Mummunan Zato Book 1
Mummunan Zato Book 1
Mummunan Zato Book 1
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 1*
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number
09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
Ya shigo gidan cike da fara'a yana faɗin "ina Umman yaran gidan nan ne?" Daga ciki
ta amsa da cewa "gani Abbansu" ya iso cikin kitchen ɗin, tsaye take tana haɗa lemun
soɓarodo yayin da A'isha ke jera ƙwanuka domin raba abinci, tace sannu Abba, yace
yauwa ƙawallin Ummanta,ya dubi Umma "ina da babban baƙo fa" ita ma ta dube shi
cikin kulawa"daga ina?"
Ya fadada murmushin sa "zakiyi mamaki idan nace miki Alhaji Sadiq Usman kt ne"
cikin mamaki take dariya " lallai munada babban bako yau kam zanga wannan Alhaji
Sadiq naka" ya juya tare da cewa " muna falo na" tace "to".
Ta amshi rabon abincin daga hannun Aisha tace "kawo nan in zuba musu,ki kai musu
abin sanyaya makoshi,kafin na zuba masu abinci ko? Aisha tace "to Umma" nan ta
shiga hada kaya kan tire,lemun zobo ne mai dan karen sanyi tare da ruwan leda shima
mai sanyi guda hudu sai kofuna guda biyu.
Tayi sallama falon Abba,inda suka kaure da hirar yaushe gamo? Suka amsa mata cike
da fara'a ta shiga kan tebur ta daura tiren sannan ta dan jaa teburin zuwa
gabansu,durkusawa tayi gwuiwa biyu a kasa tana zuba musu zobon cikin kofuna tana ce
da bakon " Uncle ina wuni?"
Ya dube ta " lafiya lau yar Uncle "gabanshi ya yi wani mugun faduwa ya daure yace
"yaya karatu?"
Tace "Alhmdllh, yaya hanya?" Yace "lafiya lau hanya,me sunan ki? Ta mike ta mika
musu zobon sannan tace " sunana Aisha".
Ya dubi Abba yace " yanzu ya'yan ka nawa Mustapha?" Abba cikin fara'a yace "su hudu
ne" Aisha fita sannan ta dawo ta kawo masu abinci Ummanta tana biye da ita cikin
fara'a suka shigo ta gaisa da Alhaji Sadik Usman dan mutan KT,ta zauna tana zuba
musu abincin tana cewa "yau dai naga Alhaji Sadiq KT" Alhaji Sadiq ya dubi Abba
yace " Friend kace kaima ko yaushe kana labari na?"
"Sosai ma" inji Abba ya cigaba da cewa "ai kai ba abokin da za a manta dashi bane"
Sukayi dariya.
___________
Kwance a masaukin baki na sukuni (Guest House) da ke nan cikin Dutse,Alhaji Sadiq
ne zurfi ya yi cikin tunani,ko shakka ba ya yi Aisha yar abokinshi Mustapha ita ce
yarinyar da duk sanda ya yi Istihara yake gani cikin mafarkinsa,kuma ita ce Malam
Mamuda ya kwatanta masa cewar ita ce uwar ya'yansa.
Sai yanzu ya tuna wata tattaunawa da suka yi da Malam Mamuda ya sanar da shi cewa
yarinyar da zata haihu da shi tana wani gari ne mai nisa da Katsina,kuma a cikin
Istiharar ta shi yana zaton akwai matsaloli can kasa cikin al'amuran,ya sani
matsalolin ba za su wuce na kaddarar da ke faruwa kan duk matar da ya aura ba,ya
sani ba kowa zai yarda ya ba shi auren yarsa ba matsawar yasan wane ne Alhaji Sadiq
K.T.
Mikewa ya yi yana kai komo cikin masaukin nashi,ko dai ya sanar da aminin nashi
matsalarshi? To in ya gaya mishi anya zai yarda ya ba shi auren yarsa Aisha? Me zai
yi yanzu? Alwala ya yi cikin toilet ya fito ya cire kayan barcin shi ya maida
jallabiya ya tada kabbara zabin Ubangiji ya shiga nema tare da addu'ar Allah ya
kawo mishi mafita cikin lamuranshi,cikin barcinshi yake ganin yarinyar zaune tare
da wasu yan yara guda biyu masu kyau da kuma kama da shi.
Da safe ya fito cikin yadin boyel fari tas,ya murza hula kube fari ya fi yawa jikin
hular,takalmanshi sawu ciki ne suma farare kamshin sa tun fil'azal ya na tashi.
Alhaji Sadiq kyakkyawan Bakatsine ne,dogo mai cikar zati yana da kyau,tare da
kwarjini,wankan tarwada ne fatar shi kurum in ka kalla ka san cewa ta goge da
hutu,kamshinsa kawai zakaji ka san ya kama kasa,gidan Friend din ya nufa wanda ba
ya da nisa daga masallacin dake bakin titi wato kan layin in an fito.
Aisha ce sanye da dogon hijabi ya fasa shiga layin ya tsaya,ya sauke gilashin
motar,ya leko "ina za ki je ne Aisha?" Ta dubi gurin motar,ta dan saki fara'a.
"Ina Abbanki?"
"Ba nisa Uncle,kuma gurin lungu ne mota bata shiga sai dai mashin."
"Eh amshi nawa."ta amsa sannan ta ce "nagode" ya ja mota ya tafi.Tafiya take amma
ranta cike da tunanin kyautar da ya yi musu ta jiya,dubu hamsin ya basu wai a sai
musu sweet bai samu ya yi masu tsaraba ba.Kai gaskiya Uncle yana da kirki,ya burge
ta musamman ma da ta ji taimakon da ya yi ma Abbansu,Allah ya ba shi haihuwa,ta
kula burin shi kenan,in ta yi la'akari da yanda ya yi ta nuna sha'awar su.
Ya fito da mashin don zuwa masaukin Friend din nashi sai kuma ya hango motarshi
tana shigowa cike da fara'a suka tari juna.Tafawa suka soma yi tare da kiran
juna,Friend kamar yanda suke yi zamanin suna B.U.K "ina zaka da?" "Gurin ka na
nufa" "da kaje ma sai dai mu dawo don kunu nake son sha,sukayi dariya sannan suka
nufi cikin gidan,kunnun tsamiya Umma ta yi da kosai,ya ci sosai ya ce "kai na dade
rabona da na ci wani abu kamar yau. Ina son wadannan abubuwan amma ba na samu"
"Ban gane ba ka samu ba iyalinka ba za ta yi maka ba?" Dan tsaki ya yi sannan yace
"kasan matanmu mace tana ganin kana da hali shi kenan sai ta kwanta wani kato dole
za ka dauka yana muku girki kana biyan shi"
"Allah ya kyauta " inji Abba "amin dai" Abba yace "Yauwa inason in tambaye ka,shin
ka taba neman taimako daga Malamanmu na addini domin samun haihuwa? Sannan me
likitar suka ce kan matar ka?" Alhaji Sadiq ya gyara zama ya sani yana da abokai
da yawa,amma ko da wasa bai hada su da Mustapha ba,dan shi yana da amana tare da
zurfin tunani,in ya baka shawara za ya yi wuya kaga rashin fa'idar abin.Tuno hakan
yasa shi sanar wa abokin nashi abinda ke ranshi game da matsalarshi,ya dube shi
friend ka san wata matsala? Abin ala'ajabi duk inda muka yi yawon ganin likita sai
ace Jummai ba za ta haihu ba,saboda ta yi amfani da kwayoyin hana daukar ciki kuma
sun lalata mata mahaifa su ko Egypt da muka je cewa sukayi an taba mahaifarta ne
sakamakon cire ciki da ta yi.Abin ya bani mamaki sosai,amma ta musa min,kuka sosai
ta yi tare da ce min sun mata sharri ne ban da tacewa tunda yar'uwata ce dole ne na
rufa mata asiri.
Yayi dan guntun murmushi irin na damuwa din nan,sannan ya ce " Abokin Alhajinmu ya
ba ni auran yarshi Murja,karamar yarinya mai kyau da kyan hali,aka yi bikinmu,amma
cikin rashin sa'a a ranar da ta cika sati biyu ta ce ga garinku nan? Tana sallar
asubahi ya ci gaba,ranar da ta cika kwana arba'in da mutuwa aka daura min da
kanwarta,abin al'ajabi kwanan ta goma ta ce ga garinku nan,cike da zargin wani abu
Abba yace " ba a gwada ta aka san mene ne musababbin mutuwar ta ba?" "Likitoci sun
gwada ba wata guba ko duka ko irin toshe numfashi din nan sam,bayan yan watanni
bayan rasuwar ta na hadu da wata yarinyar layin su Hajiyarmu,Jamila ta dawo
Islamiya na tsaida ita,dabi'unta da yanayin maganar ta sun sata shiga raina,ta nuna
min gidansu zuwana uku manya suka shiga maganar saboda an san juna tsakanin gidanmu
da na su,Hajiya Jummai matata itace ta hada min akwatuna matsayin gudunmawarta,don
itama tana son ta ganni da dan kaina kamar yanda kullum take min korafi.
Ranar dana cika kwana bakwai na bar dakinta,ran kwana tara na dawo mata.Ina cikin
yin auratayya da ita sai na ji yarinya bata motsi sai na tsaya na dubata,abin
al'ajabi sai gawa."
Ya yi shiru,sannan ya furzar da wani huci mai zafi saboda tuno tashin hankalin da
ya shiga ranar,ya dafa Abba sannan ya ce, "wallahi Mustapha ba zan iya shaida maka
tashin hankalin da na shiga ranar ba" Abba cike da mamaki yace "ikon Allah,ba ka
samu malamai ba don taya ka addu'a? Duk da cewa mutuwa ta Allah ce".
Wata rana na je Kaduna don siyan wasu injina da banki ya yi gwanjonsu,saboda bashin
da yake bin wani kamfani.
Mun fito cikin kamfanin inda na dudduba injinan,wata yarinya na gani yar siririya
ta min yanayi da yarinyar da Malam Mamuda ya ce min zata haihu min take na ce ke
mai gyada kawo,wadanda muke tare sun sha mamaki ganinsu mutum kamar Alhaji Sadiq
K.T ya sha karfin wannan gyadar,nace "gyadar ta nawa ce?" Ta ce "dari uku" na bata
dari biyar,"je ki bawa almajirai sadaka,ta ce "to ba canji" na ce "ina ne gidanku
in ba nisa je ki samo" ta ce "Badikko ne" na ce jeki na bar miki.
Bayan munyi sallama da Manajan Bankin duk da ya so mu tattauna sai na sallame shi
na ce mishi nan zan kwana,gobe zan zo mu tattauna.Injina sun min,don haka inaso sai
gobe zan zo na shiga mota na ce da direba mu bi yarinyar nan,ya ce "Yallabai ban
san in da ta yi ba ,na nuna mishi wani titi nan naga ta bi,mu bi mu na kan titin
Ahmadu Bello way ne,ita kuma ta bi titin da zai kai ta gidan Gwamnatin Kaduna ne.
Muna bi kuwa sai ga ta can ta yi nisa, kadan-kadan muke bin ta har muka ga gidan
su,ba tare da bata lokaci ba nasaka direbana ya yi sallama da Maigidan,na gabatar
da kaina matsayin mai son 'yarsu kuma na yi musu bayanin daga inda nake.
Ban samu matsala ba,cikin wata biyu suka bani auren yarinyar,abinda ya tsaya min a
rai shi ne,yarinyar ba ta sona sam,sai ina ganin zata so ni nan ba da jimawa ba,da
zaran ta haihu.Yarinyar nan kwananta tara itama ta rasu.
######
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 2*
*Page 2*
Hamshaƙiyar mace ce mai son hutu, tana da masifa tare da raini ga talaka amma game
da zamantakewata da ita tana min biyayya. Mun shafe ku san shekara Bayan rasuwa
Hafsat,wata rana naje Zariya sai na yi shawara na ƙarasa Kaduna in gaida Iyayen
Hafsat, domin duk matan da na aura ban yada iyayensu ba, duk sanda muka fitar da
zakka ina aika musu, haka nan Azumi ko sallah.
Cikin yardar Ubangiji na gaishe su tare da musu ihsani,sai na ɗauko hanyar tafiya
daidai shataletalen Bankin Habib nan Shehu Musa Ƴar'adua House, tsautsayi kurum ban
san ya ya aka yi ba kurum na buge wata yarinya,tana ɗauke da tiren ƙwai duk da ba
taji ciwo ba,sai da na kai ta asibitin Fotifo don su dubata, sannan na kai ta
gidansu da ke Abakwa.
Wannan ne silar auren Amina itama sai ta bi ƴan'uwanta,kai wannan yasa nima na san
babu lafiya,mata shida? Jummai kam kuka take tana ƙara wa tana faɗin wannan sai
wani ya ce da sa hannun ta,na ce babu saka hannun ki Jummai ba ke ki ke halitta ba,
kuma ba zaki iya kashewa ba so kada ma ki saka ma ranki wannan."
Ya dubi Abba "My Friend ka san wani abu?" Abba da tsananin al'ajabi ya hana shi
magana ya ce "ina jin ka sai ka faɗa". "wallahi sai da nayi aure tara ban da Jummai
fa, kuma ban taɓa maida wata ɗakin wata ba,sai dai itama na bata wani ɗakin. Ta
taran ma an kai ta kamar yau, washegari ta yi sallar Asubahi ta koma ta ɗan kwanta
ashe ƙwanciyar kenan.Tun sannan na haƙura domin sai na ke ganin kamar ni ne ma ke
kashe su,ji nake kamar sun rataya a wuyana. Ranar na je gaida Malam Mamuda ya ba ni
addu'o'i tare da nafilfili sannan ya bani Istihara na je na yi da kaina tunda na
soma Istihara ɗin nan wata yarinya na ke gani yawa yawan mafarkan da nake yi na kan
ganta da yara,na kan ce to ni dai na haƙura ba zan kuma taƙalo wani aure ba.
Alhaji Sadiƙ ya ce "na ji daɗi sosai Friend Allah ya ja mana gaba,sai dai ka san
irin gurin Malaman da za ka gurin su saboda aƙwai masu kauce hanya" Abba ya ce
"kada ka damu ni kaina bana ra'ayin su" Alhaji Sadiƙ ya ce "dama kuma ina son maka
albishir da cewa in har mun gama daidaitawa kan maganar kamfanin da na yi maka
maganar shi a Jigawa, zan damƙa kula da gyaran shi a hannunka, sannan in an kammala
gyaran ina mai farin cikin shaida maka insha Allahu kaine za ka zama Manajan
kamfanin"kallon shi kurum Abba ke yi ya ma rasa me zai ce, Alhaji Sadiƙ ya yi
murmushi ya tuno sanda suke makaranta duk in kaga ya yi shiru yana mishi irin
wannan kallon to ya yi mishi alkhairi,don haka ya dafa shi tare da faɗin"a'a Friend
kada ka ji komai" Abba ya miƙe tare da tuno baya.wannan kalmar Sadiƙ ke furtawa in
yaga yayi shiru ya kasa godiya sai ya ce dole inji komai Friend sai yaushe ne ni
zan taimaka maka? Haka shi kuma kan ce lokacin yana zuwa,sai kuma suka saka dariya,
tare da tafawa saboda sun tuno baya, sannan Abba ya ce"nagode Friend, Allah ya
shige mana gaba, kuma kaima Allah ya cika burin zuciyarka," "amin" inji Alhaji
Sadiƙ.
A gajiye ya fito daga cikin motar,yana saka ƙafa cikin falon Hajiya Jummai tana
isowa gurin, rungume shi ta yi tare da faɗin "Oyoyo Abubakar Sadiƙ ɗin a" shima
matseta ya yi a jikinshi yana shaƙar daddaɗan ƙamshin ta.
Cikin jin daɗi ta ce, "har ka kai ni?" Ya kalli manyan idanunta "Na ma fiki,yau fa
kwanana huɗu a Jigawa" tace "to zamu gani anjima" ya shafi wani sashe na jikinta
tare da faɗin "kin min tanadi kenan? Ta ja shi ciki "kai dai muje ka yi wanka ka
cika tunbinka, daga nan sauran labari ya biyo baya" Suna cin abinci ne yake bata
labarin nemo abokinshi da ya yi, ta washe baki "kai na yi murna, yaushe ne za ka
koma? Nima da na bika mun saba da Iyalinshi,ya ji daɗi don ba zata za ta mishi
maganar da mahimmanci ba,don haka sai ya ce, "kada ki damu,ai tunda Allah yasa
yanzun mun gano juna, mutuwa ce kurum zata raba mu.Shi yasa ma kamfanin da na je
maganar shi, Allah ya yi mun daidaita ranar Monday zan tura musu kuɗin su, shi na
ba kwangilar gyara kamfanin tare da ɗora shi Manaja in komai ya kammala. Nan take
yaga fuskar ta ta sauya, sannan ta ce " ba fa a yiwa ɗan adam saurin yarda,yanda
mutanen duniya suka lalace da son kuɗi"
Ya aje cokalin hannun shi Sannan ya dube ina zaton na jima ina miki bayani halayen
dattako tare da riƙe amanar da Friend ya ke da shi kar ki ji komai." Ta yatsina
baki bata kuma magana ba,shi ko miƙewa ya yi don ya shiga ɗakinshi,ya warware
gajiya. Yana shiga wayar shi ta soma tsuwwa,ya duba. Murmushi ya yi tare da ɗaga
wayar.
"Friend na iso har na yi wanka, kuma na ci abinci yanzu ma ƙwanciya zan yi" a can
Abba ya ce" to Alhamdulillah,na barka lafiya ka huta."
Umma ta dubeshi "Abban yara mene ne abin damuwa kan wannan? Ai abin murna ne sai
muyi ma Allah godiya." Ya ce"haka ne Umman yara,ina tunanin amana ne,kin san amana
tana da wahala,sai dai Allah ya taya mu riƙo" ta ce"Amin".
Zaune ya ke gaban Malam Dari,ya koro ma Malam Dari bayani kan matsalar abokin
nashi,shi kan shi Malam Dari ya jinjina matsalar, sannan ya ce zai yi wasu bincike
a kai, bayan ya tambayi sunan abokin Abba,ya ce mishi Alhaji Sadiƙ Usman,Malam Dari
ya ce ka bani zuwa gobe ko dai ma jibi ka zo kaji batu,,ya miƙe bayan ya ajiye
mishi dubu ɗaya, tare da faɗin "Ga sadaka" Malam Dari ya ce "to Allah ya karɓa,kuma
ya shige mana gaba."sai na ganka" "to" inji Abba "sai na zo ɗin kenan."
___________________________
Ya yi parking a harabar gidan mahaifan nasa,ya fito ɗaukacin masu hidima a gidan
suna ta isowa don gaishe shi,shi kuma ya shiga amsa musu ya shiga yi musu ihsani,
kamar yadda ya saba, duk sanda ya zo, sannan kai tsaye ya nufi falon Hajiyar mu.
A zaune ya same ta kan kujera.Dirariya mace mai kyaun haiba, tare da taƙawa.tana da
son addini,kana ganin ta ka san itace mahaifiyar Saddiƙ, tana taimako musamman
asibitoci zuwa masallatai, cike da fara'a ya shiga ya zauna gabanta ita da shi suna
yiwa juna kara nauyin shi kasancewar shi ɗan fari shi kuma bai shaƙu da ita ba,shi
yasa ya ke jin nauyin ta, yanda ya zauna gabanta da ace akwai mutane a gurin tashi
zatayi.
Ta amsa da "lafiya lau, ashe ka dawo?" Ya ce"eh,na dawo jiya ban samu shigowa in
duba ku jiyan ba, dafatan za ku min afuwa?" Ta dube sannan ta kauda kai, tunda dai
an iso lafiya Alhamdulillah,ina kuma fatan tafiyar ta yi nasara?
Ya yi murmushi.
"Nasarori ma kuwa, domin bayan nasarar sayan kamfanin na haɗu da Aminina Mustapha
Gumel, wanda ko yaushe ya ke raina." Ta dube shi tare da faɗin"ikon Allah! Lallai
tafiya ta yi nasara, domin ba ta manta yanda koyaushe yake ɗalibta da batun
Mustapha Gumel. Ya ce"Alhajinmu yana nan?" Ta kalli gefen ɗakinshi, "yana ciki amma
yanzun zai fito."
Ya yi murmushi.
Alhajinmu ya ce"ai ni na ƙosa ta ƙarasa karatun nan,na fi son auren ta." Sadiƙ Ya
ce"insha Allahu zata yi Alhajinmu." dube shi "Dama na jima ina zargin kai ke ɗaure
mata gindin ƙin auren nan ko?" Ya yi ƴar dariya , "ba haka ba ne Alhajinmu, Allah
za ta yi ka san shi aure lokaci ne, kuma insha Allah kwanan nan zata yi" Ya miƙa ta
Saddiƙ ni zan fita zuwa ofis, da akwai masu jirana." Cikin tausayawa Alhaji Saddik
ya dubi tsohon nasa, sannan ya ce"ya kamata Alhajinmu ka zauna ka huta da zuwa ofis
ɗin nan tunda ina kula da kusan duk harkokin ka,na fi son ka huta."
Cikin jin daɗi Alhajinmu ya ce "kada ka damu Saddiƙ,nima ina jin tausayinka ne
abubuwa sun maka yawa,ni dai roƙona ga Ubangiji koda yaushe bai wuce Allah ya baka
mai rama maka, inason naga zuri'arka."
Zan can Alhajinmu ya taɓa shi,don haka shima sai ya yi shiru yana jin wani abu a
iranshi sai yana jin tamkar ya yi shela ya gaya wa matan duniya cewa duk wadda ta
haihu da shi zai raba dukiyar shi ya bata rabi, Hajiya dake zaune tafi su damuwa
tana matuƙar son ta ga ƴaƴan ɗan su namiji guda ɗaya,shi kaɗai ne namiji gun su sai
ƙananan shi mata guda uku,Sadiya ta na auren ɗan gidan Sarki, Fatima tana auren
shugaban ƙaramar hukuma.sai auta Nafisa ƴar lelen yayan ta Saddiƙ,yana matuƙar son
Nafisa,sai dai kuma sam ba shiri da matarshi Jummai, duk da kasancewar ta ƴar uwar
su. Ya fito don raka Alhajinmu wurin mota sannan ya dawo gurin Hajiyar mu don ƙara
gaisawa duk da ba wata hira suke yi ba,yana son ya ganshi zaune gaban ta sai ya
dinga jin shi tamkar ɗan yaye.
######
*Page 3*
Abba zaune gaban Malam Dari,suka gaisa da masabaha,sannan Malam Dari cikin
al'ajabin abinda binciken shi ya nuna mishi,ya soma magana.
Ya girgiza kai,"ba shi da wani aboki da ya wuce ni." Ya gyara zama " abinda na gani
cikin Istaharata shine,zai auri yar Amininshi da ke nan garin,abinda na yi ta
bincike. Nayi bincike zata mutu ko bazata mutu ba,zata haihu ko bazata haihu ba?
Allah be sa na fahimta ba,amma lallai yarka ce mata ta goma sha daya da zai
aura,kuma kila ta zama uwar ya'yanshi,Allah shi ne masanin gaibu."
Bayan barin shi gidan Dari,guri ya samu ya zauna don jikinshi ya yi sanyi,shi kan
shi ya kasa sanin dalilin da ya sa shi shiga cikin tashin hankalin duk da hana
zaton baya rasa nasaba da mutuwar da duk matar da Alhaji Sadiq ya aura take yi.
Yana son yin nazari kan lamarin,da kyar dai ya isa gida.Umma taso ta gane yana
cikin damuwa ganinshi da ta yi wani iri,amma dage mata ya yi kan cewa babu komai
kanshi ne ke dan ciwo yama sha magani,sallah yake son ayi ya samu ya dan huta kila
bacci ne.
Da safe gurin karin kumallo bayan sun gama ya sallami 'yan mazan sannan ya dubi
Ummar su "ina kawallin ta ki ? Ta ce "ta na dakina,tana gyarawa." Ya ce " da ta
bari ta karya ai ko?" Umman ta dube shi "ka manta yau alhamis ? Aisha tafi mu
kokarin Azumin nan na Litinin da Alhamis,tun dan zazzabin da ka yi kwanaki ni da
kai muka saka shiririta cikin azumin"'. Ya gyara zama "shi yasa ina matukar son
Aisha ,duk da haka kuma gashi lokaci ya yi da zamu rabu,ta dube shi da sauri "ban
gane zaku rabu ba? Ya dan yi jim sannan ya ce "Aure zan mata" da sauri ta
mike,"Aure! Aure dai? Ya yi karfin hali,"mene ne to na daga hankalin?". Ta zauna
cike da damuwa,tare da fadin "dole ne na tada hankali,to ko dai kana tsokanata ne?"
Ya dube ta" kin ga na taba miki irin wannan maganar?" Ta girgiza kai tare da shafe
zufar da ke keto mata, "amma Abban yara Aisha ba ta isa aure ba,gata dama ita ba
kiba ba baka ganin da kwara?".
Ya girgiza kai ba wani kwara a cikin aure,bautar Ubangiji ne,bana son ki nuna
damuwarki,har ki karya mata gwiwa ina son mu lallashe ta nasan zata damu ko don
yanda take matukar son karatu,ki bani goyon baya,nima inason na rama akhairan da
Aminina ya jima yana min ne,wato Alhaji Saddik." Ta dube shi.Tsura mishi ido ta yi
"Alhaji Saddik za ka ba ta?" Ya ce "shine" shiru ta yi yace "me ki ka ce?" Ta
girgiza kai " babu komai,sai dai tausayin ta,yarinya ce ga shi kuma suna katsina ba
kusa ba ne" ya ce"kada ki damu,aure babu in daba ya ksi mutum,batun yarinta kuwa
duk ba komai bane,shekara kusan sha biyar ai ta girma,jiki ne ba ta dashi.Nasan
Friend za ya kula da ita,yanzun kira ta in sanar da ita" Cikin jimami ta ce " To
Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ta tashi ta kira Aishan,kallon ta yake yi a
ranshi shima yana kara tausaya mata,saboda sam batada kauri don tsinken hannun
tamkar na yara kanana.
Ta zauna kusa da Umma ,kuma ganin Abban nasu ba da alamun wasa ba,yasa ta nutsu ta
san magana ce mai mahimmanci zai mata,kila batun komawarta makaranta ne nan da
kwana hudu,ya katse mata tunaninta da fadin "Aisha" ta amsa "na'am Abba." Ya ci
gaba "ina son zan miki wata magana,sai dai ina shakka." Cikin mamaki ta dube
shi,sannan ta ce "Shakka Abba?" Ta ci gaba "bazan so in zama 'yar da iyayenta za su
rinka shakka a kanta ba,domin bani da burin bijire ma umarnin ku,ko haninku,ka fadi
ko ma me ka keson fada ba tare da shakka ba." Ya numfasa tare da jin dadin maganar
ta,sannan ya furta zancan zan miki aure ne." A tsorace ta dube shi,domin batayi
zaton faruwar haka ba,amma sai ta dake ta kuma hadiye wani abu da ke taso mata ,ta
ce "to Abba." Ya ci gaba "kuma Alhaji Sadiq wanda yazo daga katsina,shi na zaba
miki." Kanta na kasa ta ce "to" Ta dube shi kamar zata yi magana,amma tana jin da
ta bude baki hawaye zai zubo mata,don haka sai ta yi shiru.
___________________________
Hajiya Jummai tana zaune bakin gadonta kafarta daya kan daya,tunanin ta yana
can Jigawa ita kam sam ba ta so ba,Alhaji ya yanke hukuncin bawa abokin shi Manajan
wannan kamfanin ba,bayan ta jima tana mishi maganar kaninta,bataso ta ga wani kusa
da dukiyar mijinta domin duk abinda ya tara nata ne,tunda ba d'a gareshi ba,don
haka dole ta kula da dukiyar ta,ta san kuma tunda shine gaba da ita zai rigata
mutuwa,dole ma ta san matakin dauka kan wannan kamfanin bari dai ta bari a gama
gyaran.
Dai dai yayi parking wayarshi ta soma tsuwa,ya duba Friend ya furta,sannan ya
dauka.
"Lafiya qalau,batun aiki ne nake son ce maka an kusa kammalawa,sannan sai batun
taimakon da na ce maka zan nemo game da matsalarka. Da fatan kana da lokaci zan
maka bayani." Alhaji Saddik ya ce " ina jinka,ni kadai ne." Abba ya ci gaba...
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number
09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
##_###
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 4*
Sai da ya sauka masauki ya huta sannan ya yi ma Friend ɗin shi waya cewa yana nan a
Dutse fa, Abba yace "ka min bazata fa,to bari inzo in same ka inda ka sauka wancan
karon ne?" "Eh,nan ne" inji Alhaji Sadiƙ. Ya idar da sallar la'asar yana jan carbi,
Abba yayi sallama ya shigo, Alhaji Saddiƙ ya tare shi cike da fara'a tare da yi wa
juna musabaha, suka zauna. Sun gaisa Alhaji Saddiƙ yace "Friend ina yaran nawa,sun
koma karatu hutu ya ƙare ko?" Abba yace, "Sun koma,ya ya Madam?" "Tana lafiya" inji
Saddiƙ, tace in gaishe ku,(ya ari bakinta ya ci mata albasa). Ya ci gaba,"Naso
ince ka zo min da zoɓon nan da nasha a gidan ka"Abba ya yi ƴar dariya,"ai na zata
gidan ma zamu je yanzun," inji Abba, "Na fi son mu gama magana a nan shi yasa na
sauka,yi man bayani Friend danni fa bana son yanda ƴan garinmu suka shiga
tsorona,nan ma in shiga wannan halin" Abba yace "bari dai in baka labarin
komai ."nan ya koro mishi bayanin yanda suka yi da Malam Dari, Alhaji Saddiƙ bai ji
mamaki sosai ba, saboda ya san ita ce shima ya sha ganin ta cikin mafarkinshi.
Ya dubi Abba, "Friend ban sha mamaki ba, saboda ran da naga yarinyar nan na san
cewa ita ce nake gani cikin mafarkina, amma hakan ba zai sa in aureta ba,sam ba zan
zama sanadin mutuwar ƴarka ba,bayan haka ma da kunya in auri ƴarka,ai ƴata ce, kuma
da kunya sa......." Abba ya ɗaga mishi hannu alamar yayi shiru, sannan ya ce "amma
ka san cewa bai saɓa ma Shari'a ba ko? Hasali ma wata sunna ce mai ƙyau ta Manzon
Allah (S.A.W) muka yi koyi ko? Ka manta Sayyidina Abubakar (A.S) babban abokin
Manzon mu ne, sannan ya aura mishi ƴarsa Nana A'isha, Allah ya yarda da ita,Tana da
ƙarancin shekaru, shi kuma ya soma manyantaka,sam wannan ba abin kunya ba ne kamar
yanda wasu ke faɗi."
Alhaji Saddiƙ ya ce "Friend yariyar nan ƙarama ce, bayan haka mu duba irin yanda
mata suke mutuwa a gidana...." Abba ya sake katse shi da cewa "kai ne ka ke kashe
su?" Alhaji Saddiƙ ya girgiza kai, "To!" Inji Abba,"ƙwanansu ne ya ƙare itama in
nata ƙwanakin suka ƙare ko ba a gidanka ba dole ta tafi, batun ƙanƙanta kuwa wannan
ba wani uzuri ba ne, iyayenmu ko shekarunta ba su kai ba,me ya same su? In dai baka
sonta ne shi kenan."
Alhaji Saddiƙ ya dafa kafaɗar Abba "ba za ka taɓa haihuwar ƴa in ce bana sonta
ba,na amsa kuma ban san bakin da zan iya maka godiya ba, saboda kai masoyina ne,
cikin kowanne hali,in ba mai sonka ba,wanene zai yarda ya kai ɗansa mahalaka,don ni
da kaina sai in rinƙa ganin tamkar gidan nawa mahalaka ce, Allah ya yi maka
sakamako ya sa itace sanadiyyar warwarewar al'amurana."
"Amin" inji Abba. "To yanzun yaushe ka ke son matarka?"
Alhaji Saddiƙ sai ya samu kan shi da jin nauyin Abokin nashi,ya yi shiru, Abba ya
dube shi "Don Allah Friend kada ka ji komai,ba wata kunya" Alhaji Saddiƙ ya ce
"abin ne sai yana ba ni mamaki, ashe zaka haifi ƴa ni kuma in aura?" "To ai abin
Allah ne," inji Abba,"yanzu dai yaushe ne za ka turo sai a saka rana in ta dawo
hutu ayi bikin in ya so zan roƙi alfarma koda je ka ka dawo ce don Allah ka yarje
mata,don tana son karatu,burinta shine ta zama Doctor."
"Don wannan kada ka damu Friend, insha Allahu ba tun turowa daga naje zan masu
Alhajinmu bayani." Daga nan suka ci gaba da hirar aikin gyaran kamfani, bayan sun
gama tare da cewa su zo su je gidan nashi, Alhaji Saddiƙ yace"an ya sai nake ganin
yanzu kamar gidan zai min wuyar zuwa" Abba ya miƙe "to tashi muje ku gaisa da
yarinyar,don tuni na yi mata bayani" Alhaji Saddiƙ ya dubeshi da sauri "Ta amince?"
Abba ya yi murmushi "A'isha ba ta musu ko gardama,ƙwarai zaka ji daɗin zama da
ita,ko dana sanar da ita ba ta yi musu ba, amma ta yi zancen karatunta,in kaje
yanzun ka ga sai ka shaida mata karatun nata yana nan, insha Allahu" "to na
gode,sai dai in har bata so dole ne mu bar wannan maganar," murmushi kawai Abba ya
yi, sannan ya miƙe tare da faɗin "shiryo mu je, bari na yi waya" ya fita. Umma ya
kira ya ce mata ga su nan zuwa su da Alhaji Saddiƙ, kuma yana buƙatar zoɓo mai ɗan
sanyi.
Falon Abba suka shiga Umma ta leƙo sun gaisa tare da tambayar Iyalan nashi da kuma
su Hajiyarshi,ya ce duk suna lafiya,ta koma kicin inda A'isha ke harhaɗa abinci kan
babban tire. Umma ta ɗauka tare da faɗin "Shiryo musu zoɓon bari na kai wannan."
Tana direwa Abba ya dube ta, "Ni fa dake zaki haɗa min,Ummansu shi Friend sa mishi
nashi shi ɗaya, wannan zuwan ba nawa bane,na ƙawallinki ne." Murmushi Umma ta yi,ba
ta ce komai ba ta fita. Ta isko A'isha kicin tana ƙoƙarin fitowa,ƙasa-ƙasa ta yi
mata magana.
"Ki natsu ban da wauta, Alhaji Saddiƙ zai yi magana da ke,kada ki ba Abbanku
kunya." Ta ce "to" dama tsaf take. Ta nufi falon Abba,ta yi sallama ta shiga.
Daddaɗan ƙamshin sa ya gauraye falon, ta ɗan saci kallon inda yake yana sanye da
wani farin shara-sharan yadi wanda har ana iya ganin bes ɗin shi ta ciki. Ƙyan
yadin ne ya bayyana tsadar shi,hular shi ƙube ce wadda aka yi ta da farin zare. Ta
dire tire sannan ta zauna ƙasa,kanta sunkuye ta ce, "Ina yini Uncle?" Tun
shigowarta ya ke kallonta, duk da cewa sanye take cikin hijabi bai hana shi ganin
rashin jikinta ba, shi kanshi tausayinta ya ji ya amsa da cewa, "lafiya lau ƴar
Abbanta." Ta miƙe ta soma ɗauko plate don zuba mishi cous-cous, ya ce "bar shi Nana
A'isha,ba ni zoɓon nan nasha bana jin yunwa," ta ce "to" ta soma zuba mishi cikin
kofi ta rage tsawo ta bashi,hakan ya burge shi, sannan ta koma mazaunin ta ya dube
ta,ke ce kikayi wannan zoɓon?" Ta ɗaga kai alamar "Eh" ya kuma kafa kofin a bakin
shi ya shanye ragowar na cikin kofin.
"Kice zaki dinga haɗa min in kin koma gidana can Katsina? Ko ba za ki je Katsina
ba?" Cikin cinyoyinta ta tura kanta,ya ce "Gaya min in ba ki son zuwa don bana son
ki takura." Ta ɗago kanta ta ɗan dube shi "in dai zan dinga zuwa makaranta ai ba
komai," ya ce "da gaske ki ke yi?" Ta ɗaga kai ya ce, "To za ki yi karatunki in ma
makarantar da ki ke,ki ke so zan bar ki kiyi abinki,yanzun yaushe zaki koma?" Ta
ce"jibi" ya ce "to shikenan,in na kai jibi a garin nan sai na kai ki." Ta ce,"To"
bai san me zaice mata ba ma,yana jin nauyin yi mata magana, hannu yasa cikin
aljihun rigarshi ya ciro bandir ɗin ƴan Naira ɗari biyu "Gashi kiyi shopping" ta
ce,"A'a,ka barshi na gama shopping ai" ya yi yayi taƙi amsa,ta nufi cikin gida.
Abbanta ya ce har kun gaisa?" Ta ce "Eh," ta shige ɗaki bakin gadonta ta zauna.
Mutumin yana burge ta, ya iya gayu mai ƙyau da shi, tunda ya ce zatayi karatu ba ta
damu ba, sai dai zata yi kewar Ummanta da Abba.
Washegari tafiyarshi ta kama,don haka ba zai samu kaita makaranta ba, Abba ya ce
kada ka damu,dama da akwai motar da ke kai su, kuma ita ce ke ɗauko su. Ya ciro
ƙwalin waya ƴar mai ƙyau ƙirar (Nokia), "Gashi ka ba ƴar gidan tawa in dai babu
damuwa, saboda kasan ba zan dinga samun zuwa ba, duk da na san ba za ta da ita
makaranta ba,in ta dawo ma ringa gaisawa,don na bata kuɗin ne taƙi amsa shiyasa na
siyo mata da na fita ɗazun," Abba ya ce "ita da zata koma makaranta ka sai mata
waya?" Alhaji Saddiƙ ya ce ka dai bata ƙila ma zata fi amsa min magana a cikin
wayar," "shikenan" inji Abba, Allah ya biya maka da gidan aljanna,bari na turo ta
kuyi sallama," "a'a ka barta tana jin nauyina yarinyar tana da kunya bana son matsa
mata," "shikenan". Suka sake yin musabaha, sannan ya shiga mota sai Kano,ya bar
motar a gidanshi na nan Kanon, sai ya hau jirgi.
Nafisa auta itama cewa tayi Yaya Saddiƙ nima insha Allah zan soma tsayuwar dare tun
daga yau. Ya dube ta "kin yi alƙawari fa?" Ta ce "insha Allah,Yaya zan cika" shima
dama Allah ya ke gayamawa kullum sai dai ya sha alwashin dagewa.
Ya dubi Hajiyarmu wadda har yanzun ba ta ce komai ba, sannan bai karanci wani abu
game da zancan a fuskarta ba,ka ra Hajiyarmu ta yi don haka bata furta komai ba.
Amma zancan ya yi mata daɗi, duk da tana fargaban abin, ganin kallon da yake mata
yasa ta ce "Allah yasa ma abin albarka."
Yayi ajiyar zuciya tare da miƙewa,can ƙasan zuciyarshi kuwa cewa ya yi "Amin
Hajiyarmu".
Sau da yawa tana mamakin yanda Hajiyarmu da Yaya Saddiƙ suke jin nauyin juna,tamkar
surukai. Yace "to ni zan tafi,ban riga na sanar da Jummai ba tukun, sai na koma
yanzun."
Kafin ya yi magana, Hajiya ta ce "Don me? Ke Nafisa kin cika fitina," shiko ƴar
dariya ya fita yana yi, Nafisa ta bishi tana cewa "Yaya bani lambar A'isha,zan kira
ta," ya ce "ayya Nafisa, A'isha yarinya ce ƙarama, gobe ma zata koma makaranta (S.S
1) take a Munjibir, kuma ba wai shekarunta ne suka kaita (SS) ɗin ba, ƙoƙari ne,she
is fifteen."
Dariya ta yi.
"Yaya kana son ƙananan yara."
Ya ce,"to Nafisa ƴar abokina ce, shi ya bani duk da yasan matsalar gidana,ki bari
in lokacin ziyarar ɗaliban makarantar ta zo in kina gari sai muje ko?"
Ta ce, "to Yaya," Ta koma ciki,shi kam ya shige mota. Ya lura kowa yana son Aisha a
dangin nashi, yanzun saura Jummai.
Umma ta ce,"to ai Abban naki ne ya kawo" ta ɗauki wayar tana jujjuyawa,ga ta ƴar
mai ƙyau,na gode. Umma ta yi dariya.
"A'isha kenan,dama ga ki da son yin (Game)."
Tayi dariya,ta zauna tana cewa, "Bari na gani zan gane kan wayar kuwa?" Ba tako
gane ba, sai da Yaya Abdurrahman ya shigo, sannan ya koya mata.
Bayan sallar Isha'i,sun ɗan taɓa hira ta ce "bari na ƙwanta Umma,don gobe tashin
wuri zan yi saboda komawa makaranta."
Jafar ya ce, "Yaya A'isha ko dai kina son ki buga (Game) ne da wayar?"
Ta ce,"Jafar ka raina ni ko?" Ta shige ɗakinta, gado ta haye tana buga (Game) ɗin
(Bounce) kusan goma na dare wayar ta shiga ringing,ta saba da wayar Umma don haka
ba taji komai ba,ta ɗauka. Da ƴar zazzaƙar muryarta ta ce,"Salamu alaikum" ya amsa
da "wa'alaikis-salam, A'isha ce?" Gabanta ya faɗi saboda ta gano Uncle ne,ta amsa
"Eh." Ya gyara ƙwanciya, "kin san mai magana?" Ta ce "Eh," ya ce to wanene?" Ta yi
shiru ta rasa me zata ce,kina jina? Ta ce Umh,ya ce kiyi magana mana A'isha...
#######
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 5*
Ya ce kiyi magana mana A'isha,wa ke magana da ke? Ta daure ta ce, Uncle ne. Yayi
murmushi, "zan zama mijinki kuma kina ce min Uncle? Gara kin kira sunana" ta ce
"bazan iya kiran sunanka ba". "To ki samin wani sunan mana ban da Uncle". Ta yi
shiru, ya ce "to ba mu gaisa ba" ta yi maza ta ce "Ina yini?" Ya ce "lafiya lau
Nana A'isha Saddiƙa,ya ya su Abbanki da Ummanki?" Ta ce"suna lafiya." Ya ce "za ki
jini ina kiranki da sunaye duk na ki ne", ta yi shiru, shima ya kan rasa me zai ce
mata,can ya ce, to bani labari" ta ce "Na me?" Ya ce, "Na komai mana" ta yi
shiru,ya ce "To bani na ƙawayenki na makaranta."
Tamkar ya mata susa,ta ce "ƙawayena biyu ne,da Suwaiba Shehu Ringim,sai kuma Zainab
Shitu Katsina, duk suna da kirki."
"Ashe har da ƴar garinmu? Ki ce shi kenan in kin zo Katsina kina da ƙawa, sai kuyi
ta wasanku ko?".
Kalmar ta bata dariya, har ma ta ɗan dara kaɗan, sannan ta ce "wasa kuma?" Ya ce,
"Eh mana,ko baƙwa wasa a makaranta?" Ta ce "sai ka ce ƙananan yara?" Ya ce "Au,na
manta ashe fa ku manya ne,ni da har ina son in saya miki kayan wasa su Tedi, haka
su Cartoons." Ta ce "Haba dai?" Ya ce, "To shi kenan bari in bari sai kin haifa
mana Beby sai in saya mata ko?"
Cike da walwala ya dube ta,sanye take da rigar bacci mai santsi, ɗan gashin kanta
da ya rage ta tufke shi da ƙyar ma yake tufkuwa saɓanin da da take da gashin da
yawa, tsabar ƙalƙalin da take ma gashin duk ya karye.
Ya miƙa mata hannuwanshi alamun ta zo, sai ta basar ta zauna gefenshi, ta kuma cewa
da shi.
Ya ce, "ƙanwarki to be insha Allah." Ta danne wani abu da ke son taso mata.
"A ina ka samo ta? Nifa ina jin tsoron ka ƙara aure yanzu in ina tuna baya."
Ta miƙe da sauri tare da faɗin "Dama na san za'ayi haka,wato yaga kuɗi za'a ɗora
shi manajan kamfani ba dole ba, kai ma in baka so cutarshi ba ai sai ka gaya mishi
cewa gidanka duk wadda ka auro mutuwa suke yi."
Ya dube ta, "To menene na tada jijiyar wuya? Har kina gaya min cewa In ba na so
cuta ba, wato ni ne macucin ko?"
Ta miƙe tsaye "wallahi wannan karon ba zan yarda ba,ban amince da auranka ba,
shiyasa ka ke waya har kana wani cewa zata haifa maka yara? Sai dai ka zaɓa ko ni
ko ita, haka kawai kana auro matan suna mutuwa,ƙila ma ana can ana zagina ana cewa
nice ke kashe su to ba zan iya ba."
Ya dube ta,"zan auro ta, itama ta zo ta mutu,batun yarda kuma bana neman yardarki
tunda bake bace Hajiya Sa'adatu uwata ba,kin ji ko? Batun kamfani kuwa da kike
magana naga ba naki bane,bana kuma son shiga sharo ba shanu,in ma kyauta na bashi
ba ruwanki sannan ki sani rashin mutuncinki da ki ka iya kada ki yarda ya zo
kaina."
Fuu! Ta fice ta bar mishi ɗakin, kallo ya bita da shi, cikin mamakin ɗaga hankalin
ta da tayi. Sam bai za ci haka daga gareta ba, saboda duk auren da ya yi a baya
bata taɓa nuna damuwarta ba sai wannan.
Ita ko cikin ɗakinta safa ta ringa yi tare da marwa, lallai ta kula Alhaji da gaske
auren nan zai yi,ta soma magana, wallahi-wallahi ba zan gushe ba zan cigaba da
ɗaukar alhakin rayukan duk wadda ta yarda ta yi kishi dani, shima wannan karon ko
nawa zan kashe sai nasa an kama min shi, aikin banza kawai in ko ba zai gaji da
aure-aure ba nima ba zan gaji da aikawa da duk matar da ya aura barzahu ba."
Hajiya Kari ta ce, "To ya ya kikayi?" Ta ce, "buɗe wuta mana, yanzun nan in gaya
miki kaca-kaca mukayi da shi". Hajiya Kari ta ce, "Kash! Ai ke kin ji matsalar
ki,ke da zakiyi kwanto kamar yanda muka saba,me ma kika sani game da yariyar?"
Hajiya Jummai ta ce, "Me kuwa? Abinda na sani kawai ya ce min ƴar abokinsa ce,kishi
ya rufe ni na hau masifa." Hajiya Kari ta ce, "lallai kin so ki kwafsa,ko sunanta
ba muji ba, saboda haka da safe ko kuma yanzu ki je ki bashi haƙuri ki ce masa
zafin kishi ne, daga nan sai ki bugi cikin shi muji komai."
Hajiya Jummai ta ce, "sai dai goben, amma yanzun kamar ba zai saurareni ba,na san
shi sarai ina ganin wannan karon ko boka na dutse ba zai iya aiki kan Alhaji ba,
zan nemi wani tunda har yau bana juya shi yanda nake so,sai yanda ya ce, dole haka
za'ayi."
Hajiya Kari ta ce, "kada ki damu, zan zo gobe sai mu yi magana a tsanake, amma don
Allah ki kwantar da hankalinki" ta ce "zan yi ƙoƙari."
Yana saka kaya ta shigo da sallama. Ta ci gayu cikin shadda mai kalar ja, ƙyan
shaddar da tsarin ɗinkin shine ya toni asirin tsadar kayan,ƙamshinta ya cika
ɗakin,cike da salo ta iso gurinshi ta amshi (Nect tie) ɗin tana gyara mishi tare da
faɗin, "ka ganka kuwa Alhajina? Kai ka yi ƙyau." Bai ce mata komai ba, haka nan bai
saki fuska ba, kuma bai katse ta da gyara mishi (Nect tie) ɗin ba, sai da ta gama
yana kallonta,ta ɗauko turarenshi Matador ta fesa mishi kaɗan, sannan ta ce sauran
ka (break) ya ce na ƙoshi,ta dube shi da sauri ban gane ka ƙoshi ba? Kana nufin ba
zaka ci ba zaka fita?"
"Kai min afuwa,ba zan sake ba." Ta soma hawaye, mai tausayi ne musamman ga mata,don
haka ya ce "naji tashi shi kenan, amma kada ki sake,batun Break kuwa na yi latti,in
na dawo zan ci na dare" cikin shagwaɓa ta ce,"ka kula min da kanka." Ta rakashi
zuwa ƙofar falo,yana fita ta ce,zaka sani ne, tunda ka ce mata kasa gaba.
"Wai kin san da ya ya ma ya faɗa min sunanta?" Ta ɗan dakata,kafin ta cigaba "sai
da siyasa,na ce haba Alhaji ko baka huce ba ne? Kana ji ina tambayarka sunan ƙanwar
tawa amma ka min banza."
"To me zan ce miki" haka fa ya ce min sai daga baya yake ce min "A'isha." Yaƙi gaya
min ma lokacin bikin."
Hajiya Kari ta ce, "ki bar shi,ai dai in lokacin ya matso dole muji, tunda mun samu
sunanta shi ne kawai abin buƙata, yanzu kuma mun ji."
Yanzun sai mu sa ranar tafiya maguzawan, "To yaushe ne zuwan? Inji Hajiya Jummai,ta
cigaba "Kuma sai dai mu je da direbanki, kamar kowane lokaci" "Eh,ai ina sane ba
zamu bar wata kafa ko ya ya take wadda zata tona mana asiri ba,ke dai ki shaƙi kuɗi
don bokan dutse yanzun idanunshi sun buɗe da son kuɗi,da, ko akan dubu biyar ma sai
ya yi kisan rai." Jummai ta ce,"A sosai ma kuwa, ɗan iska ni har yau ma ban sai
mashi motar da yake naci ba". Hajiya Kari ta ce "ke dai bar ɗan iska ko ina ruwan
wanda ke cikin daji da mota?" Jummai ta ce,"nima shine na gani, shiyasa na share
shi,rabo na da zuwa gun shi tun aikin ƙarshe da ya yi mana,na matar ƙarshe da
Alhaji ya aura." Hajiya Kari ta ce, "ƙyale shi wannan karon sai ki sai masa ko ƴar
starlet" Hajiya Jummai ta ce "hakan za mu yi" nan dai suka ci gaba da shirya ranar
da zasu tafi.
Sam, A'isha ba tayi niyyar sanar da Aminan nata batun auren nata ba, saboda kunya
take ji, duk cika bakin da takeyi na cewa ita karatu zatayi kamar ba gobe,don
Doctor zata zama yanzun ma har Doctor Aisha suke ce mata,in ko suka ji ta san zata
sha tsokana, sai dai su shafa su ji bata dawo ba, Zainab ma ta iso kuma sun duƙufa
karatu babu wasa.
Alhaji Saddiƙ ya yaba da yanda Abba ya tsaya tsayin daka, aikin kamfanin ya
kammalu. Guri ya yi ƙyau duk mutane sun yaba,don haka shima bai yi wasa ba wurin
kawo duk wani abu da kamfanin ke buƙata don fara aiki.
Alhamdulillah,tuni kamfani ya soma aiki, Abba kuwa ya samu kujerar manaja, yanzu
sunturi yake yi tsakanin Dutse da Jigawa, Alhaji Saddiƙ ya ce mishi ya nemi gida
nan Jigawa sai a siya, sannan ya saya mishi ƴar mota,ba a jima ba suka samu gidan
suka dawo Jigawa.
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number
09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
######
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 6*
Waya ya yiwa Nafisa cewa,ta shirya zasu je visiting tana jin haka ta soma murna.
Sun ɗau hanya in da Yahaya direban shi yake jan su. Aikin shi yake yi a bayan mota
cikin laptop, harkokin business ɗin shi yake ta yi. Nafisa ko sai dai kallon
ƙauyuka take yi, sai da suka isa garin Kano sannan suka tsaya bakin Sahad Store ya
yi mata tsaraba mai ban mamaki, sannan suka ɗauki hanyar Munjibir.
Da tambaya suka isa makarantar,Henesy baƙa wul tana ta sheƙi,ta ɗauki hankalin da
yawan ƴan makarantar,gilashinta masu duhu ne,don haka suke ganin mutane. Ya dubi
direbanshi ya ce "Yahaya fita ka samo mana ofis ɗin (PC) ɗin makarantar."
"Ranka ya daɗe ga ofis ɗin can, har ma na yi mishi bayanin cewa maigidana yana son
ganinshi,kuma ya ce mu shigo" "To ai shi kenan." Inji Alhaji Saddiƙ, tare da Nafisa
suka fito. Ƙwarjinin Alhajin ya sa ya zama abin kallo gurin ɗaliban tare da masu
ziyara. Kai tsaye ofis ɗin (PC) ɗin suka nufa,suna shiga shima (PC) din ya miƙe
tare da ba Alhaji Saddiƙ hannu,don daga ganin shi ya jiƙe da Naira. Sun gaisa,
sannan suka zauna kan wasu kujeru da ke gefe,ya nuna ma Nafisa wata kujera ya ce,
"Bismilla Malama" shi ko Yahaya cewa ya yi,bari ya koma gurin mota.
"Ok" ya miƙe yana fita ya kira shugabar ɗalibai ya aike ta neman A'isha,ya dawo ya
ce bari a kira ta.
Alhaji Saddiƙ ya ce,"Ba komai" ya zauna tare da cewa, "Ranka shi daɗe ƴar ka ce?"
Alhaji Saddiƙ ya amsa da cewa "Eh,ƴar abokina ce", wayarshi ta shiga ruri,ya ɗauka
yana magana.
A tsorace ta ce,"lafiya?"
Nima ban sani ba" ta ce "Ina jiran ku" ta nufi ofis ɗin shugabar ce ta shiga,ga ta
nan Sir,ya ce ta shigo, nagode miki ta fita sannan ta ce A'isha ta shiga, ita kuma
ta tafi. Tana shiga ta ji hancinta ya shaƙi daddaɗan ƙamshin turaren Uncle,gabanta
ya faɗi amma ta daure ta shiga,sanye take da wando da riga haɗe da gyalen su, kayan
mutanen Pakistan masu kalar sararin samaniya, kai tsaye teburin P.C ɗin ta nufa,
inda ta gaishe shi cikin harshen Turanci, sannan ta ce gata,ya nuna mata Alhaji
Saddiƙ da ke waya.
"Ga masu visiting na ki." Ya miƙe "Bari na barku, ku gaisa ko?" Ya fita.
Duk sai taji kunya ta rufe ta, har ma ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskarta. Ta
dubi Nafisa,ga zatonta matarshi ce. Cike da dariya Nafisa ta ce, "zo mu gaisa
A'isha." Ta isa gurinta ta zauna, sannan ta ce "Ina yini? Ya ya hanya?" Nafisa ta
ce "lafiya lau,hope kema kina lafiya?" A'isha kanta a ƙasa ta ce "lafiya ƙalau."
Nafisa ta ce "Hajiyarmu da Alhajinmu sun ce mu gaishe ki" A'isha ta ce, "ina
amsawa, na gode."
Dai-dai sannan Alhaji Saddiƙ ya gama waya ta ɗan saci kallonshi da gefen ido. Wata
jiƙaƙƙiyar shadda ya saka kalar ƙasa,ya yi ƙyau sosai ta zamo daga kan kujera don
ta gaishe shi.
Nafisa ma dariya take yi, sannan kunyar A'isha ta burge ta, A'ishan ta mata
ƙyau,sai dai yarinya ce ƙwarai, ya ce "Nafisa yau dai ga ki ga A'isha" Ya dubi
A'isha ya ce, "Ga ƙanwata Nafisa." Ta kuma duban Nafisan.
"Sannu da hanya"
A'isha ta miƙe tana kallon Nafisa, "Bari na kira ƙawayena." Har za ta fita, ya ce
"Zo" Ta dawo ta tsugunna.
Ta rufe fuska,tana ɗan murmushi. Ya ce, "Umh,wa zaki ce musu? Ko har kin basu
labarina ne?" Ta girgiza kai, sannan ta ce, "Ce musu zan yi Uncle ɗina ne." Ta miƙe
ta fita da sauri. Dariya Nafisa ke musu, ta ce "Yaya Saddiƙ duk da A'isha yarinya
ce kun matuƙar dacewa, Allah dai ya yi mana jagora tare kuma da shige mana kan
matsalarmu." Ya ce "Amin sister."
Ta je gurin su Suwaiba ta kira su, ce musu ta yi Uncle ɗinta ne daga Katsina, suka
shigo suka gaishe shi,ya tambayi sunayen su suka gaya mishi,ya ce "Har da ƴar
garinmu? To sannuku,ku dage da karatu ko?" Suka ce, "To mungode" ya ce "nima na
gode." Suka fita suna mamakin dama A'isha tana da Uncle a katsina, Amma ba ta taɓa
gaya musu ba? Zainab kam so take ta tuna inda ta san shi.
Nafisa ta miƙe, "A'isha bari na bi ƙawayenki na ɗan miƙe ƙafa," A'isha ma ta miƙe
ta fito, kira ta ƙwalawa su Zainab.
Suka ce, "To" ta dawo ofis ɗin ta zauna, ya dube ta "Ya ya bayan rabuwa?" Ta ce "Da
godiya, shi Abbana ba zai zo ba?" Ya ce,in gaishe ki ba zai samu zuwa ba, saboda
aikin shi ya koma Jigawa. Kuma yanzun Jigawan ku ke" ta dube shi, "Mun tashi daga
Dutse?" Ya ce "Haka ne,to yanzu yaushe ne zakuyi hutu?" Ta ce, "Nan da sati biyar
zuwa shida." Ya ce, "To so nake a shirya komai kafin kuyi hutu, cikin hutunku za'a
ɗaura aure tare da bikin." Gyale taja ta rufe fuskarta. Ya ce, "Me kika ce?" Ta ce,
"Duk yadda ku ka yi,ni dai karatuna na fi ji" Ya ce, "wannan babu komai, sai
makarantar da ki ke so ita zan kai ki" ta ce "Bari na samo maka wani abu." Ya ce,
"No,bar shi am ok." Ya dubi agogo bari muyi sallah mu zo mu tafi." Ta ce, "To."
Bayan sun yi Sallah,ya dawo ya yi ma P.C alkhairi mai yawa,P.C ya rako shi har gun
motarsa. A'isha taje ta kira su Zainab su yi sallama,har ma ta ce ma Sani Yayan
Zainab,ya zo ya bi su Uncle ɗin ta mana tunda suma Katsina za su je.
Sanda suka iso gurin motar Yahaya,yana ta aikin jibge ƙwalaye a ƙasa daga boat ɗin
motar,Sani yaja baya ya tsaya yana mamakin ganin Alhaji Saddiƙ K.T. mutumin da ya
yi kuɗi da jinin mutane, yanzu kuma dabarar da ya sake kenan? Ta shigowa makarantu
yana son shan jinin ƴan makaranta? Sun gama sauke kayan suka shiga mota.
Alhaji Saddiƙ ya miƙa ma Nafisa bandir ɗin kuɗi yace ba ƙawayan nata. A'isha ta
leƙo tana cewa, "Nafisa ku sauka lafiya,ku gaida ƴan garin." Ya ce, "Ni fa ko
Nafisa kaɗai ki ka sani?" Nafisa ta ce, "yauwa ga Yayan Zainab shima Katsina zai
je". Alhaji Saddiƙ ya ce, "To ya shiga mu je." Ta zo gurin su, ina Sanin?" Yana
daga bayansu ya ce,"A'a su tafi ni dama sai gobe ina da aboki nan cikin Munjibir,ta
je tace su tafi su Zainab ma suka je sukayi godiya.
Suna tafiya sai ya zo gurin su ya nuna A'isha, "wannan mutumin ne Uncle ɗin ki?
Zainab ta ce, "Ka san shi ne? Nima ina ta mishi kallon sani."
"Sani ya ce, "kin san shi mana, Alhaji Saddiƙ Usman K.T ɗin ne baki sani ba."
A'isha ta zaro ido,me kuɗin jini kuma?" Sani ya ce, "tabɗi,ke da baki san halin
Uncle ɗin na ki ba? Koda yake ai basa cin na gida sai bare."
Jikin A'isha ya soma rawa, cikin matsanancin tsoro ta ce, "Don Allah ku gaya min
gaske ne?" Zainab ta ce, "kada ki damu zan baki labari,ku zo mu ƙwashe kayan nan."
Ta ce, "ai ni bazan ɗauki wani abu ba har sai naji labarin Uncle." Suwaiba da
Zainab har ma da Sani suka shiga ƙwashe kayan. Zama tayi bakin gado tana tunanin
baƙon al'amarin, har suka raka Sani suka dawo.
Zainab ta zauna kusa da ita, A'isha dama baki sani ba,shan jini suke yi,An ce aure-
aure ya ke yi, duk wadda ya aura ba ta sati biyu take mutuwa,aurenshi goma,
uwargidan ce kaɗai bai cinye ba, ke yanzu fa ba a bin layin gidan shi,don ance kana
cikin tafiya a layin wani abu zai ja ka zuuu sai dai ka ganka a cikin wani ɗaki a
gidan,ke kina ganin gidan kin san ana cin mutane a cikinshi, ko ba ki san gidan
ba?"
Suwaiba ta ce, "Tab! Amma ya yi ƙyan banza." Zainab ta ce "kinga gidan ne wani
mahaukacin gida ga bishiyoyi."
A'isha sai kuka,lallai Allah ya so ta tana zuwa gida zata sanar da Abbanta. Duk
kayan da ya kawo ta ce bata so,ta ma fita hayyacinta cikin ƙwana uku ta ƙwanta
ciwo,ƙwananta biyu ta ɗan samu sauƙi. Amma duk ta rame su Zainab sun yi ta matsa
mata da son jin gaskiyar lamarin ta da Alhaji Saddiƙ don sun ga yanda ta ɗauki abin
da zafi ƙwarai. Ta gaji ta gaya musu cewa Babanta ya riga ya bashi ita,sun jajanta
mata tare da kuma bata shawarar ta tashi tsaye da addu'a, Allah ya shiga tsakaninta
da sharrinshi. Sun ce suma za su taya ta.
Sun isa Jigawa misalin ƙarfe biyar na yamma,suna tsayawa A'isha ta fito tana kallon
sabon gidansu,ga dai gida mai kyau amma ta kasa jin farin ciki, kuma ta yarda cewa
iyayenta suna cin kuɗin ƴarsu ne. Nan take hawaye ya soma zubo mata,ta shiga ciki.
#######
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 7*
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```ACT}:--1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu
matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
Abdulrahman yana biye da ita da kaya, cikin wani tsararren kitchen ta hangi Umma,
Umma tana juyowa ta yi arba da ƴarta, da sauri ta fito tana cewa ga ƴan makaranta
ga ƴan makaranta." A'isha ta faɗa jikin Umma tana kuka.
Ramarta ta tsorata Umma, ta ce, "A'isha kin yi ciwo ne?" Dai-dai nan Abba da
Abdulrahman suka shigo, Abba ya ce, "ƙawallin taki ta bani tsoro, Ummansu kin ga
yanda ta ƙare?" Umma ta ce "Shine ai,wane ciwo ki kayi haka?" Cikin kuka A'isha ta
ce, "Nima ban san ciwon ba,ni dai duk jikina ne bana jin daɗin shi. Suka shiga falo
kan kujera ta ƙwanta tana ƙara kallon yanda aka tsara falon da kuɗin jini, duk sai
ta samu kanta da ƙyanƙyamin komai na gidan. Umma ta zubo mata abinci ta tasa shi ta
kasa ci, har dare Umma ta yi tayi A'isha, amma ta ƙi cin komai. Hankalin Iyayen ya
tashi, cikin dare zazzaɓi ya rufe ta saboda tsananin damuwa da kuka, dole da safe
suka nufi asibiti, duk binciken likitan bai gano komai ba, sai damuwa. Don haka
yasa mata ruwa tare da allurai don ta samu bacci.
Ƙwananta biyu aka sallame ta, tunda ta dawo ko yaushe jugum ba ta magana. Umma ta
matsa mata da tambayar abinda ke damunta,don likitan ya ce tabbas akwai abinda ke
damunta. A'isha tana son sanar da Umma amma tana tsoron kar ta gaya wa Abba, shi
kuma ya yi faɗa. Ko ma ya yi fushi da ita,don haka ta yi shiru.
Abba yana zaune yana cin abinci, ya tasa ta gaba wai itama sai ta ci nata. Umma ma
ta shigo ɗakin na A'isha, wanda ya ji uwar katifa sai (T.V) ance ba za'a cika ɗaki
da kaya bane tunda cikin hutun nan ne za'ayi bikinta, Umma ta zauna tana cewa,ka ce
kana nan na fito ban ganka ba,ya ce "eh, ina nan gurin A'isha so nake ta ci abincin
a gabana in gani," Umma ta ce "to nima dama na zo ne in tsare ta, yarinya duk tasa
kanta a uku" ta dubi A'isha wadda take ta ƙoƙarin ganin ta ci abincin,ko don
hankalin iyayenta ya ƙwanta, ta ce, "To ko saboda aurenki da Alhaji Saddiƙ ne?" Da
sauri ta kalli Abba, wanda ya tsura mata ido, sannan ta girgiza kai, "Ba haka ba ne
Abba" ya ce "ai bani ne na tambaye ki ba, Ummanki za ki bawa amsa, tunda ni dai ai
mun gama magana,jiya ma nake sanar da shi dawowarki, sai dai ban sanar dashi ciwon
ki ba, saboda zai ce zai bar aikinshi ya zo,ya ce dai zai zo kafin su kawo kaya."
Umma ta ce "bari na saka mata wayarta ma a caji, saboda ƙila zai neme ta. A'isha ta
yi ajiyar zuciya,lallai ya kamata ta sanar da Umma, domin dai ba su san komai kan
Uncle ba. Sai da Abba ya fita sannan A'isha ta dubi Umma, ta ce "Umma zan gaya miki
abinda ke damuna, amma sai kin yi min alƙawarin ba zaki sanar da Abbanmu ba" cikin
fargaba Umma ta ce, "Sanar dani,ba zan gaya mishi ba." Ta soma hawaye, "Umma ashe
Uncle ɗan yankan kai ne? Ashe duk kuɗin shi na jini ne?" Umma ta daburce tare da
cewa "Wane Uncle ɗin?" A'isha ta ce, "na Katsina, kinsan ƙawata ƴar Katsina ce nan
dai ta koro ma Ummanta labarin da ta ji game da Uncle ɗin nata, Umma ta shiga
damuwa,zufa ta shiga keto mata duk da cewar da takeyi anya kuwa A'isha zancan nan
gaskiya ne? Duk suka yi shiru kowa yana tunaninshi, can dai Umma ta yi ƙarfin hali
ta ce "A'isha wannan zancan ba na shiru ba ne, dole Abbanki ya ji, domin dai duniya
yanzu babu gaskiya, kuɗi suna kai mutane cikin halaka, sannan kai ka yarda da mutum
shi ko yana da nashi burin a kanka".
A'isha ta soma kuka tana faɗin, "Don Allah Ummata kada ki sanar da Abba,ba zai
taɓa yarda ba saboda ya yarda da Uncle ni dai na haƙura zan auri Uncle ɗin tunda
dai dama na san ƙarshena mutuwa zan yi."
Abba da ke ƙoƙarin shigowa ɗakin tun ɗazun,ya ji A'isha tana sanar da Ummanta A
ranshi ya ce, "shikenan sun ji zancan da ya ke ɓoye musu,ya zama dole ya shiga ya
sanar da su gaskiyar lamarin domin ya yarda Alhaji Saddiƙ ba zai mishi ƙarya ba,ba
zai cuce shi ba,ba zai ci amanar shi ba, kuma ba zai kasance ɗaya daga cikin masu
shan jini ba.
Da sallama ya shiga duk da baya da kuzari amma ya yi ƙarfin halin cewa "kuna hira
ne? Umma cikin damuwa ta ce "wane hira Abbansu zauna ka ji". Ya zauna tare da faɗin
"lafiya dai ko? Umma ta ce "da sauƙi dai,dama Abbansu dama ashe irin sana'ar da
yake yi kenan?" Abba ya ce "wa?" Ta ce "Alhaji Saddiƙ mana ta shiga jero mishi
bayani yanda A'isha ta sanar da ita. A'isha dake ƙwance jikin Ummanta tana kuka,ta
ce "Abba ka min afuwa na sani ranka ba zai so ba, amma duk da haka zan aure shi.
Abba ya ce "ku kwantar da hankalinku ni kaina na san wannan labarin kuma shi da
kansa ya yi min bayanin zargin da jama'a suke masa. Tabbas tun daga kan Hajiya
Jummai duk Mata da ya aura mutuwa take yi, gaske ne ya yi aure kusan tara ko goma
ne? Duk sun rasu," A'isha ta zaro ido, Abba ya ci gaba da cewa, "ina so ku sani
cewa, dukkan mai rai mamaci ne, haka nan matansa da suka riga mu gidan gaskiya,ku
yarda wa'adinsu ne ya zo, batun yana yankan kai babu gaskiya cikin zargin da
mutanan unguwar suke mishi."
Umma cikin matsananciyar damuwa ta ce, "to yanzun Abbansu matan nasa suna mutuwa
haka za'a bashi A'ishan?.
Ya ce, "Haba Fatima,ya ya ki ke dawo da hannun agogo baya? Na gaya miki na sake
gaya miki aure babu fashi, mutum baya mutuwa face ƙwananshi ya ƙare. Ya fita yana
cewa "ki zo."
Ɗakinta ya shiga, Umma ta biyo shi jikinta babu ƙwari. Ya dube ta yace, "Haba
Fatima,me zai sa kiyi min haka? Ke kin san son da nake ma A'isha,kin sani ba zan
cutar da ita ba, aure bautar ubangiji ne, zan yi murna a ce ta mutu tana ibada,don
haka ki natsu kuma ki ƙwantar da hankalin ki,ki bani goyon baya. Ki yaƙi shaiɗan mu
tattaushe ta,nima wallahi ƙarfin hali nake yi,in tana ganinmu cikin damuwa zata
kasa ƙwantar da hankalinta kullum zata zama cikin fargaba."
Umma ta ce, "Shikenan, zan yi yanda ka ce," ya ce "yauwa, addu'a kurum ita ce
magani,ki tsaya tsayin daka da addu'a,ba dare babu rana. Itama A'ishan ki tsaya
kanta ta dage da yin azkar safe da yamma. Cikin fargaba ta ce "To."
Sanda Umma ta shigo ɗakin A'isha, ta samu A'ishar tana zaune gabanta wayar ta ce
tana ta ruri tsabar tsoro ya hana A'ishar ɗaga wayar Umma ta kalli fuskar wayar
Uncle ɗina haka taga an rubuta nan take ta gane,ta cewa A'isha an sa shi mana? Ki
natsu ki ƙwantar da hankalinki,ki mishi magana cikin natsuwa,kada ki ɗaga mishi
hankali,kin ji?" Ta ce "Ina jin tsoron shi ne Umma" Umma ta ce "Daina tsoron shi,
shi ba mugu bane sharri ne mutane suke masa, ɗauki wayar." Ta kai hannu zata ɗauki
wayar, ta katse a karo na biyu.
Ya sake kira a karo na uku, Umma ta ɗauki wayar ta miƙa mata, hannunta yana rawa ta
amsa ta danna green ta sa a kunne. Cikin muryar nan tashi mai natsuwa da hikima
yace, "amincin Allah ya tabbata a gareki Humaira Beby". A'isha ta dubi Umma,harara
Umma ta zabgo mata, sannan ta fita can gefen. Ya ce "kina jina ƴar Abba?" Ta daure,
sannan ta ce, "Ina yini Uncle?" Ya ce, "lafiya lau,kin dawo lafiya?" Ta ce, lafiya
lau, ya ce "Masha Allah" a zuciyarta kuma faɗi take, Allahumma kafihim bima
shi'ita,tana maimaitawa tana sake faɗa,ya ɗan yi gyaran murya,ya ce "A'isha ina
labari?" Ta yi shiru,ya ƙara sanyaya murya,ya ce "A'isha kina ji na?" Ta ce, "Umh"
ya ce, "zan zo week end,tun Friday kin ji? Kamar ta ce A'a, sai kuma ta ce Umh, ya
yi ƴar dariya sannan ya ce "to Bebyna,me da me zan kawo miki?" Ta ce,babu komai.ya
ce Shikenan, sai na zo, tace, "To ka gaida Nafisa" cikin jin daɗi ya ce "ita kaɗai
ban da Hajiyarmu?" Da sauri ta ce "har da su." Ta ƙosa ƙwarai ya gama
maganganunshi, kamar ko ya sani, ya ce "to bari na ƙyale ki sai kin ganni ko?" Ta
ce Uhum, ta riga shi kashewa,ana shi gefen bai damu ba zaton shi kunya ce.
Daran juma'a,sam A'isha bata runtsa ba, tama rasa tunanin da zata yi, duk da
lallashin da Umma take mata, bayan sun karya, Umma ta matsa mata suka shiga kitchen
don girka abin tarbar baƙo.
Sun gama sha biyu da rabi nan Umma ta bar ta ta haɗa mishi zoɓo da sauran kayan
sha. Ta shigo falo ta ƙwanta kan kujera, Umma ta fito don zuwa kitchen ta ce har
kin gama?" A'isha ta ce,eh, Umma ta miƙa mata waya ga shi yana ta kira ni ina
wanka." A'isha ta amsa Umma ta koma ciki.
Wayar ta soma ringing. Ta tsurawa wayar ido, ita dai kullum ƙara tsoron shi ma take
yi, amma ba ta da yanda zata yi dole ta ɗaga wayar tare da addu'a a can ƙasan
zuciyarta. Sannan ta ce, "Salamu alaikum" ya ce "wa'alaikumus Salam, Beby ina ki ka
shiga ne? Ina ta kiran wayarki?" Ta soma magana cikin in'ina,
"ina....am......wannan ne a kitchen ne," ya yi ƴar dariya, "ni kike yiwa girki
kenan?" Ta yi shiru, ya ce "ok,shiru yana nufin eh ne,to na gode. Yanzu haka na
shigo Jigawa, masauki kawai zamu je, sai na iso kenan" ta ce,to, Ya kashe wayar.
Ta tsaya tana kallon wayar,daddaɗar muryarshi har yanzun tana yi mata gizo, murya
mai cike da kamala kamar yarda fuskarshi take nunawa ta tuno suffarshi a fili ta ce
lallai Uncle bashi da makusa in ban da na mugun halinshi koda dai su Umma suna
ƙaryatawa.
Ta fito wanka tayo alwalla tana idar da sallar azahar mai ta shafa sama-sama saboda
zafin garin ta zazzago farar hoda a hannunta,ta ɗan murza a fuskarta ko madubi ba
ta duba ba,dama ita bata ƙwalliya. Don haka ba ta ma duba madubi,kai ita fa ko kaya
bata da zaɓi duk wanda Abbanta ya sai mata sun yi,don tana saka kaya ne don suturta
jiki ba wai don gayu ba, ta ɗaga aƙwatinta ta ciro kayan da ke sama. Wata atamfa ce
ta mutanan Ghana, fara ce ta saka taje ta ɗauko abincinta,ta zauna tana ɗan cakula
tana dai cin abincin ne amma hankalinta duk yana kan Uncle ganinta ƙila ma tun yau
zai gama da ita. Jafar da Munnir suka shigo,suna cewa Umma ga Uncle ɗin mu ya zo
yana waje yana waya. Umma ta ce, "tare da Abbanku su ke?" Suka ce "a'a shi kaɗai
ne, amma Yaya Abdulrahman yana gurinshi, ta ce "Abbanku yau ina ga aiki ya mishi
yawa ne,ko gida bai dawo ba, ina ganin daga Office ɗin ya wuce Masallacin juma'a.
Jafar ya fita waje,jim kaɗan ya dawo. "Umma Yaya Abdulrahman,ya ce ki bada makullin
ɗakin baƙi" taje ta ɗauko, A'isha kam tana zaune kamar gunki tana jin su. Yaya
Abdulrahman ya shigo, "Umma Uncle yana ɗakin baƙi ya ce yabi ta Ofis ɗin Abba,sun
tafi masallaci, shima yaje ya yi sallah ya koma Ofis ɗin basu dawo ba shi ne ya zo
nan gida". Umma ta ce, "bai kira wayarshi ba?" Yana ta kira bai samu ba sai yanzun.
Umma ta ce, "To ai shi kenan, tunda ma ya sameshi. Ta leƙo falo "A'isha tashi ki je
ki shirya mishi abinci,ki kai mishi." Jiki babu ƙwari ta tashi ta fita.
https://hikaya.bakandamiya.com/muazzam-babi-na-daya/
*💃💃💃💃💃Wata garabasa sai tsarin bakandamiya ki sayi littafi daya ki samu damar
karanta littafai sama da arba'in,akwai litattafan manyan marubuta kamar su RUFAIDA
UMAR,LUBNA SUFYAN,MAIMUNA IDRIS SANI BELI,FATIMA DAN BARNO da sauran su,yi kokari
kada wannan garabasa ta wuce ki akan naira 500 kacal,wacce take bukata ta yi magana
ta wannan number 09068032427*
########
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 8*
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu
matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
Babban tire ne ta shaƙe shi da kuloli masu ɗauke da kalolin abinci. Sai plate da
cokali, da sallama ta shiga,ƙasan zuciyarta kuma tana maimaita addu'ar Allahumma
kafihim bima shi'ita.
Ya yi matuƙar ƙyau cikin shadda mai tsada kalar ja mai duhu,hular da takalman duk
kalar jan ne,ƙamshin daddaɗan turarenshi ya cika falon. Duk da tsoronshin da take
ji bai hana zuciyarta yaba ƙyanshi ba. Ta dire tire kan tebur ɗin, gabanshi ta jawo
teburin sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce sannu da zuwa Uncle, ya ce "yauwa
ƴar Bebyn Uncle,I hope kina lafiya?" Ta ce "lafiya lau,ya ya su Nafisa da su
Hajiya?" "Duk suna gaishe ki, cikin jin daɗi yake bata amsa, domin yarinyar ta
shiga ranshi har yana mamakin yanda wasu lokutan ya kan shagala da tunaninta,ya kan
ji kewar ƴar siririyar muryarta, da Beby face ɗin ta, abinda bai taɓa yi kenan a
kan mace ba, duk matan da ya aura baita jinsu kamar yanda yake jin A'isha ba,a
ranshi. Ta cika kofi da ruwan zoɓo mai sanyi ta miƙa mishi cike da ladabi, ta koma
gefe ta zauna, ya ce "No, come on hau kujera ki zauna,ta ce nan ya yi Uncle, ya ce
to nima bari na sakko ƙasan, ta yi sauri ta hau kan kujerar ta ɗan ɗofanu yana ƴar
dariya shima ya gyara zaman shi.
Nan ta zuba mishi da miyar agushi, ga nama manya-manya,ya cika cikinsa dam,ko
magana ba ya iya yi, sai da ya gama sannan ya dube ta yana goge fuska da fari ƙar
ɗin handkachief ya ce, Beby kin ganni babu ba ka sai kunne ko? Ta sunkuyar da kai.
Ya ce,"Beby sai naga kamar kin rame min a ido hakane?" Ta ce na ɗan yi mura bayan
haka kuma ga makaranta," ya ce "kin manta ɗayar ga kuma maganar aure". Ta rufe
fuska, ya yi ƴar dariya sannan ya ce zan sa su kawo kaya da zarar na koma gida nan
da sati biyu zuwa uku,kin zama ƴar mutanen K.T? ko?" zancan ya daki zuciyarta, nan
take ta raya ma ranta haka yana nuna nan da sati huɗu zuwa biyar zata baƙunci
kabarinta, tunda an ce matan nashi ba sa wuce sati biyu zuwa uku suke mutuwa.
Ya katse ta. "Ko ya yi nisa a rage?" Da sauri ta girgiza kai,ya ce "a barshi haka?"
Ta ɗaga kai alamar Eh. Nan ya ciro mata tsarabar ta, abubuwan ci ne tare da
turaruka har da wata ƴar Tedi ta wasan yara. Ya miƙa mata ledojin ya ce "to duk da
kin ce baki son tsaraba gashi nan ki basu Jafar ke kuma ga naki" ya miƙa mata Tedi.
Baki ta saki tana kallonshi, shima ita yake kallo tamkar masu kallon soyayya,
sannan cikin sanyin murya ta ce "Uncle me zan yi da wannan?" Ya ce "wasa mana" ta
ce, "am not a small girl," ya ce haba? Ta sunkuyar da kai tace,da gaske,ya ce
shikenan to ki ajiye min in kin haifa mana Small boy sai ki na bashi yana wasa," ga
mamakin shi sai ya ji tace "in kuma na mutu fa?"
Da sauri ya dube ta,a ranshi ya soma zargin ko taji cewa matanshi suna mutuwa ne?
Amma a fili sai ya ce,"nima ina yawan tuna haka, sai dai duk sanda na tuna cewa zan
iya mutuwa ko ke ki mutu ban ga ɗan kaina ba, ina shiga wani mawuyacin hali,
zuciyata tana sonki da yawa." Ta sunkuyar da kanta ƙasa,ko dai mummunan zato ne a
ke mishi? Ko dai zargi ne? Ƙwanan matan nasa ne suke ta ƙarewa? Ya katse mata
tunani da cewa, "ki na tsoron mutuwa ne? Ko kina zaton in kin aureni zaki mutu
ne?".
Cikin dabara ya sako mata tambayar,don yana son ji ko ta samu labarin matanshi suna
mutuwa ne? Nan take ta gane nufinshi,don haka sai ta ce "a'a bana tsoron mutuwa,sai
dai kullum tunanina yana kan ayar da ke sanar damu (kulli nafsin za'ikatul mauti),
kaga dukkan Musulmi yana da ƙyau ya dinga tunawa ranshi zata ɗanɗani mutuwa, sannan
in ajali ya yi kira ko ince in ajali ya zo ba za'a ƙara ma mutum ko second ba.
Alhaji Saddiƙ ya dube ta cike da farin ciki,ya ce haka ne Beby, lallai kina da
kaifin basira. Haka nan duk bawan da yake yawaita tunanin mutuwa zata iya riskarshi
a kowane lokaci,za ki sameshi yana mai matuƙar kiyaye dokokin Ubangijinshi, ina
saka rai kema kina ciki? Ta sunkuyar da kai tare da faɗin insha Allah ya ce, to ba
zaki taɓe ba.
Sannan ya canza zancen da cewa,me kike shiryawa bikin? Ina nufin waɗanne shagulgula
za kiyi ke da ƙawayanki? Saboda in na tafi ba zan dawo ba, sai ɗaurin aure, shiyasa
nake son in sallame ki."
Ta dube shi,a ranta ta ce, inyi shagalin me? Bayan ni ƴan ƙwanaki ne suka rage
min,a fili kuwa sai ta ce, "ba zan yi komai ba." Ya ce, "Haba! Ko walima?" Ta
girgiza kai tare da ƙoƙarin maida ƙwallar da ke son zubo mata. Ta ɗan saka hannu ta
ja hancinta kamar tana mura, sannan ta ƙago murmushi ta ce "kasan Uncle bani da
ƙawaye bayan haka ma ni ban cika son hayaniya ba,so kaga gara na barshi ko?" Ta
faɗa tare da duban shi,ya ce "shikenan Bebyna" ya saka hannu cikin aljihun ya ciro
rafar ƴan ɗari biyar guda biyu dubu ɗari kenan,"gashi gudunmawata," zatayi magana
ya tare ta da cewa, "kul ki kakiyi magana, ke dai ce ne Allah ya cika mana
burinmu,a ranta ta ce Amin in ba shanye mini jinina ba ne. Ya ce zaki shiga gida
ko? Da sauri ta ce,eh tare da kallonshi ya yi ɗan murmushi sannan ya ce, "kin ƙosa
ki tafi ko?" Ta sunkuyar da kai tare da girgiza kan alamar a'a, ya ce "to ga
kayanki nan ƙwashe. Ta miƙe tare da ƙwashe kayan ta ce mun gode. Ya ce,ba ki ɗauki
Tedi ɗin Small beby ɗin tamu ba,ta kalli Tedin sannan ta ɗauka ya ce in Abbanki ya
shigo sai ki ce ina jira, sannan ki bar wayarki a kunne kin ji? To tace,ta fita.
A gadon Ummanta ta zube kayan tare da zama gefen gadon ta rafsa tagumi. Umma ta
fito daga (toilet) ta tsaya tana kallon kayan da iyayen kuɗin da ke zube a kan
gadonta, ta ce "A'isha waɗannan kayan fa?" Ta ce "Uncle ne ya ce in kawo ma su
Jafar?" Ta ce, "wannan kuɗin fa?" Me yasa ki ka amsar masa kuɗi?" Ta ce "Umma nayi-
nayi ya bar su yaƙi wai cewa ya yi gudunmawa ya bani don na ce mishi ni ba zan yi
shagalin biki ba.
Umma ta ce duk da haka da dai baki amso ba, A'isha ta dubi Ummanta ta ce, "ki aje a
gurinki ni sai in dinga ganin tamkar yana biyan kuɗin jinina ne da zasu sha....."
Ke! Tsawa Umma ta daka mata, sannan ta ce "A'isha bana son jin irin waɗannan
surutan daga bakinki kenan kema kin yarda da mummunan zargin da al'umma suke ma
mutumin da zai zama mijinki? Duk kin bi kin ɗaga hankalinki, maimakon ki tsaya kan
addu'a Allah yasa ki shiga gidanki cikin Sa'a ko? Ta miƙe ranta ɓace ta fita falo
ta bar ta ɗauke da tagumi tana nazarin yanda ma za'ayi ta iya ƙwantar da
hankalinta.
"Sofy! Sofy," Hajiya Jummai ce ke ƙwala ma ɗaya daga cikin ƴammatan da take ɗaukowa
cikin danginta kira. Sofy ta zo cike da yatsina, ta ce "gani Anty Jummai," ta ce
suby fa? Sofy ta yi wani luu da idanu, sannan ta ce tana bedroom in kirata ne?"
Jummai ta ce, "eh kirata aikenku zan yi yanzun ku fito cikin shiri." Suka fito
cikin riga da wando ya ɗame kowacce cikinsu, Sofy ce ma ta ɗan yafa wani ɗan
kucilin gyale, Jummai ta dube su kun yi ƙyau, sai dai kema Suby je ki yana ko ɗan
irin na Sofy ɗin kin san Alaramma yana gari. Haka take kiran Alhaji Saddiƙ in zata
yi wani abu daya hane ta. Ko in ya yi mata nasiha, to ranar yini zata yi tana ce
mishi Alaramma,ko Alagafarta. Soby taje ta ɗauko tana mitar ita bata son wani yafe-
yafen gyale duk takura ne, Jummai ta ce "ya ya zakiyi tunda kina gidan Ustazai,ka
ce shi yafi kowa sanin Allah" ta ce "ga wannan ta miƙa musu wani ƙullin abu cikin
tsumma,ku kai ma Hajiya Kari,ku ce mata ga ƙasar ƙafar nan za kuma mu yi waya.
Sofy ta ce, "motar wa zamu ɗauka tunda ta mu tana gurin gyara?" Hajiya Jummai ta
soma masifa, "ku hau mashin ba zan ba ku motata ba,ku je ku buga min ku ja min
asara." Suby ta ja tsaki tayi gaba tare da cewa, "Sofy ta baki kuɗin mashin ɗin,
amma ai ba mutuncinmu bane hawa acaɓa." Hajiya Jummai ta ce "shegun yara kada ku yi
mutuncin mana, tare da jeho musu ɗari biyu Sofy ta ɗauka tana mita haka suka tafi
suna zaginta, da cewa masifaffiyar mata.
Sofy ƴat ƙanwarta ce,Suby kuwa ƴar autar su ce,yaran sam basu da tarbiyya,ba sa
shakkar kowa sai maigidan. Hatta Hajiya Jummai maida mata magana suke yi. Foly suke
zuwa da ke nan Katsina. In kin ga yanda suke ɗaukan kai da shan ƙamshi zaka zata
ƴaƴan shugaban ƙasa ne. Alhaji Saddiƙ kaɗai ke taka musu birki in yana gari.
Hajiya Kari da Jummai cikin motar Hajiya Kari, ita da kanta take jan motar suna
hirar yanda zasu tsara mutuwar Amaryar ta Alhaji Saddiƙ,waton A'isha. Hajiya
Jummai ta ce "kin san Allah Hajiya Kari, (ta cigaba) wannan karon sati ɗaya nake
son a aika yarinyar nan barzahu, domin duk cikin matan da ya yi,yayin auren ban
taɓa jin kishin wata ba kamar wannan". Kari ta dube ta "menene na ɗaga
hankali,yarinyar da ƴan ƙwanaki za ta yi ta sheƙa barzahu, har ki ke damun kanki."
Jummai ta yamutsa baki,"ina mugun jin takaicin yanda ya damu da yarinyar, duk
abokansa ya bi ya sanar da su alhalin da a ɓoye yake aurensa, sai in amaryar ta
mutu sannan su ji, amma wannan fa shi da kanshi yake buga musu waya yana cewa,zai
yi aure su taya shi da addu'a,ke wani takaici ma sai suna waya da yarinyar in kin
ji yanda yake ƙara saisaita murya zaki sha mamaki." Hajiya Kari ta ce, "dama ga
muryarshi kamar ta mata,anya ma ba salabane yake yi kuwa?" Jummai ta ce,"shi dai ya
sani,ni yanzun damuwata ba ta wuce ya Boka na kan Dutse ya ganni ba. Kari ta ce
"a'a kada ki damu,zai ganki ɗan iska nufin shi zai rama wulaƙancin da mukayi mishi
na aikin ƙarshe da ya mana na ƙin sai mishi motar da ki kayi?" Jummai ta ce
"shiyasa yanzun na taho mishi da makullin motar su Suby,don ba zan sai mishi sabuwa
ba,yana kan tsauni ban da iskanci me zai yi da wata mota?" Kari ta ce "saka ai mata
penti ki bashi ya ƙarata da ita". Jummai ta ja tsaki,"Ni tunanina me zan ce ma
Alaramman nawa in ya ce ina motar su Suby?" Kari ta ja tsaki, "Jummai kina bani
haushi,mu da muka nufi gurin masu biyan buƙata cikin gaggawa shakkar me zakiyi,ai
ki sa a rufe mishi baki yanda ba zai tuna motar ba,su kuma shegun yaran masu ɗan
iskan rawar kan tsiya sai kurum ki ringa haɗa su da na Mashinko direba ya dinga kai
su."
#######
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Ɗandano page 9*
Jummai ta ce, "sun raina Tinau direba, kullum rigima shi yasa fa Alhaji ya sai musu
ta su", Kari ta ce "ƴan iska to su fito da miji mana ki musu aure,ki huta can sa
ƙarasa karatun a ɗakunan su" Jummai ta ce "yaushe suka nutsu har zasu samu mazan
ƙwarai? Sai dai masu rarake su kuma ƙanana sa'o'insu.
Kari ta ce,"nima gidana matsalar kenan,Safina tamkar ƴar Akuya ko ince karya maza
wannan ya aje wannan ya ɗauka". Jummai tasa dariya, sannan ta ce bata yar ba,kin
tuna lokacin muna school?" Kari ta ce "kema ai Allah ne yaso ki gurin cire cikin da
Mr.Joseph ya yi miki,mahaifarki ta nakasa,da ba don haka ba ƴarki ko ɗanki ba
ƙaramin tataccen ɗan iska ko ƴar iska za'ayi ba."
Jummai taja tsaki "bar tuna min ɗan iska Mr.Joseph, shi ne ya yi min sanadi da ko
ƴan iskan na samu ai da ban Yi wahalar ɗaukar rayukan jama'a ba,tun da nasan don
rashin ƴaƴa ne yake ta wannan aure-auren." Kari ta ce, haka ne. Suna ta ƴan
hirarrakinsu, har suka isa ƙauyen da zasu je, hanya ce mara ƙyau mai cike da
ƙwazazzabai tare da dutsina.
Suna isa suka fito suka rufe motar, sannan suka soma hawa dutsen wata ƴar bukka ce
a saman dutsen nan suka nufa ashar suka zunduma ita ce sallamar shiga gurin Bokan
dutse,shima daga ciki ya ce maraba da ƴan tselan uwa,ku shigo dan abu takazar
ubanku.
Suka samu guri gefe suka zauna. Ya dubi Jummai da jajayen idanunshi,kafin ki ce
komai ki fara cika min alƙawarina,don tsakaninmu babu ƴar ɗaga ƙafa yanzun ga wuri
ga waina zamu dinga yi, tunda ke na lura ƴar rainin hankali ce. Dodo ya ce in kin
sake kuskure alƙawarinsa za ki sha mamaki."
Ta buɗe jakarta tana cewa,"kai ko gashi ka cika gajen haƙuri, gashi" ta miƙa mishi
makullin motar, ya ce "riƙe tukunna ina motar?" Ta ce "a'a tana can ni ba zan iya
jan zuwa gurin nan ba, kuma bana son in ce direba ya jawo asirina ya tonu,ko ba
haka ba ne? Yace don wannan babu ji ko su Ifiritu sai su ɗauko, amma sabuwa ce ko?"
Suka dubi juna ita da Kari, har suna haɗa baki gurin cewa dal ma kuwa,ya ce shi
kenan. Ya shiga haɗa wasu abubuwa yana surkullenshi har ya gama ya ce,to ke ma fa
kina da aiki a gabanki, domin wannan aikin ya banbanta da na baya.saboda ita wannan
yarinyar tana yawaita ambaton Ubangijin musulunci, saboda haka sai mun dage."
Jummai ta ce,gara kam a dage Boka, saboda wannan in son raina ne ta mutu a ranar da
aka kawo ta.
Hajiya Karima ta ce "in ma ta mutu ranar ya kiyaye aure," Boka ya ce "ba zata mutu
sanda ku ke so ba, domin Aljani ba zai samu aiwatar da aikinsa ba, sai lokacin da
take fashin sallah, saboda tana tsananta ambaton Ubangiji.
Tana yawan kusanta kanta da Ubangiji, sannan ke kuma zaki daina sallah daga yau har
sai lokacin da Dodo ya ce kici gaba da yi. Ya miƙa mata wani ruwa gashi nan ki
yayyafa cikin ɗakin da za'a saka amaryar, kullum sau uku a rana har tsawon kwana
baƙwai. Ya bata wani ɗan gwangwani,ki binne shi a ƙofar ɗakin amaryar in ana sauran
sati ɗaya bikin," ta ce "Boka ko'ina tiles,ya ya zan yi in saka? Ya ce "ruwan ki
in kin matsu ki sa a fasa, sannan zaki dawo in ana sauran ƙwana tara bikin" ta ce
"to sai batun mijina ya ya zanyi na sameshi a hannuna? Ya ce"wannan ba zan gaji da
gaya miki ba,ba zaki taɓa samun shi yanda kike so ba, kasancewarshi mai tsayuwa
akan duk dokokin Ubangijinshi, sannan tun yana ƙarami iyayanshi suna matuƙar tsaye
kan shi, duk bokan da ya ce zai kama miki shi to ƙarya yake yi ba zai iya ba, sai
dai ki haɗa da kissarku ta mata,to zuciyarshi tana da tausayin mace, amma ba dai
asiri ba,in ma ya kamashi ba za aje ko'ina ba, zai karye.
Jummai ta ce, "shikenan zan ga me zanyi. Suka tashi suka fita yana me ƙara tuna
mata ban da Sallah ban da Sallah. Wa'iyazu billa,kaji mushirikan mata.
Alhaji Saddiƙ ya dubi Fatima, "Sister ki duba dai ko za'a ƙara wani abu" cikin
dariya ta ce, "sun yi fa Brother,sai dai in kana son ka ƙara zaka iya." Nafisa ta
ɗaga wani takalmi mai igiya ta baya ta ce, "haba Brother wallahi wannan takalmin ya
yi ma A'isha kaɗan na yara ne fa?" Ya dube ta kaji ki to ai itama yariyar ce,she is
fourteen or fifteen,sa'ar ƴarki ce fa sister" ya dubi Fatima. Nafisa ta ce "amma ai
tafi Nana tsawo," ya ce "to ai Kuma Nana ta fita ƙiba ma," ya miƙe yana cewa, "kisa
direbanku ya ƙwasa ku kaima Hajiyarmu,in ta ce komai ya yi shikenan,sai kusa ranar
tafiya tunda gaba ɗaya yau sauran kwana sha shida bikin. Suka ce "To" bayan ya fita
suka soma dariya Fatima ta ce "ni nama rasa me zan ce ma Brother babu fa brezia ko
ɗaya,ya dai saka pants da skat zuwa su bess, amma babu bra. Nafisa ta ce "nufin shi
bata da nonon sakawa ne ko?" Suka sa dariya, Fatima ta ce "kin san shi da kanshi ya
siyo undes ɗin, zannuwa da sauran kayan duk ni ya ba zaɓi amma ko takalma sai gashi
da su" Nafisa ta ce "shikenan in ta zo gidan ya siya," suka soma shirin ƙwasar kaya
don zuwa gidan Hajiyarmu.
A'isha tana ƙwance kan katifa, zuwa yanzu ta gama sadaƙarwa ta dangana ta kuma
ɗauki ƙaddara, sannan ta amince ƙwananta ne ya ƙare. Don haka ko yaushe zaka same
ta da casbaha tana ja. Istingifari ta ke yi, domin Allah ya yafe mata zunubanta.
Wayarta da ke gefanta ce take ruri, bayan ta ɗauka tare da sallama, ya amsa, sannan
ta ce, "ina ƙwana Uncle? Ya ce lafiya lau Beby, baƙin sun taso na san yanzun ma sun
sauka a Kano, saboda jirgin Kano suka hau, ta ce "Allah ya kawo su lafiya," ya ce
"Amin" ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Beby duk abinda be yi ba cikin lefen ki gaya
min kin ji ko? Saboda bata son dogon bayani sai kurum ta ce "To" ya ce "shikenan
sai na kira ko? Ta ce,to na gode, ya ce nima haka.
Gidan cike yake da ƴan'uwa ta gefen Umma da kuma gefen Abba. Shi yasa yawancin
baƙin duk ƴan Gumel ne, sai ƴan Garki, sun zo ne don karɓar lefe kamar yarda akayi
waya aka sanar da su. Anyi girke-girke don tarbar baƙin Katsina. Su kan yiwa amarya
tsiya da cewa duk gudun auren ne ta ƙara ramewa, ita dai tana kallon su tana kuma
jin su,nata addu'a ne a zuci, Umma ma dai tana ƙarfin hali ne domin kada ta karya
ma A'isha guiwa.
Sun iso cikin motoci guda uku fararen Acadami su uku motar farko matan abokanshi ne
na Kano,ta tsakiya kuma kaya ne a ciki, sai direba ta bayan mata huɗu ne Fatima a
gaba, sai Nafisa sai kuma ƙanwar Hajiyarmu, da ƴaƴarta Talatu.
Ƴan unguwa da suka taru da kuma ƴan'uwa sun sha mamakin ganin kayan da aka kawo,
suma sun sha tarba kuma sun ga karamci sun kuma yaba. Nafisa kuwa ɗakin A'isha ta
shige lokacin A'isha tana wanka. A'isha tana fitowa taga Nafisa zuciyarta tana son
Nafisa. Ta saki murmushi tare da cewa "dama har da ke aka zo? Ta ce,eh mana aini
Brother ya yi ma ƙawance. A'isha ta zauna tana shafa mai, Nafisa na kallonta,
lallai kam yanzun nononta suke fita ashe ya kula ne. Ta ce, Nafisa ya ya Hajiya fa
dasu Aunty Fatima?" Nafisa ta ce, "ai tare da Anty Fatima, muka zo Hajiyarmu kam
tana gaishe ki ba ki ce ina Uncle ba? A'isha ta ɗan yi murmushi kawai.
Nafisa ta ce, "Naga kin rame ne" A'isha ta ɗan yi murmushi, sannan ta ce "Na sha
jinya fa tun a school har yanzu." Nafisa ta ce Allah sarki, to Allah ya ƙara
lafiya. Amin inji A'isha, tare da zura wata duguwar riga, sannan ta soma ɗaura ɗan
ƙwali. Nafisa ta ce Allah yasa ki haifa mana Beby mai irin gashin nan naki. A'isha
dai ta sunkuyar da kai, Nafisa tayi-tayi ta zo su gaisa da su Anty Fatima, amma ta
ƙi,Fatiman ce ma tace ai nima ƙanwar ta ce, bari naje mu gaisa,Talatu ma tabi
Fatima dan su ga A'isha.
A'isha ko rufe fuskarta ta yi, har dai suka gaji suka tafi, Nafisa ma nan ɗakin ta
ci abincinta, Abba yayi-yayi su ƙwana amma suka ce a'a, Kano zasu ƙwana don zasu
shiga kasuwa goben da safe,sai su wuce. Da zasu tafi an basu tukuici suma yanda ya
kamata. Nafisa ta raɗa ma A'isha a kunne, cewa ki rage bacci,ki tsaya kan
addu'a.tsayuwar dare zaki dinga yi kina roƙon Allah alkhairin da ke cikin auren ya
kuma kare ku da duk masu sherri da hassada kin ji ko? A'isha ta ce, na gode Nafisa
zan kiyaye insha Allah.
Ya fito daga wanka,wankan da ya zama mishi ƙa'ida, duk dare koda da ya yi shi ne
zai kusanci matarshi ya fi gane yayin in yaso ya sake. Matsawar bai yi wankan nan
ba,to ko ba zai samu bacci ba, kasancewar yanayi ne na zafi shiyasa. Yana fitowa ya
warware (AC) turarukan shi na ƙwanciya ya faffesa, sannan ya saka kayan baccin shi
riga da wando.
Ya zauna bakin gado yana son jin muryar A'isha ne kawai,yau ƙwana biyu kenan ba su
yi waya ba,bai san mene ne yasa yake son Yarinyar ba,yana tsoron fa kada Yarinyar
ta mutu tamkar sauran matanshi. Ya soma neman layin yarinyar,yana yi yana kallon
agogo goma ta gota a ranshi, ya ce ko kin yi bacci zaki tashi. Dai-dai lokacin ko
ita tana kan darduma, nafila take yi sanda ta sallame sannan ya sake kira.
Ta ɗauko wayar ta ɗaga tare da sallama, ya ce "oh sorry Bebyna, na tashe ki kina
bacci ko?" Ta ce, "a'a bana bacci, ya ce me ya hana ki? Ta yi shiru, ya ce to ko
abinda ya hana ni bacci ne kema ya hana ki? Ta ce um,ya yi ƴar dariya kin san
abinda ya hana ni ne? Ta ce a'a, ya ce in gaya miki? Ta ce eh,ya ce ni tunanin kine
ya hanani ke fa? Ta yi shiru ya ce Beby kina ji na kuwa? Ta ce,ina jin ka,ya ce oh
gaya min, ta ce ni ina sallah ne, ya ce good,me kike roƙo? Da sauri ta bashi amsa
da cewa cikawa da imani da rahamar kabari, tare da samun Aljanna maɗaukakiya." Ya
ce "Umhum? Yana son jin ƙarin bayani, ta ce "Shikenan nake roƙo," ya ce "batun aure
fa baƙya yi mana addu'a? Shiru ta yi jikin shi ya yi sanyi ya ce A'isha in tambaye
ki wani abu? Ta ce eh, ya ce zaki sanar dani gaskiyar maganar? Ta ce,in har na sani
ba, ya ce "kin ji wasu maganganu ne a kaina?" Ta ce kamar me? Ya yi ɗan jim sannan
ya ce koma na me? Ko kirkina ko akasin haka?.
Ta rasa me zata ce ya ce ina jinki nasan duk mai irin sunanki in dai ta ci sunan
bata ƙarya. Sanar da ni. Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Uncle duka biyun na ji
da kirkin da kuma akasin hakan. Ya ƙwanta rigingine jikinshi ya yi matuƙar sanyi
sannan ya ce "Beby tsorona ki ke yi ko? Kin tsane ni ko? Kina zargina kema ko? Na
sani na dai na burge ki ko? Muryarshi ta soma rawa, shi kenan ba zan matsa miki ba
Beby zan barki kema kina tsoron haka bana son ki mutu domin kin shiga raina sosai"
ya kashe wayar ya jefar da ita a kan gado sannan ya ɗauko filo ya rufa akan fuskar
shi tare da matsewa yana jin wani pain a cikin ranshi.
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu
matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
A ɓangaren A'isha kuwa duk sai ta ji babu daɗi har ma ta yi da ta sanin amsa shi,
sai ma duk ta ji tausayin shi ya kamata,ta ji kamar yana kuka. Abbanta zai ji daɗi
in yaji labarin nan kuwa? Ƙila ma ya ce ba zai yafe mata ba. Da sauri ta tashi ta
duba agogo,sha ɗaya saura, ta ɗauki ɗari biyu ta fita, da sanɗanta ta fice bakin
titi ta siyo kati ta dawo ta shige. Sai da ta kulle ƙofarta ta hau katifarta ta
loda katin, gabanta yana ɗar-ɗar ta soma kiran layin shi kasancewar wannan ne karo
na farko da ta taɓa kiran shi.
Dai-dai lokacin shi kuma yana ta neman layin Abba don ya shaida masa ya haƙura da
auran, amma wai layin is switch off,sai ga call ɗin A'isha Beby kamar yanda ya
rubuta a cikin wayar tashi. Ya tsura ma sunan ido, kada dai idanunshi ne suke mishi
gizo? Ya dai ɗauka ba tare da yin magana ba,ta ce "Uncle" ya ce "Na'am" ta ce
"nifa ban zarginka,don Allah kada kayi fushi dani ko da na samu labarin tun a
school ne na san dai an confuse amma ba dai na yarda bane,don Allah in nayi laifi
kayi min afuwa." Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce "ba ki da laifi Beby, domin nima
sai da nace a'a Abbanki ya ce babu damuwa, amma bari kiji wani abu,kin ga ke
yarinya ce ko? Amma zan rantse miki da wallahi-wallahi ban taɓa shan jini ba, duk
wani laifi game da sicret cold zargi ne,ban san shi ba, batun mutuwar matana ƙarar
ƙwana ce kurum,kin yarda da haka? Jikinta a sanyaye ta ce na yarda,ya ce "to Beby
ki ƙwantar da hankalinki, addu'a za ki dage da yi Allah ya zaɓa mana abin da ya fi
zama alkhairi kin ji ko?" Ta ce "to,kaima ka daina fushin? Ta ci gaba kada fa ka
sanar da Abbana," ya yi ƴar dariya bana fushi da ke, kuma insha Allah ba zan taɓa
yi ba, itama ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce "to sai da safe,ka kwanta. Ya ji
daɗin kalmarta, sannan ya ce "to zan yi yanda ki ka ce,kema ki ƙwanta tare da
mafarki mai daɗi na twins ma su kama da face ɗin ki,ta kashe wayar da sauri.
"Me ka ke nufi da waɗannan kayan?" Ya dube ta "Na ki ne mana" ta taɓe baki, "Ni fa
gaskiya duk zannuwan nan ba suyi min ba,babu kala ta, maimakon ka bani kuɗin na
saya da kaina? Kuma ina son canza kayan ɗakina, sannan ga su Suby." Ya ce, "Jummai,
gaskiya ni dai ba zan bada kuɗin wasu kaya ba,kin san nawa na siya waɗannan kayan?
Game da gyaran ɗaki dai zan baki dubu ɗari,su Suwaiba kuwa dubu hamsin zan bada
kada a kuma damuna,cefanen gida kuwa mun gama magana da Uche,ya rubuta komai." Ta
sake fusata, domin ta kula ma ƙwangilar da take so ta yi bazata samu ba kenan,
komai ƙit da ƙit? Ta dube shi "don kurum zakayi aure, sai ka dinga komai faɗa-,
faɗa? Ga wani maƙo da ka koya,da Uche ne yake faɗin abinda ake so?" Ya ce,"to ke ko
yaushe baki gida kin ma fi ƙarfin ki ce min zaki guri kaza,koda a waya ne sai dai
na dawo baƙya nan, lokaci ya ƙure min dole na sauke abubuwan dake gabana, Uche kuwa
shi ne yake girkin nan,don haka shi ne yasan abinda za'a nema.
Ta ce, "Kana lokaci ya ƙure,ba saura sati uku bane bikin? Ta ce, "batun lefe fa?
Sai ka kawo a haɗa" ya ce ai lefe ya daɗe a gidan su amarya." Ta miƙe cike da
masifa.
"Lallai Alhaji Saddiƙ aurenka na wannan karon ya banbanta da na baya, wannan karon
aƙwai ƴar zargi." Ta soma kuka, "maƙiyana sun samu galaba,wato lefen ma ban isa ko
gani inyi ba, na gode." Ta fita tana cewa gara daka nuna min babu ruwana abinda
babu ruwan mutum ai daɗin ji ne da shi. Ya bita da kallo,wato ita bata san ma ta
mishi laifi ba,bare ta bashi haƙuri ko ta mishi bayani shi ne ta zo tana tuhumar
shi,ya samu labarin ta saida motar da ya siya ma su Safiya da Suwaiba, domin wanda
ya gyara motar ne yake sanar dashi lokacin da ya je ɗaukar tashi motar. Da be ga ta
su Suwaibar ba yace sun zo sun ɗauka ne? Sai yaron mai gyaran motar ya ce, a'a wani
ne yazo ya ɗauka, kuma ya gaya mishi cewa Babanshi ne ya sayi motar. Alhaji Saddiƙ
shi dai alwashi ya sha ba zai ƙara sai wa yaran koda mashin ba.
"To kin ji yanda muka ƙwashe da Alhaji,babu abinda ya fi bani haushi wai har an kai
lefe bani da labari saboda rainin hankali, ke kayan faɗar kishiya ma shi ya siyo
min, saboda haka ina son mu koma gurin Boka, gashi bakon ya ce in biki ya rage
ƙwana goma in koma,to gashi yau sauran ƙwana taƙwas. Tunda jiya tara ya ce min ne
ko nawa ne ma oho."
Hajiya Kari ta ce, "To gobe sai mu je,in ce dai kin binne abin da ya baki?" Ta ce
"ina fa ni ban fa san taƙamaiman lokacin ba sai jiya,na san zai kama zigar waɗannan
ƴan iskan ƙannan nashi ne" Hajiya Kari ta ce "Bari mu gama da amaryar, har su ba
za'a barsu haka ba, sai mu shiga tsakaninsu." Hajiya Jummai ta ce, "Da ko kin
taimaka min,ba ma dai irin tsinanniyar Nafisan nan, gashi yafi ji da ita duk cikin
su."
Ta binne surkullen da aka bata,ta kuma yayyafa na yayyafawa kamar yadda aka umarce
ta. Sannan ta nutsu don tana son samun kuɗi a hannunshi, duk da wannan karon ya
tsuke mata bakin aljihunshi, ta samu dai-dai gwargwado.
Lokaci na ta zuwa gida kam ya sha fenti da gyara, yanda ya ba ta kuɗin canjin kayan
ɗaki, haka ya ba su Fatima da Sadiya da Nafisa kuɗi su siyo na ɗakin A'isha, sannan
shima nashi gefen sai da ya canza komai. Nan fa ta tada balli kan cewa shin wannan
amaryar ta fi sauran ne yake ta faman kashe kuɗi har da sa mata kayan ɗaki? To ba
zai yiwu ba,ya ce Jummai ki daina tada jijiyar wuyanki akan abinda ba za ki hana
ba,yarinyar nan ko ba ni ne zan aureta ba kusan dole ne in mata kayan ɗaki,
ballantana gidana za'a sa,kina cewa ba zata yiwu ba,za ki hana ne? Kema fa na baki
haƙƙinki."
Ranar ɗaurin aure ta kasance asabar,don haka ƴan ango sun iso juma'a domin ana gama
ɗaurin aure za'a ɗauki hanya da amarya. Alhaji Saddiƙ ya kasa zuwa ɗaurin
auren,waya ya yi wa Friend ɗin shi kan cewa ba zai samu zuwa ba,don ba ya jin daɗi.
Lafiyar shi lau sai dai yana ganin kamar za'ayi ta nuna shi,ko kuma Friend ya
shaidama ƴan'uwanshi halin da ake ciki,ko su iyayan in sun ganshi su dinga mishi
kallon wanda zai yi musu sanadin ƴarsu da dai sauran tunani kala-kala.
Daren juma'a aka sanya amarya a lalle,ba ta saka kowace ƙawa ba, sai dai ƴaƴan
ƴan'uwa sa'anninta. Da dare suna ƙwance a kan katifa zuciyar A'isha cike da tunanin
gobe zata rabu da Ummanta da Abbanta,ƙila ma rabuwar kenan. Hawaye ne suke bin
gefen kumatunta, wayarta tana ta ruri. Naja ta ce Amarya wayar ki na neman agaji,
A'isha tasa hannunta ta lalubo wayar,muryarta a dusashe ta ɗaga wayar tare da cewa
"Assalamu alaikum, Nafisa ce?" Ta ce "amaryar mu,na so in zo ban samu zuwa ba, sai
dai in kin zo gobe mun haɗu, " ta ce "to ina yini ya ya su Hajiya? Nafisa ta ce,
kowa lafiya, gama Hajiya nan,sai dai nasan ba zata ɗaga wayar ki ba saboda Brother
ɗinmu ɗan fari ne,tana mishi kara.
A'isha ta ce,to ki gaida ta,ta ce to ga Uncle ɗin naki dama yazo ne nace ya kira
min ke gobe. Ta ɗan yi ƙasa da murya kada ki manta da addu'o'i daren yau, saboda
Allah ya yi mana jagora a cikin ɗaurin auren da za'ayi a gobe. Shiru kawai A'isha
ta yi mata, sai kawai ta ji Muryar Uncle yana cewa, Beby kina jina? Ta ce eh,
zuciyarta kuwa sake karyewa ta yi hawaye ya shiga sintiri a kumatunta, ya ce na
kasa zuwa ne Beby sai ina ganin tamkar ban yi wa mahaifin ki adalci ba, ina jin
nauyinsu, kukan da take maƙalewa ya kufce mata, ranshi ya daɗa tsinkewa, ya ce
"A'isha kiyi haƙuri daina kukan zan yi miki magana ne," ta share hawayen ta sannan
ta yi ƙoƙarin tsaida kukan ta ce, ina jin ka, ya ce ina son ki tashi daga wannan
kukan ne kiyi alwala, nafila za kiyi tare da addu'o'i kin ji ko? Alkhairin da ke
tare da auren,ki tsaida zuciyarki,ki daina wasi-wasi,ki saka a cikin ranki cewa duk
yanda Ubangiji ya yi dake dai-dai ne,kin amince?" Ta ce "Uncle dama ni bani da wani
zaɓi sai wanda Allah ya yi min, sannan zan yi duk yanda kace." Ya ce yauwa Beby sai
da safe.
Naja ta dube ta, Angon yayi lallashi kenan mu ko munyi mun gaji kin ƙi kiyi shiru?
Ɗan murmushi ta yi sannan ta ce,Naja kenan ba zaki gane ba ne, sannan ta tada
sallah. Sai ya kasance wannan dare duk wanda yasan halin da ake ciki tsakanin
Katsina da Jigawa idanunshi biyu ya kwana, kuma tsaye gaban Ubangiji, ana ta kai
kuka. Zuwa wayewar gari kowa ya tattara komai ya miƙa wa Allah, sai sauraro duk sun
nutsu da cewa duk abinda Allah ya yi daidai ne.
A'isha kam sai ta wayi gari zuciyarta sake duk ƙuncin da take ji ya washe, sai dai
ɗan abinda ba za'a rasa ba. Hakan ya yiwa Umma daɗi har ta isko Abba cikin
ɗakinshi,tana shaida mishi cewa...
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu
matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
######
____________________________
*📗MUMMUNAN ZATO📗*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
Shaida mishi cewa yau kam A'isha ta saki ranta,suna cikin zantawa sai ko ga A'isha
ta yi sallama domin gaida Abbanta, bayan ta gaisheni ne ya ce "yauwa ƙawar Ummanta
dama ina son in kira ki domin inyi miki nasiha duk da cewa tun da bikin nan ya
matso muna tayi miki,na farko dai nasihar da zan miki ita ce, zaman aure ya
banbanta da zamanki na gida,don nan iyakaci kici abinci ki ƙwanta da dai sauransu.
Yanzun kam da zaran an ɗaura aure Akwai wasu haƙƙoƙi guda goma da suka hau kanki na
mijinki.
Na farko shine ki yi masa biyayya duk abinda ya ce kiyi,ki yi masa, matsawar bai
saɓawa addini ba, kamar yanda ki ka sani babu biyayya ga abokin halitta don saɓawa
mahalicci.
Kima zama mai tsafta kamar yanda ki ka ga Ummanki tana yi, tsafta bata jiki kurum
ba har da muhallinki.
Ta dubi Abba da sauri kamar tana neman ƙarin bayani, domin A'isha yarinya ce sannan
ba wai suna zama da ƙawayanta suna hirar samari ko ta aure ba ne,haka nan bata da
wata ƙawa wadda ta yi aure ballantana ma taji labarin zaman auran, kazalika ita ba
ma'abociyar karance-karance ba ce, ita ana ta zaton in an mata aure zata na girki
tana kai ma mijin ruwan wanka tasa mishi na buta kamar yanda ta gani Ummanta tana
yi, sai ko gyaran ɗakin Abbanta da Umman bata bari wani ya yi sai ita.
Abba ya katse mata tunani da cewa, ma'ana in ya neme ki kada ki guje shi, Umma ta
ce,nima na miki duk nasihar da ta dace,na sani ke dama mai biyayya ce,ki girmama
ƴan'uwansa,ki ɗauki mahaifiyarsa tamkar taki, haka mahaifinshi, matarsa ki yi mata
biyayya."
Hawaye suna zuba daga idanunta, ta ce insha Allah zan yi Abba da Umma, suka sa mata
albarka tare da yafe mata,ta miƙe ta fita suka bita da kallo cikin tausayin ta
yayin da ita kuma ta wuce cikin tsananin damuwa.
Ƴan ɗaurin aure sun hallara in da aka ɗaura aure. Maroƙiya ta shigo tana rangaɗa
guɗa, A'isha dai-dai lokacin tana wanka wanda Umma Rabi ta matsa mata ta yi umma
Rabi ƙawar Ummanta ce,tun suna dutse tana fitowa ta ji gidan ya kaure da guɗa, duk
sai taji wata fargaba a cikin zuciyarta. Inna Uwani Ƙanwar Umma, ita ta ciro mata
wani leshi baƙi mai ado, ruwan lemon zaki tasa ka,sun bata siket da bes da kuma
pant duk baƙaƙe.
Aunty Hasiya mata ƙanin Abba ta ce ni ban ga ma rigar nono ba cikin kayan? Umma ta
ce ba a saka ba, Umma Rabi ta ce to me za'a sakama ƙirjin ba komai, ita dai A'isha
tana jin su, Ummanta ta ce kin ji saka kayanki ki tafi nan duk iyayan banza ne suka
taru. Ta gama shirinta ta fita, bayan an ɗan natsa da gama ɗaurin aure sai kuma aka
shiga shirin tafiya Katsina,kai amarya. Duk wanda ya cancanta ya yi wa amarya
nasiha ya yi mata,dangin Uwa da na Uba. Idanu ta zuba ma Ummanta a zuciyarta tana
raya cewa, ta yi wa mahaifiyarta kallon ƙarshe. Haka nan aka fita da ita tana ta
rusa kuka.
Abbanta da sauran mutane suna waje gurin mota suna ta ce waɗanda zasu je
Katsinan,don kowa yana son zuwa, kuma tafiya ta gari ba kusa ba,don haka suka ce
dole ne wasu su haƙura ba kowa da kowane zasu je ba, an fito da ita tana cin kuka
ganin Abbanta sai kuma ta ƙwace ta nufi gurinshi.
Ya riƙe mata hannu yana cewa haba menene haka kuma? Ganin yanda take rusa kuka har
ma wasu daga cikin dangi suma sun soma taya ta, sai Abban ya kama hannunta ya ce,zo
muje, ɗakinshi suka je ya zaunar da ita ya shiga lallashinta da cewa menene na
damuwa bayan ta yi musu biyayya sannan ya san Friend ɗin shi zai kula da ita,
zatayi karatun ta duka biyun, kuma suma da an ƙwana biyu za su zo shi da Ummanta.
Ya miƙe ya ɗauko alƙur'ani izifi sittin da fiƙihu da Tauhidi ya ce ki riƙe wannan
kin ji A'isha?" Ta share hawayenta tasa hannu biyu ta amsa tare da cewa , to Abba
da gaske za kuzo? Ya ce in Allah ya so, tashi muje ga mutane can sun shiga mota ke
dama ake jira. Allah ya yi miki albarka zan kira ki in kun isa,ta ce to. Abba da
kanshi ya kai ta har mota inda ta zauna tsakiyar Inna Uwani da kuma Aunty Rabi
matar ƙanin Abba. Suka nufi Katsina bayan ta yiwa gidan su kallon ƙarshe, tare da
duban Abbanta da Yaya Abdulrahman Munnir da kuma Jafar.
Alhamdulillah ƙarfe free Pages kenan idan baki siya ba kiyi ƙoƙari ki mallaki naki
akan farashin masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son PAGES ₦400 idan
kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```1632036584
Sa'adatu Balarabe
Access Bank,a turo shaidar biya ta 09068032427 wancan account ɗin namu ya samu
matsala ne, idan mun gyara zamu dawo dashi```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari
sai kin shirya sai kiyi magana*
##########