ni ba wayana ya faɗi ban sani ba ko ya kira”

“Har yanzu baki daina halin ki na sakarci ba ko? Ya faɗi ko dai kin siyar?”

“Wallahi faɗuwa yayi”

“Namra ki yi hankali da mutane, ba kowa ne yake son ya gan ka a cikin alheri ba,
wani yana baƙincikin yaga kana jindaɗi, wasu fa hassadarsu ba ƙarama bace, kowa
abunda yake ƙoƙarin yi ya ture ka daga jindaɗin shi ya shiga, ko kuma ya ture ka
duk ku rasa, ba kowa bane zai so ki tsakani da Allah ba, idan kina da shi kowa naki
ne, sai ranar da kika rasa komai zaki gane masu son ki da gaskiya

Wani ƙiyayyar tasa a ɓoye take ba zaki taɓa ganewa ba, haka zai ta miki zagon ƙasa
har sai ya ga kin rasa komai sannan hankalinsa ya kwanta, dan haka kiyi tunani
sosai da duniya, idan baki da hankali mutanen duniya za su miki shi, ki rage damuwa
a ran ki ki sawa ran ki sassauci”

“Na gode Anty”

Ta faɗa har cikin ranta, kalaman Anty sun mata daɗi, sai dai tasan ba kowa Anty ke
nuna mata ba, sai Asim dan tana tunanin kamar da biyu ya aureta, gani take har
yanzu Anty bata yarda da Asim ba.

“Allah ya ƙara masa lafiya, na kira wayarki ban samu ba, shine Maryam ta karɓo min
number Asim”

“Eh ai naga line Maryam ne, na gode sosai”

“Tau Sai anjima”

“Okay

Daga haka suka yi sallama. Wayar na yankewa wa Namra ta tsara text ta tura mata
Anty Amarya a wayar Maryam.

“Maryam... Zo ki karɓi wayar ki”

“Na'am”

Ta aje system dake jikinta, ta taso ta nufo ɗayan ɓangaren inda Anty Amarya take.
Tana karɓar wayar text na shigo, Anty Amarya bata kula ba, ta miƙa mata wayar ta
nufi gurin sha'aninta.

_Anty ina cikin matsala, bana iya faɗa miki a waya nasan faɗa zaki min, dan Allah
ki taimaka min da kuɗi ko kaɗan ne_

Maryam ya gama karanta saƙon taja wani dogon tsaki ta danna deleted ta goge saƙon.

“Ai fa kullum haka zai riƙa saki kina yi, tun da yaga be samu abunda yake so ba,
kai mutanen duniya nan da abun haushi da mamaki suke, ala dole dan auri yar masu
kuɗi kai sai kayi arziki, to sai kaje ka ci ubanka, ya mayar da ita saniyar tatsa”

Ta koma mazauninta tana mai jin haushi Namra da Asim ɗin.

KALSOOM POV.

Hilal na kallonta ta girgiza masa idonta da hawaye.

“Wallahi ban aikata ba, ban san wannan mutumen ba Wallahi”

Hannu Hilal ya kai ya ɗauki hotunan yana kallo. A-uzubillah hotunan babu kyau
kallo, Kalsoom ce tsirara ita da wani, wani gurin yana kissing ɗinta wani gurin
kuma tana kissing ɗinsa.
Ɗaya bayan ɗaya ya riƙa duba hotunan har ya gama sannan ya kalleta yace
“Kin san wannan mutumen”

“Wallahi ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba”

Ta faɗa da kuka.

“Daga ganin wannan ma ai haɗi ne, i trust my wife's ba zaki aikata irin wannan abun
ba, duk yadda akayi wannan abun shirya sa akayi”

Ta ƙara fashewa da kuka

“Wallahi sheri ne kawai, na rantse da Allah ban taɓa ganin wannan mutumen ba”

Shiru Hilal yayi kamar mai nazari.

“Ina suka samu hoton ki?”

“Wallahi ban sani ba, dan Allah ka yarda da ni Wallahi sheri ne”

“Na yarda sheri ne, daga gani ma ai kasan haɗi ne, daɓ ga fatar fuskar ta banbanta
dana jikin hoton, kuma miyasa ba a kawo lokacin da bana nan ba, sai da ina nan? za
a iya haɗa irin wannan hoton a computer? But i can't believe is taya suka samu
hoton ki?”

“Wallahi ban sani ba”

“Baki sani ba kamar ya? What kind of nonsense is this? Aljani za a turo ya ɗauki
hoton ki ko me?”

Durƙushewa tayi ƙasa tana kuka.

“Wallahi ban sani ba Hilal na rantse da Allah ban aikata ba”

“Naji baki aikata ba, faɗa min ta ina suka aka samu hoton ki?”

Ya faɗa a tsawace irin zuciyarsa ta fara kawowa ɗin nan.

“Wallahi ban sani ba, ni ban turawa kowa hotona ba”

Ɗuƙawa yayi a hasale ya kwashe hotunan ya nufi ɗakinsa da su. Wani irin zugi
zuciyarsa ke masa, baƙin kishi ya taso masa.
Haka ya tiƙa duba hotunan kamar wanda zai haddace su, shi dai what he believe
Kalsoom ba zata aikata haka ba, sai dai kuma kansa ya ɗaure har yana jin tunaninsa
na ƙoƙarin canjawa.

Bedside drawer sa ya buɗe ya zuba hotunan ya rufe, sannan Shirya cikin ƙananan kaya
ya feshe jikinsa da turare ya ɗauki atms ɗinsa ya saka a aljihu da wasu ƴan canja,
sannan ya ɗauki wayarsa da keys, ya fice daga ɗakin fuska babu annuri.

Sheshekar kukanta ya ɗago da hankalinsa i zuwa gareta, ashe duk tsawon lokacin tana
a gurin tana aikin kuka, jikinsa ya mutu yaji ba daɗi ganin kamar shine silar
hawayenta. Ƙarasawa yayi kusa da ita ya ɗafa ta

“Kalsoom Calm down, nima fa wayayyen mutum ne nasan za a iya haɗa wannan, amman kin
ƙi ki bawa zuciyata damar yarda da hakan”

Ɗagowa tayi ta kalleshi tana kuka fuskarta da majina nashe-nashe.


“Wallahi ban sani ba, ni ban turawa kowa hoto na ba”

“Kina da grp ɗin da kika chat da maza ko?”

Ta ɗanyi shiru tana tunani.

“Grp ɗaya ne, shima kuma na koyon sana'ah ne, kuma ban taɓa magana a grp ɗin ba
Wallahi, Instagram ɗina da Facebook tun da nayi aure ban sake hawan ko ɗaya ba
Wallahi”

“Good indeed, kina instagram ba? Kina facebook?”

“Amman tun da nayi aure ban sake shiga ba”

Zaunawa yayi kusa da ita yana cire password ɗin wayarsa.

“Ba ni handle ɗin ki”

“Kalsoom_Miss-Arewa”

Instagram ya shiga yayi searching sunanta, sai ga account ɗinta. Yadda ya riƙa
ganin hotunan ta sai wani baƙin kishi ya motsa masa.

“Duba nan, yanzu miye amfanin waɗannan hotunan? Kina tallar kan ki kamar ba mace
ba, miye abun burgewa a sakin jiki wasu mazan na kallo, ke a ɗaukar ki duk wayewa
ce ko? Dole ne sai kin sa hotunan ki a instagram ko facebook?”

“Wallahi ni ba da wata manufar na yi ba”

“Nasan ba wata manufar kika yi ba, su yanzu waɗanda suke da wata manufar ai sun
ɗauka sun yi yadda suke so da shi. Duk abunda addini yake hana ƙu baku ganewa, duk
abunda kika ga musulunci yace a bar shi barin shi yafi alheri amman baku ganewa,
dubi wannan abun wani gurin ma ai rabin jikin ki a waje, ba editing kaɗai ba har
asiri sai a ɗauki hoton ki ta nan aje a miki”

Yaja tsaki yana mai miƙewa tsaye.

“Kamin na dawo ki tabbatar kin goge duka hotunan ki da suke facebook da Instagram,
ban hana ki yin chat ba amman ban yafe ki yi da wani namiji ba da aurena, duk mazan
nan nan friends ɗin ki yi unfriend ɗin su, kuma Wallahi kar na sake ganin hoton ki
a social network”

“Wallahi ni daga yau ma na daina chat ɗin gaba ɗaya, amman ka yarda da ni dan
Allah”

“Idan ban yarda da ke ba, zan zauna ina magana da ke haka? Very soon an gano wanda
yayi wannan abun, akwai mai son shiga tsakanin mu ne”

Gabansa ta dawo ta risina ta riƙe ƙafafunsa.

“Na gode Allah ya saka mana”

Ɗagota yayi ya rumgume. Zuciyarsa cike da kishin hotunan can daya kalla, duk da
yasan cewar ba haɗi ne amman yana kishin hakan.
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng
*PAGE - 30*

NOT EDITED ⚠️

Ƴan ƙuɗin da suka mata saura a jakarta, da kuma dubu ashirin ɗin nan Hajiyar gidan
ta bata, su ne take ta maneji ta su tana siyen abinci.

A kullum gidan su Mardiya take kwana, wani lokacin har zanenta take ɗaurawa, kamin
ta ɗinka kala biyar a cikin kuɗin. Tayi ta zuba ido tana jiran kuɗin Anty Amarya
har ta gaji, tun tana sa ran zata ta kira wayar har ta gaji da jiran ta fara
tunanin wata mafitar.
Da ta fito daga gida kai tsaye ta nufi gidansu Hajiya Saratu, har ta isa
zuciyarta na nuna mata illar abunda zata yi, ko ba komai zai nisanta ta da
Ubangijinta, sannan duk wanda yasan abunda ta aikata mutuncinta zai zube a idonsa,
ashe Allah zai jarrabeta da wani matsi har kuma ta nemi tsaɓa masa, idan har ta yi
haka bata kasance cikin nagartaccin bayi ba.

Juyar da fuskarta tayi gefen ti-ti tana kallon motocin dake kai da kawo, hawaye na
silalawo daga idonta, wani bangare na zuciyar yana ƙoƙarin rinjayarta akan idan har
ba ita ba, bata da wata mafita, babu kuma wanda zai taimake ta sai ita. Haka ko
wane bawa zuciyarsa take nasalta masa alheri da sheri duk ɓangaren daya rinjaye ka
shi zaka aikata.
Hannu ta kai ta share hawayenta, tana mai jin ƙyamar abun a ranta, yanzu idan taje
garin aikata ta mutu fa? Me zata cewa Allah? Haƙiƙa an jarrabi wasu gabaninta da
suka yi haƙuri kuma sai Allah yayi musu mafita, kuma bayan ita za a jarrabi wasu a
bayanta, haka Ubangiji yake jarraba bayinsa dan ya auna imaninsu da kuma yarda da
ƙaddara.

“Haƙiƙa za mu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawayar dukiyoyi da


rayuka, da ƴaƴan itatuwa , ka yi albishir ga masu haƙuri (Wajen jure waɗannan
jarabce-jarabcen) Waɗanda idan masifa ta same su sai su ce INNALILLAHI WA'INNA
ILAIHI RAJI'UN ma'ana :- mu ga Allah muka fito kuma a gare shi za a maiyardar mu.
Wanɗannan gafara da kyakkayawan yabo daga Ubangijinsu sun tabbata gare su, da
rahama kuma waɗannan sune shiryayyu.” (Baƙara: 155-157)

Tuna waɗannan ayoyin ya ankarar da ita abubuwan data manta, ji tayi kamar an
tsikareta, gashin jikinta ya tashi, a nan ta soma tambayar kanta, dan me zata yarda
zuciyarta ta rinjayeta ta tsaɓi Ubangijinta? Ta fita daga waɗancan bayin da Allah
ke yabo? Ashe Ubangijinta be mata dukan gata ba? Ashe daman Imaninta ƙanƙane ne?

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un


Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta furta a fili, har sai da mai Napep ɗin ya kalleta.

“Hajiya lafiya dai?”

“Lafiya ƙalau dan Allah juya da ni ka kai ni babbar Asibiti”

“To amman fa wasu kuɗin zaki sake biya”

“Na ji mu tafi”

“Tau Hajiya lafiya kike kuka?”

Sai a lokacin ta tuna da hawayen dake fuskarta, sa sauri ta share hawayen ba tare
data ce masa komai ba har suka isa asibitin, sannan ta fita ta ciro kuɗinsa ta ba
shi.
Ko da ta shiga cikin ɗakin Asim na zaune, kamsa ya kumbura sosai har idonsa ɗaya
ya liƙe, hankalinta ya tashi dan yanzu wannan kumburin ya fi na jiya.
Kusa da shi ta zauna zuciyarta cike da tausayinsa, har idaniyarta na ƙoƙarin zubar
masa da ƙwalla.

“Asim kaga har yanzu Anty bata kira ba, kuma bata aiko ba, ni kuma bana da wata
mafitar, ga kuɗi da ake bina ma ban san yadda zan yi ba, wannan kumburin naka yana
tsorata ni”

Ya matse ƙallah data cika masa ido.

“Namra ko gida za mu koma ne?”

“Idan mun koma za su ce mun kwaso ciwo mun dawo”

“Likita yace idan ba allura nan aka min ba yana da wahala naji sauƙi da wuri”

Hannayenta tasa ta rumgume shi tana kuka. Shi kuma a take yaji sha'awarta ta saukar
masa, ya kai hannu yana ɗan shafa ta. Data anƙaro da abunda yake nufi da ita sai
tayi saurin ɗagowa daga jikinsa.

“Ina Mama?”

“Tana waje”

Ya sake miƙa hannu yana shafa fuskarta, yana ƙoƙarin ɗaga hijabinta ya zura ɗayan
hannunsa ciki.

“Asim asibiti muke fa, kuma dubi halin da kake ciki”

Yawun bakinsa ya haɗe, ba tare daya daina abunda yake mata ba. Ana taɓa ƙofar ɗakin
tayi saurin tashi tsaye, shi kuma ya bita da kallo idonsa har sun fara canja kala.

“Mama ina wuni?”

“Lafiya ƙalau ya rana?”

“Alhamdulillah”

Ta ɗan kalleshi cike da kunya, dan gani take kamar Mama ta lura da abunda suke.

“Bari naje gurin Hajara”

Bata jira abunda zai ce ba ta fice. Sai Mama ta zauna a kujerar dake kusa da Asim
tana faɗin

“Lamarin nan naka fa ƙaruwa kawai yake yi”

“Tau Mama nayi maganar kuɗin adashen nan kin kawo wasu hujjoji na daban, ko mutuwa
na yi ai ke kika rasa ni tun da su ƴar su wani zata aura”

“Shawara da nake kenan a zuciyana, zan je nayi mata bayani sai na karɓo kuɗin daman
dubu ɗari uku ne, idan Allah yasa ka samu sauƙi sai a shiga wani kuma”

“Haka yafi, tun da kin ga har yanzu basu saje kira ba ma balle su aiko. Yaushe zaki
je?”

“Gobe nake son naje, nima kuɗin da suke hannun na duk sun tafi gurin siyen abinci,
ga tufafin nan ƙala ɗaya kullum ƙara naje ya ɗauko wasu tun da waɗanda muka zo da
su sun ƙone, da Hajara zan koma in yaso sai na dawo ni kaɗai, daman Haruna ya matsa
da maganar yaushe zata dawo”

“Ni Wallahi inda da hali ma da kin tafi yanzu, sai ki dawo gobe da wuri, dan ni
kaɗai na san halin da nake ciki, kuma kin ga yanzu aka yi ƙarfe ɗaya, nasan zuwa
yamma kin isa”

Ta ɗan yi shiru tana nazari.

“Rana be yi ba?”

“Be yi ba Wallahi, tun da kin ga ma Namra ta zo sai ta zauna nan har ki dawo”

“Tau bari na gani, ai duk na natse ma da wannan kumburin na ka”

Ta tashi ta fita cikin yanayin damuwa. Wayar Asim dake hannun Hajara Namra ta
karɓa, ta saka number Babban Yayansu ɗan Hajiya Barau, sai ta matsa can nesa da
Hajara ta kira shi.

KALSOOM POV.

Ba itace da girkin ba, amman sanin halin Rashida yasa bata tsaya jiranta ba ta
shiga kitchen ta ɗora musu breakfast, daman wani lokacin ita take shirya musu tun
da Rashida aiki take zuwa.

Sai da ta shirya komai, na karyawa sannan ta ɗauko kulolin su ta zuba musu abincin
su, sannan ta kira su ɗaya bayan ɗaya ta miƙa musu kulolin.

“Ku je gurin mota zan tashi Daddyn ku yanzu”

Ta nufi ɗakinsa, tana buɗe maɓallan rigar bachin ta. A tsakiyar gado yake kwance
yana lulluɓe irin yana jin tsayi ɗin nan.
Air conditioner ta fara kashewa sannan ta nufi window ta buɗe su duka ta ɗage
labulayen sannan ta nufo inda yake kwance ta yaye bedsheet ɗin tana taɓa masa
kunne.

“Likita tashi safiya yayi fa”

Hannu ya kai ya janyo ta saman gadon ya rumgume ta

“Ban gaji da bachi ba”

“Yara suna gurin mota suna jiran ka”

“Ya salam”

Ya ƙara rumgume ta tsamtsam ƙirjinsa, kamar ba zai tashi ba, sai faman lumshe ido
yake alamar bachi na masa daɗi.

“Doc. Doc. Doc”

Shiru be motsa bama balle ya amsa ta, hannu ta kai ta murɗa masa kunne, har sai da
tayi ƙara ya kama hannunta ya ciza sannan ya tashi, yana jan kitson ta.

“I hate dis Morning”

“Really”
Ta tsire baki tana koyonsa.

“I hate dis Morning”

Ya zare ido, lokacin da idonsa suka kai kan ƙirjinta.

“Wow”

Ya kai hannu zai taɓa ta, ta fisgi kanta cikin zafin nama, ta sauka saman gado ta
fice daga ɗakin tana masa dariya.
Tashi yayi ya shiga bathroom ya wanke bakinsa da fuskarsa sannan ya fito ya kai
yaran makaranta. Ko da ya dawo babu kowa falo, sai kawai ya nufi ɗakin Rashida dan
yaga motarta waje alamar yau bata fita da wuri ba kenan.

Tana ganin ya shigo ta juya kwancinta ta bashi baya. Hakan be da me shi sai ma
dariya da yayi ya ƙarasa kusa da ita ya juyo da ita, hawayen daya gani a idonta ya
tashi hankalinsa.

“Lafiya Pyar?”

“Bana jindaɗi ne”

“Me ke damun ki”

“Nima ban sani ba”

“Amman miyasa baki faɗa min ba?”

“Taya zan faɗa maka bayan ta shiga haƙƙina taje ta tashe ka, kuma ta san yau ba
girkin ta bane”

“Ta riga ta saba ne, saboda kina fita sa sassafe ba tare da kin damu da tashi na
ba, balle haɗa mana abun karyawa”

“Ni gaskiya ta daina shiga min haƙƙi bana so”

“Shikenan zan mata magana, amman yanzu faɗa min me kike ji yana damun ki”

“Fever, sneeze, headache and nauseous”

“Zan diɓi jininki da fitsari idan zan fita, yanzu tashi mu karya sai ki sha magana”

Ta ƙara manne masa a jiki.

“A'a ni bana so cin komai”

“Tea fa?”

“Sai dai idan kai zaka haɗa min da kan ka”

“Yes ni zan haɗa miki ai”

Ya faɗa yana murmushi, sannan ya tashi ya fice. Ajiyar zuciya Rashida ta sauke,
ranta yana mata ba daɗi, idan har zarginta ya tabbata gasjiyar tana da ciki, tana
cikin matsala dan bata iya tantance na waye ne,

‘Taya wani zai gane idan ba ni ma faɗa ba?’


Tambayar da tazo mata kenan a zuciyarta, sai kawai ta tashi ta shiga banɗaki.

Hilal sai da ya shiga ɗakinsa ya ɗauko maganinka sannan ya nufo ɗakin Kalsoom, a
lokacin tana zaune gaban madubi tana shiryawa dan fitowarta daga wanka kenan.
Daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta yace

“Wifey Yau madam babu lafiya, ba zata fito ba tea kawai zata sha, ni ma kuma bana
jin cin komai”

Kai ta ɗaga masa tayi murmushin da be kai zuci ba. Har ya wuce, sai kuma ya dawo ya
tsaya bakin ƙofar ya miƙa mata hannu.

“Taso na haɗa miki breakfast”

Ba musu ta taso ta miƙa masa hannun ba dan ranta na mata daɗi ba. A kujerar data
saba zama ya zaunar da ita, ya ɗauki kofi biyu ya haɗa tea, ya aje mata ɗaya
gabanta ya zuba mata ƙwai da sauran abubuwan da suke gurin, sannan yaƴi mata kiss
ya ɗauki tea ɗin ya nufi ɗakin Rashida.

Da kallo ta bishi, zuciyarta na sosuwa da lamarinsa, tabbas yana son matarsa fiye
da yadda yake son kansa, yanzu ya kasa karyawa saboda bata da lafiya, ta lura da
yadda yanayinsa ya canja a take, taya zata shiga rayuwar irin waɗannan ma'auratan
sannan tace zata samu farinciki?
Hannu ta kai ta shafa cikinta, hawaye masu zafi suka silalo daga idonta.

Sai da ya bata tea ɗin tasha sannan ya bata magani, sai ya sake fita yaje ya ɗauko
wasu robobi guda biyu ya miƙa mata babbar.

“Kiyi fitsari a wannan”

Hannunsa sanye da safa, ya ɗibi jininta ya zuba a ƙaramin robar sannan ya manna
mata kaɗa ya lunda mata, ya kwance robar daya ɗaure mata hannun da shi, kwashe
kayan yayi ya fice. Bayan kamar thirty minutes ya dawo ɗakin da shirinsa na zuwa
office.
Robar fitsarin ya ta bashi, ya karɓa yayi mata kiss, sannan ya fice. Ɗakin Kalsoom
ya shiga, tana jin motsinta ta lafe kamar tana bachi, itama kiss ɗin yayi mata
sannan ya fice.

Rashida na jin tashin motarsa ta janyo wayarta ta danna number Asmee, ringing huɗu
tayi sannan ta ɗauka.

“Asmee an tashi lafiya?”

“Lafiya ƙalau ya gidan?”

Ya amsa mata muryarta da alamar damuwa.

“Asmee yau ba zan samu fita ba, bana jindaɗi, sai dai kr kije idan da hali”

“Me ke damun ki?”

“Abubuwa da yawa ga jikin duk ya min nauyi”

“Ko dai ciki ne?”

“Haka nake tunani nima”

“Allah ya raba lafiya”


Jin ta faɗa ba da wani jindaɗi ba yasa Rashida Tambaya.

“Ya naji muryar ki ba daɗi?”

“Ba komai, nima bana jindaɗin ne, amman zan daure a haka naje”

“Yauwa na gode sosai, kin ce dai yana aiki sosai ko?”

“Sosai Wallahi kamar yan kan wuƙa, duk yadda mu kayi zan faɗa miki”

“Okay na gode”

Rashida na kashe wayar Asmee ta fashe da kuka.

‘Allah kasa ba gaske bane Allah, idan har da gaske ne ya ci amanata, tun da yasan
yana da shi kuma ya nemi ya kwana da ni, Wallahi dana sani ni dama ban je gunsa
neman magani ba, mugun Malami kawai’

Abunda take ta tunani a zuciyarta kenan, a fili kam kuka kawai take, kamar ta cire
idonta.

_________________________________________

Kuyi Haƙuri da wannan idan Allah ya bani iko zan kara muku wani anjima.

BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY 😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

Godiya marar iyaka gareki Daughter, na gode na gode I really did not expect this
awesome surprise from your side
Allah ya kara arziki 😘

*PAGE - 31*

NOT EDITED ⚠️

Ƴan seconds ya rage wayar ta fara ringing sai kawai ta kashe, tana tunanin yadda za
fallasawa kanta asiri idan har ta yarda ta faɗa masa danuwarta, ba duka ɗan'uwane
yake taimako dan Allah ba, ballanta shi data san dole ne ya faɗawa Hajiya Barau,
ita kuma fitar da maganar zata yi, sai a fara cewa tana roƙon dangi.

Juyowa tayi ta nufo gurin da Hajara take zaune, ita ma ta zauna tana miƙa mata
wayar.

“Har kin kira?”

“A'a ban kira ba na fasa ne”

Ta faɗa tana murmushi, isowar Mama yasa ta sadda kanta ƙasa tana watsa da yatsun
hannunta.

“Wai gida za mu koma yanzu”

Daga Hajara har Namra kallonta suka yi


“Gida kuma? Ina ba dai sokoto ba ko?”

Namra ta tambaya cike da mamaki.

“Can fa, wai so nake muje yanzu kamin yamma mun isa sai da gobe kuma mu juyo”

“Amman zuwa lafiya ne?”

Mama ta ɗan yi shiru kamar mai tunanin abunda zata ce mata.

“A'a wai kuɗi zan je na ranto idan har Allah yasa an samu sai a siye maganin da
likita ya rubuta ta, tun da naga alamun sauƙi a jikinsa amman kumburin nan na kansa
yana bani tsoro. Kuma ina son naje na ɗauko wasu tufafin gashi mai son Hajara shi
ma ya damu yaushe za mu dawo”

Namra ta sauke ajiyar zuciya cike da tausayawa, ji take kamar ace tana da mafitar
su ta ɗauka ta bada, ba sai taje neman rance ba.

“Amman Mama da zaki yi haƙuri har gobe, saboda yanzu rana yayi sosai, kuma zaku iya
zuwa ku tarar da jira a tasha, ƙara ki haƙura har da safe sai ki tafi, amman
tafiyar dare ba kyau, musamman lokacin nan na muke cikin matsalar tsaro”

Mama ta ɗan yi shiru, tana nazarin maganganun Namra.

“Nima haka nake gani, ƙara na haƙura har zuwa goben”

Ta faɗa daga tsayen da take tana gyara ɗaurin zanenta, sai kuma ta juya ta koma dan
faɗawa Asim zancen canjin tafiyar.

Sai da wuce sannan Hajara ta kalli Namra tace

“Tafiya yanzu sai kace waɗanda aka kora daga gari”

“Nima ai shi na gani, ƙara dai a haƙura har da safe, yau da gobe a duk ɗaya ne
wajen Allah”

Namra ta faɗa tana ƙoƙarin tashi

“Lallai kam, nima bana son tafiya irin wannan”

Murmushi kawai tayi ta nufi ward ɗin da nufin ƙara tausasa Mama ta haƙura da
tafiyar har gobe.
A bakin ƙofar ta tsaya cak! Tana sauraren muryar Mama da kunnuwanta suke sato mata.

“Na ce amman ai dubu ɗari sun isa ko? Kar mu karɓo kuɗin duka ya zama ba muna da
komai gurin mai dashen”

“A'a Mama ki karɓo gaba ɗaya, kin san dole ne mu siye abinci, kuma wata ƙila ba
wannan maganin kawai za a siya ba”

“Amman Ibrahim idan muka karɓi kuɗin duka mun fita daga adashen kenan fa, abinci
idan har taga babu shi ai dole ta faɗa ma iyayen nata, ni ina mamakin ace ƴarka ta
yi wuta irin haka ka kasa taimaka mata, anya wai ƴar su ce tagaske kuwa? Ni bana
ganin a kashe kuɗi dika fa”

“Haba Mama lafiya na kama da me? Idan har Allah yasa na ji sauƙi, ai sai a samo
wasu a ake shiga kuma”
“Ina za'a samu wasu Ibrahim? Kana ganin yadda suka juya maka baya, Wallahi bana
tunanin zaka samu wani abu a auren nan, duba kaga ko fa ƴar garar nan da ake ba su
maka ba, yanzu dubi halin da kake ciki ai ko basu fitar da kai waje ba, sa maka iya
ƙoƙarin su amman suja ƙyale ka”

Wani dogon numfashi Asim.yaja ya sauke zuciyarsa cike da jin zafin abunda iyayen
Namra suka masa.

“Allah dai ya bani lafiya, idan kiɗa ya canja rawa ma dole ta canja, idan su yi dan
Allah ba sa yi dan ƴar su”

Kamar an jefar da gilass a ƙasa ya tarwatse haka taji a zuciyarta, lokacin da


maganganun Asim suka daki dodon kunnenta.
Da sauri tayi baya tana maida numfashi, tare da haɗiye yawu a lokaci ɗaya. Wani
irin mamaki take tana girgiza kai, kamin tayi haramar barin gurin.
Da sauri-sauri take tafiya kamar zata haɗa da gudu, ji take kamar tayi tsalle ta
ganta a wani wajen, ta kasa yarda da kunnuwanta sun ji abunda Asim da Mahaifiyarsa
suke faɗa.

Ta tari mai Napep tana haƙi kamar wanda aka janye wa numfashi.

“Nasarawa zaka kai”

“To ɗari da Hansi, kuma sai na bi ta Yarima Estate na sauke wannan matar”

Kai kawai Namra ɗaga masa, ta shiga Napep ɗin ba dan hankalinta yana jikinta ba.
Yarinyar dake kusa da ita taja wani dogon tsaki, tana matsawa can gefe irin tana
ƙyaƙyamin Namra ɗin nan.

“Mtswww ni dama zaka sauke ta, ta nemi wani sai na biya ka kuɗin duka”

“A a haƙura dai zaki yi Hajiya, ai da kamin a ɗauke ta kika ce haka, amman yanzu na
riga na ɗauko ta kyayi wannan maganar kuma”

Mai Napep ɗin ya faɗa, yana mai cigaba da tuƙinsa. Sai a lokacin Namra ta kalle ta
da kyau.

“A'a ka sauke ni mana ka kaita ita kaɗai saboda ni ba mutum bace, ko kuma Napep ɗin
ta gidan ku ce, idan har kin isa miyasa ba'a siya miki mota ba? Ko kuma ayi miki
direba na ki na kan ki? Wallahi ƙaryar arziki kike tun da har kika iya shigo Napep”

Ƙasa-ƙasa ta kalli Namra tana wani yamutsa fuska, ita har ga Allah ƙyaƙƙyamin Namra
take. Wayarta dake jaka tayi ringing, tayi saurin fidɗo purse ɗin dake cikin jakar
ta cire wayar tare da yin picking ta kara a kunne.

“Hello Dude”

Ta ɗan yi shiru kamin ta sake cewa.

“Ni na baro motar can, Ummy ce na faɗa mata, wai bata turo direba tun da ban faɗa
mata zan fita ba”

“Eh ina kam Napep n kusa isa, okay bye safe trip Dude”

Ta kashe wayar kamar ta fasa kuka, kamin a isa Estate ɗin nasu har ta tsawala.
Har bakin gate ɗin gidansu ya sauke ta, ta ciro 1k ta miƙa masa, bata tsaya karɓar
canji ba ta nufi gidan, da sojoji suke gadi, da sauri suka buɗe mata gate shige
cikin, sai ƙyaƙƙyamin kanta take.
Kai kawai mai Napep ɗin ya kaɗa ya wuce da Namra Nasarawa road.
A ƙofar gidan su Mardiya tace a sauke ta, ta ciro ɗari biyu ta miƙa masa ya karɓa
ya bata canji sannan ta juya ta nufi cikin gidan, zuciyarta na dawo da maganganun
da kunnuwanta suka joyo mata.

A zauren gidan ta tsaya, ta jingina da ginin gurin ta lumshe.

‘Miyasa Asim yake ƙoƙarin ɓoye min sirrin sa? Me suke shiryawa shi da mahaifiyarsa?
Kar zancen Anty ya zama gaskiya, kar dai ace rayuwar Asim ta canja, da biyu ya aure
ni kenan? Soyayyar daya nuna min a baya ta ƙarya ce?’

Hawaye ya silalo daga idonta, dake lumshe, sai kuma ta girgiza kai tana cigaba da
zancen zuci.

‘Amman ya so ni a baya kuma so na gaskiya, miyasa yanzu zai canja? Na juyawa kowa
baya saboda shi, ba zai min haka ba, what if i choose the wrong person? No no no
it's Asim mutumen da yake son ki so na haƙiƙa mutumen da yace min miki ba dukiyarki
ce a gabansa ba’

Ta buɗe ido tana share hawayenta.

“Amman mi yake nufi da idan ba suyi dan Allah sa yi dan ni? Me yake nufi da idan
rawa ta canja, Allah ka fahimtar da ni, Allah ka amintar da ni, Allah kar ka saka
zancen Anty ya zama gaskiya, Allah kar kasa Asim ya zama cikin mutanen da za su min
Zagon Ƙasa, Allah kar kasa ayi ma auren nan na mu dariya”

A fili tayi furucin tana kuka, zuciyarta a karye, tana ji a jikinta ranar nadamar
ta tana daf ta ita.
Ganin wata zata fito daga cikin gidan yasa tayi saurin ɓoye kukanta.

“Namra ce a nan tsaye?”

“Eh yanzu na shigo ina wuni?”

“Ya jikin mai gidan na ki?”

“Da sauƙi sosai”

“Allah ya ƙara sauke, har yanzu dai ba mu samu mun koma mu ƙara dubashi ba”

“Ba komai ai, kuna ta sana'ah ba zama”

“Ba zama fa Allah dai ya ɗauƙe Wahala”

“Amin”

Namra ta kunna kai cikin gidan, ita kuma ta fice tana gyara hijabinta.

HILAL POV.

Yau one day da gwajin da ya kai ayi ma Rashida, dan haka yana buƙatar karɓo result
ɗin dan tabbatar da zarginsa, duk da alamu sun nuna cikin ne amman ya fi son ya
ƙara tabbatarwa.
Lokacin daya gama duba Patients ɗinsa sai ya nufi lab dan karɓar sakamakon.
To his surprise ba abunda yake zato ba kawai ya gani, a cikin result ɗin akwai
symptom ɗin HIV. Haka ya riƙa karanta result ɗin ba daɗi, but still abu ɗaya yake
gani da biyu yake gani.
Ciki da kuma symptom.
Ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yayi, kar mutanen da suke gurin su zargi wani abu. Cikin
rashin kuzari ya dawo office ɗinsa, har ya zauna sai kuma ya tashi tsaye, sai
karanta takardar yake numfashinsa na yawo, wani zafi ya riƙa jin yana masa yawo tun
daga cikin cikinsa zuwa ƙwaƙwalwarsa.

“Ko dai mistake suka yi? How could this happen?”

Ya kasa yarda, mamaki yake har yanzu, shi dai yasan yana yawan gwada kansa every 6
months da kuma iyalansa, kuma lokacin da aka auna jinin Kalsoom be nuna haka ba,
why Rashida?
Gani yake mistake ne suka yi, sai dai baya jin zai iya koma ya tambayesu, abunda
kawai zai iya, shine ya sake ɗibar jinin nata, da na ƴaƴansa da kuma na Kalsoom ya
kai ward ɗin da ake gwajin cutar, dan tabbatar da zarginsa, idan har da gaske ne ai
zai nuna yadda ta samu ciwon da kuma daɗewarsa a jikinta.

Be iya ƙarasa aikin ba ya haɗa kayansa ya ɗauki ƙaramin box ɗinsa ya cire labcoat
ya riƙe a hannu ya fice, ba tare daya tsaya kulle office ɗin ba.

Ko da ya isa gida kansa har wani zafi yake kamar an kunna masa wuta, gaba ɗaya
kalar idonsa, da fuskarsa ta canja irin kana kallonsa kasan yana cikin damuwa.
Rashida na zaune falo riƙe da plate tana cin abinci, ba laifi yanzu kan ta ɗan
samu sauƙi dan ita ma tayi girkin sa kanta. A bakin ƙofar falon ya tsaya yana
kallonta wani tausayinta yaji ya lulluɓe shi har idonsa suka cika da ƙwallah.

Ita kuma ta ɗan kalle shi kaɗan ta kauce kai, ba dan bata son kallon nasa ba, sai
dan baƙin kishi daya rufe mata ido, gani take yanzu ai ba ita kaɗai ce da shi ba.

Yana sako ƙafarsa a first step ɗin falon, sai ta tashi ta nufi ɗakinta. Shi kuma ya
tsaya a gurin ya bita da kallo zuciyarsa cike da tausayinta.

______________________________________________
Assalamu alaikum Habibaties 🌺
Ina fatar kuna cikin koshin lafiya? Allah yasa haka Amin
My dear readers idan Allah yasa muna cikin masu rai da lafiya, idan na yi page 35
tau ZAGON ƘASA na Khadeeja Candy ya koma na siyarwa, daga bakin Page 35 har zuwa
karshe na kudi ne, daga page 1 zuwa 35 free ne. Nasan zaku ga chanji yazo muku ba
ta yadda kuka zata ba, ku yi hakuri ku min uzuri, haka sauyin ya zo. Kuma ina fatar
zaku goya min baya, fiye da yadda kuke min a da, soyayyar ku da haɗin kan ku, shi
na ke fata a kullum, Allah yasa ku min kyakkyawar fahimta. 😊

Ga waɗanda suke sha'awa. Naira ɗari biyu ₦200 zaku turo ta wannan account ɗin
0314795884 Abubakar Hadiza GT Bank.
Ga wanɗanda basa da account kuma za su iya turo katin waya na line mtn na dari biyu
da hansin ₦250 ta wannan number 08036126660

Idan kun tura. Sai ku turo da shaidar biyan kudin wato screenshot ta wannan number
08036126660.

NA GODE 😊

BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng
*PAGE - 32*

NOT EDITED ⚠️

Ɗakinsa ya wuce ya aje kayan da suke hannunsa, sannan ya fito ya shiga ɗakinta.
Zaune ya same tana taunar naman abincin data gama ci, kusa da ita ya zauna yayi
mata ƙuri da ido, kamar mai tunanin abunda zai faɗa mata.

“What?”

Ta tambaya shi sam be san ta lura da kallon da yake mata ba har sai da tayi magana.

“Bana da ikon kallon ki ne?”

Ya faɗa yana murmushin ƙarfin hali.

“Kallo na nawa kuma, ai na gaji da kallon nawa ne shiyasa kaje ka ɗauko wata, kuma
ni ka faɗa mata ta daina zuwa min yawo da yara karta lalata su”

“Uhmm, Pyar ki daina sawo zance Kalsoom a gurin da muhallinta ba, ke da ita duka
ɗaya kuke a guna, wani abun da kike faɗa akanta ba daɗe yake min ba, and you know
what ita bata taɓa wani mugun furuci akan ki ba, balle kuma akan ki ba, sannan tana
kula da ƴaƴanki”

Ta taɓe baki ta aje plate ɗin ƙasa.

“Wallahi duk son ƙarya ne, babu kishiyar data zata so ƴaƴan kishiryarta, wannan duk
Zagon ƙasa ne”

Ya kai hannu ya riƙo hannunta.

“Naji pyar faɗa min when last nayi miki gwajin jini?”

“I can't remember, ba kai kake min ba?”

Ya ɗanyi shiru.

“Ina ganin anyi shekara biyu yanzu, saboda ba samun zama nake ba, miya faru?”

“Ba komai, zan sake ɗibar wani ne, wacan a mota ya ɓata fitsarin kawai na auna”

“Okay amman yau zaka ɗiba, dan gobe zan je aiki”

“Daga jin sauƙi sai kuma zuwa aiki?”

“Kasan matsalar banki tun yau ma aka so na koma”

Hannu ya kai ya shafa gefen fuskarta.

“Pyar i love you so much ki sa wannan a zuciyarki, mijinki yana son ki sosai”

“Yana son mu dai point of correction”

Ta faɗa tana wani yatsina fuska, shi kuma yayi murmushin da be kai zuci ba, ya
tashi tsaye.

“Bari na yi wanka”
“As you wish”

Bayansa ta bi da kallo zuciyarta na mugun tafarfasa, duk yadda take so mijinta idan
ta tuna da ba ita kaɗai yake so ba, sai ranta ya ɓace.

Sai da yamma lis sannan Kalsoom ta dawo, dan yau gidan su ta wuni ita da yara,
daman duk ranar da ba'a zuwa makarantan ilamiya, ta kan yi amfani da lokacin ta
koyar da su wani abu na rayuwa ko kuma addini, sai ya kasance yau kan tana buƙatar
zuwa gida gaida du Momy, shiyasa ta kwashi yaran duka suka je gidan.
Tayi mamakin ganin Rashida tayi abinci a yau bayan kuma jiya ta gama koken bata
da lafiya, kusan kwana biyu nan ma har cewa take ita ba zata iya cin komai ba.

Ta san yau Doc ba a ɗakinta yake ba, hakan yasa bata damu da dole sai ta ganshi,
dan ko da suka dawo, baya gidan Rashida ce kawai, kuma har dare be dawo ba.
Da wuri yaran suka yi bachi saboda gajiya, sai ya rage ita kaɗaice a falon sai tv
tada tisa a gaba tana kallo. Saman kanta Rashida ta zo ta tsaya sai wani yauƙi take
kamar ance mata Doc ne a gurin zaune.

“Ammyn Rafiq ya idan zaki fita da yara ki riƙa faɗawa Dadyn su, yazo nan yana ta
min faɗa wai shi baya son yawo kar a lalata masa yara”

Kalsoom ta ɗago kai ta kalleta tana murmushi

“Ai ni kaina ban fita ba, sai da na nemi izininsa, balle kuma na ƴaƴansa, I'm
friendly Rashida feel free to tell me baki son ina fita da yaran ki, is okay sai na
tura su duk inda nake so”

Bata tsaya jiran abunda zata sake cewa ba, ta aje remote ɗin dake hannunta, ta
tashi ta bar mata falon.
Da wani mugun kallo Rashida ta bita ji take kamar ta tashi taje ta maƙareta, bata
san tana kishinta ba ma sai a yanzu data kwana biyu nan a gida, ita dai gani take
Kalsoom ta tare mata guri.

‘Ni ban ga abunda matar nan ta fini da shi ba, yaje ya kwaso ta, mace sai baƙin
munafurci, Wallahi kin yi kuskuren auren mijina dan mijina mijin Rashida ne ƙadai
ba dawata macen ba’

Ƙwafa tayi tana wani huci kamar maciji, ta juya ta koma ɗakinta. Saman gado ta
zauna tana sauraren yadda zuciyarta take mata zafi, kishin Mijinta take ji sosai,
sai a yanzu take gane abunda wasu ƴan grps nata na whatsapp suke faɗa mata akan
kishiya, ya karɓe mata ƴaƴa, yanzu kuma tana ƙoƙarin karɓe mata miji, gashi Hajiya
ma tafi son Kalsoom da ita.

Wayarta ta ɗauko ta aika ma da Asmee kira, sai da ta mata two missed calls sannan
tayi picking.

“Ina ta kira hala baki kusa?”

“Eh Wallahi ya gida?”

“Gida ƙalau, ni dai ce hankali ba kwance kuma ban ji kin kira ni, Asmee idan mukayi
sake fa matar nan ƙwace min miji zata yi”

“Wallahi ban samu naje bane, bana jindaɗi sosai, amman inshallah gobe zan je”

“Ayyah me ke damun ki?”

“Ina jin ƙiba ne sai kuma Infection ya shiga ciki”


“Indai Infection ne ki nemi ɗayyar citta da tafarnuwa ki feraye cittar ki ki jiƙa
su, su jiƙu sai ki riƙa sha ko kuma ki nemi maganin nan Cantin yana yi sosai. Na
rage tumbi ko kiba kuma ki samu ganyen guava guda bakwai ki tafasa with one liter
of water kisha for seven day's mrng before breakfast da kuma last thing kafin
kwanciya, shi Momy take kuma wallahi na sauka ta rage ƙiba sosai cikin satina ɗaya
yayi mata aiki wallahi, masu ulcer ma zasuyi yana maganinsa, irin wannan yafi na
asibitin dan shi ba shida side effect. Allah ya baki lafiya”

“Amin na gode sai kin ji ni”

Daga haka sukayi sallama, Rashida ta aje wayarta tana faɗin

“Garin kwashe kwashen ki dai sai kin kwasowa kan ki, ba ko wane malami bane zai
haɗe yawunsa akan ki, ni ko zan yarda ai ba zan malaman ƙauye ba ƙazamai”

Ta ƙarasa maganar da tsire baki, duniyar tunaninta na son dawo mata.


A gogon ɗakin ta sakarwa ido daga seconds zuwa minutes take ƙirgawa har ya kai ga
hours, Doc be dawo gida ba, haka ta gaji ta kwanta saman gado idonta a ƙafe, babu
abunda take tunani sai Rashida.
Yadda ta shiga cikin gidan da kuma irin rawar data taka tun daga shigowarta zuwa
yanzu, bata ankara hawaye suka silalo mata.
Sai yanzu take jin yadda ɗacin zuciya yake, sai yanzu take jin son Hilal na haƙiƙa
a zuciyarta, sai yanzu take gane ta tabka kuskure da tabar shi ya ƙara aure, yanzu
haka zata kasance ita da wata a cikin gida? Haka itama zata gina nata rayuwar ta
karɓe mata kowa?

Tafiyar daƙiƙa biyar zuwa shida numfashinta yayi kamin ya dawo izuwa gareta har ta
ankaro da duniya take, ta samu damar amsa sallamar mai gidan nata.

“Wa'alaikassam”

Sautin muryarta ya isar masa da saƙon damuwarta, ga kuma hawaye dake kwance a
fuska. Ledar dake hannunsa ya aje ya zauna kusa da ita gabansa na faɗuwa, har
zuciyarsa ta fara raya masa wani abun na dabam.

“Miya faru kike kuka?”

“Kawai ina tunanin rayuwa ne, da kuma irin sakamakon da kayi min, bayan nayi maka
dukan hallacin”

Masauki yayi mata a ƙirjinsa, ya kai hannu ya dafa cikinta, zuciyarsa na hasaso
masa wani tunanin na daban.

‘i just can't believe that, taya wannan cutar zata kusance mu? Allah kar ka jarabe
mu da abunda zai sa rayuwar mu data ƴaƴansu cikin damuwa’

A can cikin duniyar tunaninsa, kunnuwansa suka cinto masa wasu kalamai da Rashida
take ta maimata masa.

“Ni kar ta sake fitar min da yara, kar taje ta lalata min su, kaji”

“Ba zata lalata su sai dai ta gyara tarbiyarsu, bakin ki ya daina furta mummun
kalamai a kan Kalsoom, zamana take ba zaman ki, dan haka babu ruwanki da ita”

Da gautsi ya ƙarasa mata kalam, wanda har zuciyarsa haka take, dan kawai yana son
ta ba zai yarda ta da aybanta masa amarya ba, dan shi ya san darajarta, kuma yasan
gidan data fito.

“Ƙara ma ku haɗa kan ku dan ni ba zan ɗauki irin wannan abun ba, mu taru mu gode
Allah akam kyautar da yayi mana, kuma ku yi fatar Allah ya sauke ku lafiya”

Kalamansa basa buƙatar fassara, kai tsaye ta san inda suka dosa, daman ita ta san
ciki ne da ita, to Kalsoom fa ita ma cikin ne.

A take yawun bakinta suka tsinke, cikinta ya ɗauki kuka, ba ƙaranin ƙoƙari rayi ba
wajen ƙawata fuskarta da murmushi, dan ta nunawa Hilal ta jidaɗin.

“Mashallah Kalsoom ita ma tana da ciki? What a blessed”

“Tana ma har ya riga na ki, bata da matsala sosai ne shiyasa ba za a gane tana da
cikin ba”

Amsarsa ta tabbatar mata da zarginta, daman dalilin tambayar kenan. Wata duniyar
take ƙoƙarin kai shi dan ta nuna masa farincikinta, ta kuma ɓoye masa baƙincikin da
ke son bayyana a fuskarta.

Zuwana Kalsoom yasa ya daina takura akansa a kanta, duk magiyar da yake mata yake
nuna mata maitarsa yanzu ya daina tun da ya samu wani halalin nasa, sai dai daren
yau da raya masa shi fiye da yadda yake zato, a yau tayi masa abunda ta shekara
goma bata masa ba, ta sakar masa jikinta sosai, har sai da shi kansa ya gaji dan
kansa ya bar.

Tare suka yi wanka, suka ci abinci da kuma dan abun taɓawa daya siyo musu ɗazu, a
lokacin ƙarfe biyun dare yayi. Suna gamawa ta kwanta dan ba gado haƙƙinsa, shi kam
be kwanta ba sai yayi nafisa raka'ah biyu, raka'ar farko ya karanta fatiha da
ayatul kursiyu sai ya dora kulhuwallahu sama, a raka a ta biyu kuma ya karanta
fatiha da amanar rasulu ya ɗora kulhuwallahu sama, sannan ya zauna yayi zaman
tahiya kamin ya sallame a cikin tahiyar ya faɗawa Allah buƙatarsa, sannan ya
sallame.
Sai da yayi salatin annabi da godiya ga Allah da istigifari ƙafa ɗari ɗari sannan
ya sake ɗaga hannu yayi kirari ga ubangijinsa ya nemi yafiyarsa, sannan ya sake
koro da buƙatarsa.

A cikin ɗauko abun ɗibar jini ya ɗibi jininta dan yasan da safe ba zai samu damar
ɗiba zata ce masa aiki.
Washe garin da zai kai yaransa makaranta suma ya ɗibi nasu, Kalsoom kam sai daf da
zai fita sannan ya ɗibi nata sai raki take masa tana masa shagwaɓa, wai da zafi ita
zai ƙarar mata da jini, haka ta riƙa narke masa a jiki har yayi lattin zuwa aiki.

NAMRA POV.

Kwata-kwata bachi ƙaura yayi mata daga ido, bata ma jin alamunsa balle har tasa rai
zai so mata, abu ɗaya zuwa biyu yayi mata tsaye a rai, maganganun da Asim yayi shi
da mahaifiyarsa, wata zuciyar na shawarta akan ta bayayyana masa ta kuma tambaye
shi abunda yake ƙoƙarin ɓoye mata, yayinda ɗayar kuma take ce mata ta haƙura taga
iya gudun zuwansa dan tabbatar da zarginta.

Babu amfani da raya dare da tunani bayan Ubangijinta yana kallonta, kuma yana
shirye ya amsa buƙatunta, tayi haramar ƙorar sheiɗan sannan ta samu kuzarin fita
tayi alwalah, sannan ta dawo ɗakin tayi nafila ta ɗora sa salatin Annabi.

Firgigit Mardiya ta farka daga dogon bachin da take a farkigice har tana ihu. Namra
ma dake kusa da ita sai da ta ji tsoro kowa dake cikin ɗakin ya matsa, Mahaifiyarta
ta tashi tana kallonta.
Gabanta ta fara kallo kamin ta kalli bayanta, sai kuma ta bi ko'ina na ɗakin da
kallo, ajiyar zuciya ta sauke yafi ashirin, sannan ta haɗe yawun bachin da suka
cika mata baki, ba dan tasan tayi ba.

“Ke lafiyarki?”

Ashe dai duniya take, jin muryar mahaifiyarta ya ƙara tabbatar mata da a farke
take.

“Wallahi wani mumunan mafarki na yi, wai wuta tana bina”

“Subhanallahi, ke kuwa ai addu'ah zaki yi”

Namra ta faɗa, tana rufe ƙur'anen dake hannunta, sannan ta nufi gurin bachinta tayi
addu'ah bachi ta kwanta ba dan tana jin bachin ba, sai dan tana buƙatar jinginar da
jikinta da tabar suka saba mata shimfiɗa da ita.

Washe gari...
Da sassafe ta siye tea da buroɗi ta nufi asibiti, dan bata son su Mama su
kama hanya bata isa ba, tun da babu wanda zai kula da Asim sai ita. Duk yadda take
ganin ta doka sammako sai taga har sun fi ta, dan tana shiga ɗakin taga alamar sun
kama hanya.
Bata yarda ta nunawa Asim komai ba, ta gaisheshi sannan ta masa ya jiki ta soma
zuba masa tea ɗin.

“Jiya kika tafi baki faɗa ba”

“Eh pad ɗina ne ya lalace shine naje gida na canja, su Mama sun kama hanya ko?”

Ajiyar zuciya ya sauke, yanzu kam hankalinsa ya kwanta, daman can yana tunanin ko
ta ji maganar sune yasa taje ba tare data faɗa musu ba, ashe shi da Mama ba su
canka dai-dai.

“Eh tace da wuri zata je yadda zata tararda matar da za a ranto kuɗin gareta”

“Allah yasa a dace”

Ta faɗa tana miƙa masa tea, kallon da tayi masa da kuma maganarsa sun zari
zuciyarta, miyasa Asim yake ɓoye mata? Wani tunanin ne ya zo mata sai ta kawar da
fuskarta gefe.

_______________________________

BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 33*

NOT EDITED ⚠️

Washe garin ranar da Mama ta tafi ta dawo, guraren uku da rabi na rana. Ita kaɗai
ta dawo ba tare da Hajara ba, Namra bata nuna mata komai ba ta tarbeta da far'ah
tana mata sannu da zuwa.
Tana son tayi labari Namra ta tsare su taƙi ta tashi, shi kansa Asim yana son
magana da ita amman ba dama, tun da Namra tana gurin.

Kamar ta san Namra bata tanadar mata komai, tun a hanya ta tayi gurin biredin ta da
lemu, sai ta ta ci ta ƙoshi, sannan ta tashi ta fita.
Da kanta taje ta biya kuɗin maganin dan kar taba Namra.

Ta dawo daga biyan maganin ne, Namra ta tashi tayi musu sallama ta baro asibitin.

Har ta iso gida kuka take, tana tunanin yadda Asim yake ɓoye mata lamarin, dan ta
lura da yadda suke kallon kallo da Mama, hakan ya soma tabbatar mata da abunda Anty
Amarya ke faɗa mata.

“Idan har ta tabbata Asim na son yaudarata....”

Sai kuma tayi shiru ta share hawayenta, ta miƙawa mai Napep kuɗinsa ta shige gida.

*** ***
“Thank you”

Ta faɗa tana murmushi tare da kallon mutumen daya tashi daga saman kujerar ta ya
nufi ƙofar fita. Sai da ya fice sannan ta kalli wayarta dake ringing, sannan ta kai
hannu ta ɗauka zuciyarta na raya mata irin labarin da Asmee zata bata.

“Ƴar gari kamar kin san yanzu nake tunanin ki nace ko kin samu zuwan kuwa?”

Kuka ta fara ji kamin Asmee ta ɗora mata da zancen dalilin kiran nata.

“Rashida ina ciki matsala”

“Lafiya miya faru?”

“Wani malami ne da muke zuwa gurinsa, yana ba mu taimako, shine yanzu ake ce mana
malamin yana da ciwon nan na zamani, shine tun ranar na kasa sukuni ban ma sama
naje gurin matsalar ki ba”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Asmee garin yaya? Ya taɓa sex dake ne? Ko me?”

Kuka tayi sosai har ka kasa magana.

“Ki faɗa min mana ki daina kuka”

“Ya taɓa lokacin da je neman wani taimako sai yace min sai na kawo sperm ɗin wani
wanda ba mijina ba, da jinin al'ada da shi za a haɗa, ni kuma na ce masa ban san
inda zan samo ba, shine....”

Ta ƙarasa da kuka

“Ke yanzu kin je an gwada jinin ki ance kina ɗauke da ciwon ne? Stop crying and
tell me Asmee”

“Ban je ba, tsoro nake ji ban san wanda zan faɗawa ba sai, dan bani da ƙawa irin
ki, na rasa yadda zan yi tsoron gwajin na ke, aiki ma na daina zuwa yanzu”

“Innalillahi Ya salam Ya salam”

Ta soma zagaye office ɗin tana dafe kai, da wayar a kunnenta.

“Ki kwantar da hankalin ki kinji karki faɗawa kowa, kuma karki yi abunda zai sa
mijin ki ko wani ya zargi wani abu, i will call you back”

Tayi saurin kashe wayar tana tuna jininta da Hilal ya ɗiba, idai har Asmee ta kamu
da cutar to itama zata iya kamuwa da ita tun da har suna using mutum ɗaya.
Faɗuwa tayi zaune zumi na keto mata ta ko'ina, hannu ta kai tana shafa kanta, tana
girgiza shi kamar wani ne a gabanta.

“Ko shiyasa ya sake ɗibar jinina? Amman kuma ai da ba zai kusance ni ba, amman
yanzu idan ya auna dole ya gano idan akwai shi”

A fili take furucin zuciyarta a karaye, jikinta har tsimi yake, yanzu kam hannaye
biyu tasa ta dafe kanta tana tunanoma kanta mafita.

“Dole ne na dakatar dashi daga yin gwajin, kuma dole ne nima naje na bincika kai
na, indai har da gaske ne Asmee kin cuce ni”

Da sauri ta tashi ta kaɗe jikinta ta fiddo hoda a jakarta ta gyara fuskarta sannan
ta ɗauki jakar ta fita. Sai da ta biya ta faɗa musu fitar gaggauwa ta kamata,
sannan ta fito harabar bankin ta shiga motar, ta ɗauki hanyar Asibiti.

Akwai ƴar tazara tsakaninta da asibitin, amman yadda ta sakarwa motar wuta yasa ta
isa cikin ƙanƙanen lokaci. A harabar asibitin tayi parking, ta fito ta duba gurin
da aka tanadarwa manyan likitoci dan faka motocinsu.

Motar Doc Hilal ce ta uku a gurin, that's means yana cikin asibitin, safa da marwa
ta fara yi tana tunanin ta inda zata fara. Lab ne ya faɗo mata a rai. Da fargaba ta
kutsa kai cikin asibitin ta ɗauki hanyar da zata hada ta da lab ɗin, ƙasa-ƙasa take
kallon mutane, tana fargabar haɗuwa da Hilal, dan ko ganinta yayi bata san me zata
ce masa ba.

Ta tararda mutane da ɗan yawa a gurin da aka tana da dan karɓar results ɗin jini da
fitsari, hakan yasa ta zagaya ta shiga ciki tun da ita ba baƙuwar asibitin ba ce.
Biyu daga cikin mutanen da suke gurin sun gane, tun da sun san matar Doc ce, cikin
mutunci da far'ar ta gaisa da su tana yi tana kallo ƙofa.

“Habib na ce kun gama gwajin jinin da Doc ya kawo? Za a tafi dashi wani garin ne”

Wanda ta kira da Habib ɗin ya amsa da.

“Eh tun ranar muka shi ba ai”

“Ba yau ya kawo ba?”

“A'a ina jin tun monday ne, Monday or Tuesday? Abbas kai ka bashi ko?”

Wanda aka kira da Abbas ɗin be ma kula.da zancen su ba sai rubuce-rubucen sa yake,
Habib ɗin ya kalleta.

“Ina jin Monday ne, an dai kwana biyu yanzu”

Gabanta ya faɗi sosai.

“O'o nasan ya jefar da results ɗin wani wajen shiyasa ya ƙi ya faɗa min, amman yau
be kawo maka wani ba?”

“Gaskiya be kawo ba, dan mu muka yi duty safe yanzu zamu tashi”

Nauyi zuciyarta sosai tayi mata har sai da ta tsayi ya gagareta, ta zauna a kujerar
dake gurin.
“Amman dan Allah ya za'ayi na samu results ɗin wacan gwajin? Tun da ya ɓatar nasan
ba zaku rasa a littafin ku”

“Wallahi da an fito da results ɗin an rubuta a littafi ansa a paper na results ɗin
ake kai su ɗakin ajiya, sai dai shi Doc zai iya zuwa yayi ma Doc Omar magana, sai
ya bincika masa, amman nan results kawai muke badawa”

“Okay Thank you bari na koma gurin Doc ɗin nayi masa magana”

“Okay a gaida yara”

Ya faɗa yana kallon bayanta, irin ƴan iskan samarin nan ne da basa gani su kauda
idonsu.
Ƙafafunta sun mata nauyi, ga idonta dake son ciki da ƙwalla tana mayarwa, akwai ƴar
tazara tsakanin office ɗin da lab, hakan ya bata damar tunanin abunda zata cewa
Hilal idan ya ganta, idan kuma ta koma bata shiga ba ta san zai iya samu labarin ta
shigo cikin asibitin tun da akwai waɗanda suka santa, kuma zasu iya faɗa masa.

_Thank you so much my tomatir my albasa my daddawa my miyar kuka_

Yana dannawa Ƙalsoom reply ɗin ta whatsapp. Rashida ta turo ƙofar office ɗin ta
shigo da murmushi a fuskarta.
Tashi yayi daga jinceren da yake saman kujera ya kalli da dariya.

“Surprise surprise surprise”

“Yes Darling, na biyo ta nan baya ne shina nace bari na biyo na ga farinciki na”

Ya ɓata rai sosai lokacin daya lura da yanayin tufafin dake jikinta. Suit ne mai
wando ta riga sai ɗan ƙaramin hijabi dake kanta.

“Daman Haka kike fita daga office? Ba mun yi maganar nan dake ba dan me zaki fito
baki ɗora abaya a sama ba, a cikin office ɗin ki kawai na yarda ki riƙa zama haka,
kika ce kin ji ashe ni kike ma ko? Yana ɗaya daga cikin dalilin daya sa bana son
aikin nan na ki, bana son wani na ganin matana abun nan yana min zafi”

Sai a lokacin ta kula da tufafin da suke jikinki, tsabar hankalinta baya jikinta
bata ma san ta fito a haka ba. Hannayenta tasa ta laƙamo wuyansa.

“Im sorry Wallahi fitar gaggauwace shiyasa amman ba zan sake ba i promise”

“Yanzu haka kika shigo a asibitin nan kowa na kallon ki? Haba Rashida idan an girma
a san an girma mana, kefa uwace kamata yayi idan kin ga Ezzah tayi wannan shigar
kiyi mata faɗa ba wai ki yi ba”

Ta saki wutan nasa ta nufi freezer dan ita ba faɗan da yake mata bane a gabanta,
abunda ya kawo ta take ƙoƙarin yi, tsayawa tayi ta duba da kyau drinks ɗin da tasan
babu a freezer ɗin tace masa tana so.

“Nidai nace kayi haƙuri, kuma ina son nasha coc”

Ta faɗa tana marairaice masa, daman tasan baya shan coca-cola saboda irin abubuwan
da ake faɗa akanta, kuma ta san yadda ya tsani kayan yahudawa.
Kamar zai ce mata babu, sai kuma ya ƙyaleta tun da yasan tana da ciki wani abun
dole ya ɗaga mata ƙafa, sai dai be sakar mata fuska ba dan har yanzu ransa a ɓace
yake, sai kawai ya juya ya fita.

Da sauri ta nufi teburinsa ta fara duba takardun da suke gurin, bata ga abunda take
nema ba, hakan yasa ta nufi wata ƴar ƙaramar wardrobe dake gefen kujerar, har ta
kai hannu ta buɗe sai kuma wani tunanin ya zo mata.

‘Idan na yamutsa masa takardu dole zai zargi wani abu’

Sai kawai ta fasa buɗewa ta koma ta zauna a kujerarsa ta ɗauki ƙafafunta ta ɗora
saman teburin kamar babu abunda yake damunta, alhalin a can cikin zuciyarta tashin
hankaline da tunani suka taru suka mata katutu.

Yadda ya fita haka ya dawo fuska a haɗe kamar be taɓa dariya ba, ransa ya sosu
sosai da ganin irin dress ɗin data shigo dashi cikin asibitin.
Miƙa mata Coc ɗin yayi ya nufi windows ɗin office ɗin ya rufe. Tashi tayi tare da
Coc a hannu daman can ba shanta zata yi ba, bata ma jin zata iya saka wani abu a
cikinta yanzu.

“Ni zan wuce”

Ya watsa mata wani kallo.

“Haka zaki fita?”

Ta ɗan kalli jikinta

“To ya zan yi?”

“Ban sani ba”

Ya nufi hanger ɗinsa ya ɗauko labcoat ya ɗora mata sama.

“Kuma kar ki cireta har office”

“Doc zan bi ta lab na karɓi results, nayi mafarkin na haifi ƴan'biyu”

Dariya yayi sosai, wanda be shirya yi ba

“Toh ai ba a jini ake ganin twins ba, kuma ban ma kai awon jinin ba”

“Miyasa?”

“Ba nan za min ba, Asibitin Alex zan kai, saboda asibitin su tafi ta mu kayan
aiki”

“Okay”

Ta faɗa zuciyarta cike da jindaɗin jin inda zata kai jinin, wani gurin kuma ta
jidaɗin da be riga ya kai ɗin ba.

“To ina ka aje shi? Karka sake ce min ya ɓata kuma”

“Ba zai ɓata ba yana nan cikin mota na”

Ya faɗa yana jan hancinta, ita kuma ta kai bakinta dai-dai nashi tayi masa kiss.
Har gurin mota ya rakata sai da ta shiga yaga tashinta sannan ya koma office ɗin.
A maimakon ta koma asibitin sai kawai ta jiya pharmacy ta siye abu sannan ta ɗauki
hanyar da zata kai ta gidan Asmee.

__________________________________________
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng

*PAGE - 34*

NOT EDITED ⚠️

ASIM POV.

“Naje na biya kuɗin har na magani, sun ce Nurse zata riƙa baka”

Ta faɗa tana hita da ɗan ƙaramin mafecin dake hannunta.

“Mashallah har nawa aka biya ne?”

“Dubu ɗari da goma sha ɗaya, ni ban san dalilin yasa ta kawo ka wannan asibitin ba,
ace allura guda dubu tara magani ma shegen tsaɗa”

“Asibitin kuɗi ce fa, ba kiga ɗaki suka ware mana ba”

“Allah dai ya baka lafiya mu bar Asibitin nan, ni ban ma ƙi mun koma gida ba gaba
ɗaya”

“Gaskiya ni ba zan koma gida yanzu ba, ana kallo kayi aure ka auri masu abu sai
kuma aga yadda na dawo da ciwo, kuma a can ai sai ma mun fi jin kunya tun da ƙyale
ni zasu yi, maƙiya sai su mana dariya”

“Ai ba za a maka dariya ba kam sai dai a zagi iyayenta”

“Ni dai na fi son zamana nan, a cikin kuɗin ki bani dubu ɗari na bata sai ta siye
wasu abubuwan, tun da tace BQ ɗin be ƙone ba sai mu zauna a cikin”

“A'a wane irin dubu ɗari kuma? Dubu shirin ai ya isheta ta siye komai”

“Mama har katifa fa da sauran kayan aiki, ashirin ba zasu isa ba”

“Ni zan je na siyo katifar, da kai na haka kawai za a ɗauki har dubu ɗari a bata,
idan an bata nawa ya rage ni bana da lalurar ne? Ban ga dalilin da zata ci amfanin
ka kai baka ci nata ba, wallahi tallahi na tsani yarinyar nan saboda iyayenta, sam
basu da mutunci”

Asim ya sauke jiyar zuciya.

“Ni bana ma son tunawa da su Wallahi, rai na har ɓaci yake, hmmm Allah dai ya bani
lafiya, na warke na tashi garau, Wallahi sai na basu mamaki”

“Ai kana da maƙiya kam Ibrahim Allah dai ya baka lafiya”

Da Amin ya amsa yana gyara zamam ƙafarsa.

RASHIDA POV.

Cikin mintuna ta isa gidan Asmee, tana fito mota Asmee na fitowa daga falo ta
tarbeta.
Tashin hankalin dake fuskar Rashida ya ɓatar da na Asmee dan yadda taga Rashida ta
rikice ta damu sai ita ta sassautama kanta, a tunaninta Rashida ta damu da matsalar
ta ne har haka.

Da suka shiga falo kowanne kasa magana yayi sai kallon kallo suke, Rashida na
tunanin ta ina zata fara, Asmee na fargabar irin amsoshi da zata bata.

“Wai ke ya akayi kika yi wannan kuskuren, Asmee dan me zaki cuci kan ki ki cece
mu?”

“Rashida na faɗa wani haɗi ne yayi min wanda dole sai an samu sperm ɗin wani”

“Amman ke yanzu dan baki da hankali sai ki bar shi yayi amfani dake? A maimakin
kije can waje ki samo wani? Yanzu kin ja mana masifa Asmee”

Rashida ta ƙarasa maganar da kuka.

“Ba ni da tabbacin ina shi ɗin ko bana da, an ban yi gwaji ba, wata mata ce da take
zuwa gurinsa aka ce ta kamu”

“Amman yayi ta neman ki ne har da yawa ne?”

“Kin san duk lokacin da kaje da buƙata dole ne sai sun nemi su kwanta da kai”

Kuka ta fara, yana ta dana sanin abunda ta aikata. Sai kusan azahar Rashida ta bar
gidan bayan taja mata kunne akan karta kuskure da bari kowa yaji ciki har da
mijinta.

Banki ta dawo zuciyarta cike da tunani kala-kala, masu sokanar tama ganinta da
rigar likita, dariya kawai take musu ba dan ta kula da zancen su ba. Ta shiga
office ɗinta sai zama ya gagareta, ga takardun data tarar an kawo ma tayi sigh ko
kallonsu ba tayi ba. Ta juya ta fita, office ɗin Alhaji Bashir ta nufa. Bata nemi
izinin shiga ba ta tura office ɗin ta shiga.

Hannunta ta miƙa masa kamar yadda ta saba yayi mata kiss, sannan ya zauna saman
teburin ta ɗora sama ƙafarta ɗaya saman ciyarsa tana masa wani irin abu, kamar wata
gwaggwazajiyar karuwa.

“Security Camera, dai a kashe take?”

“Ai nasa an cire min ita tuni saboda ke”

Ta ƙara matsarda ƙafarta, izuwa cikinsa.

“Bashir akwai wanda ka sani a Alex Hospital, ɓangaren Lab?”

Hannu ya kai ya naɗe wandon suit ɗin nata, ya fara shafa ƙafarta.

“Ba za a rasa wanda na sani ba, miya faru ne?”

Shiru ta ɗanyi tana tunani, idan har ta yarda ta faɗa masa, asirinta zai tono, tun
da dole ne yayi ma matarsa magana, wata ƙila ma ya sake ta.

“Wallahi wata friend ɗita ce za'ayi ma gwajin kasan asibitin sun fi ƙwarewa, sama
data su Hilal”

Ya ɗauko wayarsa yana wani lumshe ido

“Bari na kira Doc Sabo sashen jini yake aiki”


Ta sauka daga saman teburin ta dawo saman cinyoyinsa.

“Kar wani ya shigo fa”

“Babu wanda zai shigo sai ya nemi izini”

Sai da suka gaisa da likitan sannan ya haɗa shi da Rashida. Gaisawa kawai tayi da
shi sannan ta sanar masa zata karɓi number sa, su yi magana.

Sai da ta saka number a wayarsa sannan ta sauka daga saman jikinsa, daman tayi
samana hakan ne dan kar ya gano damuwarta tun da ta saba masa a duk lokacin data
shigo office ɗin.
Duk da irin kibar da yake da ita bata hanashi saurin unƙurawa ba ya riƙo hannunta
ganin zata wuce.

“Yau da wuri zamu tashi babu aiki da yawa”

“Eh amman zan je gida akwai abunda zan yi”

“Aiko dai yau na so mu haɗu”

“Gaskiya akwai abunda zan yi, yanzu fa haɗuwar mu zata riƙa wuya, ƙara kaje gurin
matar kawai”

Bata tsaya jiran abunda zai ƙara cewa ba ta fice daga office ɗin.
Lokacin data dawo office ɗinta zaunawa tayi ta ƙare duka aikin dake gabanta, sannan
ta ɗauki wayarta ta kira likitan. Bayan sun gaisa ta gabatar masa da kanta.

“Sunana Aisha bee Omar, akwai wani cousin ɗina dake fama da matsala sai yaje
asibiti aka bashi gwajin jini, to ina son idan ya kawo ka min a yi masa a kira ni a
sanar dani dan Allah”

“Amman miyasa Hajiya?”

“Idan ka kawo ka sanar min zan faɗa maka ko minene, ka turo min account number ɗin
ka”

“A wannan Asibitin bama yin abunda ya tsaɓa doka, hakan kan iya ja mana ɓacin suna
a asibitin nan”

“Ba taka doka zaka yi ba, ceton rai ne idan har ya kawo ka faɗa min dan Allah”

“Miye sunan shi?”

“Sunan shi Hilal”

“Okay”

“Karka Manta ka turo min account number ɗin”

“Alright”

Yana kashe wayar ya turo mata account number ɗin. Ta jidaɗin ganin number, ga dukan
alama zai yi saurin bata haɗin kai, jiki na rawa ta tashi ta fita daga office
ɗinta, ta je ta cikin bankin ta masa transfer 100k.

NAMRA POV.

Yau ba laifi ta samu bachi dare, duk da ba mai nauyi bane sosai, minti goma ashirin
zuwa ashirin da biyar take farkawa.
Sai dai a duk farkawar da take, a zaune take ganin Mardiya tana kallonta kamar wata
mayya, tun Namra tana dauriya ta koma bachi har ta gaji ta tambaye dalilin rashin
bachin nata.

“Wallahi na kasa bachin ne mafarkin tsoro nake, kusan kwana biyu yanzu haka na ke”

“Kiyi addu'ah kawai ki kwanta, babu abunda zai same ki, ki karanta Ayatul kursiyu
ƙafa uku ko wace da bismillah wallahi har garin Allah ya waye babu abunda zai same
ki”

“Toh na gode zan gwada”

Ta faɗa da damuwar a muryarta. Komawa Namra tayi ta kwanta ba ita ta fake farkawa
ba sai asuba.
A kulolin gidan ta ɗauka ta zuba musu ɗumamen tuwo da Maman Mardiya tayi, sannan
tayi wanka ta ɗauka ta nufi asibitin.

Ko da ta isa ta tarar har sun siye tea a bakin asibitin sun karya. Mama bata wani
sake da Namra sun gaisa ba, ciki-ciki ta amsa masa gaisuwarta, ta fice tama watsa
mata wani kallo a kaikaice kamar wata kishiryarta.
Hakan be dame Namra ba, dan ita ta san muhalin data aje ta a yanzu, tun da ta fara
fahimtar tafiyarsu.
Bayan kamar minti talatin da fitar Mama Asim ya ɗauko dubu goma sha biyar ya miƙa
ma Namra.

“Ga wannan ki siye wasu abubuwan na gida, Mama zata siyo katifa da wasu kayan”

Namra ta jidaɗi sosai, daman zama gidan su Mardiya ya fara isarta, duk da tasan
kuɗin ba zasu isheta hakan be hanata nuna farincikinta ba.

“An biya kuɗin maganin ne har wasu sun rage?”

“Eh ɗari biyu matar ta ara mana, Allah dai ya ba ni ikon biya”

“Amin, amman Asim shabiyar zasu isa siyayya kuwa? Ba mu da komai fa kasan komai ya
ƙone”

“Haka nan za a matsa ayi Namra, bafa irin siyayar gidan ku zaki yi ba, ta talakawa
zaki yi, kamin mu ga abunda Allah zai yi kuma”

“Toh Allah ya taimaka”

“Amin, likitan yayi min allurar ɗaya ɗazu, kuma yace ya kamata na ɗan fara taka
ƙafar, koda ina riƙa wani abun ne”

“Aiko ya kamata ka fara tun yanzu”

“A'a sai nan gaba, gaskiya ni tsoro nake ji”

Ta ɗanyi dariya, tana mamakin irin rakin da Asim yake da shi. Asibitin ta wuni sai
da yamma ta koma da zimmar taje Mardiya ta raka ta kasuwa suyi siyayya. Bayan
tafiyarta Mama ta siyo abinci a bakin asibiti ta ci, ta kawo mo Asim, dan kwata-
kwata ƙwara tayi daga ɗakin har sai da Namra ta tafiyarta, sannan ta dawo, Mama
irin mutanen nan ne da basu iya samun arziki ba, waɗanda idan abu ya same su a take
suke canjawa mutum, ga shegen son su yi kuɗi kamar hauka, tana daga cikin mutanen
da suka tsani masu arziki, suna ganin kamar Allah ya fi son su da su, ita a nata
rayuwar bata ƙi Asim yayi arziki ba ta kowa ne hali, ko dan ya rama abunda iyayen
Namra suka masa.
ABDOOL POV.

A hankali yake tsotsa bakinsa kamar mai shan minti, sai wasa yake da drink ɗin dake
gabansa ya kasa sha.

“Saboda Mai Martaba yace yana son ganin ka shiyasa ka wani damu ko?”

Ya ɗan ɗaga kai kaɗan ya kalli Ummi da idonsa na marar gaskiya.

“Eh mana, na san ba zai wuce yayi min maganar aure ba”

“Ai dole yayi maka maganar aure, tun da kai baka san ka girma ba, ace ko wace mace
baka so, kwana ki har ƙaryar ciwo kayi min sai gashi likitan ya ƙarya ta ka, wai
anya ba aljana take auren ka ba?”

Yayi dariya yana kallon ƙannensa mata su huɗu da suke zaune a ɗayan ɓangaren na
falo suna sha'aninsu.

“Abdool ya kamata ace kana yi ma kan ka faɗa, mahaifin ka yana son ka, kar kayi
abunda zai sa kyaunka ya ɓace a gare shi, kasan ƴan da matan uban nan naka suke,
basun ka suke su kuma zuga shi zasu yi ta yi har sai sun ga taren ku ya ɓace, duk
kuma wanda bashi da uwa a cikin gida yana cikin matsala dole ne yayi taka tsantsan”

Ya shafa kansa, yana jingina da kujerar dinning ɗin.

“Ummi Mai Martaba na da wani buri akai na, shiyasa ya natsa nayi aure, ni kuma bana
son sarautar nan, ni kwata-kwata ma ba dan shi ba Wallahi da ba zan zauna ƙasar nan
ba”

“Amman ai ba kai kaɗai ya haifa Namiji ba, amman kai ne mafi soyuwa a ransa, to dan
me ba zakayi masa abunda zai sa ya ƙara son ka ba? Indai baka fitar da wanda kake
so ba sai ya kai ga ɗaukar wata a cikin gidan nan ya haɗa ku, idan kuma ka ƙi yarda
kasan abunda zai biyo baya”

“Ummi wanda nake so ban san inda zan ganta ba, ban san yadda za'ayi na haɗu da ita
ba”

“Kamar ya?”

Ta tambaya tana kai ƙwallon anabi a bakinta.

“A Funtua na ganta bakin wani pharmacy, na fita nayi mata magana, tace min matar
aure ce ita”

“Ta faɗa maka ita matar aure ce kuma zaka so ta?”

“Sam bata min kama da matar aure ba mai igiya uku, sai da matar aure kalar aure,
ina ganin wannan take nufi, irin ƴan matan nan ne masu aji sosai, har marina tayi
fa”

Ummi ta gyara zamanta, irin na mutanen nan da naira ta zauna a jikinsu har ta nuna
kanta, ga kuma milkin dake cikin jininta, na ƴaƴan sarakai.

“Wayw Uban ta a garin nan?”

“Wallahi nima ban sani ba, irin yaran nan masu mugun ji da kan su, kuma na rasa
yadda zan yi na same ta, duk wata hanya da zata sadani da sake ganin ta nabi amman
ba nasara, har abinci naje na raba a inda ake sa ran zan ganta amman ban ganta ba,
kuma ni Wallahi ita nake so”

“To sai yaya kenan?”

“Sai na nemota duk inda na ganta zan gane ta, ba zata min marin banza ba sai na
rama, kuma gaskiya ba zan haɗu da ita hakan nan ba ga dukan alamun ita ce, dukan
matan da nake haɗuwa da su ban ji komai akan su ba sai ita”

Ya faɗa yana mai tashi tsaye.

“Anya ba aljana ka haɗu da ita ba Abdool?”

“Ba aljana bace Ummi”

A faɗa yana dariya, zuwa yayi ya mata side hug, ya ɗauki anabi ɗaya ya kai a
bakinsa, na biyu kuma ya jefe ƙannensa da shi.

“Ummi ki tsara min yadda zan cewa Mai Martaba”

Be tsaya jiran abunda zata ce ba, ya fice daga falon yana murmushi. Da kallo Ummi
ta bishi tana mamakin yadda ɗan nata yake ƙoƙarin zame mata aljani.

ANTY AMARYA POV.

Tun da Abbah yake maganar bata ce uffan ba har sai da ya kai aya. Sannan ta sauke
ajiyar zuciya tace.

“Zan musu magana, ai dukan su suna da manema, daga Hindatu har Maryam ɗin”

“Ƙara ayi musu magana su fitar da wanda suke so, da ba zan sake zaɓawa kowa miji
ba”

“To, Alhaji nacw har yanzu baka je ganin Mijin Namra ba, ya kamata ko a waya ne ka
kira shi ku gaisa”

“Ko Namra ce bata da lafiya ba zan kira ba, balle mijinta, ki daina kawo min wani
bato daya shafi Namra, baki san irin baƙin cikinta daya ke cikin zuciyata ba”

“Toh ni idan ka min izini ina son na koma naje na ganshi”

“Ba zaki koma ba, idan be gode da ganin da kika masa ba, ya bar shi, ba familyn ta
ya aura ba ita ya aura, kuma na sallama masa ita har abada, babu hannuna babu
ƙafata a lamarin Namra, ta zaɓi wanda take so sai taje ta zauna da shi”

Ko kaɗan kalaman Abbah basu yi ma Anty Amarya daɗi ba, nan take ta canja fuska,
ɓacin rai dake zuciyarta ya bayyana.

“Haba dai, wannan wane irin magana ne? Shikenan bata da damar ta zaɓi mijin da take
so? Wannan sam ba adalci ba ne, baka ƙaunar yarinyar nan kamar ba kai ka haife ta,
ɗan abu ƙanƙane sai ka ɗauki karan tsana ka ɗora mata”

Ta ƙarasa maganar da kuka.

“Ke kin fi kowa sanin na yadda na nunawa Namra so, ai ke ya kamata kiyi tunani kiga
rashin dacewar abunda Namra tayi min, ko da ace ba ni na haife ta, ya kamata ace
tayi min biyayya tun da nina raine ta har ta kai inda take yanzu, be kamata ta zaɓi
wani ta bar ni”
Kukan Anty Amarya ta cigaba da rera masa. Shi kuma ya ɗauki jaridarsa ya buɗe yana
karatu, ba dan kuma yana son karatun ba, sai dan yayi avoiding kukan na Anty
Amarya, tana da matsayi a zuciyarsa, ba kasafai yake son kukanta an itace mafi
soyuwa a zuciyarsa, duba da yadda take masa biyayya da kuma yadda take da ƙuruciya,
sama da Hajiya Barau data kwana biyu.
Idan kuma ya biye mata yasan halinta yanzu ne zata birkice masa, har ya rasa gane
kanta.

Data gaji da kukan ne, ta share hawayenta, ta tashi ta bar masa ɗakin.
Tana shigowa part ɗinta duka ƴaƴanta suka lura da yanayinta, ba ma kamar Maryam
data fi damuwa da ita sosai.

“Anty Lafiya?”

“Lafiya ƙalau, kawai ina tunanin Namra ne, ban san halin da take ciki ba babu waya
hannunta, kuma Abban ku yaƙi ya bar ni naje na duba su”

“Inshallah tana cikin ƙoshin lafiya Anty, kwana ki ma sai da ta turo da text wai ki
taimaka mata da kuɗi, ni kuma na goge text ɗin dan nasan Asim ne zai sata”

“Amman miyasa baki faɗa min ba? Baki san halin da take ciki ba, ƙaddara ce ta riga
ta faɗa mata babu yadda za muyi”

“Nayi tunanin ko shine yasa ta”

“Nawa tace a bata?”

“Bata faɗa ba”

“Gobe kije ki tura mata 300.000k sai ki kira wayar Asim ki faɗa mata, kuma kice ta
siye waya tasa layin ta, kwana kin nan mafarkin ta nake ta yi, ban san halin da
ƴata take ciki ba”

“Inshallah zan tura mata”

“Abbah ku ba ban saƙo gare ku, amman sai gobe zan faɗa muku”

Tana kai wa nan ta tashi ta nufi ɗakinta, tana share hawayen da suka zubo mata.

RASHIDA POV.

Tana gama aikin office ɗin ta dawo gida, tasan abunda ta shirya ma kanta shiyasa ta
dawo da ƙarfe shida tsaɓanin tara na dare data saba dawowa.
Ɗakinsa ta shiga tana masa bincike ko zata ga takardun results ɗin ko kuma jinin
daya ɗiba tun da yace mata be kai, amman bata ga komai ba. Har ta gaji ta dawo
dakinta .

Duk da tasan yau ba a ɗakinta Doc take ba, hakan be hanata chaɓa ado ba, dan ta
ɗauki hankalinsa. Daman ya saba duk wacce yake ba girkinta ba yakan shiga yayi mata
sai da safe, sannan ya wuce ɗakin da zai kwana.
Tun kamin ya shigo ɗakin, ta haɗa masa tea da lemun tsami dan tasan yana son haka,
ta kuma saka masa zuma a maimakon sugar, sai ta ɗauko maganin dake jakarta ta buɗe
ta kaɗa masa cikin tea ɗin har kusan guda biyar.
Tana mayarda jakar ta aje yana turo ƙofar ɗakin ya shigo, gabanta ya faɗi, abun ka
da wanda bata saba ba, sai dai ta wayance taje ta rumgume shi.

To her surprise sai ya sauke hannayensa daga saman wuyanta, yana ɗan murmushi. Bata
damu da abunda yake mata ba, dan a tunaninta fushin ɗazun ne na dress ɗin ta tayi.
Cup ɗin tea biyu ne sai ta ɗauki ɗayan ta miƙa masa.

“Ga tea”

Hannu ya kai ya karɓa ya furta

“Thank you, good night”

Har ya juya, sai kuma ya juyo ya kalleta kamar zai ce wani abu, sai kawai ya sakar
mata murmushin irin na fatar faki, ya juya ya fice.

Ɗakin Kalsoom ya nufa, ko da ya shiga ciki be ganta ba, ya duba bathroom bata ciki,
sai kawai ya nufi ɗakin su Ezzah dan yasan ba wuce tana can ba.
A tsakiyar gado ya tsame ta tana ta tofawa yaransa addu'o'i, su kuma sai bachi suke
tayi abun su. A bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta yana murmushi, har ta gama ta
taso ta nufo shi.

Hannu ya kai ya laƙƙamo kunkurunta, jikinta ya haɗe da nashi, ita kuma sai haɗiyar
yawu take tana kallon kofin dake hannunsa, ƙamshin tea ɗin yana kai ma hancinta
ziyara.
Kaɗan ya kurɓa ya kai mata kofin a baki, ɗan tsami tsamin data ji yasa ta jidaɗin
tea, ta riƙe kofin da hannu biyu har sai da ta shanye tea ɗin gaba ɗaya.

Tana shanye tea ɗin ta saki kofin tayi masa kwance a jikin, wani irin bachi mai
bala'in nauyi yayi gaba da ita.

“Hey...”

Ya faɗa yana girgizata, amman ina, tayi nisa har ƙoƙarin zubewa take a ƙasa,
hannayensa yasa ya ɗauke ta cak, ya nufi ɗakinta da ita. Saman gado ya kwanatar da
ita ya kwanta gefenta yana shafa fuskarta, zuciyarsa cike da mamakin abunda yake
cikin tea ɗin.
Ya kusan minti talatin a gurin kwance, sai yaƙi yake da bachin dake son sace shi,
yana unƙurin tashi yaji an turo ƙofar ɗakin, ƙin motsawa yayi sai ya lumshe ido
kamar yayi bachi, sai ga Rashida ta ƙaraso har gurin tana leƙen fuskarsa, har da sa
hannunta tana masa yawo da shi dan ta inda gasken yayi bachin.

Da sauri ta juya ta fita ta nufi ɗakinsa, keys ɗin motarsa ta ɗauka, ta fito waje
ta buɗe motar tana masa bincike, seat ɗinsa na gaba ta buɗe ta fara bincikar
takardun da suke gurin. Jikinta ne ya bata ana kallonta, da sauri ta fito daga
motar, sai taga Doc tsaye ya rumgume hannayensa yana kallonta.

Kasa motsawa tayi, numfashita mai sai da yayi nisan zango sannan ya dawo, jin tayi
kamar ƙasa ta buɗe ta shige ciki, a take mararta ta cika da fitsari.

___________________________________________

One free Page remained 🙌

BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY 😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng
*PAGE - 35. Last Free Page*

NOT EDITED ⚠️

Bata taɓa sanin gume na da zafi ba, sai a wannan lokacin, wani irin nauyi ta ji
kanta yayi kamar an ɗauki duniyar nan an ɗora mata, yau ganin Hilal take ya cika ko
ina na duniyar idanunta.
Yau kam ba ranar kuka ba ce, tashin hankalin daya same ta ya fi ƙarfin kuka,
hakan yasa hawaye ba kusanci idonta ba, ashe abu mai sauƙi ake ma kuka, ta kasa
yarda yau ita ce Hilal ya kama dumu-dumu ba.

“Kin san kina da HIV kike ƙoƙarin ɓoyewa Rashida? Do you know what lokacin dana
ɗibi jinin ki result ɗin ba ɓata yayi ba, nace miki haka ne saboda ban yarda da
abunda idona ya gani ba, na dawo na ɗibi jininki da na yarana da na Kalsoom nawa
dan na gwada, so that na tabbatar idan da gaske kina ɗauke da cutar ne, amman ke
kin san kina ɗauke da cutar kika bar ni ina kusantar ki?

Da ba dan wanann cikin ba, da sai mu ɗauki dogon lokaci a tare da dake baki faɗa ba
right? What if all of us mun kamu da cutar nan?”

Ƙiri-ƙiri tayi masa da ido, cikin ƙarfin hali ta cira ƙafarta da tayi mata mugun
nauyi ta tako ta ƙaraso kusa da shi.

“Kana tabbacin ni ce kaɗai nake ɗauke da cutar? Kasan ta ina cutar ta shige ni?
Miyasa idon ka zai rufe har haka?”

“Ke da kan ki kike zargin kan ki, dan me zakiyi ma Doc Sabo transfer 100,000k? Dan
me zaki ce idan ya kawo jinin kamin ya auna ya kira ki? You late Rashida ko da kika
kira shi na riga na kai jinin amman yaƙi ya faɗa miki saboda ya san ni kamin ya
sanni kuma ya san aikinsa, daman nasan ziyarar da kika kawo min ɗazu a office bata
banza bace cox na lura dake kwata-kwata hankalinki baya jikin,

Bincike da kika min da tambayoyin da kika min ya tabbatar da akwai wani abu, and
now what kin sa abu a tea ki bani nasha so that kiyi iya binciken ki ko? To bari na
faɗa miki if something happens to my wife hmmm you're in trouble”

Sai a yanzu hawaye suka samu damar cika idonta har suka silalo zuwa kumatunta.

“Saboda na san idan kasan ina da HIV ba zaka faɗa min ba, idan har ya tabba ina da
HIV Hilal to ta hanya ɗaya na same shi, wato sex kuma wani namiji be taɓa kusantana
ba sai kai, a lokacin dana bar ka ya kusance ni ban san komai ba, sai a ɗazu nasa
an nemo min Doc Sabo saboda na tabbatar idan har da gaske ina cutar ne, do you know
who i try to protect? You and your dirty wife, Asmee told me everything about your
bride but very soon gaskiya zata yi halinta, kuma ba zan taɓa yafe mu ku ba, aje
ayi gwajin”

Tana kai nan ta raɓa gefensa ta wuce cikin falon. Juyowa yayi ya bita da kallo
zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama.
Kalamanta basu kama zuciyarsa ba, amman suna ƙoƙarin zaunawa akansa, what he
believe shi dai yana da protection ɗin da ba kasafai cutar zata yi saurin kama shi
ba, ko baya da protection, he's Doctor ya san cutar bata saurin kama namiji kamar
mace, dan namiji ɗaya mai hiv zai kwanta da mace goma to dukkan su sun zama patient
living with hiv, wato sun shiga sahun masu dauke da HIV acikin al'umma.

Amman mace ɗaya mai HIV zata kwanta da namiji 10 a rana, abu ne mai sauki namiji 2
ko 3 suka mu da wannan ciwon mai karya garkuwar jiki. Namiji zai iya daukan HIV
kawai idan yana da wata kafa a gabansa abunda ya shafi kurji, yanka ko tsaga.

“He's lie”
Ya furta a hankali, yana murza saman goshinsa, zuciyarsa ta kasa yarda da zancen
ta, duk da yasan Kalsoom take nufi, dan ita daya auna jininta be nuna haka ba,
amman yasan result ɗin zai fito kuma dole gaskiya tayi halinta.

Shigowa yayi cikin falon cikin tunani da sarƙaƙiya, a saman babbar kujera ya zauna,
ya dafe kansa, ɗaurewar da kansa yayi shi ya hana shi bachi har safe.
Har yayi sallah asuba ya dawo, be ji motsin Kalsoom ba, ita daya san wani lokacin
ma takan riga shi tashi, a falon ya zauna yayi addu'o'insa sannan ya shiga ɗakinta,
yadda ya tararda ita kwance rigingim har sai da ya tsorata, wani irin ninshari take
kamarmacijin nan mesa na bachi, yayi mata girgizar duniyar nan amman ina, in ma ban
da ƙara nauyin bachi babu abunda take.

Da sauri ya fita ya shiga ɗakinsa duba keys amman be ganshi ba, sai a lokacin ya
tuna da suna guri motarsa da Rashida ta saka su jiya, da sauri ya fita daga ɗakin
ya nufi gurin motar, ashe ma buɗe ta kwana, shiga kawai yayi ya kunna ta ya bar
gidan.

Rashida na jin tashin motarsa ta duba agogon ɗakinta, 6:55am ya nuna, bata damu da
rashin warewar gari ba ta tashi ba tare data tsaya wanka ba, ta canja tufafin
jikinta zuwa atamfa ta ɗauki abaya ta ɗora sama, sannan ta ɗauki handbang ɗinta ta
fice daga ɗakin.

Cikin sauri ta shiga motarta tayi mata keys gudun kar Hilal ya dawo, dan yanzu kam
sam bata son haɗa ido da shi.
Gidan su Asmee ta nufa, cikin ƙanƙanen lokaci ta isa, haka ta riƙa musu horn har
sai da mai gadin ya buɗe mata gate, kusan da motar Alhaji Bashir ya faka motarta,
daman tasan yana nan dan yanzu be isa fita ba. Ƙofar falon ta riƙa bugawa tana
sallama kamar zata tashi gidan.

Alhaji Bashir ne ya buɗe mata ƙofar yana tambayar lafiya, dan tun da yaji muryarta
hankalinsa ya tashi, a tunaninsa ko tazo tayi masa wani abun ne.
Tun daga samansa ta kalle shi har zuwa ƙasan shi, daga shi sai guntun wando, sai da
ta kai zuciyarta nesa sannan ta iya ƙirƙiro murmushi ta yaɓa a fuskarta.

“Matar ka na nan?”

“Lafiya kika mana sammako haka?”

“Lafiya ƙalau, sirrin mu ne, saƙon zan bata”

Kamin ya ƙara cewa wani abu har Asmee ta ƙaraso gurin tana tambayar wanene.

“Nice na doko muku sammako, saƙon ki zan baki”

Rashida ta amsa da kanta, tana mata murmushi. Wani kallo Asmee ta watsa ma Alhaji
Bashir, irin ya zaka zo daga kai sai guntun wando haka. Sai kawai ya juya ya shige
ɗakinsa.
Asmee ta riƙo hannunta suka shigo falon.

“Ke lafiya kika zo haka?”

“Taimakon ki nake nema, idan har baki taimake ni ba, zamu iya rasa ran mu ni da
mijina”

“Subhanallahi miya faru?”

“Mijina ya aiko ni zuwa gare ki, maganar da zan faɗa miki sirri ce bana son kowa
yaji, ko da kuwa mahaifiyarki ce ko mijin ki”
“Ban taɓa sirri dake ba na faɗawa mahaifiyarta ba, balle kuma mijina taso muje
ciki”

Dar ƙarshen gadonta, Asmee ta kai ta suka zauna, sannan ta kalle ta tace

“Faɗa min damuwarki, matuƙar ina da maganinta wallahi zan miki”

“Irin samarin nan nake nema kidnappers”

Asmee ta daki ƙirji.

“Aka yi da wani ko za'a miki?”

“Wani muke son a a ɓoye mana shi, saboda ta hanyar shi ne kaɗai ne, mijina zai
cigaba da rayuwa da ni, dan Allah idan kin san inda irin mutanen nan suke ki faɗa
min”

“Ni ɗan maye ma miye haɗina da shi balle kuma ɗan kidnapped, Wallahi ban san wani
mai wannan aikin ba”

Rashida ta kama hannayenta ta riƙe ta fara kuka.

“Ko cikin ƙawayen ki ba kisan wacca tasan mai irin wannan aikin ba? Dan Allah Asmee
ki ceci rai na”

“Bana da ƙawar da zata iya faɗa min sirrinta har haka sai ke, ko da suna da irin
waɗannan mutanen ba zan iya sani ba, sai idan gurin wannan Malamin zaki je, sai ya
haɗa ki da wani cikin masu zuwa gurinsa, dan yana basu taimako sosai”

“A ina Malamin yake? Dan Allah ba ni addireshinsa”

“Ba a cikin garin nan yake ba, a ɗan dutse yake da kin shiga garin ɗan dutse kika
ce Malam mai gobe da nisa ko ƙaramin yaro yasan gidan sa, bari na baki number
wayarsa, kamin ki isa zan kirashi na faɗa masa”

“Na gode Allah ya saka miki da alheri, samin number”

Ta faɗa tana miƙa mata wayarta. Sai da Asmee ta saka mata Number sannan tace

“Amman kin san garin kuwa?”

“Karki damu zan tambaya har na isa garin, ai bada motana zan je ba, gidan mu zan
bina na aje motar, saboda gudun sa ido”

“Allah yasa a dace, amman ina jin tsoro Rashida”

“Babu abunda zai faru, ba mummunan abun zan aikata ba”

“Dan Allah aro min niƙab ɗin ki da Hijab”

Ba musu Asmee taje ta ɗauko mata ta saka.


A gaggauce ta fice da daga gidan, zuciyarta har wani ɗar-ɗar take, tana ayyana irin
rashin mutuncin da zatayi Doc Sabo, lallai yau zata nuna masa ta fishi zama yar
duniya, Zagon ƙasan da yayi mata ƙarami ne, yanzu zata masa babban.

Kamar yadda ta tsara, a gidansu ta biya ta aje motar, ko cikin gidan bata shiga ba,
balle su gaisa da Momi, tana rufe motar ta fito ta tari Napep ta shiga, ya ɗauki
hanyar tasha da ita.
HILAL POV.

Be daɗe ba ya dawo, daman allurai kawai yaje ya ɗauko, yana shiga ɗakin ya haɗa
allurar yayi mata, sannan ya ɗauko tawul ya jiƙa shi da ruwa, ya riƙa dafa mata a
goshi.
A hankali ta fara motsi tana nishi da miƙa irin ta gaji sosai ɗin nan, hankalinsa
ya ɗan kwanta lokacin daya ga ta buɗe idonta, sai ya sakar mata murmushi.

Daker ta unƙura ta tashi zaune, saboda nauyin da jikinta yayi mata.

“Wane irin bachi nayi haka?”

“Magani na saka miki a tea ɗin, tashi kiyi sallah”

Ta ɗan kalli window taga yadda rana ta fara hudowa, sannan ta unƙura da zimmar
tashi tsaye, sai Doc ya kai Hannu ya riƙa hannunta.

“I trust you Kalsoom dan Allah kar ki bani kunya”

Wani kallo tayi masa, irin ban gane ba. Sai kawai yayi murmushi yana ƙoƙarin ɓoye
feelings ɗinsa.

“Yanzu idan aka ce ina da hiv zaki zauna da ni?”

Dawowa tayi ta zauna, ta kai hannayenta ta riƙa fuskarsa.

“Idan har kana da hiv zan zauna da kai, kuma idan har kana da shi nima nasan ina da
shi, so babu dalilin ƙyamar juna”

“What if aka ce ke kike ɗauke da shi ba mu ba?”

Shiru ta ɗan yi tana nazarin tambayoyinsa, anya Doc zai mata irin wannan tambayar
haka kawai.

“Idan har ni nake ɗauki da cutar zan nisanta kai na daga gare ku, gudun kar ku
kamu da cutar, har sai ta zama aids, domin wannan kwayan cuta HIV (human
immunodeficiency virus) bata rayuwa da keu a wajen jiki, saboda haka akan iya
kamuwa da ita ta hanyar kissing ko kuma yin anfani da wani abu wanda me dauke da
cutar ke anfani da shi, kamar kofin shan ruwa, abun yanke farce, da brush.

Amman da zarar cutar ta kai marhala na karshe ma`ana AIDS (acquired


immunodeficiency syndrome) zan cigaba da mu'amala da ku kamar yadda na saba,
saboda ba`a kamuwa da ita ta hanyar kissing, cin abici tare da me dauke da ita,
amfani da kayayyakin ko abubuwa da me dauke da ita ke anfani da su, kamar kayan
sawa, wayan salula, agogo, wanka a swimming pool, zama a kujera, cizon sauro, ma
taci comb, tawul, da kuma tafiya, hada hanu, zama,da yin aiki tare da me dauke da
cutar, amman ba zan bari ka kusance ni ba, ko da kuwa zaka na shan magani da
amfanin da kororon roba, saboda it's risk.

Sai dai kuma ka sani, rayuwata zata tarwatse zan nisanta da ƴaƴanka, duniya zata
ƙyamace ni, kuma dole na rabu da kai”

Ta ƙarasa maganar hawaye na bin fuskarta. Ɗan murmushi yayi ya tashi yana ƙoƙarin
ɓoye hawayen da suka cika masa ido.

“Intelligent woman, je kiyi sallah zan haɗa ma yara breakfast”


Har ya fice hawaye take, zuciyarta cike da tunanin abunda yasa Doctor yayi mata
wannan tambayar.

NAMRA POV.

Ko ta koma gida, ta samu duk sun tafi walimar aure, ta wata maƙociyarsu, da ake yi
yau jumma'ah. Mardiya ce kawai a gidan, ta zauna cikin ɗakin ta rafka uban tagumi.
Sallamar da Namra tayi ma sai da ta firgita ta.

“Ke lafiya kike kuwa? Ke kaɗai aka bari a gidan?”

Namra ta tambaya tana zama kusa da ita. Ajiyar zuciya mardiya ta sauke.

“Kawai ina tunanin rayuwa ne”

“Rayuwa kuma kamar ya?”

Shiru tayi tana tunanin irin ƙaryar da zata yi ma Namra, dan bata son faɗa mata
asalin abunda yake damun ta.

“Inna ce duk ta bi ta dame ni akan rashin auren nan, kamar ni nayi ma kai”

“Ayyah wai wani abun ba'a kusa yake ba, komai yana da lokaci”

“Na sani matsalar iska ne yake damuna, ina ganin kamar shine ya hana ni aure, amman
ita inna ta kasa ganewa”

Ta bijiro da damuwarta a fuskarta kamar da gaske abunda yake damunta ɗin kenan. Ita
kuma Namra sai tausayinta take.

“Ki riƙa azkar kina faɗawa Allah damuwarki, inshallah zai miki magani”

“Ina yi Wallahi babu inda ba mu shiga akan neman taimako ko ina sai ace mana Aljani
ne ya aure ni”

“Subhanallahi, amman Mardiya, ai dole aljani ya aure ki tun da kina yawo babu
ɗankwali, gashi kina yawan sauraren waƙe-waƙe, da ace baƙara kike yawan karantawa
nayi imani ba zai samu nasara akan ki ba”

Ajiyar zuciya Mardiya ta sake saukewa, a karo na biyu, ta ƙara gyara zamanta.
Namra ta kalleta cike da tausayawa tace

“Ki samu allo ki rubuta suratul azari, daga farkon ta har ƙarshe, idan kin yi
alwala la'asar kika rage ruwa sai kiyi amfani da su ki wanke rubutun ki shanye har
kwana uku, indai matsalar aljani ne mai hana aure inshallah zai rabu da ke”

“Na gode sosai Inshallahu zan gwada”

“Allah yasa a dace, da naso ki raka ni kasuwa amman naga kamar kina cikin damuwa
bari mu bari har gobe”

Kamar kar Namra tayi maganar nan da nan Mardiya ta kai idonta gurin ƙaramar jakar
da Namra take riƙe da ita, sai kuma ta kawar da kai.

“Mu bari har goben dai yanzu yamma yayi”

“Eh nima ai haka na gani”


Ƴar nokiyar dake hannun Mardiya ce tayi ƙara, sai ta tashi ta bar ɗakin tana amsa
wayar.
Tashi Namra tayi ta cire hijabinta, ta rataye, sannan ta ɗauki jakar wanda kuɗin
suke ciki ta saka a cikin akwatin Mardiya na kaya, da zimmar ta aje a cikin dan kar
taje ta jefar da ita wani gurin, sannan ta fita ta kama ruwa.

RASHIDA POV.

Data isa tasha, shatar motar ta ɗauka ita kaɗai, ya kai ta ƙauyen. Bata sha wahala
ba gurin gane gidan, tambaya ɗaya suka yi aka nuna musu gurin, gidan ne mai kyau
kamar ba ƙauye ba. Sun tarar da layin mata sosai a gurin haka ta samu guri ta tsaya
har aka kai gareta. Sannan ta shiga.

Ƙaton ɗaki ne mai cike da kayan alatu, ba dan rawanin da taga ni a kansa ba, da
zata iya rantsuwa da Allah tace wani attajiri ne ba malami ba, sai dai hakan be
bata mamaki ba, dan tasan duk mutumen dake aiki da manyan yan siyasa dole ne ya
tara komai.
Kallo ɗaya yayi mata ya soma gyara ƙasar dake gabansa yana faɗin ta cire niƙabin
ta, ba musu ta cire niƙab ɗin tana gaishe shi. Be amsa ba har sai da ya gama bugun
ƙasar sa, sannan ya kalleta yace.

“Kin zo nan ne dan a haɗa ki da wani yayi miki wani aiki”

“Haka ne ni ƙawar Asmee ce, tace zata kira ka”

Sai da ta ciro dubu hansin ta aje masa a gabansa, sannan ta koro masa da bayani.
Sai da ta gama sai yayi murmushi yace

“Zan haɗa ki da wani, saboda kawai Asma'u ce ta turo ki, amman ba dan haka ba, babu
abunda zai sa na haɗa ki da shi, saboda shegen mutum ne, ni kaɗai zan iya sashi abu
yayi nan take”

“Na gode Malam, idan har aiki yayi kyau, kai ma zaka jidaɗi inshallah”

Wayarsa ya ɗauka ya kira, yayi tsowon minti ashiri yana lalasar mutumen sannan yaba
Rashida waya suka yi magana ya faɗa mata inda zata same shi.

Bayan sun gama malamin ya kalleta yace

“Idan buƙatata da biya ki dawo ina son ganin ki, dan gaskiya akwai matsala a tare
da ke, kuma akwai abunda yake shirin faruwa da ke, dole ne sai kin nemi taimako”

“Inshallah, zan dawo”

Da tsoro tayi masa sallama, tana ta tunanin wane irin matsala ne, zuciyarta nata
raya mata lallai wannan malamin yana aiki kam.
Tafiyar mintuna arba'in suka yi, suka dawo cikin gari, kai tsaye tace direban ya
nufi American Unique Estates da ita, a dai-dai inda ya kwatanta mata ta tsaya, ta
kira number da Malamin ya bata ta mutumen tace masa tana gurin, sannan ta sallami
direba fiye da yadda suka yi jingar.

Tsaye kawai take a gurin amman babu natsuwa a tare da ita, ji take kamar wani zai
zo ya ganta. Bayan kamar mintuna asirin da biyar wata ƙafirar mota ta faka gabanta.
Wani Namiji ne mai shigar mutunci ya fito cikin motar tare da Amira.

“Ke ce Rashida wacca Malam ya aiko?”

Namijin ya tambaya.
“Eh nice”

Amira ta buɗe mata Motar.

“Shiga muje”

Da tsoro ta shiga motar, zuciyarta duk bata natsu da su ba.

___________________________________________

Assalamu alaikum as i said yau na kai Page 35, that's means na gama free pages
kenan. Dan haka duk mai son ƙarashin wannan labari zai iya turo ₦200 zuwa wannan
account 0314795884 Abubakar Hadiza GT Bank.

Sai ku turo da shaidar biyan kudin wato screenshot ta wannan number 08036126660.
Zan saka ku group inda zan riƙa updated littafi kullum inshallah.

Na yi haka ne duba da yadda wasu suke ci da gumi na, akwai wanda ya ƙirƙiri grp a
whatsapp ana tura masa naira ɗari yana tura littafan marubutan online cikin har da
nawa, sannan akwai wanda ya ɗauki littafina na MAIRO ya maida shi application ya
ɗora a Google play store, wanda duk yayi downloading ɗin app ɗin sai google sau
biya shi, idan kuma suka ɗora talla a app ɗin kuma wannan shima sai sun biya shi,
ni da nayi rubutun ban ci ba shi ya ci. Bayan haka an ɗauki littafina na SALEENA an
saka a okadabooks, ba tare da izini na ba, wanda idan aka siye kuɗin zasu je ga
wanda ya saka littafin ne ba gare ba, idan kukayi searching duk zaku ga abunda nake
faɗa muku na Application da okadabooks.

Dan haka ya sa na canja wannan littafin uzuwa na kuɗi, dan nima na ci amfanin
abuna, da wani ya ci da gumminka ƙara ka san kai ka ci, ko yayane, dan baka san ta
rai ba. 😀
Ina roƙon duk wanda na ɓatawa rai sanadin canjin nan ko kuma littafin nan, dan
Allah ku yafe min, nima ban za ci sauyin zai zo ba, sai daga baya, da tun farko na
faɗa. Ina roƙon alfarma dan Allah kar wanda ya mai da min da Littafi document.

Na gode da shawarwari da ƙauna, Allah ya sakawa kowa da Alheri. I love you all

BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY 😘

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Write by_
*Khadeeja Candy*

*PAGE - 36*

NOT EDITED ⚠

Nitsa kai suka yi tayi cikin unguwar, sun yi tafiyar mintina goma zuwa sha uku,
sannan suka isa ƙarshen unguwar, a bakin wani makeken gate black color.

Tsoron dake cikin zuciyar Rashida ya kasa ɓoyuwa har sai da ya nuna a jikinta, gani
take kamar wani abun zasu mata har ta buɗe baki tayi magana, sai ta tuna da abunda
ya kawo ta gurin, kuma ta san bata da wata mafita sai wannan.
Sai kawai tayi shiru da bakinta ta sakar musu na mujiya har suka faka bakin wata
babbar ƙofa. Amira ce ta fara fita tana faɗin
“Fito muje”

Buɗewa Rashida tayi ta fito, sai mutun ya ja motar ya nufi wani ɓangare na gidan da
ita.
Amira tayi gaba, Rashida ta rufa mata baya sai kalle-kallen gidan take.

Cikin wani ƙaton falo suka shiga, wanda aka ƙawata da kayan alatu, kallon falon
tayi sosai ba dan ya birge ta ba, sai dan ɗaukar rahoto ta karanci wane irin gida
ne aka a kawo ta.
Kamar daga sama ta ji Amira na mata magana.

“Idan baki yarda da gidan ba, miyasa kika shigo? Ko kina tunanin za mu miki wanin
abun ne?”

Kasa cewa komai, tayi har Amira ta gaji da tsayi a gurin, ta isa gaban wata babbar
kujera ta zauna tana cire gyalen abayarta.

“Guy Son!”

Ta ƙwala mishi kira, tana nuna ma Rashida kujera.

“Zauna idan zaki iya”

Rashida ta zauna zuciyarta na ɗar-ɗar, wani tunanin ne ya zo mata. What if tafa


mutumen data sani? Ko kuma gidan yana tare da Dr Sabo fa?

Fitowarsa yayi dai-dai da sauke ajiyar zuciyar da Rashida ta yi, a yanayin shigarsa
da kamalarsa, bata zace shine Guy Son ɗin ba har sai da ya zauna kusa da Amira,
jikinsa yana Gugar na Amira.

“Wa kike son ayi miki garkuwa?”

Ya tambaya, fuska babu alamar murmushi balle wasa.

“Wani mutun ne, sunan shi Doc Sabo a asibin Alex yake aiki sashen jini”

“Cire Niƙab ɗin fuskarki kiyi mana bayanin komai”

Tasa hannu ta cire Niƙabin ta gyara zamanta sannan tace

“Mijina ne ya ɗibi jinina dana yara na ya kai masa akan yayi mana gwaji, bana da
tabbaci amman ina jin kamar ina ɗauke da cutar hiv kuma ina tunanin mijina da
kishiyata basa da shi, na karɓi numbersa gurin abokin aikina na kira mun yi magana
akan zai faɗa min idan mijina ya kawo jinin, har na tura masa dubu ɗari, sai gashi
ya yaudare ya faɗawa mijina na bashi kuɗi”

Ya kai hannunshi ya riƙa hannun Amira yasa yatsunsa cikin nata.

“So kina son ayi forcing ɗinsa ya canja result ɗin ko?”

“Haka nake so, matuƙar ya faɗi gaskiya, mijina zai rabu da ni, kuma duniya zata
ƙyamace ni, zan ba ku ko nawa kake so, dan Allah ku taimaki rayuwata”

Amira ta ɗan yi murmushi.

“Ba shi kike son ayi a ɗauke miki ba, ƴaƴansa za'ayi kidnapped sai asa shi dole ya
faɗi abunda kike so”
“Koma yaya ne ni dai yi min zan biya ko nawa kuke so”

Ta faɗa tana karyar da murya irin tausayin nan. Wayar dake hannu ya karɓa, ya saka
wata number ya kira, ana picking yace

“Zo nan ina neman ka”

Be fi mintuna uku da aje wayar ba, sai ga mutumen ya shigo cikin ƙaƙanan tufafi,
yazo dai-dai shi ya tsaya, Rashida na kallonsa gabanta ya faɗi saboda jan idonsa.

“Ka bincika min addireshin Doc Sabo yana aiki a Alex hospital sashen jini”

“Okay Boss”

Sai ya juya ya fice. Guy son ya kalli Rashida ya ce

“Bani addireshin ki, kuma karki kuskura ba ni na ƙarya dan zan gano ki”

Gabanta ya faɗi sosai, kuma ta tsorata, bata son bashi na ƙarya tun da har ya
gargaɗeta, sai dai kuma idan har ta ba shi adireshin na gaskiya, bata san abunda
zai faru ba.

“Sunana Rashida Abdullahi Kardam ina aiki a Stanbic Ibtc Bank, mijina babban likita
ne, yana aiki a Kaduna special hospital, muna nan GRA magaji road”

“You can go, zaki ga motar data kawo ki zata maida ke inda kike”

“Thank you”

Ta saka niƙabinta ta saka sannan ta ɗauki jakarta ta fice. Amira ta tashi ta nufi
gurin window falon ta tsaya, tana kallon harabar gidan. Tana sinkayar motar har
suka fice, sannan ta sauke ajiyar zuciya, ta jingina da gurin ta rufe ido.

Hannunshi yasa cikin jikinta yana murza fatar jikinta, ya fara shinshinar gefen
wuyanta. Buɗe idon ta yi ta ture shi da dukan ƙarfinta.
Kallon da zai yi sai hawaye ya gani sun silalo daga idonta. Yarfarda hannu yayi ya
cije fuska.

“So nawa zan faɗa miki bana son hawayen nan”

“Ka bar ni nayi kuka na, ai ina da dalilin kuka”

Hannu ya kai ya riƙe fuskarta iya ƙarfinsa ya matse ta.

“Ba dalili bane, idan har kina son iyayen ki dole ne ki koma gare su, amman kin
kasa kuma kin ƙi ki faɗa min gaskiya, saboda kin san mugun abun da kika aikata”

Yana kaiwa nan ya wurgar mata da fuska gefe, ya wuce ciki. Da kallo kawai ta bishi
idonta na hawaye, wani irin zafi zuciyarta ke mata, ita kaɗai tasan irin abunda
take ji.
Bata ganin laifin kowa sai Uzair da Namra, dan sune suka rusa mafarkinta, suka
gurɓata duniyarta, suka canja tunaninta, sun salwantar da farincikinta, sune
sanadin barin gidan iyayenta, sune suka sa duniya ta zage ta, sun yi nasarar
sauyata daga mutum zuwa mutum mutumen da kowa ke kallonta.

Lallai bata da maƙiya kamar su, bata da wani buri illa na ganin bayan su. Har yanzu
zuciyarta bata lurar da ita illar abunda ta aikatawa Namra ba, bata ganin asirin ne
ya koma mata, gani take kamar da haɗin bakin Namra Uzair ya cuce ta.
Tana son komawa gida amman hakan sai ya gagareta, idan ta tuna yadda ta bar kowa
nata, ta watsar da karatun ta, ta dawo nan ta zauna, sai taji kamar ta haɗiye
zuciya ta mutu.

Rayuwarta ta zame mata kamar mafarki, yadda sauyin yazo mata, sai yayi mata kamar a
shirin fim ko littafi, silar su ne take a cikin halin da take ciki. A yanzu kan
bata da mafarki sai na Namra da Uzair bata da buri sai na su.
Ƙarar buɗe ƙofar gidansu da tayi ta fita ne ya dawo mata sabo, yadda ta kai kanta
har tasa ta bar garin sokoto ne ya riƙa mata yawo a ƙwaƙwalwa.

Durƙushewa tayi a gurin ta fashe da wani irin mahaukacin kuka, tana yagar fuskarta.
Da sauri Guy son ya fito daga ɗakin daya shiga yazo ya rumgume ta yana rarrashinta.

“Shiiiiiiiiiii, I'm sorry Amira, I'm so sorry”

Ya ɗora kansa saman na ta yana girgizata, alamar lallashi, har cikin kansa yake jin
kukanta, son ta na masa yawa a ko ina na gaɓoɓinsa.

RASHIDA POV.

A inda suka ɗauke ta ɗazu, mutumen ya sauke ta, sai ta tari Napep ya kai ta unguwar
da iyayenta suke. A nesa da gurin tasa ya sauke ta ta sallame shi, sannan ta taka
da ƙafa ta ƙarasa cikin gidan.
Sai da ta buɗe motarta ta saka jakarta sannan ta, ta shiga cikin gidan, bakinta
ƙumshe da sallama. Da far'ah Momy ta amsa mata.

“Ma'aikatan kuɗi yau a gidan na mu?”

“Wallahi kuwa, yau kin san babu aiki”

“Yau kuma har da hijabi! Aiko kin ga yadda ya fitar da ke, mashallah”

Zaunawa tayi tana murmushi.

“Momy kenan, shi saka Hijabi har wani abun ne?”

“Wani abun ne mana, shiyasa abokiyar zaman ki take burgeni saboda ta san kanta
sosai, duk inda zaka ganta da hijabi zaka ganta, kin ga irin wannan matar? Da
wahala wani namiji yayi mata maganar banza, Hijabi ne abu ne mai muhimmanci Rashida
tun da har ki ga musulunci ya koyar da mu saka shi ai kinsan yana da kyau”

Ta ɗanyi murmushi, wanda be kai ciki ba murmushin rashin jindaɗin maganar da Momy
tayi na Kalsoom.

“Nikan bana burge ki ko Momy?”

“Ba haka nake nufi ba, yadda ɗabi'unta da halayenta yake haka na so naki ya
kasance, amman sai ki ari wata rayuwar ta daban kika ratayawa kanki, kika ɗauki
wani hali wanda ban san inda kika samo shi ba kika laƙabawa kan ki”

“Uhmm Momy ban yi breakfast, yunwa nake ji sosai”

Ta faɗa da nufin kawar da wacan maganar ta Momy, shiyasa bata cikin son zuwa gidan
ba, duk lokacin da tazo sai ance tayi wani abu ba dai-dai ba, yanzu ma abun ya wuce
guri har abokiyar zamanta Momy take yabo, ita kam bata taɓa ganin uwar dake yabon
kishiyar ɗiyarta ba sai nata uwar.
6ana ɗaya daga cikin dalilin dayasa Kalsoom ta zame mata ƙashin wuya, amman wannan
matsalar da take ciki yasa ta ma manta da ita sai yanzu da Momy take tsokaro mata
tsatsar ƙiyayyar da tayi mata katutu a zuciya.
A gidan da wuni, duk irin tambayar da Momy tayi mata na barin motar ta da tayi taje
wani gurin, ƙin faɗar inda taje tayi, balle ma har ta faɗawa Momy dalilin zuwan
nata.
Tasan bayan sallah magariba Hilal baya gida, dan a masallaci yake sallah
magariba kuma baya shigowa gida sai anyi isha'i, hakan yasa ta dawo gida a lokacin,
dan bata son ta dawo lokacin da yake nan.

Ta jidaɗin rashin ganin ɗaya daga cikin motocinsa hakan ya tabbatar mata da baya ma
unguwar kenan, sai da ta cire hijabin ta bar a mota sannan ta fito, ta nufi hanyar
falo.
Ɗora ƙafarta da zatayi sai gabanta ya faɗi, maido ƙafar tayi tayi baya-baya tana
sauraren bugun zuciyarta.
Ta kusan minti biyar a haka, sannan ta kai hannu ta tura ƙofar ta shiga, bata ga
alamun motsin kowa a gidan ba, hakan ya tabbatar mata da dukansu basa nan. Sai da
ta leƙa ɗakin yaranta, taga babu kowa sannan ta nufi ɗakinta.
Jakarta ta fara ajewa tana sauke gajiya, sannan ta cire tufafin jikinta, ta shiga
banɗaki tayi wanka, ta fito.
Dressing mirror ta nufa, ta shafa mai da turare sannan ta zauna tana nazarin
duniyarta, idan har ta aikata abunda take da niya, to asirinta ya rufu, sai ɗayan
kuma tana tunanin makomarta, akan abunda take ƙoƙarin aikatawa. Wani dogon numfashi
taja ta sauke. Sam bata lura da takardun dake saman gadonta ba har sai da ta unƙura
zata tashi.

Gabanta ya faɗi, a iya tunaninta bata san ta bar komai a saman gadonta da zata fita
ba, sannan yanayin takardar be yi kama da documment ko file ba. Matsawa tayi kusa
da gando ta kai hannu cikinn rawar jiki ta ɗauki takardaun.

Tana fara karantawa ta ji kamar an mata shocking, wani abu yazo mata tsam tun daga
saman kanta har zuwa cikin ƙafafunta, bata ankaro da duniyar da take ciki ba, har
sai da jini ya fara bin ƙafafunta.

NAMRA POV.

Sai da yamma sosai ƴan gidan suka dawo, abun walima ɗaya Inna ta bawa Mardiya tace
su raba ita da Namra. A tare suka ci, lemun da yake ciki Namra tacw ba zata sha, ta
bar ma Mardiya.

Bayan sallah magariba, ɗaya daga cikin matan gidan ta kawo ma, Namra tuwon masara
da miyar ganye, haka Namra tayi ta tura abincin ba dan tana so ba, abun ka da wanda
be saba ba.
Kaɗan kawai ta ci ta bar ma ƙannen Mardiya saura, ta wanke hannunta, sai ta koma
kusa da Maman Mardiya ta zauna tana labarta mata zasu koma BQ, Inna tayi mata murna
sosai, har tana cewa zata ƙara mata da wani abun.
A daren sun sha hira, ita da Inna sai labarin rayuwa take bata, irin
gwargwarmayar da ta sha kamin ta kawo yanzu, da kuma labarin ƙurciyarsu ta ƙauye,
wani abun na dariya wani na ban haushi, wani kuma na ɗaukar darasi.

Sai kusan goman dare Namra ta kwanta, har kuma lokacin Mardiya bata gidan, kuma sam
hankalin Inna be tashi ba, bata ma nuna damuwarta akan rashin sanin inda Ƴarta take
ba. Sai kusan shabiyun dare ta dawo gidan, tana ta wani ƙunshen-ƙunshe, suna sun-
sun ita da Inna a tunaninsu Namra tayi bachi.

Sai kawai ta warware Mardiya da ta zo da shi. Har suka ci suka cinye Namra bata
motsa ba balle ta nuna musu idonta ba, sun tana bachin ƙarya har na gasken yayi
gaba da ita.

*WASHE GARI*
Inna ta bada aka siyo musu koko da ƙosai, sai ta siyo ma Namra waina, dan ta lura
sam bata son koko, tun farkon kwananta gidan. Sai da ta ci ta ƙoshi, sannan ta nufi
akwatin Mardiya dan ɗauko kuɗinta, da zimmar ta siya ma Asim abinci ta kai musu.
Bata ga jakar a inda ta aje ta ba, sai ta sa hannunta tana ta lalabawa, wayan bata
ji komai ba, wale akwatin tayi tana duba sama-sama ko zata ganta, amman bata ganta
ba.

Zata canye hannunta kenan sai taji abu ya zargi hannunta kamar an soke ta da
allura, da sauri ta janye hannun tana raki.

“Waisss Ina jakar nan ta shiga ne”

Sai ta soma ɗaga tufafin ɗaya bayan ɗaya, tana dubata, ganin tayi kamar be dace ta
ya mutsa mata kaya ba, saboda neman jaka wata ƙila ma ta ɓoye mata a wani gurin,
ƙara kawai ta tambaye ta.
Har zata mai da kayan sai abu ya faɗo daga cikin ɗankwalin atamfar Mardiya,
dubawar da Namra zata yi sai ta ga wayarta, da sauri ta kai hannu ta ɗauka.
No it can't be her phone, ta duba wayar gaba da baya.

“Wayata ce wannan this is my phone, how... ”

Sai kuma tayi shiru, tana nazari. Da sauri ta barkata kayan ta kai har ƙasan
akwati, sai ga sarƙarta, da wasu manyan ƴan kunne nata, da agogon ta. Da sauri ta
ɗauki ta miƙe tsaye tana mamaki.
Cikin wani irin bachin rai ta fito waje ta isa har inda Mardiya take zaune suka
fira da Matan gida, ta ɗauke ta mari. Namra bata damu da matan da suke cikin gidan
ba haka ta shararawa mardiya mari har huɗu tana hawaye.

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Write by_
*Khadeeja Candy*

*PAGE - 37*

NOT EDITED ⚠

Sare saren jini ne ya fara zubar mata, amman hankalinta gaba ɗaya ya tattara ya
koma gurin takardar.

‘Ga result ɗin da kike nema nan, da kuma wanda Doc Sabo ya bani jiya, ranar Monday,
na biyun zai fito, idan har baki tsallake ba, za'a sake miki na uku, bana son kowa
ya san sirrin mu, na yi alƙawarin rufa miki asiri saboda ƴaƴanmu, amman ba zan
zauna dake ba Rashida idan har hakan ya tabbata, kar ki kuskura canja komai kar
kiyi unƙurin yin komai, har sai gaskiya ta bayyana kuma na baki damar zuwa gida
idan kina da buƙata, bana son wata alaƙa ta sake shiga tsakanin ki da su Ezzah a
yanzu’

Taya zai mata katanga da yaranta? Taya asirinta zai tono tun yanzu, ba zata iya
jure rashin Hilal ba ta shirya sadaukar da rayuwarta a gareshi, tana son mijinta,
miyasa zata farka daga bachi tun yanzu? Baya mafarkinta be ƙare ba?

Wani irin ihu ta saka ta silale a gurin.

NAMRA POV.

Faɗuwa Mardiya tayi ƙasa daga kan turmin da take zaune, tana kallon Namra da mugun
razana a fuskarta.
Gaba ɗaya matan gida sai hankalinsu ya tattara ya ya koma kan Mardiya da Namra.
Babu wanda yace uffan har Inna da take Mahaifiyar Mardiya, dan tasan Namra ba zata
mari Mari Mardiya haka kawai kawai ba.

“Ashe baki da zuciyar Imani? Duk zaman amanar da nake dake Zagon ƙasa kike min?
Kina ganin yadda na yi ta neman wayar nan, ashe tana gareki kika ƙi faɗa min? Taya
kika ɗauki sarƙa ta da ƴan kunne na? Faɗa!”

Namra ta faɗa a tsawace tana mai jin kamar ta kama Mardiya ta ɓanlata gida-gida, ta
watsar. A nan matan gidan kowa ya fara sun-sun da kai suna kallon-kallon ma
junansu, daman sun daɗe suna jiran zuwan wannan ranar, tun da sun san Mardiya ta na
ɗan ɗauke-ɗauke kuma sun san ba zata rasa yi ma Namra ba, tun da halinta ne.

Murje ido Mardiya tayi, ta mayarda hawayen da suke son zuba mata, wani dakewar
zuciya ta samu kanta da ita, na mayarda ƙaryarta ta zama gaskiya.

“Namra ya kamata ace kina bincike kamin ki aikata abu, kuɗin ki na canja musu
muhalline, sannan ni ban ɗaukar ka miki waya ba balle kuma sarƙa, sai idan wani
sherin zaki min”

Tassss Namra ta sake marinta ta turata can baya har ta faɗi.

“Munafuna mai siffar ƴan wuta, nayi farinciki da Allah ya nuna min ko wacece ke tun
a yanzu, na yi nadamar sanin ki a rayuwarta, baki da imani ba ki da tausayi
Mardiya, duk irin halin da nake ciki sai da kika ƙafe zuciya kika min sata? Ɗaukar
haƙƙin wani? kuma ki jira sakamakon ki”

Wannan karon Mardiya hawaye take. Mahaifiyarta ta matso tana hantarar Namra,
magangannunta sun ɓata mata rai sosai, tana ganin dan me Namra zata musu haka.

“Amma ke kam ba ƴa bace sam baki da mutunci, ai komai Mardiya tayi miki ya kamata
ace kin taushe zuciyarki kin ɗaga mata ƙafa, balle ma bayi ba dan ban haifi
ɓarauniya ba”

Namra ta kalleta da jajayen idanuwanta, ta yarfe ta da hannu.

“Kin ji kunya Wallahi, tirr da uwa irin ki mai ɗaurewa ƴarta gindi tana abunda take
so, uwar da ƴarta zata sa ƙafa ta fita ba zata dawo sai taga dama kuma hankalin ki
kwance, sai murna kike tana kawo miki abunda daɗi, kina da tabbacin inda take zuwa?
Idan har kin san hallaci ba zaki bar ƴarki ta ta ɗauki abu na ba, ko da kuwa yana
zuba a ƙasa”

Maman Mardiyar ta jinjina kai

“Lallai ɗan adam butulu, lallai mun yi kuskure yi miki masauki min yi kuskuren
yarda dake, a nan da kika yi gobara babu uban da yayi miki masauki sai mu, mu baki
ci mu baki sha amman shine zaki watsa mana ƙasa a ido ko tafiyar yawon asibitin nan
duk da Mardiya akayi shi, amman ki rasa abunda zaki saka mata da shi sai sata”

“Kune kukeyi kuskure, ni nadamar sanin da na yi mu nake, in mamakin bushewar zuciya


irin na ƴarki, na yarda da ita ace ita macuciya ce”

Hawaye take kamar an buɗa fonfo, sai ta shiga ɗakin ta kwaso kayanta ta fito da su
waje, sannan ta sake komawa ta ɗauke komai nata a ɗakin ta fito dashi waje, sai a
sannan matan gidan suka fara saka baki a maganar, suna bata haƙuri tare da
Mahaifiyar Mardiya.

“Wallahi ba zata sake kwana a gidan nan ba, indai ƴar halak ce ko ƙofar gidan nan
karki sake bi, shi kenan dan anga yarinya bata magana sai a riƙa cin amanarna kowa
ya kwaso shararsa sai ya zube akanta, to ta Allah ba taku ba Wallahi, Mardiya nan
gani nan bari kashe di uku lahaula bakwai”

Namra ta nuna ta yatsa.

“Karki soma wulaƙanta ni akan wannan gidan, nima rayuwa ce ta canja min da ko a
hanya kika haɗu da ni ba ki isa ki faɗa min magana mai ɗaci ba, kuma ni ƴar halak
ce zan tabbatar miki da hakan ”

“To mu zuba mu gani, ai mu kujera ne, muna nan zaune zaki dawo”

Namra bata sake ce mata komai ba, uffan ba saboda baƙinciki, da taimakon yaran
gidan ta kwashe ƴan tsomakaranta ta kai BQ ɗin gidan ta , sai ta zauna a balcony
ɗin gidan ta tsurawar main house ɗin gidan ido, tana hawaye.

Miyasa Mardiya zata mata haka bayan ta yarda da ita? Miyasa duk wanda ta yarda da
shi sai ya dawo yana mata Zagon Ƙasa? Ji take kamar ace akwai wani a kusa da ita ta
faɗa masa matsalarta ta labarta masa damuwarta, ta faɗa masa abunda Mardiya tayi
mata ko zata samu sassauci a zuciyarta.
Tashi tayi ta ɗauko wayarta, ta riƙe a hannun tana juyata, itace last kyautar da
Anty Amarya tayi mata, jin son wayar take ya shige ya, lallai tana buƙartar
mahaifiyarta a kusa da ita.

Ƙoƙarin kunna wayar take amman abun ya gagara, ta danna power bottom ɗin amman
wayar taƙi ta tashi, sai ta juyar da gefenta da bayan ta tta duba ko ina, bata ga
wani matsalar ba, amman wayar taƙi ta tashi.
Riƙe wayar tayi tana ta kallonta, kamin ta saka ta ajaka, ta tashi ta canja
Hijabinta ta fito harabar gidan. Yau kam sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta samu
Napep, kai tsaye tace ya kai ta asibiti.

Lokacin data shiga asibitin ta yi ta ƙoƙarin ta ɓoye damuwarta, amman abun ya ci


tura, saboda baƙin cikin abun da Mardiya tayi mata ya tsaya mata a rai.
Ko da ta shiga ɗakin ta tararda likita na duba Asim, yana wasu ƴan rubuce-
rubuce, bayan ya gama ya miƙa mata takardar.

“A siyo wannan maganin anjima za a bashi”

Hannu kawai tasa ta karɓa tana kallon likitan har ya fice, sannan ta zauna kusa da
Asim ta ɗora kanta saman kafaɗarsa, ta fara hawaye.

“Miya faru?”

Kuka ta fara rarewa a hankali.

“I just need someone to tell everything will be okay”

Zungurarta yayi da kafaɗarsa ta ɗaga daga saman ƙafaɗar tana kallonsa, shi kuma ya
wani ɓata fuska.

“Namra miyasa kike abu kamar wata ƙaramar yarinya, ya kamata ace kin san kin girma
fa amman sai ki riƙa abu kamar wata ƙaramar yarinya, haba Namra baki ga halin da
nake ciki ba, yanzu fa wani maganin ne likita ya rubuta min, ni wannan zaman
asibitin ban san ranar da zai ƙare ba, da nasan wannan ƙaddarar zata same ni da ban
je ɗauko motar nan ba”

Furucin da Asim yayi a yanzu, sai ya ninka ɓacin rai tazo da shi, tayi tunani zai
barta ta faɗa masa damuwarta ne har ya rarrashe ta, amman sai ya ƙara mata wani.
“Miyasa kowa baya fahimtar damuwata, miyasa kowa baya jin abunda nake ji? Miyasa ba
a ganin ƙoƙarina? Be kamata ka biye Mama ba, be kamata ace kana irin wannan furucin
ba”

“Be kamata ba? To idan ban biye mata ba wa zan biyewa? Ai gaskiya take faɗa, komai
ƙaddara ne amman kuma yana da sanadi, nan gaba idan ba bara ba me kike tunanin zamu
koma yi? Tun ana baka rance wata rana ai hana ka za'ayi”

Kallonsa kawai take, tana mamakin kalamansa, taya Asim.ya juya ya koma ba shi ba? A
yau ita Asim yake kallon tsabar idonta ya faɗa mata irin wannan maganar?
Turo ƙofar da Mama tayi ta shigo ne yasa tayi saurin share hawayenta, ta sanda
kai ƙasa, zuciyarta na mugun ƙona.

“Ga waya mamanki ta kira”

Hannu ta kai ta karɓa, sai ta tashi ta bar ɗakin da saurin saboda kukan dake son
cin ƙarfinta.
Mama ta bita da wani kallo.

“Me kuma aka mata?”

“Oho kukan data saba ne ta zo ta min”

“Hmmm wannan matar ita da iyayenta ba son ka suke ba, duk ta bugo wayar nan ƴarta
take kira,ƴar wayar kiran ma ta kasa ta siya mata, ni wallahi ban san me suke nufi
da kai, ni Wallahi da zaka bi ta nawa da ka saki yarinyar ka huta ma kan ka”

“Mama idan na sake ta a yanzu wace mace ce zata zauna da ni a haka? Bana da kuɗin
auren wata, sannan kina ganin halin da nake ciki, ai ƙara ma na zauna da ita duk
wahalar da zamu sha mu shata tare, komai zai ci ni sai ya ci ƴarsu”

“Hmmm Allah ya kyauta, amman wannan sun nuna maka ƙiyayyah zallarta, Allah dai ya
azurta ka ya baka lafiya”

“Amin”

Ya amsa fuska a haɗe kamar ance iyayen Namra suna gurin. Lokacin da Namra ta fita,
sai tayi can gefe nesa da inda masu jinya suke shinfiɗa dan shan iska, sannan ta
riƙe wayar tana kuka. Sai ga kiran Anty Amarya ya shigo, cikin sauri ta ɗauka ta
kara a kunne, tana cigaba da kuka.

“Lafiya Namra? Miyasa ki?”

“Ma....Ma...”

Yau kam da Mama ta kira Anty Amarya, sunan da be taɓa zuwa a bakinta ba tun
tashinta, saboda sabo da yadda kowa ke kiranta da Anty Amarya.

Anty Amarya jin kukan ƴarta take har cikin ranta, bata san abunda yasa Namra kuka
ba, sai kawai ita ta fashe da kuka tana dafe zuciyarta.

“Namra faɗa min minene? Miye damuwarki ƴata faɗa min? Indai kuɗi ne na turo miki
300,000k a account tun jiya, ko ba za su isa ba na ƙaro miki?”

“Mama ina son ganin ki, i miss you”

“Okay ki faɗa ma mijin ki idan ya bar ki zan turo direba ya ɗauko ki kin ji? Akwai
wani abun ne? Jikinsa dai ƙalau ko?”
“Ya..ji sauƙi”

Ta amsa da in'innar kuka.

“Namra ki kwantar da hankalin ki kinji? Komai zai wuce? Rayuwa bata tabbatuwa haka
nan dole ne za a jarraba bawa”

“To Anty na gode”

“Ki sayi waya ki saka layin ki, ki kira ni kin ji”

“Tau”

Ta kashe wayar, sai ta duƙa a gurin ta riƙa rusa kuka kamar wacca akayi ma mutuwa.
Ko da ta tashi har hijabinta ya ɓace da hawaye, sai ta cire ɗankwalinta ta ɗora
saman hijabinta, ta koma ward ɗin.

HILAL POV.

Tun bayan fitar Rashida daya gama shirya ma yaransa abun kari, sai ya ɗauko tsohon
result ɗin ya ɗora a saman gadon Rashida tare da takardar rubutun da yayi mata.
Sannan ya koma yayi wanka ya kwashi yaran suka wuni gidan Hajiyarsa, tayi farinciki
da murna sosai, sai da suka yi sallah isha'i sannan yace ma Kalsoom ta tashi tayi
shirin zuwa gida. Ita kuma sai ta riƙa kiran yaran da zimmar su zo suje gida sai ya
riƙe mata hannu ganin babu kowa falon.

“Ba da su zamu je ba”

“Amman....”

“Don't talk gobe da yamma direban hajiya zai mai da su gida, suna jindaɗin zaman
nan let them enjoy themselves”

“Amman suna zuwa islamiya da safe fa”

“Just for one day, please a daga musu kafa mana, yau bana son jin muryar yaran nan
a gida”

“Saboda me? Wai Doc miyake damun ka?”

Ya kwanto da kansa saman jikinta, kamar wani ƙaramin yaro.

“Ke kike damu na? Son ki ne yake wahalar da ni”

“Ba so na bane wannan, wata damuwar ce ta daban, dan Allah ka faɗa min abunda yake
damun ka”

“Tashi muje kar muyi dare”

Ya tashi da zimmar kawar da maganar dan baya son faɗa mata komai.
Shi ya fara zuwa yayi ma Hajiya sallama sannan ita ma tayi masa, suka kama hanya,
tun da suka hau titi bata ce masa komai ba in ban da ido ta da sakar masa tana
kallon yanayinsa, a fuskarsa take karantar damuwarsa, zuciyarta na nasalta mata
lallai akwai abunda yake damun Mijinta.

Parking taga yayi a gefen ti-ti, sai ya juyo ya kalleta yana murmushi, kamin ya kai
hannu ya jaka izuwa ƙirjinsa, ya rumgumeta. Ya ɗauki dogon lokaci a haka sannan ya
tashi motar suka ƙarasa.
Jikinsa ne ya bashi ba lafiya ba, tun daga lokacin da yayi parking ɗin, sai kuma ya
soma jin rashin dacewar abunda yayi ma Rashida, ko ba komai uwar ƴaƴansa ce, sai
dai babu yadda ya iya tun da hiv indan be zama aids ba, akan iya kamuwa dashi ta
hanyoyi da dama, tun da a yanzu shi dai ya samu tabbacin shi da Kalsoom da ƴaƴansa
basa ɗauke da cutar.

Sai dai ya san Rashida ba zata iya rayuwa babu shi ba, yasan yadda take ƙaunarsa,
amman zai gogeta a ransa matuƙar result ɗin ƙarshe ya fito, kuma ya tabbatar da a
sex ta samu cutar.
Sai da ya raka Rashida har ɗakinta, sannan ta fito ya shiga ɗakin Rashida.
Yanayin yadda ya ganta ya tsorata sosai, tana kwance cikin jini babu numfashi. Be
san lokacin daya ɗauke ta ya fito da ita da gudu ya nufi mota.

AMIRA POV.

Daga rarrashin da yake mata, sai wasan ya sauya salo, ya fara bin jikinta yana wasa
da dukan ɓangarorin jikinta, har yayi nasarar jan hankalinta, ya biya buƙatarsa.

Sannan ya nufi ɗakinsa ya kwanta, ita kuma ta nufi wani ɗakin, tayi wanka ta shirya
cikin wasu tufafin ta fito kamar ba ita ba.
A falon ta dawo, ta buɗe freezer ta ɗauki lemu tasha tana ƙoƙarin kawar da
damuwar dake cikin ranta dan samawa kanta nishad.
Ta zauna, saman kujera tana ƙoƙarin canja MBC bollywood, zuwa AIT, program ne suke
akan yadda za'a magance matsalar tsaron data addabi Nageria, har zata canja sai
channel sai kuma ta tsaya tana kallon yadda Abdool yake watsa turanci yana koro
bayani kamar wani ba'amerike, hakan ya ɗauki hankalinta har ta kula da kyausa, da
kuma muƙaminsa, kamin su sake naɗo sunansa.

“Major General Abdullah Ahmad Mai-Doki, wow nice guy, nice work, nice name,
everything perfect”

Ta furta a hankali tana mai maida hankali ga kallonsa sosai. Dif nefa suka ɗauke
wuta, wani irin buga ƙafa tayi, ta sosa hancinta.

“Oh they Fuck up”

Zata tashi sai ga mutumen ɗazu ya dawo, yana bata rahoton Doc Sabo. Dafe kai tayi
tana tashi tsaye.

“Eyyyyyy karka cika ni da wani magana, ga wayana nan ka duba number ta ansa banker
ka tura mata text ɗin abunda zata biya, sannan kace Samuol ya tada mana injin”

Tana kaiwa nan ta nufi ɗakin da Guy son ya shiga ɗazu.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Write by_
*Khadeeja Candy*

*PAGE - 38*

NOT EDITED ⚠

Ko da ta shigo ɗakin ta same shi tare da Mama suna magana, bata iya zago zancen da
suke amman jikinta yana bata kamar maganar ta ne suke. Cikin Ladabi ta miƙawa Mama
wayar.
“Kun gama maganar ko?”

“Eh mun gama”

“Tau madallah”

Yanayin yadda ta tayi maganar ya tabbatar ma da Namra da biyu tace haka ɗin, sai ta
tashi ta fice daga ɗakin ta basu guri.
Da kallo Namra ta bita har ta fita sannan ta zauna kusa da Asim

“Anty ta aiko min da 300,000k, zan bawa Dillaiya su in yaso sai ta bini hansin ɗin”

Asim yayi shiru be ce komai ba, sai ma yayi kamar ba dashi take magana ba, baya son
nuna mata be jidaɗi ba, sai dai a can kasa zuciyarsa rashin jindaɗin ne, ganin ba
shi Anty ta aikowa kuɗin ba, tun farkon fara rashin lafiyarsa har zuwa yanzu babu
wani abu daya fito daga hannunsu izuwa gare shi da sunan yayi lalura da su.

Hannunshi ya kai ya riƙa nata hannun.

“Namra ya zaki ji idan aka ce yau Mama bata son ki kuma kina auren ɗan ta?”

Tayi shiru tana nazarin inda maganarsa ta dosa, tambayace yayi mata mai ma'ana
ɗaya, dan kai tsaye ta san da ita yake.
Sai kawai tayi murmushi tace

“Be zai dame ni ba, saboda Kai na aura ba Mama ba, sannan ban aure ka ba dan wani
abu naka sai dan son da nake maka, to dan me wani abun zai rufe min ido har na
zarge ka?”

“Uhmm”

Ya janye hannunsa, yana kallon ƙofar ɗakin kamar mai jiran shigowar wani.
Can kuma ya kalleta

“Ina ganin idan an gama min allurar nan, ya kamata ace mu koma gida saboda asibitin
nan in ban da kashin kuɗi babu abunda suke ja mana”

“Gidan ma sai an gyara za'a zauna, saboda gate ɗin ya ɓangale gefe ɗaya, kuma BQ
nan tsoro take bani”

“A haka dai zamu daure mu zauna”

“Da ace da hali da an gyara gate ɗin, in yaso BQ ɗin sai a share a wanke”

“Sai ki gyara da kuɗin da Anty ta aiko ai zasu isa”

“Amman ba kaji nace bashi zan biya ba? Sai dai na siyar da sarƙa na gold a gyara”

Ya kalleta a kai-kaice

“Ina kika samu sarƙar gold? Ba kin ce komai ya ƙone ba?”

“A hannu Mardiya na gani ɗazu har da wayana ma, ita ce ta satar min”

“Mardiya? Ya akayi kika gani?”

“A ƙasan a kwatinta, saboda jiya na saka kuɗin daka bani a cikin kayanta, gurin
nema ne sai na wayar har da sarƙar ma, da wasu ƴan kunne da Hajiya ta taɓa raba
mana lokacin data dawo makka”
“Amman ya akayi Mardiya ta shiga har ciki ta ɗaukar miki sarƙa har da waya ma?”

“Ban san yadda ta ɗauka ba wallahi kawai dai na kamata da su ne a yau, kuma nayi
mata masifa ita da Mamanta”

“Aikowa baki kyauta ba, yarinyar duk hidimar da ake ta zuwa asibiti da ita ake
yinta, anya ma ita ta ɗauka? Dan gaskiya yarinyar nan tana da natsuwa da tarbiya”

“To idan ba ita ta ɗauka ba ya za'ayi na gani a akwatin ta? Kuma fa taji lokacin
da ina nema”

“Yanzu idan kin siyar me zaki yi da kuɗin? Namra wai kin faɗawa Abbah mun yi wuta
kuwa?”

Ƙasa tayi da kanta.

“Ban faɗa ba, babu wanda ya sani”

“Nima bana son kowa ya sani dan muna da maƙiya za su mana dariya, amman dai su ai
kamata ace sun sani, rayuwa tayi haka? Namra ki duba halin da nake ciki, babu wani
taimako sai na Allah, yanzu idan kuɗin nan da muka ranto suka ƙare kina tunanin
akwai inda za mu sake dubawa? Ban san miyasa rayuwa ta zo mana a haka ba, kana
neman ka ɗaga kayi gaba, amman sai baya kake abubuwa suna ƙaruwa”

Ya ƙarasa maganar idonsa cike da hawaye.

“Inshallah zan faɗa mata idan na je, tace na tambaye ka idan ka bar ni sai naje”

“Gurin me?”

“Tace tana son gani na ne”

Har zai ce wani abu, sai kuma yayi shiru yana nazari, idan har ya barta yaje be san
abunda zata samo ba, musamman idan ta faɗa musu halin da suke ciki.

“Amman ba zaki daɗe ba ko? Kije amman kwana biyu za kiyi ki dawo”

Hannayenta tasa ta rumgume shi, tana murmushin jindaɗi.

“Na gode daman nima ba zan wuce kwana biyun ba, Allah kara maka lafiya”

Har cikin ƙasan zuciyarta take jin son Asim, sam bata iya gani illarsa, saboda
zuciyarta tana muradinsa, a take zuciyarta ta fara raya mata ya ɓoye mata maganar
kuɗin wata ƙila saboda karta sa ci suna da kuɗi, kuma ita kanta bata san yadda yayi
ya samun kuɗin adashen ba, sai dai abunda ya faɗa a wacan lokacin ya tsaya mata a
rai, a duk lokacin data tuna sai ta ji babu daɗi, har zuciyarta ta zarge shi akan
haka.

HILAL POV.

A haukace ya isa asibiti, dan a tunaninsa Rashida ta mutu, shi da kansa ya kai ta
emergency room, tare da taimakon wasu Nurses ya shiga neman numfashinta.

Da taimakon Allah komai ya daidaita, sannan ya ɗaura mata drip, yayi mata allurar.
Tsaye yayi cikin ɗakin yana kallonta bayan Nurses ɗin sun fita.
Wayarsa ya shiga lalabe sam ya manta da tana ciki mota, sai yanzu. Fita yayi be
daɗe ba ya dawo tare da rigar asibiti da wasu kayan aiki, sai ya canja mata tufafin
jikinta, ya gyara mata jikinta sannan ya saka mata rigar, sai ya kira wata
ma'aikaciyar gurin mai share-share ta kwashe kayan.

Zaunawa yayi a gurin ya ɗafa kansa, sai ga wasu daga cikin abokan aikinsa sun shigo
duba ta, sama-sama ya amsa musu, suma sun ga damuwa ƙarara a fuskarsa, sun lura da
yanayinsa, duk a tunaninsu saboda Madam bata da lafiya ne.
Fatan sauƙi suka mata sannan suka fita, shi kuma ya tashi yaje gurin motarsa ya
ɗauki wayarsa ya kira Hajiyarsa ya faɗa mata, sannan ya kira Momy ita ma ya faɗa
mata.

A cikin motar ya shiga ya zauna ya tasa abunda ke masa daɗi duniya, baya son
yaransa su san komai a tsakanin su, kuma be san wane bayani zai yi ma Hajiyarsa ba
da Momy, sam baya son duniya tasan abunda Rashida ta aikata, sai dai kuma be san
yadda zai yi yayi ya ɓoye ba, cox he's no more to her.
Be ɗago kansa daga tunanin da yake ba, wayarsa tayi ringing, number Momy ce a
rikice take tambayarsa wane ɗaki Rashida take.

Sai da ya buɗe Motar ya fito sannan ya amsa ta.

“Kin shigo Asibitin ne ?”

“Eh ina emergency”

“Okay tsaya a gurin zan ƙaraso yanzu”

Ya kashe wayar tare da rufe motar, sannan ya nufi gurin da yake zaton take. Tun
daga nesa ya hango ƙannenta biyu. Cikin rashin kuzari ya ƙarasa inda suke ya gaishe
ta, su kuma ƙannen suka gaishe shi. Sannan ya wuce dasu zuwa ɗakin da take.
Ganin halin da take cikin yasa Momy har ta fara hawaye, kallon ta kawai Hilal
yayi yana ayyana irin abunda zata ji idana kace mata ƴarta na ɗauke da cuta mai
ƙaryar garƙuwar jiki.

“Momy karku taɓa ta, ko da ta farka ne”

“Toh amman mi ya same ta haka ne?”

“Ta samu Miscarriage ne”

“Subhanallahi Allah ya bata lafiya”

“Amin”

Ya koma ya jingina da bangon ɗakin yana kallonta, ɗaya daga cikin ƙanwarta ta
warware carpet ɗin da suka zo da shi ta shinfiɗa a gurin. Ta miƙawa Hilal Kujera,
sai kawai ya girgiza mata kai.

“No Thanks”

A gurin yayi ta tsayi har Hajiya ta iso, ita sai da ta kira shi, yaje ya taho da
ita sai suka gaisa da Momy, ta duba ta tayi mata fatan sauƙi sannan ta fito. Tare
suka jero da ɗanta sai gaisuwar girmamawa ake mata, dan kowa ya ganta ya ga Hilal
yasan itace mahaifiyarsa.

“Yanzu haka baƙin kishi ne ta sawa kanta, gashi yanzu kun yi losing wannan baby”

Shi dai be ce komai ba, ya buɗe mata Mota. sai da ta shiga, ta zauna sannan yayi
mata sai da safe direba ya wuce da ita, shi kuma ya juyo ya dawo cikin asibitin.
Lokacin daya dawo, sai ya zauna saman gadon kusa da ita, babu abunda yake kallon
sai fuskarta, rayuwarta da tasa yake ta tunani, irin yadda suka so junansu har suka
haifi ƴaƴansu, yanzu kuma lokaci ɗaya komai yana shirin sauya musu, he just can't
believe ace Rashida ta ci amanarsa da wani, haƙiƙa yana da tambayoyin da suke
buƙatar amsa daga gareta.

“Ai da ka tashi kaje gida, tun da ga mu muma ai mun isa mu kula da ita”

Can ciki ya ji muryar Momy tana masa magana. Sai ya tashi cikin rashin ƙwarin jiki
yayi musu sai da safe ya fice.

NAMRA POV.

Daga asibitin sai ta wuce bank, layi ta bi sai da ka kai gareta sannan tayi
checking balance ɗinta, dubu ɗari huɗu ta hansin ta gani, a tunaninta ko Anty
Amarya ta ƙaro mata wasu ne, sai kawai ta cire kuɗin gaba ɗaya, cikin farinciki da
jindaɗi.

Kamin ta isa gida sai ta ta fara biyawa ta gidan dillaliya, ta ƙirga kuɗinta ta
bata, sannan tasa a kira mutumen da yayi musu wacan rubutun yayi masu sheida saboda
wata rana.
Sauran kuɗin daya rage mata sai taje kasuwa ta siye kuloli, da ƴan wasu kayan
aiki da basu kai sun kawo ba, data dawo gida sai ta wanke kuloli ta siye abincin ta
nufi asibitin da shi.

Ta jidaɗin ganin Asim a tsaye yana ɗan takawa, Mama na tiƙe da shi, suna zuwa
ƙarshen ɗakin suna dawowa, wani farinciki ne ya mamayeta, bata san lokacin data aje
kulolin ba ta tsaya tana kallonsu.
Hamdala take yi ma Allah cikin ranta, tana jindaɗin yadda taga mijin nata yau ya
fara taka ƙasa, Mama ma farinciki take sosai daman ta fi kowa son haka dan zaman
asibitin ya isheta.

Sun kusa minti latalin suna, suna zagaye ɗakin sannan Mama ta zaunar da shi saman
gado.

“Allah ya bi da lafiya ya ƙara sauki”

Ita da Asim suka haɗa baki gurin amsawa da Ameen. Sannan ta zuwa ya fice.
Namra ta kalli Asim da far'ah a fuskarta.

“Da nice nace za kayi wannan yawo zaka ce min ba aka iya ba”

Ɗan murmushi yayi, shi kansa yana cikin jindaɗi a yau.

“Alhamdullillah, ban zaci zan iya ba”

“Ai babu abunda za a iya matuƙar aba'a gwada ba, Allah ya nuna min ka tashi ka koma
kamar yadda kake”

“Ameen”

Ta kwantar da kanta saman jikinsa. Shi kuma yayi shiru yana nazarin rayuwarsa, irin
mutanen da sukajuya masa baya yake lissafi a zuciyarsa, ace har abokansa da yake
ganin sun kai amman kowa ya kasa takowa ya zo ganinsa

“Hmmm”

Ya furta a fili, yana sauke ajiyar zuciya. Sai Namra ta kalleshi

“lafiya?”
“Lafiya ƙalau, kawai ina tunanin tafiyarki ne, Mama tace karki je yanzu, idan ma
wani abun ne ai aiko miki kawai, kuma ki faɗa wata komai ta waya kawai, tama kira
ba ki nan”

Shuru Namra tayi bata ce komai ba, sai dai maganar tasa bata mata daɗi ba. Hannu ya
kai ya shafa ta.

“Namra have you ever noticed that Anty bata taɓa kira kai tsaye da sunan jin jikina
ba? Haba Namra ai ko wani na kashe musu sa ɗaga min ƙafaa balle auren ƴar su na ke,
abun nan ya ɓata ran Mama sosai, nima shiyasa a duk lokacin dana ga ɓacin rai a
fuskarta sai nawa rai ya ɓace, daman irin wannan ake gudu aje ayi aure a kasa samun
kwanciyar hankali”

Shiru tayi tana taɓin hannunta, ita kanta tasan iyayenta basu kyauta ba, akan
abunda aka yi mata kuma Asim yana da gaskiya kan abunda yake faɗa, tasan Abbah kam
ba zai zo ganinsa ba, amman ya kamata ace ko Maryam ce ta zo ganinta, ganin yadda
suke da ita jini ɗaya, amman ko waya bata taɓa bugo mata ba.
Anya ta cancanci su juya mata baya har haka?
Ba su da wani excuse akan haka, sai dai a yanzu bata son ta zurfafa amincinta ga
Asim tun bayar maganar su da taji da Mama.

Kamar ya san abunda yake ransa, sai kawai ya rumgume ta.

“Ina son ki, kuma bana tunanin akwai abunda zai raba ni da ke, ina son na ɗanɗana
miki rayuwar da baki taɓa mfarkin shigarta ba, irin rayuwar jindaɗin da tafi ta
gidan ku, sai dai ina gudun ranar da zaki rabu da ni saboda wani baƙin talauci ko
mugu abu ya same ni”

“Ba zan taɓa rabuwa da kai ba Asim na maka alƙawari, ko a wane hali na samu kai na,
zan zama mai biyayyah a gare ka, zan maka sadaukarwar da ba kowa ce mace ce zata
iya ba, son nuna maka son da ba kafai ake samun irinsa ba.
Sai dai ni zuciyarta ta kasa Aminta da kai, kana ɓoye min wani abu naka Asim”

Gabansa ya faɗi, yana Allah-Allah idan ba wani zancen nasu ta ji ba.

“Me zan ɓoye miki? Miyasa zuciyarki ta manta da waye Asim a duniyarta, taya Asim
zai cuce ki, Asim be aure dan tsinkayar wani abu na gidan ku ba, shiyasa tun farko
ban so na aure ki saboda na san zaki yi tunanin saboda haka na aure ki”

Jikinta ya mutu, hawayen da taga yana zuba a idon Asim ya tsayar da nata hawayen, a
take ta manta da zargin da take masa, wani irin son sa da ƙaunarsa suka mamaye mata
zuciya.

MORNING UPDATED
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Write by_
*Khadeeja Candy*

*PAGE - 39*

NOT EDITED ⚠

Ko da ya isa gida, Kalsoom na zaune a balcony tana zaman jiransa, hankalinta ya


tashi sosai, ji take kamar itace a halin da Rashida take ciki.
Tana ganin yayi parking, ta tashi da sauri ta ƙarasa inda yake ta buɗe masa motar.
»“Ya jikinta? Da sauƙi?”

Ido ya sakar mata kamar yau ya fara ganinta, be ce mata komai ba kuma be kashe
motar ba, balle ma ya fito. Ita kuma duk ta tsorata, gabanta sai faɗuwa yake kar ta
ji mummunan labari.

“Dan Allah ka min magana mana”

Ta masa maganar irin tana daf da yin kuka. Sai a sannan ya kashe motar ya fito, ya
ɗora kansa saman na ta, ya kai hannu ya riƙe hannunta yana sauke ajiyar zuciya.

“Da sauƙi ta samu bachi”

“Amman ka kira gida ka faɗa musu?”

“Na faɗa”

“Sun zo?”

“Sun zo”

“Allah ya bata lafiya, amman dai be zube duka ba ko?”

“Ya zube”

“Ayyah Sorry”

“Sorry too”

Duk maganar da take masa yana amsa mata, kansa na saman nata ne, sai a sannan ya
riƙa hannunta, ya matsar da ita daga jikin motar ya rufe motar, ya jata zuwa ciki.

A falo ya zauna, sai ta zauna kusa da shi, tana ɗan shafa bayansa, a tunaninta
zubarwa cikin ne be masa daɗi ba.

“Doc kayi haƙuri Allah zai sake baka wani”

Ya kalleta.

“Haka ne, Kalsoom do me a favor”

“Na me?”

“Ki min alƙawarin zaki kula da yarana zaki basu kyakkyawar tarbiya, and komai suka
yi ba zaki gundura da su ba”

“Baka da buƙatar na maka alƙawari, amman miyasa kayi min wannan maganar na?”

“Zan raba muku gida ne, da Rashida zan wareta daban, ke zaki zauna a nan tare da
yara”

“Miyasa?”

“Ita ta buƙaci haka”

“Kuma ta yardar ta bar min yaran?”

“Eh amman ba na son ki faɗa musu hakan, ni zan yi magana da su, ko da sun dawo
karki faɗa musu Mamansu ta kwanta asibiti”

“Okay”

Ta faɗa a sanyaye, ita dai ta san ba lafiya ba, yanayinsa da kuma hukuncin daya
yanke ya tabbatar mata haka.

“Bari na haɗa maka tea”

Ta tashi ta nufi kitchen, zuciyarta da tunani kala-kala, ko dai Rashida ce take da


hiv! Shiyasa yake ta mata tambaboyi a baya? Kuma yanzu zai raba ta da ƴaƴanta, ai
ba zai raba ta da su haka kawai ba, kuma yadda take ganin damuwar nan ta masa yawa
ta san ba'a raba ɗayan biyu ba.
Har ta haɗa masa tea ta kawo masa tunanin take.

Fuskarsa ta tsurawa ido sosai, lokacin da zata miƙa masa tea, tana son gano
gaskiyar zarginta, idonsa sun rine irin na ɓacin rai ɗin nan da damuwa idan sun yi
ma mutum yawa.

Har zata ce masa wani abu, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, sai kawai ta zuba masa
ido har gama shan tea ɗin ya tashi ya nufi ɗakinsa.
Ita kam sai da ta gama abunda take sannan taje tayi wanka ta saka kayan bachi ta
nufi ɗakin nasa, daman yau girkinta ne, ganin be shigo ɗakinta ba, ba zai hana ita
ta kai kanta ba.

Washe gari har Kalsoom ta haɗa musu breakfast, idonsa biyu amman ya kasa tashi,
jikinsa ya ɗibge kamar marar lafiya.

“Doc breakfast is ready”

Ta faɗa tana tsaye daga bakin ƙofa. Da ker ya ɗago kai ya kalleta.

“Je kiyi yau bana jin yunwa”

Ya unƙura ya tashi, ya nufi banɗaki. Ita kuma ta juya cikin rashin jindaɗi, ta
fice. Wanka yayi ya fito, ya shiryar cikin ƙananan tufafi, ya feshe jikinsa da
turare sannan ya fito falo cikin wani yanayi marar misaltuwa.

Ummu Faisak ya gani a falon zaune tana gaisawa da Kalsoom, tana ganinsa ta fara
masa wani kallo ƙasa-ƙasa, sannan ta gaishe shi.

“Lafiya ƙalau ya ma su jiki?”

“Da sauƙi, ita ma tace na zo na ɗauko mata wayarta”

“Ta farka kenan?”

Kalsoom ta tambaya.

“Eh ta farka”

Kalsoom ta kalli Hilal

“Bari na tashi na shirya sai mu wuce tare na ganta”

“Ba yanzu ba”

Ya faɗa fuska ba yabo fallasa. Ba jira abunda zata sake cewa ba ya fice.
Kalsoom sai duk ya ji babu daɗi, Ummu Faisak ta buishi da kallon tana ayyana irin
mallakar da Kalsoom tayi masa, har yake ƙoƙarin mantawa da Rashida a nan take, da
ada ne aka ce bata da lafiya da duk ya bi ya haukaci amman yanzu dubu yadda rana ta
fito be je ba, sannan ya hana Amaryarsa taje.
Wani dogon numfashi taja ta sauke irin an gulma ta tashi ta nufi ɗakin Kalsoom.

A hanyarsa ta zuwa Asibiti, Hajiya ta kira shi ta tambayi jikin Rashida, ya amsa
mat d taji sauƙi, sai kuma g kiran Alhaji Bashir ya shigo, sai da Hilal yayi
parƙing sannan ya ɗauki kiran suka gaisa sannan ya tambaye jikin Rashida.

“Ya Madam da jiki?”

“Jiki Alhamdillah, jiy ne ta samu miscarriage”

“Ayyah Allah ya bat lafiya”

“Amin Amin na gode”

“Dan Allah idan ka shiga, ka bani ita mu gaisa, Asma'u zata zo anjima Inshallah”

Ya kashe, sannan ya buɗe motar ya fita, duk inda y bi gaishe shi ake har ya isa
ɗakin.
Wasu ƴan'uwanta ya tarar suna mata sannu ciki har da wasu Nurses da suke aiki
gurin. Sai da ya fara gaida Momy sannan ya amsa gaisuwar da ƴan'uwan nata suke
masa, ya nemi guri ya tsaya ya kafe Rashida d ido.

Momy ce ta fara fita sannan suma duk suka fita, ka barsa cikin ɗakin shi kaɗai sai
ita, jin tayi kamar tace kar su fita, dan bata da idon kallon Hilal balle bakin yi
masa magana.
Shi kuma ya tsare ta da ido kamar mai auna hawa da saukar numfashinta.

“Yanzu ba ki ji kunyar kan ki ba Rashida? Kina da aure ki bi wani namiji a waje?


Wannan wane irin ƙazanta ne? Miyasa kika ɗauki zina ba komai ba? Idan kika mutu a
yau mi zaki cew Ubangijinki? Me na rage ki da shi? Wanda kika bi miya fi ni da shi?
Ko kum kawai sheiɗan ne ya ƙawata miki yin haka? Kin manta ke uwar yara uku ce?
Miyasa Zina ta burge ki Rashida? Ashe son da kika nuna min duk na ƙarya ne tun da
har zaki iya ba wani halalina, kin lokacin da kike hana min kan ki a baya? A haka
nake haƙuri ina bin ki har Allah yasa na haɗu da Kalsoom na aure, amman ko d
mafarki ban taɓa tunanin aikata zina ba.

Tsakanin jiya zuwa shekaran jiya tausayinki nake, ina tunanin halin da zaki shiga
idan babu a rayuwarki, amman yanzu nayi tunani baki buƙata na, sam ni da ke ba mu
dace ba, nayi baƙinciki nayi nadamar da kika zama uwar ƴaƴana, faɗa min wanene
wannan mutumen?”

Tun da yake maganar, bata balle shi balle tace wani abu, hawaye kawai take, irin
hawayen nan da wani ke bin wani. Ya matsa kusa da ita ya ciro takardar take
aljihunsa ya aje mata.

“Aure na da ni da ke yau ya ƙare, na sauwaƙe miki kije ki auri wanda kike ganin ya
fi ni, ki dauwama ke da shi a duniyar da kuke son kasancewa”

Ɗagowa ta yi tmda sauri ta kalleshi, irin kallon nan da bata san tana masa ba, yau
ta rasa gane duniyar da take, sama take ƙasa take, mafarki take ko gaskiya ne? Da
gaske Hilal ne ko waninsa? Taya zata rayu ba da Hilal ba? Gidan ta da ƴaƴanta a yau
sun zama mallakin kalsoom ba ita ba.

A saman gadon ta matsa can nesa ya rumgune kanta tana zubar ido kamar mai ganin
aljanu. Ko kaɗan tausayinta a yanzu kam be ziyarci zuciyarsa ba, dan yasan ta
cancanci fiye da haka, sai kawai ya juya ya fice daga ɗakin, cikin wani irin zafin
rai da baƙinciki.

NAMRA POV.

Bata jin ko ta faɗama Anty Amarya sun yi wata, zat yarda dan ganin take kamar cewa
zatayi shi ma haɗi ne, kuma bata iya tambayarta wani kuɗin, sai kawai ta kira ta da
wayar Asim tace mata be bari ba yace ta bari har yaji sauƙi sai su zo tare, Anty
Amarya bata jidaɗin hakan ba, sai dai babu yadda ta iya tun da mijinta ne.

Da dare Namra kasa, bachi tayi har sai da taje wani BQ dake maƙota ka d nasu ta
nemi ƴar fulanin data zo ta taya ta kwana. Duk da haka har safe ba yi bachin kirki
ba dan hankalinta be kwanta da gurin ba.
Da safe sai ta aika yarinyar ta siya musu ice su ɗora girki, a abun da bata taɓa
ba a rayuwarta yau gashi zata yi. Kamin yarinyar ta dawo, sai taje waje ta ɗauko
duwatsu ta haɗa murhu, kamin yarinyar ta dawo sai ta zauna saman bolcony tana
kallon gidan.

Tunani take na ranakun baya, lokacin da Anty Amarya take saka ta girki da gas ko
electric amman ta ƙi yi ta riƙa faɗin wahala, yau gashi zayi da abund bata ma taɓa
gwada kunna wutar da shi ba, yau ga ta a ɗakin da babu katifa balle gado, duk wani
abu mai muhimmanci a rayuwart i zuwa yanzu ta rasa shi.
Hawaye ne suka silalo mata sai tayi saurin gogewa, ganin ƴar fulanin ta doso inda
take ɗauke d icen.

Sai kusan 12 ta gama girkin abun ka d wacce bata saba ba, sai ta zuba ma yarinyar
ta zuba ma su Mama na su sannan ta zuba sauran a kula, sai ta janyo ruwa a rijiya,
ta shiga banɗakin BQ ɗin tayi wanka, sannan ta fito ta shirya cikin atamfar jiya ta
saka Hijabi ta ɗauki kular ta fito, yau kam a bakin gate ma ta samu Napep, tayi
sa'ah an sauke wata ne, sai kawai ta shiga ya ɗauki hanyar asibiti da ita.
Suna kaiwa Babban titi, aka riƙa musu hannu akan su tsaya, amman ta hana mai
Napep ɗin tsayawa, har sai da suka isa bakin asibitin. ta fito tana miƙawa mai
Napep ɗin kuɗinsa, ta tsaya jiran ya bata canji, sai ta motar ta faka kusa da ita.
Abdool ya fito ya nufo ta jiki na rawa. Kamin ya ƙaraso har Mai Napep ɗin ya bata
canjinta ta kunna kai cikin asibiti, shi kuma sai sauri yake ya ci gabanta.

Mama na gurin zamanta ta sinƙayo yadda Abdool ya biyo Namra har cikin ward yana
ƙoƙarin cin gabanta, sai ta tashi tsaye, ta matsa can baya tana leƙen su, ta
tattara hankalinta gaba ɗaya ta mayar gurin.

*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Written by_
*Khadeeja Candy*

*PAGE - 40*

NOT EDITED ⚠

“Haba baiwar Allah, Wannan wane irin jan'aji ne? Dan Girman Allah ki tsaya ki
saurare ni”

Abdool ya faɗa yana haɗe hannayensa, alamar yana roƙonta. Girman Allah daya haɗa ta
dashi ne yasa ta tsaya har ta ɗaga kai ta kalle shi.

“Malam ni Matar aure ce”


“Matar aure mai igiya uku ko kuma matar aure kalar aure”

“Matar aure mai igiya uku, dan haka kar ka sake bina”

Wani irin faɗuwa gabansa yayi, a take gumi ya fara zubo masa, a take launin
idanuwansa suka canja.

“Inshaallah ba zan sake ba, dan Allah ki yi haƙuri ban san kina da aure ba”

Sai a sannan ya janye ya bata hanya, ta raɓa gefensa ta wuce, shi kuma ya juya jiki
a sanyaye ya nufi hanyar fita, kallonsa ake tayi a gurin saboda wasu sun san Namra
tana da aure, wasu kuma suna masa kallon sani tun da akan nunasa a tv akan matsalar
tsaro, kuma sun san ɗan sarki ne, tun da ga fuskar Mai-matarba nan a fuskarsa.
Sam be ji maganar da wani likita ke masa ba har sai da likitan ya cira ƙafa ya
cin masa ya dafa shi.

“Manjor ina magana fa”

Ya ɗan kalleshi yana murmushin ƙarfin hali

“Doc Husaini ya aiki?”

“Lafiya ƙalau, ka zo ganin wani ne?”

“No... Eh.. Oh.. Yeah.. Yeah.. Naga wani Cousin na mu ne”

“Allah sarki, tau ya aiki ya kwana biyu? Kun yi kuɗi kun ɓoya”

“Kai ina wani kuɗi aiki ya samu gaba ba sauƙi”

Haka suka jera suna tafiya, suna ɗan taɓa fira har Abdool ya isa gurin motarsa.
Jikin sashin kuzari ya buɗe motar ya shiga yana yima Doc Sallama.

“Tau ni kan zan wuce”

“Yanzu kan ganin ka sai manya, tun da baka ma zama garin”

“To ya muka iya, aikin ne a haka ko ina jefa mu ake”

“Allah ya taimaka, sai mun yi waya”

Daga haka ya rufe motarsa, shi kuma ya juya ya koma cikin asibitin. Ribas yayi ya
juya hanyar gidan daya baro.
Tuƙin kawai yake jikinsa ba kuzari, kansa yayi zafi sosai, sai hannu yake sawa
yana murza goshinsa, lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya har ya isa gida.

Ya daɗe zaune cikin motar, sannan ya buɗe ya fito, yayi yaƙi sosai da ƙafafunsa
kamin ya ci galaba akansu har su samu ƙarasawa da shi falon Ummi.
Be damu da farar shaddar dake jikinsa ya zube saman carpet, ya lumshe ido yana
sauraren bugun zuciyarsa. Ya samu minti ashirin zuwa ashirin da biyar a haka,
sannan Ummi ta fito cikin wata bugaggar shada ya nufo inda yake hankalinta a tashe.

Saman carpet ɗin itama ta zauna kusa da shi ta kai hannu ta riƙa kansa.

“Son tell me what happen? Larai tace min ba lafiya ba, talk to your Mom please”

Sai a lokacin ya buɗe manyan golden eyes nasa ya kalleta.

“Mom i saw her today”


“Who?”

“The woman i have been dreaming of, i finally saw her in a hospital”

“And...”

“Ummi matar aure ce”

Wani dogon numfashi Ummi taja ta sauke, tana tunanin ta inda zata fara kwantar masa
da hankali.

“Abdallah, be patient one day your princess will surely come, miji baya aure sai
matarsa, mace ma bata aure sai mijinta”

“I know, but what i don't understand is duk mace da na gani bata kwanta min, sai
wannan ita kuma yanzu matar wani ce, zuciyata tana son wahalar da ni”

“Karka damu, komai zai wuce, i will talk to Mai Martaba, zan faɗa masa ya baƙa
time, har Allah ya baka wacca kake so, bana son ka auri wace baka so ina son ganin
farincikin ka”

“Thank you”

“Anything for you”

Ya ɗan kwanto jikinta, babu abunda yake gani a idonsa sai Namra.

“Allah ka shiga tsakani na da zuciyata, Allah ka min tsari da sherin zuciya”

Be ankaro da fili yayi maganar ba har sai da yaji Ummi ta amsa masa ta Ameen, dan
shi duk a tunaninsa a zuci yayi wannan addu'ar.
Ummi tana son ɗan ta sosai, ta kan damu da damu damuwarsa, ta fi kowa son
farincikinsa, saboda ta san zafinsa.

Abdallah Ahmad Mai-doki. Ɗa ɗaya namiji gurin Hajiya Zuwaira. Kuma ɗa na uku a
jerin ƴaƴanyen Mai Martaba sarkin katsina na uku III, wato Alhaji Ahmad Abdallahi
Mai-doki, jiki gurin Isma'il Mai-doki sarkin Katsina na farko.
Shine ya gaji sarautar kakansa, tun bayan da sarautar ta bar gidansu, sanadin
rasuwar kakansa. Bayan rasuwar Sarkin Katsina na biyu, sai aka ɗauko sarautar aka
bawa mahaifin Abdallah, wato Ahmad Abdallah Mai-doki.

Matan sa biyu a yanzu, bayan fitar Ummi ya auro Hajiya Salamatu, wace ta kasance
ita ta biyu a yanzu. Hajiya Zuwaira (Ummi) Ta sha gwargwarmaya da uwar gidansa
Hajiya Shafa, dan zame mata tayi muguwar kaza, mai hana shiga akurki. Hajiya Shafa
ta haifa masa ƴaƴa bakwai, Mashkur ne na farko, sannan Salwee wace ita ce ta biyu,
sannan Ummi ta Haifi Abdallah, wanda mai martaba ya saka masa sunan babansa, hakan
yasa bata taɓa faɗar sunansa sai dai ya kira sa da Yarima ko Babana.
Mar martaba yana matuƙar son Ummi ganin ita ce ƴar'uwarsa kuma itace tafi kula da
shi sama da Hajiya Shafa, hakan yasa zaman gidan ya gagareta, saboda irin son da
yake nuna mata.
Babu inda Hajiya Shafa bata shiga ta fita ba, har sai da taga ta raba aurensu da
Mar matarba, ba tare daya sani ba yayi mata saki uku lokaci ɗaya, kuma ya karɓe
ɗansa, Abdallah a lokacin yana ɗan shekara biyu da wata uku. Son duniya nan Mai
Martaba ya ɗauka ya ɗora masa, saboda son da yake ma uwarsa, sai kuma akayi sa'ah
ya zama ɗa na gari gurin iyayensa, duk kuwa da faɗi tashin da yasha kamin ya kawo
inda yake yanzu. Mai martaba ya so ya kaishi waje karatu amman Hajiya shafa ta
hana, tasa aka kai ɗanta.
Haka tasa aka riƙa tura masa kuɗi da sunan karatu ashe yana can yana holewa da ƴan
matansa, har yayi karatun ya gama be dawo gida da kyakkyawan results ba. Abdallah
da yayi karatu a Nigeria sai ya fishi ƙoƙari da basira, sosai hakan ya ƙarawa Mai
matarba ƙaunarsa, bayan ya gama degree a nan sai ya turawa waje yayi Master's.
Hakan yasa Hajiya Uwani ma da tazo daga baya ta ɗauki ƙiyayyah ta ɗora masa, kowa
cewa yake Mai Martaba yafi son sa da kowa.

Bayan fitar Ummi a gidan Mai Martaba, sai auri Alhaji Dahiru, mahaifin Haleema da
Meesha da Fauza, tana da goyon ƴar autar ta, Amal ya rasu. Tun daga lokacin bata
sake aure ba, sai tayi zamanta a gidan da take ita da yaranta, daman ba guri ɗaya
suke da abokiyar zamanta ba. Da aka raba musu gado sai ta riƙa juya dukiyar tana
business da ita har abun ya bunƙasa.

Abdallah mutum ne mai tsantsan da kai, da kuma taka tsantsan da duniya, duk da irin
tarin dukiyar mahaifinsa da ta mahaifiyarsa da kuma sarautar da suke da ita, be
taɓa sa yayi unƙurin wulaƙanta kowa akan hakan ba.
Yana yawan samun matsala da Ƴan'uwansa a lokacin da yake gurin mai martaba, ganin
irin son da yake masa, da kuma irin rufin asirin da Allah yayi masa, ga kuma aikin
da shine sillar ɗaukaka a duniya.
Baya son fitina ko tashin hankali, hakan yasa ya tattara ya dawo gurin
Mahaifiyarsa, sai ya warewa kansa part ɗaya a gidan, daman can ya zuba musu
securities. Ko kaɗan Mai Martaba be so hakan ba, amman dole ya haƙura ganin hakan
shine mafita a garesu gaba ɗaya.
Kuma hakan be rage ƙaunarsa a zuciyar Mai martaba sai ma ƙaruwa da tayi, dan a
yanzu ne Abdallah yake nuna masa kulawa da biyayyar fiye da da. Ga kuma zumuncin
daya ƙaru tsakanin Mai Martaba da Ummi, kasancewar Kakansu ɗaya, daman can auren
gida ne aka yi. Idan har zai cilasta Abdallah yin abu to sai dai ya kira Ummi ya
faɗa mata, dan baya tun karar Abdallah kai tsaye da abunda ya san zai iya sosa
zuciyarsa.

Ya kan zauna yayi fira da shi kamar abokinsa, shine yafi kowa sanin sirrin Mai
martaba, gashi ya karanci mahaifinsa sosai, da ido kaɗai zai oya gane abunda Mai
martaba yake so ko ƙi.
A duk lokacin da suke tare baka taɓa ganin danuwa a fuskar Mai matarba, idan ba su
yi labarin zamanin baya ba, tun Abdallah zai ɗauko masa firar matsalar tsaro da
kuma sauran matsalolin da suke damun ƴan negeriya, ko kuma na siyasa.

Wani lokacin kuma idan ya shiga faɗar Mai martaba, zai zauna a kusa da shi ya riƙa
karatun alƙur'ane, Mai martaba na sauraro, hakan kuma ba ƙaramin daɗi yake masa ba.
Ga shi kuma Major abunda Mai martaba ya daɗe yana mafarki Allah be ƙaddari zai yi
ba, ɗansa yayi.
Major General Abdullah Ahmad Mai-doki, an officer of very high rank in the army.
Sunan ma kawai idan an faɗa daɗi yake ma Mai maraba.

*Back to Story*

****
Sai da ya bar cikin asibitin gaba ɗaya sannan Mama ta koma ta zauna, sai taɓe baki
take, ita dai bata san ko waye ba amman zuciyarta na nasalta masa babban mutum ne,
sai dai alaƙar dake tsakaninsa da Namra ne ya tsaya mata a rai.
Bata jiyo abunda suke cewa ba, amman dai ta ga Namra ta tsaya ta yi magana da shi,
rai ta ya sosu tana jin kamar tana taya ɗanta kishi, sai yanzu take jin rashin
natsuwa a lamarin Namra ya saukar mata.

‘To idan bata san shi ba, ya za'ayi tayi magana da shi? Miye ma na wani biyota har
asibiti? Ko ƙe tsakanin su Allah masa ni’

A baɗini take zancen, a zahiri kuma sai taja tsaki, ta gyara zamanta, tana kalle-
kalle kamar baƙuwar asibitin.
NAMRA POV.

Tsaye ta tararda shi jikin window, yana kallon wani ɓangare na asibitin.
Har Sallamarta daya amsa be sa ya juyo ba, jar sai da aje abincin ta ƙarasa inda
yake tana murmushi.

“Haka ake so Allah ya ƙara lafiya”

Ya kalleta a karkace, yana mai jindaɗi har cikin ransa, shi kansa ya san yana daf
da komawa dai-dai, dan yana jin kuzari a jikinsa sosai, ga kumburin kansa nan duk a
cire.
Shi kan sa ya san he has to fight for his life, just to achieve his goal, he
needs so many things and many things need him, so there's no point of giving up.

“I'm just trying na ga samu sauki sun sallame mu Next week”

“Inshallah indai har kana takawa haka zasu sallame mu da wuri”

Ta faɗa tana shafa bayansa, daɗi har fal har cikin ranta. Bayan ya ci abincin ta
zuba masa ruwa ya sha, sannan ya ɗauko masa zancen gyara gida.

“Har yanzu Mama bata je kasuwa ba”

“Eh wai cewa tayi tun da ga wannan kuɗin Anty ta turo miki, ta ce a bar wacan a
siye magani da shi, kin ga daman rantuwa tayi abunda yayi saura sai ta mai da mata”

“Kuɗin da Anty ta tura min har na biya bashin gado da su, sauran zan siye tufafi ne
da wasu abubuwan kuma Anty tace na siye waya”

“Amman ai kin ci kin ga zinarin ki? Da kin siyar sai a ƙara ayi lalura, idan Allah
yasa na warke sai na siya miki wani, wanda ya fishi ma zan siya miki”

Ta ɓata fuska tana kallonsa.

“Ni gaskiya ba zan siyar da zinari na ba, shi ƙadai ya rage min na kuɗi, kuma ko na
siyar sana'ah zanyi da kuɗin, dan ba zan riƙa zuwa ina roƙon kowa komai ba”

Ya taɓe baki yana mata wani kallon.

“Hmmm Namra kenan, kina min kallon talaka ko? Har zan ce ki ranta min zinarin ki yi
min complain, an faɗa miki zan dauwama a talauci ne hala? Kina ganin bana da
mafitar da zan biya ki ko? Nima zan yi kuɗi Namra, zan yi arxiki irin kuɗin da baki
taɓa mafarkin Asim zai yi ba, akwai buƙatar nayi kuɗi ko dan na rama bikin da aka
min”

“Idan nayi magana zaka ga laifi na, haba Asim shikenan sai ace kullum nice zan riƙa
biyar dangi ina roƙon su abu? Yau da gobe sai Allah, na rasa komai dana mallaka,
sauran kuɗin nan daya rage min da shi nake cefane, kuma siyen abinci ba haƙƙina
bane, kai Allah ya ɗorawa amman ka ɗauki kuɗin nan ka bawa Mama, idan nayi magana
kace rantowa kayi alhalin kuɗinka ne na adashe!”

Dammm ya wulga mata wani kallo da mugun faɗuwar gaba. Ya akayi ta sani? Ina ta ji?
Ko dai Mama ce tayi subul da baka ta faɗa mata. Ƙoƙarin kare kansa yake yana naɗe
tabarmar kunya da hauka.

“Allah sarki rayuwa, talauci be yi ba, a yau har ni kike tunanin na ɓoye miki wani
abu, yau ni kike yi ma gori akan kin siye abinci, ai ban san ba dan Allah kika aure
ni ba sai yau, kina ganin kamar ba zan iya rayuwa babu ke ba ko? Kina ganin kamar
da arzikin ki nake ci ko? Kina ganin ke kika min magani ko? Da gaskiyar Mama yanzu
cewa za ayi duk ni na ƙarar miki da komai na ki, daman haka kike so ace na auro ki
na zo na aje ki ina cin amanarki ko? So that ki samu damar fakewa da na yaudare ki,
daman na san ba dan Allah kika aure ni ba”

Tun da ya soma kwarara zantukansa kallonsa kawai take tana mamakin kalamansa, wasu
zantukan ma bata san inda suka dosa ba. Yau kam ya fara fito mata a kowaye shi, ya
bayyana mata abunda zuciyarta ta soma zargi akansa.

“Na bar jindaɗin gidan mu, na zabe ka. Na watsar da karatuna na bika, saboda kar
kace na yaudare ka. Na sadaukarda komai nawa saboda kai, amman duk ban tsira ba?
Irin kallon da kake min kenan? Nice ya kamata ace na zarge ka tun lokacin da na ji
abunda kuke magana kai da Mama amman na taushe zuciyata ina ƙoƙarin yaƙi da ita
akan ka, ka kan nuna son iyayena su taimaka kama amman duk be sa na zarge ka ba,
miyasa baka tausayina ne? Yanzu na gano dalilin rashin son da Mama take min, kuna
min kallon wawuya wacce bata san ciwon kanta ba.

Son ka ne Asim shine ya rufe min ido na kasa ganin laifin ka, babu irin furucin da
ba amin ba akan ka, amman na dage sai na aureka, a tunani na kana min irin son da
nake maka ne”

Ta ƙarasa maganar murya ƙasa-ƙasa irin kifi musulmim nama, tana hawaye. Shi kam
tsire baki yayi ya kalleta

“Kowa ya sani ba tsakani da Allah kika aure ni ba, sai da wanda zai aureki yace ya
fasa sannan aka nemo ni, yanzu kuma kina son yin amfani da damar da kike da ita na
rashin lafiya ki kula wasu mazan a waje”

“Me kake nufi?”

“Kin fi kowa sanin abunda nake nufi, waya kawo ki yanzu cikin asibitin nan? Ina
kallon yadda ya rako ki ya koma, ko kin maidani mahaukaci ne, talauci ba yin kaina
bane Namra, dan ina talaka ba zaki wulaƙanta ni a banza ba”

Ta miƙe tsaye tana masa kallon mamaki, har kofin ruwan dake hannunta ya zube.

“Ka zarge ni da komai, amman ban da Zina, dan ban sha nono ba, mahaifina be yi da
ƴar wasu ba, dan haka ba za'ayi da ni ba, ban aikata zina ina budurwa ba, ba zan
aikata da aurena ba. Kai butulu ne Asim wanda be san hallaci ba, ɗan bushiya mai
soke uwar goyonsa a baya....”

Tasss ya watsa mata yatsunsa biyar a gefen fuskarsa, a zaune da yake, sai wani
zanzana yake kamar ya riƙota yayi ta dukanta.

“Kim fita da ainahin kalar ki Namra, daman kin min duk abunda kika min ne dan wata
rana ki min gori? To mina samu a auren naki? In banda baƙar ƙaddara miye ke bi na?”

Dafe kuncinta tayi ta juya a guje tana wani irin kuka mai taɓa zuciya, ta fice ɗaga
ɗakin.

RASHIDA POV.

Kukanta ne ya shigo da su Momy a ɗakin. Duk tambayar da suka mata kasa amsawa tayi
sai kuka take kamar wace aka cirewa rai.

“Ya sake ni Momy ya sake ni! Na shiga uku na lalace na ba ni Momy mutuwa zan yi,
Wayyo Allah na”

“Me kika masa?”

Momy ta tambaya hankali a tashe. Ta kardar kawai ta iya nunawa Momy tana kuka
sosai.
Da sauri Momy ta ɗauki takardar ta buɗe.

“Ni Hilal a yau na saki Rashida saki ɗaya”

Momy na gama karantawa ta rufe takardar tana faɗin

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Sai ta riƙata, ta zaunar saman gado tana girgizata, ganin tana ƙoƙarin fita
hayyacinta.

“Ke Rashida kwantar da hankalin ki zan sa ya maida ke kin ji?”

Ta rirriƙe Momy gamgam tana zare ido.

“Da gaske Momy?”

“Da gaske mana, ki kwantar da hankalin ki kinji? Zan yi magana da shi”

“Toh”

Tayi zurun kamar sabuwar mahaukaciya. Sai kallon Ummu Faisak take wace ta shigo
yanzu.

“Lafiya miya same ta?”

Ta ƙarasa da sauri tana tambaya. Momy bata iya faɗa mata komai ba ta fita ta kira
likita, yayi mata allura, cikin ƙanƙanen lokaci ta samu bachi.
Sai da suka fito sannan Momy take labarta mata abunda ya faru cikin yanayin
damuwa.

“Af ai da sauƙi tun da sakinta kawai yayi be kashe ta ba, ai a yanayin yadda ya bar
gida na ɗauka yana zuwa zai kashe ne ma, kin ga yadda yake ji da matar nan? Hmmm”

“Aiko idan ka ganta kamar ta ƙwarai, ƙo dai wani abun ne ya haɗa su?”

“Ai haka ƴan matan zamani suke, suyi miki laflaf su kwace miki miji sannan su
koreki, ai wannan saki daga gani bana banza bane mace na ciwon zubar ciki kuma
asibiti gurin iyayenta? Hmmm”

“Ai yanzu sai an bincika za a ji ko minene, bari na faɗa ma Daddyn”

Cikin yanayin damuwa da ɗaurewar kai Momy take maganar.

Hilal ko da ya koma gida ya tarar yaransa sun dawo, daga gidan Hajiya, ko wanne
fuskarsa babu walwala sun saka Kalsoom gaba, kamar su mata kuka.

“Hey kids”

Ya faɗa yana ƙokarin zaunawa sound so cool and funny. Sai duk suka nufo shi suna
faɗar.

“Daddy wai Hajiya tace mana Ammyn mu ba lafiya tana asibiti”


Ya ɗan sosa kansa, sam ya manta yace kar Hajiya ta faɗa musu. Kalsoom dake ɗauke
Rafiq ta nufo shi tana faɗin

“I try to explain but.. ”

Da ido yayi mata alama da tayi shiru yaja hannunta ya zaunar da ita kusa da shi, ya
kalli yaran.

“Listen kids Maman ku ta ji sauƙi sosai, har ma tace na gaishe ku”

“Daddy ina son na ganta”

“Ba zaki ganta yanzu ba, amman ajima zan kira miki ita a waya ku gaisa”

“Tau”

Ulfah ce ta wayance, jin ance taji sauƙi, Ezzah kam ƙin sakewa tayi sai ƙoƙarin
kuka take.

“Duk sun ci abinci, amman ita ta ƙi ta ci”

Ƙalsoom ta faɗa tana kallon Ezzah. Hilal ya kai hannu ya riƙo hannunta.

“Sweetheart ki ci abinci kin ji? Mamanki tana nan lafiya”

Kai kawai ta ɗaga masa ta share hawayen da suka zubo mata, ta nufi ɗakinsu.

******
Rashida bata farka ba sai dare, tea aka bata ta sha sannan ta kora da magani. Yanzu
nen abunda ya faru ɗazu yake dawo mata, a ƙwaƙwalwa, da sannu-sannu take tuna
komai, sai ta gane ashe ba mafarki ne take ba.
A hankali hawaye masu zafi suka fara sauko mata, zuciyarta na ƙona kamar
garwashi.

Taya zata juye rayuwa babu Hilal? Taya zata bar ƴaƴanta a hannun Kalsoom? Yanzu me
zata faɗawa iyayenta? Ga kuma ciwon dake jikinta, da wannen zata ji? Wani irin kuka
take irin kukan nan na baƙinciki da baka son kowa ya ji.

Wayarta ta janyo ta buɗe password ɗin, kamin ta taɓa komai sai ga saƙwanin sun taso
sama, na mutane da kuma mtn.
Na number Amira ta fara buɗewa, cikin ƙarfin hali ta ƙaranta, ta yi reply sannan
ta aje wayar gefe tana kallon ƙanwarta Sa'adatu take bata haƙuri.

“Momy tace zatayi ma Daddy magana sai su yi magana da Hilal ɗin”

“A'a bana da buƙata nice nace ya sake ni, karki bari Momy ta kira shi, kije kice
nace karta kira shi”

“Amman Adda...”

“Kawai ki faɗa mata, nice nace ya sake ni, kije ki faɗawa Momy”

Sa'adatu ta tashi ta fice tana hawayen tausayin ƴar'uwarta. Rashida ta share


hawayen da suka zubo kata tana kallon wayarta dake ringing.
Number Hilal ta gani, har tayi kamar karta ɗauka, sai kuma ta danna picking ta
kara a kunne, muryar Ulfah ta ji tana mata ya jiki kamin Ezzah ta karɓa.

“Ammyn wai kin ji sauƙi?”


Cikin yanayin damuwa Ezzah ta tambaya, sai kawai Rashida ta fashe da kuka.

“Na ji sauƙi Ezzah, amman ba zaki sake ganina gidan ku ba, Abbahn ku ya sake ni ya
zaɓi Antyn ku a kaina, yace baya so na Antyn ku yake so, ita zata zama mamanku daga
yanzu, Abban ku yace kar na sake shigo masa gida....!”

Hilal be san me Rashida take ce nata ba, amman hawayen da ya ga suna zuba a idon
Ezzah y tabbatar masa ba lafiya ba. Da sauri ya ƙarɓe wayar ya kashe, yana kallon
ƴarsa dake wani irin ɗaukar numfashi tana kuka.
Kamin yace wani abu kiran Hajiya ya shigo wayarsa, cikin sauri ya ɗauka.

“Hello Hajiya”

“Ka zo yanzu ina neman ka”

Bata tsaya jiran abunda zai ce ba, ta kashe wayar, hakan ya tabbatar masa da ranta
a ɓace yake.

MARDIYA POV.

Tana suɗar yatsun hannunta ta kalli Inna tace

“Wai Inna baki san wata addu'ah da ake karantawa ba, wallahi sai nayi ta mafarki
wuta na bina, kullum sai na farka a firgice”

“To ni wata addu'ah na sani, kawai ki riƙa anbaton Allah dai idan kika firgita,
kina fa cikin maƙiya, kowa ya saki gaba, ko wannan yarinyar Namratu ba ta iya miki
sheri ba”

“Hmmm Wallahi ta Allah ba ta su ba, kuma abun duk ba a so sai gan shi gare ni
wallahi, kuma Wallahi tallahi indai ina numfashi, sai na rama abunda Namra tayi
min, sai na ɗasa mata baƙincikin da har ta mutu ba zata manta da ni”

“Ai ko ita zata so ki haukace, ni wallahi kin baɓ mamaki karma wace aka ɗaurewa
baki kin ki shiru tana ta cin zarafin a gaban mutane,
Kuma ko abunta kika ɗauka ai dole ki ɗauka mace sai rowar tsiyar, ko gobarar da
tayi ai zakkace ta fita, sai ƙaryar banza wai ita ƴar masu kuɗi ce ƴar masu kuɗi
zata zauna nan a wulaƙance”

“Ƙaryar banza ce kawai ba wani ƴar mai kuɗi, ni ko cikin nan nata sai naga kamar
zubar da shi tayi wallahi”

“Saboda me? To ko bana mijin ba ne”

“Waya sani, daga maƙota ta ɗauki ƙiyayah ta ɗora min, ai ko abunta na ɗauka be dace
ta ci min mutunci cikin mutane ba”

“Ke ai wauta kika yi da ace tun lokacin kinje kin siyar ya za'ayi ta gani”

“Toh ai ina jin tsoro ne kar naje siyarwa asiri ya tono”

“To ai yanzu kin tonawa kan ki asirin”

“Uhmm”

Mardiya ta unƙura ta tashi ta fice riƙe da kwanon. Inna ta bita da kallon tana
tsakin abun haushi.
*🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺*

*© Khadeeja Candy*

ATTENTION 👇🏻
*Duk waccce take ganin ta biya kuɗi an saka ta grp na Zogon ƙasa ina son ta san da
wannan. Baki da damar sharing pages ɗina dan kin biya kuɗi har sai book ɗin ya
kammala, idan na kai ƙarshe na ƙare book ɗin gaba ɗaya a lokacin ya zama mallakinki
kina da damar ki ba duk wanda kike so aro, amman yanzu labari ne mai tafiya, kuma
ke kuɗin littafi kika biya, ashe ko idan hakan ne sai ki jira har labari ya kammala
gaba ɗaya, sannan ki bawa wanda kike so aro. Amman fitar da pages ɗin a yanxu yana
nufi karyama mai yinsa gwuiwa ne da kuma kasuwa, hakan kuma shiga haƙƙi ne!*

*Har a bada ba zan yi ma kowa Allah ya isa ba akan littafi, wannan alkwari ne
Wallahi ba zan yi ba. Amman idan har ku na min haka ne da wata manufa ta cuta
Allah yana kallon ku. Dan yasan abunda ke zuciyar ko wane bawa, sannan ina son
kusan cewa alamomin munafuƙi guda uku ne 1. In yayi zance sai yayi karya. 2. In
yayi Alkhawari saiya sab'a. 3. In aka bashi Amana sai yayi ha'inci. Duk wanda ta
shigo cikin gidan nan ta shigo ne bisa yarda da sharaɗin da aka gindaya na gidan,
dan haka idan kin fitar min da littafi ba tare da na kammalashi ba, to kin ci amana
ta kuma kin shiga cikin waɗancan mutane da Annabi ya faɗa*

*Duk wacce take fitar min da littafi dan karya min kasuwa ko dan rai na ya ɓace ko
kuma dan ƙeta, to ta sani akwai shari'ah ni da ita gobe! Kina da damar ki bayar aro
ne, idan na gama littafin gaba ɗaya, sai ki tattara pages ɗin ki turawa duk wanda
kike so ta karanta. Amman tura pages ɗin a lokacin da labarin yake tafiya, shiga
haƙƙi ne kuma abu ne da ba zan taɓa yafewa ba!*

_Allah ka ɗora mu a dai-dai, ka tunatar da mu abunda muka manta, kuma ka yafe mana
abunda muka yi akan kuskure ko ganganci._

*PAGE - 41*

NOT EDITED ⚠

Wani kallo Ezzah take yi ma Kalsoom tana hawaye, maganganun mamanta na mata yawo
aƙwaƙwalwa. Daga Hilal har Kalsoom ɗin kallonta suke, ba sun dalilin kukan nata ba,
amman sun san ba abun ƙwarai ne Rashida ta faɗa mata ba. Doc ya kai hannunshi ya
dafa sai kawai ta ƙwaɓe hannu ta juya da gudu ta nufi ɗakinsu.

“Daddy ƙyale ta Mama tace ta ji sauƙi fa”

Ulfah ta faɗa tana lanƙwamo wuyan Kalsoom da Hilal. Ɗan murmushi Kalsoom tayi tana
riƙa hannunta.

“Na sani ta ji haushi ne ba a kai ta ta ga Mama ba”

Hilal ya miƙe tsaye zuciyarsa na raya masa akwai abunda Rashida tacewa ƴarsa.

“Bari naje gurin Hajiya tace tana nema na”

“Okay Allah ya kiyaye bari nayi magana da Ezzah”

“No karki yi magana da ita yanzu, bari sai da safe”

“Okay Allah ya tsare”


“Daddy Allah ya tsare”

Ulfah ta faɗa tana tsalle.

“Amin Sweetheart sai na dawo”

Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fice. Cikin ƴan mintuna ya isa gidan
Hajiyarsa, ba tare da fargabar komai ba ya fito mota ya shiga cikin gidan.
Yana shiga falon ƙannensa da ƴaƴan ƴan'uwansa da suke gidan suka soma gaidashi suna
masa sannu da zuwa, sai da ya gama gaisawa da su sannan ya nufi ɗakin Hajiya.

Da sallama ya shiga, ta amsa masa ba tare da ta kalleshi ba, sai sarƙoƙin dake
gabanta take gyarawa, har ya zauna ƙasan Carpet yana ɗan kallon yanayinta.

“Hajiya ga ni Allah yasa ba laifi na yi ba”

“Au ashe ka san kayi laifi? Yanzu abun da kayi ma yarinyar nan dai-dai ne? Ban samu
naje ganinta ba sai da yamman nan ina zuwa suka ce min wai ka sake ta, duk kunya ya
kamani”

Ya ɗan shafa kansa.

“Ayyah Hajiya sorry ban nemi shawarar ki ba, nima a kai tsaye sakin ya zo min, kuma
bana da wata mafita sai ta sakin ne”

“Amman fisabillillahi baka tashi sakinta ba sai da tayi ɓari? Kai baka ma tsoron
ace Kalsoom ce? Na san kana haƙuri da ita, dan kai ne kaɗai zaka iya ɗaukar abunda
Rashida take maka, amman ai tuni ya kamata ka yi haka ba yanzu ba”

“Hajiya idan na sake ta a lokacin da Kalsoom bata nan wa zai kula da yaran? Kuma
lokacin ba zan iya sakin ta ba saboda bata min komai ba”

“To me ta maka yanzu? Tun tun tun baka gano illarta ba sai yanzu? Hilal bana son ka
zama cikin irin mutanen fa”

Yayi ƙasa da muryarsa yana son faɗa mata gaskiyar lamari.

“Hajiya ba zan iya ɓoye miki ba, Rashida tana da Hiv kuma ni da Kalsoom da ƴaƴana
duka ba mu da shi sai ita, kuma ta hanyar sex ta samr shi”

Wani abu Hajiya tayi da hannu irin na ƙyama da tsoro idan sun zo ma mutum a lokaci
ɗaya.

“Kana nufin Rashida tana bin maza a waje kenan?”

“Ba wai ina nufi bane, haka ɗin ne, tun da ga alamu ya nuna kuma ta tura ma likitan
da na ba jininta ya auna kuɗi dan ya ɓoye yace ba haka ba ne”

“Idan ko har haka ne, ba kayi laifi ba Hilal dan irin wannan matar babu mai son ta
zamo uwar ƴaƴansa, ni dama can yarinyar nan bata min, ai ƙara ma daka sake ta taje
can ta ƙarata ita da uban nata daya tsaya mata”

“Amman Hajiya dan Allah karki faɗawa kowa saboda rayuwar ƴarana, zasu iya shiga
wani hali kuma duk wanda ya ji zai riƙa mana wani kallo ne”

“Haba Hilal ai wannan sirri ne tsakanin ɗa da uwa, babu wanda zai ji har abada,
amman me zaka faɗawa iyayenta ne?”

“Zam ce ta zubar min da ciki ne shiyasa na sake ta, ai nasan ba zata taɓa faɗa musu
gaskiya ba”

“Allah ya kyauta, Mahaifin ka ma be sani ba, dan ban faɗa masa ba, nima haka zance
masa. Ai Allah ba azzalumin kowa bane shiyasa asirinta ya tono tun wuri da sai duk
ta laƙa muku shi sannan a gano”

“Kwata-kwata matar nan ta fita rai na wallahi, babu abunda bana mata, babu irin
haƙurin da bana yi da ita akan zamantakewar mu, akan me zata je ta bi wani a waje?
Idan akwai abunda nake mata wanda bata so ko kuma be gamsar da ita ba ai sai ta
faɗa min ai tattauna aƙe so zamantakewar aure da fahimtar juna, dan me zata watsar
da yaranta taje ta aikata wannan mummunan abu? Allah kaɗai ya san iya tsawon
lokacin data ɗauka tana aikatawa, nayi nadamar zama da ita Hajiya.

Da nasan haka zata zama da tun farko ban aureta ba, kuma ban sa laifin kowa ba
kamar na mahaifinta dan shine ya tsaya kai da fata akan dole sai ta yi aiki, saboda
kawai baya son aurna da ita, yanzu ai sai ya aura mata wanda yake so ”

“Ƙaddarori ne idan Allah ya kawo sai haƙuri, Allah dai ya ƙara tsarewa”

“Amin ni zan wuce”

“To Allah ya tashe mu lafiya, akwai waina a kula idan zaka ci”

“A'a bana son komai yau sai da safe”

Daga haka ya fice, Hajiya na kallonsa cike da tausayawa.


Koda ya koma gida Ulfah da Rafiq sun yi bachi, Kalsoom ce kawai a falo, ta ƙurawa
tv ido, duk da hankalinta ba nan yake ba.
Shigowarsa yasa ta ɗago kai ta kalleshi fuskarta da yanayin damuwa.

“Har ka dawo?”

“Eh ke kaɗai ce a falon?”

“Eh me Hajiya tace maka?”

“Tace idan na zo na cire miki kunne guda na kai mata”

Ya faɗa yana jan kunnenta har sai da tayi ƴar ƙara

“Ouuchhh nima tace na kai mata hancin ka”

Taja masa hanci ta tashi da sauri daga gurin. Ƙyalƙyalewa yayi da dariya, yana
kallon kunkurunta.

“Kalsoom zo nan”

“No no no”

“Please?”

“No no”

Ta nufi ɗakinta da sauri, sai ya bita yana dariya.

******
Washe gari da wuri Kalsoom ta tashi kamar yada ta saba, sai da ta ciro musu uniform
ta ɗora musu saman kujera sannan ta nufi kitchen ta haɗa musu breakfast, har ta
gama haɗa breakfast ɗin tunanin Rashida take, tana ganin kamar Hilal be kyauta ba
idan be barta taje ta ganta ba.

Sai da ta zuba musu abincin a kula sannan ta shiga ɗakinsu ta tashe su, Ulfah ta
fara tayarwa t miƙar da ita tsaye tana girgizata, sannan ta shiga tashin Ezzah

“Ezzah tashi ku yi shirin makaranta na gama muku abinci”

“Ki ƙyale ni ni ba zan je ba!”

Ta faɗa a tsawace tana jan bargota ta ƙara rufa, Kalsoom bata sake taɓa ta sai
kawai ta shiga da Ulfah ta haɗa mata ruwan wanka ta fito ta nufi ɗakin Doc.
Zaune ta tararda shi yana karanta saƙon da Rashida ta aiko masa. Daga bakin ƙofa
Kalsoom ta tsaya tace

“Doc Ezzah tana ta fushi har yanzu”

Ya ɗago ya kalleta

“Kamar ya me tace?”

“Wai ba zata je makaranta ba”

“What! Ba zata je makaranta ba as how? I hate nonsense”

Ya aje wayar dake hannunsa ya nufi ɗakin nasu, Kalsoom na biye da su a baya, sai
dai bata ƙarasa shiga ɗakin ba, ta tsaya daga bakin ƙofa.

Yana shiga ya shiga tashinta, tana jin muryarsa sai ta buɗe bargo ta buɗe ido,
fuska a takure tana kallonsa.

“Tashi ki yi shirin makaranta, kika ce ba zaki makaranta ba?”

“Zan je ni bana son tana tashi na ne”

“Saboda?”

“Ni bana son ta Ammyn ta faɗa min itace ta koreta baka son Ammyn Anty kake so kuma
ba zaka sake kai mu inda take ba sai dai mu zauna da Anty kuma ba zata sake zuwa
nan gidan ba, ni bana son ta Daddy i hate her”

Buge mata baki Hilal yayi, ya katsa nata tsawa.

“Kar na sake jin bakin ki ya furta irin wannan kalamin, tashi kije ki shirya zuwa
makaranta ko na zane ki yanzu nan”

Da sauri ta tashi ta shige bathroom tana kuka. Kalsoom dake tsaye jikin ƙofa tayi
saurin barin gurin, ta nufi ɗakinta.
A gaban madubi ta tsaya tana hawaye, zuciyarta sai bugawa take,motsin shigowar Doc
ne yasa ta saurin juyo ta kalleshi

“Doc ka rabu da Rashida ne?”

Ya saka hannyensa aljihu yana ɗaga mata kai alamar eh.

“Me yasa?”

“Hakan shi yafi dacewa”

“Dan Allah ka dawo da ita ƴaranta suna da buƙatar ta”


Ta faɗa da muryar kuka hawaye na mata zuba. Matsowa yayi kusa da ita ya ɗafa
kafaɗunta yana magana a hankali.

“Basa buƙatar ta matuƙar suna tare da ke, i trust you zaki basu tarbiyan daya
kamata, kuma zaki kula min da su, ba zan taɓa maida Rashida ba ko da hakan yana
nufin ƙarshen rayuwar ƴarana ne”

“Me ta aikata maka ne?”

Ya rumgume ta ƙam-ƙam a ƙirjinsa yana shirin mantar da ita zancen da suke. Sai
gurin Takwas saura ya bar ɗakin. Ko da ya fito duk suna falo suna jirana, Ezzah
idonta yayi ja sosai daga ganin alamu kuka tayi sosai, amman sai yayi kamar be kula
ba har ya kai su makarantar be yi Ezzah magana ba balle ya rarrasheta.

Daga makarantar ya wuce asibiti dan jin kiran da Rashida take masa, sam be ji wani
abu a ransa ba, na tsoro ko kuma na tunanin irin abunda ƴan'uwanta zasu masa.
Mahaifiyarta ya tarar a ɗakin dare da Babanta sun sata gaba, ita kuma sai rusar
kuka take. Daddyn ta na ganin Hilal yayi kansa kamar zai dake shi.

“Me ka zo yi cikin asibitin nan me ya kawo ka? Marar mutunci marar tarbiya, wanda
be san hallaci ba, sai yanzu data gama zazzage maka mahaifarta dan ka auro wata
zaka sake ta? Daman can ne bana son auren ku da ita dan ban yarda da tarbiyarka ba”

“To ai yanzu sai aka aura mata wanda ka yarda da tarbiyarsa, idan ta cika idda zata
iya auren wanda kake so”

Momy ce tayi saurin riƙe hannun mijinta ganin yadda ya ware zai zabgawa Hilal mari.

“Karka so ma faɗa min maganar banza, ko ba daɗe ko ba jima sai Allah ya jarrabe ka
da son Rashida kuma wallahi ba zan bari ta koma maka ba, tun da ka ci amanar ta”

“Nima ba zan koma ba Daddy nice na nemi ya sake ni, kuma yanzu nice na kira shi
akwai abunda zan faɗa masa, dan Allah ka bar ni nayi magana da shi”

Rashida ta faɗa cikin kuka. Wata muguwar harara Mahaifinta ya watsa mata kamin ya
fice shi da Momy da idonta ke cike da hawaye.

Cikin shesshekar kuka Rashida ta kalli Hilla ta soma magana dashi tana jin
zuciyarta kamar zara narke.

“Hilal ka san ina son ka, shiyasa ka yi min haka ko? Duk irin zamantakewar da muka
yi da kai haka zaka saka min? Taya kake tunanin zan rayu babu kai”

“Ta yadda kike rayu da wani na a lokacin da nake tare da ke, haka zaki rayu da wani
a lokacin da ba ni, ƙaryar so kike min Rashida tun da har kika iya aikata zina da
wani namiji bayan ni ban rage ki da komai ba”

“Ni ba dutse bace Hilal, dole akwai lokacin da zan buƙace wani a kusa da ni, a
lokacin bana gida, idan nayi kwalliya sai dai mutanen office su yaba min, su za su
gani ba kai ba, kuma dole ce tasa na fara aikatawa kamin abun ya zame min jiki”

“Faɗa min dawa kike tarayya?”

“Ba zan faɗa maka ba, amman ina son ka san da wani abu ɗaya, har a bada ba zan
daina son ka ba, kuma ina roƙon alfarmar karka faɗawa kowa sirrina”

“Ba zan faɗawa kowa ba, kuma ba saboda ke ba, sai dan saboda Ƴaƴana”
“Ba zaka sake jindaɗin rayuwar aure ba Hilal, iya rayuwar da muka yi itace ta
jindaɗin aure, wallahi Kalsoom ba zata mallake min ƴaƴa ba, idan har ban zauna da
kai ba babu wata mace da zata zauna da kai a duniya da sunan rayuwar aure, baka isa
ka raba ni da ƴaƴana ba, wata mace kuma bata isa ta maye gurbina ba”

Matsowa yayi kusa da ita cikin zafin rai zai mata magana. Sai ga Asmee ta shigo
ɗakin. Sai kawai ya juya ya fice ba tare daya faɗa mata abunda yayi niya ba.
Da sauri Asmee ta ƙaraso kusa da ita ta dafa ta.

“Ke lafiya Hilal yake kuwa? Wai jiya bayan na bar nan asibitin na ji mummunan
labari da gaske ne kuwa?”

Kwantowa tayi kikin Asmee tana kuka

“Da gaske ne Asmee ya sake ni”

“Me kika masa?”

“Ban masa komai ba haka kawai ya sake ni”

“Hmmm sherin kishiya ne, ai kinsan yadda mijinki yake son ki ba zai sake ki haka
nan kawai ba, wani asiri ne aka masa”

“Ba zai mai da ni ba, shikenan ƙarshen aurena da shi”

“Wallahi ƙarya ne, ƙarya ne wallahi Allah ya sa kiji sauƙi da wuri, kin ga malamin
nan da na kai ki gurinsa? Wallahi ki koma yayi miki aiki a gigice Hilal zai maida
ke”

“Zan koma yayi min aiki, amman bana Hilal ya mayarda ni ba, sai dai na wani abun
daban, na riga na yafe Hilal har a bada”

“Kar kice haka Allah dai ya baki lafiya”

Ƙara fashewa tayi da kuka ta ƙamƙame Asmee tana jin wani irin zugi da zuciyarta ke
mata.

AMIRA POV.

Daga ita sai tawul ta fito daga banɗaki, ta zo ta zauna gaban mirrow tana taje
kanta. Sai da ta gama ta shafa mai tayi kwalliya sannan ta kalli Guy son dake
kwance saman gado yana kallonta tace

“Amman kasan matar nan ta raina mana hankali? Sai da tasa muka bincika ko waye
likitan sannan zata ce mana wani ta fasa”

“Manta da ita kawai, akwai wani aiki da zamu je yi Abuja jibi, akwai wanda ya kira
ni kuma na san zamu samu kuɗi da yawa”

Ta baro inda take zaune, ta nufo inda yake tana wara ido

“Da gaske?”

“Na taɓa miki ƙarya?”

“No I'm just asking, you know how a like Abuja”


“Yeah shiyasa zan je da ke ai”

Rumgume shi tayi cike da jindaɗi, shi kuma ya shiga shafa jikinta.

NAMRA POV.

Cikin wani irin kuka ta isa gida. Yau duk wani tsoro da take na gidan be ziyarce
ba, dan baƙinciki dake tare da ita tafi tsoro, yadda ta ga dare haka taga dare, sai
ta tashi tayi sallah, tayi addu'ah samun mafita da sauƙi a zuciyarta. Tana gurin
bata tashi ba har aka kira sallah asuba, kasa cin komai tayi da safe, ji take
kamar ta kashe kanta ta huta, kalaman Asim sun tsaya mata a rai, sai yanzu ta fara
gasgata kalaman Anty Amarya, ayau Asim ya nuna mata ko waye shi, ya buɗe mata
sirrin dake ransa, sannan ya zarge ta da abunda wani be taɓa mata ba.
A tau ta tabbatar da tayi zaɓen tumun dare, sai a yanzu tana ganin laifin
zuciyarta.

“Miyasa kika bar ni na kamu da son wanda ba dan Allah yake so na ba? Dan me baki
bar ni na so waninsa ba? Duka yaushe muka yi aure da shi amman yau ya sauya min ya
nuna min abunda ban taɓa mafarki ba? Yanzu ya zanyi da rai na? Na bar karatuna
saboda shi na zo garin da ban san kowa ba saboda shi amman duk ban masa ba?”

Ita ƙaɗai take magana da kanta, tana wani irin kuka mai taba zuciya. Bata ji a yau
zata iya kwana a katsina, dan a yau bata buƙatar kowa a kusa da ita sai yan'uwanta,
da mahaifiyarta, tasan ko hira kawai tayi da su zai rage mata damuwa, sama da zaman
kaɗaici da take yanzu.
Tashi tayi ta matsa kusa da inda ta aje ƴan komatsanta.
Jakarta ta buɗe taga kuɗin da yayi mata saura, sai ta shiga BQ ɗin ta ɗauko Sarƙa
da wayarta ta saka a jakarta ta sauya hijabinta ta jawo BQ ɗin ta fito tana kuka.

Sai da ta tari Napep ta shiga sannan wani tunanin ya zo mata. Idan ta koma gida da
wane ido zata kalli Anty Amarya? Me zata cewa Abbah? Masu jiran su yi musu dariya
tasan zasu yi. Har ya kai ta tasha bata samawa kanta wata mafita ba, sai dai hakan
be hana ta shiga motar sokoto ba, tun da bata da wani gurin zuwa sai can.

ABDOOL POV.

Yana zaune ƙasan Carpet yana cin abinci, Ummi dake zaune saman kujera ta tsare sa
da ido tana kallon ɗan nata cike da tausayawa.
Sai da ya gama cin abincin sannan ya kalleta yana murmushi.

“Ummi wannan kallo ai sai ki tsorata ni, gani zanje Abuja gobe ai sai kisa nayi
tunanin ko mutuwa zan yi”

Ɗan murmushi tayi ta kawar da kai.

“Kawai ina tausayin ka ne, jiya da zafin jiki ka kwana saboda tunanin nan yarinyar
how i wish ina da wani abu da zan yi akai”

“Karki damu, ni ai haka jiki na yake, mutane suna cewa ba komai bane dan kaji mutum
da zafin jiki”

“Ba irin naka zafin ba, wacan ɗan ɗumi ake nufi kuma shi ma a mace ne ba namiji ba”

Dariya yayi ya tashi tare da plate ɗin

“Ummi kenan, ni fa bana da wata damuwa yanzu sai ta Mai Martaba”


“Zan yi magana da shi ai na faɗa maka, kawai kai dai ka samu natsuwa kuma ka
kwantar da hankalin ka”

“I will try inshallah”

“Ni Allah yasa ma Abujar nan da zaka je ka haɗu da wata wanda zaka so fiye da
wannan ma”

“Ai gurin aiki zamuje ba gurin hutawa ba, idan kuma kina son na ɗauko miki soja
shikenan, sai na auro soja”

Wani tsaki taja ta ɗauke kai ta mayar gurin tv. Shi kuma yayi dariya ya shige
kitchen.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺*

*© Khadeeja Candy*

*PAGE - 42*

NOT EDITED ⚠

Da yamma lis Namra ta sauka babbar tashar sokoto, sai da kowa ya gama fita motar
kasancewar ita ce a can baya sannan ta fito jiki a sanyaye, tana kalle-kalle kamar
mai tunanin inda zata je.

A hankali ta cira ƙafarta da tayi mata nauyi saboda zaman mota ta fara takawa, ta
doshi ƙofar fita tashar gabanta sai faɗuwa yake kamar zai fito, wani abu ta ji ya
zo ya tsaya mata a zuciya, yana ƙoƙarin danne mata numfashi.

Ta daɗe a tsaye bakin ti-ti sannan ta tari Napep ta shiga, sai da ya fara tafiya da
ita suka yi nisa sannan ta ɗan karkato ya tambayeta inda za a kai ta ganin bata ce
masa komai ba tun da ta shiga Napep ɗin.

“Hajiya ina za mu?”

Shiru tayi kamar mai tunani, ta ɗauki tsowon lokaci bata amsa shi ba, har sai da ya
ƙara tambayarta.

“Clapperto....road, gurin....gawon nama”

“Dari biyu zaki biya Hajiya”

“Ok..ay.. Allah Kai... Mu lafiya”

“Amin”

Ya kai hannu ya kunna waƙar Umar M Shariff ta duniya makaranta. Sauraren waƙar take
tana hawaye, hankalinta da tunaninta gaba ɗaya ya tattara ya koma gidan su da take
tunkara yanzu. Abunda zata faɗa musu take ta saƙawa amman har ta saka samun mafita.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta furta a hankali lokacin da Mai Napep ɗin ya kunna kai cikin unguwar. Jin tayi
kamar tace ya juya da ita, sai dai idan ya juya da ita ɗin ina zata ce ya kai ta?

“Ya isa...”
Ya faɗa a lokacin daya kawo bakin ƙofar gidan su. Sai da ta share hawayen idonta
sannan ta ciro kuɗinsa ta miƙa amsa, sannan ta fita jikinta har rawa yake irin na
tsoro da rashin gaskiya yana tare da ita.

Sai da Mai Napep ɗin ya wuce, sannan ta doshi ƙofar gidansu, cikin wani irin mugun
faɗuwar gaba. Har ta kai hannu zata tura ƙofar gate ɗin sai kuma ta tsaya tana jan
numfashi.
Tafi kowa sanin waye mahaifinta, ta kuma san halinsa ba zata manta furucin da yayi
mata ba, bata san iya furucin da zai ƙara mata ba.
Babu wacce ta faɗo mata a rai, sai Gwaggo Kulu, ƙanwar Abbah, mahaifiyar Anty
Yasmin.
Tasan ƙanwar Abbah ce amman Abbah yana jin maganar ta sosai kuma tasan yadda Gwaggo
Kulu take son ta cikin ƴaƴan Abbah.

Juyawa tayi da saurin ta nufi farƙon unguwar dan ta can ne zata fi saurin samun
abun hawa. Sai da ta kusa ƙarasawa babban ti-ti sai ta ga Motar Maryam ta kunno kai
cikin unguwar. Da sauri Namra ta kawar da fuskarta dan kar Maryam ta ganta, ashe
tayi a banza dan baya-baya Maryam tayi da mota ta fara leƙen fuskarta, hakan be
gamsarda ita ba har sai da ta faka motar gefe ta fito ta fara bin Namra da ƙafa
tana kiran sunan ta.

“Anty Namra ke ce?”

Juyowa Namra tayi ta kalleta idonta da hawaye ta ɗaga mata kai.

Wani irin tsalle Maryam ta daka ta rumgumeta tana ihu.

“Wallahi ban ɗauka ke bace nayi zaton wata ce mai kama da ke, Anty Namra ina za
ki?”

“Gidan Gwaggo Kulu zan je”

Ta faɗa cikin kuka tana rumgume da ƙafaɗar Maryam. Maryam ta ɗago ta kalleta

“Miyasa ba gida kika zo ba?”

“Amman nasan Abbah ba zai bari na zauna ba, korata zai yi”

Maryam ta dafa kafaɗunta.

“Fushi kika yi?”

Tayi shiru bata amsa ta ba, hakan ya tabbatar ma Maryam amsar tambayar.

“Wani abun Asim yayi miki ne? Karki ɓoye komai Anty Namra ki faɗi abunda yayi miki,
dan ba zai yiyu ya taɓa mana ƴar'uwa ba mu ƙyale shi”

“Be min komai ba, ni dai kawai na gaji da zaman can ne”

“To ki zo muje gida”

“A'a ni ba zan je ba, Abbah zai kore ni kuma Anty ba zata ji daɗi ba”

“To ya zaki yi? Kina da inda ya fi miki gidan uban ki ne? Ko yanka namanki zai yi
yayi gunduwa-gunduwa da shi dole ne ki shiga tun da baki da inda ya fi miki nan”

“Ni dai ba zan je ba, gidan Gwaggo Kulu zan je”


“To muje na kai ki”

Maryam ta faɗa tana nuna mata motarta. Kamar ba zata shiga ba, sai kuma ta nufi
motar ta buɗe ta shiga. Sannan Maryam ta shiga driver seat ta tashi motar, ribas
tayi ta juya ta inda ta fito, sai da suka hau babban ti-ti sannan Maryam ta kalleta
tana takaicin halinta tace

“Wani lokacin Anty Namra kina ban haushi da mamaki wallahi, kina abu kamar ba kece
yayata ba, abunda kike yi ko Aisha da take ƙaramar mu ba zatayi ba. Kin san abunda
yake cutar da ke? Tsoro da gudun zuciya, da ganin ke ba zaki iya ba, sune suke
cutar da ke.

A duk kuma lokacin da kike ganin ke ba zaki iya ba, to ba zaki taɓa iyawa ba har a
bada, lokacin da zaki hankalto kice zaki yi a lokacin ba ki da time, shiyasa yan
karon magana suka ce if you say yes to others make sure you didn't say no to
yourself, saboda zaki cutar da kan ki ne kawai, ba zaki taɓa burge kowa ba a
duniyar duk abunda za kiyi wani sai yace kin masa ba dai-dai, ya kamata ace kin
canja haka nan accept responsibility for your life, ya kamata ki san it is you who
will get you where you want to go, no one else, duk wanda kika gani yana kusa da ke
wallahi da zaki waiwaya wata rana zaki ga duk babu so, sai mai miki so na haƙiƙa,
wasu duk dariyar fuska ne bda xaki san abunda yake zuciyarsa da ba zaki sake
kallonsa ba.

A maimakon ki ƙara hankali da tunani amman kullum sai wata iri kike zama, kamar
wanda ake cirewa ƙwaƙwalwa ana zubarwa, tsoron nan da yake ran ki dan Allah ki cire
shi Namra, you have to your fears, kuma ya kamata ace kisan cewa kema kina da right
and freedom...”

Tun da Maryam ta soma maganar in banda kuka babu abunda Namra take, ta san gaskiya
ƴar'uwarta ke faɗa mata, tabbas akwai tsoro a a tare da ita, tsoron abunda mutane
za su ce, tsoron ɓacin rai, tsoron ganin ita ba zata iya ba, da kuma gudun zuciyar
wanda duk take tare shi. A rayuwar Namra bata iya so ba, irin son nan take yi na
sadaukar da komai nata saboda wanda take so ko kuma ta yarda da shi. Indai Namra ta
aminta da kai to kai je ka kwanta kawai kayi kwana, ita zata maka komai idonta ya
kan makance ga duk wanda take so, bata ji bata gani.

“Mtsssssss”

Maryam taja tsaki.

“Aikin kenan sai kuka, da anyi miki abu kuka dai kuka, da kuka zai miki magani ai
da tuni yayi miki, haka kika zo kika sakarwa yarinyar Amira jiki ta yi ta cin
amanarki, Allah kaɗai yasan dalilin guduwarta daga gida, amman kullum uwarta ke
take cewa ke ce sanadi”

Unguwar Bafarawa estates Maryam ta kai Namra, gidan Gwaggo Kulu.


A bakin gate ɗin gidan tayi farkin ta kalli Namra

“Yanzu idan kin shiga sai kice mata me?”

“Zan ce nan na fara sauka ne”

“Toh nidai ba zan shiga ciki ba, kuma idan na koma gida zan faɗawa Anty duk yadda
muka yi da ita zan dawo na faɗa miki”

“Amman dan Allah karki faɗawa Abbah”

“Tau ina gaida Gwaggo”


Namra ta fita motar cikin yanayin damuwa ta shiga gidan Gwaggo. Sai da ta shige
sannan Maryam ta juya da motarta tana mamakin lamarin Namra.

Cikin sanyin jiki Namra ta shiga harabar gida,har ta ƙasa falon tana jin tsoro
kamar wanda za'ayi ma wani abu.

“Assalamu alaikum”

Cikin sanyin muryar tayi sallamar Yasmin da Gwaggo Kulu suka amsa mata. Tun da ta
shigo cikin falon Yasmin take mata wani irin kallo kamar bata gane ta ba. Kallon
gulma take mata ganin yadda tayi baƙi sosai, daman can ba fara bace amman baƙin na
yanzu ya ninka sosai, ga wata rama da tayi kamar wanda ta kwanta ciwo.
Ita kuma duk taji wani yanayi na daban, musamman ganin Yasmin da tayi a gidan.
Bata zace zata rarar da ita ba.

AMIRA POV.

Duk wani farinciki da Amira take yi na zuwa abuja, a yanzu na zama labari, tun jiya
da Guy son ya labarta mata dalilinsa na zuwa abuja da
Sam bata son aikin da Guy son yake wani lokacin ƙara kidnapped da saffara ƙwayoyi
da yake da aikin kisan kai, sai dai ta san bata isa ta hana shi wannan aikin ba,
dan be haɗa aikinsa da komai ba, bata wani daɗe da shi sosai ba, amman ya sake da
ita ya shigar da ita jikinsa ya nuna mata so da yarda sai dai be yarda ta hana shi
aikinsa ba.

“Wa zaku je yin attacking?”

Ta tambaya tana saka kayanta a jaka.

“Wani soja ne, amman ba a Abuja za muyi attaching nasa ba, daga nan sai za mu bisa
za a bamu address nasa sai idan ya koma gida za mu ƙaddamar masa”

“Kashe shi zaku yi?”

“Haka ake son mu yi”

“Waya sa ku?”

“Wata mata ce amman bata son a gane ita ce, shiyasa take son mu bishi daga nan
abuja ta yadda za'ayi zaton ko abokan aikinsa ne, yanzu haka ance mana yana cikin
garin abuja”

“Amman Guy miyasa kake son kashe rai?”

“Saboda ban ɗauki rai a bakin komai ba, kema wata rana zaki aikata”

“Bana fatan aikata kisan kai har a bada”

Zuwa yayi ya dafata yana murmushi.

“Karki damu idan har kin kashe mutum kin lasa jininsa babu abunda zai same ki, ki
shirya muje kar mu yi latti”

Cikin sanyin jiki ta rufe akwatin. Bata san wanda zasu kashe ba amman tana jin
rashin kyautawa a lamarin.
Zama tayi saman gadon kamar mai jimami har sai da ya shigo ya ɗauki akwatin nata
sannan ta tashi ta fita cikin sanyin jiki.
ABDOOL POV.
Jirgin safe ya bi ko da biyu na rana tayi har ya gama meeting ɗin da zasu yi, ya
koma masaukinsa.
Kwantawa yayi ya ɗan runtsa na mintuna sannan ya tashi ya shiga yayi wanka, ya
ɗauro alwala sannan ya fito, ƙananan kaya ya saka yayi sallah la'asar sannan ya
ɗauki wayarsa ya kunna, text ɗin Ummi ya gani, hakan ya sashi jindaɗi tare da
murmushi, sai ya danna numberta ya aika mata kira. A harabar gidan yana waya da
Ummi, sai shafa kansa yake yana mai jin shauƙin son mahaifiyarsa cikin ransa.

“Alright Ummi i will, Thank you love you lot”

Ya kashe wayar fuskarsa da murmushi, yana kallon wata kurciya dake sha'aninta a
harabar gidan nasa.

Ido ya tsura mata sosai yana son tantance abunda ya gani rataye a wuyanta. Ɗan
matsawa yayi a hankali yana kallon layar dake wuyan nata, sai ya shiga ƙoƙarin
kamata, be yi nasara ba ta yi firrrrr ta tashi sama, ta haye saman ginar gidan.

Tsaye yayi yana kallonta. Sai ya ƙwalama yaransa kira.

“Hey Boys”

“Sir”

Duk suka sheƙo da gudu, sai dai kamin su ƙaraso har ta ƙara fira ta bar gurin.

1869k words. Sorry for the short chapter 🙏🙏🙏


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺*

*© Khadeeja Candy*

*PAGE - 43*

NOT EDITED ⚠

Cikin rashin kuzari Namra ta zauna saman kujera tana kallon ƙasa kamar mai jin
kunya.

“Namra...”

Ta ɗan ɗago kaɗan ta kalli Yasmin data kira sunanta, sai kuma ta kalli Gwaggo Kulu
dakr tambayarta saukar yaushe.

“Yanzu na zo”

“Ya hanya ina mijin na ki?”

“Yana lafiya”

Kallon Namra Yasmin take zuciyarta na raya mata ba haka kawai Namra ta zo gidan ba,
idan ma wani abun ne ai gidansu zata sauƙa. Murmushi tayi ta tashi ta nufi Namra ta
riƙa hannunta.

“Tashi muje ciki kin wani zo nan kin zauna kamar baƙuwa”
Kallon Yasmin Namra tayi, murmushin data gani a fuskarta ne ya bata kwarin guiwar
tashi ta bita. Ɗayan ɗakin Gwaggo Yasmin ta shiga da ita, daman can ɗakin ta fi
zama a duk lokacin data zo gidan.

Yasmin ta buɗe bathroom ta duba ruwan dake ciki, sannan ta fito tana miƙawa Namra
tawul.

“Shiga ki yi wanka, sai na kawo miki abinci”

Idonta a ƙasa take miƙawa Namra tawul ɗin irin bata son kallonta tana jin nauyin
Namra sosai.
Hannu Namra tasa ta karɓa, sai Yasmin ta fice, ita kuma ta kwaɓe tufafinta ta ɗaura
tawul ɗin ta shiga wanka, ko da ta fito Yasmin ta aje mata gown ɗin atamfa da
abinci.

Ɗaukar rigar tayi ta saka, daman tayi alwala tun a toilet ɗin, sai kawai ta saka
hijabinta, tayi sallah. Bata ci abincin ba dan bata jin cin komai, lemum kawai ta
sha, sai ta ɗauki carbi tana tasbihi.

“Assalamu Alaikum”

Yasmin ta shigo bakinta ƙumshe da sallama, murya ƙasa-ƙasa Namra ta amsa mata, sai
ta zauna kusa da ita tana wasa da hannayenta.

“Kin abincin dai ko?”

“A'a bana jin yunwa”

Kallon fuskar Namra tayi da kyau-kyau, tana ƙoƙarin karantar danuwarta

“Namra, kiyi haƙuri na ji ance mijin ki yayi haɗari, kuma duk a familyn nan babu
wanda yaje ganinsa, ni ma naso naje na gansa Allah be nufa ba”

“Ba komai, ai yaji sauƙi”

“Allah ƙara lafiya, tare dashi kuka zo?”

“Ni kaɗai na zo”

“Amman ba kije gida ba ko?”

Ta ɗaga mata kai, kalar tausayi. Har Yasmin zata


tambaye ta ko dai faɗa suka yi da Asim, sai kuma taga rashin dacewar haka. Sai
kawai ta tashi tana faɗin

“Ni kan zanje gida, ai nan zaki kwana ko?”

Ta ɗaga mata kai. Sai Yasmin tace

“Da safe zan aiko miki da breakfast”

“Na gode Anty Yasmin”

Namra ta faɗa idonta cike da hawaye. Rayuwar da suka yi a can baya ne ya riƙs dawo
mata sabo, yadda Yasmin take treated ɗi kamar wata ƙanwarta da suka fito ciki ɗaya,
amman yau duk babu wannan, tun da Uzair ya shiga tsakaninsu.
Ɗan murmushi Yasmin tayi ta juya ta fice.

Ɗakin Mahaifiyarta dan yi mata sallama. Ko da ta shiga Gwaggo Kulu na banɗaki, tana
alwalar magariba. Gefen gado ta zauna har ta fito sannan ta miƙe tsaye.

“Gwaggo ni kam zan tafi, Uzair ya kira ni tun ɗazu wai yana gida”

“Ba zaki bari kiyi sallah magariba ba”

“A'a sai na je can zan yi”

“Toh Allah ya tsare, kin yi magana da Namra?”

“A'a ba mu yi mafanar komai ba, amman dai tace min bata je gida ba, ina ganin dai
ta zo ne ba tare da sanin mijin ba”

“Toh Allah ya sauwaƙe, shiyasa ta ƙi sauka a can ta sauka nan”

“Haka nake tunani, kuma kin san halin Abbah da zuciya ƙila ma ta je ya hanata shiga
gidan”

“Toh ai sai ta yi zamanta nan”

“Ni dai na tafi, da safe zan aiko mata da breakfast”

“To Allah kai mu lafiya”

Ta ɗauki jakarta da mayafinta ta yafa ta fito, zuciyarta cike da tausayin Namra.


Motarta ta shiga tayi mata keys kamin ta isa gida Uzair yayi mata kira biyu tana
ce masa gata nan kan hanya amman duk be yarda ba gani yake kamar tana gidan zamanta
ne, shi ta bar masa yaro sai fitina yake masa.

A harabar gidan ta faka motarta, sannan ɗauki takardun dake cikin motar da system
ɗinta ta buɗe motar ta fito, ɗayan hannunta tasa ta lanƙamo jakarta sannan ta rufe
motar, ta nufi ciki gidan.

“Assalamu Alaikum”

Tun a bakin ƙofa ta zubar da files ɗin dake hannunta da handbag, system ce kawai ta
samu ƙarasa tsakiyar falon ta aje ta saman kujera, tana kallon Uzair daya kama
hannun Adnan ya riƙe.

“Dan Allah zo ki raba ni da yaron nan, sam be jin magana wallahi, tun ɗazu yaƙi
bari na huta”

Ƙyalƙyalewa Adnan yayi da dariya yana kallon Yasmin dake murmushi yace

“Mom wai ba zai ba ni wayarsa ba, tun da ba ke kika siya ba”

“Zo ka ɗauki nawa kayi game, amman ka kwashe takardun nan ka kai ɗaki”

Ta faɗa tana nuna masa bakin ƙofa inda ta jefar da jakarta da takardun. Da gudu
yaron ya sance hannunsa daga riƙon da Uzair yayi masa ya nufi gurin ƙofar yana
tsalle.

“Wallahi duk kin ɓata min yaro, sam yanzu baya jin magana”

“Kai dai ka ɓata abun ka karka ɗora min laifi”

“Kuma na faɗa miki ki daina wucewa gida idan kin san ki bar min Adnan”

“Bloody yau ina gida sai ga Namra”


“What!... ”

Ya gyara zamansa.

“Wallahi, duk ta rame tayi baƙi sosai kamar ba ita ba”

“Me ta zo yi?”

“Ina ganin tayi yaji ne, dan ƙin sauka tayi gida sai ta sauka gidan mu”

Ya taɓe baki, irin ko a jiki na can ta matse mata.

“Ai bama zata yi kuskuren sauka gidan Abbah ba kam, ko minene ai ita ta jawa kan
ta”

“Ni wallahi tausayi take bani, da na sani tun farko dana barka ka aureta, ji duka
yaushe akayi auren amman har ta koma haka”

Ya miƙe tsaye yana wata dariya.

“Na aure ta na kai ta ina? Kin ɗin ma kin fitineni kin hanani sukuni balle kuma na
haɗa ku biyu, ai ni sai yanzu na ga hikimar rashin aurenta da nayi, na gode Allah
wallahi”

“Haƙurin da nake da kai babu macen da zata iya yinsa da kai, baka da time ɗin na,
baka bani haƙƙina kwata-kwata ma bana gabanka, in nayi kwalliyar duniyar nan bana
burge ka, ai dole nayi magana tun da ni ba ice ba ce”

“Kyaji da kan ki, kin cika jaraba ne, akwai wanda yake shekara ma babu ruwansa da
iyalinsa kuma suna zaune lafiya, sai ni kullum cikin complain kike, kuma tun da
kika ga ban gyara ba ai kinsan haka Allah yayi ni, ni bana da sha'awa”

“Wallahi ba haka Allah yayi ka ba, ko minene dai daga baya ne ya same ka, ai da can
ba haka kake ba, ko dai dan na haihu ne na daina burge ka?”

“A'a karki sawa ran ki wani abu, wallahi bana neman mata a waje, babu ruwana da
mata, kawai dai sauyin yanayi ne”

Ya sa hannayensa aljihu ya nufi ƙofar fita. Da kallon ta kaici ta bishi, har ta


fice, sannan ta sauke ajiyar zuciya ta tashi ta nufi ɗakinta dan dauke faralin da
yake kanta na sallah magariba.

A masallacin unguwar ya yi,alwalah yayi sallah magariba, shi kaɗai yayi abarsa dan
su tuni suka sauke jan'i. Bayan ya fito ne ya ciro wayarsa dake aljihu ya kira
number Hajiya Barau dan tsegunta mata labarin Namra, duk da yana tunanin ta san da
zuwan na ta.

Two missing calls yayi mata, bata ɗauka ba, har ya mai da wayar aljihu sai gata ta
kira, cikin sauri ya ɗaga kiran nata yana takowa zuwa gida.

“Hajiya ina wuni?”

“Lafiya ƙalau Uzairu ka kira ni ina sallah, ya gida ya mijina da Yasmin?”

“Suna nan ƙalau, yanzu ma Yasmin take faɗa min wai Namra ta zo, tana gida da yake
ita gida ta wuni daga gurin aikin ta wuce gida”

“Namra kuma? Amman bata sauka nan?”


“Au daman bata sauka nan ba? Ai na ɗauka ta kwana biyu da zuwa ma”

“A'a Wallahi ni ban ji labari ga kowa ba, amman ita taga Namra ɗin da idonta?”

“Haka tace min, yanzu haka tana gidan Gwaggo”

“To ko fushi take da Alhaji ?shiyasa bata sauka nan ba?”

“Idan ma fushi take da Abbah ai ke ba zatayi da ke ba, kuma ga Anty”

“A'a mu a su wa? Kishiryar uwa mai ƙaurin suna? Ta dai san ba zuwan lafiya bane
shiyasa ba zata sauka nan ba, dan tasan halin Alhaji shiyasa aka ce in za a yi
tukka a yi mata hanci don kada ta warware, irin wannan ranar ake gudu, daman ni
nasan abin da ya ci doma ba ya barin awai, yadda yarinyar nan ta ci amanarka ai
dole alhakin ka ya fita”

Uzair yayi wani shegen murmushi

“Ashe baki san ta zo ba, amman ina jin Anty ba zata rasa sani ba”

“Ina jin ta sani sai ta ɓoye, waya sani ma ko ita tace mata ta sauka gidan Hajiya
Kulu tun da tasan tana son Namra, ba zata bari Alhaji ya wulaƙanta ba, ji fa ko
gobarar nan da tayi har yau bata taɓa maganar ba, in ban da ƴan'uwana da suka ce
suka faɗa min da ban ji ba, ai ni naji daɗin da Alhaji ya juya mata ƴarta baya, dan
duk abunda take da sanin uwar nan take yinsa, ita ke goya mata baya, ko auren nan
naku da anyi da sai uwar nan ta kashe shi dan bata son ka”

“Allah ya kyauta, ai ga ta nan ta dawo mata sai tayi yadda take so da ita, Yasmin
tace min duk ta rame ta yi baƙi”

“Lallai kam, kowa ya keta riga tasa, ya san inda zare ya ke”

“Kaɗan suka fara gani”

Ya faɗa sannan yayi sallama da ita ya kashe wayar. Hajiya Barau ya aje wayar ta
cire Hijabin dake jikinta ta tashi ta nufi part ɗin Abbah.

MARYAM POV.

Da takaicin Namra ta koma gida, sai dai bata labarta ma Anty Amarya komai ba, dan
bata san ta yadda zata ce mata ba, sai bayan magariba, sannan ta labarta mata
abunda ake ciki.

Duk rikicewa Anty Amarya tayi murna da farinciki suka zo mata a lokaci ɗaya, murnar
ƴarta ta zo da kuma baƙinciki bata sauka a gidan ba, ita kan ta tasan sai anyi yaƙi
da Abbah kamin ya barta ta zauna gidan.

“Amman Maryam ita kaɗai kika ganta?”

“Eh ita kaɗai, Anty duk ta lalace ta rame Allah kaɗai yasan abunda yayi mata tun da
har kika ga ta baro shi ta zo nan, bayan kuma ta san halin Abbah”

Sai duk Anty Amarya ta ji babu daɗi, a take ta ji tana buƙatar ganin ƴarta.

“Zan faɗa ma Abbanku ta zo ganin gida ne, ai dole ya barta ta zauna”

Maryam zata yi magana sai ga wayarta tayi ringing, Sweet PaPa ta gani hakan ya
tabbatar mata da number Abbah ce, da sallama ta ɗauki wayar dan tasan Abbah ya
tsani ya kira mutum ace masa hello.

“Maryam”

“Naam Abbah”

“Ki ce Mamanki ta zo yanzu”

“To”

Ta kashe wayar gabanta na faɗuwa, duk da bata san anyi komai ba, amman ta ji kamar
ba lafiya ba, ta kalli Anty Amarya dake cikin yanayin damuwa tace

“Wai Abbah ki zo”

Shiru Anty Amarya ta ɗan yi sannan ta tashi cikin rashin ƙarfin jiki ta nufi part
ɗin Abbah ba. Zuciyarta da biyu, ta faɗawa Abbah Namra zata zo ganik gida, kuma ta
ji kiran da yake mata. Sai dai duk hanzarinta ya katse lokacin da Abbah ya gargaɗe
ta akan kar ta bar Namra ta shigo masa gidan.

“Ki faɗawa ƴar ki karta kuskura zuwa min gida, ta tsaya can inda ta sauka”

“Ƴata ce kai ba da kai ba? Ko shegiya na haifa ne?”

“Nine ubanta, amman na riga na yafe ta, kuma tun ranar da zata je gidan mijinta na
faɗa mata karta kuskura dosomin gida da sunan yaji ko saki”

“Ai ganin gida zata zo”

“Ba ganin gida ta zo ba, na dai faɗa miki karta doso min gida”

“Ƴata tana da buƙata na, kuma dole ta zo nan gidan nan tun da ina ciki, ko wane
munafukin ne ya zo ya faɗa maka sai na ci masa mutunci”

Abbah yayi banza da ita yana kallon agogon hannunsa.

“Yanzu zamu je karɓo kuɗin kwangila, karki kuskura ki bari ta shigo min gida indai
ba mugun wulaƙanci kike so na mata ba”

“Idan bata shigo ba, ni zan koma gidan mu na zauna da ita, dan ba galihu ne bata da
shi ba, abunda kake yi baka kyautawa Alhaji, musulunci be ce haka ba, shikenan dan
kawai ta auri wanda take so sai abu ya zama ɗan zane”

“Ai daman duk abunda take da goyon bayanki take yinsa, ke kika goya nata baya”

“Ni nake goya mata baya, ai daman ka saba faɗar haka, komai nice, daman na san ba
ƴata ce baka so ba, ni ce baka so, ita Hajiya da take ƴar'uwarka ai baka mata haka
ba balle ƴaƴanta, sai ni da ka auro bare, nice abar wulaƙantawa ni da ƴaƴana, ko
kuma saboda ni ban haifi ƴaƴa maza ba shiyasa kake min haka”

Cikin faɗa da kuka Anty Amarya tayi maganar. Sai Abbah yayi mata wani kallo na
mamaki.

“Subhanallahi, ai ƴaƴa maza da mata duka ɗaya ne a gurin Allah”

“Amman kai a gurin ka ba ɗaya bane, tun da gashi kana nuna min banbanci, idan baka
da rai a yau babu wanda zan kallah na ji sanyi sai ƴaƴaka, haka nima idan bana da
rai babu wanda zaka kalla ka tuna da ni ko kaji sanyi sai ƴaƴana, to dan me zasu
zama abun wulaƙantawa a gareka, ashe wata rana idan bana da rai abunda zaka ma ƴar
ciki sai yafi wannan tun da kayi mata haka ina raye, kai da ƴan'uwanka kun sa Namra
a gaba, kamar ta kashe muku wani, daman ni ce ba ku so ba ita ba”

Ta juya ta fita tana wani irin kuka kamar ta faɗi ƙasa. Har cikin ransa Abbah yake
jin kukan Anty Amarya, kalamanta sun ɓata masa rai, sai kuma sun fi taɓa masa
zuciya sosai har sun sa ya sauko daga fushin da yake.
Ɗakinsa ya koma ya ɗan kimtsa sannan ya fito ya nufi gurin da aka saba aje masa
motocinsa.

Da kuka Anty Amarya ta shiga part ɗinta, duk hankalin Maryam sai ya tashi,
kasancewar ita kaɗaice ke falon, ganin mahaifiyarta na kuka, yasa ita ta fashe da
kuka ba tare da tasan dalilin kukan na Anty ba.

“Anty me ya faru?”

“Wallahi yai ba zan kwanan a gidan nan ba, babu abunda zai sa na kwana gidan da za
a hana ƴata shigosa, yafi son ta je can ta zauna inda za a riƙa zaginta ana
tseguminta”

“Be yarda ta zauna, ban san munafukin daya faɗa masa ba”

“Anty kiyi haƙuri, zai sauko yana cikin fushi ne”

Aisha ce ta fito daga ɗakinsu ita da Hindatu suka nufo gurin da Anty Amarya take,
suna tambayar ba'asi, dan basu san abunda yake faruwa ba, suna can ɗaki suna
karatun exam.

“Lafiya miya faru”

Aisha ta tambaya tana dafa Anty.

“Abbah ne yace wai Namra ba zata shigo masa gida ba”

Maryam ta faɗa tana kuka. Hindatu ta kalleta da mamaki tace

“Amman yanzu Abbah ya kira wayar Aisha yace ta faɗa niki kije ki zo da Namra”

Anty Amarya tayi saurin kallon Hindatu tana share hawayenta.

“Da gaske? Yanzu ya kira ki?”

“Eh Wallahi”

Anty Amarya ta tashi da sauri ta nufi part ɗin Abbah, kamin ta ƙarasa ta hangoshi
jikin mota, yana jiran direbansa ya tashi motar.
Gurin ta ƙarasa ta tsaya masa a gaba.

“Kai kace azo da Namra?”

“Amman sati ɗaya na yarda ta yi”

Haka kawai ya faɗa ba tare daya kalleta ba, ya buɗe motar ya shiga. Sai ga Anty ta
dawo falon da far'ah tana cewa Maryam da Aisha su je su taho da ita.
RASHIDA POV.

Kwanan ta biyu asibiti suka sallame ta bayan anyin mata wankin ciki, sai dai duk
tsawon kwana biyun da tayi Hilal be liƙe inda take ba, duk kuwa da kasancewar a
gurin yake aiki.
Kuma duk tsoron kwanakin be kawo yaransa ba, sai dai ma'aikaitam gurin sun yi ta
zuwa ganinta, sanin cewa ita uwargidan Doc ce.
Ranar data dawo gida ta ci kuka kamar ta mutu, babu irin rarrashin da
ƴan'uwanta ba su mata ba amman sam ta ƙi ji sai da tayi kukanta har ta gaji sannan
ta saurarawa kanta.
Daren ranar da aka sallame ta ne Asmee ta zo gidan, ita tayi ta bata haƙuri tana
ƙara mata ƙarfin guiwa akan inda zata kai ta Hilal ya mayarda ita, sun kitse magana
akan zasu tafi tare gobe idan Rashida zata fita. Sun daɗe suna tattauna lamarin
kasancewar su biyu ne kawai a ɗakin, tun Rashida na kuka har ta daina.

Tun dawowarta gida bata sa komai a cikinta ba, bata komai sai tunanin Hilal da
kuma makomarta, gani take idan har da gaske tana da hiv ya makomar iyayenta zai
kasance tun da dole ne tayi mu'amala da mutane. Wayarta ta janyo ta kira wata
ƙawarta wace ta kasance likita ce. Bugu biyu ta ɗauka, bayan sun gaisa, Rashida
take ce mata

“Dr Fatima, ina son na tambaye ki ne akan hiv, wata sis nace take rubuce-rubuce
shine take tambaya ni kuma na ce bari na tambaye ki tun da ni ba sashena ba ne”

Dariya Dr Fatima tayi ta ce

“Amman gaskiya bayanin yana da ɗan tsowo, why not na yi miki ta whatsapp kina
online yanzu haka”

“Yauwa to haka ma yafi, bari na hau”

“Daman na san ba zaki kira ni haka nan kawai ba”

Rashida tayi dariya bata daɗin rai ba, ta kashe wayar. A take ta kunna datar ta sa
hau online. A contacts list ɗinta ta shiga ta nemi Dr Fatima tayi mata sallama. Sai
da ta ɗauki ƴan mintuna sannan ta amsa sallamar sai ta koro mata da bayani.

“CUTAR KANJAMAU/TSIDA (HIV-AIDS)

HIV (human immune virus) ita kwayar cuta ce da take haifar da AIDS (Acquired
immunodeficiency syndrome) ma`ana karyewar garkuwar jiki wadda aka fi sani da tsida
ko kanjamau. Ita wannan cuta, cuta ce da take karya garkuwar jiki (immune system)
wanda ke bada daman wanda, ke dauke da ita ya kamu da wasu cu tuttuka sakamakon
karyewar garkuwan jiki. rashin kiyayewa ko kula da wannan cuta kan sa mutum ya
halaka a takaitaccen lokaci kamar daga shekara 9 zuwa 11 ya danganta wani yanayi.

HANYOYIN DA AKE KAMUWA DA CUTAR KANJAMAWA/TSIDA

Ana kamuwa da ita wannan cuta ta hanyar shigar kwayan cuta HIV (human
immunodeficiency virus) chikin jini. San nan hanyoyin da kwayar cutar ke shiga jiki
na dewa, kan iya shiga ta hanyar haduwar jinin me dauke da cutar ga mara dauke da
cutar kamar ta hanyar cizon sauro, maniyi, ruwan farji (vaginal fluid) mafi yawan
cin masu dauke da wanan cuta na kamuwane ta hanyar saduwa (sex) da me dauke da
cutar. Ana kuma iya kamuwa ta hanyar yin anfani da allurar da me dauke da ita yayi
mfani dashi. San nan jarirai na iya kamuwa da ita kwayar cutar daga uwa ta hanyar
shayar wa, da lokacin da suke a ciki (pregnancy).

Ita wanan kwayan cuta HIV (human immunodeficiency virus) bata rayuwa da keu a wajen
jiki saboda haka akan iya kamuwa da ita ta hanyar sunbata (kissing) kokuma yin
anfani da wani abu wanda me dauke da cutar ke anfani da shi kamar kofin shan ruwa,
abun yanke farce, ma gogin baka (brush).
Idan yazama cutar ta kai marhala na karshe ma`ana AIDS (acquired immunodeficiency
syndrome) ba`a kamuwa da ita ta hanyar sunbata (kissing), cin abici tare da me
dauke da ita, amfani da kayayyakin ko abubuwa da me dauke da ita ke anfani da su
kamar kayan sawa, wayan salula, agogo, wanka a swimming pool, zama a kujera, cizon
sauro, ma taci (comb), tawul, da kuma tafiya, hada hanu, zama,da yin aiki tare da
me dauke da cutar”

Tun da Dr Fatima ta fara bayaninta Rashida take karanta abunda take aiko mata, sai
da ta kai nan sannan Rashida ta aika mata da wata tambayar.

“Amman Dr ya alamomin cutar yake?”

Ta samu minti biyar zuwa shida kamin tayi ma Rashida reply

“Alamomin ita wan nan cuta ta banbanta daga mutun zuwa mutum. Mutane biyu kan iya
kamuwa a lokaci guda amma ba lallai sun nuna alamomin iri day aba. Anan zamu raba
alamomin kamar kasha uku muyi bayani akai.

 (acute illness)
 (asymptomatic period)
 (advanced infection)

Acute illness

(acute illness) ma`ana alamomin farko na kamuwa da ita wannan cuta. Kashi tamanin
cikin dari 80% dake dauke da cutar na farawa da jin kamar alamomin mura (flu-like)
dake kai tsawon sati biyu zuwa hudu rukunin farko. Abubuwan dake faruwa a wannan
rukuni sune:

 Kuraje kana na a jiki (body rash)


 Zazzabi (fever)
 Boshewar makokoro (sore throat)
 Jin gajiya (fatique)
 Kumburi a (lymph nodes)
 Fashewar baki da alaura (mouth and genital ulcers)
 Chiwon nama (muscles pain)
 Ciwon gabobi (join pain)
 Amai da hamami (nausea and vomiting)
 Zufa cikin dare (night sweat)

Wa yan nan alamomin na faruwa mutum ya gaggauta zuwa kuji don gane yana dauke da
ita bai dauke da ita.

Asymptomatic period

(asymptomatic period) ma`ana lokachin bacewar alamomi. A wannan lokaci cutar bata
nuna ko wace alama na rashin lafiya ko ciwo na wasu watanni ko shekara. Amma akwai
kwayar cutar a jikin mutum. A wannan lokacin kwayar cutar na dada yaduwa
(replicating) da kuma kashe garkuwar jiki (immune system). Sannan a wann lokaci
kwayar cutar tafi karfi da kuma yadu ta hayoyin da mukayi bayani a yadda ake kamuwa
da cutar.

Advanced infection

(Advanced infection) a wannan lokachi kwayar cutar ta riga tayi damejin garkuwar
jiki (immune system) yana daukan lokachi amma idan ya kai wannan lokachi to cutar
ta kan zama AIDS (acquired immunodeficiency syndrome) mutum kan kamu da wasu
cututtuka sakamakon damejin garkuwar jiki (immune system damage) zaizama garkuwar
jiki bai iya yaki da kwayar cuta. Alamomin wannan bangare sune:

 Hamami
 Amai
 Gudawa
 Ma tsanachin gajiya
 Raguwar nauyi /rama
 Tari da numfashi sama sama
 Zazzabi me tsanani akai akai (recurring fever)
 Kwararraji masu ruwa a baki ko hanchi ko a fata da kuma alaura,
 bushewar makokoro
 kunburin lymph node na gabobi mara warkewa.
 Kidimewa, tabuwar kwakwalwa daga nan kuma watakil sai mutuwa”

Hankalin Rashida ya tashi sosai wasu daga cikin abubuwan da Likitar ta faɗa duk
tana jinsu, amman tayi tunanin ko cikine a lokacin. Ji take kamar ace ba da gaske
bane

“Amman Dr Bayan wannan babu wata alama da mutum zai iya gano tabbacin yana ɗauke da
cutar?”

Ko da ta tura mata saƙon ta riga ta sauka online, a lokacin 10:23pm ne. Kasa
natsuwa tayi har sai da ta lalobu number Dr Fatima ta sake kiranta.

“Dr kina min bayan sai kika sauka”

“Eh Wallahi mai gida ne ya shigo”

“Dan Allah ki taimaka ki ƙarasa min, gobe zata rubuta abun yanzu haka duk ta dame
ni”

“Okay bari ya gama cin abinci zan hau online”

Daga haka ta kashe wayar tana tunanin nata mijin. Whatsapp ta shiga tana duba last
seen ɗinsa, ta ga biyar da kwata na yamman nan. Dp shi take kallo wani hoto ne ya
ɗora yana sanye da kayan likitoci yana murmushi. Fashewa tayi da kuka ta rumgume
wayar a ƙirjinta.
Sai da tayi kukanta ta gaji sannan ta ɗago wayar ta sake kallon hotonsa tayi
masa kiss sannan ta shiga chat ɗin su da Dr Fatima, ashe ma tuni ta turo mata da
bayanin bata gani ba.

“Ana gano mutum na dauke da wannan cutar ta tsida ta hayar gwajin jini, (serum),
miyau, ko fitsari ta hanyar sanya musu wasu sinadarai dake sanya a gano kwayar
cutar aciki wato HIV (human immunodeficiency virus) wadda ita take haddasa AIDS
(acquired immunodeficiency syndrome) wanda mukayi bayani a sama. Anfi gano mutum na
dauke da cutar ta hanyar gwajin jini”

Ta haɗeye yawu ya fi sau biyar sannan ta sake aika mata da wata tambaya, wace ita
ce dalilin tambayarta tun farko.

“Dr ya mutum zai kare kansa ko kuma wani nasa daga kamuwa da wannan cutar?”

 “Yin gwaji don sanin akwi ko babu.


 Rage yawan saduwa.
 Anfani da roba (condom) wajen saduwa.
 Kiyaye saduwa da mata/maza daban daban.
 Gwaji da kuma maganche cututtukan saduwa STDs (sexual transmitted disease).
 Kiyaye yin amfani da allurar da wani yayi anfani da ita.
 Tabayar likita dangane shan PrEP (pre-exposure prophylaxis) shima wani hanya ne
na kiyaye kamuwa da ita wannan cutar

Rashin kiyaye ita wanan cuta kan sa mutum ya halaka da wuri. Ana kiyaye cutar ta
hanyar yin anfani da (antiretroviral drugs) magunguna ne da ake afani dasu wajen
magance cututtukan virus, kusan ita wanna cuta bata da maganin warkewa sai kiyaye
ta, ta hanyar anfani da magunguna da likitan ya dorashi mutum akai”

“Na gode sosai likita Allah ya saka da alheri”

“Ba a son mai cutar yana kusantar hayaƙi, ko cizon sauro ko wani abu makamancin
wannan, saboda abu kaɗan yana iya ƙara cutar, an fi mai cutar ya ci abubuwan gina
jiki like vegetables”

“Thank you”

Rashida ta rubuta daga ƙarshe, sannan ta kashe wayarta tana hawaye.

“Dole ne naje nayi gwaji dan na tabbatar, wata ƙila ma na ɗauke da cutar, ai za a
iya min sheri tun da ba a son zamana da Hilal”

Ta faɗa a fili tana share hawayenta. Sai kuma zancen da Asmee ta faɗa mata ya dawo
mata na zargin kanta da take tana ɗauke da cutar, ita kuma ta san tana mu'amala da
mijin Asmee. Jefar da fillon dake saman gadon tayi ta wani irin matsa gashin kanta.
Haka ta kwana har safe tana kuka idonta ya kumbura sosai kamar an zuba mata wani
abu a ciki, bata fita ɗakinta ba, abincin da Momy ta kawo mata bata ci ba, sai
kawai ta shiga banɗaki tayi wanka ta saka abaya, ta fito falo, ba dan tana jin
ƙarfin jiki ba, sai dan tafitar ta zame mata kamar dole ne.

Momy na ganinta ta cika da mamakin ganin ta fito da shirin fita.

“Ina zaki je?”

“Ina son na ɗan fita ne, zan je office na ɗauki hutu sai na je gidan Asmee”

“Haba Rashida yanzu cikin wannan yanayin zaki fita sai kace wanda bata son kanta?”

Idonta ya cika da ƙwallah

“Momy ina son fitar ne ko zan samu gwarin jiki, kuma na sha iska, ko damuwa zai
rage min”

“Kuma Sisters naki duk sun tafi school balle su raka ki, zaki iya driving ma”

“Zan iya”

“Shiga ɗaki ki ɗauka keys ɗina”

Momy ta faɗa cike da tausayawa. Ɗakin Momy ta shiga ta ɗauki makullin motarta, dan
ita yanzu komai nata yana can gidan Hilal babu abunda aka ɗauko.
Cikin ƙarfin hali take driving ɗin, kamin ta ƙarasa office ɗin ta tsaya gefen
titi tayi parking, ta kira number Malamin nan. Bayan sun gaisa ta koro masa da
bayaninta.

“Malam aiki nake son ka min akan kishiryata”

“Me kike son a mata a kashe ta ko a haukatata?”


“Bana son a mata ko ɗaya, wani daban nake son ka mata wanda mijina zai gaji da ita
ya rabu da ita sai ka min wanda zai dawo gare ni, a halin yanzu mijina ya rabu da
ni”

“Me kika masa? Ina labarin waɗancan mutanen dana haɗa ku da su?”

“Ba mu yi aikin ba, saboda auren ya riga ya mutu, kuma wallahi ina son miji zan iya
mutuwa idan babu shi a kusa da ni”

Ta faɗa cikin wani irin kuka, kamar ance mata malamin yana gabanta ne.

“Ya isa daina kuka, ai wannan mai sauƙi ne, akwai aikin da zamu masa ya dawo gunki
da gudu ma, ita kuma za mu sakar mata jini sannan mu saka mata warin jaɓa idan ya
gaji da ita zai sake ta, amman zaki kashi kuɗi”

“Kuɗi ba matsala bane zan baka ko nawa kake so, amman ina son a buga min ƙasa a
bincika min komai nawa”

“Zan miki haka, duk abunda ƙasa ta faɗi zan faɗa miki idan kin zo, amman idan kin
shirya aikin ki zo da tulo da zanen haila wanda ita kishiyarki take amfani da shi”

“Malam ya za'ayi na same shi yanzu, bayan bana gida kuma ai kasan yanzu ba'a amfani
da irin wannan abun yanzu duk pad ne ake sawa”

“Pad ɗin shima ai zai yi, ki bincika a bolar gidan, idan kuma ba zaki iya ba, kisa
zo ki biya kuɗi mu zamu sa aljani ya ɗauko mana”

“Zan zo nan da kwana biyu, na gode”

Daga haka ta kashe wayar ta ɗora kanta saman sitarin motar, kamin ta ɗago ta cigaba
da tuƙin.
Wata pravate hospital ta nufa dan yi gwajin jinin so that ta tabbatar da zarginta.

AMIRA POV.

Har suka sauka garin Abuja bata wani farinciki musamman data ga hoton wanda ake son
su kashe ɗin, sai duk jikinta ta mutu, ta tabbatar mutumen ƙwarai ne dan in ba haka
ba babu abunda zaisa wasu su nemi a kasheshi.
Mutumen data taɓa gani a tv she can't recall his name, amman dai tasan shine
wanda aka taɓa tattauna da ashi akan tsaro har ta ji ya kwanta mata a rai.

“Guy please karku taɓa mutumen nan”

Hancinsa yasa yana gogawa a kumatunta.

“Ina son ki sosai Amira, amman akan aikina zan iya ɓatawa da ke, so ki daina sa
baki a kan aikina”

Ya ciro wayarsa dake aljihu ya kara akunne

“Hello ....Okay”

Ya kashe wayar yana kallonta

“Wai ya fita, zo muje”

“Tun yanzu za ku kashe shi?”


“A'a zamu fara farautarsa ne, yana Sahaba Restaurant, akwai yara dana aje Sahaba
Hotel, kisa da inda yake, nima kuma can zanje amman sai gobe”

Ajiyar zuciya ta sauke ta janye hannunta daga riƙon da yayi mata.

“Ba zan je ba ku tafi kawai”

Duƙawo yayi ya mata kiss, sannan ya fice.


Ji take bata da natsuwa idan bata faɗawa masa abunda yake faruwa ba, sai dai kuma
taya zata faɗa masa bayan shi ɗin babban mutum ne ganinsa ba hakan ake yi ba. Kuma
idan har ta aikata ta jefa rayuwarta cikin matsala.
Sai da ta ji tashin motarsu sannan ta tashi ta shiga binciken gidan, har ta samo
paper da pen tayi rubutu akai sai ta sanya doguwar riga dan jikinta inner ne kawai
ta fito harabar gidan tana dubi-dubi.
Har tayi tunanin ta hau Napep sai kuma ta tuna Abuja ba ko ina ake farin Napep na
shiga ba, sai kawai ta koma ciki ta tashi ɗaya daga cikin yaransa ta ce ya kai ta,
yaso ya musa mata amman sanin halinta da kuma yadda Guy ke ji da ita yasa dole yaja
mota ta shiga suka kama hanya.

Suna isa Sahaba Restaurant, sai ta hango Sahaba Hotel kamar yadda Guy ya faɗa mata.
Nesa da gurin tasa ya aje ta tace ya tafi ya barta zata je gurin Guy, ba musu yaja
motar ya koma. Sai da ta daina hangosa sannan ta nufi Sahaba Restaurant zuciyarta
cike da tsoro gabanta kuma kar ma zai zube ƙasa.

Guy na daga gefe ya hango Amira ta doshi Restaurant ɗin sai waje-waje take.

“What the fuck, me Amira za tayi can ? Ko ta ɗauka ina can ne?”

Ya tambaya yana kallon yaransa da suke tare da shi cikin motar, wanda ko wannensu
ba shi da amsar ba shi. Da sauri ya buɗe motar ya tara hannayensa a baki yana mata
fiito (shewa) irin na tsuntsaye. Amira na jin kira ta san Guy son ne, maimakon ya
ga ta dawo sai kawai ta ranta cikin na kare.

ABDOOL POV.

Ganin kurciyar ta firanye sai kawai yayi musu alama da hannu akan su koma kawai.
Shi kuma ya koma cikin gidan, ya kunna tv yana kallon news, lokaci zuwa lokaci yake
jan tsaki saboda lamarin nijeria kullum abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, yau wannan kakeji
gobe wani kala ne. Idan ma kace zaka maida hankali akan abun sai tunani yayi maka
yawa.

Wuni yayi a cikin sallah ce kawai take fitar da shi gidan, sai da dare ya sauya
kayan jikinsa ya fita siyen abinci dan be yarda a dafa masa a abinci duk kuwa da
kasancewar akwai masu masa dafa masa, amman baya ci sai dai sauran ƴan gida su ci.
Ko a gurin siyen abincin ba guri ɗaya yake tsayawa ba, saboda tsaro.
Bayan ya karɓi takeaway ɗin ya biya sai ya juyo ya nufi ƙofar fita. Yana fitowa
ya hango budurwa tana gudu iya ƙarfinta ta doso inda yake, kallon mamaki yake mata
yana son tantance abunda take ma gudun.
Sauran taku kaɗan ta ƙaraso inda yake, sai ƙarar bindiga ya tashi, cikin wani irin
zafin nama ya riƙota dan ya gane ita aka harba, sai dai haka be hana bindigar
samunta, sai ta sulale a hannunsa tana banƙarar bayanta saboda zafi da kuma dafin
albarushin da taji ya soke ta abaya.

Daga shi har ita tare suka kai ƙasa, cikin hanzari ya ciro wayarsa ya kira yaransa.
Sannan ya kira head quarters.
*🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺*

*© Khadeeja Candy*

Don't read if you didn't pay...!

*PAGE - 44*

NOT EDITED ⚠

_An kaiwa Major General Abdullah Ahmad Mai-doki hari_

_An yi nasarar kashe waɗanda suka kaiwa Major hari_

_Yarima Abdullahi Ahmad Mai-doki Ɗan sarkin Katsina ya tsallake rijiya da baya_

_Wata yarinya ta sadaukar da ranta saboda ɗan Sarki_

Shine abunda kowa wace jaridar Nigera ta online ta yi ado dashi a fuskarta
shafinta, har ma da na ƙasashen waje, bayan mintuna 25 da faruwar lamarin.
Online rumors updated kuma kowa da abunda yake rubutawa, har da masu cewa har shi
an harba da masu cewa ma ya mutu, da masu cewa yaje siyen abinci da karuwarsa, wasu
kuma matarsa ko dai da irin yadda tayi masa daɗi yake ƙaƙarowa ya rubuta a social
media.

Dandazo ƴan jarida suka yi a bakin asibitin da aka kai Amira, dan jin kanun
labarai, ko wannen baya son a bashi labari.

Sai dai sojojin da ke zagaye da asibitin basu ba su damar shiga ciki ba, balle har
su ɗauki rahoto ko kuma video abunda yake kan faruwa ba.

A bakin kofa Abdallah ya tsaya yana kai da kawo har sai aka fito da ita ɗakin
tiyata, bayan an cire mata albarushin.

“Doc is she live?”

Shine abinda Abdallah ya fara tambaya ganin an fito da ita daga ɗakin galalla kamar
wanda bata numfashi, a kife take saman gadon asibitin dan a bayanta ne suka mata
aikin cirar albarushin.

“She survived, but she's unconscious now and she will take 28 -32 hours before she
wake up”

Likitan na faɗar haka ya suka wuce da ita wani ɗakin, tare da wasu Nurses. Da kallo
Abdool ya bita sai da duka shige da ita ɗakin sannan ya sauke ajiyar zuciya ya
shafa kansa. Sannan ya zauna a kujerar dake gurin ya lumshe ido yana sauraren
wayarsa da ke ringing.

Kira ne kan kira yake shigowa, tun wayar tana ringing da vibration ita kaɗai har
cinyarsa ta gara amsawa, saboda yawan kira. Shi dai yasan ba zai iya ɗaukar kira
kowa a yanzu ba, dan yasan ba zai wuce masu son jin lafiyarsa ba, abu ɗaya yaji zai
iya, magana da ƴan jarida dan tabbatar musu da lafiyarsa. Hakan yasa ya miƙe tsaye
ya ciro wayar ya miƙa PA ɗinsa dake tsaye kusa da shi.

Wani ɓangare na asibitin ya nufa, inda sauran sojojin suke. Yayi magana da su akan
a canja ma Amira asibiti zuwa asibitin sojoji da ke Abuja. Cikin sirri suka kawo
wata mota ya shiga yaje gida ya tsimtsa ya canja tufafin jikinsa dan duk sun ɓace
da jini.
Army uniform ya saka ya shiga wata motar ya koma asibitin. Ko da ya isa har an
canjawa Amira asibiti zuwa asibitin daya buƙata, wajen asibitin ya fito yayi
magana da ƴan jarida ya tabbatar musu da abunda ya faru, sannan ya juya ya koma
cikin asibiti shima aka soma duba lafiyarsa duk da sun san albarushin be same shi
ba.

“Sir Hajiya ta matsa sai ta yi magana da kai, Mai Martaba ma ya kira tun ɗazu kusan
sau biyar”

Ya faɗa bayan ya tsare masa ya maƙe guri ɗaya kamar irin ya sha jinin jikinsa ɗin
nan.
Sai da aka cire masa abun awan jini sannan ya karɓi wayar. Number Mai maitaba ce
wannan karon hakan yasa shi murmushi.

“My Royal Highness”

“Babana kana lafiya?”

“Ina nan ƙalau Mai martaba”

“Babana karka ɓoye min komai”

“Wallahi Babu abunda ya same ni, sai dai yarinya ita sun same ta”

“Ga mu nan gida duk sun rikice sai koke-koke suke, Ummin ka ma ta kirani wai nayi
waya da kai? Ta kira ba kai ka ɗauka ba, tana jin dai ko sun same ka bata san halin
da kake ciki ba”

“i'm fyn Mai martaba, yanzu nan ma nayi magana da ƴan jarida, da kun kalli news za
ku gani ai”

“Wai ya abun ya faru? Kuma su wanene?”

“Wallahi ban san su ba, amman dukan an kashe su, ni ina fito daga restaurant ne
kawai sai naga yarinya tana gudu ta doso inda nake, shine sai kawai naga wani ya
fito a wata mota dake can nesa da mu, amman haka be hana bingdigar samunta da yake
Allah ya rubuto, sai duk muka faɗi, sai na kira boys ɗin mu dake nan gida na faɗa
musu sannan na kira head quarter na faɗa musu, kamin su bar gurin sai da suka harbi
mutum biyu, kuma duk sun mutu. Sai dai dikansu basu tsira ba sai akayi musu ƙofar
rago suna ganin haka sai suka fara buɗawa boys ɗin mu wuta, suma sai suka buɗa
musu. Anyi nasara akan su dan an kashe su duka, sai dai suma sun kashe mana
soldiers biyu”

“Subhanallah Allah ya tsare gaba, amman ita yarinya ba tare take da su ba?”

“Bana jin haka da ba zasu harbe ta ba, kuma ta zo da wata takardar hannunta an
rubuta, wai nayi taka tsan-tsan akwai masu son kashe ni suna bibiyar sawuna, ba
zasu min komai a garin Abuja ba har sai na isa katsina saboda sasu akayi”

“Amman ya akayi ita yarinyar ta san da wannan? Anya ba haɗin kai ba ne?”

“Tunanin hakan yasa aka bincika bullet ɗin dan a tabbatar na ƙwarai ne ko roba, an
bincika bullet ɗin na ƙwarai ne irin wannan ne da ake shigo da shi ta waje, ta
ɓarauniyar hanya, yanzu dai duk wasu tambayoyi sai idan ta farka zamu mata”

“Allah ya tsare gaba, a riƙa taka tsantsan Babana kana wasa da rayuwarka fa”

“Kar hakan ya dame ka Mai martaba, ɗan Adam baya wuce ƙaddararsa, kuma abunda Allah
ya kawo babu mahani”

“Haka ne, amman gobe zaka dawo ko?”

Yayi dariya yana mai miƙewa tsaye ya nufi window gurin.

“Gobe kuma? Ai bamu gama meeting ba, akwai wanda za muyi gobe da jibi kamin na
dawo”

“Kai ni wannan aiki naka Babana yana tsorata ni”

“To ya muka iya? Dole ne mu saiyardar rayuwarmu dan wasu su rayu”

“Toh Allah ya kyauta. Ga Mamanka zaku gaisa”

Haka Abdool ya bisu ɗaya bayan ɗaya yana gaisawa da matan uban masa da ƙannensa da
ƴan'uwansa da suke gidan.
Yana katse kiran Mai martaba ya kira Ummi, ringing ɗaya ta ɗauka tana kuka.

“Son...”

“Ummi I'm fine Wallahi babu abunda ya same ni”

“Ban yarda da kai ba, ai ba zaka faɗa min gaskiya ba, naso na biyo mota saboda babu
jirgi yanzu amman gobe da safe zan zo”

“Ummi you don't have to, Wallahi babu abunda ya same ni, yarinyar data tare min
bullet ɗin ita aka samu, kuma an yi nasarar kashe su duka”

“I don't trust you”

“If you don't trust me, you should trust yourself, believe yourself remember how
you treated your Son he will never ever lied to you”

“You started it”

“No I'm just show it”

“Whatever ni dai gobe zan zo”

“To Allah ya kai mu”

“Amin. Ga sisters naka za ku gaisa sun ta kiran wayarka sai wani ya ɗauka”

Ɗaya bayan ɗaya ya gaisa da su sannan Ummi ta karɓa.

“Ka kira Mai Martaba ɗazu na kira shi yace shi ma hankalinsa a tashe yake be same
ka ba”

“Yanzu muka gama waya da shi”

“Okay, Son su waye ne suka maka haka?”

“Nima ban san su ba maƙiya ne kawai”

“Amman ita yarinya ta rayu? Ka santa ne? Ina ka haɗu da ita”

“Na fito ne kawai sai na ganta tana gudu ta doso inda na ke, shine suka buɗe mata
wuta, tana da rai amman tana buƙatar addu'ah dan tana cikin mawuyacin hali”
“Allah ya tashi kafaɗunta, ko dan na mata godiya for what she did to our family”

“Ni kaina ina son ta tashi dan akwai tambayoyin da na ke son ta amsa min”

“Allah ya bata lafiya gobe zan zo”

“Ummi”

“Don't!”

Ya riƙe bakinsa kamar tana gabansa.

“To Allah kawo ki lafiya”

Daga haka ya kashe wayar ya juya ya fice daga ɗakin. Ba shi ya bar asibitin ba sai
da ya karɓa waya ta fi a ƙirga ɗuk masu tambayar lafiyarsa ne ƴan'uwa da kuma
abokan arziki.

NAMRA POV.

Tun da Yasmin ta bar gidan bata fito ko bakin ƙofa ba, balle har ta fito falo,
Gwaggo Kulu bata takurata ba, dan tasan halin Namra daman can ba mai son surutu
bace balle yanzu data fuskanci kamar tana cikin damuwa.

Duk wainar da ake toyawa a falon Namra bata sani ba, dan hankalinta ma kwata-kwata
baya jikinta yana can wata duniyar tana tunanin lamarin rayuwa, yadda ta sauya mata
a lokaci ɗaya. Turo ƙofar da Hindatu tayi ne yasa ta dawo hayyacinta har ta ɗan
tsorota.

“Anty Namra”

Ta rumgune ta zumuɗi ita da Aisha. Ƴar far'ah tayi irin far'ar nan data zame maka
dole tun da tasan ba zuwan daɗi ne ta yi ba.
Sai daga baya Maryam ta shigo dan tun shigowarta tana can gurin Gwaggo tanan mata
faɗa akan rashin son zumunci, wai rabonta da gidan har ta manta.

A bakin ƙofa ta tsaya tana murmushi.

“Ta so muje ƴar Anty Abbah yace mu zo muje da ke”

“Da gaske?”

Namra ta tambaya tana zaro ido, irin mamakin ɗin nan da rashin yarda da zancen
Maryam. Sai Aisha ta karɓa mata.

“Wallahi kuwa, da gaske shine ma ya kira ki a waya yace muje mu ɗauko ki”

“Ko dai wani abun ai min?”

Ta faɗa da muryar tausayi tana kallonsu, dan bata gamsu Abbah zai ce aje a zo da
ita hakan nan kawai ba.

“Babu abunda zai miki baya ma gidan yanzu na fita, Anty ce ta buɗe masa wuta
shiyasa ya yarda”

Shiru ta ɗan yi tana tunani, kamin ta miƙe tsaye ta ɗauki jakarta ta rayata, ta
kalli Maryam.

“Dan Allah Abbah ne yace na zo?”

Maryam ta dafe kanta.

“Kai ni Allah na, Namra nawa zaki biya ni ne da zan miki ƙarya”

“Ina jin tsoro ne”

“Daman ai kullum cikin tsoro kike”

Ta juya ta fice tana mai jin haushin lamarin Namra. Cikin rashin kuzari ta fito
ɗakin tana riƙe da hannun Aisha ta zo ta risina gaban Gwaggo dake zaune falon tana
mata sallama kamar wanda bata son zuwa.
Gwaggo na kallon idonta ta kalli Maryam tace

“Duk aka haɗa baki da ke aka yi ma Namra wani abu ko? Heeeee Wallahi sai kin raina
kan ki”

Maryam ta ɗora hannu saman kai tana dariya

“Oh Ni na shiga uku, wai fuskata tayi kama da mugaye ne hala?”

“Na dai san halin ki, shegen karanbani da iyayi, kuma na faɗa miki, wallahi ran ki
sai ya fi na kowa ɓaci duk aka haɗa baki da ke”

Da dariya ta fita falon. Har gurin Mota Gwaggo ta raka su, tana yi Maryam jan kunne
ta daina tuƙin dare kuma ta kula da hanya ban da gudu.

Har suka isa gida gaban Namra be daina dakan uku-uku ba, saboda tsoro da tunanin
abunda Abbah zai mata. Lokacin da Namra ta fito motar sai ta ɗaga kanta sama ta
kalli gid, idonta ya cika da hawaye, tuna rayuwar da tayi a ciki, da hawaye shaɓe-
shaɓe Hindatu taja hannunta suka shiga falo.
Tsaye suka same Anty Amarya tana tsumayinsu, duk wani kunya da take na Namra yau
cireshi tayi sai ta zo da sauri gurin ƙofa ta rumgume ƴarta idonta cike da hawaye,
haƙiƙa tayi farincikin ganin Namra, sai dai kuma bata jidaɗin ganin yadda ta lalace
ba, kamar wance ta shekara tana ciwo.

Maryam ne da Aisha suka ɗauko mata abinci da sha suka jera saman center table.
Namra ta kallesu da murmushi.

“Thank you Sisters amman ni ba na cin komai”

“Saboda me? ”

Anty Amarya ta tambaya.

“Namra kamar akwai abunda yake damun ki?”

Shiru ta ɗan yi tana nazarin abunda zata cewa Anty Amarya, dan bata jin zata iya
faɗa mata abunda Asim.yayi mata, ta san ba zai mata daɗi ba kuma ba zata ƙyale ba,
bayan kuma koma minene itace ta jawa kanta.

“Babu abunda yake damuna, na riga na ci abinci gidan Gwaggo ne, har wanka ma nayi
ina shirin bachi suka zo”

“Amman duk da haka Namra kina da damuwa be kamata ki ɓoye min ba, dan nasan wannan
zuwan bana banza bane, babu yadda za ayi ki tsallake Asim ki zo nan bayan kin san
yana gadon asibiti kwance”

“A...an sallame shi ai, yana gida Mamanshi take jinyarsa shine yace na zo saboda na
sha kai da maganar gida ne, nima kwana biyu zan yi na koma”

Anty tayi murmushi, dan tasan ba gaskiya Namra ta faɗa mata ba.
Hajiya Barau ce ta shigo da Sallama tana faɗin maraba da baƙi.

“Yau garin mu? Ina ji maƙi baƙi”

Anty Amarya tayi dariya ta tashi ta shige ɗakinta. A ɗayan kujerar da Namra take
zaune Hajiya Barau ta zauna tana satar kallonta, sai fira suke sama-sama tana
tambayar labarin Katsina. Sai nanata mata rashin jindaɗin zuwa ganin Asim da Abbah
be barta taje ba.
Sai da dare ya raba sannan tayi mata sallama ta tashi ta fice, zuciyarta cike da
gulma.

Bayan fitarta Hajiya Barau, Aisha take labartama Namra wanda zai auri Maryam da
Hindatu duk sun zo sun gaida Abbah, kuma sun turo iyayensu, dan tsayar da magana.
Namra ta kallesu tana dariya.

“Eyyyye Amare”

Hindatu ce ta ji kunya har ta rufe ido, Maryam kan dariya ta riƙayi sai ta tashi ta
bar falon kasancewar tana waya da angon ne.

“Saura ke”

Namra ta faɗa tana wasa da hannun Aisha, sai Aisha tayi mata wani kallo.

“Ni Anty no da na ss2”

“Ƴar jss ma anyi ma aure balle ss”

Dariya Aisha tayi ta rufe fuskarta. Dammm gaban Namra ya yanke ya faɗi, jin ƙarar
tsayawar Mota, zuciyarta na nasalta mata Abbah ne ya dawo, ji take idan ya shigo
rufeta zai yi da ruwan masifa. Da sauri ta tashi ta nufi ɗakin Anty Amarya gabanta
na ci gaba da faɗuwa.

Tsaye ta tararda Anty Amarya tana gyara tufafin da suke wardrobe ɗinta, kallo ɗaya
tayi ma Namra ta ɗauke kai tana murmushi, kamar ta san abunda Namra ta jo ma gudu.

“Ai shine yace aje a zo da ke”

“Amman be ce komai ba?”

“Be ce ba, dan shi kansa yana san kina cikin matsala akwai abunda yake damun ki”

“Babu abunda yake damuna Anty”

Anty ta bar tufafin ta zo ta zauna kusa da Namra

“Farinciki da baƙin ciki abubuwa ne da basa iya ɓoye kan su Namra, jikin ki ma ya
nuna haka, dubi kiga yadda kika lalace kika rame kamar ba ke ba, Namra karki ɓoye
min damuwarki, ni Mahaifiyar ki ce babu wanda ya dace ya ji matsalar ki sai ni”

“Anty babu abunda yake damu na, kawai na zo na gan ku ne”

“Namra dubi kam ki? Kin ga yadda kika lalace?”


“Ba ni da lafiya ne”

“Me ke damun ki?”

“A nan ƙasan marana iya jin ciwo ne, sai kuma ciwon kai da nake fama da shi, ga
zafin jiki”

Duk abubuwan data faɗa gaskiya ne tana jin su sai dai bata jin wata matsala ne ko
kuma ciwo, yanzu kuma tayi ma Anty ƙarya ne dan ta ƙyale ta.

“To gobe za muje asibiti likita ya duba ki”

“Allah ya kai mu”

“Amin”

Ta faɗa tana janye blanket ɗin dake saman gadonta.

“Ki kwanta a nan ni part ɗin Abbah ku zan kwana, idan kuma ba zaki iya kwana nan ba
ki koma ɗakin Maryam”

“A'a nan zan kwana”

Ta faɗa tana kwantawa saman gadon.


Sai da Anty ta gama gyara komai na ɗakin sannan ta ɗauki wasu abubuwa ta yi ma
Namra sai da safe ta fice.

ASIM POV.

Bayan ya gama shan koko Mama ta kalleshi tace

“Yau fa kwana biyu yarinyar nan bata leƙo asibitin nan ba”

“Ai ba zata zo ba”

Ya faɗa yana goge bakinshi

“Saboda me?”

“Faɗa muka yi da ita har ma mareta kuma na faɗa mata maganganu”

“Miya haɗa ku”

“Wani na gani ya rako ta, shine wai nayi magana tace ina zarginta, har da wani wai
ta ji maganar da muke ɓoyewa na kuɗin a dashe”

Mama ta riƙe baki.

“Mai kaza aljihu baya jimirin ass, daga magana sai kuma tace ana zarginta? Daman
tasan abunda take kenan, ni kai na wallahi naga yarinyar da wani amman ban faɗa ba
saboda kar na ɓata muku zama, daman ai na faɗa maka ba da zuciya ɗaya take zaune da
kai ba”

“Ai yanzu na gane halinta, dan yi mata magana shine har ta min jawabi wai ba na da
komai ta aure na lalata mata rayuwa na rabata da karatun ta”
“Amman Ibrahim ka yi wauta, ai kamata yayi ka sa mata ido ka ga iya gudun ruwanta,
kuma yanzu idan ma gidan su ta tafi ai sai tace ka ci amanarta kuma ka zarge ka
koreta, kuma kai yanzu ko sallamarka akayi ba itace zata yi hidima da kai ba? Ni fa
gida zan koma tun da can ma akwai yara ga sana'a na baro kasan idan ba dole ba babu
abunda zai zaunar da nan, tunanin hakan tasa Wallahi ban faɗa maka ba.

Yanzu zuwa kaiwai zata yi ta ɓata maka suna, sannan idan ka rabu da ita a yanzu
kana da halin auren wata ne? Ai dole kayi haƙuri da ita har Allah ya nuna maka kaji
sauƙi sosai ka warke kayi kuɗi, ka auro wata sannan idan ita rabuwa zaka yi da ita
sai ka yi, daman sun saba yaba maka rashin mutunci, kawai ka bata haƙuri kace kayi
nadama, ai Allah ma ba zai barta ba ace da aurenka kana zina haba abun ai yayi
muni, daman can ba ƴar tarbiya bace shiyasa ta bi mutumen aka riƙa cewa kai ne ka
ɗauke ta, har ɗan'uwanta ya fasa aurenta kai aka ƙaƙaba maka ƙaya”

Ajiyar zuciya ya sauke wani irin ɓacin rai me ke ziyartarsa.

“Amman Wallahi Yarinyar nan ta ci amanata sosai”

“Haƙuri dai za kayi, ai babu yadda ban yi ba akan karka aureta amman ka tsaya kai
da fata sai ka aureta”

“Nayi tunanin aurenta zai zame min alheri ne shiyasa na yi”

“Ka kirata dai yanzu kace ta dawo, kar taje ta shafa maka kashin kaji gurin
matsiyacin uban nan nata mai dukiyar likudi (Kuɗin da ba'a iya ci)”

“Bana jin tana garin nan fa”

“Shiyasa na ce ai ka kirata ba kana da number uwarta ba? Sai ka kirata ka bata


haƙuri tun dai lafiya ta samu an kusa sallamar ka, idan ka kira karka nuna musu
wani abun ne ya haɗa ku, idan sun ce tace kayi mata wani abu kace kai ƙarya take
maka, sai idan ta gaji da auren ka ne, karka yarda ka nuna wani abun ne ya haɗa ku”

Kwantawa yayi saman gadon zuciyarsa cike da baƙinciki abunda Namra ta masa, har
yana jin kamar ba zai iya kiranta ba, dan ta ci zalinsa da yawa.

“Baka da wata mafita sai wannan, idan kuma kana ganin akwai wata hanya mai fiddaka
sai ka yi”

Ta faɗa tana ɗaukar ledar ƙosai da robar koko ta fice.

RASHIDA POV

Mataki uku ake bi gurin gwajin jinin dan a tabbatar da mutum yana ɗauke da cutar,
idan an yi na farko ba a tsallake ba sai ayi na biyu idan shima ba a tsallake ba
sai ayi na uku.
Duka an yi ma Rashida kuma results ɗaya ya bada cewar tana ɗauke da cutar, tun a
cikin asibitin ta fara kuka, har ta iso gurin motarta. Nadamar taraiya da Alh.
Bashir take taraiyarta da shi be haifa mata ɗa mai ido ba, be sata komai ba sai
baƙinnciki da da na sani.

Tunanin yadda zata faɗawa Momy take, mutuƙar da faɗa mata gaskiya ta san ita ma
gudunta za ta yi, mu'alamarta da kowa zai sauya za a fara mata wani kallo har a
gurin aikinta ta san sallamarta za'ayi, duniya zata juya mata baya kowa ya
tsangwame ta musamman idan aka ji silar rabuwarta da mijinta, babu kuma wanda zai
sake aurenta.
Dan haka ta zaɓi zama da su a haka dan ta rufawa kanta asiri. A cikin mota ta ci
kukanta ta gaji sannan ta koma gida, a lokacin yamma yayi sosai duka ƙanenta suna
gida. Sai dai bata yarda sun ga fuskarta ba har ta shige ɗaki.

Ta sake ɗasa wani sabon kuka tana jin kamar ta sha wani abu ta mutu.
Sai dai wani ɓangare na zuciyarta na faɗa mata, tana da buƙatar rayuwa saboda Hilal
da ƴaƴanta, idan har ta kori Kalsoom daga gidan to Hilal zai iya zama mallakinta
har a bada.

A kwana biyu da tace zata yi kamin ta je gurin malamin sai ta kasa, saboda mugun
ƙudirinta dan bata son ta samu wata ɗaya a gida bata koma ɗakin mijinta ba.
Hakan yasa washe gari tun da safe ya shirya ba tare da sanin kowa ba ta fita.
Napep ta tara ta shiga aka kaita tasha, sai ta ɗauki shatar mota har zuwa garin da
Malam yake.

Yau kan bata tsaya bin layi ba, dan tun a hanya ta kira shi ta faɗa masa gata nan
zuwa, hakan yasa tana zuwa sai kawai aka mata iso cikin faɗar tasa da yake tsiface-
tsifacensa.
Kamin tayi sallama wayarta tayi ringing ko da ta duba sai ta ga Hajiya Basira,
wani dogon tsaki taja dan yanzu haushi Alh. Bashir take ji matuƙa.

Guri ta samu ta zauna, ta soma roko masa bayani shi kuma sai kallonta yake yana
wasar haƙuransa dake cike da goro.

“Ai na faɗa miki wannan duk mai sauƙi ne, idan ma ba zaki iya ba yanzu nan zamu
saka iska su ɗauko mana”

“Amman ya za'ayi su iya ɗaukowa Malam?”

“Ai ko wane ɗan 'adam yana da aljanu, sai sai sun kashi kala-kala, akwai waɗanda
zaune kawai suke tare da mutum su basa magana , sune yawanci zaki ga ɗabi'unsu
ɗabi'un mutum, sai idan waɗancan aljanun waɗanda ake kira iska sun shiga jikin
mutum sune suke nunawa, sai kuma rauhanai su kam ƙarfinsu ma basa iya zama a jikin
ɗan'adam.

Irin waɗancan da basa magana ko wane ɗan adam yana da su, duk inda mutum yayi suna
tare da shi, musamman idan baya tsare addu'ah, kuma kala-kala ne akwai musulma
akwai mushirikai. aljanun da zan tura zai same su ne ya tambaye su inda take aje
ƙyalen haitarta ko kuma pad sai su nuna musu su kuma su ɗauko. Abu ɗaya ne zai hana
su ɗaukar idan lokacin data jefar tayi bismillah to ba zasu iya ɗauka ba, ko kuma
ta ƙona pad ɗin”

“To yanzun nawa zan biya?”

“Zaki bada kuɗin tulu dana jaɓa da kuma na ɗauko shi ƙyalen da za'a haɗa abun da
shi”

“Dubu hansin zai isa?”

“Ba'a bori da sanyin jiki yarinya, idan kin shirya aiki kawai ki zube kuɗi ayi miki
aiki, a take zaki ga aiki da cikawa”

“Zan biya dubu ɗari”

“Cikin satin nan kuwa zaki ji kyakkyawan labari, dan zamu yanka zaɓar ne mu haɗa da
zagen hailarta ne, sai mu yi rubuta da wasu silkulle a saka a tulum sai a je can
daji a inda babu mai zuwa a rataye tulon a ƙasan tulun za mu yi ƙaramar huduwa
wanda ruwan zai riƙa fita kaɗan-kaɗan, yadda ruwan zai riƙa zuba haka jini zai mata
zuba har sai ruwan ya ƙare sai mu sake yin wani. Ya sunan kishiyar taki?”
“Ummul khairi, dan Allah malam a taimaka min dan Allah na kawo kukana gareka, dan
Allah a taimaka min”

“Karki samu damuwa ki komawarki gida kawai”

“Malam an bincika min ƙasar nan ? An duba lamurrana?”

“Bancika ba tukuna dan ban ƴi zaton zaki zo yau ba, kuma kin ga akwai mutane da
yawa a waje, amman idan na bincika ko a waya ne zan faɗa miki”

“To na gode, dan Allah a bincika min ko zan koma gidan mijina”

“Karki samu damuwa, ƙasa zata bada bayanin komai”

Ta zube masa dubu ɗari kasa sannan ta tashi ta fito, zuciyarta cike da yaƙinin
abunda Malamin zai aikata mata.

Har ta dawo gida tunanin zuwa karɓar magani take, akan shawarwarin da likitan ya
bata, sai dai kuma ya faɗa mata idan har bata shan magani cutar zata bayyana kanta,
kuma rayuwarta zata yanke.

NAMRA POV.

Ko da takwas da rabi tayi Maryam da Hinda har Aisha sun wuce school, da wuri Anty
ta shirya ma Abbah breakfast, sannan ta zuba ma Namra nata, ita kuma ta ɗauki nata
dana Abbah ta nufi part ɗinsa da shi, dan bata breakfast ita kaɗai indai har Abbah
yana ɗakinta ne, sai dai tare da shi. Namra na cikin ci abinci sai ga Hajiya Barau
ta shigo mata da nata breakfast, tana far'ah kamar gaske.

Wanda Anty ta zuba mata ma bata ci da yawa ba, balle na Hajiya Barau ko buɗashi ba
tayi ba, sai dai tana jin ƙamshin ferfesun kayan ciki na dukan hancinta.
Tashi tayi ta wanka ta shirya cikin wasu tufafin sababin da Maryam ta ɗauko mata,
tana cikin ɗaurin ɗankwali Anty Amarya ta shigo.
Ta jidaɗin ganin abincin da Hajiya Barau ta kawo ma Namra sosai, hakan ba ƙaranin
faranta ranta yayi ba.

“Ai baki ma ci komai ba”

“Na riga na ƙoshi”

“Namra baki son cin abinci, wannan ma baki ci da yawa ba, gaskiya dole muje asibiti
a duba lafiyarki, zan je na gyara sai kije ki gaida Abbah ki”

“Tau”

Ta amsa murya ƙasa-ƙasa tana jin kamar dai kar taje. Ɗankwalin ta aje ta ɗauki
hijabin Anty ta saka ta nufi part ɗin Abbah tana wata tafiya kamar kazar da ƙwai ya
fashewa a ciki.

da Sallama ta shiga sai ta tsaya can bakin ƙofa ta risina ƙasa ta gaishe shi, kanta
na ƙasa tana mai jin kunyar haɗa ido da shi.

“Abbah ina kwana? An tashi lafiya?”

“Lafiya ƙalau”

Sai kuma ta rasa me zata sake ce masa.


“Mahaifiyarki ta faɗa miki sati ɗaya na yarda ki yi ko? Dan kin san na gargaɗe
karki kuskura dako min gida da sunan fushi ko saki”

Idonta ya cika da hawaye, a take muryarta ta soma rawa.

“Abbah ba fushi na yi ba, na zo ganin gida ne”

“Ko minene dai na faɗa miki duk kika doso min gida da sunan saki, to sai dai
mahaifiyarki ta tattara kayanta ku bar min gida, tun da kin zaɓi zama da shi sama
da Mahaifin ki sai kije can ku ƙarata”

Da sauri ta ɗago kai ta kalli Abbah, sam bata yi tunanin abun nasa ya kai har haka
ba.

“Inshallah haka ba zai faru ba Abbah, amman dan Allah ka yafe min kuma ka fahimce
ni”

Da hannu ya yi mata alama da ta tashi ta bashi guri. Da sauri ta tashi ta fice tana
kuka. Kamin ta ƙarasa part ɗin Anty Amarya ta tsaya ta share hawayenta, sannan ta
shiga.
Lokacin Anty Amarya ta fito daga wanka tana cikin shiryawa, falo Namra ta koma ta
zauna sai da Anty Amarya ta gama shirinta ta ɗauko jakarta ta fito suka fita tare.
Driver Abbah ne ya kai su asibiti, sun yi sa'ar ganin likita dan tun kamin su isa
Anty ta kaira likitan dake duba su ta faɗa masa, sai yayi ma wata likita magana
dan shi be shigo asibitin ba a lokacin.

Mutum biyu aka duba kamin ita, sannan ta shiga tare da Amarya. Bata ɓoye komai ba
da taji tayi ma likitar bayani, ita kuma sai ta rubuta mata text ɗin jini da na
fitsari, sannan ta tura gurin hoto, dan akwai buƙatar su ga abunda yake ƙasan
mararta da take ji yayi mata tsaye gefe ɗaya.

Basu bar Asibitin ba sai da suka je aka musu hoton, aka basu sai suka wuce gurin
ɗibar jini aka ɗibi jininta sannan suka bata wani roba ta shiga banɗakin gurin tayi
fitsari ta kawo musu, sai suka je sai gobe ta zo ta karɓi results, daga suka koma
gurin likitar suka kai mata result ɗin.

“Subhanallahi”

Ta faɗa lokacin da ta kalli hotonnan guda uku da suke guri ɗaya, sannan ta kalli
Namra ta ce

“Me kika sha na zubar da ciki?”

Ba Namra har Anty Amarya sai da gabanta ya faɗi.

“Ban sha komai ba”

“Kin yi ɓari amman ko?”

Ta ɗaga mata kai

“Eh na yi”

“Amman ba kije asibiti ba?”

“Na je sai dai ban tsaya ba, saboda lokacin mijina be da lafiya”

“Kin yi kuskure gaskiya, da kin tsaya an duba ki ai, yanzu kin ga rabin cikin yana
cikin mahaifarki, hakan ya haddasa miki wannan ciwon da kike ji, mahaifarki ta saki
sosai har wani ɓangare na jikin mahaifar ya buɗe ya hudu, jiki be yi saurin ɗauke
miki ba lokacin da kika yi ɓarin? Ke duk baki lura ba”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Namra ta faɗa tana kallon Anty Amarya da tashin hankali ya bayyana a fuskarta.

“Yanzu likita me ye abun yi?”

“Za'ayi mata wankin mara ne, sai mu ɗorata akan magunguna, amman gaskiya akwai
buƙatar tayi family planning na shekara biyu ko uku gudun karta ɗauki ciki har sai
mahaifarta ta warki”

Kuka Namra ta saka tana dafe da cikin nata. Anty Amarya ta riƙa bata haƙuri, tana
mamakin lamarin dan ita bata ma san lokacin da tayi ɓarin ba, kuma gani take kamar
wani abu ta sha dan ta zubar da cikin.

KALSOOM POV.

Kwata-kwata yanzu bata gane lamarin Ezzah ta ɗauke ta kamar wata maƙiyiyarta, sam
bata ma son zama falon idan Kalsoom na nan, abinci ma idan ba Doc ne yake gidan ba,
sai ta ƙi ta koma can ɗaki ta keɓe kanta.

Bayan shi babu wata matsala da Kalsoom take fuskanta, ita kuma bata ɗauke ta
matsala ba dan ba biye mata zata yi ba, zamanta da Doc lafiya ƙalau sai ƙarin so da
ƙauna, ga ɗan cikinta tana raino gwanin sha'awa ɗan satin nan data samu har tayi
fari sosai tayi ƙiba ta mulmule kamar ba ita ba, Doc har tsokanarta yake wai shi
take tsotsewa ita tana ƙiba shi be gane ba.

Ita kuma ta san babu komai sai kwanciyar hankali da kuma kulawar mijinta da take
samu a yanzu, ga Ulfah da Rafiq da suka zame mata tamkar ita ta haife su, dan ko
maganar Mamansu basa yi, indai kaga wani baƙin hali to Ezzah da kicifin dan tafi
kowa kishin uwarta yanzu.

500k words....

______________________________________________
Littafinan na kuɗi ne, idan kin san baki biya ba, karki karanta.
₦200 zaki turo ta wannan account ɗin 0314795884 Abubakar Hadiza GT Bank.

Sai ki turo da shaidar biyan kudin ta wannan number 08036126660

DON'T READ IF YOU DIDN'T PAY...!

*PAGE - 45*

NOT EDITED ⚠

Sai da Yamma lis Anty da Namra suka dawo gida, bayan sun yi mata wankin mara sai da
suka bata 6 hours suka ga condition ɗin ta sannan suka barta ta dawo gida.

Jikinta ya mutu sosai, ga tunanin dake zuciyarta, tana jin gajiya a tare da ita
amman tunanin dake cikin zuciyarta ya hana ta tayi bachi bayan sun dawo gida.
Tana jin kamar ta labartawa wani damuwarta, sai dai kuma bata san yadda za su kalli
abun ba, ace kamar Asim ya juya mata baya, sannan tana ganin idan har ta faɗa Anty
ba zata barta ta cigaba da zama da shi ba, Abbah kuma ba zai yarda ta zauna a gidan
ba.

Haka ta kwana ciki damuwa da tunani har garin Allah ya waye, karin safe ma sai da
Anty ta tirsasa sannan ta ci.
Tana cin abinci tana kukan zuci, kukan da bata san ranar tsayawar hawayenta ba,
kuka maraici amman bana rashin uwa da uba ba, kuka take kukan butulci bayan hallaci
kukan nadama da bata da gani.

“Anty Namra kuka kike?”

Hindatu ta tambaya tana dafata, yanayinta duk ya canja ganim ƴar'uwarta cikin
damuwa.
Hannu tasa ta taɓa fuskarta dan tabbatar da hawayen ya fito, sai kawai ta share
tana murmushi.

“Ban ma san ya fito ba, baki iya sallama ba ne idan kin shigo?”

“Na yi sallama baki dai ji ba ne, me kike ma kuka?”

“Ba komai, dan Allah karki faɗawa kowa kin ji?”

“Tau, ga waya Anty tace na kawo miki Asim.ya kira”

Wayar ta sakarwa ido, kamar mai tsoron karɓa, ji take kamar ba wani abun ƙwarai
bane zai faɗa mata, what if yace ya sake ta?

“Anty...”

Hindatu ta kira sunanta ganin yadda ta tsurawa wayar ido tana nazarin zuci. Sai a
sannan ta kai hannu ta karɓa, ita kuma ta tashi ta bar mata ɗakin.
Wayar na fara ringing gabanta ya faɗi, ba ƙaramin ƙoƙari ta yi ba wajen picking
ɗin call ɗin.

“Assalamu alaikum”

“Wa'alaikissalam Namra”

“Na'am”

“Kin je gida ba tare da kin sanar min ba, miyasa kika je? Kina son ki faɗa musu
abunda ya faru ne? Na san ban kyauta miki ba, amman Wallahi sherin sheiɗan ne, ni
kaina nasan ban kyauta miki ba, amman ina kishin ki ne Namra dan me zaki bar wani
ya rako har cikin asibiti kin ganin hakan kyautawa?”

Hawaye ya fara bin fuskarsa.

“Kai yi min abunda wani be taɓa min ba, ko a mafarki ban za ci zaka aikata min ba,
Asim ka yi taɓon da har na koma ga mahallacin na ba zai gogu ba, baka tambaye ni
waye ba, baka bincike alaƙa ta da shi ba, sai kawai ka zarge ni, ka ɗaga hannunka
ka mareni”

Ya fara mata kuka kamar gaske.

“Na san ban kyauta ba, kuma na cancanci ko wane irin hukumci, amman ki dubi girman
Allah ki yafe min, dan Allah karki faɗawa kowa abun da ya faru tsakaninmu, Wallahi
idan har ki ka bar zan iya shiga ko wane irin hali, haƙiƙa ni butulu ne kuma ajizi,
Namra ki dubi girman ƙaunar dake tsakanin mu ki yafe min, ni har ganin nake kamar
shiga tsakani ne”

“Ban faɗawa kowa ba, kuma ba zan faɗa ba, kuma na yafe maka”

“Na gode Allah yayi miki albarka, dan yaushe zaki dawo? Ko nasa Mama ta zo taje da
ke?”

“Ba sai ta zo ba, zan dawo cikin satin nan”

“Yaushe?”

“Nan da kwana uku”

“Kwana uku yayi nisa Namra, da a'ce da hali sai ki dawo gobe ko jibi”

“Sai jibin dai”

“Na gode sosai Allah yayi miki albarka, duk suna lafiya ko?”

“Kowa ƙalau”

“Ina gaida kowa dan Allah”

“Za su ji”

“Na gode sai na ƙara kira”

Ta sauke wayar tana cigaba da hawaye.

“Na yafe maka, amman ba zan manta ba, zan zauna da kai saboda zama da kai ya zame
min dole, son ka be amfana min komai ba Asim sai baƙinciki da damuwa”

Ta share hawayenta tana jin wani irin ƙuna da zuciyarta ke mata. Ɗan abincin da
take ci sai ya fita ranta, ta tattara kayan abinci ta ɗauki tray ta nufi kitchen da
shi, bayan ta aje ta dawo falonta zauna tana miƙawa Anty wayarta.

“Har kun gama”

“Eh wai tambaya yake yaushe zan dawo”

“Dika yaushe kika zo? Me kika ce masa”

“Nace masa sai Next week amman ya ce sai dai na dawo gobe, daker ya haƙura na kai
jibi”

“Haba Anty Namra dika yaushe kika zo ma?”

Maryam ta faɗa. Anty tace

“Zan yi magana da shi ya bar ki kiyi ko wata ɗaya”

“A'a Anty kin san ba shida lafiya sosai ma, kuma bana son satin da Abbah ya bani ya
cika ban koma ba”

Ɗaya bayan ɗaya Anty ta bisu da kallo, a tunaninta ko a cikinsu ne wani ya faɗa
mata Abbah yace karta wuce sati ɗaya.
Maryam ce ta fara tsarguwa da kallon Anty ta yi magana.

“Wallahi ba ni na faɗa ba”


Aisha
“Ni ma dai”

Hindatu.
“Balle kuma ni”

“Waya faɗa? Ko muna da aljanu ne a gidan?”

Namra tayi murmushi, irin murmushin nan na ƙarfin hali ka danne baƙincikin ka.

“Ba suka faɗa ba, Abbah ne ya faɗa min da kan sa”

“Yaushe?”

“Jiya da naje gaishe shi, yau ma ya nanata min”

Anty tayi shiru bata sake cewa komai ba. Sai dai bata jidaɗin da Abbah ya faɗama
Namra haka ba.

“Akwai abubuwan da kike buƙata ne? Dan a siya da wuri kar lokaci ya ƙure, ko kuma
kuɗi zan baki kije can ki siya?”

“Kuɗin zai fi, dan ɗaukar kaya a nan ma ai aiki ne”

“Amman Namra ba zai yarda ku dawo nan ba?”

“Kwana ki ma yayi min maganar haka, amman nace ya haƙura har yaji sauƙi sosai
sannan mu dawo”

“Gaskiya kam zama a nan zai fi, kim ga nan zai fi muku kuma kin ga nan ko ba komai
kina kusa da mu”

Sallamar Doc Faruk ne yasa suka katse firar da suke suka amsa sallamar suna masa
sannu da zuwa.
A kujerar da Namra take zaune ya zauna, kasancewar ta zaman mutum uku ce, sai ya
soma gaiswa da Anty cikin far'ah, tun da shi ba baƙon gidan ba ne.
Maryam da Hindatu da Aisha sai duk suka tashi suka bashi guri, Anty ma tana gama
gaisawa da shi, ta shige ɗakinta dan tasan abunda ya kawo shi, daman ita ta kira
shi, ganin hakan kamar zai fi sauƙi tun da likitan gida ne.

“Daman akan maganar planning ne Anty tana tsoro kar ayi mai side effects, so ni
abunda naƙe ganin ya fi shine ki yi na roba, saboda idan an saka mishi kin ga sai
lokacin yayi sannan za'a cire, ba kamar allura bane da a za'a riƙa yi duk months,
kuma kin ga shan ƙwayoyin zai iya ƙara miki matsala ma a mahaifa, za a iya tsuke
miki bakin mahaifa”

“Amman robar idan an saka ba shi da wata illa ne?”

“Eh to kin san komai karɓa karɓa ne, amman gaskiya baya da matsaloli kamar sauran,
kuma kin ga shi a duk lokacin da aka tashi cire miki za'a iya cirewa”

“Amman yanzu ina katsina da zama idan na saka ta nan za'a iya cire min a can?”

“Za'a iya cire miki mana, amman idan son samu ne inda aka saka miki a cire miki
ita, saboda aikin wani ba shine aikin wani ba, kuma idan ma son samu ne likitan
daya saka miki ita ya zama dik lokaci shine ya ke duba ki”

“Amman kana ganin ba zai haifar minnda matsala nan gaba ba?”
“Gaskiya bana jin zai haifar miki da matsala, indai ba abunda Allah ya kawo ba, sai
dai kinsan komai yana da side effects sai dai wani ya fi wani”

“Okay, ba matsala when za'a saka?”

“Ko yaushe kika tashi, a hannun hagu ake sakawa kuma idan an saka miki ba zaki yi
aikin da hannun ba tsawon 24h, amman za mu buƙaci sa hannun mijinki kamin mu saka
miki”

“Mijina baya tare da ni yana Katsina, kuma idan da hali ina son a saka min gobe”

“Consider it done, zan yi replacement ɗin mijinki a gurin sa hannu ko da wannan zan
yi alfahari”

Tayi kamar bata ji shi, sai ta tashi ta nufi ɗakin Anty tana faɗin

“Zan shiga ciki”

“Around nine za ku shigo”

Ya faɗa sannan shi ma.yasa kai ya fice.

“Mun yi magana da shi zai saka min roba ta hannu”

Ta faɗa tana ƙoƙarin zama kusa da Anty.

“Ta shekara nawa? Ita bata da matsala kamar sauran ko?”

“Eh haka ya ce, gobe da safe za mu shiga”

“Allah ya kai mu, ya baki lafiya”

“Amin”

Kwantawa tayi saman gado, Anty ta tashi ta fita.


Washen garin ranar da yace musu suka tafi aka saka mata, duk wani shirin a ranar
Anty tayi mata shi, saboda komawar da zata yi gobe.
Hajiya Barau tayi mamakin komawarta da wuri haka, a take ta raya a zuciyarta
ƙila Abbah ne yace be yarda ta daɗe masa a gida ba, ita tama yi mamakin da ya barta
har ta zauna, goma na arziki ta haɗa mata, tun daga kan kayan sawa zuwa kuɗi da
kayan mata.

Ranar da zata koma taje yi ma Abbah sallama, ranar ta sha kuka kamar ranar da za'a
kaita ɗakinta, Anty ma tayi kuka sosai har hakan ya saka sauran ƴaƴan na ta kuka.
Direban gidan aka sa ya kaita har katsina dan Anty bata son ta shiga motar haya.
Sai da ta biya gidan Gwaggo tayi mata sallama sannan suka kama hanyar katsina.

RASHIDA POV.

Washe garin ranar data dawo Malamin ya kira yana labarta mata bayanin da ƙasa ta
bada akanta.

“Ba zaki taɓa komawa gidan Mijin ki ba, matuƙar wannan matar tana cikin gidan,
sannan idan baki tashi tsaye ba, to har ƴaƴanki mijinki zai wulaƙanta su akan ta,
kuma kin yi kuskuren ba mu suna, Ummu Kalsoom take ba Ummulkhairi ba”

“Na ɗauka ai duka ɗaya ne”


“Ba ɗaya bane, sannan mun ga wani baƙin hudu a tare da ke, kuma bayani ya nuna a
halin yanzu tana sama da ke sai kin tashi tsaye”

“Malam wane irin baƙin abu ne wannan?”

Duk ta tsorta.

“Bayani be fito mana fili ba, amman lailai akwai baƙin abu yana biye da ke, kuma
akwai abu a jikinki wanda kike ɓoyewa dangin ki”

“To Malam a taimaka ayi mana aiki, ta fita gidan kamin na cika idda kuma ayi min
abunda zai jawo hankalin mijina gare ni”

“Dika za'ayi aikin ma nasa a aiwatar da shi yau”

“Amman ƙasa ta bada bayanin zan koma gidan Hilal?”

“Ƙasa ta bada bayani kan mijinki, matakin da muka ɗauka yanzu idan be yi ba, sai mu
yi na biyu idan be yi ba, sai na uku wanda shi kam dole ne a samu nasara”

“Wane mataki ne?”

“Dika zaki jisu, amman na biyu da na uku abubuwa masu matuƙar wahala”

“To Malam na gode, amman dan Allah a taimaka a bincika min baƙin duhun nan”

“Zamu bincika”

Ya kashe wayar, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya tana dafa kai. Baƙin abun nan ya
tsaya mata a rai, sai faman tunani take wane baƙin abu ne? Ko dai Ƙalsoom ce ko
kuma ciwon da take ɓoyewa ne? Bata samu amsar tambayarta ba har ta gaji da tunanin
ta tashi ta shirya ta nufi makarantar su Ezzah. A hanyarta ta tafiya ne Alh Bashi
ya kirata wai yana nemanta kwana biyu yayi kewarta, tsaki taja ta faka gefe tana
magana da shi.

“Hala baka san aurena ya mutu ba?”

»“Na sani mana, sai dai ban san dalilin mutuwar auren na ki ba”

“Kishiyata ce ta fi ƙarfina ta mallake min miji da ƴaƴa”

Daga can cikin wayar yayi dariya ya ce

“Ke yanzu kamar ki har wata mace ta isa ta fi ƙarfin ki, anya mijin ki ya san mace
kowa?”

“Hmmm ƙaddarace ta gitta irin wace zata gitta ka saki Asmee nan gaba”

“A'a aure na da Asmee ai na zobe ne, idan kin ga na rabu da ita to na mutu, indai
ina raye ba zan rabu da ita ba, idan kin ga na rabu da ita to na rabu da uwata ne”

‘Hmmm saboda ta maka mugun magani ba, ai wallahi tayi ma kan ta ƙiyamul laili’

Rashida ta faɗa a ranta, a fili kuma sai ta ce

“Kasan da ita kake zama da ni”

“Wannan ai daban, ni dai ki zo ina son ganin ki”


“Ko na zo babu abunda zan maka, dan ni period na ke”

“Na sani haba, ke dai ki zo ina neman ki, amman fa anjima idan mun tashi aiki”

“Na ji”

Ta kashe wayar, ta kunna motar ta hau titi.

ABDOOL POV.

Ko da sha ɗayan safe tayi Ummi da Jidda sun sauka garin Abuja. Kai tsaye ta wuce
masaukin Abdool, a lokacin baya ma gidan yana gurin meeting, haka ta zauna a gidan
har ya dawo sannan hankalinta ya kwanta ganin da gaske babu abunda ya same shi.

“Ummi na faɗa miki am fine amman kika ƙi yarda da ɗan ki”

“Yanzu ai na yarda, ina ita yarinyar ta ji sauƙi?”

“Eh ance min jiya ta farka, amman ban samu na je dubata ba, amman na ce suje su
ɗauƙi statement”

“Allah sarki baiwar Allah ai ta taimaka da yanzu kai ne aka harba”

“Ko bata tare ba, ba zasu harbe ni ba, dan Allah ya rubuta ba zasu same ni ba”

“Haka ne kuma”

“Ummi me kuke so a siyo muku?”

“A'a ni ba zaka ƙara siyen abincin nan ba, ai da gaskiyar Mai martaba da yake cewa
ka daina yawo kai ƙaɗai, ni gaskiya ya kamata ace ma ka yi aure dan ka huta da
wannan wahalar siyen abincin kullum”

Dariya yayi ya tashi ya fita. Be daɗe ba ya dawo, ya tsaya daga bakin ƙofa

“Ummi zan je asibitin idan kun huta kun ci abinci direba zai kai ku ku ganta”

“To a kula dan Allah”

“Inshallah”

Ya ciro wayarsa dake ringing ya amsa kiran ya juya yana magana ya fice. Sai da ya
biya wani office nasu yayi wani meeting sannan ya wuce.

Sun masa bayanin abunda suke zargi akansa, suka nuna masa bayananta da suka ɗauka
sannan ya shiga ɗakin da take.
Kife take saman gadon asibitin sanye da tufafin majiyanta, wani irin kallo take
masa irin kallon nan na mutum be san yana yi ba. Har ya zauna a kujerar dake facing
ɗinta bata ɗauke idonta akansa ba.

Hannunsa ya riƙa yawo da shi dan ya tabbatar tana cikin hankalinta ko akasin hakan.
Sai kawai ta lumshe ido hawaye ya silalo daga idon nata. She just can't believe
Abdallah take ganin da idonta, mutumen da ko a mafarki take ganin yayi mata nisa,
sai dai tasan tayi betrayed wanda yayi mata mafaka a lokacin da bata da gurin zuwa,
ga shi waɗanda suka mata tambaya a ɗazu sun tabbatar mata da ya mutu.

“How are you feeling”


Ta buɗe ido ta kalleashi, sai kuma ta kawarda kanta gefe kamar bata ji abunda yace
ba.

“Ko ba ki jin turanci ne?”

Ya tambaya yana leƙen fuskarta.

“Ina ji”

Ta amsa ba tare data kalleshi ba.

“Me kike yi ma kuka?”

“Kukan baƙinciki nake, miyasa baka bar ni can na mutu ba? Sai ka ɗauko ni ka kawo
ni asibiti?”

“Taya zan bar mace data sadaukarda ranta gare ni ta mutu?”

“Na sadaukarda raina a gare ka saboda ni na rasa nawa ran, kai kana da amfani ga
alumma ni ko bana shi, kuma na san duk na sadaukarda rai na a gareka dole ne kai ka
rayu ni na mutu”

“Sai gashi kuma sai dik muka rayu”

“Shiyasa ni nake baƙinciki, na yi tunanin ni tawa wahalar ta yanke daga nan ne,
ashe akwai sauranta”

“Wacece ke? Miyasa kike irin wannan furucin?”

“Nice wacce ta rasa uwa da uba, wacca aka koreta daga gidan su saboda saurayi ya
yaudare ta”

“Ban gane ba?”

“Ƙawata ta haɗa kai da ɗan'uwanta ta yaudare ni. Fyaɗe tasa ɗan'uwanta yayi min,
sanadin hakan na samu ciki, ni kuma sai iyayena suka kore ni, na zaje garin Kaduna,
ranar dana sauka a garin na haɗu da Guy son yaje tasha karɓar saƙo, sai ya ɗauko ni
ya kawo ni gidansa da sunan zai kwana da ni ya biya ni, daya fahimci bana da gurin
zama, sai yayi masauki a gidansa, ashe ɗan fashine kuma yana kidnapped ni ban sani
ba sai bayan mun shaƙu da shi, shi ya zubar min da cikin da ke jikina ya mayarda ni
karuwarsa”

“Ayyah sorry, amman me kika sani game da Guy Son?”

“Ban san komai akansa ba, baya bari na shiga lamurransa”

“Ya aka yi kika san yana attacking ɗi na?”

“Saboda ya san ina son zuwa Abuja, sai yace zai zo da ni, amman wani aiki zai zo
yi, na kashe wani soja wanda wata mata tasa aka she shi, amman a nan ba su kashe ka
sai ka koma Katsina”

“Ya faɗa miki wacece matar?”

“Be faɗa min ba, ban ma san kai wanene ba kawai ya faɗa min zai zo bibiyar sawon ka
ne, ni kuma naga ba zan iya bari ta kashe ka ba, shiyasa na zaɓi mutuwa kai ka
rayu, dan nasan dole zai nemi kashe ni, ni kuma buƙatana ya biya tun da ka rayu”
“Wane gari kike?”

“Sokoto”

“Amman miyasa kika zauna da shi bayan kin san yana aikata kisan kai?”

“Me kake tunani ga mace da iyayenta suka koreta? Idan ban zauna da shi ba da wa zan
zauna? Wa zai min masauki? Ina za a karɓe ni?”

Kuka ta fara rerawa tasa hannu a baki gwanin tausayi.


Kallonta yake indai har da gaske na abunda ta faɗa, to ita abar tausayawa ce, sai
dai shi yana jin be yardar da ita ba.
Jin kukan nata na son yawa yasa shi tashi ya bar ɗakin. Baga ɗaya fita yayi daga
harabar asibitin ya nufi wani part na gurin. Wani ɗaki ya shiga ya kwashe waya ɗaya
a ɗakin suna tattaunawa sai da aka ce masa ga Ummi nan sannan ya fito ya tare su.

“Jikin nata da sauƙi dai ko?”

“Da sauƙi sosai ma, mun yi magana da ita sosai sai dai a bayanan ta ban yarda da
ita ba, dan haka nasa a bincika min komai a kanta”

“Hakan yayi mi tace maka ne?”

A nan ya fara bata labarin da Amira ta bashi, suna takawa zuwa part ɗin da Asibitin
take da ƙafa.
Sosai da sosai Ummi ta ji tausayinta ya kamata, har idonta ya cika da ƙwallah, sai
Allah wadai take ma iyayenta da ƙawar data cuce ta.

Amira na jin lokacin da suka shigo amman tayi pretending like she's seriously
sleep. Fukarta kawai Ummi ta leƙa cike da tausayawa ta juyo ta fito tana mata
addu'ar samun sauƙi.

KALSOOM POV.

Tayi mamakin ganin haila a yanzu, bayan tasan tana ɗauke da ciki, kuma rabonta da
haila tun kamin ta samu ciki. Hakan yasa ta fara zargin ko dai bata da cikin ne?
Sai dai kuma ita tasan tana jin alamun masu ciki kuma Doc ma ya tabbatar mata da
haka. Wani tunanin ne ya zo mata, wata ƙila tana cikin matan da suke haila a
lokacin da suke ɗauke da juna biyu.
Ita dai abun ya ɗaure mata kai. Tun a dare da abun ya same ta Doc ya sani sai ya
ɗaga mata kafa ya saurara na tsawon kwana biyu ya gani ko jinin zai ɗauke mata,
amman be ɗauke mata ba. Hakan ya bashi mamaki.
Yayi mata tambaboyi akan lafiyarta, kamin ya ɗauke ta suje suje su yi hoto dan
tabbatar da lafiyarta.

Ya yi mamakin results ɗin da hoton ya bada wai bata da ciki, alamu ya nuna
mahaifarta ma ciki be taɓa zama ciki ba.
A tare suka dawo gida sai dai be yarda da faɗa mata abunda result ɗin ya bada
ba, dan har yanzu mamaki yake, daya sauke ta be shigo ciki ba, ya ce mata ya zai
koma gurin aiki.

Ita sam bata lura ba, dan bata kawo komai a ranta ba. Tana shiga falon ranta yayi
mugun ɓaci ganin yadda duk suka lalata falon kamar bata gyara shi ba kamin ta fita.
Saman kujera ta zauna tana kallon falon cike da takaici tace

“Ezzah zo ki share falon nan, Ulfah ke kuma ki kwashe plates ɗin nan shine bayan
fita na kuka sake ɗiban abinci kamar ba ku ci ba? Kuma duk kuka lalata falon haba
dan Allah miyasa ba ku tausayina ne?”
“Ezzah ce ta ce mu ɗibo mu ci tun da abincin Baban mu ne, wai ita bata ƙoshi ba kin
sa mata kaɗan”

Ulfah ta faɗa tana shirin tattara plates ɗin. Kallon Ezzah Kalsoom tayi cike da
mamaki.

“Abincin da nake sa muku ne baya isarku shine ba zaki yi magana a daɗa miki ba?
Sometimes ba ke da kanki kike ɗiba ba? Ezzah me ke damun ki ne? Me yake cikin kan
ki ne? Kwanakin nan kwata-kwata kin canja kina son lalata kan ki”

Wata irin harara ta bankaɗo ma Kalsoom kamar ta taso tazo ta maƙareta. Kalsoom ta
nufi inda take tana nuna kan ta

“Ke ni kike harara? Warin ki ce ne?”

Ta zungureta. Sai kawai ta fashe da kuka daman jira take.

“Wayyo Ammyn mu....”

“Ooo munafuka, daman abunda kike nema kenan ko? Na dake ki so that ace na cuce ki
ko? Ke ƙaramar yarinya da ke kin san munafurci? Tau Wallahi ba zan ɗauka ba, ba zai
yiyu na yi kishi da uwarki ba yanzu kuma na yi da ke ba, tashi ki share falon nan
ko na miki matsiyacin duka”

Cikin kuka ta tashi ta shiga kitchen ta ɗauko tsintsiya ta soma sharar. Ulfah na
daga gefe tana kallon Kalsoom cikinta dik ya ɗuri ruwa ji take kamar itama zuwa
zatayi ta dake ta.

Doc be dawo ba sai dare, tun a bakin ƙofa Ulfah ta same shi ta labarta masa abunda
Kalsoom tayi ma Ezzah, sai dai be ɗauki abun serious ba dan yasan Kalsoom ba zata
dake ta a banza ba.
Sai dai samun Ezzah a falo da yayi tana kuka ya ɗan sosa masa rai.

“Me kike yi ma kuka kuma?”

“Yunwa na ke ji, Anty tace karna sake ɗiba abinci har sai ta ga dama ta ba ni”

“Ba ki ci abinci dare ba ne?”

“Har na rana ban ci ba, wai dan nace sai na faɗa ma maka ta fita”

“Je ki ɗibi abincin zan yi magana da ita”

Ta tashi ta nufi dinning, shi kuma ya nufi ɗakin Kalsoom cike da gajiya.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: 4»»»»6»»»»»»»»»»»»»

Gaban mirror ya same ta chaɓa ado tana kallon kan ta. Dik wata gajiya da fushi dake
tare da shu sai ya kushe, saboda yana son ado, mutum ne mai son ganin mace ta yi
kwallaiya a ko yaushe. Murmushi ya ƙarasa kusa da ita yana ƙyaƙƙyawar fuskarta ta
madubi.

Ita ma murmushin take tana lumshe ido tana buɗewa, irin na ɗaukar hankalin nan. Sun
samu minti biyar a haka suna kallon junansu kamin ya risina ya rumgume ta.

“Who brought this Cute Babe here?”


Lumshe ido ta yi tana sauraren yadda yake shinshinar wuyanta.
Saukowa yayi ya duƙa gabanta ya kama duka hannayenta yayi mata kiss.

“Sweetheart, I'm sorry we lost our baby...!”

Farincikin da ke fuskarta ya gushe, idonta ya cika da ƙwalla, har sun fara zuba a
fuskarta.

“How...?”

“I have no idea kawai result ɗin ya nuna ciki be taɓa zama a mahaifarki ba”

“Amman ina jin alamu na ma su ciki, kuma kai ma ka tabbatar min da ciki ne”

“Yes sai kuma yanzu ya zo akasin tunanin mu, ko kin sha wani abun ne?”

Kai ta girgiza masa tana kuka. Sai ya jata zuwa ƙirjinsa ya rumgume ta.

“Shiiiiii Allah zai ba mu wani”

Ƙamƙame shi tayi sosai tana kuka. Har ƙasan ranta take jin zafin zubewar cikin, ta
yi buri akan cikin nan har mafarki take, kuma ita bata san ta sha komai na zubar da
cikin ba taya za a ce ya zube?

Daker ya lallaɓa tayi shiru, amman duk kwaliyar da tayi ta dale ta ɓata mata fuska
kamar yarinya ta yi kuka.

“Ya Salam, yanzu dik kin ɓata kwaliyar nan”

Bata ce masa komai ba, ta tashi ta hau saman bed ta kwanta tana sauke ajiyar
zuciya. Damuwar da take ciki yasa be yi mata maganar komai ba, sai kawai ya tashi
ya koma ɗakinsa yayi wanka ya shirya cikin kayan bachi, sannan ya dawo falon ya
kashe kayan kallo, ya tura yaransa ɗakinsu. Sannan ya ɗibi abincin mutu biyu a
plate ya shiga da shi ɗakinta.

Dik yadda ya lallaɓata ta ci abincin ƙin ci ta yi, daya matsa mata ma, sai akwai ta
fara masa kuka, a dole ya ƙyale ta ya aje abincin jefe dan shi ma baya jin zai iya
cin abinci bayan matarsa tana cikin damuwa.
Haka ta kwana cikin damuwa tana ganin kamar dai wasa Doc yake mata, cikinta na
nan tun da ita dai bata ji wani alamu na zubewar ciki ba, sai dai kuma jinin dake
mata zuba ya tabbatar mata haka. Sai da ta yaƙi zuciyarta sosai, sannan ta iya
godiya ga mahalaccinta, ta fawwala masa komai dan tasan shine mai yi, shi ne kuma
ya bata yanzu ya karɓe dan haka sai ta gode masa.

Cikin kwana biyu ta manta abun a ranta, ta cigaba da walwalarta tana sakewa kamar
yadda take a da. Ta cigaba da bawa mijinta kula sai dai har gobe matsala ɗaya take
fuskanta ta ɓangaren Ezzah dan yanzu abun nata sai ƙara ta'azzara yake tana ƙara
tirjewa.
Yau ma abunda ta saba mata a kullum shi tayi, ta ci abinci dik ta ɓata falon
kuma haka zata tashi ta barshi haka sai dai Kalsoom ta gyara.

Da kallo Kalsoom ta bita har ta zauna saman wata kujera ta zauna ta buɗe school bag
ɗinta tana fiddo littafai.

“Ezzah miyasa baki jin magana ne? Kullum idan kin ci abinci sai kin watsar kuma ki
bar ni da gyara, da nace ki gyara sai ki buɗe baki ki fara yi min kuka? Wannan wane
irin rayuwa ne?”

Gunguni ta fasa mata irin maganar nan ta can cikin maƙoshi ta wanda yara ke yi idan
suna takarar rashin kunya. Hakan ya harzuƙa Kalsoom ta har ta ƙarasa inda take ta
dangwale ta.

“Me kike faɗa? Ke marar kunya ko? Ina miki magana kina min gunguni”

Ɗan wannan abun da Kalsoom tace mata sai kawai ta ɓare baki ta fara kuka tana, ta
tashi da gudu ta bar falon.
A harabar gidan ta je ta zauna tana kuka kamar wacce aka cirewa rai.

Haka ta zauna a gurin har mahaifinta ya dawo ta sanar da shi dukan da Kalsoom ta yi
mata. Sam be jidaɗi ba dan babu abunda ya tsana kamar duka, komai zai iya ɗauka
amman ban da a dakar masa yara, dan shi be sa musu hannu ba ba zai yarda wata ta sa
musu ba, Rashida ma data haifesu baya bari ta dakesu.

“Ba ki mata komai ba zata dake ki? Kalsoom ba zata dake ki haka kawai ba”

“Wallahi ban mata komai ba, kawai tace na share falon nace ta bari na gama homework
shine kawai ta mare ni”

“To ya isa yi haƙuri zan mata magana”

“Daddy yaushe Ammyn zata dawo?”

“Ba zata dawo ba”

“Miyasa?”

“Tace ta zaɓi haka”

Ya riƙa hannunta suka shiga ciki. Suna shiga falon ta fisge hannunta ta nufi
ɗakinsu da gudu.
Kallo ɗaya Kalsoom tayi mata ta ɗauke ido tana masa sannu da zuwa.

“Yauwa me Ezzah tayi miki kika mareta”

Ya faɗa yana mai zama a kusa da ita.

“Mari? Ita tace maka na mareta haka tace maka?”

“Baki mare ta ba?”

“Haba Doc mi zai sa na ɗaga hannu na mareta sai kace wari na? Ni dai nasan na
zungureta”

“Amman Kalsoom be kamata ace kin dake ta ba, Ezzah yarinya ce dik abunda take yi
ƙurciyace, sannan rashin mahaifiyarta yana damunta dole sai kin yi haƙuri da ita,
bata da uwa a yanzu sai ke”

“Amman idan ta ɗauke ni uwa mi zaisa ta min rashin kunya? Did i treated her badly
ne? Miye bana mata tun mahaifiyarta na nan, sai yanzu dan daga bata nan zata fara
min rashin kunya? I'm tired Hilal I'm tired ba rainon ƴaƴanka na zo yi ba, nima
aure na zo, idan rainon ƴaƴanka kake so ayi maka kaje ka nemo mai raino, amman ni
ba zan iya, ba kuma zan yi ba, ko da zai zamo silar mutuwar aurena ne!”

Kallonta kawai yake irin yadda take zuba masa ruwan masifa har hantanta tashi suke,
gaba ɗaya ta fita hayyacinta saboda abunda be kai ya kawo ba.
But all what he thought tana cikin damuwar zubewar cikinta ne, he feel her pain,
hakan yasa ya ɗaga mata ƙafa be biye mata ba, sai kaiwai ya tashi ya barta falon.
Fashewa ta yi da kuka ta cire ɗankwalinta ta jefar tana kuka.

“What is wrong with me? Miye same ni? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta tashi da gudu ta shige ɗakinta tana cigaba da kuka, zuciyarta cike da tsanar
Hilal bayan be mata komai ba.

NAMRA POV.

Asim be yarda ta dawo ba, har sai da ya ganta asibitin, aiko ya dinga murna kamar
ya ɗauke ta ya haɗiye, Mama ba laifi ta tarbe ta far'ah tana na'am-na'am kamar ba
ita ba.
Namra ta jidaɗin haka, sai taga kamar saboda tayi fushi ne Asim ya tsorata yayi
canja, duk sai ta ji farinciki ya baibayeta ance so hana ganin laifi, ita dai har
gobe zuciyarta na son Asim, duk da da shakkun da take da shi akansa, dan ta ƙudiri
aniyar naira biyar nata ba zai sake shiga hannun Asim ba, tun har ta gano nufinsa.

Ya samu sauƙi sosai, dan har likitoci suna maganar sallamarsa ganin yanzu yana taka
ƙafar sai dai yayi ɗingishi, Mama ta fi kowa jindaɗin samun sauƙin nasa saboda ta
matsu ta koma gida zaman asibitin dik ya isheta.
Ranar da Namra ta kwana biyu da dawo taja ƴar fulani suka je kasuwa ta siye wasu
abubuwan na kitchen da na ɗaki, da kuma tufafi da hijabi, da ta dawo da yamma ne ta
share ɗakin ta wanke ta zuba center carpet ɗin data siyo da taimakon yarinyar ta
kira yayanta namiji ya laƙa mata labulaye sannan ta shiga da katifa, da sauran
tarkace. Ta haɗa BQ ɗin ba laifi kasancewar ɗakun biyu ne sai ta mai da ɗayan kamar
kitchen ɗinta, ta saka abubuwan zuba ruwa da sauran kayan aikinta ciki.

AMIRA POV.

Washe gari Ummi ta dawo ta ga Amira dan tasha alwashi ba zata bar Abuja ba sai ta
yi ma Amira godiyar abunda tayi ma ɗanta.

Amira ta jidaɗin haka, ta san ko ba komai ta samu shiga zuciyar Ummi ganin yadda
take tausayinta, har da zubar mata da ƙwalla, gashi jikinta ya nuna ita ɗin wata
ce, tun daga kan tufafinta zuwa yadda naman jikinta ya kwanta.
Amira ta kama hannunta ta riƙe sai hawaye take tana son shige mata jiki.

“Na ji daɗi da kika zo, na ji kamar a'ce ke mahaifiyata ce”

“Ni mahaifiyarki ce mana miyasa kike magana haka, Allah ya baki lafiya”

“Amin na gode”

Ta faɗa tana kife saman gado asibitin. Abdool na tsaye hannayensa a aljihu yana
kallonsu, shi dik ya gundira Ummi ta bar ɗakin, coz he don't trust Amira, kuma
hankalinsa be kwanta da ita ba for no reason.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: 4»»»7»»»»»»»»»»»»»»»

“Wai Daddy yace kin ce ba zaki dawo ba”

“Yaushe yace miki haka?”

“Jiya da ina tambayarsa yaushe zaki dawo, wai yace ke kika ce ba zaki dawo ba”
“Baya son ya faɗa miki ne, saboda yanzu baya so na Kalsoom yake so, idan har kina
son na dawo dole ne ki riƙa yin abunda na faɗa miki, idan kina irin haka shine sai
za ya tausaya muku yace na dawo”

“Amman ita bata jin daɗin abunda nake mata”

“Ke kina jindaɗin data koreni?”

Ta girgiza kai alamar a'a.

“Idan baki yin abubuwan da nake faɗa miki ke ma wata rana sai tasa Daddy ki ya kore
ki, sai ta mallake gidan daga ita sai nata ƴaƴan”

Ezzah ta.yi shiru tana tunani sai kallon ƴan makarantar su take masu kai wa da
dawowa.

“Ezzah dik duniyar nan baki da kowa kamar ni, duk wacce zata so ki abaya na take,
kuma ƙarya Kalsoom take tace tana son ku, tana nuna muku haka ne dan ta mallaki
Daddy, yanzu kina jindaɗi zama da ita? Bata dukan ki? Lokacin da ina nan Daddy ki
yana miki faɗa?”

Duk ta girgiza kai.

“Dole ne kiyi mata abunda na saki dan na samu na koma gurin Daddy ku, na yi muku
alƙawari ddana koma kullum gida zan riƙa zama ba zan sake fita aiki ba”

“Da gaske?”

“Wallahi, dan haka ki cigaba da abunda kike, har abunda ban saki ba ma ki aikata
indai kinsa wanda zai hassalata ne”

“Zan riƙa yi”

“I Love you”

“I Love you too”

Rashida ta rumgume ta kamar da gayya. Sannan ta ciro chocolates da Sweet Candy dake
jakarta ta miƙa mata, ta kuma bata ɗari biyu na kashewa sannan ta tashi ta fita.

Daga nan Asibiti ta nufa. Yau ce rana ta farƙo da zata fara bin shawarar likita
wajen ɗora kanta akan magani, dan samun tsawaita rayuwarta kamar yadda likita ya
faɗa mata.

NAMRA POV.

Two months later....

A zuwa yanzu babu wata matsala da take fuskanta a gurin Asim, tun bayan da aka
sallamo daga asibiti, jiki sai ƙara sauƙi yake yana mirmirjewa kamar ba shi ba.
Duk wani mugun ƙudiri dake cikin ransa, ya danne ya barwa zuciyarsa, dan yasan
babu yadda zai yi da Namra a yanzu sai kallo, idan yace zai rabu da ita matsala ne
a gare shi tun da baya sgi kuɗin auren wata, shi dai yanzu ba shi da wani buri sai
na yayi kuɗi.

Irin yadda yake nanata maganar har tsoro abun yake ba Namra, ahi dai yayi kuɗi dai
yayi kuɗi. Haka Namra zata zauna tana masa nasiha akan duniya da abunda ya ke
cikinta, amman sai dai ya kalleta kawai ya nuna mata wa'azin ya ratsashi bayan a
ƙasan zuciyarsa kuma mamakinta yake, wai ita zata zaunar da shi ta nuna masa illar
kuɗi, bayan ga ubanta can ya tara su ita kuma da su take tinƙaho.
Sam baya ganin wahalar da take da shi, bata saba wanki ba ko a gidansu amman
haka zata zauna ta wanke nata tufafin ta wanke nasa, ta kai masa ruwanka, amman
kullum sai ta matsa masa yake wanke dan ganin yake kamar tana takurasa, Allah ya
zuba masa ƙuiyar motsa jikinsa indai a bangaren aiki ne.

Maganganun da Namra take masa akan rayuwa da neman kuɗi da yake magana a ko yaushe
sai ya ƙara riƙe ta a zuciyarsa, wai bata son sa da alheri ta fi son yayi dauwama
cikin baƙin ciki da damuwa tun da ita tana da mafita.
Ga matsalar da ci masa tuwo a ƙwarya a yanzu, wacce yake ganin kamar da ganganci ne
tayi masa haka dan bata son haihuwa da shi. Ita kanta tana nadamar sanar da shi da
tayi robar da aka saka mata, sai dai babu yadda zatayi dole ce tasa ta faɗa masa,
tun kullum sai ya tunkareta kuma jinin har yau be tsaya mata ba, daman wani lokacin
haka robar yake yi mutane dan ta ji maƙonta suna firar lokacin data shiga gidan su
ƴar fulani.

Ta aika tambayarta ga wani malami ya amsa mata da cewar duk jinin daya zube bana
haila bane ya zama kamar jinin rashin lafiya ne dan haka ba zatayi fashin sallah ba
balle azumi.

Hakan yasa robar ma sai ta fita ranta dan ita bata son abunda zai riƙa rikitar mata
da addini, hakan yasa ta yanke shawawar zuwa a cire mata robar in ya so sai tasha
ƴaƴan zurma, dan maƙociyarta nan ta faɗa mata indai har ta sha ƴaƴan zurma ɗaya
yana matsayin shekara ɗaya ne idan kuma tasha biyu kuma yana matsayin shekara biyu
ne.
Sai dai ba kowa yake yi ma aiki ba, amman ta ga wani a whatsapp wanda Khadeeja
Candy take tallah shi kam idan an sha tabbas zai maka aiki, matsalar kawai ita ba a
garin take ba, kuma tana buƙatar ta bincike dan ta jin yadda abun an ce mata texted
and trusted ne. Ga Kuma Asim ya dame ta da maganar kullum, dan shi gani yake kamar
da biyu tayi haka.

Yau wake ta dafa da shinka (rice and beans) ta saka mai da taji, daman yana cikin
favorite na ta, amman Asim duk lokacin data dafa sai ya riƙa ƙin ci yana ganin
kamar tana haka ne dan karta kashi kuɗi da yawa tayi musu abinci mai kyau.
Shi yanzu har ya matso jikinsa ya koma.yadda yake ya fara fita neman kuɗi, dan ya
ayyana a ransa kuɗinta zai ranta ya fara sana'ar, har hango kansa yake ya zama wani
Alhaji.

Kullum firar da ita kenan, yau bayan ya gama complaint ɗin baya son wake, ya ɗasa
mata firar idan yayi kuɗi, ba aza a ƙara cin wake a gidansa ba.

Namra ta yi murmushi tana mamakin yadda idom Asim ya bude haka.

“Asim kenan. Idan ma zaka yi roƙon baka cewa Allah ya baka halalinka, kawai dai kai
kayi kuɗi”

“Wallahi sai na yi kuɗi Namra, Wallahi Wallahi sai nayi kuɗi, kawai naji sauƙi ne”

»“Ban ce ba zaka yi kuɗi ba, Amman yana da kyau ka riƙa cewa Inshallah kuma ka riƙa
roƙon halak, saboda gudun sherin zuciya, idan Allah ya rubuta zaka yi kuɗi zaka yi
ko da kuwa kama kwance gida ne sai sun tararda kai, saboda an riga an rubuta zaka
yi kuɗin sai dai idan kayi gajin haƙuri zaka iya samun ta hanyar da be kamata ba”

“Namra kina bani mamaki, ke yanzu da ba dan kuɗi ba iyayen ki ai ba zasu wulaƙanta
ni ba”

“Wulaƙanci kamar ya?”


“Wulaƙanci ne mana, saboda an mai dani talaka wanda ba shi da amfani shiyasa aka
saka miki wannan robar ba tare da sanina ba”

“Ba haka bane, kawai matsala ce ta taso kuma likitan yace dole ne nayi planning”

“To Allah ya kyauta, amman ko ma minene ai nafi kowa kusanci da ke, taya za'ayi ki
yi min haka”

“Asim matsala ce fa kai yanzu kana son na samu ciki ya zo ya zube ko kuma nayi ta
wahala?”

“Hmm kina dai ganin kamar ba zan iya hidama dake ba ke da abunda zaki haifa shiyasa
kuka ɗauki wannan matakin”

Ta aje kofin ruwan dake hannunta

“Ba zan ɗauki halin nan naka ba Asim, babu yadda zaka riƙa cin zarafina dana
iyayena, kullum mune marar mutumci a idonka, duk abunda muka maka baka gani, na
sadaukar da yawa Asim, har inda be kamata na sadaukar ba na sadaukar amman baka
gani”

Kamar mai jira sai kawai yayi cikinta da masifa.

“Me kika min ke da iyayenki? Me kika sadaukar min? Ran ki? Ko lafiyarki? Kullum da
kin tadhi magana kin sadaukar kin sadaukar tun da na aure ki me na ƙara shi in ɓa
tsiya ba? Ɗan abunda na tara dik ya ƙara na zo na kwanta a asibiti jiyan babu wani
ɗan'uwanki da ya ɗauki wani abu ya ba ni, an so na mutu ban mutu ba shine yanzu
zaki fara buɗe min wani babin na rayuwa, kina da kuɗi a jikin ki amman saboda baƙin
ciki ba zaki fitar aci ba sai dai a mutu? To Wallahi Asim ikon Allah ne, duk wani
mai son ganin bayana sai dai ni naga bayansa”

“Magana kake irin wannan zancen kamar mai magana da maƙiyansa, maitarka ta kasa
ɓoyuwa har sai ta fito fili? Kuɗina sana'ah zan yi da abu na, dan ba zan zauna
kullum ni ce biyar dangi a bani ba, kuma Allah be ɗora min alhakin ciyar da kai ba,
ni aka ce ka ciyar ka tufatar, yanzu ka fito a siffar ka sak Asim daman dan dukiyar
gidan mu ka aure ni ko, amman sai ka nuna mik baka son komai sai ni, ashe zagon
ƙasa kake min ka ɗauki halin samarin zamani ka ɗorawa kan ka, masu auren jari...”

Wani irin mahaukacin mari ya kifa mata ya rufe ta da duka kamar ma dukan namiji.
Shuri yake aika mata ta ko'ina tana cigaba da dukan jikinta kamar ƴarsa.

Dukanta yayi sai da yaji ya daki iya kalaman data faɗa masa sannan ya sassauta mata
ya miƙe tsaye yana ɗingishi.

“Kuma Wallahi kije aci miki wannan robar ko kuma wallahi na lahira ya fiki jindaɗi”

A fusace ya juya ya bar ɗakin. Kuka tayi har ta gode Allah sannan ta tashi zaune
tana cigaba da hawaye.
Sai ynz take tabbatar da tayi kuskuren aure, ta auri mutumen da be san darajarta
ba, mutumen da be san kowa ba sai kansa. Daman haka halin Asim yake abu kaɗan sai
duka.

Ta share hawayenta dan itama kanta tasan ba kuka bane abunda take buƙata, sam Asim
be cancanci hawayenta ba, a yanxu ta san wa take aure dole ne kuma ta shirya zama
da shi. Bata da buƙatar kokawa kowa damuwarta ita ya kamata ta gyara zaman aurenta
da kanta.
Ta tatsu iya tatsuwa dan haka yanzu ba zata sake bari guminta ya zuba akan Asim
ba.
ASIM POV.

Ta ƙarfen dake hannunsa yana dafawa ya fito gate, sai huci yake kamar wani zaki.
Yau ji yake kamar ace ya rumtse ya bude ya gansa yayi kuɗi, ta yadda zai jidaɗin
rayuwarsa. Sai yanzu yake nadamar karatunsa daya bari daman can yayi tunanin ko zai
samu wani abun a gurin iyayen Namra shiyasa ya baro garin su da ita ta yadda nan
zai ta cin karensa ba babbaka sai yayi ta aikata tana samu matsa kuɗi, amman yanzu
ya fahimci itama maƙetaciya ce kuma bata sonsa da alheri.
Gashi yanzu ko sana'ah zai yi yasan ba zai samu kuɗi a tashi ɗaya ba, amman idan
yana da karatunsa zai iya samun babban aiki.

“Mtssssss aiko karatun na yi ba aiki zan samu ba tun da nigeriyar sai da gata, su
kuma waɗannan iyayen nata matsiyata ne ba aiki za su samomin ba, aiko wallahi duk
wahalar da zan sha tare da ƴar su zan shata, sai na yi kuɗi tana ganin zata huta
kawai na aikata gidan su.
Har ni za'ayi ma mugunta, ai ko sai na yi muku baƙin ciki dan haihuwa yanzu za a
fara”

Ya ƙarasa maganar yana kallon Mardiya data doso gurin tana takawa a hankali. Tun
daga kan ƙafafunta yake kallonta har zuwa fuskarta.
Shi dai kam yana son farar mace ko ba komai farar mace ko kallonta kawai kayi zata
burgeka kuma zakaji kana son ta.
Tsaɓanin Namra da take black beauty, wace yake ganim a yanzu she's not his type,
sai dai duk da haka ya ƙudiri aniyar sai ya kai ga jikin cos he need someone near
him.
Ba zai je ya kashe kanshi da desires ba, weather blood ɗin ya tsaya mata ko be
tsaya ba babu ruwansa yau zai yi yadda yake so da ita.

“Ina wuni”

Mardiya ta gaisheshi cikin ƙirsa da kisinsina. Shi kuma ya amsa mata a far'ah har
kunne.

“Lafiya ƙalau Mardiya ya gida”

“Lafiya ƙalau ya jikin na ka?”

“Alhamdulillah”

“Allah ƙara sauƙi”

“Amin na gode”

Da kallo ya bita har ta ɓace masa da gani sannan ya dawo hanyyacin yana yaba
kyauwon surarta a zuciyarsa.

KALSOOM POV.

Ita kanta yanzu ta rasa gane kanta balle Hilal da yanzu ya saka mata ido, dan duk
ta barkace masa abu kaɗan masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.
Da gangan zata ƙi masa girki ko kuma tasa shi gaba tayi masa kuka, bayan be mata
komai ba. Tun daga lokacin ya fahimcin akwai abunda yake cikin matarsa, daman can
sha'anin ɓacewar cikin nan nata ya bashi mamaki, ga kuma jinin daya ƙi tsaya mata
wajen wata huɗu kenan, babu irin maganin da be bata ba amman abun be tsaya ba, tun
yana ganin abun kamar wasa har ya fara tsorota da lamarin.
Ita kanta tasan yanzu wannan jinin ya wuce haila ko zubar ciki ya zama na rashin
lafiya, kuma ta san hukunci mai jinin rashin lafiya.
Shi kuma jinin rashin lafiya, jini ne da yake zuba ba a lokacin al'ada ba, daga
wata jijiya da ake kira da azil. Al'amarin wanda take wannan jinin yana da
rikitarwa, saboda kama da jinin haila yake. Idan mace ta zanto jini yana zuba daga
gareta jo yaushe, ko kuma a mafi yawan lokaci wanenen zata ɗauka jinin haila da na
rashin lafiya? Domin ita mai jinin rashin lafiya hukunce mai tsarki na gareta, kuma
irin wannan hukumci shine a gurin mace mai jinin planning irin wanda yake zuba idan
anyi planning dan ya zama kamar jinin rashin lafiya.

*Hali na farko* Ta zanto tana da masaniyar kwanakin hailarta, kamin jinin rashin
lafiya ya same ta. Misali idan tana jinin haila a kwana biyar ko takwas a farkon
wata ko tsakiyarsa, watau tasan kwanakin hailarta da lokacinta. To ita wannan zata
zauna gwargwadon kwanakin hailarta ta bar sallah da azumi ta bawa kanta hukunci mai
haila. Idan kwanakin sun wuce sai haila sun wuce, sai tayi wanka tayi sallah ta
ɗauki jinin da ya cigaba da zubar mata da zuba a matsayin jinin rashin lafiya.
Dalili shine faɗin Annabi S. A. W, ga Ummu Habiba : ki zauna gwargwadon kwanakin da
hailarki take tsare ki, sannan ki yi wanka ki yi sallah. Muslim ya ruwaito shi. Da
kuma faɗarsa Annabi ga Fatima Bintu Abi Hubaish: Wannan jinin jijiya ne, ba haila
ba ne. Idan hailarki ta zo sai ki. Bar sallah. Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.

Idan iyakar kwanakin hailarta ya zo kamar yadda bayani ya gabata, to wajibi ne a


gareta tayi wanka. Kuma wanke gabanta domin ta gusar da abinda yake zuba yayinda ta
zo yin kowace salla. Kuma tayi ƙunzugu da auduga (pad) ko abu mai kama da ita wanda
zai hana kwararar jinin, sannan tayi alwala daga lokacin kowace salla saboda faɗin
Annabi : Ta bar salla a cikin kwanakin hailarta, sannan ta yi wanka kuma ta yi
alwala ga kowace salla. Abu Dawud da Ibn Maja da tirmizi ne suka ruwaito shi.

Hakan yasa Kalsoom ta cigaba da salla da duk sauran ibadarta, sai dai har gobe
halinta be canja ba a kan Hilal idan yana cikin gidan ji take babu wanda tsana a
duniya sai shi. Yara kuma abu kaɗan ta dake su, tun yana haƙuri har abun ya fara
isarsa dan yanzu shi da ita basa shan inuwa ɗaya, akan yaransa.
Gashi Ezzah kullum uwarta ƙara hure mata kunne take tana koya abubuwan da take
ganin kamar abun ƙwarai ne, bayan ita bata san tana lalata tarbiyar ƴarta bane
kawai.
Duk ranar da ba makaranta zai kwashi yaransa ya kai su gidan Hajiyarsa. Hajiya ta
lura da yanayin ɗanta damuwa ta bayyana a fuskarsa ga ramar dake jikinsa, yadda ma
yake yawan kawo yaran akai-akai ta san ba lau ba.

“Wai likita akwai abunda yake damun ka ne?”

Ajiyar zuciya ya sauke, yana aje plate ɗin abincin da ke hannunsa.

“Wallahi Hajiya ni ban san matsalar, daga ina take ba ma, Kalsoom ce yanzu kwata-
kwata na rasa ma gane kanta, indai ina gida bana da kwanciyar hankali, sai kuka
zara riƙa min tana masifa”

“Me ya haɗa ku?”

“Ba abunda na haɗa mu haka kawai zata riƙa min masifa sai kuka, kin san cikinta ya
ɓace”

“Ya ɓace kamar ya?”

“Jini kawai ta ga yana mata zuba, sai aka yi hoto aka ga babu cikin kwata-kwata a
cikin ta, amman jinin har yau be tsaya mata ba, yau kusan wata huɗu kenan”
“Subhanallahi, me ya same ta haka ne?”

“Wallahi nima van sani ba? Na rasa gane kanta”

“Abun kamar lamarin iska shi kesa ciki ya ɓata, ko kuma sihiri”

“Sai maganar saki ta ke min, ita dai na rabu da ita na ta huta”

“Kasan me? Ka samu ƙwarya mai tsarki da za'afaran, sai a ruɓuta suratul Yasin da
surar wa'ƙia da fatiha da ƙulhuwallahu ahad da ƙula'uzai da Ayatul kursiyu da kuma
amanar rasulu har zuwa ƙarshe da suratul baƙara da ayar : ƙul-a-Allahu azine lakum
am alallahi taftarun (10:59) to idan an rubuta sai a karya kummallo da shi idan ta
sha sai ta samu dabino ajwah sai kayi mata tawada nan da Al-zaitul muraƙƙa sai ta
cinye sauran kuma rubutun kuma ta shafe jikinta, da iKon Allah indai sihiri ne ko
aljanu ko wane iri ne zai rabu da ita”

“Amman Hajiya irin wannan ai sai dai kisa waki ya rubuta mata a nan sai na kai mata
ta sha”

“To zan nemi wanda zai rubuta mata inshallah, amman wannan ko Rashida ai zata iya
ƙulle-ƙulle ganin ta ɓata zamanku”

Yayi ƴar dariya.

“Sai dai ko iska ne, amman ai Rashida bata da irin wannan halin”

“Hmmm Hilal ba a shedun mace, yanzu kasa ran tayi maka wannan abun?”

Yayi shiru yana nazarin maganar Hajiya.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: »»4»»»»»»8»»»»»»»»»

ABDOOL POV.

Ɓacin rai ne shimfiɗe a fuskarsa, idanunsa sun rine zuciyarsa har wani tafarfasa
take saboda faɗan d Mai Martaba yake masa.
Har Mai Martaba yayi ya gama Abdool be ce uffan ba, dan yasan akan gaskiya yake
faɗansa, kamar yadda Ummi take masa a kullum.

“Ƙanen ka Babana ƙanenka ace yayi aure har ya haihu kai ba kayi ba, kullum girma
ƙara tunkararka yake amman baka ganewa, shekarun tafiya suke Babana yanzu da ace
kana da mata da wannan abun zai faru da kai? Sai dai ka zauna a gida ta girka maka,
ko mutuwa kayi ba mu da abunda zamu kalla mu tuna da kai sai hoton ka, ai ko mutuwa
kayi ka bar mai maka addu'ah ka more, rashin auren nan naka yana damuna Babana,
kuma kullum faɗa ake maka amman kamar ba'ayi”

Till now be ɗaga ido ya kalli Mai Martaba balle ta ce wani abu, shi kansa yana da
buƙatar auren, sai dai matsalar bayan Namra be ga mace da ta kwanta masa ba, sannan
be son ya auri mace da baya so gudun karya tauye mata wasu haƙoƙa nata, dan wanda
yake so baya jin zata samu enough time nasa balle wacce baya so.

Hullar uniform ɗin dake jikinsa kawai yake taɓi yana sauke ajiyar zuciya.

“Ba na son cilasta maka auten wacce baka so, shiyasa nake ta ɗaga maka ƙafa ina
baka lokaci, amman ka ƙi ka gane”

“Mai Martaba ka gafarce ni, ina nan ina ta addu'ah Allah ya bani matar da nake so”

“Allah ya baka, amman karka zarge ni da abuɓda zan maka nan gaba”

Har ya miƙe tsaye be kalli Mai Martaba ba, dan baya son Mai Martaba ya ga ɓacin
ransa.

“Zan tafi, Allah ya ƙara maka lafiya”

“Yau ba za'ayi min fira ba kenan ko? Tun da nayi maka faɗa?”

Ya ɗan murmusa

“Ba haka bane, kana yawan faɗa min na kula da kai na, kuma yamma tayi i want to
spend time with Ummi, dan gobe zan koma”

“Ai daman na san ita take ƙara goya maka baya kana fatali da maganar auren nan”

“Ba dan wani abu ba da sai na ce tama fika damuwa da lamarin auren nan”

“Kuma ba kayi komai a kai ba?”

“Zan yi inshallah, a ƙara min lokaci”

“Allah ya kiyaye hanya”

Ya ɗan risina kamar yadda yake masa.

“Na gode Mai Martaba”

Sannan ya juya ya nufi ƙofar fita, a bakin ƙofar ya tsaya ya saka Army shoes ɗinsa
dake gurin sannan ya shiga cikin gidan sashen matan sarkin yayi musu sallama ya
fito.

Kuɗin dake aljihunsa ya ciro ya miƙawa mutanen dake zageye da motarsa, sannan ya
shiga motarsa boys ɗinsa suka shiga wata motar already wasu na cikin motar sake
gaba sai kawai suka kama hanyar gida.

Sai da ya fara shiga part ɗinsa yayi wanka ya canja tufafi sannan ya nufo part ɗin
Ummi.
Sisters ɗinsa ya samu falon tare da friends ɗin su, cikin murna suka tarbesa, sai
ya gaisa da Friends ɗin su sannan ya nufi ɗakin Ummi.

Zaune ya tararda ita ƙasan carpet hannunta riƙe da qur'ane tana karatu. Kusa da ita
ya zauna yana sauraren ƙira'ar nata har sai da ta kai ƙarshen suratul Maryam sannan
tayi addu'ah ta shafa, ta aje qur'ane a gefe ta cire gilashin idonta ta kalli ɗanta
tana murmushi.

“Soja wuta soja”

Yayi dariya yana shafa dogon hancinsa.

“Uwar soja ma soja ce”

“So ya hanya?”

“Alhamdulillah”
“Ka ci abinci”

“Eh na ci tare da Mai martaba”

“Can ka fara biyawa kenan?”

“Eh kuma na sha faɗa akan mganar aure, Mai Martaba be gajiya”

Ummi tayi murmushi irun nasu na manya tana kallon ɗan nata cike da so da ƙauna.

“Kai ma ai baka gajiya da faɗan shiyasa kaƙi kayi auren ka huta, amman Abdool bana
son kana cin abincin mutanen”

“Ummi ki daina zargin komai, yanzu ba kamar da bane, suna sona sosai”

“Ba lallai bane ka iya gane haka, ai maƙiyin ɓoye baya taɓa nuna maka baya son ka,
kuma dik wanda ya ƙi ni to kai ma zai iya ƙin ka you have to be very careful”

“Na kan yi bismillah idan zan ci, kin san ko minene idan ka yi bismillah ba zai
taɓa samun ka ba, kuma ina addu'o'i sosai musamman da safe, kuma kin san irin
addu'o'in da nake musamman laƙada ja'akum wace idan aka karanta mutum ma ba zai
mutu ranar ba, saboda tsananin tsarinta, idan har zaka mutu a ranar yo Allah ba zai
baka ikon karantawa ba, ga a'uzu bikkalimattillahi”

“Hakan yana da kyau, nayi tunanin ko baka samun time ɗin addu'ah ne saboda aikin
ka”

“Komai nauyin aikin na na kanyi sai dai ba dika ba, amman dai bana tashi ba tare da
nayi addu'o'in tsari ba”

“Allah ya ƙara tsare ka”

“Amin ya rabb”

“Ina labarin yarinyar nan an sallame ta?”

“Ni na hana su sallame ta da tuni sun sallame dan taji sauƙi sosai”

“Ni abunda na ga yafi karka bar yarinyar nan ta koma cikin ƙazamar rayuwa, ya
kamata kayi wani abu a a kai”

“I try my best naga ta koma gidan su amman ta ƙi, ta tsaya kai da fata ita ba zata
koma gida ba, wai ji take kamar idan ta koma mutuwa za ta yi, ni kuma ban san
abunda zan mata ba”

“Why not ta zauna da mu kamin hankalinta ya kwanta sai mu mai da gida gurin
iyayenta”

“Kawai yarinyar bata kwanta min bane, ta taɓa zubar da ciki, kuma kin ga ta zauna
da mutane ƴan iska kala kala, kar tazo ta ɓata mata tarbiyar Sisters na”

“Ba zata ɓata ba, sai dai su su gyara mata tarbiyanta, she deserved everything
Abdool dik wanda ya sadaukar da ransa dan kana ya rayu ya cancanci komai a gare ka,
a yanzu bata da gurin zuwa kuma idan har muka bar ta ta koma cikin wacan rayuwar
kamar ba mu mata adalci ba, :sannan ka bincika an tabbatar maka da gaske guduwa
tayi daga gidansu, ai ya kamata ace kayi wani abu akai na ganin kaima ka maida mata
farinciki a zuciyarta ”
“Amman Ummi har yanzu babu tabbacin abunda yasa ta gudu”

“Ai kasan ita da iyayenta ba zasu fito su faɗawa duniya dalilinta na guduwa ba, ya
zaka ji idan aka ce ɗaya daga cikin ƙannen ka ne? Put yourself in my shoes zaka ji
irin abunda ko wane uba ko uwa take ji”

Ya sosa kansa yana miƙewa tsaye.

“I will think about it, lemme go and pray”

Daga haka yasa kai ya fice ɗakin.

RASHIDA POV.

Kusan kullum sai ta yi waya da malamin nan ko kuma nace boka, amman labari ɗaya
yake bata, cewar Hilal da Rashida basa zaman lafiya, kuma har gobe jini na nan yana
mata zuba.
Sai da ita bata da tabbacin hakan tun da bata ji wani motsi daga garesu ba, dan
har yanzu bata ji ya saki Kalsoom ba, kuma Ezza tana yawan faɗa mata ita bata ganin
suna faɗa har sai idan ta dake ta sannan Daddy ta yayi faɗa.
Izzah bata da labarin komai da yake faruwa tun da Hilal baya faɗa da Kalsoom a
gaba idonta, ko lokacin da Rashida take gidan idan zai yi mata faɗa ba yayi a gaban
idon yaransa gudun abunda zai je ya dawo. Balle kuma.Kalsoom da baya biye mata dan
ta fahimci bata cikin hankalin kanta duba da yadda abubuwan da take masa a.yanzu
abunda be tsammaci zata masa ba, kuma baya tunanin kishi ne da sai dai ta nuna
jindaɗinta akan barin gidan da Rashida tayi ta ƙara mallakarsa, sannan Hajiyarsa
tana yawan tunasarda shi akan ya kawar da idonsa gareta, duk wani abun da zata yi
ya riƙa sa mata ido.

Tana yawaita bibiyar shafinsa na facebook da instagram da whatsapp, wai ko zata


gano idan hankalinsa ya karta kanta amman sai ta ga tsaɓanin hakan, dan har text
take masa amman baya mai da mata amsa daga ƙarshe ma sai ya saka ta a blacklist.
Yau kam ta kuɗiri aniyar tura Asmee dan ta binciko mata irin zaman da suke, tun
da ta san Kalsoom ta yarda da Asmee kuma zata iya bugun cikinta dan ta ji
labarinta, idan ma suna zaman lafiya ko a yanayin fuskarta zata iya karantar hakan.

A gogon ɗakinta ta kalla taga 10:36Pm, ba laifi dare ya ɗan fara sai dai hakan be
hana ta janyo wayarta ta kira line Asmee ba.

“Ƴar gari... Yanzu ko na ke maganar ki da Oga”

“Uhmm gulmata kuka yi kenan?”

“A'a Wallahi kawai yana yabon halin ki ne, wai duk yadda kike da haƙuri ace Hilal
ya sake”

“Ke dai bari, ai sherin kishiya sai Allah, ni so ma nake kije gobe ki bincika min
gidan nan, ya zamantakewar su yake”

“Zan ko miki haka, nima Wallahi ina son zuwa dan naga idon munafukar”

“Da Sassfe zaki je dan Allah lokacin da Hilal.yake gida”

“Karki samu matsala Asmee ce fa ƙawarki”

“Na gode ki gaishe da ogan na ki”


“Zai ji mu kwana lafiya”

Rashida ta kashe wayar tana kallon ƙanwarta Safiya dake tsaye jikin ƙofa riƙe da
littafi.

“Shigo mana kika tsaya bakin ƙofa kina kallona”

Ta shigo tana ɗan murmushi

“Wallahi Anty ni jikina duk a mace yake”

“Saboda me mutuwa aka yi?”

“A'a, kin san mun fara zuwa asibiti yanzu...”

Ta ɗan yi shiru tana tunanin ƙarasa zancen, dan tana jin nauyin karya alƙawarin
data ɗauka a asibiti na cewar ba zata faɗawa kowa wanda ta gani ba, idan ta shiga
sashen masu hiv da sarin tb.

“To shine nake neman addu'ah, idan mun gama zamu fara exam”

“To Allah ya taimaka ya bada sa'ah, nima ina son ki min addu'ah Allah ya maido da
hankalin mijina gare ni”

“Adda Rashida kenan, kina damuwa da abunda be kamata ki damu da shi ba, mijin daya
juya miki baya meye na addu'a ya dawo gareki, bayan ya ci zalinki?”

“Ba a cikin, hayyacinsa yayi min ba, kin fi kowa sanin yadda Hilal yake so na,
kawai sherin Kalsoom ne magani tayi masa, yanzu haka ma su Ezza basa jindaɗin zama
da ita, so take ta kore kowa ta mallaki gidan”

“Kada Allah ya bata sa'ah, kuma wallahi indai mugun nufinta kenan sai ta ga abinta,
ai karka bi mutum da sheri ka bar shi ya bika da sherin abun zai koma kansa”

“Ba zan bata damar haka ba, Safiya bata isa ta shiga gidan dana shekara ina ginawa
ba a rana ɗaya ta rusa min kuma ta kore min ƴaƴa ta mallake min miji sannan na bar
ta”

“Ki ƙyale ta ki bar ta da Allah, idan ma wani asirin ne tayi miki Wallahi zai karye
zata dawo nadama lokacin da bata da amfani”

»“Haka ne Allah ya shige mana gaba”

“Amin dan Allah ki ma daina sa ran ki a damuwa”

“Ina nan ina addu'ah komai zai dai-daita inshallah”

“Allah yasa, sai da safe”

Safiya ta miƙe tsaye ta fice zuciyarta cike da tausayin ƴar'uwarta. Rashida kuma ta
sauke ajiyar zuciya tana busar da iskar bakinta. Lallai tana ji a zuciyarta, ba a
banza Hilal ya barta ba, dan tasan yadda mijinta yake son ta dan kawai ya gano tana
tare da wani be isa yasa ya sake ta ba, tasan da ada ne da komai tayi ba zai rabu
da ita ba.
Sai dai abunda har yau bata sani ba shine, daga lokacin da mijinki ya gano kina
mu'amala da wasu a waje tun kin fita daga ransa kenan indai ya san kansa, kuma
komai irin son da yake mki ba zai sake ganin darajar ki ba.
NAMRA POV.

Yau ta farka da baƙinciki da kuma tunanin mafita dan samawa kanfa ƴanci.
I zuwa yanzu ita kaɗai tasan abunda take ji a zuciyarta, idan ta soma tunani har
numfashinta yake yin sama, tsabar baƙinciki da damuwa.

Dole ne taje a cire mata robar nan, dan ba zata iya da rikitarwar da jinin yake
nata ba, kuma ga matsalar Asim da yanzu babu ruwansa da matsalarsa haka zai yi
forcing ɗinta ya yi yadda yake so da ita.
Irin yadda yake mata Allah ya isa akan rashin cire robar da bata yi abun har
mamaki yake bata, kamar ba mijinta ba, ko kuma wanda be san addini ba, abu kaɗan
zai mata Allah ya isa, ga yawan kusheta da yake, shi dai kullum ya fi son ya ganta
a cikin damuwa da baƙinciki.

Ba laifi yanzu dan ya ɗan fara fita, har ya koma aikinsa na ƙira da suke da Ƙanen
Babansa, sai dai naira ba zai cire ya bata ba, da sunan ta siye abinci balle
cefane, babu ruwanshi da matsalarta, sai dai ita tayi cefane kuma haka zai zo ya
zauna ya ci dan bashi da kunya. Ita kuma har yanzu bata yi ƙarfin halin da zata iya
hana shi abincinta ba.

“Idan na yi kuɗi, zan auro mace mai kyau mai tarbiya”

Sune kalamansa a kullum kuma sune kalaman da suka fi ƙona zuciyar Namra, a yanzu ne
take ƙara tabbatar da son Asim be gama fita zuciyarta gaba ɗaya ba.
Ta maida hankalinta sosai gurin siye da siyarwa, na kayan aiki abinci like magi
manja da sauran kayan miya, ba laifi ana siye sosai dan a unguwar ita kaɗai ce take
wannan sana'ar hakan yasa ta sabo da mutane har ta buɗe islamiya tana ɗan karantar
da su abubuwa game da addini da kuma ƙur'ane.

manage it please.....
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: ~4»»»»9»»»»»~

AMIRA POV.

Ta fara sabawa da Abdool cikin ƴan kwanaki ƙalilan ya shiga ranta, har matsuwa take
ya zo ya ganta, dan kullum sai ya zo da safe ya duba ta, da rana ma ya kan zo idan
baya da aiki, haka ma da dare sai yayi mata sallama sannan ya wuce gida.

Ta karanci abubuwa da yawa a rayuwar Abdool tun daga yanayinsa na rashin son magana
da kuma shisshigi, ba kasafai yake dariya ba, ko murmushi sai idan ta kama ne yake
yi.
Sai dai hakan be hana annurin fuskarsa bayyana, ya kan mata kwarjini sosai idan
ta kalleshi. Sai dai har yanzu matsala ɗaya ce tayi mata tsaye a rai nasa, rashin
sakewa da yake da ita, sannan idan zata shekara tana kuka ba zai iya bata haƙuri
ba, sai dai ya tashi ya bata guri. Lokuta da dama ta kam ƙirƙiri kukan ne dan ya
tausaya mata amman bata taɓa ganin alamun tausayinta a fuskarsa ba.

Wata ƙila baya da tausayi ne, ko kuma ba shi da kula da lamarin wasu, a yadda ta
karanci rayuwarsa kamar ma yana kula ta ne by force.
Abu ɗaya zuwa biyu take ta ƙoƙarin yaƙar zuciyarta akansa, faɗuwar gaban ta take
samu idan ta kalleshi, da kuma damuwar da take shiga idan ta wuni bata sashi a ido
ba.
Sai dai har yanzu ta kasa, ɗan zuwan nan da yayi katsina ya kwana biyu ya dawo
ji take kamar shekara biyu yayi. Tunani take idan ya rabu da ita ya zata kasance? A
yanzu kam bata da gurin zuwa tun da Guy son ya mutu, kuma ta san Abdool ba zai
barta ta zauna a tare da shi ba, wanda ɗaga ido ma ya kalleta yake masa wuya balle
yayi mata masauki a inda yake.

Sai yanzu take nadamar abunda tayi ma Guy son, tabbas bata kyauta ba, dan me zata
butulcewa wanda ya ɗauki ɗawainiyarta, dan kawai ta ceci ran wanda kallon ma mai
tsada ne?
Lallai tayi kuskure kuma bata bi hanya mai ɓullewa ba. Ya kamata ta yaƙi
rayuwarta dan samawa kanta yan ci, taya zata bar Abdool ya tafi haka nan ya barta
ta dabon ciwo da kuma na zuciya, bayan duk akansa tayi wannan? Ashe bata cancanci
fiye da haka a gareshi ba? Sam bata ga alamar karaminci a tare da shi ba, sam be
san darajar ɗan'adam ba, ya kamata ace a iya zaman da tayi yayi ƙoƙarin kawar mata
da damuwarta, amman sai nuna mata halin ko'in kula yake mata, sai tambayoyin banza
da yake tsare ta da su wani lokacin.

Ta share hawayen idonta ta miƙe tsaye tana shafa kafaɗunta ta nufi window ɗakin
tana sauraren zance da zuciyarta take mata.

‘Idan kika na bar Abdool ya kuɓuce min, lallai nayi babbar wauta kuma na yi hasara,
taya zan ceci ran mutum kuma ya juya min baya? Ya kamata fa ya nemawa kai na ƴanci
haka na yi ta sake har Namra ta ci galaba a kaina, tun da har na butulcewa Guy son
dole ne na samu wanda zai maye min gurbinsa.

Sometimes ina abu kamar ba ni ba, zama da Guy son ya kamata ace na ko yi abubuwa da
dama, amman sai kasa gazawa nake, a yanzu babu kowa a kusa da ni, ya kamata ace na
zama mace. Amman sai kasawa nake, i will fight the spirit ghost of me, i will
surely be my own boss, i have to answer my own name’

Ta kai hannayenta ta dafa window, dan ta ji motsin shigowar mutum kuma ta san
Abdool ne dan shi kaɗai yake mata haka. Yi tayi kamar bata ji shigowarsa ba ta
ƙirƙiri hawaye, ta soma magana cikin sanyin murya kalar tausayi.

“Allah ka zama gata na Allah, bana da kowa sai kai, ya Allah idan mutuwa hutu ne a
gareni Allah ka karɓi rai na na huta, Allah na tuba ba zan ƙara ba”

“Ai ba haka ake tubar ma Allah ba”

Ya faɗa yana tsaye jikin ƙofa sanye da ƙananan tufafi, sai faman danna waya yake
kamar ba shine yayi maganar ba.
Juyowa tayi ta sauri ta kalleshi like bata ma san yana gurin ba. Be kalleta ba,
amman hakan be hana ta ganin ƙwajininsa ba saboda yadda tufafin suka karɓi jikinsa
suka masa kyau sosai kamar daman can dansa kawai aka yi tufafin.

Lumshe ido ta yi tana sauraren bugun zuciyarta, hancinta na shaƙar ƙamshin


turarensa daya game ɗaki, hawaye ne suka silalo mata.
Yadda zuciyarta take amsa irin kiran da Abdool yake mata ya tabbatar mata da
shine mutumen da take mafarki, shine burinta a duniya bata taɓa ɗora idonta akan
wani namiji taji abunda take ji akan Abdool ba, ita kwata-ƙwata a rayuwartaa bata
taɓa mutumen da take so ba sai Abdool, duk wanda zata so sai dai ta soshi dan
kuɗinsa ko kuma da wani abun na dabam.

Amman tana jin Abdool ko bashi da komai zata iya zama da shi, ballantana ma ya haɗa
komai da ake so ga namiji, a rayuwarta bata taɓa ganin kyakkyawan mutum kamar
Abdool ba, sam be yi kama da ƴan nigeria ba. Ga tarin dukiya da kowa wacce mace
take so a gurin Namiji, ga shi kuma ɗan Sarki wata rana zai iya zama sarkin gaba
ɗaya.

“Da ace hawaye za su miki magani da sun miki tuni, kuma tun lokacin da kika saka
ƙafarki kika bar gidan ku ya kamata ace kin yi kuka kin dawo sai yanzu? Lokacin da
nadamar ki bata da amfani, do you know what? I don't believe in fiction, idan har
da gaske kin yi nadama ya kamata a ce yanzu kin kama hanyar gidan iyayenki”
Yayi mata maganar ne from the bottom of his heart, like he's seriously saying what
is inside him, daman can shi ba mutum ne mai tausayin mace ba, indai zaki shekara
kina kuka Abdool kam ko a jikinsa, wata ƙila dan ba shi da lokacin matan ne, ko
kuma dan har yanzu idanuwansa basu ga zubar hawayen wacce zuciya take muradi ba.
Sannan shi sam baya ganin tausayin ko kuma mutucin yarinyar da ta bar gaban
iyayenta, da ma ace korarta suka yi ba ita ta gudu ba.

Babu yadda Amira za ta yi da shi duk da kalamansa sun taɓa zuciyarta, ta daɗe da
karantar be iya lafazi ba, kuma babu ruwansa da tauna magana idan zai faɗa.
Sai dai hakan be sa taji haushinsa ba ko kuma ta ji ta tsane shi, sai kusanci da
shi take so, dan ta koya masa yadda zai zauna da ita.

“Amman idan na koma da wane ido zan kallesu?me zan ce musu? Ya kake tunanin duniya
zata kalle ni?”

“Tun kamin ki baro gidan ku ya kamata ki yi ma kan ki wannan tambayar, idan kika
gudu me zaki ce musu? Da wane ido zaki kallesu? Ya kuma duniya zata kalle ki?
There's no point of crying dan ke kika sai da mutunci da hannu ki”

Wani irin kallo ta watsa masa da jajayen idanuwanta, sai dai kwarjininsa be barta
ta masa kallon daƙiƙa biyar ba ta kau da idon, cikin kakkausan lafazi ta ce .

“Amman mi yasa baka bar ni na mutu ba? So that na huta da rayuwar gaba ɗaya?”

Ya gyara tsayuwarsa ya ɗaga daga jikin ƙofar da yake tsaye yana sa hannayensa
aljihu.

“I'm sorry I'm not harassing you I'm just telling the truth”

Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalleta.

“Park your things, Doc zai baki sallama, around 10am driver zai kai ki gida”

Be tsaya jiran abunda zata ce ba yasa kai ya fice. Rasss! Rasss! Rasss! Gabanya ya
yanke ya faɗi.

“Wane gida? Gidan su ko gidan mu? Ko kuma wani gidan na dabam?”

Ta tambayi kanta, dik sanyin ɗaki be hana gumi zubo mata ba. Babu inda ya fi tsaya
mata a rai a kamar gidan su. Wayyo Allah ji take kamar mutuwa za tayi idan har aka
maida ita gidan su, ita kanta tana son zuwa gidan amman bata iya iyawa, bata san
dalili ba.
Ta kasa sukuni sai safa da marwa take har Doc ya shigo ɗakin, bata ga alamun rahama
a fuskarsa ba balle ta tambaye ko yasan inda Abdool zai kai ta, kai ba zata iya
tambayarsa ba kar Abdool ya zargi wani abu.

Sai kawai taja bakinta tayi shiru, sai dai tasha alwashin indai gidansu ne ba zata
taɓa zuwa ba sai dai komai zai faru ya faru.
Sai da likitan yayi mata binciken ƙwa-ƙwaf sannan ya rubuta takardar sallama ya
miƙa mata, ya fice. Kamar yadda Abdool yace 10 na bugawa sai ga wani yazo cikin
uniform ɗin soja yace mata ta fito suje. Nan ma sai da gabanta ya faɗi.

“Ina... za...mu....je?”

“Katsina yace a kai ki, gidan Mahaifiyarsa”

Ta lumshe ido na wasu ƴan daƙiƙu, wani irin daɗi ya ziyarci zuciyarta har ta samu
maida yawun daya tsaya mata a maƙoshi.
Bata buƙatar ɗaukar komai, daman can duk kayan da tayi amfani da su shine ya
kawo mata, dan ita ko waya bata da a hannunta balle wani kayan kuma. Farincikin
dake zuciyarta ya kasa ɓoyuwa har sai da ya nuna a fuskarta.

Ko da ta fito Abdool na tsaye kusa da motar, da alama ita yake jira, sai dai kwata-
kwata hankalinsa baya gurinta yana wani wajen dabam.
Ɗaya daga cikin boys ɗin sa ne ya buɗe mata mota ta shiga, idonta na kan Abdool.
Yayi kusan minti biyar yana magana da mutanen biyu sannan ya suka shiga motar da
take sai kuma wata mota dake gabansu cike da sojoji suka kama. Shi kuma ya juya ya
koma cikin.

Juyawa tayi ta cikin motar tana kallonsa. Tana ayyanawa kanta zama abokiyar
rayuwarsa, dan wannan karamcin kawai da yayi mata ya isa yasa tayi sha'awar hakan.
Mutum me daraja da ƙima kamar wannan? What if ta zama matarsa?

KALSOOM POV.

Tun daga lokacin data fara shan rubutun da Hajiya tasa aka mata, sai ta fara jin
sauyi a jikinta, sai mafarkai take wasu ma har bata san kansu ba.
Natsuwar da take ji a yanzu, yana kan tunatar da ita rayuwar rikicin da ta yi a ƴan
watanin nan, sai yanzu take mamakin kanta duk wacan abun da ta yi sai ya zama matar
kamar mafarki.
Lallai a yanzu ta tabbatar da ta yi wasa da addu'ah, dan bata iya addu'ah safe
balle kuma ta yamma da take gani kamar ba komai ba ce. Sai dai har yanzu bata jin
ƙarfin yin addu'ah kuma jinin be ɗauke mata ba, amman dai ta dawo normal kamar
yadda take, ba kamar baya ba da take jin abu na mata yawo cikin kai kamar tsutsa.

Da wuri ta tashi ta shirya musu abun karyawa, sannan ta tashi yaran duka tayi musu
wanka da kanta, Izzah ce kawai bata bari anyi mata ba, sai wani cika take tana
batsewa kamar wata babbar mace, ada tana yi a dole dan Rashida na sa, amman a yanzu
kan na gaske take dan har cikin zuciyarta take jin tsanar Kalsoom bayan kuma bata
mata komai ba, sai dai laifinta da take gani na kore musu uwa da ta yi, sannan tana
ganim yadda komai ta yi musu Daddy su ba ya magana.

Sai da Kalsoom ta shirya su tsab sannan ya tura su gurin motar Daddy su ta shiga
ɗan ta tashi mijinta.

A bakin ƙofar ɗakinsa ta tsaya ta buɗe maɓallin rigarta sannan ta kunna kai cikin
ɗakin. Hannunta tasa cikin gashin kansa tana wasa da shi, amman be motsa ba, badan
kuma be farka ba, sai dan daɗin da yake ji akan abunda take masa. Ganin be farka ba
yasa ta kwantowa jikinsa ta zira halshenta cikin kunnensa. Still be motsa ba amman
fuskarsa da murmushi alamar idonsa biyu kenan.

Hannu tasa ta matse masa hancin iya ƙarfinta, sai ya tashi ba shiri yana kallonta.

“K.e...”

Maganarsa ta maƙale lokacin da yayi arba da rigar bachinta dake buɗe. Rabon da ta
masa irin haka har ya manta, Kullum sai dai ya haɗe mata yawu, yau ma yasan haka ne
tun da jinin har yanzu be tsaya mata ba. Hannu ya kai ya laƙamo wuyanta.

“Let us enjoy ourselves...”

“No way, yara suna waje suna jiran ka”

Ya dafe kansa.
“Ya Subhanallah, gaskiya I'm tired of driving them to school”

Ta wara ido

“Then teach me how to drive!”

“No, ba zan bari ki yi driving ba, wani zai ganemin wannan kyakkyawar fuskar ba,
sai dai na nemo direbe, idan kin san inda zamunsamu direba mai natsuwa ki nemo
mana”

Ya yaye bedsheet ɗin dake samansa yaja kumatunta, ya sauka saman gadon ya shiga
bathroom. Bakinsa ya wanke da fuskarsa sannan ya fito. Tsaye ya same ta jikin
bathroom ɗin tana jiransa.
Ya ɗan risina kaɗan yayi mata kiss a baki.

“My Happiness”

Ta moɗe bakin tana hararsa irin na ma'auratan nan masu cike da shauƙin so.

“Ni kike harara?”

Ya kama kunnenta

“Ouuuch Doc it hurt”

Yana janye hannunsa ita tayi masa yadda yayi mata, ta fito falo da gudu shima ya
biyota yana murmushi.

Ganin Asmee yasa dik suka tsaya cak, musamman ita dake ƙoƙarin gyara rigarta.
Be ce da ita komai ba, har sai da ita tabfara gaishe shi sannan ya amsa ya nufi
ƙofar fita.
Kalsoom kuma ta koma ta ɗauki hijab tasa sannan ta fito falon cike da mamakin
sammakon da Asmee ta yi musu haka kamar mai biyar bashi.

Ita kanta taji kunyar kanta, ga kuma baƙinciki ganin da tayi suna cikin walwala,
dan tana taya ƙawarta kishi ne.

“Na doko muku sammako, kuna sha'aninku”

Kalsoom ta yi dariya.

“A'a nace dai Allah yasa ba bashin ki muka ci ba”

“A'a wallahi an kwana biyu ban zo ba shine nace bari na leƙo ki ban sirrin da kika
bawa mijin ki ya kori Rashida”

Kalsoom ta rufe baki

“A'a sirri kuma? Ai duk wanda kika ga ta bar gidan mijinta inda akan rashin ladabi
da biyayya ne to ita ce ta fitar da kan ta”

“Hmmm ba son ba mu sirrin dai ko, kin ga nima daman yara na kai scul shine nace
bari na leƙo na gan ki”

“Aiko kin kyauta, an kwana biyu a a gaisa ba”

“To ai ƙara ni ke ba ko zuwa kike ba”

“Ba ya bari ne, cewa yake baya son ina yawan fita”
“Aikam baya son ki yi nisa da shi, kin ga bari na tashi na wuce sai kin zo”

Har gurin motarsa Kalsoom ta raka ta tana bata haƙurin rashin zuwa da ba ta yi ba,
da kuma cewar zata zo idan Hilal ya barta.

ASIM POV.

Ba laifi yau kan yayi wanka ya shirya kansa, ko dan yana jumma'ah ne oho, da wanka
ma be dame shi sai dai yayi kanta karya ya fita idan fita ta kama shi.
Bayan sun sauko daga sallah jumma'ah ya nufi gurin aikinsa yana mai jin haushin
aikin nasa ace kullum sai ya yi zuga sannan ya samu ƴan kuɗin kashewa shi wannan
aikin dik ya takura masa, sai jan tsaki yake yana maganganu shi kaɗai.

Tun daga nesa yake kallon wata makekiyar mota data faka gefen gurin da suke aiki,
yana ayyanata a cikin jerin motocin da zai siya idan yayi kuɗi, dan kyawon motar ya
ɗauki hankalinsa sosai.

Yana buɗe shagon da suke aikin, mai motar ta zoƙe gilashin motarta tana masa
sallama.

“Assalamu alaikum samari”

‘Tab ashe ma mace ce’

Ya faɗa a ransa, a fili kuma sai ya amsa mata baki har kunne.

“Wa'alaikissalam Hajiya ina wuni?”

“Lafiya ƙalau, dan Allah masu aikin nan gurin nake nema za a gyara min gate ɗina
ne”

Ta faɗa cikin yauƙi da rangwaɗa kamar ba babbar mace ba.

“Mu ne ai muke aikin Hajiya, ina gate ɗin na ki yake?”

“Kai ...?!”

Ta faɗa tana nunasa da hannunta, mamaki ne ya isheta, yanzu tsalelen saurayi kamar
wannan ace aikin ƙira yake, dubi ko shigarsa fa.

“Okay ga kt na idan kun tashi aikin sai kuje gida ku yi min, gate ɗin be ɓalle bane
duka rabi ne za'a gyara min”

Ta miƙa nasa katin. Yasa hannu biyu ya karɓa cikin girmamawa kamar wata uwarsa.

“To Hajiya da zarar abokan aikina sun iso zamu je muyi aikin, sai dai baki bamu
time ba”

“Ga number waya na nan a jiki kamin ku zo sai ku kira ni”

“To Hajiya za mu zo inshallah”

Ya miƙa masa 5k

“Ga wannan asha ruwa”

Yayi taku tare da nuna kamar ba zai karɓa ba.


“A'a Hajiya ki bar shi”

“Bana mai da kuɗi idan ya fito jakana, so ka karɓa kawai idan ma watsarwa za kayi
sai ka watsar”

Yasa hannu ya karɓa yana mata godiya. Ita kuma ta tashi motarta ta kama hanya. Sai
da ta wuce ya kalli jikinsa.

“Ita kan ta ta ga ban yi mata kama da talaka ba, wallahi ni babban mutum ne”

Ya juya ya cigaba da buɗe shagon farinciki fal a ransa.

RASHIDA POV.

Ta kasa zaune ta kasa tsaye tun lokacin da Asmee ta labarta mata irin rayuwar
jindaɗin da Kalsoom take da Hilal. Kenan ita sun manta da duniyarta? Hilal ya manta
labarinta?

“Ina ba za'a shafe ni a tarihim rayuwarsa, ba zai rayu da wata ba sai ni, wata bata
isa ta mallake min miji ba. Amman malamin nan ko dai yaudara yake ne? Dan me zai ce
min magani yayi alhalin be yi ba”

Tayi shiru tana nazari, wata ƙila ita ma Kalsoom tana shige-shige shiyasa ta shafe
ta a zuciyar Hilal gaba ɗaya. Daman idan kana yin abu gani kake kowa ma haka yake.
Wayarta ta janyo ta kira lamanin dan bata jin zuwa can inda yake a yau tun da ko
aikin dake gabanta bata gama ba ma, balle ta yi tunanin fita, kuma tasan ko ta fita
kamin taje ta dawo dare yayi sosai.

Kiran farko be ɗauka ba, haka na biyu zuwa na uku, amman bata sarara masa ba, har
sai da ta jera masa kira kusan 10+ sai da yayi picking sannan hankalinta ya kwanta.

Sama-sama ta gaisa ta shi sai ta koro masa da bayaninsa

“Ina zuwa bari na binciki ƙasa”

Jimmm yayo shiru na ɗan lokaci sannan ya yi gyaran murya yace

“Lallai wannan matar ta sha gaban ki, ta fiki shiga bokaye, shiyasa wannan aikin be
yi wani dogon tasiri a gareta ba”

“Kana nufin aikin be kamata ba?”

“Ya kamata amman yana ƙoƙarin fita jikinta”

“Amman idan har ya kamata ai dole Hilal.zai damu, dan bashi da wata mata sai ita
kuma har yanzu ban ji ance sun samu saɓani ba”

“Amman ƙasa ta nuna mana an samu tsaɓani, sai dai idan kece baki sani ba”

“Yanzu malam miye abun yi?”

“Abu ɗaya ya kamata daman na faɗa miki, idan wannan be yi ba sai na biyu zuwa na
uku, dole ne mu haukatata idan kuma be yi ba sai mu yi mata halbin kasko”

Ta rufe baki. Rashin imaninta be kai can ba.

“Malam babu wata hanyar ne?”


“Gaskiya wannan ce kawai mafita indai kina son mijin ki, idan ta bar gida sai ki
samo sperm mu hada miki wanda Mijinki zai maida ke gidan sa dan dole”

“Zan yi tunani a kai”

“To yayi kyau”

Ta aje wayar tana busar da iskar bakinta.

NAMRA POV.

Yau kam basu fara karatun da wuri ba, hakan yasa har suka wuce goma na dare basu
tashi ba. Amman shigowar Asim yasa ta yi addu'ah ta sallami ɗaliban nata da mafi
yawansu matan aure ne.
Har gobe ba zata daina girmama Asim ba, tana bashi haƙƙinsa a matsayinsa na
mijinta, dan ta karanta ta gani, ta san irin girman da miji yake da shi ga matarsa,
ita dai kam ta kan yi ƙoƙarin ganin ta bashi dukanin haƙƙinsa dan tasan ko mutuwa
tayi sai dai idan shine ya cuce acan Allah ya yi musu hisabi.

Ƙarfe shida suke tashi daga gurin da yake aikin, amman baya dawowa gida sai goma ta
gota na dare, zaman majalisa yake irin zaman nan da baya amfanar da komai sai
zunubi da hassada, zaman zagin wane da wace, zaman matar wane tafi matar wane,
wacce aure ya mutu wacce biyar maza take. Kusan ma shine yaro a cikin masu zaman
majalisar dan duk sun girme shi dukansu magidanta ne.

Kicin-kicin ya shigo gidan baya ƙaunar kallon Namra, idan akwai wata maƙiyiyarsa
yanzu a duniya to Namra ce. Ita kam idan sabo ta saba dan yanzu ba kasafai take
ganin rahamar fuskarsa ba.
Tufafin jikinsa ya kwaɓe ya jefar saman katifar ya ɗauki wata guntuwar jalabiya
ya saka yazo ya zauna tsakar ɗakin yana kallon kyanɗir ɗin dake hasken ɗakin

“Ina abinci na?”

Ko rufe baki be yi ba ta dire masa abincin gabansa da ruwan sha, sannan ta ɗauko
mafeci tana masa fita, sai murmushi take tana masa fira dan kawar mata da ɓacin ran
dake tare da shi. Har ya gama cin tuwon ya sha ruwa be kula taba balle ya tanka ta
a firar da take.

Tsabar ƙazanta da rainin wayo cikin kwanon daya gama cin abinci ya wanke mata
hannu. Ita kuma ta ɗauka ta kai waje ta aje. Sai gata ta dawo ɗakin da gudu jin
wayarta na ringing.

Da murna ta ɗauka ganin number Anty daman haka take kullum kamar ba jiya tayi
magana da ita ba, zaka rantse kace ta shekara ba ta yi magana da ita ba.

Bayan sun gaisa Anty take faɗa mata za a kawo lefen Maryam cikin weekend ɗin nan
mai ƙarewa, ta kuma nuna mata tana son ta shigo ko dan kwana biyu da suka yi ba su
ganta ba, kwanki babu yadda Anty ba tayi akan ta zo amman Namra ta nuna mata karta
zo yanzu ta bari har gaba.

Da fargaba ta aje wayar dan tasan ba lallai bane Asim ya bar ta taje, amman a haka
ta sake fuska tana faɗa masa Anty ce ta kira.

“Okay”

Kawai ya faɗa irin ina ruwan ɗin nan. Ya hau saman katifa ya kwanta yana mata wani
kallo da ita kaɗai ta san kiran da yake mata.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *50*

AMIRA POV.

Har suka isa katsina babu abinda take tunani sai Abdool saƙe-saƙe kawai take a
zuciyarta na yadda zata sace zuciyarsa da kuma iyalansa.
Babu abinda take annawa a zuciyarta sai sabuwar rayuwar da za ta shimfiɗa na kanta.

Duk irin yadda take misalta arzikin gidan su Abdool sai ya ci gaban tunaninta, ya
sha banban da abinda take tsamani. Haka ta zaka kamar ba wacce ta fito daga garin
Abuja ba. Idonta ya biɗe sosai lokacin da motar da take ciki ta kunna kai cikin
gida.
Ga matakan tsaron daya shimfiɗa ma gidan kamar masaukin shigaban ƙasa. Part biyu
ta gani a gidan sai dai part ɗin da suka sauka ya fi girma da tsaruwa, hakan ya
tabbatar mata da wacan ɗin part ɗin Abbansa ne ko kuma nasa.
Tana fitowa motar idonta ya sauka kan wani ƙaton Garden dake gefen part ɗin, babu
abinda kake ji sai sautin kukan tsuntsaye, ga wani swimming pool da tafi ɗaukar
hankalin a hangen nata, daga ruwan swimming pool ɗin har itacen da suke gurin komai
kore ne. Peacocks sai kai da kawo suke a bakin Garden ɗin.

“Let's go Madam”

Ɗaya daga cikin sojan da suke tarar a gurin ya faɗa yana nuna mata ƙatuwar ƙofar
shiga falon, wacce ta kasance abun kallo, idan ba wanda ya sani ba sai kan rantse
kace da zinari aka ƙerata.

A hankali ta cira ƙafarta ta fara takawa, zuwa gurin ƙofar dake kashe mata ido
saboda kyawonta. Hannu ta kai zata buɗe ƙofar lokacin data ƙarasa sai kawai ta ga
sojan ya danna wasu numbers, sannan ya matsa gaban wata ƴar ƙaramar severity camera
yayi magana. Bayan kamar minti biyu sai ƙofar ta buɗe da kanta.
Ƙofar kawai ya nuna mata ya juya ya wuce.
Tun kamin ta saka ƙafarta falon wani irin ƙamshi da sanye suka fara mata lale
marhabun. Taku ɗaya ta yi a ɗan ƙaramin downstairs dake ƙarasar da mutun cikin
falon, zuwa na biyu na uku ta tashi zamewa saboda sulɓi da kuma tsantsin da tiles
ɗin yake da shi.
Haleema ta yi gaggawar riƙeta

“Be careful”

Amira na kallonta ta san ƙanwar Abdool ce dan ga kamanin Abdool nan shimfiɗe a
fuskarta. Ita ta taimaka mata ta sauko saman stairs ɗin, tana riƙe da hannunta har
suka ƙarasa tsakiyar falon gurin da sauran ƴan'uwanta suke zaune.

“Welcome Sister”

Fauza ta faɗa tana faɗaɗa murmushinta ga Amira, Meesha kan aikin dannar waya kawai
take ko inda Amira take zaune bata kalla ba. Amal ce ta karkace fuska tana mata
kallon ƙyama ɗin nan, daman ita ta fi uban kowa wulaƙanci a gidan, cikin ma tana
tsoron Ummi da Abdool dan sam basa son wulaƙanta ɗan'adam.

Haleema da kanta ta zaunar Amira a ɗayar kujerun da suke gurin, dan falon ya
kasance mai part biyu ko kuma a'ce uku, idan a ka haɗa da dinning area.
Bayan ta zauna Meesha ta ɗaga kai ta kalleta tare da miƙa mata hannunta.

“Hey Sis Welcome, my name is Aisha aka Meesha, ke ce Amira ko?”


Amira ta ɗan ɗaga kai tana murmushin mai nuna tsantsan ladabi da kunya, da kuma
sanin kai, kana ta miƙa mata nata hannun ita ma.

“Eh ni ce nice to meet you Meesha”

“Nice to meet you too”

Ta ɗan sakar mata murmushi kaɗan, sannan ta tashi ta nufi ɗakinta, till idonta na
kan waya.
Tsire baki Amal tayi ta tashi ta nufi ɗakin Ummi.

“Shukura....”

Fauza ta ƙwala mata kira tana kallon tv kamar ba ita ce tayi kiran ba. Da gudu wata
baƙar mace ta fito da gudu daga wani ɓangare na falon ta zo haban Fauza ta tsaya.

“Hasiya ga ni”

“Ba ki ga mun yi baƙuwa ba? A kawo mata abin sha mana”

Wacce aka kira da Shukura ta kalli Amira tana washe baki.

“A'a baiko na mu ne ta zo, sennu sennu, sennu da zuwa, bari ya kawo miki abinse
yanzu, ahh sennu baiko”

Ta juya da sauri ta nufi kitchen. Yanayin shigarta da kuma maganar ya tabbar ma da


Amira bayarabiya ce. Ƙasa ƙasa Amira take kallon tsarin falon tun daga kujerun har
labulayen da flowers da aka ƙawata falon da su komai maroon color ne har center
carpet ɗin.
Ga wasu golden gulob da aka ƙawata falon da su, wanda Amira bata taɓa ganin
irinsu ba iya tsawon rayuwarta.

Fitowar Ummi ne yasa Amira ta karkata tana kallon yadda Ummi ta doso gun da take
tana murmushi. Babu shaka wannan Mahaifiyar Abdool ce dan ga kamaninsa nan sak a
fuskarta, dakakkar shaddar dake jikinta ta haske ta sosai, kamar wata sarauniya,
hauru makka guda biyu dake a bakinta sun haska fuskarta sosai.

Zubewa Amira ta yi ƙasa tana gaishe ta. Ummi ta dafata tana mai jindaɗin yadda
Amira ta bata girma.

“Tashi tashi ƴata”

Wannan furucin da tayi ya faranta ran Amira sosai, cikin kuzari ta tashi amman bata
zauna a kujerar ba sai ta zauna ƙasa ta nutsar da kai.
Ummi ta ture Amal da ke riƙe da hannunta tana zuba mata shagwaɓa ta shafa kan
Amira.

“Sannu ƴa ta ya hanya?”

“Alhamdulillah”

Ummi ta kalli Haleema tana ɗan zare ido.

“Miyasa ba a kawo mata komai ba?”

Haleema ta juyar da babban yatsanta tana nunawa Ummi kitchen. Sai fmga Shukura ta
fito ɗauke da ture da kayan ciye-ciye niƙe-niƙi a saman turen. Har zata dire turen
gaban Amira sai Ummi ta girgiza mata kai.
“No kai mata ɗakin Amal”

“Tau Mama Ummie”

Shukura ta faɗa ta nufi ɗakin Amal ɗin.

“Tashi ki bita ki shiga ciki ki yi wanka sai ki ci abincin”

“To”

Amira ta unƙura ta tashi ta bi bayan Shukura tana ƙarema ɗayan ɓangaren na falon
kallo.
Sai da ta shige ɗakin sannan Amal ta fashe da kuka kamar wata ƴar shekara uku ta
narke a jikin Ummi har da kuka.

»“Ummi za ki ce ta je ɗakina ni warinta na ƙe ji”

“That's why na ce ta je ɗakin ki, ba kece mai jin warin mutane ba? Wannan wane irin
iskanci ne zaki ce kina jin warin mutane, dan iskanci”

“Wallahi Ummi mutane wari suke”

“Tau yayi kyau, kullum ina rabaki da wannan halin kina ƙarawa ko? Wannan dai
baƙuwar Yarima ce idan kika wulaƙanta ta Dude ɗin ki kuka wulaƙanta”

Ta ƙara ɓare baki tana kuka, sai duk ƴan'uwan suka sa mata dariya, especially
Haleema data fi kowa raina ta. Ummi kan tashi ta yi ta bar mata falon ta nufi
kitchen.

RASHIDA POV.

Duk yadda take misalta yadda zata rayu ba tare da Hilal ba sai ta farka daga
mafarkin da take, bata san son da take ma Hilal yayi yawa a zuciyarta ba sai yanzu,
ta take ƙoƙorin lallasar zuciyarta ta haƙuri da rashinsa.
Saka wayarta da ya yi a blacklist ya dame ta sosai, tun da ko text ɗinta ba ya
iya karantawa a yanzu. Gashi yayi blocking ɗinta a facebook da whatsapp duk inda
take iya ganinsa ta samu sanyin zuciya bata ganinsa a yanzu.

Yau weekend ne ba ta zuwa aiki, amman kwata-kwata ta kwacewa abinci da kuma zaman
falon da take ɗan yi dan ragewa kanta damuwa.

Bata fito ba sai da ta ji motsin ƴaƴan ƴar'uwarta Ummul Faisak, da suka zo weekend,
sannan ta fito dan bata son kowa ya gane damuwarta.
Tayi ƙoƙarin yin far'ah dan da ɓoye damuwarta, amman hakan be hana Momy yi mata
magana ba.

“Yau yanzu aka fito”

Ta zauna kusa da ƙanwarta tana sotsar kanta.

“Bana jindaɗi ne”

“Ai kullum ba za ki taɓa jindaɗi ba matuƙar baki cire Hilal a zuciyarki ba, ai
mutumen be mana hallaci ba kuma ya ci amana”

Ta yi ƙasa da kanta hawaye na mata zuba, sai ta shiga murza yatsun hannunta. Ummu
ta dafa ta
“Ki kwantar da hankalin ki duk abinda take taƙamar ta miki wallahi sai ya karye,
kowa ya san wannan ba halin Hilal ba ne, mutumen da ke son ki kamar ya mutu sai
kuma.ace yau shine ya sake ki hmmm sherin mata yawa ne da shi”

Momy ta girgiza kai ta tashi ta nufi gurin da yaran suke wasa tana faɗin

“Addu'ah itace kawai mafita, idan ma wani abun ta yi miki sai kiga ya karye”

Sai da ta shige ɗakin tana gargaɗin yaran kar su mata ɓanna sannan Ummu ta Kalli
Rashida tace

“Ke ma.fa sai kin tashi tsaye, ai tun farko kece kika yi sakkiyi har haka ta faru
gashi nan kina nadama, ƴan matan nan na zamani, ai dole sai ka tashi musu tsaye
balle ance yarinyar nan ta daɗe fa ba tayi aure ba, kin ga ko ai dole ta nemi ƙorar
ki dan ta mallake miki miji”

“Ina ta ƙoƙarin yaƙar zuciyata ne wajen ganin ma fitar da son Hilal a rai na, ina
tsoron kar son da na ke masa ya kai ni ga hallaka”

“Au shikenan kin yarda ki bar mijin ki? Uban ƴaƴanki? Saboda wata can ta mallake
miki shi? Ashe ƙaryar so kike tun da ba ki iya yaƙi nemawa kan ki ƴan ci, ai yanzu
ko wani auren kika yi baki san inda zaki faɗa ba ƙila ma ta fi wannan bala'i ƙara
ma wannan ki ƙyaƙeta wallahi tun wuri”

Tayi shiru tana share hawayen ta, tare da nazarin kalaman Ummu Faisak babu shakka
tana son mijinta kuma wannan juya bayan da Hilal yayi mata a take ya tabbatar mata
da lallai ba a banza ba ne ya yi mata haka. Kuma idan bata zauna da Hilal ba waye
zai aure ta? Tasan ta gama aure duniya dan yanzu da wahala ta samu wanda xai aure
inda har wayayyen mutum ne sai ya nemi su yi gwaji idan ko har ya gano tana ɗauke
da cutar ba zai aure ta ba. Kuma a halin yanzu babu wanda ya kamata ya zauna da ita
sai shi tun da shine ya mori jikinta sai yanzu dan wannan matsalar ta same ta sai
kuma ya guje wannan ma ai butulci ne, ko da yake baya cikin hayyacinsa.

“Ke....”

Ummu ta girgizata ganin tana ta mata magana tun ɗazu amman bata jinta.

“Ke kwantar da hankalin ki, akwai wani buzu da yake unguwar mu, kuma ance yana aiki
sosai, zan masa magana yayi mana aiki akai a kare abunda ta yi masa ”

Rashida ta yi saurin dafata.

“A'a ki barsa kawai ina nan ina faɗawa Allah buƙata na kuma na san zai karɓa min,
very soon za ki ga asirin ya karye”

“Toh Allah ya amsa, amman duk da haka ta kin shiga malamai kinjinta bakin su, kin
san fa asiri ko Annabi ya kama balle wani Hilal”

“Haka ne, zan gwada amman ba yanzu ba, sai hankalina ya kwanta sosai”

“To amman ni bana son ki cika idda ba tare daya mai da ke gidansa ba”

“Karki da mu komai za yi dai-dai inshallah, bari na leƙa gidan su ƙawata Asmee”

“Ai ƙara kan kina fita ko damuwa zata rage miki. Bari na shiga na gaida Dady”

“Ai baya nan ya tafi ɗaurin aure”

“Okay”
Rashida na shiga ɗakinta ta ɗauki jakarta ta saka hijabinta ta ɗauki makullin mota
ta fito a gaggauwacw tayi ma Momy sallama fitar ta fice daga gidan kamar zata tashi
sama...

Ba gidan Asmee zata ce je ba, daman ta faɗa ne dan ta yi hujja da gidan kawai.
Garin da Malamin ya ke ta nufa, bata ko tsoron tuƙi ita kaɗai gata mace yadda take
gudu kai ka ce wani ne ya biyota. Sai kuwa gashi ta isa garin cikin ƙanƙanen
lokaci.

Yau bata tararda layi kamar ko yaushe ba. Bayan mutane dake gabanta sun gama abinda
zasu yi sun fito sai ta shiga da kuzarinta.
Haka ta zauna gabanta tana zayyana masa irin son da take ma mijinta da kuma neman
komawa gidansa ta ko wane hali.

Kuɗi mai tsoka ta ciro a jakarta ta miƙa masa da sunan somin taɓi, sannan tayi masa
alƙawarin idam har aiki yayi zata kai shi makka ta siya masa mota kuma ta bashi
gidan ta dake a cikin garin Zaria.

A take ya fara tsiface-tsifancesa sannan ya ɗauko wani kanko mai ruwa, ya aje
gabansa ya karanta wasu dala'ilai sannan ya kira kwari da baka suka zo da kansu
gabansa suka tsaya. Rashida taji tsoro sosai amman a haka ta dake ta tsaya a inda
take tana ƙara girmama iya aikinsa.

Kwari da bakan ya haɗa ya saita ruwan yana karanta wasu abubuwan da shi kaɗai yasan
yaren da yake sannan ya ɗora da

“Ajib ya dala'ilu, ajib ya sargirfir... Kalsoom Kalsoom Kalsoom...”

Haka ya kira sunanta har sau uku, sai ga hoton Kalsoom ya bayyana tana zaune a falo
tare da Rafiq sai wasa take masa. Sai Malamin ya harba kwarin cikin ruwan. Sai ta
yi tsaye tsakiyar ruwan, a take ruwan ya soma sauya kala zuwa launin ja kamin daga
bisani ya zama jini gaba ɗaya.

Sannan ya kalleta

“An jima zamu yanka baƙar kaza, da kuma kaza mai wake-wake, ke kuma ki dafa tuwon
dawa ki yi sadaka, idan ba zaki iyaba sai ki siye”

“Na gode Malam shikenan yanzu?”

“Eh yanzu kam shikenan ki koma gida kawai ki saurari sakamako”

Ta ji babu daɗi duk da tasan bata da wata mafita sai wannan, yanzu kam tasan tun
da akayi ma Kalsoom harbin kanko shikenan haukacewa za ta yi, dole ne kO Hilal.ya
rabu da ita ko kuma ya mayarda ita gidansu dan ya nemo wanda zata riƙa masa ɗansa.
Cike da farinciki ta dawo gida wani ɓangaren kuma tana ganin rashin dacewar
abunda ta aikata, sai xuciyarta ta kan zuga wajen ganin abun ya gushem mata a
zuciya, tana ayyana yadda ita ma Kalsoom tayi mata ta raba ta da mijinta........

Pray for my mother she's sick.


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *51*

NAMRA POV.
Ashe wuya tana canja mutum, iɗan ka hango Namra a yanzu ba zaka taɓa cewa ita ce
ba, ta canja sosai tun daga kan hallitarta zuwa suturar dake jikinta. Zane daban
riga dabam sai faman hurin wuta take hayaƙi duk ya boɗe gurin, sai fama.take ta
itacen kamar wata tsohuwa.
Sam bata damu ba da hanin zuwa tarbar lefen da Asim yayi mata, ta san ko ba komai
ita tana shakar zuwa yanzu dan bata san yadda ƴan'uwanta za su kalleta ba, duk ta
wani koɗe kamar ba ita ba.
Daker ta samu wutar ta kama har ta dumama tuwo sannan ta wanke kular da take sakawa
Asim abinci ta zuba masa ta kai masa sai ta sake fita ta ɗebo masa ruwa ta aje
masa.
Gefensa ta zo ta zauna ta lanƙwashe ƙafafunta irin ladabin nan, sannan ta soma
magana gabanta sai faɗuwa yake

“Asim magana nake son mu yi ina son ka ba ni aron hankalin ka”

“Ai kunne ne yake ji ko?”

Ya faɗa yana auna ɗummen a bakinsa.

“Asim ba zai yiyu kullum na riƙa ci da kai na ba, Allah be ɗora min ciyar da kai na
ba, fisabilillahi abinda kake min baka kyauta min, bana yin abinci ka yaba, baka
bani abin dafawa balle ma kuɗin cefani yanzu tsakani da Allah ka kyauta kenan?”

Ya ɗaga kai ya kalleta yana suɗar hannu.

“Namra kenan, wallahi kina da matsala wani lokacin ƙwaƙwalwarki ƙarama ce, yanzu
idan nace zan baki abinci kawai ko kuɗin cefane ina su ke? Ba sai da abu ake yinsa
ba? Ko babu zan ba ki?”

“Amman naga kana fita aiki Asim ba za ace kullum baka samowa ba ki kaɗan ne dole
wata rana sai ka samo”

“To ɗan abinda na ke samowa ai ba zai wuce na hau achaɓa ba, ba fa wani samu muke
sosai ba, ni kaina na fiki son na ciyar da ke dan Aallah ya fi bawa mai yi
iyalansa, sannan babu Namijin da zai so mace ta ciyar da shi ko dan gudun irin
wannan gorin”

“Ba gori na ke maka ba, gaskiya nake faɗa, idan mu ka zauna muka ce wannan kuɗin na
sana'ah kullum shi za'a ci, sai mu cinye sana'ar mu zauna a haka babu komai”

“To ya zan yi Namra? Sata zan yi na baki ko kuma kai na zan siyar na ciyar da ke?
Kina gani ba wata sana'ah ce da ni ba daga yanzu ki lissafa duk abinda san kin
kashe na ciyar da kan ki da ni idan na yi kuɗi zan biya ki, ni bana son gori akai
na farau rashin arxiki? Ko kuma ni na kawo tauasaci duniya? Idan ma kin gaji da
zama da ni ne sai ki faɗa min kawai ba wai ki riƙa min magana any how ba”

“Babu mace da zata zauna da kai a yadda na zauna da kai Asim, na watsar da jindaɗin
gidan mu dan kawai na yi maka biyayah na zo na zauna a nan gidan ina rayuwar da ban
taɓa mafrkin shiga, ka dubi jikina, duk wanda yasan ni ya gan ni a yanzu ba zai ce
ni ba ce, amman kullum baka gani sai anbanta ni kake”

“Mtssswww kaji ba, sai jawabi da ƙaryar arziki, duk arzikin gidan ku me suka ƙulla
miki? Babu wanda zai gan ki yace ke ƴar gidan ce, tun da kika yi aure har yau babu
wanda ya taɓa tako ƙafarsa ya zo gidanki, haka ake rayuwa, ai ko bunsuru kike aure
idan basu yi dan ni ba sayi dan ke, ko riƙon ki ake ya kamata ace wani naki yazo
garin nan ganin amman ko ciwon da nayi har na warke babu wanda ya leƙo kamar na
kashe musu wani”
“Me zai kawo ƴan uwana a gidan ka, bayan sun san dalilin aure na da ka yi? Me za su
zo su yi? Ciwon da ka yi wane irin jawabi ne ba ka min akan jinyar da kayi sai ka
ce sune suke da alhakin ɗaukar naunyin ɗawainiya da kai, Mama da take mahaifiyarka
me tayi maka? Kuɗin data karɓo ai dashen da kuke ne, duk ni nayi ɗawainiya da kai”

Tasss ya watsa wanke mata fuska da mari, ya hau shurinta sai kaurar fuskarta yake
yana faɗin.

“Duk iskancin ki ya tsaya a kan ki, karki kuskura saka uwata a cikin sheɗancin ki,
dan ba warin ki ba ce”

Kuka take yi sosai tana rufe idonta da ta ke jin kamar ƙasa ta watsar mata a cikin.
Be kula irin aika-aikar da yayi ba yasa ƙafa ya fice.
Haka ya wuni a ɗakin tana aikin kuka kamar ta cire idonta, sai da aka kira salla
azahar sannan ta samu kukan ya tsaraita mata har ta unƙura ta tashi.

Wanka tayi tare da alwala sannan ta saka wasu tufafin tayi salla. Sai ta ɗauko
qur'ane tana karatu.
Guraren uku da kwata wayarta tayi ringing ita har ta manta da sha'anin wayar sai
yanzu. Bata kula wayar ba sai data ta kai ƙarshen suratul Yasin, sannan ta rufe
qur'anen ta yi addu'ah daga bisani ta maida alƙur'anen mazauninsa, sannan ta nufi
wayar ta duba.

Number Anty Yasmin ce. Ta yi mamakin ganin kiran Yasmin har four miss calls, ta
manta when ma Yasmin ta kirata tun suna shiri. Bata da kuɗin da zasu isheta magana
amman tasan ba zata rasa na flashing ba.
Kamin ta kira sai ga Yasmin ta ƙara kira. Namra tayi saurin picking ta kara a
kunne.

“Assalamu alaikum Anty”

“Na'am My Sis ykk”

“Lafiya ƙalau, ya Gwaggo”

“Tana can gida, ni na zo katsina seminar ne, tun shekaran jiya yau zan koma, kuma
bana son na wuce ban gan ki ba”

Gaban Namra ya faɗi bata ƙaunar wani yace zai kawo mata ziyara a yanzu, sai dai
bata jin zata iya hana Yasmin zuwa gidanta tun da har ta nuna son zuwa.

“Ayyah Anty Yasmin yanzu za ki zo?”

“Eh anjima kaɗan zamu koma”

“Okay ki ce a kawo ki Nasarawa, idan an kawo ki sai ki shiga ta cikin unguwar zaki
ga gidan daya ƙone sai ki shigo nan”

“Okay gani nan zuwa yanzu”

Ta kashe wayar. Namra ta juya tana kallon ɗakinta, to be frank bata son kowa ya san
halin da take ciki, sai dai babu yadda ta iya.
Kimtsa ɗakin ta shiga yi dan yau duk batayi shara ba tun da wuni tayi kukan
dukan da Asim yayi mata.
Wajen gidan ma ta gyara bakin inda zata iya dan baɗin gidan ba mutum ɗaya ne zai
iya share shi duka ba, yaro ta aika da kuɗi aka siyo ma Yasmin gala da ruwan sanye
ta aje mata. Sannan ya canja tufafin jikinta ta saka masu ɗan kyau ta zauna zaman
jiran isowar Yasmin.
Tana jin an turo ƙofar gate ɗin gidan gabanta ya yi mugun faɗuwa. Cikin ƙarfin hali
ta taso ta doso gate ɗin gun da Yasmin take tana doka sallama da kallon gidan tana
mamaki.
Rumgume ta Namra ta yi tana nuna murnar ganinta. Ita ma baki har kunne, ta ke
ɗokin ganinta.

“Namra ke ce? Duk kin canja”

“Ni ce Anty”

“Duk kin canja kin, kin yi baƙi Namra kin lalace”

“Bana jindaɗi ne kwana biyu, mu shiga ciki”

Cike da ƙyaƙyami Yasmin ta zauna dan ita duk gidan be mata ba, mamaki ma take yadda
Namra take zaune gidan.
Namra ta dire mata gala da ta siyo mata ta aje mata tare da ruwan sanyi

“Ban yi girki ba yau shine na siyo miki gala”

“My Sis meya samu fuskarki?”

Ta tambaya ganin fuskar duk ya kumbura. Namra tayi shiru bata ce mata komai ba.

“Haka kike wannan rayuwa Namra? Dube ki dubi gidan da kika zaune, yaushe kuka yi
gobara?”

“Tun Asim na asibiti an kwana biyu, abubuwan ne suka sauya amman yanzu ai ya samu
aiki komai zai walwale”

“To Allah yasa”

Sama sama suka yi fira, bata wani daɗe ba tayi ma Namra sallama ta ciro 20k ta
bata. Har bakin gate Namra ta rakata, sai da ta shiga motar da ta kawo suka kama
hanya sannan Namra ta koma cikin gida.

ASIM POV.

Cike da ɓacin rai ya fito gida, ya doshi gurin sana'arsa. Ko da ya isa ya tararda
abokan aikinsa har sun buɗe shagon suna fitar da kayan aikin.
Haka ya samu guri gefe ya zauna sai fuci yake kamar sune suka masa wani abu. Har
suka gama fitar da kayan aikin suka rura wuta suka zauna suka fara zuga. Yana can
gefe yana tunanin rayuwarsa yadda zai yi ya rama abinda Namra da iyayenta suka
masa.

Wayarsa ya ciro ya dannan number Hajiyar nan dan yayi saving ɗinta tun jiya.
Ringing tayi sai da tana daf da katsewa sannan ta yi picking.

“Hajiya Ina wuni”

“Lafiya ƙalau who's this?”

“Asim ne Hajiya, wanda kika ba number ki jiya, kika ce za a miki gyaran gate”

“Oh that Handsome Guy ko? ”

Yayi dariya cike da jindaɗin lafazinya


“Hajiya, ɗan talakan nan dai”

“Ai ajinka ya wuce talaka, kawai dai ka riƙe sana'ar da bata dace da kai ba ne”

“Hajiya abin ne sai a hankali kin san nigeria tayi zafi”

“Ta yi zafi ga wanda be san kanta ba, amman wannan sana'ar ai bata dace da kai ba
sam. Anyway yaushe zaka zo ka duba min gate ɗin ne?”

“Wai da yanzu zan ɗauko abokanin aikina sai mu zo mu gani”

“Eh amman kai ya kamata ka fara zuwa ka ga yadda aikin yake, sai ka ce su zo daga
ba ya, ko kuma ka koma ka ɗauko su”

“To aikin yana da yawa ne”

“Ba wani yawa gefe ne kawai ya ɗan ɓalle”

“Okay to bari na zo yanzu na duba yadda aikin yake”

“Sai ka iso, number ka ne wannan?”

“Eh Number na ne Hajiya”

“Okay”

Ta kashe wayar. Shi kuma sai faman murmushi yake

“She's so friendly, bata wulaƙanta mutane duk da tana da arziki, ta hutawa kan ta”

Ya faɗa a fili sannan ya tashi yana kaɗe rigar ya nufi gurin aikin nasa, sai da ya
sanar musu da aikin ya faɗa zai je ya duba ne sai ya dawo sannan ya tari ɗan a
chaɓa ya hau.

Kai tsaye gidan Hajiya Sadiya ya nufa, be sha wahalar ganewa ba, saboda ta karanta
address ɗin na ta tun farko.
House number 7 ya shiga, kai tsaye ya shiga gidan kamar wani wanda ta saba zuwa,
sai wara ido yake yana ƙara kallon gida da kyau da kyau. Mai gadin ne ya tare shi
yana tambayar inda zaije.
Kamin yayi ma mai gadin magana ya ciro wayarsa ya kira number ta.

“Hajiya ga ni na iso, mai gadin ki na ƙoƙarin hana ni shiga”

Sai kawai ya miƙa masa wayar. Mai gadin na karɓar wayar ya kara a kunne sai kawai
ya ce

“To Hajiya”

Ya miƙawa Asim wayarsa, yana nuna masa inda zai shiga. Ka ɗa kai kawai yayi ya
doshi gurin daya nuna masa yana tsaki, dan ya tsani mai gadi ya wulaƙantasa,
shiyasa baya son zuwa gidan da za a tambayeshi inda zai je.

Manyan motoci ya gani a harabar gurin jere, ciki har da wacce taje da ita gurinsa
jiya. Tsayawa yayi ya ƙwanƙwasa ƙofar har sai da aka masa ixinin shiga sannan ya
tura ya shiga yana sallama kamar ba shi ba.

Da murmushi a fuskarta ta tarbeshi tana nuna masa kujera.


“Maraba da samari”

“Hajiya ina wuni”

“Wuni ko kwana? Ko ɗazu fa wuni kace min ko matar ka ta caja maka kai ne? Kasan
matan yanxu sai a hankali, ko da yake baka yi kama da mai aure ba”

“Bana da mata gaskiya, sai dai zafin ƙasar nan”

Tayi dariya tare da nufar gurin freezer ta ɗauko masa lemu da kofi ta zuba masa.

“Ga lemu ka sha, na san dai ka karya ko a kawo masa breakfast?”

“A'a na gode”

Ya ɗauki lemun ya sha, yana kallon ƙaton tv ta na bango dake can ƙarshen ɗakin.
Kallonsa take sosai tana murmushi, tare da gyara doguwar rigar atmafa dake jikinta.

“Na ce ka duba gate ɗin in ya zo gobe sai ku zo ayi aikin, dan yau zan yi baƙuwa
gaskiya”

“Okay to ba matsala, gate ɗin na bakin ƙofa ne?”

“Wh ka tambayi mai gadi zai nuna maka”

Ya aje lemun bayan ya shaye shi kaf sannan ya tashi.

“Yo bari naje na duba gobe kamar gaushe zan zo?”

“Da la'asar idan rana ya yi san yi”

Wani irin rausayarda ido take lokacin da take magana da shi tana wani langaɓarda
jiki. Shi kuma yayi murmushi yana sa hannayensa aljihu.

“Tau ina zuwa”

Ta juya ta soma tafiya cikin wani irin karairaiya, ta nufi ɗakin. Bata wani daɗe ba
ta fito riƙe da sabbin yan ɗari biyu biyu ta mika masa.

“Ga 10k ka hau a chaɓa, sai na gan ka goben”

Ya faɗa tana murmushi tare da shafo hannunsa a lokacin da zai karɓa ɗin.

“Haba Hajiya ayi haka?”

“Ba komai ai irin ku abun tausayawa ne masara aikin yi”

“Na gode Allah ya saka da alheri ya ƙara aixiki”

Ya fito daga falon baki har kunne. Sai da ya tambaya mai gadin ya gwada masa gurin
da gyaran yake sannan ya wuce.

KALSOOM POV.

Yau da wuri ta sallami yara da Hilal kasancewar yau Monday ce ranar aiki. Sannan ta
shiga gyara gidan, baya ta share ko ina tayi mopping sannan ymta shiga kitchen ta
haɗa kayan wanke-wanke ta somawa wankewa tana sauraren ƙira'ar dake wayarta.
Tsin-tsin'tsin ta riƙa jin kamar ana tsokararta, sai tsikar jikinta ya fara tashi.

“A'uzubillahi minal shaɗanin rajin”

Ta furta tana girgiza kanta da take jin yayi mata nauyi. Tunawa tayi da bata da
ɗankwali a kanta, sai ta yi saurin komawa falo ta ɗauki ɗankwalin ta ɗaura, ta koma
kitchen ɗin ta cigaba da wanke-wanken. Tana cikin wanke wanke ta ji kamar an kiran
sunan, cikin muryar Hilal tsayawa tayi tana saurere ba tare data amsa ba, daman can
bata da ɗabi'ar amsa kira idan har sau ɗaya ne, sai kuma ta ƙara jin kiran a karo
an biyu, a maimakon ta amsa sai kawai ta aje wanke-wanke da take ta nufo falo dan
taga idan har Hilal ɗin ne. Har waje ta fito tana dubawa amman vata ga motar Hilal
ba balle alamunsa. Tana juyawa ta koma ta sake jin an kirata in Hilal voice.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Allaahumma munzilal-kitaabi, saree'al-hisaabi,


ihzimil-'ahzaaba, Allaahumma ihzimhum wa zalzilhum. ،‫ َسِريَع اْلِحَساِب‬،‫الَّلُهَّم ُمْنِزَل اْلِكَتاِب‬
‫َأ‬
‫ الَّلُهَّم اْهِز ْمُهْم َوَزْلِزْلُهْم‬،‫” اْهِزِم ال ْحَزاَب‬

Gabanta ya faɗi da farko, kuma ta tsorata sai dai addu'aj ɗa tayi yasa taji tsoron
ya guje mata a take. Daman addu'ah ce ta neman tsari daga makiya.

Sai kawai ta koma ciki ta cigaba da wanke-wankenta. Wani irin ƙwallowa tayi Rafiq
dake bachi ya buga. Ba shiri tayi bar wanke wanke ta nufin ɗakin yaran. Ƙasa ta
tararda shi yana fisge-fisge kamar wanda za a cirewa rai.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta ƙarasa da sauri inda yake ta ɗaukesa tana girgixawa. Amman ina ido da jiki duka
a ƙafe sai wani ƙogi yake yana kallon silin, aje shi tayi ta nufi ɗakinta da gudu
ta ɗauki wayarta ta kira Hilal.

AMIRA POV.

Tana shiga ɗakin ta tararda komai na ɗakin pink color ne, sai manyan hotunan Amal
dake jikin ginin ɗaki har da waɗanda ta yi ƙasar waje, wani gurin tana tare da
Abdool wani gurin kuma da Ummi wani da Meesha wani da Fauza sai kuma wanda suka yi
da Haleema, ma bin su shine wanda tayi da duka familynsu Hilal yai ma Ummi side hug
yai mata kiss irin na nuna tsatsar ƙaunar nan na ɗa da uwa.
Wanda Amal tayi da Hilal ta fi tsurawa ido tana kallon yadda Hilal yake feeding
ɗin Amal ranar birthday ta. Hannu ta kai ta shafa hoton tana murmushi.

“Kai na daɗe ina mafarki Abdool, kai ne irin mijin da nake so, sai yanzu na gane
dalilin daya sa na bar gida na, ashe rabo ne kirana, saboda kai akayi ni Abdool
nima kuma saboda ni aka yi ka, haƙiƙa ban yi sadaukarwar banza ba”

Ta juya ta jingina da ginin gurin ta lumshe ido tana sauke wani sayyayen numfashi.
Babu wanda take gani sai Abdool, rayuwarta da tasa take hangowa irin jindaɗi da
kuma rayuwar da za su yi idan ya aureta.

Bayan tayi wanka ta maida tufafin dake jikinta ta zauna ta ci abinci tana ƙara
ƙarewa ɗakin kallo. Ta jinjina kai

“Lalai ba ƙaramin dukiya Abdool ya tara ba shi da mahaifiyarsa, amman ina


mahaifinsa yake? Ina jin baya nan gidan dan gidan be nuna alamun gidan sarauta ba”

Ta sauke ajiyar zuciya tana auna kanta a matsayin matar Abdool. Irin kallon da yayi
mata take tunowa yadda idonsa yake da fari har wani ruwa ya kwanta a ciki kamar
balarabe. Tashi tayi ta ƙasara gurin madubi tana kallon kanta, bata da munin da
namiji zai ganta yace baya son ta. Idan har baka yabe ta ba to ba zaka kusheta ba.

Shukura ce ta dawo da dare ta kawo mata abinci sai ta kunna mata tv ta ɗauki wasu
ɗaga cikin kayan da Amal za tayi amfani da su, da dukan alama Amal ɗin ce tasa a
ɗauko mata har da ƴar ƙaramar iphone ɗinta.

________________

Ni kam nace Kar Hajiya ta lalata mana Asim 😏😏


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *52*

KALSOOM POV.

Ta yi masa kira biyar be ɗaga ba, ga dukan alamu suna tiyata ko meeting dan shi
kaɗai ne yake hana sa ɗaukar wayarta.

“Wayyo Allah na na shiga uku Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta furta cikin muryar kuka hawayen na bin fuskarta, zubewa ta yi a gurin hannunta
ɗaya saman kai, ɗayan kuma riƙe da waya tana ƙoƙarin kiran Hilal. Still be ɗaga ba,
a nan ta jefar da wayar ta koma ɗakin da Rafiq yake tana kuka. Wannan karon abinda
ta gani ya bata tsoro dan har kumfa yake fitarwa a bakinsa.

Da sauri ta ɗauke shi ta fito da gudu ta nufi harabar gidan tana ihu. Mai gadin ne
yayi kanta yana tambayar ba'asi. Ganin halin da yaron yake ciki ya sashi sallalami
tare da karɓarsa ya girgiza.

“Hajiya ki kira Alhaji ki faɗa masa”

“Na kirasa be ɗaga ba”

“Ki sake kiransa kar yaron nan ya mutu”

Jin an ambaci mutuwa yasa ta ƙara rikicewa ta falla da gudu ciki, ta koma ɗakin ta
ɗauki wayarta a inda ta jefar da ita.
A rikice ta kira numbersa wannan karon tayi sa'ah kira ɗaya ya ɗaga cikin muryar
daya saba mata a duk lokacin data kirasa

“Maman yara...”

Kukanta da yaji yasa gabansa tsinkewa ya faɗi.

“Kalsoom what happend?”

“Rafiq ne Hilal ka zo gida yanzu kar ya mutu...”

Tana jin haka ya katse wayar ya mike daga zaman tattaunar da suka gama yanzu-yanzu
ya nufi gidan hankali a tashi. @360 ya hau titi duk hankalinsa sai ya tattara ya
koma gida, zuciyarsa sai yayo masa take, wani abun Rafiq ya hau ya faɗo ko kuma
wuta ta jashi, kwata-kwata be kawo ma ransa abinda ya tarar yaron na yi ba. A
firgice ya fito motar ya nufo gurin da Kalsoom take riƙe da Rafiq tana kuka.

Ya sa hannu biyu ya karɓe sa ta juyo da sauri ya nufi mota, dan babu lokacin
tsayawa tambayar abunda y same shi.
Komawa tayi ciki ta ɗauko Hijabinta ta saka, ta ɗauki jakarta ta fito da sauri
kamar tana son haɗaw da gudu, sai kuka take irin mai nuna tsantsar tashin hankali.
Ba tare data kulle gidan ta fito titi, tari adai-dai sahu ta hau, tana faɗa nasa
inda zai kai ta. Be sauketa ko ina ba sai American hospital inda Hilal yake aiki,
sai da ta sallami mai Napep ɗin sannan ta nufi emergency duk da bata da tabbacin
can ɗin ne ya kai shi ko a'a. Wasu nurser ta tambaya, suka tabbatar mata da xuwansa
da kuma ɗakin daya nufa da yaron. Da gudu ta ƙarasa gurin tana share hawayen da
suka ƙi su tsaya mata.

Kai da kawo ta riƙa yi ita kaɗai tana jiran fitowar Hilal ko kuma wasu daga cikin,
amman shiru har kusan mintuna arba'in da takwas.
Sannan wasu Nurser suk fito daga ɗakin, ita kuma ta zura kai sai leƙo take ko
zata ga wani halin da Rafiq yake cikin.

Hilal ne ya fito, sai ya janyo ƙofar ya kulle. Fuska babu annuri ya nufi office
ɗinsa, ba tare da kula ta ba, balle ma ya bata amsar tambayar da take masa.
Binsa tayi a baya tama tambayarsa amman be kula ta ba har sai da ya shiga office
ɗin. Ita kuma duk hakalinta ya tashi a tunaninta ko Rafiq ya rasu ne.

“Me kika ma Rafiq ? Ya aka yi ya ci guba?”

Itace tambayar da Hilal ya fara mata suna shiga office ɗin. Ras ras ras gabanta ya
faɗi har jakar dake hannunta ta faɗi idonta na kan Hilal tana kallonsa hawaye sai
zuba suke mata ba tare data sani ba.

“Gu....Ba....Bah...”

Ta maimaita cikin rawar muryar tana mamakin furucin daya fito a bakin Hilal. Shi
kuma sai kallonta yake fuska babu annuri.

“Eh guba, ya aka yi ya ci guba?”

“Wallahi ban sani ba, amman Rafiq ko abinci safe be ci ba, bachi ma yake, sai kawai
na ji ƙyalowarsa ina shiga ɗakin na tararda shi a ƙasa yana fusge-fisge”

“Be ci komai ba guba zata zo ta shiga jikinsa ne? Ni dai a sanina indai ba batir
ɗin remote ba mu da wani abu mai guba, da Rafiq zai yi saurin ɗauka ya saka a baki”

“Ban gane ba me kake nufi?”

“Ina baki damar da nake baki ne Kalsoom dan ki samu damar zama uwa a gurin ƴaƴana,
kuma dukansu kamar marayu suke a gare ki tun da babu uwarsu a tare da su, babu
abinda Ezzah bata faɗa min amman bana kulawa saboda na ɗaukeki a mtsayin uwar data
haife su, a tunani ba zaki taɓa musu abinda be kamata ba but wannan yayi yawa, idan
ba shi akayi ba taya kamar Rafiq zai ɗauki guba ya ci?”

Ta yi shiru ta kasa magana, sai idonta ne suke magana. Jikinta ya mutu lis har ji
take kamar ta zube a gurin. Ba ita ce ta bashi gubar ba, bata da tabbacin gubar ce
ma yaci tun da tasan be karya ba, sai dai kuma bata da abinda zata wanke kanta, dan
tage gun da kalaman Hilal suka dosa.

“Idan na cutar da Izzah na kashe Rafiq me zan ji?”

“Nima ban sani ba Kalsoom, ban sani ba, wata ƙila ba ki son zama da su ne ko kuma
kin gaji da su, amman ni ina son ƴaƴana fiye da yadda nake son rayuwata, kuma zan
iya barin komai a kan ƴaƴana, dan sune zasu zauna da ni ko a wane hali nake ciki
ina ta avoiding abinda kike ma yaran nan Kalsoom but you cross your limit”

Bata ce masa komai ba, tasa hannun hijabinta ta goge hawayenta, ta duƙa ta ɗauki
jakarta ta juya jiki ba gwari ta fice. Binta yayi dan zuciyarsa na raya masa ɗakin
da Rafiq yake zata je. Hanyar da zai kai mutum ward ɗin ta nufa ga dukan alamu can
ta nufa, tun da ga hanyar fita harabar asibitin nan ta bari. Daga inda yake ya
ɗaga muryarsa ta yadda zata iya jiyosa yace

“Kalsoom don't, we don't need you for now”

Tsayawa tayi cak! Kamin ta juyo ta soma takowa ta dawo inda yake. Sai da ta kawo
daf da shi sannan ta ɗaga muryar cikin zafin rai ta ce.

“Thank you, thank you so much”

Ta faɗa in low voice sannan ta juya, hawaye na cigaba da zuba a fuskarta ta nufi
hanyar data zai fitar da ita harabar asibitin.

NAMRA POV.

Tun faɗan da suka yi da Asim ya fita bata sake saka shi a ido ba sai washe gari,
ita kaɗai ta kwana a gidan, tana aikin data saba na kuka, bayan ta faɗa ma Allah
buƙatarta.

Sai da safen ta gurka sabon abinci dan kwata-kwata jiya bata yi girki ba, saboda
bata cikin ɗaɗin rai. Bayan ta gama, ta gyara gidan, ta ɗora ruwa tayi wanka sannan
ta zuba abincin ta zauna ta ci sai kawai ta fashe da kuka, haka ta riƙa rera kuka
har tayi ya isheta sannan ta share hawayenta ta ɗauki abinci ta mayar. Dan bata iya
ci. Har zata kwanta sai wasu yara suka shigo siyen magi da manja, sai da ta sallame
su sannan ta shimfiɗa tabarma waje ta ɗauko matashin kai zata kwanta kenan sai ga
Asimya shigo.

Sai da tayi kamar kar ta masa magana ganin be shigo da sallama ba, kuma be kalli
inda take ba, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, ko ba komai mijinta ne dole ta yi
haƙuri ta zauna da shi a haka.
Binsa ta yi cikin ɗakin, sai ta same shi yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa. Yana
ganinta ya wani kawar da fuska, ya ƙara haɗe rai.

“Sannu da zuwa. Jiya baka kwana a gida ba lafiya?”

Ya tsaya daga cire wandon da yake ya kalleta

“Uwata ce da zan sanar miki dole? Ke kike iko da ni ko kuma ni nake iko da ke?”

“Ba ni bace amman ina da haƙƙi, Asim mi yasa kake min haka ne? Ina ta ƙoƙarin
taushe zuciyata dan na zauna da kai lafiya amman baka so, look at me, haka nake a
da duk na bi na canja saboda kai har kunya nake ji wani ya gani a halin da na ke,
kana cin amanata Asim kana zalumtana”

Ya nuna kansa.

“Nine azzalumin?”

Baya baya tayi ta girgiza masa kai, dan ta san dukanta zai yi.

“Yi haƙuri dan Allah”

“Bakin ki ya saba da furta kalami mai daɗi a gare ni ko kuma jikinki ya faɗa miki”

Ɗaga kai tayi ta kalleshi da idonta dake zubar da hawaye, Asim ɗin baya take
hangowa Asim ɗin da yake ce mata idan babu ita a duniya ba zai iya rayuwa ba, wanda
yake ce mata zai iya sadaukarda komai na sa danta, zai iya bata dik abinda take so,
Asim ɗin data watsar da kowa a kansa, wanda ta bijerewa Abbah saboda, wanda Maryam
da Anty suka yi ta tunantar da ita akansa amman idonta ya rufe, yau shine yake
gargaɗinta. Wani baƙin abu ne mai kamar ƙaho taji ya tsaya mata a zuciya har
ƙafafunta suka kasa ɗaukarta ta zube ƙasa tana yaƙi da baƙincikin dake neman
numfashimta.

“Kur wallahi kurwata kur sai dai ki ci kan ki”

Ya faɗa yana yatsine ganin kallon da take masa ɗazu. Lumshe ido tayi, ta rarafa ta
ƙarasa saman katifar ta kwanta, tana sauraren ciwon zuciyar daya game ilahirin
jikinta. Nan take jikinta ya ɗau rawar fever sai kuma zafin jiki. Bedsheet taja ta
lulluɓa dan tsanyi take ji ya baibayeta.

Asim kan ko a jikinsa, fita ma yayi daga ɗakin yaje yayi wanka ya dawo ya saka wasu
tufafin ya mata waɗanda ya cire a tsakar ɗaki yayi lafiyarsa.

Gurin aikinsa ya koma, daman yayi da abokan aikin nasa zasu je gurin Hajiya Sadiya
gyaran gate. Dan haka yana isa suka wuce.
Shine yayi musu jagora a cikin gidan har suka yi aikin suka gama, sannan ya koma
ciki ya sanar mata da sun kammala aikin sai ta ɗauko 30k ta bashi akan aikin da be
wuce 8k ba. Hannu biyu yasa ya karɓa yana mata godiya.

“Allah ya saka da alheri Hajiya Allah ya ƙara arziki, wallahi halin ki na musaman
ne”

Ta yi dariyar jindaɗi.

“Na ce ka iya mota kuwa?”

“Eh na iya mota Hajiya”

Ya amsa da sauri jikinsa har rawa yake.

“Idan ba damuwa, ina son ka riƙa jana a mota dan yanzu bana da direbe, kuma kaga
gidan nan yayi min girma da yawa dole akwai buƙatar wanda za a aika a duk lokacin
da aka tashi da kuma mai ban ruwan fulawowi da sauran ayuka”

“Wallahi Hajiya duka zan iya, wallahi komai kika sani zan iya”

“To idan ka shirya sai ka min magana, idan ban takurawa aikin ka ba”

“A'a ai aiki ina yi dan na samu na taɓawa, ai ko a yanzu ai na tashi”

“A'a kaje dai kayi shawara dan ni a gidana zaka dawo idan har ka fara aikin”

“Ba matsala Hajiya, zan iya zama a gidan ki”

“Yanzu dai idan ka kimtsa sai mu yi waya”

“Toh Hajiya na gode Allah ya saka miki da aljannah”

Da murmushi ta amsa nasa ba tare data ce amin ba. Sai ya juya ya fito baki har
kunne zuciya kuma fal da farinciki.
A bakin ƙofar ya tsaya ya cire 20k ya saka a ɗayan aljihunsa, ya ƙarasa da 10k ya
miƙa musu yace su ta bashi. Su kansu sun yaba da 10k ɗin sai kowa ya cire na abin
hawan da ya hawo suka komawa Ƙanen Babansa da sauran kuɗin sai ya miƙawa kowa nasa.
Duk da 20k dake aljihun Asim be hana shi sa hannu ya karɓi abinda Ƙanen mahaifin na
sa ya bashi ba.
Basu tashi aikin ba sai 6 kamar yadda suka ba, sannan suka rufe kayan aikin na
su. Sai dai ba su bar gurin ba sai da suka yi sallah magariba.
Sannan yayi sallama da su ya nufo gida, ba kuma gida kai tsaye ba, unguwarsu dai
dan be shiga gida ba sai da 10pm. Babu abinda yake ransa sai saƙe-saƙen tunanin
yadda zai sarrafa 20k tare da sauran kuɗin da yake ajiya su zame masa millions.

Yana ganin halin da take yasan vata da lafiya, dan tun fitarsa da zazzaɓin ya
rufeta bata tashi daga inda take sai idan sallah zatayi, maganin ciwon kai ma sai
da wata mai siyen magi ta shigo sannan ta aike ta ta siyo mata ta sha. Amman saboda
ƙarfi hali yaƙi yace mata sannu balle tambayarta abinda yake damunta.
Haka ya kwaɓe tufafin jikinsa ya saka ɗan guntun wando data wanke masa jiya ta
farar falmara, ya je ya ɗibi abinci ya ci sannan yaje ya rufe gidan, yazo bayanta
ya kwanta yana lallubarta. Tabbas bata da lafiya dan yaji jikinta da zafi sosai.
Cikin ƙarfin hali ta ɗaga kai ta kalleshi.

“Haba Asim bana jindaɗi”

“Ai na ji Allah ya sauwaƙe ya baki lafiya”

Sai dai hakan be sanya shi daina abinda yake da niyar yi ba....

AMIRA POV.

Tare suka yi breakfast da sukan ƴan matan Ummi, da kuma Ummi ita kanta. Yadda Ummi
take ƴaƴanta ya burge Amira ainun hakan yasa ta kwaɗayin shiga cikim familyn dan
ita ta zama ɗaya daga ciki. Suna gama cin abincin safe Abdool ya kira Ummi ya
gaishe ta, bata iya jin abinda yake cewa duk da taso haka ganin fuskar Ummi da
Murmushi alamun wata magana ce yake mata mai daɗi mai kuma muhimmanci.

Tsakaninta da Ummi akwai tazara sosai, dan tana ɓangaren falon ne ita da Haleema.
Ummi kuma tana ɗayan ɓangaren ne. sai dai hakan be hanata kashe kunne ta jiyo
abinda Ummi take faɗa masa ba.

“Good son haka na ke son ka zama”

“Allah ya kai mu me za a girka maka?”

“To yayi kyau ɗan Mai Martaba kuma Babansa”

Ƙyalƙyalewa Ummi tayi da dariya, ga dukan alama ita ma wani abin yace mata. Haka
kawai Amira ta samu kan ta cikin farin ciki, ta san ko ba komai yanzu Abdool.yana
can cikin walwalah da farinciki.

Farincikin dake zuciyarta ne yasa ta kai hannu ta riƙo hannun Amal dake shirin aje
school bag ɗin a doguwar kujerar da Amira take zaune.

Wani irin ƙyalowa Amal tayi tana yarfarda hannu alamar ƙyaƙyami ta nufi bathroom
ɗin falo dan wanke hannunta.

Haleema ta girgiza kai.

“Haka take, ƙyanƙyamin mutane take, Amal ƴar iskar yarinya ce, sai kin yi haƙuri da
ita”

Amira tayi murmushi tana nuna abinda a Amal tayi be dame ta ba ko ɗan.

“Ba komai ai wata rana zata daina”


“Yeah amman Amal will never change, bari na koma ciki zan yi bachi”

“Ba ku da class ne?”

“Muna da amman sai da yamma”

“Okay sleep tight”

“I will thanks”

Ta wuce ɗakinta tana rangaji irin na ji da kai ɗin nan. Da Ido Amira ta bita har ta
shige sannan ta ƙara mai da hankalinta gurin Ummi dake faɗawa Shukura abinda za a
girka musu. Sai da Ummi ta tashi sannan Amira ta bi bayan shukura kitchen ta karɓi
girkin ta girka musu white rice and pepper soup. Ummi bata san Amira tayi girkin ba
har sai da taga tana jerawa a dinning. Ita kuma tana saukowa daga stairs.

“Shukura...”

Ummi ta ƙwala mata kira. Sai gaba da gudu tazo gaban Ummi ta tsaya.

“Ya kika barta tana jera kaya? Aiki aka ce miki ta zo yi ne?”

“A'a Wullahi Haseya sene yase zse girka ni in tafee”

Ummi tayi murmushin jindaɗi da kuma yabawa da halin Amira.

“To je ki taya ta jera kayan”

Da sauri shukura taje tana taya Amira har suka gama.

YASMIN POV.

Tun da ta dawo tunanin Namra take damunta, tana ganin idan har bata faɗawa Anty
halin da Namra take ciki ba bata kyauta ba. Sai dai kuma tana tsoron faɗa musu kar
ya zama tayi ma Namra kashin aure ko kuma ita Namra ɗin taga laifinta.
Dan Uzair ya gargaɗe ta akan karta faɗa tun lokacin data faɗa masa a irin halin
data samu Namra.
Yau ma nanata mata yake kamar kullum.

“Babu ruwanki da matsalarta idan abin ya dame ta ai ita zata faɗa da kan ta, ba ita
ta zaɓe shi ba, kin manta irin cin mutuncin da yarinyar nan tayi min?”

“Komai tayi maka Uzair be kamata mu ƙyaleta a halin da take ciki ba, wallahi baka
gan ta abin tausayi, har dukanta yake duk ta canja kala”

“Ina ruwanki da canja kalar ta? Ba auren soyayyah tayi ba? To taje can su ci
soyayarsu, wallahi Yasmin idan baki fitar da maganar nan daga ran ki ba, sai mun
samu matsala da ke, kiji da cikin da yake jikinki dan Allah”

“Amman Uzair ni lauyace kuma..”

Ya taso ta haɗe bakinsa da nata......

DEDICATED THIS CHAPTER TO ZAGON K'ASA PAID GROUP MEMBERS. I LOVE YOU ALL 💖💖💖
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *53*
KALSOOM POV.

Haka ta fito asibitin hawaye na bin fuskarta amman bata damu ba, kamar ma bata san
suna zuba ba. Bata iya gani sosai saboda hawayen daya cika idonta, sai dai hakan be
hana ta tsayar da Mai a daidaita ba.
Tana shiga be sauke ta ko ina ba sai unguwar su Salma mai Napep ɗin ya sauketa,
ɗari biyar ta miƙa masa bata tsaya karɓar canji ba ta smtura gate ɗin gidan ta
shiga hawaye na bin fuskarta.
Ganin motar mijin salma yasa ta tsayawa a bakin ƙofar falon ta share hawayenta ta
gyara tsayuwar hijabinta sannan ta tura ƙofar ta shiga tana sallama da muryar kuka.

Babu kowa a falon kasancewar yau monday ce yara basu dawo scul ba kuma ita da
mijinta suna ɗaki. Saman kujera Kalsoom ta xauna ta dafe kanta tana sauraren
hawayen da suke son zubo mata. Ta ɗauki mintuna talatin zuwa talatin da biyar a
haka sannan Salma ta fito daga ɗakin mijinta tana dariya. Ganin Kalsoom ya
razanata, dan da farko ta zata ko ba ita bace sai daga baya ta yarda Kalsoom ɗin ce
jin sheshshekar kukanta. Ƙarasawa tayi ta dafata

“Ke miya same ki”

A maimakon ta yi magana sai kawai ta ƙara fashewa da kuka. Hakan yasa hankalin
salma ya tashi sosai, har zauna kusa da ita tana girgiza ta

“Dan Allah ki yi magana ko wane ni ya mutu”

Daker ta samu natsuwar sai ta kanta sannan ta kalli salma ta soma mata bayani ba
tare da hawayen sun daina mata zuba ba.
Salma ta girgiza da jin labarin har ta rasa yadda zata fassarashi tun da Kalsoom
tace be ci guba ba.

“Kalsoom ko dai ya ci baki sani ba?”

“Wallahi be ci ba, bachi ma yake yi”

“Dole ne ya zarge ki Kalsoom ni kaina zan iya aikata kwatankwacin abinda Hilalya
aikata, ba ze iya banbance ƙarya da gaskiya ba a yanzu, wata ƙila ya ci gubar ne ba
tare da kin sani ba”

“Ba mu da abinda Rafiq zai yi saurin ɗauka ya ci a yanzu, he's just three years
old, ni kuma ba zan dauka abu mai cuta na bashi ba, wallahi ban masa komai ba”

“Ba za ki masa ba Kalsoom ba halin ki ba ne, amman taya haka ta faru”

“Ban sani ba Salma wallahi ban sani ba”

Ta faɗa cikin wani irin kuka mai ban tausayi. Salma ta dafa ƙawarta tana hawaye ita
tace

“Rashida bata zo gidan ba?”

“Bata zo ba, tun ranar daya sallameta bata sake zuwa gidan ba, kayanta ma sai daga
baya ta turo ƙannenta suka ɗibi wasu”

“Allah kaɗai ya san ko mienen wannan abin. Amman abin akwai ban mamaki”

“Amman dai ɗazu na ji ana kirana a muryar Hilal lokacin dana leƙa ban ga kowa ba,
har sau uku, a lokacin ne na ji ƙyalowar Rafiq”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah yasa ba lamarin iska ba ne, kar ace ke
aka jefa ya faɗa kan yaron ko kuma tayi ma yaron jifa dan ya mutu ace ke ce”

Kalsoom ta kalleta da sauri

“Ɗan ta ne fa”

“Ko ɗan ta ne fa? Ai zata iya aikatawa, idan zuciyar mutum bata da imani komai zai
iya aikatawa”

“Na ji ni zata iya yin amman ba zata iya yi ma ɗanta ba, mu riƙa kyuatata zato
Salma”

“Hmmm Allah dai ya kyauta, yanzu ina zaki je?”

“Ni ban sani ba, idan naje gida ban san me zan faɗa musu ba, ba lalle bane suma su
yarda da ni”

“Kar ma kije gida a yanzu ki koma ɗakin mijinki”

“Amman yace min basa buƙata a yanzu”

“Komai yace miki tun da be ce kije gida ba karki je, idan kin koma gidan ki sa masa
ido shi da yaransa babu ruwanki da sha'aninsu, har sai idan ya saki, amman yanzu
idan kika koma gida zai ƙara jin haushin ki ne, ki bashi lokaci ya huce ya fahimci
komai shi da kansa zai dawo yayi miki magana”

“Idan kuma na koma gidan ya wulaƙanta ni fa?”

“Ki jira har ya wulaƙanta ki ɗin amman yanzu gaskiya ban baki shawarar zuwa gida
ba, Kalsoom ki koma ɗakin mijinki”

“Da nasan haka aure yake da ban yi ba, tun da na shiga gidan kullum da matsalar da
take buɗe min sabon shafi, idan kuma ka zauna ba kayi auren ba jama'ah su zage ka,
idan kuma auren ya mutu ace ka kaso auro ka dawo ma zaman gida, ba su san matsalar
ka ba”

“Haƙuri zaki yi, haka LAMARIN DUNIYA (my previou novel) yake, kowa da yadda Allah
ya tsara masa tasa rayuwarwa, no matter what you do how you try you can't escape
your destiny and you can't change your past, all what you can do is wait for your
future with hope and smiled behind your tears, rayuwar aure kala kala ce kowa wace
ta kalar nata jarrabawar idan kika ji wani ma sai kin riƙe ba ki marriage is like
going to a restaurant and order your choice from the menu, and then look at
neighbouring table n wish you”d ordered that dole ki yi haƙuri babu komai a cikin
rayuwar aure sai ƙalubale shiyasa kika ji akan ce kayi haƙuri haƙuri dai, kuma idan
kika yi haƙuri tun a duniya sai Allah ya saka miki”

Kuka kawai take, bata iya cewa komai ba har Salma ta gama nusar da ita akan hanyar
da take ganin kamar ita ce mafita a gareta.
Sai da tayi sallah la'asar sannan salma ta raka ta ta shiga Napep ta koma gidan
mijinta, ba dan ranta yazo ba.
Cikin fargaba da tunani ta koma gidan a zatonta ko Hilal ya dawo, kar ya tambaye
ta ina ta fito bata san me zata ce masa ba, tun da ba gida yaje ba. Sai ta tarar be
ma dawo ba sai su Izzah da suka lalata falon da shinkafa suka watsar da uniform ɗin
su a tsakar falon da scul shoes da bags duk a falon. Saman kujera ta zauna tana
sauke ajiyar zuciya. Sai ga yaran sun fito cikin shirin islamiya sun, Ulfah ce taje
ta rumgume ta, Izzah kam ko gefenta bata kalla ba ta fice.

“Anty mun dawo baki gida”


“Eh naje wani gurin ne”

Ta faɗa tana murmushin ƙarfin hali idonta duk ya cika da ƙwalla.

“To mun tafi makaranta kina da biyar ki ba ni?”

Ta tambaya tana cizon hijabinta. Naira ashirin Kalsoom ta ciro daga jakarta ta miƙa
mata.

“Ki raba ke da Izzah”

“To mun gode”

Ta daka tsalle ta nufi ƙofa. Tana daf da ficewa Kalsoom ta kira, sai ta juyo tana
kallon Kalsoom dake hawaye.

“Ki min addu'ah kin ji?”

“To mi zan ce?”

“Kice Allah yayi min mafita”

Sheƙowa tayi da gudu ta dawo ta rumgume Kalsoom tana share mata hawayenta.

“Ki daina kukan zan miki addu'ah i love you”

“I love you too”

Ta sake ta, ta juya da gudu ta fice tana kiran sunan ƴar'uwarta.

“Ezzah jira ni......”

Sai da suka fice sannan Kalsoom taja dogon numfashi ta cire hijabinta ta shiga
gyaran falon.

YASMIN POV.

Duk irin jan kunne da kuma gargaɗin da Uxair yayi mata akan karta faɗawa kowa halin
da Namra take ciki bata ji ba. Dan ta kada samun sukuni tun lokacin data ga halin
da namra take ciki. Abin ya tsaya mata a rai, da ace ba Namra bace da kotu kawai
zata saka Asim ta nemawa Namra haƙƙinta, an suna da ƙungiyar data hana cin zafin
mata musmman mata hausawa da basa iya magana akan komai.

Daga kotu bata zame ko'ina ba sai gidan Anty. Daga Aisha sai Anty Amarya kawai ta
tarar a gidan. Daga Hajiyia Barau har su Maryam sun je walima.
Anty Amarya tayi mamakin ganinta, duk dai ta kan biyo wani lokacin idan Uzair ya
kawo ta gaishe da Hajiya Barau, sai dai ba kamar yau ba, dan ta sake sosai kamar ba
ita, ta koma Normal kamar yadda take da.

“Yau Yasmin gidan mu? Hajiya ko bata nan”

“Eh Na sani ai, dan nasan zata je walimar Fateema, gurim ki na zo ma”

“Mashallah yau tafiyar tawa ce kenan”

Anty Amarya ta faɗa tana murmushi. Aisha ta dire mata drinks sai ta bar musu falon,
daman can tun lokacin data na shiri da Namra jininta be haɗu da Aisha ba balle
yanzu da suka koma zaman doya da manja.
Sai da ta sha lemun sai ta fara tunanin ta inda zata fillowa Anty dan bata jin
zata iya faɗa mata maganar kai tsaye.

“Na ce when last kika je gurin Namra”

“An daɗe gaskiya tun mijinta na jinya, na so na koma sai tace na yi zamana ai za ta
zo, lafiya dai ko?”

“Ayyah nima samina mukaje katsina sai na biya gidan ta”

“Ai ko kin kyauta Yasmin ko ke fa? Amman ace ɗan abu kaɗan dan ya shiga sai taren
ku ya ɓace? Yadda kuke da Namra kamar wacce kuka fito ciki ɗaya da ita”

“Ni kai na da nasan haka rayuwar auren Namra zata kasance da ban hana Uzair aurenta
ba...”

Jindaɗi da Murmushin dake fuskar Anty Amarya ya ɓata, ba tare da ta ƙarasa fahimtar
gun da kalaman Yasmin suka dosa ba.

“Wani abin ne ya faru?”

“Anty da dai kin shirya kin je da kan ki kin ga Namra, kar na zama sheɗan”

“Babu wani Sheɗan Yasmin faɗa min, dan Allah ki faɗa min”

“Anty Namra tana cikin wani hali tana rayuwa irin rayuwar da babu wanda ya taɓa
mafarkin zata shige ta, gidan da take ciki na ƙone a bq sune zaune, kuma mijinta ba
shi da sana'ar yi, manja da magi take saidawa, kuma ko da naje fuskanta duk ya
kumbura da alama dukanta yayi, tayi baƙi ta lalace kamar ba ita....”

Jikin Anty Amarya yayi sanyi sosai, har ta kasa furta kalma daga bakinta, mamakin
labarin da Yasmin ta bata take ta sakarwa Yasmin ido tana kallonta har Yasmin ta
koma.tunanin wata ƙila Anty bata yarda da maganar ta bane.

“Kishirya kije ki gano ma idon ki dan Allah karki ce ni na faɗa miki”

Kai kawai Anty ta ɗaga mata ta kwanta a kujera ta lumshe ido tana yaƙi da hawan
jinin dake son taso mata. Yasmin na ganin hakan gabanta ya faɗi sai duk tsoro ya
rufe ta kar wani abu ya samu anty ace ita ce, da sauri ta ɗauki makullin motarta da
wayarta ta fice.

RASHIDA POV.

Tana aiki wayarta tayi ringing, amman bata ɗaga ba sai da ta kammala dukan abinda
take. Sannan ta duba Number mai kiran.
Cousin ɗinta ce Shafa wacce suke aiki a asibiti ɗaya da Hilal.

Sai da ta kiran numbers ɗin da suka kira bayan ita suka gaisa suka yi maganar da za
su yi sannan ta kira Shafa.

“Matar likita, ina ta kira baki ɗaga waya ba”

“Wallahi ina office ne aiki yayi min yawa, ya kike?”

“Au har kin samu damar aikin ɗan ki na kwamce asibiti”


“Ɗa na? Ɗa na na cikina ko na ƴan'uwa”

“Wai tsaya karki ce min baki sani ba”

“Wallahi ban sani ba me ya faru?”

“Wallahi ɗa zu da safe aka kawo shi guraren goma wai ya ci guba daker aka ceto shi”

“Guba...?! Garin ya?”

“Wallahi ban sani ba, mu dai muka taimaka masa gurin coto rayuwar yaron. Ni kam
nayi mamakin rashin ganin ki a gurin”

“Guba ta bama ɗana kuma?”

Rashida ta faɗa cikin kuka.

“Au wai baki sani ba? Zance duk ya karaɗe asibiti ɗan doc ya ci guba an kawo shi
asibiti, amman dan Allah ki rufa min Asiri karki ce gare ni kika ji”

Kashe wayar Rashida tayi ta tashi yana kuka ta fice daga office ɗin. Tana fitowa
kowa ya soma tambayar ba'asi ganin tana kuka.

“Kishiya ta ce ta sama ɗana guba, yana can asibiti”

Kowa Amsar data ke basa kenan. Su kuma sai tsinewa Kalsoom Albarka suke suna
aybantata. Kamin ta ƙarasa gurin motarta har ta kira su Momy ta faɗa musu.
Wani irin kuka take tana tuƙin motar har cikin ranta take jin abinda Shafa ta
faɗa mata. Kamin ta ƙasara asibitin ana ta kiranta numbers ɗin ƴan'uwa da alama
suma sun ji ne.

AMIRA POV.

Wani kalar daɗi ne ya baibaye ta tun lokacin data ji Ummi na labarta ma ƴaƴanta
Abdool na nan zuwa dan sun gama meeting ɗin da zasu yi, ya samu free days zai dawo
gida yayi su, daman tun faruwar abin nan be zo gida ba.
A ranta take shirya irin nata tabarda zata masa, wanda take tunanin zai ɗauki
hankalinsa izuwa gareta. Girki ne abinda ta fara kawowa a ranta dan tasan ta ƙware
a wannan fannin. Sai dai matsalarta ɗaya Amal dan itace mai cewa ba zata ci abinda
Amira ta girka ba, a kullum idan Amira tasa hannunta a abincin gidan sai ta ce ba
zata ci ba.

Ta baro part ɗin falon inda take zaune ta nufo gurin da Ummi take zaune ta zauna
ƙasa kusa da Ummi kamar ta shige jikinta.

“Eh haka nek son ayi idan ya dawo sai kuje a duba gidan nan a gyara a zuba sabbin
ƴan haya, dan gidan marayu ba a barinsa haka”

Sai da Ummi ta ƙare zancen da take sannan ta kalli Amira dake ƙasa zauna tana
murmushi.

“Amira akwai da son jiki kamar Abdool”

Amira tayi murmushi idonta na cika da hawaye.

“Haka nake jin ki kamar mamana kina tuna min da mamana sosai, yanayin rayuwarki”
Hawaye ya silalo daga idon Amira, wannan maganar har cikin zuciyar Amira take,
tabbas tayi missing Ammy gashi kuma bata san ranar da zata sake haɗuwa da ita ba,
bata san halin da take ciki ba.
Zubar hawayen Amira yasa Ummi ta ji babu daɗi, wannan karon da kanta tasa
hannunta ta share mata hawaye.

“Ki daina kuka kin ji? Zan zame miki uwa inshallah, kuma nan gaba zaki koma gurin
uwarki na miki alƙawari”

“Na gode”

Ta rumgume Ummi tana wani irin kuka mai taɓa zuciya........

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *54*

Hankali a tashe ta isa asibitin, hawaye na bin fuskarta. Duk wanda ya ganta a
lokacin sai ya tausaya mata dan sun san abinda ya kawo ta asibitin. Daman tuni
labarin ya karaɗe asibitin cewa Amarya Doc ta saka ma ƙaramin ɗansa guba. Sai ma a
yanzu ne wasu ne suke jin cewar Doc ya rabu da Rashida.
Kowa tsinewa Kalsoom yake wasu na faɗin daman kishiyoyin yanzu haka suke su shigo
su kore uwargida kuma su mallake ƴaƴan miji da miji.

Wani irin banka tayi ma ƙofar office ɗin Hilal ta shiga kamar zata tashi ɗakin.

“Ina ɗa na yake?”

Shine abinda ta tambaya hawayen na bin fuskarta. Ɗagowa yayi daga dafe da kan da
yake ya kalleta. Be yi msmakin ganinta ba daman yasan zata zo tun da akwai
ƴan'uwanta a asibitin da zasu kai mata labari.

“Ina ɗa na yake Hilal?”

Ya sake tambaya ganin yayi mata ƙuri da ido kamar ba dashi take magana ba.

“Ɗan ki ko ɗa na?”

“Ɗa na, si kai baka san zafin sa ba da baka bari wata ta kai ga ba shi guba ba”

Miƙewa yayi tsaye ya daki teburin dake gabansa.

“How dare you, idan kin san zafinsa ai bs zaki taɓa zuwa wani gurin ki aikata zina
ba, ba zaki taɓa bada kan ki ga kowa ba sai ubansu, amman haka kika taka igiyar
aure Rashida kika tsallae ƴaƴanki kika aikata zina da namijin da ba muharramin ki
ba, na ƴi nadamar haɗa zuri'ah dake da ace wats na aura ba da rayuwar ƴaƴana bata
kasance a halin data kasance a yanzu ba”

Tun da yake maganar take baya baya har ta jingiya da ginin ƙofar idonta na hawaye.

“I need to my son”

“You won't see him”

Ta muna kanta yana mamakin yadda duniyar Hilal ta birkice mata.

“Hilal ni ce!”

“And so what? Get the hell out of my office”

“Kotu zata raba mu da kai ba zan ƙyale kai da matarka ku kashe min ɗa ba”
Ta buɗe ƙofar da ƙarfi ta fice. Be damu ba dan yasan ya riga ya kulle ɗakin da
Rafiq yake ciki tun bayan tafiyar Kalsoom.
Ba shida wani aiki amman haka ya zauna a office ɗin dan baya son zuwa gida kwata-
kwata gidan ya fita aransa.
Haka ya riƙa karɓar masu shigowa suna masa jajen abinda ya faru tare da masa
Allah ya tsare gaba, wasu kan tambaye shi ta ya lamarin ya faru wasu kuma su kuma
basa tambaya ganin kamar cin fuska ne.

Bayan yayi salla magariba ya koma ɗakin da Rafiq yake ya zauna yana kallonsa. Ga
dukan alamu ya samu sauƙi dan bachinsa yake hankali kwance, humfashinsa na tafiya
dai-dai kamar yadda ake so. Ana daf da kiran salla isha'i Hajiya ta iso tare da
wasu ƙanensa.
Hilal na ganinta ya tashi a kujerar da yake zauna ya miƙa mata ta zauna, sannan
ya soma miƙa mata gaisuwa. Bata karɓa ba ta kalli Rafiq cikin tausayi tace

“Hilal ya aka yi haka ta faru? Wai Kalsoom tasa masa guba?”

Shiru yayi yana tunanin ta ta inda zai soma maganar da bata daɗin faɗi. Idan har ya
amsa da ita ɗin ce bashi da tabbaci ita ɗin ce idan kuma ba ita ba ce to wanene
bayan daga ita sai Rafiq ne abin ya faru?

“Wallahi ina meeting ta kirana ni ban ɗaga ba sai daga baya na kirata sai ta ce min
na zo fida Rafiq babu lafiya, ina zuwa na tarar bakinsa na kumfa ko da na ɗauko na
kawo sa asibiti kamar ba zai yi rai ba, bincike dai ya nuna guba ya ci. Tun ɗazu
aka masa hoto amman ban karɓo ba”

Hajiya ta taɓa hannu tana salati.

“O o ita kuma haka take? Hilal baka dace da matan ƙwarai, yanzu ɗan wannan ƙaramin
yaro ko kashe tayi me zata ji? Kai duniya”

Shi dai yayi shiru be ce komai ba, hannyensa zube a aljihu. Kamin su ƙara cewa wani
abu sai ga Ummu Faisak ta turo ƙofa ta shigo fuska babu annuri irin yau tana cikin
masifa ɗin nan.
Hajiya tayi mata kallon marar kunya da tarbiya ganin yadda take huci kamar baƙin
maciji.

“Haba Maman Faisak ai ko ɗakin kafirai ne kya dokko ƙofa kamin ki shigo balle
musulmai”

Uffan bata cewa Hajiya dan tana cikin zafin rai tasan kuma idan har tace zata tsaya
maidawa Hajiya magana to dukansu rayuwarsu sai ta ɓace dan Hilal ba ƙyalewa zai yi
ba.

“Ɗa zu Adda Rashida ta zo nan ka hana ta shiga ta ga ɗan ta, akan wanenen dalili ko
ita ba uwarsa bace? Ba zamu ɗauki tsarin wulaƙancin da kake son mana ba akan
shegiyar matar ka, ta fitar da Rashida cikin gidan yanzu kuma tana son ta bi
ƴaƴanta ya kashe, idan ba zaka iya wani abu ba mu za mu iya dan ba zamu zuba ido ta
kashe mana ƴaƴa ba”

Wani wulaƙantancen kallo Hilal ya watsa mata kana yaja tsaki, sannan ya kai hannu
ya kwaɓe wayar wata ƙanwar Rashida dake ɗaukar Rafiq a waya.

“Ku fita ku bani guri ko nasa ayi muku wulaƙanci, idan ita Rashida bata iya ba ke
taya zaki iya, banza a banza, ko dan kina ƴar jarida? Ku fitar min daga office
yanzu nan”

“Za mu fita ai bamu zo dan zama ba, amman ka jira sakamakon ka, ba za mu ɗauki a
wulaƙanta mana ƴar'uwa ba”

Cewar Khady sannan ta duƙa ta ɗauki wayarta, Suka fice. Hajiya ta dafe kai.

“O Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wannan masifa da me ta yi kama? Hilal ka


rabu da matar nan ka huta daman masu tsantsar ladabi sun fi komai cuta”

Balki ta taɓe baki.

“Ni wallahi ban zata Kalsoom zata iya aikata haka ba, shiyasa ake cewa baka shedun
mutum, mutum mugun ice”

“Hilal ka rabu da matar nan tun wuri kamar abin yayi maka yawa, ko ma shari'ah za
su yi da ita suje can su yi amman ba tana gidan ka ba, sannan duk mace data fara da
ƴaƴanka wata rana akan ka zata faɗa”

“Idan na rabu da ita kuma.. Da wa zan zauna”

“Sai ka nemi ƴar gidan malamai ka aura, kai ni ma zan nema maka ga mu da su a
family masu hankali da natsuwa”

“Amman Hajiya zai zama ina ta aure aure”

“Ai kowa ya ji dalilin ka dole ya ɗaga maka ƙafa, amman ni gasjiya ban baka
shawarar zama da matar nan ba”

Agogon hannunsa ya kalla.

“An kira Salla bari naje kar na rasa jan'in”

“Muma ai tashi za mu yi, amman wa xai kwana da shi?”

“Ni zan kwana da shi gida zan koma na canja tufafi sai na dawo”

“A'a ga Balki da Amina ai zasu iya kwana a nan”

“Akwai abubuwan da zan masa idan ya farka, so zai fi kyau na kwana da shi ɗin”

“Allah ya sauwaƙe ya bashi lafiya”

“Amin ya rabb”

Tare suka fito, sai da ya raka su gurin mota sannan ya nufi masallacin asibiti yayi
salla isha'i.
Bayan ya fito daga masallaci ya koma office ɗinsa ya kulle office ɗinsa sannan ya
nufi ɗakin Rafiq ya duba ya fito ya nufi gurin da aka tanadar likitocin asibitin su
yi fakin ɗin motocin su.
Motarsa ya shiga, yayi mata key. Har ya fita harar asibitin be daina jin baya son
zuwa gida ba. Be ƙara jin gidan ya fita ransa ba sai da yayi farkin harabar gidan.
Ya ɗan daɗe cikin motar sannan ya fito.ya shiga cikin gidan.

Da gudu Ezzah da Ulfah suka zo suka rumgume ahi suna masa sannu da zuwa. Durƙusawa
yayi a gurin yana shafa kansu.

“Dady Anty tana ta kuka tun ɗazu tace min Rafiq be da lafiya wai yana asibiti”

Ulfah ta faɗa tana wasa da rigarsa.


Be ce musu komai ba sai kawai ya nuna musu kujera alamar suje su zauna. Ezzah ce ta
riga zuwa dan yau tana cikin nishaɗi, ganin Kalsoom na kuka duk yasata jindaɗi
kamar wata kishiryarta.

Tashi yayi ya shiga ɗakinsa. Kwantawa yayi saman gadon ya lumshe ido yana sauraren
kansa da ke tsarawa. Buɗe idonsa da zai yi ya ga Kalsoom tsaye a kansa hawaye
shaɓe-shaɓe a fuskarta, ta canja kama sosai fuskarta ta ɗan zurma idonta kuma ya
kumbura har bata gani sosai da shi.

“Ya aka yi?”

Ya tambaya yana tashi zaune.

“Ya jikinsa?”

Maimakon ya amsa mata sai kawai ya miƙe tsaye ya soma cire kayansa har ya ɗaura
tawul be ce mata komai ba sai kawai ya shige bathroom. Ta so ta nuna masa takardar
sammaci da ɓoye a bayanta wanda Rashida ta aiko mata, amman rashin samun damar haka
yasa ta juya ta koma ɗakinta, cikin wani irin baƙiciki da take jin kamar ta mutu a
yau ta huta.

Bayan ya fito wanka ya saka wasu tufafin ya ɗauki abinda yasan zai buƙata ya fice
daga gidan. Har ya kai gurin mota sai kuma ya dawo yayi ma yaransa sallama tare da
shafa kan su ya samu albarka sannan ya fice.

ANTY AMARYA POV.

Ta daɗe kwance a gurin tana jin zujin da zuciyarta take mata ga numfashinta dake ta
sama. Daker ta unƙura ta tashi ta ɗauki ruwan da aka kawo ma Yasmin ta sha. Sannan
ta samu ɗan saussauci.
Ko da Aisha ta fito har abun ya ɗan kwata mata. Ita ma sam bata jidaɗi labarin da
Anty ta faɗa mata na Namra ba, duk da tana ƙarama amman sam be mata daɗi ba, kukan
Anty Amarya yasa ita ta fara rera tana kukan tana bawa Anty haƙuri.

Sai kusan la'asar Maryam da sauran ƴan gidan suka dawo, suma duk ba su jidaɗin
yadda suka samu Anty ba, dan abinda suka zo dashi na walima sai duk suka kasa a ci.

“Ni daman na yi mamakin hana mutane zuwa gidanta da take wallahi daman nasan ba ban
xa ba”

Cewar Maryam tana riƙe da hannun Anty Amarya dan tausasa mata zuciyarta.
Anty ta share hawayen ta

“Zuwa zan yi na zo da ita, gobe goben nan, bana son na mutu na barta a cikin halin
damuwa, ita ce yayarku idan bana da ita za zata riƙe ku. Ba ina ƙyalar talauci bane
amman wannan rayuwar sam bata dace da Namra ba”

“Amman Abbah zai bari kuwa?”

Cewar Hindatu dan tasan halin Abbah idan yace A'a to a'a ne no matter what.

“Ba zan faɗa masa da ita zan zo ba, sai idan na dawo ya ganta, idan kuma ya ce ba
zata zauna masa a gida ba, to zamu bar masa gidansa ni da ita, ban san minene yake
bibiyar Namra ba, ina jin tsoron wannan rayuwa nata”

Maryam ta sauke ajiyar zuciya.

“Amman Anty kin san Abbah ba zai bari kije ba”


Anty tayi shiru tana sauraren sanyin ac dake tsara jikinta. Duk wata magana da suka
yi a tsakanin su suka yi ta Anty bata sake cewa komai ba, dan jin take zuciyarta ta
riƙe har cikin bayanta. Sai dare ta nufi part ɗin Abbah a lokacin ta tabbatar ya
gama cin abinci duk da tasan yau ba girkin ta ba ne.

Yana ganinta yasan akwai damuwa a fuskarta, dan ya karanci matarsa sosai, yakan
gane nishaɗinta da kuma akasin haka, a duk lokacin daya kalli fuskar sahibarsa.

“Lafiya dai ko? In ce ba ni nayi laifi ba?”

Tun kamin tayi magana yayi mata tambayar ƴana kallon yanayinta, gaba ɗaya
hankalinsa ya tattara ya koma gurinta. Ita kuma ta kasa magana saboda Hajiya da ke
badroom ɗinsa tana gyara zanen gwadon da bata samu canjawa ba ɗazu saboda fitar da
suka yi. Sai da ta gama abinda za tayi ta fita sannan Anty ta zauna dai-dai gaban
Abbah tana shirin masa kuka ta soma magana cikin muryar data san shiga ƙwaƙwalta,
dan tasan Abbah baya son kukanta, duka kuwa da ita ɗin ba ƙaranar yarinya ba ce
amman wani lokacin haka zata sashi gaba tayi ta masa kuka akan abubuwa.

“Gobe da safe ina son naje katsina, sai na dawo da yamma”

“Gurin me? Miya faru?”

“Namra bata da lafiya ina son ganin ta”

Yayi shiru kamar be ji ba. Babu abinda yake tunanin sai maganganun Hajiya Barau
data faɗa masa shekaran jiya akan halin da Yasmin ta samu Namra.

“To ki shirya sai direba ya kai ki, amman dai ganin kawai zaki yi, karki ɗauko min
ita, dan ba zata kashe aurenta tazo gidana ta zauna ba, ko bana da rai ban lamunta
ba”

Anty bata musa masa ba, dan tasan idan ma tace xata tsaya jayayya dashi sai su
kwana a nan suna yi abu ɗaya. Amman dai tasan idan har ta dawo da Namra, duk abinda
zai faru sai dai ya faru idan ma ya tsaya haƙai akan Namra ba zata zauna masa a
gida ba ita zata bar masa gidan wanda ta san ba zai so haka ba.
Tashi tayi ta karɗe jikinta ya fito daga part ɗin xuciyarta da ɗan sanyi barinta
da Abbah yayi taje gurin Namra.

Tun cikin daren Anty ta soma shiri, ta kuma kira driver ta faɗa masa sai yaje gidan
man Abbah ya cika motar dan ta faɗa masa tun 6 zasu kama hanya dan samun dawowa da
wuri.
Duk yadda Maryam ta so binta Anty ƙiyawa tayi dan tasan zasu iya rigima da Asim
can, Aisha da Hindatu kuma makaranta.

*WASHE GARI...*

Kamar yadda tace tun da tayi salla asuba ta shirya, sai dai bata ci komai ba dan
bata jin cim abinci daman haka take idan zata yi tafiya balle kuma tana cikin
rashin daɗin rai.
Har gurin mota suka rakota. Hajiya Barau kam ta window ta tsaya tana leƙenta tana
tabe baki zuciyarta cike da gulma kala-kala, ganin Anty amarya bata faɗa mata inda
zata ba tasan baya da buƙarta ta san inda zata je, ita kan ta bata tabbacin inda
zata ɗin dan Abbah ba lallai ne ya faɗa mata ba, dan ba kasafai yake faɗa ma sirrin
wata matar ga wata matar ba.

Tun da suka kama hanya babu abinda Anty taje sai salati da istigifari. Duk bayan
awa ɗaya Maryam take kiranta ta tambaye ta ya hanya, Hindatu ma da take makaranta
ba abarta a baya ba, ta kan kira ta tambayar.
Hakan suka share awa shida suna tafiya a hanya ba tare da sun tsaya ba. Ba laifi
direban yana ɗan gudu dan Anty ce ta buƙaci hakan ta matso ta ganta gurin ƴarta.
Ana saura awa ɗaya su isa Katsina motarsu ta fara basu matsala, Anty ta tsorota
sosai ganin a hanya suke, sai direban ya riƙa ƙoƙarin kwantar mata da hankali akan
cewar zasu isa lafiya kamin ta tsaya in yaso sai su samu wanda zai duba musu ita a
can katsina ɗin.

Sun isa Katsina lafiya, sai a mararraba motar ta soma gaba tana baya, hakan yasa
direban fakawa gefe ya fito yana duba motar.
Anty ma fitowa tayi tazo ta tsaya gaban motar gurin da direban yake tana duba
abinda yake taɓawa tare da tambayar abinda ya samu motar.

Motocin dake kai da kawo babu wacce ta tsaya, sai wata kafirar mota mai matuƙar
kyau da ɗaukar hankali, ita har ta wuce sai ta dawo kusa da su ta faka.
Buɗe motar Abdool yayi ya fito ganin dattijowa kamar Anty a cikin zafin ranar nan
ya hana shi wuce ce, dan daga gani yasan motar ce ta tsaya. Cikin wani irin taku ya
ƙaraso gurin, shi ba na sauranta ba ba kuma na yana sanye da kakin soja ba.

“Lafiya me ya samu motar?”

“Wallahi muna tafiya ne ta fara bamu matsala ina jin ko ingin ne”

Matsawa yayi ya duba motar ya buɗe abubuwa ya gani, sai ya koma motarsa ya ɗauko
ruwa da baƙin mai ya zuba mata sannan ya maida komai ya gyara shi kamar yadda yake.

“Shiga ka tashi motar mu ga”

Da sauri direban ya shiga ya tashi motar yayi baga yayi baya yaga ta dawo normal
sai ya faka ya fito yana godiya.

“Mun gode Sosai”

“Ba komai amman a riƙa kula da irin waɗannan idan za'ayi tafiya mai nisa”

“Inshallah mun gode”

“Allah yayi maka albarka”

Anty Amarya ta faɗa tana ɗan murmushi, dan tasan ko waye Abdool tun da tana ganinsa
a tv, sai dai bata tabbatar da shi ɗin ne ba tun da ya tsaya ya taimake su, sai dai
kuma kakin dake jikinsa da stars sun nuna haka.

Ɗan rinawa yayi yana murmushi.

“Amin Mama na gode”

Juyawa yayi ya koma motarsa. Suma suka shiga tasu, da hau titi sai da ya ɗaga musu
hannu sannan ya cigabansu da mugun gudu.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *55*

*NAMRA POV.*

Yau kan ta ɗan samu sauƙi ba kamar jiya ba. Dan yau har aiki ta samu tayi, ta gyara
gidan tas sannan tayi wanke-wanke, sannan ta shiga tayi wanka. Ta shirya cikin
baƙar abaya sannan ta fito harabar gidan ta ɗauko murhunta na gawai ta ɗora girkin
rana.
Bayan ta ɗora ta tashi ta koma cikin ɗakin ta ɗauko tabarma da filo ta shimfiɗa,
dan ta soma jin ciwon kan na taso mata.
Bachine ya soma ɗaukarta, sai gyangyaɗi take, bata son yin bachi ta bar girkinta ya
ƙone. Hakan yasa ta tashi ta wanke shimkafa ta zuba ta gyara wutar sai ta koma ta
xauna tana kallon gate dan horn ɗin ta take ji ta yi yawa.

Bata jin za ta iya zuwa ta ga mai horn ɗin, duk da tana jin a gidan ake horn amman
bata zaton za tayi wani baƙo mai mota, da zai iya zuwa gurinta yanzu.
Kwantawarta tayi tasa ɗan tsinƙe tsintsiya tana gyara akaifarta. Bata ɗago ba har
sai da aka turo ƙofar gate ɗin aka shigo. Sannan ta ɗan juyo taga ko waye ne. Ganin
Anty yasa ta tashi tsaye da sauri tana mamakin ikon Allah. Mafarki take ko gaske?
Anty ce ko aljanarta? Tsaye tayi a gurin kamar an dasata. Idan har da gaske Anty
zata yi farinciki ganinta dan tayi marmarinta sai dai kuma bata fatar amAnty taga
ganta a halin da take ciki.
Bata gasgata Anty bace har sai da ta ƙaraso inda take ta dafa tana mata kallon
mamaki dan duk yadda Yasmin ta faɗa mata sai taga abun yafi haka muni.

“Namra...!”

Rumgume Anty tayi ta fashe da kuka. A maimakon Anty ta rarrashe ta sai kawai ta
tureta daga kafaɗarta.

“Wane irin hali ne wannan Namra? Jibe ke, a haka kike zaune kamar baiwa? Namra me
yake ƙwaƙwalwarki? Kina rayuwar da ko amafarki ban taɓa tunanin za kiyi ba?”

“Idaba nake Anty, bautar Allah na ke, talauci da arzki duka na Allah. Da ace
talakawa Allah yayi mu da sai dai mu hange wasu masu kuɗi suna sha'aninsu, mu muna
cikin talauci. Dan kawai ina ƴar mai kuɗi ba shi yake nuna zan dauwama a daular
duniya ba, duk wanda yayi arziki dole ne arzikin ya barsa ko kuma shi ya mutu ya
bar arzikin, amman ba'a dauwama da duka biyu”

A natse take maganar cikin hikima tana son Anty tayi ma maganarta karatun ta natsu,
ƙoƙarin lurar da Anty take kwaɗayin dukiya ba zai sa ta ƙi zaman aure ba. Ajiyar
zuciya Anty ta sauke, tabbas ba xata iya canja abinda Allah ya rubuta ga Namra ba,
amman tana ganin rashin dacewa a zamantakewar auren ta, wanda abu ne mai wahala da
iya ɗauke idonta akan haka, bayan kuma tasan Asim ɗin ba dan Allah yake zaune da
ita.

“Namra wannan rayuwar bata kamace ki, ƴar gata ce dubi inda kike zaune, yaushe
gidan ya ƙone? Baki faɗa ba? Kina tunanin zurfin ciki zai miki magani ne?”

Ta share hawayenta ta hannun rigarta.

“An daɗe da yin gobarar, ban faɗa ba ne saboda ba lalle bane ku yarda a wacan
lokacin”

“Je ki haɗa kayan ki, gida zamu je yanzu, zaman ki a gidan nan ya ƙare, an faɗa min
har dukan ki Asim ya ke Namra wai me ke toshe miki ƙwaƙwalwa ne?”

Gabanta ya faɗi, tana jin rashin kyautawa a abinda Anty take ƙoƙarin aikatawa, dan
me zatayi tattaki dan kawai ta kashe mata aure?

“Abbah ne yace ki zo da ni?”

“Ki shiga ki ɗauko hijabin ki na ce...!”

Anty ta katsa mata tsawa... Ja da baya Namra ta yi tana hawayen

“Ba zan biki ba Anty, Abbah ya faɗa min kar na kuskura na tunkaro gidansa da sunan
saki ko yaji, ya nanata min lokacin da naje gida, ya ce duk na zauna masa a gidan
sai dai ya kore mu ni da ke. Ba zan kashe miki aure ba, ba zan ƙara jefa kai na a
halaka ba, mutane ba zasu jefe ni da biyu ba, ace na kashe miki aure kuma na
bijirewa mahaifina”

Har cikin zuciyarta take faɗin haka, dan ta haƙiƙance a ranta ba zata taɓa biyar
Anty ba, ba zata ja mata wani zagin ba, sai ace taje ta kashe mata aure. Bayan kuma
tasan Abbah ba zai taɓa yarda ta zauna a gidan sa ba, ta kuma san Anty zata iya
rabuwa da Abbah akan ta.
Wani irin kallo Anty take mata na mamaki da rasa abinda zata ce mata.

“Namra ke ba cikakkiyar mutum ba ce, ke rabin mutum ce! Ban san wanda ta haife ki
bayan ni ba, da sai nace ke ba ƴata ba ce, ina da sanyin hali amman be kai ka ki
ba ke sakarya ce, marar hankali dabba wace bata san ciwon kan ta ba. Na yi tunanin
kin yi hankali na ɗauka kin gane inda duniya take a yanzu, ashe ke wawuya ce....”

Cikin zafin rai da ɓacin rai Anty take maganar sautin muryarta na fita ko'ina da
ace ba babban gida bane da tuni an yi musu taro. Hawayen takaici.

“Na yi hankali Anty kuma zan zo gareki idan har Allah ya ƙaddaro rabuwa da tda Asin
ya bani takardar sallama”

“Tam Allah ya ba ku haƙuri zama”

Ta duƙa ta ɗauki carbinta daya faɗi sannan ta miƙe tsaye ta kalli Namra da kyau da
kyau. Sannan ta juya ta soma tafiya jiki ba ƙwari.
Rugawa Namra tayi a guje ta sha gabanta ta rumgume ƙafatunta, tana kuka sosai.

“Dan Allah Anty karki yi fushi da ni, dan Allah ki fahimci ne”

“Ba zan taɓa fushi dake ba Namra, ba zan tdine miki ba, Allah yayi miki albarka,
idan kin lalace dole za a ce ƴata ce, idan kin ɗaukaka dole kuma ace ƴata ce, amman
ba zan sake wauwayar gidan auren ki da Asim ba ko da kuwa gawarki ce a ciki, kar
kuma ki sake roƙo na komai, ba zan baki ba matuƙar ba ki yi hankali ba kisa wannan
a zuciyarki...!”

Ta janye ƙafarta ta bar Namra nan tana aikin kuka, ta nufi gate hawaye ya gangaro a
idon Anty. Wani irin kuka Namra take, kukan da ita kanta ta manta when last tayi
irinsa, ko ba komai tasan ta ɓata ran Anty, tabbas Asim ba mijin aure ba ne, amman
ta yi alƙawarin zama da shi har iya rayuwarta dan kawai ta cika umarnin Abbah. Idan
har ta bi Anty a yanzu duniya zasu zage ta ita da Anty kuma zata ƙara ɓata ran
Abbah.

Tashi tayi taje gurin gate ɗin ta tsaya tana kuka, tana kallon motar Anty har ta
suka bar unguwar. Sai ta zube a gurin ta ƙara fashewa da kuka tan mai jin kamar ta
falla da gudu ta bi Anty.

Iya hawayen da Anty tayi a gidan Namra ne hawayen tausayin Namra, har ta suka isa
gida bata sake wasu hawayen ba, dan yanzu ta fahimci Namra ba abar tausayu bace tun
da bata tausayin kanta. A hanya Namra nata kiranta amman ta ƙi ta ɗaga wayar.
Su Maryam tun kamin ta yi musu bayani suka fahimci komai tun daga yanayinta da kuma
ganin ba a zo da Namra ba.

Bayan ta huta ta faɗa musu abinda ya faru, duk basu jidaɗi ba, musamman Maryam da
tafi so zafin rai, kasa haƙuri tayi har sai da ta kira Namra ta yi mata faɗa kamar
wata yayarta.

A ɓangaren nan kam


Haka ta wuni cikin kuka daman aikinta ne shine ya zame mata abokin fira. Sai goman
dare Asim ya dawo kamar yadda ya daba yana ganin yanayin Namra ya san ba lafiya ba,
amman saboda mugun hali yaƙi ya tambaye ta damuwarta.
Sai ƙoƙare kai mata buƙatarsa yake. Ture masa hannun tayi ta tashi zaune cikin
ƙunar zuciya ta ce

“Aikin kenan, Asim ka rako maza duniya, kai wayayye amman wayewar ka bata maka
amfani ba, babu ruwanka da damuwa kai dai na gurka kawai ka ci, dare yayi ka kawo
min buƙata, shine kawai...!”

Nuna kansa yayi duk da ɗakin babu wani haske sosai.

“Ke ni kika faɗa ma wannan maganar? Wuyanki yayi kauri ko Namra? Kin rai nani
saboda bana da naira saboda ni takala ne ko?”

“Idan har talaucin ya dame ka miyasa baka yi ihun arxikin ya zo maka ba? Miyasa
idonka ya rufe akan neman abinda za ka mutu ka bari, kai ne baƙon arziki shiyasa
kake yawantar faɗarsa”

Tashi yayi ya ƙara motsa kusa da ita da zimmar dukanta, jikinsa har bari yake.

“Ni kike faɗawa wannan maganar Namra? Ni sa'anki ne?”

Mari ya kai mata ta gauce, ta fita waje da sauri. Bata zame ko'ina ba sai inda take
girki, wuƙa ta ɗauko ta shigo ɗakin da ita idonta a kafe irin yau ba imani ɗin nan
ta nuna sa da ita.

“Karka kuskura kace zaka taɓa ni Asim, zan iya kashe ka Asim, baƙin cikin da yake
rai na zan iya juye maka shi a yau, tun da ka shigo gidan nan baka tambaye damuwa
na ba, baka tambaye waya mutu waya rayu ba kai dai kawai matsalarka ka sani, saboda
kai na ɓata ran mahaifina, saboda kai yau mahaifiyata ta koma gida cikin ɓacin rai,
na kira ta bata ɗaga ba Maryam.ta kira ki babu irin cin mutumcin da bata min ba duk
a kan ka Asim. Tam ya ƙare yanzu wuta ba zata sake cin ƙara ba, sai dai quta ta ci
wuta...!”

A baki take furucin zuciyarta cike da yaƙinin ita ɗin zata iya, shi kansa Asim yaga
hka idonta sai dai babu abinda zuciyarsa ta ayyana masa sai aljanu, ganin yake
aljanun Namra ne suka taso cikin daren nan. Nan da nan marar ta cika da fitsari, be
nuna tsoro a fuska ba, amman a zuci tsoron har yayi masa yawa, ala-ala yake kar
aljanun su caka masa wukar, dan shi dai yasan Namra da kanta ba zata iya masa haka
ba.
Uffan be ƙara cewa ba, sai kawai ya ɗauki tabarma da filo da abin rufa ya koma
waje ya kwanta, dan baya jin zai iya kwana ɗakin karya kasheshi cikin dare.

A wajen ma sai ya koma can nesa da ƙofar ɗakin sannan ya shinfiɗa ya kwanta. Duk
bayan minti ɗaya biyu yake farkawa ya tofe kansa da addu'a sannan ya sake komawa.
Kamin safiya ta qaye har ya matsu. Yana fita salla asuba, yai fitar gaba ɗaya.

*AMIRA POV*

Tana jin parking ɗin mota, ta ayyana a ranta cewar Abdool. Da sauri ta ƙarasa shafa
hodar da take ta ɗauki ɗankwalinta ta yafa saman kai ta biyo sawun kannensa dake
masa oyoyo.

Amal ce taje da gudu ta rumgume shi, Ummi da sauran ƙannensa kuma suka tsaya a
jikin ƙofar falo suna jiran ya ƙaraso. Hannu Amal ya riƙa suka nufo falon hularsa a
hannu yana murmushin data ƙayata kyausa.
Ɗan risinawa ya yi lokacin daya kawo bakin ƙofar falon, ya gasheta da Ummi kamar
yadda ya saba. Sai ta amsa masa murmushi tana faɗin.

“Mu duk mun ɗauka jirgi zaka biyo fa”


“Wallahi haka kawai naji ina buƙatar driving da kai na”

“Amman ka biyo haka babu kp ƴan rakiya Abdallah abinda Mai Martaba yayi ta maka
magana akai kenan, kana da maƙiya fa ya kamata kana bawa kan ka tsoro mana”

Murmushi yayi ya lanƙama Ummi suka shiga falon tana faɗin.

“Abinda Allah ya bututa babu mahani”

Amira bata jidaɗin yadda ya wuce ta ba, sai yayi kamar be ganta ba. Ba kuma dan be
ganta ba ɗin sai dai rashin kular da yake nuna mata, dan shi sam bata burge shi.

Saman kujera ya zauna tare da Mahaifiyarsa yana dariyar yadda take masa faɗan ya
take masa na zuwan da yayi ba tare da bodyguards ɗinsa ba.

“Haba ummi bodygrsd zasu tsare ni ko Allah?”

“Ni ba wani wa'azi na ce ka min ba”

Ya ɗaga hannayensa sama yana dariya. Kallonsa kawai Amira take cike da shauƙi, bata
zaci yana dariya haka ba.

Ruwan sanyi Amal ta kawo masa tare da kofi, ya sha ruwan sosai ya jiƙa maƙoshinsa.
Sannan ya tashi ya fice daga part ɗin ya nufi part ɗinsa. Tuɓewa yai ya ɗaura tawul
ya shiga banɗaki yai wanka tare da alwala, sannan ya fito ya shirya cikin ƙananan
tufafin daman sune tufafin daya fi so inda a gida yake. Sai da ya feshe jikinsa da
turare sannan ya fito. Ya nufi masallacin gidansu yai salla azahar, bayan ya gama
ya gaisa da wasu mutanen unguwar tare da sojojin da suke gadin gidan. Be fita da
komai a aljihunsa ba shi kuma mutum ne mai alheri baya jindaɗin ya ganka be baka
komai ba, sai dai kam akwai zuciya dan baya ɗaukar raini. Tsayar da mutanen yayi ya
dawo cikin gida ya ɗauki kuɗi masu ɗan yawa ya miƙawa wani soja yace ya raba masu.
Aiko har da waɗanda ba su yi salla a masallacin ba sai sheƙowa suke suna samun nasu
rabo.

Sai da ya tabbatar kowa ya samu sannan ya juyo ya dawo cikin gida. Part ɗin Ummi ya
nufa dan cin abincinsa na rana.
Duka ƙanensa suna dinning har Ummi suna cin abinci, Amira ma ta maida hankalinta
sai cin abincin take kamar bata ga shigowarsa ba, Amal ce kawai ta kawarda kai tana
yamutsa fuska kamar mai ƙyanƙyami.

Kujerarsa yaja ya zauna yana naɗe hannun T-shirt ɗinsa yana rabon ido, dan be san
wane abinci zai fara ci ba.

“Dude don't..!”

Amal ta faɗa tana yarfar da hannu.

“Why?”

“All these things wannan yarinyar ce ta girka”

Ta faɗa tana nuna Amira. Daga Ummi har Abdool ɗin da kansa be jidaɗin abinda Amal
tayi ba. Ɗan murmushi Amira ta yi, irin murmushin na rashin jidaɗi ta tashi daga
cin abincin da take ta nufi ɗakin Amal ɗin wanda yanzu ya zame mata kamar ɗakinta a
yanzu.

Sai ta ta shige sannan Ummi ta kalli Amal cikin xafin rai tace
“Dan ta girki abinci kike cewa karya ci ita ba mutum bace? Bata taimake ku ba? Bata
fiye muku wannan inyamurar da take girka muku abinci ba? Miyasa kika ɗauki rayuwa
da zafi ne Amal, ke dai baki rayu da babanki ba, balle na ce shine ya koya miki,
wannan sam sam ba ɗabi'ar ƙwarai ba ce, ɗan 'adam ba abun wulaƙamtawa be ne”

Fashewa Amal.tayi da kuka ta tashi da gudu ta shiga ɗakin Meesha. Abdool ya zuba
abinci ya soma ci yana faɗin

“Ummi you shouldn't talk to her that way marainiya ce”

“Ai daman kai kake buɗe mata ƙofar yin abinda duk take so, babu dama ayi ama Amal
faɗa a gidan nan, duk abinda take yi hundred percent kai kake supporting ɗinta”

“Ummi ba haka bane, Amal itace ƙarama a cikin mu, kuma yarinyar nan ko da ta yashi
bata san mahaifinta ba, ya kamata ace tana jin sanyi wani gurin”

Ummi tayi shiru tana cigaba da cin abinci. Tasna abinda Abdool yake faɗa gaskiya ne
da acw mahaifin su an nan da ko hararsu Ummi bata isa tayi ba, dan game da yaransa
ba shi da kyau babu mai taɓa masa komai kusancinsa da kai, musamman Amal da yake
jin ta kamar ransa. Sai dan tana marainiya ba zai bata damar wulaƙanta kowa ba,
Ummi bata da wannan halin daman can halin mahaifinsu baya burgeta, Amal ce ta
kwashe halin gaba ɗaya, sai kuma Meesha dake ko-in-kula da mutane.

“Amman shi kenan, dan tana marainiya sai ta riƙa irin wannan halin? Dubi ka ga
yarinyar nan wai har warin mutane take ji haba wannan iskanci ai har yayi yawa”

Abdool ya yi dariya

“Ƙurciya ne zata daina nan gaba kaɗan”

“Allah yasa”

“Amin”

Yaja tissue ya goge bakinsa, sannan yaja kujerar ta yi baya, ya miƙe tsaye ya nufi
ɗakin da Amira take.

Kife ya tarar da ita saman gadon tana kuka. Sai ya zauna a kujerar dake ɗakin yana
ƙarema ɗakin kallo kamar baƙonsa.

“Funny you indai akan Amal zaki riƙa kuka zaki ƙarar da hawayen ki ne kawai baki
gama kukan ba, the more Amal knowing you are crying for her the more she will do
something to insult you, haka rayuwarta take akwai ƙuruciya a cikin ta sosai”

Daga lokacin da kalaman Abdool suka fara shiga kunnenta sai ta ji duka kukanta ya
yanke, sautin muryarsa da take ji sai tsigar jikinta ta tashi. Tashi tayi zaune ta
share hawayenta, ɗaga kanta da zatayi caraf cikin idanuwansa. Eyeball to eyeball
suke kallon juna ita da shi, kowa da irin abunda yake tsaƙawa a zuciyarsa. Ita ta
riga kawar da nata idon saboda kwarjinin da yayi mata, sai ta kawarda fuskarta
gefe. Tana murmushi a zuci.

“Sorri for what Amal did to you”

“Never mind”

Miƙewa yayi tsaye ya fice ɗaga ɗakin ya nufi ɗakin Meesha inda Amal take. Ita ma
lallaɓata yayi har tayi shiru sannan ya fito ya koma part ɗinsa ya canja kaya ya
nufi gurin Mai Martaba.
Ba shi ya dawo ba sai da dare ya raba, daman duk yaje gurin Mai Martaba ko da rana
ne sai ya daɗe balle ya je late. A falo ya sami Ummi Amal na saman ƙafafunta tana
bachi, murmushi yayi ya zauna kusa da su yana kallon Amal ɗin.

“Har kun shirya”

“Ta ya za'ayi uwa da ƴa, ita ta kawo kanta tace min ta daina”

“Hmmm Amal kenan wannan ɗabi'ace kawai ta ɗan adam, amman idan kin lura har
ƴan'uwanta bata bari ba”

“Jiya ma haka suka yai ita da Haleema akan Amirar nan”

“Ai tana gama wannan makararar ƙasar waje zan kai ta tayi karatu a can a huta”

“Ta dai ƙara lalacewa”

Dariya yayi ya miƙe tsaye.

“Ummi good night”

“Aha night, Abdallah yaushe zaka koma?”

“Jibi, akwai aiki a gaban mu abuja”

“Ai kai Allah be raba ka da aiki ba, ni dai kamin ka koma ina son kaje gidan nan na
Haleema ka duba mana shi, yadda gyaran zai kasance sai ka kira yaron nan Isma'il ka
faɗa masa, dan kasan gidan marayune ƙara a gyara idan ma wasu ƴan hayar za a zuba
sai”

“Okay zaje gobe inshallah dan gobe babu inda zan je, a ina ne gidan ya ke? Tun da
akayi gobarar nan ma ban je na duba shi ba”

“Yana nan Nasarawa na can wajen gidan action kuɗi ƙasa, kasan irin abubuwan nan sai
maza, ni mace wano abu sai dai na ɗaga ƙafa”

“Inshallah gobe zanje”

“Allah ya kai mu”

“Sai da safe”

Yana hamma ya fice daga part ɗin dan duk ya gaji sosai.

*HILAL POV*

Lokacin daya isa asibitin be wuce ɗakin da Rafiq yake ba sai da ya biya ya karɓo
hoton da akayi ma Rafiq ɗazun. Sai dai ba iya ya buɗe hoton ba har ya koma office
saboda fargaba, sai yanzu ya gane irin abunda majinya suke ji idan wani nasu aka ce
yana da wani ciwon ko kuma za ayi masa aiki.

Zamansa kenan a office, sai ga Alhaji Bashir ya shigo cikin mayan tufafin na
shadda, tun kamin Hilal yayi masa uwarnin zama ya zauna yana nuna alhininsa akan
abinda ya faru.

“Ɗazu nake jin labari babu daɗi ban samu na shigo ba sai yanzu”

Ya faɗa yana miƙawa Hilal hannu su gaisa. Hilal ya maiyarda Hoton gefe ya aje yana
sosa kansa yace

“Ƙaddarori ne”

“Wallahi shiyasa kaga bana son ƙara auren nan dan rigima ce kawai ko wacce da kalar
matsalar da take zuwa da ita, yanzu miye abin na sawa yaro guba”

“Babu tabbacin ita tasa Bashir, amman dai ita kaɗai ce a gidan”

“To ai shi ya nuna ita ɗin ce, kuma kasan fa ita ta fitar da Rashida a gidan yanzu
kuma tana son ganin bayan ƴaƴanta, gaskiya abun be yi daɗi ba, ai ota Rashida tace
ba zata ƙyale ba, dan Asma'u ta ce har ta aika mata sammaci ko? Amman dai ban
jidaɗi ba gaskiya”

Hilal ya jingina da kujerarsa yana lilo.

“Ni ne na saki Rashida da kaina san ganin damana, maganar kotu kuma taje duk inda
zata je ta kai Kalsoom i will surely depend her”

Alh. Bashir ya masa kallon mamaki.

“Doc kasan abinda kake faɗa kuwa? Ɗan ka ne fa ɗan ka ta nemi kashewa”

“Kana da hujjar ita ɗin ce ta kashe shi? Amanarta na karɓo a gurin iyayenta yanzu
haka tana ƙarƙashin kulawa ta ne, dole na yi abunda zan kare ta”

“Kana nufin za ka ci gaba da zama da ita kenan?”

“What do you expect?”

Ya ɗaga kafaɗunsa.

“Nothing, ya mai jiki”

“Da sauƙi bachi ya ke”

“Okay Allah ya ƙara lafiya, ni zam koma da safe zan zo na duba shi”

Hilal ya miƙa masa hannu suka sake gaisawa.

“Na gode sosai”

Wani kallon Alh Bashir yayi masa, yana mamakin yadda Hilal ya sauya masa kamar ba
shi, duk irin tare da suke a can baya yana aure Kalsoom duk ya watsar ta ɗauke masa
hankali. Lallai yanzu ya yarda da maganar da ake cewa magani tayi masa, tun da har
Hilal ya furta zai tsaya mata, bayan kuma ɗansa ne tayi ma wannan karen aiki.

Bayan Alh Bashir ya wuce Hilal ya koma saman kujear ya zauna, yana tunanin maganar
sammacin da Alh Bashir yace Rashida ta aika Kalsoom. Duk waɗancan maganganun yayi
ne kawai dan ya nuna kamar ya san abinda yake faruwa bayan kuma besan komai, yayi
hakan ne dan bayan son ayi Alh Bashir yai insulting ɗin matarsa. Saboda ya tsani
haka.

Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin yadda zai ɓullowa lamarin. Sai kuma ya kai
hannu ya ɗauki hoton ya buɗe yana dubawa. Abinda ya gani ya tayar masa da hankali,
da sauri ya tashi yana ƙara dubawa dan tantance abinda yake ganin ɗin. Da sauri ya
bar Office ɗin ya nufi inda zai laƙa hotunan su fito a majigi...
*RASHIDA POV.*

Tana sauke wayar ta ƙara ɓata fuska, zuciyarta ta sosu matuƙa, akan abinda Alh.
Bashir ya gama faɗa mata, na cewar Hilal zai tsaya ma Kalsoom, a tunaninta shi da
kansa zai saka ta kotu yadda tasan yana jin da ƴaƴansa.

Hawaye suka zubo mata sai tasa hannu ta share. Hankalin ƴan'uwa sai duk ya dawo
kanta, daman tun ɗazu maganar da suke kenan har da wata ƙawarta wacce suka yi
makaranta a tare.

“Ke mai ya faru?”

Khady ta tambaya tana dafa ta.

“Wani abokinsa ne ya kira ni yanzu yana faɗa min wai Hilal yace zai tsayawa
Kalsoom”

Ummu Faisak ta daki ƙirji.

“Da gaske? Lallai wannan Kalsoom ɗin ta wanke ta bashi ya sanyen, kan uban nan ayi
ma ɗanka abu amman kasa yin komai har kace zaka tsaya mata”

Dukansu jinjina lamarin suke. Zainab ta kada baki tace

“Wannan abun har ƴan Human Rights sai mun saka, ai idan ya san wata be san wata ba,
ƙaramin yaro zaka bari a wulaƙanta yama baki ɗan kawai tun da bayan son zuri'arki”

Ummu ta jinjina kai.

“Hmmm Ai wallahi sai na masa rashin mutucin, dan har a tv sai na nuna su, ai daga
ganin wannan abin kinsan Hilal ba cikin hankalinsa yake ba. Kuma wallahi tallahi
matuƙar ina numfashi sai Kalsoom.ta bar gidan nan, ba ko mallaka ne aikinta wallahi
ko a gabanta bokanci ya yake saƙa sai na nuna mata shayi ruwa ne, ai ko baba da
babansa”

Rashida tayi saurin rufe mata baki 5ana kuka.

“Dan Allah ki ƙyaleta, ni dai bana iya, ita ta sani can ita da Allah”

“Ai ban ci ki iya ba bada kuɗin ki zan yi ba, amman wallahi tun da ta taɓa ki sai
na taɓa ta”

Wani yatsine yake tana tsine ɗankwali irin ita ga ga tantsiriya ɗin nan. Maimunatu
ta girgiza kai

“Daman kin yi sake tun farko Rashida Namiji kamar Hilal kinsan duk wace ta shiga
gidansa kan ba fita, ni da nice ke Wallahi da wannan abokin nasa zan aura, in yaso
ya mutu....”

Ta murguɗa baki. Fashewa Rashida tayi tda kuka tana narke musu kamar wata ta
ƙwarai, su kuma sai tausayinsa suke suna bata haƙuri....

INA JINDAƊIN COMMENTS NA KU. THANKS........🙏


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *56*

Idonsa ya cika da hawaye, jikinsa ya mutu sosai har yana ƙoƙarin zamewa ya faɗi
kamar ba Namiji ba.
Hannunya kai ya taɓa hancinsa ya lumshe, tana girgiza kai. Abinda yake bashi
mamakin results a yanzu ya nuna ba guba bace gas ya nuna kuma har yayi effecting
ɗin ƙwaƙwalwar Rafiq, that's mean zai zama wani iri kenan. Wanda abu ne mai wahala
ya koma dai-dai, ko da kuwa an ɗora shi akan ganine.

Ya daɗe idonsa a lumshe, _Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un_ Shine abinda yake ta
maimatawa a zuciyarsa. Daker ya buɗe idon ya ƙarasa ya ciro hoton ya bar ɗakin yana
mai jin kansa kamar marar lafiya.
Be shiga office ɗinsa ba sai kawai ya nufi ɗakin da Rafiq yake kansa na mugun
sarawa. Tsaye yai a bakin ƙofa yana kallon Rafiq cike da tausayin Rafiq, ya daɗe
jikin ƙofar kamar mai tsoron ƙarasawa. Juyawa yayi ya koma office ɗinsa, ya zauna
kaman kujera ya dafe kansa still takardun na riƙe a hannunsa. Babu abunda ya faɗo
masa a rai sai ya sake ɗaukar wani hoton ya gani, wata ƙila wannan ƙarya ya nuna
masa...
Ɗaga kai yayi ya sake kallon hotunan, yana sauke ajiyar zuciya. Ya ɗauki mintuna
talatin yana kallon hotunan sannan ya buɗe wani gurin ya saka su ya ɗauki abubuwan
daya shigo dasu office ɗin ya fito, da kansa ya kulle office ɗin sannan ya nufi
ɗakin da Rafiq yake. Har lokacin bachi yake abunsa, be farka ba.
Wani ɗan ƙaramin tebur Hilal ya nufa ya ɗora kayan a kai sannan ya ƙarasa gurin
da Rafiq yake yaja kujera ya zauna, ya riƙe hannunsa yana hafawa, wani irin
tausayin Rafiq ne ya ke shiga zuciyarsa.

Haka ya zauna ya tsare Rafiq da ido yana jin kamar yayi masa kuka, ko da kuskure
bachi be doshi idonsa ba.lokaci lokaci yake sauke ajiyar zuciya kana ya haɗe yawu.
Rafiq be farka ba sai kusan uku da rabi na dare. Murje-murje ya fara yana kiran
ruwa kamin ya buɗe ido. Da sauri Hilal ya tashi ya buɗe jakar da ya shigo da ita ya
haɗa masa tea ya ta sheshi zaune ya soma bashi tea ɗin, yana masa sannu kamar wani
babba.

Yana gama shan tea ɗin ya langwaɓarda kansa jikin Hilal bakinsa yai gefe kamar zai
talalarda yawu.

“Rafiq”

Hilal ya faɗa yana girgiza sa dan zuciyarsa ta katse gaba ɗaya. Ɗagowa Rafiq yayi
kaɗan ya kalli Daddynsa sai ya maida kai gurin ƙofa yana kallo kamar mai jiran
shigowar wani.
Can kuma ya ɗaga kai yana kallon ɗakin, kamin ya sake kallon Daddynsa.

Rumgumesa Hilal yayi yana hawaye. Daga bisani ya ɗauko wasu magunguna ya bashi,
sannan ya maida shi a ƙirjinsa ya kwantar. Haka suka kwana, Rafiq na kwance a
ƙirjinsa, Hilal kuma be rumtsa ba, a kan idonsa aka kira salla asuba. A hankali ya
kwantar da Rafiq yai alwala a toilet ɗin ɗakin ya nufi masallacin asibitin.

Ya daɗe yana addu'a bayan yai salla, a nan masallacin ma sai da ya gaisa da wasu da
suka sanshi har suna masa ya jikinsa ɗansa.
Sai da ya koma ɗakin ya ganshi sannan ya fito harabar Asibitin yana amsa wayar
Hajiya dake tambayarsa ya jikinsa. Be faɗa mata a results ɗin da hoton ya bada ba,
dan ba labari bane mai daɗin ji.
Ko da ya isa gida 6:30am, dan garin be ƙarasa wayewa ba a lokacin. A mota ya zauna
har 30 ɗin ta ƙarasa sannan ya buɗe ya shigo nufi ƙofar shiga gidan. A kulle ya
jita hakan yasa ya kai hannu ya ƙwanƙwasa, sai ya kawar da fuskarsa. Bayan kamar
minti biyu zuwa uku Kalsoom ta buɗe ƙofar.

“Sannu da zuwa”

Ta faɗa cikin sanyayayyiyar murya. Be amsa ba be kuma kalleta ba sai kawai ya raɓa
gefenta ta shiga cikin falon.
Kai tsaye ɗakin su Ulfah ya nufa, shiri ya tarar suna yi na makarantar
boko.Dukansu ya shafa kansu yana masa good morning ɗin da suke masa, sannan yaja su
jikinsa ya rumgume.

“Gobe za ku koma gurin Hajiya da zama, a can za ku zauna har na gama gyara wannan
gidan”

Ezzah ta daka tsalle, tana murna, Ulfah ma Murna ta yi, dan suna son zuwan gidan
Hajiya ko dan su yi wasa da ruwaz ga gidan akwai yara da yawa sa'aninsu.

“Daddy har da Anty?”

Ulfah ta tambaya cikin zumuɗi. Shiru Hilal yayi kamin ya amsa mata.

“A'a Anty a nan zata zauna”

Bata wani damu ba dan tana son gidan Hajiya, sai dai ta san zatayi missing Anty kan
sosai, a ranta take auna a weekend zata zo ta ganta.Bayan kamar minti biyar ya miƙe
tsaye ya nufi ɗakinsa. Yana tura ƙofar ɗakin yana Kalsoom zaune saman gadonsa tana
hawaye.

Be kulata ba ya nufi wardrobe ya buɗe yana cire wasu tufafin. Da kallo ta bishi har
ya gama cire kayan sannan ta soma magana cikin muryar tausayi.

“Baka buƙatar canjawa yaran ka gida Hilal, ni kake buƙatar canjaw! Ni kaina ban
cancanci zama da ƴaƴan da mahaifinsu be yarda da ni ba, ko kaɗan ɓan ga laifin ka
ba akan abinda ka aikata, ko ni kwatankwacin haka zan aikata”

Sauka tayi daga saman gadon ta durƙusa ƙasa ta haɗe hannayenta alamar roƙo.

“Ma gafarta min akan abunda na yi maka Hilal, ba zan sake hararar yaran ka ba
balle na cutar da su”

Juyowa yai ya kalleta.

“Kin Aikata kenan?”

Kai ta ɗaga alamar eh.

“Na aikata kuma ina neman ka yafe min, dan dajarar iyayenka ka sake ni a yau, irin
sakin da aure ba zai sake shiga tsakanin mu ba, irin sakin da ko na so na yi
tunanin zuciya zata hanani, irin sakin da zan manta da wanzuwarka a doron ƙasa,
irin sakin da zai sa na cire ka a zuciya.

Ina roƙon ka Hilal karka horar da ni da irin horon da zan cutu, karka saka zuciyata
cikin ramen da ba zata iya fita ba”

Tun da take maganar hawaye take, irin hawayen nan dake hana sautin kuka fita.
Miƙewa tayi tsaye ta ɗauko takarda da biro dake gefen gadon ta zo gabansa ta aje
masa gabansa, ta miƙe tsaye ta bar ɗakin.
Notebook ɗin ya tsurawa ido yana nazarin kalamanta.

Wanka yai ya shirya cikin wasu tufafin ya feshe jikinsa da turare, sannan ya ƙaraso
gurin gadon ya ɗauki takardar yayi mata rubutu, ya naɗe ya ɗauki kayansa ya fito.

Ɗakin Kalsoom ya shiga, sai ya same ta zaune ƙasan gado tana rusar kuka. Tsayawa
yai cak yana sauraren kuka nata dake shiga har cikin zuciyarsa, be san dalili ba
duk da abinda Kalsoom ta aikata masa still yana son a zuciyarsa, har yanzu
natsuwarta da yadda take gudanar da al'amuranta burgeshi ya ke. Sai da ya ɗan yi
gyaran murya sannan ya ƙarasa cikin ɗakin ya miƙa mata takardar.Idonsa na shiga
cikin nata gabansa yayi mugun faɗuwa, ta rame sosai kamar ba ita ba, ga wani ja da
idonta yai, kamar ta saka garwashi a ciki, a take tausayinta ya rufe shi. Ita kuma
ta sakarwar takardar ido sai kallo take tana tsoron karɓa, ta haɗe yawu ya fi a
ƙirga kamin ta miƙa hannunta dake ɓari ta karɓi takardar.

“Na gode Allah ya haɗa ka da mata ta gari..”

Cikin sarƙewar murya ta faɗa bayan ta karɓi takardar. Har ya buɗe baki yai magana,
sai kuma ya fasa ya juya ya fice.

A jikim mota ya tarar da yaransa suna jiransa. Yana shiga suma suka shiga, har suka
isa scul ɗin Ulfah bata daina tambayarsa ina Rafiq ba, sai dai be amsa mata ba dan
be san me zai ce mata ba, Hilal irin mutanen nan da idan matsala ta shiga
tsakaninsa da iyalansa baya son kowa ya ji, har yaransa, dan aganinsa ba muhallinsu
ba ne.

Ƴan canji ya zaro a aljihunsa ya miƙa musu, sannan ya kama hanyar asibiti yana
neman number Rashida daya saka a blacklist ya kira ta. Ta daɗe tana ringing kamin
ta ɗauka, dan sai da ta tabbatar ta tantance cewar number Hilal ɗin ce sannan tai
picking.

“Ki janye maganar kotu nan”

Shine abinda ya fara faɗa mata, a tunaninta zai bata haƙuri ne ko kuma yai mata
wata maganar ta daban.

“Ba zan janye ba, ba za a dake ni a hana ni kuka ba, ba zaka cutar da ɗana kuma ni
ka hanani ɗaukar mataki ba”

“Ɗan ki ko ɗa na? Bakin ki yana kurkure gurin faɗar kalmar nan”

“Ai da ɗan ka ne da baka ce za ka goyi bayan ta ba, wai har ka kace zaka tsaya mata
bayan ita ce take ƙoƙarin aika ɗan ka lahira, dan kawai ta mallake ka”

Ya taka burki.

“Kar ki soma faɗa min maganar banza, ni ba wawa ba ne irin ki, kuma na faɗa miki ki
janye zancen kotunan ko kuma na faɗawa duniya dalilin sakin ki da na yi kuma try me
ki gani”

Be tsaya jiran abinda zata ce ba, ya kashe wayar. Sai ya kira wayar Alh Bashir sai
da yai masa two missing calls sannan ya ɗaga, Hilal be tsaya jiran komai ya ce

“Idan kana son shiga cikin maneman Rashida ka shiga kawai ba sai ka riƙa ɗaukar
maganar da muka yi ba ka kai mata, wannan ba girman ka ba ne”

Ya katse wayar ya jefar a front seat yana wani huci da bugu sitarin motar.

*RASHIDA POV*

Mamaki ya isheta, yadda Hilal ya juye ya zama maƙiyinta, mutumen da ko a mafarki


aka ce zai mata zata musa, balle kuma a fili.

“Lallai na yi sake da har na bar ka ka auri wata ban mallake ka a lokacin ba,
Kalsoom ki biya bokan ki haƙiƙa ya iya aiki. Zan janye maganar kotu, amman kuma
dukan ku sai kun ƙwamace kiɗa da karatu...! Wallahi wasan yanzu aka fara, Hilal sai
ka zo da kan ka ka nemi yafiya ta, Wallahi zan aikata ko minene matuƙar buƙatana
zata biya... Sai na banbance muku aya da tsakkuwa”

Tashi tai tsaye ta cigaba da shirin zuwa office da take zuciyarta a dake irin na
masara imani ɗin nan, dan a yanzu babu imani a kusa da inda take ma balle ace kusa
da ita.

Sai da ta shirya tsaf sannan ta ɗauki jakarta da keys ɗin mota ta fito falo,
already tai breakfast tun 6:30. Ɓangaren Mahaifinta ta nufa dan har Momy tana can.
Cikin ladabi ta shiga ta samu guri ta xauna ta gashe su sannan ta ɗora da..

“Daddy zan janye maganar kotu nan, mu barta kawai da Allah”

“Wallahi kin yi tunani Rashida, nima abunda naga yafi kenan, indai cin amana ne
baya taɓa ɗaurewa, Allah zai nuna mata sakamakonta tun duniya”

Momy ta faɗa cike da jindaɗin hukumcin da Rashida ta yanke. Dady yaja dogon tsaki.

“Ku kan Allah ya waddaran zuciyarku komai sai a ace a bari ga Allah? Ai musulucin
ya ce idan an yi maka cuta ka rama gwargwadon abunda aka yi maka idan ba zaka iya
yafewa ba, sannan irin wannan abun bw kamata ace a ba ga Allah ba, sai fa anje
lahira kenan fa? Haba ai ƙara ayi mata tun duniya ta kunyata dan Wallahi idan yai
wasa har shi sai nasa an kulle”

“A'a Alhaji ya kake magana kamar ba mai tunani ba? Haka sam be dace ba, hukuncin
data yanke shine dai-dai”

Ya kawarda fuskarsa daga ta Momy ya kalli Rashida dan a tunaninsa ko Momy ce tayi
mata wannan shawarar.

“Ke kina son abi miki kadin yaron ki?”

Ta girgiza kai.

“A'a Abbah na janye, na barta da Allah”

“Akan me?”

“Kawai haka naga ya fi”

“To ni zan bi kadin jika na (grandson) idan ku baku san abunda ake kira da humanity
ba, ni na sani... Tashi kije office Allah ya kiyaye hanya”

Ba zata iya musawa Dady ba kar ya zargi wani abu, sai dai zuciyarta bata so haka
ba, dan babu banbanci mahaifinta ne yasa ba ita ba. Tasan Hilal zai iya cewa wani
sabon salo ne ta mayardar shari'ar gurin Mahaifinta.

A hanyar ta zuwa office ta kira Mom Shuraim, bayan sun gaisa take faɗa mata idan ta
tashi daga aiki zata biyo ta gidanta, akwai magana mai muhimmanci da zata yi da
ita.har da narke murya tana faɗin wai tana cikin matsala, amman dai sai tazo zata
ji komai.

*ABDOOL POV*

Sai ten ya tashi bachi, dan yana yin sallah azuba ya koma bachin gajiya, farkawar
da yayi ma a yanzu ba dan ya gaji da bachi bane, sai dan son zuwa gurin da Ummi
tayi masa magana ne jiya. Be fito part ɗinsa ba sai da yayi wanka bugaggar shadda
mai tsana blue color, ta fito da shi sosai kasancewar fari sol, ga ɓaƙar hulal da
ya ɗora akansa kamar wani sabon balarabe,baƙaƙen takalmi ya saka sannan ya feshe
jikinsa da turare, ya fito daga part ɗinsa ya nufo part ɗin Ummi shaddar har amsawa
take a jikinsa, ga wani maiƙo da take kamar an zuba mata mai.

Ita kanta Ummi sai da tayi murmushi ganin yadda ɗan nata ya fito mashallah kamar ta
cinye abunta.

“Ina fatar ka yi addu'ah”

“Addu'ah me?”

“Idan mutum yayi kwaliya ya dubu kansa a madubi yana kyau yace Mashallahu laƙuwwati
illa billah, to ko wani yayi maka baki (kanbun baka) Ba zai kama ka ba, idan ma
zaka ita ka riƙa karantawa da safe kullum sau uku”

Dariya yayi yana kallon cucumber da Ummi take yankewa ya ɗauki ɗaya ya ci.

“To ni da ba mace ba miye na wani kanbu zai kama ni, amman dai zan riƙa yi”

“It better”

Ya faɗa tana cigaba da yanka cucumber take. Shi kuma ya zauna kusa da ita yana
tambayarta yaje yanzu ko sai anjima.

Ƙamshim turarensa ne ya isarwa da Amira saƙon isowarsa a falon. Ras! ras!! ras!!!
Ga banta ya faɗi kamar yadda ya basa mata a duk lokacin da ta ji ƙamshin turarensa.
Da sauri ta walƙato ta sauko daga saman gadon da take ta nufo falon idonta cike da
maitar ganin Abdool kamar bata taɓa ganinsa ba.
Cikin wata irin siga take tafiya, takalmin dake ƙafarta plate ne amman hakan be
hana su amsa amon gurin ba saboda yadda take buga da tiles ɗin gurin. Ummi ce kawai
ta ɗago ta kalleta wanda kuma ita bata so haka ba. Abdool kam ƙin ɗagowa yayi dan
sarai zuciyarsa ta raya masa Amira ce, dan yasan by this time duka ƙanensa suna
makaranta.

“Ina kwana”

Ta gaishe shi cikin ladabi har tana son risina masa.

“Lafiya”

A kaikaice ya amsa, yana mai miƙewa tsaye. Wanda hakan be ma Ummi dadi ba,sai kawai
ta kada baki ta ce.

“Amira shiga ciki ki ɗauko mayafin ki ki rana yayanki unguwa”

Ta fasa zaman da zata yi ta miƙe ta nufi ɗakin data fito. Sai da ta shige sannan
Abdool.ya kalli Ummi yana ware hannayensa ya ce

“Haba Sweet Mom ya za ki min haka? Kin san fa ni Allah be haɗa jinina da mata ba,
kuma it so annoying naje da ita unguwa”

Wani Kallo Ummi ta masa.

“Abdool... Karka soma halin Amal, tun da yarinyar nan ta zo kullum tana ciki gida
bata fita ita ma ai ƙara ta ga gari ko?”

Be ƙara cewa komai ba ganin Amira ta fito, sai kawai ya jiya ya nufi kowa yana wani
shan ƙamshi.
Ko da ta isa har ya tashi motar ita kawao yake jira su wuce. Tana shiga ya fisgi
motar kamar baya son ransa har sai da Amira ta tsorata.
Bata ce masa ba, shi ma be ce mata ba haka suka yi ta tafiya har suka isa
nasarawa. A bakin gate ɗin gidan yayi parking ya fito yana ƙarewa gidan kallom
ganin yadda ya kone.
Yana rufe gambun motar Amira ta buɗe ta fito, sai ya kalleta ya ce

“Ba daɗewa zan yi ba, kina iya zama a cikin kamin na dawo”

Ba musu ta koma cikin motar ta zauna, zuciyarta cike da tunani kala-kala.

Baya tunanin akwai mutane a gidan dan Ummi bata faɗa masa ba, hakan yasa be yi
sallama ba ya tura kofar gate ɗin kawai ya shiga ciki. Gaban gidan ya fara dubawa
kamin ya zagaya baya, tana nan ya hango mace tana girki a BQ. Hannayensa yasa
aljihu ya nufi bq ɗin yana sallamar da kusan shi kaɗai ne zai iya jinta, sai kuma
wanda yaga bakinsa ya motsa.

Namra na ganin mutum tayi saurin komawa ciki ta ɗauko hijabinta ta saka sannan ta
fito. Ko da ta fito har ya ƙaraso bq ɗin yana ƙare ma bq ɗin kallo dan ita bata yi
komai ba.

“Haba Malam waye kai zaka shigo babu sallama”

Dago da dubansa yayi gurin mai maganar. Ganin Namra yasa numfashinsa hijira daga
jikinsa ma ɗan wasu daƙiƙu, sannan ya dawo. Be ɗauke idonsa daga gareta ba be kuma
kyafta ba, haka ya ƙafe da ido kamar wani hoto. Nan da nan zuciyarsa ta soma rabawa
jijiyoyin jikinsa jini da ƙarfi.
Rassss rassss rassss gabansa yake faɗuwa, sai dai kuma ba irin wacan faɗuwar ba,
ta tsoro ko fargaba, faɗuwar gaba ne da shi kansa ba zai iya fassara na minene ba.

Ita sai yanzu ta gane ko wanene shi, daman tun ɗazu ta ga ganin kamar fuskar sani,
mutume daya bita asibiti. Ƙamshin turaresan ya haddasa mata ciwon kan da bata yi
zato ba, daman tun jiya bata cikin daɗin rai.

“Subhanallah malam wannan kallo ya haramta a musulumci”

Daɗin sautinsa yasa shi lumshe ido yana murmushi.

‘A'uzubillahi minal sheidanin rajin’

Ya furta a zuciyarsa yana ƙoƙarin da abunda sheiɗan yake son masa, sannan ya buɗe
ido ya haɗe fuska kamar be taba dariya ba.

“Su waye ku?”

“Mu ne waɗanda suka kama hanyar wannan gidan”

Ta amsa masa a gautse.

“Bq kuka kama ko Main house”

“Main house muna ciki aka yi gobara sai muka dawo nan da zama”

“Ina mijin ki?”

“Baya nan ya tafi kasuwa”

“To idan ya zo ki ce an baku one week ku tashi za ayi gyaran gidan”


Gabanta yayi mummunan faɗuwa.

“Innalillahi wa'inna ilaihi dan Allah ku gyara babban gidan sai ku bar mana BQ ɗin
wallahi ba mu da gurin zuwa idan muka bar nan, dan Allah ku taimaka mana”

Ta haɗe hannayenta idonta na son cika da ƙwalla.

“Da yaushe ake tarar da mijin ki?”

“Da safe ko kuma da dare guraren goma”

“Okay zan zo na yi magana da shi gobe”

“Allah ya kai mu na gode”

Be sake cewa wani abu ba, ya juyo hannayensa zube a aljihu ya fito gidan. Har
lokacin Amira na cikin mota zaune tana jiransa, yana shiga motar yayi mata key suka
juya. Wannan karon ita ce ta ke ɗan jansa da fira shi kuma jikinsa duk ya mutu baya
ma iya amsa mata. yawancin tambayarta akan gidan ne da kuma unguwar, sai kuma yaba
garin Katsina da take. Shi dai har suka isa gida sai dai ya ɗaga mata kai kawai.

Ta rigashi fita daga motar, dan yau ranta fes yake ta ta fita tare da sahibinta.
Bata tsaya a falo ba sai kawai ya wuce ɗakinta tana ƙoƙarin ɓoye nishaɗinta. Shi
kuma ya zauna a falo, kusa da Ummi da take zaune a inda ya barta ɗazu, sai dai
wannan karon ita da Shukura ne kuma carrots take gyarawa.

“Har kun dawo?”

“Yeah ai ba wani nisa”

“Kaga gidan ko?”

“Eh duk ya lalace idan aka ce za a gyara shi sai anci kuɗi kam ”

“ Ai dole a gyara shi tun da gidan marainiya ce, a ciro kuɗinta ayi mata gyaran,
daman kasan Amal bata da daɗi ta matsa min tuni kamar ni ce na ƙone gidan.Yanzu sai
ci nawa idan za a gyara shi?”

“A lot, nawa kika siya mata shi?”

“Ba da kai aka yi cinikin ba, da Alhaji Ƙasimu da Mansur”

“Kai ai bana iya tunawa kin san abu da yawa”

“Nine million aka siye shi”

“Na siya 15 million”

Ummi tayi saurin dubansa.

“Joking abii?”

“I'm serious wallahi na siya”

“Ba zamu siyar ba”

“Saboda me?”

“Muka sani ko zinari aka gani a gidan zaka mana wayo”


Ta faɗa tana tashi ta nufi kitchen, dan ga dukan alamu yai da kanta zata yi girki.
Dariya Abdool yayi ya cire hular kansa ya jingina da kujera yana faɗin

“Indai Amal ce ai abu mai sauƙi ne”

Lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya. Babu wacce yake gani sai Namra, da sauri
ya buɗe ido ya tashi ta nufi Gardem.

FIVE READ MORE.....🙌🏻

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *57*

Bata taɓa sanin haka jikin da zuciya suke ba idan wani abu marar daɗi ya faru da
mutum sai yau. Duk tashin hankalin da ta shiga lokacin da Rafiq ya kamu da ciwo be
kai wanda take ciki ba yanzu.
Wannan karon kuka ma yayi ƙaura daga idonta duniyarta sai juya mata take. Gani
take kamar mafarki take ba da gaske ba ne Hilal ya miƙa mata wannan takardar.
Miƙewa tayi tsaye sai gata ta dawo xaune saboda rashin ƙarfin jiki, ga wani sanyi
da take jin ƙafafunta sun mata.
Wani abu taji yayi mata tsaye a zuciya, hango kanta take a bazarawa, irin rayuwar
da tayi ta budurci kuma yanzu ace aurenta ya mutu bayan bata daɗe gidan mijin ba.
Takardar ta ƙurawa ido tana auna yadda Mominta zata ji.

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shi tai ta maimatawa sannan ta samu ƙarfin jiki,
har ta unƙura ta tashi. Durowarta ta buɗe ta ɗauki canjin da yake ciki da Atm ta
saka a jikarta tare da takardar ta saka hijabin ta fito falo. Saman kujera ta zauna
tana maida numfashi kamar wanda tayi gudun fanfalaƙi. Hannu ta kai ta rufe bakinta
saboda kukan daya zo mata gadan-gadan.
Sai dai hakan be hana hawayenta zuba ba, ashe da gaske hawaye suna da zafi, sai
a yau ta tabbatar dan yau ta ji hawayenta kamar ruwan zafi.

“Me yasa zan yi kuka akan abunda ba zai sauyu ba? Miyasa zan kuka akan mutumen daya
zaɓi rabuwa da ni? Anya Hilal ya cancanci hawaye na?”

Sune tambayoyin da tayi ma kanta a fili, sai dai har ta tashi ta kai bakin ƙofar
falon bata samu amsarsu ba. Kamin ta ƙarasa gate ta gyara fuskarta, ta goge idonta
da Hijabin gudun kar wani ya gani ya zargi wani abu.

Sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu Napep, sai da ta shiga sannan ta faɗa
masa inda zai kai ta. Har suka isa estate ɗin su idanuwanta basu daina cika da
ƙwallah ba.
Tana biyan Mai Napep ɗin ta shiga gida hawaye na bin fuskarta. Bata samu kowa a
falon ba, daman by this time ba zata samu kowa a gidan b Sai Momynta. A saman
kujera ta zauna ta haɗe kai da gwuiwa tana kuka. Sautin kukanta ne tashi daga bachi
da take ta fito da sauri falo. Ganin Kalsoom ya tashi hankalinta, tasan da maganar
kotu da Rashida ta sata amman bata zaton shine zai sa Kalsoom wannan kukan bayan ko
kotun ba'a shiga ba. Kusa da ita ta zauna tana ƙoƙarin ɗago kanta.

“Ke miya same ki?”

Ɗagowa tayi cikin kukan ta rumgume Mominta. Girgiza Momi tayi

“Ke ki min magana mana, waya mutu? Ko Rafiq ɗin ne ya mutu?”

“Ni ce Momi Hilal ya sake ni...!”


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, me kika masa?”

Kasa magana tayi sai kuka take kamar zata shuɗe, Momi ma hawaye take, ita kanta
bata jidaɗin maganar da Kalsoom ta faɗa mata ba, babu mace da zata so auren ƴarta
ya mutu sai dole, balle Kalsoom da aka samu aka yi auren daker.

“Ya isa bari kuka, aure rai ne da shi idan lokacin yin sa yayi sai an yi, idan kuma
mutuwarsa yayi dole ya mutu, ki kwantar da hankalinki”

Ta faɗa tana share mata hawaye, sai dai kuma ita na ta hawayen ba su daina zuba ba.
Daker Momi ta lalaɓa Kalsoom tayi shiru, har ta shiga ɗakin Momi ta kwanta, kanta
sai sarawa yake, ga wani ɗan banzan nauyi da yayi mata kamar an ɗora mata dutse,
idonta kuma har ji take kamar ƙasa ce a ciki.

Momi kan cikin rashin kuzari tayi girkin yau, sai dai har tayi ta gama bata lasa
miyar ba balle ma ta ci abincin. Sai da ta zuba a plate sannan ta kaiwa Kalsoom,
banɗaki ta tararda ita tana alwala, dan lokacin ɗaya da rabi tayi, ta daɗe a
banɗakin tana aikin kuka sannan ta fito.

“Haba Kalsoom ina ce kin saba da irin wannan jarrabawar, komai fa idan an yi haƙuri
za'a ga riba”

Momi ta faɗa tana kallon fuskarta data kumbura. Kusa da ita Kalsoom ta zauna,
idonta cike da ƙwalla ta ce

“Momi yanzu duniya zata ɗauka da gaske na aikata, yanzu kowa zai zarge ni akan ni
ce ma bawa Rafiq guba, tun da ga shi har Mahaifinsa ya zaɓi rabuwa da ni”

“Amman baki masa bayani ba ne? Ko da yake ba lallai ne ya gamsu ba, saboda gidan
daga ke sai yaron ne, kuma abun mamaki ne ace ya sha guba, dole duk wanda ya ji ya
zarge ki, ni ba ma abunda ya ɓata min rai kamar zuwa kotun nan da za'ayi”

“Ya ce min babu maganar kotu, ɗazu da zai ba ni takarda”

“Allah ya sauwaƙe, idan auren ku akwai alheri a ciki Allah ya maida shi, idan babu
kuma Allah ya kawo miki na ƙwarai, shi kuma ya haɗa shi da matar ƙwarai”

“Ina jin saki uku ne, aure ba zai sake shiga tsakamin mu ba”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, miya kai shi aikata wannan babban kuskure? Har
saki uku? Ai idan rai ya ɓace hankali baya gushewa, amman Hilal be yi ɗa ba, ai
komai bincike yake so”

Ƙasa tayi da kanta tana kuka.

“Daddyn ki ba zai ji daɗin wannan lamarin ba, ana murna an yi abu sai gashi kuma ya
zama na riƙici, ko da yake malamai sun ce idan saki uku aka yi shi a lokaci ɗaya za
a iya ɗaukarsa a matsayin ɗaya”

“Ba furtawa yayi ba, a rubuce ya bani”

“Rubuta ya yi saki ɗaya, biyu, uku? Kalsoom bana son ki dawo xaman gidan nan ne,
sannan duk wanda ya ji dalilin mutuwar auren ki ba zai aure ki ba, saboda wannan
ɓacin suna ne. Nasan ba halin ki bane ko kin ji kin haɗu da mugayen ƙawaye ne masu
kai mutum kai hallaka”

“Wallahi ban aikata ba, ke ma zargina kike ko?”


“Ba zargi bane Kalsoom kawai ina tsoron sherin zuciya ne, da kuma kishi, babu
abunda basa sawa”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah kaɗai zai shede ni shi kaɗai zai shede
ni da ban aikata ba”

“Ba zargin ki na ke ba Kalsoom, amman wannan lamarin abu ne mai sarƙaƙiya, ga


abincinki ki ci”

Kai ta girgiza hawaye na mata zuba.

“Ki daure dai ki ci, Allah zai kawo mafita inshallah, wallahi wahala bata taɓa
tabbata, kuma tun da har ya ci amanar ki sai Allah ya saka miki, Hilal butulu ne”

“Karki ga laifinsa Momi ni na nemi ya sake ni, a tunani na hakan shine mafita, ashe
bala'i ne, ni ce na ce yayi min saki uku”

“Subhanallah Kalsoom ke kika jawa kan ki matsala, dam me zaki yi haka? Kin fi son
ki dawo gida ki zauna tare da ni? Mutane da suka zage ki lokacin da aure yayi miki
tsawaiko su sake buɗe miki sabon shafi? Kin tonawa kan ki asiri kowa zai ji dalilin
fitar ki gidan miji, gashi ba saki ɗaya bane balle a gyara saki har uku wallahi
baki da hankali Kalsoom kin yi wa kan ki, da wane ido zaki kalli baban ki? So kike
ciwon zuciyarsa ya tashi ko?”

Ta ƙasara da kuka. Tana mai jin kamar ta kama Kalsoom ɗin tayi ta dukanta. Wani
irin kuka Kalsoom take sai yanzu take nadamar abunda ta aikata.

“Ina takardar take?”

Momi ta katsa mata tsawo. Jikarta ta nunawa Momi tana cigaba da kuka. Tashi Momi
tayi taje ta ɗauki jakar ta zazzage kayan ciki sai ga takardar ta faɗo, ita kanta
ta ji wani ɗarrr kamar ka ta ɗauki takardar sai dai tana da buƙatar sanin ko saki
nawa ne idan da gyara a gyara tun kowa be ji ba.

Warware takardar tayi tana karantawa. Wani dogon tsaki taja lokacin data gama
karantawar ta jefa ma Kalsoom takardar ta fice tana faɗin.

“Yayi tunani da hankali wallahi...”

Sai da Kalsoom ta ci kukanta ta ƙoshi sannan ta ɗauki takardar tana dubawa cikin
kuka.

_Idan na sake ki ina za ki? Wa kike tunanin zai aure ki a halin da kike ciki yanzu?
Kowa yana zargin ki da kin kore Rashida kina son kashe ƴaƴata, saboda basu san
dalilin sakinta da na yi ba._

_Zan miki uzuri Kalsoom akan abinda kika aikatawa ɗa na, saboda kin nuna musu so a
can baya, xuciya bata da ƙashi, dukan abunda kika aikata dan kina so na ne, kina
kishi na shiyasa kika aikata, kina ganin kamar ina son ƴaƴan da ba naki ba da yawa
ko?_

_Ba zan sake ki ba, saboda naga so na a idonki, kina neman sakin ne saboda kina
ganin kamar shine mafita a gareki ko? To ba zan sake ki ba, har abada haka zamu
zauna da ke, amman ba zan sake barin ƴaƴana a tare da ke ba, ba zasu sake raɓar ki
ba, saboda zuciyarki ta sauya a yanzu, kin tashi daga Kalsoom ɗin da nasan ki kin
koma wata dabam, amman hakan ba zai hana na so ki ba, ba xai hana na xauna da ke
ba, ina son ki sosai Kalsoom amman ban cancanci abinda kika min ba, nasan mace ce
ke kina da rauni shiyasa kawai na ɗaga miki ƙafa_

_Idan kuma har sakin kike so da gaske sai ki kai ni kotu._

*Ur Faithful Husband*

Shine abinda ya rubuta daga ƙarshe cikin manyan harufa. Rumgume takardar tayi a
ƙirjinta tana sauke ajiyar zuciyar da bata san lokacin data zo mata ba.
Wani sanyi ta ji ya saukar mata tun daga saman kai har ƙasan ƙafafunta, nan take ta
nemi ciwon kanta da kuka da take ta rasa, wani irin ƙaunar Hilal ne ta ji ya ratsa
zuciyarta.

Hijabinta da ta bari falo Momi ta jefa mata.

“Tashi ki koma ɗakin ki tun Mahaifin ki be dawo ba”

Buɗe ido tayi tana kallon Momi da murmushi a fuskarta babu ko kunya.

“Bari na yi sallah”

“Idan kin je can kya yi, amman wlh karki sake kuskure cewa ya sake ki, in ba dan
Allah yasa yana da tunani ba ai da shikenan”

Bata musa ma Momi ba ta ɗauki hijabin Momi ta saka ta ɗauki takardar da jakarta ta
fito falo ranta tasss kamar ba ita ce ta gama kuka ba. Har bakin gate Momi ta
rakata tana mata gargadi, sai da ta hau Napep sannan Momi ta koma ciki tana yi
Allah Hamdala tare da sawa Hilal albarka...

*NAMRA POV*

Sai da dare Asim ya dawo, kamar yadda ya saba, idan ka ganshi ba zaka ce shine ya
fita da tsoro ba ɗazu, yau yayi ciniki shine sirrin farincikin na yau.
Ba laifi ya ɗan sake fuska ya shigo har da sallama, kamar ba shi ba. Ita kanta
Namra da mamaki ta amsa masa sallamar tana ƙara kallon fuskarsa dan ta tantancesa.
Ya zauna kusa da ita, yana shewa.(fito)

“Sannu da zuwa”

“Yauwa ya gidan?”

“Gida yana nan yadda ka bar shi, masu gidan ma sun zo guba abun su kuma sun ce mu
tashi”

“What? To ina za mu koma? Ai kuɗin dana biya be ƙareba, ba zamu tashi ba wallahi”

“Su zaka faɗawa ba ni ba, ni dai na faɗa masa ya zo da safe ko da dare zai same ka”

“Bari ya zo ɗin amman wallahi ba zamu tashi ba, duk inda za a je sai dai aje, amman
wannan iskancin ba zan ɗauke shi ba, haka kawai dan ina talaka sai a nemi wulakanta
ni”

“Miye abun wulaƙanci dan masu guri sƴn nemi aba su abun su? Sai mu tashi mu basu
gidan su, ni dai na roƙe su akan su bar mu mu zauna bq idan har basu yarda ba
shikenan sai mu nemi wani gurin kuma”

“Ai kaji matsalar masu kuɗin nan, wallahi duk inda yake baya ƙaunar talaka”
“Ka cika mai da zazzaɓi ciwo Asim, yanzu sun san kai mai kuɗi ne ko talaka? Amman
kasan babu talakan da zai iya kama gida kamar wannan ya zauna ko?”

“Sun san talaka nake mana tun da na zauna bq, nima lokaci na yana zuwa zan yi kuɗi
har na mamaki”

“A haka za kayi kuɗi matarka tana cikin ƙunci? Ban taɓa ganin ragon namiji irin ka
ba Asim, sai dai na girka na baka da ƙarfin ka da komai?”

“Dan Allah ki yi haƙuri Namra, kin ga ɗan aikin da nake be wuce na samu na shan
ruwa ba, amman yanzu na samu wani aiki, sai dai aikin mai gidan ya faɗa min cikin
gidan zan koma da zama saboda aike-aike idan sun taso, kuma a matsayin driver zai
ɗauke ni kuma yaron gida, tun last week muka yi maganar amman nace ba zan kama
aikin ba sai na ji ta bakin ki”

Ta jidaɗi dan tasan aikin ya fi wanda yake yi yanzu, sai dai maganar komawa can ne
bata gane ba.

“Amman ka koma can har da ni? Ko ya”

“A'a ni kaɗai zan koma can saboda ya fi son ana kwana ta can”

“Amman kai ba aikin gadi ba ce kuma sai ka kwana ina ma laifin kaje da safe wuni”

“Ba kullum zan riƙa kwana can ba, ina jin wani lokaci ne kawai, kin ga ƙara mu samu
mu riƙa wannan aikin kamin mu ga abinda Allah zai yi gaba kuma”

“Allah yasa haka shine mafi alheri”

“Amin ya rabb”

Ya rumgume ta yana murmushin jindaɗi, daman ya faɗa mata ne kawai dan ta karta
daina ganinsa da dare, amman ko da tace bata aminta ba zai sa ya fasa aikin ba.

*ABDOOL POV*

Suna dinner yake nanatawa Ummi maganar siyen gidan da zai yi, but still bata yarda
ba, duk da ta ga alamun da gaske yake.

“Wai mi za ka yi da gida daya ƙone har xaka siye shi 15m?”

“Just”

Ya faɗa yana ɗaga kafaɗu.

“Dude na bar maka, ko kyauta ma zan iya baka ma”

Amal ta faɗa jikin har rawa yake. Kallon Ummi Abdool yayi yadda take watsawa Amal
harara yasa shi dariya, sai ya aje spoon ɗin hannunsa ya tashi ya ɗauki kofin tea
ya wuce ɗakinsa. Haka kawai ya samu kansa da murmushi ba dalili.

Wata ƙaruwar durowa ya buɗe ya ɗauko wata ƴar ƙarmar jaka baƙa. Ya nufo part ɗin
Ummi hannunsa ɗaya riƙe da tea ɗin.
Saman kujera ya jefar da jakar yana kallon Meesha dan ya yarda da natsuwarta.

“Aisha zo ki cire min 15m a nan, ko wanne 1m ne”


Dinning ɗin ta baro ta zo ta zauna saman kujera ta buɗe kuɗin ta fara ƙirgiwa har
ta cire 15m, ta aje gefe.

“Ga su”

Sai ya kalli Ummi

“Ummi ga kuɗin”

“Abdallah ana ciniki dole ne? Na ce ba xa a siyar ba”

“Amman mai abu tace ta siƴar”

“Wai me za ka yi da gidan ne”

“Kawai ki sai da min”

“An siyar maka, shikenan?”

“Thank you”

Ya ɗauki ragowar kuɗin ya maida ɗakinsa. Saman madubi ya ɗora copin tea ɗin ya faɗa
saman gaɗon zuciyarsa cike da nishaɗi.

Haka ya kwana da nishaɗin da be san ta ina yake xo masa ba balle dalilinsa ba. Shi
dai baya iya faɗin abunda ɗaya ta san ya shi ne silar farincikinsa tun jiya har
zuwa yau.
Yau zai koma abuja ko ba komai dole yayi sammakon tashi, balle kuma Namra tace
masa da safe ake samun mijinta.

Be tsaya wani karin kirki ba, dan a tunaninsa kamar idan ya daɗe ba zai samu mijin
nata ba
Ko da bakwai tayi yana ƙofar gidan, sai dai be shiga ba sai da ya buga gate ɗin,
ganin babu wanda ya fito yasa ya tura gate ɗin ya shiga cikin, black suit ne
jikinsa yayi mugun masa kyau kamar balarabe.

Nesa da bq ɗin ya tsaya yayi sallama cikin muryarsa mai sanyin da daɗin saurora, da
ace ma'aikatan sa zasu ganshi a yanzu da sun rantse wannan muryar arota yayi.
Asim ne ya fara fitowa yana samawa, daman tun da yaji sallamar ya raya a ransa
cewar masu gidan ne. Sai dai yayi mamakin ganin mutuen duk da be san sunansa amman
yasan shi ne ya biyo Namra asibiti. Ƙarasowa Asim ya yi yana masa wani kallo da
shi kaɗai ya san fassararsa.

Hannu Abdool ya miƙa masa.

“Sunana Abdallah Ahmad Mai-doki, na zo ne a kan maganar wannan gidan, matarka na


ciki?”

Be masa hannun nasa ba sai kawai ya ce

“Eh miye haɗin ka da matata?”

Abdool ya ɗan wara ido tare da taɓe baki haɗi da ɗaga kafaɗu.

“Nothing, jiya na zo akan maganar gidan nan ne sai take roƙo na akan dan Allah na
taimaka na bar su a bq su zauna dan basu da gurin zama, so shiyasa na yi ƙoƙarin
mai da gidan mallakin ku gaba ɗaya”

Asim ya washe baki, tare da miƙa masa hannu


“Mashallah Allah ya saka maka da alheri”

Daga nan da yake ya ƙwalama Namra kira. Sai gata ta fito cikin hijabi, kamin ta
ƙaraso gurin asim fuskar Abdool kawai yake kallo ya gani idan ya kalli Namra. Babu
abinda yake rayawa a zuciyarsa sai munafurcin da Namra take masa, wai shi za a
maida wawa ya kawo mata gida ya ce ya basu dan tasan idan ya bata ita kaɗai dole za
a gane abunda yake tsakanin su. A fili kuma murmushi yake kamar gaske yana kallon
Namra da take gaishe da Abdool. Kallo ɗaya Abdool yayi mata ya ɗauke kai ya ciro
takardar dake aljihunsa ya miƙawa Asim

“Daga yau wannan gidan ya zama na ku, ba zaku sake biyan kuɗin haya ba balle ace ku
tashi”

Hannu biyu Asim yasa ya riƙe hannunsa yana masa godiya kamar zai shige cikinsa.
Namra kan mamaki ya hana ta tace komai balle har ta yi godiya.
Sai Asim ne yake ta zuba masa godiya yana murna baka da zuci dan yasan shi zai
mori gidan ba Namra ba.

“Mun gode sosai Allah ƙara arziki ya ƙara wadata jazakallahu khairan”

“Amin”

Ya faɗa sannan ya juya ya nufi gate, yana ƙara kallon gidan. Har cikin ransa yaji
addu'ar da Namra tayi masa. Sai da ya wuce sannan Asim ya juyo ya shigo gida
zuciyarsa cike da zarge zarge. Sam be nunawa Namra ya gane shi ba, sai kawai ya
nuna mata ya fi kowa farinciki abinda yayi musu duk da zucin ma farinciki ne dan
yasam shine zai ci amfanin abun.

“Kin gani ko yanzu kan alheri ya fara shigo mu, yanzu duk wannan gidan na mu ne kai
Alhamdulillah Allah”

Namra tayi murmushi dan ita tun ɗazu mamaki take da tunanin dalili kyautar gidan da
Abdool yayi mata, bayan acan baya ya taɓa binta yace yana sonta, ko dai akwai biyu
a kyautar ne? Bata bar Asim ya gane abunda yake ranta ba, gudun karya zargenta, ko
kuma yayi wani tunanin na daban daman can ya taɓa zarginta.

Dumamen shimkafar da tayi ne ya zuba masa, ya ci sannan ta kai masa ruwan wanka
yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin data wanke masa. Sannan ya fito waje ya
ciro ɗari biyar ya miƙa mata.

“Gashi ayi cefane”

Hannu biyu tasa ta karɓa tana muryar yau mijinta yyi abun kai

“To Allah amfana”

“Amin sai na dawo”

“Allah ya tsare”

Ya nufi gate zuciyarsa cike da ƙunar cin amanar da Namra take masa, abun har ya
fara wuce gurin har ana kai ga kyauta gida.

“Hmm Lallai ma wannan matar wai har ni za a rainawa hankali, bari na zama Asim ɗi
na na ƙwarai ki ga yadda zan yi da ke, ku yi ta abun ku yanzu na ba ku dama”

Ya filin yake maganar ya miƙe hanyar data zata kai shii babban titi, sai dai hanyar
gidan su Mardiya ce, da gangan ya bi dan ya ganta.
Ya ko yi nasarar angota da ɗaura gaba tana tsaye ƙofar gida tana ciniki a warwaro
da mai tutu-rutu, ƙirjinta kawai yake kallo yana siffantawa kansa ita, har ta kawo
kusa da inda take.

“Barka da safiya Asim”

“Yauwa barka Mardiya ya gida?”

“Lafiya ƙalau, ina Namra?”

Ya ɗan ƙara washe baki dan be yi tunanin zata kawo maganar Namra a yanzu ba.

“Tana nan ba kin guje mu ba”

“A ni na isa ku ne dai kuka guje ni”

Dariya yayi ya ƙarasa gaban mai ɗan kunnen yana kallon kayan

“Me aka siya?”

“A warwaro ne da ɗan kunne”

Babu ko kunya take masa magana kamar bata sam ɗaura gaba ne a jikinta ba. 1k ya
ciro ya miƙa mata

“To a siya da yawa”

Hannu tasa ta karɓa.

“Na gode sosai Allah kawo wa su, ayi irin mu huɗu”

Dariya yyi kamar ba shi ba ya amsa da amin yana tsayardar mai okada. Sai da ya hau
sannan ya faɗa masa inda zai kai sa.
Hajiya Sadiya tayi mamakin ganinsa sosai dan a ƴan kwanakin daya ɗauka ta zata
ko ba zai dawo ba ne, ruwa ta kawo masa da abinci, sai wani ƴauƙi take kamar ta ga
mijinta. Shi kuma ya sake jikin sosai kamar gidansa, baya kallonta idan tana
kallonsa ko taɓa gabansa sai ta bada baya yake kallonta.

“Baka buƙatar kwaso kayan ka ko wani abu, akwai komai da zaka buƙata a ɗakin da za
a sauke ka, ni na ɗauka ma ba zaka dawo ba”

“Me zai hana? Mutum ya bar samu?”

Dariya...

“Aiko dai, ina kallon lokacin da kake ta ciwon nan kamar ba zaka tashi ba”

Gabansa ya faɗi dan be yi tunanin ko ta san shi ba, se dai be gama saƙe saƙensa ba
ta cigaba.

“Lokacin da muƙa ɗauko ka daga asibitin Funtua zuwa nan katsina, lokacin kana cikin
ciwo ba zaka gane ba, amman na san kana da mata ka ɓoye min ne kawai”

Ido cikin ido yake kallonta dan tantance abinda take faɗa.

“Ban gane ba”

“Hmmm Asim ko? Ni ce na ɗauko ka da mota na na kawo ka Asibitin katsina na biya


kuɗin gado da magani, amman nasan ba zaka iya tunawa kancewar lokacin kana cikin
ciwo”

“Eh...eh..ha...k...a..ne.... Ashe kin san ni”

“Na san ka nima farko ban gane ka ba sai daga bayan lokacin da nasa ayi min bincike
akan ka”

“Bincike kuma?”

“Eh mana ai duk wanda xaka xauna da shi kana da bikatar sanin ko waye shi, gudun
abinda zai je ya dawo amman miyasa kace min baka da mata bayan kana da ita?”

Ya ɗan sosa kansa yana cire hannunsa daga abincin daya fita ransa.

“Wallahi Hajiya naga kamar ba ki son mai matar ne shiyasa, ni kuma bana son na rasa
wannan aiki na ki”

Tayi murmushin ƙasaita.

“Ba mai mata ne bana so ba, yadda nake son a min spending time ne nasan mai mata ba
zai iya ba”

“Zan iya wallahi dan ni na fi ƙarfin matana na, duk abinda kike so zan miki”

“Hakan yana da kyau, namijin duniya irin ka na ke so”

Ya jidaɗi sosai.

“Anything for you Hajiya”

“Gobe aikin ka xai fara, yanzu idan ka gama, sai kaje gurin mai gadi ya nuna maka
wasu abubuwan”

“Hajiya ai ni na gama ma”

“Ka daina kirana da Hajiya ka kira ni Sadiya na”

“Ai da nauyi sai dai ko nace Anty Sadiya”

Wata harara ta watsa masa.

“Na yi maka kama da Antyn ka ne?”

Kallonta yayi a zahiri kam tayi yi, dan wannan yasan ba sa'arsa bace sai dai kuma
bata isa haihuwarsa ba.

“A'a Sunan ne ba zan biya faɗi a fili ba”

“To ka riƙa ce min Sadiya Babe, amman idam cikin mutane ne ka riƙa kirana da Hajiya
na”

“To am gama na gode”

Har ya juya tace

“Kuma bana son sa ido, kar ka damu da baƙina ko ƴaƴan 'uwan da suke zuwa gidan nan
kai dai kawai ka yi aikin ka”

“Inshallah ba zaki same ni mai tsaɓa uwarnin ki ba”


“Albashin ka 100k per month”

Da sauri ya kalleta fuskarsa ƙarara da mamaki, sai gashi kurfane ƙasa yana mata
godiya.

“Allah ya ƙara miki arziki Allah yayi miki yadda kika min”

“Amin kai dai ka cigaba da biyayya kawai zaka iya samun fiye da haka ma”

“Inshallah”

“You can go, sai ya nuna ma ɗakinka da kuma aikin ka”

Ya juya ya fice yana jin wani irin nishaɗi da be taɓa jin irinsa sai yau.

*ABDOOL POV*

Ko da ya isa gida duka ƙanensa sun wuce scul Ummi ce kawai a dinning sai Amira suna
karƴawa. Tun daga nesa Ummi ta hango nishaɗin dake fuskar ɗanta. Har ya ƙaraso kusa
da su ya zauna a kujera daya saba zama.

“Ina ka je da safen nan haka?”

Be son maganar gaban Amira, sai kawai yayi murmushi ya ɗauki kofi ya soma haɗa ma
kansa tea.

“Good Morning Yaya”

“How are you dear..”

_Dear_ taji kalmar har cikin ranta, shi kuma ya amsa mata ne da murmushi kuma ba
tare da wata manufa ba.

“Ummi yau zan koma fa”

“Yeah i know i just want to know the secret of your smile?”

Shi kansa be san yana murmushi sai yanzu da Ummi ta yi magana. Yayi saurin kawar da
murmushin

“Nothing”

Ya miƙe tsaye yana kallon agogon hannunsa.

“Around 9: za mu tashi”

Amira ta ji babu daɗi. Sai ta tashi jiki a sanyeye ta nufi ɗakinta, sam bata son
Abdool yayi nisa. Komawa Abdool yayi ya zauna ganin Amira ta shige ɗaki.

“Ummi ina wata da na taɓa baki labari nace miki na ganta a pharmacy da hospital har
na ce ina son ta sai tace min ita matar aure ce?”

“Yeah yeah na tuna what happed?”

“Ita ce take haya a gidan Amal ita da mijinta, sune suka yi wuta yanzu sun koma bq
da zama saboda mijin nata talaka ne sasai”
“So...?”

“Shi ne sai na siya musu gidan...”

“Saboda me?”

“Just”

“You still love her ko?”

Ya ɗan yi shiru yana tambayar kansa. Kamin ya ɗaga kai alamar eh

“Yeah and i d....”

Be ƙarasa ba Ummi ta mikr tsaye tana dakan dinning ɗin ta katsa masa tsawa

“That it, baka da lada baka yi da Allah ba, kai baka ji kunyar kanka ba ace matar
wani kake so? Kai zaka so wani ya kashe maka aure ne?”

“Ummi ba auren ta zan kashe ba, i just help”

“Help? You want to use her dan kasan mijinta talaka ne, ka kashe mata aure huh?
Duk ƴan matan garin na ka rasa wacce zaka so sai matar aure Abdallah mike damun
ƙwaƙwalwarka, abunda kake be kamata ba, kallon ta a gareka haramun ne, kamata yayi
ace kana yaƙi da sheɗen ba wai kana bari na kai zuciyarka ga halaka ba.

Dole zan yi magana da Mai Martaba dole ayi maka aure ko baka so, dan na fahimci
baka da hankali”

Cikin fushi ta ƙarasa maganar tana mai ƙyamar abunda ɗan ta ya aikata. Shikam kasa
cewa komai yayi dan be da bakin magana.
Duka abunda suke Amira na jikin ƙofar ɗakinta tana sauraensu duk da akwai ta zara,
dan da farko bata ji abunda Abdool da Ummi suke tattaunawa ba sai da Ummi ta ɗaga
murya tana masa faɗa.

‘Wace mai sa'ah ce wannan wanda Abdool yake so? Me take da shi?’

Tambayar da tayi ma kanta kenan tana mai ƙarasawa gaban modubi ta dubi kanta.

*HILAL POV*

Yana isa asibitin ya wuce ɗakin da Rafiq yake, zaune ya same shi yana kuka. Amina
da wata nurse na kusa da shi tana lalaɓashi, bakinsa ya karkace sai dalalarda yawu
yake kamar musaki, ko kuma irin yaran na dolaye. Yana ganin Hilal.ya riƙa ƙokarin
sauka yaje inda yake, sai Hilal ya ƙaraso da sauri kusa da shi cike da tausayawa ya
ɗauke shi.

“Shiiii Daddy ya zo”

“Good mornig Sir”

Nurse ɗin ta gaishe shi sannan ta fice, Amina ma ta ɗora da nata gaisuwar tana nuna
masa abincin da Hajiya tace a kawo masa.

“Okay”

Ya faɗa yana ciro wayarsa dake ringing.


“Ya aka yi?”

“Wallahi nayi lallaɓa Dady yace shi sai ya saka ƙarar”

“To shikenan aje kotun ai sai Allaura ta tono garma, amman wannan abun da za ayi ba
zai na ƙi tsayawa Kalsoom ba she's my wife”

Ya kashe wayar ya maida Aljihu. Amina sao kallonsa take tana mamakin furucin da
yayi, a zuciyarya ta ƙumshe zance da sunan dai ta je gida ta faɗawa Hajiya.

*RASHIDA POV.*

Bayan Rashida ta ƙare waya da shi ta cigaba da aikinta, kamar yadda ta saba. Sai da
lokacin tashinta yayi sannan ta shiga tayi ma Alh Bashir sallama ta fito. Kai tsaye
gidan Mom Shuraim ta nufa. Ita kanta tayi mamakin ganin Kalsoom mace da zata
shekara bata kira a waya ba ma balle kuma ziyara amman yau gata gidan ta.

Abinci ta kawo irin nasu na ƴan nijar ya ji albasa har ya gaji, da ruwan sanyi
sannan ta zauna suka soma firar yaushe gamo. A cikin firar na Rashida take labarta
mata mutuwar aurenta da kuma abinda Kalsoom tayi mata. Mom Shuraim ta cika da
mamaki matuƙa. Sai Allah wadai take tana tsinewa Kalsoom.

“Ke dai bari wallahi ina cikin matsala shiyasa na zo gurin ki ko kin san wani
malami inda zamu iya zuwa a kare wannan asirin dam ance min ƴan nijar kan suna da
abubuwa da yawa”

Mom Shuraim tayi shiru dam ba kowa bane yake son buɗe sirrinsa.

“Ai ko nan akwai su”

“Ni dai ki taimaka min idan zaki kai ni.can nijar ɗin ko kuma ki haɗa da wanda zata
kai ni amman fa idan kin san mai aiki na gwarai”

“Toh Yanzu dai sai na bincika can gida idan na yi waya da su, zan faɗa miki”

“To na gode zan kira ki inshallah”

“Amman xaki.iya xuwa har can?”

“Wallahi ko chana ne zan iya xuwa balle nijar”

Dariya Mom Shuraim tayi ta rakota har ƙofar gida tana ta tunanin maganar a
zuciyarta, sai da Rashida ta miƙawa yaranta 500 kowanensu sannan ta shiga motar ta
f ɗauki hanyar gida. Ba dan zuciyarta ta gamsu Mom Shuraim ɗin zata kai ta ba, ɗan
bata ga alamun haka a tare da ita ba.
Tunaninta duk ya tattara ya koma gurin abokanta, har ta isa gida tunani take
wacece cikin ƙawayenta take da wannan shige shigen malamai.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *58*

Cikin rashin daɗin rai ya bar katsina saboda faɗan da Ummi tayi masa, shi kansa sai
yanzu ya ke jin rashin daɗi akan abinda ya aikata. Sai dai shi yasan be dan wata
manufa ba, be kuma yi ba dan ya kashe mata aure, sai ya yarda da abu ɗaya, shine
son ta abu ne kuma da ba zai iya cirewa kansa shi ba amman yana ta yaƙi da
zuciyaraa wajen gani ya anta da Namra a duniya.

Damuwarsa bata hana shi aikinsa ba, amman duk wanda ya ganshi a ya san akwai damuwa
sosai a tare da shi. Maganar Ummi ta tsaya masa a rai na auren da ta ce zata ma Mai
Martaba magana ayi masa, wata ƙila shi ne fita a garesa, sai dai yana tsoron auren
mace da baya so gudun kar ya cuci kansa ya cuce ta.
Har gobe babu wacce yake gani idan ya rufe idonsa sai Namra, dukan mafarkansa
akan ta ne, miyasa baya da tunani sai matar wani? Dan me zai riƙa mafarkin da babu
ranar farkawarsa.

“What's wrong with me? There's something inside me, this is not me it's another
Abdool behind me”

A fili yayi furucin ya miƙe tsaye ya nufi window office ɗinsa ya tsaya, yana hango
wasu sojoji dake farati a rabar wajen. Kallonsu yake amman hankalisa baya gurin,
can kuma ya ɗauke kansa ya juyo ya jingina da gurin yana kallon office ɗinsa.

Wayarsa dakr kan dinning tayi ƙara, alamar saƙo, kallo ɗaya yayi ma wayar ya ɗauke
kai, yana cigaba da tunanin abinda yake ganin kamar shine a gare shi.
Ɗan risinar da kansa yayi yana shafa dogon hancinsa, tare da jan dogon numfashi.

Ya samu minti talatin tsaye a gurin sannan ya nufi kujerar zamansa, ya koma ya
zauna yana lilo. Hannu ya kai ya ɗauki wayarsa. Saƙon sama ya buɗe wanda aka aiko
masa da baƙuwar number.

_If you love something, let it go. If it comes back, it was meant to be. If it does
not, hunt it down and kill it. *Smile* good evening hope you had a nice day and a
pleasant evening as well._

*AMIRA*

Ya ɗan taɓe baki yana maman inda Amira ta samu waya bayan yasan bata da waya a can
baya.

“Maybe Ummi ta bata”

Ya faɗa a fili sannan ya kai hannu ya ɗauki telephone ɗin dake saman tebur ɗinsa
tana ringing.

*AMIRA POV*

Murmushi tayi ta tana wanda yasa Haleema kallonta.

“Kin saka number?”

“Eh na saka sai ta wa kuma?”

“Sai ta Meesha”

Haka ta riƙa bata number kowa na gidan cikin har da Amal da Shukura. Ɗaya bayan
ɗaya Amira ta riƙa sawa har ta gama, sannan ta kalli Haleema tana murmushin jindaɗi
tace

“Na gode sosai Haleema Allah ya saka miki da alheri”

“Ba komai ai nasan zata rage miki kewa ko da game kawai”

“Sosai ma wallahi, Allah ya bar zumunci”

“Karki damu ai komai yi ma kai ne”

Ya faɗa tana murmushi sai ta tashi ta nufi ƙofar fita tana dannar wayarta. Amira
kan wayar ta sakarwa ido tana kallo, farincikin saƙon data aikawa Abdool take, bata
damu da rashin reply ɗin da be mata ba, daman bata sa ran zai mata ba. Rumgume
wayar tayi a ƙirginta, wani kalar nishaɗi ne ya same ta, marar misaltuwa. Tunawa da
faɗan da Ummi tayi masa akan wata yasa ta jin babu daɗi, that's means akwai wace
take ransa kenan, bata gane dalilin faɗan na Ummi akansa ba, sai dai taji yana
faɗin bashi da lada, sai kuma maganar da tace masa idan shi ne zai so wani ya kashe
masa aure.

‘Wacce yake so matar aure ce ko kuma an mata engaged ne? Akwai buƙatar na san ko
wacece wata ƙila tana da wasu halaye da Abdool yake da su. Sai dai taya? Taya zan
nuna na san wata da yake so? Idan har na nuna hakan za su ce ina musu sa ido, bayan
kuma sun yarda da ni’

A zuci take zancen a fili kuma sai ta ce

“What's the solution?”

Kanta ta ɗaga sama tana kallon pop.

‘An ya zan iya bari wannan damar ta wuce ni? Ace na shiga rayuwar Abdool kuma ba
bari wata ta ƙwace min shi? Anya zan iya barin wannan daular ta wuce ni? Zuciyata a
yanzu Abdool kawai take so mutumen dana saɗaukar da rayuwata akan sa’

Ajiyar zuciya ta sauki, tana ta zancen zuci, sai dai har aka kira salla bata samu
wata gamsasshiyar mafita ba. Unƙurawa tayi ta tashi ta nufi ɗakinta tana auna irin
abunda za tayi ma Abdool wannan karon.

“Amira...”

Daf da zata shiga ɗakinta Meesha tayi mata kiran tana nuna mata ɗakin Ummi da alama
Ummi ce take kiranta. Juyowa kawai ta yi ta nufi ɗakin Ummi cikin ladabi. Kusa da
Ummi ta zauna ƙasa ta matse Ummi sosai kamar zata shige cikinta.
Sai da Ummi ta gama abinda take sannan ta cire madubin idonta ta kalli Amira a
natse ta ce

“Amira ina tunanin yanzu hankalin ki ya kwanta, natsuwarki kuma ta dawo jikin ki,
zama haka ba shi yi, ya kamata ace izuwa yanzu kina gaban iyayenki, ba mu san halin
da iyayen ki suke ciki ba, i'm mother too i know how it feel like idan ɗan ka baya
kusa da kai, musamman mace”

Ɗagowa tayi ta kalli Ummi idonta cike da ƙwalla.

“Dan Allah Ummi ki min haƙuri ki bar har nan gaba, ni kaɗai nasan halin da nake
shiga idan na tuna da iyaye, kuma nasan dole na koma garesu”

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke.

“Ba komai Allag yasa haka shi ya fi alheri, Haleema ta baki waya ko?”

“Eh ta ba ni”

“Yana da kyau ki kira wani daga cikin familyn ki ku gaisa”

“Zan yi ƙoƙarin yin haka Ummi na gode”

Ta miƙe tsaye cikin rashin kuzari ta bar ɗakin. Ɗakinta ta dawo ta xauna gefen gado
tana kuka, ita kanta tasan abar tausayi ce idan ta tuna da rashin iyayenta.

“Na rasa iyaye saboda kai Uzair, ka cuce ni ka yaudare ni, kai ne ka saka rayuwarta
ta koma a haka, na rasa iyayena da duka family amman ba zan rasa Abdool da familyn
su ba, ba zan zama loser ba”

A fili tayi furucin zuciyarta cike da yaƙinin abinda bakinta yake faɗa.

“I have to make it work, i can't lose them both, i deserve happiness too”

Saman gadon ta faɗa ta rumgume filo tana wani kuka mai taɓa zuciya.

“Kin cuce ni Namra abotarmu bata amfana min komai ba sai nadama da baƙin ciki, nayi
nadamar sanin ki a rayuwata, You and Uzair have to paid for what you both did to
me”

Wani kuka take Sosai tana buga ƙafafunta kamar wata ƙaramar yarinya. Turowa ƙofar
ɗakin da Haleema tayi ne yasa ta saurin tashi ta goge hawayenta, gabanta sai faɗuwa
yake tana ala-ala idan bata ji zancen da ta yi ba.
Kusa da ita Haleema ta zauna cike da tausayawa, dan akan kunnenta Amira ta faɗi
komai.

“Kin cancanci farinciki Amira, ba kiyi ƙarya ba kin cancanci komai daga wanda kika
sadaukarda ranki gare shi, mu kuma kin cancanci soyayyarmu tun da kika ceto
ɗan'uwan mu”

Hannayenta Haleema ta kama, ta riƙe

“Ba zaki rasa mu ba, ba zaki rasa familyn Abdool ba har a bada”

Da mamakin Amira take kallonta kamar wacce bata fahimci inda zantukanta suka dosa
ba.

“Na daɗe da fahimtar kina son Ya Abdool, tun lokacin da kika shigo gidan nan, na
lƴra da ke Amira kina rasa natsuwarki idan Abdool yana cikin gidan nan, a yanzu ma
bayan Number Ummi Numbersa kika tambaya a na biyu, kina son Abdool Amira i can't
hide it”

Rumgume ta Amira tayi a ƙirginta gamgam, tana kuka.

*ASIM POV.*

Bayanai gadi ya gama nuna masa ko ina na gidan, sai ya dawo falon dan faɗa ma
Hajiya yadda suka yi da mai gaɗin. A inda ya barta a nan ya same ta tana zaune ta
ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaƴa tana kallon ƙofa kamar ta san da shigowarsa.
Saman kujera ya zauna dan shi yanzu jin gidan yake kamar nasa, yayi sallama sai
dai bata amsa masa sallamar ba har ya zauna tana murmushi.

“Hajiya an nuna min komai, gida mashallah”

Sai a lokacin ta buɗe baki tana masa magana kamar mai nauyin baki.

“Amman bana son ka faɗawa kowa abinda ka sani game da ni”

“Hajiya ai ban san komai ba, balle ma na faɗa, kuma ni bana daga cikin mutane nan
masu yawan surutu”

“Zaka sani ne ai shiyasa nake gargaɗin ka tun yanzu, zaka san komai a kai na, tun
da har ka furta zaka iya yin komai”

“Wallahi zan iya miki komai Hajiya”


“Yayi kyau, kaga ɗakin ka?”

“Eh yayi kyau sosai”

“Anjima zan baka kaje ka siyo abubuwan da babu, sai ka sawa ɗakin, saboda ina son
ya zama ɗakin ka na ainahin, so nake ka manta da cewar kana da wata mata dabam”

“Ba komai Hajiya komai kika ce shi za'ayi inshallah”

“Thank you you're very loyal”

Ta tashi ta nufi ɗakinta tana murmushi, har a zuciyarta take jin Asim dan taga
alamun zai iya komai na neman kuɗi, haka take so daman.

Shi kuma sai daɗi yake ji yadda take masa, ko kaɗan be kawo komai a ransa ba, abu
ɗaya yake tunanin zata nema a gunsa, wata ƙila ba zai wuce sex ba, kuma he's ever
ready indai wannan nan ne, sai dai kuma shi ɗin kansa yana buƙatar sanin ko wacece
ita, dan be ga alamun tana da yaya ba.
Zuciyarsa cike da nishaɗi ya fiddo ƙaramar wayarsa ya shiga duniyar facebook.
Notifications ya tarar mai yawa, ga massage da friend requests. Rabon da hau
duniyar facebook tun Namra tana amarya tana ɗan cikin yanayin jindaɗin nan kamin
komai ya canja.
Notifications ɗin ya fara dubawa yaga na gani sannan ya shiga massage, ya samu
mata da yawa daga cikin masu masa massage kansancewar hoton dake profile ɗinsa yayi
kyau, sosai idan ka ganshi sai ka ɗauka wani shege ne.
Sama-sama ya amsa massages ɗin sannan ya duba friend requests yayi accepting wasu
ya bar wasu.

Be wani daɗe ba ya sauka daman be cika jindaɗin hawa da ƙaramar waya ba, rabon da
yayi chat da babbar waya kuma tun yana farko farkon scul ana yayin karyar nan.

Saukowar Hajiya Sadiya ne yasa shi ɗaga kai yana kallonta. Sai kuma ya sauke irin
wai shi ladabi tun da ita ce boss. Keys ɗin mota ta jefa mishi tare da Atm.

“4782 shine password ɗin, ka siye duk abunda ya kamata, ɗan bana son ƙazanta”

Ya ɗauka ya miƙe tsaye har wani zumuɗi yake, zuciyaraa fes.

“Toh Na gode sosai”

Bata amsa shi ba, shi kuma be damu da sai ta amsa ɗin ba sai kawai ya fice yana
auna yadda Allah ya maida shi wani a dare ɗaya.
Be sa ko wace mota bace har sai da ya danna makulin tayi ƙara sannan ya nufi
motar ya buɗe ya shiga.

‘Kamata yayi na siyar da gidan nan, idan ya zo sai na riƙa juyawa ina siyen zinari
ina sai dawa, ga wannan albashi walh nan da nan za ka ga na yi kuɗi, sai dai kuma
ban sani ba ko bata son na haɗa da wani aikin, wata ƙila ma zata iya min kyautar
mota fa, ji yadda ta yarda da ni nan take har da ba ni atm ɗinta ta faɗa min
password, daman mai haƙuri mawadaci’

Shine abinda yake ta saƙawa a zuciyarsa yana tukin motar da yake hango kansa a
matsayin wani ƙaramin alhaji.

*RASHIDA POV*

Ajiyar xuciya ta sauke har da hawayen ƙirƙira dan kawai Teema ta tausaya mata,
haƙiƙa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne Teema ta tausaya mata sosai har tana jin kamar
tayi mata maganin matsalarta yanzu.
“Ki kwantar da hankalin ki Rashida, zan taimake ki akwai wani malami yana nan ɗan
ƙauye sokoto ne, wlh malamin har ƙasa ƙasa ake ɗaukarsa yayi aiki, aikinsa kamar
yankan wuƙa yake, a take komai kike so zai miki zan kai ki gurinsa idan kin shirya”

“To ai ni kullum a shirye na ke, ni ko yanzu kika ce muje zamu je wlh”

“A'a ban da yau dan ban shirya ba amman dai gobe ki zo da wuri sai mu tafi”

“To inshallah zan zo”

“Amman aikin ki fa nasan ba hutu kuke samu ba”

“Karki damu da aikina wannan ita ce muhimmiya”

Teema tayi dariyar mugunta. Tashi Rashida tayi, Teema ta raka ta har gurin motar ta
ta shiga motar tana ɗagawa Teema Hannu.
Daga gidan Teema ta wuce Asibiti dan karɓar maganinta, a mota ta tsaya ta saka
niƙabi da hijab sannan ta fita.
A wani gurin ta tsaya kusa da inda ake ba da maganin, tana kalle kalle mutane,
daman haka take duk ta zo wai gudun kar taga wanda ta sani. Duk da wannan shine
zuwanta na biyu.

Bayan ta gama dube dubaneta ta shiga ciki ta ga likita, ya ƙara mata shawarwari,
sannan ta fito ta nufi gurin karɓar maganin kai tsaye. Security dake gadin ƙofar
asibitin ce ta saka ta cire nikaɓ ɗinta dan haka dokar asibitin ta gada, Rashida
bata damu ba ta cire niƙab ɗin daman ko wacan zuwan da tayi sai da tasa ta cire
shi.

Da fargaba ta kunna kai a gurin tana ɗan kallon mutane ƙasa-ƙasa, gabanta sai
faɗuwa yake kamar zai faɗo. Kamar daga sama taji an dafata ana ƙoƙarin juyowa da
ita, juyowar da ta yi sai kawai suka yi ido huɗu da Safiya cikin Uniform ɗinta.
Wani irin kallo Safiya take mata kamar wacce ta rude cox she's can't believe
Rashida ce ta gani a nan ƴar'uwarta jininta.

Ita kanta Rashida mamakin ganinta take, dan iya saninta wannan ba asibitun su bace,
ya aka yi ta zo nan me ya kawo ta.? Yawu Safiya ta haɗe ta wuce da sauri ta fita
daga gurin gudun kar wani daga cikin manyan su ya ganta, daman fitowarta kenan daga
wani ɗakin ta hango mai kama da Rashida, ashe ba kama bace, ita ɗin ce amman mai
zai kawo Rashida HIV/TB unit.? Shine abinda ya tsaya mata a rai.
Miƙewa Rashida tayi cikin dakewar zuciya ta cigaba da tafiya tana son ɓatarwa da
Safiya da lissafi, sai dai kuma yanzu bata san liyin da zata bi, tb ko hiv?

*HILAL POV*

Asibitin ya wuni, da rana ma Hajiya ce ta kawo masa abinci. Duk wanda ya zo sai ya
tauyasawa Rafiq ganin yadda ya koma musaki sai dalalar da yawu yake. Tuni Hilal ya
ɗosa shi akan magani, yasa aka sake masa wasu hotunan dan ganr ainahin matsalarsa.
Ƴan'uwansa da dama sun yi ta xuwa ganin ɗan nasa, ƴan uwan Rashida ma sun zo, sai
dai ba sosai ba, Dady Kalsoom ma ya zo shi da Momy, duk da suna jin nauyi ganin
kamar ƴarsu ce ta aikata abun.

Sai da yayi ma Rafiq Alurra bachi sannan ya rufe ɗakin. Ya koma office ya cigaba da
aikinsa, bayan ya gama, ya sake leƙa ɗakin yaga har yanzu bachi yake. Sai kawai ya
nufi gurin motarsa dan yana buƙatar taje gida yayi wanka.
Yana hanyarsa ta tafiya Hajiya ta kira shi wai zata shigo da dare akwai magana mai
muhimmanci da take son suyi, shi dai da to kawai amsa mata ba dan ransa yana cikin
daɗi ba, ya faka a rabar gidan ya fito jiki ba ƙwari ya shiga ciki.
Tun a falo gabansa ya soma faɗuwa jin sautin kukan Kalsoom, da sauri ya karasa
ɗakinta, sai dai kamin ya shiga ya ji ba acan kukan yake fitowa ba, a ɗakin su
Ezzah ne. Ƙarasa yayi ɗakin ya tsaya daga jikin ƙofa yana kallonta. Juyowa tayi ta
kalleshi da idonta da suka yi ja saboda kuka.

“Haƙiƙa ina son ka Hilal, dukan abunda ya dangance ka ina sonsa ko da kuwa abun nan
mai cutar da ni ne, miyasa zuciyarka ta yarda na aikata bayan ban aikata ba? Ka
raba ni da ƴaƴanka Hilal bayan yanzu sun zamo jinin jikina, ban aikata abinda kake
zargina da shi ba Hilal Wallahi ban aikata ba”

Ya rumgume hannayensa yana mai jingina da jikin ƙofar.

“To waya aikata?”

“Ban sani ba, amman na rantse maka da Allah ban aikata ba, idan har na aikata Allah
ya isar masa ya saka masa, kuma ya bayyana gaskiya”

Jikinsa yayi sanyi sosai, yasan ba zata yi ma kanta wannan mugun furucin ba. Kasa
cewa kamai yayi sai kawai ya juya ya nufi ɗakinsa. Saman gado ya zauna, ya dafe
kansa dake masa wani zafi.

Jin yayi ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ɗagowa da zai ya ga hannunta rike da ƙur'ane
da dukan alamu rantse masa zata yi. Da sauri ya tashi ya ƙarasa inda take.

“No need Please ki aje ƙur'anen nan Kalsoom”

“Rantse maka zan yi Hilal ko zaka yarda da ni”

“Na yarda da ke aje please”

Bata son musa masa, sai kawai ta aje ƙur'ane saman durowarsa tana kuka. Rumgume ta
yayi tsantsan a ƙirjinsa ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya.

*NAMRA POV.*

Tun lokacin da Asim ya bata 500 yace tayi cefane bata dake saka shi a idonta ba,
kullum idan ta kira zai ce mata aiki ne ya sashi gaba, yau kusan kwana uku kenan.
Ita kam abun duk yabi ya dame ta, musmman yanzu da take ɗan samun sakewa da shi sai
kuma aiki ya ɗauke masa hankali.
Sai dai kwana biyu bata jindaɗin jikinta, yawun bakinta ya kan canja ɗanɗano, ga
kasala da take fama da shi, sai yawan amai akai akai, ga ciwon kai.

Sai dai bata kawo ma kanta komai ba, sai hawan jini, duk da bata san alamominsa ba,
amman tana jin kamar wannan ba zai rasa nasaba da hawan jinin ba, a iya saninta ta
saka roba balle tace ko ciki ne, dan tana jin irin alamomin da ake faɗi na masu
ciki. Tun jiya ta ci alwashin zuwa asibiti dan bincika matsalarta gudun kar ciwo
yayi mata zurfi a rasa gane kansa, amman Allah be yi ba sai yau. Dan haka da wuri
ta shirya ta nemi ƴar fulani data raka ta suje tare, dan bata son xuwa ita kaɗai
musamman inda bata saba zuwa ba.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *59*

*RASHIDA POV.*

Ganin Safiya ta fita yasa ta juyo bata tsayawa karɓar maganinba, ta fito gabanta
dai faɗuwa yake, saƙe-saƙe take na abinda zata cewa Safiya yau kan ta san kashinta
ya bushe, bata da wata mafita sai ta Allah.
Kalle-kalle ta fara lokacin data fito harabar gurin ko zata Safiya amman bata
ganta ba, da sauri ta nufi harabar asibitin gurin da tadan tayi parking motarta.
Zagawa tayi ta ɗayan ɓangaren ta buɗe motar sai taga Safiya tsaye tana kallonta,
idonta cike da hawaye. Yanzu kan babu kayan ɗazu a jikinta, daman suna saka su ne
idan zasu shiga ciki.
Dakewa ta yi tana ƙoƙarin ɓoye tsoro da fargabar dake ranta ta kalli Safiya tana
murmushin ƙarfin hali

“Ke baki wuce ba, tun ɗazu nake neman ki fa”

“Ke na zo nema daga asibitin ku nake aka ce kun zo nan ku yi wani aiki”

“Ni...?”

Ta nuna kanta cike da mamakin yadda ƴar'uwarta take ƙoƙarin canja abunda yake a
zahiri.

“Amman bayan kin gan ni kin cigaba da tafiya ciki...!”

Ajiyar zuciya Rashida ta sauke a hankali yadda Safiya ba zata ji ba, sannan ta
kalleta da fargaba ta ce

“Safiya kar dai kina zargina da wani abu ne? Don't you trust your sister?”

“I trust you but... Me kike nema gare ni?”

“Akwai inda na so ki raka ni, but seems you don't trust me ba sai na je da ke ba”

Bata tsaya jiran abunda Safiya zata sake cewa ba, ta buɗe motar tana mai nuna
tsananin ɓacin ranta ita ala dole abunda Safiya ta gani ba shi bane, gaskiya take
son canjawa ƙiri-ƙiri.
Da kallo Safiya ta bita har ta tuƙa motarta ya bar harabar asibitin, kallo na
mamaki abinda Yayarta take son canjawa, da kuma tunanin abunda ya kawo ta asibiti a
hiv unit. Tana ɗa buƙatar bincike dan gano gaskiyar lamarin, dole ne ta bincike
ƴar'uwarta, wata ƙila ma tana da masaniya akan Asmee tana da shi.

‘What if ita ma tana da shi fa?’

A zuci tayi furucin tana tafiya, da sauri ta girgiza kai.

“No no A'uzubillahi min shaidanin rajin”

Ƙoƙarin kawar da abin take, dan tana ganin kamar hakan ba zai faru ba, idan kuma
har ya faru to sai idan Mijinta ne ya laƙa mata shi, dan bata san yayarta da
ɗabi'ar banza ba, sai dai kuma abinda ya tsaya mata a rai tunanin abinda zata faɗi
a gida, idan ta faɗi ta tonawa ƴar'uwarta asiri idan kuma ta rufa na su asirin ya
tonu.

Tun a cikin mota Rashida ta fara kuka, ganin take kamar asirinta ya tonu, tun da
Safiya ta ganta, har kuma ta soma zarginta, idan kuma har ta faɗa a gidan to tasan
kowa zai gujeta ne, sunanta zai ɓace haka zai dagula lamarin komawarta gidan Hilal,
sannan kowa zai dan dalilin fitar ta gidan, za'asan alaƙar dake tsakaninta da mijin
Asmee taren su da Asmee zai lalace, duniya zata san ko wacece ita...!

“Anya zan iya bari wannan abun ya faru? Ya zan yi na hana Safiya faɗa? I can't let
her do this, zata saka rayuwata a matsala data tsaka ni a matsala ƙara komai zai
faru ya faru”

A fili ta yi furucin, bayan ta faka motarta a harabar gidan, ta ɗan ɗauki lokaci
kamin ta buɗe ta fito tana farucin
“Idan Asirina ya tonu ai zaman gidan nan ma sai ya gagare ni, duniya ba zata kawo
ƙarshe yanzu ba, i can't let it happen”

Jakarta ta ɗauka ta rufe motar already ta cire hijabin tun a hanya. Sannan ta nufi
ciki tana ra saƙe-saƙe a ranta, da tunanin mafita.
Bata bari kowa yaga dawowar ta a gidan ba, saboda bata son a takura da magana ko
wani abun na daban, nata ya isheta, har aka yi salla magariba bata leƙa falo ba,
sai ana daf da salla i'sha, shima kuma dan taji muryar Safiya ne, sai ta fita ta
zauna falo tana ganin kamar idan tana gurin Safiya ba zata iya faɗar komai ba.
Kallonta kawai Safiya take tana saƙe-saƙen faɗar ko a'a, ita kuma taɓa mata kallo
ɗaya ta ɗauke kanta tayi kamar bata san da ita ba a zaman falon. Da zaman ya isheta
ne yasa ta tashi ta nufi kitchen ta ɗubi abinci ta zo falo ta zauna tana ci ba dan
taɓa son cin ba sai dai ta nunawa Safiya kamar babu komai a ranta.
Ita dai Safiya bata ce mata komai ba, bata kuma nuna mata ba sai kallon mbc 2
take, sai dai a ranta ta ƙudiri aniyar sai ta binciki ɗakin Rashida gobe da safe
tun da tana rigan kowa fita a gidan saboda aikinta.

Sai da ta gama ci tsab sannan ta tashi ta maida plate ɗin ta sha ruwa, ta wuce
ɗakinta, babu komai a zuciyarta sai tashin hankali. Saman gado ta zauna tana
mamakin yadda duniyarta ta canja mata lokaci ɗaya, lallai duniya idan ta so ka, kai
wawa ne, idan kuma ta ƙi ka, ka shiga uku, kai ne ya kamata ka ƙi ta a lokacin da
take so ka, take zaurencen ka, ka so ta a lokacin da take ƙin ka, tana nuna maka
kai ba kowa bane, ta haka zaka gama rayuwarka ba tare da ta yaudare ka ba.
Hawaye take, irin hawayen da baƙin cikinsu kan hana kuka fita, makomarta kawai
take tunani ta san ko yau ba, wata rana zata samu kanta a irin wannan rayuwar da
take gudun shiga, dan tasan asirita ba zai cigaba da rufuwa ba har abada.

“Na yi dama wallahi, duk wannan Alh Bashir ɗin ne yaja min, laifin Asmee ne ita
taje ta ɗibo a wani gurin ta saka mana, wallahi duk na shiga matsala ita sai ta
shiga, sai na sata a matsala”

Kaɗan-kaɗan take rera kukanta dan bata bukatar kowa ya ji, yau ma ya zame mata
kamar ranar da Hilal ya sake ta, har garin Allah ya waye babu abunda take tunanin
sai rayuwar da ta yi a baya, yadda take farkawa a gidan, ta wuni da Hilal sahibin
ruhinta, yau kuma duka babu wannan, wacan rayuwar ta zamar mata kamar mafarki.

Wani abu taji ya tsaya mata a ƙahon zuciya ya yana numfashinta tafiya dai-dai har
tayi salla asuba. Haƙiƙa wanda Halal be wadata shi ba, to Haram ba zai wadatar da
shi ba, ko da kuwa ya wadatar da to ya aure shi ne na ɗan wani lokaci ya sake shi,
a lokacin ne zai gane illar abinda ya aikata. Zina ya zama ruwan dare yanzu babu
matan aure babu budare, an maida abun ado, wasu har gobe suna cin ribar abun saboda
Allah yayi musu istijira'i na ɗan wani lokaci, kamin su haɗu da shi, wasu kuma tun
a duniya Allah zai bayyana su. Da yawa sun ɗauko ƴaƴan da bana miji ba an kawo ciki
gida walau ta gurin bin bokaye ko kuma ta gurin aiki ko abokan banza, shiyasa zaka
ga yara suna kashe iyayensu ko kuna musguna musu ko suna wani abu da bae dace ba,
wanda abu ne mai wahala ɗan halak ya aikata haka. A social media ma yanzu zina ake
macen aure ta kawo wanda ba muharraminta ba gidan mijin ta,, gidanta na sunna, har
ta jashi su aikata alfasha. Wasu akan yi musu lamani kaɗan, wasu kuma da yawa, sai
dai babban tashin hankali gurin haɗuwa da Ubangijin ka...!

Sai a yanzu ta soma nadamar abunda ta aikata, sai dai nadamar bata yi tasirin yanke
kuɗirin dake zuciyarta ba, na komawa gidan Hilal, ta yarda asirinta ya tonu amman a
gidan Hilal, ta yarda ta kauce dukan hanyar da zata kauce inda har zata koma a
gidan Hilal.

Bayan ta yi wanka ta shirya cikin atamfa pink color ta ɗauki mayafinta ta yafa
sannan ta ɗauki handbag ɗinta, bata tsaya karyawa ba ta fice, daman ko ta tsaya ba
zata iya cin komai ba. Kai tsaye gidansu Teema ta nufa ita kanta tayi mamakin
sammakon data dako mata tun da safe, sai ta shirya ta karya sannan Teema ta faɗawa
Iyayenta wai zata raka Rashida gidan Rasuwa, sannan suka fita.

Rashida take driving Teema na nuna mata hanya har suka isa garin ɗan-ƙane, cikin
dajin suka kai kutsawa har suka isa gidan mutumen. Wannan kan ba'a kira sa da malam
ba sai dai boka, dan babu komai a jikinsa sai walki da fatu, irin arnanan ne na
kaduna masara imani waɗanda zasu iya aikata komai ba tare da fargaba ba.

Sun tarar mutane da dama, cikin har da ƴan siyasar da Rashida ta sansu, da kuma
wasu matan manya, inda Allah ya taimake ta ta saka niƙab ba kowa ne zai gane ta ba.
Sai da mutane da ke gabasu suka gama shiga, sannan suka shiga a lokacin sun cin ma
layi.

Irin kayan tsafe-tsafen da ta gani yasa gabanta faɗuwa, har da wani ƙaton madubi
baƙi an masa rubutun larabci da jan jini. Cikin fargaba da tsoro ta zauna gaban
bokan tana kallon walkin dake jikinsa.
Zata fara bayani ya ɗaga nata hannu.

“Bana buƙatar ki faɗa min komai, ni zan baki labarin duniyarki, sai dai idan baki
son kowa ya ji zamu iya sallamar ƙawarki”

Ta jidaɗin maganarsa dan har ga Allah bata son Teema ta ji sirrinta, dan daga ganin
wannan mutumen ba zai ɓoye komai ba.
Ba tare da tace ba, Teema ta tashi ta bar mata ɗakin.
Shi wannan bokan da jini yake duba a maimaikon ƙasa da wasu suke yi da ita, sai
da yayi rubuce-rubucensa sannan ya dubeta ya ce

“Auren ki ya mutu, saboda mijin ya gano kina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki,
kin yi asiri wa kishiryar ki da take gidan mijinki ya faɗawa ɗan ki! Wata
ƴar'uwarki na daf da shirya miki wani abu, akwai yiyuwar ki koma gidan mijinki
amman idan har kin yarda ki daina salla azahar na tsawon sati ɗaya, tabbas buƙatar
zata biya, idan har kika zake jefar abokiyar zaman ki to buƙatar ki zata biya zaki
same ta, amman akwai yiyuwar jifar ta dawo kan ki, haƙiƙa baƙin duhu yana
bibiyarki, wannan baƙin duhun baƙar rana ce...!”

Da sauri Rashida ta miƙe tsaye tayi baya-baya tana kallonsa tashin hankali ƙarara a
fuskarta. Bata iya ce masa komai ba ta fice daga ɗakin kamar wacce ta ruɗe. Tana
fitowa hannun Teema kawai ta kama ta jata tana hawaye suka fice daga gurin. Teema
na tambayar lafiya amman Rashida bata tsaya faɗa mata komai ba, ta shiga motar tayi
mata key ganin hakan yasa Teema ta shiga gidan gaba, kamar za su tashi sama haka
Rashida ta riƙa tuƙin motar suna ratsa dajin, har sai da Teema ta riƙa ta tana
girgizawa, sannan ta dawo hayyacinta har ta rage gudun ta faka gefen titi tana
kuka.

*ABDOOL POV.*

Satinsa biyu a kaduna, kusan kullum sai Amira ta tura masa saƙon barka da safiya da
dare ma haka, sai dai har yanzu be taɓa mata reply ba, shi kan ba ma ita ce gabansa
ba. Kusan kullum sai yayi waya da Ummi kamar yadda ya saba, ya maida hankali akn
aikinsa sosai dan aiki ne mai muhimmanci.

Yau kam be kira Ummi da safe ba har sai da ya shiga office, yana shirin kiranta sai
gata ta kira shi. Da sauri ya ɗauka Cikin jindaɗin kiran na mahaifiyarsa

“Ummi na ta kai na good morning”

“How are you?”


“Im fine i miss you, na ga nawa satin nan ya zo na zo gida na ganki”

“Nima ai ina son ka zo akwai maganar da zamu yi da kai”

“Wace magana ce?”

“Idan ka zo zaka ji, akwai kayan da nayi oda daga paris za su iso Lagos jibi, zan
tura maka address ɗin sai ka aika a karɓo min”

“Yes Ma'am”

Dariya tayi ta kashe wayar shima ya sauke yana murmushi cike da ƙaunar
mahaifiyarsa.

Ɗayan ɓangaren kuma yana jin rashin daɗin maganar da tayi ma mai martaba na cewar
yace a nema masa mata, sai dai babu yadda ya iya tun da shi kansa ya san yana
buƙatar auren a yanzu, idan be yi ba a yanzu sai yaushe, lokaci tafiya yake baya
jiran kowa, kuma shi har yanzu be da wacce zai iya fitarwa a matsayin matar
aurensa.
Sai dai shi kuma ya sha alwashin aurar da duka ƙanensa dan ba zai yarda Ummi ta
riƙa matsa masa ba bayan ga ƙanensa mata nan duk sun isa aure.

*Ummi*
Tana gama waya da shi, sai ga Amira ta shigo da sallama cikin ladabi, already ta
gaishe da Ummi da safe so bata buƙatar repetitive, sai kawai tace

“Ummi me za a girka na rana?”

“Ayi mana mana miyar kuɓewa sai Shukura tayi tuwon semo”

“Tau”

Ta miƙe tsaye ta fice cikin tsantsar ladabin nan. Bata kira Shukura ba da kanta
tayi tuwon semo miyar kuɓuwa sannan kuma tayi miyar agusi dan kawai ta burge su. Ko
da azahar tayi har ta gama komai ta jera a dinning sannan ta shiga tayi wanka.
A lokacin ne su Amal suka dawo makaranta tare da Haleema, daman yau Meesha bata
je ba, dan su da lacca. Fauza ce kawai ta tafi sai Haleema.

A ɗaki suka samu Ummi da Meesha suna duba wasu atamfofi da aka turo ta whatsapp.
Jikin Ummi Amal ta faɗa tana zuba shagwaɓa wai ita ala dole ga auta.

“Ummi yunwa”

“Ai ga abinci can ana gama”

“Me aka girka”

Haleema ta tambaya tana zaunawa kusa da Meesha.

“Tuwon semu miyar kuɓewa”

“Ɓi bana so, sai dai ki girka min makaroni”

“Kai Amal kin cika son rigima wallahi, miyar tayi daɗi fa”

“Wa yayi? Wannan Amira ko”

“Eh miya har kala biyu tayi”


.“Ni bana so bata iya komai ba sai ƙazanta”

Haleema ta buge mata baki

“Data saba girkawa kina ci fa? Wai Amal miyasa baki da kunya, ke uban kowa kin
raina, Amirar nan aiki da take ko da muke cikin gida albarka, tana ƙoƙari sosai
wallahi”

“Ta riga ta saba wahalar ne tun gidansu, maybe talakawa ne”

Cewar Meesha, tana taba eyebrows.

“Ba wani sabo wallahi kawai dai tana da mutunci ne, kuma gani nake kamar Big bros
take so, dama an haɗa su wlh dan zata kula da shi”

Meesha ta tofarda yawu

“Tuuu Allah kiyaye big Bros da wannan yarinyar amman wallahi Haleema baki da
hankali zuwa makaranta be amfane ki ba, daga ganin yarinya an taimaka mata ki ce
wai ta auri yayanki, ke anya kina son yaya kuwa? Ke nifa ban ma yarda da yarinyar
nan ba, tsantsan ɗinta yayi ta cika shige mana jiki, waya sani ko cutar mu ta zo
tayi”

Amal ta haye saman gadon Ummi tana hararar Haleema.

“Sai na gayawa Dude, mu mana son ta”

Ummi ta kama kunne Amal.

“Bana raba ki da yi ma manya rashin kunya ba?”

“Ooo Ummi it hurt”

Ta riƙe kunne, tana son kuka. Haleema yaja wani dogon tsaki

“Ke kin wuce shiga halin da ta shiga ne hala? Idan Allah ya tubuta shine mijinta ya
zaki yi?”

Ummi ta kalle ta kallo da babu wasa a fuskarta.

“Ke Haleema ki daina wannan maganar, yarinya daga taimako sai kuma neman wuce gurin
tana da tarbiya zata bar gaban iyayenta ana neman ta koma bata so sannan ki ce ta
auri ɗan'uwanki dan baki da tunani? Kin san iya zaman da ta yi taraiya da su? Wanda
yayi maka hallaci ya cancanci hallaci shiyasa take zaune tare da mu, amman nan gaba
kan gurin iyayenta zan maida ta, Allah ya bata miji na gari”

“Amman Ummi ta mana hallaci wallahi, kuma idan ba a barta ta auri Yaya kamar ba a
mata hallaci ba”

Meesha ta zungureta

“Ai ke sai ki mata hallaci ko? Yayan manya ma Big Bros be so ba sai ita yarinyar
data ƴan fashi, ashe za'a iya haɗa kai da ke ayi ma masa wani mugun abu, haka kawai
daga ganin yarinya ki ce a haɗa su amman baki da hankali Haleema”

“Ke da kika da shi ai sai ki ara min na saka, ko ita ba mutum bace? Ke idan kina so
wani ya zaki ji”
“Ba zan so wanda ya fi ƙarfina ba balle har na damu, ke daga ganin ajin Yaya kin
san yafi ƙarfin Amira wallahi, yarinyar data gama bada kanta ga mazan banza sai
kuma ta dawo yaya ya aureta, ai abun kunya ma ne wallahi”

Cikin faɗa Meesha ta ƙarasa tana jin kamar ta kama Haleema tayi mata shegen duka.
Ita Haleema ji take kamar ta daki yar'uwarta. Har sai da Ummi ta katsa musu tsawa.

“Haleema kar na sake jin irin wannan kalamin a bakin ki, Aisha ke kuma ya isa tun
da ba cewa aka yi za a aura masa ita ba, ku Shafa min lafiya dan Allah ku tashi ku
bani guri”

Duk miƙewa suka yi suka fita, ban da Amal data laƙe jikin Ummi ita ala dole sai an
dafa maya makaroni.

“Ai kema kin iya dafawa, Amal har mota kike tuƙi fa amman ki zo kina min abu kamar
jaririya, idan yanzu aka miki aure ai sai zama dan kin girma, ba kece auta ba
autana tana nan zuwa”

Ummi ta faɗa da raha a fuskarta. Amal ɗin tasa dariya dan tasan abu ne mai wahala a
yanzu.

“Za a ce tsohuwa ta haihu”

Ummi ta tiƙi bayanta tana dariya

“Yes Tsohuwa maman Amal, tashi ki cire uniform”

Tashi ta yi ta fice tana dariya.

*NAMRA POV*

Kamar yadda suka saba yi duk mai ciwo, bayan ta faɗa masu matsalarta sai suka bata
gwajin jini da fitsari, suka sa kuma taje ta yanki sabon kati dan duba wacan
matsalar nata na robar dake hannunta dan a bayanin da ta yi ma likita ya fahimci
ciki ne a jikinta. Sai dai bashi da tabbacin haka tun da ta faɗa masa tana saye da
roba, duk da yasan ana samun irin wannan matsalar a wani lokaci.

Awan fitsari kawai ta samu yi, a take, na jini cewa suka yi sai da yamma ta zo ta
karɓa, su kuma waɗanda zasu dubata a ɓangaren robar sun tashi aiki.
Tun da karɓo results ɗin ta kasa ta buɗe dan bata son ta ga abinda yake ciki,
tasan idan har ciki ne tana cikin matsala dan bata gama warkewar ciwon mahaifarta,
kuma ga roba jikinta ace tayi ciki tasan duka ƙarin matsalar ne. Ko da ta koma
gurin likitan yana shirin tashi, har ya haɗa kayansa, a tsai-tsaye ya duba takardar
tana fuskarsa da mamaki ya ce

“Kina ɗauke da juna biyu”

Ras ras ras gabanta ya faɗi, sai ta faɗi saman kujera tana hawaye. Da sauri likitan
ya aje kayan hannunsa.

“Hey wannan ba wata matsala bace ana samun irin haka daman, amman abunda yafi zan
rubuta miki hoto sai kije ayi hoto a bincika lafiyar cikin, kuma ki tabbar kin je
an cire miki wannan robar”

“Doc mahaifa tana da matsala shiyasa aka samun robar”

“Ba lallai ne har yanzu matsalar ki tana nan ba, shiyasa nake son ki yi hoton”
Ya ɗauki wata takardar yayi rubutu ya miƙa mata.

“Kije ayi miki hoto, zuwa gobe sai ki kawo na duba ki, ko kuma ki dawo wani likitan
ya duba ki, ki kwantar da hankalin ki ba wani abu nima mai ɗaki na ta taɓa haka”

Jakarsa ya ɗauka ya rataya ya face. Sannan ita ta tashi ta fito tana hawaye,
maimakon taje gurin hoton sai kawai ta yanke shawarar komawa gida dan ita har yanxu
jikinta na bata ba ƙalau take ba, balle bata da kuɗin da zasu isheta hoto tun katin
ganin likita na asibitin ma kusan ɗari bakwai ne.

Tun cikin Napep take ta kiran Asim amman ya ƙi ya ɗaga saboda yana gaban Hajiya,
wacce ta zame masa kamar uwa a yanzu, yadda yake jinta ko Mama data haife sa baya
jinta haka nan.
Hakan yasa ta yanke shawarar tura masa saƙon karta kwana.

Ƙin ɗaga wayar yayi dan akwai yana gaban Hajiya, ita ta jidaɗin hakan da yayi ko ba
komai tasan ya girmamata, gashi tun da yazo gidan be taɓa fita da sunan yaje gida
gurin matarsa ba.
Sai da ta gama lissafa masa abunda zai siyo mata sannan ta bashi kuɗin tana
murmushi ciki ladabi ya karɓa ya tashi ya fice.

Sannan Hajiya tayi murmushi ta maida dubanta ga ƙawarta, Hajiya Ubaida.

“Gaskiya yaron nan yana da ladabi ina kika damo shi?”

“Uhmm tsuntsune daga sama gasasshe Allah ya bani daga gyaran gate”

A nan ta kwashe labarin komai ta bawa Aminiyarta yadda suka haɗu da sharaɗin data
gundaya masa da kuma zaman gidan da yake, da kuma ƙudirinta a kansa.
Hannu Hajiya Ubaida ta bata suka taɓa

“Shegiya Sadiya duk abunda kika sawa gaba sai kin ga bayansa, hala yarinyar mai
kyau ce?”

“Tana da kyau wallahi ta haɗu ba ƙarya, sannan kin ga na samu dama biyu, daman
Alhaji Usaini ya dame ni na samo masa sabin shiga, wai duk wanda nake kai masa basa
da ladabi kuma an taɓa amfani da su, kwana biyu sai su fara masa tsageranci”

“Ai kin san manyan mutanen nan sun fi son tsaida mutum ɗaya, wanda zasu riƙa amfani
da shi kullum”

“Eh shi ma haka yace, wai idan yana bin irin guys ɗin nan za'a iya gane shi, yafi
son tsaida mutum ɗaya, kuma kin ga irin wannan zai fi jindaɗinsa dan ga alama zai
yi ladabi, sannan garin su ɗaya, idan ta kama ya koma can ma, ni sai ya barmin
matar a nan, dan ba zan taɓa nuna masa ina don matarsa ba, shi wata rana zan iya
buƙatarsa”

Hajiya Ubaida ta ƙalƙyale da dariya.

“Ke Allah dai ya yafe mana, ya shirya mu”

“Amin kedai ai ina son tuba amman sai nan gaba, dan bana son Zeenat ta san halin da
nake ciki”

“Gaskiya kam, ai ƙara ai daina da wuri kar azo aji kunya”

Hajiya Sadiya tayi fuskar tausayi kamar mai tsoron Allah da gaske, tana kallon
Hajiya Ubaida wacce sana'arsu ta zama ɗaya.
*ASIM*

Be wuce kasuwar ba, sai da ya bi ta gida dan jin abinda Namra zata faɗa masa, badan
saƙonta da yaga ni babu ma abunda zai sashi bi ta gidan. Kamar baƙin haɗari haka ya
doshi gidan bakinsa ƙumshe da maganganu kala-kala, dan gani yake a yanzu shi ma ya
kai matsayin da zai iya faɗawa magana son ransa, balle Namra da yake gani kamar
banza.

A ɗaki ya tararar da ita kwance sai hawaye take. Daker ta ɗago ta kalleshi, duk da
tana cikin yanayin damuwa hakan be hanata, kallon irin shigar dake jikinsa ba.
Takalmin dake ƙafarsa kaɗai zasu iya kaiwa dubu 10+ balle wando da T-shirt.
Be ji zai iya zama a ɗakinba, sai kawai ya tsaya jikin ƙofa yana mata wani kallo,
azuciyaraa yake hantararta ganin yadda ta ƙara lalacewa.

“Ya aka kika samu ciki?”

Wani kallo tayi masa zafin furucinsa yana zuciyarta.

“Kamar ya? Ina da wani mijin ne bayan kai”

“Ni ya za'ayi na sani, yanzu ai ba a shedun mutum”

“Shigowarka Asim irin wannan furucin zaka min? Tun da kasa ƙafa ka bar gidan nan
babu ruwanka da ni kamar ba matar ka”

“Ya kike so nayi Namra aikin zan bari na zo na tisaki gaba nayi ta kallo ko me?
Yanzu ma a hanya nake saƙon da kika min ne yasa na biyo”

Kawarda kai tayi ta haɗe hawayen da take da tabbacin idan har suka fara zubar mata
bata san lokacin tsayawarsu ba.

“Daga Asibiti na ke likita ya ce ina da ciki, kuma akwai roba a jikina”

“To ya aka yi haka?”

“Nima ban sani ba, amman yace min daman akan samu hakan wani lokaci, yace naje nayi
hoto aga lafiyar cikin, Asim ina tsoron ko mahaifata bata gama warkewa ba”

“To a zubar da cikin mana”

Miƙewa tayi tsaye tana kallonsa.

“A zubar fa kasa kasan abunda kake faɗa?”

“Na sani mana, Namra wannan ba lokacin samun yara bane, muna planning na neman kuɗi
kuma yara zasu shigo, ki duba irin wahalar da muka sha a baya yanxu kuma hanya ta
fara buɗe mana sai kuma haihuwa ta zo, gaskiya ni ban shirya ba”

“Ni kuma na shriya Asim, ni nake da matsalar da nake da a mahaifata kuma im ready
to give birth saboda nima haihuwata aka yi, Allah ba xai bani kyauta na jefar ba”

Cikin wata murya tayi furucin muryar da bata san tana da ita ba sai a yau. Shi kuma
ya gyara tsayusarsa yana mamakin ta

“Wallahi Namra sai yanxu na gane lallai ke ba masoyiyata bace. Kin manta lokacin da
nake cewa kije ki cire robar nan amman ki ƙi, ko wannan zubar da ciki da kika sha
ban san lokacin da kika sha ba, wata ƙila kin yi zubar da cikin ne shiyasa har
mahaifarki ta samu matsala, sai yanxu da kika ga zan yi kuɗi ko shine zaki nuna min
baƙin hali ki ɓullo min ta haihuwa, to ni ban shirya haihuwa yanzu ba dan haka dole
a zubar da cikin nan”

“Wallahi tallahi ba zan zubar da wannan cikin ba, ko da kuwa wannan cikin yana nufi
ya rayu, ni na mutu”

“Haka kika ce?”

“Haka na ce kuma haka xaka gani”

“To sai dai ki zaɓa ko ni ko cikin nan...!”

Wani kallo tayi masa na ƙara tantance zancen daya fito daga bakinsa. Shi kuma sai
ya ɗaga mata kai dan ya tabbatar mata da maganarsa.

“Yes Idan har baki xubar ba sai dai kije can gidan ku ki haife ɗan, ke kan ki ba
samun lafiyarki bane ace kin haihu cikin kuɗi kuma a lokacin mahaifarki tana lafiya
ƙalau, na baki lokaci ki yi tunani akai”

Juyawa yayi ya fice, zuciyarsa cikr da tabbacin abinda yayi be yi kuskure ba.

*ANTY AMARYA POV*

Sai da dare Abbah da Hajiya Barau da Anty suka samo ganin lefen da ka kawo, Abbah
ya yaba sosai, Hajiya Barau ma ta yaba amman yabon baka yabon daya zame mata cilas
dan sam bata jidaɗin ganin yadda aka zubawa ƴaƴan Anty wannan uban lefen ba.
Hindatu kala 54 Maryam kuma 79 cikin su kuma babu shege balle ɗan iska.

“Allah yasa alheri ya nuna mana lokacin, amman na ɗauka Namra zata xo tarbon lefen
nan”

Anty Amarya taji babu daɗi, sai dai bata nuna ba, sai kawai ta ce.

“Ta so tazo mijin nr ya hana ta yace wai ta bari dai nan gaba sai su zo tare”

“Allah ya taimaka, lefe yayi mashallah”

Haka ta taso ta fito daga falon da ƙahon baƙinciki daya tsaya mata a zuciya. Part
ɗinta ta shigo tana shiga ta shige ɗakinta ta zauna, babu abunda take tunanu sai
duniyar da Abbah xai kashe masu gurin auren, kamar ita ba a ma ƴaƴanta.

Ummi ce ta shigo ƴar gurin Hajiya Barau mai sunan mahaifiyarta hakan yasa take
kiranta da Ummi.
Duk cikin ƴaƴanta mata ita kaɗaice tazo tarbon lefen. Kusa da mahaifiyarta ta xauna
tana kallon yanayinta kallonta Hajiya Barau tayi

“Kin gani ke kina son kashe na ki aure su kuma suna yi, idan so kike ki dawo gida
mu zauna sai ki dawo”

“Haba Hajiya wallahi ni na gaji da irin wannan rayuwar da yake nuna min, kwata
kwata bana gabansa, baya da aiki sai neman mata, tun abu na ɓoye har magana ta fara
fita, ko fita nayi sai ya kawo wata a gida”

“Ina ruwanki da neman matansa? Ai kedai yana baki ci da sha ko yana baki na kashewa
ina ruwan ki da lamarin, yanzu neman maza ma ake balle mata, abun ai yyi ne wanda
be yi ba to bashi da kuɗin yin ne, ko ni ya nema kya ce ki kashe auren ki ki dawo
gida balle kuma wata can daban”
Miƙewa tayi tsaye cikin ɓacin rai ta fice, dan tasan duk yadda take son
mahaifiyarta ta fahimci matsalarta ba fahimta zata yi ba.
Ƙwafa Hajiya Barau tayi taja wayarta tana soma labartawa abokin gulmarta rashin
zuwan Namra tarbar lefen ƙannenta.

Duk hirar da suke be nuna mata jindaɗin hakan ko rashin jindaɗin saboda yana gaban
Yasmin ne, yawancin maganar bata wuce uhn a'a ato, Har suka gama wayar.

Ƙaton cikin Yasmin ya kalla yana murmushi.

“Allah yasa karki haifa minɓɗa mai kahuwa”

Ta tsuke baki

“Mai hali dai baya fasa halinsa, ni wallahi haushi kake bani sosai”

“Daman duk kina da ciki ai baki ƙaunata kamar na kashe miki wani”

Ya faɗa yana jawo wayarsa da tayi ringing, number abokinsa Tahir ya gani.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ”

Shine abunda ya furta bayan ƴan daƙiƙu da karɓa wayar.

“Okay gani nan zuwa”

Ya tashi tsaye da sauri, har Yasmin ta kalleshi

“Lafiya?”

“Wai Najeeb yayi hatsari, nan cikin gari”

“Subhanallahi, ina fatar be ji ciwo ba”

“Ban sani ba, sai naje tukunan”

Da sauri ya ɗauke Adnan da ke saman jikinsa ya ɗauki wayoyinsa ya zuba aljihu tare
da keys ya fice hankali tashe.

*HILAL POV*

Lallaɓata yayi har sai da tayi shiru sannan yaja ta zuwa saman gadonsa ya zaunar da
ita ya kama hannayenta ya riƙa.

“Na yarda ba ki aikata ba shikenan?”

“Har zuciyarka ka yarda da ni?”

“Na yarda da ke?”

“Zaka daina fushi da ni?”

“Zan daina”

“Zaka dawo da su Ezzah”

“Idan Hajiya ta yarda”

Haka yake ta amsa mata kamar tambayar babba da yaro, sai ya hau saman gadon yaja ta
ƙirjinsa ya rumgume.

“I Love You”

Ƙamkamshi tayi

“I love you too”

Sun daɗe a haka kamin ya sake ta ya shiga yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin
sai ta ɗauko masa abinci. Ba dan yana so ba ya zauna yayi ƴan lomomi kaɗan ya tashi
ya nufi gidan Hajiyarsa.

Da shigarsa Ezzah da Ulfah da sauran yaran gidan suka rugo da gudu suka tarbeshi.
Ulfah ce kawai ta tambayi Kalsoom Ezzah kan ko a jikinta. Bayan ya gama ganinsu ya
miƙa musu chocolates ɗin ya shigo da shi sannan ya wuce gurin Hajiyarsa.

Tun daga yanayin yadda ta amsa masa sallamarsa yasan akwai abunda ya faru. Guri ya
samu ya zauna yana kallon tv dake ɗakinta, kamin daga bisani ya gaishe ta. A
maimakon ta amsa sai kawai ta hau shi da faɗa

“Yanzu fisabilliahi abunda kake ƙoƙarin yi kyautawa ne? Kace xaka kare ta idan kun
je kutu bayan ga abunda tayi ma ɗan ka, irin waɗannan matan fa zama da du matsala
ne dan kai ma xata iya maka haka”

Daga yanayin maganar ta ya gane Amina ce ta kawo mata zancen, dan ita kaɗai yasan
yayi zancen a gabanta sai kuma Alh Bashir.

“Amman Amina munafukace wallahi, zuwa tayi ta faɗa miki ko?”

“Ai dole ta faɗa min mana tun da abun yayi mata zafi, ni kama rabu da wannan matar
ka nemi wata ka aura”

“Gaskiya ba zan iya rabuwa da ita ba”

“To ko zaka auro wacce zata riƙa maka ƴaƴanka, dole ne ka ƙara aure ko kuma ka rabu
da ita idan baka shirya zama da mata biyu ba”

“Haba Hajiya, kuskure ne nima a yanzu na gane ba ita ce ta aikata ba”

“To waya aikata? Ga abu ƙiri da muzu ka nemi takewa dan kana son ta, ah lallai ba
banza ta barka ba, Ezzah ma tana ta faɗar irin abunda take musu a gidan, cin amana
zalla”

Dariya abun ya bashi yau kuma Hajiya da kanta take irin wannan furucin.

“Babu maganin komai Hajiya, amman wannan matsalar nima ban san kan ta ba”

“To ni dai na faɗa maka ko ka ƙara aure ko ka rabu da ita, tashi ka bani guri”

Kansa ya dafe yana sauke ajiyar zuciya

“Hajiya ki fahimta...”

“Ba zan fahimta ba, ka tafiyarka kawai”

Yasan duk yadda zai yi ba zata fahimta sai kawai ya tashi ya fice da jimmar idan ta
huce zai dawo ya fahimtar da ita.
-----------------------------------------------------------------

*Jiya naje biki ban samu na yi typing ba, so wannan zai zama na jiya, na yau kuma
sai dare zan kawo. Thank you 🖤*

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *60 - NOT EDITED ⚠️


*

*RASHIDA POV.*

“Teema ya faɗa min abinda ya fi ƙarfin zuciyata da tunani, ya bani labarin yau da
kuma gobe na, ƙoƙari raba ni yake da Ubangijina”

Ta faɗa cikin kuka, tana mai jin tsantsar ƙyama da kuma tsanar bokan a ranta, ta
kuɗiri aniyar zata iya aikata komai akan duniyarta amman ba zata iya aikata abunda
ya faɗa mata ta aikata ba.
Teema ta tsire baki, tana mamakin ƙawar ta'ta.

“Ai kin daɗe da rabuwa da raba hanya da Ubangijinki, tun da kika soma neman
taimakon wani daga cikin bayinsa, Abunda zaki yi kawai ki aikata wannan in yaso
daga baya sai ki nemi yafiyar”

“Ya ce min baƙin hudu yana bibiyata, kuma wannan baƙin duhun baƙar rana ce, what if
ranar mutuwa na ne? Ba shine na farko daya faɗa min haka ba, Teema ina tsoro”

Kyalƙyalwa Teema tayi da dariya har da taɓawa tana kallon Rashida.

“Amman Wallahi kina da abun dariya, miye abun tsoro kuma? Ashe ke sabowar shiga ce
wannan harka, ba lallai baƙar rana ta zama ranar mutuwa ba, yana nufin akwai abunda
zai same ki marar daɗi wanda ke da kan ki zaki kira abun da baƙar rana”

Ta ɗan ji sassauci a zuciyarta, har ta samu damar haɗe yawun da ya tsaya mata a
maƙoshi.

“Ni dai ina ganin haƙura zan yi, kar naje na sake mata kuma ya dawo kaina dan yace
zan yi nasara amman akwai yiyuwar ya dawo kai na”

“Amman wallahi Rash kin ban mamaki, ke da na ke ganin, kamar zaki iya aikata komai
akan Hilal, ashe son da kike masa na ƙarya ne, tun da har zaki iya bar wa wata shi,
yanzu duk soyayyar da kuka yi ta tashi a banza kenan? Ƴaƴanki sun zama nata mijinki
ya zama nata? Ko akwai wani wanda kike so bayan Hilal?”

“Babu shi, Hilal ne kawai, wallahi ina sonsa sosai”

“Kuma kin yarda ki barwa wata shi ko?”

“Na samu matsala akan jifar da nayi mata Teema, na jefeta ya faɗa kan ɗa na, kin ji
ai yanzu yana faɗa min, yanzu haka Rafiq yana can kwance asibiti babu lafiya, ya
damu matsalar ƙwaƙwalwa”

“Lallai wannan mata ita bata tsaya akan ta, irin wannan matar maganinta ki samu
fitsari ki zuba mata a ruwa ya jiƙa ta sha, wallahi duk wani magani na tsari jikin
data sha sai ya karye, amman kin ce tana shiga malamai ita ma?”

“Haka nake gani, saboda gaba ɗaya Hilal ya haukace ba shi da magana ta kowa sai na
ta, baya kula ni a yanzu, kuma kin ga da dane ba zai iya sakina ba amman yanzu duba
ki ga ya sake ni”

“To ina ganin ba tsari bane itama ta iya shige-shigen ne, sai aka bata aljana ta
tsare ta, kin san wasu suna haka fa dan akwai su cimma burin su”

“Da gaske? Ballatana ta daɗe ba tayi aure ba zata iya haka”

“Dan haka ki kwantar da hankalin ki, ki share hawayen ki matuƙar ina raye sai kin
koma cikin ƴaƴanki, yanzu kin ga mun fito cikin tashin hankali baki masa sallama
ba, amman yanzu idan hankalinki ya kwanta natsuwarki ta dawo jikin ki, sai mu koma
yayi mana aikin kawai”

“Amman ya ce sai nayi fashin salla fa?”

“To miye a ciki? Wasu ma baki ga rai suke kashewa ba? Ai daga baya sai ki ranka ki
nemi yafiyar ubangijinki Allah fa gafurun rahimun ne, kin ga sai ma ki daina kwata
kwata”

Shiru tayi tana nazari, tasan idan har ta aikata wannan abun ta yi, babban saɓo, ta
yi fashin salla saboda biyan buƙatar da bata da tabbacin zata biya? Ajiyar zuciya
ta sauke ta cigaba da tuƙin.

“Zan yi tunani akai Teema, amman ina jin tsoro sosai”

“Ai da tsoro zaki cuci kan ki, kawai ki cire wannan tsoron ki yaƙi zuciyarki”

“Zan yi ƙoƙarin yin hakan”

Daga nan Teema ta ɗauko mata firar ƙawarsu, ita mai bin bokaye marar tsoro, wance
ta mallake miji da uwarsa.
Duk tana yi ne dan kawai ta ƙara tunzira Rashida ta aikata, so that ita ma ta samu
abokin shiga wuta, dan mugu be son ace shi kaɗai yake aikata abu.
Sai da ta fara biyawa ta sauke Teema a gidansu, sannan ta wuce na su gidan dan ta
yi shirin zuwa gurin aiki, ganin karfe ɗaya ma bata yi ba.

Tun da tayi parking a harabar gidansu ta fara saƙe-saƙen abunda zata faɗa gurin
aikin, dan gaba ɗaya kashe wayarta tayi. Tana shiga falo sai ga Momy ta fito daga
ɗakinta jiki na rawa, Rashida na ganinta ta gane hankalinta a tashe yake.

“Momy lafiya?”

“Lafiya ba lau ba, tun ɗazu nake cikin zullumi Rashida”

“Me ya faru?”

Momy ta tsaya tunanin ta inda zata soma, dan tana jin faɗin kalamar kai tsaye.

“Safiya tace min ta ga ƙawarki Asma'u a... Hiv unit....”

Yadda kasan cida haka gaban Rashida ya riƙa faɗuwa, zuciyarta na zillo kamar ta
fito, a take yawun bakinta ya tsarƙe ta har sai da ta soma tari. Tasan Momy ba
Asmee take nufi ba, idan kuma har da gaske Asmee take nufi to Safiya ce ta faɗa,
kuma taya Safiya zata ga Asmee ita ce ta gani.

“Safiya ce ta faɗa?”

Momy ta ɗaga mata kai tana hawaye.

“Ni ta ce ta gani ko?”

Nan ma kai Momy ta ɗaga mata.


“I tell not once not twice several times, naje nemanta ne a asibitin amman ta ƙi ta
yarda gani take kamar ni ce naje a karan kai na...”

Maganar take tana nuna da gaske take, amman bata son kallon Momy. Kai Momy ta
girgiza na tausayin ƴarta da kuma ganin wautarta akan abunda take ta ƙoƙarin
ɓoyewa.

“What about the results?”

Da sauri ta kalli Momy, tana mamakin kalamanta. Kenan bincike suka mata lokacin da
bata nan! Ita da tayi ma results ɗin mugun ɓoyo taya aka yi suka gani?
Durƙushewa tayi a gurin ta fashe da kuka mai ƙarfin gaske. Momy bata san lokacin
data ƙarasa gaban ƴarta ta rumgume suka soma kukan tare.

“Taya haka ya faru Rashida ta ya? Miyasa kika yi ƙoƙarin ɓoyewa?”

Cikin kuka Momy take tambayarta, tana jinjigata. Da sauri Rashida ta zame jikinta
daga na Momy ta tashi da sauri ta shige ɗakinta ta kulle da maƙulli. Jinginawa tayi
jikin ƙofar tana kuka, irin kuka mai sa kaji kamar ka cire ranka ka huta.

Momy ma kuka take sosai, dan yanzu ne ta ƙara tabbatar da zancen Safiya. Daman tun
Safe Safiya ta shiga ɗakin Rashida tana mata bincike har Momy ta same ta a ciki,
anan takr faɗawa Momy haɗuwarsu da Rashida a asibiti. Da kuma maganin da abokan
aikinta suke bawa ƙawarta Asmee, a wacan Asibitin ta su.

Babu irin bugun ƙofar da Momy bata yi ba, amman Rashida ta ƙi ta buɗe, kuma ta ƙi
tayi magana, sai kuka take. Waya Momy ta ɗauka ta kira Dady ta faɗa masa, cikin
ƴan'mintuna sai gashi ya dawo gida hankali a tashe, ɗan har gumi ke keto masa ta
ko'ina.

Kai tsaye ɗakin Momy ya nufo, sai ya same ta itama tana kuka.

“Ya aka yi haka ta faru? Amman an tabbatar?”

Kallonsa Momy tayi idonta na zubar da ƙwalla.

“Safiya ce ta faɗa, nima ban yarda ba har dai yanzu dana nuna mata na ga takardun,
bayan kuma ban gansu ba nace ne kawai dan na gano gaskiyarta, kuma the way she act
ya nuna tana da shi”

Jiki a sanyaye Dady ya zauna idonsa sun rine sun yi wani ja sosai, irin na ɓacin
rai da damuwa sun sauka ga mutum. Can kuma ya sauke ajiyar zuciya yana ta nazarin
inda Rashida zata samo hiv da tsakar rana.

“Amman ƙara dai a bincika, ba lallai ba ne tana ɗauke da ciwon to ina ma zata kwaso
wannan ciwon?”

“Hilal mana, ai shi kaɗai ne mutunen da take taraiya da shi”

Cewar Momy tana kuka, zuciyarta na ayyana mata shi ɗin ne tun da shine kaɗai mijin
Rashida. Da sauri Dady ya kalleta

“Wallahi idan kuwa shi ne ya saka mata shi, sai na ɗaure shi gidan yari har ƙarshen
rayuwarsa, marar mutumci marar taddako wanda be san halin girma ba, Allah ya usar
mana, wallahi ya cuce mu, shiyasa ya sako ta. Ina Rashida take ne?”

“Tsna ɗakinta, ta ƙi ts buɗe tun ɗazu sai kuka take, ta ƙi tayi magana ma”

Tashi yayi yana cire ƴar saman suit ɗinsa, yana sassauta necktie ɗinsa, ya nufi
ɗakinta jikinsa har rawa yake kamar mazari.

Sai da ya soma kiran sunanta, jin bata amsa ba yasa ya soma ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.

“Rashida ni ne buɗe mana... Ba wani abun za mu miki ba kawai magana za mu yi, kuma
ba zamu faɗawa kowa ba”

Tana jinsa amman ta kasa amsa masa dan bata da abinda zata faɗa masa, tasani
matuƙar suka gano gaskiyar dalilin cutar nata ba zasu zauna da ita ba, who else
kuma zai zauna da ita bayan iyayenta, lallai ko a haka rayuwa ta tsaya mata ta san
ta kai karshenta.

Babu irin maganar da Dady be mata na rarrashi da tausasa zuciya ba, amman ta ƙi ta
amsa masa balle ma har ta buɗe ƙofar.
Dawowa yayi ɗakin Momy ya tsaya daga jikin ƙofa fuskarsa da damuwa ya ce

“Ko dai za mu kira shi ne mu tambaye shi?”

“Idan shine taya zai amsa cewar shi ne? Zai yi ƙoƙarin kare kansa ne, kuma kasan
babu wanda Rashida take mu'amala da shi sai Hilal dan shin mijinta kuma ni ƴata ba
ƴar iska ba ce, ta bakinta ya kamata aji komai”

“Ta ƙi tayi magana, ɗakin ma ta ƙi ta buɗe”

“Zata yi magana, dole zata buɗe kabarta hankalinta ya kwanta kawai, ka koma gurin
aikin ka”

“Ba zan iya wani aiki ba ko naje, jikina ya riga da ya mutu, Wallahi Hilal ya cuce
mu, amman miyasa Rashida ta yi ƙoƙarin ɓoye irin wannan babban al'amari?”

“Allah kaɗai ya sani, amman rufawa irin wannan mutumen asiri ai ba abun yi ba ne,
wallahi sai na sashi yayi nadama sai ya ƙwammace kiɗa da karatu”

A bakin ƙofar Dady ya zauna irin zaman nan na baka san ka yi ba, hankalinsa baya
jikinsa, natsuwarta ta gudu ta barsa.

*NAMRA POV.*

Maganganun Asim sun tsaya mata a zuciya, duk bayan dogon numfashinta sai kalmar
rabuwa da yayi mata ya maimata kanta a kunnenta. Da zancen ta kwana a ranta, tana
mamakin Asim, yadda yayi tsaye yana faɗa mata magangu kamar wani ɗan shaye-shaye.
Bw ɗauke a matarsa ta sunna ba be riƙe ta da muhimmaci ba, shiyasa har ya zaɓi
aikin da yake sama da ita, yanzu kuma yake neman rayuwa da ita saboda tana da
ciki. Sai yanzu take nadamar rashin bin Anty, dan tasan babu makawa Asim rabuwa
zai yi da ita, matuƙar bata zubar da cikin ba, dan ta ga gaskiyar maganarsa a
idonsa, sai dai ita kuma bata jin zata iya zubar da cikin ko da kuwa shege ne balle
na Sunna.

Sai dai idan Asim ya sake ta ina zata je? Ta koma gida da ciki ta faɗawa Abbah
Asim ya sake ta? Ta bi sawon Anty bayan ta nemi taje gidan ta ƙi yarda sai yanzu da
Asim ya sake ta kuma take ɗauke da cikinsa.?
Tashi ta yi zaune, sai ta nemi kuka da take ta rasa, washe ƙaramin abun ake yi ma
kuka, tashin hankalin dake tare da ita baya barin hawayenta zuba.

“Kaico na ni Namra, Ina zan sa kai na sanyi? Ina zan sa rayuwar na samu sassauci?
Haƙiƙa wanda duk ya so abinda iyaye suka ƙi yayi hasara, da nasan haka aurena da
Asim zai kasance da ban aure shi ba, Allah ka yi min gata Allah”

Hannayenta ta ɗaga sama, tana roƙon Ubanjiginta, zuciyarta cike da yaƙinin lallai
Allah zai ƙarɓa mata.

“Ya Allah ka tsare min mutunci na, ka tsare min lafiyata,


Allah ka yi min gata ka tsare min imani na da hankalina,
Allah ka yi min sutura ka kwantar min da hankali
Allah ka kyautata min rayuwa ta, Allah idan aure da Asim Alheri ne Allah ka
tabbatar da shi, idan rabuwa da shi ne samuwar jindaɗina Allah ka zaɓa min abunda
yafi zama Alheri a gare ni,
Allah ka shirya tsakani na da iyaye na, Allag ka gafarta min kurakurai na
Allah ka tabbarda duga duga-dugaina akan addinin ka”

Bayan ta shafa ta koma ta kwanta, ta kai hannu ta shafa cikinta, tana mai jin
tsantsan ƙaunar abinda yake kwance a mararta.

*ABDOOL POV.*

Misalin ƙarfe biyu da rabi na rana jirginsa max air ya sauka a tashar sauka da kuma
tashin jirage da ke katsina.
Be sanar da Ummi zuwansa ba, dan haka be tsamaci ta tarbe shi ba, ko ta aiko da
motar da zata ɗauke shi. Sai dai hakan be a aiko masa da motar da zata ɗauki daga
headquarter ba dan sun san da zuwansa.

A yadda suka tarbi shi ya burge kowa a gurin, mota uku suka faka. Already sun buɗe
motar suna hangosa tafe sai suka duk suka fito wajen motar suka tsaya, a jikin
kayan gida yake amman hakan be hana dukansu su tsara masa ba, babu wanda yayi motsi
a cikin su har sai da ya shiga motar sannan suka rufe masa suka shiga.

“Gurin Mai Martaba zamu je”

Yanda yayi maganar ba ka ce shi ne ba, dan hankalinsa gaba ɗaya yana kan wayarsa
sai faman duba shafukan yana gizo yake dan sanin abinda ƙasa take ciki.
Har aka isa Ahmad Mai-doki road, Abdool be ɗago ya kalli mai driving ɗinsa ba,
balle ti-ti. Yana jin motar ta tsaya ya buɗe ya fito ƙamshin gidan ne yasa shi
murmushi, dan ƙanshim gidansu daban yake, ko'ina ya ke zai iya gane ƙanshin gidan
Mai-martaba.

Sai da ya shiga cikin gidan ya gaishe da mahaifansa, matan sarki sannan ya wuce
faɗar mai-martaba. Be same shi a faɗar ba, hakan ya tabbatar masa da yana can
turakarsa yana hutawa, tun da yaga motocinsa a waje balle yayi tunanin ko ya fita.
Ta faɗar ya bi ya shiga turakar Mai-Martaba, a falon farko ya same shi zaune yana
duba air conditioner da ake kan saka masa. Faɗawan na ganin Abdool duk suka faɗi
suna ɗiban gaisuwa, shi dai hannu kawai ya ɗaga musu dan baya son irin gaisuwar nan
da suke masa, ya fi gane a tsara masa ko a maƙe idan an ganshi. Da murmushi ya zube
gaban mahaifinsa yana ɗiban gaisuwa.
Kallonsa Mai-Martaba yake da mamakin zuwan ba zata ta, sai kuma ya kai mafeshin
Peacock dake hannunsa ya shafi ka ɗansa da shi. He didn't say a word dan baya son
magana da Abdool a gaban faɗawansa ko baboro, yafi son sai ya keɓance yadda zai
dake da shi kamar ba ɗansa ba.
Ko ba komai nuna tsantsar ƙaunar da kake wani daga cikin ƴaƴansa babban laifi ne
kuma ya kan haddasa ƙiyayah, sai dai hakan be hana familynsa depending ya fi son
Abdool da kowa ba, dan abu ne da ko ya ɓoye sai dai ya ɓoye mai yawan ka buɗe
kaɗan.

Yana unƙurawa zai miƙe tsaye sai faɗawansa suka zo da sauri suka tara rigunansu,
suna masa kirari har ya miƙe tsaye sannan suka rufa masa baya suna masa fita.
Hannu kawai ya ɗaga musu suka fahimci baya buƙatar su raka shi har can, sai
kawai suka juyo gurin Abdool suna masa nasa kirarin. Be tsaya jinsun ba ma balle ya
nuna masu jindaɗin abunda suke masa sai kawai ya bi bayan Mai-Martaba hannayensa
laƙƙame a baya yana tafi guda-guda kamar mai takewa President baya.
Sai da suka wuce falon biyu da na uku, suka wuce garden ɗin Mai-martaba sannan Mai
Martaba ya ƙarasa a wata ƴar ƙaramar rumfa mai kyau da ɗaukar hankali ya zauna, shi
kuma Abdool ya zauna ƙasa complain ɗin kiraren da suke masa.
Ɗan murmushi Mai-Martaba yayi irin na na manyan sarakuna, yana kallon ɗan nasa
cikin farinciki da jindaɗi.

“Wata rana kai Sarki Abdool, irin wannan kalaman be kamata yana fita daga bakin ka
ba”

“Haba Mai -Martaba ta ya zan zama sarki bayan Ina da yaya? Kuma ni wannan sarautar
sam ba burgeni take ba”

Mai-martaba ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora akan ɗayar yana murmushin ƙasaita.

“Har gobe Babana baka san Sarauta ba, saboda ka guje mu a lokacin daya kamata acr
ka zauna ka karanci komai na gidan nan, baka san jidaɗin sarauta ba, shiyasa kake
wannan furuci, na kan lura da yanayin ka sam baka sakin jiki a harkokin sarautar
gidan nan, balle na wani gurin, abu kake kamar ba ɗan sarki ba, ai yanzu kuɗi da
milki su ake ɗubi abawa mutum sarauta balle kuma kai da ka cancanta dan kana da
natsuwa da hankali ga tarbiya”

“Mai martaba wannan sarautar fa dai ku. Ina fatar na samu sarki cikin ƙoshin
lafiya”

“Yareema ya samu Mai Martaba cikin ƙoshin lafiya da walwala, ya aka yi ka yi mana
zuwan ba zata? Gashi ba ko wane abinci kake so ba balle na ce a ɗibo maka”

“Na samu hutu ne jiya, shiyasa na dawo gida as surprise kasan turawa sun ce
surprise is better than disappointed”

“Aiko kayi tsara kan gaɓa, daman akwai ɗaurin auren Abubakar Saturday, daman kai na
ke son ka walkice ni, kuma daman can Abubakar ɗin nan abokin ka ne”

Abdool ya shafa kai

“Wai har auren ya tashi ne ? Kwanaki wani friend na mu yake ce min an kai masa
kaya”

“Kai ma ai naka yana kusa, mun soma duba maka na dangi kamin mu fita waje, tun ka
bamu zaɓi”

Ko be tambaya ba yasan Ummi ce tayi wannan maganar, on behalf of him. Ɗan murmushi
yayi ya ce

“Ina za'ayi ɗaurin auren?”

“Zariya, ƴar sakin Zazzauce zai aura, Saturday nan”

“Okay zan je inshallah”

“Ba wai zaka je ɗin ba, ka tabbatar an ganka, zan haɗa tawagar da za kuje daga nan,
kuma zaka je ne cikin shigar sarauta, sadauki zai naɗa maka rawani idan kunje can”

Ƙure yayi ma Mai martaba da ido yana kallonsa. Mai martaba yasan waye ɗansa kuma ya
san kallon da yake masa.

“Kar ma ka soma, kai shikenan baka son shiga mutane? Ƴaƴan saraku irinka amman baka
son shiga cikin su? Rabon ka da rawani tun a hawan salla, ni wannan rayuwar ta ka
bata min Yareema, wasu ma basu kao darajarka ba basu kai muƙamin ka ba, sannan
sarautar ta su ƙarama ce amman su yi ta tinƙaho suna nuna isa balle ka!”

Yayi tsuntsun da kai, yana murmushi, dan yasan Mai Martaba ya kamo tasharsa.

“Ai ban ce komai ba Mai martaba”

“Na san zaka ce ɗin ne. Tashi ga ruwa can ɗauko ka sha, kar kaje ka ce wa uwarka
baka ci komai gidan Mai Martaba ba”

Ya tashi yana murmushi ya nufi wani ɓangare na gurin da aka jera freezer biyar a
gurin dan shan ruwa kawai da lemu.

Be bar gidan ba sai da Mai- Martaba yasa aka daba masa wani abu ya ci. Bayan yayi
la'asar, yayi ma Mai Martaba sallama sannan ya nufo gida gurin Umminsa.
Gaisuwar ban girma da tadabi sojojin gida suka masa suna masa maraba da zuwa.
Har zai wuce part ɗinsa sai kuma yaji ba zai iya ba har sai ya saka mahaifiyarsa
a ido. Da far'ah da zumuɗi ya nufi part ɗinta.

Tun daga yanayin yadda yaga falon zuciyarsa ta raya masa Ummi bata cikin gidan.
Sai ya ɗauki remote ya kashe plasma ɗake falon sannan ya nufi ɗakin Ummi dan
tabbatarwa. Haleema ya gani kwance saman gado Amira kuma na gurin tufafinta tana
gyarawa.

“What nonsense is this?”

Ya faɗa a tsawaci. Daga Haleema har Amira zuyowa suka yi suka kalleshi dan babu
wanda yasan da shigowarsa. Da sauri Amira ta zube ƙasa tana miƙa masa gaisuwa
zuciya na bugawa da ƙarfi, haka kawai ta samu kanta tana mai tsantsar kunyarsa.

Be amsa gaisuwar ba sai kawai ya watsawa Haleema harara, ita kaɗai tasan abunda
Hararar tasa take nufi sai ta sauka saman gadon da sauri ta kama hannu Amira suka
fice.

Sai ya ƙofar ɗakin ya rufe da key, ya cire keys ɗin ya nufi part ɗinsa da shi. Yana
shiga ya cire tufafin jikinsa ya ɗaura tawul ya shiga Bathroom.

Ya ɗauki kusan mintuna arba'in a banɗakin yana cuɗa jikinsa kamar wanda zai canja
fatarsa. Bayan ya gama wanka ya ƙarasa gaban madubi yana ƙara gyara gemensa da
babu komai a gurin.

Sallamar da yaji ana ta dokawa ne yasa ya wanke fuskarsa ya fito. Ya nufo falonsa.
Amira ya samu tsaye a gurin hannunta riƙe da cup ɗayan hannun kuma riƙe da wasu
dinner set an rufe su da ɗayansu.
Tana kallonsa gabanta yayi mummunan faɗuwa, bodybuilding ɗinsa ne ya tashi
hankalinta, yadda aka tsara jikinsa da faffanɗan ƙirjinsa, ga fararen idon nan
kamar an watsa masa madara tabbas shine irin mijin da take so.

“How may i help you?”

Ya tambaya ganin yadda take kallonsa kamar bata san da shi a gurin ba. Sai da ta
gyara tsayuwarta gudun faɗuwa sannan ta miƙa masa duka abunda yake hannunsa.

“Coffee and fruits, tuwo ne aka yi kuma Haleema tace ba ka son tuwo, shine na haɗa
maka wannan”

“Thanks i'm not a coffee drinker”

Fruits ɗin kawai ya karɓa ya aje saman kujera ya bar mata coffee. Har ya juya sai
kuma ya juyo ya kalleta

“By the way bana son texts ɗin nan da kike tura min, ki daina please”

Kai ta ɗaga masa idonta na son cika da hawaye.

“Note”

“You may go”

“Thank you”

Jikin sanyi jiki ta juya ta fice, hawaye na bin fuskarta. A yadda ta fahimta kamar
bata burge Abdool kwata-kwata irin ɗan sakewar nan ma baya mata shi.

Haleema na gani hawayenta tasan ba lafiya ba, daman kuma tasan za'a rina indai
Abdool ne.

“Wani abun ya ce miki ne?”

“A'a kawai ina ganin kamar bana gabansa, kwata-kwata bana burgeshi”

“Daman ai shi namiji ba zai so ki lokaci ɗaya ba, komai a sannu yake zuwa, ni yanzu
abinda nake so ki yi ta yin abinda zai ja hankalinsa gareki, har shi da kansa ya
furta yana son ki, dan naji Ummi na maganar wai Mahaifinsa yayi masa mata”

Amira ta kalleta da sauri.

“Da gaske?”

“Wallahi amman kin ga idan shi da kansa ya ce ke yake so kin ga dole ki a ƙyale”

“Amman me kike ganin zai sa ya so ni?”

“Irin wannan ladabin da kike cigaba, kuma ki riƙa shige masa ki riƙa haɗa masa abu
ko da be buƙata ba, sannan idan da hali ki koma gidanku, saboda zama a gaban iyaye
yana da muhimmanci, sosai Ummi ma da kanta zata fi ganin darajarki idan kina zaune
a gidan ku”

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, har ga Allah ita kanta tana son komawa a gurin
iyayenta amman ba hali bata iyawa, bata san yadda zata yi ba.

“Zan yi ƙoƙarin yin hakan inshallah”

“Allah ya taimaka nima ina son ki auri Yaya Wallahi”

Amira tayi shiru yana cigaba da tunanin rayuwarta.

*ASIM POV.*

Tun ranar daya bar gidan Namra be sake leƙawa ba, duk jin yake ya tsane ta ma,
daman can baya akan cilas ne yake zaune da ita yanzu kuma yaji zai iya auren wata.
Sannan yana ganin haihuwa a yanzu zata iya kawo masa matsala, dan haka shi be
shirya haihuwa a yanzu ba.

Yau ma kamar kullum da tea da kwai yayi breakfast, sai da ys ci yayi nas sannan ya
tashi yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin wasu tufafin masu kyau da tsada ya
shiga sashen uwar ɗakinsa dan gaisheta.
Be same ta a falo ba, sai kawai ya wuce har ƙurƴar ɗakinta dan ta daɗe da bashi
damar hakan matuƙar ba mutanr ya tarar a gidan ba. Bedsheet ya tarar tana gyara
jikinta sanye da kayan bachi.

Yana ganinsa ta zauna saman gadon tana murnushi.

“Asim an tashi?”

“Eh Hajiya ina kwana?”

“Lafiya ƙalau Alhamdullah, ka yi kyau mashallah”

Ya ɗan sunkuyar da kai.

“Hajiya na ce ko akwai abunda za'ayi miki?”

“A'a gaskiya yanzu kam babu sai dai zuwa anjima. Amman karka manta fa na faɗa maka
za mu yi baƙo gobe zai zo daga garin ku, kuma dan kai kawai zai zo garin nan, ina
fatar zaka ba shi haɗin kai, yana gida a nan idan ya zo a gidansa zaka je, zan baka
maganin da zaka sha, kums ka tabbatar kana kallon videos dana tura maka ɗin dan
kasan yadda zaka sarrafashi”

“Karki da mu inshallah ba za'a samu matsala ba”

“To yayi kyau haka na ke so, sai kuma a samu wata ƴar sana'a a riƙe gudun zargin
mutane, ina ganin ma nan gaba kadan garin ku zai maida kai dan can yake”

“Nima ai zan fi jindaɗi dan akwai waɗanda na ke son su san nayi kuɗi dan sai na
rama wulaƙancin da duk aka min”

“Allah dai ya taimaka, idan ka saki jiki ina faɗ Maka nan gaba kaɗan sai an saka ka
a cikin matasan da suka fi kowa kuɗi a nigeria”

Wani kalar daɗi ne yaji marar misaltuwa. Kaɗan ya labarta mata irin gwargwarmayar
da yayi da iyayen Namra sannan ya taso ya fito yana auna kansa a mizanin arziki.

Falonta ya dawo ya zauna, yana duba shafin facebook da sabuwar wayarsa. Yau ma ya
tararda friend requests kamar wacan lokacin. Da kuma da kuma saƙon wata kyakkyawar
yarinya ta tura masa dan katun ɗin nan na facebook mai cewa mutane Hi.

Reply yayi mata.

_“Hey How you darling”_

Sannan ya shiga profile ɗinta yana duba hotunanta.

“Wow wannan kan ba dai fari ba da kyau, irin wannan idan ka samu irinta ai ka huta”

Nan da nan yayi saving hotunanta, sai ya dawo inda taƴi masa reply yana ƙara amsa
mata.

_i'm fine. By the way am Nabila Lawal Alƙali aka Pretty Nably. from Katsina living
in Abuja_

_Nice to meet you dear, i'm Asim Ibrahim Sanusi aka Asim From Sokoto living in
Katsina_

Bayan kamar minti ɗaya sai ta sake aiko masa wani.


_Wow which area in Katsina? I know Katsina in and out_

_Nasarawa road. Send me your number let's chat on whatsapp_

Cikin ƴan mintuna ta turo masa number. Sai da yayi saving sannan ya sauka daga kan
facebook ɗin ya tashi ta fito ransa fari fes.
Motar daya saba shiga ya shiga, wacce ta zame masa kamar tasa.
Tun da ya doshi hanyar Nasarawa rayuwarsa ta soma baci, sai faman jan tsaki yake
yana nasalta yadda zai tararda Namra.

“That's why i hate baƙar mace, da sun kwana biyu zaka ga sun lalace babu ko kyau
kallo, ji jikinta dan Allah duk ta bi ta zube sai ƙassa me zaka kallo a jikinta ma
ka yi sha'awa, mtsssss”

Be ji zai shiga da motar cikin gida ɗan haka ya faka ta a ƙofar gidan ya shiga yana
wani yatsinar fuska, kamar bada aka yi rayuwa a gidan ba.

Zaune ya hango ta tana ta faman wanki tufafinta. Tana jin sawon tafiyarsa amman ta
ƙi ta ɗaga kai ta kalleshi dan be yi sallama ba, kuma tasan abunda ya kawo shi a
gidan be wuce abunda take zargi ba.
Zaunawa kawai yayi kusa da ita yana mata wani kallo kamar ba matarsa ba.

‘Ai dole na yi aure a ina zaka nuna wannan ka ce matar ka ce? Abu busasai haka’

Furucin da yayi a zuciyarsa kenan, a fili kuma sai ya ce.

“Sannu da aiki”

“Yauwa”

Ta amsa ba tare data kalleshi.

“Kin koma asibitin ne?”

“Bana da kuɗin hoto”

“To ma ba wannan ba, wace shawara kika yanke ne?”

Kallonsa tayi sai hawayen dake maƙale a idonta suka zubo

“Yanzu abunda kake min ka min adalci kenan? Shikenan kai babu ruwanka da danuwata
kullum ni kaɗai nake kwana a cikin gidan nan idan ma wani zai shigo yayi min fyaɗe
ko ya kashe ni sai dai ya zo? Asim miyasa kake min haka ne? Ka mayarda ni kamar
karya marar amfani”

Hannu ya kai yana shafa ta, dan har ga Allah yayi missing ɗin jikinta.

“Ba haka bane Namra, sai da muka xauna da ke muka yi magana kan aikin nan kika ce
kin yarda sai kuma yanzu ki fara complain ko dai ki shi kike ne?”

“Kishin me?”

“Kin ga zan yi kuɗi mana”

Ya faɗa da ƴar dariya, ita kuma sai tayi masa wani kallo.

“Ka min ka yi kuɗi Asim, dubun ka sun yi, wasu sun mutu sun bar kuɗin, wasu kuma
kuɗin sun guɗu sun bar su. Kamin ka sanya rigar dubu goma, sai da nasa ɗan kunnen
biliyan biyu da rabi na zinari, dan haka kuɗin da zaka yi basa burge ni balle na yi
ƙyashinka”

Wata dariyar rainin wayo yayi.

“Amman ai kyau abu akan gashi a ƙasa, da muka yi aure mi Babanki ya kawo mana?”

“Me zai kawo maka, bayan yasan ka auri ƴarsa saboda abun hannunsa ne? Ai shi ba
lurasari ba ne, irin Mama mai nuna sun abun duniyarta a fili”

Ya nunata da yatsa.

“Karki sake uwata a maganar ki wallahi”

“Nima karka sake saka ubana, dan cin mutunci ba gado bane kowa ya iya”

“Dube ki dan Allah ni in ban da kaɗɗara ma mi zan yi da irin ki?”

“Lallai kam kaɗɗara ce Asim da nima babu abunda zan yi da irin ka, dacan baka san
da haka ba, sai yanzu? Dan kana jin nera ta fara keta wuyanka? Ko da yake hausawa
sun ce ɗan talaka be iya samun guri ba”

Tasssss ya wanke mata fuska da mari. Ita kuma ta ɗauki bokitin da take wanki da shi
ta juye masa ruwan wanki ta jeɗa masa bokinta. Zuciyarta ta kawo sosai ita kanta a
yanzu ta san ba kuka take da buƙata ba, dan ta fahimcin idai har ta ƙyale Asim zai
iya hallakata.

“Karka sake kuskuren taɓa min jiki dan ni ba baiwa ba ce kuma ba jaka ta siyo ba”

“Ni kika jiƙe da wannan ruwan? Wallahi sai kin raina kan ki dan sai jikinki ya gaya
miki, ba ke fa wallahi yanzu ko ubanki nafi ƙarfinsa balle ke, banza a banza, kuma
wallahi kije a zubar da cikin nan ko yanzu ki yi gidan ubanki wallahi, dole ki
zaɓa”

“Wallahi ba zan zubar ba. Sai dai ka sake ni amman ba zan zubar da wannan cikin ba”

“Haka kika ce?”

“Haka nace kuma haka na zaɓa”

“To kije gidan ku na sakeki sa..ki ...ɗaya.... Idan kin zubar ki dawo zan maiyar da
ke”

Kamar an sako duwatsu haka Namra taji saukar furucin Asim da bata tsammaci zai mata
shi da gaske ba. Zubewa ta yi ƙasan guiwowinta tana masa kallon mafarki.

“Da gaske Asim ka sake ni?”

“Na sake ki mana, ba kin zaɓi abunda be isa aka masa numfashi ba balle ma har ya zo
duniya ba, sama da ni”

Kai ta ɗaga masa wasu hawaye masu zafi suna bin kumatunta tace

“Na zaɓe shi sama kai, kamar yadda na zaɓe ka sama da iyaye na acan baya, na zaɓi
ka sama da karatu na, na zaɓe ka sama da jindaɗi da arzikin da yake gidan mu, na
zaɓe ka sama da samarin da suka yi so na, na biyo ka garin da ban san kowa ba
sabida kai. Amman yau ni ka yi watsawa ƙasa a ido, lallai kai butulu ne Asim, ka
tabbata ɗan bushiya. Duniya ce Asim wanda be zo ba ma ta shiriya masa balle wanda
yake cikinta, ka taka a sannu dan duniya ƴar ɗauka da ajewa ce...”

Tsaki kawai yaja ya ɗauki keys motarsa da suke gurin ya juya ya fice cikin fushi.
Da kallo Namra ta bishi wani irin abu ya soma zillo yana neman numfashinta.

*Best regards 🌺*
*Khadeeja Candy ♥*
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: Akwai inda na yi mistake jiya nasa ɗan kunnen
biliyan biyu da rabi, miliyan biyu da rabi na ke nufi typing errors ne kuma ban yi
editing ba.

*61*

NAMRA POV

Kwance tayi a gurin tana ɗaukar numfashi, sai lumshe ido take tana buɗewa, abu ya
zo ya tsaya mata a zuciya kamar ƙashi kamar dutse.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Allahumma ajirna fi musibati wa'kalif ni


khairan min ha”

Shine abunda take ta maimatawa tana yaƙi da zuciyarta, tana ji tana gani
idonnuwanta suka fara nuna mata ba haka, sai dinshi-dishi take gani, kalmar sakin
da Asim ya furta mata ne yake ta mata yawo a ƙwaƙwalwa. She just can't believe Asim
ya sake ta, ina zata je? Minene a fita a gareta yanzu bata sani ba.

Hango kanta take a cikin gidansu Abbah yana korarsu ita da Anty. A ɗayan ɓangaren
tana tunanin abubuwan da mutane zasu faɗa idan har aka ji aurenta ya mutu, duk
wanda be son aurenta da Asim zai mata dariya idan ya ji aurensu ya mutu. Duka
yaushe aka yi auren da har za'ace auren ya mutu, gashi duk ta lalace ta koma wata
iri? Ciwon da yake jikinta za a ce sai da ta kwashi ciki da ciwon mahaifa sannan ta
dawo gida.

“Azzalumi ma cuci Allah ya isa tsakani na da kai, Allah ya bi min haƙƙina”

Daga kwance da take tayi furucin tana kuka mai taɓa zuciya. Bata san inda zata je,
tun da taƙi ta bi Anty Amarya tun da farko, yanzu kuma tace mata me?
Haka ta kwanta a gurin jikinta ya ɗige gaba ɗaya, kamar an zuba kayan wanki.

Sai ta taji an kira sallah azahar sannan ta samu kuzarin unƙurawa ta miƙe tsaye.
Har taje tayi wanka tayi alwala abu ɗaya ne yake mata yawo.
Idan har Asim ya dawo ya tararda ita a gidan zai zaci ko dan tana son ya mayar da
ita ne. Ita kuma yanzu ta yanke ƙauna da shi, idan akwai wanda ta tsana a duniya
Asim ne, kuma har gobe bata nadamar zaɓar abunda yake cikinta saman da Asim.
Bayan ta yi sallah azahar ta ɗora da nafili sannan ta rokowa Allah buƙatarta, ta
kai masa kukanta ta miƙa masa lamurranta.
Jingina ta yi da ginin gurin tana kuka, da hawaye masu zafi. Irin mutanen da
suka yi nemanta aure take tuna amman kowa ya zo tace sai Asim, ayau Asim ɗin ne ya
zaɓi rabuwa da ita saboda cikin shi, jininshi.

Tashi tayi ta koma saman katifa ta kwanta, tana kukan zuci wanda ya fili illa da
baƙinciki. Wayarta tayi ƙarar saƙo duk da taji daɗin kwanciyar hakan be hanata
unƙurawa ta ɗauƙi wayar ta duba ba.

_Karki kuskura cewa za ki siyar da gidan nan, amman na miki lamani ki zauna har ki
canja shawara, idan kin yi tunani mai kyau na shirya maida ki a matsayin mata ta!_
“Kaico...”

Shine kawai abunda ta furta bayan ta gama karanta text ɗin ta share hawayenta.
Kanta ta ɗaga sama tana kallon ɗakin, kwata-kwata jin tayi gidan ya fita a ranta.
Sai dai kuma bata da gurin zuwa, duk inda zata je be yi kamar gidan mahaifinta ba,
da ace Abbah ba xai wuƙantata ba, da ba zata damu da maganar mutane ba matuƙar tana
gidansu, a ƙarƙashin iyayenta.

Hijabinta ta ɗauka ta saka, ta ɗauki jakarta da wasu ƙaƙanan abubuwa nata ta saka a
jakar sannan ta fito, tun da ta baya bq ɗin baya ta sake kallon ta ba har ta fice
daga gidan.
Fuskarta ta kumbura sosai haka ma idanunta, duk wanda ya ganta zai san tayi kuka,
hakan yasa ta sanda kai ƙasa har ta isa titi. Napep ta tara sai da ta shiga sannan
ta soma tunanin inda zai kai ta. Bata da wadataccen kuɗin da zata kama wani gidan
ta zauna, kuma ta san ba mutuncin ta ba ne ta kama gida a wani gurin. Kuma bata jin
zama a gidan dan zata iya aikata komai saboda baƙinciki.

“Hajiya ina za a kai ki?”

Tsayawa tayi tunani, har tashi Napep ɗin.

“Kai ni tashar mota, inda ake hawa motar sokoto”

“To amman yanzu tashar gov sun tashi sai dai babbar tasha”

Ya hau kan titi yana ƙara ƙure volume ɗin napep ɗin dake tashin wakar Umar m
shariff. Ita dai saurare kawai take tana hawaye har suka isa, ɗari biyu ta ciro ta
bashi ya miƙa mata canjin naira hansi sannan ta fita shi kuma ya juya.

“Sokoto, Kano, Kaduna, Abuja, jigawa, Kebbi, Zamfara”

Haka ƴan union ɗin suke ta faɗi suna neman passengers. Wasu suka yo kan Namra da
gudu suna tambayar ta inda zata ta, tsaye kawai tayi tana tunanin inda zata ce duk
da ta zo da niyar zuwa sokoto ne sai kuma ta ji ba zata iya, har tana jin ma kamar
ta koma gida...

“Hajiya Kaduna zaki je?”

Wani daga cikin su ya tambaya, sai ta ɗaga masa kai.

“Eh Kaduna zan je”

“Ga mota can daman mutum biyu ake jira, ina kayan ki suke?”

“Bana da kaya”

“Okay muje ga mota can”

Shine yayi mata ja gaba har gurin motar, sannan ya faɗa mata kuɗin motar. Cikin
rashin kuzari ta cire ta biya, sannan ta shiga motar tana ta doubting akan taje can
ɗin ko kuma a'a. Idan taje kaduna gurin wa zata je? Tun da bata taɓa zuwa ba duk da
akwai taubashiyar Anty Amarya a can amman bata tunanin zata gane inda take tun da
zuwan da duka yi tun da daɗewa ne kuma da motar gida, sunan unguwar ma bata riƙe
sosai ba.

ASIM POV

A sale ya fito daga gidan, bama abunda ya fi baƙanta masa rai kamar jiƙa masa
tufafi da Namra tayi, Yana ƙoƙari buɗe motarsa ya hango Mardiya tafe, ɗan tsayawa
yayi yana kallon takunta, cikin yanga izza take tafiyar dan kuma kawai ta ɗauki
hankalinsa ne. Shi kam yasakar mata ido sosai yana kallonta duk da jiƙaƙin tufafin
ne a jikinsa, amman hakan be hana shi tsayawa gurun motar ba har ta iso, dan kawai
ta ga shine yake tuƙa motar, yasan ko ba komai zai burge ta tun da yasan mata sun
fi son mai mota.

Sai da ta kusa ƙarasowa sannan ya buɗe motar ya ciro ƙyale yana goge jikinsa.

“Asim ina kwana?”

Ta gaishe shi cikin kashe murya da ƙarawa muryar zaƙi. Da sauri ya kalleta yana
murmushi kamar ba shine ya fito rai a ɓace ba.

“Ah lafiya ƙalau Mardiya ya gidan?”

“Gida ƙalau wallahi miya jiƙa mata kaya haka?”

“To sha'anin ne kin san halin na ku sai a hankali. Gari za a ne?”

“Eh wallahi zan ɗan shiga gra ne”

“Okay shige na aje ki”

“Mashallah ka siye sabon mota ne?”

Ta faɗa tana kallon motar cike da burgewa.

“Eh ai tama kwana biyu, sabuwa dai muke jira”

Buɗewa tayi ta shiga, sai shima ya shiga yana ƙoƙarin tashin motar ta kalli gate
ɗin gidansa ta ce

“Kar fa Namra ta hango mu ko a kai mata rahoto”

“Mtsssss amman Mardiya ma kin mai yarda ni wani wawa, ni kam ai nafi ƙarfin matata
ba irin mazan nan bane na banza, ashe ke matsoraciyace ba zaki iya kishi da ita ba”

“Ai kishi dabam, da ace yanzu aurna na ne zaka yi to bana shakar taji komai, amman
kaga yanzu babu wata magana ta aure dole na ji tsoron irin maganar da zata je mata
a kunne”

“To kisa a ranki auren ki zan yi”

Ya faɗa yana ƴar dariya. Itama dariyar tayi mai cike da jindaɗi. Har ya kai ta inda
zata je fira suke kamar masu masoya ita kuma sai wani lanƙwashewa take tana
karairaya. Daman shi tuni da kasheshi da kalamanta ma.
Daga gra ya wuce gidan Hajiya Sadiya, be same ta a gidan ba hakan ya tabbatar
masa da akwai inda taje kenan. Ɗakinsa ya shiga ya canja tufafin jikinsa ya saka
waƴan can a washing machine sannan ya dawo ya zauna. Yarinyar ɗazu ce ta faɗo masa
a rai a ƙoƙarinsa na kawarda tunanin Namra a ransa dan ganin yake ita babbar
maƙiyiyarsa ce, ko kaɗan baya nadamar sakinta da yayi kuma he's ever ready ya mai
data idan ta yarda ta zubar da cikin.
Number yarinya ya nemo ya danna mata kira, ringing biyu ta ɗauka ciki muryarta mai
sanyi. Cikin turanci ta soma watsa masa tambayar wake kiran shima ya maida mata da
yaren da tafi ganewa. Nan da nan ta sake da shi suka gaisa duk kalmar da tayi masa
sai ya maida mata, ya ɗan tambaye kaɗan daga rayuwarta, sai da amsa masa a inda
abunda take tunanin ya sani. Ya jidaɗin da tace masa ita ƴar Katsina ce, daman ta
faɗa masa tun a chat amman a yanzu ne take faɗa masa sunan unguwarsu a Katsina.

Sun daɗe suna waya sannan yayi mata sallama ya kashe wayar. Ko da ya kalli ogagon
ɗakinsa ƙarfe biyu saura ya gani, sai ya tashi yaje yayi alwalah yayi salla a cikin
gida. Bayan ya sallame zancen gidan ya faɗo masa rai, wai kar dai Namra tace zata
sai da gidan ta gudu da kuɗin. Wayarsa ya ɗauka ya aika mata text sannan ya kunna
data shi.

HILAL POV

Yana cikin aiki wayarsa tayi ringing. Sai dai be duba mai kiransa ba har sai da ya
kai ƙarshen duba marasa lafiyar da yake.
Sai da ya gama da duka katinan da suke gabansa, sannan ya tashi ya nufi office
ɗinsa yana duba wayar. Number Dady ya gani Abbah Rashida, yayi mamakin ganin kiran,
sai dai be kawo komai a ransa ba dan a tunaninsa, akan maganar shiga kotu ne zai sa
ya kira shi tun da monday nan mai zuwa za a shiga.

Sai dai ganin text ɗinsa ya sa gabansa faɗuwa, miyasa yake son ya zo gidansa ya
gansa? Duk akan maganar ne ko kuma wani abun daban. Ba tare da shakar komai ba ya
shiga office ɗinsa ya cire ƴar samansa ya ɗauki keys ɗinsa ya fice.
Cikin ƴan mintuna ya isa gidan su Rashiida yayi gudu ne a hanya sosai, dan baya
son Rafiq ya farka baya kusa. Yana ganin Motar Rashida da ta Dadynta yasan tana
cikin gidan.

Be fita cikin motarsa ba har sai da ya kira Dady yace masa gashi ya iso.

“Ka shigo ciki”

Shine reply ɗin da ya masa a wayar cikin tsawa, ko kaɗan Hilal be ɗauki haka a wani
abuba dan har gobe yana girmama iyayen Rashida tun da akwai ƴaƴa a tsakaninsu,
kuma duk mutumen daya aura maka ƴarsa ya fi gaban ka raina shi ko da kuwa kun rabu
da ƴar ne.
Buɗe motar yayi ya fito, yana tuna when last ya shigo gidan nan. Babban falon
Dady ya nufa daman ko lokacin da yana surukinsu a can Rashida take sauke shi idan
sun zo gidan.

Yana shiga ya samu Dady zaune yana jiran ƙarasowarsa. Momy ma tana zaune daga gefe
tana watsa masa harara. Cikin ladabi ya ƙarasa ya zauna saman kujera yana gaishe
shi. Dady be amsa ba dan ba gaisuwar ce a gabansa sai kawai ya hau shi da kalamai
masu zafi.

“Ma cuce mayaudari, yanzu da kaga ka laƙa mata ciwo shine ka sake ta ko? Ai ni
daman nasan sakin da ka yi mata bana Allah ba ne, kaje can kayi yawon ka ka samu
cuta kaxo ka laƙa mata”

Ɗaga kai yayi yana kallon Dady maganar ta xo masa a baibai kuma da halshe biyu.
Radhida ce ta faɗa musu ko kuma su suka gano haka? Har da shi tace yana ɗauke da
cutar ko kuma ita kaɗai?

“Dady zan so Rashida tana nan kamin na yi magana”

“Ta zo ka kunsa mata baƙinciki ko? Ka zo ka ƙaryata ta ka ƙara mata baƙinciki ko?
Ɗan iska marar mutumci, wallahi Allah sai ya isar mata”

Wannan karon Momy ce take magana tana wani ɗagowa kamar ta kama Hilal ta dake shi.

“Kuna magana ne a jahilce baku san gaskiyar lamari ba, ya kamata a kira Rashida ayi
komai gani ga ta sai a fitar da wanda be da gaskiya”
Dady ya kalli Momy.

“Jeki ki kirata. Wallahi na rantse maka Hilal sai duk abunda na tara ya ƙare amman
tun da kayi ma ƴata haka sai na wulaƙanta ka”

Ya ƙarasa yana kallon Hilal, jijiyar kansa har wani tashi take irin na ɓacin rai
ɗin nan ya kai maƙura.
Momy ta tashi a hasale ta nufi sashenta. Kai tsaye ɗakin Rashida ta nufa sai da
ta soma da buga mata ƙofa amman ta ƙi ta Buɗe har yanzu, sai kawai Momy ta zauna a
gurin ta soma mata kuka.

RASHIDA POV

Babu yadda Momy batayi amman Rashida ta ƙi ta buɗe ƙofar har duka ƙanenta suka dawo
daga makaranta.
Sai da aka yu salla la'asar sannan ta buɗe shima dan Momy ta zo ta zauna a gurin
tana kuka ne. Da sauri Momy ta shiga cikin ɗakin cike da tausayin ƴarta.
Bata yarda ta zauna kusa da ita ba, sai dai space ɗin dake tsakaninsu ba wani mai
tsawo bane sosai.

“Hilal ne ko? Shine ya saka min wannan cutar shiyasa ya zaɓi rabuwa da ke”

“Miye amfanin sanin wanda ya sa min wannan cutar, bayan cutar ta riga da ta kamani,
babu amfanin ayi ta jayayar abu har a tona asirinsa, duk abunda ya faru da ni, Dady
ne ya ja min”

Momy ta kalleta

“Ga Hilal can mum kira a falon Dady ki amman ya ce ba zai yi magana ba sai kina
nan”

Gabanta yayi dakan huɗu-huɗu har bata san lokacin data kalli Momy baki sake ba.

“Miyasa kuka kira shi? Me zai muku?”

“Shine silar wannan ciwon na ki Rashida dole na zauna da ke, dan me zai sake ki”

Fashewa tayi da sabon kuka.

“Ni bana son ganinsa dan Allah yayi tafiyarsa”

“Ba zai je ko'ina ba har sai an tabbatar da wannan maganar yau”

Momy ta riƙa hannunta suka fito tare. Ba dan Rashida ɗin ta so ba, sai jan Momy
dake janye da hannunta har suka isa falon. A jikin ƙofar Rashida ta tsaya ta risina
kanta na ƙasa dan bata son kallon Hilal.
Shi kuma ya tsare ta da ido tausayinta duk ya kama shi.

“Dawo nan ki zauna, babu abunda ya isa yayi miki”

Cewar Dady yana nuna mata kusa da shi. Tasowa tayi ta dawo nan tana shirin zama
kukan da take ɓoyewa ya fito fili.

“Yi shiru yanzu ba lokacin kuka ba ne, faɗi maganar ki”

Kasa magana Rashida tayi har sai da Hilal ɗin da kansa ya soma bada labarin abunda
ya faru from a to z. Sun gamsu sun kuma samu tabbaci ganin yadda Rashida take ta
kuka ta kasa ta kare kanta.
Dady ne ya miƙe tsaye ya soma safa da marwa. Ajiyar xuciya kawai yake saukewa yana
maimaita

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Momy kan saka kanta yai cikin hijabi tana kuka. Rashida ma kukan take kamar ta
mutu. Dady ya kalli Hilal cikin idonsa na marasa kunyar iyaye ya ce

“Zaka iya tafiya”

“Na gode”

Hilal ya furta sannan ya miƙe tsaye ya fice, jiki a sanyaye.

“Kin cuci kan ki Rashida kin kuma watsar da tarbiyar dana baki yanzu ai kin ci
ribar zina sai kije ki auri wanda kuke aikata saɓon tare, uban waye ne ma wannan
mutumen?”

Dady ya tambaya a tsawace. A nan Momy ta ɗago kai ta kalleshi cikin ɓacin rai ta
ce.

“Duk waya ja mata wannan abun ba kai ba? Tana zamanta lafiya ƙalau da mijinta kace
dole sai ta yi aiki, babu irin lallaɓar da yarinyar da mijinta ba su maka ba, amman
ka dage akan dole sai tayi aiki, ai ga ribar aikin nan ta kwaso ta kawo maka, shine
yanzu zaka taso ka rufe ta masifa ka barta ta ji da abunda yake cikinta ko so kake
ta kashe kan ta”

Tashi Rashida tayi ta bar musu falon tana wani irin kuka kamar ta mutu. Momy ma
miƙewa tayi tsaye ta fice a hasale tana kuka da bata san ranar tsayawar haweyen ba.

Komawa Dady yayi ya zauna har yanzu xuciyarsa bata gama gamsuwa Rashida ƴarsa tana
ɗauke da cutar ba, shi dai ya fi son ayi wani gwajin.
Ajiyar zuciya ya sauke, wani yana tuna wani kalami da wata tayi masa a 1952.

KALSOOM POV

Har yanzu hankalinta ba a kwance yake ba, amman ba kamar da ba, dan yanzu tana da
tabbacin Hilal ya yarda da ita, ta kan samu sassaucin hakan idan ta tuna.
Sai dai har yanzu bata cin abincin kirki, sai dai abu mai ruwa ko kuma ruwan
kawai.

Tana cikin kitchen ta ji ƙarar tsayawar motarsa, nan da nan ta je aikin da take ta
nufi ƙofar falo ta tarboshi.
Yanayinsa ya kararta da ita damuwar mijinta, dan haka bataa buƙatar tambayarsa
akwai damuwa ko babu mafi ala kawai ta kwantar masa da hankali sannan ta nemi sanin
dalilin damuwar tasa.

Da kanta ta zaunar da mijinta ta ɗauko ruwan sanyi ta siyaya masa a kofi ta kai
masa a baki, kaɗan ya sha, ya ɗauke baki, sai ta cire ɗankwalinta ta soma shafe
masa gefen fuska.

Hannunta ya riƙe ya jata zuwa ƙirjinsa ya rumgume ta, zuciyarsa cike da tsantsar
ƙaunarta.

“Hajiya ta har yanzu bata yarda da ke ba”

Ya faɗa dan ya canja tunaninta izuwa wacan damuwar ta gurin Hajiya.


“Ba lallai ne tayi saurin yarda da ni ba, kuma tana da damar ta zarge ni yadda
ranta yake so, zan ɗauki ko wani irin hukumci Hajiya ta yanke matuƙar hakan xai sa
ta aminta da ni”

Tana kwance a ƙirjinsa take maganar hawaye na bin fuskarta.

“Hukuncinta ɗaya ne, wai sai na ƙara aure”

Ɗagowa tayi ta kalleshi ta girgiza kai ta fashe da kuka. Ɗan murmushi yayi dan
kukanta ya sashi nishaɗi, yana shafa gefen fuskarta ya ce

“Ba zaki yarda mijin ki ya ƙara wata ba ko?”

Kai ta ɗaga masa. Sai ya ce

“To ya zaki yi da Hajiya?”

“Wallahi ban aikata ba Hilal Allah shine shaida na”

“Ai ba nine ban yarda ba, Hajiya ce bata yarda dake ba”

“To a tambaye Rafiq ɗin ai yana magana idan na bashi wani abun zai faɗa”

“Rafiq baya magana yanzu, ya koma wani iri kamar ba shi ba”

Cikin rashin jindaɗi yayi magana, yana ciro wayarsa dake aljihu tana ringing.
Saurin picking yayi ganin number Nurse ɗin dake kula da Rafiq.

“Subhanallah okay gani nan zuwa”

Yayi saurin ɗaga Rashida daga jikinsa, ya tashi ya nufi ƙofa hankali tashe. Rashida
sai tambayar lafiya take be kula ta ba.

ABDOOL POV.

Sai da dare ya dawo Part ɗin Ummi ɗan ya tabbatar ta dawo a lokacin. Duka falo ya
same su zaune suna ta fira. Ummi na ganinsa ta aje lemun fata dake hannunta tana
masa kallon mamaki.

“Ni nace fa naga Motar ka Haleema tace min wai ba kai ba ne”

Ya ɗan wara ido yana kallon Haleema, kamin ya zauna a kujarar da Amira take zaune
dan three seater ce.

“Ai ba zata faɗa ba, a ɗakin ki na same su suna ta miki taɓe taɓe ita da wannan
yarinya”

Ya nuna Amira data tsare shi da ido.

“Wallahi gyara ne Amira take miki, ba wai komai muke miki ba, hba sai ka ce yara”

Ummi bata bi ta kan Haleema ba ta kalli Abdool.

“Ya hanya? Ka ci abinci?”

“Na ci gidan Babana, ku da ban ma tarar da ku ba”

“To ai baka faɗa ka ce za ka zo ba, gashi ma miyar kifi aka yi kuma baka son kifi”
“Ni wallahi wannan zuwan ma be min daɗi ba, ɗan hutu ne na samu ina da zumuɗi zan
zo gida shine wai kuma Mai Martaba sai naje zaria ɗaurin aure”

“Ai shine dai-dai kai kenan baka son shiga mutane kamar wani aljani. Me za'a girka
maka?”

“Wa zai girka min?”

“Ni”

“Okay to a min wani abu new. Ba wanda aka saba ba”

Tashi Ummi tayi ta nufi ɗakinta tana dariya.

“Kai kam matarka ta shiga uku kullum.ba maimata abinci sai anyi wani abu new”

Shima.dariyar yayi ya tashi ya rufa mata baya yana faɗin

“Lallai kam, idan kam mace bata iya abincin ba zamu samu matsala da ita”

“Ko da kana son ta?”

“Aifa...”

Amira ta bishi da ido, daɗi har cikin rai. Dan tasan indai ɓangaren abincine ba
daga baya ba, tun daga kan waɗanda ake yayi har na gargajiya gwargwado ta iya. Ga
kuma xama da yayi a kujerar da take zaune abun yayi mata daɗi.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *62*

*1952*

```Cikin rawar jiki ta shigo gidan sai rabon ido take idonta tab da ƙwalla, kana
ganinta kasan tana cikin halin damuwa. Bata san inda zata dosa ba tun ba data samu
masu gadin suka barta ta shigo cikin gidan, gaba ɗaya a rikice take har bata iya
kwantar da hankalinta ta banbanta parts ɗin

“Ke me kike a nan?”

Da sauri ta juyo ta kalle tana ganinsa sak tasan ɗan mai gidan ne, hakan yasa ta
risina har ƙasa ta gaisheshi muryarta na rawa. A maimakon ya amsa mata sai kawai ya
ƙara haɗe fuska dan ya fahimci irin mutanen ne masu zuwa gurin mahaifinsa a taimaka
musu

“Gurin Mai gidan nan na zo, taimako za a min, mahaufiyarmu ce bata da lafiya shine
aka rubuto mata magani a asibiti kuma sun ce za a mata aiki, shine aka ce na zo nan
za a taimaka mana”

Da kuka ta ƙarasa maganar tana nuna masa takardun asibiti dake hannunta. Karɓar
takadardun yayi yana kallon fuskarta da kuma yanayinta, taga komai a rubuce amman
saboda mugun nufinsa ya kasa gasgata ta.

“Wata ƙila ma ƙarya kike, haka kuke dan kawai kun ga mahaifina yana taimakawa
mutane, kowa sai ya kwaso ƙaryarsa ya kawo ”

“Wallahi ba ƙarya na ke ba, idan baka yarda da ni ba zamu iya zuwa ka duba ta tana
nan babbar asibibiti, layin masu ciwon ulcer”

Kallonta yake da kyau, irin kallon da idonsa zata siffanta masa sigar jikinta,
yarinya sai dai ba sosai ba, fara ce kyakkyawa mai ruwan fulani, ko kuma na ce
buzayen jajaye. Hawunta ya haɗe a bakinsa kana ya ce

“Nawa ne ake buƙata?”

“Dubu ɗari biyu da sittin”

“Tam yanzu kin ga mahaifina baya nan, ya za'ayi”

“Ina zan same shi?”

“Baya nan ta tafi Lagos ganin shugaban ƙasa” (A lokacin Lagos ce fct ba Abuja ba)

“Yaushe zai dawo?”

“Wallahi ban sani ba, amman idan kina so ni zan iya taimaka miki”

“Ina so dan Allah”

“Amman fa sai idan nima za ki taimaka min”

Kallon rashin fahimta tayi masa dan a iya ganinta da tunaninta baya buƙatar wani
taimako daga gareta.

“Me zan taimaka maka?”

“Idan har kina son na baki kuɗi to ki iskoni a ɗayan gidan baban mu da yake nan
kwalkwaɗa, zan ninka miki fiye da abunda kike so ba”

Sak tasan abunda yake nufi, kuma ta fahimci inda kalamansa suka dosa, ita kuma bata
koyi wannan tarbiyar ba, kuma bata ji zata iya sadaukarda mutuncinta ba. Sai kawai
ta kaɗe jikinta ta tashi tsaye.

“Ni ba ƴar iska ba ce, dan kawai na zo neman abu gurin mahaifiya ba shi yake nuna
ni ƴar iska bace, rashi mahaifi ne, kuma duka dangi babu mai shi, idan har zaka
taimaka min dan Allah ka taimaka min”

“Daman ƙarya kike ciwon mahaufiyarki be da me ki, da kin aikata komai akan ta. Wuce
ki ba mu guri”

Da kuka yarinyar ta bar gidan. Shi kuma ya juya ya shiga ƴar marsandin mahaifinsa
ya fita daga gidan. Kai tsaye ɗayan gidan mahaifinsa ya nufa, dake can bayan babban
gidansu, daman ya saba a duk lokacin da mahaifinsa baya nan a can yake tarewa yana
sharholiyarsa da abokansa wani lokacin har da mata, abu ɗaya ne baya yi shine
shaye-shaye.

Bayan kamar sa'a ɗaya da isarsa gidan sai ga yarinyar ɗa zu ta dawo, a nan ma sai
da ta nemi iso suka zo suka faɗa masa sannan suka bata dama sannan ta shiga.
Har cikin faɗar da yake zaune ta isa ta zube masa a ƙasa tana kuka.

“Na roƙe ka, na haɗa ka da girman Allah ka taimaka min mahaifiyata zata iya rasa
rayuwarta daga yanzu har zuwa wani lokaci inji likita, saboda ulcer ta taɓa
hanjinta har ya lalace”

“Idan kina son ran mahaifiyarki ai sai ki bada na ki rai, ni bana da wani taimako
da zan miki wanda ya wuce wannan, idan kin san riƙona ne kawai ya kawo ki to ƙara
ma ki tashi ki koma kar dare yayi miki”

Ɗaga kai tayi tana kallon idonsa, rashin imanin dake zuciyarsa take hangowa. Ta
karanci tantiranci da ke cikin idonsa lallai idan har bata shirya siyar da
mutuncinta to ko mahaifiyarta zata iya rasa ranta bayan kuma ita kaɗai ce ta rage
mata a duniya. Hkan yasa ta yarda ta amince tana ji tana gani ya keta mata haddi,
abunda bata taɓa kawo ma zuciyarta ba, cewar zata bada budurcinta ga wani wanda ba
halalinta ba.
Wani tsabar zalumcin kuma sai da ya gama amfani da ita sannan ya ƙirga rabin
kuɗin ya bata wai shi kawai suka rage masa, da tayi maganar har da zaginta yana
faɗin daman ai buzaye kowa yasan ƴan iska ne. Da kuka ta bar gida tana mai jin
zafin keta mata haɗi da yayi. Shi kuma ya kwanta a ɗakin zuciyarsa cike da nishaɗi,
yana jindaɗin abunda ya aikata wanda a gareshu ba sabon abu ba ne.

bachinsa ya kwasa a gurin har sai da ya hantse, sannan ya tashi, yayi salla, sai ya
aika mai musu aiki ya siyo musu abincin. yana cikin cin abincin sai ga yarinyar ta
dawo idanuwanta a kumbure, wannan karon bata sha wahala a gurin shiga gidan ba
ganin ɗazu yace a bar ta ta shiga. A falon ta same shi yana cin abincin hankali
kwance. Kuɗinsa ta aje masa tana kuka.

“Ba ayi mata aikin ba saboda rai yayi halinsa, ga kuɗinka bana buƙatar ganin su ko
amfani da su, dan amfaninsu a gare ni ya ƙare. Ka kita min haddi akan abinda be
wuce ka bani sadaka ba, saboda kawai na zo nema gun ka, to ka rubuta ka aje ko ba
daɗe ko ba jima, sai an yima ƴarka abunda ka yi min, sai ka ɗanɗana idan da daɗi,
sai Allah ya ninka maka baƙincikin raina sau biyu, wata rana sai ka wayi gari kana
nadamar abinda ka aikata min, na roƙi Allah ya isar min ya nuna maka a kan ƴar
cikin ka...”

Bata gama kalamin ba ya ɗauki abinci ya jefeta da shi, ya hau ta ta shuri yana
zaginta. Shi kansa ya ji babu daɗi a kalaman da tayi masa, duk da ya ba, amman duk
waɗanda yake da su, sune suke kawo kansu ko ya neme su kusan dai za'ace karuwai ne,
wannan ce kawai ya keta ma haddi da gangan...```

Ajiyar zuciya Dady ya sauke, hawaye suka silalo daga idonsa, sai jan majiya yake.
Yanzu kan ya tabbatar da alƙawarin Allah gaskiya ne, kuma kowa yayi da ƴar wani sai
an yi da tashi, sai dai nashi sakamakon mai zafi ne, tun da na ƴarsa har da cutar
kanjamau, kuma ta keta mutuncin aurenta, wannan babban abun baƙinciki ma ita ta ba
da kanta ba wai keta mata haddi aka yi ba, dan baya tunanin hakan da keta haddin ne
da tuni ta faɗa.

Miƙewa yayi tsaye zuciyarsa na masa wani irin mugun zafi ya shiga ɗakinsa hawaye na
cigaba da masa zuba. Nadama ce tsantsarta a zuciyarsa sai yanzu yake baƙincikin
abunda ya aikatawa ƴar mutane, lallai zina bashi ce! Dole wata rana ka biya ko a
biya maka....

RASHIDA POV.

Ɗakinta ta koma ta zauna tana rare kukan baƙinciki daya cika mata zuciya. Ji take
kamar ta rataye kanta ta huta, ta san duk wanda yaji tana ɗauke da wannan cutar ba
zai zauna da ita ba, ga kuma Hilal da yanzu take da tabbacin ta rasa shi kenan har
a bada. Iyayenta ma a yanzu ta san ta rasa su dan ta san zamanta da nasu dole zai
banbanta, dole a yanzu duniya ta san abunda ta aikata, rayuwar da take gudun shiga
ta san a yanzu dole ita zata yi.

Duk kukan da take Momy na tsaye jikin ƙofar ɗakin tana kallonta tare da rera nata
kukan. Haƙiƙa tana tausayin ƴarta sai dai babu yadda ta iya tun da ita ta jawa
kanta.

“Za muje mu ƙara gwaji, so that mu tabbatar idan har da gaske kina ɗauke da cutar”

Ɗagowa kawai ta yi ta kalli Momy da idanuwanta da suke ta zubar da ƙwalla har ɓata
gani sosai da su. Sai kuma ta maida dubanta gurin hannayenta tana duba jikinta
kanta take kaɗawa tana jinjina lamarin ubangijinta dan shi kaɗai ya isa yayi mata
haka, sauyin rayuwa a take....

HILAL POV.

A firgice ya isa asibitin dan tun bayan abunda Nurse ɗin ta faɗa masa sai
hankalinsa ya tashi sosai.
Ko parking ɗin kirki be yi ba ya buɗe motar ya fito hankali tashe har yana gudu.
Likitan yara uku ya tararar akan Rafiq suna ƙoƙarin ceto numfashinsa, amman ina rai
yayi halinsa. Ƙasarawa yayi a rikice yana girgiza Rafiq, tare da kiran sunansa. Da
sauri ɗayan likitan ya riƙe shi yayi baya da shi yana masa magana.

“Haba Doc ya kake abu kamaɗ ba likita ba, mutuwa wace iri ce ba mu gani ba? Ka yi
imani da kaddara mana, komai ka yi ba zai sai Allah ya fasa abunda yayi niya ba,
dan kasan ba'ayi Rafiq dan kai ba, kamar yadda ba'ayi Rafiq dan ka ba”

Lumshe ido Doc yayi ya dantse bakinsa, yana ta ganin Rafiq yana masa yawo a
ƙwaƙwalwa, ƴana buɗe idon sai hawaye. A hankali ya furta Innalillahi wa'inna ilaihi
raji'un. Sannan ya juya ya fita daga ɗakin. Rufa masa baya likitoci suka yi suna
tausasa masa zuciyarsa.
Ba laifi ya samu gwarin gwuiwa daga ƴan'uwnsa likito wanda hakan ya hana shi
bayyana damuwar mutuwar ɗansa a fili, duk da yasan abunda da zai daɗe a zuciyarsa
yana masa yawo kasancewar ƙananan yara suna da shiga rai.
Da kansa ya kira Hajiyarsa ya faɗa mata, kamin ya kira wasu daga cikin ƴan'uwansa
da kuma ɓangaren Rashida.
Sannan abokansa suka saka shi a motarsu , shi kuma ya shiga a ɗayar motar
abokinsa suka nufo gida dashi. Tun da Kalsoom taji ƙarar buɗe gate ɗin gabanta yayi
mummunan faɗuwa, tana jin tsayawar mota ba ɗaya bugun zuciyarta ya ƙaru. Balle kuma
da taga Hilal ya shigo idonsa a rine.

“Ya rasu ko?”

Kai kawai ya ɗaga mata ya zauna saman kujera. Ita kuma ta ɗora hannu saman kai ta
fashe da kuka ta durƙushe a gurin. Yana unƙurawa zai tashi Hajiya ta turo ƙofar
falon ta shigo tana kuka, tare da wasu sisters na shi.
Da sauri Hilal ya tare ta yana faɗin ta daina kuka.

“Hajiya be kamata ki masa kuka ba, haka Allah ya kaddara babu yadda muka iya”

Hajiya bata daina kukan ba ta nuna Kalsoom ta ce

“Idan baka saki wannan yarinyar ba ban yafe maka ba Hilal, kuma sai dai ka nemi
wata uwar ba ni ba...!”

A gigice ya kalli Kalsoom sai kuma ya kallon bakin Hajiya da yayi wannan furucin.
Kalsoom ma kallon Hajiya take hawaye na bin fuskarta. Rashida ta turo ƙofar ɗakin
ta shigo tana kuka.

“Ina ɗa na? Ka hana ni ganinsa lokacin da yake da rai yanzu na zo na ga gawarsa ina
ɗa na yake?”

Rumtse ido Hilal yayi ya zauna saman kujera ya dafe kansa ya dantse bakinsa gam.

NAMRA POV.

Ana kiran salla magariba suka sauka babbar tashar kaduna, da sauri passengers suke
fita wasu saboda suna nesa ganin dare ya soma yi wasu kuma dan su samu bin jam'in
salla magariba. Ita ce kawai ta fito daga motar kamar marar kuzari tana tafiya tana
kallon tashar da bata taɓa mafarkin zuwa ba. Tana fita daga gurin da motoci suke
sai masu Nepep irin wadanɗa suke tsayawa a gefen tashar suna neman masu shiga gari.

“Malama ina za kije?”

Ɗaya daga cikin matasan dake tsaye a gurin masu Napep ya tambaya yana shafe ruwan
dake alwala dake fuskarsa. Matashin saurayi ne mai jini a jika fari kyakkyawa da
shi, a zahiri akwai natsuwa da sanin ya kamata a shimfiɗe a fuskarsa. Ga sajensa
gwanin sha'awa.

“Cikin gari...”

Ta faɗa da muryarta mai kamar zata yi kuka.

“Okay, shiga muje amman zan tsaya a hanya na samu jam'i”

“Ba matsala”

Ya jefar ledar pure water dake hannunsa ya shiga napep ɗin tasa mai kamar sabuwa ya
kunna, ita kuma sai ta shiga gidan baya ta zauna tana ta tunanin inda zata ce ya
kai ta. Har ya kunna Napep ɗin ya fara tuƙi be tambaye a ina za'a kai ta cikin
garin ba, dan shi dai danuwarasa a yanzu ya samu jam'i.
Ba suyi tafiya mai nisa ba ya faka a gafen titi, ya fita yana faɗin

“Bari na yi salla a masalacin”

Kai ta ɗaga masa tana kallon mutane dake ta haɗa haɗa a kan babban titin. Tunanin
unguwar da zata ce masa ya kai ta take, amman har yayi salla ya dawo bata samu
unguwa ɗaya da zata ce ya kai ta, dan bata san garin kaduna balle yace ga inda zai
kaita.

Sai da yayi mata sallama sannan ya shiga Napep ɗin ya tasheta ya hau titi. Can ya
ciro wani ƙyale ya kare ƙasar salla dake goshinsa ya juyo kaɗan ya kalli Namra.

“Wace Unguwa za muje?”

“Uh...m ca..an can..gur.in gra”

Ta faɗin hakan ne dan bata san inda zata ce masa ba, amman ta san ko wane gari
akwai gra.

“Okay GRA ta gurin ina?”

“Ta gurin manyan gidajen nan”

Daga nan wata kalma bata sake shiga tsakaninsu ba, shi dai ya mai da hankalinsa
gurin tuƙinsa, ita kuma hankalinta gaba ɗaya ya tattara ya koma gida da tunanin
inda zata kwana yau a garin kaduna. Ganin sun shiga GRA har suna ƙoƙarin wucewa
bata ce ga inda za a sauke ta ba yasa yayi mata magana.

“Malama mun shiga GRA ɗin fa”

Sai kawai tayi shiru ba dan kuma bata ji shi ba, sai dai bata san abunda zata ce
masa ba. Hakan yasa ya ƙara maimatawa yana mai rage gudun da yake.

“Gaskiya ni ban san inda zanje ba”

Juyowa yayi ya kalleta.


“Baki san sunan mai gidan ba ne? Kuma baki da number waya?”

“Ban sani ba, kuma bana da number, sau ɗaya na taɓa zuwa”

“Amman irin wannan tafiya ai it risk, ace baka da number wanda zaka sauka gunsa
kuma ba kan guri ba?”

Tayi shiru bata ce komai ba. Sai a yazu take nadamar zuwan da tayi a kaduna ita
kanta ta san tayi wauta.
Jin bata ce komai ba yasa ya ce

“Ina zan sauke ki dan ni akan aiki na ke”

“Wallahi idan ka sauke ni ban san inda zanje ba, dan bana da kowa a kadunar nan sai
Allah, tun da ban san gurin wanda zan sauka ba”

Cikin muryar kuka tayi maganar, juyowar da zai ya kalleta sai kawai yaji shesshekar
kukanta. Baya iya ganin hawayen idonta dan Napep ɗinsa bata da wutar ciki wance
wasu suke sakawa, hasken dake gefen titin be iya ya haska fuskarta har yaga
hawayenta ba,amman a yadda ya karanta kamar tana cikin wani hali ne.

“Bawai Allah ke mutum ce?”

“Ni mutum ce wallahi kuma ba cutar da kai zan yi ba”

A nan ta saka ƙafarta ta sauka daga cikin Napep ɗin ta saka hannunta a jaka ta ciro
ɗari biyu ta miƙa masa.

“Ba ni canji”

Ta faɗa tana ta ƙoƙarin tare kukanta dake son fitowa. Kasa karɓar kuɗin yayi kuma
ya kasa tafiya, kallon fuskarta yake dan yanxu hasken gurin ya haska fuskarta, bata
yi masa kama da mugayen mutane ba, jikinsa be bashi zata cutar da shi ba, hakan
yasa shi idan har ya barta a nan gurin be kyauta masa ta, kuma besan abunda zai
same ta ba tun da tace masa bata da kowa sai Allah.

“Shiga mu je”

“Na gode”

Ta faɗa tana share hawayenta, sai ta shiga Napep ɗin da sauri. Tun da ya soma tuƙin
be tsaya ko ina ba sai malali, a mararraba ya tsaya ya miƙa ɗari da hansi aka bashi
canji sannan ya ƙarasa ƙofar gidan na su mai cike da rufin asibiti, dan a kira su
da talakawa ba kasancewar suna da rufin asiri da wadatar zuci. Sai dai a zahiri kan
talakawa ne sosai masu ginin bulu wanda ba ayi ma filistaba.

“Fito muje”

Ya faɗa bayan ya kashe Napep ɗin. Cikin sanyin jiki ta fito tana dansar bakumi
saboda mugun murɗa da mararta take mata. Yana gaba tana biye har suka shiga cikin
gidan mai ɗauke da ɗakuna uku, duk da dare ne hakan be hanata ganin yalwantaccen
tsakar gidansu ba mai ɗauke da bishiyar mangoro guda biyu ɗaya a jikin ɗaki ɗaya
kuma a tsakiyar gidan.

“Neine (Inna da yaren fulatancin) ga baƙuwa”

Wacce saurayin ya kira da neiner ta miƙe daga saman tabarmar da take ta nufo Namra
tana murmushi.
“Maraba maraba laƙe marhabun baƙonƙa annabin ka, siter ƴata sita (Zauna zauna)”

Ya faɗa lokacin da take ƙoƙarin zaunar da Namra saman tabarmar da take zaune. Namra
ta zauna tana kallon yaran gidan da suka kewaye waya suna kallon india hausa a wata
ƙaramar wayar hannu. Gaba ɗaya hankalinsu ya tattara ya tafi can sam basu ma san da
zuwanta ba.
Neine da kanta ta shiga ɗaki ta ɗauki ma Namra tuwon masara ta aje mata gabanta,
sai ta nufi wani ɗan madaidaicin tulu ya bulbulo mata ruwa a kofi ta kawo mata tana
mai sakar mata fuska kamar ta santa.

Shi dai yana daga can gefe yana bawa cat ɗinsa kifi, amman hankalinsa yana gurin
Namra yana kallon yanayinta.

-----------------------------------------------------------------
I PITY RASHIDA 😢
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *64*

Suna ta gaba-gaba suna tare Abdool kamar wanda wani abu zai same shi, sai kirari
suke masa wasu na ture mutane dake gefen gurin dan Abdool ya samu hanya. Mutane sai
kallo a ke wasu ma har sun wuce sai suka dawo ganin duka numbobin motar an saka
YARIMA ABDOOL, duk wanda kuma yaga jajaye kaya yasan sarki ne ko kuma ɗan sarki.

Abdool be nuna tausayi a fuskarsa ba, na ganin irin raunin da aka yi ma Lamido, sai
dai a can zuciyarsa ne yake tausayinsa ganin yadda jini yake masa zuba a kai kuma
ya riƙe ƙafarsa sai cizar baki yake alamar yana jin zafi sosai, kowa yaga yadda
Napep ɗin tasa ta yi sai ya tausaya masa duk ta lalace kai baka ce ma wanda yake
ciki zai yi rai ba, saboda buguwa da tayi da transformer garin ya kauce musu har ya
transformer ta faɗo kan Napep ɗin tasa, shi da be yi hanzarin fita ba da Allah
kaɗai yasan irin ciwon da zai ji.

Lamido ya kalli Sadauki ya soma magana da shi kaɗan-kaɗan, yana gama maganar ya
juya da sauri suka soma take masa baya, suka buɗe masa motar ya koma. Sannan
Sadauki ya kalli sauran dogara ya ce

“Yarima ya yi umarnin a kai shi asibiti”

Da sauri Dogaran suka nufi gurin Lamido suka riƙa shi suka saka shi motar su. Sai
suka sauya hanya daga masaukin Abdool zuwa Asibiti mafi kusa da su.
Anyi masa kyakkyawar karɓa, a asibitin, duk da kasancewar basu san Yarima Abdool
ba amman suna ganin motoci ya dogarai sun san babban mutum ne.
Duk abinda aka yi aka maga Abdool na ciki mota zaunensa har aka gama dubasa aka
saka masa baldeji a kai suka rubuta masa magani, a cikin asibitin dogaren yaje ya
siya masa magani sannan suka dawo da shi gurin motar. Da gudu Sadauki ya nufi Motar
Yarima Abdool ya ƙwanƙwasa gilashin motar sai ɗayan dogaren dake ciki ya sauke
gilashin motar.

“Ran Yarima ya daɗe, an kammala masa komai, sun ce yaji ciwo kai sai kafarsa da
ɗan targaɗe kaɗan”

Da Abdool yake magana amman yayi kamar be jisa ba, idonsa na kan Lamido dake tsaye
jikin wacan motar yana kallon titi. Kallonsa sosai Abdool yake a zahiri yana da
kyaun natsuwa da kuma kyaun fuska, gashi dogo ga fari ga dogon hanci gashin kansa
kawai idan ka kalla zaka gane bafulatani, sai dai hakan be hana Yarima Abdool jin
wani iri akansa ba, wata ƙila akwai wani giɓi a tare da shi, ko kuma akwai wani abu
a tare da shi wanda Yarima Abdool baya so, dan ya tsanar mutum haka nan kawai.

Haka Abdool ya kwashe daƙiƙu talatin da wani abu be ce da Sadauki komai ba, wata
ƙila yau jinin sarautar ni ya motsa har yayi abunda be saba ba, kuma abunda yake
ganin kamar be dace ace mutum yana yi ba.

“Za mu bi ta gidan su mu aje shi sai mu wuce”

Ba dan sun saba ba, da ba zaka zaci da su Yarima yake ba, yanayin yadda yayi
maganar muryarsa na ƙasa sosai, ko kaɗan idonsa ba su kalli Sadauki ba, har yanzu
idonsa suka kan Lamido yana masa kallon rashin dalili.

“Allah yaja zamanin Yarima, an gama”

Ya bar jikin motar da sauri ya nufi gurin wacan motar da Lamido yake tsaye.

“Kai ɗan talakawa shiga mota muje, Yarima mai jiran gado ya ce aje a kai ka gida”

Maganar ta daki zuciyar Lamido har sai da ya kalli Sadauki sai kuma ya kalli Motar
yarima duk da baka iya hango wanda yake ciki sai dai na ciki ya ganga. Har zai yi
magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi, sai kaeai ya rage tsawonsa ya shiga
motar, still ransa ya sosu da furucin da Sadauki ya yi masa. Sai da ya shiga motar
sannan Sadauki ya dawo a motar ya Yarima ya shiga suka kama hanyar Tudun wada.

Lamido ne yake ta nuna hanyar da za abi har aka isa gidansu. Ganin masu jajayen
kaya sun fito tare da Lamido yasa mutane suka fara taruwa ana kallonsu, dan kowa
yasan daga gidan sarki ne. Masu boko suka karantar number motar, yara kuma suka
shiga cikin gidan da sauri suka sanar da Neine cewar ga wasu nan sun zo da Lamido
ciki motar sarki an ji masa ciwo. Ba shiri suka fito daga gidan gaba ɗayasu suka
nufo Lamido. Bugun gabansa ne ya ƙaru ganin Namra a cikin mutanen dake fitowa daga
cikin gidan, ita ma hankalinta a tashe yake kamar wani nata ne aka jima ciwon. Sai
da suka saka shi cikin gidan, sannan ɗaya daga cikin dogaran ya zo ya buɗewa Yarima
mota ya fito.

Ƙarƙashin itacen mangoro suka shimfiɗe Lamido, uwani ta ɗauko matashin kai a ka aza
masa. Kusa da shi Namra ta zauna tana ta kallon kansa tare da yi masa sannu, idonta
cike da ƙwalla, har cikin jikinta take jin ciwon Lamido.
Shigowar Yarima Abdool yasa Namra ta ɗago kai ta kalli ƙofa, karam idonta ciki
cikin nasa, sai yayi saurin kawar da nasa idon, ya cigaba da takawa kamar wani
ɗawuisu, ya tunkaro tsakar gidan, dogarai na take masa baya. Ita kam kallonsa take
da kyau dan tantance wanda ta gani ɗin, da gaske shi ɗin ne ko kuma waninsa mai
kama da shi? Daman Ɗan sarki ne? Anya shi ke wacan kuwa na Katsina wanda yayi mata
kyautar gida ko dai twins ne?

Har ya ƙaraso gurin idonta na kansa, shi kuma ya ƙi ya kalleta sai kallon ƙyakkyami
yake ma gidan abunda ba halinsa ba. Da sauri Uwani ta ɗauko wani Babban tabarma ta
shimfiɗa masa, jikinta har rawa yake. Baya cikin kayan sarauta hasalima farar
shaddace jikinsa, wanda ta haska kyaunsa. amman hakan be hana ƙwarjinsa fita ba,
dan du Ƴaƴan sarakuna da ban suke a duk inda suke.

Be zauna ba, kuma be cewa kowa ko ƙala ba har sai da Neina da sauran matan unguwar
suka miƙa masa gaisuwa, nan ma hannu ya ɗaga musu sai dogaran suke amsa musu da
sunan Yarima ya amsa, kuma ya gaishe ku.

“Allah ya sauwaƙe”

Shine kawai abunda ya furta, shi kuma iyakar laɓɓansa Sadauki ne ya maimaita dan
suji. Sannan ya ciro cak ya miƙawa Sadauki shi kuma ya karɓa ya miƙa wa Neina dan
ita yake zaton ma mahaifiyarsa ce.

“Godiya take Yarima”


Hannu biyu tasa ta karɓa jikinta na rawa, badan tasan ko takardar me ne ba. Kuma
tsoro ya hana ta tambayar ko minenen.

Juyawa yayi ya sai dogoran suka take masa baya. Tunani biyu ne a zuciyarsa miya
kawo Namra gidan ita da take Katsina? Mine alaƙarta da ƴan gidan? Ko kuma
ƴar'uwarta ce? Mijin ta ne wacan to wannan fa? Ko dai yayanta ne? To ai ba suyi
kama ba. Shine abunda yake ta tunani har ya doshi motar.

_Miyasa ba zaka iya yaƙin zuciyarka ba? Dan me zaka nace abunda ba halalinka ba?
Idan ita ce sai me miye ruwanka da ita?_

Iskar bakinsa ya furzar yana sauraren bugun zuciyarsa, da kuma tunanin yadda
ƙaddara take kawo masa mai kamaninta.

“Ya Rahman”

Ya furta yayinda yake ƙoƙarin zama cikin motar. Wannan karon hankalinsa ba akan
jarida yake ba, gaba ɗaya ya tattara ya koma can gurin Namra daya gani, idanuwansa
suna kan titi ruhinsa kuma yana can gurin motar da ba tasa ba.

Daga nan basu tsaya ko ina ba sai masaukinsa, kamin ya fita motar sai da ya duba
agogon hannunsa ɗaya saura ya gani, hakan ya sashi ɗan hanzarin fita yana magana da
sadauki.

“A kira Mai Martaba a sanar masa mun iso, wayana a kashe yake zan ɗan kwanta na
huta”

“Allah ya taimaki Yarima yadda ka ce haka za'ayi”

Gaba ya wuce suka buɗe masa ƙofa, duk jin yake rayuwarsa babu daɗi, kuma be san
dalili ba.

HILAL POV.

Jikin ƙofar ɗakin ya jingina yana kallonta da sauraren kukan da take rerawa.
Rumgume hannayensa yayi yana tunanin ta ina zai fara. Ita kam bata ma san da
shigowarsa ba, ta maida gaba gabas sai rusar kuka take.
Sauke hannayensa yayi ya nufi inta take zaune ya zauna gabanta yana kallon idonta.

“Yanzu abinda kike min adalci ne? Ki zauna kina kuka kin san yadda nake ji kuwa? Na
rasa ɗa na ke kuma kin zauna a nan ki na kuka”

Ɗagowa tayi ta kalleshi

“Kai ɗa ka rasa, kuma kana da wasu, ni kuma miji na rasa”

“Ba ki rasa ni, kin san abinda na ke so da ke?”

Ta girgiza nasa kai.

“Zaki zauna nan for a while as zaman idda kamar yadda addini ya ce, ni zan je gida
na faɗawa su Momi komai, wannan fushi na Hajiya na kwana biyu ne na nasan nan gaba
kaɗan zata sauka, dole ne Hajiya tayi fushi Kalsoom saboda bata fahimce kamar yadda
ni na fahimta ba”

“Ta yarda na zauna ne?”

“Bana jin zata hana, abunda na ke so dake ki yi mata uzuri kuma ki bata lokaci. Zan
ɗauke ki muje gida anjima a can zan maida aure na”
Kai kawai ta ɗaga masa ta share hawayenta. Har ya mike tsaye sai kuma ya juyo ya
kalleta ya ce

“Hajiya ta ce za a maida zaman makoki a can”

Nan ma kai ta ɗaga masa. Sai ya juya ya fice zuciyarsa babu daɗi. Zaune ya hango
Hajiya a falon tana kallon ƙofar ɗakin Kalsoom daya fito fuskarta babu annuri. Kai
ya girgiza cikin yanayin damuwa ya ƙaraso kusa da ita ya dafa kujera yana kallonta.

“Hajiya karki zama cikin iri surukan nan”

“Ba ƙoƙarin zama nake ba Hilal amman duk abunda yake gaskiya dole a faɗe shi, idan
kai ta maka magani ni bata min ba, kuma Wallahi tallahi sai ka ƙara aure ko da kuwa
bana numfashi, dole ka auri wacce zata riƙa maka ƴaƴanka mace ƙwarai ba mai ƙoƙarin
kashesu ba, ni zan nema maka mata da kai na”

Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita ranta na ƙololuwa a ɓaci. Shi dai
da kallo ya bita har ta fice sannan ya saka hannyensa aljihu ya nufi ƙofar ransa a
jagule.

RASHIDA POV.

A nasu gidan suke nasu amsar gaisuwar daban, duk da kasancewar waɗanda badu san
aurenta ya mutu ba suka je can gidan gidan har sai idan sun tambaya ne sai ace musu
gata nan. A harabar gidan suka shimfiɗa tabarma duk da kasancewar yaro ne hakan be
hana ayi masu taro ba, sai dai ba irin zuwan nan ake na wuni ɗaya ba sai dai su zo
su zauna na ƴan mintu su yi mata gaisuwar su wuce.
Tabarmarta daban tana zaune gefe ɗaya, ƴan gidan suna zaune gefe ɗaya. Idonta
kumbura sosai duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata wasu har da Allah ya isa suke
mata duk a tunaninsu tana kuka ne saboda rashin ɗanta, sai dai a gurin Rashida abun
ba haka yake ba, ita tana kuka ne saboda tunanin makomarta ganin asirinta ya tonu
tun yanzu, tasan dole zamantakewar ta da ƴan gidan dole zai canja dan taga alamun
hakan tun yanzu.

Misalin biyu da rabi Teema ta zo gidan gurin gaisuwa, sosai take son magana da
Rashida amman babu dama saboda mutanen dake ta kai da kawo. Tana gurin kuma sai ga
Asmee bayan ta fito gidan Hilal ta nufo nan.
Duk abunda ya faru a gidan sai da ta bawa Rashida labari. A nan Rashida take
labarta musu maganar sakin da Hajiya tasa aka yi ma Kalsoom, dan su ba susan da
maganar ba. Duk daɗi suka ji har mutenan dake gurin da kuma Asmee da basu san kan
abun ba, amman ban da Teema da ita kan tasan komai.

“Amman Hajiya ta kyauta, daman ai ni za ci tuni zata sata shi aikata sakin, duk
wanda yayi maka haka ga jika kan ai be cancanci zama da ɗan ka dan wata shi zata
hara”

Gaskiya kam. Abunda suka mutanen suka masa da shi, sannan ƙananan maganganu suka
biyo baya. Teema ta kada baki ta ce

“Gaskiya Hajiyar ta kyauta daman tun tun tun Hajiyarmu take cewa ya kamata ace
Hajiya ta saka Hilal ya rabu da matar nan”

Rashid ta kalleta tana murza idonta.

“Hajiyar ku ta san ta ne?”

“Eh sukan haɗu a harkar siyasa wani lokacin, suna gaisawa sosai”
“Allah sarki”

Cewar Rashida. Sai kuma ta kawar da fuskarta tana kallon Asmee irin kallon nan da
ita kaɗai ta san dalilinsa.
Teema kuma wani gurin take kallo tana wani tunanin na daban. Sai da aka kira
la'asar sannan Teema ta wuce gida, Asmee kam a gidan tayi sallah sannan ta fice
bakinta cike da magangu amman bat samu damar yi ma Rashida ba, ganin Safiya duk
yasa ta tsargu, hakan yasa ta yi a zamar barin gidan.

Tashi Rashida tayi ta nufi cikin gidan rayuwarta duk babu daɗi saboda abunda take
tunanin su momi sun fara nuna mta na ƙyama tsakanin jiya zuwa yau. Babu abunda ke
ranta kamar ta bar musu gidan ta kama wani, tasan hakan zai fi mata kawanciyar
hankali.

ASIM POV.

Yana ji a jikinsa akwai rashin dacewa a abinda suka aikata. Musamman yanzu da yake
jin abu kamar ƙashi ya tsaya masa a takashinsa, ga wani zafi zafi da yake ji kamar
an zuba masa barkono. Wasu ƙwayoyi dattijin Alhajin ya miƙa masa kusan kala huɗu ya
ce ya sha, daman kamin su aikata sai da ya bashi wasu, tun jiya da dare suke abu
ɗaya har yau da safe, sai yanzu nan ne Asim ya samu kansa. Sai a yanzu yake ƙarema
Alhajin kallo, tabbasa ya sanshi a cikin manyan mutane. Amman duk misalin da yake
masa jiya be gane shi ba sai yau. Daman tun lokacin daya ji sunansa ta ayyana a
ransa ko shi ɗin ne, sai gashi mitumen ya fere ma tun daga biri har wutsiya.

“Na bawa Hajiya miliyan biyu ta baka, na siya maka mota ta miliyan uku. Idan ka
riƙe min sirrina nan da ƴan wasu watan ni za'a far ƙirgaka a cikin manyan Alhazai.
Zan wuce Abuja yau, idan na dawo zan samr ka a nan ko kuma nas Hajiya ta aika min
kai a can sokoto”

Alhajin ya faɗa yana shafa fuskarsa. Asim kan daɗi har cikin kai, hankalinsa da
zumuɗi gaba ɗaya sun tattara sun koma gida, babu abunda yake ransa kamar motar nan,
a take ya ji duk jikinsa ya warysakr kamar babu wani ciwo jikinsa.

Be bar gidan ba sai da ya ci ya ƙoshi, sannan Alhajin yasa direba ya mai da shi
gida.
Yana fita cikin motar sai ga Nably ta kira shi kamar ba zai ɗauka ba dan ya matsu
ya ga motar da Alhajin yake ce masa. Sai dai farincikin dake ransa ba zai hana shi
ɗaukar wayar Nabila ba.

“Hello my girly”

Ya faɗa cikin wani irin yanayi na shauƙi da annashuwa. Ita kaɗan ta karanci hakan a
muryarsa.

“Da alama yau akwai labari mai daɗi a tare da kai..”

Ƙyalƙyalewa ya yi da dariya.

“Labari mai daɗi, na kusa zuwa Abuja na gan ki”

“Nikam ba zan iya jura har jibi ba, akwai birthday friend ɗita da za'ayi yanzu take
faɗa min ni kuma na ce dole zan zo ko dan kai”

“Wow Amman gaskiya kin kyauta min, i can't wait to see you”

“I can't wait to see you too, sorry zan katse kiran, Momy na kira na zan kira ka
idan mun gama”

Hajiya Sadiya ce ta fito waya a hannunta tana faman kiran waya, fuskarta ɗauke da
murmushi, ganin Asim.

Shima Murmushin ya mayar mata ya doshi inda take cike da zumuɗi, sai kawai ta jefa
mishi keys ɗin mota ta nuna masa motar tana cigaba da murmushi sai ta nufi wani
ɓangaren na gidan tana amsa wayar da aka yi picking yanzu.
Wani irin tsalle Asim ya daga tsinkawo motar da yayi, da gudu ya doshi gurin yana
wani irin gurnani kamar mahaukaci.

NAMRA POV.

Abdool na fita Uwani ta karɓi takardar hannun Neine ta duba, tana gani tasan cak ne
sai dai bata iya gane ko nawa aka rubuta ba, kasancewar ilminta be kai har can ba,
zero da ta ga a rubuce sun mata yawan karantawa.

“Minene?”

Neine ta tambaya, cike da son sanin abunda yake ciki.

“Ni wallahi ban gane kan abun ba, amman dai takardar kuɗi ne”

Uwani ta faɗa, dai Namra ta kai hannu ta karɓa tana dubawa.

“Miliyan ɗaya ne cif”

Uwani da Neina sun daki ƙirji tare da zaro ido.

“Miliyan ɗaya?”

Duk mutane da suka shigo cikin gidan duk ko wanne sai da ya riƙe baki, har ga Allah
yawan kuɗin suke gani, Namra kam bat ɗauke su a bakin komai ba, abun ka da wanda
yasan kan abu. Wani dogon tsaki Lamido yaja ya kawardar da kansa.

“Sam sam sam mutumen be san darajar mutane ba Wallahi”

Aiko yayi ƙoƙori irin wannan kuɗin haka! Ƴaƴan manyan mutane da da zasu taka rai su
bar mutum balle har ya baka wannan kuɗin. Shine abunda mafi yawan matan maƙotan
gidan suke ta faɗa.

“Ai dole yayi min mana, tun da ya lalata min Napep dole ya bada kuɗin jinya dan
siyen wata”

Neine ce ta saka bakinta wannan karon tana nuna Abdool ya kyauta iya kyautawa.

“Wallahi da wani can ba zai kula ka ba Abdool ba gasu nan muna gani ba, wannan
kuɗin ka siye sabon Napep har ka rage. A dole ya nuna wannan halin kasan a jinin su
yake, babban mutum kamar wannan”

“Da Sarauta kawai zai fi ni, amman ina tabbacin be fini ilmi zamani ba, balle ma na
addini, ji yadda yake kallon mutane warwatse”

Har cikin ransa yake maganar yana mai jin tsanar Abdool sosai. Namra kam bata ce
komai ba hankalinta ma gaba ɗaya yana wani gurin, sam bata lura da kallon baƙuwar
fuskar da mutanen dake shigowa cikin gidan suke mata ba. Murɗawar da taji mararta
na mata ne yasa ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinsu. Ƙasa ta zauna tana riƙe tsararta
tana dannar baki alamar tana jin zogi sosai. Tun tana juriya a zaune har ta kasa ta
kai kwance tana rumtse ido.
SAI MUN HAƊU BAYAN SALLAH 😍
INA NEMAN YAFIYAR DUK WANDA NA ƁATAWA, ƊAN A'ADAM AJIZINE. WATA ƘILA ZAN KAI
BAYAN SALLAH, WATA ƘILA BA ZAN KAI BA. KU MIN ADDU'A IDAN LABARIN MUTUWA NA YA SAME
KU KUMA KU YAFE MIN ALFARMAR ANNABIN RAHAMA S.A.W 🙏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *63*

Kasa cin tuwon masarar Namra ta yi sai kawai ta sha ruwan tulun mai jiƙa maƙoshi
kamar ruwan freezer.
Da fulatanci matar da ba zata wuce mai shekaru hansin da huɗu ba ta yi ma yaran
magana akan ba su gaishe da Namra ba. Sai duk suka taso cikin ladabi suka gaisheta
cikin su har da manyan ƴan'mata da kuma ƙanana. Da murmushi Namra ta amsa su sannan
ta maida kanta ƙasa tana murza yatsun hannunta.

“Ban wayence ta ba”

Neina ta faɗa da yaren fulatanci tana kallon Saurayin. Shima da yaren ya maida mata
da amsa.

“Ni ban san ta ba, kawai na ɗauko daga tasha ne, sai tace bata da gurin zuwa na
taimaka mata shine na kawo ta nan”

“Amman Lamido taya zaka ɗauko yarinya baka santa, baka san inda ta fito ba? Kasan
ko wace iri ce?”

“To Inna idan na bar ta can ban san halin da zata faɗa ba, kuma kin ga tace bata da
kowa nan”

“Bata da kowa a nan zata zo? Lamido karka mana jaye-jaye muna neman abinda mu ka
ci”

Da yaren fulatanci suke maganar, a zahirin gaskiya Namra bata jin yaren duk kuwa da
kansacewar kakaninta fulani ne. Amman hakan be hanata fahimtar zancen ne suke ba.

“Ni ba macuciya ba ce lalura ce ta kawo ni nan, mijina ne ya sake ni kuma mahaifina


ya riga daya gargaɗe ni akan karna kuskura na je gidansa, shiyasa na zo garin
kaduna, amman idan ba ku yarda da ni ba ba zan zauna a nan ba, dan ba zan takura ku
ba”

Wannan karon cikin halshen hausa Neinah ta ce

“Duniya ce a yanzu ake tsoron mutane, ba kowa ake yarda da shi ba, amman me kika
aikatawa mahaifinki ya yi miki haka kuma a ina mahaifinki ya ke?”

“Mahaifina yana garin sokoto da zama, ni kuma a Katsina nake aure, sai dai ba zan
iya labarta muku labarin aure na a yanzu ba, ina neman ku min lamani har zuwa gobe
zan faɗa muku ba zan ɓoye ba”

Daga Neinah har Lamido shiru suka yi babu wanda ya iya cewa uffan, shi baya son
yayi magana mahaifiyarsa ta ga kamar yayi mata katsa ladan ita kuma har yanzu bata
gama gamsuwa da ita ba saboda halin da duniyar yau take ciki. Ɗaya daga cikin ƴan
matan da suke zaune gurin ne ta taso ta dafa Namra tana murmushi ta ce

“Ba komai mun yarda da ke, ba ki yi kama da mugayen mutane ba, kuma na san ba zaki
cutar da mu ba”

“Na gode”
Namra ta faɗa cikin muryar kuka.

“Uwani zuba mata ruwa ta yi salla”

Lamido ya faɗa cikin halshen fulatancin yayinda yake ƙoƙarin miƙewa tsaye ya jefar
da ledar kifin dake hannunsa. Cikin ladabi ta tashi ya ɗauko mata buta ta miƙe mata
sannan ta nuna mata banɗaki. Kamin namra ta yi alwala har ta shinfiɗa mata tabarma
ta ɗosa mata sallaya sama ta aje mata carbi. Sannan ya ɗauko ɗayar tabarmar ta
shimfiɗa mata gefe ɗaya ta ɗauko zanen gado ta shimfiɗa mata ta aje mata matashin
kai. Sai ta dawo ta ɗauki abincin taje can kusa da tabarma ta aje mata.

Namra bata tashi daga saman sallayar ba sai da tayi salla insha'i sannan ta ƙara
faɗawa Allah buƙatarta ta sai ta tashi ta koma inda Uwani tayi mata shimfiɗa ta
kwanta. Babu abunda ya zo mata a rai sai gidan su, a ɗayan ɓangaren kuma idan ta
tuna irin abunda Asim yayi mata sai ta ji kamar zuciyarta zata rabe biyu tsabar
baƙinciki.
Kusa da ita Uwanin ta zo tayi shimfiɗa, ta kwanta, sauran yaran gidan kam sai da
dare ƴa raba sannan suka nemi guri suka kwanta. Juyi Namra ta yi ta yi har safe ba
yi bachi ba, abun nan da take jin ya tsaya mata a ƙahon zuciya yaƙi saukar mata har
yanzu numfashinta ma daker take yinsa.
Bata san kan gidan ba amman haka be hanata tashi da wuri ba dan gabatar da salla
azuba, sai duk sakkon tashin da tayi sai ta hango Lamido a ƙofar ɗayan ɗakin 6ana
salla nafila, kallo ɗaƴa tayi masa ta ɗauke kai. Sai da tayi alwala tana daf da
gamawa sai ga Neina ta tashi sai ta tashi dukan sauran yaran gidan har da waɗanda
ba su wuce shekara bakwai ba zuwa takwas.

Bayan sun yi alwala dukan mazan sai suka tafi masallaci su kuma suka yi nasu salla
a gida. Tun da Neina ta maida gabanta gaban bata juyo ba sai ta ta gama lazumin da
take. Uwani ma ta maida gabanta gabas tana nata karatun ƙur'ane, ɗayar ma da tsawon
su zai iya zuwa ɗaya da uwani ita karatun take, duk yaran masu ɗan tsawo da wayo
kowa ya kama surar da yake yana karantawa. Ƙananen kawai suka koma bachi, sai ita
kuma ta jingina jikin icecen dake tsakar gidan tana tasbihi da hannu. A hankali ta
karkata kanta tana kallon Lamido take can ƙofar wani ɗaki yana nashi karatun cikin
natsuwa da ƙira'ah mai daɗin saurara.

Hakan ya karantar ita irin tsantsar natsuwa da kuma ilmin da ƴaƴan gidan suke da
shi, tun daga yaran su har ƙanana, ta samu kanta da ɗan sakewar zuciya tun bayan
daga irin karatun ƙur'anen ta suke, daman sauraren karatun ƙur'ane yana saukar da
natsuwa karanta shi kuma yana sa kwanciyar hankali da walwalah.

Bayan duk sun gama sai suka duk suka zo suka gaishe ta, ta amsa musu da far'ah
sannan ta gaishe da Neina, kamin ta kalli Uwani dake mata murmushi ta ce.

“Ina kwana?”

“Lafiya ƙalau ai daman na ce sai dai ki gaishe ni, ba dai ni na gaishe ki ba, dan
nayi ƙanwa da ke”

“Ni...?”

“Eh mana Lamido da kike gani ni nake binsa kin ga kuwa ni yayarki ce”

“Gaskiya ban yarda ba”

“Ta girme ki ƴar nan, jikin ne haka ba'a gane girman ta, yaran nan da kika gani
duka ƴaƴanta ne”

Neina ta saka baki a maganar su da Namra tana murmushi. Namra tayi mata kallon
mamaki.

“Amman ba za a ce ke ce kika haifesu ba, dube ki fa”

“Kowa haka yake cewa sai wanda ya sani, kin san jikin fulani”

“Allah sarki Allah ya shirya miki su”

“Amin. Maryam tashi ki ɗumama mana tuwon can”

Da sauri Namra ta kalli wacce uwani ta kira da Maryam ɗin tana murmushi.

“Marƴam sunan ƙanwata kenan, amman ita kam uwar masifa ce”

“Hmm wannan ma ai ba baya ba, ga shegen rashin kunya da kauɗi ɗuk ta tara kamar ya
kashe ta”

Neina tayi dariya tana ƙoƙarin tashin tana faɗin.

“Maryam bar ni na gyara abu na da kai na, karki je ki min ƙire-ƙire da shi”

Uwani ta kalli Namra.

“Ke kan sai dai asiyo miki koko ko shayi ko? Naga ko jiya ba ki ci komai ba”

“A'a kawai bana jin cin abincin ne”

“Saboda me?”

“Damuwar da ke raina ba zata bar ni na ci abinci ba”

“Hmm idan kika ce zaki saka damuwa a ranki zaki samu matsala, kin gan ni nan
damuwar da take rai na mai yawa ce, amman a haka na ke sakewa ina walwalah kamar
komai”

“Wata ƙila damuwar ki bata kai tawa ba”

“Ko kuma ke na ce damuwarki bata kai tawa ba, kin ki yaran can? Ubansu yana nan da
ransa amman babu ruwansa da mu, saboda mahaifiyarsa bata so na tun ina auren fari,
sai take ganin kamar na mallake mata ɗa, kullum kalar masiba daban har na haifi
yara biyar ina da cikin na shida can ne tasa ya sake ni, kuma tun daga lokacin babu
ruwansa da cin mu da sham mu, balle sutura yau tsawon shekara biyu kenan, Lamido ne
da Neina kawai suke hidima da mu, sai kuma ƴar sana'ar da na ke. Kin ga kuwa
damuwarki bata kai tawa ba”

“Kowa dai irin ƙaddararsa, amman miyasa ba ku sashi kotu ba? Ai kamata yayi ace an
karɓa muku haƙƙin ku”

Daga can gaban murhu da Neine take ta amsa ma Namra tambayar da tayi ma uwani

“Muna kotu yanzu haka, amman shari'ar ta zama wani iri saboda mu talakawa ne, shi
kuma yana da rufin asirin da zai tsaya masa a ko'ina, duk da yakr matsalar daga
gurin muguwar uwarsa ne”

Namra ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina lamarin.

“Rayuwa kenan! Kows da kalar ƙaddararsa, kowa da yadda aka rubuta masa tasa, wani
matsalar daga gurin mijin ne, wani uwar miji wa su ƴan'uwan miji wasu kuma ahaɗa
musu duka”
“Haka ne kowa ai baya wuce ƙaddararsa, shiyasa idan kaga ta wani sai ka gode Allah
da ta ka”

Cewar Neina tana ƙalla itace yana sakawa cikin murhu. Lamido dai yana daga jikin
ƙofar ɗakin yana dannar shakiɗin ka baƙauyensa kamar baya jin firar da suke.

“Kin ga tawa ƙaddarar ta so tayi yanayi da taki, nima saboda ciki dake jikina
mijina ya sake ni, kuma saboda ya san babu inda zanje tun da na riga da na ɓata da
mahaifina”

Dukasu kallonta suka yi, except Lamido, kowane cike da mamaki da kuma shauƙin son
jin labarin nata. Sai dai duk da haka Lamido be ɗago ba balle ya nuna hankalinsa
yana kan labarinta sai dannar wayarsa yake alhalin kuma dukan hankalinsa da jinsa
ya tattara ya koma gindin iccen mangoro da Namra take zaune.

Babu abunda Namra ta ɓoye su, tun daga neman aurenta da Asim da irin gwagwarmayar
da suka sha, kamin auren da kuma irin abubuwan da suka biyo bayan auren da irin
wulaƙancin da Asim yayi mata har i zuwa jiya da ya sake ta.
Sun tausaya mata. iya tausayawa ganin yadda tayi sadaukarwa amman ace ya ci
amanarta, duk da basu sanshi ba hakan be hana su tsine masa ba tare da roƙon Allah
ya isar mata.
Kuka take sosai duk da irin haƙurin da suke bata be hana ta zubar da hawayen
baƙinciki ba. Wannan karon idon Lamido yana kan Namra, be ce uffan akam labarinta
amman yana jinjina irin cin amanar da Asim yayi mata, a ransa yake ƙyama da kuma
mamakin irin mazan nan da suke auren ƴaƴan masu kuɗi dan su gina nasu rayuwa, ya
daɗe yana jin irin wannan labarin na auren jari yau kuma sai Allah ya haɗa shi da
wace aka yi ma.
Haƙiƙa rayuwar Namra abar tausayince,duba da irin rayuwar da zatayi da kuma wacce
tayi, ga kuma tunanin makomar abunda tafi nanata musu a labarin na ɓatawar da
mahaifinta yayi da ita. Saukowa yayi daga saman banrandar da yake ya saka
takalminsa ya nufo gindin bushiyar ya ciro ɗari biyu ya miƙawa Maryam

“Karɓi ki amso mata tea da bire a waje”

Sai da Maryam ta karɓa ta fita sannan ya kallin saman kan Namra yace

“Kuka baya magani abunda Allah ya rubutawa ma bawa, haƙuri ya kamata ki yi, Allah
zai bi miki haƙƙin ki, abunda ya fi akwai kiyi ƙoƙarin shiryawa da iyayen ki babu
kamar iyaye duniya komai kika zama a duniya idan babu albarka iyaye sai kin lalace
kuma komai kika lalace idan akwai albarkar iyaye sai kin kai inda baki zato”

Ɗagowa tayi ta kalleshi ido cikin ido.

“Ta ya zan shirya da su? Na je gida da cikin wanda suka hana na aura? Bayan
mahaifina ya yi min gargadi? Naje na faɗa mu su Asim ya sake ni? Ya kake ganin za
su karɓe ni?”

Ɗauke kai yayi daga kallonta saboda zubar hawayen da take, ya samu kansa a
tausayinta. Hannayensa ya zuba cikin aljihu ya nufi ƙofar fita gidan zuciyarsa nata
raya masa abubuwa da dama.

Tea kawai ta sha, sai Neina tasa ta shiga ɗakinta ta kwanta, ganin an kawo musu
wutar safe wai ko ta samu ɗan bachi. Lamido kuma ya dawo yayi wanka ya shirya cikin
wasu tufafin yayi ma mahaifiyarsa sallama ya fita zuwa gurin a neman halalinsa.

KALSOOM POV.
“Ba zaunawa za kayi ba sakin ta nace ka yi ko baka ji ba?”

Hajiya ta faɗa a tsawace tana kallon Hilal. Gaba ɗaya sai hankalin Rashida ya
tattara ya koma gurin da zancen da Hajiya tayi duk da bata san wainar da ake toyawa
ba, hakan be hanata karantar akan mutuwar Rafiq ba ne, sai kawai ta ƙara narkewa ta
fashe da kuka tana faɗin.

“Ina gawar ɗa na? Hilal ina ɗa na ya ke”

“Yana waje a motar Doc Noor”

Durƙushewa tayi a gurin wani kukan gasken ya zo mata. Sai ta Ummu Faisak ta shigo
tare da wasu ƙanenen Rashida ciki har da Safiya.

“Da gaske ya rasu kenan? Kalsoom kin ci amana ta, kin kashe min ɗa sauran ƴaƴa ma
na bar miki suma ki kashe”

Rashida na kaiwa nan ta tashi ta fice tana wani irin kuka. Ummu Faisak ya nuna
Kalsoom da yatsa.

“Wallahi baki da imani Kalsoom kin kashe shi kin huta, yanzu sai ki zuba ruwa ƙasa
ki sha, kin ƙori ƴar'uwarmu kin kashe ɗan ta hankalinki ya kwanta ko? Tam
congratulations”

Ita ma ficewa ta yi tana kuka, tare da sauran ƴan'uwan. Kai kawai Kalsoom take
girgizawa alamar a'a dan bata iya magana saboda kukan daya ci ƙarfinta.
Hilal har cikin ransa yake jin kukan Kalsoom cos shi kam he believe ba ita ta
aikata ba.

“Hajiya kar mu aiakata abunda za mu zo muna nadama, wallahi ba ita bace ta rantse
min”

“Iyyye nadama? Ah lallai Hilal yau kai da kan ka kake faɗin haka? Kasan hukumcin
wanda ya aiakata kisan kai kuwa? Tafa kashe maka ɗa har lahira amman kake wannan
maganar kamar wanda baya cikin hankalin kansa, ka sake fa nace ko kuma wallahi na
tsine maka a yanzu”

Kalsoom ta matsa ta kama ƙafafun Hilal tana kuka tana girhiza shi

“Sake ni Hilal, ka sake ni a yau karka sallaaƙe maganar mahaifiyarka, ka sake ni


dan girman Allah Hilal”

Kallonta yake kamin ya ɗaga kai ya kalli Hajiya idonsa da hawaye.

“Haba Hajiya da wanne zan ji? Rashin ɗa na ko kuma wannan matsalar? Ki bari komai
ya laɓa za'a gano gaskiya”

“Da uwarka zaka ji, wawa kawai marar hankali, a yau fa sai ka zaɓa ni ko ita”

Ya maida dubansa akan Kalsoom da fatar fuskarta ta soma ja saboda kuka. Cike da
nauyin baki ya ce

“Na sake ki saki ɗaya...”

Wani irin abu taji ya ratsata tun daga saman kanta har zuwa ƙasan ƙafafunta, wani
sanyi ya ratsa gefen jikinta.

“Tashi ka yi ma ɗan ka sutura akai shi makwancinsa”


Ba musu ya tashi ya shiga ciki. Ya ɗan ɗauki lokaci kamin ya fito ya nufi waje. Da
kansa yayi masa wanka daman yasan wanka gawa kamar yadda ake wankan tsarki ake
yinsa, banbanci shine wannan ana saka masa magarya da kuma turare, sai kuma na mata
daya ɓanɓanta dan shi akan tufke kan mace gida uku ne sannan a yarfar da shi a
bayanta saboda hadisin Ummu Aɗiyya wajen siffanta wankan gawar ƴar Annabi S. A. W
tace sai muka kitse gashin kanta tufka uku muka yarfa shi a bayanta _Bukhari da
muslim ne suka ruwaito shi_ sai kuma inda take cewa na kasance cikim waɗanda suka
yi wa Ummu Kulsum ƴar Manzo Allah s.a.w wanka lokacin data rasu farkon abinda
Manzon Allah ya fara ba mu shine gyautonsa, sannan taguwa, sannan mayafin ka,
sannan mayafin jiki sannan aka lulluɓe baki ɗayan jikinta da wata tufar. _Ahmad da
abu Dawud suka ruwaito shi_ (Amman yanzu duk yadda aka samu yi ma mamaci ake indai
ba an haɗu da masu illimi a gurin wankan gawar ba, Allah kasa mu cika da imani kasa
ayi mana kamar yadda ma'aiki ya koyar)

A cikin gidan akayi masa salla, duk da yake gidan mai faɗi ne kuma ƙaramin yaro ne
amman hakan be hana mutane da dama halartar zina'izar ba, wasu saboda Hilal wasu
kuma saboda Hajiya wasu na ɓangaren Rashida ne wasu kuma dan gulma ne, saboda
labari ya ishesu ɗan da kishiyar uwarsa tasa masa guba ya rasu, so that su samu
damar bada labarin ai da su ma akayi salla yaron. Har da masu ɗaukar hoton gawar
suna ɗorawa status duk da kasancewar wasu ƴan'uwane amman hakan be hana su yaɗa
abunda suke ganin ya zame musu wajibi ba. Kan kace kwasi.har labarin mutuwar Rafiq
ya cika social media, kowa sai faɗin albarkacin bakinsa ya ke, alhalin wasu basu
sam komai akai ba.

Bayan sun tafi kai Rafiq ne maƙota mata suka shio cikin gidan, suka zazzauna tare
da Rashida dake ta kuka kamar ranta zai fita suka bata haƙuri wasu kuma a ransu
suke tsine mata suna faɗin wai kuna munafurci ne, daman wasu ganin fuskarta ya kawo
su cikin har da Asmee Aminiyar Rashida.

Bayan sun dawo daga kai shi ne, mutane suka soma yi ma yi ma Kalsoom da Hilal
gaisuwa. Tashi Kalsoom tayi ta shige ɗakinta ta bar su Hajiya falo dan duk sai ta
tsargu da zaman Hajiya a falon.
Aikaws Hajiya tayi aka kira mata Hilal sai ta koma can ƙarshen falon ita da shi
ta faɗa masa wai a maida zaman makokin a gidanta zai fi, shi dai to kawai ya amsa
mata, dan ransa baya masa daɗi.

“To ita wannan yarinyar fa?”

“Hajiya a nan zata zauna ai kinsan Musulumcin ya yarda mace ta yi idda a gidan
mijinta”

“Ikon Allah anya Hilal kana cikin hankalin kan ka? Wai wace hujja kake da ita ne na
yarinyar nan ba ita ta aikata ba?”

Ajiyar zuciya ya sauke, dan har ga Allah be da abunda zai nunawa Hajiya a matsayin
dalilinsa na ba ita ta aikata ba, shi dai a rantsuwar da tayi masa ya gamsu, kuma
jikinsa na bashi ba ita ce ta aikata ba, wata ƙila dan yana sonta ne.
Ganin be ce komai ba yasa ta ce

“Zamu wuce can, idan ka gama lelenta sai ka kaita gidan su”

Juyawa ta yi ta koma gurin mutanen da suke zaune falon, shi kuma ya nufi ɗakin
Kalsoom jiki a sanyaye.

ASIM POV.

Har yanzu bashi da damuwa akan abunda yayi ma Namra, shi yana nan yana jiran ta
kira shi ko kuma ta aiko masa da saƙon ban haƙuri. Yana yawan waya da Nabila Nably
da kuma Mardiya, a ɗan kwana ɗayan nan har ya saba da Nably kusan kullum sai sun yi
waya sau biyar ko fiye da haka. Ya tura mata hotunsa ita ta turo masa, sai yaba
kyawunta yake yana faɗin nan gaba kaɗan zai zo Abuja dan ta kawai.

Yau ya tashi da nishaɗin ɗaya kwana da shi tun jiya da dare da Hajiya Sadiya ta
labarta masa zuwan baƙonsa. Yasan saɓon Allah ne zai aikata amman zuciyarsa a wanke
take saboda burin samun kuɗin da Hajiya ta faɗa masa zai samu idan har ya sake jiki
da mutumen. Suna breakfast ta ke ƙara nanata masa yadda zai masa da kuma irin
shigar da zaiyi, already ta siya amsa turaruka masu kyau da tsada da zai saka.

A gida ya wuni duk da kasancewar ta yi nata bakin amman a ɗakinsa dan ta faɗa masa
iɗan har tana da baƙi bata da buƙatar ya shigo gurinta idan ba wani babban dalili
ba. A gida yyai Salla magariba bayan yayi isha'i ya shiga yayi wanka ya cuɗa
jikinsa sosai kamar zai cire fatan, sannan ya fito jikinsa sai ƙamshin sabulan
wankan yake kamar wanda ya saka turare, saboda tsadarsu, wasu ma ayau ya fara
amfani da su.

Gaban madubi ya zo ya xauna kamar wani mace yana kallon jikinsa, tare da gyara
gashin kansa. Mayuka masu kyau da saka laushin jiki ya shafa sannan ya bi jikin
nasa da humra na maza sannan ya shafa wasu turarukan masu tafiya da imanin mutum ya
shafe duka jikinsa. Sannan ya ɗauki wani baƙin jean ya saka da farar riga mai kyau,
sannan ya ɗauki facing cap baƙa ya saka ya ɗauki wani turaren ya feshe jikinsa, da
shi ya ɗauki lipstick ya shafa a bakinsa ka ɗan, sai kuma ya ɗauki baƙin madubin
ido ya saka. Tsayawa yayi gaban madubi yana duba kansa da kansa, shi kansa yasan ya
yi kyau mashallah, hakan yasa shi murmushi tare da ɗaukar kansa hoto.

Shigowar Hajiya Sadiya ne yasa ƴa ɗan natsu ya rage murmushin da yake.

“Wow...... Gaskiya Asim kana da kyau, kaga kan ka kuwa”

Ta taɓa masa gemu tana murmushin jindaɗin ganin yadda yayi kyau, har ya ɗauki
hankalinta.

“Lallai za a je da kai Asim, wannan ƙamshi haka hhmnn ka iya business, to sai ka
fito ga mota can ya aiko da dareba a ɗauke ka”

“To Hajiya”

Ya faɗa kamar a kumyace, sai kuma ya samu kansa da faɗuwar gaba. Ita kanta ta lura
da yanayinsa na alamar tsoro ko kuma fargaba da ke cikinsa.

“Ka kwantar da hankalinka ka sake jiki ka ci arziki babu abunda zai faru, jeka mota
na jiran ka”

“Okay”

Ya faɗa kana ya ɗauki agogon hannunsa ya saka, bayan ya ƙara fesa turare, ya nufu
ƙofar fita. Ita kuma ta bishi da kallo tana murmushin jindaɗi.

ABDOOL POV.

Da wuri yyi breakfast gurin Ummi saboda tafiyar data zame masa ta dole, dan tun
cikin dare Mai Martaba ya kira shi ya faɗa masa ya tura tawarga da za su je tare
tun da rana, shi kuma zai bi jirgin safe ya sauka kaduna, dan da ƙarshe biyu za a
ɗaura aure, so zai sauka da wuri dan ya samu ya huta ta kuma kimtsa cikin lokaci.

Duk cin abincin da yake idon Amira na kansa, irin kallon take masa na rasa yadda
zan yi da kai. Sai dai bata bari ya ganta ko kuma Ummi ta ganta duk kallon da take
ƙasa ƙasa take masa shi wanda ba kasafai mutum zai kula ba.

“Dude za ma zaka je da ni”

Amal ta faɗa tana ƴar dariya tare da kallon Ummi.

“Yaje dake ya aje ki ina? Shi da zai je ɗaurin aure kuma”

“To yau Assabar ba aiki”

“Ba shi na ke magana ba, yau zai je yau zai dawo”

Ummi ta amsa tana cin wainar ƙwai. Daman duk weekend sune suke rigan karyawa,
sauran ƴan matan gidan duk sai dai su yi ta kwanan gajiya.

Agogon hannunsa ya kalla sai yayi saurin miƙewa tsaye yana dire kofin tea ya ce

“Ummi ayi mana addu'ah”

“To Allah ya tsare ya kiyaye hanya”

“Amin ya rabb, dude sai na dawo ko?”

“To Allah ya tsare”

Ta ɗaga masa hannu. Har ya juya sai Amira ta kira shi.

“Ya Abdool”

Yana juyowa ta miƙa masa tissue paper dan ya goge bakinsa. Hannu ya kai ya karɓa
yana murmushi.

“Thank you. Sai na dawo”

“Allah ya tsare”

Ta faɗa tana murmushi kamin ta biyo sawunsa tare da Ummi suka raka shumi har gurin
mota. Sai da ya bar gidan sannan suka koma ciki.

Goma da rabi na safe ya sauka kaduna, daga airport motocin Mai Martaba suka
tarbosa, dukansu dagarawa ne cikin jajayen kaya sai bashi girma suke suna masa
kirara, abunda ya tsana a rayuwarsa, shiyasa ya fi ƙaunar ya zo da a cikin motar
Army's.

Yana shiga motar suka kama hanyar masaukin Mai Martaba da ke kaduna, dan acan
zai huta sannan ya shirya su ɗauki hanyar Zaria. Jaridar dake cikin motar ya
ɗauka yana duba, sababin labarai ne a cikin. Akwai labaruka kala-kala na abubuwan
da suke faruwa a nigeria da kuma na ban aljabi.

Kerrrrr motar dake gabansu ta taka burki, sai direban dake jan Abdool ya tsayar da
motar da suke ciki. Abdool be damu daya tambaye dalilin tsayawar motar ba, shi dai
hankalinsa gaba ɗaya ya tattara ya koma kan jaridar.
Ɗaya ɗaga cikin dogaran da suke motar gaba ne ya zo ya ƙwanƙwasa ma direban dake
tuƙa Abdool da kuma dogarin da ke front seat. Zuƙe gilashin motar dogarin yayi yana
sauraren abunda ɗayan dogarin yake ce masa.

“Subhanallahi”
Kalmar da diriban motar yayi ne ya ɗago da hankali Abdool a izuwa gare shi.

“Ran Yareema ya daɗe, wani mai Napep ne aka kaɗe”

Dogarin dake front seat ya faɗa 6ana ɗaga ma Abdool hannu irin girmamawa nan.

“Garin yaya?”

Dogarin dake tsaye jikin motar ne ya amsawa Abdool.

“Allah ya taimaki Yarima Kutse yayi mana, yyai aron hannu ne mu kuma zo da gudu.
Amman za'a wuce da kai gida ne mu sai mu ji da da shi”

Uffan Abdool be ce ba, sai kawai ya aje jaridar dake hannunsa ya buɗe motar zai
fita, da saurin sauran dogaran duk suka yo kansa, na gaban yayi sauri buɗe gambun
motar wa Abdool yana mai girmamashi.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *65 NOT EDITED⚠️
*

*ASIM, AMIRA, MARDIYA, UZAIR, RASHIDA. Duk suna muku barka da sallah 😂*

Da ƙarfi take cije bakinta, tana mulmula saman tabarma dake ɗakin, sai faman rumtse
ido take tana buɗewa, ita kaɗai tasan irin zugin da take ji.
Hawaye ne ya fara mata zuba, lokacin da ta ji abu mai ɗumi ya fara bin ƙafafunta,
bata buƙatar a faɗa mata abunda yake shirin faruwa da ita, tasan abunda yake
cikinta yake ƙoƙarin rabuwa da ita, sai dai ita kam har ga Allah bata shirya rabuwa
da shi ba, dan tana jin kamar shi kaɗai ne mafita a gareta, ko ba komai bata son ta
mutu bata bar abunda za a kalla a riƙa tuna ta ba. Babu banbanci tsakanin wacan
ciwon da ta ji da kuma wannan, sai ma jin da take kamar wannan ya fi tsananta masa.

“Innalillahi wa'inna ilaihi”

Shi ta samu ta furta da ƙarfi tana ƙoƙarin fita hayyacinta. Kana ganin yadda take
yaƙi da numfashinta, kasan tana da buƙatar ratuwarta, wata ƙila saboda wasu dalilai
na ta na karan kanta, ko kuma saboda cika wasu kuɗirinrika da suke gabanta.
Lokaci zuwa lokaci numfashinta yake barin jikinta, sai ta yi hanzarin dawowa da
shi tana sauke ajiyar zuciya da ƙarfi.
Uwani ce ta shigo ɗakin da sauri tana tambayar.

“Lafiya Namra?”

A yanayin yadda ta ga Namra yasa ita ma ta furta innalillahi tana riƙa ta.

“Inna waurei”

Ta faɗa da yaren fulatanta tana mai ɗaga murƴa ta yadda Neina zata ji ta. Aiko sai
ga Neina cikin ɗakin da gudunta har da ɗayar maƙociyarsu mai ganin sanin abunda
yake faruwa, Maryam ma tana bayansu tare da ƙanenta maza.
Neina na ganin halin da Namra take ciki ta yi saurin kora Maryam da ƙanenta da kuma
maƙociyar waje, ta sauke ƙyauren ɗakin.
cikin ƙarfin hali ta riƙa Namra, tana ƙoƙarin zame mata uwa a wannan lokacin,
aiko nan Namra ta kama hannun Neina ta riƙe gam tana hawaye.

“Sannu ƴata sannu Allah kawo miki sauƙi, uwani ki je ki ɗibo mana lafiya dubu da
wasu itatatuwan gidan su Mama a'i”

Neina ta faɗawa Uwani tana kallon Namra cike da tausayawa. Cikin sauri uwani ta
tashi ta fita, bata ɗauki lokaci ba sai gata ta shigo da ruwa a kwano daga ta dire
gaban Neina daga bisani ta miƙa mata ganyayyakin. A cikin ruwan Neina ta mirza su,
ta miƙawa Namra, daker ta ɗan kurɓa kaɗan, sannan Neina ta shafa mata lafiya dubu a
goshi, sai ta maida kwanon ta aje gefe da taimakon Uwani suka riƙa ta ta miƙe
tsaye.

“Tashi muje banɗaki”

Tana fara takawa jiri ya ɗibeta sai ta rafke a gurin ta faɗi ƙasa. Hakan yasa Neina
ta tura ƙofar ɗakin, ta rufe gudun kar wani ya shigo.

Gaba ɗaya idonsa da hankalinsa ya tattara ya koma kan ƙofar ɗakin, baya buƙatar
a faɗa masa komai tun shi ba ƙaramin yaro ba ne, tun daga yanayin ihun Namra da ya
ji da kuma gayyen da ga Uwani ta samo, yasan abunda yake faruwa. Wani irin
tausayinta Namra ne ya lulluɓe masa zuciya, gaba ɗaya ya manta da nasa ciwon, he
feel her pain, masu shigo suna masa sannu ma ba jinsu yake ba, sai dai ya amsa masu
sama-sama, dan gaba ɗaya hankalinsa yana can, ga masu shigowa sai tambayar Neina
suke daga shi har su Maryam babu wanda ya iya furta ga inda take, sai duk suka yi
kamar bata cikin gidan. Hankalinsa ya fara tashi ganin an ɗauki lokaci, daga Neina
har uwsni babu wanda ya sake leƙowa, ya san duk wani abu da Neina zata mata ba zai
kai na asibiti ba.

“Maryam zaki iya zuwa bank ki ciro kuɗi?”

Ya faɗa yana kallon Maryam ɗin dake zaune kusa da shi. Kai ta girgiza masa alamar
a'a.

“Okay je gidan su Mustafa ki ga idan yana nan ki ce masa ya je ya samo mota kuma ya
ciro min wannan kuɗin sai a kaita asibiti”

Ya miƙa masa takardar kuɗin da Yarima ya bashi na one million. Zuwa tayi ta karɓa
sannan ta sakata cikin hijabin dake jikinta ta nufi ƙofar fita. Bata ɗauki lokaci
ba sai gata ta dawo sai faman sauri take.

“Baya gida”

“Aro min wayar uwani na aro wayarta na kira shi”

Miƙa masa takardar ta yi sannan ta nufi ɗakin tana buga ƙofar.


Daga can cikin ɗakin Neina ta tambayi waye, sai Maryam ta amsa da.

“Ya Lamido yace Uwani ta aro masa wayarta zai kira mustafa a kai Namra asibiti”

“Ai ba sai anje asibiti ba, Allah ya kawo mata sauƙi”

Buɗe ƙofar Neina ta yi, sai ga Namra tana takawa a hankali Uwani na riƙe da ita an
ɗaura mata zane saman wani zane suka fito. Kallo ɗaya Lamido ya yi mata ya ɗauke
kai be sake kallon inda take ba, har suka shige banɗaki.
Har cikin ransa yake aiyana irin zafin da Namra ta ji, a take wani irin tausayinta
ya lulluɓe masa zuciya, idan kuma ya tuna irin rayuwar da ta fito ciki sai yaji
kamar ya zubar mata da ƙwalla.

Uwani ce ta taimaka mata wajen gyara jikinta, sannan ta fito ta ɗauki kuɗi cikin
jakar Namra ya aika Maryam ta siyo mata Pad, sai ta bi ta gidan maƙotansu ta karɓo
mata bashin pant guda huɗu hannu Sadiya mai haja.
Neina ta gyara ɗakin sam kamar ba ayi komai ba, sannan taje ta ɗora mata ruwan
wanka masu ɗan ɗumi ta kai mata banɗakin ki. A nan ne uwani ta bar mata banɗakin
dan ta yi wanka.

Ta ɗan samu ƙarfin jikinta lokacin da ta yi wanka ta saka pad sannan ta ɗauki zanen
da Uwani ta ɗora mata saman ƙofar banɗakin ta ɗaura ta saka hujabi, ta ɗan ɗauki
lokaci zaune a banɗakin sannan ta unƙura ta fito. Da sauri uwani ta zo ta riƙa ta
suka nufi ɗayan ɗakin da su Maryam suke kwana.
Saman katifar ta kwanta idonta tab da hawaye, tausayin kanta take ji irin
ƙaddarar dake faɗa mata ɗaya bayan ɗaya, idan ta fita wannan sai kuma wannan. Bata
da tabbacin cikin ya zube gaba ɗaya amman a yadda taga tsare tsaren jini bata zaton
akwai abunda ya yi saura a cikinta. Bata bari Uwani taga hawayen da suka zubo mata
ba, har sai da ta fita sannan tasa hannu ta shafa cikinta, tana tuna dalilin barin
gidan Asim saboda cikin da yanzu babu shi, kuma bata da madafa, dan ba zai yiyu ta
zo ta zauna musu a gida haka nan kawai ba, sai dai har yanzu tana tsoron komawa
gurin Abbah, to tace masa me? Mutumen daya ce kar tayo fushi ma balle kuma saki ya
shiga tsakaninta da Asim.

“Ba adili ba ne”

Ta furta a fili zuciyarta cike da ƙololon baƙinciki, tana tuna irin hallacin da
tayi masa yayi mata wannan sakamakon.
Kai kawai take iya girgizawa tana tuna yadda ta rabu komai nata saboda shi, shi
kuma a yau ya butulce mata. Dafata da Maryam tayi ne yasa ta dawo daga duniyar
tunanin da take.

“Ki yi haƙuri Allah zai sake baki wani”

Kai ta ɗaga mata, tana mata kallon wacan Maryam ɗin ƙanwarta.

“Haka ne, babu abunda bata faɗa min ba, amman na ƙi na yarda na riƙa ƙaryata ta,
yau gashi na ga komai daman duk wanda ya ƙi ji ba ya ƙi gani ba”

Da kuka ta ƙarasa maganar kamar wanda bata cikin hayyacinta. Maryam ta girgiza ta.

“Namra lafiya kike kuwa?”

Da sauri ta ɗaga mata kai tana ƙoƙarin share hawayanta.

“Lafiya ta ƙalau”

“Tau ga Maltina nan Ya yace ki sha da madara, mustafa zai karɓo kuɗi a kai ki
asibiti”

Ta faɗa tana dire mata gwangwanin maltina guda biyu da madara.

“Ba sai an kai ni asibiti ba, na gode sosai Allah ya saka muku da alheri”

“Amin”

Maryam ɗin ta miƙe tsaye ta bar mata ɗakin. Dawowa tayi gurin da Neina take zaune
da Uwani da Lamido, suke zaune ta zauna tana faɗin.

“Tace wai ba sai an kaita asibiti ba, ta gode Allah ya saka mana”

“A'a ba za'a barta haka ba kam, bari dai mustafa ya dawo”

“Ai taji sauƙi Lamido ko ba a kai ta ba, ko minene a cikinta be nina ba”

Neina ta faɗa, Lamido ya kaɗa kai.

“Ƙara dai aje asibiti nan ba zasu rasa abunda zasu mata ba”

“Kuɗin zaka ɗauka ka kashe kuma? Lamido kana ganin Napep ɗin nan taka ta lalace an
baka ka siya wani ka samu na jari sai kuma ka ce zaka kashe”
“Haba ai kuɗin yayi yawan da ba zan iya kashesu duka a maganin baiwar Allah nan ba,
kuma ko duka za a kashe mata wallahi zan iya badawa, kai ko Napep ɗin ce zan iya
siyarwa dan nemaw yarinyar nan lafiya, wallahi mugun tausayi take ba ni”

Daga Uwani har Neina kallon juna suke da mamaki. Maryam ce ma tayi ƙoƙarin magana.

“Lallai Yaya kana tausayin yarinyar nan, Allah dai yasa labarin gaskiya ta ba mu
dan kasan duniya yanzu yadda take”

“Amman ta miki kama da wacce zata baki labarin ƙarya? Haba Mairo ki duba yanayinta
mana”

Har Neina zata yi magana sai ga Mustafa ya shigo, sai kawai ta sauya maganar da
amsa masa sallamarsa. Kusa da abokinsa ya zauna yana bashi labarin yadda suka yi a
bank.

“Wallahi akwai layi sosai, kuma naga rashin lafiya ne shiyasa sai nace bari na dawo
sai ayi amfani da abunda yake aljihuna in yado idan aka ciro kuɗin sai na ɗauka,
kuma kasan manyan kuɗi ne ba zan iya zuwa ni kaɗai ba, kar abiyo ni”

Duk da Lamido baya jin dariya hakan be hana shi darawa ba.

“Wallahi kai dai Mustafa kamar baka yi boko ba, ko da yake karatun naka iya diploma
ya tsaya, amman miliyan ɗaya indai ƴan dubu dubu ne ai ba wasu kuɗi ba ne”

Neina ta girgiza kai.

“A a nan Alhaji Isa ba dubu ɗari ya zo dasu gida akan haka aka kashe shi balle mai
miliyan ɗaya, ni tun ranar da Allah ya yi ni ban taɓa ganin dubu ɗari biyar a idona
ba, balle kuma miliyan ɗaya”

Mustafa ya amsa.

“Wallahi fa ai zamani ne ya riga da ya lalace shiyasa komai sai an yi kafa kafa da


shi”

“Allah dai ya shirya mana, ko bana ma son ana faɗar an fashi kuɗi har haka da yawa”

Cewar Neina tana miƙewa tsaye. Uwani ta ce

“Ai babu wanda ya sani idan ba mustafa ba, tun da ba mu faɗawa kowa ba”

“Allah dai ya tsare mu”

Duk suka amsa da Amin har Maryam dake ƙoƙarin tashi ita da Uwani su basu guri.
Bayan sun wuce Mustafa ya kalli Lamido.

“Wallahi babu wanda ya faɗa min haɗarin nan da ka yi in ba dan daka kira ni ba”

“Toh ai ba wani abun daɗi ba ne balle a riƙa yayatawa, kuma ba a daɗe da yin abun
ba, Allah ma dai ya tsare”

“Allah ya ƙara tsarewa, amman dai wannan ɗan sarki ko sarki zan ce Allah be yi shi
da rowa ba har miliyan ɗaya! Kamar wanda be san zafin kuɗi ba”

“Ya za'ayi ya san zafin kuɗi? Iyayensu suna kawashe kuɗin ƙasa, yanzu dai idan ka
fita ka biya ka biya bilya kuɗin maltina da madara na aika am karɓo mata”

“Okay maganar asibitin fa?”


“Tace ba sai an jibe kuma naga kamar Neina bata son aje, ƙara mu ɗan saurara
tukuna”

“Okay yayi Allah bata lafiya, amman ƴar'uwar ku ce ko? Naga kamar baƙuwar fuska ce”

Shiru ya ɗan yi yana tunanin faɗawa abokinsa nasa, sai dai baya jin zai iya ɓoyewa
mustafa komai, kamar yadda mustafan baya ɓoye masa, kuma yasan idan ma be faɗa masa
yanzu ba zai faɗa masa gaba, ko kuma ƴan gulma su tsegunta masa.

Hakan yasa be ɓoye masa komai daga haɗuwarsa da Namra da kuma labarin da Namra ta
ba su nata.
Shi kansa Mustafa ya girgiza kuma ya tausayawa Namra matuƙa. Babu ma abunda yafi
taɓa shi kamar rabuwa da tayi da iyayinta.

“Ai kaji matsalar mata suna da ƙaramar ƙwaƙwalwa, dan me zaka rabu da uwayen ka kan
saurayi?”

Lamido ya numfasa.

“Ai mutum baya iya tsallake ƙaddararsa, sannan mu kan mu maza muna da matsala, da
yawa sai ki ga dan kuɗin gidansu yarinya ake son ta, ni ina mamakin irin mazan nan
wallahi, haka kawai abun wani ya tsune maka ido, ni dai Allah be sa min irin wannan
rayuwar ba wallahi”

“Ai irin ka irin ka kaɗan ne Lamido, ni ma nan idan na ga arziki ba zan ƙi bi ba,
masu arzikin nan suke kawai suke watayawa, ka duba kaga tun yaushe ka gama digiri
ka yo bautar ƙasa, amman aiki ya gagareka, yanzu da kai ɗan wani mai kuɗi ne, da
yanzu kana can Abuja kana hanawa kana aiki a wani babban kamfani”

Ajiyar zuciyar Lamido ya sauke.

“Muma Allah be manta da mu ba, kuma kaga wannan sana'ar Napep ɗin da nake? Ni ta
wadarta da ni kamin Allah ya buɗo min wata hanyar kuma”

“Allah ya tabbatar mana da alheri, amman babu wanda ya ƙi kuɗi”

“Ita yanzu kallo ɗaya zata yi ma duka mazan takalawa alhalin ba haka muke ba, dan
bamu taru muka zama ɗaya ba”

“Uhm, rayuwar ce sai a hankali, Allah ya bata wani na gari, ya shirya tsakaninta da
iyayenta”

“Amin Amin”

*ABDOOL POV*

```Yana tsaye jikin wani upstairs, ya hango ta tana wani irin gudu kamar zata faɗi,
kare na biye da ita a baya yana mata haushi, da alama karen take ma gudun, bata
ankara da ƙaton ramen dake gabanta sai kawai ta faɗa cikin kamar an jefata. Daga
can cikin ramen ta ɗagowa Abdool hannu tana son ya taimake ta sai kuma take, shi
kuma ya yi tsaye yana kallonta kamar zai je, kamar ba zai je ba.```

Firgigit ya farka daga ɗan kajeren bachin daya kwashe shi yanzu-yanzu.
Haƙi yake sosai yana maida numfashi, jin yake kamar a zahiri ne abun ya faru.
kyakkyawan askin kansa ya shafa, ya lumshe ido ya buɗe yana kallon agogon ɗakin.

“Mtsssss mi zai sa ba zan yi mafarkinta ba? Bayan na kwanta da ita a raina? Why
this? Miyasa na zurfafa akan yarinyar nan ne? I'm totally mad”

Ya unƙura ya tashi ya nufi bathroom, zuciyarsa na raya masa ba zai yi mafarkinta


haka nan kawai ba, shi kumasai yaƙar zuciyar tasa yake yana ƙaryata ta, dan ganin
yake idan har ya yarda da ita to zata kai shi ga hallaka ne kawai.
Sai faman faɗa yake ma kansa kamar wani taɓaɓɓe. Har yayi wanka ya fito mafarkin
be daina tsaya masa a rai ba. Haka ya shirya cikin tufafi na alfarma, wata musulmar
shadda ya saka har wani maiƙo take tana shining daya ya motsa sai shadda ta amsa
amo, shaddar ta karɓesa sosai, ta zauna a jikinsa kasancewarta sky blue, shi kansa
da ya kalli kansa a madubi sai da yayi murmushi.

Wayarsa ya ɗauka ya ɗauki kansa hoto, sannan ya baro gaban madubin baya ya feshe
jikinsa da turare mai mugun tsada da ƙamshi.
Already ya saka agogo hannunsa da zabban azurfa.

Yana doso sitting room mafarkinsa ya faɗo masa a rai. Wani irin faɗuwa gabansa ya
yi har sai da ya rumtse ido ya murƙushe bakinsa.

“Wai miyasa yarinyar ta tsaya min arai ne? Ko dai akwai wani abun ne? Yeah na ga
kare yana binta, ta faɗa rame? Me wannan yake nufi ne?”

“Allah ya taimaki Yarima, ba mu da masaniya akan abunda kake magana a kai, Allah
yaja kwanan ka”

Kallon mamaki yayi musu yana juyar da kai, dan shi be san ya iso sitting room ba ma
sai yanzu, ashe a fili yake maganar.
Iskar bakinsa ya furzar ya kalli tsadadden agogon hannunsa. Ƙarfe biyu saura
minti goma ya gani, ya san ɗaurin auren ƙarfe biyu ne.

“Allah ya taimaki Yarima, tuni Mai martaba, ya kira kana bachi har ya bada umarnin
tashin ka”

Hannayensa ya zuba cikin aljihu.

“Yanzu dole sai an naɗa min rawani?”

“Allah ya taimaki Yarima, haka Mai Martaba ya ce, har alkibar da zaka saka mun zo
da ita”
Haka ya zauna suka naɗa masa rawani akai, ya fito fes Sarki, ba ma ɗan Sarki ba.
Miƙewa yayi tsaye suka saka masa baƙar alkyabar mai ratsin zaiba, sannan suka fiddo
takalmin alkyabar suka aje masa ƙasa. A ƙoƙarinsa na saka takalmin ya kalli Sadauki
ya ce.

“Idan ka yi mafarki kare yana bin ka me hakan yake nufi?”

“Allah ya taimaki Yarima, Maƙiyi ne.”

Ya ɗan yi shiru na wasu mintuna, kamin ya sake furta.

“Idan kuma ka faɗa a rame fa? Sai kuma ka miƙo min hannu kana son kamo ni?”

“Wannan Makaru ne, Allah yaja kwanan ka, idan kuma ina miƙa masa hannu to ina neman
taimakon ka ne”

Sai da Sadauki ya gama amsa masa duka tambayoyinsa sannan ya saka takarmin, zai
soma tafiya Sadauki ya ciro wani turare zai fasa masa.

“Allah yaja kwanan ka Mai Martaba ya ce afesa maka wannan”


“Na saka turare bana da buƙata”

“Allah ya taimaki Yarima, wannan na gidan sarautar ne, na Masarautar Katsina ne,
ƙamshinsa ne zai sanar da isowar ka, kuma wannan turaren na gidane da ake haɗawa
tun gadon gadon”

Ba dan yana so ba, ya tsaya suka fesa masa turaren sannan suka shiga gaba, wasu
kuma a baya, shi kuma sai wata tafiya yake kaɗan-kaɗan, mai cike da tsantsar
kasaita, da nuna isa, bayan kuma shi hankalinsa yana can wani gurin dabam.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *66 NOT EDITED ⚠️


*

AMIRA POV.

Ta san yau zai dawo, amma hakan be hana ta kiwarsa ba, duk sai taji gidan ya mata
girma kamar ita kaɗai ce a ciki. Tana son aika masa da saƙon tana tuna gargaɗin da
yayi mata akan ta daina.
Bata san hawaye sun zubo mata ba, har sai da ta ji ɗuminsu a kumatunta, ɗan
murmushi ta yi ta kai hannu ta share hawayen tana magana da kanta.

“Idan na ce zan yaƙi zuciya akan ka, zan cuce kai na, ban cancanci komai ba sai
kyakkyawan sakamako, zan iya barin komai a kan ka, zan jure haƙurin rasa komai akan
ka amman ba zan iya raka ka ba, ni nafi dacewa da kai Abdool, ba zan jure ganin
wata ta raɓe ka ba, ba a hallinta maka wata matar aure ba, face Amira.
Wallahi ina son ka Abdool fiye da irin son da uwa take yi ma ɗan ta, kai mafarki,
kuma kai kaɗai ne cikar burina, idan har na rasa ka Abdool to sai dai ko wace mace
ta rasa ka”

Cige bakinta ta yi tana karɓar kukan da ya zo mata gadan-gadan. Mulmulawa ta yi ta


mulmulo saman gado tana jin abu marar daɗi yana ratsa zuciyarta. Hoton da Abdool ya
yi da Amal tafi tsurawa ido, tana masa wani kallo kamar wacce bata san shi ba.

“Kin yi sa'ar ɗan'uwa ni kuma zan yi sa'ar miji, ina son ka da iyalan ka Abdool”

Bata ankaro da ɗauki lokaci tana kukan ba, har sai da ta ji abu na ƙoƙarin rufe
mata ido, alamar idon ya kumbura kenan.
Muryar Ummi da ta ji ne yasa ta sauri sauka saman gadon ta shiga bathroom ta wanke
fuskarta, ta fito ta nufo falo.
A tsaye ta samu Ummi tana rataye da jakarta, mayafinta a hannu, Amal ma na tsaye
a bayanta sai kumburi take, ita ala dole ga auta.

Tun da Amira ta soma saukowa downstairs Ummi take kalle da yanayinta, ga kuma
kumburin da idonta da ƴa yi, fuskarta har ya soma ja abun ka da farar mace.

“Ba ki da lafiya ne?”

“A'a... Eh... Kai na ne yake ɗan ciwo”

Ummi ma uwace, ta fahimci Amira tana cikin damuwa ne, ko da bata fito a fili ta
faɗa mata ba. Hannu ta kai ta shafa kan Amira zuwa wuyanta.

“Ki yi haƙuri kin ji, komai mai wuce wa ne, kin ji? Rayuwa bata tabbata haka amman
dai ki yi tunani kin ji? Mu zamu fita, Haleema da Meesha ma sun fita Fauza ce kawai
take bachi”

“Okay to sai kun dawo, me za'a girka?”

“No no kije kawai ki kwanta Shukura za ta yi komai, kije kawai ki yi ma kan ki


karatun ta natsu”

Daga haka Ummi ta fice Amal na binta a baya, tana waigo Amira da harara dan ita har
yanzu haushinta take ji, wai ta maida mata ɗaki kamar nata, daman can Amal ba son
mutane take ba.
Maganar Ummi ta tsaya a mata a rai, me take nufi da ta yi ma kanta karatun ta
natsu? Me hakan yake nufi? Juyawa ta yi ta nufi upstairs zuciyarta da tunani kala-
kala.

RASHIDA POV.

Tana kewar ɗan ta sosai, wata ƙila dan kasancewarsa shi kaɗai ne ɗa namiji a
gareta, ko kuma dan ita silar mutuwarsa.

“Na rasa abubuwa da dama, na rasa mijina, ɗa na, na rasa lafiya ta, yanzu kuma ina
ƙoƙarin rasa iyayena, ni ka ɗai ce mai Aure da nake aikata zina? Ba suna nan da
yawa ba? Miyasa ni bana da sa'a?”

Miƙewa ta yi tsaye daga saman prayer mat da take ta cire hijabinta ta nufi window.

“Idan har na bar gidan nan kowa zai tambayi dalili, kuma dole wasu za su gane
abunda yake faruwa, idan kuma na zauna zan fuskancin tsagwama da takurawa, miye
mafita?”

Hannu ta kai ta riƙa window, wannan karon sai ta koma zancen zuci.

‘Hakan yana nufin na rasa aure kenan har a bada? Idan kuwa gaka ne, to ba ni kaɗai
zan shiga matsala ba, har Asmee tana ciki, kamar yadda nima ta jefa ni, kuma
mijinta ma yana ciki, dan asirina ba zai tonu su na su ya rufu ba, bayan su ne
silar komai, idan har na rasa Hilal ba zan rasa Alh Bashir ba’

Juyowa tayi ta jingina da window, yana motsa bakinta.

‘Idan kuma har na tona musu asiri na tonawa kai na, na matso da mutuwa ta kusa
bayan kuma tana nesa da ni.
Amman kuma ba zai yarda ya tonawa kansa asiri ba, dan ba zai yarda ya rasa
martabarsa da aikinsa ba, ni kuma ba zan rasa mijin aure ba, kuma hakan ba ƙaramin
ƙona zuciyar Hilal da Asmee zai yi ba, su ma ya kamata su ɗanɗana yadda zafin baƙin
ciki yake. I will never gave up, i will fight for my happiness, i deserve happiness
again’

‘Idan kuma har Hilal ya rasa ni, be cancanci sake farin ciki ba, ya kamata ya
ɗanɗana zafin rabuwa da ni, yasan akwai banbanci tsakanina da ita, Idan har ban
more Hilal ba the love of my life be kamata wata ta more shi ba’

Komawa ta yi saman gado ta zauna ta ɗauki wayarta ta soma kiran Teema.

HILAL POV.

A gidan Hajiyarsa ya zauna har dare, sai da kowa ya watse sannan ya shiga sallama
da Hajiya zai mata sai da safe.
Wani kallo uku saura kwata ta yi masa iron kallon Namijin da be san ciwon kansa
ba, ƙasan carpet ya zauna kansa a ƙasa yana mai nuna mata tsantsar ladabinsa.

“Ban yarda ku kwana daki ɗaya da matar nan ba, kai dai ba jahili ba ne tun da kasan
babu aure a tsakanin ku a yanzu”

Ba tare da ya ɗago kai ba ya ce


“Amman musulumci ya yarda da zaman idda, Hajiya zan bi duk wani umarni na ki, amman
dan Allah karki gina katanga tsakanina da matana wallahi ina son ta”

“Kai wawaye Hilal, baka iya son mata ba, kana zurfafawa har ya zama baka iya ganin
laifinta, ba zan gina katanga tsakanin ka da matar ka ba, dan ni ba irin surukar
nan ba ne, amman zan nisanta ka da ita har sai ta gane kuskurenta ta yadda gaba ko
ance ta aikata ba zata aikata ba, kuma ya zama dole ka ƙara aure!”

Ajiyar zuciya ya sauke still be ɗago ya kalleta ba, sai dai ransa be masa daɗi ba
akan kalamanta.

“Zan yi duk yadda kika ce Hajiya, ke na fara sani kamin na san kowa a duniyar nan,
ba zan zaɓi wata akan ki ba”

“Allah ya yi maka albarka, zan nema maka matar da zaka aura da kaina inshallah mai
mutunci”

“Consider it done Hajiya, mu kwana lafiya”

Miƙewa ya yi tsaye idonsa sun rine sun yi ja sosai, irin ran maza ya ba ce sosai.

KALSOOM POV.

Tun da kowa ya watsa aka barta ita kaɗai sai duk ta ji babu daɗi ga kuma danuwar
data saka ta gaba, tana ji a jikinta Hajiya ba zata barta ta zauna da Hilal ba.
Haka ta zauna ta ci kukanta tun tafiyarsu har dare bata aikin komai sai kuka.

Tana jin tsayawar motar Hilal gabanta yayi dakan uku-uku. Ji take kamar ya zo mata
da wani sabon abu, jin take kamar wata maganar zai faɗa mata wacce kunnuwanta ba
zasu iya ɗauka ba.
Bata ƙarasa tsorata ba, har sai da ta ga ya ɗauki tsawon lokaci be shigo cikin
gidan ba, hakan yasa ta unƙura cikin rashin kuzari ta miƙe tsaye, ta fito falo.
Zaune ta same shi saman kujera ya haɗa kan sa da gwuiwa.

Ta ji babu daɗi sosai, sam bata jin damuwarta, ta sa damuwar take ji, bata san me
Hajiya tace masa ba, amman a yanayin yadda taga mijinta ta karanci damuwarsa, duk
abunda Hajiya zata ce mata ba zai wuce akan zamanta gidan ba, ko kuma wani abun
daya shafe ta.
Juyawa ta yi zata koma ciki, sai kawai ta ji muryarsa ta daki dodon kunnenta.

“Ɗauko mayafin ki zamu je gida mu yi na su Momi bayani”

Bata juyo ba, ba kuma amsa masa ba, sai kawai ta cigaba da tafiyarta, hawayen na
bin fuskarta.
Hijabinta yana kusa da gadonta, amman tsabar hankalinta baya jikinta haka ta bi
tufafinta ɗaya bayan ɗaya bata ga Hijabin ba, sai kawai ta bude wardrobe ta ɗauko
wani, Sannan ta ɗauki wayarta, ta handbang ɗin ta ta fito hawaye na cigaba da bin
fuskarta.

Kamar mai koyan tafiya haka ta fito daga ɗakinta zuwa falo, shi kuma har lokacin
yana nan zaune a yadda ta bar shi. Zuwa tayi ta tsaya bayansa tana hawaye.
Be yarda ya haɗa ido da ita ba, sai kawai ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa ba tare da
ya ce da ita komai ba.
Sai da ya yi ma motar key sannan ta fito daga falon ta shiga gidan baya, ja
fisgi motar da ƙarfi, mai gadi na buɗe masa gate ya fara gudu kamar zai tashi sama.
Shesshekar kukanta ne yasa ya rage gudun da yake ya faka gefen titi. Ya juyo ya
kalleta.

“Try and cry so that i can tell you not to cry, Na fi ki shiga damuwa Kalsoom, ga
damuwa na ga na ki ga na Hajiya ga na ƴaƴana ga na rashin yaro na duk ni kaɗai. Ba
ki san waye Hilal ba shiyasa kike damuwar kan ki, yanzu haka za muje gida kina ciki
damuwa da kuka? Kuka ba komai yake ƙara min sai karya min gwuiwa”

Be jira abunda zata ce ba, ya hau ttiti ya cigaba da tuƙa motar a hankali, har suka
isa estate ɗin su. Gabanta ya faɗi sosai lokacin da ya danna horn a ƙofar gidansu.
An ɗan daɗe kamin a buɗe musu gate ɗin kasancewar a lokacin goma da ɗan gota,
daman can a al'adar gidan da tara ta yi suke rufe gate.
Sai da mai gadin ya fara buɗe gate ɗin ya leƙo su ya ga su ne sannan ya koma ciki
ya buɗe musu gate ɗin. Nesa da motocin gidan ya faka motarsa sannan ya jingina
kansa jikin sitarin motar yana karanto irin bayanin da zai ma Daddy har ya fahimta.

“Ni ce zan faɗa musu komai?”

Dagowa ya yi ba tare da ya juyo ba ya ce

“Ta wace fuska?”

“Ta fuskar da za su fahimta, ka jira ni a nan”

Gefen hijabinta ta saka ta ƙara goge fuskarta sannan ta buɗe motar ta fita. Ita
kanta tana fargaba yadda zata faɗa musu tun da ba magana ba ce mai daɗi, sai dai
basa buƙatar a ɓoye musu komai. Ta daɗe tsaye jikin ƙofar falon tana tunani kamin
ta tura ƙofar ta shiga.

Sallama tayi can ƙasan maƙoshinta, muryarta a dakishe alamar kuka ya kamata, babu
kowa falon kuma kayan kallo a kashe, hakan ya tabbatar mata da sun shiga bachi ko
kuma ƙannenta suna can suna karatu. Sai kawai ta juya ta fita daga falon ta nufi
falon Dady.
Tun daga bakin ƙofar falon ta jiyo muryar tv, da alama yana kallon labarai ne.

“Assalamu alaikum”

Ta faɗa a daƙishe, haɗa baki suka yi gurin amsa mata. Duk da mamaki suka kalleta
Momy ta aje plate ɗin abincin dake hannunta.

“Kalsoom shigo mana kika tsaya jikin ƙofa kamar baƙuwa”

Shigowa ta yi tana kuka, ta zauna kasa tana duƙunƙune fuskarka. Kallon natsuwa Dady
yayi mata kana yayi gyaran murya ya ce

“Idan kin jin wani abu ne ya shiiga tsakanin ki da mijinki kuma ke ce mai laifi kar
ma ki soma ba mu labari”

Cikin muryar kuka ta ɗago kai ta kalle shi

“Ba ni ce mai laifi ba, kuma Hilal ba shi da laifi, mahaifiyarsa ce ta saka ya sake
ni”

Momi ta dafa ƙirjinta.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Dady kuma ya rumtse ido yana sauraren yadda maganar ta daki dodon kunnensa.

“Me kika mata?”


Momi ta sake tambaya.

“Wallahi ban mata komai ba, saboda mutuwar Rafiq ne”

A nan ta kwashe labarin duk abunda ya faru ta faɗa musu, sai da ta kai aya, sannan
Dady ya kalleta ya ce

“Je ki shigo da shi”

Ba musu ta tashi tana kuka kamar ta shure ta fita. Hilal na tsaye jikin mota ta
fito, yadda ya hango ta zuciyarsa ta nasalta masa bata faɗa musu gaskiyar abunda
ya faru ba.

“Dady ya ce ka shigo”

Ta faɗa tun kamin ta ƙaraso kusa da shi, sai kawai ta juya, shi kuma ya rufa mata
baya, zuciyarsa cike da zullumi.
Jimmm yayi lokacin da ya isa bakin ƙofar falon, sannan ya shiga da sallama yana
mai sadda kansa ƙasa. Can jikin ƙofa ya zauna dan baya jin sakewar da zai ƙarasa
kusa da su ya zauna.

“Kalsoom ta faɗa mana komai, kuma ba mu ga laifin ka ba, ko nine kwatankwacin


abunda zan aikata kenan”

Cewar Dady. Hilal ya ɗan ɗago kaɗan ya ce

“Fushin Hajiya na ɗan wani lokaci ne, nan gaba kaɗan zata sake, shiyasa na ce za
tayi zaman idda acen kamin Hajiya ta yarda na mai da ta”

Dady ya gyara zamansa, yana yi ma Hilal kallon hankali da kamala.

“Hilal ina son ka kasance mai haƙuri a duk halin rayuwar da ka tsinci kan ka.
Kalsoom zata koma gidan ka amman ba yanzu ba, zata zauna a nan har sai lokacin da
Hajiya ta ce ka zo ka tafi da ita, kuma ina mai baka shawara ka nemi matar da
mahaifiyarka dake jin hankalinta ya kwanta da ita ka aura”

Da sauri Hilal ya kalli Dady

“Amman Dady bata hana....”

Dady ya ɗaga masa hannu.

“Ni a ɗana na ɗauke ka, kuma ba zan baka shawarar da zata cutar da kai ta cutar
ƴata ba. Ka ɗauki shawarata kawai”

Maida kansa ya yi ƙasa.

“Amman Dady ita Kalsoom ta yarda?”

Dady ya kalli Kalsoom da ke kusa da Momi tana aikin kuka ya ce

“Zata yarda, ai tasan mahaifinta ba zai mata abunda zai cutar da ita, ka tashi ka
je kar dare ya yi maka, ke kuma ki wuce ɗakin ƴar'uwarki”

Ita ce ta riga tashi ta nufi hanyar da zata sadata da ɗakunan tana kuka. Hilal kuma
ya miƙe tsaye jikinsa a sanyaye ya bar falon, zuciyarsa na raya masa Dady yayi
fushi ne shiyasa har ya yanke wannan shawarar.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *67*
Rasa ya yi inda zai sa kansa, gaba ɗaya ganin yake gabas da yamma sun haɗe masa,
musamman ma daya dawo gida.
Sai tunani ya taru ya yi masa yawa, wanka daya saba yi kamin ya kwanta yau kam
be yi ba, ko kayan jikinsa ma be damu ya canja ba haka ya hau gado ya kwanta, bachi
ya ƙwauracewa idonsa gaba ɗaya, har safe be rumtsa ba, sai juyi yake kan gado.
Biyar da rabi na safe ya yi sallah asuba, bayan ya gama tasbihinsa ya ɗauko
alƙu'ane ya buɗe ya fara karatu.

Ƴar ƙara wayarsa ta yi alamar saƙo ya shigo, sai dai be duba wayar ba, har sai ya
gama karatun nasa yayi addu'ah sannan ya maida ƙur'ane mazauninsa ya aje. Kayan
dake jikinsa ya cire ya ɗaura tawul ya shiga wanka, ya daɗe zaune a bathroom ɗin
sai tunane yake kamin ya samu kuzarin watsa ruwa ya fito. Cikin rashin daɗin rai ya
shirya, Farar shadda ya saka, be damu da duba kansa ba a madubi ba, ya saka agogon
hannunsa tare da hulla, sannan ya ɗauki wayarsa yana duba ya nufi ƙofa,
Tunawa yayi da be saka turare ba hakan yasa shi ya dawo ya saka turaren sannan
ya fice.

_Ka yi blocking ɗin number na, ka raba ni da ƴaƴana, Hilal ka ci amana ta, ina
roƙon ka alfarma, dan Allah dan Manzon Allah ka bar ƴaƴa su dawo a gare ni su ne
kawai gata na_

Yana karanta saƙon yasan daga inda ya fito duk da ba number ba ta bace. Wani godon
tsaki yaja.

“Duk halin dana shiga ke ce sanadi Rashida”

Sai da ya yi deleted ɗin saƙon sannan ya buɗe motarsa ya shiga. Ya ɗauki hanyar da
zata kai shi gidan Hajiyarsa.
Be iso mutane sosai a gidan ba, kasancesar Safiya ne, kuma mutum na ƙaramin yaro
ɓe ba babba ba, ita kanta a lokacin da ya shiga cikin gidan tana can cikin ɗakinta
tana shiryawa.
Guri ya samu a falonta ya zauna, yana kallon tv duk da hankalinsa baya gurin, ɗai
da ɗai ƙannensa da mutanen gidan suka riƙa shigowa suna gaishe shi da yi masa ya
haƙuri, shi kuma yana amsa musu kamar an cilasta masa.
Sai takwas saura Hajiyaraa ta fito daga ɗakinta. Ta yi mamakin ganinsa a falon
kamar wani baƙo mutumen da ya saba shiga har ɗakinta idan ya shigo cikin gidan.
Ƙarara Hajiya ta ga damuwa da rashin bachi a idon ɗanta, ba ta yi mamaki ba,
daman can ta tsammaci haka, sai dai ita aabunda yake duba mas ba shi yake hangowa
ba.

“Hajiya ina kwana”

Ya gaishe ta ba tare da ya ɗaga ido ya kalleta ba.

“Lafiya ƙalau ya haƙurin mu?”

“Alhamdullah”

“Ka yi haƙuri Hilal haka rayuwa take zuwa wani lokacin, kai taka ƙaddarar ta rashin
mata na gari ne, ta ɗayan ba daɗi wannan ma ba halin ƙwarai, amman inshallah zaka
ji daɗi, zan nema maka mata mai hankali da ladabi, mun yi magana da mahaifin ka ma,
da ba dan wannan gaisuwar ba da kaje ka ganta, dan bana son auren ku ya wuce wata
biyu ko uku ba, yarinyar ƴar gidan mutunci ce”

“Duk yadda kika ce Hajiya haka za'ayi amman ina roƙon alfarmar zan je aiki idan da
dama a yi addu'ah yau, tun da yaro ne kuma daman can sunna bata koyar da mu wannan
zaman kwana ukun da ake ba....”
“Eh Mahaifinka ma yayi wannan maganar amman naga tun da kwana uku ne, kuma kaga
yanzu kwana ɗaya ya rage ai ƙara ka yi haƙuri kawai,amman kai zaka iya juwa aikin
ai”

Kamin yayi magana sai ga Ezzah da Ulfah sun fito cikin shirin makaranta, da gudu
suka zo suka rumgume shi.

“Dady i miss you”

Ulfah ta faɗa. Ita Ezzah sai tasa kuka.

“Dady shikenan Rafiq ba zai dawo ba?”

Kansu ya shafa cike da ƙaunar ƴaƴan nasa, da kewarsu kamar ba jiya ya rabu da su
ba.

“Kin taɓa ganin wanda ya rasu ya dawo? Sai dai ki yi masa addu'ah”

“Ni kam i hate Anty Kalsoom ita ta kashe mana Rafiq”

Ya buge mata baki kaɗan.

“Kar na sake ji, akwai mai kashe wani bayan Allah ne? Kar bakinki ya sake irin
wannan furucin”

“Dady wallahi ita ce ta kashe shi”

Ulfah ma ta faɗa, ta fuskanta kamar za ta yi kuka.

“Kuje driver na jiran ku zaku je school”

Hannu yasa aljihu ya ciro dari biyu ya mika musu, suka karɓa da far'ah suna godiya.
Da kallo Hajiya ta bi su har suka fice sannan ta ce

“Ni wallahi tausayi suke ba ni, shiyasa nake son ka auri yarinyar nan dan ga alama
tana da natsuwa zata kula da su”

miƙewa ya yi tsaye yana dai-daita hular kansa.

“Zan leƙa office, idan na gama abunda na ke zan dawo”

“Amman ka karya kuwa?”

“A a zan karya a can”

“Allah ya tsare amman da ka tsaya ka karya a nan dan na san a can ba komai za ka ci
ba”

“Zan ci”

Daga haka yasa kai ya fice, ransa a jagule.

NAMRA POV.

A ɗakin ta wuni har yamma, tun tana kuka mai hawayen har hawayen suka daina zuba,
sai dai tayi kukan kawai babu hawaye.
Gaba ɗaya yanzu hankalinta ya tattara ya koma gida, tana kewar ƴan'uwanta sosai,
duk da tadan itace bata kyauta musu ba, sai dai tana jin son mahaifiyarta a ranta
tana kewarta.

“Bana jin ina daga cikin masu daɗewa a duniya, ina ji kamar mutuwa ta tana kusa da
ni, ina da bukatar ki Mama, Abbah ka yafe min na tuba”

Magana take da kanta kamar wata taɓɓabiya. Miƙewa ta yi tsaye ciki da ƙargin hali
dan bata jin karfi sosai a jikinta, fitowa ta yi waje, tana sun sun da kai kamar
mai jin kunyar kallon inda su Neina suke.

“Ba wuta ai ƙara ki fito nan kam ki sha iska”

Neina ta faɗa tana gyara mata gurin da zata zauna. Ita kuma har ga Allah kunyar
haɗa ido takw da Lamido balle kuma ta zauna inuwa ɗaya da shi.

“Zo ki zauna mana, jiri zai iya ɗaukar ki idan kina tsaye”

Ya faɗa ganin yadda ta tsaya a bakin kofar kamar ba zata zo ɗin ba, sosai gabansa
yake faɗuwa, har murƴarsa na ƙoƙarin gargadar a maganar da yake mata saboda
faɗuwan gabansa da ya tsananta.
Tana fara takawa gabansa ya fara fisgarsa yana wani zillo, da zaka tsaida idonka
a lokacin da kyau a ƙirjinsa zaka ga yadda zuciyarsa take bugawa. Saurin ɗauke
kansa ya yi daga kallo tafiyarta da yake kamin ta ƙaraso kusa da su.
Tana ƙaraso gurin sai kawai ta ɗauki filon da Neina ta aje mata, ta kalli Uwani
ta ce.

“Dan Allah dan duba cikin jaka na akwai waya sai ki ɗauko min”

Ba musu Uwani ta tashi nufi ɗakin. Bata ɗauki tsawon lokaci ba ta fito da wayar a
hannu ta miƙa wa Namra.

“Na gode”

Ta faɗa sai ta juya da zimmar komawa.

“Ai da kin zauna a nan”

“A.a daman wayar kawai nake son ɗauko wa”

“Zauna a ɗakin kawai, make yourself comfortable”

Kai kawai ya iya ɗaga masa, ta juya ta koma cikin ɗakin. Zaunawa ta yi tana sauke
ajiyar zuciya, sai kuma ta kafe wayar da ido kamar mai shakkun kunnawa.
Can dai ta kunna wayar zuciyarta cike da fargaba, da tunani kala-kala. Gabanta ya
soma faɗuwa lokacin da saƙwanni suka riƙa shigo mata bayan ta kunna wayar. Sai dai
mafi yawanci su duka na Mtn ne, sai saƙo ɗaya mai ɗauke da number Yasmeen. Saƙon ta
fara buɗewa, tana tunanin wane irin saƙo ne Yasmin ta aiko nata.

_Salam Namra na haihu na samu baby girl, na kira wayarki ban samu ba_

Murmushi ta yi tare da hawaye a lokaci ɗaya.

“Allah ya raya miki babyn ki, ya baki lafiyar shayarwa”

Shine furucin da tayi a fili, ta rumgume wayar ta lumshe ido.

‘Ya kamata na koma gida, ko me me zai faru ya faru a can, na yi kuskure tun farko
da ban sauka gidan mu’

Tunanin da take a ranta kenan, kamin ta buɗe ido, ta fara kallon ɗakin.

“Gobe... Gobe ya kamata na je gida, an cire duk wani fargaba da yake rai na, zan
cire tsoro zan gwada ƙarɓar sunana ko Alƙah zai za na dace, ba zaka taɓa winning ko
losing ba matuƙar baka taɓa gwadawa ba, i hate to try”

A fili ta yi furucin zuciyarta cike da yaƙinin lallai zata iya, kuma ta shirya
fuskantar ko wane irin hukunci na Abbah.

“Taya zai yafe min idan ban je ba? Taya zan shirya da Anty idan ban je ba? I have
to do this, Allah ka taimake ni”

Komawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.

ABDOOL POV.

“Lafiya ƙalau aka ɗaura aure”

“Mashallah Allah ya nuna mana na ka, ya maka albarka”

“Amin Mai Martaba”

“Ka yi kyau sosai, ka fito kamar wani babban sarki”

Kallon Mamaki Abdool yayi kamar ance masa Mai Martaba yana tsaye gabansa.

“Waya faɗa maka?”

“Babu ruwanka, ai har hoton ka an turo min alkyabar ta karɓe ka sosai”

Dariya yayi cike da mamaki, dan shi dai be san ya ɗora hoton daya saka alkyaba ba a
media balle yace ko wani ne ya tura masa.

“Mai martaba kasan ance informer hukunsu ɗaya da da mai fashi da makami ko”

“To ayi haƙuri Major ayi haƙuri muma muna kan aikin mu ne”

Ƙyalƙyalewa yayi da dariya daga shi har Mai Martaba, daga bisani Mai martaba ya
ɗora da.

“Ƙarfe nawa zaka ta so?”

Shiru yayi kamar mai tunani, haka kawai ya samu kansa da rashin jindaɗin tafiyar.

“Zan turo maka dogarawan ka sai a bar min Sadauki, zamu kwana biyu kamin mu dawo”

“Why?”

“Just kawai ina son ganin kaduna ne, kasan rabo na sa kaduna since... I can't even
remember”

Ya ɗan sosa kansa yana kallon titi da mutake ta kai kawo suna sha'aninsu.

“Fine as you wish, amman aikin ka fa”

“Mun samu hutu ai ko ka manta?”


“Haka ne, to ba matsala amman dai karka ɗauki lokaci i have surprise for you”

“Thank you super Dad”

Daga haka ya kashe wayar ya kalli Sadauki dake front seat ya ce.

“Mai Martaba ya ce sauran za su iya kama hanya yanzu kai kawai zaka tsaya sai jibi
za mu koma”

“An gama Yarima, Allah ya ƙara maka lafiya”

Be amsa ba sai kawai ya maida hankalinsa kan titi. Can kuma ya kalli agogo
hannunsa.

“Yaushe zamu isa Kaduna?”

“Allah ya taimaki Yarima, nan da minti goma sha biyar zamu isa”

Daga nan be sake cewa komai ba har suka isa masaukinsa. Su suka buɗe masa mota ya
fito suka rufa masa baya suna masa kirari, iya ƙofar falon suka tsaya. Sai ya juyo
ya kalli Sadauki ya ce.

“A ba ko wannensu 30k kai kuma ka shirya anjima zamu je mu duba marar lafiyar nan”

“An gama Yarima, takawarka lafiya ɗan sarki jikan sarki, an gama ɗan adalin Sarki”

Sai da ya shige sannan suka janyo ƙofar suka rufe masa. Alkyabar jikinsa ya fara
cirewa sannan ya buɗe maɓallan rigarsa, ya kishingida saman kujera, ya lumshe ido.
Tun da ya shiga ciki be fito ba sai da aka yi kiran sallah magariba daman basu
baro zariya ba sai da aka yi la'asar.
Tare da Sadauki suka yi sallah a masallacin da ke kusa da gidan, sannan suka
nufo gida. A hanyar su ta dawowa ne Abdool yake masa jan kunne.

“Bana son abunda kake min, karka sake ɗauko min takalmi ka aje min, kuma daga yau
kar na sake jin wani kirari nawa a bakin ka, ka kira ni da Abdool kawai ko Yarima
amman ba sai ka min kirare ba”

“Allah ya taimake ka za a daina”

Ya faɗa cikin girmamawa.

“Zaka iya tuna inda muka je gidan mai Napep ɗin nan da muka kaɗe?”

“Allah ya taimake ka, zan gane”

“To za mu koma mu duba shi, akwai canji a hannunka ko? Zamu siya musu fruits”

“An gama Yarima”

“Zan shiga na canja sai muje”

“A canja da kyau ɗan Sarki, Allah yaja zamanin ka”

Kallo ɗaya Abdool yayi masa ya kauda ido yana girgiza kai.

******************
Bayan salla magariba Uwani ta shigo ɗakin ta kunna mata kendir, ta aje mata maltina
da Madara da kuma tea mai kauri, tare da biredi.

“Kuma ɗawainiya da ni na gode sosai”

Mirmushi Uwani ta yi

“Ba komai ai yi ma kai ne. Ki ci dai ki samu karfin jiki”

“Ni kaina ina son na samu ƙarfin jikin ko zan samu damar komawa gurin iyayena”

“Tafiya za ki yi?”

“Gobe na ke so idan Allah ya yarje min”

“Amman ina laifin ko nan da sati idan kin ƙara jin sauƙi?”

“Wata ƙila idan suka ga na samu sauƙi su ƙi karɓa na, amman ganina a hakan zai sa
su tausaya min”

“Amman dai da kin yi haƙuri har ki ji sauƙi”

“Ina son tafiyar ne”

“To bari na faɗawa Neina”

Ta juya cikin rashin jidaɗi dan yanzu sun ɗan fara sabawa da Namra, zancen
tafiyarta be mata daɗi ba.

“Neina wai kin ji Namra zata tafi”

Abunda ta fito tana faɗa kenan, ganin Yarima yasa ta yi saurin sadda kanta ƙasa
jikinta ya shiga rawa.

“Barka da dare”

“Barka...”

Ya amsa kaɗan-kaɗan yana tsaye kan Lamido, dan ya kasa zama tun da ya shigo gidan
yanzu ma ya samu kansa da ƙyamar gidan. Farar shadda dake jikinsa sai ƙara haska
shi take. Uwani ta yi mamakin ganin sa ba dogorai, sai dai haka be hana ta gane shi
ba.

Unƙurawa Lamido yayi ya tashi zaune daga kwance da yake, dan zuwan Abdool be sashi
ya ɗago ba duk da cika masa ido da yayi, da kuma kwarjinin da ya yi masa, yana jin
rashin sakewa da Abdool wata ƙila saboda ba matsayin ɗaya ba, ko kuma dan kaɗewar
da yayi masa ne ya hana shi ganin farinsa sai haushinsa yake ji. A ƙoƙarinsa na
avoiding ɗin Yarima ya kalli Uwani da Neina ya ce.

“Wani abu aka mata ne?”

“A'a wallahi sai dai ko ta gaji da zama ne, ko tana son ta koma Katsina ne”

Cewar Neina. Sai Uwani ta amsa da

“A'a wai ta ce tana son ta koma gida ne, ko zasu tausaya mata su karɓe ta, kuma wai
gobe zata je, kamar wace ake kora”
“Amman Namra bata da tunani, taya zata koma gurin iyayenta cikin wannan hali?”

“Wlh kuwa, ni ma na ce ta yi haƙuri dai har gaba...”

Tsawa Sadauki ya katsawa Uwani, wanda shi kansa Lamido sai da ya zabura balle kuma
Neina da daman jikinta rawa yake, ganin ɗan sarki tsaye a gidansu.

“Ke ƴar talakawa ba a wata magana a gaban Ɗan Sarki, kama kan ki ki iya bakin
ki...”

Sosai Uwani ta shiga natsuwarta tsabar tsoro ma har ji tayi kamar ta amayar da
hanjin cikinta. Abdool kuma wa watsa ma Sadauki Harara, dan sosai yake jin daɗin
maganar da suke, sarau zuciyarsa ta raya masa da Namra ake, duk da bashi da
tabbacin hakan.

Tsawar da Sadauki yayi ma Uwani ne yasa Namra ta san da akwai baƙo a gidan dan ta
ji muryar da ba ta ɗan gidan ba. Hakan yasa ta aje maltinar dake hannunta, ta gyara
tsawyuwar Hijabin dake jikinta ta leƙo ƙofar ɗakin.

Bata gane ko waye ba, bata kuma ta mu da ta sani ɗin ba, sai kawai ta juya ta koma
ɗakin. Shi kam Abdool sarai ya gane ta, dan ya daɗe da haddace fuskarta, duk da
duhun magariba ya fara saukowa hakan be hana shi gane ta ba.
Ya daidaita tsayuwar hannayensa da ke cikin aljihu, ya juya ba tare daya ce da su
komai ba, sai sadauki ne yake musu Allah ya ƙara lafiya, duk suka amsa da Ameen ban
da Lamido.

Be yarda yayi ma Abdool kallon banza ba, ko wata yassar magana sai da ya juya baya
ya fice.

“Wani zai nunawa isa, girman kan tsiya”

“Aa Lamido karka jawa kanka, dan Allah ka iya bakin ka”

Neina ta faɗa zuciyarta cike da tsoro. Wani wawan tsaki Lamido yaja ya wuyar da
fuskarsa zuwa ɗakin da Namra take ciki.

**************

Tafiya yake guda guda yana tsotsar bakinsa kamar mai shan minti. Jinginawa yayi da
motar da suka zo, yana kallon Sadauki yana tsaya gefensa cike da ladabi.

“A bincika min baƙuwar fuskar da take gidan nan, wacce ta zo daga Katsina i can't
recall her name amman ai ka ji yarinyar da suke magana akai ko?”

“Za a bincika, Allah yaja zamanin ka, ya ƙara maka lafiya”

Wannan karon Abdool da kansa yayi driver zuwa suka ɗauki hanyar masaukinsa, sai
tariyar maganar su Uwani yake, yana analyzing.

ASIM POV.

Ledodin dake hannunsa ya dire mata yana sauke gajiya tare da miƙa mata ragowar
canji.

“Yayi Kyau Asim kana ƙoƙari sosai. Ya kamata ka hutu kam nima zan je gida na da
yake can cikin gari dan yata zata zo, kuma bata san ina wannan sana'ar ba, dole
acan nake sauka idan zata zo, dan haka zaka yi hutun kwana biyu sai kaje gurin
matar ka ku yi murnar mota ka ɗauke ta kuje gari ku shana”

Ya ɗan yi murmushi tare da sosa kansa, shi kansa ya jidaɗin wannan hutun da zata ba
shi dan zai bashi dama ya je gurin baƙuwarsa, kuma daman can yana son ɗaukar
Mardiya su fita gari.

“Ai bana da mata Hajiya bana da mata yanzu, ina dai kam nema”

Ta masa kallon rashin fahimta.

“ Kamar ya ba nasan kana da mata ba ada?”

“Eh mun ɗan samu matsala ne, har mun rabu ai”

“Subhanalillahi, kai kam Asim me ya kai ka?mata mai haƙuri da juriya haka? Me ta
maka”

“Wlh Hajiya ta cika kwaɗayi ne, ga complain akan aiki nan, shiyasa kawai naga
rabuwar ta fi, yanzu dai wata na ke so idan Allah ya yarda”

Idan ran Hajiya Sadiya yayi dubu ya ɓace a yanzu dam bata jidaɗin maganar nan ta
Asim ba

“Amman Wallahi sam ba ka yi tunani ba, taya zaka sakin matar da ta rufa maka Asiri
har haka, ka gaggauta mayarda matar ka matuƙar tana son mu shirya da kai, ni bana
son ana ciwa mace mutuci”

“Wallahi Hajiya bana jin daɗin zama da ita ne, duk ita ce silar halin rayuwar dana
shiga, sam arziki na da nata be haɗu ba, daman can ban yi istiƙara ba na aure ta,
yanzu muna rabuwa komai nawa ya dawo daidai, arziki sai shigowa yake”

“Na dai faɗa maka, rufin asirin ka ka maida auren ka a yanzu duk inda matar ka take
ka yi gaggawar mayar da ita shine kwanciyar hankalin ka, kaje ka yi tunani, ni sam
bana son ana wulaƙanta mace akan aure, to kacewa iyayenta me? Sam dam baka da
tunani Asim, idan ma akan aikin ka ai da ka yi sahawara da ni dole za mu samu
mafita yadda za'ayi”

Miƙewa ta yi tsaye cike da ɓacin rai ta nƴfi ɗakinta. Shi kam Asim da kallo ya bi
ta yana mamakin yadda ta haƙiƙan akan Namra kamar wata ƴar'uwata, tunani yake yi da
ace ya fada nata gaskiyar rabuwarsu da Namra akan ciki ne wata ƙila ma ranta ya fi
haka ɓaci.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *68 NOT EDITED*

Ta ina zai fara neman ta? Taya ma zai je neman yarinyar da yake ganin rabuwa da ita
kamar ya huta da ƙaya ne?

“Zata dawo, na san bata je gidan su ai da yanxu an kira ni, amman na san zata dawo
gare ni dole, amman neman ta yanzu a gare ni ai aiki ne sabo, kuma zata jidaɗi
sosai idan har na neme ta”

Abunda yake faɗa kenan yana tuƙa motarsa a hankali. Wayarsa ce ta yi ringing, da
sauri ya ɗauka ganin mai kiran har da murmushi a fuskarsa.

“Hello Babe”

“Hey how are you?”


“Fine i'm just thinking of you”

“Kar ka damu ai gobe za mu haɗu, zaka gan ni a fuska nima na gan ka a fuska”

“I can't wait, me kike so a shirya miki?”

“Na yi waya da Mom nawa zata shirya min komai”

“Ya yi kyau lallai Mom tana ji da ƴar nan ta ta”

“Ai dole ta ji da ni, ni kaɗai gare ta, ko ƙawaye na ma Mom son su take balle kuma
ni”

“Wow kai lallai ko zata so miji ki ma sosai”

“Sosai ma”

“Gaskiya na yi sa'ah”

“Sa'ah?”

“Eh mana, ai kin san dole Mom ta so ni sosai, to da ni mijin Nably ne right?”

“Uhnn. Yeah”

“Ko dai ban kwanta miki ba ne?”

“Idan baka kwanta min ba, ai ba zan tsaya ina baka lokaci na ba, ni fa ban ma yarda
da rayuwar social media ba amman kai lokaci ɗaya ka shiga rai na sosai wallahi”

“Haka nake so kin san ni da gaske na ke yi wallahi auren ki zan yi matuƙar kika
amince min”

“Wannan maganar ya kamata sai idan mun haɗu tukuna mu yi ta”

“To na bari gimbiyata”

“Zan duba abu sai na kira ka”

“Okay i love you”

“Thank you”

Daga haka ta katse kiran. Shi kuma ya mannawa wayar kiss zuciyarsa cike da
farinciki dan har ga Allah yana ƙaunar Nabila, kuma ita yake fata ta maza matarsa
ta biyu.
Wani tsiririn tsaki ya ja lokacin daya isa bakin gate ɗin gidansa, cox he hate
one thing buɗe gate, gani yake a yanzu ya kamata ace buɗe masa ake, shi gaba ɗaya
gidan ma ya ishe shi, plan ɗinsa a yanzu na samun sabon gida ne mai rai da lafiya,
gidan da duk wanda ya kallesa sai yayi magana ba wannan ƙonanne ba.
Sai da ya fito ya buɗewa kansa gate ya shiga da Motar sannan ya dawo ya rufe
gate ɗin. Kusa da BQ ya faka motarsa, ya faka motarsa ya buɗe ya fito, daga
shigarsa cikin ɗakunan da suke BQ ɗin sai ya fara ya ƙuna fuska, like yana ƙyama,
gurin duk ya yi datti kamar be taɓa zama a gurin ba. Da shigarsa ɗakin first thing
da ya fara yi ɗauko murhun gawaye da ragowar gawai ɗin da Namra ta bari, ya zuba
masa kanazir ɗin da Namra take kunna wuta da shi ya saka kofinta na roba na ƙyasta
ashana, nan ta ke wutar ta kama, kamar an saka mata hetur.
Ƙamin tukunyarta ya ɗauka ya ɗauraye ya zuba mata ruwa, ya ɗora saman wutar
sannan ya shiga ciki ya ɗauki tsintsina ya share ɗakin tsab kamar mace, ya ruba
zuwa yayi mopping, sannan ya cire tufafin jikinsa ya ɗaura tawul, ya zo ya zube
ruwan a roba ya sirka da ruwan sanyi, ya kai ɗaki.

Sai da ya tura kofar ɗakin, sannan ya cire tawul ɗin jikinsa ya zauna cikin
robar, kamar wani ƙaramin yaro. Ƙasansa yake gasawa, dan har yanzu zafi yake masa
duk da ya sha magani, kuma yana kan sha, amman gurin na masa zafi musamman idan zai
duƙa ko kuma zai yi bayan gida.
Sai dai Hajiya ta faɗa masa dan yana sabon shiga ne da ya saba komai ba zai ji ba.

Ya samu kusan minti talatin a cikin ruwa, sannan ya tashi ya ɗaura tawul ɗin ya
ɗauki ruwan ya zubar a can waje. Be da mu da ƙorar da tufafinsa na ɗazu suka yi ba,
ya ɗauke su a haka ya saka, ya kwanta saman katifa, yana danna wayarsa.
Number Mama ya saka, duk da yana da ita a contact ɗinsa be tsaya nema ba sai
kawai ya saka ya danna mata kira.
Ta daɗe tana ringing kamin ta ɗauka tana masa complain

“Ai na ɗauka na manta da ni, ka sake wata uwar”

“Hahha Mama kenan ni na isa duk duniyar nan ai bana da uwa kamar ki”

“Amman Ibrahim ace ko ɗan kiran nan na waya babu, babu aike, babu komai, daga na yi
jinyarka ka warke shikenan Namratu ta karɓe min kai?”

“Wallahi Mama kina nan cikin rai na, kawai dai akwai irin da na ke ne, akwai kuɗin
da nake jira ina son da na zo zan siya miki gida na nema miki mai aiki, na saka
miki komai ba za ki nema ba”

“Ibrahim da gaske?”

“Wallahi Mama”

“Wane irin kuɗi ne wannan? Karka ka jefa kan ka a halaka, garin neman gira a rasa
ido, zamani ya lalace tsafi ya yi yawa”

Dariya ya yi dan yasan abunda Mama take tsoro, kamar kar ace tsafi ne a bada ita.

“Ba tsafi na ke ba, kuma ko tsafi na ke ai ba zan bada ke ba, wannan matar data
ɗauke ni aiki ce take ba ni kuɗi kuma kullum idan na mata ciniki a shagonta riba
uku ake kasawa ita da biyu ni da ɗaya”

“Wane irin sana'ah ne haka?”

“Wayoyi ne mu ke sidawa, da zinari”

“Hahaha Mashallah, ka ga abun Allah ko? Sannu-sannu sai ka fi haka ma, ai ina nan
ina maka addu'ah indai kuɗi ne suna nan zuwa”

“A cigaba da yi mana addu'ar nan ai ita cw ke bin mu. Nan da wata ɗaya zan zo gurin
ki”

“To Allah ya yarda, ya dafa maka, ɗan Albarka, irin alheri”

Dariya ya yi kana ya ɗora da.

“Zan aiko miki kuɗi ta hanyar Yusufa, zai kawo miki dubu dari da hansi ki riƙe
kamin na zo”

“Kai Alhamdulillah Ibrahim Allah ya biya ka yau ɗa na ne yake ba ni wannan kuɗi


Allahu akbar...”
Sai kawai ta sa kuka. Shi kuma ya kashe wayar yana dariya, da ganin kuɗin a gare
shi yanzu ai ba wani abun ba ne, he past that level, manyan su ma yake hange, he's
feeling so high.

KALSOOM POV.

Life goes on yadda take tsammanin rayuwa ba haka ta zo mata ba,tana iya ƙoƙarinta
wajen ganin ta kwamtar da hankalinta, 5ana koyar yadda zata yi rayuwa babu abokin
rayuwarta, but she can't duk abunda take tunanin sauƙi ne a gareta, sai ta ga ba
haka ba.
Duk lokacin da tayi unƙurin danne abunda yake zuciyarta, ta manta da komai, sai
ta kasa. Sai yanzu take gane aure rahama ne dan har ta manta da ɗan zaman da tayi
na budurci a gidan, sai take ganin kamar yanzu ne ta ke koyon komai, ga maganganun
mutane su na ta kai kawo a kunenta, wai ta kashe aurenta ta dawo gida, some people
be like daman can irin wayayun ƴan bokon nan basa zaman aure, wasu kuma wai ta
kashe ɗan kishiyarta mijin ya sake ta, maganganu dai kala-kala har da na fitar
hankali.

Abincin da ta ɗibo ta saka a gaba tana kallo, ta san dai ba iya ci zata yi ba, dan
ba ta jin cin komai ga kuma yunwa tana ji, kusan kullum haka take wuni, ta fi son
abu mai ruwa sai kuma ɗan furau-furau, wannan abincin ma Momi ce ta cilasta mata
ɗibowa wai ko zata iya ci, amman ta kasa.

Ɗaukar abincin ta yi ta nufi falo da shi, da zimmar kai wa kitchen.

“Ba ki ci abincin nan ba ko?”

Cewar Momi da ke zaune saman kujera.

“Wallahi Momi ba na zan iya ci ba”

“Sai yaushe za ki cirewa kan ki damuwar nan ne Ummu?”

“Momi dole na damu, ki duba ko abunda abunda mutanen unguwar nan suke cewa, wai na
kore uwar gidana na kashe ɗan ta, ni wallahi da na san haka auren mai mata yake da
ban aureshi ba, ni da ma na san haka rayuwar auren ta ke tun farko da ban yi ba”

Ta ƙarasa zancen da kuka. Ajiyar zuciyar Momi ta sauke.

“Na san ba abunda mutane suke cewa ba ne ya fi damun ki, hukuncin da mahaifin ki ya
yanke ne ya hana ki sakewa, ina son ki san be yi hakan dan ya cutar da ke ba, sai
dan nema miki yanci, ba wai dan ya shiga tsakanin ki da Hilal ba”

Hawayen idonta ta share, ta aje plate ta zauna.

“Ba wai rai na ya ɓace ba ne da hukuncin Dady ,kawai abun yana damu na ne, duk duk
yaushe na yi auren nan yanzu ace har na dawo gida, a can gidan auren ma ba wani
daɗi na ji ba, matar nan ta hana ni sakewa, ta bi ta fitine ni bayan fitar ta kuma
kishi ya koma tsakanin ni da ƴarta, wallahi yaron nan ban san lokacin da ƴa ci guba
ba, amman sun ce ni ce na kashe shi, da wanne zan ji? Ga shi mahaifiyarsa ta sa ya
sake ni na dawo gida kuma mutanen unguwa sun ɗasa na su gulmar, dole na yi damuwa”

Da kuka ta ƙarasa maganar tana rufe fuskarta. Momy taja wani dogon numfashi ta
sauke tana kallon ƴarta cike da damuwa.

“Allah zai saka miki ai zalumci baya ɗorewa, gaskiya zata bayyana sakamakin ki zai
fito, kawai ki cigaba da addu'ah kina faɗawa Allah buƙatar ki, zai yaye miki komai”
Kuka ta yi sosai, sannan t tashi ta nufi kitchen ta aje plate ɗin ta fito.

“Ko za ki je gidansu gidan Salma ki ɗan yi fira ko zaki rage damuwa”

Da to kawai ta amsa ma Momi ta nufi bedroom ɗin ta, fuskarta ta fara wankewa sannan
ta ɗauki hijabi ta saka ta ɗauki jakarta, ta fito.

“Na tafi”

Ta faɗa murya can ciki.

“Sai kin dawo ina a gaishe ta”

A hankali ta fito daga gidan, tana.fitowa gate ta yi sa'ar samun Napep kasanceqar
an sauke wata ne gidan da ke kusa d na su, tara kawai ta yi ta shiga tana faɗa
masa ind zai kai ta.

“Sauke ni a nan”

Ta faɗa tun kamin ya ƙaraso kusa da gidan Salma. Naira ɗari ta miƙa mas sannan ta
fita daga napep ɗin ta ƙars da ƙafa.

Tun da ta hango gate ɗin buɗe ta fahimci Salma zata fita ne.

A hankali take tafiya har ta ƙarasa harabar gidan. Lokacin da ta isa ƙofar falon
si t ki hannu zta buɗe sai ga Mijin Salma ta buɗe ya fito. Ja ta yi da baya tana
ƙirƙiro murmushi, tare da gaishe shi, shi kuma ya amsa mata yana gyara hular kansa.

“Lafiya ƙalau Kalsoom ce a gidan na mu!”

“Eh wallahi yau na ce bari na leƙo Salma ne”

“Ayyah gashi bata gida Wallahi ta je suna”

Juyawa ta yi tana faɗin

“Okay idan ta zo a gaishe ta”

“Wuce wa za ki yi?”

“Eh”

“Bari na sauke ki mana, nima fita zan yi”

“A'a zan hau Napep”

“Haba di Kalsoom sai ka ce baƙuwa”

Yayi saurin ƙarasawa gurin motar ya buɗr ya shiga yayi mata key, sannan ya buɗe
mata front seat.

“Bismillah”

Bata kawo komai a ranta ba, ta shigaotar tare da mai da ganbun ta rufe.

Tun da suka hau titi bw ce da ita komai ba, ita kuma t tattara duka hankalint tmaid
gurin titin. Can ya kai hannu ya kunn fm, sai ya ɗan kalleta kaɗan.

“Kalsoom na ji abunda ya faru kuma sam ban jidaɗi ba, amman ki bar wa Allah komai
xai fito miki da haƙƙin ki, ai duk wanda ya san wacece ke ba xai yarda kin aikata
ba, wallahi tun da na ji labarin kika ban tausayi sosai, inshallah zaki samu wani
na ƙwarai”

“Ai be yarda na aikata ba, laifin mahaifiyarsa ne ita ta saka sai ya sake ni”

Wani guntun tsaki yaja.

“Shi ma dai da laifinsa, ai ba a bin umarnin iyaye a saɓawa Mahalicci, dan wannan
saɓawa Allah ne, ni da zaki bi shawara ta da kin bar shi kin fita harkarsa ko da ya
dawo, duk da n san kina son sa sosai, amman fa kin san mu maza ba a nuna mana so”

Ya ƙarasa maganar tare da parking a bakin gate ɗin gidan su. Buɗe motar ta yi ta
fita tana faɗin

“Na gode”

Ba ta jira ya amsa mata ba, bata kuma waigo ba, shi kuma be bar ƙofar gidan ba sai
da ya ga ta shige sannan ya kaɗa motarsa yayi gaba.

ABDOOL POV.

Lemun d ke hannunsa ya aje yana murmushi

“Amman dai Ummi idan ban kira ba ai kamata ki kirana ni kiji ko lafiya”

“Ai na san lafiya, da ba zaka yi shiru haka nan ba, kasa muka shirya maka abinci
amman baka zo ba”

“Amman ban ce amin komai ba, indi ba neman a ɗora min laifi ba”

“Yayi kyau, gobe kaga mai sake maka, faɗa min me ya hana ka dawowa jiya?”

“Kawai ina son ƙara ganin garin ne, kin san na daɗe rabona da Kaduna”

“Yanzu yaushe zaka dawo?”

Ya ɗan sosa kansa

“Uhhhh Maybe laraba”

“Allah ya kai mu”

“Amin thank you Ummi”

Ta katse kiran shi kuma ya sauke wayar cike da ƙaunar mhaifiyarsa.


Juyawa yayi ya kalli Sadauki.

“Je ka shigo d shi”

Da sauri Sadauki ya tashi ya fita, Abdool kuma ya ƙarasa gurin window falon yana
kallon wani ɓangare na gidan.
Tare suka shigo da Sadauki, bakinsa ƙumshe da sallama. Juyowa Abdool yayi
fuskarsa ɗauke d murmushi ya nunawa Mustafa gurin zama. Ba musu Mustaf ya zauna
yana miƙa masa gaisuwar girmamawa.

“Lafiya Ƙalau sannu, ya Sunan ka ma?”


“Mustafa”

“Yeah, ka san ni ne?”

“A'a Sai dai na ga fuskar sani”

“Ina son zan baka wanki ne da guga ance kana yi da kyau”

“Ƙwarai ko ai sana'a ta ce”

“A ina kake da zama?”

“Nan unguwar malamai”

Abdool yayi wani abu da kai kamar da gaske he know him.

“Yeah na tuna kai na na kusa da gidan su Lamido ko?”

Mustafa ya washe ba ki jin an ambaci sunan abokinsa.

“Ashe kasan lamido”

“Sosai ɗan'uwan mu ne, ai kwana ki ma wata ƙanwata a gidan ta sauka, yanzu haka
wata ma tana nan”

Abdool ya faɗa yana kallon Saɗauki.

“Je ka haɗo masa kayan wanki”

Sai kuma ya mai da hankalinsa gurin Mustafa.

“Ance min yaji ciwo ma ko?”

“Eh Wallahi, wani neya kaɗe shi, ni da yake bana nan sai da y kira ni na ke ji ma,
Ai Allah ma ya tsare abun ya zo da sauƙi”

“Idan na samu dama zan je na duba shi”

“Aiko masu kuɗi fitar ku wuya ta ke muku”

Abdool ya ɗauki remote ya canja channel yana hamma kamar gaske.

“Mu ai har zama gidan mu na yi, baka ga baƙuwar fuska ba?”

Mustafa yayi shiru dan ya gano kamar yana bincikensa ne.

“Ina kayan su ke ne?”

Abdool yayi masa wani kallo.

“Za'a kawo”

Sai ga Sadauki ya fito da tufafin da basu fi kala huɗu ba, ya miƙawa Mustafa. Shi
kuma yana karɓa y miƙe tsaye. Sai Abdool ya zaro sabin kuɗi a aljuhunsa ya miƙa
masa.

“Gashi ko, a wanke da wuri”


Da mamaki Mustafa ya karɓa ganin kuɗi haka da yawa.

“Na gode Allah yasa albarka, gobe zan kawo maka su”

Murmushi kawai Abdool yayi masa as respond, ya bishi da kallo ya har ya fice.

‘Duk wannan ba zai yi ba, kawai naje na samu yarinyar nan na yi magana da ita kawai
shi ya fi’

‘Idan kuma ta ƙi ta saurare ni fa?’

Ya ɗaga kafaɗunsa yana cigaba da zancen zuci.

‘Sai na ƙyale ta, ta yi ma kanta’

Miƙewa yayi tsaye ya nufi bedroom ɗinsa.

RASHIDA POV.

HILAL POV.

Yana tsaye jikin motarsa, yana kallon takunta har ta ƙarasa kusa da shi.

“Assalamu alaikum”

Ya faɗa cike da tsananin kunya da tsantsandar da kai.

“Wa'alaikissalam, Teema ko?”

Ta ƙara yin ƙasa da kanta

“Haka ne ina wuni?”

“Lafiya ƙalau ya gida?”

“Lafiya ƙalau”

“Mashallah, sunana Hilal kamar yadda aka faɗa miki Hajiyata ta ce min ta miki
bayanin komai, zan zo mu gaisa da ke ne”

“Haka ne, ni kuma sunana Fatima Abdullahi, a nan nake zama ina ƙarƙashin iyayena”

“Mashallah haka yayi kyau”

Ya faɗa 6ana kallom yadda ta zuba hijabi har ƙasa gwanin sha'awa.

“Ba zan tsayar da ke ba, daman na zo ne kawai mu gaisa duk wani labari kamata yayi
sai idan mun sake haɗuwa ko”

Murmushin jin kunya tayi ta ƙara ƙasa da kanta.

“A gaida min Hajiya”

“Zata ji”

Ya buɗe motar ya ɗauko ƴar siyayyar da yayi mata ya miƙa mata.


“Ga wannan”

Sai a lokacin ta ɗaga kai ta kalleshi, sai ta yi saurin girgiza masa kai.

“A'a na gode”

Bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta nufi cikin gidansu da sauri dan kar ta karɓi
kayan. Shi dai da kallo ya bita fuskarsa ba yabo ba fallasa har ta shige sannan ya
ƙarasa gaban ƙofar ya aje mata ya juya.
Cikin wani yanayi ya shiga motarsa ya bar gidan. Har ya isa gidan Hajiyarsa be
wani sake jiki sosai ba, shi kansa be san dalili ba, yana jinsa dai kamar cikin
wani sabon yanayi.

Da far'ah Hajiya ta tarbesa dan tasan inda ya fito tun da ita ta haɗa masa abunda
zai kai mata ma. Bata bari sun yi maganar a falo ba, har sai da ta shiga ɗakinta
shi kuma yana biye da ita, bayan ta zauna, ya zauna y soma labarta mata yadda suka
yi, farinciki duk ya cika Hajiya.

“Ai yarinyar akwai kirki ga mutunci, ina fatar dai ta maka”

“Ba laifi, umarni nake bi ai”

“Hilal bana son kana abu kamar ina tirsasa ka, ni sam....”

Shigowar Dadyn Hilal ne yasa ta maƙale maganar bata fito ba.

“Amman bn taɓa sanin baki da hankali ba, sai yau, ki kashe mas aure ki sashi neman
wani aure? Bayan kin san yana son matarsa? Dan me zaki shiga tsakaninsu? Idan ma
aure kike so ai sai kice ya ƙara aure amman ba sai ya saki matarsa ba, ni duk
abunda ake ban sani ba, ban ɗauka abun har ya kai ga saki ba sai ɗazu”

Miƙewa tayi tsaye tana kallon Alhaji da ransa ya gama.ɓaci.

“Haba Alhaji, baka ga abunda yarinyar nan ta aikata ba ne? Zata iya kashe yaran
nan, shi kansa ma”

“Shi be fiki sanin zafin yaransa ba? Be fiki damuwa da kansa ba? Kar wannan maganar
ta sake fitowa bakin ki, idan aure kike so ya ƙara wannan daban amman babu yadda
zaki shiga tsakanin shi da matarsa”

Hilal dai be ce Uffan ba har sai da Alhaju ya kallesa ya ce

“Tashi muje gidan su”

Miƙewa yayi tsaye ya bi bayan Alhaji da ya kaɓa rigarsa ya wuce, Hajiya ta saki
baki tana kallon ikon Allah.

“Wato maganin yanzu har da ubansa ta yi ma, tayi min ta ga ni be kama ni sai ta
koma ga ubansa, to wallahi ni ba ki isa ba, kurwata kur kashede uku lahaula bakwai”

Cikin fushi ta yi furucin tana jin tsanar Kalsoom a ranta.

MARDIYA POV.

Fisgice ta farka tana faɗin

“Innalillahi”
Mafarkin wutar nan da ke zo mata jifa jifa yau ma ta sake yinsa, bama kamar yanzu
da har bayanta zafin gaske yake mata kamar ta tsaya kusa da wuta. Sai da ta karewa
ɗakin kallo sannan hankalinta ya kwanta ganin inda take.

“Allah ka min maganin wannan masifar, ko minene yake bi na Allah ka kawar mon da
shi, idan ma wata jifar ce aka min Allah ka mayar da ita ga wanda yayi ta”

Har da kukanta take wannan maganar dan har ga Allah wannan mafarkin wutar da take
ya isheta, kuma ya hanata sukuni.
Kasa komawa bachi ta yi daman duk ranar da ta yi irin wannan mafarkin bata iya
komawa bachi, idonta biyu har aka kira sallah asuba, amaimakon ta bari sai ta yi
sallah sannan ta kwanta sai kawai ta buge da bachinta, ba ita ta farka ba sai sha
ɗaya na safe, ƙirƙiri ta yi sallah azuba babu ko kunya, ko da yake abun ya samo
asali ne daga gurin mahaifiyarta da bata tsawata mata.

Tana sallame sallar wayar Asim ta shigo mata, da sauri ta ɗauka tana kwabar da
tasbihin da take.

“Hello”

“Good morning Mardiya ya kika tashi?”

“Lafiya ƙalau na yi missing ɗin ka”

“Nima Haka har na so na ɗauke ke ki muje yawo dan akwai maganar da nake son mu yi
mai muhimmanci”

“Wace magana ce?”

“A'a ba za tayi a waya ba, kamata yayi sai mun zauna”

“Okay yaushe zaka shigo?”

“Idan na samu time zan kira ki, sai na zo na ɗauke ki”

“Okay ina jiran ka”

Daga haka ya kashe wayarsa, ita kuma ta miƙe tsaye cike da jindaɗi ta nufi waje dan
ɗibar neman mai siyo mata indomie.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *69*

Be ji zai iya kwana a yau ba,ba tare da yaje gurin Namra ba, daman yasan duk daɗin
bakin da yake yi ma Ummi ba wani barinsa zata yi ya daɗe ba, kuma idan har ta bar
shi Mai Martaba ba zai bar shi ba, and what's on his mind nowa ya ji labarin
yarinyar duk da bashi da tabbacin ko zata yarda ta saurareshi ma.

Miƙewa yayi tsaye yana duba shaddar da ke jikinsa.

“I really need to do this, ko zan samu peace of mind”

Closet ɗinsa ya buɗe ya fiɗo wata kafirar shadda golden color, ya buɗe ɗayar
wardrobe ya ɗauko hular ƙobe ya aje saman shaddar, sannan ya shiga Bathroom ya
watsa ruwa.
Bayan ya tsane jikinsa da tawul ya shafa mai, sannan ya saka body spray, ya saka
short da white singlet, sannan ya shafa wani turare, ya ɗauki shaddar ya saka.
Wani mai ya ɗauka ya shafa ma fuskarsa, sannan ɗora da turare. Ya ɗan soma jin
babu daɗi lokacin daya tuna gidansu Lamido zai je, yasan he has zero reasons to
hate Lamido, but he still hate him.
“Maybe he's bad person”

Ya faɗa yana murza wani turaren a wuyansa, kamin ya ɗauki hular ya saka a kansa.
Agogon hannunsa ya kalla, yaga tara da kwata, hakan yasa shi ɗan hanzarin ɗaukar
wayarsa ya fice.
Sadauki na ganinsa ya tashi, sai Abdool ya ɗaga masa hannu.

“Ni kaɗai zan je”

“Allah ya tsare ya kiyaye hanya, Allah ya kare ka daga dukan ni abun ƙi, Allah yaja
kwanan ka”

Abdool be kula shi ba, balle ya amsa addu'ar da yake masa, sai da ya kawo gurin
motocin da suke harabar gidan sannan ya ƙwalama Sadauki kira, sai ga shi ya fito da
sauri.

“Key wacan motar na ke so”

Ya nuna masa wata baƙar mota mai baƙin gilashi, wanda ke aje can gefe. Da Sauri
Sadauki ya koma ciki ya ɗauko masa key ɗin motar ya miƙa masa, sai da ya sake duba
agogon hannunsa sannan ya nufi motar ya shiga, gabansa sai faɗuwa yake.

Sai da ya hau titi, sannan ya ciro wayarsa ya dannawa Ummi kira. Sai da yayi mata
one missed call sannan a na biyu ta ɗauka.

“Assalamu alaikum”

“Wa'alaikissalam. Ummi ki min addu'ah zanje wani guri neman abu a yanzu, kuma babu
tabbas zan yi nasara, idan kuma har na ƙyale abun hankali ba zai kwanta ba”

“Abdool mi zaka aikata? Thought baka aiki yanzu ka ce sun baka hutu?”

“Eh ba aikin office ba ne, wannan aikin nawa ne na sa kai”

“Abdallah karka aikata abunda zai sa rayuwarka cikin haɗari, ka dawo gida gobe”

“O my god”

Ya dafa kansa.

“Allah Ummi ba wani abun ba ne, kawai i need your prayers”

“Ka dawo gida gobe na faɗa maka, kasan dai kullum rayuwarka tana cikin haɗari ko?
Karka kuskura ka wuce gobe, umarni na ke baka”

Ta kashe wayarta cike da fushi, dan ta san idan ba haka ta masa ba, ba zai ji ba,
gashi duk ya tsorata ta, da wannan maganar na shi daman ita ba son take yana tafiya
nesa da ita ba.
Iskar bakinsa ya busar yana cigaba da tuƙinsa a hankali.

“Daga neman sa'ah sai kuma abu ya zama ɗan zane, ban san salon da ya kai ni faɗa
mata ba, Allah ka taimake ni”

Unguwar bata da kyau sosai, amman haka ya riƙa kunno kai cikinta yana kallon
ƙananan gidajen da suke unguwar har ya isa bakin ƙofar gidan. Wani tunanin ne ya zo
masa, sai kawai ya ƙara gaban da gida sannan ya faka motar, ya buɗe ya fito.

Ya samu minti salati tsaye a gurin sannan ya kira wani almajiri da ke bara ya nuna
masa gidan su Lamido.

“Je can gidan ka ce ana sallama da baƙuwa”

Sai da almajirin ya kama hanya, sai kuma Abdool ya kira shi ya dawo.

“Ba haka zaka ce ba, ka ce Abdallahi daga Katsina ya na sallama da Namra, Namra ko?
Yes Namra zaka ce”

“To”

Almajirin ya nufi gidan da sauri. Faɗuwan gabansa ya ƙaru lokacin daya fara tunanin
irin amsar da almajirin zai dawo masa da ita.

NAMRA POV.

Ba laifi yau ta dan sake bisa da jiya, ko dan yau sun ɗan tausasa ta ne kuma ta
wuni a tsakar gidan ansha fira da ita. Sai dai bata janye maganar tafiyarta ba, ta
yarda ta bari har sai nan gaba, idan ta ƙara jin sauƙi abubuwa sun ɗan dai-dai.

Yau ba iya Maltina da madara kawai Lamido ya bada aka siyo mata ba, har da
gasasshen nama, sai dai bata ci ba kasancewar komai bata jindaɗinsa a yanzu.
Sai da aka yi sallama magariba sannan ya bada aka siyo mata tea, yadda yake
damuwa ta ci abinci shi kansa be damu da ya ci abincin ba, sam mantawa yake da nasa
ciwon wata ƙila ko dan be jimu sosai ba, yake dauriya irin ta maza, ko kuma dan
hankalinsa ya ɗauko gurin Namra ne. Shi kansa yana mamakin yadda yake damuwa da
Namra, sai dai yana fi karkata hakan da tausayinta da yake, su kansu su Neina suna
kula da halin kuwalar da Lamido yake bawa Namra, duk da sun san halinsa na karancin
amman wannan kamar yana ƙoƙarin wuce guri, dan ko magana ake Namra ta saka baki
zasu ga ya tattara hankalinta ya miƙa mata ya natsu sosai yana saurarenta.

Yau Neina taja Namra da fira sosai musamman bayan Sallah isha'in nan, abinci na
fula take labarta masa da kuma al'adansu na fulani, a nan take taɓo labarin Baban
su Lamido da kuma ƙuruciyar Lamido, dariya sosai Namra take idan ana faɗin labarin
halin ƙiriniyar da Lamido ya yi. Shi kam iya karsa murmushi idan Neina ta faɗi wani
abun.

“Salamu alaikum, wai Abdullahi daga Katsina ya ce yana kiran Namra”

Dam dam dam, gabanta ya tsinke ya faɗi, duk wani farinciki da yake zuciyarta sai ya
ta neme shi ta rasa, a take murmushin fuskarta ya disashe. Da sauri ta kalli
almajirin dake tsaye can jikin ƙofar gidan yana jiran amsa.
Bata san ko waye ba, amman jikinta ya bata wani yanayi na daban, ga shi kuma anxe
daga Katsina, kuma an faɗi sunanta, lallai ko wanene ya santa. Sai dai ya akayi ya
san inda take zaune? Miyasa be zo da rana ba sai da dare? Shin waye Abdallah ma? Ko
dai Asim ne ya canja suna? Amman taya Asim zai san inda take?

“Ko mijin ki ne?”

Tambayar da Lamido yayi mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Kai
ta girgiza.

“A'a ba haka ne sunansa ba”

“Ɗan'uwan ki ne?”
Shiru ta yi tana tunanin irin amsar da zata bashi, idan har ta ce ɗan'uwanta ne
zata sanu damar fita ta ga ko waye ne, to idan kuma ya kasance Asim ne ya canja
suna fa?
Idan ma shi ɗin ne ai babu yadda zai yi da ni, dan yanzu babu aurensa a kai na,
idan kuma har aurensa ya zo maidawa to yayi satti, dan na cika idda tun da na yi
ɓari!

“Eh ɗan uwana ne”

Sai a sannan hankalinsu ya ɗan kwanta, Neiɓa ta ce da almajirin.

“Je ka ce tana zuwa”

Sai da almajirin ya juya sannan ta kalli Namra ta ce.

“Ɗauki fitila ki je”

Miƙewa tayi tsaye sai Lamido ya ce.

“Ya aka yi ya san gidan nan?”

“Ni na kwatanta masa, a waya”

Kai tsaye ta bashi amsar ta nufi fitilar ta ɗauka ta nufi ƙofar fita gabanta sai
faɗuwa yake. Sam Lamido be so ta fita ba, haka kawai ya samu kansa da rashin
jindaɗin kiran da aka mata duk da be san me kiran ba. Neina kuma ta kawo wani zargi
a ranta, dan tana ganin kamar Namra ta ɓoye musu wani abu ne.

Zuciyarta cike da tsoro ta fita daga gidan, da tunani biyu, Asim ne ko kuma wani
nasa yake mata sallamar. Bata ga kowa a ƙofar gidan ba, hakan yasa ta ɗan ɗaga
fitilar tana yade, hangota da ya yi yasa ya tako ya ƙaraso kusa da ita.

“Assalamu alaikum”

Ya furta nata cikin murya mai taushi, da sanyaya zuciyar mai sauraro.

“Amin wa'alaikassalam”

Ta amsa masa ba tare data wayence shi ba. Ya ɗan yi gyaran murya.

“Na san baki gane ni ba”

Ya fido wayarsa ya kunna fitar wayar ya haska fuskarsa. Wannan karon ba faɗuwar
gaba kawai Namra ta ji ba, har da tsoro, ja tayi da baya yana nuna shi da yatsa,
sai maganar ta naƙale ta ki fitowa.

“Nasan zaki yi mamakin gani na, amman ina son ki ba ni aron lokacin ki kuma ki
saurari abunda zan faɗa miki”

“Ba kai ba ne ɗan sarki daya kaɗe Lamido?”

“Ni ne, kuma na san ba a nan kika san ni ba, a Katsina ko?”

Kai ta ɗaga masa duk da bata da tabbacin zai ga hakan kasancewar akwai duhu a
gurin.

“Miyasa kake bibiyata?”

“Ba saboda ke na zo garin Kaduna ba, ke ma kuma ina da tabbacin ba dan ni kika zo
ba, amman zuciyata ta kasa natsuwa da hakan, direba ne ya kaɗe yaron gidan sai kuma
na gan ki a gidan shine abun yake bani mamaki, bayan nasan a Katsina na san ki”

“Ba wasu kalamai na ce ka min ba, amman bari na gargaɗe ka, karka sake zuwa ƙofar
gidan nan da sunan gurina ka zo”

Ɗan murmushin takaici da mamaki yayi.

“Babu mace da ta taɓa ɗaga hannu ta mare ni sai ke, babu mace da nake gani na
bibiya sai ke, babu mace da ta taɓa faɗa min irin wannan maganar sai ke. Zan bar
ƙofar gidan nan amman ina son ki faɗa min tsakanin ki da Allah kina da aure? Kuma
ina son ki faɗa min tsakanin ki da Allah waye Mahaifinki, kuma miye alaƙarki da
mutanen gidan nan?”

Wani haushi ne ya cika mata zuciya, har take jin kamar ba zata iya amsa masa
tambayoyinsa ba, amman Allah daya haɗa ta da shi ne take jin ba zata ɗaga daga
gurin ba har sai ta ba amsa.

“Ba na da aure, kuma babu wata alaƙa tsakani na da mutanen gidan nan, sunan
Mahaifina Manjo Usman Zamau”

Bata tsaya jiran Abunda zai ce ba ta juya ta shige ciki gidan. Shi har tsoro ta
bashi cox the way da take bashi amsar kamar tana masa faɗa.

“Wow”

Ya faɗa yana shafa fuskarsa, kamin ya zuba hannayensa aljihu ya nufi motarsa.

Sorry for the short chapter 🙏🙏🙏


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *70*

‘Manjo Usman Zamau, Manjo Usman Zamau’

Sunan yake ta maimaitawa, tana tunanin kamar ya san mai sunan amman ya kwanta masa,
sai dai jin Manjo ma ya tattabatar masa da soja ne.
Murmushi ya samu kansa da yi lokacin daya tuna wasu kalamai da Namra ta yi masa.

“She's so Unique”

Rage gudun da yake, ya fido wayarsa ya nemo number Sadiq ya aika masa kira. Ringing
ta yi sai da ta kusa katsewa sannan aka ɗaga.

“Shegen gari baka kira sai ta samu”

Ƙyalƙyalewa ya yi da dariya.

“Chief Sadiq Northwest”

“Au yau Chief na samu kuma? Kai dai faɗa min abunda yasa ka kira ni”

“Kiran ka kawai na yi na gaishe ka, ko kuskure ne kiran manya kuma?”

“Na ji, ya gida ya hutu, ku ai kun samu hutu”

“Gaskiya ba laifi, amman ba wani mai yawa ba ne, ina Madam”


“Madam na nan ƙalau go straight to the point miyasa ka kira ni?”

Dariya sosai Abdool ya yi kamar ba shi ba, sam ba zaka za ci akwai mutumen da
Abdool yake sakewa da shi ba, bayan mutanen gidansu.

“Kasan waye Manjo Usman Zamau?”

“Aha ni nasan akwai wata a ƙasa, ai baka kiran mutum hakan nan kawai”

“Ni dai amsa min kawai, ban ce ka min surutu ba”

“Na san shi, kai ma ai kasan shi, amman yanzu ya yi ritaya ai”

“Nima ina jin kamar na san shi amman sunan ya kwanta min”

“Ai mun yi zama barrack da shi ai, a Yola, shine mahaifin su Salwee and Abdulraman
na manta sauran ɗiyansa dai, yanzu ina jin yana sokoto zaune, ance ya zama babban
ɗan siyasa ma”

Abdool ya bugu sitiyari motarsa da ƙarfi.

“Yes I knew it!”

“Easy Man what happened to him?”

“Ba komai, kawai wani ɗan bincike na ke ne”

“Okay abokin su ekwieu ne tare suka yi aiki, suna shiri sosai”

“Amman kana da addireshinsa?”

“Kai Malam, tun da ba shi na ke wa aiki ba, haka kawai zan aje addireshinsa”

“Okay okay bye”

Sai kawai ya katse kiran zuciyarsa cike da farinciki. Wata number ya sake lalubowa
ya aika mata kira.

“Salim a bincika min addireshin Manjo Usman Zamau mai ritiya, kuma a bincika min a
cikin ƴaƴansa akwai Namra, aɗan min bincike akan ta”

Be jira abunda Salim ɗin zai bashi amsa ba ya katse wayar, dai-dai loƙacin daya
faka a harabar gidan. A yanayin yadda ya shigo cikin gidan ba zaka ce shine ɗazu ya
fita a haka ba, yadda ka san wanda aka yi bushara da aljanna haka ya dawo fuskarsa
a sake, zuciyarsa fari ƙal.

Yana shigowa falo ya zauna saman cushion yana kallo falon kamar wani baƙo. Kallo
ɗaya zaka masa ka fahimci yana ciki nishaɗi, dan hankalinsa ma baya gurin da yake
kallo. Wayar hannunsa ya kallo kamar mai son magana da wayar, sai kuma ya watsa
yatsunsa saman screen ɗin ya danna number Sadauki, bugu ɗa ya ya ɗauƙa.

“Sadauki ga ni a falo ina jiran ka”

Be jira abunda Sadauki zai ce ba, ya katse kiran fuskarsa shinfide da murmushi. Ba
ayi minti biyu ba sai ga Sadauki cikin falon da rawar jikinsa.

“Allah ya taimaki Yarima, Allah yaja kwanan ka, Allah ya baka abunda kake so”
Abdool ya kallesa fuskarsa da Murmushi.

“Amin Sadauki, addu'ah tana tasiri sosai, kaga Allah ya fara ba ni nasara. Yariman
ka ya kusa samun gimbiya”

Sadauki ya riƙe baki tare ta washe da dariya

“Mashallah, babban goro sai magogin ƙarfi, Allah ya taimaki Yarima, Mai Martaba zai
fi kowa jin farincikin wannan labari”

Abdool ya ɗan risino daga zaunen da yake

“Ya kake auna farincikin Mai Martaba idan ya samu labarin na samu matar aure?”

“Allah ya taimake ka kamar mutum ne, da yake cikin tsamman nin ƴanci, yake cikin
baƙin ciki da damuwa, ga yunwa da ƙishin ruwa ya dame sa, masaukinsa kuma babu
daɗin zama, me kake tsammani idan aka aka basa sabon masauki mai cike da ƙuramon
wanka, ga kuma abinci da abun sha, bayan kuma an ƴanta shi?”

Komawa Abdool ya yi dai-dai saman cushion ɗin ya ɗora hannayensa saman kushin ɗin
yana kallon silin.

“Zai kasance mai tsananin farinciki, har zai ji kamar ya haɗe zuciya ya mutu saboda
jindaɗi”

“Toh haka zuciyar Mai Martaba zata kasance matuƙar ya samu labarin Yarimansa ya
samu Gimbiya”

Murmushi mai ƙayatarwa Abdool ya yi, ba tare da ya kalli Sadauki ba ya ce

“Bana Sadauki da kai za'aje Umara”

Faɗuwa Sadauki ya yi yima Abdool godiya, yana zuba masa kirari, da yabo. Hannu
Abdool ya ɗaga masa alamar ya tashi ya bashi guri, haka ya tashi ya fice baki har
kunne tsabar murna da farinciki.

Sai da Sadauki ya fice sannan Abdool ya maida dubansa gurin wayar yana lalubo
number Mai Martaba. A handsfree ya saka wayar ya ɗorata saman center center tebur
ya nufi freezer ya bude ya ɗauko power horse, ya kai bakinsa.
Daga inda yake tsaye yana jiyo muryar Mai Martaba da yayi picking wayar tare da
sallama.

“Allah ya taimaki Mai Martaba, i have a good news for you”

“I have good news for you too Son”

“Amman nawa ya fi na ka daɗi, dan nawa idan ka ji ma sai ka bani goro”

“Nima ai sai ka bani goro ba kuma ɗan ƙarami ba ma”

“Me zaka ba ni idan nayi maka albishir da abunda ka daɗe kana jira”

“Zan baka yankin Bakori da kewaye, kuma za a naɗa ka motar Mai Martaba kai fa wace
kyauta zaka min?”

Zauna Abdool yayi saman kujera yana dariya har da buga ƙafa, ko ba komai Sarautar
da Mai Martaba ya ce zai bashi ta sashi dariya balle kuma yau yana cikin nishaɗi.
“Ni kuma bana da gumi na zaka je Ummara gaida Ubangiji”

“Lallai yau Ɗan Sarki yana ciki farinciki, ɗan tsakura min kaɗan daga cikin labarin
ka mana”

“ Ina ai ba tsakure, sai ga ni ga ka, gobe zan sauka sokoto cikin rahamar ubangiji,
kuma ba zan kwana ba, har sai na labarta maka abunda zan labartawa Ummi”

“Allah ya kai mu, ya dawo da kai lafiya”

“Amin ya Rabbi. Na gode Mai Martaba, mu kwana lafiya”

Daga haka suka yi sallama, sai Abdool ya ɗauki wayarsa ya nufi bedroom yana kalle
kallen gidan kamar yau ya fara shigo shi.
Bayan ya rage tufafin jikinsa ya aika ma wani yaronsa saƙo. Akan ya nema masa
jirgin da zaije Katsina gobe.

Bayan kamar minti goma sha biyar yaron yayi masa reply da akwai wanda zai tashi da
safe zuwa Katsina.
Daga nan Abdool ya aikama Sadauki da text na maganar tafiyarsu gobe gida, akan
yayi duk abunda ya kamata cikin lokaci, duk da be so hakan ba, sai dan Ummi da
ranta ya ɓaci.

NAMRA POV.

Da tunanin abunda zata faɗa ma su Neina ta shiga gida, a ɗayan ɓangaren kuma tana
tunanin bibiyar da Abdool yake mata. Babu abunda ya fi tsaya mata a rai kamar
tambayoyin da ya yi mata.

“Har ya tafi?”

Tambayar da Neina ta yi mata ya firgita ta, har ta zabura, sam bata san ma ta kawo
kusa da su ba.

“Eh ya wuce”

Karaf idonta cikin na Lamido da ke dannar waya, kasa kawar da idon ta yi, shi ma
kuma ya kasa janye nasa, suka yi ta kallo kallo ita da shi, har sai da Uwani ta
maimaita tambayar da take mata.

“Na ce shi ne wanda kika sani ɗin?”

Sannan ta lumshe ido, tana sauraren bugun zuciyarta. Kamin daga bisani ta buɗe idon
dake cike da hawaye ta kaɗawa Uwani kai alamar ‘Eh’ ta wuce ɗaki.
Samun kanta ta yi da kuka marar dalili, wani abu take ji yana ratsa mata zuciya
mai wuyar fassara, numfashi take da ƙarfi kamin ta samu saita kanta, ta numfasa a
hankali tana gode Ubangijinta.

Abdool ya tsaya mata a rai, tambayar ina ya fito ina zaije ya hana ta sukuni, wace
manufa yake da ita akanta, shi ya hana ta rumtsawa har dare ya raba.

RASHIDA POV.

Hawaye ne suke mata masu zafi sosai suke mata zuba, keys ɗin dake hannunta take ta
juyawa, tana mamakin irin abunda iyayenta suka mata.
‘Ashe akwai ranar da iyaye suke tsanar ƴar cikin su? Ashe rana zata zo da Momi da
Dady zasu buƙaci na bar gidan nan? Ban ga laifin Hilal ba dan ya zaɓi rabuwa da ni,
ga shi yanzu iyayena ma sun zaɓi haka’

Matsa ƙwallar tayi ta kai hannu ta ɗauki wayarta ta nemi number Teema ta aika mata
kira.

“Ƴar gari”

“Teema kin ce zaki shigo kuma har yau baki zo ba, wallahi ina cikin matsala”

“Me ya faru wace irin matsala kuma?”

“Daddy na roƙa ya ba ni keys ɗin gidansa da yake by pass”

“Me hakan yake nufi?”

“Zan fi jindaɗi idan ina ni kaɗai, shiyasa na roƙa ya bani gidansa can na zauna,
kuma ya anince min, yanzu matsalar da nake ciki ta rashin makama ne, Teema ina son
na koma gidan miji na ko ta halin yayana”

Daga can cikin wayar Teema ta sauke ajiyar zuciya.

“Rashida miyasa ba zaki haƙura da mijin nan ki ba? Ya nuna miki ƙiyayya tsantsarta,
ki ƙyale shi mana, Allah zai kawo miki wani”

“Teema har yanzu baki san miye so ba, saboda ba ki taɓa yi ba, bakin irin zafin da
mace take ji idan ta rabu da uban ɗiyanta ba, dan Allah ki taimaka min”

“Gaskiya Rashida taimako ɗaya zan iya miki, kawai ki haƙura da shi, Allah zai saka
miki, amman idan kuma baki ji ba, zan zo gobe na kai ki gurin wani malamin wanda
zai taimaka miki ko Allah zai sa a dace”

“Eh ki zo dan Allah, da ƙarfe nawa zaki zo?”

“Tara da rabi?”

“Sai kin zo, daga nan ma sai ki taya ni maida kayana wacan gidan”

“Okay Allah ya kai mu”

“Amin Sai na ji ki”

Ta katse kiran tana share hawaye.

“ I deserve happiness, Allah ka duba lamari na, Allah ka sassauata min wannan
rayuwa, ka rufa min asiri, Allah ka juyo da hankalin mijina a gare ni, Allah na
tuba ka yafe min”

Ta shafa addu'ar fuskarta shakaf da hawaye, tana jin tsantsar nadamar zinar data
aikata da aure, tun da itace silar shigarta duk wannan halin da take ciki, ta rasa
kowa nata saboda ciwon dake jikinta, idan ta tuna yadda Mahaifinta ya matsu ta bar
gidan sai ta ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu.

KALSOOM POV.

“Anty Kalsoom, Daddy yana kiran ki, yana falon baƙi tare da Hilal da Abban Hilal”
Da sauri Kalsoom ta ɗago ta kalli Saleena dake tsaye riƙe da gambun ƙofarta tanaata
magana. Gabanta ya faɗi sosai, a take ta aje jaridar dake hannunta ta ɗauki
Hijabinta ta saka, ta ƙaraso kusa da ƙanwarta Saleena.

“Me kika ji suna tattaunawa?”

“Ban ji komai ba, amman dai har Momi tana can, kuma duka fuskokinsu ɗauke da
farinciki”

Ajiƴar zuciya ta sauke sannan ta ratsa ta gefen Saleena ta nufi hanyar da zata
sadata da falon Dady, zuciyarta cike da fargaba.
Cikin natsuwa ta shiga falon, bakinta ƙumshe da sallama, sai da ta fara gaishe
da Abban su Hilal sannan ta zauna kusa da Momi kanta ƙasa.

“To ga mijin ki nan shi ba zaki gaishe shi ba?”

Cewar Dadyn Hilal yana murmushi, sai duk suka sa dariya har Hilal ɗin da zuciyarsa
ke cike da farinciki. Dady ya kiran sunan Kalsoom a natse, ta yadda zata maida
hankali ga abunda zai faɗa mata.

“Kalsoom. Hilal ya mayarda sauran igiyoyin aurensa da ke tsakaninku, kuma yace yana
da buƙatar ki koma ɗakin ki”

Samun kanta ta yi da kasa furta ko da kalma ɗaya, wani abu ta ji yana ratsa
zuciyarta shi ba farinciki ba, ba kuma ɗan 'uwansa ba, wato baƙinciki. Su kuma duk
natsu suna son su ji abunda zata ce, ganin hakan yasa Abban Hilal magana.

“Ai ba zata iya cewa komai ba, kasan ita mace ce, kuma ko ba komai suna son
junansu. Kawai shiga tsakani ne irin na mata, kai kuma ka biye musu ka zama macen”

Dadyn Kalsoom ya ƙyalƙyale da dariya.

“Matan ne ai sai a hankali, ni na so ta zauna har sai yayi auren ne, tukuna ta
koma, zamanta a can a yanzu zai ƙara saka tsanarta a zuciyar Hajiya ne kawai”

“A a ƙara ta koma ɗakinta, aure kuma ban hana yayi ba, kin dai shirya zama da
kishiya ko?”

Ya ƙarasa yana kallon Kalsoom wacce ta noƙe kai tana mai jin kunya.

“Tashi ki ɗauko kayan ki muje”

Sai a lokacin Momi ta saka baki

“Tun yanzu ai da an bari har gobe sai ƙanwarta da Ƙawarta ta raka ta”

“A'a nima ai na isa na rakata, tashi ki ɗauko kayan ki”

Kasa tashi Kalsoom ta yi har sai da Momi ta zo ta riƙa ta suka bar falon tare.
Daddy Hilal ya kalli Daddyn Kalsoom yana faɗin

“Wato abun ne da ɗaure kai, kasan kuma zuciya wani lokacin bata da ƙashi, ni kai na
abun ya ɗan ɗaure min kai da farko, amman ganin soyayyar dake tsakanin dole a ɗaga
musu ƙafa, kuma koma minene shi uban ɗa be yarda ba, kai miye na ka a ciki har ka
raba musu aure ƙaramar ƙwaƙwalce kawai ta mata”

Murmushi Dadyn Kalsoom ya yi ya girgiza kai


“Allah dai ya kyauta ya bayyana gaskiya”

Dukasu suka amsa da Amin har Hilal dake ƙoƙarin miƙewa tsaye.

YASMEEN POV.

A gajiye ta aje hakar hannunta ta karɓi Babynta daga hannun mai mata reno tana
murmushi.

“Sorry Dear i'm back”

Uzair ya aika mata wani kallo mai cike da jin haushi.

“Ni fa wannan aikin na ki ya ishe ni, ace har kana jego ma sai kaje, yau kwana biyu
da suna har kin fara fita”

Kallonsa ta yi fuskarta da annuri.

“Am sorry dear, daga yau ba zan sake fita ba sai next week”

Wani tsakin haushi yayi

“Ai kaji fa fitan ya fara kenan, ai ba aure lawyer ba, zamanta a gida ma aiki ne”

Dariya tayi tana gyara sunan da take ba ƴarta, tare da kallon Adnan dake wata
tafiya a wahalce.

“Kai me ya same ka?”

Bude baki yayi zai yi magana sai Uzair ya karɓe.

“Da...”

“Ina jin Basir ne yake damunsa, ko kuma ya zauna wani abu ne, ɗazu ma na duba gurin
ya masa ja sosai, i will take him to hospital”

Yana gama faɗar hakan ya miƙe tsaye ya riƙa hannu Adnan da sauri suka fice, ita
kuma bata wani ɗauke abun serious ba, ta maida hankalinta gurin Mai mata reno.

“Me aka girka?”

“Wake aka yi, shi yace na girka ta daya ga Namra na ta kuka”

“Ayyah Namra na, i'm sorry ba zan sake fita ba dake ba, i love you”

Ta aikawa babyn kiss tana murmushi. Sannan ta tashi ta nufi ɗakinta tana cire
ɗankwalin kanta, ɗayan hannunta kuma na ɗauke da new babynta Namra.

ASIM POV.

Be farka ba, sai bakwai da rabi, yana yin sallah asuba ya sake komawa baci,ba shi
ya tashi ba sai sha ɗaya na safe, wayarsa dake kusa da shi ya ɗauka ya lalubo
number Mardiya dan yau a bachinsa na safe ita yayi mafarki, be wani daɗe sosai yana
waya da ita ba, ya miƙe ya shiga wanka.
Sha biyu saura ya shirya ya fita, kai tsaye gidan Hajiya Sadiya ya zuwa, tun kamin
ya taso ya tanadi ƙarya da zai mata akan Namra, sai ya tarar bata gidan, mai gadi
ya labarta masa tun jiya da dare ta bar gidan wai taje birnin kebi.
Ko kaɗan Asim be jidaɗin hakan da Hajiya tayi masa ba, sai ya zuciyarsa ta soma
nuna masa ko dai Hajiya ta yi fushi da shi ne, shiyasa har taje Kebi bata faɗa masa
ba, duk da ta faɗa masa zata bashi hutu saboda baƙi zata yi ai bata ce masa zata
bar garin ba. Har ya ciro wayarsa ya kirata sai kuma wata zuciyarta ta hanasa, a
ganinsa yanzu ba zata sauraresa ba tun da tana cikin fushi ƙara ya bari har sai an
kwana biyu sannan ya kira ta, idan bata dawo ba.

Ƴar ƙara wayarsa ta yi, yana duba ya ga alert daga diamond bank saƙon miliyan biyar
ya shiga asusun ajiyarsa.

“Wow”

Ya faɗa yana karanta sunan wanda ya aiko masa da kuɗin.

“Yayi Kyau Alhajina”

Ya faɗa cike da tsananin farinciki, kaminɓya ɗora da saƙon daya biyo baya.

“Na aiƙo maka da kuɗi, kazo gobe sokoto ina son ganinka, kuma ka zama mai riƙe
sirri”

“Zan zo gobe tun da safe inshallah”

Haka ya mayar masa da amsa, sannan ya rumgume wayar a ƙirjinsa yana dariya har ta
fitar hankali. Komawa yayi motarsa ya shiga, yana cigaba da dariya har da jijjiga
jiki.

Yana yi ma motar ki kiran Nably ya shigo wayarsa, cikin sauri ya ɗauka yana dariya.

“Hello my second wife”

“Au ba ma nice ta farko ba kenan?”

“Yes karki sa ma ranki zaki zauna ke kaɗai a gidan Asim”

“Ashe kai ba Saurayi ba ne?”

“Saurayi ne kuwa sabo hul, amman bayan ke wata zan ƙara, ko kuma ma akai ku ku biyu
a tare”

“Kai da bakinka kake faɗin haka, lallai na yi fushi, na bar mata”

Da sauri ya haɗe hannayensa kamar tana gabansa.

“Sorry my nurul khalbi, wasa nake miki just to get your angry, yanzu dai ya hanya?”

“Au kasan da tafiya na, amman baka kira ka tambaye ni ba”

“i'm sorry dear i'm just kind of busy, In fatar kin sauka Lafiya”

“Na sauka ƙalau idona sai ƙaiƙayin ganinka suke yi ”

“Gani na kan hanya nan da mintuna talati”

“I can't wai to see you”

“The same here”


Yana aje wayar ya ƙara ma motarsa jiya ya nufi wani boutique, dan siyen kaya mai
kyau da tsana wanda zai sa yaje gurin gimbiya Nabila.

ABDOOL POV.

Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi jirginsa ya sauka Katsina, yana sauka ya kira Ummi ya
faɗa mata ya sauka, amman ta ƙi ɗaukar wayarsa, har sai da ya aika mata da saƙo,
Sannan ta aiko masa da direba.
Daga filin jirgi zuwa gida tafiyar minti goma sha biyar ce, amman sai yaga ta
yi masa tsayi kamar na awa ɗaya saboda zumuɗin da yake na bawa Ummi labarin dake
cikin ransa.
Suna shiga harabar gidan farincikin fuskarsa ya ɗaɗa ƙaruwa, ko fakin ɗin kirki
direban be yi Abdool ya buɗe ya fito, sai duk sojojin da suke gidan suka maƙe guri
ɗaya suna sara masa, hannu kawai ya ɗaga musu ya nufi Babbar ƙofar gidan.

Amira da Haleema na tsaye dinning suna jera abinci Abdool ya shigo da sallama.
Da gudu Amal taje ta rumgume shi.

“Dude i miss you”

“I miss you more”

Kaɗan kaɗan Amira take satar kallonsa tana murmushi, Haleema ma kallonta take tana
murmushi dan tasan abunda yake zuciyarta. Fitowar Ummi ne ya ɗago da duka
hankalinsu har Amira ta samu damar kallon Abdool da kyau tana auna irin missing
ɗinsa da ta yi.

“Ka kuru da baka dawo yau ba ko”

Dariya yayi yana wasa da hannun Amal.

“Ummi ina da labari mai daɗi da zan ba ki, duk da kin katse min uzuri na”

Zaunawa tayi saman kujera tana murmushi.


Sai shi ma ya zauna yana tambayar Amal abunda ya hana ta zuwa makaranta. Lemu Amira
ta ɗauko ta kawo masa a gabansa ta dire masa, tana masa sannu da zuwa.

“Yauwa Thank you so much”

Ta jidaɗin kalma nan da yayi mata, bama kamar murmushin da ta gani shimfiɗe a
fuskarsa. Cikin natsuwa ta tashi ta nufi dinning dan zuba masa abinci.

Kallon Ummi yayi fuskarsa ɗauke da abunda ke zuciyarsa.

“Ummi kin yi suruka, matar da na taɓa baki labari ina so na samo ta, finally
mafarki na zai zama gaskiya...”

Tartsatsa... Suka ji ƙarar fashewar plate mai ɗauke da abinci, wanda Amira ta sake
saboda maganarsa da ta soki gadon bayanta, da sauri ta ɗuka tana kwashewa, kamar
wacce ta ruɗe, a take hawaye ya fara bin fuskarta, sai dai su basu gani ba
kasancewar ta basu bayana ne.

“Ba ki ji ciwo ba?”

Ummi ta faɗa tana ɗan leƙen ta. Sai Haleema ta yi saurin amsawa.

“A'a plate ɗin ne kawai ya fashe”


Ummi ta maida hankalinta gurin ɗan ta.

“Im happy for you Son, na daɗe ina jiran wannan ranar, you have no idea how happy
you make me, sai dai ban gane wacce kake magana ba akai kam ba”

“Ye... ”

Ringing ɗin da wayarsa ta yi ne ya hana shi ƙarasa maganar sai yayi saurin tashi ya
nufi wani ɓangare na falon yana amsa wayar.

“Salim”

“Sir mun bincika, Manjo Usman Zamau yana sokoto da zama a unguwar clapperto, yana
da mata biyu da ƴaƴa goma sha uku Namra ita ce ta goma, kuma ainahin sunan ta shi
ne Khadija, ta yi makaranta a dan fodio tana level 300 aka yi mata aure, kuma har
yanzu tana gidan aurenta zaune, facebook username ɗin ta Khadija Usman Zamau
instagram kuma Namra's, haka yake a twitter da snapchat”

“Amman ba ku bincika zaman auren ta ba? Har yanzu tana da aure?”

“Binciken mu ya nuna har yanzu tana da aure kuma tana a garin katsina da zama,
sunan mijin da take aure Ibrahim amman anfi kiransa da Asim”

“Thank you”

“Your Welcome Sir”

Wayar ya ƙurawa ido yana mamakin yadda Namra zata masa ƙarya, bayan ya tambaye
tsakaninta da Allah, taya aurenta zai mutu kowa bai sani ba, hakan yana mufin ƙarya
ta masa kenan ko kuma akwai abunda take ɓoyewa.
Juyowa yayi yana ƙoƙarin ɓatar da mamakin dake fuskarsa ya kalli Ummi yana
tahowa ya ce.

“Wani aiki ya tashi Ummi Ana nema na a Kaduna yanzu yanzu nan”

“What?”

Ummi ta faɗa da mugun mamaki. Shi kuma ya ɗan ɗaga gira yana kallon Amal.dake
zumuɗin labarin daya fara badawa.

Hello habibaties nasan kuna haƙuri da ni dan Allah ku ƙara haƙurin. Wallahi abubuwa
ne suke min yawa, ga kuma rashin wutar nepa a gusau, yau four days babu wuta, sai
an tashi engine ne muke samu mu saka. Idan kuma ka matsa za'a ce sai ka biya na Mai
😂 you know how our grandma's are, sai haƙuri 😂


Love you all fisabilliah ♥️
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *71*

Ɗauke kansa yayi daga kallon da yake ma Amal ya kalli Ummi, irin babu zacen wasa a
kalamansa.

“Nima sai da na ce miyasa ba su bar ni nayi aikin ba acan ba sai yanzu da na dawo”
“Abdallah ka ce min kun samu hutu fa? Aikin me zaka je yi yanzu?”

“Wai General ne zai zo daga Abuja zuwa Kaduna gobe, kuma dole ne muje. Bari naje ya
canja kaya gobe da safe ai zan dawo”

Be jira abunda Ummi zata ce ba, ya nufi ƙofar fita yana lalabar number Salim dan ya
sama masa jirgin da zai koma Kaduna yanzu ko da Yammar nan.
Ummi dai da kallo Mamaki ta bishi, ta fi kowa sanin ɗanta dan haka ta san ba aiki
ne zai maida shi Kaduna ba, sai dai wani abun na daban, kai ta girgiza tana kallon
Amal data wani turo baki.

“Be ma ƙarasa mana labarin ba”

Ummi ta miƙe tsaye ta nufi kitchen tana faɗin

“Uhnm kya ji da shi”

AMIRA POV.

Tana gama kwashe plate ɗin da ya fashe ta zuba a shara, sai ta nufi ɗakinta cikin
wani irin kuka marar misaltuwa.
Saman gadon Amal ta faɗa ta kife tana rera kukanta a hankali yadda wani ba zai
ji.

“Shikenan na rasa komai, wata yake so ba ni ba, shi ma na rasa shi”

Tausayin kanta take da kanta tana tunanin irin rayuwar da zata yi nan gaba. Bayan
ta rasa duk wani abun da zai iya saka ta farinciki. A hankali Haleema ta turo ƙofar
ta shigo fuskarta ɗauke da tausayin Amira,wanda har zuciyarta haka ne. Kusa da ita
ta zauna ta kai hannu ta taɓa ta.

“Ki yi haƙuri Amira, ni kai na ban san haka zai faru ba...”

Da sauri Amira ta ɗago ta kalleta da idonta da suka gana canja kala saboda kuka.

“Ke ma kin yarda na rasa ɗan uwanki ko? Babu wani abun da za kiyi? Dan Allah ki
taimaka min Haleema kema mecece zaki iya shiga a halin dana shiga, kin san irin
abunda nake ji, Wallahi ina son Yaya kuma tsakani da Allah zan zauna da shi, idan
har na ci amanarsa na yarda amanar Allah ta ci ni, na rantse da Allah ba zan cutar
da shi ba”

Kuka take sosai zuciyarta a narke, ta kama hannayen Haleema ta riƙa tana mai jin
kamar Haleema ta yi mata maganin damuwarta.
Cikin kuka Haleem ta ce.

“Babu wani taimako da zan iya yi miki Amira, Big Bro babu mai saka shi dole idan ba
Ummi ba, kuma idan har ya nuna baya so ita ma bata so, babu abunda ya cutar da ke
kamar zama ba a gurin iyayen ki ba”

“Ba zan iya komawa ba, ban san yadda zan yi na koma ba”

Ya zube ƙasa zaune tana rushewa da sabon kuka. Haleema ta riƙa ta tana bata haƙuri.
Kamin ta tashi cikin ɓacin rai ta nufi hanyar fita, Amal ta samu tsaye jikin ƙofar
ta yi wani wuƙi-wuƙi da ido.

“Ummi tan kiran ki”

Ta faɗa a sagarce, sannan ta falfala da gudu ta nufi ɗakin Ummi ɗin. Haleema ta
rufa mata baya tana share hawayenta. Ƙusƙus ta tarar Amal na yi gurin Ummi, hakan
ya tabbatar ma da Haleema Amal ta ji abunda suke cewa.

Meesha na gaban maduba Ummi tana ɗanɗasa kwaliya ita da Fauza, dan su basu ma san
Abdool ya dawo ba.

“Ummi ga ni”

Ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zama kusa da ita.

“Gulma ta kuke yi?”

Da sauri Haleema ta sake kallon Ummi baki sake, kamin ta maida dubanta gurin Amal.

“Amman yarinyar nan munafuka ce Wallahi, gulamar ta kika ce na yi, aiko sai na miki
ɗan banzan duka a gidan nan”

Ummi ta katsa mata tsawa.

“A'a akan me? Maganar me kuke ke da ita har kuke kuka?”

“Walahi akan big bro ne, dan ta ji ya samu mata shine take kuka ina bata haƙuri”

“Dan ya samu mata sai aka yi me?”

“Kin san son shi take sosai wallahi”

“Amman dai Haleema baki da hankali, ke ko a mafarki aka ce yayanki zai aureta idan
kika farka ai kya nemi tsarin Allah, macen data zauna da yan fashi? Kika san ciki
nawa ta zubar? Baki san zaman ta a nan ma it very risk ba”

“Haba Ummi ciwo ƴa mace na ƴa mace ne, yanzu idan nice a wannan hali zaki jidaɗi?
Ba ita ta ƙaddaro ma kanta ba, kuma ta yi sadaukarwa ma Big Bro ita ta cancanci ya
so ta wallahi”

Ummi kasa magana ta yi saboda mamakin furucin Haleema. Meesha ta taso daga gaban
madubi da take zaune tana faɗin.

“Kin san me Ummi zata iya saka mana guba duka mu mutu idan har ta ji Big Bro ba zai
aureta ba, ƙila ma turo ta aka yi, ta ina ma.taji Yaya ya samu mata? Kodai ta ga
alamun ba zai so ta ba ne”

Fauza ta amsa.

“Kuma Wallahi irin waɗan nan ba tsoron kisan kai suke ba, tun da sun saba”

Ran Haleema ya ɓace sosai.

“Ku daina judge mutane ne, hakan be da kyau, Allah ma yana karɓar tubar bayinsa
balle kuma mu....”

Shigowar Abdool ne yasa duk suka warsar da maganar, Fauza da Meesha suka fara
ɗaukin shigowarsa tare da masa sannu da zuwa.

“Ai kune ba ku san ya dawo ba, mu tuni muka sani har ya ba mu labarin matarsa da
zai aura”

Ya ɗaga gira ɗaya yana kallon Amal, ita kuna ta shigar da kai jikin Ummi dake
dariya, ita ala dole ga auta.

“My girls ku fita za mu yi magana”

Ya faɗa yana ƙoƙarin zama a kujerar dake fuskantar gadon Ummi. Ba musu duk suka
fita har Amal uwar son zancen dan bata ga alamun wasa a fuskarsa ba balle ta tsaya.

“Maganar gaskiya Ummi ba aiki zani ba, gurin yarinyar nan zan koma, kawai ki min
addu'ah, gobe da safe zan dawo”

“Na gama karantar ka sarau Lamiɗo kallon ka kawai na ke yi. Allah ya kai ka lafiya,
kuma a gaishe min ita sosai da sosai”

‘Ai ba gaisuwa ba, ni kaina ban san makomata ba’

Zance daa ya faɗo masa kenan a rai kamin ya ɗago ya saurari zancen da Ummi ta ɗora
da shi.

“Dan Allah ka nemo iyayen yarinyar nan, idan ba zata iya zuwa ba, su suzo su tafi
da ita”

“Ummi laifin wa? Idan na yi magana ai cewa kike na ɗaga mata ƙafa”

“Ai ba ƙafa ba komai ma.an ɗaga mata, yanzu kam ya kamata ace tana gaban iyayenta”

Miƙewa yayi tsaye yana faɗin

“Don't worry Ummi, if she planning something evil, za a sanar da ni, ai akwai mai
kula da cctv camera. A min addu'ah jirgin mu zai tashi nan da ten minutes”

“Allah ya kiyaye ya kai ku lafiya”

Tasowa ta yi ta suka fito tare da shi yana labarta mata maganar da suka yi da Mai
Martaba.

Ko da ya isa airport sauran minti uku jirgin ya tashi, abun ka da manya a take aka
masa checking ya wuce.
Be da sukuni har sai da jirginsu ya sauka garin Kaduna, yana sauka airport yayi
waya daga Abuja, suka kuma suka yi waya a kaduna, cikin minti ashiri sai ga direba
in military uniform sun zo ɗaukarsa.

A cikin motar ya sha ruwa, kamin ya buɗe biscuit ya ɗan ci kaɗan yana faɗa musu
inda zasu kai shi. A masallaci unguwar ya ce a aje shi, suna yin parking da sauri
wani ya fito daga cikin motar yazo ya buɗe masa yana sare masa, umarni ya basu na
suje sai ya nemesu. Ba musu suka sake tsara masa suka koma cikin motar suka juya.
Yi yayi kamar be kula da mutanen da suke kallonsa ba, yayi alwalarsa ya bi jam'i,
har aka gama sallar kowa da abunda yake faɗa, wasu wai ya zo bincike ne, wasu kuma
wai akwai wanda zai kama, shi dai yana gama sallah la'asar ya kanyar kwanar da zata
sadashi da gidansu Lamido,daman daga masalacin zuwa cikin gidan babu wani nisa
sosai. Hango mustafa da yayi yasa shi sauri juyawo ya ciro wayarsa a aljihu ya
neman number direban Mai Martaba da yake gidansa da suka sauka da ke Kaduna.

Cikin mintuna da basu bi goma sha ɗaya ba sai ga direba ya iso, be faka ko'ina ba
sai gaban Abdool da sauri Abdool ya buɗe ya shiga, yana nuna masa inda zaije.
Mustafa na zaune gindin wani icce yana kallon motar har suka faka ta dai-dai
ƙofar gidan su Lamido. Ya maida hankali sosai da son ganin wanda zai fito daga
motar, sai kawai yaga baƙuwar fuska ta fito daga gidan gaba mazaunin direba yana
buga ƙofar giɗansu Lamido.

“Waye...”

Suka amsa daga can ciki kamin ɗan uwani ya fito waje ganin mai buga ƙofar.

“Shiga ciki ka ce Abdallahi daga Katsina yana sallama da Namra”

“Toh ya juya da gudu ya koma”

Shi kuma direba ya juyo dan mayarma da Lamido saƙo.

“Wai Ance bata nan”

Yaron ya faɗa yana tsaye jikin ƙofar gidan. Abdool ya buɗe motar da kansa ya fito.

“Kije ka ce idan bata fito ba, ni zan shigo”

Yace da yaron babu alamar wasa a maganarsa, haka ma a yanayinsa. Da gudu yaron ya
koma, ko minti biyu ba'ayi ba sai ga Namra ta fito cikin farin Hijabi ta doso inda
yake. Yana kallonta dukan natsuwarsa taje gareta, kalaman daya tara zai watsa mata
marar daɗi sai duk ya neme su ya rasa har ta ƙaraso kusa da shi ta tsaya.

“Ban ce kar ka sake zuwa nan ba? Jiya jiya ban maimaita maka wannan maganar ba? Ka
ɓace ka bar ƙofar gidan nan”

Ta faɗa a tsawace, fuskarta babu annuri. lumshe ido Abdool yayi ya buɗe ya kalleta.

“Kina burge ni idan kina ba ni Umarni, da ma ace bakin ki be iya faɗar ƙarya ba,
kin ce ba ki da aure bayan kina da shi”

“Idan na maka ƙarya nawa zaka ba ni? Miye ribata idan na maka ƙarya bayan ka
tambaye tsakani da Allah?”

“Amman ƴan gidanku sun tabbatar mana da kina da aure, Asim be sake ki”

Wani irin kallon ta jefa mata mai cike da tashin hankali da mamaki.

“Ina ka san ƴan gidan mu? Waya faɗa naka sunan mijina? Waye kai? Me kake nema a
gare ni”

“Naje har gidanku ne neman auren ki, kuma sun tabbatar min da kina da aure, auren
ki be mutu ba”

Ta ɗora hannu saman kai.

“Na shiga uku na lalace, ka ɓata komai yanzu shikenan ba za su karɓe ni ba, miyasa
baka bari na faɗa musu mutuwar aurena da kai na ba? Kaico na ni Namra, duk inda na
dafa taɓen mi yake yi, ka cuce ni shiyasa ka tambaye ɗan ka ƙara jefani a halin
baƙinciki da damuwa? Wayyo ni Allah na”

Ta juya da sauri ta koma ciki tana kuka. Shi dai kallonta kawai yake har ta gama
faɗa masa abunda zata faɗa masa ta juya ta shige. Jikinsa yayi sanyi sosai, ko bata
faɗa masa ba yasan there's something behind those words and tears da ya ga suna
zuba a idonta. Juyawa yayi zai buɗe motar ya shiga sai ga Mustafa ya iso.

“Ranka ya daɗe naje kai maka kayan aka hanani shiga, kuma aka ƙi karɓa wai baka
nan”
Ko kallonsa Abdool be yi ba ya ɗaga masa hannu.

“Na bar maka”

Ya shige motar, cikin rashin jindaɗin rai. Tun kamin su bar unguwar kalaman Namra
suka riƙa dawo masa, idan ya tuna hawayen da ya ga suna zuba a idonta sai yaji wani
abu ya tsaya masa a zuciya marar daɗi.

“Ranka ya daɗe ina za muje?”

Ya tambaya ganin har sun hau titi amman Abdool be ce da shi komai ba.

“Masaukin Mai Martaba”

Ya faɗa cikin sanyayiyar murya mai nuna mutun yana cikin damuwa.

-----------------------------------------------------------------
Ku yi haƙuri da wannan.

*72*

Da kuka Namra ta shiga gidan, bata kula su Neina da ke tsakar gidan suna gyaran
giɗa ba ta wuce ɗakin Uwani, saman katifa ta faɗa tana cigaba da rera kuka.

Duk mamakine ya kama su, daman tun jiya ba su gane ma kanta ba.

“Uwani je ki gani mana”

Lamido ya faɗa yana kallon Uwani, duk ya ji babu daɗi ganin tana hawaye.
Da sauri Uwani ta tashi ta shiga ɗakin, hannu ta kai ta ɗago Namra tana tambayar

“Lafiya miya same ki?”

Sai kawai Namra ta faɗa jikinta ta cigaba da kukan. Jin kukan nata ya ƙaru yasa
Neina shigowa ɗakin.

“Ke lafiya miya same ta?”

“Wallahi nima ta kasa min magana, sai kuka take”

“Toh Allah dai ya sa lafiya, ko wani ne ya mutu?”

Sai a lokacin Namra ta samu ta girgiza musu kai, tasa hannunta ta share hawayenta.

“Mutumen da ya zo yanzu, shi ne mutumen da ya zo jiya, kuma shine mutumen da ya


kaɗe Lamido”

Ba shiri Neina ta zauna sake da baki dan shan labari, Uwani kuma ta yi ma Namra
kallon Mamaki.

“To miyasa kawo shi? Miya ce miki”

A nan Namra ta kwashe labarin abunda ya faru, ta faɗa musu, sai dai bata yarda ta
faɗa musu sanin da ta yi masa a Katsina ba.
Dukansun cika da tsananin mamaki, bama kamar Neina da take ganin kamar lokacin da
ya zo gidan ba su yi ido biyu da Namra ba.

“Amman Namra in ban da abin ki miye abun kuka a ciki? Ke da Allah ya kawo miki
ɗauki? Yanzu ko abunda tsohon mijin nan na ki ya yi miki ai wannan idan kika duba
sakamako ne Allah zai miki”

Uwani na kai aya. Namra ta yi mata kallon baki fahimce ni ba.

“Ya ƙara ɓata min komai Uwani, yanzu iyaye na sun ji aure na ya mutu, kuma za su yi
tunanin ko nice na tura sa neman aure na, idan yanzu na koma gida ban san mi zan ce
musu ba”

Neina ta ɗaga kai ta kalleta

“A yadda na fahimta, idan har yana son ki da gaske ne, hakan ba zai sa ya ƙi ki ba”

“Ya so ni, ko ya ƙi i, ni duka ɗaya ne a guri na, ban shirya mutuwa sau biyu ba,
ban shiryawa yaudara Namiji ba, wani na Namiji ba zai sake ɗiga min baƙinciki a
rayuwata ba, na rufe shafin Namiji a rayuwata, dan haka ni ba shi nake ji ba,
iyayena na ke ji da makomata”

Duk shiru suka yi, suna sauraren kukan da take rerawa. Kamin hankalinsu ya koma kan
sallamar da Mustafa yake yi. Neina ce ta tashi ta fita Uwani kuma ta tsaya yana
bawa Namra haƙuri.

“Maraba da Mustafa, yau an dawo shago da wuri?”

Ya zauna saman kujerar tsakar gida ta mata, yana faɗin

“Wallahi yau ban ma je ba, ya mai jiki?”

“Jiki yayi sauƙi Alhamdulillahi”

Lamido ya amsa da kansa yana miƙa masa hannu su gaisa.

“Allah ya ƙara sauƙi, naga kun yi wani babban baƙo ne a waje, amman kamar be shigo
cikin gidan ba”

“Eh gurin Namra ya zo ɗan'uwanta ne”

Cewar Lamido, kamin Neina ta amsa da

“Wai Ɗan Sarki nan ne da ya kaɗe ka, shine ya zo wai yana son ta, kuma har yaje can
gida ita bata ma sani ba”

Da sauri Lamido ya kalli Neina, wani irin abu ya daki ƙirjinsa, be ji daɗin maganar
ba, kuma be ji rashin daɗinta ba, sai ya samu kansa cikin wani kalar yanayi na
dabam.

“Me ta ce masa? Ai na ga ta dawo da kuka”

Ya tambaya kamar ba komai, sai a baɗini yana jin zuciyarsa kamar ta rabe biyu. A
nan Neina ta kwashe labarin da Namra ta faɗa musu ta faɗa ma Lamido.

“Ba duka maza ne ƴan iska ba, ba duka maza ne mayaudara ba, ba a taru aka zama ɗaya
ba, yadda wani yake da kwaɗayi ba haka wani yake da shi ba, ba a taru a zama ɗaya”

Ya faɗa a hankali yana kallon wani gurin kamar mai nazari. Har Neina ta buɗe baki
zata yi magana, sai Mustafa ya jinjina kai ya ce.
“Amman abun da ya ba ni mamaki, wannan mutumen yayi min kama da wanda na sani, kuma
shine mutumen da ya aiko yaronsa ya kira nia ka bani wanki, ya ɗauki dubu goma sha
ɗaya ya ba ni wai na wanki ne, har yake labarta min wai shi ɗan'uwan ku ne, kuma
yana zuwa gidan, da neje kai masa wankin sai aka ce baya nan, ina nan kuma zaune
sai na gansa, ina masa magana wai ya ba ni tufafin”

Lamido ya riƙe baki.

“Wallahi ba mu da wani alaƙa da shi, ai baka nan lokacin daya kaɗe ne da ka gani,
anya ba yana da wata muguwar manufa ba ce akan yarinyar nan da mu ma?”

Neina ta yi saurin rufe masa baki.

“Dan Allah ka rufa mana asiri, ɗan Sarki ne”

“Dan yana Ɗan Sarki fa? So what? Ba a da ikon faɗar gaskiya, ku kuke tsoron sa”

Mustafa ma ya saka baki.

“Kai da ka rufa ma kan ka asiri. Ko ma minene iya karka ka yi addu'ah ka zura na


mujiya”

“Wallahi ba zan yi ba, ba zan zuba ido wani ya cutar da yarinyar nan ba, iya
wahalar da tasha ta ishe ta haka”

Ya faɗa cike da ɓacin rai. Mustafa ya miƙe tsaye bakinsa cike da maganganun da be
samu furtawa ba, yana musu Allah ya sauwaƙe.

“Amin an gode Mustafa”

Neina ce ta amsa da haka, Lamido kan hankalinsa na can wani gurin.

ABDOOL POV.

Samun kansa yayi da damuwar abunda be kamata ace ya dame shi ba, ya sara sukuninsa
tun hawayen da ya gani suna zuba a idon Namra.

“Na ɓata komai? Na ƙara ruguza mata rayuwa? Mi take nufin da hakan?”

Magana yake yi da kansa yana kallon tv, babu abunda kunnuwansa suke da buƙata a
yanzu kamar jin labarin Namra.

“Allah kai ka san ina son yarinyar nan, kuma Allah kai ka saka min son ta, ya Rabb
help me, wallahi daga gani sai ta yi taurin kai”

Ya shafa fuskarsa yana busar da iskar bakinsa. Can kuma ya kai dubansa ga wayar
dake gefensa ya ɗauka ya danna number Ummi. Bugu ɗaya Amal ta ɗauka.

“Dude zaka cigaba da ba ni labarin matar ka ko?”

Murmushi yayi marar sauti kamar tana gabansa.

“Ina Ummi?”

“Tana falo, ni ina game da wayarta”


“Tau ki ce mata na isa lafiya ƙalau kin ji”

Be jira abunda zata ce ba ya kashe wayar, yana sauke ajiyar zuciya. Sam be jin yau
zan iya haƙura be ji labarin Namra ba, dare kawai yake jira yayi masa ya koma
unguwar, sai dai me idan tace ba zata faɗa ba fa?

“Tau ya zan yi? Ni Wallahi tsoro ma yarinyar nan take ba ni”

Ya sake magana a fili kamar mai magana da wani. miƙewa yayi tsaye ya nufi bedroom
ɗinsa yana ware hannayensa.

“Ina ta ƙoƙarin zama mahaukaci akan wannan yarinyar, Allah ka da ka jarrabe ni ta


wannan hanyar”

RASHIDA POV.

Da taimakon Teema suka kwashe duk wani abu na amfaninta suka mayar a gidan da
Mahaifinta ya bata. Ɗan madaidaicin gida ne mai ɗauke da ɗakuna biyar, da kuma
madaidacin tsakar gida.
Gidan yayi datti sosai duk da kasancewar ba a taɓa zama a cikinsa, sai dai daɗewa
da aka yi ba a buɗe shi ba yasa ya koma kamar anyi yaƙi a cikinsa. Tare da teema
suka jera komai, sam bata yarda ta nunawa Teema damuwarta akan komawarta gidan ba,
hasali ma tana yawan maimaita ita hakan ya fi mata daɗi kuma ita ce ta nemi Dady ta
bata gidan alhalin ba haka ba ne, duk yadda hawaye suka yi ƙoƙarin zubar mata sai
ta yi kamar abu ya faɗa mata a ido.

Sai dai abunda Teema ta saka samun natsuwa da shi, ganin babu ɗan'uwanta ko ɗaya
daya zo rakata a gidan, ko kuma su tausasata akan karta bar wacan gidan ta dawo nan
ita kaɗai. Bata nuna mata komai ba har suka gama tsara komai suka share iya inda za
su iya, sauran ta ce almajiri zai gyara mata, daf da za su fita Momi ta iso gidan
da kukanta kamar wance aka cirewa rai. Duk dauriyar da Rashida ta ke sai da ta fasa
na ta kukan, sai ita da Momi aka rasa mai bawa wani haƙuri.

“Ni Wallahi sam ban ga amfanin wannan kukan ba, miye na barin gida Rashida in ban
da abun ki? Ai ƙara ki zauna cikin danginki, ko danuwa ai kya rage”

Rashida ta share hawayenta, tana jan majina.

“Ni na zaɓi zama a nan, na fi son na zauna ni kaɗai”

Momi kan bata iya cewa komai ba, sai kawai ta miƙe tsaye tana faɗin.

“Dadyn ki ya ce zai aiko da furniture da abinci, da kuɗi kuma duk abunda kike so ki
riƙa faɗa mana”

Daga haka ta fice hawaye na cigaba da mata zuba. Bayan fitarta da minti goma
shabiyar Rashida ta tashi ta shiga bathroom ta yi wanke fuskarta ta fito suka ɗauki
hanyar dutsen Malam.
Rashida ce take driving, Teema kuma na zaune front seat, sai kallon Rashida ta
ke yi ƙasa-ƙasa. Ɗan ƙauye ne da yake can waje gari sai dai kuma ba sosai ba. Shi
wannan malamin da alama aikinsa ba yayi ko kuma sabon farawa, dan babu ƙowa a ƙofar
gidansa. Matan biyu masu far'ah da son mutane, suna shiga suka ɗauko musu tabarma
suka shimfiɗa musu da zimmar za su aika a kira Malam wai yana gona.
Sai ga shi ya iso cikin ƙanƙanen lokaci, jikinsa har ɓari yake, bakin nan cike
da goro. Bayan ya gaisa da su yayi musu iso zuwa ɗakin da yake aikin nasa.

“Bismillah”
Ya nuna musu gurin zama yana ɗauko farra ƙasarsa dake cikin ɗan ƙaramin windi. Sai
da Teema ta fara gabatar masa da Rashida sannan ta fara faɗa masa matsalolinta da
kuma abunda ke tafe da ita. Kai ya girgiza ya sake girgizawa sannan ya shiga duba
ƙasar, can ya ɗago ya kalli Rashida ya ce.

“Wato ni bana ɓoye komai, magana ta gaskiya ƙasa ta bada bayanin ba zaki taɓa
komawa gidan mijin ki ba”

Rashida ta daki ƙirji.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Sai hawaye ya fara bin fuskarta. Teema ta nuna damuwa sosai.

“Malam ko dai ƙasar bata ba da bayani dai-dai ba ne? Dan Allah a sake bincikawa”

“Ai babu wani bincike, ni ba zan cuce ku ba, kun ga idan wani ne sai ya nuna muku
kamar aiki zai ci ya riƙa cin kuɗin ku”

Miƙewa Rashida ta yi tsaye tana hawaye

“Teema tashi mu je”

Kamin Teema ta tashi har Rashida ta kai ƙofar gida.

“Zan kira ka Malam”

Teema ta faɗa tana aje mishi kuɗi masu ɗan dama gabansa. A tsakar gidan ma Teema ce
ta yi musu sallama da godiya, ko da ta fito waje har Rashida ta yi ma motar key ita
kawai take jira.
Wani mahaukacin gudu Rashida ta fara, kamar marar hankali, har sai da Teema ta
riƙa ta.

“Idan har kw baki son kan ki ni ai ina son ki, be kamata kina wannan gudun ba,
yawancin bokayen nan ƙarya suke faɗa fa, ki bari zamu je wani gurin”

Uffan Rashida bata ce cewa Teema ba har suka isa ƙofar gidansu Teema.

“Idan Hankalin ki ya kwanta ki kira ni zan kai ki wani gurin”

Sai ta buɗe motar ta fita. Rashida ta fi ƙarfin minti goma a gurin tana kukan
sannan ta kaɗa motarta ta yi gaba.

ASIM POV.

“Nice House”

Ya faɗa yana ƙarewa gidan kallo, hannu Nably tasa taja hancinsa.

“Gida zaka yaba ba ni ba?”

“Ke ai babu kalmomin da zan iya amfani da su na ya be ki da su, amman gida ko akwai
kalmomi da zan yabe shi da shi”

Ɗan murmushi ta yi, tana ƙara kallon harabar gidan.

“Momi na ta so ta gaisa da kai, sai dai tafiyar gaggauwa ta kama ta yau, amman gobe
dole ne ka dawo, dan momi ta ga wanda nake yawan bata labari”
Ya kai hannunsa ya riƙo nata.

“Wato gulma na kike?”

“Ba wani gulma, ba kai ba ne ka sace mata zuciyar ƴa ba”

“Ko kuma ƴarta ta sace zuciyar wani ba”

Cikin wasa ta kai masa duka, shi kuma ya goce yana mata wani kallo, tuni idonsa har
sun soma canjawa. Yar yar daya fara jin jikinsa na yi ne yasa ya saki hannunta yana
faɗin

“Bari ma zo ma tafi na wuni a gidan na ku ai”

“Wato har ka gaji da gani na kenan?”

“Kai ni har na isa, kawai dai naga magariba tana gabatowa ne, ai kin ga dole jibi
naje na kai ki birthday ɗin friend ɗin ta ki, kuma mu zaga gari”

“Ai gobe ne”

Ya buɗe ido.

“Tab aiko dai gobe tafiya za mu yi da oga na, ban da haka kan wallahi babu abunda
zai hana ni kai ki ko ina ne a faɗin duniyar nan”

Ta wara ido.

“Kar ka damu, nima ai ban cika son kaje ba gudun kar wata ƙwace min kai”

Sai da aka soma kiran sallah, sannan ya tashi, ta rakoshi har gurin motarsa, ta
buɗe masa, har zai shiga sai kuma a juyo ya kalleta ya ce

“Haka zan je ba good bye?”

Murmushi ta yi ta juya ta juyo, kamar mai nuna masa mazaunanta, daman jikinta babu
mayafi, sai kawai ta kai masa kiss a baki.

“Shikenan?”

Ya ɗaga mata kai yana wani shegen murmushi. Sannan ya shiga motarsa tana ɗaga masa
hannu har ya bar gidan.

“Wow wayayiyace sosai, i'm so lucky”

Abunda ya furta kenan yana ƙarawa motarsa giya. Be tsaya ko ina ba sai da isa
unguwarsu, a lokacin har an sauko daga sallar magariba, sai da ya shiga gida yayi
wanka sannan ya fito a masallacin unguwar yaje ya yi alwala ya yi sallah, sannan ya
koma cikin gidan ya ɗauki motarsa ya ƙarasa ƙofar gidansu Mardiya.

Ko da ya kirata yace yana kofar gidansu, bata cikin gidan, dan haka sai da ya
jirata har na tsawon mintuna talati sannan ya ta iso gurin da saurinta. Ta kanta ta
buɗe motar ta shiga tana masa sallama.

“Ya gida ya su Mama?”

“Wallahi lafiya ƙalau, ya naka gidan?”


“Gida na babu daɗi fa”

“Subhannalla miya same ka?”

“Kin san na zama gwauro yanzu, tun da kin kore min Namra”

Mardiya ta riƙe baki kamar gaske.

“Wai da gaske ne da ake cewa Namra ta fita?”

“Ba ki sani ba? Kuma saboda ke ta bar gidan?”

“Saboda ni kuma?”

“Eh dan ta gano ina son ki, shine ta so na sake ta ni kuma na ƙi na sake ta, shine
sai ta tafiyarta”

“Kai amman ban jidaɗi ba, kaje ka dawo da ita dan Allah”

“Ni yanzu ba ta ita nake ba ta ki na ke”

“Ni kuma?”

“Eh mana, ni fa tsakani da Allah na ke son ki, kuma auren ki zan yi, shine abunda
ya kawo ni yanzu, na baki kwana biyu ki je ki yi shawara”

“Amman Namra ba zata ce komai ba?”

“Ke kike ta kanta, ga wannan ni zan wuce, dan gobe zan yi tafiya yau nake son na
fara shiri na”

Ya miƙa mata dubu goma, ƴan ɗari biyar-biyar. Ƙin karɓa ta yi har sai da ya matsa
mata sannan ta karɓa tana masa godiya, ta buɗe mota ta fita.

KALSOOM POV.

Be barta ta yi aikin komai ba, shi ya haɗa musu abun kari, kuma ya haɗa musu ruwan
wanka. Daman ita ta gaji sosai, tun da ta yi sallah asuba ta koma bachi, shi kuma
ganin hakan yasa be tashe ba, ya barta ta yi bachinta, har ta gaji ta tashi dan
kanta, sannan ya shigo ɗakin fuskarsa da Annuri.

“Tun ɗazu breakfast yake jiran ki”

Ya faɗa yana zama kusa da ita. Agogon ɗakin ta kalla ta ga sha ɗaya har da kwata.

“Kai ya aka yi nayi bachi haka?”

“Kin gaji ne, shiyasa ban tashe ki ba”

“Amman kai ka karya ko?”

A maimakon ya amsa mata sai kawai ya sakar mata ido yana kallonta, fuskarsa da
mirmushi. Ɗan sunkuyar da kai ta yi itama tana maida masa da saƙon murmushin.

“Amarya ta”

Ya faɗa, tana mai cigaba da kallonta.


“Amaryar ka tana nan zuwa, ni kuma na zama uwargida a yanzu”

Murmushi yayi mai sauti, dan yaga kishinsa a cikin idonta.

“Ai ba gida ɗaya zaku zauna ba, kuma ita zata zauna da yara ne, that's means ke ce
Amaryar”

Kai ta girgiza tana dariya, kamin ta mike tsaye.

“Bari na je na wanki bakina”

“Lemme help you”

Ya miƙe tsaye shi ma suka shiga banɗakin tare.

NAMRA POV.

Tun da ta shige ɗakin, bata fitowa sai idan fitsari zata yi ko shan ruwa, duk ta bi
ta damu kanta, ta takura kanta. Duk yadda Neina ta so ta fito waje su yi fira sai
ta ƙi, haka ta wuni da yunwarta daman can ba abinci take ci ba, sai Maltinar da
Lamido yake badawa ana siyo mata, yau kuma ko maltinar ta ƙi ta sha.

Bayan sallame sallar isha'i yaro ya shigo, da sallama yana riƙe da kwanonsa ya
bara yace

“Sallamu alaikum wai ance ana sallama da Namra, wai Abdullahi ne daga Katsina”

Tana cikin ɗaki ne, amman hakan be hanata jin abunda almajirin ya faɗa ba, sai
kawai ta lumshe ido tana sauraren tsaran da kanta ke mata.

‘Wannan wane irin mutum ne?’

Ta tambaye kanta, tambayar da bata da amsa.

“Je ka ce bata nan”

Cewar Lamido zuciyarsa har wani kawowa take.

“A'a kai je ka ce gata nan zuwa”

Yaron na ficewa Neina ta kalli Lamido ta ɗora da

“Saboda girman Allah ka rufa mana asiri, muna neman abunda za mu ci ka jefa mu
cikin wani halin kuma”

“Amman Neina tun da bata so ai ba ci aka ana cilasta ba”

Cikin yaren fulatancin ta mayar masa da amsa.

“Lamido babu ruwanka baka san yadda abun nan yake ba, kai dai ka cinto gefen tiri
baka san tsakanin su ba, ka kama kan ka, ɗan Sarki ne fa”

Tana gama faɗar hakan ta nufi ɗakin da Namra take.

“Namra tashi kije yana kiran ki”

“Ni babu inda zan je”


Ɗukawa Neina tayi kamar zata zauna ta haɗe hannayenta.

“Ki yi ma girman Allah ki rufa mana asiri kije, haba Namra kar ki ba ni kunya mana
na faɗa masa ga ki nan zuwa, dan Allah ki tashi ki je”

“Neina ko naje mi zan ce masa? Ni na riga na faɗa masa karya sake dawowa ƙofar
gidan mu”

“Wallahi ban ce ki faɗa masa komai ba, saurarasa zaki yi, ki rufa mana asiri Namra”

Magiya Neina ta riƙa yi ma Namra kamar zata fasa mata kuka, sannan Namra ta tashi
cikin ɓacin rai da zafin zuciyata ta fita.
Gurin da ya tsaya ɗazun a nan ya sake tsayuwa, duk da dare ne hakan be hana
farin wata haskar fatar jikinsa ba, ga manyan idonsa da ya tsare ta da su har take
ƙoƙarin faɗuwa kamin ta ƙaraso kusa da shi. Kasa furta masa komai ta yi, duk wasu
kalamai da take da unƙurin faɗa masa sai ta kasa, suka tsaya mata iya cikin cikinta
zuwa maƙogaronta, dan bakinta ƙin bata haɗin kai ya yi, ga ƙamshin turarensa da ke
ta kaiwa hancinta hari.
Hannayensa dake rumgume aƙirjinsa ya cire ya maida cikin aljihu.

“Bude ba ki kiyi magana, faɗa min duk kalmar da kike tunanin ta cancanta a da ni,
ki yi duk abunda kike ganin idan kin min saki samu salama.
Ayau na tsayu gabanki ne saboda kawai na ji tarihin rayuwarki, ban je neman
auren ki, amman nasa a min bincike akan ki, tsakanin jiya zuwa yau labarin ki da
hawayen ki sun nuna min akwai abunda kike boyewa”

Hawaye ta fara, tana ƙoƙarin ture kalamansa dake son su yi tasiri a zuciyarta.

“Ba lallai ne na cimma burina akan ki ba, mman lallai ne na faranta miki rai, kuma
na taimaka miki ki cimma na ki burin, ina roƙon ki ki bani kaɗan daga tarihin
rayuwarki ko zan samu sukunin rayuwa, Namra ni ba ƙaramin mutun ba ne, kuma ba wasa
ya kawo ni nan ba, ki taimaka min wata ƙila ni ne silal farin cikin ki”

Ɗaga kai ta yi ta kalleshi.

“Ta ya farinciki zai dawo ga yarinyar da ta butulcewa iyayenta? Taya farinciki zai
dawo ga macen data zaɓi saurayinta sama da iyayenta? Faɗa min ta ya?”

Yayi shiru yana karantar kalamanta. Yawun bakinta ta haɗiye.

“Ba kowa ba ce ni, fa ce wacce ta butulcewa iyayenta, da zabi saurayinta sama da


su, wanda shi ne ya kai ni ga hakala.......”

Ƙoƙarin tsagaita kukanta take, dan ta samu damar labarta masa tarihin rayuwarta ko
zai samu salamar rabuwa da ita. Zagayawa yayi ya buɗe bayan motarsa ya ɗauko carpet
ya shimfiɗa mata. Sai da ta zauna sannan shi ma ya zauna nesa da ita zuciyarsa cike
da tsumayin jin labarin nata.
Sai da ta share hawayenta, sannan ta soma bashi tarihin rayuwarta...

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *73*

Idonsa sun kaɗe sosai sun yi ja, duk ɗigar hawayenta ɗaya sai ya ji kamar an watsa
masa ruwan zafi, ya kasa ɗauke kansa daga barin kallonta, har cikin ransa yake jin
kukanta da kuma zubar hawayenta, samun kansa yayi da mugun tausayinta.
Ita kuma ta rumgume ƙafafunta sai kuka take, ba ƙaƙƙautawa.

Handkerchief ya riƙo daga aljihunsa ya aje mata, ba tare da ya ce da ita komai ba.
Hannu ta kai ta ɗauka ta share hawayenta sannan ta fyace majina.
“Kin yi kuskuren zabar saurayinki sama da iyayen ki. Shiyasa Allah ya jarrabe ki,
bayan Ubangiji babu wanda ya cancanci girmamawa sama da iyayenki”

Ɗagowa tayi ta kalleshi idonta taf da hawaye.

“Amman wanda mahaifina yake son na aura ba cancance ni ba...”

Ya tari numfashinta.

“Amman ai ya baki damar fitar da wanda kika so, sai kika nace sai shi saboda kar ya
ce kin yaudareshi, ko ba haka kika faɗa min ba yanzu?”

Ta yi shiru tana sauraren hawayen dake bin fuskarta.

“Daga ƙarshe sai kuma ya yaudare ki, ya ci amanar ki, da ace kin aure wanda
mahaifin ki yake so, babu yadda za a ayi ya guje ki, wata ƙila sanadiyar hakan sai
ya shiryu, kuma duk abunda yayi miki dole su ne da laifi ba ke ba, baki san fushin
Ubanguji yana tare da fushin iyaye ba? Idan iyayen ki sun yarda da ke, to haka shi
ma Allah ya yarda da ke, kin yi aure mahaifinki yana fushi da ke taya za ki ga
ribar auren?

Kin yi kuskuren rashin komawa gida Namra, ko yanka namanki za su yi su dafa su ci,
bai kamata ki dawo nan ki tare ba”

“Idan kuma suka ƙi karɓa ta fa? Mahaifina ya ce karna kuskura na dawo gidansa da
sunan saki ko yaji”

“Komai ya ce miki haka ne, saboda yana cikin fushi ne, da kin koma ai ba zai iya
korar ki ba, idan kuma har idonsa ya rufe ya kore ki, to duniya zata miki masauki,
su kuma ta juya musu baya, jama'ar gari kuma su zage su, har sai shi da kansa ya
koma neman ki”

Ta bikita ɗaƴan ɓangaren na handkerchief ya share majiyar data cika mata hanci.

“Na yi nadama yanzu, na gane gaskiya”

“Kin yi nadama a lokacin da bata da amfani, kin sake tafka kuskure a cikin kuskure.
Namra ba mutum kika aura ba, mutum mutume ne mai kama da mutum, siffarsa da kamarsa
tasa kika ɗauka mutum ne, har kika masa inuwa, shi kuma ya saka ki a rana, mutumen
da bai shirya haɗa zuri'ah da ke ba, amman Namra da yanzu a ace m cikin ki yana
nan, a nan za ki zauna ki haihu kenan? Ba tare da kin koma gurin iyayen ko ba?”

Miƙewa ta yi tsaye ta yi tsaye ya saka takalminta, da zimmar komawa cikin gidan.


Sai shi ma ya miƙe tsaye.

“Can i have my handkerchief!”

Juyowa ta yi ta kalli handkerchief ɗin, sannan ta kalleshi.

“Yayi ƙazanta”

Ya faɗa cikin muryarta mai gaf da yin kuka.

“Please...”

Ya ɗaga mata gira ɗaya, like he's serious. Ta ɗan ɗauki mintuna kamar mai shawarar
miƙa masa abunda yake mallakinsa na ne.
“Please stop cry..”

Ya faɗa cikin muryarsa mai rawa kamar mai shirin yin kuka. Sai kawai ta miƙa masa
handkerchief ɗin cike da ƙyama. Shi kuma ya miƙa hannu ya karɓa idonsa na kan
fuskarta. Bata tsaya komai ba ta shigerwa tana ƙirƙirar wani sabon kuka.
Damƙe handkerchief ɗin yayi da dukan no ƙarfinsa, kamar abunda za a ƙwace masa,
ya kai fuskarsa ya lumshe ido.

Har cikin zuciyarsa yake jin sanyin hawayenta, ya samu mintuna biyu zuwa uku a haka
kamin ya buɗe motarsa ya shiga. Still da handkerchief ɗin a hannunsa yake driving.

“Da kin auri wanda Mahaifin ki yake so wata ƙila da ba mu haɗu ba, da ba zan iya
kawowa rayuwarki ɗauki ba”

Ya faɗa yana mai sa ɗayan hannunsa ya fiddo wayarsa, sai da ya hau babban titi
sannan ya rage gudun da yake ya danna ma Mai Martaba kira.
Ta ɗan jima tana ringing kamin a ɗauka.

“Assalamu alaikum”

“Wa'alaikassalam, Allah ya taimaki Mai Martaba”

“Babana kana lafiya?”

“Lafiya ƙalau Mai Martaba, Mai Mairtaba yanzu idan Madina (Sister sa wance suke uba
ɗaya) ta zaɓi saurayinta sama da kai ya zaka ji? Bayan kuma kai ka yi mata zaɓi?”

“Ba zan ji daɗi ba, sai dai kuma ba zan hana ta aurensa ba, amman kuma ba zata ga
da kyau ba, ba kuma dan ina mata fata ba, no saboda ba kasafai auren da iyaye basa
so yake zama alheri ba”

“Idan kuma bayan ta yi auren mijin ya sake ta fa? Bayan ya gana mata azaba, sai ta
dawo gare ka, ya za kayi?”

“Zan karɓe ta da hannu biyu na mata masauki ta yadda zan shimfiɗa mata sabuwar
rayuwar, ita da kanta zata yi nadama ta gane lallai Uba, Uba ne, ta yadda wata rana
idan ta ga wanda zai aikata hakan ita da kanta zata hane shi”

“Lallai Mai Martaba kai ne za ka taimaka min wajen dawo da martabar Namra”

“Wacece Namra?”

“Gobe da safe zan dira Katsina zan tabarta maka komai Mai Martaba”

“Allah ya kai mu”

“Amin mu kwana lafiya, Allah ya ƙara mana nisan kwana da lafiya”

Ya aje wayar yana murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa.

AMIRA POV.

Tana gama rubuta wasiƙar ta naɗe cikin wata paper, sannan ta ɗauki salati ta saka,
ta ta saka ta cikin wani madaidaicin kwali ta yi rolling da wani jan gayenta sai ya
fito kamar gift.
Sai da ta gama abunda ta ke sannan ta kwashe komai ta gyara gurin. Saman gado ta
koma ta kwanta tana kallon sili kamar mai tunanin wani abu. Haleema ce ta turo
kofar ɗakin ta shigo fuskarta ɗauke da damuwa dan ita har ga Allah tausayin Amira
take.
Kusa da ita ta zauna tana kallon kwalin dake gefenta.

“Yau duk baki leƙo mu ba? Ko abinci ba ki ci ba”

Sai a lokacin Amira ta tuna rabonta da abincin tun jiya da rana. Sai dai kuma har
yanzu bata jin yunwa. Duk ta wani zurma kamar marar lafiya.
Unƙurawa ta yi ta tashi.

“Bana jin yunwa, Dan Allah Haleema ki taimaka min ki kai ni tasha na bada wannan
saƙon”

“Saƙon minene Amira?”

“Wasiƙa ce na rubutawa mutumen da ya fara cuta na, wata ƙila idan ya karanta zai
gane ina raye har ya wanke, na koma gurin iyayena ko Allah zai sa Yayan ki ya so
ni”

Bata damu da sanin abunda yake cikin wasiƙar ba, ta miƙe tsaye

“Okay, bari na ɗauko mayafi na”

Tana ficewa Amira ta tashi cikin rashin kuzari ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta
da hawaye ya ɓata ta fito. Wannan karon Hijabi ta ɗauka ta saka, sai ta zauna gefen
gado tana kallon kwalin zuciyarta sai bugawa take.

“Mu tafi”

Haleema ta baɗa yayinda ta turo ƙofar ɗakin makulin motarta na hannunta. Da sauri
Amira ta ɗauki kwalin suka fice. Maganganu masu daɗi da tausasa zuciya Haleema ta
riƙa mata har suka isa tashar. Suna shiga aka riƙa tambayar inda zasu sai Amira ta
amsa da

“Motar Sokoto muke nema”

Aka nuna musu, almajira suna haɗawa da gudu ganin haɗaɗiyar mota a zatonsu ko da
kayan dako ne. A gafen motoci Haleema ta faka motar suka fito tare, da ƙafa suka
ƙarasa kusa da inda ake lodin motar sokoto suka samu direban yana daga gefe zaune
yana jiran a gama haɗa masa passengers. Sallama suka fara masa sai ya amsa tare da
mutanen da suke gurin.

“Dan Allah saƙo za a kai mu a sokoto”

Cewar Haleema.

“Ok na minene?”

Amira ta dire musu kwalin, kana ta ɗora da.

“Wannan abun za a kai ga addireshin”

Ta ƙarasa tana miƙa masa wata ƴar ƙaramar takardar. Hannu ya kai ya karɓa.

“Okay to zaki bada kuɗin mota, da kuma number wayarki da wanda za a kaiwa saƙon”

“Zan dai baka number na, amman ban da number wanda za'a kaiwa saƙon, shiyasa na
rubuta maka addireshin sa, dan Allah ka taimaka min ka kai masa har gida”

“Okay ba matsala, amman gaskiya ko baki yo ba sai kin bada dubu uku, dan za a kai
masa har gida ne, kuma kin ga yanayin da ake ciki ba mu cika son karɓar saƙo ba ma”

“Ina zuwa”

Haleema ta faɗa, sai ta juya ta nufi gurin motarta, bata ɗauki lokaci ba ta dawo ta
miƙa masa dubu uku ƴan ɗari biyar biyar.

“Gashi amman dan Allah ka tabbatar saƙon ya isa, ki bashi number wayarki so that
idan ya kai sai ya kira ya faɗa miki”

Ta ƙarasa tana kallon Amira. Ba musu Amira ta karɓi number wayarsa ta saka a
wayarta, sai ta masa flashing number ta ta fito, sai da ta tabbatar yayi saving
sannan ta juyo ita da Haleema suka nufi gurin da suka faka motar su.
Haleema ce ta fara shiga sannan Amira, har suka isa gida babu wanda yace da wani
uffan, Haleema na wani tunanin na dabam, Amira ma haka har suka isa gida.
Tun kamin su faka motarsu Haleema ta gane yayanta ya dawo, ganin yadda sojojin
suka koma cikin natsuwarsu sosai.

“Big bro ya dawo kenan!”

Ta faɗa tana zare key ɗin motar, Amira dai bata ce komai ba, har suka fita motar
suka nufi ƙofar shiga falon.
Gabanta ya faɗi sosai lokacin data saka ƙafarta cikin falo, ta yi ido biyu da
Abdool.
Abinci yake aunawa a cikinsa yana zubawa Ummi satti, yanayin fuskarsa kawai zaka
kalla ka fahimci baya cikin damuwa, dan annuri ne shimfiɗe a fuskarsa.

Cikin sanyin jiki Haleema ta ƙarasa kusa da Ummi dana wasar haƙura, dan tasan
laifinta na fita bata faɗawa Ummi ba.

“Daga ina kike?”

Ummi ta tambaya fuskarta babu alamun dariya. Ta ɗan sosa kai tana tunanin irin
ƙaryar da zata yi ma Ummi dan bata jin zata iya faɗa mata gaskiya.

“Ya Abdool an sauka lafiya”

Amira da ke can gefe Haleema ta miƙawa Abdool gaisuwa. Ba tare daya ɗago ya kalleta
ba ya amsa.

“Lafiya ƙalau”

Sai ya miƙe tsaye yana yi ma Haleema wani kallo.

“Daga Ina kuke?”

“Pizza na ce ta raka ni na siyo kuma ban samu ba”

Ta faɗa tana pretending like she's serious.

“Amman idan zaku je siyen Pizza sai kawai ki kama hanya ku fita without
permission?”

“I'm sorry Ummi i promise ba zan sake ba”

“You're very stupid, haka kawai zaki saka kafa ki fita ba tare da kin faɗa ba? Baki
san rayuwarku tana cikin haɗari ba? Ba ni kaɗai za a riƙa farauta ba har da ku”

Abdool ya faɗa yana kallonta har handkercheif ɗin dake hannunsa ya faɗi.
“Haba Big Bros Wallahi ba zan ƙara ba, dan Allah ku yi haƙuri”

Ta faɗa kamar mai shirin yin kuka. Amira kan idonta na kan Abdool, annurin
fuskarsa kawai take kallo, a ɗayan ɓangaren kuma tana Allah-Allah ya manta da
handkercheif ɗinsa ta ɗauke, ta yadda zata fi jin daɗin tuna sa idan tana tare da
shi.

“Miya hana ki zuwa makaranta?”

Ya tambaya yayinda ya risina ɗaukar handkercheif ɗin.

“Yau ba mu da lacca sai four”

Be sake ce mata komai ba, ya kalli Ummi.

“Zan je gurin Mai Martaba”

“Mu zaka ku? Tun da ka sauka naga ka kira shi fa, akwai abunda kuke shiryawa ko?”

“Kedai Ummi kawai ki sa ido ki yi kallo, wannan tsakanin ɗa da uba ne”

“Idan tayi tsami ma ji, miye sunan in-law ɗin tawa?”

“Da saura Ummi, bata kama hanyar zama in-law ba tukuna, sai mun yi settling
abubuwa. Her name is NAMRA...!”

Wani irin faɗuwa gaban Amira yayi har sai da kanta ya tsara.

‘Namra’

Ta maimaita sunan a ranta tana, tuna wacan Namra wacce take ganin ita ce silar
shiga ta wannan halin rayuwar. Kamin ta kalli Abdool da ya kai hannu ya ɗauki apple
ya fice yana wasa da shi. Ummi kuma ta tashi ta nufi Kitchen, sai ya rage daga
Amira sai Haleema ne a falon. Amira ta matsa kusa da Haleema ta dafa kaɗatar.

“Haleema zan shiga ciki, idan Ummi fa faɗi abunda za a girka da ranar nan kya sanar
da ni please”

“Okay Sleep well”

Cikin sanyin jiki ta juya ta nufi ɗakin Amal da ya zame mata kamar ɗakinta.

ABDOOL POV.

Cike da zumuɗi ya isa faɗar Mai Martaba, kai tsaye ya wuce part ɗinsa da yake zama.
A babban falonsa ya same shi, Hajiya Shafa na haɗa masa abun karyawa, yana ganin
ɗansa ya washe haƙura, wanda hakan sam be yi ma uwaegidan Mai Martaba daɗi ba.

Cikin girmamawa Abdool ya gaishe ta, ta amsa masa kamar babu komai sannan ya gaishe
da Mai Martaba yana masa kirari.

“Ba wani daɗin baki da zaka min sai da ka fara gaishe ta sannan zaka miƙa min
gaisuwa”

Dariya yayi shi da Hajiya Shafa, sannan ya ce

“Ayi haƙuri Mai Martaba, zafi zafina na zo dan labarta maka komai”
“Muma nan ai mun aje maka labari har da ɗuminsa”

Hajiya Shafa ta faɗa. Abdool ya ce

“Tau a fara bani na sha”

“Wannan albishir kuma Mahaifinka zai maka shi”

Ta tashi ta fice tana dariya. Mar Martaba ya miƙa ma Abdool tea da aka haɗa masa
shi kuma Abdool ya aje tea a gefe ya shiga haɗa ma Mai Martaba wani yana labarta
masa labarin Namra.

Sai kusan Sha ɗaya da rabi suka gama karyawa tare da Mai Martaba yadda Abdool ya
zage yana cin abincin ba zaka ce ya ci abinci gurin Ummi ba.
Mai Martaba ya jinjina lamarin Namra sosai kuma ya tausaya mata duk da be ganta,
bama abunda ya fi taɓa shi kamar yadda ya ji tana raɓe a gidan wasu bayan kuma
uwarta da ubanta suna raye.

“Amman Ina ka haɗu da ita?”

Abdool ya yi shiru yana tunanin faɗawa Mai Martaba gaskiyas lamari.

“Ranka ya daɗe ina binka bashin albishir fa”

“Albishir ɗin ka, zan faɗa maka idan ka samu natsuwa kun kai ƙarshen wannan
matsalar”

“Yanzu ya kake ganin za a ɓullowa lamarin?”

Mai Martaba ya gyara zamansa.

“Abunda za mu yi, zan sa a rubuta masa wasiƙa daga nan Masarautar zuwa can inda
yake, ai kana da addireshinsa ko?”

“Eh ina da shi, dan nasa an min bincike akan sa”

“Okay zamu saka a aika ma Sarkin Musulmi na sokoto shi kuma zai aika wani ya kai
masa wasiƙar”

“Amman Mai Martaba me zai hana ka aika masa kai tsaye?”

“Ai mu sarakuna bama haka, dole ne sai sarkin gari ya san da abunda wani sarkin
yake so a garinsa. Musamman babban sarki kamar shi”

“Okay zuwa yaushe za a aika?”

“Yau zamu aika, ina tunanin gobe zata isa gare shi”

Abdool ya ji daɗin haɗin kan da Mai Martaba ya bashi sosai da sosai. Daman ya
tsammaci haka, dan ƴasan yana samun goyon bayansa a dukan abunda zai yi.

KALSOOM POV.

*Bayan wata biyu*

Tun da aka soma shigo da kayan har aka aje,be ji motsinta a falon ba hakan ya
tabbatar masa da tana kitchen, kai tsaye ya nufi kitchen ɗin, fuskarsa ɗauke da
murmushi. Ta baya ya yi hugging ɗinta ya aika mata da kiss a gefen fuska.

“Me kike girkawa?”

Wuƙar dake hannunta ta aje ta juyo tana dariya.

“Hancin ka zan girka”

“An ya zaki iya cin hancin na?”

“Kwarai kuwa ta yadda Amaryar nan da taga baka da hanci zata ce ta fasa auren”

Ƙyalƙyalewa yayi da dariya, ya zageye kunkurunta da duka hannayensa.

“Shikenan sai ki kashe min kasuwa ko?”

“Eh mana ai ƙara ni kaɗai zan riƙa ganin kyan ka”

Ya riƙa hannunta yana dariya.

“Zo ki ga wani abu”

Gabanta yayi mugun faɗuwa, haka kawai ta annayana a ranta ba abun alheri ba ne,
cire hannunta ta yi cikin na shi.

“Bari na juya miya sai na zo”

Be mata musu ba, ya juya ya fice. Ta ɗauki minti goma a kitchen ɗin tana ta
fargabar fita, duk da bata san abunda zai nuna mata ba, tana ji a ranta kamar ba
alheri ba ne. Ba ƙaramin dauriya ta yi ba kamin ta wanke hannayenta ya juya miyar
sannan ta nufo ƙofar falo.
Tana ganin akwatuna jere a tsakiyar falonta, bugun gabanta ya ƙaru, idonta kuma ya
cika da hawaye. Ga invitation card da kwalayin minti da cinka a saman akwatunan mai
yawa ana ɗora. Jikinta yayi sanyi sosai, hawayen dake maƙalle a idonta ya gangaro
zuwa kumatun ta.

“Ashe haka Rashida ta ji lokacin da za a auro ni ko?”

Ta faɗa muryarta na rawa. Ɗagowa Hilal yayi ya kalleta, sai ya miƙa mata hannu
alamar ta zo, sannu ta fara takowa har ta kawo inda yake ta miƙa masa nata hannun.
Sai ya zaunar da ita ƙasan kujerar ya ɗora mata hannayensa saman kafaɗunta,
kasancewar shi yana saman cushion zaune ne.

“Ki duba ki ga idan akwai abunda babu zan ƙaro”

Kai ta girgiza ta miƙe tsaye.

“A'a ni nabar mata kayan duka ka kai mata, ina da kayana”

Shima.ya miƙe tsaye.

“Na sani ai, ba tsirara na auro ki ba”

Sai ta yi ƙasa da kanta tana hawaye. Hannunsa ya saka cikin nata yaja zuwa
ƙirjinsa, sai kawai ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi.

“Sorry dear, zan canja miki komai idan kina buƙata, just be strong”

Kuka tayi sosai har sai da ta ɓata mishi gaban riga da majina, sannan ta sake shi
ta nufi toilet ɗin falo saboda amai da taji ya cika mata baki.

ASIM POV.

Tun safe ya tashi ko da goma tayi yana cikin garin sokoto, A hotel ɗin Shukura ya
kama ɗaki, sai da ya ɗan huta sannan ya kira Ubangidansa ya sanar masa da ya iso.
Ya bashi tabbacin sai dare zasu gana, da alama can zai kwana inda yake, dan ya faɗa
inda zai same shi a gidansa da ke Sama road.
Fitowa yayi ya biya kuɗin wuni ɗaya, sannan ya ɗauki hanyar gidansu, zuciyarsa
cike da nishani, yana mai jin kansa lallai shi a yanzu wani ne.

Ko da ya isa unguwarsu ƙarfe ɗayan rana yayi, dan haka irin mazan nan masu zaman
kashe wando duk basa nan sai da yamma suke zama, kasancewar unguwar minannata, haka
suke da yamma ta yi, amman hakan be hana wasu ganinsa ba, dan tabbatar da shi ɗin
ne yasa wasu gayu zuwa su bashi hannu shi hannu su gaisa suna masa yaushe gamu.

“Kai ke da wannan?”

Ɗaƴan ya faɗa yana nuna motar dake kusa da su.

“Eh Wallahi sai a taya mu addu'ah”

“Toh Allah ya taimaka ya tsare. Kace kai ma ka shigo gari, ko da yake kana sirikin
Manjo Usman ai dole ka hau wannan motar”

Ɗan murmushi yayi.

“Babu ɗigon dukiyarsa nan”

Duk dariya suka yi, ba dan sun yarda ba, sai suka ƙara gaba suna nasu zancen.

Da farinciki ya shiga gida, yana doka sallama kamar wani baƙo. Da gudu Mama ta fito
dan tabbatar da muryar ɗan na ta ne ko bashi ba, ganinsa yasa ta daki ƙirji tana
ƙare masa kallo

“Ibrahim kai ne? Allahu akbar”

Ta shiga shafa kayan jikinsa tana kuka, shi kam sai dariya yake yana kallon ƙanensa
dake sanye da uniforn ɗin makaranta suna kallonsa. Da alama suma basu gama tabbatar
da shi ɗin ba ne.

“Ji yadda kuka tsaya kallo na”

Sannan suka yi dariya suka rugo a guje suka rumgume shi, suna murna. Sai da suka
gama zumuɗinsu sannan Mama ta ɗauko tabarta ta shimfiɗa masa tsakar gida, ko zama
be yi ba sai ga maƙota sun soma shigowa ƴan ganin gwan, kar ayi ba su, dan kace
kwabo har labari ya fara zaga unguwar.

Ya sha gaisawa da mutane sosai, dan sai a lokacin wasu ke masa ya jiki. Sai kusan
La'asar ya samu keɓewa da Mama suna tattauna lamuran duniaya.

“Amman wannan matar Allah yayi mata tausayi, irin wannan hidima haka? Ko dai auren
ka zata yi? Allah dai yasa taimakon Allah ne take maka”

“A'a ai matar babbar macece, kuma ta san ina da mata, Allah yayi mata tausayi ne
kawai”

“Ai har gobe na Allah basa ƙarewa, Allah saka mata da alheri, ba irin waɗannan
lalataccin mutanen ba, ai na so ka zo da Namra ta yadda zaka je kaita su ga irin
buɗin da Ubangiji ya yi maka”

Ya ɗan yi shiru kamin ya ɗora da.

“Ai na saki Namra...”

Mama ta daki ƙirji tana buɗe baki tare da gwalo ido.

“Kai ɗan nan? Yaushe?”

“Yanzu an kusa sati biyu gaskiya, bata zo nan ba?”

“A'a wallahi ai da tazo da sai mun samu labari”

“Daman na yi tunanin ba zata zo nan ba, amman nasan duk inda taje dole zata dawo”

“Hmmm ai ƙara ma daka sake ta, sai mutane gane ba dukiyar ubanta bace,dan nasan
yanzu duk wasu haka zasu ɗauka, kai lokacin ma da baka da lafiya har da masu cewa
wai ubanta ne ya ɗauki nauyin komai, ko zaka maida ita sai nan gaba”

“Wallahi Mama ina sakinta sai abubuwa suka buɗe min komai yanzu ba ni da
matsalarsa, yanzu haka zuwan da na yi na zo ne na faɗa muku na samu matar aure kuma
zan siya muku gida mai kyau na miliyan biyu haka sai ku zauna”

Tashi Mama ta yi tana rawa, kamar wata bayarabiya sannan ta ɗire tana ma Allah
godiya tare da sujada.

“Kai ɗan nan Allah ya zuba maka albarka, da mahaifinka na nan da rai da ya gode
maka”

Dariya yayi yana mai jin kansa sosai da sosai. Sun deɗe suna fira kamin ya cire
kuɗi mai yawa ya bata wai ta siyo kayan abincin, gida kuma ta sa abincika mata idan
an samu ayi masa magana. Sai da magariba ta yi. sannan ya yi wanka ya canja kayan
daya zo da su, ya gyara jikinsa ya bar gidan sai ƙamshin turare ya ke.

RASHIDA POV.

Juyi kawai take saman katifar da saboda wani mugun ciwo da zuciyarta ke mata, tea
ma daker ta iya tashi ta haɗa ta sha.
Bata yi mamakin ganin irin kiran da take ta samu daga ƙawayenta ba, ciki har da
Asmee, sai dai bata damu da ɗauka ba dan a tunaninta ko zasu tambayeta dalilin
barin gidan iyayenta ne, taji zafi sosai da taga har da ƙawayen da take nesa da su
ne cikin masu kiranta, babu shakka labarin barin gidan iyayenta ya same su kenan.

Wannan tunanin yasa ta ƙara jin wani irin zafi ya rufe mata zuciya, yana ɗaya daga
cikin dalilin daya sa ta ƙaurawace whatsapp saboda yawan tambayar gaskiyar mutuwar
aurenta da ƙawayenta ke yi, wasu kuma suna jajanta mata akan mutuwar Rafiq.
Yanzu ma wayarta ce take ringing, wannan karon Momi ce dan haka ita kam ba zata
ƙi ɗaukar wayarta ba, cikin hali na kamar marar lafiya ta ɗauki wayar ta kara a
kunnenta.

“Hello Momi”

“Ke Rashida kin san abunda ya ke faruwa kuwa?”

Ta tashi zaune da sauri cikin rashin gane zancen da Momi take mata.
“Miya faru?”

“Kina da labarin Hilal zai ƙara aure?”

“Eh na taɓa ji amman ban tabbatar ba”

“Kin san Teema ce matar da zai aura”

Haka maganar ta riƙa yi ma Rashida yawo cikin kai har tana jin kamar ɗakin ya juya
mata.

“Wace Teemar? Ba dai ƙawata ba ko?”

“Ita fa”

“How true it's?”

“Ga Iv nan Ummu Faisak ta zo da shi, ko ba ita bace Fatima Jafar Mai Goro?”

“Ita ce, ta ya hakan zai faru?”

Tayi saurin kashe wayarta ta kira Asmee, bugu ɗaya ta ɗauka.

“Hello na kira baki ɗauka ba, kinji abunda yake faruwa kuwa?”

“Da gaske ne kenan?”

“Ashe kin ji”

Ta katse kiran ta jefar da wayar saman katifa cike da tashin hankali, rasa gane ta
yi inda take sama ne ƙasa ne, duniya ne ko lahira, sai juya mata ɗakin ke yi, tana
numfashi guda guda.

“It can't be Teema, idan har ta tabbata da gaske ne sai na ci Uwarki...!”

Ta faɗa cikin wani irin zafin rai, a take ta zari mayafinta ta fice.

YASMEEN POV.

Yana jefar da scul bang ɗinsa, yasa hannu yana ƙwaƙwala gurin kashinsa, yana tafiya
ararrabe ya nufi kitchen.

“Momee na dawo”

Be same ta a gurin ba, sai Mai mata raino ya samu tana girka mata abinci.

“Ina Momee”

Ya faɗa yana jan rigarta.

“Tana ɗakinta”

Juyawa yayi da fuskar kuka ya nufi ɗakin nata, yana cigaba da ƙwaƙwala gurin kamar
mai jim ƙaiƙayi. Da hannu ɗaya ya tura ƙpfar ɗakin ya shiga.

“Momee na dawo, kin ce zaki ba ni chocolate da safe”

Harara ta watsa masa dan ta tsani wannan soshe-soshen da yake yawan yi.
“Ba zaka cire hannunka a nan ba? Zan ci ubanka Adnan idan baka daina saka hannu a
gurin ba, kai ƙazami ne ko?”

Ya yi saurin cirewa.

“A'a Momee ciwo ne yake min”

“Bari Dadee ya dawo ya saka maka magani, yana can ɗakinsa”

Ya faɗa, dan hana kowa ya saka masa ganin sai shi kaɗai, hakan yasa ya aje ganin
gurinsa shi kaɗai zai riƙa saka masa ganin.

“Zo mu gani”

Ta aje Namra dake hannunta, ta riƙa wandon makarantarsa ta cire, sannan ta sake
cire pant ɗinsa.

“Wannan ciwon yaƙi ya warke, ko dai maci ɗan wawa ne, amman kuma shi ai ba nan yake
fitowa ba”

Ta ƙara buɗe gurin da kyau tana dubawa.

“Momee da zafi, Dadee yace na daina bari a na buɗewa, kuma ya ce karna faɗawa kowa
zai dake ni idan na faɗa”

“Okay sorry ina duba maka ne, ai idan ya ji nice ba zai dake ka ba”

“Ya ce har da ke, kuma ya ce idan na faɗa abunda yake min sai ya yanke kamar yadda
ake yanka rago, ya cinye nama na, ya soye”

Dariya ta yi dan bata ɗauki abun gaske ba.

“Wasa yake maka, ba zai maka komai ba”

“Wallahi yayi rantsuwa, kuma ...”

Ya faɗa cikin muryarsa mai kamar kuka. Yasmee ta juyo da shi, ta zaunar.

“Kuma me Adnan..?”

Sai kawai ya soma matsa ƙwallah.

“Talk to your Mom”

“Yace zai ba ni duka da yawa idan na faɗa”

“Minene”

Ganin kamar ya tsorata yasa ta ƙyalƙyale da dariya ta soma masa cakulkuli, sai ta
jashi jikinta ta rumgume.

“Zo mu yi sirri da kai, ba zan faɗawa kowa ba”

Cikin dariyar cakulkulin da take masa ya ce.

“Allah zaki faɗa”

“Ba zan faɗa ba i promise”


“To kawo kunnenki”

Ta matso da kunenta bakinsa. Kaɗan-kaɗan ya raɗa mata.

“Dadee yake sa min abun shi nan, a baya”

Ta ɗago da mamaki tana kallonsa.

“Kai Adnan mu yi gaskiya da kai”

Kamin ya ƙara cewa wani abu mai aikinta ta ƙwalo mata kira.

“Anti Ana sallama”

Sakin sa ta yi ta tashi ta nufi falon, Zuciyarta da ɗayan biyu. Mai gadinta ta samu
tsaye a falon riƙe da kwali yana shirin miƙa mata.

“Ga saƙo wani ya kawo yace a ba Alhaji wai hannuna hannunsa”

Karɓa ta yi tana faɗin.

“Okay, wanene?”

“Wallahi ban san shi ba. Ya wuce dai”

Tana karɓa, ya juya ya fice. Ita kuma ta kalli yar aikinta.

“Abincin be yi ba ne?”

“Saura kaɗan”

Juyawa ta yi ta nufi ɗakinta, cike da son jin maganar da Adnan ya soma tsaƙura
mata.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *75*

Ko da sha ɗaya na safe ta yi Abbah da Anty Amarya suna katsina, amman basu samu
ganin Mai Martaba sai da aka sauko daga sallar azahar, duk da haka kuma be ba da
izinin a shigo da su ba sai da ya kira Abdool dan ya sanar da shi. Sai dai yasa an
masu masauƙi a gefen sauƙar baƙi, duk abunda ya kamata a yi musu, an musu, abinci
ma kusan kala biyar aka jera musu shi drinks, ba a maganarsa.

Mai Martaba be fito ba sai da Abdool ya iso. Sannan suka fito fada tare, ɗaya daga
cikin dogarai aka aika ya yi musu iso.
Daga Anty Amarya har Abbah faɗuwa gabansu yake, dukansu zuciyarsu ɗauke take da
fargabar kiran da Mai Martaba yake musu. Tun daga ƙofar faɗar Abbah ya tada kai
yana kallon irin dukiyar da aka narka a gurin, daman tun farkon shigowarsa gudan ya
koma baƙauye, dan duk kuɗin Abbah wasu abubuwan be taɓa ganinsu ba, sai a gidan Mai
Martaba, wata ƙila saboda yana sarki ne, shine abunda ya fi ayyanawa a ransa, ga
uban sojojin da aka zube a gidan sun matuƙar burgesa, ko ina na gidan cctv cameras
ne.

Be ƙara raina kansa ba, sai da aka walgale masa ƙofar faɗa ya shiga. Komai na faɗar
ruwan zinari ne, daga kan kujerun har center carpet, da fankar tsaye da ta sama
hatta da maɓallin wutar faɗar golden color ne, ga bangon gurin an masa kwalli da
wani abu mai kamar zinari, ga wani ƙaton agogon gmt na zinari a gefen faɗar.
Alkyabar Mai Martaba ma yau golden ya saka, kamar takalminsa, sai farin rawani da
ke kansa. Yarima Abdool na zaune gefensa, cikin shiga ta farar shadda, ya ɗora
baƙar hula a kansa, fuskarsa sai wani sheƙi take kamar ango.
Kallo ɗaya Abbah yayi ma Mai Martaba ya yi saurin sadda kansa, saboda wani kwarjini
da Mai Martaba ya yi masa, sai gashi ya zube ƙasa yana kwasar gaisuwa, kamar wani
ƙaramin talaka.
Mai Martaba be amsa ba sai dai dogaransa ne suke amsa, kamin ya ɗaga musu hannu, ya
muku musu izinin fita ba tare da yaƴi magana ba. Tsif ɗakin yai sai sanyi ac dake
tsara jikinsu, Abbah dai be sake cewa komai ba, balle kuma Anty Amarya da ko ɗaga
kai ba ta yi ba tun da suka shigo.

Tun daga shigowarsu, Abdool ya fahimci Anty Amarya ce mahaifiyar Namra, dan ga
kamanin Namra nan shinfiɗe a fuskarta. Mai Martaba yai gyaran murya, wanda hakan ya
tatttaro hankalin Abdool ya dawo gurinsa, dan jin shinfiɗar da Mai Martaba zai yi.

“Kai ne mahaifin Namra?”

Da sauri Abbah ya amsa gabansa na faɗuwa, tare da ɗaga hannunsa ɗaya yana bawa Mai
Martaba girma.

“Allah ya taimake ka Ni ne”

Mai Martaba ya ɗauki daƙiƙu ashiri da uku kamin ya ɗora da...

“Amman kamaninka da yanayinka be nuna zaka iya aikata abunda ka aikata ba, sam ba
kayi kama da mutumen da ya kori ƴarsa saboda ta zaɓi wanda take so ba”

Anty Amarya ta ɗan ɗago kaɗan ta kalli Mai Martaba da kuma Abdool, da take ganin
kamar ta san shi.

“Ko kana da dalilin yanke wannan ɗanyin hukuncin?”

Abdool ya tambaya, cike da son jin labarin ta ɓangaren Abbah, wata ƙila ya sha
banban da na Namra, idan kuma ya zo ɗaya, Namra ta faɗa masa gaskiya daman be zaci
zata masa ƙarya ba, sai dai yana tunanin zata iya ɓoye mata wani abu daga
labarinta, ko kuma laifin da ta yi ma Abbah ta.

“Ta zaɓi son ranta ne, bayan kuma na yi mata zaɓi, sannan ina ganin kamar wanda ta
zaɓa be dace da ita ba, ta ɓata taraiyyata da mahaifiyar yaron, kuma ta watsa min
ƙasa a ido cikin family mu shiyasa na sallama masa ita gaba ɗaya.”

Mai Martaba ya rausayar da kai, tare da kallon ɗansa kaɗan ya ɗauke kai ya mayar
gurin Abbah.

“Idan ta kasance kai ne kake son mata fa? Sai kuma iyayenta suka hana ka aurenta
har ya zama ka aure ta sai su yi fushi da kai, ya kake tunanin rayuwarka zata
kasance?”

“Allah ya taimaki Mai Martaba, ba zan jidaɗi ba”

“Miyasa ka auna ƴarka a muhallinka ba? Kai fa uba ne, ban yi tunanin zaka iya
aikata abu kamar wannan, ka kai matsayin da idan wani ya aikata ka kirashi ka yi
masa faɗa. Ƴarka ba ƙarar ta kawo a nan ba, kaga yaro gashi nan shi ya ji abunda
ya faru ya gurgiza da lamarin har yasa muka kira ka anan”

Mai Martaba na ajewa Abdool ya ɗora.

“Mijin da take aure ya sake ta, saboda ya ce a zubar da ciki ta ƙi, yanzu haka bata
cikin garin katsina tana Kaduna, gidan wasu rakuɓe, ba abincin kirki babu abun sha
na ƙwarai, kuma kullum kuka take, tana tunanin yadda za tayi ta koma gida har ka
karɓe”
Tun da Abdool ya soma magana Anty Amarya ta ɗago tana kallonsa, hawaye sai bin
fuskarta suke, daman kullum cikin kukan rashin sanin Halin da Namra take ciki take.
Sai dai zancen sakin da Abdool ya labarta mata ya sanyaya mata rai, hankalinta ya
kwanta sosai lokacin data ji dalilin kiran da Mai Martaba yake musu, daman da daɗi
tana addu'ah sai yanzu Allah zai amsa mata.

“Kasan abunda nake so da kai?”

Abbah ya girgiza kai tareda ɗaga hannu sama.

“A'a Allah ya taimake ka”

“Ina son ka yafe mata abunda ta yi maka, ko da ba zaka zauna da ita ba, ni zan
zauna da ita a matsayin ƴata, daman ni gida na gidan ƴaƴa ne, amman idan ka yafe
mata kuma ka saka mata albarka zata ga haske a rayuwarta”

Abbah ya sauke ajiyar zuciya.

“Allah ya taimake ka, ba wai bana son Namra ba ne, kawai ta aikata min abunda ban
taɓa mafarkin zata aikata min ba ne, ta zaɓi wani sama da ni, ta bar karatun ta da
danginta saboda shi...”

“Wallahi ta yi nadama yanzu, abunda kawai Mai Martaba yake so ka yafe mata mu zamu
zauna da ita”

Abdool ya faɗa yana mai saukowa ƙasa ya zauna kusa da Abbah. Anty Amarya ta ɗago ta
kalli Abdool.

“Idan har ya yafe mata, ni na fi kowa cancantar na zauna da ƴa ta”

Abbah ya data kai ya kalli Anty Amarya sannan ya kalli Mai Martaba.

“Mamana ta shiga rigarka ta samu alfarmarka, duk da yake ina jiran zuwan wannan
ranar da Mamana zata gane kuskure da kuma gangancin abunda ta aikata, na sani wata
zata dawo a gareni ko da kuwa mijinta be wulaƙanta ba, nasani wata rana zata gane
muhimmancin iyaye, da kuma irin gudumawar da suke badawa a rayuwa, ko da babu saki
na sani akwai ciwo, ba fata nake mata ba, amman nasan wata rana zai iya kamata ba
duk miji bane yake zama da mace mai wani ciwo, sam bana son na mutu na bar Mamana a
cikin halin da ta zaɓi kasancewa a ciki, na sani wata rana zata ratu ba ni, sai dai
bana son ta rayu a cikin halin ina fushi da ita, dan nasan ba zata ga dai-dai, ina
son Mamana sosai, kuma na yafe mata duniya da lahira”

Mai Martaba yayi murmushin ƙasaita irin nasu na manya.

“Lallai kana son ƙulla abota da ni”

Abdool ma yayi dariya mai cike da farinciki da har suka bayyana haƙoransa da kuma
dimples ɗinsa ya ce

“Ni da Mai Martaba muna godiya”

Anty Amarya ta share hawayen idonta tana murmushi.

“Dan Allah idan tana cikin gidan nan ku faɗa mata Mahaifinta ya yafe mata, ta fito
mu ganta”

“Bata tare da mu, tana can a Kaduna a wani gida rakuɓe, bata san Mai Martaba ya
aika maka ba, ni ne kawai na ga tana cikin matsala kuma na san irin matsalar da
rashin zama kusa da iyaye yake haifarwa”
“Allah ya maka albarka Allah ya raya maka iyalanka, ya cika maka burinka, ya
taimake ka akan dukan lamurranka, na gode sosai yadda ki yi wannan jihadin Allah ya
baka abunda kake so”

Ya amsa da “Amin” Yana wani sunsun da kai, shi ala dole ga surukin da ba san da shi
ba 😂.

Mai Martaba ya miƙawa Abbah hannu yana murmushi.

“Yanzu kam zamu yi gaisuwar mutunci da kai, kaga har ƙoƙarin raba uwa da ƴa kake.”

Mai Martaba ya faɗa yana miƙewa tsaye. Da sauri Abbah ya miƙe tsaye, da hannunsa
biyu ya riƙa hannun Mai Martaba yana dariya.

“Tuba na ke ranka ya daɗe, Allah yaja kwanan ka”

Juyawa Mai Martaba ya juya Abdool ya miƙe tsaye da sauri ya take masa baya. Har
turakarsa Abdool ya rakashi farincike shinfiɗe a fuskarsa, Mai Martaba na shiga
Babban falonsa Abdool ya riƙa alƙyabarsa ya cire masa ya jingine, sannan Mai
Martaba ya cire rawaninsa da kansa ya aje a gefe, da sauri Abdool ya ɗauki rawanin
ya aje a muhalinsa. Sannan ya zo ya zauna ƙasan carpet ya dafa ƙafafun Mai Martaba
yana dariya.

“Na gode sosai da karamcin da Mai Martaba yayi min, ba zan taɓa manta wannan ba,
Allah ya ja zamanin ka”

Murmushi yayi sai da aka ɗauki daƙiƙu sannan Mai Martaba ya amsa da

“Amin. Nan da minti talatin zamu je ɗan dime ƙaddamar da zakka, idan da hali sai ka
shirya muje”

“...A...”

Sai kuma yayi shiru. Kallonsa kawai Mai Martaba yayi hakan ya cilastashi ƙarasa
maganar.

“Da naso naje ne can Kaduna na kai su inda take”

Mai Martaba ya sake kallon ɗansa, irin kallon nan na akwai wani abu a ƙasa.

“Babana be kamata kana saka kanka a cikin irin wannan rayuwarba, karka manta kai
ɗan sarki ne, kuma nan gaba kaɗan kai Sarki ne, sannan kai mutun ne mai babban
muƙami a nigeria, be kamata ana ganin fuskarka a ko'ina ba, wani gurin kamata yayi
ka aika, ko kasa ayi. Shi babban mutum ba ko ina ake son yana kasancewa ba,
musamman ƴaƴan sarakuna, yana janyo raini, wani gurin ma yakan zubar da mutumcin
mutum, amman kai sai naga kamar baka damu da hakan ba”

Yayi ƙasa da kansa, dan yasan Mai Martaba ya faɗi gaskiya, sai dai shi kan har ga
Allah yana son ya zama na farko da zai fara yi ma Namra wannan albishir ɗin ko ba
komai zai ƙara kwarjini a idonta.

“Amman Mai Martaba ina son na kasance nina zan yi ma yarinyar nan Albishir, idan
mun kama hanyar Kaduna yanzu kasan kamin yamma mun isa”

Mai Martaba ya shafa fuskarsa.

“Idan har ganinta kake son yi, zaka iya aikawa a taho da ita”
“She's so stubborn ba lallai bane ta zo, kuma abun zai fi burgewa idan iyayenta da
kan su sukaje suka ɗauko ta”

Kallon tsab Mai Martaba yayi ma Abdool sai ya ɗauke kansa, tare da ɗaga masa hannu,
alamar go ahead.

*** **** ****

Fitar da Mai Martaba da Abdool suka yi ne, yaba Anty Amarya damar data kai ta ƙare
ma Faɗar kallo. Manyan hotuna da ta gani na Abdool ɗaya a cikin kayan sarauta ɗaya
kuma a cikin kakin soja, yanzu kan sarai ta tuna waye Abdool. Mutumen da ya taɓa
taimaka mata lokacin da motarsu ta lalace ana ruwan sama.

“Gaskiya yana da kirki, matar ka da ƴaƴanka sun yi dacen uba na gari”

Ta faɗa idonta kan hoton Abdool. Abbah dai be ce komai ba, sai fama idonsa abinci
yake yana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi faɗar.

Fitowar Abdool ne yasa duk suka maida dubansu gurinsa. Wata shigar ce a jikinsa
bata ɗazun ba, wannan ma ta fitar da kyausa, da kuma annurin fuskarsa. Zuwa yayi ya
risina gabansu, ya yi ƙasa da muryarsa sosai.

“Idan kun shirya zamu je Kaduna yanzu sai na nuna muku inda Namra take”

“Abunda muke jira kenan”

Anty Amarya ta yi saurin amsawa.

“Mai Martaba yana shiri ne, idan ya fita muma zamu kama hanya”

Ya faɗa yana kallon fuskar Abbah dan yaji me zai ce. Murmushi kawai Abbah yayi ya
ɗaga masa kai, yana masa kallon mutum mai hankali da natsuwa.

NAMRA POV.

Murmushi kawai take, sai ɗaga kai tana maidawa, duk firar da ake, bata saka baki
saboda itama nata ya isheta, su kansu suna firar ne ɗan kawai su rage mata kewa.
Amman ta ƙi ta sake, sai dai a kan yi murmushi ko ɗaga kai, gudun kar suce ta ƙyale
su, tun da Abdool ya takalo mata maganar gida sai ta koma wata irin, tunanin
rayuwar jindaɗin da take ciki ta baya ta riƙa dawo mata, da kuma tunanin halin da
Asim ya jefata, ga halin ko in kula da ya nuna mata, da kuma ƙin son haɗa jini da
ita, ace duk tsawon wannan lokacin be neme ta, da gaske baya da buƙatar ta kenan?
A ɗayan ɓangare kuma tana tunanin yadda zata shirya da iyayenta har ta koma ta
zauna a tare da su wanda take ganin abu ne mai matuƙar wahala yin haka.

Duk dariya suka sa lokacin da Lamido yake bada wani labari na ban dariya, ita kam
Namra sai ta saka kuka tana mai ɗaga murya dan damuwarta tasa ta manta da agaban
jama'ah take, babu wanda hankalinsa ya fi tashi kamar Lamido, dan ya tsani ganin
Namra cikin damuwa balle kuma zubar hawayenta. Sai da taga hankalin kowa ya dawo
kanta sannan ta sassauta kukan da take ta tashi da gudu ta shige ɗaki. Ajiyar
zuciya Lamido ya sauke cike da rashin daɗin rai ya ce

“Yarinyar tana cikin damuwa, ni ko bana son ganin ta cikin wannan halin, dan zai
ƙara mata damuwar ne kawai, babu abunda yake raina a yanzu kamar na maza sanadiyar
farincikinta, zan yi iya yadda zan iya na ganin na cire ta cikin wannan halin
inshallah”

Neina ta miƙe ƙafafunta tana kallon ɗanta cike da son sa da kuma tausayinsa ta ce
“Cire yarinyar nan a damuwa abu ne mai wahala Lamido, ga dukan alamu ƴar babban
mutunce, shiga irin lamarin gidan su sai yi wahala gareka tun da kai ba ɗan kowa ba
ne”

Ɗauke kansa ya yi ya maida gurin ƙofar da Namra take. Sai da Neina ta tashi sannan
ya miƙe tsaye yana ɗan ɗingishi ya nufi ɗakin. Zaune ya same ta kusa da ƙofa tana
raira kukanta mai ban tausayi da taɓa zuciya.

“Namra kukan nan da zai miki magani da tuni yayi miki, kina ƙara saka kan ki ne
cikin damuwa ne kawai”

Ɗago kai ta yi ta kalleshi.

“Idan ban yi kuka ba mi zanyi? Kana tsammanin mace data shiga cikin halin da nake
ciki zata yi abota da dariya ko farinciki? Ba zaka gane abunda nake ji ba”

“Nasan kin shiga rayuwa kala-kala amman kuka ba zai miki magani ba, ki taimaka min
ki tausaya min ki daina wannan kukan Namra, saboda gani nake kamar nine silar zubar
hawayenki, ina damuwa sosai”

Hannayenta biyu tasa ta share hawayenta, sannan ta miƙe tsaye ta nufi gurin katifa
ta zauna, ta yo ƙoƙarin tsayardar kukanta ne kawai dan ta lura da damuwar da Lamido
yake idan tana kukan, balle kuma har ya kai ga yi mata magana, ita kanta tasan ba
kowa ne zai juri zama da ita ta dinga masa kuka kamar ƙaramar yarinya.
Ajiyar zuciya Lamido ya sauke ya shafa fuskarsa sannan ya juya ya fice. Ba tayi
minti talatin da zaman ba, taji yaro ya doko sallama wai Abdallah daga Katsina yana
sallama da Namra. Wani baƙin haushi ta ji ya turniƙe ta, yau kuma da wacce ya zo?
Me yake nema a gareta ne? Ba zai barta da damuwarta ba! Tana jin motsin shigowar
Neina ta yi saurin kwantawa saman katifar ta lafe sosai kamar ta yi bachi.

“Na san ba bachi kike ba Namra, kuma kon ji lokacin da aka ce ana sallama da ke a
waje, ki rufa mana asiri ki tashi kije”

Neina ta faɗa zuciyarta Fal da tsoro, dan ita tun da taji ance ɗan sarki ne, duk
fargaba da tsoro suka kama ta, kullum zulluminta ɗaya kar yasa ayi musu wani abu.
Sosai Namra ta so tayi pretending like tayi bachi amman jin yadda muryar Neina take
mata magana kamar mai magiya, yasa ta motsa har ta buɗe ido ta kalle

“Neina ban san me mutumen yake nufi da ni ba, me zai zo yayi min a yanzu?”

“Kije dai Allah, ko ma minene zaki ji, kin rufa mana asiri Namra, kin ga mu
talakawa ne bayin Allah, karki ja mana abun ba zamu iya ɗauka ba”

“Bana nufin janyo muku komai Neina, amman kamar ba ki fahimci abunda nake nufi ba”

“Na fahimta, kawai ki tashi ki tafi, idan kuma har baki jin tafiyar, ni zan iya
bashi izinin ya shigo nan yayi magana da ke, wata ƙila ma carpet ɗinsa da daya
manta shekaranjiya ya zo karɓa”

Kamin ta Namra ƙara yin magana. Lamido ya ɗaga labulen ɗakin ya kunno kai yana
faɗin.

“Neina kina tsoron masu milki da yawa”

“Dole na tsoraci masu milki Lamido, kafi kowa sanin sune sanadin shigar mu wannan
halin”

Tana kaiwa nan ta juya ta fice. Shi ma Lamido juyawa yayi ya fice cikin rashin
daɗin rai, yakan samu kansa a cikin rashin jindaɗi a duk lokacin da Yarima ya tsaya
ƙofar gidansu da sunan kiran Namra.
Namra bata motsa daga inda take ba, sai ga Neina ta dawo ɗakin riƙe da carpet ɗin
ta miƙa mata.

“Tashi kije ki kai masa, ko ba komai wulaƙanta ɗan Adam babu kyau, balle babban
mutun kamarsa”

Wannan karon Namra bata yi mata musu, ta tashi ta karɓi carpet ɗin ta miƙe tsaye,
already tana da hijab ɗinta sanye, sai kawai ta bi bayan Neina suka fice tare,
takalminta ta zura, ta nufi ƙofar fita.

As usual gurin daya saba tsayuwa ya tsaya, tana tunkara inda yake tsaye gabanta ya
soma faɗuwa, ta rasa dalilin daya saka yake mata kwarjini, tana isa kusa da shi ta
miƙa masa carpet ɗin ta ce

“Ga carpet ɗin ka dan nasan ita ka dawo ƙarɓa”

Be ɗago ya kalleta ba, balle ta gane maganarta ta ratsa kunnensa, sai sha'aninsa
yake da wayarsa, kamar be san da tsayuwarta a gurin ba.
Tayi tsayuwar minti ɗaya a gurin zuwa biyu, kamin ya ɗago ya kalleta ta cika sosai
da taji kamar ta jefa masa wata baƙar magana amman bakinta be bata haɗin kai ba,
gashi sai jin take kamar ta jefa masa carpet ɗin, sai dai kwajininsa ya hana
hannunta kuzari, ballema ta yi ƙoƙarin yin hakan.

Babu enough hasken da zai iya haske fusakarta sosai, amman hakan be hana shi
karantar tana ciki fushi ba, ko ba komai yasan ya ɓata mata lokaci, kuma ya shiga
huruminta na ƙinjin gargaɗin da tayi masa akan kar ƙafarsa ta sake tako ƙofar
gidansu.

“Ƙomai naki kyau yake min Namra, fushinki da faɗanki da tsawarki duka burgeni suke,
abu ɗaƴa ya rage min yanzu na gani naki, shine dariyarki”

Ya faɗa yayinda ya ke cigaba da dannar wayarsa, amman hankalinsa da idonsa suna kan
Namra. Wannan karon tayi nasarar yaudarar kanta, har ta samu haɗin kan idanuwanta,
ta jefe Abdool da wani shegen kallo.

“Carpet ɗin ka kawai na fito kawo maka, ban fito dan ka yaba fushi ko faɗa na ba,
kuma bana tunanin an halicceka dan ka ga dariyata kawai, saboda haka karka ɓatawa
kanka lokaci, ka karɓi Carpet ɗin ka”

“Miya hana ki bar carpet ɗin a inda na barta tun ranar? Wane salo ne yasa kika
ɗauke ta? Yanzun da nazo na aika nace a bani carpet ne? Wato ba zaki iya ganin abun
Abdool ki ƙyale ba ko?”

Wannan karon da murmushi a fuskarsa, ya soka mata wannan maganar, ya gyara


tsayuwarsa yana kallon taurarin da suka yi sama ado.

“Ai mu ƴaƴan Sarakuna bama shimfiɗa kuma bama ɗaukewa, wacan karon ma ba na
shimfiɗawa kai na bane a karon kai na, nasan wata rana zan rubuta a diary, bayan
Mai Martaba da Ummina, na taɓa shimfiɗawa Namra carpet har ma na zauna da ni da
ita”

“Amman kai ka baka da aikin yi Wallahi, Allah yayi min tsare da mugun ƙudirinka,
baka cikin hayyacinka ne? Miyasa zaka zo kana min wasu kalamai kamar wanda be san
halin da nake ciki ba?”

“Ina ma ina da mugun ƙudiri a kanki! Da kin ga yanzu sace ci kawai zan yi na gudu
naje nayi rayuwarda da nake so da ke, ni kaina ina mamakin halin dana shiga saboda
ke, ban san miyasa ƙwaƙwalwata take ƙoƙarin zautuwa da lamarin ki ba”
Kai ta girgiza ta jefar da carpet ɗin a ƙasa.

“Wallahi baka da tausayi baka da tunani kwata-kwata a zuciyarka, taya zaka kalleni
ka yi irin wannan maganar, you're fake Prince ba asalin Yariman ƙwarai bane kai,
wata ƙila sarautar ta ku ta ƙauye ce, dan yariman ƙwarai ba zai tsaya mace kamar ni
tana faɗa masa magana ba”

Lumshe ido yayi yana murmushi, tare da tsutsar baki kamar mai shan Sweet Candy. Ko
da ya buɗe idonsa har ta ɓace daga gurin kamar walkiya.
Murmushin da ke fuskarsa ya faɗaɗa, kamin ya shiga muhalin massages ya aika
saƙo. Cikin mintunan da basu fi goma ba, sai ga wata mota ta faka a gurin ɗauke da
Anty Amarya da Abbah.

“Ga gidan can”

Ya faɗa yana nuna musu da kai, sannan ya buɗe motarsa ya shiga. Su kuma suka doshi
ƙofar gidan, Abbah ne ya tsaya daga waje, Anty Amarya ta kunna kai ciki, zuciyarta
sai bugawa take fat fat fat...

HILAL POV.

Ba a'ayi wasu events ban da walima, daman can shi baya ra'ayi sai kuma aka ci
sa'ah amaryar tasa uztaziyace ita bata da son duniya. Ranar jumma'ah akayi walimar
bayana an saka amarya lalle kamar yadda al'ada ta gada. Sai aka ɗaura aure ranar
asabar, an yi taro sosai musamman ta ɓangaren Teema tun da ita aurenta ne na fari,
kuma ita ta farko mace da mahaifinta zai fara yi ma aure. Yadda Hilal yaƙe yaƙar
baki yana amsa gaisuwar mutane da ala sa albarka sai ka ɗauka auren so da ƙauna ne
suka yi shi da Teema, tun da sha biyu aka ɗaura aure aka yi liyafar cin abinci
bayan a sauko daga sallar azahar. Shi kam be samu dawowa gidansa ba sai da yamma ta
yi lis.
Yadda ya tararda Kalsoom be yi zaton zai same ta haka ba, ta bala'in ruɗashi, kyau
tayi har na fitar hankali, bakar shaddace jikinta an mata riga da saket, ɗinkin ya
matse ta ya fitarda surar jikinta sosai, ta kashe ɗaure ɗankwalinta ya kalli kudu
masu gabas, ga wata uwar kwalliyar kanti da aka mata a fuska, yadda take motsa
bakinta ma abun kallo ne.

“Ango ka sha mai”

Ta faɗa tana wani fari da ido. Shi dai mutuwar tsaye yayi a ƙofar falon yana
kallonta, sallama ma sai ta gagari bakinsa, ji yayi kamar ya je ya rumgumeta sai
dai ƙanenta da kuma Amiyarta Salma dake falon sun han shi rawar gaban hantsi.
Yana amsa gaisuwar da suke masa ya nufi ɗakinsa, zuciyarsa cike da ƙaunar matarsa,
dan yaji daɗin halin daya same ta ta bashi ƙwarin guiwa sosai, shi da ya zo da
zimmar ya lallaɓata kar ta saka ranta a damuwa, sai gashi yaga kamar ma ta fi shi
farinciki.

Babbar rigarsa ya fara cirewa sannan ya zauna saman gado, sai gata ta shigo
hannunta riƙe da copin madara ta yanka masa ayaba ciki ta saka sugar kaɗan. Saman
ƙafafunsa ta zauna ta riƙa aika masa madarar a baki, shi ko sai wani lumshe ido
yake yana buɗewa kamar wani tsohon ɗan iska, kamin yasa hannayensa ya zagaye
kunkurunta.

“Wannan ado haka ai sai ki haukata, so kike amaryar nan ta rasa gane kai na ko?”

Murmushi ta yi ta aje kofin a ƙasa tasa hannayenta ta riƙa kunnensa ta ɗora


goshinta saman nasa.
“Ai niban yarda zata gane kan ka ba, dan wata mace bata isa ta shigo gidana ta fini
gane mijina ba, da dai Rashida ce da ita ba zan musa mata ba, saboda ta rigani
saninka, ni kuma a yanzu na fi Amaryar ka sanin waye kai”

Murmushi yayi yana shafa bayanta da suka hannayensa biyu. Dauke kanta tayi daga
nassa but stilll hannayenta na rike da kunnensa guda biyu.

“Wai ance ƙawar Rashida ce da gaske?”

Ya ɗaga mata kai yana wani lumshe idonsa da suka kaɗe.

“Uhnn amman ai ba ni nace ina son ta ba, Hajiya ce ta haɗa auren saboda ta yaba da
tarbiyarta”

Ta yi murmushi kamar ba komai, alhalin na ciki na ciki.

“To Allah ya baku zama lafiya”

Sai ta saki kunnensa ta riƙa hannayensa dan tana jin yana ƙoƙarin wuce gona da iri,
ta miƙe tsaye.

“Ina zaki?”

“Aiki zanje na ƙarasa”

Yayi saurin miƙa hannu ya riƙota.

“Haba karki zalince ni baiwar Allah”

“Ba wani zalinci, nima fa mai tsada ce kamar amarya, dan haka ni jiki zaka siya ba
baki ba”

“Ai har kin fi amarya tsada, ke da ga wannan ciki, amman dai amin farashi mai sauƙi
ta yadda zan iya biya”

“Ba yanzu zamu yi cininki ba, kai fa ango ne karka manta, nan da ƙarfe goma na dare
sai yadda ka ga dama zaka yi da amaryarka”

“Bari wanka da kashi indan ganin hadari, ayi jiran abunda ba tabbas bayan ga ki ina
gani”

Ta fisge hannunta ta nufi ƙofa.

“Ni kan nan gani na bari wannan wunin da daren ba nawa ba ne”

Ganin zata fice da gaske yasa shi wara ido, jikinsa a mace yace

“Wai da gaske kike yi? Ki taimaki bawon Allah, karki jefa rayuwarsa cikin haɗari”

“Au naka wasa ne kenan!”

Ta fice tana dariya kamar ba komai, sai dai can cikin zuciyarta ji take kamar an
aza mata garwashin wuta a ciki, saboda kishi da baƙinciki. Tana ta ƙoƙarin yaƙar
zuciyarta ne, dan bata son ta saka kanta cikin matsala saboda cikin dake jikinta,
daman can lafiyar cikin be isheshi ba, idan kuma tace zata saka damuwa a ranta, to
zata cutar da kanta ne kawai, tun dai aure an ɗaura, kuma tasan mijinta yana sonta,
sai dai ɗan kishi da ba'a rasa ba.
Bayan fitarta, ta shiga bathroom ɗinsa yayi wanka, ya fito ya shirya cikin wata
shaddar gizna mai kyau da sheƙi. Yana cikin saka agogon hannunsa Kalsoom ta shigo
ɗakin ɗauke da plate ɗin abinci. Fried rice ce and pepper chicken sai ƙamshi take,
kallo ɗaya yyi ma abincin ya ɗauke idonsa wai shi ala dole yana fushi da ita.

“Waya ce miki abincin zan ci? Ai ba yunwa na ke ji ba”

“Shikenan kuma ango sai yayi fushi ranar aurensa?”

“Waya ja nayi fushin? Sai ka taɓa abu a hanaka lasawa, ai wannan cin zalin ne”

Gwalo ta mishi taja ƙofar ta fice. Sai ta fashe da dariya.

“I love you”

Ya furta tana shirin zama ya ci abincin. Shi kansa be san yaji yunwa kamar haka ba
sai yanzu, tass ya cinye abinci da da lemun kankana data haɗa masa mai lemun tsami
ciki da sugar kaɗan, har ƙashin sai da ya taune ya tsotse ruwan, dan yaji daɗin
abincin sosai, ga lemun da sanyi sai rmratsa ƙwaƙwalwarsa yake, bayan ya gama ya
tashi yana hamdala. Tana shigowa ta saka masa ɗariya, har da riƙe ciki.

“Ni dai nasan mijin Amarya yana jin yunwa”

Shima dariyar kansa yake dan yasan yayi aiki.

“Ai ba ni na ci ba, aljanuna ne suka ci”

Matsawa yayi ya maita kiss a goshi.

“Amarya tace ta yafe miki daren nan na ta”

“Uhmmmm”

Ta wara ido.

“Wace sakaryar amaryace zata yarda ta yafe wannan daren mai tsada a rayuwar ko wacw
ya mace, balle kuma da gwarzon namiji kamar ka”

Ya kalli kansa yana wani kaɗe shaddarsa.

“Allah? Ina jin daɗin yadda kike yaba ni”

“Ai ka haɗu ne Malam, dole a faɗa”

Ya riƙa fuskarta ransa fari ƙal da farinciki.

“I love you so so so very much”

Murmushi ta masa as respond, ya fice yana dariya. Sai ta ji tashin motarsa cire
ɗankwalinta ta jefar, ta faɗa saman gadonsa ta fashe da kuka.

ASIM POV.

“Yes...!”

Ya bugi ganbun motarsa yana dariyar da har zuciyarsa ita ce.

“Kin biyani Mardiya, zan baki mamaki, kuma auren mu nan kusa nake sonsa ba sai nesa
ba, dan haka daga yanzu ki shirya a ko yaushe zan iya zuwa gaishe da iyayenki,
sannan na turo magabatana”

Hannayenta biyu tasa ta rufe fuskarta 5ana dariya, sai tayi cikin gidansu da gudu
kamar wata mai kunyar gaske.
Ya daɗe tsaye a gurin yana kallon ƙofar gidansu, sannan ya zaro wayarsa dake
ringing ya kara a kunne.

“Na'am Hajiya kin dawo ne?”

Ban ji ma tace masa ba, sai kawai naga ya gyaɗa kai yana faɗin.

“Okay kina ina yanzu?”

Can kuma sai naga fuskarsa ta canja.

“Eh nasan gurin. Okay gani nan zuwa”

Ya sauke wayar kamar mai tunani. Can kuma ya ɗaga kafaɗunsa. Ya buɗe motarsa ya
shiga.

Yana cikin driving ya kira ƙanen mahaifinsa dan jin yadda aka yi maganar gida.

“Eh yana da kyau sosai? Bedroom nawa ne a gidan? To ko dai mu bari sai an samu
wani? Okay ba matsala”

Ya kashe wayar, sannan ya ƙara gudun motarsa, cikin ƴan mintuna ya isa unguwarsu
Nably, a kusa da gidansu ya faka ya sake kiran Hajiya.

“Gani na ƙaraso unguwar, amman ban ganr gidan ba”

Daga ɗayan ɓangaren ta amsa masa.

“Baka ga wani green gate ba?”

“Na gani, Mai farin fenti”

“Eh to ka shigo ciki amman ka tsaya daga gate zan fito na kawo maka”

“Okay”

Ya tashi motarsa ya nufi gate ɗin gidan. Be ƙara gasgatarwa ba har sai da ya shiga
harabar gidan, kusa da gate ya faka, yana ƙara kallon harabar gidan.

“Akwai bura'uba...”

Ya faɗa yana kallon Hajiya Sadiya wacce ta fito riƙe da ƙatuwar leda, sai faman
sauri take kamar wacce ta yi sata.

“Ka saka min a wannan account ɗin”

Ya miƙa masa farar takarda tare da ledar dake hannunta. Cikin ladabi ya karɓa ya na
faɗin

“Hajiya wannan ma gidanki ne?”

“Eh jeka dan Allah da sauri, bana son a tararda kai”

“Okay”
Ya koma cikin motar yana ta kallon gidan. He just can't believe gidan Hajiya ne, mi
hakan yake nufi ita mahaifiyar Nably ce ko yar'uwarta.? Har ya bar gidan be samu
amsar tambayarsa ba.

YASMEE POV.

Tana jin tsayawar motarsa ta tashi da sauri ta nufi kitchen, cox she dunno what to
do, kuma tana jin kamar bata son ganinsa, duk da tana ƙoƙarin yaƙar zuciyarta dan
sanin gaskiyar lamari. Hannayenta biyu tasa ta dafe fuskarta tana busar da iskar
bakinta.

‘Ni fa lauya ce, ni nake fawa wasu magana, ni na saba bincike, dan me yau kuma zan
rikice, i need to do this ko dan na cire kaina daga zargi’

A zuciyarta take wannan maganar, a fili kuma murmushi ne shimfiɗe a fuskarta ta


juyo tana amsa kiran da yake mata.

“Yau wace rana baki je office ba ne?”

Yayi mata kiss.

“No naje yau cases biyu ne kawai da ni, ina gamawa na dawo, ya aikin naka?”

“Alhamdullah, ina da labari mai dadi, Abbah (Baban Namra) ya buɗa mana wani sabon
kamfani a Abuja, kuma nasan niɓe zan kula da shi”

“Wow amman Abbah ya kyauta mana, Allah yasa hannu a ciki, ko shi yasa aka aiko maka
da wasiƙa? Ɗazun an kawo wasiƙa a aje maka”

“Waya kawo”

“Wallahi ban sanshi ba, tana nan ɗakinka na aje maka”

Freezer ya buɗe ya ɗauki gorar ruwa ya nufi ƙofar fita yana tambayar abunda aka
dafa. Da kallo Yasmin ta bishi bayan ta bashi amsa idonta cike da ƙwalla.

“Allah ka sani ina son mijina, Allah karka tabbatar da zargina akan sa”

Ta share hawayen da suka zubo mata. Tana ƙoƙarin fita sai gashi ya shigo riƙe da
wasiƙar hankalinsa tashe.

“Kin karanta wasiƙar nan Yasmin?”

“A'ah miya faru?”

Ba komai, ya juya ya fita da sauri. Sai da ta tabbatar ya shige ɗakinsa sannan ta


rufa masa baya. A bathroom ɗin falo ta tsaya ta sakama ƙafafunta ruwa gudun kar
yaji sawun takun ƙafarta. A bakin ƙofar ɗakinta ta kara kunnenta, sai dai bata ji
alamar motsinsa a cikin ɗakin ba. A hankali ta tura ƙofar ɗakin daman be mata rufin
ƙwarai ba, nan ma babu alamunsa har toilet ɗinsa taje ya leƙa bata ga kowa ba.
Mamaki ne ya kamata ina yaje,da sauri ta juyo ta fito. Har zata shiga ɗakinta, sai
kuma ta nufi gurin engine ɗin wankinta. Daga inda take tsaye ta hangosa yana waya,
daga gani ba wayar aiziki bace yake, dan yadda yake jinjiga jikinsa yake safa da
marya na ya nuna haka. Yana gama wayar ya juyo yana faɗin.

“Namra bata zame min matsala ba ke zaki zame min, babu wanda ya isa ya datsa min
rayuwar jindaɗi wallahi”
Karaf idonsa cikin na Yasmin, dake tsaye gafen ƙofa.

THE GAME IS ABOUT TO START...😿


_____________________________________

I feel much better Alhamdulillah. Na gode sosai da addu'ah da kulawa, Allah ya bar
zumunci. Jazakallahu khairan all 😘
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *74*

Ko parking ɗin kirkir bata yi ba a gidansu Teema ta fita Motarta, zuciyarta na


bugun bugawa, taron mutanen da tara a gidan ya ƙara tabbatar mata da maganar Asmee
da kuma Momi.

Teema na hangota ta tashi daga cikin mutanen da take ta nufi wani ɗakin wanda babu
kowa a cikinsa.
Kai tsaye Rashida ta bita daman ta ga shigowarta, wasu daga cikin ƙawayen Teema har
sun fara magana, dan wasun su sun san mijin Rashida ne zata aura, wasu kuma a yanzu
suke samun labari, ganin yadda ta shigo cikin gidan a birkice.
Da wani irin ƙarfi Rashida ta banki ƙofar ɗakin da Teema take ta shiga hasale.

“Marar mutumci wacce bata gaji arziki ba, ni zaki yiwa ha'inci? Ki zagaya ta bayan
idona ki ci dunduniyata”

Hannayenta biyu Teema ta kama ta riƙe tana hawaye.

“Dan Allah ki saurare ni, karki yanke min hukumci ba tare da kin saurare izuri na
ba...”

Rashida ta fisge hannunsa tana mata wani kallo na uku saura kwata, kamin ta katsa
mata tsawa kamar wata ƴarta.

“Babu wani daɗin baki da zaka min, macuciya wai tsabar rashin kunya ni zaki ciwa
amana..”

“Ban ci amanarki ba Rashida ko kowa ya zarge ni ke be kamata ki mun haka ba, ni


kaina ban san da wannan haɗin ba, dan be taɓa zuwa fira gurina ba sai da zai kawo
min iv, su Hajiya ne suka haɗa komai”

Ta ƙarasa da kuka tana wani ƙara narkewa kamar gaske. Rashida ta watsa mata wani
kallo.

“Ke kar nake kallon ki, kamar naira a hannun yaro, yadda kika yi boka haka na yi
karki nemi raina min hankali, wallahi mafitarki ɗaya ki fasa auren nan ko kuma na
ci uwarki”

Teema ta yi wani Shu'umin murmushi tana kawardar hawayen ƙarya dake fuskarta.

“Idan kuma ba ki ci uwata ba, ni sai na ci ubanki, da aka halitto Hilal an ce miki
ke kaɗai zaki aure shi ne? Ke in ban da haukarki ma miye na kishi bayan ya sake ki
da ya kama ki da wani ƙato ko kin ɗauka ba'asan abunda ya fitar da ke gidan Hilal
ba? Kina ganin kamar ba san komai a rayuwarki ba ko? To malamin dana kai ki gunsa,
shi ya faɗa min komai a kan ki”

Jikin Rashida yayi sanyi har tana sassauta murƴarta duk da tana cikin zafin rai ne.

“Yayi dai-dai kuma ina fatar ya duba miki ya faɗa miki igiyar aure ba zata taɓa
shiga tsakanin ki da Mijina ba, dan Wallahi sai na rusa wannan auren ko ta yaya,
dan babu yadda za'ayi yar iska irin ki ta tarbiyantar min da yara, sai na faɗawa
Hilal irin matar da zai aura”

“Yar iska kamar uwarsu ko? Ai abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne, kuma idan baki rusa
auren nan ba, baki haihu ga uwarki da ubanki ba, ai Hilal ba mijin ki bane mijin
Kalsoom ne da Angon Teema, ƴar baƙin asiri kinje kin yi ma kiahiya ya dawo kan ki
kin kashe ɗan ki da hannunki, Ni ko nafi ƙarfin ki gaba ɗaya ke da danginki, kuma
wallahi duk kika kuskura sake saka baki a maganar auren nan sai na faɗawa duniya
dalilin mutuwar auren ki, da kuma dalilin mutiwar ɗan ki, ga kuma cutar da take
tare da ke, dole har ƴaran ki su gujeki, ko kin ɗauka ba a san dalilin korarki da
ubanki yayi ba?”

Gaba ɗaya jikin Rashida ya gama sanyi, zafafan kalaman da Teema tayi masa sun ƙatse
mata duk wani hanzari da take da shi, har ta samu kanta da nauyin baki kasa furta
mata komai, abun ka da mai sauri karaya nan da nan sai ta fara hawaye.

“Kin fi kowa sanin yadda na ke son mijina Teema, amman kika min zagon ƙasa har kika
ja hankalinsa akan ki, waya sani ko asiri kika masa?”

Teema ta yi ƴar dariya.

“Wallahi ban masa magani ba, uwarsa cw da haɗa mu, kuma yaga yana so na, nima ina
sonsa shikenan fa, amman ki kwantar da hankalinki zan ƙwatar miki ƴancin ki, kuma
zan miki hanyar da zaki dawo gurin mijinki”

“Allah ya isa tsakanina da ke, kin ci amana ta kin min zagon ƙasa Teema wallahi ba
zan taɓa yafe miki ba”

Tana kaiwa nan ta juya ta fice fuskarta da hawaye.


Wani banzan tsaki Teema taja.

“Aikin banza ai daman Allah ishenshe ne, kinji na roƙe ki ki yafe min ne, ni
wallahi ko ubanki yayi min aurensa zan balle wani mijin ki ex-husband mtssssssss”

Rashida ya fito ɗakin idon kowa yana kanta, wasu na Teema rashin gaskiya wasu kuma
suna ganin bata yi laifi ba, daman yanzu ko mijin ƙawarki ne aure shi za'ayi balle
ita da har ta fita gidan miji. Bama kamar hawayen da suka gani a fuskarta. Ita kam
ba ta nasu take ba, haka ta fito abunda yake ranta ya isheta, damuwarta tayi mata
yawa.

Har ta shiga motarta ta fara driving bata da wani kuzari, hawayen da take kuma sun
ƙi su tsaya mata. Wayarta da ke front seat ta yi ƙara alamar kira, kallo ɗaya ta yi
ma wayar ta ɗauke kanta tana cigaba da rera kukan da bata san ranar tsayawar
hawayenta ba, Alh Bashir ne, tasan shi ma ba zai wuce ya labarta mata Hilal zai
auri ƙawarta ba, ita mamakinta ma ko Hilal ya manta Teema ƙawarta ce? Tsayawa tayi
tunanin duk da tasan bata da ƙawaye barka tai hakan amman ba zai rasa sanin Teema
ba, wata ƙila yayi mata haka ne dan ya rama abunda ta yi masa. Haka zuciyarta take
nuna mata, cikin sauri ta ɗauki wayar ta faka gefen ti-ti, tana tunanin abunda zata
faɗawa Hilal, da kiransa zata yi, sai kuma wata zuciyar ta bafa shawarar aika mata
da saƙo. Sannan ta jefar da wayar ta cigaba da tuƙinta tana kuka har ta iso gida.
Ga wayar sai ringing take, friends har da waƴanda suka daɗe basu kira ta ba, yau
kiranta suke dan su ji ƙwan. Bata samu gurin faka motarta ba, saboda Motar Ummu
Faisak da ke waje ta tare nata hanyar gareji, daman can gidan ba wani yarwantaccen
gida ne ba, gida ne na zaman mutun ɗaya.

Ba ta damu da share hawayen fuskarta ba ta shiga falon a haka. Ganin Momi da Ummu
Faisak yasa ta ƙara narkewa ta fashe da kuka har da faɗuwa saman kujera. Nan take
Ummu Faisak tasa kuka ganin yar'uwarta cikin damuwa. Momi kan tsawa ta katsa musu
daga ita har Ummu Faisak ɗin.

“Miye abun kuka ga hukuncin Ubangiji? Ba ke kika jawa kan ki ba? Ai kin yi arziki
da sai da kika fita gidan miji ita zata shiga, kuma ba ƴar'uwarki ce ta ci amanar
ki ba! Ai ke kika fara yi ma kan ki zagon ƙasa da kan ki, kika taka mutumcin
aurenki kika je kika bada kan ki ga wanda ba muharramin ki ba, ke wannan ma be
isheki ishara ba? Cutar da take jikin ki bata isa ta nuna miki Allah ɗaya ne ba? Ai
cin amanar miji Rashida ba ƙaramin haƙƙi ba ne, mijina yana can yana fafutar neman
abunda zai kawo miki ke da ƴaƴansa, amman ke kina can kina cin amanarsa? Aiki hauka
ne? Nasan 95% mahaifinki ne ya ja miki shi da ya tsaya kai da fata akan sai kin yi
aiki, amman be ce kije can ki yi lalata ba, ai ba ke kaɗai ce mace ma'aikaciya ba,
akwai da yawa waɗanda suke kare mutuncin mazan su da kuma na ƴaƴansu da na su da na
iyayensu, ba ga ƴar'uwarki nan ba? Ummu Faisak aiki take, ita bata lalace ba saboda
ta san mutuncin kanta, ki ba abun baƙin cikin ki ba ne ace wani namiji wanda ba
mijin ki ba ya san surar jikin ki? Kin ɗauki rayuwar turawa kin sawa kan ki, baki
da lokacin tarbiyantar da ƴaƴanki, tufafi ko sai waƴanda kika ga dama kike sakawa,
nan aka auro miki Kalsoom na zo ina yaba shigar da take irin tarbiyar da ta samu a
gidansu, kika ce min na fi son ta, da ke, kika ce ina miki abu kamar ba ni na
haife ki ba, a lokacin ruɗin duniya na ke guje miki amman idon ki ya rufe.

Dan baki da hankali zaki wanke ƙafafu kije gidansu Teema to ki ce mata me? Ki zauna
ki yi wa kan ki karantun ta natsu, ki nemi yafiyar ubangijinki, kuma ki nemi
yafiyar mijinki tun haƙƙinsa be cigaba da binki ba, dan duk abunda kika aikata da
aurensa haƙƙinsa yana saman kan ki, kin yi sa'ah da Allah ya rufa miki asiri tun
wuri, dan duk mai cin amanar mijinta sai taga ishara wallahi ko ba daɗe ko ba jima,
kiyi taka tsantsan da duniya Rashida dan ta fara barinki tun kamin ke ki barta,
karki yarda ki ci amanar wani, ƙara ke a ci amanar ki, balle kuma miji. Tashi muje”

Momi ta ƙarasa tare da kallon Ummu dake gefenta, kana ta miƙe tsaye idonta cike da
ƙwallah, ranta kuma a ɓace ta fice, Ummu Faisak ta rufa mata baya tana cigaba da
hawaye.

Hannu Rashida ta ɗora saman kai, tana kallon ɗakin kamar sabuwar mahaukaciya.

“Innalillahi Allah kasa mafarki na ke yi, Allah ka farkar da ni daga wannan


mummunan bachi, Allah ka farkar da ni Allah, Allah ka tashe ni...”

Ta rushe da wani irin kuka tana dafe da kanta da take jin yana jujjuya mata.

HILAL POV.

_Hilal ka san wacece Teema kuwa, wallahi wallahi bokaye ta ke bi, kuma ta fi karfin
iyayenta, karka aure ta Hilal dan Allah, ban yardar ta tarbiyantar min da ƴaƴaba,
ka auri ko cece amman ban da Teema_

Yana gama karanta saƙon ya saki tsaki, ya aje wayar saman teburinsa, ya miƙe tsaye
ya fice daga office ɗin.
Duk inda ya wuce ango ake ce masa daman wasu tun jiya ya basu iv wasu kuma sun
samu labari, yana isa gurin karɓar results ya buɗe ciki ya shiga. Daya bayan ɗaya
ya gaisa da su, sai tsokanarsa suke, wai ango ka sha mai.

“A'a ban sha fa da saura”

Sai duk suka sa dariya har shi Hilal ɗin da yayi magana, ɗaya daga cikin likitocin
dake tsaye ward ɗin ya ce

“Doc baka da kunya”

“To kunyar me zan ji kowa ai yasan komai, kai bani results ɗin Amarya ta na gani”
“Amarya ko uwargida?”

“Amarya dai, to duka yaushe na yi auren ?ba ƙaddarori bane dai idan Allah ya kawo
babu yadda za'ayi”

“Aiko yanzu na ke shirin kai naka result ɗin, dan kana tafiya Doc Ahmad ya wanka
hoton ya ce ina kake nace ya kawo wannan albishir ɗin ni zan yi ma madam shi da
kaina”

“Ai ana ɗaukarta Hoton ta sha mun kai na maidata gida, ita dai ciwo take ji,
shiyasa kaga na masu na ƙarɓi results ɗin so that na san abunda yake damunta kar mu
yi cuta daban magani daban, tun jiya kuka take min wai tana jin abu a mararta kamar
dutse sai amai take”

Kamin ya miƙa masa results ɗin sai da ya miƙa masa hannu.

“Congratulations ba dutse ba ne alheri ne, sai dai idan ka duba zaka gani”

Ya karɓa zuciyarsa fari ƙal.

“Wow ka ce na yi aiki Alhaji...”

Sai duk suka kwashe da dariya. Shi kam be ma kula su ba hankalinsa ya tafi gurin
Hoton.

“Six months i'm surprise, kwata kwata ban kawo wa rayuwata ciki ba ne, dan tace
ƙasan mararta kuma ita pain her, ko tsayin kirki bata iya yi, jiya gaba ɗaya a
rikice muka kwana”

“Yeah yayi mata kwance ne, baka ganin yadda yake, sai kun kula da shi sosai
gaskiya, Allah ya raba lafiya”

“Amin”

Ya fice da sauri, ɗaukar wayarsa ce ta zame masa dole, ba dan haka ba , ko office
ɗin ba zai koma ba, a gaggauce ya ɗauki wayar ya fice. @360 ya bar asibitin tsabar
zumuɗi ji yake kamar ma ya rumtse ido ya gansa gida. Cikin ƙanƙanen lokaci ya isa,
daman be sa ran zai tarar da ita falo ba, dan haka ya wuce bedroom ɗinta kai tsaye,
kwance ya same ta ƙasa ta duƙunƙune da bargo sai rawar sanyi take. Wani irin
tausayinta ne ya kama shi, sai ya aje keys da takardar dake hannunsa saman mirror,
ya kwanta bayanta ya yaye bargon dake jikinta ya ɗora fuskarta saman nata, jikinta
yayi zafi aosai amman hakan be hana shi rumgumarta ba.

Ta buɗe ido da ker ta ɗan taɗo kai ta kalleshi.

“Gadon baya min daɗi”

Ta faɗa da muryar ta nan ta marar lafiya. Lumshe ido yayi yana murmushi.

“i'm sorry dear it's all my fault”

“Dan Allah ka min allura ko zan samu sauƙi”

“Ke da samun sauƙi sai nan da five months”

Ta yi dauriyar sake kallonsa cikin idonta na marar lafiya.

“Whats do you mean?”


“Sweetheart ƴou're pregnant”

Ƙarfin halin tashi ta yi, sai ya riƙa ta tashi zaune da kyau, ya kwantar da ita
jikinsa.

“Da gaske?”

“Yes Dear six months”

Ta yi saurin kai hannu ta taɓa cikin, yo hwr surprise cikinta be yi girma ba,
impact babu wani alama na ciki na jikinta idan ba wannan ciwon da ta yi ba.

“Amman ko dai one months...?”

“No wata shida dai, kin ga hoton da aka miki ɗazu can”

“Amman na yi menstruation last months fa”

“Nima abunda ya bani mamaki kenan, but kin tuna wacan lokacin da kika samu ciki ya
ɓata? Ina tunanin shi ne ya kwanta miki, sai yanzu ya tashi, daman ana samun hakan
nan wani lokacin, that's why we need to take good care of it, saboda mu samu ya
dawo dai-dai”

Ɗagowa ta yi ta kalleshi, hawaye suka zubo mata.

“Congratulations”

Sai ya aika mata da kiss a goshi.

“Thank you Dear”

Ta ɗora kansa saman wuyanta, hannayensa zube saman cikinta.

ASIM POV.

A can ya kwana gurin Alhajinsa, da safe yasa aka kawo musu abun karyawa, sannan
suka yi wanka, yadda Alhaji Nasir ya shirya cikin manyan tufafi ba zaka kalleshi
kace yana aikata wani mugun abu ba.

Asim ma ya fito cikin ƙananan kayana kamar wani mutumen arziki, hankalinsa kwance
zuciyarsa cike da natsuwar abunda ya aikata. Ba laifi yanzu be ji zafin da yaji da
farko ba, sai dai har yanzu be fara jin daɗin da Alhaji Nasir da Hajiya Sadiya suke
labarta masa zai ji ba, wata sai ya ƙara gwarewa akan harkar.

Alhaji Nasir ya saka turare ya kalli Asim ya ce.

“Har yanzu baka ƙarasa ƙwarewa ba a kan harkar nan, ya kama a sama maka kasuwan
turawa nan ka kalla,dan ina son haɗa ka da manyan mutane ta yadda zaka ƙara
gwarewa, ka ci moriyar ƙurciyarka”

Wani daɗi ne ya lumluɓe Asim, dan yasan kuɗi zai samu, daman burinsa kenan ya yi
kuɗi.

“Zan ƙoƙarta Inshallah, ina godiya sosai”

“Idan kana da buƙatae wani abu ka riƙa min magana, dan yanzu nauyinka ya dawo kai
na, shiyasa na tura maka wannan kuɗin dan ka samu na ƴi ma kan ka hidima, amman fa
a riƙe sirri, kuma ni ina da kishi gaskiya ɓana son ka yi mu'amala da wani idan har
ba ni na haɗa ku ba”

“Zaka same kamar yadda ka tsammace ni inshallah”

Daga haka Alhaji Nasir ya miƙe tsaye.

“Ni zanje Abuja ajima kaɗan, yanzu zan leƙa gida ne”

“Ba matsala Alhaji Allah ya kiyaye hanya”

Sai da ya fita da kusan mintuna latatin sannan Asim ya fito daga gidan ya nufo
gida. Ko da ya shiga Mama har ta soya nasa dankali da ƙwai ymta haɗa masa tea mai
kyau dan tasan shine favorite ɗinsa, shi kam ko kallon su be yi ba, dan yanzu ya
wuce gurin kwaɗayin irin waɗannan, beside yama riga da ya ƙarya gurin Alhaji Nasir.

“Nayi tunanin zaka dawo jiya muka ta jira baka dawo ba, na kira wayarka kashe”

“Eh masallaci na kwana, bayan gama sallah isha'i daman na kan yi haka ko a gida
yanzu saboda ina nafila dare”

Yayi mata ƙaryar ne saboda bashi da hujjar cewa ya kwana a wani guri bayan kuma ga
gidansu. Ita kam daɗi ya mamaye ta.

“Ai haka na da kyau, ƙara a riƙa godiyar Ubangiji, sai kaga yana ƙara maka, kuma ya
kamata ka samu lokaci muje gurin Malam na Allah ya baka ƙaiƙayi koma kan masheƙiya
saboda maƙiya”

Miƙewa yayi tsaye.

“Kai Mama ni duk bana da lokacin wannan, yanzu dai ga kuɗi nan ki rabawa maƙota,
idan na samu gidan sai a faɗa min”

“Toh ya yi Allah ya tsare min kai, amman har zaka koma yanzu? Jiya jiya fa ka zo
garin nan ”

“Wallahi aikwai aiki a can, kuma ki ciri kuɗi ki buɗe account a bank zan turo miki
kuɗi ki bawa su Baba sani, kuma ki faɗa musu anytime zasu iya jin kirana akan
maganar auren nan”

Yadda yake mata magana kamar yana bada umarni ne. Wani jin kansa yake yanzu kamar
minister. Ta so ya tsaya su yi fira amman bata samu dama ba dan ya nuna yafi son
tafiya kamar wanda ake tsakala. Har bakin mota ta rako shi tana faɗar masa

“Yanzu sai iyayen Namra sun samu labari ka yi kuɗi, amman basu san ka sake ta ba,
tun da bata zo gida ba”

“Dole ne ai su samu labari, ni nafi son haka ma”

Ya buɗe motarsa ya shiga. Tana ɗaga masa hannu har ya kama hanya.

Be tashi da wuri ba, dan ko da ya baro sokoto shabiyu har da kusan rabi. Ko da iya
isa Katsina yamma ta yi sosai, sai dai Nably ta yi masa kira ya fi biyar dan jin
lafiyarsa, Mardiya ma ta kira ta faɗa masa tana son ganinsa.
Yana isa katsina ya kira wayar Hajiya ya fara gaisheta, still ta faɗa masa tana
birnin keebi, dan ya so ya fara zuwa ya gaishe da uwar ɗakin tasa ko zai goge
laifinsa. Gidansu ya sauka yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin sannan ya wucce
gurin ƙanen dad ɗinsa wanda ya manta rabonsa da yaje can sun suna aikin ƙira kamin
su haɗu da Hajiya Sadiya.
Su kansu sun yi mamakin ganinsa, daman suna jin labarin yayi kuɗi sama-sama a gurin
jama'ah, bama abunda yafi basu mamaki kamar yadda kuɗin suka taso masa lokaci ɗaya.
Sun yaba da motarsa da kuma shigarsa har suka masa fatan Allah ya tsare, a nan ya
ɗauki kuɗi mai yawa ya bashi, abkan da suka yi aiki tare ya raba musu wani abu. Sai
da Ƙanen Baban nasa ya rakosa zuwa gurin motar yake labarta masa dalilin zuwan
nasa.

“Gida nake so a sama min kamar na miliyan biyar, mai kyau sosai”

Shin kam riƙe baki yayi jin Asim ya ambaci miliyan har biyar, yana mamakin ace yana
da wannan kuɗi haka da yawa, a take zuciyarsa ta raya masa ba kuɗin halal ba ne,
sai dai babu damar faɗa masa gaskiya dan yana tsoro, daman idan kana da abun hannu
ana tsoron faɗa maka gaskiya balle Asim da yasan zai iya yin cikinsa da masifa.
Da zimnar idan an samu za a kira shi a sanar da shi suka aje, sannan ya yi masa
sallama ya kama hanyar gidansu Mardiya.

YASMEEN POV.

Tana shiga ta aje kwalin, ta koma kan Adnan daya sauka ƙasa yana zare zaren shoes
ɗinsa, da hannu ɗaya but still hannunsa ɗaya yana gurin sai susa yake. Yana ganin
Yasmee yayi saurin dainawa, yana wara idonsa na marasa gaskiya.

Hannu biyu tasa ta ɗauke shi sai ta zauna ta ɗora saman jikinta tana murmushi.

“Aya tell me mi Dadee yake ma ka?”

Rufe ido ya yi yana dariya, ita kuma ta maida kunnenta gurin bakinsa.

“Faɗa min mana ko mu ɓata”

“Ba zaki faɗa ba?”

“Ba zan faɗa ba”

“Wannan abun ƴake sa min a nan”

Ya nuna mata gurin fitsarinsa, sai ta sauke shi ƙasa.

“Nuna min mi yake sa maka”

“Wannan abu yake samin a baya, sai yacw na kwanta, kuma da zafi sosai yace idan na
faɗa sai ya yanka ni da wuƙa ƙamar yadda ake yiwa rago”

Ya cire wandonsa ya nuna mata. Wani irin faɗuwa gabanta ya yi, a take ta samu kanta
cikin wani irin tashin hankali, wanda bata taɓa sa masa rana ba, a take zuba ta
fara karyo mata, numfashinta yayi mata mugun nauyi, sai tayi saurin rumgume Adnan
dan kar ya ga hawayen dake ƙoƙarin zubo mata.

“Your Dadee did a great thing”

Ta soma shafa bayansa cike da tausayinsa kanta da kuma nata, sai dai ko kaɗan bata
son ya ga hawayenta. Sai ta sauke shi ta mike tsaye.

“Bari na zuba maka abinci ka ji”

Ta yi saurin juya ta bar ɗakin. Kitchen ta shiga sai ta samu mai aikinta tana yanka
salat da tumatur.
“Jeka kawai zan ƙarasa”

“Toh”

Aje ragowar da ke hannunta ta fice. Hannu biyu Yasmin tasa ta riƙe kitchen cabinets
sai ta fashe da wani kuka marar sauti. Ƙafafunta kasa ɗaukarta suka yi, sai gata
ƙasa jikinta har karkarwa yake.

“Innalillahi wa'inna ilaihi”

Shine abunda take ta maimaitawa, gudun kar kukan ya ci ƙarfinta. Kulolin ta buɗe
ta ɗauki plate ta zuba masa white rice and pepper soup, ya saka nasa spoon, sannan
ta ɗauki ruwa ta wanke fuskarta ta fito tare da abincin.

Ɗakinta ta nufa riƙe da abincin, hawaye sun ƙi tsaya mata. Aikin baban giwa ta samu
yana yi, dan har ya buɗe kwalin data aje, azatonsa wani abun ci ne a ciki ko
chocolate ganin. Ita bata ma bi ta kan kwalin da ya fasa ba, shi kawai take kallo
har ta aje abinci, tausayinsa duk ya kama ta, sai ta riƙo hannunsa ta karɓi
takardar dake hannunsa ta aje gefe. Taja shi jikinta, ta rumgume.

“Momee babu komai a ciki”

Cikin kuka ta amsa shi.

“Ba na ka ba ne, na Dadee ka ne”

Kuka take sosai tana ta ƙoƙarin ƙaryata abunda zuciyarta take son yarda da dashi,
can kuma ta sake shi ta janyo abinci ta aje masa a gabansa. Ta zauna ta tsare shi
da ido hawaye na cigaba da mata zuba.
Kamar kuma an tsikare ta share hawayen idonta, ta miƙe tsaye ta ɗauki wasiƙar da
jimmar maidawa cikin kwalin, babu abunda ya bata mamaki kamar ganin da tayi babu
komai a kwalin sai wasiƙa, babban kwali kamar wannan a'ce babu komai a ciki sai
wasiƙa, to me wasiƙar ta ƙumsa ne haka?
Zaunawa ta yi a kusa da kwalin ta warware wasiƙar, gabanta sai faɗuwa yake ta soma
karantawa.

_Zuwa ga Azzalumin mutun, macuci mayaudari, nasan kana nan raye kamar ƴadda nima na
ke raye, ko kuma na ce ka so ka halaka ni Allah be baka dama ba, ka yaudare ni
Uzair kace Namra zamu ma Asiri ashe ka haɗa kai da ita ne ni kuka yi ma wannan
asirin na bar gida, ban taɓa gane haka ba, sai a yanzu da nake da buƙatar da dawo
na kasa, Wallahi Wallahi kaje ka karya wannan asirin ko kuma na sa a kashe ka, dan
kasan na san ka, kuma na san inda kake, ni ko baka san inda na ke ba a yanzu, kuma
ina tabbacin baka san ko wacece ni ba_

Sai number wayarta daga ƙarshe. Abunda ya tsayawa Yasmin a rai, wacece wannan
yarinyar? Sannan mi suka ƙulla da Namra? Mi mijinta ya aikata ne?
Ta miƙe tsaye cike da rashin kuzari, abubuwa biyu sun tsaya mata a lokaci ɗaya kuma
akan mutun ɗaya. Wani tunanin ne ya zo mata, da sauri ta ɗauke kwalin ta fita da
shi ta saka cikin shara, sai ta dawo ɗakin ta ɗauki wasiƙar ta mayar da ita a yadda
take, sai ta je cikin littatafanta na aiki ta samu wata silver paper, ta yi
wrapping ta naɗe wasiƙar ciki da kyau ta saka salatif, ta kai masa ɗakinsa ta aje
masa.
Tana shigowa ɗakinta jiri ya kwasheta, ta faɗi dafe da kai.

ANTY AMARYA POV.

Cikin ƙarfin hali ta unƙura ta nufi part ɗin Abbah, dan yau bata jin daɗin jikinta
sosai, wata ƙila fever ɗin ne zai sake dawo mata. Yadda ta tararda Hajiya Barau da
Abbah a falon ya ɗan tashi hankalinta, dan a zatonta ya aika kiranta ne dan su
tattauna maganar auren da ake na su Hindatu da Maryam. Zaunawa tayi tana kallon
yanayin Hajiya Barau da ta riƙe baki tana kallon Abbah, sam bata lura da takardar
dake hannun Abbah ba sai da ya mika mata takardar.

“Wai wasiƙa ce daga Faɗar Mai Martaba sarkin Katsina, wai ana bukatar gani na gobe”

“Subhanallahi miya faru?”

Anty Amarya ta tambaya zuciyarta na rawa fat fat fat.

“Wallahi ban sani ba, ni abun ya ban mamaki mi na aikata da Sarki Katsina zai aiko
kirana? Ina ma na san shi?”

Hajiya Barau ta mere baki, har da wani ƙis take.

“Allah yasa ba Namra ta yi maka janye janye ba”

Kallo ɗaya Anty Amarya ta yi mata ta ɗauke kai, maganar na sukarka, ta miƙe tsaye
ta bar musu falo.

“Zan sa ana ma min jirgin da zai je Katsina gobe da wuri zan sauka dan jin ko
minene”

“To Allah yasa mu ji alheri, Amman da ka kira Abdulraman (Baban ɗansa) kun je tare,
kar ka je kai kaɗai”

Ya ɗora ƙafarsa ɗaya saman ɗaya, Yana sosa gemunsa da hannunsa.

“A'a da Larai zan je (Anty Amarya)”

Uffan Hajiya Barau bata ce ba, dan maganar bata mata daɗi ba, sai kawai ta miƙe
tsaye ta fice daga falon.

___________________________________________

There are no words to explain how sorry I am. Nasan duk abunda zan faɗa muku ba
zaku yarda ba, wallahi i'm kind of busy those days, ku yi Hakuri dan Allah ku
gafarta min Love you all Fisabilliah 🌹

I dedicate this chapter to Hajiya Ramatu, Mrs tijjani, My Asmee, Ahmad Ismael. I
really did not know how will to write in words! But your gesture is such 😘 Thank
you very much Allah ya ƙara arziki, ya bar zumunci.♥️
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *76*

“Me kike a nan?”

Ya tambaya yana haɗe fuska. Bayanta ta nuna ba tare data juya ba, sai dai bata san
abunda zata faɗa masa ba. Ya nunata da phone ɗinsa.

“ I know kin karanta wasiƙar nan Yasmin”

Still wata kalma bata fito daga bakinta, wani kallo take masa kamar mai nazari.
Raɓawa yayi gefenta zai wuce sai kuma tsaya yana kallonta ido cikin ido.

“Ba sai mun yi playing wannan game ɗin, nasan ke lauyer ce”
Da kallon mamaki ta bishi, ta kasa gasgata abunda kunnuwanta da idanunta suka ji
mata. Me yake nufi da Namra bata zame masa matsala ba ita ba zata zame masa ba?
Wacece ita? Da waya yake waya?

Da sauri ta rufa masa, sai ta same shi sitting room ya haɗa kansa da guiwa ya dafe.
Tsaye tayi masa aka.

“Me waɗannan abubuwan suke nufi Uzair? Wacece wannan ? Mi kuka aikata kai da Namra?
Da wa kake waya?”

Ɗagowa yayi ya kalleta, idonsa sun kaɗe alamar damuwa da ɓacin rai na tare da shi
lokaci ɗaya.

“Miyasa kike son saka kanki ga abunda idan kika ji zai iya zame miki matsala? Miya
kike son saka kanki ga abunda be kamata ya dame ki ba?”

Ya tambaya muryar ƙasa ƙasa kar ba komai. Zama tayi kusa da shi tana masa kallon
mamaki.

“Ni matarka ce Uzair, damuwarka damuwata ce, Namra kuma ƴar'uwata ce, be kamata ka
ɓoye min komai ba, please tell me maybe i can help”

ya shafa fuskarsa yana cikama bakinsa iska.

“Is about some business da zamu yi da yayanta, shine take min sheri, shine nace
Namra bata zame min matsala ba ita zata zame min yarinyar da ta yi min ƙazafin
Luwaɗi”

Wani ɗan murmushi tayi mai cike da rainin hankali, shi kansa ya fuskanci hakan.

“To be frank i read the message, Uzair you can't hide the truth jus...”

Yayi saurin riƙa hannayenta jikinsa a mace.

“Yasmin trust me please, kin san ina son ki”

“Ba maganar so ko ƙi muke a nan ba”

“Just promise me ba zaki bar ni ba”

Hawaye sun zubo mata.

“Idan har zargina ya tabbata a kan ka dole ne zan rabu da kai, ba zan iya zama da
mutuemn daya zaɓi saɓon Allah sama da tsoronsa ba, mutumen daya zaɓi zubar da
mutuncin iyalansa, zan iya yafe son da nake maka Uzair”

Ya girgiza mata yana ƙara damƙe hannunta cikin nasa.

“No Wallahi sherin sheɗan ne Yasmin, ba da son raina na aikata ba, kuma duk zugar
su Najeeb ce, kuma nayi ne dan na kare kai na daga cin mutuncin da Namra ta yi min”

Maganarsa ta sha banban da tunaninta, ita gun data dosa daban shi kuma maganar da
yake mata daban.

“Me ka aikata Uzair?”

Ya saki hannayenta.
“Ina ruwanki da abunda na aikata ne Yasmin?”

Ya faɗa a tsawace, sai kuma ya dafe kansa ya miƙe tsaye ya nufi windo.

“Ki tsaya a matsayin ki na matata Yasmin, zai fi miki”

Ta miƙe.tsaye itama cikin ɓacin rai.

“Yes zai fi min idan na rabu da Azzalumin mutun irinka, tirr da halin ka Uzair, ina
kotu ina cases ashe akwai babban Case a gidana, nayi nadamar Auren ka a yau nayi
nadamar daka kasance a cikin zuri'ar mu, nayi nadamar da ka zama uban ƴaƴana, ashe
gaskiya Namra take faɗa, amman ka murje ido ka ƙaryatata...”

Ya juyo a fusace yana nuna saman kamta da ɗan tsayansa.

“Ke je ki faɗawa duniya nine na sace Namra, ni na haɗa kai da amiyarta aka mata
asiri ya koma kan ƙawarta, amman karki manta ɗan'uwanki kika tonawa Asiri, kuma
mahaifinta zai karɓe komai nasa daga hannuna, but i'm still your husband Yasmin the
love of your life kuma uban ƴaƴanki biyu, asirina asirinki ne, kuma tona min asiri
kamar tonawa kanki ne da ƴaƴanki”

“Ka buɗe shafin da ban san da shi ba Uzair, ashe kai ka sace ta? Sannan ka haɗa kai
da amiyarta ka mata asiri? Wane irin zuciyane da kai Uzair? Wata ƙila ma ita ka
aikata mata irin abunda ka aikatawa ɗan ka, you raped your very own son Uzair Allah
yayi tirr da halinka”

Dariya ya soma yi ya doso inda take.

“Allah ya faɗa acikin matan ku akwai maƙiyanku, sai yanzu na gane kan ayar nan,
amman ke babbar maƙiyiya tace Yasmin, ki rasa abunda zaki zarge ni da shi sai
wannan? Kina da wata hujja ne? Ke daina ganin ke lawyer ce zan iya maka ki kotu,
akan wannan mummunar kalma da kika jefe ni da ita, ai ko da gaske na aikata masa be
kamata ki fito ki jefe ni da wannan maganar ba, idan ma na masa ina ruwanki ɗan ki
ne?”

“Shiyasa bana burge ka ko? Baka da time ɗina, saboda ba mata bane a gabanka maza
ne, mu kwana gado ɗaya mu tashi amman baka yarda ka bani haƙƙi na ba, da na maka
magana, ka ce baka da lafiya, ko na cika desire, ashe kasan abunda kake aikatawa,
kasan irin hukuncin da Allah ya tanadarwa masu irin wannan aikin kuwa? Cewa aka ƴi
idan an kama su a jefosu daga saman bene su faɗo ƙasa, ko kuma a samu dutse a buga
musu a kai, miye bana da shi ne Uzair? Wace hasara ce ta cin maka na neman maza
ƴan'uwanka? Uzair me kake ji idan ka neme su?”

Hannayenta ya kama, ya faɗi ƙasan gwuiwoyinsa.

“Ki rufa min asiri Yasmin, ki taimaki rayuwata, kar kowa taji maganar nan, na miki
alƙawarin ba zan ƙara ba, kuma zam je nasa a kare asirin dake kan Amira i promise,
Yasmin ki dubi girman Allah ki yafe min, sherin zuciya ne, da zama da miyagun
abokai”

Kuka da take ne ya ƙaru.

“Ka cutar da yarinyar nan Uzair, kasa mahaifinta da duniya suka zargi ta gudu taje
gurin saurayinta ne, sanadinka kowa a familyn mu ya tsane ta, duk halin da ta shiga
kai ne Uzair”

“Ki yi ta tunanin wasu har ki manta da ni, ki rufa asirin wasu ni ki tona nawa,
idonki yayi ta rufewa akaina har maƙota suji abunda na aikata”
“Ba maƙota kaɗai zasu ji ba, duniya ce zata ji, sai duniya tasan wanene kai, sai
kowa yasan abunda ka aikata”

Ya miƙe tsaye

“Wallahi duk kika bari wannan maganar ta fita, sai kin yi nadamar zuwanki duniya,
sai kin gwammace kiɗa da karatu, kuma komai na zama ni mijin Yasmin ne, ai komai
yana da buƙatar uzuri da bincike, kije duk abunda zaki aikata ki aikata ɗan shege
ka fasa, indai kotu kike taƙama da ita sai na nuna miki baki san komai ba akan
aikin ki”

“Haka ka ce?”

“Wanda duk yaƙi ji aiba zai ƙi gani ba”

“Baka bani mamaki ba, daman masu aikata irin aikinka ai basa da kunya, kuma basa
tsoron Ubangijinsu balle jama'a tirr da halinka, wallahi sai na ƙwatowa Namra
haƙƙinta, sai ka raina kan ka Uzair”

“Ni mijinki kike faɗawa haka?”

“Kai mijina ne zaka taka min bayan ɗa?”

“Sai ki fito fili ki faɗa mana, kice ɗana zaki min ƙazafi, ba wai ki raɓa da Namra
ba, aikin banza kaiwai... Mtssssswww”

Yaja wani dogon tsaki ya wuce daga falon kamar walƙiya. Ita kamar jiran take ya
fita, ta shiga ɗakinta ta zari mayafi ta, ta goyawa Mai mata reno little Namra, ta
kama hannun Adnan suka fice.

NAMRA POV.

Da hawayw ta shiga cikin gidan, sai dai kasancewar dare ne, kuma babu wutar nefa a
gidan shi ya hana su gane akwai hawaye a fuskar Namra, da wannan tayi nasarar
shigewa ɗaki ta kife saman kafitar tana kukanta a hankalin ta yadda ita kaɗai zata
iya jin sautin kukanta.

Da sallama Anty Amarya ta shiga cikin gidan, sai duk suka haɗa baki gurin amsa
mata, gaisuwa ce ta biyo baya, sannan ta ɗora da tambayar Namra, duk kallon rashin
sani suka mata, ko wanne abunda zuciyarsa ta bashi, wata ce ta tare da Yarima, wata
ƙila taƙi ta saurareshi ne shiyasa ya turo wata.

“Eh tana nan ciki lafiya?”

Lamido ya tambaya. Cikon murya mai kamar ta kuka Anty Amarya ta ce

“Dan Allah ku yin magana da ita...”

Kamar an jefo Namra haka ta fito daga cikin ɗakin, tana ganin Anty Amarya ta rumtse
idonta ta damƙe hannayenta gam, tana maimaita.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Saboda ta kasa yarda da abunda kunnuwanta da idonta suke nuna mata, ji take kamar
mafarki take kuma ba mafarkin ba ne. Ta buɗe ido ta ƙarasa gaɓan Anty Amarya ta
kama hannayenta, ta taɓa ta murja ta sake kallon fuskarta, sai kawai ta rumgume ta
fashe da kuka.
Anty Amarya ma kuka take, ita da Namra aka rasa mai rarrashin wani, su kam su
Neina sai kallon ikon Allah suke. Kuka sosai Anty Amarya da Namra ke yi kamar an
muutuwa, sannan Namra ta zube ƙasan kafafunta ya kama kafafun Anty Amarya.

“Ki yafe min Anty, na tuba dan Allah ki yafe min, ki roƙi Abbah ya yafe min,
haƙƙinku ma ta bina Anty, dan Allah ki roƙa min Abbah ya yafe min”

Ta ƙamƙame ƙafafun Anty amarya, tana wani irin kuka mai yaɓa zuciya. Yanzu kam
Neina da Lamido sun fahimcin wacece Anty amarya. Anty ƙasa magana ta yi saboda
majina data cika mata hanci. Can Namra ta ɗago kai ta kama hannayen Anty Kaamar
wace ta ruɗe.

“Anty da gaske kece?”

Ta kalli Lamido da Uwani.

“Kuna ganin abinda nake gani, ko dai mafarki nake?”

Lamido ya ɗaga mai cike da ɗaurewar kai, Uwani kuma tace

“Muna gani Namra”

Anty Amarya tasa hannu biyu ta riƙo Namra ta tashe ta tsaye.

“Nice Namra, ba mafarki kike ba, Mahaifinki ma yana nan waje, tare muka zo da shi
lokacin komawarki gida yayi”

“Anty waya faɗa muku nan? Na kasa yarda ba mafarki nake ba, kaina nake jin yana
juyawa”

Ta miƙe tsaye ta nufi ƙofae waje. A gurin ta samu Abbah tsaye ya maida hannayensa
baya kansa ƙasa kamar mai nazari.

“Abbah....”

Ta furta tana kallonsa da kyau da kyau. Ɗan murmurshi yayi kaɗan irin murmushin da
be kai zuci ba. Sai kawai Namra ta faɗa jikinsa ta rumgumeshi numfashinta na rawa,
kuka yazo mata a lokaci ɗaya.

Sai da tayi kukanta mai isarta taji ta samu natsuwa sannan ta sauko gurin ƙafafunsa
ta riƙe.

“Dan Allah Abbah ka yafe min, ban kyauta maka ba, kwata-kwata abunda na aikata be
dace ba, Abbah Asim ya sake ni, tsoron abunda zaka min ya hanani komawa gida, dan
Allah ka yafe min Abbah”

Kanta ya shafa fuskarsa ba yabo ɓa fallasa.

“Idan ban yafe miki ba, ba zan zo nan ba Namra, nasan yanzu kin riga da kin gane
kuskurenki, tashi tsaye kar ki tara mana mutane”

Fitar Namra yaba Anty Amarya gaisawa da ƴan gidan, wato su Neina har take faɗa musu
ai tare da Abbah ta suke yana waje.

“Haba kije kice ya shigo mana ya zai tsaya daga waje”

Sannan Anty Amarya ta nufi ƙofa da jimmar faɗa masa sunce ya shigo. Sam sam sam
Lamido be jidaɗin ganin iyayen Namra ba, duk wani farinciki da son da yake ta
shirya da iyayenta sai yaji baya sonsa, musmaman yadda zuciyarsa take raya masa
Yarima ne silar hakan,ko ba komai yasan Namra zata fi son Abdool sama da shi, shi
ko yana da ƙudurora da yawa akanta, dan ya ɗaukarwa kansa alƙawarin sai ya nuna
mata banbancin dake tsakaninsa da Asim na kyauwon hali, duk da suna ɗaya zasu amsa
a fagen talauci,so yake Namra tasan ba duka talaka ne mai irin zuciyar Asim ba.
Wani abu yaji yazo ya tsaya masa a zuciya, tun ba aje ko ina ba, yana jin ya fara
missig Namra, zata nisanta da shi yanzu, kuma ba lallai bane ya sake ganinta.

Sallama Abbah ce ta katse masa hanzari, ya dawo daga duniyar tunanin da yake ya
miƙa idonsa i zuwa inda ƙofar gidan take yana kallon Namra dake riƙe da hannun Anty
Amarya. Saman shimfiɗar da Neina tayi musu suka zauna, ita kuma ta zauna a saman
ɗaƴar tana gaisawa da Abbah.

“Amman na jidaɗin da kuka zo gurin ƴarku, Namra bata da tunani sai naku, kullum
cikin kuka take, nasan babu iyaye na gari da zasu ƙyale ƴarsu, matuƙar ƴar nan ta
sunna aka haife ta, su iyaye dole sai kana kai xuciya nesa, sau da yawa ɗa zai
aikata abu kai ka daurewa zuciyarka ka ƙyale gudun kar ɗan nan ya faɗawa halaka,
kuma idan mutum ya gane kuskurensa babu a abunda ya cancanta da shi sai yafiya da
kuma nuna masa illar abun nan da ya aikata, ƴaƴa da mata kamar kiwo ne, ko wanne za
a tambaya ubngidansa akan irin kiwon da ya bawa iyalansa, yadda mu muke da haƙƙi
akan ƴaƴanmu haka muma ƴaranmu suke da haƙƙi a kan mu. Wallahi kun faranta min
zuciya dana ganku da ƙafafunku kun tako cikin gidan nan ku tafi da ƴarku, a halin
da Namra take da ace bata haɗu da mu ba da zata iya faɗawa ko wane irin hali,
saboda bata san kowa a Kaduna ba, kun ga ko a nan rayuwarta tana cikin haɗari”

“Gangar jikina ne kawai a gida, amman kullum zuciyata tunanin Namra take, ban san
aurenta ya mutu ba, da wallahi ba zata zauna ko ina ba sai a gida, kowa kuwa
mahaifinta zai zaɓi rabuwa da ni ne, kullum a tunani tana can yana azabbatar da
ita, nasan Halin Namra idan abun duniya zai cita ya cinye ba zata faɗawa kowa ba,
itace babba amman ita marar wayo da tunani a cikinsu, da wannan tunanin naƙe bachi
naƙe tashi wannan tunanin ya kan hanani sukuni wani lokacin, shiyasa ƴan'uwanta
suke ganin kamar itace silar ciwon nan nawa, kullum cewa suke, Namra ce ta kwantar
da ni, duk da nasan gaskiya suke faɗa amman a haka zan musa musu, kudun kar suce
nafi sonta sama da su, ni ko kullum tunanin kar na mutu na barta a cikin wannan
halin”

Namra ta kama hannayen Anty Amarya ta riƙe.

“Ba zan sake aikata abu makamancin wannan ba Anty, ni ba zan sake aure ba balle har
na tsallake wani sharaɗi na ku, hawayenki ba zai sake zuba a kan Namra ba”

Uffan Abbah be ce ba, idonsa na kan pure water da Maryam ta aje musu mai tsanyi,
wadda ta siyo shago.
Maganar duk da suke tana cikin kunnensa, sai dai be jin zai iya furta wata kalma
data ɗanganci labarin da suke. Ba laifi sun ɗan yi fira sosai da Neina, kamar
waɗanda daman can san juna, sai duk firar da ake Namra na cikin jikin Anty hawaye
sun ƙi su tsaya mata. Abbah ya kalli agogonsa tare da miƙewa tsaye yana faɗin.

“Ya kamata mu tafi yanzu, da safe Namra zata zo ta muku sallama kamin mu kama
hanya”

Yana faɗar hakan ya saka takalminsa ya nufi ƙofar fita, Lamido da kallo ya bishi
yana aunasa a matsayin lallai zai iya aikatawa Namra haka, da ga alamu yana ji da
kansa, ko kuma be gama hucewa bane oho.

“Allah sarki Namra, ashe kuwa zamu yi marmarinki”

Uwani ta faɗa cikin rashin jidaɗi, dan har ga Allah ita tana tunanin rabuwa da
Namra dan yanzu sun ɗan tsaba da juna.
“Nima ai sai na yi Marmarin ku, mutane masu karamci da sanin darajar ɗan'adam”

Namra ta furta tana mai jin kamar karta tafi ta barsu. Har bakin mota Neina da
Uwani da Maryam suka rakosu, ko da suka fito har Abbah ya shiga mota, Anty Amarya
ta fara shiga sannan Namra, su Neina na ɗaga musu hannu direban yaja mota.

RASHIDA POV.

Ta rame sosai ta koma kamar ba ita ba, tun ranar da taje gidansu su Teema bata sake
leƙa ko ina ba, gurin aikinta sun yi kira sai ta tura musu saƙon bata da lafiya ta
email, sannan ta kashe wayarta, saboda yawan kiran da ake mata akan auren Teema da
tsohon mijinta. Bata iya cin komai banda tea, sai ɗan lemu wani lokacin, kullum a
kwance take salla ce kawai take tashinta. Musamman jiya ta san itace ranar ɗaurin
auren Teema da rabin ranta 😢. Babu wanda yasan inda take balle azo gurinta, Momi
kuma ta juya mata baya da duk ƴan gidansu, lallai sai yanzu ta gane duniya ta juya
mata baya, shiyasa ake cewa idan kana son duniya da yawa ka fara barinta kamin ta
barka, idan har ita ta fara barinka to ba zaka ga da kyau ba. Yanzu kan ta fara
gane baƙin duhun da yake bibiyarta sai dai bata san iya inda zai tsaya mata ba.
knocked ɗin ƙofar falo da taji ana yi ne yasa ta unƙurin tashi taje ta buɗe. A
zatonta Momi ce ko wata daga cikin ƴan gidansu, ga mamakinta sai ta ga Asmee.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Rashida haka kika koma?”

Rashida ta sakar mata ƙofar ta dawoɓsaman cushion ta zauna, Asmee ma zama tayi a
kujerar dake fuskarta ta Rashida, tana yayw mayafinta.

“Haba Rashida, na san kina son Hilal kuma na san Teema bata kyauta miki ba, amman
idan ta samu labarin halin da kika shiga ai daɗi zata ji, kin ware kanki ke kaɗai
kina saka damuwa a aranki”

“Ya akayi kika gane gidan nan?”

“Gidanku naje aka kwatantamin nan, zulfa'u da Rafia duk sun je gida sai a ce musu
kin yi tafiya, nima ban da na matsa da ba za a faɗa min inda kike ba, dan Allah
Rashida ki cire damuwar Teema a ranki”

“Ba auren Teema abunda yake damuna a yanzu ba, irin rayuwar da zata shimfiɗa a
cikin gidana yafi damuna, ita zata reni ƴaƴana, kuma wallahi azzalumace zata iya yi
musu komai, gata ta iya neman magani zaya iya raba su da ubansu”

“Toh ya zakiyi Wallahi Teema ta ci amana”

“Teema ta ci amana kamar yadda nima na ci amana, ta auren min miji kamar yadda nima
nayi taraiya da mijin aminiyata, Asmee duk halin dana shiga a yanzu mijin ki ne
sila...”

Asmee ta gyara zama.

“Ban gane ba. Kamar ya mijina ne sila?”

“Kin ci amanar mijinki kin bada kanki ga wasu saboda neman mallakar miji, ahi kuma
ya ci amanar ki ya bada kansa gare ni, mijinki shi ya saka min cutar hiv, saboda
kin samo gurin wannan bokan kin saka masa, tun daga lokacin da naji kince ana
zargin bokan da cuta, hankalina ya tashi saboda nasan bayan mijina, mijinki ne na
biyu da nake mu'amala da shi, sanadin hakan naje nayi gwaji, aka tabbatar min da
ina ɗauke da cutar, har Hilal ya gane gaskiya yaje yayi gwaji shi baya da shi da
ƴaƴansa, da matarsa, sanadin hakan ya sake ni, shi kansa mijinki be san da hakan
ba, amman ke nasan kin san kina ɗauke da cutar, saboda haka na ci amana, nima Teena
ta ci amanata, sai dai ban san makomar yarana ba, ban san wane irin tarbiya zata
basu ba”

Miƙewa Asmee ta yi tsaye gume na keto mata tashin hankali ya hana hawayen dake
maƙale a idonta zuba.

“Duk yarda da Amincin dake tsanina da ke, ace kin rumtse ido ta auren ki kin yi
zaman banza da mijina? Ina tunanin nayi abunda zan iya na hanasa aure, ashe na
kashe macijina ban tsare kan ba, wallahi ko a mafarki ban za ci zaki min haka ba,
ƴar iska macuciya, ai wallahi sai kin ga abun ki, dan Teema sai ta salwantar da
rayuwar ƴaƴanki... Kuma Allah ya isa tsakanina da ke!”

Ta fisgi gyalenta ta fice a fusace. Rashida kan kuka kawai take, tana mai jin
tsantsar damuwa da nadama a zuciyarta. Kuka tayi sosai, daman kullum cikin yinsa
take, sannan ta koma ɗakinta ta ɗauki kkaton hijab ta saka ta saka niƙab ta ɗauki
makullun motar ta ta fice.

ABDOOL POV.

Tun da ya baro ƙofar gidansu Lamido cikin farinciki yake, dan yasan sahibarsa ma
tana can tana farinciki, kuma yasan zai samu ladar sulhunta uwa da ƴarta, horn ɗaya
yayi aka buɗe masa gate, cikin nishaɗi yayi fakin motarsa ya fito da murmushi kamar
wanda aka yi ma albishir.
What he saw a bakin ƙofar shiga part ɗinsa was surprise him, kurciyar daya gani a
abuja itace a nan? Haske ne ta ko ina a gidan kamar rana, hakan ya bashi damar
ganin layan dake wuyanta.

“Umar...”

Ya ƙwalawa Mai kula.da gidan kira, sai ga shi da gudu yana amsa kiran da yake masa.
Keys ɗinsa ya miƙa masa.

“Zagaya ta baya ka buɗe ƙofar nan a hankali, kurciyarta nake son ta shiga ciki mu
kamata”

“Ranka ya daɗe ai za'a iya halbeta da danƙo”

“Kana da danƙon ne? Kasan yadda zaka halbeta bata tashi ba?”

“Eh za a iya saitawa, amman ranka ya daɗe kurciya da dare baka san me take nufi ba,
balle kuma ga laya a wuyanta”

“Idan mutum yana addu'ah babu abunda zai same shi, kawai ka halbe min ita idan zaka
iya”

“Toh”

Ya nufi wani part ɗin na gidan, da ɓangarensu yake a can, be ɗauki dogon lokaci ba
sai ga shi ya dawo da danƙon har da duwatsunsa guda biyar. Ayatul kursiyo ya
karanta sannan ya saita inda take ya harba da bismilla. Firr tayi zata tashi sai ta
faɗi saboda ya same ta a ƙafa. Da sauri Abdool ya ƙarasa zai kamata sai ta sake
unƙurin tashi ta kasa har ya kama ta, sai da yayi bismillah sannan ya cire layar
dake wuyanta. Umar ya miƙawa kuciyar ya shiga buɗe layar. Wasu surkulle ne aka yi
aka kulle da fatar baƙar akuya, sai wata farar takardar a tsayarki takardar an
rubuta sunan Namra da larabci.

“Namra”
Ya maimata sunan cike da mamaki da ɗaurewar kai.

“Miya kawo sunan Namra anan? Waya aikata mata haka?”

Yayi ma kansa tambayar da bashi da amsar ta.

“Umar kasan yadda ka yi da wannan kurciyar”

Ya faɗa sannan ya shiga cikin falon da abun a hannunsa.

KALSOOM POV.

Hannu ya kai ya shafa fuskarta.

“Haba dai baki kishi ranar ɗaura aure ba sai yanzu zaki yi? Ko dai wani ne ya zuga
ki?”

Kai ta girgiza masa alamar a'a, ta janye hannunsa daga fuskarta ta miƙe tsaye.

“Zan shiga wanka”

Hannunta ya riƙe.

“Kalsoom ko na miki wani abu da ba daidai bane?”

Ta saka mashi kuka.

“Baka min komai ba, kawai dai...”

miƙewa yayi tsaye ya haɗe bakinsu, yana shafa bayanta alamar rarrashi. Sun ɗauki
tsowon lokaci a haka sannan ya sake ta.

“I promise you ba zan miki wani abu da xai cutar da ke ba”

Ya kwantar da kanta ƙirjinsa. Ba shi take ji ba, Amaryar tasa take ji dan bata san
da me tazo mata ba, bata son ta sake shiga irin rayuwar da tayi da Rashida a baya.
Sai da ya tabbatar ta samu sukuni sannan ya sake ta yana tambayar me zai siyo mata.

“Ina son zogale”

“Okay”

Yayi mata kiss, ya shafi cikinta sannan ya juya ya fice. A gurin ta tsaya har sai
da ta ji tashin motarsa sannan ta shiga wankan. Tana cikin wanka taji tsayawar mota
sai kuma kamar ba ta Hilal ba, hankali kwance ta yi wankanta ta ɗaura tawul ta
fito. Haka kawai ta ji bata da natsuwa idan bata leƙa taga wanda ya shigo ba, dan
haka tana fitowa ta zira doguwar riga ta ɗora ɗankwalin a saman kanta ta nufi
falon.
Abunda ta gani ya bala'in ɗaga mata hankali Rashida ce zaune saman kujera tana
kallonta, fargaba da tsoro suka tunkarota lokaci ɗaya, idonta be gama tantance
Rashida ɗin bace ko waninta, dan ta lalace sosai ta rame, idan har ita ɗince mi
tazo yi gurinta, ga ta cikin hijabi niƙab a hannunta.

ASIM POV.
Yana saka kuɗin sai ga kiran Hajiya Sadiya, sai da ya shiga mota sannan ya yi
picking.

“Hajiya na saka kuɗin”

“To yayi kyau, ina son muyi wata magana da kai Asim mai muhimmaci”

“Okay na zo kenan?”

“A'ah ba sai ka zo ba, saboda ƴata bata riga ta tafi ba”

“Toh ya za'ayi kenan”

“Ka same ni a wacan gidan, akwai zan maka wani tayi ne kuma ina fatar ka amsa”

“Okay what time zan zo?”

“An jima da yamma”

“Okay Allah ya kai mu”

Ta kashe kiran. Kai ya girgiza yana cizon bakinsa.

“Ta tabbata Nably ƴarki ce”

Ya kunna motarsa ya bar gurin. A unguwar su Hajiya sadiya yayi sallah la'asar, 6ana
hango lokacin data shiga cikin gidan. Sannan shima yaja motarsa ya shiga cikin
gidan.

Yana ta sallama bata amsa masa ba sai da ta fito bedroom sannan ta amsa masa. Cikin
ladabi ya gaisheta yana kallon yanayin fuskarta mai ɗauke da damuwa.
Shi ya fara zama sannan itama ta zauna tana kallonsa.

“Asim ya maganar matar ka ta dawo kuwa?”

Ya ɗan sosa kansa.

“A'ah nayi nayi taƙi dawowa, kuma yanzu ta daina ɗaukar wayata ma, gashi ba gidansu
ta je ba”

“Yanzu dai babu zancen dawowar ta kenan?”

“Gaskiya babu shi, daman ni dan kin matsa ne shiyasa nake son na dawo da ita”

Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta kalleshi a natse ta ce.

“Asim ina son ka auri yata, kuma auren shekara ɗaya, zan baka miliyan ashiri, zan
baka gurin da zaku zauna, bana buƙatar ka yi komai, zan maka lefe zan baka kuɗin
sadaki, zan mallaka maka shagona na siyar da zinari da sabuwar kasuwa, kuma duk
wani event da za ayi ni zan ɗauki nauyi”

Da sauri Asim ya miƙe tsaye yana mamakin irin wannan narkakkiyar dukiyar da zata
bashi, saboda kawai ya auri ƴarta ƴar da bata taɓa labarta masa tana da ita ba.

________________________________

BEST REGARDS 🌹
I LOVE YOU ALL♥️

*77*

Kalsoom ta yi baya-baya kamar zata koma ɗaki, sai Rashida ta yi saurin miƙewa tsaye
ta ɗaga mata hannu.

“Dan Allah ki tsaya ki saurare ni, ba cutar da ke zan yi ba, zuwa na yi na roƙe ki
kuma na nemi taimakon ki”

“Akan mi, mi zan miki?”

“Ki dubi girman Allah ki taimaka min ki riƙe min ƴaƴana...”

“Ban gane ba, kamar ya ƴaƴanki?”

“Bana son amaryar da Hilal yayi ta riƙe su, saboda bata da tarbiya kuma azzulamace
zata iya cutar da su”

Kalsoom ta nuna ta da yatsa tana mai jin duk wani tsoro nata ya tafi.

“Ke Rashida yadda kika yi boko haka nima nayi, karki nemi raina min hankali wato na
rikasu a sake cewa zan kashe su ko? Naga dai yanzu mu biyu ne, be kamata ace ni
kaɗai kike kishi da ni ba”

Hawaye ya cika idon Rashida.

“Ba kishinki nake ba wallahi, gaskiya nake faɗa miki kuma nake roƙon ki, ki taimaki
rayuwar ƴaƴana ki riƙe su”

“Teema ce tafi kowa dacewa data riƙa ƴaƴanki, saboda ita ce ta gari a idon Hajiya,
kuma an yarda da tarbiyarta, sannan naga ƙawarki zata kula miki da su kamar ke, dan
haka ki fita ki bar min gida ko na kira Hilal yanzu na faɗa masa”

Ta share hawayen da suka zubo mata.

“Ba sai kin kira shi ba, zan fita, na gode da kika saurare ni, ban cancanci ki
saurareni ba amman kin saurare ni na gode sosai”

Ta saka niƙab ɗinsa, sannan ta juya cikin kuka ta fice. Rufa nata baya Kalsoom ta
yi, ta tsaya bakin ƙofa tana kallonta, har sai da taga ta shiga motarta mai gadi ya
buɗe mata gate ta fice sannan hankalinta ya kawanta.

“Allah ya min tsari da sherin ki ni wannan wane irin mugun kishi ne!”

Ta faɗa tana maida ƙofar falon ta rufe.

*** *** ***

Da wani irin kuka Rashida ta ƙarasa gida, tana mai jin zuciyarta kamar zata tsage
biyu, saboda baƙinciki da damuwa, ta rasa inda zata sa ranta taji sanyi, ta rasa
inda zata saka rayuwarta ta samu sassauci, lokaci ɗaya duniya ta juye mata ta zo
mata baibai.
Bata samu gurin faka motarta ba saboda motar Alhaji Bashir da ke waje, hakan ya
tabbatar mata da yana ciki kenan.
Tafiya take kamar wata tsohowa, daman bata da wani kuzari saboda rashin cin abincin
kirki da kuma damuwar da ta gama karya mata gaɓoɓin jiki.

Safa da marwa ta hango yana yi a ƙofar shiga falonta, ko be faɗa mata ba, tasan
Asmee ta kai masa labarin da ta faɗa mata ɗazun ne, dan tana iya hango tashin
hankalin dake shimfiɗe saman fuskarsa. Tun kamin ta ƙaraso inda yake, ya soma nuna
ta da hannu, cikin wata irin murya da shi kansa be san yana da ita ba.

“Macuciya azzaluma, dan taki rayuwar ta ƙare shine kike neman abokin kuka ko? To
nafi ƙarfin ki Wallahi baki isa ki rushe min rayuwa ba”

“Kamin ka zo nan kana min hargagin banza ina fatar kaje asibiti sun tabbatar maka
da kana ɗauke da cutar ko? To ni ba abokin kuka nake nema ba, kai ne kake neman
abokin mutuwa, dan rayuwa sai ta fi taka tsawo, sannan na gama rushe maka rayuwa
Alh Bashir matuƙar baka aure ni, dan ban dace da zama da kowa ba sai kai, kai ne ka
sani a halin da nake ciki”

“Ko kuma kika sani ciki ba, daman ai na daɗe ina zarginki, duk mace da zata bada
kanta ga wani namiji ba mutum ɗaya zata tsaya ba, waya sani ma ko mijinki ne ya
ɗauko cutar ya saka miki ke kuma kika saka mana, ni ban san ƙaddararta kai ni
mu'amala da ke ba”

“Ni bance ka zame min ƙaddara ba kai zaka ce na zame maka? Na rasa abubuwa da dama
sanadin mu'alama da kai, ƴan'uwana sun guje ni, mijina ya sake ni, na rasa lafiya
ta, da duk wani farinciki nawa sanadinka Bashir, duk kai ka jani ga wannan halaka”

“Ko kuma kika jani ba, da baki sake jikinki ba zan gani ne har na yi sha'awa? Idan
baki yarda ba fyaɗe zan miki ne? Baki kiji na faɗa miki da zarar naje aka gwada
jinina aka tabbatar ina ɗauke da wannan cutar kutu ce zata raba ni da ke...!”

Yana kaiwa nan ya doshi gurin motarsa. Ita kuwa ta raka shi da maganganu tana
hawaye.

“Idan ka fasa kai ni kotu baka haifu ga uwarka da ubanka ba Bashir kai ba ɗan halak
ba ne, azzalumi macuci wanda be ji kunya keta dokar Allah, sakarai mai neman Matar
abokinsa Allah ya isa tsakanina da kai”

Sai ta ta kunna motarsa ya bar gidan sannan ta durƙushe a gurin tana kuka.

“Kaico na ni Rashida, ina ake siyar da farinciki ne na siya! Ina zan yi musanyar
damuwa da kuka na samu sanyin zuciya! Mi na ma duniya haka ne? Miyasa suka
ƙaddarori zasu taru a kai na ne? Allah na tuba ka yafe idan zunubi na ne yasa ni a
wannan halin”

Kuka take sosai tana ji kamar ƙasa ta haɗiyeta ta mutu ta huta gaba ɗaya da wannan
rayuwar. Ra rasa dalilin daya sa rayuwa take koya mata darussan da take ganin bata
cancanci koyansu ba.

NAMRA POV.

Kai tsaye direban ya nufi gidan Mai Martaba kamar yadda Yarima ya umarce shi, horn
ɗaya yayi aka buɗe musu gate, ɗayan part ɗin gidan ya nufa da su, sai ya faka
daidai ƙofar part ɗin ya fito da sauri ya buɗe ma Abbah ƙofa.

“Ya ce akwai komai a ciki, idan akwai abunda kuke buƙata zaku min magana”

Kai kawai Abbah ya ɗaga masa ya nufi ƙofar. Anty Amarya ce ta amsa masa da to,
Namra na riƙe da hannun Anty kanta kuma kwance saman kafaɗar Anty, har suka shiga
falo, sanyin ac ne ya fara musu martabun, daga bisani ƙamshi ya biyo baya. Kai
tsaye Abbah ya nufi wani ɗaki dake ɗayan ɓangare da wasu ɗakunan, yana shiga ya
hango manya tufafi kala biyu saman gadon, sai kuma kayan bachi da ba a cire daga
leda ba kala ɗaya, an ɗora takalmi da turare da hula mai kyau saman kayan, hakan ya
tabbatar masa nan ne ɗakinsa, ɗan murmushi yayi kaɗan ya rage kayan jikinsa ya nufi
bathroom.

Mamaki ya cika Namra da Anty Amarya lokacin kowa ya samu tufafin sajawa da kayan
bachi saman gadonsa, bama kamar Namra da ta tarar har da pants da pad ya aje mata,
ya akayi yasan bata sallah shine abunda ya fi tsaya mata a rai. Bathroom ta shiga,
ta yi wanka, sannan ta shirya cikin kayan bachi masu kama da na maza, ta fito ta
nufo falo. Anty Amarya da Abbah ta samu zaune a dinning suna cin abinci. Abbah ne
ya fara ɗagowa ya kalleta, murmushin da ta gani a fuskarta yasa idonta cika da
ƙwalla.

“Toh Sarkin kuka zaki fara ko?”

Cewar Anty Amarya fuskarta ɗauke da annuri, tana miƙawa Abbah tea da ta haɗa masa.

“Komai ya zo min kamar mafarki, gani nake kamar ba gaske bane, ban yi zaton Abbah
zai saurare ni haka da wuri ba har ya yafe min, nasan nayi muku abubuwa marar kyau
da yawa, amman duk da haka suka samu fili a zuciyarku kuka yafe min”

“Kin cancanci yafiya Mamana, saboda kin gane kuskurenki, sai dai kin shiga rigar
mutane masu mutunci wanda hakan yasa kika samu yafiyata a kusa, sai dai ina fatar
ba zaki ƙara aikata irin wannan kuskuren ba”

“Wallahi ba zan sake ba Abbah, na maka alƙawari har na koma ga mahallici na,ba zan
sake aikata kwatankwacin wannan kuskuren ba”

“Allah yayi miki albarka”

“Amin Abbah na gode, i love you so much”

Ta zo da sauri ta rumgume shi tana kuka. Anty Amarya ta share hawayen idonta tana
kallon Abbah.

“Allah ya saka maka da alheri, na gode”

“Yanzu ai ta kuka da ciwon zuciya ya ƙare ko?”

Cewar Abbah fuskarsa da murmushi yana kallon Anty Amarya cike da son Amaryarsa.
Daga bisani ya kalli wayarsa da ke saman dinning tana ringing. Hajiya Barau ce
rubuce a screem ɗin wayar. Miƙewa yayi tsaye, sannan ya kai hannu ya ɗauki wayar
yana danna picking ya nufi bedroom.

A kujerar da ke kusa da Anty Namra ta zauna, tana share hawayen da suka ƙi tsaya
mata.

“Na haɗa miki tea zaki sha?”

Ta gyaɗa kai.

“To ki zuba abincin ki ci idan kin gama zan haɗa miki”

“Bana jin yunwa Anty, tea kawai ya isa”

Ajiyar zuciya Anty ta sauke, ta shiga haɗa mata tea, tana faɗin.

“Namra duk kin rame kin koma wata iri, kin yi baƙi sosai, Yarima ya faɗa mana Asim
ya sake ki ne saboda kina da ciki!”
Ta gyaɗa kai tana share hawaye.

“Kuma har yanzu be neme ni ba, ina gidansu Lamido cikin ya zube”

“Kin san ciki ba zai taɓa tsayawa a mahaifarki ba Namra saboda matsalar da kika
samu, na yi mamaki ma da kika samu ciki bayan an saka miki roba”

“Shi yace sai na cire, kuma da ma samu cikin yace be shirya haihuwa yanzu ba, sai
dai na zaɓa tsakanin cikin da shi, ni kuma na ƙi yarda na zubar shiyasa ya sake ni”

“Kin samu ƴancin kan ki yanzu, Allah zai bi miki haƙƙin ki. Amman ina kika haɗu da
wannan yaron”

A nan Namra ta kwashe labarin komai na sanin da tayi ma Abdool ta faɗa ma Anty.

“Yana da mutunci sosai, kuma ina fatar zaki masa hallacci duk ranar da ya nemi
ladan alherin da yayi miki”

“Kamar ya?”

Ta tambaya dan har ga Allah ita bata gane inda zancen Anty ya dosa ba. Anty ya miƙe
tsaye tana murmushi.

“Kamar haka, ki je ki kwanta dare ya yi, zan kira Maryam na ce ta shirya zan vata
mamaki, daman ta fi kowa damuwa da auren nan na ki”

“Na gode sosai Anty sai da safe”

Ta daɗe a gurin zaune sai ƙarewa falon kallo take sannan ta tashi ta nufi bedroom.
Har garin Allah ya waye, dan har yanzu ta kasa yarda da abunda ya faru, ganin komai
take kamar mafarki. Idonta biyu aka yi kiran sallah asuba, unƙurawa ta yi ta tashi,
sai ta nufi gurin maɓallin kutar ɗakin ta kunna. Ta shiga toilet ta tsabtace kanta
sannan ta yi wanka ta fito.
Bata tsaya shafa mai ba, ta ɗauki abaya ta saka, sannan ta ɗora da hijab, gefen
gado ta zauna sai ta ɗauki carbi tana lazimi, ba ita ta tashi ba sai bakwai da rabi
saura, shi ma dan ta ji ana buga ƙofar falon ne.
Bata damu da tambayi ko waye ba kawai ta kai hannu ta buɗe ƙofar. Suna haɗa ido
gabanta yayi mugun faɗuwa, da sauri ta sadda kanta ƙasa, shi kam ƙin sauke idonsa
ƴayi har ta miƙa masa gaisuwa.

“Ina kwana?”

“Nan ba ina kwana suke cewa ba”

Ɗan murmushi ta yi wanda be kai zuci ba.

“An tashi lafiya?”

“Lafiya ƙalau, i hope you sleep well?”

“I did”

“Amman idonki ya nuna kamar ba ki yi bachi ba”

“Kana da buƙatar wani abun ne?”

Ta tambaya da nufin kawar da maganar. Wani dogon numfashi yaja ya sauke

“Ban sani ba ko kuna da bukata ne, yanzu zan kama hanya, Mai martaba ya kira ni
yana da buƙatar gani na, ajima direba zai ɗauke ki zai kai ki a miki passport, da
ƙarfe uku jirgi zai tashi, so za a muku duk wani abun da ya kamata, around nine za
a kawo muku breakfast. I think Abbah suna bachi, ki faɗa musu na tafi”

Kai ra gyaɗa masa, sai ya zuba hannyensa aljihu ya juya zai wuce.

“Ab...da...llah”

Ta kira sunansa cikin wata irin siga da ba'a taɓa kiransa sunan yayi masa daɗi
kamar yadda ita ɗin ta kira shi ba, har cikin zuciyarsa ya ji kiran nata da
muryarta dake kamar zata fasa masa kuka. Juyowa yayi ya kalleta da manyan
idanuwansa.

“Thank you”

Gira ɗaya ya ɗaga mata, alamar for?

“For helping me out”

Murmushi yayi mata mai fidda annurin fuskarsa.

“Safe flight”

“Wish you the same”

Murmushi yayi mata as respond ya juya ya cigaba da tafiya abunsa, kamar wanda baya
son taka ƙasa. Haka kawai ta samu kanta da kasa ɗauke ido a kansa har sai da ya
shige part ɗinsa.

ASIM POV.

Kallo Hajiya Sadiya ta bishi da shi, zuciyarta Allah-Allah ya amince.

“Miyasa zaki min tayi mai tsada akan kawai na auri ƴarki?”

“Saboda kai ne kaɗai na yarda da tarbiyarka, kuma nasan ƴata tana son ka, saboda ta
nuna min hoton ka har tace zaka zo ka gaishe ni”

“Ko baki bani komai ba zan iya aurenta saboda aurenta na yi niyar yi, amman ki faɗa
min gaskiyar abuda kike ɓoyewa wata ƙila zan iya taimakon ki”

“Ko da baka aureta ba, na yarda ka yi zina da ita, idan ta samu ciki sai ka rabu da
ita”

“Miyasa sai ni?”

“Saboda ba zan iya facing yata na faɗa mata ta auri wanda bata so ba, kuma nasan ba
zan saka ta aikata zina ba”

“Da baki yi gaggauwa ba, da aurin ƴarƙi zan yi, miyasa baki bar ni na aureta ba,
iya ka kice min na turo iyayen Sai a ɗaura mana aure. Ki faɗa min gaskiya mana
Hajiya”

“Zauna zan faɗa maka komai, saboda na yarda da kai kuma ina fatar zaka taimake ni”

Ya zauna yana fuskantar ta.

“Sunana Hajiya Sadiya kamar yadda ka sani, an haife ni a garin nan, amman ko da na
tashi ban san iyayena ba, mahaifina da mahaifiyata duka Allah yayi musu rasuwar tun
kamin na mallaki hankalin kai na, dan haka na tashi a gidan kakana Sarkin Katsina
na wacan lokacin, na samu gata iya gata a gidan, duk da bani kaɗai bace wacce ake
riƙo a gidan, amman saboda ni marainiyace, be yarda ya bar mu mun yi karatu a nan
ba, a lokacin govnati na ɗaukar nauyin karatun saboda ana ƙyamar bokon ne, so duk
wanda ke da ilmi za a ɗauki nauyinsa zuwa ƙasar waje karatu, Zuwaira da Murja da
Sadiq su aka saka a ƙarƙashin govnati ni kuma shi ya biya min a cikin aljihunsa.
Dukan mu mun yi karatu, duk da ba ƙasa ɗaya aka kai mu ba, dan ni na zaɓi London
ne, su kuma Egypt aka kaisu suka yi karatun lafiya.

Na fi sawa shashanci gaba, saboda farar fatar da nake tare da su, na kan rakasu
gurare daban-daban hakan yasa muka shaƙu da su sosai. Su san burina saboda ina
yawan faɗa cewar nafi son nafi kowa ɗaukaka a makarantar nan, ranar sai wata take
ce mun zata faɗa min wani sirri, zata kai ni inda za'a taimaka min na samu ilmin da
ya fi na kowa, kuma na fi kowa ɗaukaka a makarantar. Ban yi musu ba, na biyeta ta
sani a cikin wata ƙungiya, ashe ƙungiyar asirice, buƙatata ta biya tabbas, saboda a
wannan shekarar ni nayi ta ɗaya a duk faɗin makarantar, daga haka sai abubuwa suka
buɗe, duk abunda nake da bukata zan je ne kawai na faɗa kuma sai buƙata ta biya, a
lokacin muna meet duk ƙarshen wata, amman lokacin dana ƙare karatun na dawo nan sai
suka haɗi ni da manyan da suke abuja, a nan naga manyan mutane, maza da mata a
cikin har da manyan ƙasar nan. Duk lokacin da za'ayi meeting ɗin, na kan bar
Katsina na je abuja da sunan ganin wata Sister mu ƴar sarki, sai naje meeting idan
an gama da kwana biyu na sai na dawo.

Na samu babban aiki a lokacin, nama fi kowa kuɗi a gidan mu, da haka na haɗu da
baban su Nabila. Bayan mun yi aure yace baya son aiki, sai na haƙura, a nan su kuma
suka soma saka min ƙa'idojin da ban san da su ba a wacan lokacin.

Sun ce min dole ne na riƙa neman mata ƴan'uwana, idan ba haka ba, ba su yarda na
fitar da zakka ba. A dole na ɗauki ka'idar mu'amala da mata ƴan'uwana, tun ban saba
ba har abun ya zame min jiki, ya koma bana jin daɗi mu'amala da mijina sai mata.
Daga baya kuma suka ce suna son a riƙa kawo musu sabbin membobi saboda tsofin ciki
suna mutuwa ne, kuma ina son a riƙa yaɗa abun.
A abuja nake zaune da mijina, ɗan haka duk lokacin da naso zuwa kawai nake gurin
meeting ɗin ba tare da ya sani ba, wata rana da muka yi meeting sai suka ce suna da
buƙatar na Sadaukar musu wani daga cikin iyalaina, ba ni da zaɓi dole na bada
mijina, sai ya samu haɗarin mota ya mutu, daga nan kuma sai babban ɗa na, sai mai
binsa, sannu-sannu suka cinye min duka ƴaƴana, Nabila ce kawai ta rage min.
Shekaran jiya da nace maka zanje birnin keebi ba can naje ba, Abuja na je, gurin
meeting ɗin. Yanzu kuma Nabila suke so, ko ɗanta. Ni ko da na bada ita ƙara na
bayarda kai na, shiyasa nake son ka taimake ni, ka ceci rayuwata da ta ƴata saboda
ita kaɗai ta rage min”

Asim ya sake miƙewa tsaye a karo na biyu.

“Wallahi Allah yana so na, wato da yanzu sai dai ki bada ni? Dan nasan zasu ma iya
cewa ki kawo yaron gidanki, ko kuma idan mun yi aure ace ko bada surikin ƴar ki, ai
ni duk sun kuɗi na be kai na iya rayuwata ba kuma ni daga yau na barki har a bada
wallahi”

“Kar kayi saurin yanke hukuncin Asim kaje ka yi tunani”

“Ba wani tunani da zan yi, salon ki sani cikin mugun hali”

“Da ina da niyar saka ka da na saka tun farkon dana saka tun farko dana fahimci
kana da son kuɗi, amman ba kai nake target ba matarka, saboda nasan idan na sata
cikin ƙungiyar zasu biya kuɗi mai yawa wata ƙila ma ya iya zama fansar ƴata, amman
sai gashi ka saki matarka, da yanzu ace zaka iya kawo min matarka zasu iya ɗaga min
ƙafa”
Tsayawa yayi kallonta.

“Indai har Namra zata iya zana fansar ƴarki to zan iya kawo miki ita, bisa sharaɗin
zaki bani naira billion uku”

“Wallahi zan baka, kuɗi ba matsala ta bace idan na faɗa maka abunda na tara sai ka
haukace, kuma Namra ba kasheta zamu yi ba Wallahi, cikin ƙungiyar kawai za mu
sakata”

“Amman taya zan kawo miki ita?”

“Zaka maida aurenka, sannan duk abunda zai biyo baya ya biyo, kuma idan kana so
zaka iya auren Nabila”

“Ƴarki kam na yafe, amman Namra zaki sameta kamar yadda kike buƙata”

Ta miƙe tsaye ta shiga ɗakinta bata jima.ba ta fito riƙe da amt ta miƙa masa.

“Akwai milion talatin a ciki kayi amfani da su”

Ya miƙa hannu ya karɓa sannan ya juya ya fice.

TEEMA POV.

Tana kwance saman jikinsa, shi kuma sai faman dannar waya yake yana murmushi.
Azatonta dan tana shafa jikinsa yake murmushi, shi kam hankalinsa gaba ɗaya ya tafi
kan waya sai faman chating yake da Kalsoom.
Ƙyalƙyalewa yayi da dariya sannan ya kashe datarsa ya kalleta.

“Bari na leƙa office”

“Okay Allah ya tsare min kai”

“Amin dear. Amm anjima Hajiya tace zata aiko da su Ezzah”

Sam bata ji daɗi ba, duk da tasan dalilinsu aka auro ta, amman bata yarda ta nuna
masa ba.

“Kai Amman ko na jidaɗi daman ina ta jiran su zo, Allah kawo su lafiya”

“Amin”

Ya faɗa yana ɗaukar hulal dake saman hannu kujera ya saka a kai.

“Okay I love you”

“Love you too”

Da kallo ta bishi sai da ya fice sannan ta miƙe tsaye.

“Sati uku da aure ace za a ɗauko yara a kawo maka, nifa ba bautarsu na zo yi ba, ko
amarci ban gama ci ba za'a haɗa ni da ala ƙai ƙai, yara zaggan-zaggan da su, su
riƙa sa maka ido idan ka yi ma miji wani abu, mtsssss”

Taja wani uban tsaki ta wuce bedroom ɗinta. Bata jima ba ta fito ta nufi kitchen,
girki ta ɗora sai mita take ranta duk a ɓace, dan har ga Allah bata so a kawo su
yanzu ba.
“Daman fa ance wasu uwayen miji ba son suruka suke ba, in banda sheri kin san ina
Amarya ɗan Amarcin ma ba za'a bari na yi ba, kai kayi naka lokacin sai kace wani ba
zai yi ba, nasan dan su aka auro ni amman ai a bari na ci lokacina, tun da can ba
saman ƙaya suke ba, daga zuwanka da ƙurciya zaka fara aikin ƴaƴan kishiya”

Kamar mai faɗa da wani haka ta riƙa zuba surutanta har ta yi girkin ta gama mita
take, sai da tasa komai a muhallinsa sannan ta shiga ciki ta yi wanka. Tana fitowa
ta shirya cikin yellow atamfa, ta kashe ɗauri ta feshe jikinta da turare sannan ta
fito falo ta zauna.

Tana jin tsayawar mota ta ƙara gyara ɗaurin ɗankwalinta, tana zaton ko Hilal sai
kawai ta ji mota ta tashi, su Ezzah sun turo ƙofa sun shigo fuskarsu da far'ah
bakinsu kuma ƙumshe da sallama.

Ciki-ciki ta amsa musu tana murmushin da be kai zuci ba.

“Maraba da ƴaƴana”

“Momi ina wuni? Momi ina wuni?”

“Lafiya ƙalau”

Sai suka zauna saman kujera. Daga nan bata sake bi ta kansu ba, sai da ta ji motar
Hilal sannan ta tashi ta koma tsakiyarsu ta zauna ta jasu jikinta ta rumgume tana
murmushi.

“Ku bani labarin Hajiya...”

ABDOOL POV.

Around ten ya sauka Katsina, sai da ya fara biyawa Mai Martaba ya ganshi sannan ya
wuce gurin Ummi. Da murmushi ya shiga part ɗin Ummi, kamar yasan ita kaɗaice a
falon, dan duk ƙannensa sun tafi makaranta.

“Ummi barka da safe”

Ya taɓe baki tana kallonsa.

“Ni ban ga amfanin wannan hutu naka ba, kullum kai ne yawo ba zama gida, yanzu da
aure kake yi wace mace ce zata ɗauki wannan rayuwar”

Kusa da ita ya zauna yana dariya.

“To ai gurin matar na je, yau zan baki labarin komai saboda na samu mafitar matsala
ta, amman fa nasha wuya but at the end yau tace min Thank you”

“Kana nan kana wahalar da ƴar mutane ai dole wata ta saka cin kwakwa, tun da ka
tagi Amirar nan kuka take, na rasa gane kanta idan kuma na tambaye ta sai tace
babu komai, yau ma ce min tayi gida zata je daker na hana ta”

“Ina take?”

“Tana ɗakinta”

Ya miƙe tsaye ya nufi ɗakin Amal. Yana tura ƙofar ɗakin ta ɗago ta kalleshi sai
kuma ta juya,
“Amira can we talk?”

“Maybe Later i need some space”

Ta faɗa da muryarta ta kuka.

“Okay but i just want you to know that i care for you, if you need someone to talk
to, i'm downstairs”

Daga haka ya juya ya fice. Ita kuma. Ta fashe da kuka.

*78*

Kusa da Ummi ya sake zama yana kallon tv.

“Tana son ta saka kanta cikin matsala ne kawai Ummi amman tasan ba zan taɓa son ta
ba”

“Nasan tana son ka har zuciyarta, amman sam ban yarda da yarinyar nan ba, mutanen
da sukayi ƙoƙarin su kashe ka, waya sani ko plan ne aka yi ta yadda idan ta aure ka
zata fin jindaɗin kashe ka”

Yayi murmushin gefen baki.

“Ko babu plan Ummi bana son ta, ko da kuwa tun can farko ita mai tarbiya ce,
because if i love someone i mean it no matter what she did or whoever she is, and
if i said i do i do, so i don't love Amira, i only fell in love once because i have
never been in that kind of situation, but when it comes to Namra i take it so
serious, and i love with all my heart and blood and mind and soul i love her more
than you think Ummi”

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke, ta kalli ɗanta fuskarta da alamun damuwa.

“Tell me more about her”

Miƙewa ya yi tsaye ya nufi freezer.

“She's so simple and kind, but difficult to handle. You know when we first meet,
she slap me and insult me in front of my boys, but i can't slap her back”

Ya ƙarasa yana bulbula ruwan da ya fiddo a cup. Ummi ta yi murmushi.

“I know how my son is ba ya faɗa da mata”

“Yap bana faɗa da mata because we are not in the same level, strength, brain,
heart, soul and lot. Ban taɓa jin ina son wata mace ba, but lokacin da na ji ina
son Namra, nasan our souls mean to be, duk da a lokacin na san tana da aure, amman
zuciya ta kasa haƙura, and now what! Her husband divorce her ta je wani gida ta
zauna, kuma ƙaddara ta sake haɗa mu kaduna na kaɗe yaron gidan ina zuwa sai gata a
gidan, hmm' mmm funny, and now ni ne silar shiryawa da iyayenta, i hope you love
her too?”

“Of course i love her ai dole naso matar da ɗa na yake so, but i'm just worried
about Mai Martba, ba lalle ne shi ya so ta”

“Why”

“Saboda Bazawara ce! And i hear that Mai Martaba and Hajiya Shafa sun maka mata”
“What...!”

Ya aje cup ɗin ruwa dake hannunsa saman dinning yana kallonta fuskarsa cike da
tashin hankali.

“How true it's?”

“Mai Martaba ya kira ni da kan shi, yana neman shawara akan zai ɗoraka a Sarautar
Katsina, da na nuna masa be dace ba sai ya nuna ɓacin ransa, the following day ya
sake kira a waya ya faɗa min Hajiya Shafa tace be kamata a ɗoraka a Saurata baka
tare da iyalaiba, dan haka ta maka mata, zata aura maka Zaliha ƙanwarta, idan anyi
auren da watanni sai a baka Sarautar, kuma Mai Martaba yayi na'am da hakan”

“Miyasa baki faɗa musu ina da wacce nake so ba?”

“Idan na faɗa zai ga kamar ina kare ka ne, amman ina son ka min wani abu Abdallah,
duk yadda Mai Martaba zai yi karka yarda ka karɓi Sarautar nan, kai ne ɗa na uku a
gurin shi, be kamata ya tsallake su ba, ya ɗauki Sarauta ya baka, nasan yana son
ka, amman hakan ba zai jawo maka komai ba sai ƙiyayya da ganin laifi, kai kuma ka
yi ƙanƙanta da irin rayuwar nan, kuma idan har ka yarda ka auri Zaliha, to ka jefa
rayuwarka da ta mu cikin matsala, tun da ƙanwar Hajiya Shafa ce, kuma kasan wacece
Hajiya Shafa a gareni da gare ka. Ka da ka amince da duka biyu idan har ya yi maka
magana”

“Ai ba zan amince ba, ina son aiki na kuma ina alfahari da shi, ni ba Sarauta ba ce
a gabana, kuma Namra ce kaɗai matar da nake so”

“And be careful with her love too, kar ya rufe maka ido ka saɓawa Mahaifin ka”

“My Dad is...”

Ummi ta miƙe tsaye tana tarar numfashinsa.

“I know who your Dad is, he's my ex-husband the Father of my own male son”

Ta nufi bedroom ɗinta. Shi kuma ya faɗa zaune saman kujerar dinning yana bugashi da
ƙarfi.

“Damn it! miyasa abubuwa zasu zo min haka kuma yanzu? Shine surprise ɗin da Mai
Martaba yake ta faɗi? Ya Salam...!”

Ya miƙe tsaye, sai ya nufi kitchen duk da ya san babu abunda zai ɗauka a gurin. He
need some fresh air, sai ya buɗe ƙofar baya ya fita, jin ya gaba ɗaya gidan ya masa
wani irin, kai tsaye ya nufi Garden, ko ba komai yana son kukan tsuntsaye maybe zai
sashi relaxing ya sama ma kan shi mafita.

Gaban icen guava ya zo ya tsaya yana kallon pool, motsin mutum ya ji a bayansa,
yasan cikin biyu ba za'a rasa ɗaya ba, Maybe Amira ce tun da ita kaɗai take gidan
ko kuma barewa, dan tana masa haka a duk lokacin da ya shigo Garden ɗin. Juyowa
yayi sai yayi ido huɗu da Amira fuskarta shakaf da hawaye.

“What do you want?”

“You told me if i need someone to talk to”

“It Abdool who told you that, and now i'm someone else, and my words could hurt
you, i'm not in the mood”
Cikin muryar kuka ta ce.

“You already hurt me because i learn the truth, i know you upset because of what
Ummi told you, we share the same pain, i'm in love with you while you're in love
with someone else”

Ta share hawayenta da haɓar rigarta.

“Maybe i will have peace of mind if you tell me that you never love me, maybe i
will back to my senses, think about my future and....”

Kuka ya ci ƙarfinta. Taku biyu yayi ya matso kusa da ita.

“Do you know what is best for you, ki koma gida cikin iyayenki, ki manta da ni a
rayuwarki, and i promise you zan rufa miki asiri ba zan faɗawa kowa abunda kika
aikata ba”

“Zan koma gurin iyayena, nima a yanzu babu abunda na ke so sai su, but forgetting
you is the hardest thing ever, thank you so for letting me staying with your family
and know you better, can you take me home now please, am eager to see my parents”

“Yeah... Zan ma direba magana, ki shirya kayan ki”

“Ban zo da komai ba a nan”

Har ta juya sai kuma ta juyo.

“Ina matar da kake so take?”

“Why?”

“Saboda ta fi kowa sa'ah a duniya, ina son na ganta ne kawai”

“I can't tell you Amira, i'm sorry to say this, i don't trust you”

“I know i shouldn't...”

Ta juya ta shiga ciki da kuka. Da kallo ya bita sai da ta fice sannan ya haka
hannunsa aljihu ya ciro handkerchief yana shinshinawa.

“I loved you so much”

Ya ɗauki tsawo lokaci a gurin sannan ya nufi part ɗinsa. Be daɗe ba ya fito da
takarda hannunsa ya kira ɗaya daga cikin direban gidan ya miƙa masa.

“Zaka kai Amira a wannan addireshin, karka yarda ka sauketa ko ina sai nan”

“Toh Ranka ya daɗe”

Ya nufi part ɗin Ummi. Su biyu ya samu a falon Amira ta yi kneel down tana riƙe da
hannun Ummi tana kuka, Ummi kuma na hawaye.

“Ki min hallaci Ummi kin riƙe ni kamar ƴar cikin ki, baki taɓa nuna min banbanci da
ƴaran ki ba, na yi fatar wata rana zata zo da zan saka miki abunda kika min, Na
gode da karamcin ina fatar zaki yafe min duk abunda na miki”

“Ba ki min komai ba Amira sai alheri, Allah ya miki albarka”

Kuka ta yi sosai sannan ta saki Ummi ta nufi ƙofar fita kamar zata faɗi. Kai Ummi
ta girgiza ta kalli Abdool ta ce

“Is not fair ya kamata ace mu muka kai ta gida”

Ya ɗago daga jikin ƙofar da yake jingine ya nufo Ummi

“No hakan zai fi mata, dole ta tanadi abunda zata faɗawa iyayenta, idan suka gan mu
kawo ta za suyi zaton ko ina son ta ne, kuma dole zasu tambayi inda na haɗu da ita,
ni ko kin san gaskiya zan faɗa musu, beside irin waɗannan mutane ba a yawo da su it
risk baki san abunda suka tana da ba”

Kai ta kaɗa masa cike da gamsuwar bayanin da yayi mata. Sannan ya juya suka fita
tare gurin mota suke je suka tsaya, ita kuma tana daga ciki sai faman kuka take.
Hannu Abdool yasa a aljihu ya ciro takardar kuɗi ya miƙa mata.

“Maybe you will need this”

“No i don't”

Ta kawar da fuskarta tare da cewa direba su tafi. Daga Ummi har Abdool tsaye suka
yi suna kallonta har aka buɗe musu gate ɗin farko, bayan sun fice aka rufe gate
ɗin sannan suka daina hango motar ta.

“Ina jin kamar ba mu kyauta mata ba, kuma bata jidaɗi ba ta ƙi ya tsaya har su
Fauza su dawo”

“Zamu iya mata alheri daga baya idan mun fahimci da gaske ta shiryu, ai ƙara haka
idan suna nan ai zasu ta kuka suma”

“Allah yasa ta shiryun, but wata rana zamu yi visiting na ta”

Ya miƙa hannunsa yana miƙa.

“Bari na shirya na koma gurin Mai Martaba”

“Okay”

Ummi ta juya. Shi kuma ya nufi part ɗinsa. Cikin rashin jundaɗi ya nufi part ɗinsa,
dan bana jin kamar be kyautawa Amira, but he has no choice but to let her go. Cikin
mintuna shirin ya watsa ruwa ya shirya cikin manyan kaya dan cox he know how Mai
Martaba hate ƙananan kaya, yana fitowa part ɗinsa sai ƙamshin turare ke tashi. In
five minutes ya isa kan wuri. He got lucky Mai Martaba be je ko'ina ba, duk da yana
da niyar fita yau, sai dai ya tararda fadar cike saboda baƙin da suka zo daga
jibiya. Yana shiga suka fara miƙa masa gaisuwa da kirari, hannu kawai ya ɗaga musu
ya juya ya fita.

Barori ya samu a babban falon Mai Martaba suna hidimar chanja carpet, da sauri suka
zubar da abunda ke hannunsa suka zube ƙasa suna masa gaisuwa. Kamar wanda be gansu
ba, haka yayi ya nufi ɗayan falon nasa, zama yayi saman kujera yana duba jaridu,
can kuma ya ji gurin is so boring ya miƙe ya nufi can ɓangaren Mai Martaba inda
babu wanda ya ke shiga sai iyalansa.

Saman wata kujera ya zauna mai lilo yana kallon pop ɗakin. Zuwa can ya fara jin
bachi, daman a gajiye yake. Shigowar Mai Martaba ne yasa shi saurin sauke ƙafafunsa
ya tashi zaune.

“Allah ya taimaki Mai Martaba ya ƙara maka lafiya”

Zaunawa yyi da murmushi a fuskarsa.


“Yarima Abdallah, kuma sarkin mu na gobe”

Yayi dariya.

“A dai bar ni a Yariman, har yanzu bana mafarkin zama Sarki”

“Aiko ƙara ja shirya, damin very soon zaka zama Sarki, kasan har yanzu ban faɗa
maka albishir ɗin ka ba ko?”

“Shiyasa ma ka ga na zo yanzu”

Mai Martab ya ɗora ƙafa saman ɗaya yana kallon Abdool cike da natsuwa.

“Wato Albishir ɗin ka guda biyu ne, kuma dukaninsu suna da muhimmanci, kuma ina
fatar zaka karɓa ka yi na'am da dukansu. Na farƙo dai ina maka albishir da cewar
Hajiya Shafa ta baka Zalihatu kyauta, abu na biyu kuma mun yanke shawarar naɗa ka
sabon Sarkin Katsina...”

Wani irin kallo yayi ma Mai Martaba kamar Ummi bata faɗa masa komai ba, sai ya
sauka ƙasa yana nuna kansa.

“Mai Martaba ni?”

“Kai fa”

Ya faɗa da murmushi a fuskarsa.

“Ka fi kowa karantar waye ni Mai Martaba, ka fi kowa sanin abunda ya dace da ni, ba
zaka taɓa zaɓa min sheri ba, kuma na san kafi kowa son farinciki da walwala. Sai
dai akwai abun dubawa a maganganun ka Mai Martaba, kamin ni kana da ƴaƴa biyu,
waɗanda ko baka raye su suka fi cancanta a ɗora a sarautar nan, bayan kuma Sarkin
gari, da Baba Macido ƙanenka ne da ke tunanin idan a yau baka raye, za a iya basu
sarautar Katsina, babu wanda zai jidaɗi a cikinsu, idan a ɗauki Sarautar nan aka
bani ko da baka raye ballantana kana da ranka kuma kai da hannunka zaka ɗauki
Sarautar nan ka ba ni, a iya sanin da na yi ma Sarautar nan, zaɓe ake idan za'ayi
sabon sarki, nasan mutane da yawa za su ce ka shigo da sabon tsari ka nuna son kai.
Na sani idan cancanta ake dubawa, na cancanta, amman ana barin Halak dan kunya, ni
Wallahi ina son aikina kuma ina ƙaunar na mutu ina yinsa”

Mai Martaba yaja wani dogon numfashi ya sauke yana gyara zama. Tabbas Abdool yayi
magana mai kyau da kama hankali, hakan kuma ba ƙaramin ƙara burge Mai Martaba ya yi
ba, a ƙara karantar irin basira da fikrah da ɗansa yake da ita.

“Haƙiƙa kafi kowa dacewa da Sarautar Katsina, ana son Sarki mai fikra da Nagarta,
kuma an fi son Sarki da baya son Sarautar kwata-kwata a ransa. Sai dai hakan be isa
yasa na cilasta maka ba, wata ƙila gaba zaka iya neman Sarautar da kan ka”

Hannayensa biyu yasa ya riƙe ƙafar Mai Martaba ɗaya da ke ƙasa.

“Na gode sosai da ka fahimce kuma ka min Uzuri, Allah ya ƙara mana lafiya da nisan
kwana. Abu na biyu kuma Mai Martaba na samu matar da na ke so...”

“Namra?”

Yayi ƙasa da kansa yana jin kunya.

“Zamu aura maka duk mace da kake so Babana, ba zamu maka cilas ba, abun da kawai
yake da muhimmanci kana son ta”
“Ina fatar hakan ba zai ɓata maka rai ba, kuma ina son na ji ra'ayinka akan auren
bazarawa”

“Baka san Annabi S.A.W ya auri Bazawara ba, Nana Khadija ta haifi ƴaƴa ma a wani
gidan sannan ta auri Annabi yana yaronsa, balle wannan da ɓata ma haihu ba, indai
yarinyar ƴar kirkici mun yarda ka aureta ɗari-ɗari”

Miƙewa yayi tsaye yayi wani tsalle ya dire kamar ƙaramin yaro

“I knew it, daman na faɗawa Ummi tace wai ba zaka yarda ba, har musu take min wai
she know you better than i”

Mai martaba yayi murmushi.

“No my son know me better than her”

Rumgume Mai Martaba Abdool yai cike da jin daɗi yana jin kamar ya haɗe shi.

NAMRA POV.

Daga gurin passport tace direba ya wuce da ita gidan su Lamido. Idonta tab da
hawaye ta shiga cikin gidan, muryarta kamar wacce zata fasa kuka ta yi sallama.
Lamido ne mutumen da ta fara ido huɗu da shi a gidan, kuma ya ƙi ya amsa mata
sallamarta balle kauda idonsa daga kallon tarayyar da idanuwansu suka yi.

“Kin zo ban kwanar ne? Ai dama baki dawo ba saboda zaki ƙara saka zuciyana cikin
ƙuna ne kawai”

“Don't you happy na shirya da iyayena”

“I won't lie Namra, yes i'm not happy because you are going to leave,kuma ba nine
silar wannan farinciki na ki ba bayan wannan shi ne mafarki na a kullum, ina kishin
mutumen da ya shirya ki da iyayenki sosai, kamar mutumen da cire min duka tufafi ya
bar ni tsirara, kin san ya tozarta ni ko? Ko ba komai idan kika tuna shi zaki yi
murmushi ni fa?”

Ta share hawayen da suka zubo mata.

“Namra bata zo gidanku dan ka so ta ba, saboda Namra ta gama so a rayuwarta, na yi


rilaya, ɗakin so kuma sai dai wata mai sunana ta shiga amman ba ni ba, ka daina
yaudarar kan ka dan Allah”

“Daman na tsammaci haka, saboda ni ba Yarima ba ne, kuma ba wan....”

Hannu ta ɗaga mishi ta tsaka mishi tsawar da tasa su Neina fito daga cikin ɗaki da
gudu.

“Shi haka yayi ya yaudare ni, wani namiji ba zai ƙara burgeni ba, put this in your
mind i will never ever ever ever love someone again”

Murmushi yayi yasa kai ya fice. Neina ta nufo tana tambayar abunda ya faru.

“Babu komai kawai na zo na yi muku bankwana ne anjima kaɗan zamu wuce”

“Ƙaraso ki zauna mana”


“Ba sai na ƙaraso ba, direba yana jirana a waje”

Sai kawai ta rumgume Neina ta fashe da kuka.

“Zan dawo Neina, rabuwa ba mutuwa ba ce kun min halaccin da ba zan iya mantawa ba”

Nan Neina da Uwani suka saka kuka, dan Maryam bata nan a lokacin. Kamar ba zasu
rabu ba haka suka riƙa riƙe juna suna kuka kamar an yi mutuwa, har maƙota suka leƙo
suna kallon ikon Allah.

Namra na komawa aka aiko musu da abincin rana, lokaci na yi direba ya zo ɗaukarsu
zuwa airport, kamar su ake jira suna isa jirgi ya kama hanyar sokoto. Suna sauka
Abbah yayi ma direbansa waya ya zo ya ɗauke su, kuka sosai Namra ta riƙa yi cikin
motar ta daman tun a jirgi ta fara abunta, sam bata ji daɗin kalaman da ta faɗawa
Lamido ba, sai dai bata da wani zaɓi sai wannan, ga kuma kukan rabuwa da Neina, da
kuma kuka dawowa sokoto birnin shehu birni mai albakar da karamci tare da iyayenta
komai ya zame mata kamar sabo, bama kamar ta motarsa ta nutsa kai cikin gidan duk
an fence shi an sabunta komai saboda bikin Maryam da za'ayi.

Suna jin mota duk suka fito waje har Hajiya Barau da Zinatu da zo jiya suna jiran
Abbah da Anty su fito. Abbah ne ya fara fita daga cikin motar sannan Namra ta fito
fuskarta da hawaye. Wani irin ihu Maryam ta saka taje a guje ta rumgume Namra suka
fashe da kuka, sannan Hindatu da Aisha suka je suka rumgume ta, suma suka saka
kuka, Hajiya Barau ce Mamaki ya hanata komai har Abbah da wuce da Anty Amarya
sannan ta nufi Namra kunya kunya.

“Wai Namra ce nake gani nan ni mamaki ma ya hanani komai”

“Itace Hajiya, Abbah yaje ya taho da abar sa”

Cewar Maryam tana sharewa Namra hawaye. Sannan suka riƙa hannunta suka nufi cikin
gida da ita.

YASMIN POV.

Lokacin da ta bar gidan mijita sai ta nufo gida, sai dai bata yarda ta nunawa
mahaifiyarta damuwarta ba, gudun kar ta hana ta aikata abunda take da niyar yi,
wuni ta yi a gidan suka sha fira kamar ba komai sai dare ta fito suka koma gida ita
da yaranta da kuma mai aikinta. Bata tarar da Uzair cikin gidan ba hakan yasa ta
ɗan ji sanyi dan bata ƙaunar ganinsa a yanzu. Abunda kawai take da buƙata ya za'ayi
ta haɗu da Namta akwai buƙatar ta tattauna da ita kamin ta fallasa Uzair, ma'ana ta
jawa Namra haƙƙinta ko zata samu sanyin zuciya akan abunda ya aikatawa ɗan sa. Haka
ta kwana tana tunanin mafita washe gari ma kasa zuwa aiki ta yi duk da tana da
cases a kotu, da an kira ta sai tace bata da lafiya ne. Uzair kuma be kwana a gidan
ba, da alama akwai gun da ya kwana, sai dai hakan be dame ta ba ko kaɗan tun da
tasan wanene shi a yanzu. Bayan ta gama waya da wani Barrister, sai ga kiran
Mahaifiyarta ya shigo wayarta.
Bayan sun gaisa take labarta mata ance Namra ta dawo, kuma wai Abbah ne yaje ya
taho ta ita, Yasmin ta nuna murnarta sosai daman abun nema ya samu. Dan haka tana
kashe wayar ta aje little Namra ta shiga wanka, tana fitowa ta yi ma mata sannan
suka shirya daman Adnan yana makaranta. Ƴar aikinta kawai ta bari a gidan ta nufi
gidansu Namra.

Tana fita Uzair na shigowa, ciki wani irin yanayi ya buga ƙofar falon, sai mai
aikinsa ta buɗe masa ƙofa.

“Sannu da zuwa”
Wani wawan kallo ya jefa mata, ya wuce ciki, ita kuma ta koma kitchen ta cigaba da
abun da take.

TEEMA POV.

Yau da wuri ta gama girkinta saboda yau da fara amfani da abubuwan da ta karɓo
gurin bokanta. Zoɓo ta haɗa masa ta zuba abun a ciki sannan ta saka wani a miyar
giɗa, kana ta bi gidan ta turare ko'ina.

Sai da ta gama sannan ta shiga ta sake wanka, ta chaɓa ado, ta buɗe durowarta ta
ɗauko wani rubutu ta zuba a hannunta ta yaye zanen gadonta ta watsa shi, sannan ta
shafa wani a ɗayan hannunta, tana jiran ya dawo ta samu sa'ar shafa masa a jiki.

Tana jin tsayawar motarsa ta koma bayan ƙofa ta laɓe, a zatonta shine zai shigo
ashe direba ya aiko ya kawo su Ezza da Ulfa. Sai duk suka watsar da jakunkunansu
saman kujerarta. Ganin shiru-shiru ba a shigo ba yasa ta fito ta nufo falo.

“Kan Uban nan, uban wa zaku jefarwa da jaka nan? Ku kwashe su da sauri ku kai su
ɗakin ku, kuma kar a sake zama min saman kujera, wannan ai rashin tarbiya ne manya
su zauna a kujera ku ku zauna ni ba zan ɗauki wannan ba”

Ulfa ce uwar tsoro da sauri ta nufi jakarta ta ɗauka ta nufi ɗakinsu. Ezzah kan
banza ta yi kuma ta ƙi sauka daga saman kujerar.

“Ke dan Ubanki ba da nake ba”

Sai a sannan ta ɗago kai ta kalleta.

“Mu a saman kujera muka saba zama”

Ta faɗa tana sauka ƙasa, badan hannun Teema da ke da rubutun ba da babu abunda zai
hana ta dake ta.

“Wallahi kuka kuskura min rashin kunya zaki wahala a gidan nan”

Sai kawai ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinsu, Ulfah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin tana
leƙo ta shige da sauri.

[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *78*

Kusa da Ummi ya sake zama yana kallon tv.

“Tana son ta saka kanta cikin matsala ne kawai Ummi amman tasan ba zan taɓa son ta
ba”

“Nasan tana son ka har zuciyarta, amman sam ban yarda da yarinyar nan ba, mutanen
da sukayi ƙoƙarin su kashe ka, waya sani ko plan ne aka yi ta yadda idan ta aure ka
zata fin jindaɗin kashe ka”

Yayi murmushin gefen baki.

“Ko babu plan Ummi bana son ta, ko da kuwa tun can farko ita mai tarbiya ce,
because if i love someone i mean it no matter what she did or whoever she is, and
if i said i do i do, so i don't love Amira, i only fell in love once because i have
never been in that kind of situation, but when it comes to Namra i take it so
serious, and i love with all my heart and blood and mind and soul i love her more
than you think Ummi”

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke, ta kalli ɗanta fuskarta da alamun damuwa.

“Tell me more about her”

Miƙewa ya yi tsaye ya nufi freezer.

“She's so simple and kind, but difficult to handle. You know when we first meet,
she slap me and insult me in front of my boys, but i can't slap her back”

Ya ƙarasa yana bulbula ruwan da ya fiddo a cup. Ummi ta yi murmushi.

“I know how my son is ba ya faɗa da mata”

“Yap bana faɗa da mata because we are not in the same level, strength, brain,
heart, soul and lot. Ban taɓa jin ina son wata mace ba, but lokacin da na ji ina
son Namra, nasan our souls mean to be, duk da a lokacin na san tana da aure, amman
zuciya ta kasa haƙura, and now what! Her husband divorce her ta je wani gida ta
zauna, kuma ƙaddara ta sake haɗa mu kaduna na kaɗe yaron gidan ina zuwa sai gata a
gidan, hmm' mmm funny, and now ni ne silar shiryawa da iyayenta, i hope you love
her too?”

“Of course i love her ai dole naso matar da ɗa na yake so, but i'm just worried
about Mai Martba, ba lalle ne shi ya so ta”

“Why”

“Saboda Bazawara ce! And i hear that Mai Martaba and Hajiya Shafa sun maka mata”

“What...!”

Ya aje cup ɗin ruwa dake hannunsa saman dinning yana kallonta fuskarsa cike da
tashin hankali.

“How true it's?”

“Mai Martaba ya kira ni da kan shi, yana neman shawara akan zai ɗoraka a Sarautar
Katsina, da na nuna masa be dace ba sai ya nuna ɓacin ransa, the following day ya
sake kira a waya ya faɗa min Hajiya Shafa tace be kamata a ɗoraka a Saurata baka
tare da iyalaiba, dan haka ta maka mata, zata aura maka Zaliha ƙanwarta, idan anyi
auren da watanni sai a baka Sarautar, kuma Mai Martaba yayi na'am da hakan”

“Miyasa baki faɗa musu ina da wacce nake so ba?”

“Idan na faɗa zai ga kamar ina kare ka ne, amman ina son ka min wani abu Abdallah,
duk yadda Mai Martaba zai yi karka yarda ka karɓi Sarautar nan, kai ne ɗa na uku a
gurin shi, be kamata ya tsallake su ba, ya ɗauki Sarauta ya baka, nasan yana son
ka, amman hakan ba zai jawo maka komai ba sai ƙiyayya da ganin laifi, kai kuma ka
yi ƙanƙanta da irin rayuwar nan, kuma idan har ka yarda ka auri Zaliha, to ka jefa
rayuwarka da ta mu cikin matsala, tun da ƙanwar Hajiya Shafa ce, kuma kasan wacece
Hajiya Shafa a gareni da gare ka. Ka da ka amince da duka biyu idan har ya yi maka
magana”

“Ai ba zan amince ba, ina son aiki na kuma ina alfahari da shi, ni ba Sarauta ba ce
a gabana, kuma Namra ce kaɗai matar da nake so”

“And be careful with her love too, kar ya rufe maka ido ka saɓawa Mahaifin ka”
“My Dad is...”

Ummi ta miƙe tsaye tana tarar numfashinsa.

“I know who your Dad is, he's my ex-husband the Father of my own male son”

Ta nufi bedroom ɗinta. Shi kuma ya faɗa zaune saman kujerar dinning yana bugashi da
ƙarfi.

“Damn it! miyasa abubuwa zasu zo min haka kuma yanzu? Shine surprise ɗin da Mai
Martaba yake ta faɗi? Ya Salam...!”

Ya miƙe tsaye, sai ya nufi kitchen duk da ya san babu abunda zai ɗauka a gurin. He
need some fresh air, sai ya buɗe ƙofar baya ya fita, jin ya gaba ɗaya gidan ya masa
wani irin, kai tsaye ya nufi Garden, ko ba komai yana son kukan tsuntsaye maybe zai
sashi relaxing ya sama ma kan shi mafita.

Gaban icen guava ya zo ya tsaya yana kallon pool, motsin mutum ya ji a bayansa,
yasan cikin biyu ba za'a rasa ɗaya ba, Maybe Amira ce tun da ita kaɗai take gidan
ko kuma barewa, dan tana masa haka a duk lokacin da ya shigo Garden ɗin. Juyowa
yayi sai yayi ido huɗu da Amira fuskarta shakaf da hawaye.

“What do you want?”

“You told me if i need someone to talk to”

“It Abdool who told you that, and now i'm someone else, and my words could hurt
you, i'm not in the mood”

Cikin muryar kuka ta ce.

“You already hurt me because i learn the truth, i know you upset because of what
Ummi told you, we share the same pain, i'm in love with you while you're in love
with someone else”

Ta share hawayenta da haɓar rigarta.

“Maybe i will have peace of mind if you tell me that you never love me, maybe i
will back to my senses, think about my future and....”

Kuka ya ci ƙarfinta. Taku biyu yayi ya matso kusa da ita.

“Do you know what is best for you, ki koma gida cikin iyayenki, ki manta da ni a
rayuwarki, and i promise you zan rufa miki asiri ba zan faɗawa kowa abunda kika
aikata ba”

“Zan koma gurin iyayena, nima a yanzu babu abunda na ke so sai su, but forgetting
you is the hardest thing ever, thank you so for letting me staying with your family
and know you better, can you take me home now please, am eager to see my parents”

“Yeah... Zan ma direba magana, ki shirya kayan ki”

“Ban zo da komai ba a nan”

Har ta juya sai kuma ta juyo.

“Ina matar da kake so take?”


“Why?”

“Saboda ta fi kowa sa'ah a duniya, ina son na ganta ne kawai”

“I can't tell you Amira, i'm sorry to say this, i don't trust you”

“I know i shouldn't...”

Ta juya ta shiga ciki da kuka. Da kallo ya bita sai da ta fice sannan ya haka
hannunsa aljihu ya ciro handkerchief yana shinshinawa.

“I loved you so much”

Ya ɗauki tsawo lokaci a gurin sannan ya nufi part ɗinsa. Be daɗe ba ya fito da
takarda hannunsa ya kira ɗaya daga cikin direban gidan ya miƙa masa.

“Zaka kai Amira a wannan addireshin, karka yarda ka sauketa ko ina sai nan”

“Toh Ranka ya daɗe”

Ya nufi part ɗin Ummi. Su biyu ya samu a falon Amira ta yi kneel down tana riƙe da
hannun Ummi tana kuka, Ummi kuma na hawaye.

“Ki min hallaci Ummi kin riƙe ni kamar ƴar cikin ki, baki taɓa nuna min banbanci da
ƴaran ki ba, na yi fatar wata rana zata zo da zan saka miki abunda kika min, Na
gode da karamcin ina fatar zaki yafe min duk abunda na miki”

“Ba ki min komai ba Amira sai alheri, Allah ya miki albarka”

Kuka ta yi sosai sannan ta saki Ummi ta nufi ƙofar fita kamar zata faɗi. Kai Ummi
ta girgiza ta kalli Abdool ta ce

“Is not fair ya kamata ace mu muka kai ta gida”

Ya ɗago daga jikin ƙofar da yake jingine ya nufo Ummi

“No hakan zai fi mata, dole ta tanadi abunda zata faɗawa iyayenta, idan suka gan mu
kawo ta za suyi zaton ko ina son ta ne, kuma dole zasu tambayi inda na haɗu da ita,
ni ko kin san gaskiya zan faɗa musu, beside irin waɗannan mutane ba a yawo da su it
risk baki san abunda suka tana da ba”

Kai ta kaɗa masa cike da gamsuwar bayanin da yayi mata. Sannan ya juya suka fita
tare gurin mota suke je suka tsaya, ita kuma tana daga ciki sai faman kuka take.
Hannu Abdool yasa a aljihu ya ciro takardar kuɗi ya miƙa mata.

“Maybe you will need this”

“No i don't”

Ta kawar da fuskarta tare da cewa direba su tafi. Daga Ummi har Abdool tsaye suka
yi suna kallonta har aka buɗe musu gate ɗin farko, bayan sun fice aka rufe gate
ɗin sannan suka daina hango motar ta.

“Ina jin kamar ba mu kyauta mata ba, kuma bata jidaɗi ba ta ƙi ya tsaya har su
Fauza su dawo”

“Zamu iya mata alheri daga baya idan mun fahimci da gaske ta shiryu, ai ƙara haka
idan suna nan ai zasu ta kuka suma”
“Allah yasa ta shiryun, but wata rana zamu yi visiting na ta”

Ya miƙa hannunsa yana miƙa.

“Bari na shirya na koma gurin Mai Martaba”

“Okay”

Ummi ta juya. Shi kuma ya nufi part ɗinsa. Cikin rashin jundaɗi ya nufi part ɗinsa,
dan bana jin kamar be kyautawa Amira, but he has no choice but to let her go. Cikin
mintuna shirin ya watsa ruwa ya shirya cikin manyan kaya dan cox he know how Mai
Martaba hate ƙananan kaya, yana fitowa part ɗinsa sai ƙamshin turare ke tashi. In
five minutes ya isa kan wuri. He got lucky Mai Martaba be je ko'ina ba, duk da yana
da niyar fita yau, sai dai ya tararda fadar cike saboda baƙin da suka zo daga
jibiya. Yana shiga suka fara miƙa masa gaisuwa da kirari, hannu kawai ya ɗaga musu
ya juya ya fita.

Barori ya samu a babban falon Mai Martaba suna hidimar chanja carpet, da sauri suka
zubar da abunda ke hannunsa suka zube ƙasa suna masa gaisuwa. Kamar wanda be gansu
ba, haka yayi ya nufi ɗayan falon nasa, zama yayi saman kujera yana duba jaridu,
can kuma ya ji gurin is so boring ya miƙe ya nufi can ɓangaren Mai Martaba inda
babu wanda ya ke shiga sai iyalansa.

Saman wata kujera ya zauna mai lilo yana kallon pop ɗakin. Zuwa can ya fara jin
bachi, daman a gajiye yake. Shigowar Mai Martaba ne yasa shi saurin sauke ƙafafunsa
ya tashi zaune.

“Allah ya taimaki Mai Martaba ya ƙara maka lafiya”

Zaunawa yyi da murmushi a fuskarsa.

“Yarima Abdallah, kuma sarkin mu na gobe”

Yayi dariya.

“A dai bar ni a Yariman, har yanzu bana mafarkin zama Sarki”

“Aiko ƙara ja shirya, damin very soon zaka zama Sarki, kasan har yanzu ban faɗa
maka albishir ɗin ka ba ko?”

“Shiyasa ma ka ga na zo yanzu”

Mai Martab ya ɗora ƙafa saman ɗaya yana kallon Abdool cike da natsuwa.

“Wato Albishir ɗin ka guda biyu ne, kuma dukaninsu suna da muhimmanci, kuma ina
fatar zaka karɓa ka yi na'am da dukansu. Na farƙo dai ina maka albishir da cewar
Hajiya Shafa ta baka Zalihatu kyauta, abu na biyu kuma mun yanke shawarar naɗa ka
sabon Sarkin Katsina...”

Wani irin kallo yayi ma Mai Martaba kamar Ummi bata faɗa masa komai ba, sai ya
sauka ƙasa yana nuna kansa.

“Mai Martaba ni?”

“Kai fa”

Ya faɗa da murmushi a fuskarsa.

“Ka fi kowa karantar waye ni Mai Martaba, ka fi kowa sanin abunda ya dace da ni, ba
zaka taɓa zaɓa min sheri ba, kuma na san kafi kowa son farinciki da walwala. Sai
dai akwai abun dubawa a maganganun ka Mai Martaba, kamin ni kana da ƴaƴa biyu,
waɗanda ko baka raye su suka fi cancanta a ɗora a sarautar nan, bayan kuma Sarkin
gari, da Baba Macido ƙanenka ne da ke tunanin idan a yau baka raye, za a iya basu
sarautar Katsina, babu wanda zai jidaɗi a cikinsu, idan a ɗauki Sarautar nan aka
bani ko da baka raye ballantana kana da ranka kuma kai da hannunka zaka ɗauki
Sarautar nan ka ba ni, a iya sanin da na yi ma Sarautar nan, zaɓe ake idan za'ayi
sabon sarki, nasan mutane da yawa za su ce ka shigo da sabon tsari ka nuna son kai.
Na sani idan cancanta ake dubawa, na cancanta, amman ana barin Halak dan kunya, ni
Wallahi ina son aikina kuma ina ƙaunar na mutu ina yinsa”

Mai Martaba yaja wani dogon numfashi ya sauke yana gyara zama. Tabbas Abdool yayi
magana mai kyau da kama hankali, hakan kuma ba ƙaramin ƙara burge Mai Martaba ya yi
ba, a ƙara karantar irin basira da fikrah da ɗansa yake da ita.

“Haƙiƙa kafi kowa dacewa da Sarautar Katsina, ana son Sarki mai fikra da Nagarta,
kuma an fi son Sarki da baya son Sarautar kwata-kwata a ransa. Sai dai hakan be isa
yasa na cilasta maka ba, wata ƙila gaba zaka iya neman Sarautar da kan ka”

Hannayensa biyu yasa ya riƙe ƙafar Mai Martaba ɗaya da ke ƙasa.

“Na gode sosai da ka fahimce kuma ka min Uzuri, Allah ya ƙara mana lafiya da nisan
kwana. Abu na biyu kuma Mai Martaba na samu matar da na ke so...”

“Namra?”

Yayi ƙasa da kansa yana jin kunya.

“Zamu aura maka duk mace da kake so Babana, ba zamu maka cilas ba, abun da kawai
yake da muhimmanci kana son ta”

“Ina fatar hakan ba zai ɓata maka rai ba, kuma ina son na ji ra'ayinka akan auren
bazarawa”

“Baka san Annabi S.A.W ya auri Bazawara ba, Nana Khadija ta haifi ƴaƴa ma a wani
gidan sannan ta auri Annabi yana yaronsa, balle wannan da ɓata ma haihu ba, indai
yarinyar ƴar kirkici mun yarda ka aureta ɗari-ɗari”

Miƙewa yayi tsaye yayi wani tsalle ya dire kamar ƙaramin yaro

“I knew it, daman na faɗawa Ummi tace wai ba zaka yarda ba, har musu take min wai
she know you better than i”

Mai martaba yayi murmushi.

“No my son know me better than her”

Rumgume Mai Martaba Abdool yai cike da jin daɗi yana jin kamar ya haɗe shi.

NAMRA POV.

Daga gurin passport tace direba ya wuce da ita gidan su Lamido. Idonta tab da
hawaye ta shiga cikin gidan, muryarta kamar wacce zata fasa kuka ta yi sallama.
Lamido ne mutumen da ta fara ido huɗu da shi a gidan, kuma ya ƙi ya amsa mata
sallamarta balle kauda idonsa daga kallon tarayyar da idanuwansu suka yi.

“Kin zo ban kwanar ne? Ai dama baki dawo ba saboda zaki ƙara saka zuciyana cikin
ƙuna ne kawai”

“Don't you happy na shirya da iyayena”

“I won't lie Namra, yes i'm not happy because you are going to leave,kuma ba nine
silar wannan farinciki na ki ba bayan wannan shi ne mafarki na a kullum, ina kishin
mutumen da ya shirya ki da iyayenki sosai, kamar mutumen da cire min duka tufafi ya
bar ni tsirara, kin san ya tozarta ni ko? Ko ba komai idan kika tuna shi zaki yi
murmushi ni fa?”

Ta share hawayen da suka zubo mata.

“Namra bata zo gidanku dan ka so ta ba, saboda Namra ta gama so a rayuwarta, na yi


rilaya, ɗakin so kuma sai dai wata mai sunana ta shiga amman ba ni ba, ka daina
yaudarar kan ka dan Allah”

“Daman na tsammaci haka, saboda ni ba Yarima ba ne, kuma ba wan....”

Hannu ta ɗaga mishi ta tsaka mishi tsawar da tasa su Neina fito daga cikin ɗaki da
gudu.

“Shi haka yayi ya yaudare ni, wani namiji ba zai ƙara burgeni ba, put this in your
mind i will never ever ever ever love someone again”

Murmushi yayi yasa kai ya fice. Neina ta nufo tana tambayar abunda ya faru.

“Babu komai kawai na zo na yi muku bankwana ne anjima kaɗan zamu wuce”

“Ƙaraso ki zauna mana”

“Ba sai na ƙaraso ba, direba yana jirana a waje”

Sai kawai ta rumgume Neina ta fashe da kuka.

“Zan dawo Neina, rabuwa ba mutuwa ba ce kun min halaccin da ba zan iya mantawa ba”

Nan Neina da Uwani suka saka kuka, dan Maryam bata nan a lokacin. Kamar ba zasu
rabu ba haka suka riƙa riƙe juna suna kuka kamar an yi mutuwa, har maƙota suka leƙo
suna kallon ikon Allah.

Namra na komawa aka aiko musu da abincin rana, lokaci na yi direba ya zo ɗaukarsu
zuwa airport, kamar su ake jira suna isa jirgi ya kama hanyar sokoto. Suna sauka
Abbah yayi ma direbansa waya ya zo ya ɗauke su, kuka sosai Namra ta riƙa yi cikin
motar ta daman tun a jirgi ta fara abunta, sam bata ji daɗin kalaman da ta faɗawa
Lamido ba, sai dai bata da wani zaɓi sai wannan, ga kuma kukan rabuwa da Neina, da
kuma kuka dawowa sokoto birnin shehu birni mai albakar da karamci tare da iyayenta
komai ya zame mata kamar sabo, bama kamar ta motarsa ta nutsa kai cikin gidan duk
an fence shi an sabunta komai saboda bikin Maryam da za'ayi.

Suna jin mota duk suka fito waje har Hajiya Barau da Zinatu da zo jiya suna jiran
Abbah da Anty su fito. Abbah ne ya fara fita daga cikin motar sannan Namra ta fito
fuskarta da hawaye. Wani irin ihu Maryam ta saka taje a guje ta rumgume Namra suka
fashe da kuka, sannan Hindatu da Aisha suka je suka rumgume ta, suma suka saka
kuka, Hajiya Barau ce Mamaki ya hanata komai har Abbah da wuce da Anty Amarya
sannan ta nufi Namra kunya kunya.

“Wai Namra ce nake gani nan ni mamaki ma ya hanani komai”

“Itace Hajiya, Abbah yaje ya taho da abar sa”


Cewar Maryam tana sharewa Namra hawaye. Sannan suka riƙa hannunta suka nufi cikin
gida da ita.

YASMIN POV.

Lokacin da ta bar gidan mijita sai ta nufo gida, sai dai bata yarda ta nunawa
mahaifiyarta damuwarta ba, gudun kar ta hana ta aikata abunda take da niyar yi,
wuni ta yi a gidan suka sha fira kamar ba komai sai dare ta fito suka koma gida ita
da yaranta da kuma mai aikinta. Bata tarar da Uzair cikin gidan ba hakan yasa ta
ɗan ji sanyi dan bata ƙaunar ganinsa a yanzu. Abunda kawai take da buƙata ya za'ayi
ta haɗu da Namta akwai buƙatar ta tattauna da ita kamin ta fallasa Uzair, ma'ana ta
jawa Namra haƙƙinta ko zata samu sanyin zuciya akan abunda ya aikatawa ɗan sa. Haka
ta kwana tana tunanin mafita washe gari ma kasa zuwa aiki ta yi duk da tana da
cases a kotu, da an kira ta sai tace bata da lafiya ne. Uzair kuma be kwana a gidan
ba, da alama akwai gun da ya kwana, sai dai hakan be dame ta ba ko kaɗan tun da
tasan wanene shi a yanzu. Bayan ta gama waya da wani Barrister, sai ga kiran
Mahaifiyarta ya shigo wayarta.
Bayan sun gaisa take labarta mata ance Namra ta dawo, kuma wai Abbah ne yaje ya
taho ta ita, Yasmin ta nuna murnarta sosai daman abun nema ya samu. Dan haka tana
kashe wayar ta aje little Namra ta shiga wanka, tana fitowa ta yi ma mata sannan
suka shirya daman Adnan yana makaranta. Ƴar aikinta kawai ta bari a gidan ta nufi
gidansu Namra.

Tana fita Uzair na shigowa, ciki wani irin yanayi ya buga ƙofar falon, sai mai
aikinsa ta buɗe masa ƙofa.

“Sannu da zuwa”

Wani wawan kallo ya jefa mata, ya wuce ciki, ita kuma ta koma kitchen ta cigaba da
abun da take.

TEEMA POV.

Yau da wuri ta gama girkinta saboda yau da fara amfani da abubuwan da ta karɓo
gurin bokanta. Zoɓo ta haɗa masa ta zuba abun a ciki sannan ta saka wani a miyar
giɗa, kana ta bi gidan ta turare ko'ina.

Sai da ta gama sannan ta shiga ta sake wanka, ta chaɓa ado, ta buɗe durowarta ta
ɗauko wani rubutu ta zuba a hannunta ta yaye zanen gadonta ta watsa shi, sannan ta
shafa wani a ɗayan hannunta, tana jiran ya dawo ta samu sa'ar shafa masa a jiki.

Tana jin tsayawar motarsa ta koma bayan ƙofa ta laɓe, a zatonta shine zai shigo
ashe direba ya aiko ya kawo su Ezza da Ulfa. Sai duk suka watsar da jakunkunansu
saman kujerarta. Ganin shiru-shiru ba a shigo ba yasa ta fito ta nufo falo.

“Kan Uban nan, uban wa zaku jefarwa da jaka nan? Ku kwashe su da sauri ku kai su
ɗakin ku, kuma kar a sake zama min saman kujera, wannan ai rashin tarbiya ne manya
su zauna a kujera ku ku zauna ni ba zan ɗauki wannan ba”

Ulfa ce uwar tsoro da sauri ta nufi jakarta ta ɗauka ta nufi ɗakinsu. Ezzah kan
banza ta yi kuma ta ƙi sauka daga saman kujerar.

“Ke dan Ubanki ba da nake ba”


Sai a sannan ta ɗago kai ta kalleta.

“Mu a saman kujera muka saba zama”

Ta faɗa tana sauka ƙasa, badan hannun Teema da ke da rubutun ba da babu abunda zai
hana ta dake ta.

“Wallahi kuka kuskura min rashin kunya zaki wahala a gidan nan”

Sai kawai ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinsu, Ulfah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin tana
leƙo ta shige da sauri.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *79*

Su Maryam na wucewa Zinatu ta rufa musu baya ita ma tana murmushi. Hajiya Barau
kuma ta koma part ɗinta, bedroom ɗinta ta shige ta ɗauki wayarta ta kira Uzair.
Bugu biyu ya ɗauka, saman-sama ya gaisa da ita saboda shi ma be cikin daɗin rai,
sannan ta labarta masa Namra ta dawo, he was shocked and surprise, sai ya ji
maganar kamar daga sama.

“Da gaske kike yi?”

“Wallahi da ido na na gani, yanzun nan Alhaji ya dawo tare da ita, kasan na labarta
maka ai Sarkin Katsina ya aiko ƴana nemansa ni na ɗauka ko wani abu ta yi, sai
gashi kuma na ga sun dawo da ita”

“Aurenta ya mutu ne?”

“Bari naje gurin Alhaji na ji”

“Okay ki sanar da ni duk abunda kika ji”

“Tau”

Tana kashe wayar ta nufi part ɗin Abbah. Ko da ta shiga yana banɗaki, har ta zauna
sai kuma ta yi saurin tashi ta koma part ɗinta, fruit ta yankawa Abbah ta saka
madara, ta ɗauka ta nufi koma part ɗinsa. Wannan karon zaune ya same shi saman gado
yana waya, sai ta zauna kusa da shi tana riƙe da fruits, sai da ya gama wayar
sannan ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace.

“Hajiya fatar dai lafiya”

“Lafiya ƙalau bana da ikon da zan zo na ga miji na ne? Ga ɗan abunda na haɗa maka,
abinci na kan wuta ban ƙarasa ba”

“Ai bama na ma jin yunwa kamin na taso sai da muka ci abinci”

“A can gidan Namra?”

“A'a a gidan Mai Martaba Ahmad Mai-doki Sarkin Katsina, dake Kaduna”

“Ban gane ba, baka labarta min zaka dawo da Namra ba, duk lokacin da na tambaye ka
sai ka ce min wani babu wata matsala dai, ya akayi ka dawo da ita bayan kace ba
zaka karɓe ta ba?”

Wani kallo Abbah yayi mata.

“Ya kike magana kamar wacece bata ji daɗin dawowar Namra ba? Komai ta yi min
aduniyar nan she still my daughter, ko lalacewa ta yi dole za'ace ƴar gidan nan ce,
ballantana ina son ta, kawai dai ta ɓata min rai ne kuma ta gane kuskurenta”
“Ta gane kuskurenta kamar ya? Alhaji yanzu baka tunanin mutane zasu zarge ka akan
ka yi magana kuma ka zauna? Wannan ai talalace ka yi mata yarinya ta yi laifi kuma
yanzu da miji ya wulaƙanta sai kace kayafe mata haka ake yi?”

Abbah yayi murmushi, yana gyara zamansa.

“Baki gane abun ba ne Hajiya wato da muka sauka Katsina...”

Ya kwashe labarin abunda ya faru ya faɗa mata, daman can Anty Amarya ce ta hana a
faɗawa kowa wai tana son kawai su ganta ne. Mire baki Hajiya Barau ta yi ta miƙe
tsaye.

“Yanzu Alhaji im ban da su mai da wani iri sai da Asim ya gama wulaƙanta ta ya sake
ta sannan yanzu su haɗa baki da uwarta su nemo wani a kai ga Sarki, wannan ma ai
rainin wayo ne, yarinyar ta yi wasa da hankalinka, yanzu kuma kai har ka yarda ta
gane kuskurenta haba Alhaji wannan ai ka bata damar ƙara aikata abunda ta aikata ne
kawai”

Wani wawan kallo Abbah ya watsa mata.

“Na bata damar, ko yanzu Namra ta kawo min wanda take so zan aura mata, daman na
lura da ke ba son yarinyar nan kike ba, mi ko duk wanda be son Namra bana son shi,
dan Namra jinina ce, ƴata ce, ina kula da yadda kika ɗauki matar nan ita ba haka ta
ɗauke ki ba, baki son ta ita da yaran ta, ana gobe za mu bar garin nan nan cikin
falon nan nawa kika saki wata magana wai Allah yasa Namra bata yi mana jaye-jaye
ba, a gaban uwarta amman ta miki kawaici ta tashi ta bar miki falon bata ce komai
ba, shiyasa na zaɓi zuwa da ita na ƙi na tafi da ke, iya haƙuri matar nan ta nayi
yinsa da ke amman ke baki ga, ina kula da abun nan da Namra ta yi kamar daɗi yayi
miki, ba zan ɗauka ba kar bakin ki ya sake furta mummun kalma akan ƴaƴana!”

Ta riƙe baki.

“Alhaji kai kake faɗa min wannan maganar akan Namra? Daga na faɗa maka gaskiya har
kace wai bana son ta ita da uwarta? Kuma ka ce baka da so na saboda ƴarka? Anya
banza matar nan ta barka Alhaji”

“Ba banza ta bar ni ba, ta kula da ni fiye da yadda kike tsammani, dan tana son ki
ke da ƴaƴanki, ba kamar yadda kike nuna mata ba, kuma daga yau sai yau, kar wani
munafurci da wata magana marar daɗi ta sake fitowa bakinki akan Ƴaƴa ko wannan
matar tau a bakin auren ki! Kar wacce ta aake tadarmin fitina yadda na ga dama haka
zan yi a gidana”

Mutuwar tsaye Hajiya Barau ta yi a gurin, tana mamakin Abbah ta ya juye kamar ba
shi ba, wai yau shi yake faɗa mata wannan maganar, har yake cewa bakin aurenta.
Uffan bata yarda ta sake cewa ba, ta nufi ƙofa cike da nauyin jiki fice sun-sun-
sun, hannayenta a baya tana jin kamar an ɗora mata dutse saman kai.

NAMRA POV.

Cikin falo suka riƙa hugging ɗin juna ita da ƴan'uwanta, suna jin kamar su haɗe
juna ita da su, sai faman kuka suke. Anty Amarya ta fito daga bedroom ɗinta
fuskarta da dariya ta ce

“To ko haɗe ta zaku yi?”

“Anty Faɗa mana yadda aka yi ta yarda ta biyo ku kuma har Abbah ya amince”

Aisha ta faɗa tana laƙƙame da wuyan Namra.


“To ku sake ta taje ta yi wanka ta shirya zan baku labarin komai”

Aisha da Hindatu ne suka saketa yayinda Maryam ta laƙƙame hannunta suka nufi
bedroom tare. Bayan sun tashi Zinatu ma ta tashi ta nufi part ɗin Mahaifiyarta. A
sannan ne Anty take tambayarsu yaushe Zinatu ta zo.

“Tun ranar da kuka tafi, wai faɗa tayi da mijinta ya ce taje gida, shi ne wai ta
baro masa yaransa”

“Subhallahi, miya haɗa su haka?”

“Wallahi bata faɗa ba, ai kin san Hajiya ba zata bari ta faɗi gaskiya ba, dan ita
Hajiya ma ce mana ta yi bikin Maryam ta zo”

“Tau Allah ya sauwaƙe yayi mata mafita, ku tashi ku girka mana abinci dan ni dai ba
zan ci taliya ba”

Hindatu ta mike tsaye tana dariya.

“Komai kuke so za a muku, sai ku ba mu labarin abunda ya faru”

A ɗaki da suka shiga Namra take labartawa Maryam irin abunda Asim yayi mata, da
yadda ta yi rayuwa gidansu Lamido da kuma haɗuwarta da Abdool ya yadda ya haɗa ta
da su Anty.

“Ke ni wallahi na jidaɗin da auren ya mutu kuma cikin ya zube, dan zai iya cewa ya
maida ki ko dan ɗansa ko kuma ya ce zai maida ki kamin ki cika idda amman yanzu ba
ciki ba goyo dole ya ƙyale ki dan ubansa, tsinan nen banza”

“Ba laifinsa ba ne Maryam, laifina ne a gareni ya ga wannan damar kuma ni na zaɓe


shi sama da iyayena. Amman yanzu Alhamdulillahi tun da Abbah ya ƙarɓe ni”

“Gaskiya nima na jidadin hakan ciwon Anty zai warke, kuma za'ayi biki da ke, amman
dai wannan yaron son ki yake ko?”

“A'a ba so a tsakanin mu, bikin wa za'ayi?”

“Bikina mana ni da Hindatu sati mai zuwa za'a ɗaura aure, Wednesday za'a fara biki”

“Amman shinw ba a faɗa min ba?”

“To ba kin zaɓi wasu family sama da mu ba”

“Haba Maryam, ai komai na zama ni ƴar'uwarku ce jininku, be kamata ku min haka ba”

Maryam ta laƙƙamo kafaɗarta tana dariya.

“Ai yanzu kin dawo ma hanya, komai da ke za'ayi Maman su Babanmu”

Ɗan Murmushi Namra ta yi ta miƙe ta shiga wanka. A wunin ranar haka suka riƙa treat
ɗin Namra kamar wata sarauniya, sai faman dare-dare suke suna rumgume ta. Suna
cikin haka sai kawai ta fashe musu da kuka da kuma dariya lokaci ɗaya.

“Ban taɓa tunanin rayuwa zata dawo haka ba, i miss my family a lot”

Hannu Aisha tasa ta share mata hawayenta, sannan ta miƙa mata wayarta da ke
ringing.
Namra na karɓa ta zaro ido.

“Asim ne”

“Asim”

Maryam ta amsa da ƙarfi, kana ta ce.

“Ba ni shi”

Anty ta ɗaga mata hannu

“No barta ta yi picking mu ji me zai ce”

Sai da ta yi ajiyar zuciya sannan ta danna picking ta kara a kunne.

“Hajiya Namra kenan! Ina kika shiga na yi nemanki cikin garin Katsina da kewaye
baki ciki”

“Ina kake tsammanin zan kasance bayan gidan Ubana”

“bakya giɗan ubanki kam dan na bincika aka ce min baki can, faɗa min inda kike je?
Karki damu da tambayar da nake miki ina son naji lafiyar Baby na ne”

“Bka da wani Baby Asim saboda ka zaɓi rabuwa da ni ne saboda shi”

“Yanzu kuma ina son abuna sai yaya?”

“Amman babu kaskantacce wulaƙantacce wawa kamar ka Asim, yanzu da baka da kunya
zaka kira ni ka ce min wai lafiyar cikin ka zaka ji?”

“Bana da damar hakan ne? Ai Allah ya ɗora min haƙƙin kula da ke har sai kin haihu,
kuma dole ne na bincika ko da kina da buƙatar wani abun sai a kawo miki”

“Kai har kana ganin ka yi arzikin da zaka iya ɗaukar nauyin cikin ka, ka daina
wahalar da kan ka dan ni yanzu babu ciki a jikina kuma karka sake kirana”

Tana kaiwa nan ta kashe wayarta tana huci. Anty bata muƙatar ta faɗa mata dalilin
kiran nasa dan ta fahimci komai. Ko minti biyu ba tayi ba ya aiko mata sako.

_Wallahi duk kika zubar min da ciki sai mun shiga kotu da ke_

Namra na gama karanta ta nunawa Anty.

“Karki sake ɗaga wayarsa karki sake ce masa komai, har sai mun ji abunda Abbah ki
zai ce”

Maryam ta yi ƙwafa.

“Wallahi samun family masu haƙuri irin wannan yana da wahala, wlh da wani guri ne
da sai an wulaƙanshi kam uban nan...!”

Anty ta nuna ta yatsa.

“Maryam ki cire wannan zafin ran da kike da shi, aure zaki yi kuma mace kike,
abunda duk haƙuri be baka ba rashinka be baka shi, duk wanda ya ci amana kin taɓa
ganin ya ƙare da kyau, kar dai karka yarda ka ci amanar wani barshi shi ya ci
amanar ka, ki zuba masa ido ki gani ba zai ga da kyau ba”
“Amman wani lokacin mutun yana buƙatar gargaɗi kai, da wannan haƙuri kike ta cutar
da mu da kan ki, gashi nan a gida kullum mine ba mu da gata, komai na gidan nan
Hajiya ce take da iko da shi, da an yi magana sai ki ce ayi hakuri, fisabilliah har
na waje kuma sai a riƙa bari suna takamu”

Ta ƙarasa tare da miƙewa tsaye ta nufi bedroom ɗinta.

“Ke kan Maryam Allah ya shiryaki, da wannan rayuwar babu inda zata kai ki, ni ban
san inda kika ɗauko wannan baƙin hali ba, ni dai ba haka na ke ba”

Bayan sun yi Sallah magariba, Anty ta shiga part ɗin Abbah da abinci a hannunta ta
tsakura masa labarin abunda ya faru.
Washe gari Namra ta daɗe tana bachin safe saboda gajiya da kuma kwanciyar
hankalin yau tana gida bata da wata matsala. Maryam ce ta shigo ita da Aisha suka
tashe ta wai zasu je siyen wasu kayan kitchen, kuma ta fito da Yasmin a falo tana
jiranta. Mulmula ta riƙa yi saman gadon sai da suka fice, sannan ta miƙe tsaye tana
miƙa ta shiga bathroom, bakinta ta wanke, a nan take kallon kanta a madubi ita
kanta ta san ta chanja kamar ba ita gaba ɗaya ta fita daga kamamninta, ta yi baƙi
sosai idonta sun ƙara fitowa.

“Namra ko har yanzu baki tashi ba”

Jin muryar Yasmin yasa ta yi saurin barin gaban madubi ta nufo ƙofar fita tana
zumuɗin haɗuwa da Yasmin.

“Anty”

Ta faɗa jikin Yasmin suka rumgume juna.

“Ashe kin ji na dawo”

“Eh Gwaggo ce ta faɗa min komai. Ban jidaɗin abunda ya faru ba Namra sai dai
dawowarki ta min daɗi, saboda Uzair, ko da baki zo ni zan je har inda kike”

Gaban Namra ya faɗi ta mata wani kallo mai cike da mamaki.

“Uzair kuma, miya faru?”

Yasmin ta kama hannayen Namra ta riƙe.

“Ina son ki faɗa min tsakani da Allah, da gaske kin taɓa kama Uzair yana luwaɗi?”

“Dan Girman Allah Anty ki rufa in asiri na dawo yanzu cikin family na kuma saki
sake tayar min da wannan maganar? Ko so kike Abbah ya sake kora ta ne?”

“Ko kaɗan, Namra kawai ina nema miki justice”

“Justice for what...?”

“For what Uzair did to you, shi ya ɗauke ki ranar da aka ce kin gudu kin je gurin
Asim”

Idon Namra ya cika da ƙwalla.

“Waya faɗa miki?”

“Shi ya faɗa min da kansa, kuma yayi rape ɗinsa da kansa Namra, na rasa yadda zan
yi abun yana ta ci na a rai, na kasa faɗawa kowa, amman na yi ma kai na alƙawari
sai na shigar da ƙarar Uzair kotu da kai na, akan ki sai na nema miki haƙƙinki,
saboda ɓacin suna da yayi miki kuma yasa duniya ta zargi kin gudu da saurayinki”

Kai Namra ta girgiza masa.

“Na yafe masa, dan Allah dan Annabi ki taimaka min ki bar wannan maganar”

“Kin tuna lokacin da Amira ta gudu? Shine sila saboda ke aka yi ma maganin sai ya
koma kan Amira saboda ta ci amanar ki, Namra you deserve justice”

“Ke da kan ki zaki shiga kotu ki ƙalubalanci mijin ki?”

Cikin kuka Yasmin ta ce

“Yes Goyon bayan ki kawai na ke nema”

Namra ta yi saurin miƙewa tsaye fuskarta da hawaye.

“Zan yi tunani a kai, just go please”

Bata mata musu ba, ta share hawayenta ta mike tsaye ta fice. Tana fitowa falo ta
karɓi Little Namra hannun Anty ta fice, ko sallama bata yi ma Anty ba. Anty na
ganin hakan ta san ba lafiya dan haka ta tashi ta nufi ɗakinta inda Namra take.

ASIM POV.

Yana fita gidan Hajiya Sadiya, ya kira Matdiya ya faɗa mata ta faɗawa mamanta yau
da dare zai zo ya gaishe ta. Haka kuwa aka yi, dare na yi yaje yayi wanka ya shirya
cikin tufafi na alfarma, ya shiga motarsa da ya sa aka wanke masa, ya nufi wani
boutique ya haɗu mata sabulai da mai da turaruka masu ɗan karen tsaɗa sai da ya
kusa ciki bayan motarsa sannan ya shiga ɓangaren kayan ciye-ciye yayi leda uku,
bayan ya biya ya kama hanyar gidansu.

Tass ya samu ƙofar gidan yau kam an share ba kamar kullum ba, zamansa yayi cikin
mota ya kira ta a waya, ya shaida mata yana nan waje. Yau kan ta fi masa kyau fiye
da kullum dan ta chaɓa ado da sari kamar wata amaryar india. Sama-sama suka gaisa
yana mata wani kallo mai cike da alamar tambaya, ita kuma sai wani noƙe kai take
ita ala dole tana jin kunya. Sannan ta yi masa iso, suka shiga cikin gidan tare. Ya
raina gidansu sosai dan shi gani yake yanzu ya wuce irin wannan rayuwar. Bayan ya
gama gaisawa da mahaifiyarta ya aje mata dubu hansi, sannan shiga ko wane ɗaki na
gidan yana gaisawa da su sannan ya aje musu dubu goma. Su kan sai murna suke suna
yabawa Mardiya kan ta yi miji, masu jin zafi suna ji, dan wasu har sun soma maganar
ai yadda yayi ma Namra ita sakinta zai yi da ana kwana biyu.

Bayan sun fito yasa yara suka kashe kayan da ke bayan motarta suka shigar ma
Mahaifiyar Mardiya da su cikin gida. Ita Mardiya ji tayi kamar ta ɗauke shi ta haɗe
saboda ƙaunarsa dake ƙara mamaye mata zuciya, ko a mafarki bata zaci mutum mai kuɗi
kamar Asim zai so ta ba, balle ma har ya ce zai aureta. Sun sha fira sosai sai
kusan ƙarfe goma sha ɗayan dare sannan suka yi sallama.

A daren da farinciki suka kwana daga ita har Asim, har yana jin ba zai iya bari ta
jima sosai ba. Sai dai abunda ya tsaya masa a rai miyasa bata nuna masa dangin
ubanta ba? Ko lokacin da ya ce zai turo cewa ta yi bari ta faɗawa Uncle ɗinta.

“Idan ma bata da uba miye ruwana tun da ita nake so ba ubanta ba”

Ya faɗa yana fesa turare a jikinsa. Sannan ya ɗauki glass ya saka ya ɗauki makullin
motarsa ya fice. Kai tsaye gidan ƙanen Babansa ya nufa, daman yasan a irin wannan
lokacin yana gida kamin yaje gurin da yake aikin ƙira. Har ciki gidan ya shiga, sai
qani ƙyaƙƙyami yake da ginin ƙasa, ya gaisa da matansa sannan suka fito waje suna
tattauna maganar auren da Asim yake labarta masa na Mardiya akan maganar tura
magaba, a nan suka kitse maganar sati mai zuwa sai nemi sauran ƴan'uwa suke je su
nema masa aurenta, sannan kuma ya ɗora masa da maganar gidan da aka ce masa akwai
amman milinya takwas ne.

Gidan ba shi da nisa sosai da unguwar hakan yasa suka ƙarasa da mota aka kira Mai
gidan ya shiga da Asim ciki ya ga komai. Ya yaba da gidan sosai, komai na cikin
gidan sabo ne ga sabo fenti ga fulawowi daman irin gidan nan ne da ake ginawa
sababbin a saida. Ko tayawa Asim be yi ba, suka kutse magana akan idan ya dawo daga
sokoto zai zo tare da shedu a bashi makulin gida takardu shi kuma ya bada kuɗi.
Mutunen sai godiya yake ganin Asim be taya ba ya amince zai ba shi kuɗin. Bayan sun
dawo ya aje Ƙanen Baban nasa ya miƙa masa dubu ashiri, sannan ya kama hanyar gidan
Hajiya Sadiya yana aikawa Namra kira.....

Tsaki yaja bayan ya kashe wayar, lallai ma yarinyar nan ta raina masa hankali, shi
zata yi ma ɓoyun ɗansa? Allah yasa ma da gaske ta zubar da cikin nan ta ga yadda
zai yi da ita ƙut! ya yi ƙwafa.

Yayi mamakin ganin Hajiya Sadiya a gidan nata, bayan yasan a wacan take zama saboda
ƴarta. Bayan sun gaisa ya zauna saman kujera yana kallonta.

“Mun yi waya da Alhaji yace na same shi sokoto, kuma na samu labarin Namra tana
sokoto har ma na yi waya da ita, amman kin san ba lallai ba ne ta amince ta dawo
gidana ba ko?”

“Nasan da hakan shiyasa ka ga na dawo nan gidan ai, nasan zaka zo nema na, abunda
nake so da kai ka yi ta try har sai kaga ta aminci, idan kuma hakan be samu ba, to
zan baka abunda zaka bata, kuma ka tabbatar ya kai ga bakinta, ma'ana ta ci”

“Mi zaki ba ni?”

“Ina zuwa”

Ta miƙw tsaye ta nufi wani bedroom. Shi kuma ya ƙurawa pop ido kamar yau ya fara
ganinsa.

“Wallahi duk kika zubar min da ciki ko? Hmmm, Allah yasa ma Ubanki ne ya zubar da
shi ta yadda zan fi jindaɗin shari'ah da shi...”

Fitowar Hajiya Sadiya ce tasa ya mai da dubansa gareta yana kallon farin ƙyalen da
ke hannunta. Tana ƙarasowa ta warware ƙyalen ta miƙa masa apple ja.

“Ka tabbatar ta ci wannan apple ɗin ko da kaɗan ne, amman sai idan ta ƙi yarda ta
koma ɗakinta”

Ya ƙurawa Apple ɗin ido

“Kar fa wani abu ya same ta, i mean kar ta mutu, akwai baby na a jikinta”

“Babu abunda zai same ta, ka yi yadda na ce kawai”

“Okay”

Ya miƙe tsaye tare da saka apple ɗin a aljihu, ya fice. Be yi nisa da barin gidan
ba Nably ta kira shi, amman sai ya samu kansa da ƙin ɗauka shi kwata-kwata yanzu ta
fita ransa, Mardiya ce on top.
KU YI HAƘURI DA WANNAN🙏

*Ku yi ta yaudarar kan ku da sunan wata ta siya ta ara muku ku karanta, idan mun je
can inda baki be magana zamu tsaya gaban Allah ni da ku ya mana hukunci.*

HILAL POV.

SIX MONTHS LATER...


Suna jin ƙarar tsayawar Motar Dadynsu suka fita da gudu suna masa oyoyo. Zaune suka
same shi cikin motar yana waya, hakan yasa Ezzah zagayawa a front seat ta zauna
tana jiran ya gama wayar ta fara masa complain.

“Dady muna dawowa daga makaranta Mama Teema tasa mu wanki”

Yana sauke wayar daga kunnensa kenan, ta soma labarto masa abinda ya faru yau. Wani
kallo yake mata, irin kallon nan na ɗa da ƴa, kamin ya kai hannunsa ya kama
fuskarta ya riƙe.

“Ezzah kin yi ƙanƙanta da irin abubuwan nan, kullum sai kin ce Teema ta miki kaza
bla bla bla, wannan sam be dace da ke ba, babu abunda Teema zata muku sai tarbiya,
ƴar'uwarki bata taɓa faɗar an mata wani abu ba sai ke”

Ta turo baki zata masa magana da kuka a lokaci ɗaya.

“Dady ni bana son ta, a kawo mana Mummie mu”

“Ba za'a kawo ba, kuma kar bakin ki ya ƙara furta kalmar ƙi ga matata, ke kowa ai
baki so, har Kalsoom ba haka kika mata ba? Saboda ku Hajiya tasa na auri Teema
yanzu kuma ki bijiro min da wannan maganar! Kar na sake ji”

Ya fita daga motar ya kama hannun Ulfah, sannan Ezzah ta fito ita ma tana share
hawaye ta rufe masa motarsa, ta rufa musu baya.

Teema na tsinkayarsu dan tana tsaye jikin window ne, sai dai ba zata iya jin me
suke cewa ba. Tana ganin ya doso ƙofar falon sai ta bar gurin da sauri ta shige
bedroom ɗinta ta zauna bakin gado ta soma ƙirƙiro kuka. Tun da ya saka kafarsa a
falon ya ji be ji motsin Amaryarsa ba ya saki hannu Ulfah ya doshi bedroom.
Zaune ya same ta bakin gado tana rusar kuka, zama yayi kusa da ita cikin damuwa,
dan yasan dalilin kukan nata baya buƙatar tambayarta.

“Sau nawa zan faɗa miki ki yi haƙuri Teema? Wasu ma sai da suka shekara ashiri a
gidan miji sannan Allah ya ba su haihuwa, balle ke da baki yi shekara ɗaya ba ma?”

Ta ɗago kai ta dube shi.

“Hilal ina tsoron kar a'ce ba zan haihu ba ne gaba ɗaya, tun da na zo gidan nan ko
ɓari ban taɓa yi ba”

“Idan Allah ya ga dama zai baki just be patient, wani lokacin abun mutum nesa yake,
na shigo da farinciki kuma kin rusa min shi”

“Ka yi haƙuri rai na ne yake ɓaci”

Ta share hawayenta, har ga Allah wannan matsalar tana damunta, sai dai ta kan
yawaita yi ma Hilal kukan hakan ne gudun kar ya zargi ta ci amanar ƴaƴansa, duk
lokacin da ya tarar da ita cikin irin wannan halin ya kan kasa mata maganar yaran,
ko da kuwa sun je masa sun kai masa ƙararta ne.

“Kuɗin da na faɗa miki muna jira jiya dai Allah yayi sun fito, dan haka yanzu ki
shirya muje kasuwa da yara mu yi siyayya, gobe kuma zan je da Kalsoom Hajiya kuma
kuɗi zan bata, sauran kuma sai mu ƙara a account, idan na samu hutu sai mu leƙa
waje”

Hannayenta ta kama ta riƙe tana murzawa a hankali.

“Hilal ya kamata ka yi tunanin ma kan ka future, kai kake ta hidima da Hajiya duk
da tana da waɗanda zasu iya mata beside Abbah ka yana da rai balle ace ko zata rasa
wanda zai mata ne, ya kamata ace ka tanada abun ka har sai ranar da zaka nema ko
kuma ita Hajiya zata nema sannan ka ɗauko ka yi amfani da shi, ƴaran ka babu abunda
suka nema suka rasa, dan me za'ace a riƙa kashe musu kuɗi haka nan kawai a banza?
Ka fara ginawa kan ka rayuwa Hilal, yanzu nan kuɗi ba ƙara ka gina gida da shi ba”

“Ina da gida Teema ba ɗaya ba ba biyu ba uku ba, kuma naga yanzu mi zan yi da
gida?”

“Baka mafarki tara zuri'ah kamar ta Mahaifinka? Baka fatar haɗa ƴaƴan da matanka
guri ɗaya yanzu? Ni abun da naga ya fi kawai ka kawo ko 150.000k ne asiya mata lace
da atamfa, sauran kuɗin kuma ka ba ni nawa ita kuma Kalsoom ka bata ta siya abinda
take so, Hajiya na san idan ka bata kuɗin kashewa zata yi amman idan aka siya mata
kaya, ko sakawa ta yi ai ka ji daɗi, ni k8ma ina son na fara business”

Miƙewa yayi tsaye.

“Zan yi tunani akai, bari na je na duba Kalsoom ta ce min kan ta na ciwo”

“Ka gaishe min da ita, tun da ka ƙi yarda na ganta, amman ba zaka bari ka ci abinci
ba”

“A'a sai na dawo kinsan matsalar mai ciki”

Ya faɗa da murmushi a fuskarsa sannan ya juya ya fice, zuciyarsa da kwankwato, ya


lura duk lokacin da ya shigo da zimmar yi ma yaransa ko Hajiya abu sai Teema ta
nuna masa ba haka ba, abunda Kalsoom da Rashida ba su taɓa masa ba kenan. Duk da
yana tunanin wannan karon ta yi magana mai ma'ana kuma da bada dalili. Miƙewa ta yi
ta rakoshi har gurin mota, ya shiga ta maida ganbun motar ta rufe tana ɗaga masa
hannu har ya fice.

Ajiyar zuciya ta sauke, ta gaga mallakar mijinta har yanzu, iya shige-shigen da
take tunanin zata yi ta yi amman kan Hilal ya gagara mallaka, bata da ƙudiri raba
shi da mahaifiyarsa, sai dai tana ganin kamar hidimar da yake mata yayi yawa, tun
da ba shi kaɗai ta haifa ba.

“Ulfah, Ezzah..!”

Sai ga su da gudun su, bama Kamar Ulfah da hanjin cikinta ke kaɗawa, dan jikinta
har rawa yake kamar zata saki fitsari.

“Uban mi kuke faɗawa Baban ku ɗazu...?”

Ulfah ta yi sauri ɗaga hannunta sama.

“Wallahi ba ni ce ba, Ezzah ceta faɗawa Dady wai kin sata wanki”
Teema ta miƙa hannu ta kama kunnenta har sai da ta yi ƙara.

“Wato dan na saku wankin uniform shine abun magana? Ke komai sai kin kwashe kin
faɗawa Dadynki? Sau nawa nake ja miki kunne akan faɗawa Dadynki magana idan na miki
abu?”

Ta nuna mata wani ɓangare na gidan inda rana ta baje a gurin, kamar an hura wuta.

“Oya wuce can ki kama kunnenki, kuma karki taso sai na ce ki taso”

Da sauri ta ɗuka ƙasa ta riƙa kafafun Teema.

“Dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba”

“Wannan tsinin bakin na ki ba, ke me baƙi hali tun da kin yi mugun gado ko? Kije ki
kashe min aure! Ke ce uwar rashin kunya uwar gulma ko? Zaki ci ubanki a gidan nan
ba dai duk lamanin da na ke miki baki gani ba”

Ta faɗa tana matsar bakinta. Daman ta saba yi mata irin wannan horon a duk lokacin
da ta yi mata ba daidai ba. Ta buge mata hannu.

“Ba zaki wuce ba sai na yi ƙwallo da ke?”

Ulfah ta sa kuka.

“Mama Teema Wallahi ba da ni ba”

“Ai ba da ke ba ita kaɗai, ki ki wuce ki gyara min kitchen”

“Tau”

Ta wuce da gudu idonta cike da ƙwalla. Ezzah kuma ta tashi tana kuka ta nufi gurin
da ta saba tsayawa kama kunne ta kama kunnenta.

Juyawa Teema ta yi ta koma cikin falon, har ta zauna sai kuma ta miƙe tsaye ta nufi
bedroom ɗinta tana ta saƙe-saƙe a ranta. Wani irin ihu ta ji da muryar Ulfah ba
shiri ta zaɓura ta fito daga bedroom ɗin a firgice ta nufi kitchen.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Na shiga uku uban waya aike ki taɓa miya?”

A razane ta yi furucin kamin ta ƙarasa gaban Ulfah da ke kwance ƙasa lame-lame tana
murje-murje da ihu kamar bata san inda take ba, jikinta har ya sale.
Har ta ɗaga ta tasheta sai kuma ta saketa ta fita a firgice tana kiran Ezzah.
Karo suka yi ita da Ezzah duk ta haɗa uban gumi.

“Mama Teema ga ni”

“Je ki Kitchen ki kama ƴar'uwarki yi sauri”

Ita kuma ta juya da sauri ta koma ɗakinta dan kiran Hilal.

KALSOOM POV.

tana zaune falo Hilal ya shigo bakinsa ƙunshe da murmushi da kuma sallama a lokaci
ɗaya. Itama da murmushin ta amsa masa tana ƙara miƙarda ƙafafunta. Kusa da ita ya
zauna daman tana zaune ne saman carpet ya kai hannu ya shafa ƙananan kitson da ke
kanta yana murmushi.

“A bani canji na na kitso”


“Ba wani canji mai kitson ma ta ce sai an ƙaro”

Dariya yayi ya kai hannu ya shafa cikinta.

“Sai kice mata ai ke mijinki bawan Allah ne, ba mai kuɗi ba ne”

“Ba wani nan, ni sai ka ƙaramin”

“Baki da matsala yarinya ko nawa kike so za a ba ki, ƙuɗin da na ke faɗa miki ina
jirajiya sun fito”

Ta zaro ido.

“Da gaske Alhamdulillahi”

Ya lanƙaci hancinta.

“Yes”

“Allah yasa musu albarka”

“Amin mi kike so a siya miki?”

“Ka fara cirewa Hajiya nata, sannan mu sai kuma ƴaƴanka, kai ai ko baka samu ba, ba
matsala”

“Sai dai na ɗauki na ki”

“Ba matsala ai daman ni bana siyen komai yanzu”

“Ko da kin haihu?”

“Hilal anya zan haihu?”

“Haba ki daina wannan maganar mana, ke da Teema maganar haihuwar nan na ku ya ishe
ni”

“Ƙara ita ai bata yi cikin ba, ni kuwa shekara har da wata huɗu ban haihuwa ba,
cikin nan ya ishe ji nake kamar na cire shi na aje”

“Zaki haihu inshallah, tun da an bincika babu wata matsala”

“Allah yasa”

“Amin. Zaki haifa min Baby girl mai kama da ke”

“Baby Boy dai zan haifa mai kama da kai”

Bakinshi ya kai zai yi kissing ɗinta sai wayarsa ta yi ringing, kawar da fuskarta
ta yi dan ta bashi damar picking ɗin wayarsa.

“Hello...”

Ya miƙe tsaye da sauri.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, gani nan zuwa”

“Miya faru? ”
Kalsoom ta tambaya a firgice.

“Wai Ezzah ne da Ulfah suka yi faɗa shine Ezzah ta watsa mata miya”

“Subhanallah miya haɗa su haka, ko na ɗauko hijab ɗina muje tare?”

“A'a zauna duk yadda aka yi zan kira ki”

Ya fice a firgice. Daker ta unƙura ta miƙe tsaye da tulelen cikinta.

Yana isa ya ɗauke ta suka yi asibiti tare da Teema, Emergency ya wuce da ita
surgical Ward, wata Dr Khadija ce ta shiga bata taimakon gaggawa, dan Dr Hilal
tsaye kawai yayi yana kallo saboda jikinsa duk ya mutu ko da suka kawo ta asibitin
ma ta suma.

AMIRA POV.

Tun da suka kamo hanyar sokoto take ta aikinki kuka, har suka iso sokoto idonta ya
kumbura sosai. Direban na yin horn a bakin gate ɗin gidansu, ta jita cikin wani
irin yanayi marar misaltuwa, wani sabon kuka ne ya sake rufeta, musamman lokacin da
ta ji muryar mai gadin su yana tambayar wa suke nema.

“Amira na kawo ka min magana da iyayenta zan danƙata hannun Mahaifinta ko


mahaifiyarta”

“Amira...!”

Mai gadin ya daki ƙirji. Kamin Direban ya sauke gilashin motarsa ya hango Amirar ce
da gaske. Jiki na rawa ya wangale musu gate sannan ya shiga cikin gida da gudu.
Sai ga Mahaifiyarta da duka ƙanenta sun fito har da Baban yayanta. Duk motar suka
nufa. Ammy ce ta fara buɗe motar sai ga Amira ta fito daga ciki tana kuka, suka
rumgume juna, ƙanenta kuma suka daka tsalle suka yi kanta, Big bro ɓata ne ya tsaya
a gurin ya dake yana kallon ikon Allah.

“Ke ce Mahaifiyarta?”

Ammy bata iya amsawa ba sai kuka take, Babban yayansu ne ya amsa da.

“Eh ita ce, waye kai?”

Ya fiddo id cart ɗinsa ya nuna masa,sannan ya miƙa ma Ammy waya.

“Zaki yi magana da Ogan mu”

Cikin muryar kuka Ammy ta ce

“Hello”

“Ke ce Mahaifiyar Amira?”

“Eh nice”

“Kina magana da Major Abdallah Ahmad Mai-doki, da ga rumdunar bada tsoro ta Kasa
wato Nigerian Army, da fatar ƴar ki ta shiga hannun ki”

“Ta shigo na goɗe muku”


Daga hakan ɗireban ya janye wayarsa ya buɗe motarsa.

“Wait...”

Big bro nata ya faɗa sannan ya ƙaraso kusa da shi.

“Ina kuka haɗu da ita?”

“Ba ni da wani abun da zan ce ita zata muku bayanin komai da bakinta”

Ya shige motarsa ba tare da ya tsaya jiran abunda zai ƙara tambayarsa ba ya juya a
guje ya bar gidan. Sai da Ammy da Amira suka ci kukan su sosai a gurin sannan suka
shiga cikin giɗan still suna kuka ita da ƴarta.

NAMRA POV.

“Miya haɗa ki da Yasmin?”

Anty Amarya ta tambaya.

“Ba komai saboda kawai na ƙi amincewa ta maka Uzair kotu ne”

“Kotu a wane dalili?”

A nan Namra ta labarta mata yadda suka yi da Yasmin.

“Karki yarda da ta sa sake jefa ki cikin halin da mahaifin ki zai tsane ki”

“Nima ba zan yarda ba Anty idan munje lahira Allah zai mana hukunci ai”

“Wannan shi ya fi, kin samu kin dawo gida kuma za su kawo miki wani ruɗani, qaya
sani ko da mijinta aka haɗa kai ta aikata miki haka”

“Ƙoma ba da shi ba ne babu ta yadda zan yarda ta kai mijinta kotu saboda ni”

“Hakan ya yi ki karya kije ki gaishe da mahaifinki, breakfast ɗin ki na nan


dinning”

“To na gode”

Tare suka fito da Anty, suka zauna dinning sai tattauna maganar suke, bayan ta gama
karyawa ta koma ɗakin Anty ta ɗauki Hijab ta saka ta nufi part ɗin Abbah.

“Assalamu alaikum”

Ta faɗa yayinda ƙafafunta duka biyu suka tsunduma cikin falon Abbah. Abbah dake
dinning area ya ɗago ya kalleta idonsa sanye da farin gilashi fuskarsa kuma ɗauke
da murmushi.

“Mamana”

“Na'am Abbah ina kwana”


Ta duƙa har ƙasa ta gaishe shi tare da Hajiya Barau dake ƙoƙarin barin dinning ɗin,
kamar zata fasa ihu tace wayyo haka ta bar falon. Sai Abbah ya nunawa Namra kujerar
da ke kusa da shi.

“Zo nan ki zauna Mamana”

Ta zauna cikin wani irin jindaɗi marar misaltuwa.


“Kin tashi lafiya, kin karya ko?”

“Na karya”

“Mamana ina son na tunatar da ke akan rayuwa. Ki riƙa haƙuri da abunda ya same ki,
kar hakan ya saka ki sakewa ko kuma wani tunani, ko wane bawa da irin ƙaddararsa,
dukan abunda ya faru ga bawa zai zamo masa darasi ne ko kuma izna ko wata hanya ta
samun cigaban rayuwa, ko da kuwa abun nan mai daɗi ne ko akasin haka, dan haka bana
son ki saka damuwa a ranku ni dai na yafe miki, kuma ina son idan kin ɗan hutu kin
samu sawaba sai kuma ayi maganar karatu, ina tunanin idan kika koma makaranta sake
fi sakewa ki manta da komai”

“Na gode sosai Abbah Allah ya saka maka da alheri, kamin abunda ban taɓa mafarkin
zaka min ba, ni kuma na maka alƙawarin va zan sake tsallake zaɓinka ba har a bada
ko da kuwa a tufafi ne”

“Allah ya miƙe albarka, ni zanje na shirya akwai inda zan je kwana biyu nan ban
samu na fita ba”

Ya miƙe tsaye yana faɗar hakan, ita ta miƙe tsaye.

“Tau Abbah Allah ya tsare”

“Amin”

Ya nufi hanyar da zata sadashi da bedroom ɗinsa, ita kuma ta juya ta fice zuciyarta
cike da farinciki.
Ko da ta dawo part ɗin Anty ta tararda su Maryam sun dawo, ga manyan ledoji a
gabansu amman sun riƙe baki sai mamaki suke, da alama akwai abunda ya faru.

“Lafiya?”

Maryam ta riƙo hannunta.

“Ke ƴar gidan Abbah wai Amira ta dawo”

“Amira kuma? Daman tun tafiyar da ta yi bata dawo ba sai yanzu?”

“Wallahi sai yanzu, kuma jiya ita ma ta dawo kamar ke”

“Amman kun ji wani abu game da ita?”

“A'a nima Iklima ce take faɗa min ta dawo”

Anty Amarya ta ce

“Allah ya kyauta”

Duk suka amsa da Amin.

UZAIR POV.

Yana shiga bedroom ɗinsa ya fito ya nufi na Yasmin dan yana son ya bincika ko da
akwai sauran abunda ta boye, jikinsa na bashi ba saƙon wasiƙar ne kawai ba. Bincike
ya fara mata cikin durowoyin ɗakinta kama ya koma gurin wasu takardu da suke gefen
gadonta, be samu abunda yake so ba, sai kaiwa ya juya ya fita ya nufi wata ƴar
ƙaramar durowarta da take aje takardun aikinta da littafanta duk ya bi ya watsar
sai bincike yake mata. Wani abu ya ji ya tsoki tsararsa, kamar an soma masa mashi a
kunkuru, tun yana juriya da riƙe kunkurun nasa har ya ji abun ya ƙara sukarsa da
wani mugun zugi, wata zarananniyar ƙara ya saki yana jin abun masa ƙasa cikin
ƙashin ƙafafunsa, ihu kawai yake yana mirgina, abun ba kyau maza a ƙasa😖

Da gudu mai aikinsu ta so kansa tana tambayar ba'asi. Ganin abun ba na banza ba ne
ƴasa ta fita neman mai gadi ko zai iya taimakawa. Ko da Mai gadin ya shigo Uzair
wani abu yake kamar mai ɗaukar rai. Da sauri Mai gadi ya kira Yasmin ya faɗa mata
abinda yake gudana.

YASMIN POV.

“Zan turo maka number ka kira mahaifiyarsa ka faɗa mata”

Amsar da Yasmin ta mayar masa kenan ta katse kiran, ta aika masa number sannan ta
cigaba da kuka tana zanawa mahaifiyarta abubuwan da Uzair yake mata wanda hakan
kawai ya isa ya tabbatar da gaskiyar abunda ya yi ma ɗanta, bayan ta fito gidansu
Namra ta nufo gidansu dan ta na jin bata buƙatar komawa gidan a yanzu.

“Ko ma minene shiru ya kamata ki yi ki rufawa mijinki asiri”

“Irin wannan rufa Asirin ne yasa mata da yawa maza suke cutar da su, idan aka muku
fyaɗe ko aka yi ma ƴaƴansu, wannan abun yana cutar da mata da yawa, mu muke faɗar a
daina ɓoye abu a riƙa fitowa a ana faɗa yau kuma sai a same ni da wannan aikin na
ɓoyewa? Ɓoyewar nan da ake shi kw basu damar ƙara aikata abunda suke aikatawa, at
least ko da ba a hukunta su ba, duniya zata kunyata su kuma asan ko su waye, ban ga
dalilin rufawa Uzair asiri ba ko da kuwa ubana ne balle mijina, ina yawan faɗar
cewa ni dai i would never in my life encourage anyone to live with an adulterer tun
da har Allah ya ce a jifasu su mutu, they are as good as useless to be seen alive
in this world, sai kuma na zama ni ce zan rufa masa asiri miye amfanin aikina?”

“Nidan indai zaki ɗauki shawarata ban ga abun burgewa ga mace ta kai mijinta kotu
ba da sunan wai yayi ma ɗansa fyaɗe, kina da hujja ne?”

“Ko bana da ita dole zan samo ta”

“Ni kam ba da yawun baki na ba Yasmin wannan sam be dace ba, idan ma zama ne ba
zaki iya da shi ba, sai ki nemi ya rabu da ke kawai ki hutu”

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

AMIRA POV.

“ji na yi gidan nan ya isheni ina ta jin kamar idan ban gudu ba wani abun zai iya
faruwa da ni. Ban tsaya ɗaukar komai ba sai kuɗi, tun daga lokacin da na bar gidan
nan nahau mota na kama hanya ban sake sanin inda nake ba, ban san inda direba ya
sauke ni ba ban san ya nayi rayuwa ba, sai a ƴan kwanakin nan da wannan sojan ya
tsince ni a bolar gidansu, shine yayi ta min addu'ah da komai har hankalina ya
dawo, na faɗa masa inda nake ya saka direba ya kawo ni gida”

Duk kai suka girgiza cike da tausaya musamman Ammy da ke kuka kamar yadda Amira ta
ke yi.

“Amman Namra ta ci amanar abota, ai gashi nan ta fara ganin abunta, ɗazu-ɗazu
hajiya Haulat ta ƙira ta faɗa min ita ta dawo gida aure ya mutu, kuma ance can
gidan auren ta ci kwakwarta”
Salman Big bro nasu ya kalli Ammy dake wannan maganar yana faɗin

“Ai ba laifinta ba ne, ita Amira ai cin amanar ta tashi yi, da yanzu da gaske ne
idan an sakawa Namra wannan abun maganin zai kamata ai kim ga ita ta ci amana
kenan, waya sani ma ko koma miki ne yayi, a haɗa baki da ke a sace ta har a ayi
mata ƙazafi, wallahi kun ci amanar juna ke da ita”

Abban Amira ya ɗaga masa hannu cikin ɓacin rai.

“Idan kasan bakin ka ba alheri zai faɗa ba, ka tashi kawai ka bar falon nan. Allah
zai saka miki Amira zura mata ido kawai daga ita har ɗan'uwan na ta”

“Wane irin a sa muku ido? Aja mata haƙƙinta dai, babu irin abunda ba'ayi ba amman
yarinyar nan ita da mahaifiyarta suka tsaya kai da fata akan babu hannunsu a ɓatan
Amira, aka kiɗa aka raya aka daka yarinyar ta ƙeƙashe ƙasa tace bata san gaibu ba
akan ɓatan Amira sai yanzu kuma gaskiya ta bayyana za'ace a ƙyaleta”

Taɓe baki Salim yayi ya miƙe tsaye ya fice daga falon.

“Babu wani haƙƙi da za a ja mata ku zuba musu ido kawai, ko bayan rage kika zagaya
kika ɗauki wani hukunci sai na ɓata miki rai Wallahi, tun da na ce a bar maganar
nan barinta shine ya fi kawai”

Ya miƙe tsaye ya fice daga falon. Kuka sosai Amira take, sai dai ba kuka dawowa
gida ba, kukan rabuwa da Abdool tana jin kamar zata mutu idan ta tuna baya kusa da
ita a yanzu.

ABDOOL POV.

Ya ware hannayensa.

“You see Ummi na faɗa miki Mai Martaba bashi da matsala, na zauna na fahimtar da
shi kuma ya fahimta”

“Hakan na da kyau ai, sauran yarinyar ko?”

“Wannan ba matsala ba ne, zan ji da shi, so na ke sai an kwana biyu sai naje na
ganta ko?”

Ummi tasa dariya, the way da yake mata maganar kamar wani ƙaramin yaro.

“Allah ya baka sa'ah”

“Amin my happiness. This week zan koma aiki, hutun mu ya ƙare”

“Ai daman ai baka yi hutu ba, ina fatar da kana da number wayarta”

“Wallahi bana da ita saboda yarinyar akwai jan aji amman zan sa a nema min. Am ɗazu
mun yi waya da mahaifiyar Amira ta isa gida lafiya ƙalau”

“Mashallah, yau za su kwana cikin farinciki, ita kanta zata fi sakewa”

Kafaɗunsa ya ɗaga irin ina ruwana ɗin nan. Ummi ta watsa masa harara.

“Bari yarinyar nan ta ƙi amincewa da kai, ta yi ta baka wahala”

Ya sa dariya.

“Haba Ummi karki min baki mana”


Ya miƙe tsaye ya fice yana dariya.

ASIM POV.

Da rana ya sauka sokoto, kai tsaye gidansu ya nufa, duk da be so sake dawowa garin
ba tare da an canja musu gida ba, sai dai matsalar har yanzu ba a samu gidan da
suke so ba. Mama ta yi mamakin ganinsa sosai tun da be kirata ya faɗa mata zai zo
ba balle ta tanadar masa da wani abu.

“Wannan zuwa haka ba waya ga shi komai ba a tanadar maka ba”

“Ba komai nima zuwan ya kamani ne kawai”

“To Allah yasa dai lafiya”

“Lafiya ƙalau, na ji ance Namra tana garin nan ne, shiyasa na zo dan zan maida
aurena ne”

Mama ta daki ƙirji.

“Auren ka Asim? Kai kam mi ya kai ka daga Allah ya raba da ƙaddara”

“Kin san tana da ciki fa na sake ta, ni gaskiya yanzu so na ke na maidata”

“Amman Asim kana ganin zaka iya tunkarar gidansu yanzu ka ce zaka maida aurenta,
mahaifinta ai sai ya yanka namanka da wannan fitinanniyar ƙanwarta”

“Koma minene dai sai naje gidan, ai yanzu be isa ya wulaƙanta ni ba, dan na fi
ƙarfinsa Wallahi”

Tattaunawa suka soma yi kan maganar aurensa da Mardiya da irin abubuwan da ya


shirya, sannan ya bijiro mata da maganar samun gidan, a nan take labarta masa am
samu wani a Abdullahi Fodio Road amman wai har miliyan uku, ita gani take kamar
yayi tsada, waɗannan da ake samu kusa kuma duk bata son unguwar.

“Ƙar hakan ya dame ki, indai gida yayi miki za a biya kuɗi a saka komai sabo sai ku
koma”

“Yanzu kana da har miliyan uku na gidanmu?”

“Akwai su, zinari fa na ke siyarwa, kin san kuɗin da mike samu kuwa?”

“Allah ya ƙara arziki ai haka nake so, sai ka samu kawon ka Na Malam ku yi magana
shi ya san inda gidan ya ke”

Haka suka wuni suna fira sallah ce kawai ke tashinsa, sai da akayi magariba sannan
ya shiga yayi wanka ya shirya cikin ƙananan tufafi ya saka turare ya shigo ɗakinta.

“Mama ni zanje wani guri da abokina sai gobe zamu dawo”

“To Allah ya tsare hanya”

Ya sa kai ya fice sai ƙamshin turare yake. Be daɗe da fita ba aka aiko ana yi ma
Hajara sallama.

“Je kace tana nan zuwa”

Sai Hajara ta tashi ta ɗauki kayan kwaliyarta ta gyara fuskarta sannan ta saka
Hijabinta ta fice. Bayan fitarta Mama ta ɗauki tabarma ta shinfiɗa a waje ta zauna
tana sauraren Garkuwa Fm.
Tana haka sai ga Hajara ta dawo, ta doso inda take.

“Mama Yaya Asim ya bar makulli a ɗauko wayarsa a mota ya barta sai kiransa ake,
kuma Mahmud (Saurayin da ya zo gurinta) Idan wasu suka ga wayar zasu iya fasa
gilashin motar su ɗauka”

“Amman ya fita da wayarsa, sai dai idan ba ɗaya ba ce, lalaba aljihun wandon da ya
cire ɗazu ko daki samu makullin ni dai be ba ni ba”

Ta faɗa tana tsakalen haƙori, da karen darbejiya bushesshe. Hajara ta nufi ɗakin
Mama inda ya sarkafa wandonsa ta soma lalabawa ta ji kuɗi mai mugun yawa kamin ta
yi arba da makulin.

“Ga makullin nan bari na ɗauko, amman Mama kin ji Aljihun yaya kuɗi cike”

“Ke da gaske?”

Mama ta yi sauri ta tashi ta nufi ɗakin. Hannu tasa cikin aljihunsa ta ciro rabonta
saka inda take ajiyar kuɗi, sannan ta koma waje gurin tabarmarta zauna. Sai ga
Hajara ta shigo da wayoyi biyu da makullin sannan kuma da Apple hannunta.

“Aje masa, wannan karki canye ki rage min”

Ta miƙa mata wayoyin da Apple ta juya, hankalinta yana gurin Mahmud kar ya ce ta
bar shi.

“Ina kika samo tuffah”

“A motar Yaya”

Mama ta yi murmushin jidaɗi.

“Oh Yaro yayi kuɗi har tuffa ake ci a mota yanzu haka ya manta da ita da wayoyin
nasa da ya bari, ko da yake abun ba ɗaya ba naga fa ya fita da wasu”

Ta faɗa tana gantsara apple ɗin, babu ko bismilah balle kuma ta damu da wankewa.
Haka ta kama shi ta wanke tass tana cewa idan Hajara ta zo ta bata kuɗi ta siya
wani wani tun da akwai shi a titi, har ta ƙaro mata ma dan wannan ma ta jidaɗinsa.
Sau biyu ana kiran wayar Asim sai ta ɗauka ta ce baya kusa.

[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *Mama (Hajiya Zainab Kano) wannan shafin na ki ne,
Allah kara miki lafiya*

*81*
Kaɗan-kaɗan ta fara tari alamar sarƙewa, tun tana yi a hankali har ya taso mata
gadan-gadan ba sauƙi, sai faman bubbuga ƙirjinta take, daker ta unƙura ta sha ruwa,
bata baro gaban firjin ɗin ba ta soma aman jini babu ƙaƙƙautawa, tun tana iya gane
duniyar da take har ta daina ganin komai sai hudu, gashi yaran duk basa nan Hajara
ya gurin fira, ba ita ta dawo ba sai goma har da dare, ganin Mama bata kan
shinfiɗar tabarma dake waje yasa ta zargi ko ta shiga banɗaki ne, dan hankalinta be
kawo ta kalli gefen da firjin ɗin yake ba, ledar turaren da ke hannunta kawai ta
aje ta sake fita dan dawo da ƙannenta gida.
Moƙota ta shiga ta kira su, ta sako su a gaba tana biye har suka iso gida, sai a
lokacin idonta ya kai gurin da Mama take kwance cikin jini, ihu tasa tana faɗin

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Ta nufe ta da sauri tana ihu, tana ƙarasa gurin da take nefa na yin tsiyarsu na
ɗauke wuta, sai kawai ta ƙwala ma mai binta kira.

“Ɗauko Fitila Amina, ɗauko fitila yi sauri”

Da sauri Amina ta ɗauko fitila ta kunna ta nufo gurin da Hajara take. Suna yadawa
duka suka saka kuka da ihu, Hajara ta shiga girgiza Mama tana kiran sunanta, amman
ina idonta a ƙafe tana kallon sama. Da gudu Hajara ta fita ta shiga maƙota tana
kuka, kan kace kwabo gidan ya cika da jama'a, kowa ya shiga sai ya fita yana
girgiza kai wata maƙociyarsu ce da tafi kusa da su tasa hannunta tana kalmar
shahada ta rufewa Mama idonta, da taimakon wasu mutane aka dawo da ita ɗaki,
Maƙotan suka share gurin suka wanken jini, Amina da Hajara da ƙanensu kan sai kuka
suke,ana ciki haka sai ga ƙanen Asim ya shigo nan take shi ma yasa kuka, sai kiran
wayar Asim.ake baya ɗauka, unguwa har ta ɗauka wai Asim ya bada uwarsa, daman suna
zargin ba kuɗin arziki ba ne.

Tun da direba ya ɗauke shi ya kai shi gurin Alhajinsa, suka ci amai kyau aka sha
mai daɗi sannan suka koma sha'ani. Ba su bar juna ba sai da asuba shi ma dan zasu
yi sallah ne bayan sun gama Asim ya nufi gurin da ya aje wayoyinsa ya duba dan
yasan ya saka su silent ne. Missed calls ɗin da ya tarar ya ɗaga masa hankali
sosai, daga ƙanensa da Number Mama a ɗayan ɓangare kuma ga na Hajiya Sadiya da na
Mardiya ga kuma na Nably har sai ya rasa wanda zai fara kira. Maida wayar yayi ya
aje dan yasan aduniya Alhajinsa ya tsani kiran waya ko kuma chat da wani a lokacin
da suke tare da juna. Komawa ya yi suka kwanta wannan karon bachin gajiya suka yi
saboda an kwana ana saɓa ma Allah. Ba su suka farka ba sai 11am, shi ma dan Alhajin
nasa yana da meeting ne. Ada idan Asim ya aikata irin wannan saɓon yana jin ba
daɗi, yanzu kan ba ya jin komai har daɗi abun yake masa, sai da suka yi sallama
sannan Alhaji ya sa direba ya mai da shi gida, bayan ya faɗa masa zai sake aukowa a
ɗauke sa za a kai shi gurin wani amininsa da yake minister of defence, Asim ya
jidaɗi sosai da sallamar ƙwarai Alhajin yayi masa, ga kuma wanda ya ce zai haɗa shi
da shi yasan shi ma zai samu kuɗi gareshi.

Taron da ya tarar a ƙofar gidansu na maza ya tashi hankalinsa sosai, daman tun da
dreba ya sauke shi yake ji babu daɗi. Nuna shi jama'ar gurin suka riƙa yi a sannu-
sannu suna tsikumin wai shi ne babban ɗanta, wasu na cewa ya bada uwarsa yayi kuɗi.
Yana shiga cikin gidan ya tarar da taron mata gabansa yake sake faɗuwa, bama kamar
yadda ya ga ƴan'uwan mahaifiyarsa da mahaifinsa mata duka a zaune tsakar gidan wasu
har kuka suke, amman ko kaɗan be kawowa ransa mahaifiƴarsa ce ba ya fi alaƙanta
abun da ɗaya daga cikin ƙanensa.

“Wai lafiya mi ya faru?”

Ya tambaya muryarsa har gargada take, dan yanzu kan ya fara tsarewa. Babu wanda ya
amsa shi cikin mutanen da ke waje sai duk suka zuba masa ido kamar yau suka fara
ganinsa. Hakan yasa ya nufi ɗakin Mama dan be ga ɗaya daga cikin ƙanensa waje ba.

“Hajara miya faru?”

Yana shiga cikin ɗakin ya aikawa Hajara da tambayar. Sai kawai ya ji an sauke masa
mari har biyu a fuska. A gigice ya kalli wacce ta mare shi ɗin, Mama Inno ce, yayar
mahaifiyarsa wato elder sister ɗin Mama.

“Baka da mutunci Ibrahim tir da kai tirr da halin ka, ace wai tun jiya ka bar gida
baka san ka dawo ba, kuma ayi ta kira wayarka ka ƙi ka ɗaga, to burin ka ya cika
daman ko gawarta baka son gani ko? To ba zaka ganta ba, an kaita gidanta na gaskiya
sai kaje ka yi ta sharholiyarka daman ita ka sawa gaba”

Ta ƙarasa da kuka. Ji yayi kamar ana zooming ɗinsa, sam.ya manta da wayarsa na
silent duk da yana da niyar idam ya fito zai kira duka wanɗanda suka kira shi dan
ya ga har da new numbers, amman farincikin albishir ɗin da Alhaji yayi masa ya
ɗauke masa hankali, zuciyarsa sai nuna masa take Mama ce yana kaicewa, a take
idonsa ya cika da hawaye, mutumen da kukansa ma aiki ne.

“Kar dai ace min Mama ce...ce...ce


..”

Ya faɗa cikin kuka yana kallon gadon da ka agware.

“Ita ce, jiya da dare Allah ya karɓi abarsa..


Da sauri ya doshi gurin Hajira da ta amsa masa da kuka, ya ɗuka ya riƙa Hijabinta.

“Miya same ta Hajara miya faru faɗa min?”

Cikin kuka Hajara ta shiga masa bayani.

“Nima ban san abunda ya faru ba, ni dai kawai ina waje muna Fira da Mahmud bayan ya
tafi na shigo cikin gida sai na samu babu kowa, naje maƙota ka kira su muka dawo
gida sai kawai na hango ta can gefen firjin kwance idonta a ƙashe ta yi aman jini,
ko da naje na kira maƙota kowa sai yace babu ta, maman Haruna ce ta rufe mata ido,
na yita kiran wayarka baka ɗauka ba, kuma na ɗauki wayarta na kira ka baka ɗaga ba,
na kira su Mama Inno da kawo Amadu na faɗa musu... Da suka zo aka kira wani likita
(Maƙocinsu) ya duba ta yace ta rasu, da safe kuma aka yi ta kiranka baka ɗaga ba,
har aka mata sutura aka kai ta”

Faɗuwa yayi zaune, ya dafe kansa wasu irin hawaye masu zafi suka soma masa zuba, ta
ya za'ace mahaifiyarsa ta rasu daga ya bar ta kawai yaje ya dawo, sam be kawowa
zuciyarsa zancen Apple ɗin nan ba.
Kuka ya dinga rerawa a gidan har sai da ya tashi kukan kowa a gidan, wani irin
abu yake ji ana baƙinciki a zuciyarsa, be taɓa jin ɗacin da dafin mutuwa ba kamar
wannan lokacin, daman ko da ya tashi be san mahaifinsa ba, dan haka be san zafin
rabo ba sai a wannan lokacin, haka ya ɗinga rera kuka kamar mace, abun har babu
kyau, tun wasu na tsine masa dan suna ganin kamar ya mafa mahaifiyarsa ne har suka
fara tausayinsa.

NAMRA POV.

Duniya juyi-juyi a yayinda ake kuka mutuwar Mama, ta ɓangaren Namra murna ce ta
cika gida ko ina sai guɗa kake ji ana yi, da kiɗin ƙwarya dan yau aka saka mare
lalle, wato Maryam da Hindatu.

A cikin gidan aka yi sa salle ba kamar yadda wasu suke ba a ɗauka a kai wani guri
inda ƴan'uwa. Yanzu ne wasu ƴan'uwan suke zuwa na garuruwa da kuma na cikin gati
dan jiƙon lalle. Ƙarfe goma na safe aka saka jiƙon lalle wato ceremonial setting.
Amman ko da 9am ta yi gidan ya cika da jama'a abun da mai jama'ah, ba daga ɓangaren
Abbah ba bana Anty Amarya ba, da kuma na Hajiya Barau, har mutane ƙauye sun iso.
Goma dai-dai ƴan gidan angaye suka zo jiƙon lalle, yadda aka riƙa faka motoci a
bakin gate ɗin gidan har aka rasa gurin aje wasu. Mutane sai mamakin ganin Namra
suke da su a idonta suna mata kallon ta lalace ta yi baƙi, ita ko tana ganin har ta
ɗan yi ƙuba a zaman nan na kwana biyu da ta yi a gida. Duka abubuwan da aka raba a
gurin sa lallen daga ɓangaren Abbah ne aka kawo, wato gwaggwanin amare. Misalin
huɗu na yamma aka yi wanki amare a gidan sama road gidan Alhaji Salisu Yayan Abbah
amman wanda suke ƴan wa da ƴan ƙane (Cousin). An yi watsin kuɗi kamar ba gobe, bama
kamar Hajiya Barau yadda ta zage tana watsin kuɗi sai ka rantse da Allah har a
zuciyarta farincikin auren take, bayan kuwa ta ciki na ciki.

An raba abubuwa da dama a gurin bikin, bayan an raba abubuwan da al'ada ta tanada
(Al'adar sokoto) wato raba kayan mata (Hakin maye) a gurin awankin amarya, sannan a
ɗora ta su lalle da salatif da tsinke da ƙwarya da sauran kayanyakin aiki mata,
daga bisani aka biyo da kayan ciye-ciye da na tanɗe-tanɗe.

Daman can tun kamin ka shigo gate sai an miƙa maka ledar takeaway, drinks kuwa sai
wanda ranka yake so zaka ɗauka, bayan wanda zaka tarar a muhalin da zaka zauna tare
da kayan tanɗe-tanɗe.

ASIM POV.

Haka ya koma kamar marar lafiya, sallah ma daker yake unƙurawa ya tashi ya yi, ya
rufe wayoyinsa gaba ɗaya. Mutane sai gaisuwa suke masa. Bayan isha'i mutane sun
fara laɓawa, ya koma cikin motarsa ya zauna sannan ya kunna wayarsa, yana haska
cikin motar sai Apple ɗin yake nema, sai a lokacin ya tuna da wayoyinsa da suke
cikin motar, da sauri ya fita motar wayarsa na ringing. Hajiya Sadiya ce take
kiransa, sai ya koma can gefe inda babu mutane ya natsu ya amsa wayar.

“Asim ina ta kiran ka tun jiya baka ɗaga ba, ɗazu kuma na kira wayarka a kashe”

“Bana kusa ne”

Ya amsa mata cikin rashin daɗin rai dan zuciyarsa sak yanzu zarginta yake.

“Ina Apple ɗin da kace zaka bawa matarka? Wata ka bawa ne ko mi ya faru? Ni an kira
ni sai faɗa suke min, wai an basu tsohuwa, ni kuma na san ba wannan maganar muka yi
da kai ba, miya faru ne”

“Apple ɗin faɗuwa yayi a hanya ina da niyar kiranki na faɗa miki, maybe wata ta
tsinceta ne”

“Amman Asim sai da na yi ta nanata maka kar a samu matsala yanzu gashi wata banzar
tsohowa taje ta samu, garin yaya ma ka jefar da shi? Ko dai baka son kuɗin ne wai?”

“Ina so mana, ai yanzu akwai wani ko?”

“Eh amman sai naje na faɗa musu sai su ban wani, yaushe zaka zo?”

“Nan da kwana biyu”

“Zan je na ƙarɓo maka, amman dan Allah karka min sakakace irin wacan”

“Ba za a samu matsala ba wannan karon sai kin fi kowa farinciki”

“Haka nake so”

Ta katse kiran. Shi ko ya cige baki yana kallon wayar cike da baƙinciki. Yana son
ya tambayi Ƙanwarsa yadda aka yi apple ɗin ya fito daga motarsa har Mama ta ci yana
tsoron kar ta zargi wani abu.

“Kun samu sa'ar jinin Uwata... Wallahi kin yi nadamar sanina da kika yi a
rayuwarki, sai na ɗanɗana miki wannan baƙincikin”

Yayi wulgi da wayar iya ƙarfinsa, yana huci.


UZAIR POV.

Tare da ƙannensa biyu suka iso gidan da kuma mahaifiyarsa, tana ganin irin halin da
yake ciki suka ɗauki shi zuwa asibiti.
Emergency suka wuce da shi layin ƴan haɗari aka ware masa ɗaki daban likitoci
suka hau duba shi, sai ihu yake kamar wanda be san inda yake ba, bayan sun yi ɗan
bincike su aka tura shi gurin hoto, bayan an masa hoton suka sake dawowa da shi
ɗakin suka masa allurar bachi, amman kamar an ƙara masa zafin ciwo yake ji gaba
ɗaya ya fita hayyacinsa sai ihu yake. A take suka sake rubuta masa wani hoton, aka
je aka ɗauka.

Lokacin da aka fito da hoton, sai Likita ya kira Hajiya suka nufi wani ɗakin da ita
sai ya ƙala hotunan a jikin computer. Yana nuna mata.

“Ɗan ki ya taɓa yin haɗari?”

“Gaskiya be taɓa ba, amman ban sani ba ko be faɗa min ba”

“Gaskiya ƙashinsa na baya na karye, kuma na cinyarsa ma ya karye, sannan....”

Kamin ya ƙarasa ta miƙe tsaye ta sauri har kujerar da take zaune samanta ta faɗi.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ganin hakan yasa likitan dakatar da bayaninta, dan ya ga alamun zata fara masa
kuka, shi kansa yasan be kamata ya yi mata wannan bayanin ba, ganin tana mace amman
babu yadda ya iya tun da babu wani namiji babban da yayi kusa da mahaifiyarsa. Da
sauri ta juya ta fice daga office ɗin tana kiran wayar Abbah. Dan babu wanda ya san
an kai Uzair Asibiti dan basu faɗa ba, tun bayan da Yasmin ta daqo gida ba ta damu
da tasan dalili ba, tana ganin kamar yayi hakan ne saboda ta janye ƙudirinta.

HILAL POV.

“Miya same ƴar ka haka ne Doc?”

Doc Zara ta tambaya cike da mamakin irin ƙunar da Ulfah ta yi. Hannayensa ya zuba
aljihu yana sauke ajiyar zuciya, ita kan Teema tuni ta kusa cikin ɗakin tana hawaye
kamar gaske.

“Faɗa suka yi da ƴar'uwarta shi ne wai ta watsa mata ruwan miya dake kan wuta”

“Amman gaskiya ya kamata ka sa ido sosai akan yaranka Uzair, irin wannan abun yana
sa kisan kai fa”

“Ƙaddarori ne kawai idan Allah ya kawo abu”

“Allah ya tsare gaba, Ina uwargida har yanzu bata haihu ba?”

“Har yanzu fa”

“To Allah ya raba lafiya”

“Amin”

Tun da suka jero suke maganar basu rabu ba sai da ta kawo kusa da pharmacy sannan
ta ɗauki wata hanyar shi kuma ya ciro wayarsa ya kira Hajiya ya faɗa mata, ita
Rashida text kawai ya aika mata, sai kuma ya kama hanyar gida dan yi ma Ezzah
hukunci.
Sai da ya kama hanyar gida sannan ya kira Kalsoom ya faɗa mata halin da ake ciki,
dan yasan zata tashi hankalinta sosai.

Bugu ɗaya ta ɗauka.

“Kana ina ne?”

“Ina hanyar gida, na kaita asibiti da sauƙi”

“Na je gida ban samu kowa ba sai Ezzah tana ta kuka, sai ta biyo ni gani cikin
asibitin ma”

“Oooooo Kalsoom miyasa baki ragawa kan ki ne? Ba fa ke kaɗai kike ba a yanzu, da
izinin wa kika fita, yanzu da wannan tulelen ciki yama zaki yi driving?”

“Napep na hau”

Ajiyar zuciya ya sauke.

“Tau gani nan juyowa”

Ya katse kiran ya juya ya koma hanyar asibitin. Yana isa aibitin su Hajiyarsa na
isa yare da Mama ladi (kanwar mahaifiyarsa) da ƙanensa guda biyu. Jerowa suka yi
suna tafiya yana yi ma Hajiya bayanin yadda abun ya faru.

Kalsoom na hango shi tafe tare da Hajiya ta ji babu daɗi musamman dan tana tare da
Ezzah tasan dole Hajiya za tayi magana wata ƙila ma zata ce ita ce ta haddasa
wannan husumar. Duk sai ta rasa yadda zata yi ga tulelen cikin nan ya mata tsaye
kamar wacce zata haihu yanzu.

“Hajiya ina wuni”

“Lafiya ƙalau”

Tana amsa gaisuwar da Kalsoom ta yi mata ta wuce bata ko bi ta kanta ba. Hilal ne
ya tsaya gurin matarsa.

“Miya hana ki shiga?”

“Ban san ɗakin da aka kai ta ba”

“Tau muje”

“A'a sai Hajiya ta fito, kar ta gan ni da Ezzah”

“Cemin ta yi wai tana tsoron karka dake ta”

“Ai ba duka kaɗai ba karye ta ma zanyi, ba dai ke har kin kai ki ɗauki ruwan zafi
ki watsawa ƴar'uwarki ba...?”

Sai kawai Ezzah tasa kuka ta kama Hijabin Kalsoom ta riƙe gamgam tana kuka. Hilal
be bi ta kanta ba ya nufi sashen da zai sadashi da ɗakin Ulfah, Kalsoom ta rufa
masa baya tana faɗin Ezzah ta yi shiru ba zata bari ya daketa ba.
Ko da suka shiga Hajiya na kusa da Ulfah dake bachi, tana duba ƙonuwar cike da
tausayi, can jikin ƙofa Kalsoom ta tsaya tana kallon Ulfah, Ezzah na riƙe da
Hijabinta har lokacin tana kuka. Hajiya ta ɗago ta kalli Ezzah cikin tausayi da
ɓacin rai ta ce
“Amman Ezzah baki da zuciyar ƙwarai, ko ɗauki ruwan zafi ki watsawa ƴar'uwarki
haka?”

“Wallahi ba nice ba Wallahi Mama Teema ce...!”

Ta faɗa cikin kuka.


[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *82*

Teema ta katsa mata tsawa tana zare mata ido alamar dik kika faɗa sai na ci ubanki.

“Ke karki min ƙarya, munafukar yarinya fitsararriya”

“Wallahi ba ni bace, ke kika kira ni kika ce na zo naje kitchen na duba Ulfah ta


ƙone...”

Hajiya ta kalli Teema ta kalli Ezzah, ƙoƙarin ɗaukar maganar ta ke, sai kawai ta
jiyo kukan Teema wai Ezzah ta mata ƙazafi.

“Wallahi ba zan taɓa yafe miki ba, makira kawai munafuka”

“Ezzah kike cewa haka? Sai kace wata babbar mace? To wai kina aikin me haka ya
faru”

Cewar Hajiya tana sake da baki. Ta soma bayani tana kuka da kallon Hilal ko zai
kareta ɗin nan.

“Ina cikin kitchen ina girki, na ƙare tuwo sai na ce bari na ɗora miya, sai na ce
ta daga kamin daddawa ita kuma Ulfah ta gyara min tabarnuwa, ni ban san gardamar mi
suke ba sai kawai naji an taɓa tukuyan miyar da ƙarfi sai ihun Ulfah na ji ina
juyowa na ga ta juye mata miyar”

Izzah ta tuma ta dire ta sake tuma ta dire tana kuka da jan Hijabin Kalsoom tana
faɗin ba ita ba ce, amman babu wanda ya kula ta Hilal in banda harara babu abunda
yake mata, yana cike da haushinta sosai Allah ka ɗai ya san irin hukunci da zai
mata idan suka koma gida. Sai kawai ta saki Kalsoom ta ruga gurin Hajiya tana kuka.

“Wallahi ba ni bace Hajiya...”

“Hilal ka saurareta mana”

Kalsoom ta faɗa cike da tausayin kukan da Izzah take yi.


Hilal ya girgiza mata kai.

“Ba wani saurare da za'a mata, ai kin san halinta”

Izzah har da faɗuwa take a gurin taɓa tashi ta kama gyalen Hajiya ta riƙe ƙam.

“Ba zaki rufewa mutane ba ki ba, Wallahi zan dake ki yanzu nan, ba sai mun je gida
ba”

Hilal ya faɗa ciki fushi yana mai jin kamar ya kamata ya ɓallata gida biyu. Ihunta
ne ya tashi Ulfah daman can ba wani dogon bachi ta yi ba, saboda zafin wuta ko an
maka allurar ba bari yake ka yi bachi ba.

“Wayyo Allah Momie, Hajiya, Dady ka kai ni inda Momie ko Anty Kalsoom ko inda
Hajiya, bana son gurin Mama Teema ta watsa min wuta, wayyo zafi dady zafi Mama
Teema ta ƙona ni, Anty Kalsoom, Momie, Hajiya”
Sune ƙawai sabbatun da take tana murza jikinta sai da Hilal ya riƙe mata hannu.
Suna haka sai ga Rashida ta shigo hankalinta a tashe, tana kallon Teema hawaye suka
fara mata zuba.

“Ɗaya bayan ɗaya za ki bisu ki kashe, na sani Teema kaɗan daga halinki ne amman ki
sani kin ci amana kuma kema amana sai ta ci ki”

Sai kuma ta juyo gurin Kalsoom tana kuka, itana Kalsoom ɗin kuka take, Hajiya ma
haka, balle Teema dake ƙoƙarin kare kanta, ƙanen Hilal ma babu wanda baya hawaye.

“Kin ci amanata, sai da na ce miki ki riƙe min yara na amman kika ƙi, yanzu ga shi
abunda ya faru, bana da kowa a duniyar nan sai su, su ne farinciki na”

Jakar da ke hannunta ta saki ta nufi gurin ƴarta dake sabbatu, magangun ɗazu kawai
take maimaitawa. Rashida ta gadon ta riƙe tana kuka.

“Laifina ne, nice ban riƙe mutuncin aurena ba, ni na kasa zama da ku ni na cuceku
Ulfah laifi na, kuma na ci amanar matar da ke riƙon ku tsakani da Allah...”

Ezza ta yi gunta da kuka.

“Momie Wallahi ba ni bace, Dady ya ce sai ya raba ni gida biyu.. Wallahi ba ni ba


ce”

“Ba zan ɗauka ba, wannan ba zata kwanta jinya ba, ka kama wannan ka karya min ba,
ka saurareta Hilal Wallahi ba ita ba ce, karka ɗauki alhakin yarinyar nan Hilal”

Cikin kuka Rashida take maganar gwanin ban tausayi. Hajiya ta share hawayenta tana
kallon Ezzah.

“Miya faru faɗa mana”

Ras Ezzah ta zana musu abunda ya faru, duk wani tsoro na teema yau baya tare da
ita, tun da ta ji zancen Hilal yace zai raba ta biyu. Duk suka cika da mamaki sai
kawai Teema ta ƙara rushewa da kuka, Hajiya ta girgiza kai tana faɗin.

“Amman Fatima kin ban mamaki, kw da ake yabo da salla?”

Hilal yayi saurin ɗaga mata hannu.

“Hajiya dan Allah kar ayi maganar nan a nan, asibiti muke, kullum sai ace nine
family na cikin matsala”

“Kai dalla gafara can, kai har yanzu baka san ciwon kanka ba akan ƴaƴanka, ko wace
mace ka aura da irin azabar da take gwadawa ƴaƴanka, Kalsoom ta kashe Rafiq wannan
kuma tana ƙoƙarin kashe Ulfah wannan wane irin masifa ce”

Rashida ta kalli Hajiya tana hawaye.

“Wallahi ba Kalsoom ba ce ta kashe shi, Wallahi nice ni na kashe ɗana da kai na...”

Sai duk kallo ya koma kan Rashida har Kalsoom ɗin kallonta take. Hajiya tasa wani
dogon numfashi ta sauke ta ce

“Muje gida mu yi wannan maganar, Hilal muje gidanka a yi wannan maganar, Ke ki


tsaya nan ki kula da Ulfah”

Ta faɗa tana kallon ɗaya daga cikin ƙanensa, sai kawai ta nufi ƙofar fita tare da
tawagarta. Rashida ma fita tayi ta rufa musu baya dan ta shirya fasa ƙwan yau kam,
bata san gidan Teema ba dan haka ta nufi tsohon gidanta kuma gidan Hilal inda
Kalsoom take zaune. Hilal kan sai ya bawa ƴarsa magani tare da allura ta koma bachi
sannan ya sako matansa gaba suka kama hanyar gida. Ko da suka shiga falon Hajiya
na zaune falon tana jiransu, Ezza kuma na riƙe da Hijabin Kalsoom kamin ta saketa
ta nufi gurin uwarta da gudu.

“Maimata abunda kika faɗa ɗazu ko kina da wata shaida”

Cewar Hajiya tana kallonta. Rashida ta girgiza kai.

“Bana da wata shaida sai Allah da kuma Teema, amman Wallahi Kalsoom bata da hannu a
mutuwar Rafiq, ni naja komai”

“Kamar ya ki fito ki yi bayani mana”

Hilal ya katsa mata tsawa, Teema ta yi saurin saka baki.

“Karki ci amanata Rashida ni ban san komai akan ɗan ki ba”

Rashida bata kulata ba, ta soma koro da bayani.

“Bayan da Hilal ya sake ni, sai na riƙa zagaya makarantar su Ezzaha ina zana mata
irin makirci da rashin kunyar da zata yi ma Kalsoom, ina tunani kamar idan ta yi
hakan zai tausaya musu ya dawo da ni, da naga hakan be samu ba, sai na koma bin
bokaye, ina neman yadda za ayi Kalsoom ta bar gidan Hilal kuma ya dawo gareni, naje
wanu gurin aka mata magani aka sako mata jini, cikin dake jikinta ya kwanta ya ɓace
bat, na sake komawa na yi mata wani a wannan karon be faɗa kanta ba, ya faɗa kan ɗa
na Rafiq, ni kai na ban san ya faɗa kansa ba, har sai da naje na kaiwa Teema kukana
ta kaini gurin wani malami shi ya faɗa min cewar na yi magani ma kishiyata ya faɗa
kan ɗa na, shiyasa a asibiti aka rasa gane kan wannan matsalar sai ya nuna guba ne
sai kuma ya nuna gas ne, ba komai ba ne sai sihiri. Duk wani shige-shige da nake na
magani tare da Teema nake yinsa, ta kai ni gurare da dama, saboda ta fini sanin
bokaye, nayi mamakin da aka ce Hilal zai aureta saboda na san an gudu ba a tsira ba
ne. Sai dai na ɗauki hakan a matsayin cin amanar aure da nayi na keta haddin Allah
na tozarta aure, dole nima Allah ya tozarta ni, na ci amanarki Kalsoom na yi ta
miki abubuwa ko a zaman da muka yi da ke a gidan nan, ashe ma ke ƴar'uwata ce ba
kishiya ba...”

Kuka take sosai ita da Kalsoom da Teema, sai dai ko wannensu da abunda yake yi ma
kuka. Kalsoom babu komai a zuciyarta sai farincikin yau Allah ya wanke ta da kuma
tausayin Rashida da ƴaƴanta.

“Na yafe miki Rashida, Wallahi na yafe miki har a bada, kuma na miki alƙawarin zan
kula miki da ƴaƴanki fiye da yadda ke zaki kula da su, amman idan Hajiya ta yarda”

Kalsoom ta faɗa tana kallon Hajiya data soke kai tana hawaye.

“Haƙiƙa na cutar da ke Kalsoom, na miki kurkuren fahimta, na ɗauki alhakinki, na


cutar da ke matuƙa, Wallahi na ji kunyar kai na sosai”

“Haba Hajiya ai ko nice a matsayin da kike kwatankwacin abunda zan aikata kenan,
saboda gaskiya ba ta bayyanaba a lokacin kuma ɗan adam da zahiri yake aiki sanin
baɗini kuwa sai Allah, ni dai abunda kawai na ke so ki yarda da ni kawai”

“Wallahi na yarda da ke ɗari bisa ɗari kalsoom, kuma daga yau yaranki gurinki zasu
zauna. Teema baki yi ƴa ba, kin bani mamaki, ina gani kamar na ɗauko ma ɗauka
mutuniyar kirki ashe ɓara gurbi ce”

Kuka sosai Teema take ta sauka daga saman kujera ta zauna ƙasa kusa da Hajiya ta
kama ƙafafunta.

“Wallahi Hajiya ƙarya take min, na miki alƙawarin zan canja daga yau, ba zan sake
yin wani abu marar kyau ba”

“Nasa Hilal ya aure ki ne saboda ita tunanin ke ta ƙwaraice, Fatima ko da mun zauna
da ke babu aminci a tsakanin ke da mijinki da ƴaƴansa da kuma ni, mace mai shige-
shigen malamai iya mata sai Allah karki je ki yi mana irin na Rashida, kin ga ƙara
a rabu tun abu be yi nisa ba, kije can Allah ya haɗa ki da rabon ki, ni kan Hilal
ba dan kar na zama uwar banza ba da na baka shawarar rabuwa da yarinyar nan...”

Ta ƙarasa tana kallon Hilal. Shi kan uffan be ce ba sai kallon pop yake abun duniya
ya taru ya tsaya masa, idan ya shiga wannan ya shiga wannan. Miƙewa ya yi tsaye ya
fice cikin rashin daɗin rai.

Bayan fitarsa Hajiya ta miƙe ta fita, ta bar Teema na kuka, Rashida kuma na hawaye.
Bata yi minti talatin da fita ba Rashida ta tashi ta fice, a lokacin ne Teema ta
kalli Kalsoom ta ce.

“Zan taimaka miki ki haihu, nasan hanyoyin da zan bi ki haihu, wannan cikin na ki
yanzu shekarar ɗaya da wata huɗu cikin na biyar, amman idan kika taimaka min kika
hana Hilal ya sake ni, ina son ki saka baki a lamarin auren mu domin a yanzu na
fuskanci kina da ƙima a gurinsa da kuma mahaifiyarsa fiye da ni”

Ido kawai Kalsoom ta sakar mata tana kallon ikon Allah, ta ya zata ce ta kaita wani
gurin bayan yanzu aka gama rigimar tana bin bokaye, ita bata ma tsoron wani ya ji.
Kamar daga sama suka ji muryar Hilal da ke tsaye bakin ƙofa rumgume da hannayesa a
ƙirji yana kallonsu, dan sam basu san da shigowarsa ba.

“Kalsoom bata iya shige-shige irin na ku ba, kuma idan lokacin haihuwarta yayi zata
haihu, ke ai naga haihuwar kike nema miya hanaki bin bokayen su baki haihuwa?”

Ta miƙe tsaye yana kallonshi.

“Haihuwar da na ke so Hilal saboda kai nake son ta, ina son na haihu da kai saboda
ina ƙaunar ka ne, yanzun kuma abunda nake ƙoƙarin yi ma saboda ina ƙaunarka ne
Hilal, miyasa ka kasa ganin haka? Tun kana mijin Rashida na ke mafarki miji irin ka
saboda kana kula da ita yadda ya dace, ashe ma Allah yayi sai na kasance ɗaya daga
cikin matan ka, ka tausaya min Hilal, zan iya yi maka alƙawarin ba zan sake bin ko
wane malami ba indai wannan ce kawai matsalar...”

Ta ƙarasa tare da risinawa kamar mai neman gafara.

“Ba wannan ce kawai matsalar ba, ko na zauna da ke ba zan aminta da ke ba, kuma mai
hali baya fasa halinsa, ai yanzu aka gama wannan rigimar amman kika ɗaga ido kika
kalli Kalsoom har kina neman ki taimaketa, dan ta saka kar na sake ke, kin manta
ita da ke duka a ƙarƙashin kulawata kuke? Hajiya ma dake gindaya min sharaɗi yin
abu ko hani ta bani umarnin idan na ga dama na sake ki, tun dan me zaki dawo gurin
Mamata kina neman ta taimake akan abunda zan iya yanke hukuncinsa yanzu?”

Kalsoom ta girgiza masa kai.

“Saboda ta san zan iya saka ka yi ne...”

“Kalsoom karki saka bakin ki cikin wannan maganar please”

Teema ta hasala ta miƙe tsaye cikin ɓacin rai da zafin zuciya.

“Ka daɗe baka sake ni ba Hilal, ni wannan wuƙancin da Rashida take ɗauka ni bana
ɗaukarsa, sai kace kai ne kaɗai na miji ana magana kana ƙara butsewa, ka sake mana
ai ni tafi nono fari, zaman gidanka ko zaman wahala haka kawai za ku ɗauko ni wani
kula da yara wato ga ƴar aiki kenan ko saboda an maida ni shim mai ruwa uku sha-
sha-sha, da ƙurciyata na lalata kaina gurin gina rayuwar ƴaƴan wata nawa ko zuwa
duniya ba su yi ba”

“Shiyasa kike cutar da su? To Allah ya toni asirin ki, kuma ki je na sake ki saki
ɗaya...!”

“Ai ni da uku ka yi da ka fi burgeni”

“Ɗayan dai zan miki ƙyaji da shi”

“Tafi nono fari, ai ba kai ne autan maza ba”

“Na sani shiyasa na sake ki saboda ki samu damar auren wani”

“Aiko zaka gani dan sai kasan kayi hasarar mace irina”

Ta kaɓe masa Hijab ɗinta ta fice kamar zata tashi sama.

“Hakan be dace ba Hilal kana wasa da saki, daga wannan maganar zaka ce ka saketa
kuma kana ganin yadda take ta lallaɓaka akan ka barta ɗakinta...”

“Na faɗa miki babu ruwanki da irin maganganun nan, kin cika salo da saka kanki
cikin irin lamurran nan shiyasa komai aka yi sai a kin saka bakin ki shiyasa komai
ake ɗora miki laifi”

“Amman....”

“Na ce ki min shiru ko?”

Uffan bata sake cewa ba sai ta cigaba da wasa da kan Ezzah shi kuma ya juya ya
fice.

UZAIR POV.

Gaba ɗaya jikinsa yayi nauyi ji yake kamar idan ya motsa jikinsa zai rabu biyu,
idonsa kawai yake iya zagaye ɗakin da su. Hakan ya bashi damar ganin mutanen da ke
ciki a ɗakin ciki har da Abbah.

“Sannu Uzair, Sannu Allah ya baka lafiya”

Shine abunda kowa yake faɗa, sai dai shi abunda be gane ba, miya ke damunsa! Abunda
zai iya tunawa kawai yaji abu ya tsikare shi sai ya faɗi, daga nan be iya tuna
abunda ya faru.

Be iya amsa musu da komai ba in banda ido da yake binsu da su da kallo, har suka
masa sannu suka fice cike da tausayawa. Abbah ne ya zauna kusa da shi sannan
Mahaifiyarsa.

“Uzair ka ɗauki abunda ya faru da kai matsayin ƙaddara komai yana zuwa ne daga
abunda Allah ya rubuta maka, kuma haƙuri shi ne zai kai ka ga har kaga ka ci riba
ka samu a nan ka samu a acan”

“Wai mi yake faruwa da ni ne?”

Sai a lokacin ya samu damar tambaya.


“Uzair ka haɗu da matsala ne a ƙashinka na baya da kuma ƙashinka na ƙafarka, you
wouldn't be able to walk again”

“Taya taya za a ce mun haka bayan ba haɗri na yi ba, ba wani ciwo na ji ba haka nan
kawai za a ce mun na samu matsala”

“Nima abunda ya ba ni mamaki kenan, za a fitar da kai waje a duba lafiyarka”

“Abbah mi yake faruwa da ni ne?”

“Muma ba mu sani ba, likitan da ya duba ka ya tambaye ni wai ko ka taɓa haɗarin


mota nace masa aa, ko ka taɓa yi baka faɗa ba?”

Hawaye suka fara masa zuba.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Wannan wane irin bala'i ne? Miya faru da ni ne
haka, Hajiya ko dai mafarki na ke yi? Allah kasa na farka Allah wayyo ni Allah na”

Haka ƴa ɗinga maganganu Abbah sai kallonsa yake cike da tausayawa, suna haka sai ga
wasu friends nasa sun shigo duba shi ciki har da Dr Tahir, da wasu abokanin sha-
shancinsu na Abuja. Abbah suka fara tambaya ya mai jiki ya amsa musu da sauƙi
sannan suka gaishe da Hajiya dake ta sharar hawaye, suka matsa kusa da Uzair suka
tsaya suna masa ya jiki.

Amsa musu kawai yake amman kana ganinsa kasan ya rikice, ba fita hanyyacinsa yayi
ba, amman wannan ƙaddarar da ta faɗo masa ya gaza yarda da ita, ta ya zai zama haka
mutumen da ke tafiya lafiyarsa ƙalau shi ba faɗowa yayi ba shi ba haɗari ba ace ya
haɗu da wannan matsalar, ta ya haka zai faru?
Sun aje masa kuɗi mai yawa ban cin siyayyar da suka masa, Abbah na yayi musu
godiya, suka kama hanya suna Allah ya sauwaƙe, sai kawai Uzair ya ƙwalawa Tahir
kira, cikin sauri ya juyo ya nufo inda yake su kuma sauran abokan suka fice.

“Ina son mu yi magana da kai Abbah dan Allah ku ɗan ba mu guri”

Daga Hajiya har Abbah tashi suka yi suka fita, sai Tahir ya zauna a kujerar da
Abbah ya tashi yana fuskantar Uzair ya ce.

“Na je gida na samu baka nan, matar ka ce kawai, naje na saboda na ta buga wayarka
ban samu ba, kuma naje guest house ɗin ka baka nan, babu abunda matarka bata faɗa
min ba, har ɗan wuta ta kira ni, daman ta san kana wannan harkar ne?”

“Shekaran jiya ta gano, lokacin da na Amira ta aiko min da saƙo, ni zargin nake ma
ko ita ce ta yi min wannan asirin na koma haka ne? Da wannan daga gani lamarin iska
ne aljanu ne”

“Ko kuma Amira ba saboda ta dawo na samu labarin gurin Yayanta”

“Lallai zata iya min asiri, yarinyar nan muguwace”

“Zata maka ko kuma zai dawo kan ka idan na jikinta ya kare? Kasan fa bokan nan yace
maka idan be kama Namra ba, zai dawo gun ka ne, sai gashi ya kama Amira yanzu kuma
Amira ta dawo ina tunanin kai zai dawoma”

“Dan Allah Tahir kaje gurin bokan nan ka faɗa nasa halin da muke ciki, idan ma wani
ne yayi min ya san yadda zai yi ya kare shi, idan kuma wannan aikin ne ya kare shi
dan Allah Tahir”

Tahir ya dafa shi.


“Zanje karka samu damuwa zan je har can na masa magana duk yadda aka yi zuwa yamma
zan dawo na faɗa maka”

“Tahir ba sai yamma ba, kaje yanzu baka ganin halin da nake ciki...?”

Ya ƙarasa cikin kuka mai ban tausayi.

“Okay zanje yanzu Allah ya baka lafiya”

“Na gode”

Ya faɗa hawaye na zuba a idonsa. Jikin sanyin jiki Tahir ya fice yana mamakin
lamarin Uzair.

ASIM POV.

Yayi rama sosai a ƴan kwanakin nan da aka yi na amsar gaisuwa, Ranar da aka kwana
ɗaya da rasuwar Ƴan gidansu Mardiya suka zo har da Mardiyar gurin gaisuwa, a nan ne
yake nunawa wasu ita yana cewar ita ce matar da yake son aure.

Bayan an yi addu'ah uku ya ɗaure ya ƙara kwana biyu saboda masu zuwa ƙara masa
gaisuwa. A ranar ne Mama Inno ta raba yaran ta ɗauki Hajara da ƙanenta biyu wasu
daga ɓangaren mahaifinsu suka raba sauran ƴaƴan, abun gwanin tausayi, ranar Asim ya
ci kuka kamar zai haɗiye zuciya ya mutu dan baƙin ciki, ashe Mama bata da rabon ta
shiga gidan da yake da niyar sai mata, be taɓa baƙin cikin haɗuwa da Hajiya Sadiya
ba sai yau, ji yayi kamar ace tana kusa da shi ya kamata yayi mata gunduwa-gunduwa,
gashi ita kuma sai damunsa take da kira, yana ce mata bashi da lafiya.
Be yarda ya labartawa Nably abunda ya faru ba, amman yana faɗa mata bashi da lafiya
kuma tace zata zo ganinsa ya hana, ita kuma duk hankalinta ya tashi hakan ya hanata
komawa Abuja, dan ya faɗa mata ranar da zai dawo.

Ranar da bar sokoto sai da yayi kamar zai kashe kansa, gudu ya riƙayi da motar yana
kuka kamar zai tashi sama. Da wuri ya isa Katsina saboda ya tashi tun asuba ne, ɗan
kawai kar Hajiya ta gane halin da yake ciki ne yasa ya sauka nasarawa, dan yin
wanka ya shirya ya canja tufafi. Daga wankan har shirin be ɗauke shi minti talatin
ba, yana gamawa ya fito ya nufi gurin da motarsa take. Juyowa ya yi yana kallon
gidan.
Be taɓa jin yayi missing ɗin Namra ba sai yau, haka kawai yau da ya tuna ta sai
ya ji babu daɗi, daya tuna mamarsa sai Namra ta faɗo masa a rai, jikin rashin daɗin
rai ya nufi gidan Hajiya Sadiya.

Sai da ya kama hanyar gidan sannan ya kira ya faɗa mata gashi nan ya shigo katsina
har ma ya iso gidan.

“Okay okay galni nan zuwa”

Ko minti goma sha biyar ba'ayi ba, sai gata ta iso. Yayita ƙoƙarin danne damuwarsa
ya nuna mata mara rashin lafiya ne kawai matsalarsa, bayan sun zauna a falo yake
labarta masa yadda rashin lafiyar ta fara da fever kwanansa biyu asibiti.

“Gaskiya ka ji jiki sosai, ka rame Allah ya ƙara lafiya”

Da Amin ya amsa yana mata wani irin kallo wanda shi kaɗai yasan Manufarsa da kuma
abinda yake ji a ransa a tare da shi. Ta shi tayi ta shiga ɗaki dan ɗauko masa
apple ɗin, shi kuma ya fidɗo wayarsa ya aikawa Nably saƙo.

_Ki same ni a Dahir Exclusive Restaurant, yanzu ina gurin_


In few minutes ta masa reply.

_Okay on my way_

Ya aika mata da saƙon ne a yanzu dan ya samu ta fita gidan kamin Hajiya ta san wani
abu kai, dan yasan ba zata bari ta fita ba.

Ta daɗe a ɗakin sannan ta fito riƙe da farin ƙyale da kuma jika ƙarama mai kamar
hand bag, jakar ta fara jefa masa.

“Miliyan biyar ne a ciki, dan Allah Asim ka tabbatar ba a samu matsala irin waccan
karon ba, ka ɗauki abun nan da muhimmanci sosai”

“Ba za a samu matsala ba wannan karon na miki alƙawari”

Ya faɗa kamar da gaske. Sannan ya miƙa mata hannu, ta bashi apple ɗin ya ɗauki
jakar ya fice zuciyarsa har mazari take ya isa gurin da yake zaton Nably ta isa.
Yana shiga mota tana kiransa tace masa gata nan gakin gate.

“Gani nan zuwa yanzu”

Ya kashe wayar, a hanya ya tsaya ya siye wani Apple green, sannan ya ƙarasa
restaurant ɗin, yana fakin motarsa ya hangota tsaye jikin wata mota da yake zaton
ta tace. Tana hangoshi ta ƙaraso kusa da shi idonta tab da ƙwalla, ji tayi kamar ta
rumgume shi dan har ga Allah ta yi missing ɗinsa kuma tana son Asim sosai.

“Ya jikinka?”

“Alhamdullah”

Tare suka shiga ciki suka kama tebur, sai yasa aka kawo musu plate da ƴar ƙaramar
wuƙa sai fork. Apple ɗin ya fiɗo ya za a mata ɗaya ya ɗauki ɗayan mai green.

“Wannan ita ce tsaraba ta zuciyata na baki ita har abada, wannan kuma ki ɗauke ta a
matsayin zuciyarki ce Asim zai cinye”

Dariya ta yi mai cike da shauƙi da kuma so da ƙauna.

“Ai ka daɗe da cinye zuciyata, har ma da ganganjikina gaba ɗaya”

Ya kalli wayarta yana murmushi.

“Ki kashe wayarki kar wani ya dame mu da kira”

Ba musu ta kashe wayar, shi kuma tsoron yake kar Hajiya ta kirata.

“Bana son ki raga komai daga zuciyata. I love you”

“I love you too”

Ta faɗa sannan ta fara hanya apple ɗin ta tasoma ci kamar yadda shi ma ya fara cin
nasa, sai fira yake mata kamar gaske ita kuma sai faman murmushi tana faɗa masa
irin yadda ta yi missing ɗinsa.

Sai da suka gama cin apple ɗin sannan ya haɗa ma wayarsa alarm ɗin ƙarya ta yadda
zai yi kamar an kira shi.

“Ko na miki oder abinci...?”


“A'a na ƙoshi wannan zuciyar taka ba zata bar ni na ci komai ba”

Ya fiddo wayarsa dake saman cinyarsa, yana faɗin.

“Kai Ogaba na kirana”

Yayi picking cikin ladabi kamar gaske.

“Okay to gani zuwa”

Ya sauke wayar tare da miƙewa tsaye.

“Am so sorry Dear Wallahi ana nema Urgent, amman idan kin min izinin tafiya”

“Ba komai daman ni dai burina na ganka, kuma na ganka, take care of yourself”

“I will my love, ke ma ki kula min da kan ki, bari ma saukeki gida ko?”

“No da mota na na zo”

Sai da yaje ya biya kuɗi sannan suka jero suka fito tare, har gurin motarta ya
rakata ta kama hannunta ya riƙa ya ɗan murza, yana mai jin tausayinta a ransa, sai
dai kuma idan ta tuna Mama sai yaji babu wani tausayi a zuciyarsa. Sai da ta kama
hanya sannan ya nufi motarsa ya shiga.

SORRY MY FAN'S🙏
[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *84*

*Shafin na ku ne ƴan ZAGON ƘASA CONVERSATION I HEART YOU ALL*

Wani irin taku Abdallah yake mai ɗaukar hankali da burge duk wata mace mai
kallonsa. Ko da wasa be kalli gurin da Lamido yake ba, yayi kamar ma be san da shi
a gurin ba.

“Surprise...”

Namra ta faɗa tana tare hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata. Ɗaya daga cikin
murmushinsa mai tsadar nan ya ɗauka ya miƙa mata, yana kallonta cike da shauƙi dan
ta masa kyau sosai.

“Surprise is better than disappointed, haka naji turawa na faɗa, faɗa min wanda ya
saka idon nan nawa kumbura, na hukuntasa”

Ya faɗa dai-dai lokacin da ya ɗoro ƙafarsa saman matattakar balcony ɗin da suke
tsaye. Kallon mamaki na musamman Namra ta yi masa.

“Idon ka ko nawa?”

“Idon ki ai nawa ne”

Ya bata amsa kai tsaye, and yana acting like akwai wani abu a tsakaninsu. Saurin
kawar da maganar tare da cewa.

“Meet my Brother. Lamido meet Abdallah”


Lamido ya danne abunda ke zuciyarsa, na kalaman da ya ji Abdallah yayi a yanzu, ya
miƙa masa hannu.

“Am Aliyu Adam Lamido”

Wani kallo Abdallah ya watsa masa irin like sai a yanzu ma ya lura da shi, sai kuma
ya tsaya kallon hannun kamar mai karantar abu a jikin hannun. Sai kawai ya zuba
hannayensa duka biyu a aljihunsa yana ɗaga masa.

“Nice to meet you Lamido”

Ɗan murmushin ƙarfin hali Lamido yayi ya janye hannunsa, abunda be yi ma Namra daɗi
ba.

“Baka ga ne shi ba ne? Lamido ne fa wanda...”

“Na gane shi *ABNAM* let talk something important”

New name ɗin da Abdool ya bata ya bata mamaki yana abu kamar su ɗin daman can
masoyana, a ɗayan ɓangaren kuma bata jidaɗin kalmarsa ta ƙarshe da ya furta akan
Lamido ba. Sai kawai ta kalli Lamido ta ce

“Zan kawo maka keys ɗin kaje ka duba”

Kai kawai ya iya ɗaga mata, fuskarsa na nuna rashin jindaɗin da ke zuciyarsa.
Saukowa ta yi saman balcony ɗin ita da Abdool suka nufi ɓangare Abbah gurin da yake
sauke baƙinsa.

“Faɗa abunda yasa ki kuka mana Abnan”

“Abun farinciki ne da tsoro da mamaki a lokaci ɗaya”

“Kamar...”

Ajiyar zuciyarta ta sauke ta kai hannu ta tura ƙofar falon.

“Bismillah”

“Thank you”

Ya faɗa sannan ya saka ƙafafunsa cikin falon, sai da ya shiga sannan ita ta shiga
ta maida ƙofar ta rufe, sai ta nufi wata ƙofar da zata sadata da part Anty Amarya.

Bata samu kowa a falon Anty ba, sai kawai ta nufi ɗakinta dan labarta mata zuwan
Abdallah nan ma sai ta samu bata nan, ɗakin Aisha ta shiga.

“Ke Anty ta shigo nan?”

Ko kallonta Aisha bata yi hankalinta yana kan computer ta, ta kaɗa mata biro alamar
no. Namra ta janyo ƙofar ɗakin, ta nufi freezer tana ta tunanin abunda zata haɗa
masa, ya zo mata a bazata, bata shirya masa komai ba, Lamido ma bata masa komai ba,
su biyu ɗin sun zame mata ƴan uwa babu na wulaƙantawa a cikinsu. Hannu tasa ta dafe
kanta kamin ta kai hannu ta buɗe firiza ta ɗauko fruits ta haɗa masa fruit salad,
sannan ta haɗa tea da coffee ko wane one cup sai kuma ta ɗauki ƙaton ture ta ɗora
kayan sama. Wani tunani ya zo mata na ta canja tufafin da ke jikinta, kar kuma ya
ɗauka dan ta ganshi ta canja kaya he may think otherwise. Kai ta girgiza sai kawai
ta ɗauki turen ta nufi part ɗin Abbah.

Zaune ta same shi ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana kallon tv, sam ta manta ma bata kunna
masa tv ba. Ta dire turen gabansa tana faɗin.

“Na manta ban kunna maka kallon ba”

“Ai na kunna ni ba baƙo ba ne”

Yayi maganar cikin wata kalar murya.

“Ka zo unexpected, ba a shirya maka komai ba”

Ta faɗa tana ɗora fruit salad ɗin da Drink a saman wani ƙaramin tebur da ta janyo
ta aje gabansa.

“Tea or coffee?”

Ya daɗe yana kallon gashin kanta da ya buɗe kamar ba zai ce komai ba.

“Da rana”

“Ban san abunda zan kawo maka ba ne... Wai ka ɗan ci kamin na girka maka abinci”

Ta faɗa kamar wacce ta ji kunya.

“Ban zo dan ki girka min komai ba, i just come to see you, kuma na gan ki hankalina
ya kwanta”

Ya koma saman kujera ta zauna tana murmushi. Ya sauko da ƙafafunsa ya ɗauki fruit
salad ɗin ya fara sha, still idonsa na kan ta yace.

“Ba ni labari”

“Kamar na me...?”

“Komai da komai”

“Nothing new”

“Seriously! What bought Lamido here?”

“Oh... He's my new driver”

“Driver...?”

“Yep Abbah ya kawo min shi ɗazu, zan fara zuwa scul Monday shine Abbah ya samo min
sabon direba”

“Nice”

Ya faɗa kamar ba komai. Wayarsa ya fiddo ya kashe flash camera sannan ya shiga
ɗaukarta hoto ba tare da ta sani ba, dan yasan idan har yace zai ɗauke hoto ba zata
bari ba, kuma sisters nasa da Ummi sun dame shi akan suna son ganinta.
Haka suka ɗauki dogon lokaci a falon ita da shi babu wanda ya iya sake cewa
ɗan'uwansa wani abu, kowa da abunda yake tunani, Namra gaba ɗaya hankalinta ya tafi
akan halin da Uzair yake ciki, shi kuma hankalinsa ya tafi gurin Lamido dan yana
ganin kamar zai masa zagon ƙasa ne, taya zai zauna ya zuba mata ido shi ya riƙa
driving ɗinta scul ya sace zuciyarsa shi ya bar shi a nan.

“Zamu iya gaisawa da Abbah?”


“Yeah Yeah yes, bari na kira shi”

Ya miƙe tsaye tana taɓa kanta dan gaba ɗaya hankalinta ya tafi gurin wacan tunanin
nata.

Ƙofar da zata sadata da ɗayan falon Abbah ta nufa, tana tura ƙofar falon ta jiyo
muryar Abbah sai ruwan bala'i yake, shesshekar kuka na tashi, cike da faɗuwa gaba
ta shiga ɗakin Abbah, sai ta samu Anty Amarya da Hajiya Barau zaune ƙasan carpet ko
wannensu na kuka. Hajiya Barau ta rashi tana kuka ta fice daga falon, Anty Amarya
ta kama ƙafafun Abbah ta riƙe tana kuka.

“Dan Allah karka aikata abunda zaka dawo kana nadama a lokacin da bata da amfani,
dukanninmu ƴan'adam ne kuma ajizai masu yawan laifi da kuskure”

“Idan baki daina saka min baki a lamarin gidana ba, ke ma zaki haɗu da ɓacin rai
na...”

Juyawa Namra ta yi ta koma jikinta a sanyaye, ba tare da ta kalleshi ba tace.

“Maybe idan ka sake dawowa zaku gaisa”

“Why...?”

“Abbah is not in the mood now”

Hawayen dake idonsa ya zubo muryarta kuma ya soma rawa alamar kuka yana tare da
ita. Da sauri Abdool ya taso ya nufo inda take tsaye.

“Faɗa min Abnam, minene? You can't hide the truth”

“Mutumen da na taɓa baka labarin yace ƴana so na kuma ɗan luwaɗi ne, yanzu haka
yana asibiti cikin mawuyancin hali, kuma ɗazu ya tara mu ya faɗi gaskiyar duk
abunda yayi, ciki har da asirin da ya haɗa kai da Aminiyata Amira yayi min akan na
gudu na bar gida, sai gashi asirin be kama ni sai ya kama Amirar Amiyar tawa ita ta
gudu ta bar gidansu bata dawo ba sai ranar da na dawo garin nan...”

Ta ƙarasa cikin kuka.

‘Amira...’

Ya maimaita sunan a zuciyarsa, yana kallon zubar hawayen gimbiyarsa.

“Wannan ba abun kuka ba ne abun dariya ne da murna, amman komai daren daɗewa sai
gaskiya ta bayyana kuma mai haƙuri mawadaci”

“Aminiyata ce fa, ace ta min irin wannan aikin ai dole na yi kuka, babu yadda
ƴan'uwana ba su yi ba akan na rabu da ita amman na ƙi”

“Kin share hawayen ki, shiga ciki ki canja kamin na dawo, zan nuna miki wani abu”

“A'a Abbah ba zai bari ba”

“Zai bari just go”

Be jira amsarta ba, ya juya ya fice yana danna wayarsa.


MANAGE IT PLEASE 🙏
[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *83*

Cikin nishaɗi da walwalah ta isa gida, tana faka Motarta Hajiya Sadiya ta fito
hankalinta a tashe ta nufi inda take tsaye ta riƙa ta.

“Daga ina kike Nabila?”

“Mun ɗan fita ne da Asim, Lafiya”

“Na kira wayarki a kashe, ina kika je ne?”

“Munje cin abinci ne”

“Me kuka ci? Talk to me”

Ta riƙa fuskarta tana girgizawa. Itakam mamaki duk ya cika ta tashin hankalin da ta
gani a fuskar Mahaifiyarta ta ruɗa ta.

“Miyasa kika tambaya?”

Hannunta ta riƙa ta jata suka nufi cikin falon sannan ta zaunar da ita saman kujera
itama ta zauna fuskarta da damuwa ta ce.

“Ina tsoron kar ya baki wani abun ne, kin san mutane ba abun yarda ba ne”

“Hmmm Momi Asim ba irin mutanen da kike tunani ba ne, yana da kirki sosai”

“Ba daga nan take ba, Nabila ina fatar be baki Apple kin ci ba?”

“Ya bani apple kam kuma shi ma ya ci”

Ta dafa kanta ta sauko ƙasa ta riƙa hannayen Nably tana kuka.

“Wane irin apple ya ba ki? Na shiga uku na lalace, ya kai ki ya baro Nabila shi
kenan, tawa ta ƙare”

“Momi me ke damunki ne?”

Kuka ta yi sosai har hankalin Nably ta tashi sannan ta labarta mata abunda ta
shekara da shekaru tana aikatawa. Kuka Nabila ta saka zuciyarta ta cika da
baƙinciki.

“Asim yayi daidai idan har da gaske ya bani apple ɗin na ci, na cancanci mutuwa a
yanzu, ke ba uwa ba ce Momi, kin shirya kashe wata saboda tsiratar da ƴarki, kin
shirya aikata komai saboda duniyarki”

Ta tashi da gudu ta nufi ɗaki tana kuka, saman gado ta zauna tana kunna wayarta,
saƙon da ya shigo mata be bata mamaki ba saboda momi ta faɗa mata komai tun kamin
Asim yayi mata wannan saƙon.

_Apple ɗin da kika ci Mahaifiyarki ce ta ba ni tace na kaiwa tsohuwar mamata, bayan


kuma ta san na mutuwa ne, mahaifiyata ta ci ta mutu dan haka na yi ɗaukar fansa da
ke_

_Ba ka yi kuskure ba Asim, Mahaifiyarta ta cancanci fiye da abunda ka yi mata, ni


kuma na yi kuskuren yarda da kai, amman har gobe ina son ka_
Shine amsar da ta mayar masa, ta share hawayenta ta kwanta saman gado tana kallon
window. Yayinda Hajiya Sadiya take tsaye a falo tana ta buge-bugen waya akan a
taimaka mata kar ƴarta ta mutu, idan ta kira wannan tana kuka ta kira wannan duk ta
bi ta haukace sai kuka take kamar zata tashi gidan. jin kamar ƴarta na tari yasa ta
bar falon a guje ta nufi ɗakin tana kiran sunanta, amman ina Nably ta yi nisa har
bata iya magana, duk ta ɓata gadon da aman jini kamar wacce ta amaye hanjin
cikinta. Hannayenta biyu tasa tallafo kanta tana shafata.

“Nabila karki ta fi ki bar ni ke kaɗai kika rage min, na shiga uku na saka kai na a
halaka, wannan baƙar ƙungiya bata min rana ba”

Kallonta kawai Nabila ke yi a wahalce tana numfashi da ker, hawaye na bin fuskarta
har ta amsa kiran mahallicinta.

Wani uban ihu Hajiya Sadiya ta saki ta fita a ɗakin a guje, tana kaiwa harabar
gidan ta zame ta faɗi ƙasa ba sumammiya.

UZAIR POV.

Wasa-wasa yau kusan talatin da ɗaya ana abu ɗaya babu sauƙi, sau biyu ana fita da
shu waje amman babu abunda yake canjawa kuma ko ina aka je abu ɗaya ake faɗa cewar
ba zai sake tafiya ba.
Tun ranar da ya aika Tahir be gane kan maganarshi ba, sai yawo yake ta masa da
hankali, kullum da kalar abinda zai faɗa masa, kuma duk tsowon lokaci Yasmin bata
taɓa taka asibitin da sunan ta zo ganin Uzair ba, abunda ya bawa kowa mamaki ciki
har da Abbah. Ranar wata Lahadi duka ƴan'uwa suka saka ta gaba ana mata faɗa da
tambayar dalilin ƙin zuwa ganin mijinta, amman ta kasa furta musu komai sai kuka
take, a dole tasa suka ƙyaleta suka saka mata ido.

Ana sauran kwana biyu Abbah ya sake fitar da shi india, Tahir ya zo dubasa daman
duk bayan kwana biyu yake zuwa ya gansa.
Yau ya fi bashi tausayi fiye da ko yaushe, ya rame sosai kamar ba abokinsa ba,
wai yau Uzair ne kwance a nan baya iya komai, lallai duniya abun tsoro ce. Hawayen
da ya gani a idon Uzair ya tashi hankalinsa sosai hakan yasa yau ya yanke shawara
faɗa masa gaskiya, da kuma ba shi shawarar abunda yake tunanin zai zame masa
mafita.

Ajiyar zuciya Tahir ya sauke yana kallon Uzair ya ce.

“Na yi ta maka wasa da hankali akan maganar Malamin nan, magana ta gaskiya Uzair
mutumen baya raye, lokacin da naje gidansa na samu ranar ake sadakan bakwai nasa,
na ɓoye maka ne saboda karka tashi hankalinka”

Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Uzair, ya haɗe yawun bakinsa cike da tausayin
kansa ya ce.

“Tawa ta ƙare kenan! Haka ƙarshe na zai zo ni kuma? Ina ma ace mutuwa na yi na
huta...”

Tahir ya dafa ƙafaɗarsa ya matsa kaɗan.

“ina tunanin abunda ya fi, ka samu Namra da iyayenta ka yi musu bayanin komai, kuma
na nemu yafiyarsu, wata ƙila abunda ka aikata ne haƙƙi yake biye da kai, idan kuma
har ba haka bane, to Amira ce ta yi maka asiri, idan zaka fallasa komai ka fallasa
tare da Amira idan tana gurin, hakan zaisa guiwarta ta yi sanyi ta je ta kare
abunda ta yi maka”
“Zan aikata Tahir indai har wannan zai sa na samu lafiyata, amman ya za'ayi Amira
ta zo nan? Da wane ido zan kalli Abbah na ce ina son magana da Namra?”

“Zan kawo maka Amira, Namra kuma ka faɗawa Abbah kana son ganinta tare da Abbah”

Ya jinjina kai, shi dai ya shirya yin komai akan lafiyarsa, dan bai jin zai jure
zama a irin wannan rayuwar. Bayan Tahir ya fita Mahaifiyarsa ta dawo ɗakin daman
yanzu ita ce take jinyarsa ita da wani ƙanensa da kuma ƙanwarsa.

“Umma ina son ganin Abbah da Namra”

Ta kalleshi cike da mamaki.

“Ta maka me? Yarinyar da tun da ka kamu da rashin lafiyarnan bata taɓa cewa tana
gaisheka ba balle ta zo duba ka ita zaka nemi gani yanzu?”

“Zan yi wata magana da ita mai muhimmanci, dan Allah ki taimaka min itace kawai
mafitar wannan ciwon da nake yi, da ta zo zan samu sauƙi”

“Ban gane ba? Kamar ya itace mafitar ciwonka? Kana magana kamar wanda baya cikin
hayyacinsa, Uzairu cuta fa ba mutuwa ba ce”

“Ki taimaka min ki kawo min ita mu yi magana zan faɗa muku komai,ciki har da
dalilin daya sa Yasmin ta ƙi ta tako asibitin nan”

Da farko Umma ta ɗauka zafi ciwo ne yasa shi wannan maganar, daga baya kuma sai ta
fahimci yana cikin hankalin kansa, sai dai maganganun da yake sun ɗaure mata kai.

Tahir na barin gidan ya nufi gidansu Amira, kamin ya isa sai da ya kira yayanta ya
faɗa masa shi baya gida amman Amira tana gida. Harabar gidan ya shiga da motarsa,
sannan mai gadin ya shiga ciki yace ana sallama da Amira, bayan ƴan mintuna ya dawo
yace wai ance wanene?

“Kace Tahir ne abokin Big Bro”

Sai mai gadin ya koma, ya dawo ya ce wai ance ya shigo ciki. Ba musu ya doshi
babbar ƙofar Falon. Da sallama ya shiga Ammy ta amsa masa tare da Amira sannan ya
zauna, suka gaisa ya faɗa musu abunda yake tafe da shi. Ba Amira ba har Ammy ta yi
mamakin jin Uzair na son ganinta to me zai ce mata? Bayan duk abunda yayi mata,
daman tun da suka samu labarin bashi da lafiya Ammy da Abban Amira suke cewa wai
amanar Amira ce ta kama shi.

“Yana nemana kamar ya ? Me zai ce mun?”

“Nima ban sani ba, amman yace maganar tana da muhimmanci, sosai”

Ammy ta ce

“To ba zata ita kaɗai ba, tare zamu je, kuma sai Abbah ta ya dawo duk abunda ya ce
shi zamu yi”

Tahir ya miƙe tsaye yana faɗin

“Kamin na zo nan sai da na yi magana da Big bro, idan har wani abu ne mai cutar da
ke ba zai bari na shigo nan na faɗa miki ba”

“Koma dai minene sai mahaifinta ya dawo”


“To hakan yayi, ni zan wuce”

“A gaida gida”

Ammy ta faɗa sannan ta bishi da kallo har ya fice. Gaɓa ɗaya jikin Amira yayi
sanyi, zuciyarta sai yaye-yaye take mata, ta rasa dalilin da zai sa Uzair ya so
ganinta, to ko yana zargin tana da hannu a ciwonsa ne? Ko kuma wani abun ne kuma ya
faru? Maganar Abbah ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.

“Bari na kira Abbah ki na faɗa masa”

Kai kawai ta iya ɗagawa ta cigaba da tunanin da take.

NAMRA POV.

Bayan an gama bikin Maryam da Hindatu, Abbah ya shiga fafutukar nemawa Namra
Admissions a wata makarantar koyarda ilmin computer. Kasancewar duka jami'o'i a
yanzu sun gama ɗaukar ɗalibai, gashi kuma bata da komai a yanzu saboda ƙonewar da
takardunta suka yi a motarta lokacin da Asim ya taɓa haɗari, ba ƙaramin kuɗi Abbah
ya kashe ba wajen fito mata da tsofin takardun da suke makarantar primary da kuma
Secondary school. Jami'ah kuma sai next year zata fara, tun da ta riga ta lalata
karatunta tun a wacan lokacin.

Sai dai wannan karon kan Alhamdulillah komai ya zo da sauƙi, kasancewar Abbah ya
saki ƙuɗi cikin ƙanƙanen lokaci aka yi komai. Aiko murna gurin Anty Amaeya da Namra
ba a magana kamar su haɗe Abbah, dan jindaɗi.

Monday mai zuwa Namra zata fara zuwa makaranta, ranar Assabar da Safe Abbah ya kawo
mata sabon direba da zai riƙa kai ta makaranta, Namra ta yi murna sosai dan bata
tsammaci haka daga gurin Abbah ba.

“Abbah ka yi min abubuwan da ban yi tsammani ba, ka nuna min sosai, Allah ya ba ni
ikon saka maka”

Duk suka amsa da Amin har Anty Amarya dake ƙara jin son Abbah har cikin ɓargon
ranta. Namra ta ɗauki ɗankwalin abayarta ta yafa ta fita dan ganin sabon direban
nata. Tsaye tayi cak a baki ƙofa tana furta

“Lamido”

“Yes Ma'am”

Ya amsa a natse, yayi fari yayi kyau sosai ƙananna kayan da ke jikinsa sun ƙarɓe sa
sosai. Ta nunashi da yatsa sai ta kasa magana. Murmushi yayi ya gabatar da kansa.

“My Name is Aliyu Adamu Lamido your new driver”

“How.... How....”

Maganar ta laƙe ta ƙi fitowa sai ta sake nuna shi da yatsa.

“You...”

Murmushi ya sake yi yana kallon yadda ta canja ta yi kyau kamar ba ita ba, baƙin
nan nata sai sheƙi yake ga dogon hancin nan da farraren idonta da suka ƙara fitowa.

‘Black beauty akwai kyau’


A zuciyarsa yayi maganar a fili kuma murmushi yake mata mai ɗaukar hankali. Juyawa
ta yi ta koma cikin falon, cike da ruɗani ta kalli Abbah ta ce.

“Abbah da gaske shine sabon direba na?”

“Eh ko be miki ba ne?”

“Me direban yayi”

Anty Amarya ta tambaya. Zaunawa Namra ta yi tana faɗin.

“Anty Lamido ne fa”

“Wane Lamido kin san shi ne?”

“A gidansu na sauka Kaduna, shi ya ɗinga ɗawainiya da ni har kuka zo kuka ɗauke ni,
Lamido na gidansu Neina fa”

“Au shine? Ya akayi ya zo nan ne?”

“Nima ban sani ba, abun ya ɗaure min kai ne, Abbah ina ka haɗu da shi?”

“A can ƙamfani ya same ni, wai yana son a ɗauke shi direba idan zai samu, kuma baya
son na kamfani na gida yake so, kin san daman ni kuma ina neman direban da zai riƙa
kai ki scul yana maido ki, shiyasa na ɗauke shi”

Namra ta girgiza kai.

“Abbah why not ka ɗauke shi aiki a kamfanin ka, yayi degree fa, aikin ne be samu
ba”

“Ko zan ɗauke shi ba yanzu ba, sai naga gudun ruwansa, idan dai be miki ba za a iya
canja miki wani”

“Oh no yayi min, ba matsala Allah ya saka maka da alheri”

“Amin, yanzu sai ki tashi muje Asibiti, Uzair ya ce min yana son ganinki”

“Ni?”

Ta nuna kanta, ba ita kaɗai ba, har Anty Amarya mamaki ta yi.

“Ya za'ayi Uzair ya cw yana son ganin Namra? Kin yi wata magana da shi ne?”

“Anty ya za'ayi na yi magana da shi, tun da na bar garin nan har na dawo wata kalma
bata taɓa shiga tsakani na da shi ba”

“Ɗazu dai Mahaifiyarsa ta kira ni tace min dan Allah na zo da ke, Uzair yace zai yi
wata magana da ke mai muhimmanci”

“Ni gaskiya ba zani ba”

“Sai fa kin je, indai har zan baki umarni ki bi, bawan Allah nan ban san abunda ya
tare miki ba, daga kawai yace yana son ki, kuma na ga yanzu ko lafiyar jikinsa bata
ishe shi ba, ya aikamata ki je ki masa sannu”

“Zan je kawai bisa Umarnin ka”

“To tashi ki saka Hijabin ki”


Ba musu ta tashi ta nufi ɗakinta dan ɗauko Hijabin.

“Wai ko na taso muje har da ni ne?”

Anty Amarya ta faɗa tana kallon Abbah, dan taji me zaice, dan tana cike da son
sanin dalilin kiran Namra da Uzair yayi bata son a bata labari.

“Tashi muje komai dai son gulmarki sai kin ba su ɗaki sun yi magana”

Abbah ya faɗa da fuskar zolaya. Anty Amarya ta tashi tana dariya ta nufi ɗakinta.

Cikin ƙanƙanen lokaci suka isa asibitin, gaban Namra sai fat fat fat yake, duk da
bata san ta yi wani laifi ba, tana jin tsoron kiran da Uzair yake mata. Bama kamar
lokacin da suka shiga ɗakin ta yi ido huɗu da Amira, kallon kallon Akuya kallon
Kura suka riƙa yi ita da Amira, ko wannen kuma.ya kasa cewa ɗan'uwansa uffan. Daga
su har Ammy da Anty Amarya, Ammy sai faman hararar Anty Amarya take da Namra, Abbah
ne kawai ya gaisa da Abban Amira, sannan Big Bro ya gaishe shi, ya kuma gaishe da
Anty Amarya sai kuma ya kalli Namra fuskarsa da murmushi ya ce.

“Namra ba gaisuwa, kin san ni fa yayanki ne”

“Ina wuni”

Ta gaisheshi ba tare da tayi murmushi ba, ita hankalinta gaba ɗaya ya tattara ya
koma kan Uzair yanayin yadda ta ganshi ya bata mamaki, daman hausawa suka ce abunda
duk ya baka tsoro wata rana sai ya baka tausayi, gaba ɗaya ya tafi da imaninta, ya
rame sosai, ga ledar fitsari an saka masa ta ƙasanshi, saboda rashin tashin da
yake. A ɗayan ɓangaren kuma tana mamakin ganin Amira a ɗaki tare da iyayenta da
kuma abokinsa Tahir.

“Ka tara mutane a nan kuma baka ce komai ba”

Umma ta faɗa cikin rashin daɗin rai, dan bata so ya kira Amira ba, duk da bata san
dalilinsa na kiranta ba.
Ya ɗauki dogon lokaci kamin hawayen da suke masa zuba su tsagaita masa har yaja
dogon numfashi ya sauke, sannan ya soma magana.

“Abbah zaka iya tuna wani lokaci a baya da aka ce Namra ta gudu taje gurin Asim? Ni
na ɗana mata tarko tare da aminiyarta Amira, na bata sabon number da sunan zata zo
ta ga Asim a bayan gidansu su gaisa, alhalin ni ne ba Asim ba, bayan na ɗauke ta
sai abokaina suka canja min shawara da sunan kar na mata komai, na maidata a can,
abokina ne ya faɗawa mai gadin gidana abunda zai faɗa akan ya tsince ta a bayan
gidan ana ƙoƙarin yaga mata mutunci, kuma ana kiran sunan Asim... Kasan dalilin da
yasa na yi mata wannan sheri? Saboda ta tona min asiri akan abunda na ke aikatawa,
wato na neman maza ƴan'uwana, ba ƙarya ta faɗa ba, ta gan ni da gaske ina aikata
wannan abun, amman na ƙaryata ta ne saboda ina ganin kamar asirina zai tonu ne, a
lokacin, shine dalilin da yasa na ɓullo da maganar neman aurenta, sai ita kuma ta
ƙi yarda, sanadin hakan da kuma gudun karta tona min asiri abokina Najib ya kai ni
gurin wani boka muka mata asiri, yace sai an kawo rigarta da ita za ayi wannan
asirin, sai na samu Amira na biyata na faɗa mata haka kuma ta yarda ita taje ta aro
min rigarta da sunan ita zata saka muka kai akayi mata asiri da wannan rigar, daman
can bokan ya faɗa mana duk lokacin da ta saka rigar idan har asirin be kamata ba to
zai dawo kan mu ne, saboda Namra tana da ƙarfin addu'ah. Da asirin be kama Namra ba
sai ya kama Amira, sanadin hakan ta gudu ta bar gida, ban sake jin ɗuriyarta ba,
sai a lokacin da ta aiko min da wasiƙar cewar idan har ban je na kare wannan aikin
ba zata iya aikata min komai. A lokacin ne Yasmin ta gani, kuma ta gano abunda ya
shiga tsakanina da Adnan, wata rana ne da rana na shigo sai na tarar bata cikin
gidan, sai kawai na afkawa ɗa na, daman can nafi son yi namiji, tun daga lokacin na
keɓe Adnan ina jiyarsa bata gane ba, sai daga baya, sanadin hakan tace zata kai ni
kotu, ni kuma na ƙaryata gaskiyarta, Washe garin ranar ne Hajiya barau ta kira ni
ta faɗa min Namra ta dawo, daman ita take labarta min halin da Namra take ciki, da
kuma duk wani abu dake gudana a gidan...”

Tun da ya fara maganar be tsaya ba sai da ya kai aya. Idon Abbah sun rine sun yi ja
sosai, Abbah Amira ma kansa ya ɗaga sama ya maida hannayensa baya yana jinjina
lamarin. Anty Amarya da Ammy kuma suna hawaye, Amira kan kasa kuka ta yi duk ta
rikice jikinta sai rawa yake gumi na keto mata ta ko'ina.

“Miye dalilinka na faɗar gaskiya Uzair miyasa ba ka yi shiru da bakin ka ba? Miyasa
baka ɓoye sirrinka ba kamar yadda nima na ɓoye nawa? Ban yi niyar faɗawa kowa
abunda ka aikata ba Uzair, duk da rayuwar da na shiga ta fi wacce kake ciki a
yanzu, dan ni nafi ƙaunar irin ciwon nan naka na san zai sadani da lahira a nan
kusa, sama da jiran gawon shanu, jiran abunda babu ranar zuwansa. Ban taɓa tunanin
haka ba, na yi tunanin ka haɗa kai da Namra ne ka cutar da ni ashe ni na cutar da
kai na! Yanzu na fahimci dalilin da ya sa na gudu na bar gidan mu, kuma bayan na
gudu ban faɗa hannun ƙwarai ba, sai na faɗa hannun ɗan fashi, ya mayarda da ni
kamar matarsa, ta sanadinsa na ceci wani mutun wanda nake wa jiran gawon shanu, a
familynsu na zauna, ina ganin kamar wata sabuwar rayuwa zan shimfiɗa ashe a saman
wuta na yi shinfiɗar....”

Amira ta ƙarasa tana durƙushewa a gurin cikin wani irin kuka da yake jin kamar ta
haɗiye zuciya ta mutu ta huta. Lokuta da dama ta kan ji hakan idan ta tuna yadda
Abdool ya juya mata baya, mutumen da ta fi ƙauna fiye da komai a rayuwarta, a yanzu
haka bata da buri sai na shi, shiyasa ta kasa maida jikinta duk da tana tare da
iyayenta.
Gaba ɗaya Namra ta ruɗe ta kasa gane komai, daga Uzair ɗin har Amira kallonsu
take tana hawaye.

“Yasmin ta kasa samun fili a zuciyarta ta yafe min, saboda na yi mata sara ne a
baƙin wuya, amman ke na san zaki iya yafe min, duk da kema na miki illah, amman ki
dubi girman Allah ki yafe min ko Allah zai tashi ƙafaɗuna. Idan kuma har wani aikin
ne Amira ta yi min dan Allah ki je ki warware shi, saboda na tsorata da kalamin da
kika rubuta min cewar zaki ɗauki mataki. Ba zan iya jure zama cikin wannan rayuwar
ba, ki taimaka min ki yafe min Namra...”

“Ba zata yafe maka ba, ashe kai ne silar komai, Namra ba zata yafe maka ba...!”

Abbah ya faɗa a tsawace, har sai da Namra ta kalleshi. Ya nufi ƙofa a hasale ya
buɗe.

“Mamana wuce mu je”

Abban Amira yayi saurin riƙe Abbah.

“Haba ai babba baya haka, babba baya taɓa zama ƙarami, kuma tun da har yayi nadama
ya kamata ka yafe masa”

Abbah ya girgiza masa kai yana ɓanɓare hannunsa daga riƙon da yayi masa.

“Sake ni Alhaji, yaron nan be kyauta min ba, babu abunda ban masa ba a rayuwa, acw
ya rasa wanda zai yi ma zagon ƙasa sai ni da iyalina, wannan wane irin abu ne?
Yanzu da be shiga wannan halin ba babu wanda zai san gaskiya, sai dai ayi ta zargin
Namra, babu abunda ban ma yarinyar nan ba saboda shi, ashe tana kan gaskiyarta...”

Tuni Anty Amarya ta kama hannun Namra suka bar ɗakin, sannan Abbah ya rufa musu
baya. Bayan fitarsu Big Bro ya kalli Amira dake taugune a gurin tana kuka ya ce
“Kinji kunya wallahi kin ci amanar ƙawarki”

Ya ƙarasa tare da jan tsaki ya juya a fusace ya bar ɗakin. Baka jin kukan kowa a
ɗakin sai na Umma da Amira, dan Ammy hawaye kawai take, kamar yadda Tahir ke yi..

***

Kuka sosai Namra ta dinga yi a a motar har suka iso gida daga Anty Amarya har Abbah
babu wanda ya iya buɗe baki ya furta wata kalmar balle kuma ya bata haƙuri.
Inda suka bar Lamido a gurin suka same shi zaune, Abbah be bi ta kansa ba ya wuce
Anty Amarya ma haka, Namra ce ta tsaya dai-daice tana share hawayenta da Hijab
ɗinta ta nuna masa wasu ɗakuna da suke can gefen gardem.

“Kaje ka zaɓi ɗaya daga cikin ɗakunan can, zan kawo maka keys ɗin ɗakin anjima...”

Gaba ɗaya hankalinsa na kanta, ya tsorata da yanayin da ya ganta saboda ya tsani


zubar hawayenta.

“Allah yasa ba nine dalilin zubar wannan hawayen ba!”

“Ba kai ba ne, gaskiya ce ta yi halinta...”

Ta faɗa tana kallon sabuwar motar da aka buɗewa gate ta kunna kai a harabar gidan.
A gurin da aka tanada dan faka motoci, aka nufa da motar kasancewarta mai baƙin
gilashi baka iya hango wanda yake cikin motar. Ya ɗauki daƙiƙa goma sha biyar zuwa
ashirin kamin ya fito daga cikin motar. Gaban Namra yayi mugun faɗuwa hango Abdool
daya fito daga cikin motar sanye da farin yadi fuskarsa sai sheƙi take..
[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *85*

Bayan Abdool ya fita Namra ta koma cikin falon Abbah, har lokacin tana jiyo
shessehakar kukan Anty. Hannu ta kai ta tura ƙofar ɗakin Abbah ta tsaya daga bakin
ƙofa tana hawaye. Bata san abunda Abbah yayi ba ko yace, sai dai tasan yadda ransa
ya ɓace hakan nan dole sai wani abu ya faru.

Kallo ɗaya Abbah yayi mata ya ɗauke kai, ya zauna saman kujera yana kallon Anty
Amarya.

“Dan Allah ki tashi ki ba ni guri ni bana son hayani”

Unƙurawa Anty ta yi ta tashi tana cigaba da kuka ta fito sai Namra ta riƙa ta suka
nufi part ɗinta.

Saman kujera ta zauna tana kuka, Namra ta zauna kusa da ita ta kama hannunta ta
riƙe.

“Anty mi Abbah yayi? Miyasa kuke kuka?”

“Yace Hajiya ta tafi ta bar masa gidansa, nayi nayi da shi amman ya ƙi, taya zai
tura mace mai ƴaƴa da ƴawa kuma uwargidansa ya ce ta bar masa gida? Wannan sam be
dace ba, komai ta aikata aiko ƙyaleta yayi ya barta da kunyarta, gaskiya dai ta
riga ta bayyana babu abunda zata koma yi, amman yanzu ai ƴaƴanta ba za su ji daɗi
ba”

“Ya sake ta ne?”

“Be sake ta amman ya ce da tafi duk inda zata je sai ya nemeta”


“Idan ya huce zai maida ta Anty, kowa dole ne yaji baƙinciki ace da matarsa za a
haɗa kai a cuci iyalansa”

“Nasan abunda ta yi bata kyauta ba, amman ki duba ki ga halin da yaron nan yake
wannan kawai ya isaahe ta ishara, ita sai ya zuba mata ido ko dan ƴaƴanta, wani
lokacin mahaifinki yana rufe ido ya aikata abu kamar bai san kowa ba sai kansa”

“Zai dawo da ita, kawai ki bashi lokaci”

“Allah yasa”

“Amin. Abdallah ya zo”

Anty ta share hawayenta tana faɗin.

“Yaushe?”

“Yanzu ya tafi amman yace zai dawo”

“Na manta kin kaiwa Lamido abinci?”

Namra ta miƙe tsaye da sauri dan ita ta manta da shi gaba ɗaya.

Kitchen ta shiga ta haɗa masa fruits da drinks, ta dauƙa nufi waje. Zaune ta same
shi cikin ɗakin hannunshi a bakinsa kamar mai nazari.

“Sorry mun cinye abincin rana amman yanzu xan girka maku wani”

Janye hannunsa yayi yana murmushi ya karɓi turen ya aje yana faɗin.

“Kin manta da direban ki saboda sahibin ki ya zo”

Wani kallo tayi masa mai cike da mamaki.

“Kai da Abdallah duk matsayin ku ɗaya a gare ni”

“Ba ɗaya ba ne, Shi ɗan masu kuɗi ne”

“Kai kuma ɗan talakawa”

“Shi ɗan sarauta ne”

“Kai kuma ɗan bayi”

“Yana da matsayi a zuciyarki”

“Kai kuma baka da shi. Na gode”

Tana miƙewa tsaye shi ma ta miƙe yana ƙokarin shan gabanta.

“Am sorry ban yi dan na ɓata ran ki ba, kawai ina ganin ba zan taɓa taka matsayin
da Abdallah ya taka a zuciyarki ba ne, daga yau zan sauka a matsayin masoyinki,
daga yau ni yayanki ne”

Ya faɗa cikin muryarsa marar daɗi, kallonsa kawai ta yi ta ɗauke kai, ta fice. Tana
fitowa ta hango Abdool tsaye tare da Abbah suna magana, yadda Abbah yake watsar
haƙora zaka rantse da Allah ba shi ya gama yi ma Hajiya Barau faɗa ba. Har zata
wuce Abbah ya kira ta
“Mamana”

Sai ta ƙarasa gurin cikin ladabi.

“Ba ki ga ɗa na bane? Ko baki iya gaisuwa ba”

Ɗan risina tayi ta gaishe da Abdool suna haɗa ido ya kanne mata ido ɗaya ƴana
murmushin gefen baki.

“Mun samu ku lafiya”

“Lafiya ƙalau”

“Je ki shirya zaki zaka shi wani guri”

Abbah ya faɗa, har ta buɗe baki ta yi magana sai kuma ta yi shiru ta amsa da to
kawai ta nufi part ɗin Anty.

Ya kusan awa ɗaya yana jiranta sannan ta fito cikin ƙaton hijab, a lokacin Lamido
na jikin window yana kallonsu, a front seat ta shiga sannan yayi ma motar key suka
fita.

AMIRA POV.

Tun tana kuka hawaye na mata zuba har hawaye suka daina kukan kawai take ba hawaye.
Gashi tun da suka dawo gida Mahaifinta be ce da ita uffan ba, Ammy xw kawai take
bata magana.

Tashi ta yi ta nufi ɗakinta, tana shiga ta maida ƙofa ta rufe. Haƙiƙa ta yi rashin
abubuwa da yawa, ta rasa mutuncinta ta rasa martabarta ta rasa wanda take so yanzu
me ya rage mata?
Ta ci amanar ƙawarta dole ita taga ba daidai ba, tabbas hassada bata haifar mata
da komai ba sai nadama da dana sani. Da ace tun farko bata hassadar Namra da bata
yarda ta aikata abunda ya kai ta ga halaka ba, da ace ta zauna da ita da zuciya
ɗaya da duk wannan be faru da ita ba.
Yanzu gashi daga ita har Uzair babu wanda yake cikin rayuwar jindaɗi, Allah ya
jarrabeta da son Abdool idan ta tuna shi har ji take kamar zuciyarta zata rabe
biyu.

Bugar ƙofar ɗakinta Ammy tayi dan tana tsoron kar ƴarta ta saje shiga cikin halin
da ta shiga a baya, musamman yanzu da take ganin duniya ta juya mata baya.

“Amira an kira wayarki”

Miƙewa tayi tsaye taje ta buɗe ƙofar da idonta da suka kumbura sosai suka ƴi ja
kamar an zuba mata barkono a ciki. Hannu Ammy ta kai ta shafa fuskarta.

“Amira karki sa ranki a damuwa, dan adam be isa ya wuce ƙaddararsa ba, Allah ya
rubuto haka zai faru da ke babu yadda zaki yi, dan Allah kar zuciyarki ta sake
tunanin guduwa ki bar mu”

“Idan ma na gudu ina zanje? Ko wace mace bata da daraja sai a gurare biyu, gidan
iyayenta ko gidan mijinta, guduwa da na yi a wacan karon yasa na gane iyaye suna da
muhimmanci sosai a rayuwa, rashin zaman mace a gaban iyayenta yana karyarda
darajarta, wannan ne ya hana Abdool da family sa su kalle ni da daraja da ace ina a
gidan iyayena xauna wata ƙila da zai iya aurena”

“Wanene Abdool kuma?”


“Shine mutumen da ya hana zuciya sukuni, Allah yayi min jarawata ta nan ne, ina son
shi, shi kuma yana son wata”

Komawa ta yi ta zauna, Ammy ta zauna kusa da ita tana kallon ƴarta cike da damuwa.
A nan Amira ta faɗawa Ammy komai a zaman da tayi da Abdool da kuma wanda ta yi
kamin da haɗu da shi da yadda ta sadaukarda kanta gareshi.

“Kin sadaukarka da kanki gurin da bashi da amfani, kin salwantar da rayuwarki gurin
da ba a san darajar rai ba, kin yi sadaukarwar da ba zaki taɓa cin ribarta ba, kin
yi kuskuren da ba zaki iya gyarawa ba, kuma ina tsoron kar ɗaya daga cikin ƴaran
mutumen nan ya farauci rayuwarki, kin yi kuakuren ba rin zuciyarki ta kamu da son
mutum kamar wannan”

“Na sani, amman zuciya bata da laifi babu yadda ta iya, ina son sa Ammy amman shi
baya so na, be san hallaci ba”

NAMRA POV..

Ta share hawayen da suka zubo mata cike da tausayin labarin da Abdool ya bata.

“Amman wannan yarinyar ta cancanci komai daga gareka, ya kamata kai ma ka yi mata
hallaci, duk wanda ya sadaukarka da ranshi a gareka ya cancanci ko wane irin
sakamako daga gareka, da yanzu ta mutu kai ka rayu”

Murmushi yayi yana cigaba da tuƙinsa hankalinsa kwance.

“Ashe ko na cancanci ko wane irin sakamako a daga gareki, dan na daɗe da salwantar
da rai na akan ki”

“Kar zuciyarka ta raya maka abunda ba shi bane a Abdallah karka cuci kan ka ka
cutar da yarinyar nan”

“Namra baki taɓa tambayar kan ki miyasa Abdool yake son ki ba? Baki taɓa wannan
tunanin ba? Ko dan ban taɓa furta miki ina son ki ba?”

“Babu so agaban Namra a yanzu balle har ta yi tunanin dalilin na ka son, kar
zuciyarka ta yaudareka a yanzu Abdool ban shiryawa irin wacan rayuwar ba”

“Ashe ke ba mumuna bace Namra, har yanzu kina da sauran cikon imani a zuciyarki tun
da baki yarda da ƙaddara ba. Miyasa zuciyarki take ta nuna miki Asim kamar Abdool
yake, dan me kike tunanin irin rayuwar da kikayi a gidan Asim irinta zaki yi a
gidan Abdool? Mahaifiyata bata da buri a yanzu wanda ya wuce na maganar aurena da
ke, ina da ayukan yi da yawa Namra amman na danne su na tako garin nan saboda ke
kawai”

Hannu ya kai ya canja fm zuwa wata sannan ya ce

“Wata kila zuciyarki wani take so ba ni ba, na lura Lamido na da matsayi a


zuciyarki sama da ni”

Kalamansa da fakin ɗinsa sun rikita ta a lokaci ɗaya, ya faɗa mata abunda yau ma
Lamido ya faɗa mata, dan me suke ƙoƙarin saka ta cikin matsalar da bata daɗe da
fita ba?

“Miya kawo mu nan?”

A fili ta tambaya tana kallonsa, ba tare daya kalleta ba ya sauke wayar kunnensa
yace

“Zaku gaisa da yarinyar ne”

“Nan gidan su Amira ne”

“Ita ma yarinyar sunanta Amira”

Kamin ta ƙara wata magana sai ga Amira ta fito da gudu daga cikin gidan ta nufo
motarsu. Buɗe motar Abdool yayi ya fita sai tazo gabansa ta durƙusa ta riƙe
ƙafafunsa ta tada kanta sama ta kalleshi. Shi ma kallonta yake kamin ya janye
ƙafafunsa ya nuna mata front seat. Bata fahimci mi yake nufi ba, ta shiga ko kuma
ta buɗe ta gani, sai dai bata tambayeshi ba ta tashi tsaye ta nufi motar ta buɗe.
Ganin Namra yasa ta murmushi da hawaye a lokaci ɗaya.

“Itace?”

“Itace”

Ya amsa mata kai tsaye. Sai ta ƙara faɗaɗa murmiahinta.

“Kayi dacen mata, itama kuma ta yi dacen miji, congratulations Namra Allah ya baki
abubuwa da dama, ciki har da wanda na fi so sama da komai, Allah ya haɗa kan ku ya
baku zama lafiya”

Uffan Namra bata ce mata ba, har tayi surutunta ta gama ta koma gurin Abdool.

“Haƙiƙa kun dace da junanku, namiji irinka be dace da ko wace irin mace ba sai
Namra kamar yadda ita ma bata dace da ko wane miJi ba sai kai, na yarda da ƙaddara
haka Allah ya so ta kasance a gareni...”

“Amir...”

Ta ɗaga mishi hannu.

“Na fahimta, na gane ƙaddaratace a haka”

Bata jira abunda zai faɗa ba ta juya ta koma cikin gidansu, hawaye na mata zuba
kamar ruwa. Buɗe motar Abdool yayi ya koma ciki ya zauna yana kallon fuskar Namra.

“Itace yarinyar da ta cutar da ke ko?”

“Abunda ta yi min tsakanina da ita ne, kai kuma sadaukarwar da ta maka tsakanin ka
da ita ne, ka maida ni gidanmu ban yi tunanin ka ɗauko ni dan ka ɓata min rai ba,
na tsani yarinyar nan na tsane ta, idan ma kana son ta ni ina ruwana karka sake
kawo ni gurin, idan ma zaka so ka kaje can ka so ta ni karka sake sako ni a
matsalar ku”

Shiru yayi yana saurarenta har ta yi masa faɗan ta gama sannan ya tashi motar yana
murmushi ya suka nufi hanyar gida. Sarai kalamata suka wanke masa zuciya ɗan ya
fahimci inda ta dosa. Yana yin fakin ya buɗe motar ta fita a hasale ta shiga cikin
gida.
Wayarsa ya ɗauka ya kira Abbah suka yi magana sannan ya faka motarsa ya fita ya
shiga part ɗinsa.

Yayi awa ɗaya a part ɗin Abbah sannan ya fito tare da Abbah ya shiga motarsa ya
kama hanya.
KALSOOM POV.

FIVE MONTHS LATER...


Daga ita har su Izza basa da wata matsala a yanzu, tana zaune da yaran lafiya ƙalau
ga Hajiya sai nuna musu kulawa take. duk wani rashin kunya na Izza ta watsar, ulfah
kan ba a magana daman tun da warke daga jinyar ruwana zafi sai ta ƙara ladabi, dan
sosai yanzu suka gane muhimmanci Kalsoom, gashi lokaci-zuwa lokaci takan kira musu
mahaifiyarsu su gaisa, ranar weekend kuma Hilal ya kaisu gidan Hajiya. Idan zai
dawo Hajiya ta bashi rubutu ya kawo mata na neman ta sauka lafiya. Babu yadda Teema
ba tayi ba akan ta dawo gidan amman Hilal da Hajiya suka ƙi, su Izzah kan ko
zancenta basa so.

***
Bayan ta ƙare waya da Salma ne ta kalli Hilal dake kwance gefenta yana wasa da
wayarsa tace.

“Salma na gaishe ka”

“Ina amsawa, bari naje na ɗauko su izza scul”

Ya faɗa yana unƙurin tashi, kai kawai ta ɗaga masa dan maganar ma wahala take mata
ko wayar da take da Salma na ƙarfin hali ne, tun jiya take jin abu amman ta kasa
faɗa, duk da ta kan ji irin haka lokaci lokaci amman wannan ya tsananta mata da
yawa. Aiko kamar karya tashi daga gurim ta soma jin ana tsikararta, har zaman ya
gagareta sai da ta kwanta.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Shi take ta maimaitawa tana rumtse rumtsen ido. waƴarta na kusa da ita amman ta
kasa miƙa hannu ta ɗauka, wani irin juyi take jin duniya na mata, tun tana faɗar
Innalillahi a hankali har ta fara yi da ƙarfi tana ta rumtsar ido da buɗewa kamar
wacce ta ci bashi. Ko da Hilal ya ɗauko su Ulfah daga makaranta Kalsoom ta jigata,
jini har ya fara mata zuba, daman tun safe ya kula da yadda cikin yayi mata ƙasa
sosai. Ɗakinsa ya shiga ya ɗauko kayan karɓar haihuwa ya dawo ɗakinta ya shiga ya
rufe ƙofar ya shiga bata taimako, because ya san it too late yace zai ɗauke ta suke
asibiti a yanzu bayan ga har kan yaro ya fara fitowa😷

ASIM POV.

Tun bayan rasuwar Mama ya daina ganin kam kowa da gashi, gani yake tun da yayi
losing mahaifiyarsa a yanzu baya gudun komai, haka zai shigo cikin sokoto ya kwana
gurin ogansa, ba zai leƙa ƙanensa ba sai zai tafi sannan ya basu kuɗi mai yawa,
babban gida ya siya musu, dan yana ganin kamar su ne family da suka rage masa
yanzu. Sai duk lokacin da ya shiga sokoto sai ya binka labarin Namra ace masa tana
nan lafiya, har wani ya ɗauka mai aikin bincika masa labarinta, dan a tunaninsa
tana nan ɗauke da cikinsa, burinsa kawai ta haifa masa ɗan ko ya ya ɗauke ta dan
kawai ya ɗasa mata baƙin ciki. Sati ɗaya da rasuwar Mama aka saka ranar aurensa da
Mardiya, yadda yake kashe mata kuɗi sai ka rantse da Allah shi ne yake buga kuɗi,
dan yana samun kuɗi sosai a yanzu manyan mutane yake tare da su. Ya faɗa musu baya
buƙatar komai dan tun kamin a kai lefe ya saka komai a gidan da zata zauna, kama
daga kayan kitchen har zuwa na kwalliya da sutura kai kace ma be mata lefen gaba
ɗaya ba sai taje can, har kayan abinci babu abunda be zuba ba, freezer goma ya saka
a gidan jo wace cike take da kayan daɗi.
Ranar talata aka fara event an zubar da naira a kamu sosai kasancewar Asim ya
bawa kawaye amarya kuɗi sosai, gashi shi ma yaje shi da abokaninsa dan yanzu yayi
sabin abokai yayan manya sai kuma masu irin aikinsa, duk wani gaye mai kuɗi da
kasani a cikin garin katsina mai ji da kansa sai Asim yayi abota da shi, dan gani
yake sune sa'o'insa.

Friday aka yi walima, a instagram Namra take ganin bikin kamun su, tayi mamakin da
ya auri Mardiya dan bata manta lokacin da yake yawan maimaita mata cewar shi sai
ƴar da ubanta ya fi nata kuɗi zai aure, wata ƙila farin jikinta ne ya jashi
hankalinsa ko kuma bayan ya aureta zai ƙara wata.

Tun ranar da aka gyara ɗakin aka saka komai Asim yake kwana a gidan. Wasu abokansa
da suka zo daga sokoto da Abuja sai ya kama musu hotel wasu kuma ya sauke su a
ɗayan gidansa dake GRA, shi kuma ya koma Light up road inda gidan amaryarsa yake
dan kwana. Light up unguwace ta masu kuɗi ko wanne gida ka gani sai ya burge ka,
amman duk da haka a layin da Asim yake gidansa ya fi ko wanne gida kyau da tsari,
kana ganinsa kasan ba ƙananan kuɗi aka kashe ba gurin gina shi.
Ƙarfe ɗaya da rabi na dare ya shigo gidan, cikin wani irin yanayi marar
misaltuwa, yana jinsa a wani matsayi na daban kwatankwacin matsayin da ya riƙa jin
kamsa a lokacin da zai auri Namra, freezer da ke kitchen ya nufa ya buɗe ya ɗauko
power horse ya fito falo yana sha. Kansa ya ɗaga sama yana kallon pop zuwa
labulayen da aka saka falon, hantin kawai idan ka kalla sai ya burge ka, balle kuma
kujera da plasma da flowers, daga kujera har center carpet da labulayen da da
fantin ɗakin milk and red ne, dinning area kuma aka ƙawata gurin da red color.
Relaxing yayi sama cushion yana furta sunan Namra, a zuciyarsa, haka kawai ta faɗo
masa a rai, duk wacan dukiyar da aka narka masa a wacan gidan da Namra ta kama musu
haya ubanta ne ya narka masa ita yayinda wannan kuma shi ne ya narka ma Mardiya.
Haƙiƙa Namra ta yi masa hallacin da ba duk mace ce take yi ma namiji irin wannan
hallacin ba.

“Dole wata rana zaki dawo gare ni Namra, dole idan kika haifa min ɗa ki dawo kina
so na idan na karɓe abu na, zaki dawo ki ga yadda Asim yake amsa sunansa a cikin
garin Katsina, daga lokacin zan nunawa Ubanki iko na da kuma karfin kuɗi na”

Ya furta yana jefar da kwankwanin power horse ɗin sannan ya ciro wayarsa daga
aljihu ya nemo number Sufiyan ya aika masa kira, be damu da ganin dare yayi ba
ganin yake tun da yana biyansa kuɗi dole ne ko a wane lokaci ya yi masa abunda yake
so.

“Hello oga Allah yasa lafiya ka kira ni a wannan lokacin”

Ya faɗa cikin muryar bachi.

“Lafiya ƙalau, kana da labarin Namra? ”

“Akwai labari oga amman da ka hakƙura har da safe”

“Ba zan haƙura ba, faɗa min kawai”

“Oga wannan monday da ta wuce ta fara zuwa makaranta, na bita har makarantar na
ganta Mahaifinta ya ɗaukar mata sabon direba, amman oga sam babu alamun ciki a tare
da ita, dole ne idan har akwai cikin da zai tsawon wannan watannin ya nuna ko da
kaɗan nan, sam ban ga alamun tana da ciki ba, kuma kaga da tana da ciki da ba zata
koma karanta ba yanzu”

“Ka tabbata?”

“Na tabbata oga”

Ya katse kiran yana lasa lips ɗinsa.

“Idan ko har kika yi kuskuren zubar da cikin nan sai kin yi nadama Namra, ke da
ubanki sai na kaskantaku”

Yayi ƙwafa tare da busar da iskar bakinsa. Ɗan kishingiɗawa yayi kaɗan sai bachi
yayi gaba da shi daman a kwai gajiya sosai a tare da shi. Be yi bachin awa biyu ba
ya soma jin hancins ana mugun yaji numfashinsa na sama-sama sai sarƙewa yake, ba
shiri ya farka a firgice sai hayaki ya turniƙe masa ido, duhu ya soma gani sai tari
yake kamin ya waiga ɗayan gefensa ya hango bedrooms ɗin suna ci da wuta. Wani irin
tsalle ya daka ya sai gashi gaban ƙofar falo yana ƙoƙarin ɓanɓanreta amman ina
hayaƙi da tsage ƙofar. Mai gadinsa ne ya farko yaga halin da ake ciki ya fita neman
jama'a abunka da unguwar masu kuɗi sai kowa yayi maaa banza sai gaba ɗaya mutane
suka fiffito, daker aka samu aka ɓalle ƙofar falon, suka fito da Asim, domin
hayaƙi ya turniƙe shi tuni ya faɗi a gurin yana haƙi.

Kan kace kwabo sai ga ƴan fire service mota kusan uku aka shiga kashe wutar, amman
kamar ana ƙarawa, haka wutar ta riƙa ci har asuba, bata mutu ba sai da ta ƙone
komai na gidan.

Ta ɓangaren Mardiya ma ƴan kashe wutar gobara ne suke ta kai da koma amman wutar da
ƙi mutuwa, babu abunda yaba jama'ah tsoro kamar yadda wutar take ta sama kamar abar
da ake sawa fetur, ba ɗakinsu wutar da tashi ba, amman bata rage komai da yake
ɗakinsu Mardiya ba, har da kayan baƙi ƴan zuwa biki sai da wutar da cinye, sannan
ka bi sauran ɗakunan gidan duk ta cinye.

Mardiya na maƙota aka faɗa mata, daman tun da aka fara bikin maƙota take kwana
ita da ƙawayenta, ko da ta zo wutar ta ci har ta cinye babu abunda ya rage a cikin
gidan, a take ta saka kuka ganin komai ya ƙone babu abunda take ji kamar kayan
mutane da suka ƙone, babu daɗi ace kaje biki wani abu ya faru. Bata ƙara firgicewa
ba har sai da wani abokin Asim ya zoɓya labarta mata halin da suke cikin ma ƙonewar
da wacan gidan yayi wanda za a kaita.

Hannu ta ɗora saman kai ta fashe da kuka tana kiran ta shiga uku.

“Allah yasa ba wutar da nake mafarki bace take bi na ba, na shiga na lalace”

Kuka ta riƙa yi kamar mahaukaci sai da ka riƙeta ana bata haƙuri.

RASHIDA POV.

Bayan ta gama sallah azahar ta tashi tayi nafila sannan ta ɗauki carbi tana lazimi,
haka take kullum cikin ibada take fatanta kawai Allah ya yafe mata kamar yadda
mijinta da Kalsoom suka yafe mata, a iya yanzu ta yarda da ƙaddarar da Allah ya
aiko mata kuma ta aminta babu mai iya yaye mata ita sai Allah, tabbas tasan Allah
yana son ta tun da har ya ganar da ita tun gabanin ya karɓi rayuwarta.

Ta miƙa lamurranta ga Allah, kwata-kwata ta cire rayuwar daga yin aure dan tasan ba
zata samu mijin da zai aureta ba, da ma kuma ta samu bata tunanin zata iya zama
aure da namijin wanin Hilal. Daman ta daɗe da aje aikinta, duk wani abunda da take
da buƙata Mahaifinta yana yi ma, abokanta kuma suna kawo mata ziyara a gidan,
waɗanda suka wayanci miye hiv wasu kuma tuni sun ƙaurace mata gudun kar suma su
ɗauka.

Ta ɗauki darasi a rayuwarta sosai, tun daga cin amanar aure da tayi, da kuma neman
taimakon wanin Allah wato bokaye da ƴan duba, a iya kallon rayuwar Kalsoom da tayi
ta fahimci darasin da yake tattare da itazm, tabbas wanda duk ya miƙa lamurransa ga
Allah, lallai Allah yayi alƙawarin jiɓantar al'amarinsa, babu irin shige-shige da
bata yi ba wajen ganin da raba Kalsoom da Hilal ko ta raba ta da lafiyarta amman
addu'o'in da take suka mata kariya da katangar tsari daga duk wani sherinta. Hakan
yasa itama ta tattara lamurranta ta miƙa wajen Ubangiji, ta samu natsuwa da
kwanciyar hankali sosai, duk da tasan ciwon dake jikinta ba zai taɓa rabuwa da ita
ba, amman tana Allah ya sanyaya mata zuciyarta har ta samu ƙarfin halin sakewa tana
fita cikin mutane.

Bayan ta gama istigifari ta ɗauke carpet ɗin ta naɗe ta maida mazauninta, sannan ta
nufi kitchen dan ɗora abunda zata ci. Vegetables soup ta girka da white rice daman
likita yana yawan faɗa mata ta riƙa cin su. Falo ta fito ta zauna tana cin
abincinta hankali kwance tana kallon tv, wayarta ce ta yi ringing sai ta miƙe tsaye
ta ɗauko, murmushi ta yi ganin number Hilal a zatonsa zai sadata da su Ulfah su
gaisa ne sai kawai ya miƙawa Izzah ta yi masa albishir ɗin Anty su ta haihu.

“Mashallah me aka samu?”

“An samu Baby boy, Momi Mai kyau sosai”

Wannan karon Ulfah ce take magana.

“Allah ya raya ashe kun samu ƙane ko? Ina dady ku?”

“Yana can gurin Anty be san mun kira ba, Momi Boy ɗin kato ne sosai kuma fari”

Ezzah ta faɗa with so much joy and excitement. Idon Rashida ya cika da ƙwalla dan
har gobe har jibi tana son mijinta sai dai tasan yayi mata nisa.

“Zan zo gobe na ga Baby kun ji”

“Toh Momi”

Suka kashe wayar, ita kuma ta share hawayen idonta tana tuna lokacin da ta haifi
Rafiq yadda Hilal ya dinga ɗauki kamar zai haɗeta ita da yaron.

‘Allah sarki duniya’

Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuma sai ta amsa salamar da Alhaji Bashir yake
yayinda yake turo ƙofar falon ya shigo.
[7/21, 10:29 AM] Khadeeja Candy♥: *86*

“Miya kawo ka gidana?”

Murmushi yayi ya zauna saman kujera yana kallonta fuskarsa da annuri.

“Haba Hajiya ai ko baki san inda na fito ba kya saurara min ko?”

“Na fi ƙaunar ganin baƙin maciji da kai, bana son abunda zai sake kusantar da ni a
gareka Alhaji bashir dan Allah dan Annabi ka tashi ka fitar min daga gida”

“Ban zo gidanki da wata manufa ba Rashida sai ta alheri”

“Babu alheri a tare da kai, dan Allah ka tashi ka bar min gidana”

“Miyasa kike alaƙanta rayuwar da kika shiga da laifina? Bayan kuma idan baki amince
ba ba zan iya miki da ƙarfi ba?”

“Nasan nayi kuskure ai a lokacin shiyasa yanzu na tuba na koma gurin Ubangijina,
kuma Alhamdulillah rayuwata da dai-daita”
“Nama ai tuban na yi shiyasa nake son dai-daita rayuwa da taki, har ga Allah
Rashida ina son ki ba wai so na zina kawai ba, so na haƙiƙa kawai saboda babu yadda
zan yi ne, ni da ke kukan mu munyi kuskuren faɗawa a halaka, ke saboda baki da
lokacin da zaki tsaya ki bawa mijinki kulawa shi ma kuma ya baki, ni kuma na kasa
ƙara aure duk da ina ganin sha'awar wasu matan saboda sherin da matata ta yi min,
yanzu kuma Alhamdullillah na gane kuskurena kuma am ready to marry you idan kin
aminta, saboda kin rufa min asiri a lokacin da ya kamata ki tona min, kin rufe
bakin ki kin haƙura kin bar ni akan aikina, bayan kuma kina da damar da zaki tona
min asiri, ki faɗawa duniya abunda muka aikata”

“Ban shirya aure yanzu ba Alhaji Bashir idan ma shi ya kawo ka ka tashi ka bar min
gidana”

“Kin fi son ki yi ta zama a haka? Indai akan Asmee ne karki damu bata isa ta hanani
ƙara aure ba yanzu”

“Baka tsoron ace ka auri mai cutar ƙanjamau?”

“Daga lokacin da kace zaka damu da matsalar mutane zaka saka kan ka ne kawai cikin
matsala, ni da ke da Asmee duka muna ɗauke da abu ɗaya, miye amfanin ke na ƙyale ki
akan gudun abunda duniya zata ce min? Zan yi ritaya gudun kyamar da za a nuna min
gurin aiki, amman karki manta ina da hannu jari kuma ina da kasuwancin da zai iya
riƙe jikokina ma ba ƴayana da matana kawai ba, ki yi tunani Rashida karki yaudari
kanki akan abunda zuciyarki take muradi”

Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya fice. Da kallo ta bishi tana sauke ajiyar zuciya,
sam bata shirya irin wannan rayuwar ba, aure yanzu? Ita da yanzun tana jin ta samu
sukuni a rayuwarta, taya zata yi aure ta sake jefa rayuwarta cikin wani halin kuma?
Ita kan bata shirya kishi da Asmee ba.

KALSOOM POV.

Hilal kamar ya haɗe yaron dan murna, duk wanda ya ga Baby boy ɗin sai yayi mamaki
ace da kanta ta haihu musamman da suka ji gida ta haihu, wasu daga cikin abokansa
suka riƙa zolayarta wai ai matar doc ce dole ya karɓi haihuwarta. Hajiya ta nuna
farincikinta sosai duk bayan kwana biyu sai ta zo gidan duba jikanta, Salman kam
kullum tana biye da hanya, sai da aka kwana uku sannan Rashida ta zo ganin Baby shi
ma kuma da dare, ta yi siyayya mai yawa ta kawo, sai dai bata yarda ta karɓi yaron
ba duk da Kalsoom ta yi kawaicin miƙa mata shi, bata yi minti ashirin a gidan ba ta
fito su Ulfah suka rakota har bakin mota ta basu kuɗi da chocolate.

Ranar suna Baby ya ci sunan mahaifin Hilal wato Abubakar aka yi masa laƙani da
Rafiq. Fuskarsa sak ta Hilal yaro ya sha stickers har ya gaji, an raba abubuwa da
yawa ranar sunan, da yamma aka yi walima ta gani ta faɗa, kuloli da manyan kofuna
da agogo sai har ma da handbags masu kyau, wasu kuma su samu shoes.

An kashe kuɗi da yawa gurin walimar nan kai kace ma yanzu ne Hilal yake samun
haihuwar fari, yadda ya zuba mata kayan barka ma a abun kallo ne, ga kuma waɗanda
ta samu daga ɗai-ɗaikun mutane ƴan uwa da kuma abokan arxiki.

ABDOOL POV.

Tafiya yake shaddar dake jikinsa tana amsa amo saboda maiƙon da ke jikin shaddar da
kuma sabuntakarta.

Ko da ya shigo part ɗin Ummi yana waya da Mai Martaba dake faɗa masa yana nemansa,
a falon ya zauna sai da suka gama tattaunawa sannan ya kalli Ummi da ke cikin
shirin ta na fita ya ce
“Ummi fita zaki yi?”

“Eh Asibiti zan je na duba Hajiya Sadiya kasan ciwon nata ya zama abunda ya zama,
kuma kaima ya kamata ace ka duba ta, tuɓ da ta kwanta asibitin nan baka taɓa zuwa
duba ta ko sau ɗaya, wai anya ma ka mata gaisuwar yarinyar ta da rasu?”

Ya shafa kansa yana murmushin rashin gaskiya.

“Kin san ko da ta rasu ina Abuja, amman dai na kirata a waya”

“Abdallah baka da kirki sam, kai kullum aiki ƴan uwanka ma baka da lokacin
ziyartarsu? Sai yaushe zaka huta ne?”

“Ai yanzu zani iya zuwa na mata gaisuwar daga nan na duba jikin nata”

“Allah ya sauwaƙe maka wannan rayuwa, wai ya maganar yarinyar nan ne?”

“Muna nan muna ta sutsa kai, yanzu haka maganar da Mai Martaba yake min kenan, yace
min yayi magana da Abbah”

“Ban gane ba, ita bata son ka ne?”

“To gani dai wani ne yake min zagon ƙasa, ita kuma tana min jan aji, yanzu haka
anjima kaɗan gurinta zanje, domin hankali yaƙi kwanciya tun lokacin da yaron nan na
zo gidansu, last week ma da naje gidan kamar...”

Sai kuma ya fasa maganar ya miƙe tsaye.

“Muje na dubata Ummi, sai na wuce airport flight zan hau”

“Ka fara bani labari baka ƙarasa ba, zan ƙarasa”

“Zan ƙarasa miki idan na dawo”

“Ƙanenka dai ga su nan sai himmar fitar da maza suke kai kana nan”

“Nima ina kan hanya”

Dariya ta yi ta miƙe tsaye suka fita tare. Kai tsaye asibiti suka nufa, ko da suka
shoga ɗakin tana kwance wata ƴar'uwarta tana jinyarta, ta rane sosai bakinta duk ya
bushe, Abdool ya ji tausayinta sosai da sosai, duba da yadda take damawa kuma gata
mai jiki amman yanzu ta dawo haka. Tana ganin Ummi ta fara hawaye.

“Nikan tawa ta ƙare, Nabila ta tafi ta bar ni”

“Kiyi haƙuri Hajiya Sadiya duk mai rai mamaci ne, duk haka ƴaƴanki suke mutuwa kuma
ki haƙura, na san Nabila ita kaɗai ta rage miki amman Allah baya barin wani dan
wani, dan Allah ki sawa zuciyarki sassauci”

Shiru bata ce komai ba, sai hawaye take ita kaɗai ta san dalilin mutuwar Nably kuma
ita kaɗai ta san dalilin wannan ciwon nata.

“Sai Yaushe zasu sallame ki ne?”

Ummi ta sake tambaya. Wacce ke jinyarta ta kada baki tace

“Ba yanzu ba, wai sai sun mata aiki”


“Aiki kuma?”
.
“Eh wai wasu abubuwa ne a cikinta masu kamar ƙanƙara sun ce dole ne sai anyi aiki
za a cire”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. To Allah ya sauwaƙe, amman da waje aka je naga
sun fi ƙwarewa a irin aikin nan”

“Nima haka na ce mata, amman ta ƙi”

“Allah ya bata lafiya ai da nan da can duk ɗaya a gurin Allah”

Wannan karon Abdool ne ya faɗa yana kallon agogon hannunshi. Dubu talatin da ƴar
siyayya Ummi ta aje mata sannan suka taso muna mata Allah ya sauwaƙe ya bata
lafiya.

A mota Ummi take ta labartawa Abdool irin rayuwar da suka yi ta ƙurciya, yadda aka
riƙa ta a gidansu da kuma irin nasarorin da tada samu a rayuwarta.

“Kai Mai rai ba komai ba ne”

Abdool ya faɗa yayinda yayi parking a harabar gidansu. Cikin yanayin damuwa da
jimami Ummi ta fita daga motarsa, shima ya fito yana faɗa mata yanzu zai kama
hanya.

“Allah ya tsare ya kiyaye ya kuma kai ka lafiya”

“Amin Ummi”

Sai da ya shiga part ɗinsa ya fito, sannan ya shiga wata motar direbansa yayi
driving ɗinsa zuwa airport.

***

An sake fitar da shi waje kamar yadda Abbah yayi alƙawari, sai dai tun daga lokacin
Abbah be sake leƙa asibitin da sunan yazo ganinshi ba, wani kuma daga gidan be sake
zuwa ba, duk da ƴan'uwa sunta ƙoƙarin shiga tsakani na ganin an sasantashi da
Abbah, amman Abbah be saurara ba dan ya riga ya bashi baya a yanzu, kuma duk wanda
ya ji dalilinsa dole yayi masa uzuri, dan kaf a ƴaƴan ƴan'uwa Abbah ya fi son Uzair
da kowa. Babu wanda be yi mamakin jin abunda Uzair ya aikata ba na neman maza
ƴan'uwansa, a lokacin ne wasu ke cewa ashe Namra tana da gaskiya, wasu kuma su
labarta tsegumi da zargin da suka ji ana masa, daman abun duniya baya ɓoyuwa. Har
kuma tsawon lokacin Yasmin bata taɓa zuwa ta duba shi ba ko da sau ɗaya. Shi kam
duk ya biya rame ya lalace, sauƙi ɗaya ya samu yanzu yana iya tashi zaune,ko ya
kwantar da kansa, kuma ya kam miƙa hannunsa ya ɗauki abu ko ya karɓo, sai dai bayan
haka babu wani abu da yake iyayi ma kanshi.

Bayan ya gama cin abinci likita ya shigo ya duba shi, ya bashi magani sai kuma yayi
masa allura, sannan ya rubuta wasu ya bawa Umma yace a siyo masa su. Sai da ya fita
Umma ta rafka uban tagumi tana kallon ɗanta, tabbas be kyautawa kansa ba da ya saka
kansa a wannan rayuwar, gashi yanzu kowa ƙyamarsa yake ana masa kallon kamar ba
mutum ba, shi kansa a yanzu ya gane ba kowa ba ne, duk abokaninsa sun guje shi
cikin ƴan watan ni sun manta da shafin rayuwarsa ga matarsa ta nuna masa tsantsar
ƙiyayya, yanzu da Mahaifiyarsa bata raye haka rayuwarsa zata ƙare kenan a
wulaƙance?

Turo ƙofar da akayi ne yasa duk suka ɗago suka kalli ƙofar daga shi har Umma,
Yasmin ce sanye cikin suit da alamu daga gurin aikinta ta biyo asibitin. Ba Umma
kaɗai ba shi kansa da yake mijinta sai da yaji tsoron zuwan nata.

“Miya kawo ki mi kika zo ki yi? Ai na ɗauka kina da zuciyar da ba zaki iya taka
ƙafarki ba ma a asibitin sai idan ya mutu a akai miki gawa, wai ke nan har kin isa
ki wulaƙanta mijinki akan wannan abun daya aiakata, kowa fa be wuce ƙaddaraba,
mutane nawa ne suke zama da mijinsu bayan kuma sun san mijin yana aikata irin
wannan abun, amman su rufa masa asiri su zauna da shi”

“Matan da suke rufawa mazansu asiri akan wannan aikin suna yi ne akan kwaɗayin
kuɗin mijin, ni ko na dan dukiya na auri Uzair ba, wasu kuma suna yi saboda
ƴaƴansu, ni ko ya keta haddin ɗa na, ko be faɗa miki yayi raped ɗa na ba? Idan be
faɗa miki ba to yau ki sani, kuma dalilin zuwa na a nan saboda ina son na karɓi
takardata ne, idan kuma be shirya sakina ba ni na shirƴa kai shi kotu”

Yasmin na maganar hawaye na zuba a idonta, hannu Umma tasa ta rufe baki tana kallon
Uzair, furucin da Yasmin ta yi a yanzu yayi nauyi, sai dai ta fahimci gaskiya
Yasmin ta faɗa tun da ya kasa ƙaryatata har ma ya sadda kansa ƙasa yana hawaye.
Yasmin ta kalleshi tana share hawayenta

“Ka daina yaudarar kanka da sunan wani yayi maka asiri, mugun abunda kake aikatawa
ne ya kama ka, kuma Allah ya yanke maka wahala komai ya zo maka da sauƙi, da ace
kana da lafiyarka wallahi da ko wace jarida sai ta buga hoto na da naka, dan sai na
bawa duniya mamaki da kai mijina kuma uban ƴaƴana kotu, kuma ko yanzu ka taki sa'ah
ne mahaifiyata ta hana ni, amman idan har shiga kotu kake so ka yi ƙoƙarin yin
jayayya da ni akan aurena...!”

Juyawa ta yi ta fice tana kuka. Ajiyar Zuciya Umma ta sauke cikin muryar kuka ta ce

“Abun naka har ya ɓace Uzairu, wannan ba halina ba ne kuma ba halin Baban ka ba ne,
ban san inda ka ɗauko wannan rayuwarba, yanzu a ce har ɗan cikin ka zaka aikatawa
wannan abu? Ko a masu yi ƙoƙarin kare iyalinsu suke kada su faɗa wannan halaka
balle kuma har su saka su da kansu, abun da naki ji a redio yau a gidana zai faru?
Na yi tunanin ko zafi ciwo ne yasa ka faɗar haka a baya ashe dai da gaske ne,
Uzairu baka kyautawa kan ka ba”

Ta rufe fuska tana kuka. Shi kan hawaye yake sai a yanzu yake ayyana zancen Allah
na cewar cikin matan ku maƙiyanku, a cikin ƴaƴanku akwai maƙiyanku, ji yake kamar
ma shi aka saukarwa ayar dan tsanar da Yasmin ke nuna masa ta yi yawa.

Wasa-wasa abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa magani yake amman babu sauƙi, haka ya kwashe
wata shida a asibitin sannan aka sallamoshi ya dawo gida gurin Umma. Daman tun a
asibiti aka siya masa keken guragu yana tura kansa a ciki duk lokacin da wani abun
uzuri ya same shi ko kuma yayi sha'awar fita waje.

Ranar da Yasmin ta samu labarin ya dawo gida, ta samu Mahaifiyarta a falo akan
maganar shigar da shi kotu tun da har yanzi ya kasa aiko mata da takardarta.

“Wai ke Yasmin wace irin zuciya ce da ke haka? Ke bakya ganin tausayinsa ne? Ki
duba halin da yaron nan yake ciki wannan kawai be isa ya saka ki barshi da Allah
ba, ai da Allah ya tashi kama shi sai ya kama shi ta wannan hanyar da babu wanda ya
isa yai masa magani sai shi, ko ba komai fa Uzair ɗan'uwanki ne Yasmin ya kamata ki
riƙa tausayinsa, sannan uban ƴaƴanki ne, ko ƙin ki ko kin so kin riga kin haihu da
shi, nan gaba kina tunanin yaransa zasu ji daɗi idan suka samu labarin abunda kika
yi ma Ubansu?”

Fashewa ta yi da kuka

“Idan na fita wani lokacin har nuna ni ake, na rikice gaba ɗaya yanzu ko gurin aiki
ba komai nake ganewa ba, so nake ya sake ni ko na samu sukuni na natsu”

“Damuwace kika sawa ranki, bayan kuma be kamata ya dame ki, tun da ba ke kika
ƙaddarawa kanki wannan rayuwar ba, focus on your journey ki cire komai a rankiz ina
nan ina miki addu'a da sannu komai zai wuce”

Tashi tayi ta shige ɗaki tana kuka.

NAMRA POV.

Satin Hajiya Barau biyu ta Abbah ya dawo da ita saboda haƙuri da ake bata da kuma
ganin idon ƴaƴanta, ita kanta yanzu ta saduda dan satan bata kyauta ba, duk abunda
take tana yi ne dan kishin Anty Amarya tana ganin kamar Abbah yafi sonta da ita.
Ga kuma ƴaƴanta da suka sata gaba suka nuna mata rashin jindaɗinsu, ko ba komai
dai ya ga ishara a zmfitowar da ƴarta tayi wato Zinatu, yanzu ba Namra ba ce kawai
take zawarci a gidan har da ƴarta da uwar miji ta hanawa zama.

***
Anty Amarya na kallonta ta yi murmushi.

“Wannan shaddar duk tsadarta Lamido zaki bawa?”

Ta gyaɗa kai tana murmushi.

“Lallai ana jin Lamido nan, kar fa ya karɓe min faɗar ɗa”

Dariya ta yi wannan yaron tana shafa shaddar.

“Anty kina jin ɗan nan na ki”

“Ai bana da kamar sa ne Namra, kema kuma idan ba kin yi butulci ba baki da kamarsa,
abubuwan da kike masa basa min daɗi, yaron nan yana son ki wallahi, kin san yafi
ƙarfin wulaƙanci idan ba ke ba babu wacce ta isa ta wulaƙanta namiji kamar
Abdallah”

“Ba wulaƙanci ba ne Anty, ni rayuwarsa ce bana so, ya cika zafin kishi, kuma bana
jindaɗin abunda yake ma Lamido”

“Ai naji mahaifinki yana zancen sama masa aiki dan yace ya kusa barin driving ɗin
ki”

“Saboda me?”

“Nima be faɗa min ba”

Ta faɗa fuskarta da Murmushi. Namra ta baro gurin da take zaune ta zauna kusa da
Anty.

“Dan Allah Anty ki faɗa min”

“To aure zai miki”

“Anty Aure yanzu? Ni gaskiya ban shirya ba, halin mazan zamanin nan duk yaushe na
fita daga wannan rayuwar kuma za a ce na sake wani”

“Toh sai ki tashi ki faɗawa Mahaifinki ai yana part ɗinsa”

Ta yi saurin rufe baki tana dariya, sai ta tashi ta ɗauki shaddar ta fice. Murmushi
Anty Amarya ta yi tana unƙurin tashi ta nufi part ɗin Abbah.

Yau weekend ce daman babu aiki kuma babu wani taro ko wani abun da zai fitar da
Abbah, dan haka yana part ɗinsa yana hutawa. Da sallama ta shiga, ya amsa mata yana
kallon labaran bbc. Plate ɗin dake kusa da shi da ɗauke ta aje ƙasa ta zauna
bakinta ƙumshe da murmushi.

“Yanzu na ke shirin kiranki”

“To Allah yasa samu ne”

“Samu ne kan, ɗana nake nemawa auren ƴarki idan kun aminci”

“Ai Abdool ɗana ne ba ɗan ka ba, ni ya kamata na nema masa aure”

Dariya Abbah yayi yace

“Amman miya hana ya biyo ta gefen ki? Ko dai ƴarki bata son sa ne? Bana son na sake
mata wani zaɓin ne wanda ba shi ranta yake so ba, kar a sake samun matsala”

“Ba wata matsala, yanzu haka maganar da na gama da ita kenan”

“Toh Allah ya shige mana gaba, amman zan so jin ta bakin Namra”

“Ai gaka gata, waya isa ya shiga tsakanin uba da ƴa?”

Anty Amarya ta faɗa tana dariya.

*** *** ***

Kai ya girgiza mata alamar ba zai karɓa ba.

“Ba dan ki bani abu na zo gidanku ba”

“Ni ma na sani shiyasa na siya maka wannan shaddar, da wata manufa na yi ba”

“Na sani na gode?”

“Ba zaka karɓa ba kenan?”

“Gaskiya bana so”

Miƙewa ta yi tsaye ciki da jin haushin ƙin karɓar da yayi ta baro garden ɗin. Ko da
ta shigo falo wayarta dake kan kujera tana ringing cikin sauri ta kai hannu ta
ɗauka, Abdool ne rubuce a screen ɗin wayar. Tsayawa tayi kallon wayar sannan ta
danna picking ta kara a kunne.

“Abnam gani kan hanya?”

“Ba zaka daina yi min zuwan ba zata ba ko?”

“Zan daina daga ranar da kika zama mallakina”

“Allah ya kawo ka lafiya”

“Amin Sweet Abnam thank you”

Shi kanshi baya son zuwan ba zata da yake mata, sai dai yana yin hakan ne dan ya
riski Lamido gani yake kamar ya tare masa komai ƙara dai ya riƙa masa ba zata yadda
zai riƙa fahimtar alaƙar dake tsakaninsu.

Kitchen ta shiga ta sarrafa masa abu mai sauƙi sannan ta haɗa masa fruit salad dan
ta fahimci yana son sa sosai. Sai kuma ta shiga ta yi wanka ta saka abaya da jan
mayafi. Tana jin lokacin da mota ta shigo harabar gidan kuma zuciyarta ta ayyana
mata shi ne, amman saboda ƙarfin hali ta ƙi ta fita ta tarbe shi, har sai da ya
buga ƙofar falon.

Turare ta ɗauka ta feshe jikinta sannan ta fito falo taje ta buɗe masa ƙofar,
jinginawa yayi yana kallonta fuskarsa sa annuri, sai dai hakan be ma murmushinsa
damar fitowa ba.
Yadda ƴake kallonta ta yi zaton zai ce mata tayi kyaune kamar yadda ya saba sai
kawai taji ya ce.

“Ina Anty?”

“Tana ciki, ka shigo mana”

“No ba sai na shigo ba, ai baki bukatar ganina”

“Nace maka? Abdool miyasa kake irin wannan maganar ne? Sai kace wata maƙiyiyarka
kace bana son ganinka”

Ya wara ido.

“Wasa nake miki fa, ai nasan ni kika yi wa wannan kwaliyar”

Sai kuma ta ji kunya.

“Zaka shigo ko part ɗin Abbah zaka je”

“Cikin wata tara kin zama wata babbar mace”

Ya salam. Ta juya ya bar masa jikin ƙofar, sai kawai yayi murmushi ya shigo. Daman
gidan ba baƙonsa bane sai dai duk lokacin da zai zo Abbah ne kawai yake sanin
shigowarsa garin. Kasa sakewa Namra ta yi haka take duk lokacin da ya shigo part
ɗin shi kuma sai ya bi ya tsare ta da ido duk wani motsi nata yana idonsa.

Fruit salad ta fara kawo masa da ruwa sai kuma pineapple juice da ta haɗa masa.
Gabanta sai faɗuwa yake kar Anty ta tararda su, tana jin kunyar Anty ta ganta da
Abdool sosai.

“Gaskiya na yi sa'a, Matata ga iya abinci ga iya kwalliya ga haƙuri da kawaici”

Ƙasa ta yi da kanta tana murmushi, this is not the first time da yake yaba girkinta
a duk lokacin da ta girka masa wani abu.

Kamar munafuka haka take satar kallonsa, yana mata kyau yau fiye da ko yaushe, ga
wani ƙyalli da fuskarsa take.

Ƙarar da wayarta ta yi ne ya dukan su suka kalli wayar, ita sam ta ma manta da


wayarta tana saman kujera dan tun da tayi waya da shi ta aje ta a gurin. Hannu ya
kai ya ɗauka.

“Waye Dr Faruk?”

“Likita na ne”
Ido ya sakar mata kamar be yarda da maganarta ba, kuma yaƙi ta bata wayar sai
ringing take.

“Me zai sa ya kira ki yanzu? Baki da lafiya ne?”

Kasa amsa mashi ta yi. A take yanyinsa ya canja sai kawai ya miƙe tsaye ya aje mata
wayar ya fice, zuciyarsa na masa mugun zafi.

AMIRA POV.

Kullum cikin ɗaki ta wuni duk tabi ta takura kanta, akan abunda ta san har a bada
ba zai taɓa zama nata ba, babu yadda Ammy bata yi akan ta riƙa fita tana shan iska
amman ina, har ta gaji yanzu ta saka mata ido sai kuma addu'ah da take mata.

Cikin rashin ƙwarin jiki ta fito ta daga ɗakinta ta haɗawa kanta tea, bayan ta haɗa
tea ta zauna a falo, saboda ta samu falon babu kowa a ciki sai tv dake ta aikinsa.

Ƙofar falon aka turo aka shigo, mai gadinsu ne, hannunshi riƙe da wasiƙa, sai da
kai ƙasa sannan ya miƙa mata takardar.

“Gashi inji wasu mutane suka ce a baki”

“Su waye?”

“Wlh nima ban sani ba, cikin mota suke kuma sun tafi”

Hannu ta kai ta karɓa, shi kuma ya tashi ya fice, sai da ya fita sannan ta warware
takardar ta fara karantawa...

ASIM POV.

Yanzu tsawon wata tara kenan ana abu ɗaya, a duk lokacin da ya gina gida da sunan
Mardiya sai gidan ya ƙone, idan ya kama haya ma abu ɗaya ne, tun lokacin da aka
ɗaura auren ta gagara tarewa sai dai su kwana a hotel ko kuma gidan abokai, dan ko
lokacin da aka ɗaura auren hotel ya kama mata, baya jin zafi cire kuɗi ya gina mata
gida ko ya zuba mata dukiya amman ta kasa mararta saboda yawan gobara da take. Ita
kanta yanzu abun yana damunta sosai, musamman da ta samu labarin Asim yana neman
auren ƴar masu kuɗi, tasan babu namijin da zai juri zama da ita tana gora dole ko
wanene ya nemin ƙarin aure, ga mafarkin wutar da take har yanzu bata daina ba,
lallai haƙoƙan mutane da yasa yana kanta, domim ba Namra ce kawai ta taɓa cuta ba,
mutane da tayi ma cuta suna da yawa ga satar da tayi ta yi, ga kuma yawan banza
data ɗaukarwa kanta. Shi kansa Asim sai yanzi ƴake gane yayi zaɓen tumun dare, dan
duk ƙyalƙyalin da yake hangowa sai ya tarar na ɗan maciji ne, be same ta a budurwa
ba, kuma daman be aureta dan Allah ba, auren sha'awa yayi mata daga lokacin da ya
kai ga jikinta sai duk da fita ranshi daman yanzu ba maxe ba burgeshi take ba,
wannan ma da zai aureta dan kawai kariyar kai ne, kuma yana son ganin shi wutar
take bi ko Mardiya.

Babu irin neman taimakon da ba ayi ba akan wannan matsalar, wani gurin ace aiki ne
aka mata wasu kuma su ce iska ne yake mata, tana zuba kuɗi da yawa dan ganin ko za
a dace amman babu wani sauƙi sai abunda ya cigaba.

A unguwa kuma sai gulma ake mata kowa da irin abunda yake faɗa, waɗanda suka san
halinta suce amanace ciki har da masu cewa ai taci amanar Namra tun da ta aure mata
miji....
[7/22, 10:00 PM] Khadeeja Candy♥: *87*
NAMRA POV.

Shiru-shiru bata ga Abdool ya dawo ba, hakan ya tabbatar mata da fushi yayi. Miƙewa
tayi tsaye ta fita sai ta hangoshi jikin motarsa yana kallon ƙofar falon. Ƙarasa
tayi cikin wani taku mai jan hankali da ƙasaita, ta rumgume hannayenta tana
kallonshi.

“Ina da matsalar mahaifa ne Abdallah, ciki baya iya tsayawa tun ina gidan Asim,
wannan matsalar ce tasa Dr Faruk ke kula da lafiyata”

Uffan be ce mata ba, sai kawai ya kawardar fuskarsa yana kallon part ɗin Abbah.

“Abdallah...”

“Abnam...”

Ya kira sunanta kamar yadda ta kira nashi, still be kalleta ba.

“Baka yarda da ni ba ko?”

“Babu rashin yarda a tsakani na da ke, sai dai zai fi idan muka bar maganar nan”

Murmushi tayi ta juya koma ciki. Haka ya tsaya a gurin har sai da yaji ya samu
sassauci a zuciyarsa sannan ya nufi part ɗin Abbah. A falo ya samu Abbah daman
yasan da zuwansa sun samu awa ɗaya suna tattauna akan rayuwa da abubuwan duniya sam
ba zaka ce Abdallah ne yake neman auren ƴar Abbah ba, sam ba zaka ce surukinsa ba
ne.

*ONE MONTHS LATER...*

Har yanzu jikinsa na nan a yadda yake, Umma yanzu na hausa take nema masa wai ko
Allah zaisa a dace.
Bayan ya gama shan magani ya turo kekensa ya fito harabar gidan. Wayarsa dake
cikin aljihun wandonsa ya ciro ya kira Tahir.

“Bros ya ne, ya jikin naka ne?”

“Alhamdullah, ya aiki?”

“Mun gode Allah”

“Tahir tun ranar baka sake ce mun komai, ko baka kai mata ba ne?”

“Wallahi na kai mata, sai dai ban ji wata magana daga gareta ba, Uzair ina son
na.baka shawara akan rayuwa, ka yi haƙuri ka rumgumi ƙaddara, wannan abun da ka
gani na ishi kowa ishara ni kaina wannan ciwon naka yasa na zubar da duk wata
muguwar da nake da ita, ba kai kaɗai ba, yawancin duk mai aikata irin wannan
matsalar ce take faɗa musu, ka duba lamarinka Uzair ba haɗarin mota ka yi ba, ba
kuma faɗowa kayi daga wani guri ba, haka kawai rana tsaka ance ka kamu da irin
wannan ciwon, ita kanta Amira yanzu ta kanta take balle ka zargeta da aikata maka
wani mummunan abu”

Tun da Tahir ya fara masa maganar jikinsa yayi sanyi, be san lokacin da hawaye suka
zubo masa ba, lallai maso rai wawa, haƙiƙa yanzu Tahir ya lurar da shi abunda be
kasa ganewa.

“Na gode”
Shine kawai abunda ya faɗa ya katse kiran. Hawaye na cigaba da masa zuba, tabbas
wannan kawai ya isheshi ishara, a yanzu idan ba Mahaifiyarsa babu kowa a tare da
shi, zai barwa ɗansa mumman tahirin da ba zai taɓa goguwa ba har a bada.

Kekenshi ya tura ya koma cikin falon, ƙanensa na zaune sai sha'aninsu suke ko kula
da shi basu yi haka ya tura kansa ya shiga ɗakin da aka ware masa ya zamo kamar
nasa. Farar takadarda da ya gani a saman gadonshi ya kai hannu ya ɗauka.

Sammaci ne daga kotun high court, ganin sunan Yasmin yasa shi murmushin da ya fi
kuka ciwo, sannan ya sake tura kekena ya fito falon yana tambayar wanda ya kai masa
wasiƙar.

“Ɗazu ne kana shan magani aka kawo, na shiga ban ganka ba shine na aje saman
gadonka”

Ƙaramar ƙanwarsa ta faɗa. Sai kawai ya kaɗa keken ya nufi ɗakin Umma.

***

Hankalin Mai Martaba ya kwanta yanzu, har ma da na Ummi. Ganin an tsayarda magana,
ranar da Mai Martaba ya aika aka yi maganar aure har da sadaka sai da yayi. Sai dai
tun daga lokacin magana ta riƙa zuwa tana dawowa akan Abdallah zai auri bazawara,
abun mamaki ne mutun kamar Abdallah ace zai auri bazawara kuma ɗan Sarkin Ƙatsina,
wanda hakan sam be yi ma Mai Martaba daɗi ba, sai dai ya kan zuciyarsa nesa domin
kawai ya farantawa ɗansa, domin yasan Annabi ma ya auri bazawara kuma yana
sauranyinsa.

Ita kanta Ummi tana shan magana akan aure wasu su ce kar ta barshi wasu kuma su ce
kamata yayi ya haɗa biyu. Sai dai duk wannan maganganun da ake be taɓa zuwa kunnen
Abdool ba, ko da wasa ƴan'uwa da abokai basu taɓa masa wannan maganar ba, saboda
sun san waye Abdool idan yana yin abu yana yi ne no matter what, ao faɗa mishi irin
wannan maganar zai sa ya ɓata da kai ne kawai, ko kuma kai ma ya faɗa maka marar
daɗi, sai dai abokai sun ka zolayeshi cikin wasa. Babu abunda yayi masa daɗi kamar
auren da Abbah be yarda aka saka nesa ba, shi kansa da ansaka auren nesa zai roƙa a
rage ne, domin ya matsu ya ɗauke Namra daga gidan. Ta ɓamgare ɗaya me yake jin zai
iya zame masa matsala karatunta da take yanzu.

NAMRA POV...

Babu inda zance baikon Namra be kai ba cikin garin Sokoto da kewaye, a social media
kan ba zaka iya lissafawa ba, babu abunda zai baka mamaki kamar ace bazawara ce aka
yi ma wannan kayan, kuma duk da sunan an gani ana so abunda aka san budurwa ake
yiwa. Kayan ƙwalah da maƙulashe ba zaka iya ƙigarsu ba, ga akwati goma da aka sako
na tufafi har da zinari duk a cikin an gani ana so, kowa abunda yake faɗa to lefen
me za'ayi?

Ba a gidan aka kawo kayan ba, daman haka Abbah yake duk lokacin da za a yanka ma
ƴaƴansa sadaki ko a kai lefensu, gidan ƴaƴanshi yake turawa.

Ko da ake hidimar kai kayan Namra tana makaranta a lokacin duk da yake asabarce
amman a ranar tana da darasin (lecture) da zata ɗauka a makaranta, bayan sun gama
tayi sallama ta abokanta ta nufo gurin da tasan Lamido ya saba tsayawa ya jirata.
Ko da ta isa yana zaune cikin motar buɗewa kawai ta yi ta shiga ta zauna sai
kawai taji ya ce
“Congratulations”

Tasan abunda yake nufi, yanayin muryarsa ya karantar da ita baya cikin daɗin rai.

“Na amince da auren Abdallah ne saboda mahaifina, kuma na san kai ma baka ƙi goya
min baya ba wajen amincewa da hakan”

“Abdallah ya kasa ni, daman ya faɗa min zai kasa ni, ta tabba yanzu shi ne a
zuciyarki ba kowa ba”

“Ya faɗa maka? Alfahari yayi, fariya yayi da zai kasa ka? Yaushe bakin ka ɗa nashi
ya taɓa haɗuwa?”

Yayi ma motar key yana cigaba da magana a hankali.

“Bayan tafiyarki, abubuwa da tawa sun faru, ciki har da dalilin zuwa neman aurenki,
da kuma neman zama direba a gidanku...”

Ta gyara zamanta a gidan bayan da take.

“Ban gane ba dan Allah ka ƙara min bayani, karka ɓoye min komai”

“Bayan kin bar Kaduna da kwana biyu, Yarima yasa aka ɗauko ni daga Kaduna aka kawo
ni Katsina, mahaifata garin da ƙabarin ubana yake, kuma garin da nayi alƙawarin ba
zan sake takawa ba.....”

Kamar wanda ya tuna abu sai kawai yayi shiru ya cigaba da driving ɗin da yake. Ita
kuma gaba ɗaya natsuwarta ta bar jikinta hankalinta ya karkata kan labarin da
Lamido ya fara bata...

IS BETTER THAN NONE... 😎 YI HAKURI DA SHORT CHAPTER 🙏


[7/23, 9:21 PM] Khadeeja Candy♥: *88*

“Ka tsayarda motar nan Lamido”

Ta faɗa a tsawace, umarninta yake bi tunda danta yake wannan aikin, a dole ya faka
mota a gefen ti-ti, sai dai be juyo ya kelleta ba balle yace mata wani abu.

“Miyasa Abdallah ya sa aka kai Katsina? Miya ce maka? Miya faru bayan na baro
Kaduna?”

“Faɗa miki abunda ya faru ba zai yi maganin komai ba”

“Wata ƙila zai yi wata ƙila kuma ba zai yi ba, amman faɗin shine mafi a'ala”

“Ni da Mahaifina asalin mu fulanin Katsina ne, mahaifiyata kuma ƴar asalin jihar
kano ce, mahaifina ɗan kasuwa ne ya kan ɗauki kaya daga Katsina ya kai Kaduna idan
ya siyar sai ya siyo na Kaduna ya kawo Katsina da hakan abun nasa ya girma, har ta
kai ya kan ɗauka daga Katsina ya kai Nijar, a lokacin muna ƙanana, iya gata
mahaifinmu ya nuna da kulawa mun taso cikin jindaɗi, arkizin mahaifinmu ya bunƙasa
cikin ƙanƙanen lokaci, sai dai mahaifin mu be da amini irin Alhaji Mu'azu, ita
kanta mahaifiya bata da ƙawa irin Hajiya Zuwaira, ba unguwar mu ɗaya ba, amman duk
ranar weekend sai an kawo yaranta gidanmu su yi weekend, bana da wayo sosai a
lokacin, amman ina jin yadda Mahaifina yake faɗin idan har ya haɗa wannan kuɗin ya
tura aka turo masa kaya zai samu kuɗi sosai, haka ya tattara komai na shi ya haɗa
kai da Aminsa ya tura kudaɗensa masu yawa sosai. Shiru-shiru babu kaya babu
labarinsu, har ta kai mun fara shiga wani hali na ha'ila i, Alhaji Mu'azu ne yake
aiko mana da cefane wani lokacin kuma har da ɗinkuna da wasu abubuwan na more
rayuwa, ashe duk wannan yana masa ne a cikin kuɗin da yake binsa, wata ranar
Assabar mahaifina yake labarta masa kayansa suna nan zuwa, har an kamo hanyar
nigeria da su ta jirgin ruwa, haka muka ɗauki tsawon wata ɗaya muna jiran isowar
jirgin, sai kawai dirar ƴan sanda muka gani a gidanmu, wai ana zarginsa da safarar
muyagun ƙwayoyi, haka suka tisa ƙeyarsa a gaba suka tafi da shi, sau ɗaya suka bar
mu muka ganshi tun daga lokacin ba mu sake ganinsa ba, sai dai abokinsa ya zo ya
faɗa mana cewar ana nan za a sako shi, amman shiru har Allah ya karɓi ransa. Bayan
rasuwarsa Alhaji Mu'azu yake faɗa mana cewar babu dukiyar Mahaifinmu ko taro a
hannunsa, sanadin haka muka bar garin Katsina ni da Mahaifiyata, sai muka koma
garin Kaduna da zama wato mahaifarta, a gidan data gada gurin mahaifinta, tun daga
lokacin garin Katsina ya fita daga raina duk da kasancewar a nan mahaifar ubana
take, sai sai bayan rasuwar mahaifina babu wanda ya sake waiwayar mu a cikinsu”

Namra ta share hawaye idonta cike da tausayawa ta ce

“Ba shi na tambayeka, abunda Abdallah yayi maka na tambaye ka”

“Abdallah yasa an ɗauko ni daga garin Kaduna aka kawo ni Katsina saboda kawai yana
ɗan sarauta kuma ɗan mai kuɗi yafi ƙarfin ya bar garinsa ya zo kaduna saboda ni”

“Har yanzu baka faɗa min dalilin ɗaukoa da yasa aka yi ba”

Shiru be sake ce mata komai ba, hara aka kira sallah la'asar, tasan ba zai faɗa
mata ko minene a yanzu ba. Zata sake magana wayarta ta yi ƙara number Abbah ta gani
cikin sauri ta yi picking.

“Gamu nan kan hanya”

Shine kawai abunda ta faɗa ta sauke wayar. Shi kuma ya tashi motar suka hau ti-ti.
Ta madubin gaban mota take kallon yadda hawaye suke zuba daga idon Lamido.

Sai da suka kusa isa gida sannan ya ciro handkerchef ɗinsa ya share hawayensa.
Yana faka motar ta buɗe ta fito sai shi ma ya buɗe ya fito ya miƙa mata keys ɗin
motar.

“Aikina ya ƙare daga yau! Gobe zan kama hanyar garin mu”

“Ba a gurina ka karɓi keys ɗin motar ba, ba ni na ɗauke ka driving ba”

Tana bashi amsa ya gyara tsayuwar littafan da ke hannunta ta nufi hanyar falo.
Tana shiga Maryam da Wasu old friends ɗinta suka jo kanta suna mata murna da
zolaya. A abubuwa biyu ta samu kanta, farincikin da akasinsa, ba data dalilin yin
duka biyu ɗin, dan har ga Allah bata shirya aure a yanzu ba, sai dai babu yadda ta
iya tun da Abbah ya nuna yana son ta yi, a ɗayan ɓangaren kuma idan ta tuna halin
da Lamido yake ciki sai ta ji Abdool ya fita a ranta. Cikin ƙarfin hali take musu
dariya tana nuna musu farincikinta sannan ta wuce ɗakinta. Littafanta ta jefar
saman gado ta shiga banɗaki ta yi alwala, ko da ta fito wayarta na ringing, wasu
kawayenta ne na makaranta hakan yasa bata ɗauka ba, tasan ba zai wuce su taya ta
murna ba, ko kuma su faɗa mata yadda zancen engaged ɗin ta ya cika social media.
Har ta saka Hijab ɗinta sai wayar ta sake ringing wannan karon Abdool ne, tana son
magana da shi sosai hakan yasa tayi picking tana aika masa sallama.

Ya amsa mata yana ƙarantar saƙon dake cikin muryarta na ranshin daɗin rai.

“Tell me i'm wrong, amman kamin ki yanke hukunci ya kamata kisan duk abunda aka yi
Mai Martaba ne yayi ba ni ba”

A tunaninsa ko akan kayan ta ya tura ne wani abun be mata daɗi ba, sai kawai yaji
ta ɗauko masa wata magana ta daban.
“Miyasa kasa aka ɗauko Lamido daga Kaduna ka kawo shi Katsina? Mi kace masa?”

Yannu ya kai yana shafa dogon hancinsa, tare da maimaita sunan Lamido a zuciyarsa.

“Be faɗa miki abunda Yarima Abdallah yayi masa ba? Be faɗa miki gaskiyar abunda ya
faru ba?”

“Be faɗa min ba, amman ga dukan alamu abunda ka yi masa babba ne, domin har hawaye
na gani a idonshi”

Ƙafarsa ya ɗora ɗaya saman ɗaya yana imaging fuskar Namra a wannan lokacin duk da
kuwa bata kusa da shi.

“You're crying...”

Sai kawai ta katse kiran ta share hawayen idonta ta miƙe tsaye ta kabbatar sallah.
Har ga Allah tana jin son Abdool a zuciyarta sai dai bata fatar ta yi amfani da
wannan damar ta cutar da Lamido, dan tana jin rashin kyautawa a abunda ta yi masa,
sai dai bata da zaɓi bayan na Allah daman can shi ta miƙawa lamurarranta, har gobe
roƙon Allah take idan har babu alheri a aurenta da Abdool Allah ya musanya mata.

Haka ta kwashe kwana biyu, babu wata magana mai daɗi dake shiga tsakaninta da
Abdool, saboda tana ganin kamar yana amfani da saurautarsa da kuma kuɗinsa ne wajen
nuna mata ƙarfin iko ya ita da Lamido, ga kuma farin jikin daya samu a tsakanin
iyayenta wanda hakan ya hanata ko da wasa ta cewa Anty wani abu ya shiga tsakaninta
da Abdool ba.

Har yanzu Lamido ne yake kaita makaranta, bata tambaye shi yadda yayi da Abbah ba,
shi kuma be ce mata komai ba. Sai dai ta kan tsargu da abu ɗaya a yanzu, ya kan
tsura mata ido ta madubi mota ko kuma idan tana waje kamar madubinshi.
Ita kuma a yanzu bata magana da shi saboda ya ƙi ya faɗa mata.

ABDOOL POV.

Tun da ya karanci halin da Namra ta sashi, sai ya ke ganin kamar Lamido ne yake
masa zagon ƙasa, daman shi zuciyarsa bata natsu da zaman lamido a gidan ba, a duk
lokacin da ya tuna sai yaji kamar zuciyarsa zata rabe biyu, musamman da yasan shi
yake kaita makaranta ya ɗauko ta, tabbas yayi sake da yaba har tsawon wata takwas
tana keɓancewa da Lamido, aiko dole ta so shi fiye da shi.

Kamar an masa allurar ƙarfi haka ya zabura ya miƙe tsaye be damu da saka hula ba
duk da shaddace a jikinsa ya fito ya nufo part ɗin Ummi.

Be same ta a falon ba, sai Amal ya samu tana ta faman solved Maths.

“Dude Ina Ummi?”

“Tana Garden lalle ake musu, Dude na taso mu yi wannan assignment ɗin?”

“No bari sai na dawo fita zan yi”

Ya juya ya fice. A garden ya sameta zaune saman carpet ta jera ƙafafunta ana zizira
mata lalle irin wannan na zamani.

Tsaye yiyi ya jingina da icen guava yana wasa da keys ɗin hannunsa.

“Ummi na canja shawara, zanje na ga Mai Martaba”


“Shawarar me?”

“Nan da One Months nake son a yi auren nan?”

Da mamaki Ummi ta kalleshi.

“saboda me?”

“Kawai ni nafi son haka ne”

“To su ƙanenka da aka saka date ɗin aurenku a tare fa?”

“Su a barsu sai lokacin ni kan gaskiya i can't wait, zan samu Mai Martaba mu yi
magana”

“Amman zai zama kun yi magana biyu Abdallah, da ka yi haƙuri har lokacin nan da
wata biyar a ba wani abu ba ne”

“Haƙuri ba zan iya ba Ummi, kawai ki min addu'a”

“Toh Allah yasa alheri, amman nasan Mai Martaba ba zai amince ba”

“Zai amince ki daina ƙwanƙwanton mahaifina akai na”

Hannu ta ɗaga masa.

“Tafi kai da kan ka zaka dawo ka ba ni labari”

Murmushi yayi ya juya ya bar Garden ɗin tana ta saƙe-saƙe a ranshi har ya isa faɗar
Mai Martaba.
Be same shi a gida ba, saboda wani taro da taje, haka ya zauna a gidan har aka yi
sallah magariba, bayan ya fito daga masallaci ne Mar Martaba ya dawo, dan shima sai
da ya tsaya a can suka yi sallah sannan ya kamo hanyar gida.

Mai Martaba na gaba Yarima Abdool na biye faɗawa sai zuba masa kirari suke har aka
shiga fada. Kai tsaye Mai Martaba ya wuce turakarsa Abdool ya rufa masa baya yana
masa bangajiya. A saman fafaffaɗa kuma ƙasaitacciyar kujera Mai Martaba ya zauna ya
cire rawaninsa ya miƙawa Abdool. Bayan ya aje rawanin ya dawo kusa da ƙafafun Mai
Martaba ya zauna yana mai natsar da kai kasa kamar yana gaban sukurinsa, ya kan yi
hakan a duk lokacin da da yake neman wata alfarma a gurin mai Martaba saboda kawai
Mai Martaba yaji tausayinsa ya amince.

“Buɗe baki ka yi magana, Babana ni mahaifinka ne idan ban maka uzuri ba waye zai
maka?”

“Allah ya taimaki Mai Martaba ya ƙara maka lafiya, daman magana ce na zo da ita
akan auren mu, sai dai ban san ta fuskar da zaka kalli abun ba”

Mai Martaba ya jingina da kujera yana cigaba da kallon ɗansa. Abdool ya cigaba ba
tare da ya ɗago ya kalli Mai Martaba ba.

“Idan har ka amince min, ina son ka roƙa mahaifin Namra akan ya rage lokacin da ya
saka na aurenmu saboda yayi tsawo...”

Sai da aka ɗauki tsawon ɗakika talatin da huɗu wata kalma bata fito daga bakin Mai
Martaba, sannan ya nunfasa kana ya ce
“Ni kaina na yi tunanin hakan, saboda maganganun da suke ta zuwa suna dawowa, ba a
son magana ta yi yawa akan aure, kuma idan har aka ja abu nesa wannan kan iya
haifarda da wata matsala wace ba a tsammanin zata zo, sai dai ganin lokacin auren
yayi dai-dai da lokacin auren ƴan'uwaka yasa ban ce komai a kai ba”

Abdool ya jidaɗin wannan maganar, daman yana neman da inda zai fake yayi hujja da
shi akan maganar auren. Sai gashi Mai Martaba ya taɓo masa inda yake masa ƙai-
ƙaiyi.

“Nima hakan na gani, kada sheɗan ya shiga ciki, ko kuma baki yayi mana yawa”

“Gaskiya ne, amman kai zuwa yaushe kake ganin ya dace a saka auren?”

“Allah ya taimake ka ina son ace nan da wata ɗaya”

Mai Martaba yayi masa wani kallo.

“Nan da Wata ɗaya sai kace wanda zai auri ƴar tsana? Wata ɗaya yayi mana kaɗan da
shirya lamarin auren ka”

“Allah ya taimake ka duk yadda ka yanke dai'dai ne, amman be yi kaɗan ba, indai
matsalar lefe ne ciki sati ɗaya za a iya haɗawa, kuma na san bama buƙatar komai
daga gareta”

Ɗan Murmushin gefen baki Mai Martaba yayi, lallai ya tabbatar da ɗansa ya matsu,
hakan ma yasa shi gane Abdool yama neman girma a yanzu, bayan kuma a da neman masa
ake yana gudu.

“Za mu yi tunani akai, kar ya zama mun matsa musu, zan yi shawara da Umminka, nan
kuma cikin gida zamu shawara”

Mai Martaba na gama faɗar hakan ya miƙe tsaye...

__________________________________

I think we should create a team for LAMIDO ko 😢i pity him bawan Allah 😢
[7/24, 9:38 PM] Khadeeja Candy♥: *89*

Yau day ta leƙa whatsapp domin ta kwana biyu bata hau ba, daman bata hawa sai idan
tana da time saboda karatun da ta sawa gaba.

“Abbah na kiran ki”

Aysha ta faɗa tana tsare jikin ƙofar ɗakin Namra.

“Okay ga ni zuwa”

Ta kashe data ta sauka saman gado. Ko da t fito Zinatu na zaune falo ita da Anty
Amarya suna cin ɗatun zogale (kwaɗo). Wara ido tayi ta sha mur

“Lallai Anty shi ne cika zauna da ƴarki kika ci ɗatu ni aka ƙyale ni”

“To idan ban ci da ƴata ba da wa zan ci? Kaji min yarinya”

Anty Amarya ta faɗa fuskarta da annuri tana murmushi. Zinatu tasa dariya.

“Na gan ki online fa kuma na miki magana kika share ni”


“Allah ban duba ba, hankalina yana can ina duba chat ɗin grp”

“Gashi ai sai ki zo ki ci”

“Abbah ya kira ni, aje min na dawo”

Ya aje wayarta saman kujera ta nufi part ɗin Abbah. Zaune ta same shi sanye da
jallabiya, idonsa sanye da farin gilashi hannunsa da jaridar daily trust. Ƙasa ta
zauna bayan ya amsa mata sallamar da tayi idonta kan Arewa24 da suke maimaita
shirin Daɗin kowa.

Remote Abbah ya ɗauka ya kashe tv, ya aje jaridar da ke hannunshi sannan ya


fuskanci Namra ya ce.

“Magana na ke son mu yi a tsakanin ni da ke, kuma bana son ki takura kan ki, na fi
son ki faɗi ra'ayinki”

Ta ɗan kalleshi kaɗan.

“Abbah maganar me ce?”

“Akan date ɗin da aka saka ne na aurenki, Mai Martaba ya kira ni yace a rage musu
ranar da aka saka ta yi musu tsawo, amman yace baya son a cilasta miki yafi son sai
anji ta bakinki”

“Abbah ban da wani zaɓi sai naka, abunda duk zai fito daga bakinka shi xai fito
baki na, kai da Mai Martaba duka iyayene a gurina, duk yadda kuka yanke yayi, idan
ma a yanzu kuke son a ɗaura auren babu matsala ni dai a guna, sai idan gurin
Abdool”

Abbah ya jidaɗin maganarta sosai, daman haka yake son ta kasance gareshi mai biyar
dukan umarninsa da yarda da abunda ya zaɓa mata, babu ruwanshi da duba zamani ya
canja a ƙyale yara su yi ra'ayin kansu, yafi son duk yadda ya zaɓa maka kawai ka
bi.

“Na jidaɗi da wannan kalami na ki Namra, kuma tun da har kin amince zan faɗawa Mai
Martaba kuma na san shi ma zai jidaɗin wannan maganar, daman shi yana son a saka me
nan da wata ɗaya”

Dam! Gaban Namra ya yanke ya faɗi sai ɗai bata nuna komai a fuskartaba.

“Babu matsala a gurina Abbah, amman ya maganar Lamido?”

Abbah ya sauke ajiyar zuciya.

“Yadda kike so Namra ba zai yiyu ba, ba zan ɗauki mutun haka kawai na bashi MD,
mutanen duniya a yanzu ba abun yarda ba ne, abunda Uxair yayi min kawai ya isa ya
lurar da ni duniya, zan iya bashi aiki dai a ƙarƙashina, kuma daman ina da niyar
gyara musu gidansu kuma na ƙullawa mahaifiyarsu jari, ko da be yi komai ba zan iya
masa haka balle kuma ya taimake ki sun riƙa ki tsakani da Allah, na san yana son ki
Namra kuma kema kin san da haka, sai dai hakan ba zai sa na ɗauke shi haka kawai na
bashi mb ba”

“Amman Abbah idan ya fara aikin nan ka aminta da shi zaka iya bashi md, wallahi
mutumen kirki ne”

Abbah yayi murmushi.


“Har yanzu akwai ƙurciya cikinki, ai ba a gane mutum mai amana a fuska sai a aiki,
sai dai na yarda da abu ɗaya, duk yadda duniya ta lalace za a samu na ƙwarai, zan
jarrabashi na gani”

“Na gode Abbah”

“Allah ya miki albarka”

“Amin Thank you”

Haka ta tashi jiki babu gwari ta fice. Tun daga lokacin aka fara shirye-shirye, a
dukan ɓangarorin guda biyu. Kullum sai Abdool ya kirata safe, rana da dare domin
jin muryarta da kuma son sanin ko akwai abunda take shiryawa, sai dai duk lokacin
da ya tambaye cewa take bata shirin komai.

Hakan yasa ya baro Abuja a daren ranar ya sauka sokoto, dan kwata-kwata ya rasa
gane kan matarshi (His wife to be). Haƙuri yayi har sai da yayi sallah isha'i
sannan ya doshi gidansu Namra. Wannan zuwan na musamman ne baya son kowa yasan da
zuwanshi sai ita, a harabar gidan ya faka motarshi ya kira a waya yace mata yana
gefen gate. Bata yarda ba har sai da ta saka Hijab ɗinta ta leƙo ta hango mota a
gurin sannan ta yarda da gaske yake.
Ƙarasa ta yi kusa da motar ta buga ƙofar motar sai ya fito ya buɗe mata motar ta
shiga sannan ya koma mazaunin direba ya zauna. Wasa take da ƴatsun hannunta ta kasa
buɗe baki ta gaisheshi ma balle ta yi masa wata maganar, ta dai yi shiru tana
shaƙar turarensa da ke kaiwa hancinta ziyara. Wani dogon numfashi yaja ya sauke
kana ya kalleta ya ce.

“Na miki zuwan bazata, saboda na lura kamar baki cikin yanayin da ya kama ki
kasance, idan har bakya ra'ayin aurena Namra, wallahi ba zan cilasta miki ba, duk
yadda nake son ki zan iya bawa zuciyata haƙuri matuƙar ke hakan shine farincikinki,
ba jindaɗina ba ne muyi aure kuma mu koma muna zaman da be kamata ba ni da ke, ba
zan aureki dan wani abu ya shiga tsakanin mu har na sake ki ba, burina idan mun yi
aure ni da ke mutuwace kawai zata raba, ba zan aureki dan wani abu na ki ba sai dan
so da tausayi waɗanda abubuwa ne guda biyu da ba zasu taɓa saka ka ganin laifin
mutum ba, shiyasa bana ganin laifin abunda kike min, sai dai ina kallon hakan da
rashin so, ina ganin kamar na cilasta miki ne akan abunda baki da niya...”

Ɗagowa ta yi ta kalleshi idonta tab da hawaye, cikin rawar muryar ta fara magana.

“Tun bayan abunda Asim yayi min, ban taɓa tunanin zan so wani ɗa namiji ba, haka na
saka a zuciyata kuma haka na ayyana. Amman daga lokacin da na saka ka a idona
gidansu Lamido, sai wani irin kwarjini da ƙimarka suka kama ni, sai kuma gashi ka
zama sanadiyar haɗa ni da iyayena, wannan ne yasa son ka ya ɗasu a zuciyata, ko da
ban aureka ba, zan son ka Abdallah, irin son nan da ƴan matan hausawa suke yi ma
mazan hausa novels da larabawa, kasan irin wannan son yafi ko wanne haɗari da saka
rayuwa cikin ƙunci da nadama, da kuma ganin munin kowa, sai gashi Allah ya ƙaddara
zan zama matarka, amman son da na ke maka doesn't give you the chance to hurt
innocent people”

Sanyayiyar ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta irin kallon nan mai cike da shauƙin so
da ƙauna.

“Wana cutar?”

“Lamido, ya ƙi ya faɗa min abunda ka yi masa amman nasan abunda ka yi masa ba


ƙarami ba ne”

“Dukan abunda na yi masa saboda ke ne Namra, saboda ina son ki ne, nasa an kawo min
shi daga kaduna zuwa katsina ne saboda na masa magana a akan ki, nace zan biyashi
ko nawa ne, ya ƙyale ki saboda bana son mu tarayya ni da shi a lokaci ɗaya mu raba
miki hankali, saboda na lura yana son ki, kuma zuciyata tana nuna min zai bibiyeki,
amman shi be ƙarbi tayin da na masa ba, har ma yayi min iƙirarin shi ne zai mallake
zuciyarki, kuma yayi nasarar aurenki, amman duka be faɗa miki wannan ba sai a yanzu
da yaga komai ya kankama kuma ya ɓoye miki saboda yana son shiga tsakanin mu,
wannan yasa na roƙi Mai Martaba akan ya nemi a rage tsawon lokacin auren da aka
saka, saboda magangu sun yi yawa akan zan auri bazawara, kuma gashi Lamido yana
ƙoƙarin yi min zagon ƙasa, ina gudun kar shedan ya shiga ciki ya lalata lamarin
aurenmu, saboda duk lokacin da aka shirya abun alheri za'ayi sai ka ga shedan na
neman ɓata abun”

“Amman abunda ka masa baka kyauta ba”

Ta faɗa da muryarta mai kamar zata yi kuka. Shi kuma ya kwantar da kansa jikin
kujera yana kallonta, dan har cikin jininshi maganarta ta shiga ta zauna, a take
kasala ta sauƙo masa.

“Naji Gimbiyata ayi haƙuri a gafarta min”

Yanayin yadda yayi mata maganar yasa ta jin kunya har murmushi ya suɓuce mata bata
shirya ba.

“I love you, i can't wait to see us on one bed...”

Ya faɗa muryarsa ƙasa sosai kamar mai raɗa. Buɗe motar ta yi zata fita sai yayi
saurin riƙo hannunta, ta zaro ido tana faɗin.

“A'uzubillahi...”

Sai ya saki hannunta da sauri.

“I cross the limit... But sorry wai ba mu gama maganar ba”

“Mun gama mana”

“Dan Allah ki yi magana da kyau Abnam ki daina kashe min jiki”

Ƙyalƙyale ta yi da dariya, saboda har ga Allah ya bata dariya ita bata yi dan ta
kashe masa jiki amman shi yana ƙoƙarin juyarda abun. Shima dariya ya samu kansa da
yi saboda be taɓa ganin ta yi irin wannan dariyar a gabanshi, ta tafi da imaninshi
sosai.

“You're so cute Abnam na fi kowa sa'ar mata”

Ƙoƙarin kawarda maganar ta yi.

“Na san maganar akan events ne, so bazawara zaka aura bana buƙara events bayan
walima”

“Amman ni saurayi ne ai, ina buƙatar ayi mana wani ɗan event haka ko da biyu ne ko
ɗaya”

“Ni dai idan ta ɓangarena ne bana so”

Ya ɗaga kafaɗunshi.

“As you wish your royal highness”


Dariya ta yi ta rufe masa motarta ta tafi. Shima murmushi yayi yana mai jindaɗi.

Namra ta kusan minti talatin tsaye a jikin windo tana kallon motar Abdool, sai ya
kunna motarsa ya bar gidan sannan ta fito ta nufi sashen BQ.

Tun daga nesa ta hango Lamido zaune yana danna wayarsa. Ta ƙarasa kusa da shi tana
masa sallama.

“Wa'alaikissalam, Hajiya”

“Na'am hutawa kake yi”

“Ina ɗan duba duniyar facebook ne”

“Hakan na da kyau, amman miyasa bakinka yayi nauyi har ka kasa faɗa min Abdool ya
nemi ka siyar masa da soyayyata ne?”

Murmushi yayi ya cire hular taɓani ka ji hadisi da ke kansa ya ce

“Saboda soyayyarki tana da girma a gareni, amman ina fatar ya faɗa miki mahaifinshi
ne dalilin talaucewar mu”

“Abunda ke tsakanin Mahaifinka da mahaifinshi be kamata ya shiga tsakanin ku ba,


balle kuma ni har na shigo ciki, be nuna min ya san kamin lokacin ba kuma kai ma
baka nuna min ka san shi, dan haka babu ruwana da abunda ke tsakaninku”

“Na gode Namra na gode sosai”

Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya shige ɗakinshi. Ita kuma ta juyo ta dawo part ɗin
Anty Amarya, a bakin ƙofa ta samu anty amarya a tsaye tana mata wani mugun kallon.

“Me kika je yi can?”

“Magana na yi da shi”

“Wace magana bata da suna ne? Ban miki maganar tun ranar akan ki daina keɓewa da
shi ba?”

“Wallahi ba abunda kike tunani ba ne, yana ta ƙoƙarin shiga tsakani da Abdool ne ni
kuma ban ga ne ba sai yanzu, shi ne na masa magana”

“ko ma minene karna sake ganin ki part ɗin nan, ai ba zarginki nake ba, kawai ina
gudun shaedan ne, kuma tun da yana son ki zai iya aikata miki komai, ki yi taka
tsantsan”

Ta gyaɗa kai.

“Ba zan sake ba daga yau”

“Good”

Anty ta bata hanya sannan itama ta shiga.


Ko da Namra ta shiga ɗakinta ta tararda missed calls na Abdool. Dan haka tana cire
Hujabinta ta kirashi.

“Hi Babe-Abnam”

“Abdallah”
“Faɗa min wani abu mai daɗi...”

“Ni ko tambayar ka zan yi, miye tsakanin mahaifinka da Mahaifin Lamido”

“Me kuma ya sake ce miki?”

“Yace wai mahaifinka ne silar talaucinsu”

“Ya ɓoye miki ne kawai ko kuma be san gaskiyar zancen ba, a da mahaifinshi abokin
Mai Martaba ne kamin a bashi sarauta, sai dai mahaifinshi yana safarar ƙwayoyi ne
daga wata ƙasar ana sakawa cikin kayanshi da yake oder, sai yace musu zai kai kaya
kaduna alhalin ƙoyoyine yake safara, babu irin jan kunne da mahaifina be masa ba
amman yaƙi ji, ranar da ya shirya dainawa sai ya aika duka kuɗinsa waje ya siyo
kayan fasa ƙwairi,wanda sanadin hakan customs suka kama kayan, kuma aka bincika aka
gano yana safarar ƙwayoyi sanadin hakan aka maka shi, amman sai yake ganin kamar
mahaifina ne ya saka shi a matsalar”

“Amman daman ka san Lamido baka taɓa faɗa min ba?”

“Ban san shi ba Wallahi shi ma kuma be san ni ba, sai a lokacin da nasa aka kawo
min shi daga Katsina, a lokacin ina gida ne gurin Ummi, Ummi ce ta ganshi ta gane
shi, shi ma kuma ya ganeta bayan ya tafi take bani labari, dan ni ban san anyi abun
ba ma, lokacin da aka yi abun ina waje gurin karatu, so duk wasu abokai na Mai
Martaba ni ban sansu ba domin ban dawo naija ba sai da na yi digiri na biyu”

Namra ta jinjina lamarin sosai, daga nan zance ya cigaba, har ya ɗauko mata labarin
labarin zamansa a England.

*** *** ****

A GURGUJE...

Gyara na musmman Anty tasa ake mata irin wanda ake ma amare, tun daga kan dilka da
kuma kayan mata.

Daga Dubai Abbah yayi mata odar furniture aka kawo su ta jirgin sama, saboda jirgin
ruwa za a iya ɗaukar watanin basu iso ba, gashi kuma aure ya maso kusa, duk da Mai
Martaba yace kar su kashe kuɗinsu hakan be hana Abbah siya mata kaya mai shegen
tsada ba dan nemawa ƴarshi mutumci da ƙima a idon manyan mutane.

Ranar da aka kayo lefen Namra ana sauran sati ɗaya, bikin ranar kowa ya sha mamaki,
sai dai duk wanɗa ya ji labarin ɗan sarkin Katsina zata aura sai su daina mamakin
dan sun sa waye mahaifinsa balle kuma shi ɗan da kansa, an kashe neira a ɓangaren
Abbah saboda tarbar lefe yayi duk abunda ya kamata wajen ganin ya kashe kunya.

Bayan kowa ya watse Hajiya Barau da Anty suka zo suna ƙara duba kayan, daga ɗan
kunne har ribbon babu wanda aka siya a naija duk daga waje Ummi taje ta ɗawa ɗan
lelenta lefe. Akwati ashirin da bakwai ɗan ƙaramin akwatin zinari ma daban ne,
motar da aka kawo lefen da ita ba a koma da ita ba wai ita tana cikin lefen, ga
kuɗin tsintuwa da ake sakawa a gefen akwati su daloli suka saka. Ko kaɗan wannan be
yi ma Anty Amarya daɗi ba, domin ta tsani bidi'a a rayuwarta, dukan wani abun da
za'ayi almubazzaranci da kuɗi Anty bata son shi.

“Ai ƙara ma da ba za ayi wani Event ba, da Allah kaɗai yasan iya bidi'ar da za'ayi,
shi kesa aure yaƙi yin ƙarƙo, ni wannan abun ba burgeni yake ba”

Hajiya Barau ta yi murmushi tana danne abunda ke zuciyarta.


“Ai ke baki ga komai ba ma, mu da muka je jere mu muka ga abu, kin ga gidan da ya
ƙera mata kuwa? Kamar ba Katsina ba, wallahi an kashe kuɗi sosai”

“Uhm Allah ya kyauta”

“Amin ai kinsan su masu abun idan ba sun fitar da kuɗin ba ne sun kashe basa jin
sun yi, kuma tun da har Allah ya hore ai ƙara ayi, abunda kawai ba a so a zubar da
kuɗin kamar kari haka”

“Ke dai Allah ya kyauta kawai, amman bidi'ah bidi'ah ce”

Haka suka yi ta firarsu suna duba kayan da tsayawa ƙirga ko kala nawa ne ɓata
lokaci ne. A daren ranar Abbah ya kira Lamido ya bashi offer kuma ya sanar masa
aikinsa ya ƙare a gidan da sunan driving. Ba laifi yayi farinciki duk da ɗayan
ɓangaren yana baƙinciki an kasashi. Sai dai matsalar rashin aikin yi ita ta fi
damunshi fiye da kowace irin matsala.

RANAR JUMMA'AH...

Da misalin ƙarfe biyu na rana aka ɗaura auren Abdallah Ahmad Mai-doki da Khadija
Usman Zamau, a masallacin Muhammadu Maccido da ke Amir Yahaya. Duk wanda ya wuce a
gurin sai ya tambaya ɗaurin auren wa ake saboda yadda aka taru sosai, ga manya
mutane minister da sarakuna da ɓangaren Mai Martaba, da kuma gwannan Katsina, da na
kano wasu kuma basu samu damar zuwa ba suka tura akillansu. Mr Presiden ma
Wakiltarsa aka yi, saboda baya ƙasar.

Bayan an ɗaura aure aka yi ƙiyafar cin abinci a Shukura Hotel. a ranar Mai Martaba
da muƙarrabansa suka koma Katsina, da dare Mai Martaba yayi nasa liyafar shi da
manyan baƙinsa, a faɗarsa da aka sauyawa hallita kamar ba a naija kake ba.

Ta Ɓangaren Namra bayan an ɗaura aure da rana. Da dare suka yi walima, saboda an
sauya salo yanzu walimar dare ake, an raba kayanyaki masu ɗubin yawa da burgewa.
Sai dai ƴan ɓangaren ango basu halarta ba saboda Ummi ta ce zata yi nata walimar
idan an kawo Amarya, saboda wasu haka suke sai idan an kai amarya sannan suke nasu
walimar...

KALSOOM POV.

FIVE YEARS LATER...

“Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday dear Izzah Happy
birthday to you”

Tana yanka birthday Cake ɗin suka saka ihu.

“EyyyyyPpppppppp”

Sai kawai tasa dariya ta yanki wani abu daga cake ɗin ta sakawa Kalsoom a baki,
Kalsoom ma ta yanka ta saka mata a baki, sannan ta bi sauran mutanen da suke gurin
tana feeding the ɗinsu suma suna bata, bayan an yi musu hotuna Kalsoom ta basu guri
ita da ƙawayenta su cashe...

Kalsoom ta shigo falo ɗauke da ƴarta Amatullah da ke ta kuccekuccen a barta can ta


yi wasa.
“Ba zan barki can ba Amatullah su ture min ke na koma zaune”

Faɗuwa ta yi ƙasa ta fara shureshure da ƙafafunta tana kiran sunan Ezzah.

“Ijca ijca....”

“Easy girl, Ijca yau bata da time ɗin ki casu suke”

Haka ta cigaba da kuka, Kalsoom ta share ta a gurin, ta hau whatsapp tana saka
hotonsu a status. Sai ga Rafiq ya shigo da gudu ya shiga kitchen ya ɗauko plate ya
fito.

“Kai Plate ɗin nan na Dadyn ku ne, karka fasa min kaya”

“Cake za a sa mana ni da Amatullah”

“Kai mata wayo ka cinye ko..?”

Yasa dariya har da ƙyalƙyatawa, ya saba duk abunda za a saka masa sai yace shi da
Amatullah za a saka musu saboda ya cinye ya barta. Sai ga Ezzah ta shigo idonta tab
da hawaye kamar ta fasa kuka.

“Anty kin ga Husna wai sai an bata wannan cake ɗin ɗayan, gaba daya, kuma bamu gama
hotuna ba”

Kalsoom ta aje wayar hannunta ta riƙe baki.

“Yanzu Husna ce zata riƙa saki kuka gaban abokanki? Ke baki jin kunya su ga idonki
ya cika da hawaye? Shekara goma sha hudu ace ƴar shekara uku tana saki ƙwalla gaban
friends ɗin ki? Wallahi Izza ki rage wannan shagwaɓar”

Ta turo baki tana matsar ƙwalla.

“Je ki kirata ki ce tazo ga wayata ta yi game”

Ta amsa da to ta fice ita da Rafiq. Tana fita Ulfah ta shigo.

“Anty Momie ta kira?”

“Eh tace ba zata samu damar zuwa ba, yanzu suka taso daga Abuja”

“To Anty ki ce Ezzah ta ba mu cake ɗin mu ai Dady yace saboda mu yasa aka yi cake
da yawa”

“Ku ara mata ta yi hoto, ku bari a gama nama, ai ba gudu zai yi ya barku ba”

Ta buga ƙafa tana son kuka.

“A'a ni dai ta bamu abun mu, ko na kira Dady na faɗa masa”

“Duk kika faɗa masa sai na ɓata miki miyasa baki da nasiha ne ke? Kullum ke ce
cikin rashin jituwa da ƴar'uwarki haba Ulfah”

“Ai itama bata raga min”

“To bari na ga kin ɓata mata party wallahi na ɓata miki rai”

Ta faɗa saman jikin Kalsoom tana kukan shagwaɓa.


“Yi ta kuka yarinya ki ɓata kwaliyarki”

Sai kawai ta zabura ta kaɓe rigarta ta koma gurin party. Amatullahi ta miƙe da
saurinta ta bisu tana tafiyarta ta ta-ta-ta...
[7/27, 9:54 PM] Khadeeja Candy♥: *90*

On Sunday Amarya da muƙarrabanta suka kama hanyar Katsina, ta rigasu isa saboda ta
jirgi suka je ita da Maryam da ƴan'uwan Anty Amarya su biyu.

A wani gidan Abdool da ke can bypass suka sauka daman tun kamin su zo Ummi ta yi
masa wannna shawarar na su sauka a gidan saboda su samu damar sakewa su huta.

Tun lokacin da Abbah da Anty Amarya da Hajiya Barau suka saka ta gaba suna mata
nasiha kan aure, ta fara kuka, sai duk ta ji wani yanayi na daban, kamar lokacin da
za ayi aurenta na farin, banbanci wannan ba irin wacan auren ba ne.

Yasa an kawo musu komai daga hotel kama daga abinci har abun sha. Misalin ƙarfe uku
Yarima ya kira wata ƙanwar Abbah wacce gwaggo ce gurin Namra ya faɗa mata zai aiko
da motocin da zasu shiga ita da Namra da wasu mutun uku aje faɗar Mai Martaba.

Namra na zaune a ɗayan bedroom ɗin tare da Maryam da wasu Cousins ɗinta da Aysha da
suka zo tare, gwaggo Ramatu ta shigo tana faɗin.

“Ki shirya angon zai aiko da mota a ɗauke mu muje faɗar mai martaba”

Maryam ta daka tsalle.

“Yeeee kaga daɗin abun malam, mu shiga cikin masarauta muna tinƙaho kowa yayi mana
iskanci musa a tsire shi a gari”

Sai duk suka sa dariya, har Namra dake leƙa duniyar gizo. Gwaggo Ramatu ta juya ta
fice tana jinjina kai.
Maryam ta nufi babban akwatin Namra da aka zo da shi ta buɗe tana duba irin tufafin
da Namra zata saka. Wani tsadadden lace ta ɗauko red color da mayafi ta aje saman
gado.

“Raihanatu duba min wannan lace ɗin yayi”

Wacce aka kira da Raihanatu ta miƙe tsaye tana duba lace ɗin.

“Kai wannan ai sai ace matar president ce gaba ɗaya”

“Gaskiya kam wannan lace ɗin yayi kyau sosai”

A gajiye Namra ta miƙe ta shiga wanka ta shirya cikin lace ɗin sai suka gyara mata
fuskarta, ana cikin ɗara mata ɗankwali wayar Namra ta yi ringing.
Tana ganin Number Abdool ta yi dariya.

“Ango ango”

“Maryam ya gajiyar biki? Ina Amaryata? Na kira wayarta ta ƙi ta ɗaga ki ce ina


gaidata kuma ki ɗaukar min pictures ɗinta”

“An gama ranka ya daɗe”

Ya sauke wayar tana dariya tare da amsa sallamar Gwaggo Ramatu.

“Ku fito ga motoci can an zo da su, Maryam ke kaɗai kin isa ni da Talatu zamu je
sai a samu wasu cikin ƙannen Anty Amarya su biyu kuma suje tun da ance mutum biyar
sun isa”

Raihanatu ta mike tsaye tana kare ɗankwali.

“Haba Baba Ramatu wane irin Maryam kuma ita da take da aure, ai ƙara dai ki ce ni
ko zan samu ɗan saurayi da zai ɗauke cikin ƙannen Yarima”

Sai duk suka bushe da dariya Gwaggo Ramatu ta ce

“To shirya har ke aje da ke”

Motocin dake waje guda biyu sun kusan awa ɗaya sannan Namra ta fito tare da Gwaggo
Ramatu da su Maryam da Raihanatu suka shiga motocin.
A tunaninsu za a wace ne gidan sarkin kai tsaye sai suka ga ya kai su gidan
Ummi. Kunya sosai Namra ta samu kanta da ji lokacin da motar ta faka a bakin ƙofar
shiga falon Ummi. Meesha da Fauza suka fito da wayoyinsu a hannu suka ɗaukarta
video, Amal kuma ta zo da gudu ta rumgume ta.
Sam Amal bata gane wace Namra ba, sai dai ita Namra ta gane ta tun a wayar Abdool
da take kallon hotunan family ɗin ƴan gidansu. Cike suka tarar da gidan da mutane
tana saka ƙafarta cikin falon aka ɗauki guɗa. Ɗakin Ummi aka wuce da ita yayinda su
Maryam da Gwaggo suka tsaya a waje a falo suna gaisawa da jama'ah dan basa iya
tantance Ummi balle ma bata falon. Namra na shiga Ummi ta shigo sai ta yi saurin
yin ƙasa tana gaishe da Ummi. Domin sarai ta san ita mahaifiyar Abdool ga kamanin
Abdool nan xube a fuskarta kuma tana ganin ƴadda yake koɗa mahaifiyar ta shi a
instagram. Da Murmushi Ummi ta zauna saman gado tana dafa Namra.

“Tashi Tashi Ƴata Allah yayi miki albarka”

Sai Namra ta ɗago sai dai bata yarda ta koma saman gadon ba sai ta zauna ƙasa
fuskarka rufe da mayafinta.
Amal ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo cike da zumuɗin ita ƙanwar ango.

“Ummi kin ga fuskarta? Mu bata buɗe mana ba”

“Ai zata buɗe muku har sai kun gaji da ganinta”

“Ni dai ba zan iya haƙuri ba”

Ta faɗa a shagwaɓe. Ummi ta miƙe.tsaye tana gyaɗa kai ta nufi wata dorowa ta buɗe
ta ɗauko wasu robobi guda huɗu ta dawo ta zauna.

“Ungo wannan shanye duka”

Hannu biyu Namra tasa ta karɓa ta kafa kai ta shanye abunda yake ciki tas sannan ta
sake amsar na biyu ta shanye a na ukun ma shanyewa ta yi sai a huɗu ne Ummi tace
karta shanye ta raga. A nan Amal ta samu damar ganin fuskarta har ta yi mata hoto
da wayar Ummi.

Bayan Namra ta gama sha Ummi tasa Amal ta ɗauke robobin ta fitar, sai mai Makeup ta
shigo da kit ɗinta ta yi zaman dishin a gaban Ummi tana miƙa mata gaisuwa.
Meesha ce ta shigo ɗakin ɗauke da wani koren lace ta aje saman gado.

“Ummi ga shi”

Ummi ta kalli Namra tana nuna mata wani ƙaramin ɗaki dake gefen bathroom ta ce

“Ƴata shiga can ki shirya da wannan kayan”


Meesha ce ta riƙa ta sai suka nufi gurin tare Amal na gaba tana cigaba da leƙen
fuskarta.

“Ummi hancinta dogo ne.. Kuma tana da manyan ido.. Fuskarta ma mai D ce”

Ummi ta riƙe baki tana kallon ikon Allah, gulmar mutun a gaban idonshi, wannan
ƙulalaici ma Amal har ina!

Bayan ta saka lace ɗin ta fito sai duka suka fita suka barta da mai makeup ɗin,
ta zauna saman kujera Mai Makeup ta fara mata fentin fuska amman mai ma'ana, bayan
ta gama ta ɗaura mata ɗankwali. Ita kanta wacce ta yi mata kwaliyar sai da ta ɗauke
ta a hoto saboda kyau da tayi. Three later Ummi da Fauza da Meesha da Amal suka
dawo ɗakin

“Wowwwwwwwwwww”

Shine abunda duk suka faɗa ban da Ummi da ke murmushi. Ɗaukarta suka shiga yi hoto
suna selfie. Farar Alkyaba Ummi ta ɗauko miƙawa mai Makeup ɗin ta saka mata. Sannan
ta ɗauko fararen takalmi ta aje mata, sannan ta ɗauko akwatin turarenta ta buɗe
sisters ɗin Abdool suka shiga fesa mata. Ummi da kanta ta kamo hannunta ta saka
mata awarwaro, a ɗayan hannun kuma ta saka mata agogo.
Sannan ta miƙe tsaye, yayinda Namra take ƙasa risine ta saka mata sarka, sai ta
miƙawa mai makeup ɗin ta manna mata ƴan kunne.

“To ku fita ku bamu guri”

Kamar umarni suke jira duk suka fita daga ɗakin aka bar Ummi daga ita sai Namra.
Ummi ta kama hannayen Namra biyu ta riƙe.

“Ƴata ke tauraruwace, yanzu kin shigo cikin wani sabon shafi, ki haƙuri da duk
abunda zaki ji, ba kowa ne zai faɗa miki magana ki mayar masa ba wanna ba tarbiya
ba, ki zama mai riƙe sirrin mijinki da iyalansa, idan yayi miki ba dai-dai ba ki
fara kawo ƙararsa a guna kamin ki kai ko ina.

Sannan yanzu zaku je gidan Mai Martaba ne wato mahaifin Abdallah, zaki gaishe da
shi da iyalinsa, idan kin shiga a tsakiyar falon zaki zauna, karki raɓi kujera,
idan kuma kika fito Amal zata ɗauki takalmin ta juyo miki da su ki saka, karki
yarda idonki ya haɗu da na matan mai martaba balle ma mai martaba da kansa, karki
yarda ki ci abunda za a baki za a miki kallon rashin kunya ko marar tarbiya.

Da misalin ƙarfe tara zaku fita gurin walimar cin abinci da Mai martaba ya shirya
muku, Sai dai kamin kuje gurin walimar uwargidan Mai Martaba nasan zata nemi canja
miki tufafi, zata aiko barorinta su canja miki kaya, karki yarda su canja miki
komai, zan bawa Meesha da Fauza kayan da zaki canja anjima kuma kai makeup zata iso
ƙarfe bakwai ta gyara miki fuska. Sai dai karki yarda lokacin Sallah yayi baki yi
ba, Allah ya miki albarka”

“Na gode Mama na gode”

Ummi taɓshafa kanta tana murmushi sai ta miƙe tsaye ta fita. Bayan few minutes
gwaggo da Maryam suka shigo suka riƙa Namra suka fita tare.

Mashallah shine abunda duk wanda ya kalli fuskar Namra da tufafinta yake faɗa.
Motar da Namra ta shiga daban ita kaɗai ake driving su kuma suka shiga wasu
motocin.

Suna isa Faɗar Mai Martaba, aka ɗauki busa ana zuba musu kirari, sai barori suka
sheƙo da gudu suna guda aka shimfiɗawa Namra carpet mai sunan Masarautar, sai wani
ƙaton mutum cikin kayan dogarai yazo ya buɗewa Namra mota.

Hasbunallahu Namra ta karanta a zuciyarta sannan ta saka ƙafarta ta sauko daga


cikin motar. Sai barorin suka rufa mata baya, wasu kuma suka wuce gurin tawagar da
suka zo tare da Namra aka musu iso zuwa cikin gida.

Cike da hankali da natsuwa Namra take takawa barori suna take mata baya har suka
isa gaban wata ƙatuwar ƙofa. Bakin ƙofar barorin suka tsaya sai Dogarai suka
wangale mata ƙofar suka bakin ƙofar suna zuba mata kirari.

“shiga da ƙafar dama yar gidan girma, ƴar da tafi ko wace mace sa'ah a duniya, an
gaishe ki gimbiya matar yarima, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana”

Kunna kai ta yi cikin faɗar, tana wuce carpet na farko ta cire takalminta saboda ta
ga jerin takalmi a gurin. Wani irin maryaba da girma ta ji ya kamata musamman ta ta
risina gaban mai martaba tana gaishe shi.

“Sarki ya amsa kuma ya gaishe ki”

Shine abunda mafadawan suke faɗi, sannan mai martaba yayi musu hannu suka tashi
suka bar shi da Namra. Nasiha sosai yayi mata akan rayuwa da kuma zaman aure sai
kuma kan haƙuri da iya kula da mutane.
Sai da Mai Martaba ya tabbatar Nasihar ta shiga jikinta sannan ya sallame dan ta
shiga cikin gida ta gaishe da matansa.

ASIM POV.

Tun bayan da ya saka ƙarin aure a gabansa be waiwayi kowa ba, duk da da irin kuka
da magiyar da Mardiya ta riƙa masa akan karka ya ƙara auren. Sai dai be ji ba sai
da ya auro ƴar manyan mutane wato Balkisu.
An kashe dukiya sosai gurin auren daga duka ɓangarorin guda biyu, domin ko gidan
da ya sakata mai tsada ne sosai.
Gida ne mai part biyu a ɗayan part ɗin ya saka Mardiya ta ƴar tabarmarta ta
shinfiɗa saboda bata katifa kuma malamin da suka je gurinsa ya faɗa musu karta
yarda ta saka katifa ko gado a gidan, abun shinfiɗa kawai zata je da shi sai kayan
abinci.

Haka ta riƙa zama har tsawon wata tara duk wanda ya leƙa part ɗinta sai ya sha
mamakin ganin babu komai a ciki, part ɗin Balkisu kam Aljannar duniya. Wannan
matsalar ta damu Mardiya sosai har ta kai bata da wani sukuni a rayuwarta, ga
mafarkin wutar da take bata daina ba, sau da dama zata zauna ta yi da kuka, wani
lokaci kuma ko da tana cikin mutane zaka ganta ta koma wata iri kamar wacce aka
ɗauki tunanin duniya aka ɗora mata. Ita da tayi aure dan jindaɗi abu ya zame mata
ɗan zane, ta san matsalar daga gareta ne saboda yawan mafarkin wutar da take kuma
gashi ita Balkisu wutar ba kama ta ko da sau ɗaya.

Ba ko wace ranar girkinta ba ne Asim yake kwana part ɗinta saboda bata da katifa
balle kuma gado, sai a lokacin da yaji yana buƙatarta. Yau ma part ɗin Balkisu ya
kwana, bayan yayi wanka ya shirya ya leƙo part ɗinta suka gaisa, duk ta yi wani
zurun-zurun gwanin tausayi kamar marar lafiya, bayan sun gaisa ya dawo part ɗin
Balkisu da yi mata sallama, sai ya samu tana tsaye jikin ƙofa tana jiranshi.

“Sai ina?”

Ta faɗa ta wani langaɓar da wuya tana kaɗa jiki, kamar wata tsohuwar karuwa.

“Gari zan shiga, amman zan dawo ajima saboda zamu je wani biki da za'ayi a faɗar
Mai Martaba, kuma an gayyace mu kinsa ɗansa abokina ne”

Ya faɗa irin yana alfahari ɗin nan.

“Okay to a dawo lafiya, kar dai aje ayi gane-gane”

“Ni wa zan gani, ga ni da ke cikin gida”

Matsowa ta yi ta masa kiss, sannan ya juya ya tafi tana ɗaga masa hannu.

WHAT DO YOU EXPECT NEXT...?

[7/28, 10:15 PM] Khadeeja Candy♥: *91*

Kamar yadda Ummi tace mata a duk ɗakin da ta shiga ta kan zauna a tsakiyar ne har
ta gama gaisuwar ta tashi, bata yarda ta haɗa ido da matan mai martaba. Sai dai a
yadda take tararda ko wanne falo tana auna yawan family da mai martaba yake da su a
gidan, wata ƙila kuma saboda tana amarya ne suke zuwa ganinta.
Bayan ta gaishesu aka kaita ɗakin Hajiya Shafa, sai aka kawo musu abinci da
drinks. Bata ci komai ba duk kuwa da irin matsa mata da suka riƙa yi. Ana yin
sallah magariba duk suka shiga shiryawa, wasu motocin Abdool ya aiko aka ɗauki su
Maryam aka mayarda masaukinsu domin suma su shirya. Bayan sun wuce wata cikin
ƴaƴan Hajiya Shafa ta shigo tana faɗin.

“Hajiya tace Mai Makeup zata zo ta gyara miki fuskarki, kuma za a kawo miki kaya ki
canja”

Namra ta amsa da to. Har Amal ta buɗe baki ta gatsawa yarinyar magana sai Meesha ta
riga ta.

“Ai ko har Ummi ta yi magana da mai Makeup zata zo yanzu ta mata”

“Auoak”

Yarinyar ta faɗa sai ta juya tana tafiya cike da isa ta fice. Amal taja tsaki tana
binta da harara.

“Wai yarinyar nan tun ɗazu nake ganin tana ta wani shauƙi”

Meesha ta zaro ido.

“Ina ruwanki? Amal me yake cikin kan ki?”

“Aljanuna akai na”

“Ƴar gadon baƙar magana duk abunda kika yi sai na faɗawa Ummi”

Ta tsuƙe baki ta juyarda fuska. Around eight o'clock mai Makeup ɗin ta iso. Namra
bata yarda an mata makeup ɗin ba sai da ta yi sallah isha'i.

Ƙarfe tara dai-dai Abdool ya aika aka kwaso ƴan'uwan Namra aka kaisu tsohuwar faɗar
Mai Martaba inda aka shirya taron.

Sai tara da kwata Amarya ta iso barori na take mata baya, farin lace ne mai
shegen kyau da farar Alkyaba, fararen takalmi da farar sarƙa, mai video na biye da
iya ita yana ɗauka har aka ta kai zamanin da aka tanadar mata dan ta zauna. Bayan
kamar minti biyar da zamanta Abdool ya shigo shi da abokaninshi, farar shadda ce
jikinshi da fararen takalma sai farin rawani da farar alkyaɓa, kallonsa take kamar
yadda kowa yake kallonsa, ita kanta ta san ta yi sa'ar miji, yadda yayi mata
kwarjini da haiba ga fuskarsa sai annuri take, ɗaya bayan ɗaya yake tafiya ana masa
kirari ana koɗashi. A kujerar da Namra take zaune ya zauna sai masu busar suka koma
gefe suka cigaba da busar. Ko ina ka duba masu kaki kake gani sun cika gurin wato
gayyar Abdool ne kawai sai kuma na ƴan'uwansa. Saboda Mai Martaba be gayyaci kowa
ba walima ce da ya shirya a cikin gidanshi domin addu'ah kawai da kuma son tara
family ɗinsa guri ɗaya, wannan walimar ta al'ada ce da ya saba shiryawa a duk
lokacin da ya aurar, ko da kuwa mace ce zai gayyato mijinta azo gidan ayi walima.

Yara da rabi Mai Martaba ya iso, daman matanshi sun daɗe da isa gurin tun kamin
amarya da ango su isa. Karatun alqur'ane aka buɗe filin da shi sannan Hajiya Shafa
ta miƙe tsaye ta karɓi microphone tana yi ma kowa barka da zuwa.

ASIM POV.

Tsaki yake ja lokaci zuwa lokaci kamin ya kalli wanda ya shigo motar yanzu ya ce.

“Kaga Mubarak bana son jira, na tsani jira wallahi, ni da nasan haka zaka ɓata min
lokaci ba zan je ba wallahi”

Mutumen ya kalleta yana murmushi.

“Sorry Man ai gani na zo yanzu”

Asim ne yake driving har suka isa Kan wurin sarki, ba a basu damar shiga ba duk da
guest pass ɗin da suka nuna, sojoji ne jibge a gurin babu abunda suke sai kai da
kawo suna ta ƙoƙarin ganin su bada tsaro agurin. Har Asim yaja motarsa su koma sai
Abokinshi ya hana shi.

“Bari na kira shi”

Wayarsa ya fiddo ya kira wayar ƙanen Abdool wanda suke uba ɗaya wato Zayyan.
Bayan ya faɗa masa abunda ya faru sai ya miƙawa Sojan wayar suka yi waya, sannan
aka buɗe musu page ɗin suka shiga. A gate na buyu aka nuna musu inda zasu faka
motarsu, sannan suka fito sojoji suka tantance su sannan aka buɗe musu gate ɗin
suka taka da ƙafa suka shiga harabar gidan.

Ba Zayyan ne kawai a gurin ba, domin yasam abokansa da yawa sun je bikin dan haka
ya kira wani abokinsa yayi directions ɗinsu inda ake bikin saboda gidan ya kasu
kashi kashi. Fitowa yayi ya shiga da su saboda yasan duk yadda zai faɗa musu ba
ganewa zasu yi ba.

Wani kalar baƙauye Asim da abokinshi suka zama tun a bakin ƙofar shiga, a takw ya
manta da a katsina yake, saboda gurin ya koma kamar sabuwar Abuja, daman tun farkon
shigowarsa gidan ya gane shi ɗin ba kowa ba ne a cikin masu kuɗi, dan ya fahimci ko
akaifar Mai Martaba be kamo ba indai akan dukiya ne. A bakin ƙofar faɗar ma sai da
aka tantance su sannan aka basu guri suka sshiga. Ko da suka shiga Malama Hauwa na
tsaye tana gabatarda ƙasida akan haƙoƙin mijin aka mata. Har Asim ya zauna be gane
Namra ba ce saboda ta canja gaba ɗaya ta koma kamar ba ita ba, sai da ya gama
gaisawa da waɗanda ya sani a gurin sannan ya zauna ya natsu tare ta tattara
hankalinta gaba ɗaya ya mayar gurin mai wa'azin. Kama da Namra yake gani a fuskar
Amaryar sai dai wannan kamar ta fi Namra kyau da haske, baya iya ganin angon saboda
rawanin da ya rufe masa fuska.

“Kamar Namra wallahi”


Ya faɗa a fili yana kallon abokin na shi, fuskarsa with so much confused.

“Wacece Namra?”

“Matata mana”

Har abokin yasa dariya sai yayi saurin rufe bakinsa tunawa da inda suke.

“Haba Asim kamar wanda ya sha wani abu, matarka ɗan sarki zai aura? Look at you”

Ya ciro wayarsa ya kira yaron daya saba bashi labarin halin da Namra take ciki sai
aka yi rashin sa'ah be ɗauka ba. Sai kawai ya kira wani abokinsa da ke sokoto dan
gaba ɗaya natsuwarshi ta bar jikinshi. Miƙewa yayi tsaye da zimmar fita daga gurin
saboda ƙarar loudspeaker ba zata bar shi yayi magana yadda yake so ba, miƙewarshi
ke da wuya ya hango Maryam ta je tana magana da Namra a kunne.

“Wallahi wannan Matatace, Namra ce Wallahi”

Abokin yayi saurin riƙo shi ya zaunar domin shi kaɗai yake jin abunda Asim ke faɗa,
hankalin kowa yana can gurin amarya da ango.

“Matata ce wannan wallahi”

“Na ji matar ka ce muje gida”

Ya faɗa dan yana ganin kamar Asim baya cikin hankalin kansa.

Asim ya fisge hannunshi zuciyarsa na mugun bugawa da ingizashi yayi duk abunda zai
yi.

“Baka yarda da ni ba?”

Biyu daga cikin mutanen da suke gurin ne hankalinsu ya dawo gurin Asim, har ɗayan
ta tambaya ganin yadda Asim ke hucin hanci.

“Wai miya faru ne?”

“Wannan matar yake cewa Matarshi ce”

“Asim ko ka sha wani abu?”

Ɗayan ya faɗa yana kallonshi.

“Babu abunda na sha gaskiya na ke faɗa wallahi, matatace wannan”

“Ka rufa mana asiri mu fita gurin nan lafiya, wane irin matarka wai? Matarka zata
fita daga gidan ka ta auri wani?”

“Tana gidansu ai tana gidansu, ita ce matata ta farko da na fara aure”

“Ka sake ta ko? Shi kuma ya aura ai daman na ji ance bazawara ce ya aura”

“What...? Wallahi wannan Namra ce”

Zayyan ne ya juyo yana kallon Asim dake kumfar baki, yana sauraren abunda yake
faɗa, sai ya baro mazauminsa ya dawo kusa da Asim ya zauna yana faɗin.

“Ina fatar dai lafiya”


Da lafiya ƙalau duk suka amsa mashi suna murmushi, sai Asim ya girgiza kai ya ce.

“Ba lafiya ba, wannan matar matatace wallahi”

Wani wawan kallo Zayyan ya aika masa.

“Baka da hankali Asim wallahi, ƙa fara shaye-shaye ban gayyace ka a nan dan ka ɓata
min rai ba, tashi ka bar gurin nan”

“Kana tunanin bana da hankali ko?”

Asim ya nuna kanshi yana ƙoƙarin tashi tsaye..


[7/30, 7:12 PM] Khadeeja Candy♥: *92*

Zayyan yayi saurin riƙe shi

“No karka ja kanka wahala a gurin taron nan, muje waje na saurareka wata ƙila kana
da hujja”

Yana faɗar haka, ya miƙe tsaye suka fita daga faɗar suka nufi wani ɓangare na
masarautar sai ga wasu abokansa sun biyo bayanshi.

“Faɗa min taya wannan matar ta zama matarka?”

Asim ya natsu sosai yana tsara irin ƙaryar da hankali zai ɗauka.

“Wannan yarinyar sunanta Khadija amman Namra muke kiranta, sunan mahaifinta Manjo
Usman Zamau a sokoto yake da zama, ni kuma ai kasan ɗan sokoto ne ko? A can muka
haɗu da ita a makaranta iyayenta basa so na a haka muka yi aure daga baya itama ta
fara tsanata sanadin hakan ta gudu da cikina kuma ba gidansu ta koma ba sai taje
wani gurin daban domin na aika nemanta a gidansu aka ce bata zo ba, daga lokacin
ban sake sakata a ido ba, sanadin hakan nayi aure na auri Mardiya yanzu kuma ga
wannan amaryar da na yi, kuma ta inda na tabbatar da wannan itace tana da ƙanwa
Maryam wacce ta yi magana da ita a yanzu”

Zayyan yayi shiru yana nazari, tabbas ɗan'uwansa bazarawa ya aura kuma ƴar sokoto
idan be manta ba kamar Mai Martaba ya taɓa faɗa masa ƴar tsohon soja ce bayan haka
kuma sunanta Namra.

“Amman kai baka sake ta ba?”

Abokinshi ya tambaya.

“Idan na saketa mi zai sa na zo yanzu na ce matatace”

“Lallai akwai jan aiki, ta yaudari Abdallah kenan”

Zayyan ya faɗa yana zuba hannayensa a aljihu.

“Ka min wani lamani mana Asim, ka haƙura har a gama walimar nan sai na samu Mai
Martaba na faɗa masa”

“Na aminta”

Ya faɗa zuciyarsa na mugun bugawa. Daga Zayyan ɗin har Friends ɗinsa ruɗani suka
shiga da tunanin yadda haka zai faru da kuma halin da ko wannensu zai shiga idan ya
samu labarin abunda Asim yace.
Ko da suka koma ciki wani malami ne yake wa'azi akan haƙoƙin mace akan mijinta.
Zaunawa suka yi kowa da abunda yake saƙawa a zuciyarsa, ta ɓangaren Asim kuma yana
jin zai yi ganganci idan har ya kuskura cewa Namra matarsa ce tun da yasan har ga
Allah ya sake ta, sai dai what yasan tana da cikinsa ta bar gidan, and yana ganin
kamar wayo ne Zayyan zai masa a zasu iya taushe maganar idan babu wanda ya sani
amman idan aka ji dole a tsaya a bincike.
Wani irin abu ne ya fisgi zuciyarsa sai kawai ya miƙe tsaye ya ɗaga kujera da yake
zaune ya jefar dan kawai hankalin kowa ya dawo gurinsa. A take kowa ya juyo yana
kallonsa kasancewar yana can baya ne, sojoji kuma suka yo kansa da gudu, sai ya
kware baki yana ihun.

“Wannan matar ta yi aure kan aure ne, matatace Namra matatace”

Ba kowa ba ne yake jin abunda yake faɗa sai waɗanda ke kusa da shi, sai dai kowa
zai iya fahimtar faɗa ne yake, kamin sojaji su buga masa bindiga a ƙwari (knees) ya
faɗi a gurin sai wani ya aika masa wani mugun shuri a ciki kamin su miƙar da shi
tsaye su banƙareshi su fita da shi, babu wanda yace uffan har Zayyan da yake
abokinsa.
Bayan an fita da Asim, Zayyan ya miƙe tsaye ya ƙarasa gaban Mai Martaba ya kai
bakinsa dai-dai kunnensa yayi masa raɗa.

NAMRA POV.

Kaganin komai take kamar a mafarki, a kujerar da take zaune kawai a abar kallo ce,
yau itace ake yi ma walimar aure da ɗan sarki, kuma sarkin yana zaune yana
kallonsu. Wasu hawaye ta ji sun zubo mata masu sanyi, kamin hankalinta da dubanta
ya karkata kan hayaniyar da take hangowa.

Wani irin mugun faɗuwa gabanta yayi, tasan yana nesa da ita amman idonta ba zai
mata gizo ba, tabbas Asim take hangowa, sai dai bata iya jin abunda yake faɗa.

‘Miya kawo shi a nan?’

Itace tambayar da ta fara zuwa mata a zuciya. Sai kawai ta ji hannun Abdool cikin
nata yana ƙoƙarin luma yatsunsa cikin nata, matse mata hannu yayi gam kamar za a
ƙwace masa ita, be wayancin Asim sosai ba kasancewar gani ɗaya yayi masa lokacin da
zai bata kyautar gida, gashi kuma yana nesa da su balle ya iya tantancewa, sam be
kawo zuciyarsa Asim zai so gurin ba, a tunaninsa wani ɗan shaye-shaye ne a cikin
ƴaƴan manya maybe wani abokinsa ko ƴan'uwansa suka gayyato shi.

Hawayen da ya tsinkaya a idon Namra ne yasa shi zira hannunshi ya kama nata, domin
idan akwai abunda ya tsana a duniya a yanzu zubar hawayenta ne.

A tsanake aka yi komai cikin kwanciyar hankali da lumana, yadda aka gabatar da
walimar kowa sai yabawa yake, babu ƙaryar kuɗi kuma komawa ya samu takeaway, abinci
kuma sai wanda ranka ke so zaka je ka ɗiba.

Nasiha mai ratsa jiki da kunnuwa Mai martaba yayi ma duka ma'aurantan guda biyu,
sannan kuma yayi jawabin godiya. Bayan anci an sha sai wani babban malami ya miƙe
tsaye yayi addu'a akan ma'auratan da kuma Mai Martaba gaba ɗaya.

Sai a lokacin da za a tashi sannan Abdool ya sake hannun Namra suka miƙe tsaye a
tare ana musu busa da kirari a lokaci ɗaya.
A tare suke aje ƙafa, su ɗauka a lokaci ɗaya har suka kai bakin ƙofar faɗar. Anan
sojojin da aka jera a gurin suka fara tasu busar suna sare masa barori na watsar
jar fulawa wasu kuma na fesa turare. Mai Video Camera na gaba yana ɗauka, ɗayan
kuma yana a baya yana nashi ɗaukar, masu ɗaukar hoto kuma suna aikinsu.
Bayan Ango da Amarya sun wuce ƙannen Abdool mata suka jera ɓangaren dama kowa da
sari ja, mazan kuma suna ɓangaren hagu da farar shadda, haka suka jero suka biyo
hanya gwanin ban sha'awa suna wucewa. Mai Martaba ne na uku bayan sun wuce, masu
busar suka biyo shi suna masa busa dogarai na tare shi dama da hagu har ya wuce.

A harabar Masarautar suka tsaya suna hoto tare da ƴan'uwa, Mai Martaba kuma suka
isoshi faɗarshi aka ɗauke su hoto.
Ɗakin Hajiya Shafa aka Mayardar da Namra, yayinda Abdool kuma ya nufi
ɓangarensa da ke cikin gidan.

A lokacin ne Meesha ta cirewa Namra Alkyabar da ke jikinta ta miƙa mata abinci


domin ita da Abdool basu ci abinci ba a gurin walimar.

“Bana jin yunwa”

Hankalinta gaba ɗaya yana gurin Asim, ta kasa gano dalilin daya kawo shi gurin.

“Dan Allah je ki kira min Maryam”

Amal ta aje wayar da ke hannunta ta miƙe tsaye da sauri.

“Adda Namra bari na kira ta”

Meesha ta taɓe baki.

“Ƴan ƙwaran suna nan kenan”

Bata ɗauki lokaci ba sai gata ta dawo tare da Maryam ɗin. A nan Meesha ta miƙe
tsaye ta kama hannun Amal suka fice saboda ta san komai yana buƙatar sirri.

“Anty Namra ga ni”

“Maryam kin ga wanda ya tada rigima ɗazu?”

“Eh amman ban ga ko waye ba”

“Asim ne fa”

“Asim?”

Ya amsa da ƙarfi.

“Miya kawo shi a nan? Ko ganin ƙwan ya zo zuciyarsa ta kasa ɗauka shi ne ya tada
rigima, yaso ya ɓata bikin ne Allah be bashi dama ba”

“Tsoro nake ji Maryam idan ba wani abun ya zo yi ba, idan ba haka ba to me zai kawo
shi nan?”

“Ya zo yaga abunda za a yi ne, babu wani abunda zai yi rigima ce kuma ya samu dai-
dai shi”

Maryam bata gama rufe baki ba wata mai kama da Abdool ta shigo ɗakin cike da ladabi
ta ce

“Adda Namra Mai martaba na son ganinki yanzu”

Gabanta ne ya yankeya faɗi, cikin rawar muryar tace

“Maryam ɗauko min mayafina”


Maryan taƙe tsaye ta ɗauko mata farin mayafin da dake saman gado ba tare da ta kawo
ma kanta komai ba.
Sai da ta yafa mayafin sannan ta miƙe tsaye yarinyar ta kama hannunta suka fice.

Ɓangaren Mai Martaba Yarinyar ta nufa wato turakarsa, wani ɗan ƙaramin falon Mai
Martaba yarinya ta kaita, cike da ladabi Namra ta shiga kanta a ƙasa, sai dai hakan
be hanata ango Abdool dake gaban Mai Martaba kamar mai neman gafara ba.
Ita ƙasa ta zauna, sai Yarinyar ta juya ta fice tare da rufo ƙofar.

Sun daɗe a haka, baka jin sautin komai a ɗakin sai sanyin ac dake tsara jikinsu.
Zuwa can Mai Martaba ya ɗora ƙafarsa ɗaya saman ɗaya ya soma magana a tsanake.

“Namra kin san Asim?”

“Allah ya taimaki mai martaba, tsohon mijina ne”

“Taya zamu iya tabbatar da ya sake ki?”

“Ya sake ni a shakarar da ta gabata, kuma iyayena sun san da hakan”

“Akwai takardar saki a hannunki?”

“Be bani ba, da baki yayi furucin Mai Martaba, Allah shine shaidata”

“Mutumen da ya ɗauki hankalin mitane a ɗazun tsohon mijinki ne, kuma yana da'awar
be sake ki ba har ma akwai akwai ɗa a tsakanin ku...”

Da sauri Namra ta ɗago kai ta kalli Mai martaba for the first time, idonta har ya
kawo ƙwalla, kai ta girgiza.

“Ƙarya yake yi Mai Martaba, Wallahi ya sake ni”

Sai hawaye suka fara mata zuba. Kan Abdool na ƙasa saboda Mai Martaba be bashi
damar magana ba.

“Babana!”

Mai Martaba ya kira sunanshi. Sai.ya ɗago da idonshi da suka rine suka canja kala
saboda ɓacin rai ya ce

“Wallahi ya sake ta Mai Martaba”

“Kana da takardar sakin ne?”

“A'a amman nasan ba zata min ƙarya ba, kuma na san babban mutum kamar Manjo ba zai
yarda ƴarsa ta yi aure kan aure ba”

Mai Martaba ya ɗauki wayarsa ya kira wata number.

“A shigo da shi”

Yana faɗar hakan ya sauke wayar. Ko minti uku ba a ƙara ba, sai ga Asim an shigo da
shi yana tsingilta, gaba ɗaya kammaninsa sauya jini sai zuba yake a kansa.
Dogarawa suka durƙusar da shi gaban Mai Martaba.

“Me aka masa haka?”

“Allah ya taimake ka dukan da sojoji suka masa ɗazun ne”


Kai kawai ya ɗaga musu suka juya suka fice. Mai Martaba ya kalli Asim da kyau ya
ce.

“Wannan ita ce matarka?”

Sai kawai ya fashe da kuka ya girgiza kai.

“A'a ba ita bace ƙarya na ke”

“Karka ji tsoro kar dukan da aka maka ya tsoratar da kai, na maka alƙawari babu
wanda zai sake sa maka hannu, faɗa min gaskiya wannan itace matarka?”

Mai Martaba ya faɗa a natse. Da idonsa ɗaya ya kalli Namra saboda ɗayan ya kumbure,
sai kuma ya maida dubansa gurin Abdool, sai a yanzu ya iya tantance Abdool.saboda
ɗazun be san ko waye ba.

“Itace ranka ya daɗe. Namra ina ɗa na? Da cikina ta gudu, kuma sanadin wannan
mutumen ta gudu, saboda yana tare da ita har yayi mata kyautar gida sanadin hakan
na daketa sai ta gudu ta bar gidan, gidan yana nan a unguwar nasarawa”

Kai kawai Namra take girgizawa hawaye na mata zuba. Abdool kuma zuciyarsa ta yi
mugun kawowa sai dai babu yadda zai yi tun da a gaban Mai Martaba suke, kuma duk
wani unƙuri da zai yi zai ƙara ɗaure kansa ne kawai. Can ciki ya jiyo muryar Mai
Martaba na jefo masa tambaya.

“Ka taɓa mata kyautar gida kuma tana da aure?”

Sai da ya taushe fushin da ke zuciyarsa sannan ya iya furta.

“Na taɓa Mai Martaba, amman ba da wata niyar na yi ba, a lokacin basa da kuɗin
biyan hayar ne kuma Ummi ta basu lokacin tashi, saboda gidan Amal ne wanda gobara
ta ƙone, a lokacin za ayi gyaransa ne”

Mai Martaba yayi shiru yana nazari a zuciyarsa, yasan ɗansa ba zai masa ƙarya ba,
kuma baya daga cikin ƴaƴanan mazinata balle har ya zarge shi, kuma yasan lokacin da
ya kawo masa labarin Namra, sai dai ɗan yau ba a shaidunsa, kuma zai iyayuwa ita
Namra ɗin ta yaudari ɗansa.

“A wani guri kake zaune?”

Mai Martaba ya tambayi Asim a take ya amsa masa ya faɗa masa.

“Tashi ka yi tafiyarka”

Har ya miƙe tsaye sai kuma ya ce

“Mai Martaba kar naje gida wani abun ya same ni”

“Babu abunda zai same ka, indai ni na haifi Abdallah ko hararka ba zai sake yi ba”

Da tsinginta ya fice. Sannan Mai Martaba ya kalli Namra ya ce.

“Za a maidaki gurin Ummi ba zaki tare a yau ba, zan yi magana da mahaifinki”

Cikin wani irin nauyin jiki da zuciya Namra ta miƙe tsaye jiri na ɗibarta, aiko
tana kaiwa bakin ƙofa ta sai tayi baya-baya ta faɗi ƙasa sumamamiya.
A take Abdool ya manta da agaban Mai Martaba yake, a guje ya ƙarasa inda take
yasa hannunshi ya ɗauke yana kiran sunanta amman ina ta riga tayi nisa.
A firgice ya fita da ita a falon kamar wanda ya tallaɓo jaririya. Mamaki da aljab
ya hana kowa magana sai kallon ikon Allah suke, Abdool ya talloɓo Namra sai gudu
yake ya nufi parking space da ita. Sojojinshi na hango halin da yake da sauri suka
buɗe mota ɗayan ya shiga a driver seat yayi ma motar key, Abdool na isa ya saka
Namra gidan baya, sannan shi ma ya shiga.
Wasu sojojin suka shiga wata motar suka rufa masa baya.

@360 suka isa asibiti kai tsaye aka wuce da ita emergency, likitoci suka shiga bata
taimakon gaggauwa.
Yana gurin zaune ya dafe kai wasu ƴan gidansu suka iso, cikin har da Hajiya Shafa.
Bayan kamar mintuna talatin likitocin suka fito, ɗaya daga cikinsu ne ya tsaya
yana yi ma Hajiya bayani wai a barta ta samu bachi sun mata allura saboda akwai
gajiya sosai a tare da ita.

Abdool na zaune a gurin har su Hajiya Shafa suka shiga suka fito, tare da sisters
na shi.

“Babangida (Sunan da take kiransa da shi kenan kasancewar sunan mahaifin Mai
Martaba ne aka sakaasa) Mu zamu tafi tun da abun da sauƙi, kuma likita yace ana
buƙatar ta huta, Hajiya kilishi zata tsaya nan ta kwana, kuma ka faɗawa sojojinka
kar su bar kowa ya shigo, ga kuma dogarawa nan Mai Martaba ya iko maka in case
of...”

Kai kawai ya iya ɗaga mata, sai sisters ɗinsa da waɗanda suka zo tare suka masa
Allah ya sauwaƙe.

Sai da suka fice sannan ya miƙe tsaye yana faɗawa sojan da ke kusa da shi cewar kar
ya bar kowa ya shigo gurin, yana rufe baki sai ga Asiya Sister shi ta dawo da gudu
ta miƙawa sojanshi carpet da hijab.

“Wai ance a bawa Gwaggo”

Da kanshi ya karɓi sallayar da Hijab ɗin ya nufi ɗakin. Wani abun burgewa sai da
sojan ya sare masa sannan ya miƙa nasa.

Yana tura ƙofar ɗakin ya hango Namra kwance gefen gadon an ɗaura mata drip. Hajiya
Kilishi kuma na zaune saman kujera sai amsa waya take. Tana ganinshi ta miƙe tsaye
ta fice, ƙarasawa yayi ya aje carpet ɗin ya zauna saman gadon ya kai hannunshi ya
shafa fuskarta. A hankali ya sauke ajiyar zuciya sai ya sauka ya zagaya ta bayanta
ya hau saman hagon ya rumgumeta ya luma yatsunsa cikin nata, sai hawaye suka
gangaro daga idonshi suka sauka saman ƙananan kitson da ke kanta.
Jin wayarsa na ringing yasa ya fiddota daga aljihun wandonshi ya kashe ta gaba
ɗaya, ya lumshe ido yana ƙara janta jikinsa.

A wani ɗakin Hajiya Kilishi ta kwana, domin be sauka daga kan gadon ba sai da aka
kira sallah asuba. Sannan ya sauka saman gadon ya shiga banɗakin dake room ɗin yayi
alwala ya fito shi da sojojinsa suka nufi masallaci yayinda aka bar dogarawa suna
cigaba da gadinta.

Bayan ya fita ne Hajiya Kilishi ya dawo ɗakin ta yi sallah asuba, bayan ta gama ya
hau amsa wayar da ake mata dan tambayar jikin Namra. Sai ga Abdool ya dawo ɗakin a
dole ta miƙe tana amsa gaisuwarsa ta fice daga ɗakin.
Wannan karon saman kujera ya zauna ya matsa can kusa da fuskarta ya ɗora tashi
saman gado ya kwantar, sai hancinshi ya riƙa gogar nata, numfashinsu na taraiyya da
juna.

A hankali ta buɗe ido karaf cikin nashi, bakinta da ke saitin nashi yayi ma kiss
sannan ya tashi zaune daidai yana riƙa hannunta, sai itama ta tashi tana cigaba da
kallonshi idonta sun yi wani fari.
Har cikin jininshi yake jin tsanyin dake cikin hannunta, zuciyarsa cike da
tausayinta.

“Sannu”

Ya faɗa yana kai hannu ya shafa gefen fuskarta.

“Sallah”

Ta ce a kasale. Miƙewa yayi tsaye ya shiga bathroom ɗin ɗakin ya ɗauko ƙaramin
bokin da ke ciki ya fito sai ya buɗe ƙofar ɗakin yayi magana da boys ɗinsa da suke
gurin, sannan ya dawo ya zauna a kusa da ita.

“Za a kawo ruwa yanzu, muje ki yi fitsari”

Ƙoƙarin saukowa ta riƙa yi sai kawai ya ɗauke ta ya nufi bathroom ɗin da ita.
Ƙoƙarin ɗaga mata saket ɗin ya riƙa yi sai ta riƙe, ya kalleta.

“Baki da ƙarfi Abnam”

“Zan iya”

Baya son musa mata, sai kawai ya fito yaja mata ƙofar. Da dafe dafen bango ta yi
fitsarin ta fito, sai ya sake ɗaukarta ya maida saman gadon.

“Allah ya baki lafiya”

Ya faɗa yana kwantarda kanta saman kafaɗarshi. Cikin ƙanƙanen lokaci aka buga ƙofar
ɗakin sai ya ɗagarda kanta shi kuma ya tashi ya buɗe ya karɓo robar da carton ɗin
ruwan faro, sai da ya buɗe ruwan sannan ya zauna kusa da ita ya kama hannayenta ya
wanke mata su sau uku, sai ya zuba ruwa a hannunshi ya kai mata a baki ta kurkure
bakinta ta zuba cikin robar sai yasa yatsansa ya wanke mata haƙora, sai ya sake
zuba ruwan a hannunshi ya kai mata a baki ta kkurkura har sau biyu sannan ya shaƙa
mata hanci sai kuma ya riƙa mata hancin ta face, ya wanke mata fuskarta sannan ya
wanke hannayenta zuwa murafiƙai, ya shafa mata kai ya ƙwaƙwala mata kunnuwa sai ya
saukar da robar ƙasa ƙasa ya kama ƙafafunta ya tsattsafe ya wanke su tas, sannan ya
ɗauke robar ya kai bathroom ya fita ya karɓo mata carpet da hijab.
Sai da ya shinfiɗa mata carpet ɗin sannan ya saka mata hijabin, ya sauƙo da ita
saman gadon ya tsayar, ganin jikinta rawa yasa ya zaunar da ita, ya tattara
hankalinsa ya miƙa mata yana kallon yadda take sallah a zaune cike da tausayawa.
Tana ƙarewa ya dawo kusa da ita ya zauna, sai ta kwantar da kanta saman kafaɗarshi
tana hawaye. Hannayensa biyu yasa ya ɗago fuskarta ya kai bakinshi daidai hawayenta
yayi mata kiss.

“Babu wanda ya isa ya shiga tsakanin mu Inshallah”

Ya faɗa kamar mai raɗa, sai kawai ta fashe da kuka shi kuma ya rumgumeta a
ƙirjinsa, ya lumshe ido yana sauraren sautin kukanta dake tashi a hankali.

RASHIDA FINAL POINT OF VIEW (POV).

Ita ce ta biyu wacce ta miƙe tsaye ta yi jawabin bayan shugabar ƙungiyarsu ta gama,
kasancewar yanzu ita ce mataimakiyar shugaba, a duk inda za a je da ita ake zuwa
cikin da wajen garin kaduna, har South west, south south suke zuwa gurin wayarda
kan al'umma akan a daina ƙyamar masu ɗauke da cutar hiv, suna kuma wayarda kai akan
masu cutar su daina takura kansu da ganin kamar mutuwarsu tana kusa da su.
Har ƙauyuka suna shiga su wayarda kai, abun yanxu yayi gaba har nijar da sudan
ghana sukan leƙa wani lokacin domin halartar taron ƙarawa juna sani ko kuma na
ƙungiyoyin duniya qani lokacin ma.har.

Ta tattara rayuwar aure ta aje gefe, duk kuwa da irin tayin da Alhaji bashir da
kuma wasu mazan suke mata, bata son abunda zai sake ɗaga mata hankali a yanzu,
shiyasa bata kawowa kanta zancen aure a kusa.
A duk lokacin da ta tuna da Kalsoom ce take riƙe da ƴaƴanta sai ta yi ma Allah
godiya, domin bata san Kalsoon ƴar'uwa ba ce sai a yanzu, tana ƙoƙari gurin ganin
ta bawa yaranta tarbiya, basa mata complain ɗin sun rasa wani abu ko an musu wani
abun sai ɗan abunda rai ba zai rasa ba, sai yanzu ta tabbatar good people are still
exist, ba ko wace abokiyar zama ce kishiyaba wata kan ƴar'uwa ce.

Bata da matsala ta ko ina a yanzu, sai dai tana nadamar abunda duk ta tuna sai
baƙinciki ya rufeta, wato sanadin wannan ciwon nata, a duk lokacin da aka tambaye
ta dalilin wannan ciwon nata ta kan ce ta same shi ne ta hanyar ƙarin jini da aka
mata, domin kawai ta kare kanta.

Shekara biyar da shiga ƙungiyar zuwa yau rayuwarta ta zama abar kwatance, rayuwarta
darasi ce ga duk mace mai irin rayuwarta, ko kuma halinta, ita kanta yanzu ta koyi
abubuwa da yawa na rayuwar duniya da kuma zama da mutane.

Ko da aka yi birthday ɗin Izzah tana Abuja gurin wani taro, washe garin ranar da ta
dawo taje gidan ta kai musu tsarabarsu da kuma birthday gift ta bawa Izzah.
Ta jidaɗin yadda ta same su, baka iya banbance tsakanin Ƴaƴan Kalsoom da nata a
gurin Kalsoom wato Amal da Rafiq da Husna, sam mutum ba zai iya cewa su ne ƴaƴan
Kalsoom ba, sau da dama zata bawa su Izza abu ta hana ƴaƴanta.

Bata daɗe a gidan ba duk da ƴaran sun so haka, amman ta ƙi a duk lokacin da taje
gidan haka take bata daɗewa take fitowa.
Ko da iso gidanta uku da rabi yayi, dan haka tana shiga bathroom ɗinta ta yi
alwalar la'asar ta fito ta shimfiɗa sallaya ta saka hijab taja carbi tana la'zimi
kamin lokacin tada sallah yayi.
Wayarta ce tayi ƙara daman ta ji tsayawar mota a harabar gidanta, sai kawai ta miƙe
tsaye ta nufi falo ta buɗe masa ƙofa.

“Hajiya...”

“Alhaji Bashir”

Shigowa yayi yana faɗin

“Aiko na taki sa'ah dan ban tsamaci kina garin ba”

“Jiya na dawo”

“Mashallah ya Abujar?”

Ya tambaya yayinda yake ƙoƙarin zaunawa.

“Abuja sai hamdallah, ya aikin naku”

“Aiki da godiya, iv na zo na kawo miki”

“Ba dai na aurenka ba ko?”

“Shi mana ba kin ƙi ni ba”

“Dana ƙi ka ya hana dubu su soka ne?”


“Cikin dubun ai na ƙawo ƙoƙon barata a gareki amman kika ƙi yarda, kuma ni wallahi
ko a yanzu kika yarda zan aure ki”

Ruwan tsanyi ta dire masa tana dariya tare da kai hannu ta karɓi iv ɗin.

“Lallai mutumen da gaske kake, budurwa ce ko bazawara”

“Budurwa ce yarinya ce ba zaki sha wahala gurin kishi da ita ba”

“Ai ni na yafe kishi da kowa, sai dai ina fatar tasan halin da kake ciki”

“Ta sani kan, sai dai bayan ke da ita da kuma Asmee babu wanda ya san da wannan
maganar”

“To ita mai cutar ce kenan”

“Ai kema kin sani baƙya buƙatar na faɗa miki”

“Amman Asmee ta ji?”

“Ta ji mana, to me zata yi?”

“Ba komai kawai ina tuna lokacin da take cewa ba zaka taɓa aure ba ne”

“Ni kaina ina tuna wancan lokacin da ina son aure amman sai na kasa yi sanadin
hakan muka faɗa hallaka ni da ke, sai dai kin san komai lokaci ne da shi, ko magani
kika yi kika ga ya kama to daman can Allah ya rubuta zai kama ɗin”

“Na yarda da hakan ai ni sai dai na faɗawa wani, kuma ina fatar idan ka yi wannan
auren zaka ɗaga min ƙafa, saboda mutane suna ta zargin muna tare ne, kuma zaka iya
tonawa kanka asiri indan kana cigaba da ziyarta na, saboda kai ma za a iya gano
kana ɗauke da cutar, abu na uku kuma kasan ance idan mace da namiji suka kasance su
biyu sheiɗan ne na ukunsu, dan haka bana son wata alaƙa ta saɓon Allah ta sake
shiga tsakanina da kowa”

“Nima bana nufin wani abun makamancin wannan saboda i realized that duk abunda ka
yi wa ɗan wani sai an yi ma naka, tun bamu je ko ina ba a scul wani malami yayi
raped ƴata, ban taɓa faɗa miki ba ne saboda ba labari ne mai daɗi ba, amman a
lokacin na samu kai na a wani irin kalar mutum, abun da ciwo sosai Rashida, sai na
dinga jin kamar na kama duka familynshi nayi musu yankan rago, but a dole na rufe
magana domin idan na buɗe yanzu ne zata shiga duniya kowa yasan abunda ya samu ƴata
bayan kuma nine sila saboda ban tsare kaina ba, kuma zan jawa ƴata abun faɗi ne
kawai”

Ya share guntun ƙwalla da suka zubo masa.

“Ki dubi Family Hilal ki gani da yake ya tsare kansa, sai Allah ya tsallakar da
shi, duk da kina a cikin gidanshi Allah ya tsare ƴaƴansa da matarsa da shi kansa mu
kaɗai muka kwashi abun, dubi rayuwar gidansa ki gani gwanin sha'awa, ni ko rayuwa
baƙinciki ne da kuka, saboda halin da muke ciki, ko wannan ciwon da ke jikinmu
tawace gashi kullum muna cikin kafakafa kar ƴaranmu su ɗauka, muka tsoron mu kai su
wani gurin riƙo asirinmu ya tonu”

Rashida ta girgiza kai cike da tausayawa.

“Ba ku kyautawa rayuwar ƴaƴanku ba, ku ɗauke su ku kaisu gurin ƙaƙaninsu mana, ko
karka yi sake yaranka suma su kwasa su girma suna nadamar da kasancewar ƴaƴanka,
karka ɓata rayuwar ƴaran ka tun suna da ƙurciya, ka taimaki future ɗin su, kai taka
ta ƙare su kuma ka yi tattalinsu...”
Ajiyar zuciya ya sauke yafi sau goma sannan ya miƙe tsaye jiki a mace ya fice ba
tare da ya ce da ita komai ba.
Rayuwa kenan sau da yawa Allah yake maka talala kayi ta iskancin da zarar ya
tashi kama ka ba zaka ga da kyau ba, kuma matuƙar be yafe maka ba, zaka je lahira
ka tararda abunda ka aikata. Duk magane-magane da Asmee ke yi tana ganin kamar ta
ci riba wajen hana mijinta aure ashe ba riba bace lokacin auren ne be yi ba sai
yanzu, tun da gashi yanzu zai yi auren,garin neman gira an rasa ido ta kwaso musu
cuta tana nadamar da babu ranar daina kukanta. Ita kanta Rashida dake yi wa Kalsoom
magani a dole ai yanzu ta saka mata ido ta ɗauke ta ƴar'uwa tun da taga addu'ah da
tsarin Allah yana tare da wanda duk ya nemi taimakon Allah, tayi iya yinta amman
bata raba Kalsoom da gidan mijinta ba saboda Allah ya riga ya rubuta ita ɗin ce
dai.
Mata da yawa suna shiga haƙƙin mazajensu wajen ganin sun hanasu aure ko kuma sun
mallake miji da kishiya, bayan kuma sun san Allah zai tsayar da su a gabanshi yayi
masu shari'ah ranar da baki baya iya magana.

Jiki a mace ta miƙe ta yi nafila wato ƙabli asri sannan ta ɗora da la'asar ɗin,
tasbihi da hailala da hamdala ne suka biyo baya tana gode Allah da ya nuna mata
kuskurenta tun a nan duniya da ake karɓar tuba, kuma ya bata ikon tuban, kana ya
tsare mata yaranta kuma ya basu uwar da zata riƙesu ta tarbiyantar da su, tabbas
yanzu ta tabbatar Ubangijinta yafi kowa sonta, shi ta tsaɓawa kuma ya yafe mata har
ya musanya mata ta wani ɓangare.
[7/31, 9:26 PM] Khadeeja Candy♥: *93*

Lafewa ta yi a ƙirjinsa tana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa, sai ƙara shigar da
kanta take tana shaƙar ƙamshin turarenshi.

Hannu yasa yana shafa bayanta, idanuwansa a lumshe. Wani abu yaji yana sauko masa
marar misaltuwa, be taɓa hugging wata mace kamar yadda yayi a yanzu ba, wata mace
kuma bata taɓa kwantawa a ƙirjinsa kamar haka ba, ɗayan hannunta dake cikin
hannunshi ya soma matsawa a hankali yana lume baki.

Jin shafar da yake mata ne ya sauya salo ne yasa ta ɗago kanta ta kalleshi, idonsa
har yanzu kulle yake, hakan yasa ta ɗaga daga jikinsa gaba ɗaya ta zare hannunta
daga nashi.
Sai ya buɗe idonsa yana kallonta, fararen idonsa sun fara rinewa zuwa ja ga wani
ruwan hawaye da ya kwanta masa. Hannyensa yasa ya riƙa fuskarta.

“I Love you so much Abnam”

Kallonshi take kamar yadda shi ma yake kallonta, sai hawaye suka zubo mata.

“Ban san mi Asim yake nufi da ni ba, ban san miyasa ya ɓullo ta wannan hanyar ba,
na masa iya hallacin da zan iya, saboda shi na rabu da iyayena, na bishi na zauna
da shi a inda ban taɓa mafarkin zan zauna ba, lokacin da arziki ya zo masa sai ya
guje ni, yace min baya son haihuwa, da cikin ya kure na je garin kaduna ba tare da
na san kowa ba, Lamido yayi min masauki a gidansu, a gidan cikina ya zube.

Wallahi tallahi ya sake ni Abdallah, ban san miyasa ya canja min ba, har yana
tambayar ɗan sa”

Hawaye na bin fuskarta take maganar zuciyarta cike da rauni. Fuskarta ya saki ya
kama hannayenta ya riƙe gam.

“Na yarda da ke Abnam, Asim yana son shiga tsakaninmu ne, saboda yana tunanin zamu
fara sabuwar rayuwa mai kyau, karki saka ranki cikin matsala nasara bata zuwa ba
tare da wahala ba”
Ƙofar da Hajiya Kilishi ta buga ne yasa shi kallon ƙofar sannan ya kai hannu ya
share mata hawayenta. Sannan ya miƙe tsaye ya buɗe ƙofar.

“Hajiya...”

“Na'am, Abdallah ya mai jikin”

“Ta ji sauƙi”

“Ga breakfast nan Hajiya ta aiko su Amal su kawo ance wayarka na kashe”

“Oh Okay bari na kunna”

“Okay ka gaishe da ita”

Ta juya shi kuma ya rufe ƙofar ya dawo yana ciro wayarsa da ke aljihu ya kunna, sai
ya kira Ummi.

“Abdallah na kira wayarka kashe”

“Na kasheta ne saboda Doc yace min ana bukatar ta samu bachi, barka da safiya”

“An tashi lafiya ya jikinta? Miya same ta? Meesha tace min kawai sun ga ka fito da
ita a sume”

“Ummi labari ne mai tsawo da rikitarwa zan zo anjima”

“Okay ga abinci nan na aiko muku nasan zata buƙaci abincin a yanzu, amman dai ka
faɗa min ko minene”

A nan ya soma labarta mata abunda ya faru. Ta kiɗima sosai abun ya zo mata kamar
almara, sai dai ta kwantarda hankalinta saboda kar hankalin ɗanta ya tashi.

“Allah zai muku mafita Abdallah”

“Na gode Ummi I love you”

“Allah ya maka albarka”

Yana sauke kiran wayar Mai Martaba ta shigo, cike da ladabi yayi picking.

“Assalamu Alaikum Mai Martaba”

“Wa'alaikassalam, Babana ya mai jiki”

“Alhamdullillah ta ji sauƙi fatar ka tashi lafiya”

“Alhamdullah, Babana bana son ka tashi hankalinka na san kana sonta sosai, sai dai
bana son da kake mata ya iya rufe maka ido ka tsallake gaskiya, kai ɗana ne nafi
son komai za'ayi ka tsaya kan gaskiyarka”

“Mai Martaba kafi kowa sani na, ba zan taɓa aikata abun assha ba, kuma zan
saurareshi matuƙar yana da hujja”

“Allah ya maka albarka”

“Amin Mai Martaba Allah yaja kwananka”

Daga haka ya sauke wayar sai ga kiran sisters ɗinsa ya shigo sai kuma na Maryam,
sai dai be ɗaga ba sai kawai ya kashe wayar. Ya miƙe tsaye ya fita. Sojojin da ke
gurin da dogarai ya sallama sai dogara ɗaya ya bari, sannan ya dawo ɗakin.

Wannan karon jikin windo ya same ta tsaye fuskarta na kallon ƙasa kasancewar inda
suke gidan sama ne. Ƙarasawa yayi ya riƙe kunkurunta ya ɗora kansa saman wuyanta.

“Jiya ya kamata ace na tare, amman hargitsin da ya faru jiya ya hana hakan, dare
biyu kenan na amarci ina kwana ba cikin daɗi ba, a wacan daren fargaba da tunanin
halin da na bar mahaifina da kuma tunanin makomar aurena, yanzu kuma wannan
hargitsin ya taso, Ina roƙon Allah ya tsayar a nan kar wannan abun ya shafi rayuwar
auren da zanyi nan gaba”

Ɗayan hannunshi yasa ya zagaye cikinta.

“Wannan rigimar ma na ɗan lokaci ne, kar zuciyarki ta sake irin wacan tunanin, ko
kaɗan Abdallah be yi kama da Asim ba, a halitta balle kuma a hali da ɗabiyu da
halaiya, Wannan karon da Abdalla aka ɗaura miki aure ba Asim ba, kar ki sake irin
wacan mafarkin”

Juyowa tayi ta riƙa fuskarsa tana hawaye.

“Zuciya bata iya tantance gaskiya da ƙarya a yanzu, shi ma haka yayin ya yaudare ni
da daɗaɗan kalamai, da su ya siye ni har na rufta a duniyarsa mai cike da duhu da
kuma hayaƙi”

Jin an buga ƙofa yasa tayi saurin janye hannunta daga fuskarsa ta zauna saman gadon
tana share hawaye. Haleema ce da Fauza sai Shukura mai aikin Ummi.
Sai da suka fara gaisawa da Abdool sannan ta ƙaraso kusa da Namra tana mata ya
jiki.

“Senu senu Ajiya, Allah kew wo sauƙi, Allah baka lafiya get well soon”

“Thank you, ya Mama?”

“Lafiya ƙalau yace a agaise ki”

Haleema ta matsa tana ƙare mata kallon tare da yi mata ya jiki.

“Sannu adda Namra Allah baki lafiya”

Sai Fauza ta ɗora da nata

“Ummi tace a gaishe ki, Allah ƙara sauƙi”

“Amin amin na gode”

Bayan sun dire mata kulolin abinci suka tafi. Da kanshi ya ɗauki plate ya zuba mata
abincin da aka kawo ya soma bata da kanshi sai da ya tabbatar ta koshi sannan aje
plate ɗin ya ɗauki ruwa ya bata, yana dire kofin sai ga Sisters nashi sun shigo
tare da Maryam sun kawo abincin cikin manyan kuloli na alfarma masu mugun tsada.
Da sauri Maryam ta zauna kusa da ita tana mata ya jiki cike da tausayin ƴar'uwarta.

“Na ji sauƙi kin yi waya da Anty?”

“Eh tun ɗazu take son ta yi magana da ke wayarki na hannuna shi kuma wayarsa a
kashe, tace mun ma sun kamo hanya ita da Abbah da asubar nan”

“Kin faɗa musu abunda ya faru”


“Eh Abbah ma yace Mai Martaba ya kira shi, Namra karki saka ranki a damuwa Asim
yana son ya saka ki cikin matsala ne kawai kuma yana son ganin zubar hawayenki
saboda yasan a yanzu ba zaki taɓa dawowa gareshi ba”

Abdool ne yayi saurin katse musu fira saboda baya son sisters ɗinshi su gane inda
matsalar take, duk da bashi da tabbacin ko Mai Martaba ya faɗa a masarauta.

“Maryam ku zo ku tafi Doc yace ana buƙatar ta huta sosai”

“Okay Allah ya baki Lafiya”

Maryam ta faɗa idonta cike da ƙwalla ganin hawayen da ke zuba a idanuwan ƴar
uwarta. Tare da Sisters ɗinsa suka fita sai ya sake buɗe kulolin ya zuba mata
abincin da aka kawo amman bata ci ba shi ma kuma baya jin cin abincin sai kawai ya
aje. Yana kallon Likitan da ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, murmushi suka yi ma juna
shi da da Abdool kamin ya miƙa masa hannu su gaisa.

“Ango Ango daya tare a asibiti, ina fatar dai ba ƙarfin amaryar mu ka ci ba har ka
kawo mana ita asibiti, kasan baƙauye be iya sintar agogo ba”

Abdool yayi murmushin ƙasaita Hafiz abokinsa ne tare suka yi karatu a waje.

“Ni dai duba min matata please bana son ƙananan magana”

“Ai yanzu kana da baki jiya da na tsaya iya bayani ai ko kallon inda nake baka yi
ba”

“Ai ban ma san da kai ba”

“Ai ba zaka sani ba, hankalinka yana tashe”

Ya shiga duba hannun Namra da Abdool ya cire mata drip. Sannan ya tambayi Namra
abunda take ji.
Magani ya rubuta mata sannan ya faɗi yadda za a bata shi ya kuma rubuta musu
takardar sallama, daman ba wani ciwon ba ne sai gajiya da kuma iɗima a lokaci ɗaya.

Sai basu bar asibitin ba sai da an gidansu Abdool ta ɓangaren Mai Martaba suka cika
motoci suka zo ganin Namra, hakan kuma ba ƙaramin faranta ran Namra yayi ba, at
least tasan ta shigo familyn da ake marhabun da ita kuma ake sonta da ɗaukinta ta
ko wane ɓangare.

Sai ƙarfe goma sha ɗaya har da rabi sannan suka bar asibitin, Abdool be nufi gida
da ita ba kasancewar shi ne yake tuƙin motar sai Sis ɗinsa ɗaya da ke gaban mota
yayinda Namra da wasu ƴan gidansu suke baya su uku.

Ya tararda gidan cike da mutane kasancewar har yanzu ƴan biki basu gama watsewa ba,
balle ma yau Ummi take da niyar yin nata walimar sai dai wannan abun daya faru ya
kashe mata jiki, ganin hakan yasa be shigo ba, sai su Meesha da Ƴan Gidansu wato
Maryam da Raihanatu da Gwaggo Ramatu, ba laifi tana iya tafiya dan ta samu ƙwarin
jiki sosai tsaɓanin jiya da bata da wani kuzari sosai.
Da kanta take takawa har suka isa bacony ɗin, sannu mutanen da ke cikin falon
suka riƙa mata har aka nufi ɗaƙin Ummi da ita saboda Ummi tace a shigo da ita
cikin.
Kanta a ƙasa ta shiga ɗakin, dan haka bata iya gane mutanen dake cikin bathroom ɗin
sai dai taɓa jin ba Ummi bace kaɗai a ɗakin.

Da ɗai-ɗaya Ummi ta riƙa nuna mata su tan gaishesu a nan Namra take ɗan ɗaga ido ta
kallesu saboda ta tantancesu.
Sai sannu suke mata suna tsinewa Asim Albarka duk da basu san shi ba, domin Ummi
ta faɗa musu komai, ganin ƴan'uwanta babu abunda zata ɓoye musu.

“Tashi ki zauna saman gadi magana zamu yi”

Ummi ta faɗa fuskarta da murmushi kamar babu damuwa cikin ranta. Sai duk suka tashi
suna dariya tare da cewa basu su bata guri, daman ana ta kiransu su zo su duba
Donuts ɗin da ake haɗawa idan yayi. Namra na zaunawa saman gado Hajiya Sadiya ta
buɗo ƙofar Bathroom ta fito ta fito.
Suka haɗa ido da Namra sai ta yi tsaye jikin ƙofar kamar marar gaskiya, Namra kan
saurin kawar da idonta tayi saboda bata gama yarda ita ɗince ba ko a'a idan ɗince
miya kawo ta nan? Anya ma itace wannan ta rame sosai kamar ba ita ba, duk jikinta
nan ya zube ta koma siririya sosai.

“Hajiya Ƙaraso ku gaisa da ƴar ta ki”

Ummi ta faɗa ba tare da ta lura da halin da take ciki ba, cikin kasala da rashin
kuzari ta ƙarasa tana kawarda fuska kamar mai jin kunya. Sai Ummi tace

“Kin ga ɗayar nan itama ƙanwata ce”

Cikin nuna ladabi Namra ta gaisheta.

“Ina lafiya wuni”

Ta amsa murya na rawa idanuwanta kuma na cika da ƙwalla.

“Lafiya Ƙalau ya jikin na ki?”

“Alhamdullah”

“Daman ita ce wacce Abdallah ɗin ya aura?”

Ta tambaya tana kallon Ummi.

“Eh itace”

“Yayi sa'ar mata Allah ya baku zama lafiya”

Ummi ta amsa da Amin, sai Namra ta ɗago kai ta kalleta, Hajiya Sadiya ta sakar mata
murmushin da yafi kuka ciwo ta juya ta nufi ƙofa.

KU SANI A CIKIN ADDU'AN KU, ALLAH YA BIYA MIN BUƘATUNA KUMA YA YAYE MIN DAMUWA😭
Wallahi I'm not in the good mood today, na yi typing ne kawai saboda nasan kuna
jira. Pray for me please included me in your addu'ah ba a rubuce nake so ba a cikin
five daily prayers naku nake son ku saka ni Alfarmar Annabin Rahama rasululliah
salallahu alaihi wassalam 😭
[8/1, 10:44 PM] Khadeeja Candy♥: *94*

“Ƴata Abdallah ya labarta abunda ya faru, nasan ba komai ba ne wannan sai hassada
da neman fitina, komai zai wuce karki saka ranki a damuwa, ni dai nasan ni na
haifina nasan halinsa kuma nasan abunda zai iya yi da wanda ba zai iya ba, nasan
ɗana ba xai aikata irin wannan abun ba, dan haka na yarda wannan tsohon mijin na ki
na neman fitina ne kawai”

Namra ta share hawayen daya zubo mata yana kallon Ummi dake mata magana cike da
natsuwa da kuma nuna kulawa.
“Allah na miƙawa almurrana, kuma ni dai nasan a kan gaskiya na ke, wallahi ya sake
ni kawai yana neman tayar min da hankalin ne kawai”

“Karki damu Allah baya bachi zai shiga a cikin wannan lamarin, Allah ya miki
albarka”

“Amin”

“Ɓari naje na duba aikin da ake kar a min ba daidai, ki kwanta ki hutu”

Kai kawai ta iya ɗagawa, sai Ummi ta miƙe tsaye ta fice. Harabar gidan ta fita gaba
ɗaya ta duba yadda ake kwaɓa donuts ɗin, sai Hajiya Sadiya ta kamo hannun Ummi suka
nufi can ɓangaren garden inda babu mutane.

“Zuwaira na ce ko Namra tace miki wani abu?”

“A'a magana ce kawai muke akan lamarin auren nan da tsohon mijinta ya ɓullo da
wannan lamarin”

“Ok na ɗauka ko tace miki wani abun ne, naga kamar zata yi wata maganar”

“Akwai abunda ya kamata ta faɗa min ne? Ita fa lamarin nan gaba ɗaya ya hanata
sukuni”

Shiru Hajiya Sadiya ta yi tana sauke ajiyar zuciya.

“To yanzu ya za'ayi wannan lamarin Zuwaira?”

“Shine abunda nake tunani tunda ya tsaya kai da fata shi be sake ta ba”

“Wallahi yaron nan macuci ne, azzalumi ne kuma mayaudari, maƙetaci ne so yake ya
shiga tsakaninsu so yake ya raba su, Asim mugun mutum ne wallahi, a lokacin da ka
yi masa hallacin a lokacin yake ƙoƙarin cutar da kai”

Sai kawai ta fashe da kuka ta durƙushe, Ummi mamaki ya hanata cewa komai ga
sunanshi da ta ambata, duk da bata da tabbacin sunan ne saboda bata taɓa jin sunan
ba.

“Hajiya Sadiya kin sanshi ne?”

Ummi ta faɗa tana dafata. Kamar wacce ta tuno wani abu sai tayi saurin tashi tsaye
tana share hawaye.

“Eh na taɓa taimakonsa a lokacin baya da lafiya Wallahi yarinyar nan ita tayi ta
wahala da shi, kuma ya taɓa min aiki a lokacin ne ma yake faɗa min ya sake ta”

“Alhamdullilah Allah mun gode maka, kema ai sheida ce”

Ummi ta faɗa cike da farinciki. Sai Hajiya Sadiya ta daki ƙirji ta zaro.

“Ni kuma? Dan girman Allah ki rufa min asiri kar ma ki kawo zance na a gaban kowa,
wallahi babu ruwana”

Bata tsaya jiran abunda Ummi zatace ba ta nufi gurin mutane gudun kar Ummi ta sake
mata wata maganar, ta tsorata sosai ba kuma dan tana tsoron Asim ba sai dan gudun
tonuwar Asirinta, ba dan hakan ba babu abunda zai hana ta ballasawa Asim asiri
saboda ya cutar da ita.
ASIM POV.

A tsorace abokaninsa suka kai shi Pharmacy aka bashi magani aka saka masa bandeji a
wani gurin sannan aka masa allura, sai suka dawo da shi gidansa saboda baya iya
tuƙa motar ma, lokacin da suka sauke shi be shiga part ɗin Amaryarsa ba gudun kar
taga halin da ya ke ciki sai ya sauka part ɗin Mardiya. Hankalinta ya tashi sosai
ganin mijin a cikin irin wannan yanayin mutumen da ya fita lafiya ƙalau ya dawo
haka.

Lokacin da ke labartawa Mardiya abunda ya aikata ta cika da tsananin mamakin da


al'ajan ita kanta idan bata manta ba ya taɓa faɗa mata ya saki Namra.

“Amman Asim ba ka sake ta ba?”

Ya warga mata wani mugun harara.

“Uban waye ya saketa? Na sake ta zan dawo na ce matatace? Ko da na na sake ta a


dole ta bani ɗa na domin da cikina ta gudu, wallahi duk abunda za'ayi sai dai ayi
amman sai na dawo da Namra gidana”

“Taya zaka dawo da ita gidanka bayan ta zama matar wani? Ya kake magana kamar wanda
baya cikin hankalin kansa”

“Hankalinki na ara na ke amfani, sakaryar banxa a duk ta fiku dan ita ba kuɗi na
take so ba ni take so, kuma tana zuwa nan ta samu ciki ku fa kin je ki ɓarar da
mahaifarki kin zubar da yaranki tun kamin ki shigo gidan ni nayi nadamar aurenki
Wallahi”

Magana yake kamar zai cire haushin dake ransa a kanta. Ita kan zuciyarta ya kawo
sosai dan me zai aibantata.

“Karka so ma min maganar banza kana son matarka ka sake ta ka auro ni, ba nan kake
faɗar laifinta ba, sai yanzu dan ka gama more jikina sannan zaka ce kayi nadamar
aurena? Ai ni ƙara ma da Allah yasa ban haihu da kai ba, mutum kullum sai kusanceka
sai dai yabi ta bayanka ba ta inda Allah ya hallata masa ba”

“Ai dan kuɗina kika auri ne ba dan kuɗi na ba zaki aure ni ba, ƴar iskar banxa mai
bin mazan waje”

“Ai ni wallahi allura ce cikin ruwa ko da kuɗinka sai da rabonka, yanzu ai ka auro
wacce ta fini ko? Gata nan na gani”

“Namra dai zan dawo da ita sai dai ki mutu, ai ga alhakin mutane nan saman kanki
kullum cikin gobara kike, ɓarauniyar banza ko ɓera be kaiki sata ba, duk inda nayi
ajiya a gidan nan sai kin ɗauka, jahilar banza ashe ma ko karatu baki yi ba,
shiyasa kike nan kamar dabba”

Ƙyalƙyalewa tayi da dariya.

“Mahaukacin banza Namra kan ta maka nisa sai gani sai hange daman can ba ajinka ba
ce nice daidai kai, Namra kan ta yi gaba shine kake mata hassada ko? To Wallahu
kayi kaɗan kai da dawo da Namra a gidan nan sai dai mai sunanta, ko kuma a mafarki
daman can baka san tana da martaba sai yanzu”

“Wallahi kika sake wata magana marar daɗi sai na sakeki a cikin daren nan, kuma ki
zuba ido ki gani kina cikin gidannan zan daqo da Namra sai dai ki mutu, wallahi ko
zaki ran rasa raina ne sai na dawo da ita, ita ai nasan tana so na”

Tsire baki tayi ta tashi ta bar masa gurin zuciyarta cike da ɓacin rai. A daren
daga shu har ita da tsoro suka kwana saboda tunanin ko sojojin zasu sake biyoshi su
zo gida su hallakashi.

Da safe jikinsa sai ya ƙara yin tsami har idon ɗaya ya kumbura, ɗayan kuma daman
tun jiya ya kumbura. Ƙafar da yake tsingilta da ita sai ma ya kasa takata gaba
ɗaya.
Yana son yace Mardiya ta ɗora masa ruwan zafi ya gasa jikinsa amman babu dama
tun da sun yi faɗa tun jiya da dare. Haka ta riƙa mulmula saman tabarmar dake falon
sai tunanin yadda zai ɓullowa lamarin yake. Yana haka sai ga dogaran Mai Martaba ya
aiko a tafo da shi, babu ruwansu da uzuri balle su tausaya masa umarnin Mai Martaba
suke bi kuma ya zame musu dole su cika shi. Da aka je da shi can ne Mai Martaba
yasa ya kira ƙanen Mahaifinsa da na mhaifiyarsa ya sanar da su halin da ake ciki,
sannan ya kira waɗanda suke bakori
ya sanar da su halin da ake ciki. Mai martaba da kansa ya aika da Mota aka ɗauko na
bakori sannan ya aika ɗayar a sokoto dan a ɗauko wasu daga cikin familynsa.

LAMIDO POV.

Tun da ana sauran kwana uku a fara bikin Namra ya bar gidan saboda baya son wani
abun da zai kusantarda shi ga bikin. Sai dai a gida su Neina basu yi mamakin hakan
ba, daman sun sa ran haka zai faru, tausasa masa zuciya kawai neina ta riƙa tana
faɗa masa ita da shi ɗin basu dace ba, sai dai ta nuna masa jindaɗinta akan kyautar
da Abbah yayi masa na kuɗi yace a kawo musu, ga kuma aikin da yace an samo masa,
sai duk suka riƙa murna suna faɗin zaman Namra yayi musu amfani a gidan.

Uwani ce ta riƙa cewa ta so ta ga Namra amarya, daman komai yana da lokaci gashi ya
wuce har suke ɗauko zancen zaman da tayi a gidan suna yaba tarbiyarta da kuma irin
haƙuri da tayi da zama da Asim duk da basu sanshi.

A duk dare Lamido yana kwantawa da tunanin Namra a ransa, har ga Allah yana son
Namra kuma ya so ya aureta saboda kawai ya nuna mata ba duka talaka ne azzalumi ba,
kuma yaso ya tarairayeta ya muna mata rayuwar jindaɗi sai dai Allah be nufa ba a
dole ya barwa Allah komai. Ko da yaushe yana ƙirga kwanakin da aka ƙara na bikin
har aka kai asabar ranar da aka aka ɗaura mata aure, ranar wuni yayi kamar marar
lafiya gaba ɗaya yaƙi ya sake ko abinci kasa ci yayi,Neina ta lura da hakan ta saka
shi a gaba tana nuna masa halin rayuwa tare da ƴi masa tambihi akan abunda duk
Allah be rubuta naka bane ba zai zama naka ba, tayi masa nasiha sosai wacce ta
shiga jikinasa kuma ya yarda da hakan ɗin Allah ya ƙaddara babu yadda ya iya.

Ranar Monday da safe Abbah ya kira shi bayan sun gaisa Lamido yake tambayar ya
hidimar biki, sai Abbah ya roko masa da zancen yana son su haɗu a Katsina yau.

“Lafiya Abbah”

“Lafiya ƙalau, ina son mu haɗu da kai acan kuma bana son ka rigani isa dan haka ina
son ka tashi tun yanzu”

“Ok inshallah, amman a ina zan sauka?”

“Idan ka shiga Katsina ka kira ni”

“Okay Abbah”

Daga haka ya katse kiran zuciyarsa cike da ruɗani, yasan Abbah ba zai nemi ganinsa
haka kawai ba, amman kuma me yasa yake son su haɗu ɗin kuma a Katsina? Haka yaƴi ta
saƙe-saƙe har yaje ya gaishe da Neina ya faɗa mata sai kawai tayi masa addu'ah ta
kuma bashi ƙwarin guiwar zuwa.

Ɗumamen da Uwani ta yi yaci ya kora da ruwan tea sannan ya shiga yayi wanka ya
shirya cikin ƙanƙanen lokaci ya kama hanyar Katsina zuciyarsa cike da zullumi, sai
dai hausawa sunce karka ji tsoron kira kaji tsoron laifin da ka aikata.

NAMRA POV.

Ummi na fita sai ta ɗalle gadon ta lumshe ido tana da shakar ƙamshin turaren Abdool
dake jikinta saboda rumgumar da yayi mata ɗazu da safe. Meesha ce ta turo ƙofar
ɗakin ta shigo sai ta shiga bathroom ta haɗa mata ruwan wanka mai ƙamshi da ɗumi,
bayan ta haɗa ta fito ta nufo gurin da Namra take ta ɗan taɓa ta kaɗan tana
murmushi.

“Adda Namra zaki yi wanka za a maida ƙe gidan Mai Martaba, kuma ga wasu nan zuwa su
ganki”

Namra ta buɗe idonta dake cike da hawaye ta miƙe tsaye, sai Meesha ta ɗauko mata
tawul sai dai Namra bata ɗaura tawul ɗin ba ta sai da ta shiga bathroom ɗin. Ta
samu ƙarfin jiki sosai lokacin da tayi wanka ruwan zafin ya gasa mata jiki sosai,
ga ƙamshim turare kamar karta fito.

Ko da ta fito ta samu shadda ash color saman gado aje da mayafi ja kamar yadda
aikin shaddar yake, sai kuma kayan ciki wato underwears. Bata shafa mai ba dan bata
jin yin wani kwalliya gaba ɗaya hankalinta baya jikinta, sai kawai ta ɗauki shaddar
ta saka ta ɗaura ɗankwalin ta ɗauƙi jan mayafin ta yafa ta zauna gefen gado tana
murza yatsun hannunta. Sai ga Haleema ta shigo da turen abinci Meesha kuma ɗauke da
drinks.

“Ummi tace ki ci abinci Mai Martaba ya aiko kiranku tare zaku je”

“Ba da ita zamu yi walima ba?”

Meesha ta tambaya

“Haka Ummi tace wai ko basa nan za ayi walima”

Tashi suka yi suka bata guri yadda zata samu ta ci abinci. Amman har suka dawo
yadda suka bar abincin haka suka tararda shi, Meesha ta lallaɓata akan ta daure ta
ci abinci amman ta ƙi ita yanzu ba abinci ne a gabanta ba.

Sai da aka fita da ita aka sakata cikin mota sannan Ummi ta dawo ɗakin ta sake wani
shirin ta fito tana kiran Hajiya Sadiya da wata ƴar'uwarta guda ɗaya wacce zasu je
tare. Amman sai Hajiya Sadiya ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba zata je ba, aka yi aka yi
tace ba zata je, har sauran ƴan'uwanta suka ce a canja aje da wata mata sai kawai
Ummi ta kashe ƙafafunta da cewar ai ƙara ita dai tun da Asim ya taɓa mata aiki kuma
har tasan da sakin Namra. Ba su ba har Namra sai da tayi mamakin jin kalamin Ummi,
domin Asim be taɓa faɗa mata cewar yayi aikin a gurin Hajiya Sadiya ba, sai a
lokacin ta tuna da ya taɓa faɗa mata uwar ɗakinsa ai macece. A nan kowa ya saka
baki akan ƙara ita taje ɗin saboda tasan shi, sai ta sake nuna ƙin son zuwa ɗin a
nan wasu kecewa ko dai tasan da wani abu ne idan ba haka be mai xai haka taje bada
shedan akan matar ɗanta tun da Abdool zama ɗa yake a gareta.

“Bama fa lallai Asim ɗin yaje ba saboda Mai Martaba ne ya kira ni yace na zo da ita
da kuma wasu ƴan'uwana ba lalle bane ya zama Asim ɗin yana nan, wata ƙila ma wani
zancen ne zai yi daban”

Cewar Ummi tana ƙoƙarin kawar da Hajiya Sadiya tunani, sai dai hakan be hana ƴan
uwanta tursasa taje ɗin ba. Babu yadda ta iya a dole ta shiga motar aka je da ita,
uta kanta ba dan tana gudun abunda zaije ya dawo ba da babu abunda xai hana ta faɗi
gaskiya game da Asim.
Suna isa cikin gida sai Ummi tasa direban yayi parking a ɓangaren Mai Martaba dan
bata buƙartar shiga cikin gida, daman ita tama manta when last ta ganta a gidan, ba
kasafai taje zuwa ba sai idan za ayi wani babban abu. Direban na fakawa ta kira Mai
Martaba ta sanar masa data iso, sai yace ta shigo tun da gidan ba baƙonta ba ne.

Suna gaba ita da Namra su Hajiya Sadiya da Hajiya Mairo da Anty Farida suna biye,
gaban Hajiya Sadiya kamar ya faɗo ƙasa saboda fargaba da tsoron abunda zata tarar.
Wani Babban falo ne na Mai Martaba wanda ba kasafai yake shiga da mutane ciki ba, a
cike suka tararda falon da mutanen amintatun Mai Martaba sai kuma Abbah da Anty
Amarya dake zaune a kujera ɗaya, yayinda Abdool yake zaune a kujerar dake kusa da
ta Mai Martaba, sai kuma Asim da ke zaune ƙasa shi da Lamido, sai kuma ƴan'uwan
Asim.da ke gefe ɗaya zauna, wato yayar mahaifiyarsa da kuma ƴan uwan ubansa su
huɗu.

Mai Martaba kuma yana zaune a wata ƙasaitacciyar kujera Mai Kyau da Haske irin da
manyan sarakuna. Namra na haɗa ido ta Anty Amarya sai ta fara hawaye, Anty kuma ta
sakar mata murmushi kamar ba komai.

Ummi ta zauna a kujera zaman mutun uku sannan Hajiya Mairo da Anty Farida suka
zauna a saman kujerar Hajiya Sadiya kuma ta zauna ɗayar kujerar ta noce kai ƙasa,
Namra kuma ta zauna ƙasa.

Asim na ganinta gabanshi ya faɗi, ya rasa yadda akayi ta haɗu da Ummi duk da bsan
wacece Ummi sai dai yasan bata rasa nasaba da Namra saboda yaga tare suka shigo,
zance ɗaya zuciyarsa ke nanata masa, wata ƙila Namra ce ta faɗi inda take akaje aka
ɗaukota, sai kuma wata tambayar ta sake faɗo masa a rai ya akayi Namra ta san yayi
mata aiki?

Waziri ne ya miƙe tsaye yana yima kowa sallama sannan ya kalli Mai Martaba ya sake
kallon mutane ya ce.

“Muna saba data tara mu a wannan guri saboda jayayyar aure ne, ɗan wannan masarauta
wato Yarima Abdool ya auro wata yarinya daga sokoto, kamar yadda kowa ya sani
wannan yarinya bazawara ce, kuma sai da ta shekara ɗaya a gudansu har da wata uku
sannan aka ɗaura mata aure da Yarima, bayan an taho da ita a nan Katsina sai Tsohon
mijinta ya taso da zancen cewar shi be saki Matarsa ba, kuma har yana iƙirarin
akwai ɗa ɗaya a tsakaninsu, a bisa wannan ne Mai Martaba ya tara mu saboda aji
bakin kowa”

Waziri ya koma ya zauna, sai Mai Martaba ya kalli Asim ya ce.

“Ko zaka iya faɗa min dalilinka na cewar kai baka saki matarka ba?”

Asim babu kunya babu tsoron Allah ya soma magana ko tsoro baya ji.

“Allah ya taimakeka ni ban saki matata ba, idan har na sake ta dole ne na mata
takardar sakinta, kuma babu yadda za'ayi na saketa bayan tana ɗauke da cikina kuma
ni mai tsananin son haihuwa ne, ni dai nasan rigima ta shiga tsakani da ita har na
dake ta kuma na ta gudu amman ni ban sake ta”

Malamin faɗa ya ɗaga hannu. Sai Mar Martaba ya bashi izinin magana, daga inda yaƙe
zaune ya aikawa da Asim da tambaya.

“Yaro karka ruɗi kanka kar kuma kayi wasa da hankalinka, idan har ta gudu miyasa
baka bita ba har tsowon wannan lokacin ka ƙyaleta”

“Saboda na san iyayenta basa so na ko naje masan ba zasu bani ita ba”
Kowa sai ya girgiza kai. Malamin ya kalli Namra ya ce.

“Allah shi taimakeki ɗaga baki ki yi magana”

Namra ta ɗago hawaye na bin idonta.

“Idan har yasan ina ɗauke da cikinsa miyasa be bini ba har aka shekara be binciki
inda ɗansa yake ba? Taya zan haihu ba a neme shi ba bayan kuma cikinsa ne? Tabbas
Asim ya sake ni sanadiyar cikin da naƙe ɗauke da shi saboda yace na zubar na ƙi sai
ya sake ni yana faɗa min shi be tashi haihuwa yanzu ba, a sanadin hakan na bar
garin Katsina na koma kaduna da zama duk da yake bana da kowa a can, amman sai
Allah ya haɗa ni da mutanen ƙwarai wato iyayen Lamido agidan cikina ya ɓari, kuma
Lamido gashi nan zaune zai iya bada sheda”

Lamido yayi shiru har sai da idon kowa ya dawo kansa.

“Gaskiya ne wannan, a gidanmu cikinta ya zube, kuma mahaifiyarta ita ce tayi mata
komai, na rantse da Allah cikin Namra ya ɓare a gidan mu, na fi tsoron Allah da
kowa”

Namra ta lumshe ido tana jin wani rin sanyi a ranta. Ummi ta ce.

“Mai Martaba wannan ƙanwata ce Hajiya Sadiya kuma ka santa, itace wacce wannan
yaron yayi aiki a gurinta kuma ita ma tace tasam lokacin da ya saki Namra”

Hajiya Sadiya ta kar da ido tana kallon Asim shi ma yana kallonta kallo-kallo akuya
kallon kura.

“Tabbas ya sake ta saboda ya faɗa min a lokacin, har ma na nemi ya dawo da ita
amman yaƙi”

“Ke macuciya karki soma samin bakinki a nan, Mai Martaba wacan Matar da ka gani ba
musulmar ƙwarai bace, a cikin ƙungiyar asiri take kuma tace Maida Namra ne sabosa
tana son ta bada jininta”

Subhanallah kowa ke ta faɗi ana masa kallon marar hankali. Ita kuma ta soma haukace
masa.

“Saboda na faɗi gaskiya sheri zaka min? Amman Asim baka da mutunci duk hallacin da
na maka?”

“Hallacin me kika min? Kika haɗani da ƴan luwani ko kuma jinin mahaifiyarta da kika
shanye, Mai Martaba wannan matar da ka gani itace ta bani apple tace na bawa Namra
sai gashi mahaifiyata ta ci ta mutu, kuma ta sake bani wani ni kuma na bawa ƴarta
Nabila ta mutu, kuma Wallahi ba ƙarya na ke mata ba, sanadin hakan ta rasa lafiyar
jikinta, kuma tiyatar da aka mata saboda maɗigon da take aikatawa ne tana shan
Sperm sai ya zame mata kamar ƙanƙara sai da aka mata aiki aka cire shi, wallahi ƴar
ƙungiyar Asirice duk ta cinye ƴaƴanta, dan haka ni ban yarda da ita ba”

Mai Martaba ya ɗaga masa hannu.

“Ba shi ya tara mu a nan ba, ko minene acan yake tsakaninku”

Kowa a falon ya cika da mamaki, wasu na masa kallon marar hankali, Hajiya Sadiya
kam kuka kawai take tana cewa sai ta yi ƙararsa, Ummi da Mairo kuma mamaki suke,
saboda akwai ƙamshin gaskiya a maganarsa. Wata muguwar harara Abdool yake watsawa
Asim kamar ya tashi ya shaƙe shi.

Malamin faɗa ya gyara zama yana kallon Asim ya ce.


“Kasan idan aka samu irin wannan matsalar ana zartarda hukumcin rantsuwa ne, saboda
haka zaka rantse da alƙur'ane akan kai baka saki matarka ba, saboda kai ne kake
jayayya”

Ba shiri Asim ya saki baki yana kallon Malamin.


[8/3, 9:06 PM] Khadeeja Candy♥: *95*

Kallon Malamin yake kamar wanda be fahincin abunda yake faɗa ba, taya zai rantse
bayan yasan rantsuwa zata iya kama shi, musamman idan da ƙur'ane ne dama ace ba da
alƙur'ane ba da zai iya rantsewa da wallahi ko billahilazin saboda yana tunanin
kamar su ba zasu ci shi ba.

“Ni ba zan rantse ba sai dai Namra ta rantse...”

Duk kallonsa suka yi suna mamakin kalaminsa, Abdool ya katsa masa tsawa cikin wani
irin zafin rai.

“Karka rainawa mutane hankali a nan gurin, Mai Martaba zai ce ka yi abu kace sai
dai wani yayi, wani irin mahaukacin mutun ne kai, idan har kana da gaskiya miya
hana ka rantse, idan baka rantse a nan ba zaka rantse a kotu saboda hukuncin da aka
maka a nan shi za a maka a can”

Waziri ya ɗaga masa hannu.

“Allah ya huku zuciyarka Yarima Allah ya baka haƙuri”

Ba jikin Asim ba har anta cikinsa rawa take saboda tsawar da Abdool yayi masa ga
fuskarsa babu annuri. Sai a yanzu ya gano kuskuren da yayi na saka kansa cikin
wannan matsalar, idan har ya ƙaryata kansa yasan dole ayi masa hukunci saboda yayi
wasa da hankalin Sarki ne da kuma ɗan sarki har ma da jama'ar faɗa gaba ɗaya,
sannan za a tukume shi da laifin tada husuma a gurin walimar babban mutun kamar
Abdallah, bayan kuma kuma Namra zata nesance shi har a bada.
Idan kuma ya rantse yasan Allah ba zai barshi ba, sai dai yasan Allah gafurun
rahimun ne zai iya yafe masa idan har yayi rantsuwar idan ya koma gida sai ya tuba,
shine abunda yake ta saƙawa a zuciyarsa.

“Kai ɗan takalawa, buɗe ka yi magana ko kuma faɗa ta hukunta ka yanzu”

Cewar ɗaya daga cikin manyan faɗar a tsawace yana kallon Asim.

“Ni ba zan rantse ba, sai dai ita ta rantse saboda ita tayi jayayyar cewa na sake
ta, bayan kuma ban sake ba, har taje ta yi wani aure, ni dai a iya yadda nake jin
labarin faɗar nan ance min Mai Martaba mutun me mai adalci da kamanta gaskiya,
shiyasa nayi iƙirarin gaskiyata saboda nasan za a ƙwatar min haƙƙina, da ace wani
sarkin nin tsaɓanin wannan babu abunda zai ya fito nayi wannan maganar sai dai na
barta da Allah”

Ya faɗa yana ƙoƙarin kwashe ƙafafun Mai Martaba, saboda yasa Namra ta rantse ba shi
ba. Abdool ya buɗe baki yayi magana Mai martaba ya ɗaga masa hannu.

“Wannan maganar ta tsaya a haka, idan har muka cilasta wannan yaron yin abunda be
tashi ba to mun shiga haƙƙinsa, dan wannan faɗa mai adalci zata bashi damar shigar
da ƙara kotu domin tantance wanda yake da gaskiya tsakaninsu”

Abbah ya ɗaga hannu, sai waziri ya ce

“An baka dama farin mahaifi uba ga Gimbiya Namra”


Abbah ya kalli Namra dake kusa da Ummi zaune ya ce.

“Mamana tashi ki yi alwala ki rantse”

Babu wanda be yi mamaki furucin Abbah ga Namra ba, sai dai hakan ya karantar da
kowa cewar gaskiya ce Abbah yake son ya buɗe. Namra kamar daman jiran Umarni kawai
take sai ta miƙe tsaye ta nufi hanyar fita duk da bata san hanyar da zata sadata da
banɗaki ba ko kuma wani gurin makamancin wannan. Hanyar da Ummi ta biyo da ita ta
bi tana tafiya har ta fito part ɗin ba, sai barorin dake tsaye habarar gidan suna
shanya tufafi suka rugo da gudu suka zube ƙasanta suna kwasar gaisuwa.

“Allah ya taimaki gimbiya ko da wani abun da kike buƙata ne”

Ɗaya ɗaga cikinsu ta faɗa.

“Banɗaki za a kai ni alwala zanyi”

Ta faɗa tana share hawayen da bata san sun zubo mata ba sai a wannan lokacin.

“Yana ta nan Gimbiya”

Sai suka shiga baga tana biye har suka shiga part Hajiya Shafa, a nan wasu Barorin
ne suka zube suna ɗubar gaisuwa, Namra zata buɗe baki ta yi magana sai wata daga
cikin barorin ta rigata.

“Allah ya taimaki Gimbiya Farida, Gimbiya Namra zata shiga banɗaki ne”

Gimbiya Farida ta miƙe tana aje wayar dake hannunta ta riƙa Namra.

“Muje ta nan”

Tare suka shiga wani ƙaton ɗaki Mai cike da kayan more rayuwa sannan ta kaita bakin
ƙofar Bathroom ɗin ta buɗe mata.

“Bilmillah Amaryar mu”

Ta faɗa fuskarta da murmushi Namra tayi bismillah ta shiga, sai da ta fara tsarki
sannan ta yi alwala ta fito, a bakin gadon ta samu Farida zaune tana kallon ƙofar
ɗakin kamar mai nazari.
Zuwa tayi ta riƙa Namra suka fita tare, ita ta rakata har part ɗin Mai Martaba
sannan ta juya ta koma, sai waiwayen Namra take.

Hasbunallahu wani'imal wakil Namra ta karanta sannan ta saka ƙafarta ta shiga


falon.
Duk kallon sai ya koma kanta, ita kuma dubanta yana gurin Malamin faɗa dakw riƙe
da ƙur'anen fuskarsa da ruwa da alama shi ma alwalar yayi, ƙarasawa tayi ta karɓi
alƙur'ane ta riƙe tana kallon Asim ido cikin ido, kamin ta kawarda fuskarta ta
kalli Malamin dake karanto mata yadda zata faɗa. Ƙur'ane ta ɗaga sama ta soma
ƙaranto rantsuwar kamar yadda Malamin ya faɗa mata, sai da ta rantse sau uku sannan
ana ƙarshen tace.

“Ya Allah ka nuna mai gaskiya tsakanin ni da shi”

“Allahu akbar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Shine abunda kowa ya faɗa yana girgiza kai, Asim kan idonsa tsaya dake laƙe suka
ƙara fitowa gumi ya soma keto masa ta ko ina.

“Amman Namra baki tsoron Allah da gaske baki so? Yanzu sai da kika rantse? Ni ban
sake ki Amman tun da kika rantse amana zata kama ki”

Abunda Asim ya faɗa kenan muryarsa na rawa kamar wanda ya ruɗe. Sai Yayan
Mahaifinsa ya soma masa faɗa tana Allah wadan da halinsa. Sai kawai ya soma rantse-
rantse.

“Wallahi Baba ban sake ta, idan kuma har na sake ta kada Allah ya tayar da ni a nan
gurin lafiya”

Kowa sai mamaki ya kamshi tsakanin ita da shi waye mai gaskiya, ita tayi rantsuwa
da Alƙur'ane akan hakan shine gaskiyarta, shi kuma yace idan ƙaryar yake kada Allah
ya tayarda shi lafiya, sai dai kowa yasan dole akwai wani abu ya faru da ɗayansu
wanda baya kan gaskiya.

Tun da Namra ta soma rantsuwar Abdool ya rumtse idonsa yana saurarenta muryarta,
zuciyarsa kuma cike da tsanar Asim. Maganar da Malam ya fara ne yasa shi buɗe ido.

“Tun da har Namra ta rantse akan ka saketa, ya tabbata aurenta da Yarima Abdallah
yana nan, idan kuma har akan ƙarya ta rantse to Allah zai nuna mata isha dan Allah
ba abun wasa ba ne, daman ana samun irin wannan matsalar idan har miji yayi
jayayyar shi akan sashi rantsuwa ne, idan kuma mata tayi musun haka akan sata ra
rantse ne, duk wanda yake akan gaskiya Allah ya sani kuma zai masa hukunci. Saboda
haka akwai aure tsakanin Yarima Abdallah da kuma Gimbiya Namra, idan kuma har yana
da ja akan hakan zai iya zuwa kotu saboda tabbatar da gaskiyarsa”

Allahu akbar suka faɗa. Asim kuma ya girgiza kai yana kallon Namra hawaye na bin
idonsa ya ce.

“Da gaske ba zaki dawo gareni ba kenan! Ko da ke kika rantse, shikenan na rasa ki
har a bada”

Cikin wani irin zafi rai Abdallah ya miƙe tsaye sai Mai Martaba ya ɗaga masa hannu
alamar kar yace komai ko ya aiwatar da wani abu.
Mai Martaba yayi gyaran murya yana kallon Asim.

“Yaron ka gamsu da wannan hukuncin da akan yanke?”

Ya gyaɗa kai hawaye na masa zuba.

“Na gamsu ranka ya daɗe, tabbas na yi kuskure”

Ya maida dubansa gurin Namra da itama hawayen ta ke.

“Ina son ki faɗa min gaskiya tsakanin ki da Allah, zubar da cikin nan kika yi ko
kuma ɓarewa yayi?”

“Babu dalilin da zai sa na zubar da ciki Asim, da ace zan zubar da na yarda na zaɓi
zama da kai na zubar da cikin kamar yadda ka buƙata, cikin ya zube ne ta dalilin
matsalar da nake da ita a mahaifata na rashin tsayawar ciki”

Murmushi yayi tana tuna lokacin da ya cilasta mata zaɓen cikin ko kuma aurenta,
lokacin da yake iƙirarin be shirya haihuwa ba, yanzu kuma yana kan nema Allah be
bashi ba, a tunaninsa idan har Namra ta rantse to za'ace ta koma ɗakinta ne, yana
tunanin kamar yayi mata wayo yadda rantsuwar ba zata kama shi ba.

“Na gode Mai Martaba da ka saurareni Allah ƙara maka lafiya”

Ya faɗa kamar ba shi ba, gaba ɗaya jikinsa yayi la'asar ya saduda da lamarin dan
yasan ya rasa Namra har a bada, bayan kuma yanzu ne yake jin mashin son ta na sukar
zuciyarsa, yasan nan Mai Martaba yayi masa da sauƙi ne idan aka je kotu shi za a
saka ya rantse, duk da yasan Abdool ba zai ƙyale shi ba.

“Baba ku tashi muje”

Ya faɗa yana fashewa da kuka. Sai duk suka miƙe tsaye jikinsu na rawa suka yi ma
Mai Martaba sallama suka bi bayan Asim da ya rigasu fara tafiya. Kamar jira ake ya
kai bakin ƙofar fita falon sai gashi yayi waɓi mugun faɗuwa kamar wanda aka
kwashewa ƙafafu, Subhannallahi ƴan uwansa suka riƙa faɗa suka ƙarasa da sauri suka
mashi suka tayar tsaye, amman sai ya kasa tsaye ƙafafunsa suka murɗe kamar an
shanyesu, a nan kowa ya ƙara girmama Allah a take ishara ta bayyana iƙirarin da
yayi na cewar idan ƙarya yake kada Allah ya fitar da shi lafiya ya kama shi, da ace
ma shine yayi rantsuwa kamar yadda Namra ta yi da take zai faɗi ya mutu saboda
bashi da gaskiya, da kama-kama suka fitar da shi.

Falon yayi tsit kamar ba kowa sai lamarin Allah suke jinjunawa, bayan kamar mintuna
goma Mai Martaba ya ɗaga kai ya kalli kowa da ke cikin falon ya ce.

“Allah kenan ba a masa wasa, wani lokacin ɗan'adam muna da rauni da gazawa, da kuma
isgili da gajin haƙuri, bayan ba mu wuce Allah yace mana ku mutu mu faɗi mu mutu
ba, ko da beyi wannan isgilin ba dole ne yaga ba dai-dai ba saboda ƙoƙarinsa na
raba auren sunna da kuma ƙoƙarinsa na saka auren cikin rikici.

Nasan hakan zai faru, dole ne a cikinsu akwai mai gaskiya, walau ita ko kuma shi
yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa na hana Abdallah yi masa komai saboda za ayi
duban kamar shi Abdallah baya da gaskiya ne ko kuma an zalumce amman yanzu shi
kansa ya san tsakaninsa da Allah ne ba da mu ba, ƙara Allah yayi masa sakamako da
ace nan aka cutar da shi, nasan zuciyarka ta kawo Abdallah zaka iya masa komai ido
a rufe, sai dai ko da yaushe ina yawan faɗa muku da ku cuci mutum ƙara ka bari shi
ya cuce ka, kar ka yarda ka ɗauki haƙƙin wani ko kuma ace haƙƙin wani yana kan ka,
Ubangiji yana yafiya, amman baya yafe laifin wani akan wani, kuma duk lokacin da
kaci amana ko haƙƙin wani ya hau kanka zaiyi ta cinka ne a dukiyarka ko lafiyarka
sannan kuma idan kunje lafiya Allah ya karɓa masa haƙƙinsa.

Ko wace rayuwa tana zuwa da jarabawa, wani lokacin aka gwada mutun dan a auna
imaninsa, kuma aga iya tawakkalinsa da haƙurinsa, abunda duk haƙuri be baka ba to
rashinsa ba zai baka shi ba, da ace ba ayi haƙuri ba da yanzu ba kawo nan ba, kuma
daga ƙarshe ba za a ga abunda ake so ba. Ina addu'ah wannan aure Allah yasa masa
albarka kuma ya kawarda duk wata fitina da zata zo nan gaba, Allah ya muku albarka,
kuma yau Namra zaki kwana ɗakinki da yardar Allah”

Nasihar Mai Martaba ta ratsa zuciya da jikin duk wanda ke cikin falon, tabbas mai
martaba yayi musu nasiha mai haɗe da wa'azi a lokaci ɗaya.

Hajiya Sadiya ce ta riga tashi ta fice daga falon, sannna Ummi ta tashi tare da
Namra suka yi ma Mai Martaba sallama, sannan suka fito, jingine da mota suka samu
Hajiya Sadiya tana hawaye, har sun buɗe motar sun shiga sai Ummi tace a ɗan jira
kamar tasan Mai Martaba zai aiko kiran Namra, sai ga Waziri da kansa ya zo ya faɗa
ma Ummi cewar Mai Martaba yana kiran Namra, sai Ummi tace ta buɗe mata motar ta
fito ta bi bayan waziri. Falon da suka fito suka koma sai dai wannan karon babu
kowa sai Anty Amarya da Abbah, da alama Mai Martaba ya basu dama su tattauna ne,
waziri ma yana kawowa bakin ƙofa ya kama gabansa.

Ƙarasa Namra tayi cikin kuka ta faɗa jikin Anty Amarya da ke murmushi ta rumgume
ta.

“Mamana kenan kin ga rayuwa, wannan duka sharar fage ne alamu ne na rayuwar jindaɗi
da farinciki tana nan tafe, Allah ya miki albarka”
Bayan abunda Abbah ya faɗa sai Anty ta ɗora da nata nasihar akan rayuwa da kuma
zaman aure kamar yadda tayi mata a can gida. Abbah ma sai da ya kara mata da wani
abu, sannan suka mata sallama saboda yau zasu koma, aiko nan Namra tasa musu kuka
kamar zasu yi rabuwar har abada har Anty sai da tayi kuka, sai da Ummi ta shigo.ta
fita da ita sannan ta tsagaita kuka da take. Sai dai Hajiya Sadiya kan har aka koma
gida kuka take, a motar Hajiya Mairo ke ce mata ta barsa da Allah ai ga amana nan
ta fara kamashi, a tunaninta Hajiya Sadiya tana kuka ne saboda ƙazafin da Asim yayi
mata.
Ko da suka isa gidan ana shirye-shiye fara walimar da Ummi ta shirya zata yi,
wasu tufafin Ummi ta ɗauko ma Namra sanna aka kora Mai Makeup cikin ƙanƙanen lokaci
da canja mata kamanin zuwa na amare, sannan ta ɗaura mata ɗankwali.

Fauza da Haleema ne suka riƙa hannun Namra suka fita da ita gurin walimar suka
zaunar da ita a muhallin da aka tanada na zaman Amarya. Kowa ya fita zuwa gurin
Walimar banda Hajiya Sadiya da ke ƙunshe cikin ɗakin tana aikin kuka, sai kuma Ummi
dake cikin gida tana gyara wasu abubuwan, sai da Hajiya Sadiya ta tabbatar hankalin
kowa yana can gurin walimar sannan ta suɗaɗa ta fita ta bar gidan gaba ɗaya.

Anyi walima lafiya, kuma an tashi kowa na sam barka da yabawa. Bayan mutane sun
watse ne Ummi tasa Namra a mota ita da su Maryam da Raihanatu da kuma Gwaggo Ramatu
aka maida su masaukinsu tare da sauran mutane da suka zo walima, bayan sun koma
gida ne Namra take labarta musu abunda ya faru.

ASIM POV.

Babu mai mota a cikinsu kasancewar Mai Martaba shi ya aika aka ɗaukosu hara Asim
ɗin, a dole tasa sai da suka fita masarautar gaba ɗaya sannan suka samu Napep suka
hau, sauran kuma suka hau wata Napep ɗin ana shawarar inda za a kai shi, wasu su ce
asibiti wasu kuma su ce gida ya kamata a barshi albashi sai a fidda masa konon
rantsuwar da yayi. Daker aka shiga Napep ɗin da shi saboda ƙafafunsa da basa
tafiya, ko da suka isa fida a wahale yake saboda shi kaɗai yasan abunda yake ji a
jikinsa.

A falon Amarya aka aje shi a take ta bada kuɗi aka je aka siyo gero aka cire masa
kono sai dai abunda basu gane ba ai ba shi yayi rantsuwarba, shi isgili yayi na
cewar kada Allah ya tashe shi lafiya idan har ƙarya yayi. Babu irin kuka da Mardiya
ba tayi ba sai nanata zancen take wai daman tasan haka zai faru tun da yace be sake
ta bayan kuma ya san ya sake ta.
Ganin har rana ta faɗi babu wani sauyi, yasa suka ɗauke shi zuwa asibiti, ana
kiran magariba aka bashi gado, likitoci suka shiga bashi taimakon gaggawa, sannan
suka tura shi ɗakin hoto. Allura suka masa a nan ya samu bachi.

***

Ƙarfe tara dai-dai aka jera motoci ƙofar gidan da su Namra suke wato masaukinsu.
Hajiya Shafa da wasu family na mai Martaba suka shiga ciki suka yi bikon amarya da
kuɗi da kuma siyayya.
Ana guda aka fito da Namra tana cikin lifaya fuskarta a lulluɓe, sai ƙamshin
turare take.
Barorinta suka buɗe mata mota ta shiga sai aka maida ƙofar motar aka rufe, sai
sauran suka shiga sauran motocin, aka akama hanyar gidan Mai Martaba da ita,
lokacin da aka shiga da ita faɗar Mai Martaba na shaƙe da mutane da kuma talakawa,
sai ta yi gaisuwar ban girma Mai Martaba yayi musu addu'a sannan aka shiga ɗakin
ɗayar matarsa tayi musu addu'ah sannan aka yi canji mutane da wato mutanen da suka
je bikonta ba su zasu raka ta ɗakinta ba.

Ko da aka isa da ita ɗakinta shaɗaya har ta gota, babu wanda beyi mamakin ganin
irin gidan da aka kaita ba duk kuwa da kasancewar dare ne, baka iya banbance shi da
rana saboda hasken da gidan ke da shi, yanayin gidan zuwa fenti da kwaliyar gidan
duka irin na masarautarsu ne yayi, wani abun burgewa kuma yadda aka ƙawata gidan da
komai fari kamar fentin gidan, wato furnitures da aka zubawa Namra komai fari ne
har labulayenta, da center carpet, kai har agogon bangonta fari ne, duk inda suka
yi masu camera na biye suna ɗauka, tun farkon fitowarta har zuwa gaisuwa da kuma
kawo ta gidan.

A ɗakin da yafi ko wannne haɗuwa aka kaita, kasancewar ɗakuna biyar ne a gidan kuma
ko wanne sai da aka saka masa kaya, sai ta hau tsakiyar gadon ta zauna, kanta
lulluɓe da mayafi.
Wasu daga dangin ango suka mata Allah sa albarka suka fice, sannan wasu daga
ƴan'uwanta suka kama hanya, sai aka bar Maryam kawai sai Raihanatu da kuma wata
ƴar'uwarsu Husaina.

Bayan kamar minti talatin sai suka soma jin busa da algaita da kirari irinta ta
ƴaƴan sarakuna, shi ma mai nasa video yana biye da shi yana ɗauka. Har aka shigo da
shi cikin ɗakin, sai ya zauna bakin gado yana ƙamshin turare, fuskarsa ta sha
rawani kamar Mahaifinsa. Abokaninsa sai zolayarasa suke shi ko bakinsa har kunne.

Nasiha suka musu akan zamantakewar aure da kuma haƙuri, masu auren cikinsu sai
zolayar samarin suke, wasu kuma na zolayar Abdool wai ango sai sha mai. Sai da suka
ga shabiyu ta gota sannan suka musu addu'ah da fatan alheri, sannan suka saka
Maryam da waɗanda suke tare gaba, har wasu na cewa suna son Maryam a zatonsu
budurwa ce.
[8/5, 7:03 PM] Khadeeja Candy♥: *96*

Bayan abokansa sun wuce Abdool ya tashi ya rufe ƙofor falo ya dawo ɗakin fuskarsa
da murmushi, rawanin kansa ya fara cirewa ya aje sannan cire babbar rigarsa.

“Amaryata wacce ta wacce amarya tsada”

Ya kai hannu zai yaye gyalenta, sai ta matsa baya ta ƙara jan gyalen ya sauko.
Matsawa yayi kusa da ita ya sake miƙa hannun sai ta kauce hannunta mai zanen lalle
ta ziro masa. Murmushi yayi yasa hannunsa aljihu ya ɗauko wani ɗan ƙaramin box ya
ɗora mata saman hannu, sai ya miƙa hannun ya yaye mata mayafin. Idonta a rufe
fuskarta ɗauke da murmushi

“Har da idon sai na siya...?”

“Ai kace wannan amaryar ta fi ko wace Amarya tsada”

Murmushi ya sake yi sai ya cire tsadadden agogon hannunsa ya ɗora mata saman
hannu, sai a lokacin ta buɗe ido ta saka su cikin nashi haƙoranta a washe.

“Kin manta ban siye murmushin ba”

“Maganar ma ai baka siya ba an yi maka nasiha ne kawai”

Hannu ya kai ya riƙa gefen fuskarta yana shafa shi da babban yatsansa.

“Godiya ga Ubangijin da ya mallaka min wannan halittar, lallai na fi ko wane Namiji


sa'a a duniyar nan”

“Kana koɗa Namra da yawa, har kana sa tana jin kamar ta fi ko wace mace zama
sarauniya”

“Na haɗu da mata da yawa ciki da wajen ƙasar nan amman babu wacce ta sace min
zuciya sai Namra, she ko ma ƙaramar sarauniyace ba”
Lumshe ido tayi tana murmushi. Box ɗin ya amsa ya buɗe ya fiddo zobe mai kyau ya
kama hannunta ya saka mata.

“I Love you so Much Abnam”

“Na gode sosai”

Matsawa yayi kusa da ita.

“Godiya kawai? Ai hausawa na cewa yaba kyauta tukuici”

Ta rufe fuskarta domin ta gano ma'anar zancensa. Shi ma dariyar ya yi, ya jata
ƙirjinsa ya rumgume, a hankali ya sauke numfashi ya ɗora kansa kaman nata.

“Gani komai nake kamar a mafarki, ina tuna lokacin da na fara ganinki irin halin
rayuwar da na shiga saboda ke kuma gashu yanzu komai ya zama tarihi, inshallah ni
ne mijinki ke kuma matana har Aljanna”

Lafewa ta yi a ƙirjinsa kamar babu wanzuwarta a doron ƙasa, gudun zuciyarsa take
sauraren tana auna yada nata zuciyar yake hawa da sauka tare da ta shi.
Sun daɗe a haka sannan ya ɗagota ya mata kiss saman ido.

“Karki min bachi saman jiki kisa na ƙarye”

Tayi dariya tana bugar masa chest.

“Ouuuuch”

Ya faɗa yana kanne mata ido ɗaya. Shi ya fara sauka saman gadon sannan ya miƙa mata
hannun, ta riƙa hannunsa ta sauƙo suka shiga bathroom ɗin tare, shi ya fara alwalar
sannan ya taimaka mata ita ma tayi suka fito. Sallaya biyu ya shinfiɗa ɗaya a gaba
ɗayar kuma tana baya da shi kaɗan.
Mayafinta ya ɗauka ta rufe jikinta kasancewar fafaɗa ne kuma mai kauri. Yana gaba
tana biye har suka yi raka'ah biyu, sannan suka sallame. Hannunsa ya ɗaga masa ya
riƙa kwaroro musu addu'ah tana amsawa da amin sanna suka shafa, sai ya juyo ya
kalleta.

“Hajiya Akwai wata sunnar bayan wannan?”

Ta zare masa ido. Sai ta gurgiza masa kai alamar a'a. Dariya yayi ya tashi ya ɗauko
ledojin da gefen gadon ya kawo gabanta ya aje, sannan ya fita daga ɗaga ɗakin gaba
ɗaya. Be ɗauki dogon lokaci ba sai gashi ya dawo da plate da cup ta aje a gabanta
sannan ya zauna yaja ledar ya buɗe ya fido ƙatuwar kaza ta ɗora saman plate ɗin sai
ya mayardar ragowar gajin a gefe ɗaya, ya buɗe madara ya zuba musu a cup ɗaya
sannan yasa hannu ɓare kazar ya soma kai mata a baki. Kawar da fuska ta yi tana
murmushi.

“Ki taimaki bawan Allah nan ki bar shi ya ciyarda dake a wannan daren da yafi ko
wane dare muhimmanci da daraja a gareshi”

“Na hutar da kai, zan iya wannan aikin”

“Ai bana son hutun ne, idan dare ya lula ke da kanki zaki min kukan gajiya ki neman
na hutar da ni, amman ba yanzu ba yanzu ai ai ba aiki na ke ba”

Ta ɗan fiddo ido tana kallonsa, sai ya kanne mata ido ɗaya, ba shiri ta buɗe baki
tana mamakin yadda yake ƙoƙarin faɗar maganganu kai tsaye. Hakan ya bashi damar
saka mata naman a bakin.
Cikin so da ƙauna yayi feeding ɗinta, sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya
cilasta mata ita ma ta yi feeding ɗinsa a dole ba dan ranta ya so ba, bayan sun
ƙare ya kwashe plate ɗin ya buɗe wardrobe ya fiddo kayan bachi kala ɗaya amman na
maza da mata, na matan ya miƙa mata shi kuma ya shiga ƙoƙarin zame kayan jikinsa ya
canja zuwa na bachin sai ta zaro ido.

“Wai nan zaka canja su?”

“To miye? Naga an zama ɗaya”

“A'a da saura, bari na baka guri ka canja”

Wani shu'umin murmushi yayi har da cije baki.

“No ba sai kin fita ba, bari na baki guri ki canja nima kuma sai na canja a wani
ɗakin ko, ƙina da gaskiya ai ba mu zama ɗaya ba amman mun kusa raba gari”

Ya fice yana dariya kamar ba shi ba. Yana fita ya ɗauki kayan bachi da zimmar
canjawa sai ta ga ɗan ƙaramin wando sai wata fikicar riga iya cibiya sai kuma
babbar mai kamar rariya wacce zata rufe jikin gaba ɗaya. Mayardar kayan ta yi ta
aje taja gyalenta ta ƙara rufe jiki.

Shima irin kayan bachinta ne jikinsa bancanci shi baya da wannan ficikar rigar
ƙirjinsa a sake yake. Tana kallonsa gabanta yayi mugun faɗuwa, ta razana sosai
kamar bata taɓa ganin ƙirjin namiji a waje ba, yana doso inda take ƙanshin turaren
da ya saka ya riƙa dukan hancinta, ko da ya ƙaraso kusa da ita ta rufe idonta gan
numfashinta har rawa yake.

“Baki canja kayan ba?”

“Da wannan zan kwanta”

Ta faɗa ba tare da ta buɗe idon ba.

“To tashi ki hau gadon ki kwanta”

“Na fi jindaɗi a ƙasan”

“Ƙasa zamu kwanta kenan”

“A'a kai ka kwanta saman gadon, ni na kwanta a ƙasa”

Duk maganar da sukw bata yarda ta buɗe idonta ba. Shi kuma ya lura da hakan.

“Look Abnam karki tauye kan ki, ni ba baƙon tsanani ba ne, ma zan zo na takurawa
masu gida ba, idan kina son kwantawa saman gadon kawai ki kwanta”

Ta yi saurin kwantawa a gurin.

“Ni ko gida ƙasa na ke bachi”

Ya ɗaga gira ɗaya like serious. Ya sauko da bedsheet ɗin ƙasa.

“Tashi a shimfiɗa”

“Dan Allah Abdallah ka bar ni nan”

Ta faɗa kamar mai shirin yin kuka. Sai kawai yayi murmushi ya mayardar bedsheet ɗin
ɗale saman gadon ya jefo mata matashin kai.
“Gashi nan kar na matso kuma ki ce wani abun zan miki, amman kin san shure-shire
baya hana mutuwa ko?”

Sai a lokacin ta buɗe ido ta ɗauki filon ta tare kanta ta yi rufa da gyalenta.
Hannu ya kai gurin kan bed ɗin ya kashe wutar ɗakin. Wani tsoro ne ya ƙara
baibayeta, kwatakwata ta manta da irin rayuwar da ta yi a gidan Asim, ta fi jin
sakewa da shi fiye da Abdool wata ƙila saboda yanayin hallitarsu ba ɗaya ba.

“Ka kunna wutar man...”

Bata ƙarasa rufe baki ba taji mutun a bayanta yasa duka hannayensa yajata jikinsa
ya rumgume ta. Sai ya kawo bakinsa dai-dai kunnenta.

“Shiiiiiiii ba wani abun zan miki ba, kawai dai ba zai yayu nakwana da mace ɗaki
ɗaya ba kuma ace mu kwana a rabe ba, kawai ina son jinki ne a jikina that's all”

A dole ya gunɗe bakinta ta rumtse ido, tana jin yana ɗan taɓa ta amman ta haƙura
har bachi yayi gaba da ita. Washe gari ta rigashi tashi saboda bachin rabi da rabi
tayi ko da aka kira assalati idonta huɗu ba ma biyu ba. Tana unƙurin tashi sai shi
ma ya tashi saboda tana a ƙirjinsa ne duk wani numfashinta yana ji balle kuma
motsinta.

Sai da ya fara shiga bathroom ɗin yayi wanka da alwala sannan ita ma ta shiga ta yi
alwalah, tare suka yi sallah sannan ta koma bachi, shi kuma ya buɗe ƙur'ane dake
cikin wayarsa ya soma karatu, ba shi ya tashi daga gurin da yake ba sai da aka buga
masa waya aka sanar masa an aiko musu da abinci. Wannan karon Ummi bata aiko masa
ba saboda ta san za'a aiko masa daga gidan Mai Martaba.

Sai da ya zuba abinci sannan ya shiga ɗakinta. Zaune ya sameta a gurin da ta yi


bachin tana kallon ƙofa.

“Acici daga jin motsin ƙuloli har kin tashi”

Dariya ta yi

“Ai ba kai aka kawo ma abincin ba ni aka aiko ma”

“Ai ba kai aka kawo ma abincin ba ni aka aiko ma, yanzu ai kin kina da baki ko?”

Ya kai kayeta yana wani girgiza kai da kashe murya. Ya miƙa mata hannunsa

“Zo nan muje ki wanke bakin ki”

Kamar wata ƙaramar yarinya haka ta miƙa masa hannun ya tasota, da kanshi ya wanke
mata bakin bayaɓ sun gama ya ɗauke ta ya kaita dinning.

“Kai a she nauyi ne da ke, na ji kamar jijiyoyina zasu katse”

Ya faɗa yana dariya. Shi yayi feeding ɗinta sannan yayi feeding kansa. Ko da aha
biyu ta yi daga ita har shi duk sun shirya cikin fari yadi mai kamar shadda sky
blue. Tana gaban madubi tana kwaliya ya ƙaraso kusa da ita ya ɗauki sarƙa ya saka
mata sannan ya juyo da ita ya kalleta.

“Kin yu kyau Abnam”

“Faɗa min ma'anar sunan nan”

Bakinsa ya kai dai-dai nata ya haɗe ya tsotse jan bakin da ta sha sannan ya ɗauke
bakinsa ya mayar gurin hancinta idonsa kamar mai jin bachi. Ita kan nata a lumshe.

“A-B Abdallah N-A-M Namra = ABNAM”

Murmushi ta yi ta buɗe ido tana jin yadda danshin yawunta ke zaga ko ina na
bakinta, shi ma murmushin ya mayar mata yasa yatsunsa ya riƙa lips ɗinta yana
murzawa a hankali, cikin hikima ya zura mata manuninsa cikin bakinta ya riƙa wasa
da halshenta.

“Zan je na gaishe da su Mai Martaba da Ummi”

Ya faɗa yana kallonta, sannan ya zare hannun daga bakinta ya miƙe tsaye yana saka
yatsan cikin bakinsa ya tsotse yawun.

“Allah ya tsare”

Ta faɗa tana tsotsa halshen nata. Sai kawai yasa mata dariya ya zuba hannayensa
aljihu ya fice zuciyarsa cike da farincikin.

Bayan fitar da ƴan mintuna su Maryam suka dawo saboda yi mata sallama,ragowar kajin
da suka tarar suka cinye suna zolayar Namra da ke ta aikin kuka wai zasu je su
barta.

Sai da ya fara biyawa gurin Ummi ya gaisheta sannan ya wuce gurin Mai Martaba,
Wannan karon har da Mai Martaba gurin jansa.

“Ango ango”

Wata kunya ce ta kamashi sai ya zauna ya kasa haɗa ido da Mai Martaba. Cikin
girmamawa suka gaisa, sannan Mai Martaba ya ce

“Ɓan sani ba ko matarka bata da buƙatar barori shiyasa ban aika mata da su ba, idan
ka yi shawara da ita tace maka tana buƙata sai ya faɗa min”

“Godiya muke Mai Martaba Allah ya ƙara lafiya, amman ina tunanin ba sai an kawo
mana su ba, saboda ba nan zamu zauna ba, hutun da suka ba ni ma na sati biyu, dole
Abuja zan koma da ita, kuma ga karatun da take a sokoto sauran wata bakwai ta ƙare
diploma”

“Hakan na da kyau, amman kasa ido kan rayuwa, Babana kana da maƙiya da yawa matarka
ma sai ta yi taka tsantsan, ni kaina a yanzu hankalina zai fi kwanciya idan kana
abujar fiye da ace kana kusa da ƴan uwanka, saboda za a iya amfanin da su a cutar
da kai ko kuma a cutar da matarka, duk da bana jin akwai wanda zai sake wani
unƙurin sake aikata abunda Hajiya ta yi Unƙurin aikata maka”

“Wace Hajiya Mai Martaba?”

“Hajiya Karima, (Matar ƙanensa) itace tasa waɗanda ƴan bindigar unƙurin hallaka ka,
saboda ita da mijinta suna tunanin idan bana raye babu wanda ya dace ya hau
sarautar Katsina sai mijinta, ni kuma ina tutuyar kai ne zaka yi milkin garin
Katsina ko da bana raye”

“Mai Martaba ina ka samu wannan labarin?”

“Abdallah kenan, ai ko babu komai na kan aa ido akan ƴaƴa balle kuma kai da
mahaifiyarka bata cikin gidan nan, tun daga lokacin da aka maka wannan aika aikar
tunani ya bani ba daga waje ba ne, sai dai ko daga nan cikin gida ne, saboda bana
tunanin ina da wasu maƙiya bayan na cikin familynmu kuma akan sarautar mu, hakan
yasa na zurfafa bincike ta ƙarƙarshin ƙasa sai gashi wanda aka aika gurin yin abun
ya same nan a cikin faɗar nan ya faɗa min komai, wannan yasa ya tara su ita da
mijin nata da duka family mu na gargasu a lokacin hankalinka yana gurin Amaryarka
shiyasa ban taɓa labarta maka wannan ba”

Abdallah yayi murmushi yana auna irin son da Mai Martaba yake masa.

“Babana idan na kalleka na kan jidaɗi nasan ko bana raye kai mutum ne zaka iya riƙe
gidan nan kuma ka riƙe ƴan'uwanka, iyakar soyayyar da zan nuna maka na tarbiyantar
da kai na baka ilimi kuma na baka duka, yanzu addu'a ce kawai zan binka da ita,
Allah ya maka albarka”

“Amin Mar Martaba na gode, Allah ƙara maka imani da lafiya”

“Amin”

Daga haka suka ɗauko wata fira, na familynsu da kuma sarautar Katsina, be bar gidan
ba sai la'asar.

***

Bayan sun yi sallah azahar suka yi shirin tafiya aiko Namra ta ƙara tsaresu da kuka
tun suna juriyar sai da ta saka Maryam ma ta yi kukan, isowar familynsu Abdool
waɗanda suka zo ganin Amarya ne tasa ta tsagaita kukan har suka samu suka tafi.
Mota mota suka riƙa zuwa ganinta kasancewar wasu yau zasu tafi wasu kuma gobe har
na ɓangaren Ummi wasu ma nan suka yi sallah magariba ana kiran isha'i sannan suka
fice.

Ko da Abdool ya dawo ya tarar bata cikin daɗin rai, shi ma kamar jira take yana
taɓa fuskarta ta faɗa jikinsa ta fashe masa da kuka, daman yasan za a rina, saboda
ya samu labari a faɗar mai Martaba cikin mutanen da suka kawo kara suna cewa tare
zasu koma gaba ɗaya.

“Ooo an tafi an bar ƴar Mamarta”

Ya faɗa yana zama saman kujera riƙe da ita.

“Bari na kira miki mamanki”

Ya fiddo wayarsa ya kira Ummi ya miƙa mata ba ko kunya har da faɗa nata wai kuka
take masa su Maryam sun tafi su barta. Ummi ta yi dariya

“Aure ai haka ya gada yi haƙuri kinji ƴata, duk abunda yayi miki ki faɗa min”

“Toh Ummi, na gode”

Abdool ya karɓe wayar.

“Mai Martaba ma haka ya faɗa mata wai idan na mata abu ta zo ta faɗa masa, ni idan
ta min wa zan faɗawa”

“Ai mata basa laifi kuma su ƴan gata ne shiyasa, kai duk abunda ta yi maka sai ka
yi haƙuri ka haɗiye”

Namra ta masa gwalo, shi kuma ya kama kunenta ɗaya ya mirɗe.

“Ummi sai da safe tun da ƴarki kika shigarwa”


“Ato da kai zan shigarwa? Dan baka da kunya ƙato da kai, Allah ya shirya ka”

Ta katse kiran. Shi kuma yasa ɗayan hannunsa ya riƙe kunnen nata ya ƙara mirɗewa.

“Wallahi da zafi”

Ta faɗa cikin shagwaɓa, sai ya saki kunnen yana dariya.

“Gobe ma bakinki ya sake min gwalo”

Dariya tayi ta unƙura zata tashi sai ya jata ta faɗa jikinsa. Hannunsa yasa cikin
ɗigarta tana ƙoƙarin taɓa ƙirjinta da ke tada mishi hankali tun jiya.

“Ina zaki je?”

Tayi shiru bata amsa shi ba, shi kuma be fasa abunda yake ba, natsuwa tayi tana
karɓar saƙon da yake aika mata, har ga Allah tana jin daɗin yadda hannunsa ke
zagaye rigarta, kamin ya ɗago fuskarta ya haɗe bakinsu.
Yadda ya riƙa tsotsa mata halshe yasa ta sake jikinta gaba ɗaya, tana sauke
numfashi a hankali, kamar wacce ta tuna wani abu sai ta zabura ta miƙe tsaye. Wani
kallo yayi mata idonsa sun kaɗe kamar ba shi ba, jikinsa har rawa yake, yana mikewa
tsaye ta matsa baya.

“Ba a taɓa min irin wannan wasan ba karki soma yanzu Abnam please”

Ya faɗa a wahale, sai ya ƙara matsawa ta matsa, baya tana murmushi.

“Ban yi sallah isha'i ba kuma wanka zanyi”

Rumtse ido yyi ya faɗa saman kujerar yana cizar baki. Da dariyar ƙeta ta wuce
ɗakinta ta yi wanka sannan ta yi sallah.

Wasu kayan bachi ta fiddo masu abun arziki ta saka sannan ta ƙarasa gaban madubi ta
soma shafa mai. Tana cikin shafa man ya shigo sanye da nasa kayan bachin, kamar na
jiya sai da waɗannan fararene. Kallo ɗaya tayi masa a madubi ta ɗauke kai, maida
ƙofar ɗakin yayi ya rufe, sai ya karaso gabanta ya durƙusa har ƙasa ya kama ƙafarta
yayi mata kiss, tun daga kan ɗan yatsanta taji abu ya tsikareta har cikin gashin
kanta, a take gashin jikinta ya tashi ba shiri ta rumtse ido. Hakan ya bashi damar
luma babban farcen ƙafarta cikin bakinta ya tsotsa kamar mai shan sweet candy, ji
tayi kamar ba zata iya bashi abunda yake buƙata a yanzu ba, kuma ba zata iya
hanashi ba. Sai kawai ta miƙe tsayw da sauri duk da idonta a rufe yake, sai kawai
taji ya rumgumeta yana ɗaukar numfashi. Zafin jikinsa ne ya rika ratsa nata jikin,
a hankali ya ɗauketa ya kwantar saman gadon ya saka bakinsa cikin nata yana shafa
fatar jikinta, tana ji tana gani ya tabata da kayan jikinta yana arba da chest ya
sauke wani irin ajiyar zuciya sai ya kai hannu ya kai ya kashe wutar ɗakin, sannan
zame nasa kayan bachin.

Sun makara gurin sallah asuba kasancewar basu yi bachi da wuri ba, more especially
ma Namra da bachi be mata daɗi ba gaba ɗaya, da asubar ma sai da taimakonsa ta
tashi azabar da taji a gurin Abdallah yafi wanda ta ji a darenta na farko da Asim,
cikin ruwan zafi ya zaunar da ita ya riƙa gasa mata jiki sannan ya ciƙa mata buta
ya riƙa mata tayi wankan tsarki, sannan ya naɗata cikin tawul suka fito, ba tare da
shi ya ɗaura tawul ɗin ba kasancewar ɗaya ne na bathroom ɗinta, sai da ya aje ta
saman gado sannan ya ɗauki rigar bachinsa ya ɗaura ya nufi ɗakinsa.

Da Hasbunallahu da Innalillahi ta unƙura ta sauka saman gadon ta buɗe wardrobe ta


ɗauko doguwar riga ta koma ta zauna tana dantsar baki.
Sai ga Abdallah ya shigo ya ƙaraso kusa da ita da sauri ya riƙa rigar ya saka
mata.

Bayan sun yi sallah ta koma saman gado ta kwanta, shi kuma ya buɗe ƙur'ane cikin
wayarsa ya soma karatu, wannan karon be daɗe yana karatun ba, ya aje wayar ya koma
bayan Namra ya kwanta ya rumgumeta. Wani irin daɗi yake ji for the first time in
history ya kusanci halalinsa ciwon cikin da yake fama da shi yau ya kau, yana jin
daɗi sosai Namra ta kai shi duniyar da be taɓa mafarkin zuwa ba, yaji daɗin ɗa be
taɓa ji ba a rayuwarsa.

Basu farka ba sai da aka kawo musu abincin safe kamar jiya, sai dai yau kam basu
karya ba sai sha biyu na rana bachi wahala Namra ta riƙa yi, tana farkawa ta fara
zuba masa shagwaɓa tana narke masa a jiki, shi ko duk yabi ya susuce sai
tarairaiyarta yake.

*** *** ***

Bayan an kwana biyu abubuwa sun ɗan laɓa Ummi ta shirya ta je gidan Hajiya Sadiya,
tun lokacin da abun ya faru ta kasa natsuwa zuciyarta na nuna mata kamar akwai
ƙamshin gaskiya a abunda Asim ya faɗa.

Ta yi sa'ar tararda ita gida, sai dai ba cikin yanayin jindaɗi da walwala ba. Sama-
sama suka gaisa da Ummi tana wani noce kanta kamar mai jin kunya, Ummi na lura da
ita amman sai tayi kamar ba ta kula ba ta ɗora da zancen da ya kawo ta.

“Na kasa natsuwa da maganar nan ne da yaron nan ya faɗa a faɗar Mai Martaba miye
gaskiya a ciki?”

“Babu komai Zuwaira ƙarya ce yake min kinsan halin mutanen yau ka saka musu da
alheri su maka sheri”

“Ɓana son ki ɓoye min komai Hajiya ni ƴar'uwarki ce, ko zaki ɓoyewa wani ba zaki
ɓoye min ba, ba ni kaɗai naji wannan maganar ba amman nafi kowa damuwa, na san ko
zai miki kazafi ba zai miki na wannan ba”

Jikin Hajiya Shafa ya mutu sosai tabbas wanda ke son ka ne kawai zai damu da kai,
sai dai mi bata tunanin zata buɗe sirrinta a gurin da ake ganin ƙimarta.

“Gaskiya ne, amman bana son labarta miki komai daga abunda baki sani ba, rufe
wannan sirrin zai fi buɗe sh alheri”

“Kina tunanin kamar zan labartawa wani abunda kika aikata ne?”

“Idan na labarta miki zaki daina ganina a mutun ne, kuma kwana kaɗan ya rage min a
duniyar nan saboda sun faɗa min lokacin da zan mutu”

Hawaye sun soma zirya a kumatunta.

“Mu kaɗai muka rage, iyaye duka sun tafi idan ba mu kula da junan mu ba wa zai kula
mana, zumuncin da kullawa daga kan mu zai fara sannan ƴaƴanmu su ɗauka”

“Ba zan iya labarta miki komai ba, saboda babu amfanin faɗa miki komai, nasan Allah
ba zai yafe min ba”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shirka kika aikata Hajiya?”

“Ina ma shirka ce da zan iya tuba na gyara imani na kuma Allah ya yafe min, wannan
fa? Allah baya yafe wani kan wani, na lalata da yawa na salwantar da rayuwar mutane
da yawa cikin har da na ƴaƴana da miji na wallahi bata yi ba wallahi cul...”

Sai ta ƙasa ƙarasawa ta fashe da kuka. Ummu ta fashe komai duk da bata fili ta faɗa
komai ba, jikin Ummi yayi sanyi sosai har ta rasa abunda zata ce mata jiki ba gwari
ta tashi ta ɗauki jarka zata fice.

“Ai na faɗa miki faɗin bashi da fa'ida, zaki daina ganina a mutun ne ki riƙa ganina
kamar wata dabba ko aljana”

“Ban daina ganinki a mutun ba Sadiya, kowa baya wuce kaddararsa, rayuwa tana zuwa
mutun ne ta yadda Allah ya tsara masa da kuma yadda sheɗan ya kawata masa, zan
kasance mai miki addu'ah da kuma rike sirrinki, sai dai ina baki shawara ki gyara
tsakanin ki da Ubangijinki domin shi mai yawan gafara ne mai rahama”

Daga haka Ummi tasa kai ta fice zuciyarta cike da tausayin ƴar'uwarta. Fashewa
Hajiya Sadiya tayi da kuka, tabbas ratuwa tana tafiya ne ta yadda Allah ya tsara da
kuma son zuciya, da ace tayi haƙuri da bata shiga wannan rayuwar ba, saboda Allah
ya kaddara zata samu abunda zata samu, sai dai ya danganta da imaninta da kuma
gajin haƙurinta, abunda duk Allah ya rubuta ka same shi sai ka sameshi sai dai ya
danganta da yadda mutun yayi haƙuri idan ka yi gajun haƙuri ya zo maka ta haram
idan kuma ka yi haƙuri ya zo maka ta halal amman tabbas abunda Allah ya rubuta naka
ne, naka ne no matter what...!
[8/7, 2:47 PM] Khadeeja Candy♥: UZAIR POV.

Be yarda an shiga kotun ba kamar yadda ita Yaamin ɗin ta so ganin ya ƙi ya bata
takardar sakinta, tun da Ummu ta ga takardar tasa ya rubuta mata takardar sakin
yana kuka ta aika mata, Uzair yana son Yasmin amman babu yadda ya iya tun da ta
zaɓi rabuwa da shi, shi kanshi yanzu yasan babu wanda zai zauna da shi sai
mahaifiyarsa, wata biyar da faruwar hakan wata lalurar ta sake samunshi, ta yoyon
kashi a dubura, daman tun last year ya fara wannan abun maganin da yake sha'ane
yasa abun tsaya masa, yanzu kan babu magani kuma ga zaman keke wanda ya zame mata
jiki tun da kullum a nan yake zaune. A yanzu ne kowa ya ƙara tabbatar da gaskiyar
abunda Namra ta faɗa.

Ranar da labarin ɗaurin auren Namra ya same shi yayi kuka har sai da idonshi
suka canja kala, tabbas yasan ya cuci yarinyar sai dai ba haƙƙinta ne kaɗai ya ke
binshi ba har saɓawa Allah da yayi, saboda ya tsallake iyakarsa, ya aikata laifin
da Ubangiji ya hana bayinsa tsarkaka su aikata, yasan baya cikin bayin Allah na
gari.
Kaito! Da wata rayuwa dai ƙara babu, yau gashi baya amfanarda kanshi da komai, ga
kuma kunyar duniya ta isheshi, ƙanensa ma basa da lokacinshi, mahaifiyarshi ce
kawai take kula da shi, ita kanta da taga abun yayi yawa sai ta nemo mai kula da
shi ana biyanta duk ƙarshen wata, saboda ragewa kanta wahalar ita kaɗai.

Sai a yanzu ya gane ashe babu riba a cikin tsaɓawa Allah da cin amana, yayi nadanar
da babu amfanin tun da yasan Abbah ba zai taɓa yafe masa ba, abunda Matarsa ta yi
masa ma ishara ne idan yaronsa idan ya girma ba zai samu labari mai daɗi ba, ji
yake kamar ya mutu ya huta, kunyar duniya ta ishashi a family da abokai babu wanda
be ji abunda ya aikata ba, yana ji yana gani jindaɗi da kwanciyar hankali ya
gagareshi lafiyarsa jikinsa ma ta tafi ta barsa, komai ya zo masa kamar mafarki,
haka wani lokacin zai zauna yayi ta kuka idan ya tuna irin rayuwar jindaɗin da yayi
yau ga shi ya koma wani kalar mutun da a gidansu ma uwarsa ce kawai ta damu da shi,
sai a yanzu ya gane yayi kuskuren aikata abunda ya aikata sai dai lokaci ya ƙura
masa babu ta yadda zai gyara komai ko da kuwa zai so haka, duk ya bi ya rame kamar
ba shi ba gaba ɗaya halittarsa ta canja a Wheelchair ma idan ya zauna sai yayi
kamar zai koma gefe, sai a ayanzu ya gane ashe cin amana da tsaɓawa Allah babu riba
a ciki duk romon da yasha yana ganin kamar ya more ashe sakayyah na biye.
KALSOOM POV.

Tana jin kamar ta fi ko wace mace sa'ar miji a duniya, bata da mtsala ta ko'ina,
mijinta na nuna mata so da kulawa ƴan'uwanshi ma haka, ga su Ezzah da suka zame
mata kamar ita ce ta haifi yaran.

Wani lokacin ta kan zauna ta auna irin rayuwar da tayi a gida zuwa aurenta irin
rigingimun da gwargwarmayar da tasha a lokacin da tayi kishi da Rashida amman yanzu
komai ya zama tarihi, babu komai a cikin duniyarta sai farinciki jindaɗi komai ya
zo kamar a mafarki, addu'ah da ta daɗe tana yi aje an amsa mata tuni jindaɗin na ne
yake nesa, tabbas wani jinkiri alheri ne, kuma bayan wuya sai daɗi, rayuwa bata
tabbata a guri ɗaya dole akwai canji ɗan adam baya taɓa zama a cikin wahala kullum
maruƙar ka riƙe gaskiyarka kuma ka ji tsoron Allah ka yi haƙuri wallahi sai kaga
canja domin dukan tsanani yana tare da sauƙi haka Allah ya faɗa.

Ta zama uwar ɗiya bayan ƴaƴanta uku da ta haifa ga ƴaran Rashida da su a yanzu sun
tasa sosai. Shi kansa Hilal sai a yanzu ya fahimci irin tasirin da Kalsoom ta keda
shi a zuciyarsa da kuma rayuwarsa, domin gudumawwa take bashi ta ko ina, sai a
yanzu ya gane mai haƙuri mawadaci lalla yayi dacen mata, a cikin ɗari yayi nasara
zarar ɗaya, komai jindaɗi suke yinsa da kwanciyar hankali ga soyayyar da suke
nunawa juna kamar Romeo and Juliet.

LAMIDO POV.

Ya girgiza da Asim yadda ya mayarda ƙaryarsa gaskiya, har ya nemi ƙetare iyakar
Allah, be yi mamakin abunda ya same shi a tun a falon ba, a tunaninsa ma ya
cancanci fiye da haka. Bayan Mai Martaba ya tashi sai yayi ma su Abbah sallama
Abbah yayi masa godiya, sannan ya kama hanyar Katsina.

A gida ne yake labartawa su Neine abunda ya faru, su kansu da basu ga yadda abun ya
wakana ba amman sun jinjina lamarin suna yaba ƙoƙarin Asim na ketare iyakar Allah
duk da basu san shi ba.

Abinci ya siya musu da kuɗin da Abbah ya bashi da kuma ƴan kayan masarufi, sannan
ya koma Neine na masa addu'ah da kuma saƙon gaisuwa ga su Abbah.
Kwana biyu da komawarsa ya fara aikin a kamfanin Abbah wato Zamau Metals Work
kamfanine da ke sarrafa ko wane irin ƙarfe da kuma dukan abunda ya shafi ƙarfi
hakaɓ yasa ana yawan bashi kwangila saboda yana hulɗa da ƴan siyasa sosai kuma yana
cikin mutane da ake damawa da su ciki da wajen jihar sokoto.

A gidan yake zama lokacin aiki ya tafi idan ya dawo kuma baya komai sai ya zauna a
gida, hakan yasa wani mugun shaƙuwa da kula juna ya shiga tsakaninsa da Aisha, har
ta kai idan bata ganshi ba sai ta kira shi ita ma haka, babu abunda yake ci mata
tuwo a ƙwarya kamar tafiyan da yake akan abun hawa idan zaije aiki ko kuma fita
wani gurin daban, wani lokacin ta kan ɗauki makullin motar Anty tasa ya kaota wani
gurin, ta saka Abbah gaba da zancen ya siya masa mota sai Abbah ya mallaka masa
motar da yake jan namra ada wato wacce yake kaita makaranta. A ranar Aysha ji tayi
kamar ta haɗe Abbah dan murna tana ta jindaɗi sosai, daga lokacin duk inda zata je
shi yake kaita matuƙar ba aiki yake ba ko kuma zaije ba, shi kansa yana jindaɗin
fura da kuma sakewa da Aisha, lokuta da dama tana masa yanayi da Namra, yana samun
nishaɗi sosai idan yana fira da ita. Kwana biyu ɗa bashi motar Neine da wani
ɗan'uwanta suka zo yi ma Abbah godiya, kwanansu ɗaya suka koma, Yadda Aysha ta riƙa
kula da Neine ya karantar da Abbah ba iya mutuncin ne a tsakaninta da Lamido ba har
da soyayyar da ma ya lura da irin shaƙuwar da ke tsakaninsu, hakan kuma ba ƙaramin
faranta ran Abbah yayi ba, a kullun tunaninsa da ina zai farantawa Lamido ya saka
masa da abunda yayi masa, tun daga lokacin da yaje ya bada shedar a faɗar Mai
Martaba Abbah ya ji daɗin abunda yayi masa.

YASMIN POV.
Tana ji tana gani kuma tana ciki gari aka yi bikin Namra ta ƙi ta leƙa saboda tana
ganin kamar idan taje za a riƙa nunata ne, ko kuma mutane su tuna abunda ya faru.

Duk wani tunani na rayuwa da zullumi sai ta tattarashi gefe ta aje ta maida
hankalinta kan aikinta, tun bayan abunda ya faru da Uzair sai ta tattara lamarin
namiji ta aje gefe ɗaya saboda tana tsoron faɗawa a wacan halin na baya. Sai dai ba
tayi nasarar yin hakan ba tun bayan da ta cika idda sai manema suka riƙa fito mata
ciki har da abokan aikinta. Hakan yasa mahaifiyarta matsa mata akan ta yi aurenta
zai fi mata mutuncin fiye da zaman gida domin mace bata da wata daraja idan ba
gidan mijinta take ba, kuma hakan zai taimaka mata gurin da tarbiyar ɗanta, Allah
ta riƙa roƙo akan ya zaɓa mata alherin a cikin manemanta.

AMIRA POV.

Mace ko mai mutuncin ta a yanzu tana wahalar samun miji balle kuma wacce mutane ke
ganin ta riga ta zubar da ƙimarta, abunda ta aikata yafi damunta a yanzu saboda
zantunkan mutane da kuma tsangwa da take samu a duk lokacin da wani ya nuna yana
son ta, daga ya kwana biyu yana zuwa munafukan unguwa zasu labarta masa tsawon
lokacin da tayi ba a gida ba sai mutun ya gudu wasu kuma daga gidansu ake labarta
musu yarinyar ƴar mutunci ba ce dole mutun ya kama gabansa, tun abun baya damunta
har yazo yana ci mata rai, bama kamar idan ta duba duka ƙawayenta sun yi aure ita
kaɗai ce a haka, karatun ma ta kasa komawa saboda damuwa da ta sawa ranta, lokacin
da maganar auren Namra da Abdallah ya same ta tayi kuka sosai har sai da ta raina
kanta, domin har gobe tana son Abdallah. Wani lokacin ta kanji kamar ba zata iya
auren ƙaramin mutun ba, sai dai ganin babu sarki sai Allah yasa ta fara kula Sani
Engineer, wato mai yi ma Mahaifinta gyaran mota a duk lokacin da ta samu matsala,
shi ma kansa ba dan arzikin da yake ganin ubanta na da shi ba da babu abunda zai sa
ya aureta saboda familynsa suna yawan magana akan su basu yarda da ita ba, duk kuwa
da kasancewar ita ce ta uku a cikin matansa.

Duk wani abu da take ji akansa ta kan yi haƙuri ta danne zuciyarta saboda samawa
kanta da kuma iyayenta farinciki, duk da tana jin kamar ba zata samu farincikin da
take so tun da ba sonshi take ba, kuma gashi yana da mata da ƴaƴa taya zata jidaɗin
zama a gidansa, da ta nemi ya kama.mata haya sai ya ce mata bashi da wannan halin
kuma wai shi baya son raba kan iyalansa, a dole tasa Mahaifinta ya kama mata haya,
domin ƙannenta ma an aurar da su sai ita, kusan rabin hidimar auren ma duk
Mahaifinta ne yayi saboda shi ba mai kuɗi ba ne sai rufin asiri duka abunda aka
ɗora masa Mahaifinta ne yake yi saboda ya samu dai ta yi auren.

Assabar aka ɗaura aure bayan anyi ahagulgulan biki kamar yadda ake ma ko wacce
Amarya, duk da ita Amira bata so haka ba Ammy ce ta matsa ayi wai saboda asan ita
ma tana da gata kamar ko wace yarinya, ba kowa ba ne yasan wanene mijinta saboda
ɓoyewa ake wasu kuma indan suka ji ance Engineer sai su ɗauka ko wani babban
Engineer ne.
Ranar da aka ɗaura aure aka kaita gidan mijinta unguwar minannata.

ASIM POV.

Kusan hoto kala biyar ana masa amman result ɗaya yake badawa, jijiyoyinsa na ƙafa
sun murɗe, akan maganin likitoci suka ɗorashi wai ko za a dace amman shiru babu
wani labari, tun da aka kawo shi asibin sau biyu kawai abokansa suka riƙa zuwa suna
dubasa, ko su ba dukansu ba, masu ɗan sauran imani domin basa kula mutun idan baya
da lafiya ganin suke bashi wani amfani, Ubangidansa be taɓa zuwa duba shi ba sai
dai ya turo masa da kuɗi kusan miliyan ɗaya ya siye magani, ganin babu wani canjin
a ciwon nasa yasa suka nemi ya fita waje ko Allah zai sa a dace. India ya fara zuwa
watansa ɗaya a can shi da Amaryarsa amman babu wani canji, bayan sun dawo naija ne
ya sake biyan wasu kuɗin aka fitar da shi ingila nan ma labarin babu wani
banbancin, can kan satinsa biyu kawai yayi ya dawo saboda kuɗinsa sun fara ƙasa
komai na tsada ne a can. Wata asibitin ya canja da suka dawo nigeria, haka yayi ta
kashe kuɗi amman babu wani sauƙi balle ma canji wani lokacin idan abun ya taso masa
sai yaji kamar a cire masa ƙafafunsa gaba ɗaya ya huta. Lokacin da Amaryarsa ta
fara lura da abubuwa sun yi ƙasa sai ta koma gidansu aka bar Mardiya da jinya.

A familynsu babu wani mai arziki sosai da zai iya ɗaukar ɗawainiyar Asim, wani
lokacin ma zuwa su ganshi yana musu wahala musamman yanzu da suka ji shine dalilin
mutuwar mahaifiyarsa sai kowa ya daina tausayinsa, suna cewa shi ya jawa kansa, mai
gidansa ma tun yana ƙoƙarin aiko masa kuɗi yace ya siye magani har ya daina ganin
ɓba sauƙi zai ji ba, kuma bashi da wani a amfani a gareshi yanzu, daman idan suna
sonka to kana amfanarsu ne. Wasa wasa ciwon nan ya jawa Asim hasara da yawa duk
abunda da ya tara sai da ya ƙare be ji sauƙi ba, hakan yasa suka tattara suka koma
gida.

Daga nan ya fara saida filayensa guda biyu da kuma gidansa guda ɗaya da suka rage
masa a rayuwa, ranar da aka kawo masa kuɗin jikinsa ya tsananta sosai har ya bawa
Mardiya tsoro sosai.

“Asim ko asibiti zamu koma ne?”

Kai ya girgiza mata hawaye na masa zirya, ga wani wahalallen numfashi da yake.

“Ni kaɗai nasan irin azabar da nake ji Mardiya, ina zanje da waɗannan kayan?”

Kuka kawai take tana riƙe da hannunsa da yayi mugun zafi, sai shi ma ya kalleta
cikin hawaye.

“Na yi hasara na tsaɓi Allah, yanzu gashi zan koma gareshi ina ƙazami, bana da ɗa
Mardiya balle na samu mai min addu'ah kaico na!”

Ya damƙe hannunta ƙawai zuciyarsa na wani irin fisgarsa har jikinsa sai ya girgiza.

“Makomata tana jirana Mardiya, kwanciyar ƙabari Mardiya, idan Allah ya tambaye
miyasa na aikata luwadi me zan ce masa? Nice silar mutuwar Mama, nine na keta
haddin Allah, Mardiya na cutar da Namra, na yi isgili, na tara kuɗin da Allah zai
tambaye ta ya na samu naira taya na kasheta, na tara kuɗin da basu tare min hisabi
ko azabar ƙabari ba, Allah ya ce kar a kusanci mace ta dubura ni na yi, ina zan je
da waɗannan kayan Mardiya zafi nake ji zafi zafi...”

Ya fara tari muryarsa na sarƙewa, a take baƙin idonsa ya ɓata sai farin akwai akw
gani, halshensa ya karye, tana son ƙara wata magana amman ya ƙasa sai hawaye ke
masa zuba, yana wani irin banƙara yana numfashi daker, zafin fitar rai ya tattara a
jikinsa sai karkawar yake yana kallon sama.
Tashi tayi a gudu ta fita daga ɗakin ta shiga maƙota domin kiran jama'ah a kama
mata ta kaishi Asibiti, tana ganin alamun ya fara fita hayyacinsa.

Kusan mutun shida suka shigo mata huɗu maza biyu domin taimaka mata, sai dai
yanayin yadda suka tararda shi yasa jikinsu mutuwa, idonsa a kafe kansa ya malguɗe
halshensa ya fito.
Dattijiwar cikinsu ce ta duba da kyau tana girgiza kai ta ce.

“Sai haƙuri Mardiya mijinki na amsa kiran mahallincinsa”

Da gudu Mardiya taje tana girgiza gawarsa tana kuka.

“Asim Asim”
Dattijuwar tasa hannu ta shafe masa idonsa tana hawaye kamar yadda kowa ke yi.
Kamar wacce ta haukace haka Mardiya ta koma tana tsalle tana direwa tana kirama
kanta hallaka, da shiga uku.

“Wayyo Allah na shiga uku Asim ya tafi ya bar ni, na bani na lalace wayyo ni Allah
na kaicona ni Mardiya”

Sai da jama'a suka riƙata aka fitar da ita waje. Ba'a masa jana'iza ba sai da ƙanen
mahaifinsa dake sokoto suka iso, misalin huɗu da rabi na yammancin ranar talata aka
sanya Asim a cikin ƙabarinsa bayan an masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya
tanada, a saman ƙabarinsa suka tsaya suna masa addu'ar samun sauƙin karɓa tambayar
mala'iku kamar yadda Annbi ya koyar. Rayuwa kenan Allah kasa muyi ƙyaƙƙyawan
ƙarshen, dukan mai rai dole ya bar duniya😭

NAMRA POV.

Tun da suka je abuja kullun sai ta yi waya da Anty Amarya da Abbah saboda kewarsu,
da gangan Abdool ya hanata zuwa ɗauren auren Yasmin duk da taso zuwa, wai baya son
yawan nan zata wahalar masa da baby, haka ta saka shi a gaba ta yi masa kuka amman
ya ƙi ya barta taje.
Bata zuwa sokoto sai idan zasu yi jarabawa, shi ma dan babu yadda zai yi ne kawai,
aiko tana ƙarewa be sake barin ta leƙo sokoto ba.

Katsinar ma tun aurensu Meesha da Haleema da Fauziya, shi ma dan Ummi ta matsa ne
da yaso ba zata zo ba sai ranar da za'ayi ɗaurin aure su zo tare, Ummi ta tirsashi
ya kawo ta wai zai koya mata ƙin shiga mutane bayan kuma yasan familynsu suna da
yawan hidima.

A falo suke zaune, Namra na saman kujera yayinda shi yake zaune a ƙasa ta ɗora masa
ƙafafunta saman kai suna kallon wani series drama ya ɗauki hankalin Abdool sosai,
saboda criminal case ne ake. Sai dai duk yadda yake son maida hankali gimbiyar ta
hana shi, sai wasa take da kunnensa tana sa kunnensa a babban yatsan ƙafarta ta
matse sai ya ture mata ƙafa ta maida ya sake turewa ta maida, can kuma ta saka
ƙafarta ta dinga zungurar masa kai, duk abunda tayi masa ƙyaleta yake saboda kawai
yana son drama da ake.

“Omri yunwa na ke ji, ka ji? Yunwa na ke ji sosai”

Ya kama ƙafafunta gaba ɗaya ya riƙe yana cigaba da kallon tv.


Be bi ta kanta ba sai da ya gama kallon da yake sannan ya tashi ya zuba mata
abincin da ke kan dinning a plate ya kawo mata ya koma ya ɗauko mata lemu da cup ya
aje a saman tebur ɗin da take gabanta, shi ya riƙa feeding ɗinta har ta ƙoshi
sannan ya miƙe tsaye ya kwashe kayan ya kai kitchen sannan ya dawo ya miƙa mata
hannu ta riƙa hannunsa ta miƙe tsaye.

“Ɗazu Anty ta faɗa min wai Maryam bata da lafiya”

“Allah ya bata lafiya, babu inda zaki je”

Ta taɓe fuska kamar ta fasa kuka.

“Wallahi ni na gaji da zaman nan, kullum guri ɗaya”

“Ke kin fi son kullum kiyi ta yawo baki Katsina baki sokoto, haba Abnam ki riƙa
tausayin abun da yake cikinki mana, kuma nima ki riƙa tausayina kin san ba son nake
kina nisa da ni ba”
“Malam ba wani tausayinku, shikenan sai na kashe kai na ku na raya ku? Haka fa ka
hanani zuwa gaisuwar Hajiya Sadiya ƙiri-ƙiri, kuma yanzu Maryam bata da lafiya ace
ba zan je ba”

“Bari na kira Maryam ɗin naji yadda jikinta yake, kin san ai rashin lafiyarta ba
zai wucw a ce ciki ne ba”

“Ni bance ka kirata ba”

Ta faɗa kamar tayi fushi ɗin nan. Zagayowa yayi ta bayanta ya ɗora hannunsa saman
ƙaton cikinta.

“Idan kin haihu sai kije ki gansu ai, Abnam miyasa baki tausayin kan ki ne wai?
Yanzu baki ganin ko guntun tafiya kika yi yadda ƙafarki yake kumbura balle kuma
babba ace daga nan har sokoto haba Hajiya, a riƙa tausayawa kai mana”

Ta ture masa hannu ta nufi ɗakinta. Binta yayi yana rarraahinta shi kanshi yasan
tayi missing ɗin gidan, sai dai shi baya son ta je ko'ina saboda cikin nan nata
gani yake kamar da ta ɗaga wani abun zai same shi, hakan yasa indai ba aiki yake ba
kullum yana gida saboda yi kula da ita da kuma kama mata wani aikin duk da likita
yace ta riƙa ɗan wala jininta.
Duk ta bi ta motsaye ta tsomaye saboda cikin ya janye ta, Abdool kawai ke ta ƙiba
abunsa hankalinsa kwance bashi da matsala ta ko'ina. Ita kaɗai ke ta fama ɗan chat
ɗin da take tana rage kewa yanzu duk ta tattara ta watsar komai baya mata daɗin a
duniyar nan, cikin ma ji take kamar ta cire shi ta aje. Wani lokacin idan suna fira
da Abdool ta kance ashe haka iyaye suke ji shiyasa ake cewa ƴaƴa suna da haƙƙin
iyaye, haka zata zauna tana masa kuka kamar ƙaramar yarinya, wai cikin ya haye mata
zuciya ko ya taushe mata mara.
Kusan kullum shi yake daba abinci saboda bata cin abincin kowa sai nasa, ko
takeaway yayi musu sai dai ya cinƴe abunsa wai warinsa take ji, ko ita ta girka
abincin bata cinsa sai dai Abdallah yayi mata, da wasa-wasa ya ƙware gurin girki
saboda yau idan yayi mata wannan gobe wacan zai mata.
[8/7, 2:48 PM] Khadeeja Candy♥: Ranar Monday EDD ta ya cika amman bata haihu ba sai
wata assabar a babban asibitin Abuja, murna gurin Abdallah kamar ya soye Namra da
yaron da ta haifa ya cinye dan tsabar jindaɗi da farinciki, Allah ya nuna masa ya
ga jikansa ta ɓangaren Abdallah.
Mai Martaba ma sai ya rasa inda zai sa ransa saboda farinciki, tun a waya yasa
aka turo masa hoton jaririn ta whatsapp. Ƴan uwan Abdallah babu wanda be saka hoton
a instagram ba, a can sokoto ma murna suke, family Abbah da kuma Mai Martaba da
suke Abuja suka ne suka riƙa kula Namra, awarta guɗu a asibiti bayan ta haihu sai
da suka sa ta yi bachi sannan suka sallameta.
Ko da ta dawo gida yamma yayi a dole ta haƙura ta bi jirgin gobe. Tare da family
Abdallah suka sauka sokoto, su sukaje da kansu suka kai Namra har gida, iya gata an
nunawa Namra ta ko wane ɓangare.

An zuba mata kayaɓ barka kamar ba gobe, kayan jariri sai ka ɗauka wani ƙaramin
shago za a buɗe na siyar da kayan jarirai, ga shi ƴan uwa sai kawo mata ake ta
ko'ina.

Ranar suna yaro ya ci sunan Mai Martaba, wato Ahmad, akayi masa laƙani da Sultan.
An kashe naira ranar suna kamar ba a san zafin nemanta ba, duk faɗin gidan sai da
ya cika da jama'a, musamman ma da yamma da ƴan'uwansu Abdallah suka zo da kuma na
Ummi. An ci ana sha kuma an watse cikin farinciki da kwanciyar hankali, kowa sai
yabon bikin yake ana Allah sam barka.

Duk bayan kwana biyu sai Abdool ya zo sokoto ganin ɗansa, kira kan waya kan waya ta
safe daban ta rana daban ta dare ma haka. Kamin ta yi arba'in duk ya takura, kunyar
Anty yasa ya kasa magana har sai da ta ƙara sati biyu sama sannan aka maida ta
Abuja, tare da bayinta guda biyu sabida su taimaka mata hidimar gida.
Komai ya koma musu kamar su suka tsarawa kansu yadda rayuwar zata zo musu, suna
bawa junansu kulawa yadda ya kamata, sai dai wani lokacin tana fuskantar matsala ta
ɓangare Abdallah saboda zafin kishi da yake da shi. Lokuta da dama yakan hanata
zuwa wani gurin ita kaɗai duk kuwa da kasancewar a garin Abuja ne amman ganin yake
kamar wani zai mata magana idan ta fita ba tare da shi ba.

Yau ma duk da tana son fitar dole ta haƙura har sai da yawo, ya ci abincin yayi
wanka sannan ya ɗauki Sultan ita kuma ta riƙa jakarta suka fita, shi yake driving
Sultan na jikinsa rumgume ita kuma tana front seat har suka isa, wani babban
Shopping.
Tana gaba yana biye haka suka shiga shopping ɗin. Yana riƙe da Sultan har ta siye
abunda duk zata siya aka zo gurin biyan kuɗi ya bada atm ɗinsa aka cire adaɗin
kuɗin da ta kashe, sannan suka koma cikin motar ya ɗauki hanyar gidansu Hajiya
Umaima, wato Ƙanwar Mai Martaba wacce take nan Abuja.

Ta tarbesu da far'ah daman ta jima tana masa magana akan ya kawo mata Namra. Hannu
ta kai ta karɓi Sultan da ke hannun Abdool tana faɗin

“Ai har na yi fushi na ce ba zan sake maka magana ba”

“Ko yanzu ai nice na matsa”

“No.wonder ni nasan sai ƴata”

“Haba Hajiya taya zaki biyeta ni nace ta shirya mu zo fa”

Hajiya Umaimai tayi dariya.

“Duk abunda zaka faɗa ba zan yarda ba. Mardiya kawo lemu kamin abinci ya ƙarasa”

Ta ƙarasa tana ƙwalawa mai aikinta kira, ba a ɗauki tsawon lokaci ba sai ga Mardiya
ta fito daga kitchen ɗauke da drinks da cups. Gabanta ya faɗi lokacin da tayi arba
da Namra, ita kanta Namra tayi mamakin ganinta sai dai daga ita ha4 Mardiyar babu
wanda ya iya yima wani magana, har sai da ta wuce sannan Namra ta kalli Hajiya
Umaima ta ce

“Hajiya ina kika san Mardiya?”

“Wallahi daga Katsina aka kawo ta, na ce a nemo min wace zata riƙa taya ni aiki ne
sai aka kawo min ita, kin santa ne?”

“Eh a Katsina take shiyasa na yi mamaki ganinta nan”

“Aiki ta zo yau satinta biyu ma”

“Allah sarki”

Umaima ta miƙawa Namra Sultan.

“Bari na duba abincin nan, kar na shiga muku da yaro Kitchen”

Abdool yayi dariya

“Wai ina su Jamila ne?”

“Wlh duk sunje biki kasan halin ƙanen naka sai a hankali idan kunnensu ya ji biki,
ba manyan ba ba yara ba”
Hajiya Umaima na shiga Kitchen sai Namra ta miƙe tsaye ta miƙawa Abdool Sultan ta
nufi ɗakin da ta hango Mardiya ta shiga. Da sallama ta shiga, amman Mardiya bata
iya amsa mata ba saboda bata son ta gano kuka, gyaran ɗakin ta tarar tana yi. Har
Namra ta juya zata fita sai Mardiya ta juyo ta ce.

“Namra Asim ya mutu, Asim ya koma ga Ubangijinsa”

Namra ta juyo tana zaro ido.

“Yaushe? Miya same shi?”

“Rashin lafiyar da ta kama shi a faɗar Sarkin Katsina bata barsa ba sai da ta tafi
da ransa”

“Innalillahi wa'inna ilaihi”

Ta faɗa tana dafe kanta hawaye na zubar mata. Mardiya ta risina ƙasa tana kuka.

“Namra ki taimaki Asim ki taimake ni ki yafe mana, amanarki da na ci ta hanani


sukuni, duk wanɗanda na yi ma zalumcin na nemi yafiyarsu ke kaɗai kika rage min, na
tsorata da irin mutuwar da Asim yayi, bana son na yi irin mutuwarsa”

Namra ta duƙo dai-dai Mardiya tana dafata.

“Miya samu Asim?”

Babu abunda ta ɓoye mata daga rayuwar Asim daga rashin lafiyarsa da kuma mutuwarsa
zuwa irin rayuwar luwaɗin da tasan yana yi, ga kuma saduwar da yake yi da ita ta
baya.

“Bayan mun gama wanka aka raba mana gadon kuɗin da ya bari na gida da filayen da ya
siyar, a take nawa kuɗin suka ƙare gidan da na siya kuma ya ƙone, ga rashin lafiyar
da take jikina saboda saduwar da yake yi da Ni ta baya, a duk lokacin da wannan
ƙaiƙayin ya taso min sai na ji kamar zan mutu, na kasa daina mafarkin wuta Namra,
ada ina tunanin ko wutar da na kunna miki ce gidanki ya ƙone, amman sai nake ganin
kamar har da wutar lahira ce take jirana, ki taimake ni ki yafe min Namra, na ci
amanarki, na han'ince ki, na cutarda ke”

Wani kuka take marar murya saboda bata son Hajiya Umaima ta ji.

“Na yafe miki Mardiya shi ma Asim na yafe masa, Allah ya masa rahama”

Ta miƙe tsaye tana hawaye.

“Ki rufa min asiri karki faɗawa kowa sirrin, yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa
na bar Katsina na dawo nan ga aiki saboda na canjawa kai na rayuwa, kuma na rufawa
kai na asiri da abunda zan ci, na taimaki uwata da ƙannena”

“Babu wanda zai ji, na miki alƙawari ba zan taɓa faɗawa kowa ba”

Sai da ta share hawayen sannan ta fice. Sai dai hakan be hana Abdool gane ta yi
kuka ba. Tana zaunawa kusa da shi ya kalleta ya ce

“Kin yi kuka saboda kinji Asim ya rasu ko?”

Da sauri ta kalleshi.

“Ka sani kenan?”


“Abnam har gobe kina son Asim”

“No ba haka ba ne, kawai ina tausayinsa ne”

“Tausayi ne silar so”

“Ba irin wacan tausayin ba”

Ya miƙe tsaye tare da ɗansa, ya ɗauki car keys ɗinsa ya fice. Tana zaune a gurin ta
ji tashin motarsa. Lumshe ido ta yi ta buɗe sannan ta ɗago tana amsa maganar da
Hajiya Umaima ke mata.

“Lafiya Babangida ya tafi?”

“Wai zai ga wani abokinsa ne, yace idan an ɗan jima kisa direba ya kai ni”

“Okay toh taso muje ɗaki ga abincin nan Mardiya zata kawo yau mun ranar girki”

“Wallahi Hajiya na ci abinci”

“Ai nasan kin ci abincin, karki so ma min musu ba tarbiya ba ce”

Da murmushi Namra ta tashi ta bita suka shiga ɗaki. Kamin ta gama cin abinci ayi
sallah la'asar har ta tsawwala saboda tunanin Abdool yana can gida cikin ɓacin rai.
Tana gama sallah la'asar ta yi ma Hajiya Umaima magana tasa ka direba ya kai ta
gida. Bata same shi a falo ba, hakan tasa ta nufi ɗakinsa, kwance ta hango shi
saman gado, Sultan na saman ƙirjinsa idonsa a lumshe kamar mai bachi.

Tasan ba bachi yake ba, domin be saba bachin yamma ba, sai dai wannan baya rasa
nasaba da ɓacin ran da take tunanin ya sawa kansa akan abunda har ga Allah ba haka
yake ba. Be buɗe ido ba har ta ƙarasa kusa da shi ta zauna saman gado.

“Ya Omri...”

“Abnam please, bana son na fara ganin laifinki, bana son zuciyata na ƙonuwa akan ki
ina gudun na fara ganin baƙinki, dan Allah ki fita sai zuwa anjima”

Ya faɗa ba tare da ya buɗe idonsa ba. Kwantawa tayi a gurin, sai ya buɗe ido ya
kwantar da Sultan gefensa na dama ya juya mata baya. Hakan ya bata damar matseshi
sosai ta kurɗo hannunta ta ƙasan haɓarsa ta ɗora shi dai-dai zuciyarsa.

“Namra tana nan Ya Omri kuma tana nan a bayan ka, tun bayan abunda Asim yayi min
sai na daina ganin maza a mutane ina musu kallon wani abu daban, amman daga lokacin
da na ganka sai na ganka a mutun cikakkensa, kai ne mutumen da ya tsayar da zubar
hawaye a lokacin da nake tunanin hawaye ba zasu taɓa tsayawa ba, kai nw ka dawo min
da farinciki na da kuma na iyayena, Wallahi na rantse maka da Allah babu son kowa a
zuciyata sai kai, ka shiga ka mamaye ko ina na zuciyata, ban taɓa mafarkin samu
miji irinka ba, saboda ina tunanin kamar ba ayi ni dan jindaɗin rayuwar aure ba.
Sai dai bana ganin laifin zuciyar mai Imani idan har taji tausayin rai da zata koma
ga Allah yana kirawa kansa hallaka, irin wannan tausayin na ke ma Asim ba irin
wancan wanda kai kake tunani ba”

A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya kai hannunsa ya shafa hannunta da ke ƙirjinsa.

“Kinji bugun zuciyata...! Duk ranar da kika so wani ba ni ba mutuwa zan yi Abnam
don't ever try it”

“Ina son ka mijina, ina son ka sosai”


Juyowa yayi ya rumgumeta yana sumbartar goshinta, lafewa tayi a ƙirjinsa, hannunta
yana gurin kunnenta tana wasa da shi, ɗayan kuma yana cikin yatsunsa.

Basu tashi daga gurin ba sai da aka kira sallah magariba, shi ya fara tashi yayi
alwala sannan ya dawo gurin gadon ya sumbance ta ya sumbaci Sultan.

“Tashi ki yi sallah magariba ta yi”

Sai da ya fice sannan ta miƙe tsaye ta shiga banɗaki. Be dawo gidan ba sai da aka
yi sallah isha'i, ko da ya shigo ita ta gama nata sallah ta shirya cikin wani
shegen riga da ɗan guntun wando, ta kama kalabar kanta ta yi masa tukkuwa wato tayi
parking ɗinsa guri ɗaya. Ko da ya shigo tana tsaye gurin dinning tana haɗa ma
Sultan madara.

“Wow”

Ya faɗa sannan ya ƙarasa kusa da ita ya zagaye kwankwansonta da hannayensa yasa


halshensa yana wasa da kunenta.

“Ba zaki daina bawa yaron nan madara ba ko?”

“Ya cika ci da yawa idan ba a bashi madara ba zai riƙa tsutse ni ne”

Ya juyo ta ita ya ɗagata ya ɗora saman dinning ɗin.

“Ke baki cin abinci ko?”

Ta matso da fuskarta har hancinta na gugar nasa.

“Ni abincin mutane nake ci”

Ɗayan hannunsa tasa ya ɗauke ta cak ya nufi ɗaki da ita.

“Shi kuma yaro na abincin aljanu yake ci?”

Tasa masa dariya hannayenta lanƙame da wuyansa. Ko da wasa Namra bata yarda ta
tayarda firar Asim a gaban Abdallah ko da kuwa muagunarwar da yayi mata ne zata
faɗa gudun kar ya ce ta tuna da su, yadda yake nuna mata kishi akan Asim baya nuna
mata haka akan Lamido, wata ƙila saboda Abbah ya rigaya haɗa auren Lamido da Aisha
ne, ko kuma dan yana ganin shi Asim ya taɓa aurenta ne.

Tayi zaton idan zata je bikin auren Aisha sai ya saka mata dokoki kamar yadda
yake mata a duk lokacin da yasan zata je bikin da zata haɗu da wasu mazan ko da
kuwa ƴan uwanta ne ko nashi, ko mata ne wani lokacin ya kan cilasta mata rufe
jikinta wai hakan ne mutuncinsa da na gidansu da kuma nata, sai ya ɗora mata da
cewar baya son tana sakin jikinta ko da kuwa cikin mata ne ƴan uwanta domin a yanzu
akwai ɓata gari, wanɗanda siffarki kawai zasu gani sheidan ya ƙawata musu
sha'awarki.

Ciki farinciki da annashuwa aka yi bikin Aisha da Lamido, ranar Assabar aka ɗaura
aurenta kuma ranar aka kai amarya, a unguwar sama road dake cikin sokoto, a lokacin
Sultan na da shekara ɗaya da wata takwas, Namra kuma na ɗauke da wani cikin duk da
bata haye Sultan ba saboda Abdool ya hana wai zai cutu.
Duk wanda ya ga Sultan baya buƙatar tambayar ɗan waye ne, domin kamaninsa ɗaya da
Abdool kai baka ce ma Namra uwarsa ba ce kasancewarta black beauty Sultan kuma fari
tas kamar ɗan larabawa.

Family Lamido da kuma na Namra yanzu an koma kamar ƴan'uwa, tun da har auratayya
ya shiga ciki, sai dai duk da haka Abdool be taba barin Namra taje Kaduna da sunan
gaishe da Neine ba, wai ai zata iya haɗuwa da Lamido tun da yana yawan zuwa akai
akai. sai Neine da Uwani sun je Abuja lokacin da ta haifi ƴarta ta biyu wato
Fatima, daman suna son zuwa yi mata godiya, ta jidaɗin ziyarar haka ta haɗa musu
goma ta arziki lokacin da zasu tafi, har tana waƙen sai ta zo Kaduna idan tayi
arba'in duk da tasan Abdool ba zai barta ba.

Wasa-wasa Namra ta zama uwar mata domin bayan ta haifi Fatima sai ta ƙara haifo
Juwuriyya da Mai sunan Ummi wato Zuwaira, wacce ake kira da Nasrin, sai kuma mai
sunan Anty Amarya da ake kira da Iman, sai a haihuwarta ta shida ta haifi Muhammad
Kabir. Ko da wasa ta dake su Abdallah rufe ta yake da faɗa wai bata san zafin
haihuwa ba tana cin amanar ƴaƴansa, duk wani horo da zata musu sai idan baya cikin
gidan, domin ji yake yi da abunsa wai ita zata iya gudunsa amman ƴaransa ba zasu
guje shi ba, ita kanta yana nuna mata kulawa yadda yake treating ɗinta ba zaka
ɗauka ita ce ta zuba masa waɗannan yaran ba, sai idan ka gansu. Babu ruwansa da ta
haifi yara da yawa kullum kamar amarya take a gunsa, ita kuma tana kula da jikinta
sosai da duk wani abu da tasan mijinta na so.

ALHAMDULILLAH.
Godiya ta tabbata ga Ubangijin da ya bani ikon fara rubuta littafin nan, kuma na
kammala. Ina roƙon Allah ya yafe min kuraranda na yi akan ganganci ko rashin sani.

Zan yi amfanin da wannan damar na roƙi yafiyar duk wanda na ɓatawa a cikin rashin
sani ko da gangan, mai rai ajizine, masu cewa littafin nan yayi tsawo dole zai zo a
haka kasancewar labarin ya kasu gida uku ne, kuma dukan abunda yayi farko zai yi
ƙarshe.

Ku yi haƙuri da yadda labarin ya zo muku, fatana dai a ɗauki darasin da ke a ciki,


kuma a guji mugun hali ko ɗabi'ar da ba ta ƙwarai ba. Allah ka ɗora mu a dai-dai ka
bamu ikon bin gaskiya da tsareta, ka tsaremu daga mugun ji da mugun gani da tsaka
mai wuyar sani da aikin inda na sani...

SON SO FISABILILLAHI, godiya ta musamman ga Zagon Ƙasa paid group 1 and 2, da male
abroadcast. Sai mun hadu a littafina na gaba *HAFSATU MANGA* _Yarinyar ƙauye_ I
😍😘❤💜🌷✨

LOVE YOU ALL ♥️

Zan yi missing ɗin ku 😭😭😭

You might also like

pFad - Phonifier reborn

Pfad - The Proxy pFad of © 2024 Garber Painting. All rights reserved.

Note: This service is not intended for secure transactions such as banking, social media, email, or purchasing. Use at your own risk. We assume no liability whatsoever for broken pages.


Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy