Jinnul Aashque by Yar-Fillo-1
Jinnul Aashque by Yar-Fillo-1
Jinnul Aashque by Yar-Fillo-1
🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
_NA_
_HARIRA ALIYU_ ( *Yar Fillo*)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*Bissmillahirrah manirrahim*
Fatan alkhairi ga kowa inafatan za ayimin hakuri abisa ga wasu kura kuran da kila
zanyi
AGE📕 1⃣
Gid'ane madai-daici dayike cike taf da jama'a idan kakalli kowa zaka fuskarsa
dauke da farinciki da annashuwa banda wacce akayi taron da gayyar dominta
Kallo daya zakamata kagano tashin hankali da tsananin fargaba atare da ita
Batawuce seconni batare data duba agogon wayarta ba faduwar gabanta na dada
tsananta
Babbar aminiyarta ce tafahimci halin datake ciki ta matso gab da ita tafara magana
ahankali
Kai kawai Rauda tagyada ma salma dantasan bazata fahimci tashin hankalin
datakecikibane
Hakanma bakaramin dauriya takeyi ba
Tajinjina kai tare da kara lalubar numbansa amma har lokacin akashe
"To"
Me lallen tace batafi minti biyar ba kuwa tace tagama
Mikewa tayi ganin mama tashigo suka shiga dakin matar gidan dasuke lallen
"Salma bansan yazanyi da rayuwata ba tundazu nike kiran wayar umar batashiga,gashi
yanzu biyu harta gota amma banji alamun wani nasa yazoba bare maganar daurin aure
ba
Salma inason umar bantaba son wani kamar yadda nike sonsa ba,idan narasasa bansan
yazanyi da rayuwata ba......
Salma tasauke ajiyar zuciya hakika itama tagama karaya amma bataso ta nunama Raudan
bataso hankalin raudan yakara tashi
yaye labulen dakin tayi dasauri wanda ke fuskantar cikin layin tafara hange hangen
inda zata hangosa
Daga can nesa tahangosa cikin abokanansa yasha wata purple din shadda abunka ga
fari tas
Kallon salma tayi tana yar dariya "karkiga laifina kawata kinsan yadda nike sonsa
kuwa?
"salma bazaki gane bane aure biyu anafasawa dole hankalina yatashi bare umar danike
sonsa kamar raina"
"allah dai yasa yadda kike son umar shima yana sonki haka"
"lallai salma bakida saiti,tunda nike aduniya bantaba yima umar musu ba
Ko bani da lafiya nakasa cin abinci idan yacemin inci sainaci kobadadi
Anguwa ma haka idan yace kar inje to ko inason zuwa fasawa nikeyi
Kekomai idan Umar yace inyi atake nikeyi bana bata lokaci
Bare kuma abunda ya dade yana muradi sai kawai in hanasa saboda wani ajin
banza......
Yanzu nasan ko rijiya Umar yace kifada fadawa zakiyi wannan soyayyar taki tayi yawa
wallahi
Jama a sunshaida
Fatiha
"madam yadai"
Kinsan hidimar bikinnan jiya agajiye nakoma gida dasafe kuma mutanene suka
addabeni da kira
Shiyasa nakashe"
Numfashi tasauke
"kasani cikin fargaba da tsoro bazan iya kwatantamaka tashin hankalin dashiga ba"
"jaana"
(sunan datake kiransa kenan)
Ya katseta
"chuchu inasonki fiye da yadda kikesona,
Zan iya yin komai akanki zan iya yin komai dan inga nakasance
Tare dake har abada
Kece farinciki
Lumshe idanuwanta tayi wasu hawayen farinciki masu dumi suka gangaromata
Murmushi Rauda tayi,tayi kasa da muryarta tare da kara matse wayar akunnenta
Yarfillo
[20/10, 8:34 pm] Sumiee B.: 🌹JINNUL
AASHQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU( *Yar Fillo*)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
AGE📕 2⃣
Motocine manya masu tsadan gaske sukazo daukansu zuwa gurin reception din
ansha shagali sosai saikarfe bakwai akatashi Harsu salma sunshigo motar datake
Tanazaune tayi shuru tana tunani batasan yashiga motarba harsaida yashafamata wuya
Ya gyada kai
"ook fadamin wani hotel kikeso muje mukwana"
Yadaga gira
"yes hotel ko da aurena zan kwana nikadaine?
Ta rausayar da kai
"dan allah kabar wasa mutafi gida"
"mene bazeyuwuba?
Tasauke numfashi
"tayaya bamu tare ba zamutafi hotel?
Ganin zetada motar yasa tarike mai hannu tana langabar dakai
"jaana please kayi hakuri kasani bazantaba iya yima musu ba amma hakan badai dai
bane
Kallonsa kawai takeyi tasan ransa yabaci itama saitaji zuciyarta babu dadi
"jaana.....
Zatai magana yayi saurin dakatar da ita tahanyar daga mata hannu batare da ya ko
dubeta ba
Tadaga kai
Yacigaba da cewa"to yanzu hanyar gidan nikeyi ai dan haka banason surutu please"
Fakawa yayi agefen titi yazuba mata manyan idanuwansa masu juya mata lissafi
"amma....
Sai lokacin taji hankalinta yakwanta bata kaunar bacin ransa kwata
Taci kuka kamar ranta zefita dan tanada kawa zuci sosai ko tafiyar kwana biyu tayi
allah allah takeyi takoma inko tayi sati to dama wajibine saitayi rashin lafiya
Cikin wata hadaddiyar unguwa suka shiga wani kayatacce fankacecen gida me kama da
gidan sanator
ko nawani gomna gidan yatsaru sosai gaba d'aya wadanda suka rakota sakin baki
sukayi suna kallon gidan
Yan uwan Umar ne suka futo da ga ciki yayarsa me suna kaltum itace tazo tarungumota
Tana rangada buda
Atsakiyar falon anty kaltum tazaunar da ita inda sauran suka zagayeta
"masha allah"
Sauran yan uwansa suka fara fada suna yaba kyanta
Kasa tayi dakanta dangani takeyi kaman zaginta sukeyi yadda sukeda tsananin kyau
har zasu dubeta su kirata kyakkyawa
Suma yan uwan umar din fashewa sukayi yan kaduna suka juyo yan niger suka nufi
masaukinsu
Anty kaltum ce kawai tarage itama kuma tanajiran zuwan angwaye ne takama gabanta
Saida akayi sallar issha sannan umar yashigo tare da babban abokinsa zayyad
Nan itama takarayimusu tata nasihar sannan tamusu sallama shima zayyad yayimusu
nasa
Takakaro murmushi
"kaman kasani jinikeyi kaman intashi inkoma"
"lallai yarinya bakiji dakyau ba keda zuwa kaduna saikin shekara kila ma da jariri
zakijemusu"
Ya jinjina kai
"lallai kam"
Tamike tabude kofar dakin tafara saukowa daga step tana karema falon kallo
Azuciyarta tana yaba kyansa dakuma kokarin mijinnata
Lallai umar yanasonta dayawa dan ko tsinke kinyarda ayimata yayi shi yayi komai
"kwaram"
Taji karar wani plate din yafado
Bata koma dauke plates dinba gaba kawai tayi tarufo kofar kicin din
Dariya yayi
"oh my dear tsoronki yayi yawa wallahi waye zebiyoki?bayan kinsan gidannan dagani
saike?
Hmmmmmmmm
Tasauke ajiyar zuciya
"nidai yanzu bazankara fita nikadai ba saidai muje tare"
Yakwashe kayan yamaidasu gefe sannan yadauro alwala itama yace tadauro
Sallah raka a biyu sukayi yayimata tambayoyi game da addininta ta amsa mai
Magana uku yayi yace "ook kubashi taimakon gaggawa ganinan zuwa"
Waro idanuwanta tayi tana kallon agogo sannan tamaida idanuwanta kansa
"please honey kiyi hakuri naje ance mutumin yana cikin wani hali please....
Dago kanta tayi daga jikinsa
Tazuba masa fararen idanuwanta
"amma kasan bazan iya kwana nikadai acikin gidan nan ba ko?saidai inmutafi tare"
Ya waro ido
"dawa?baze yuwu ba ba bu inda zakije acikin darannan
"chuchu bata lokacinnan danikeyi bawan allahn can ze iya rasa ransa da haka natafi
Bin bayansa tayi da kallo cike da tsananin damuwa dan ita ko agida batasaba kwana
itakadai
Mikewa tayi ta janyo windon dakin dayike abude iska nata kadashi
Tayi karfin halin dawowa bakin gadon tasa hannu tana laluben wayarta
Jitayi antaba mata kafa dasauri tahaye gadon tana karanto duk addu o in da suka zo
bakinta
Yarfillo.
[20/10, 8:35 pm] Sumiee B.: 🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
AGE📕 3⃣
Hannunta na rawa takunna fitilar wayar,tahaska tsakar dakin inda takejin kaman
akwai wani atsaye
Amma idanuwanta sunkasa tsayawa wuri daya kalle-kallen dakin kawai takeyi
Azuciyarta kuma tana karanto addu'o in neman tsari.
Dai-dai lokacin akafara ruwan sama wanda yataho da karfi kaman da bakin kwarya
Hankalinta yakara tashi dantasan yadda ruwan yataho da karfi,to lallai sai anyi
tsawa,itakuma allah ya jarabceta da jin tsoron tsawa
Inbanda ayatul kursiyyu ba abunda bakinta ke iya furtawa,itama din bata kaiwa
karshenta take dawowa farko.
Jin karar sawun tafiyan daf da kofar dakin datakeciki,yasa ta cusa kanta cikin
gwiwo winta
Danbataso taga abunda ze shigo din tasan ba alheri bane
Da karfi tafara karanta ayatul kursiyyu,amma har lokacin takasa dago kanta bare
taga me shigowar,
Saida tadan dauki lokaci sannan tadena kukan takomai sauke numfashi ahankali
"chuchu,meyasa kikeda tsoro dayawane? Bakisan yawan tsoro babu kyau ba?
Wai akanme tasan yaune natare zata kirani,shine yacemin injuyo shi zeduba marar
lafiyan
Karar mota kuma ya zayi kiji?bayan kin sama zuciyarki tsoro,sannan kuma kinmanta
ruwa akeyi?
Tagyada kai
"hakane amma please jaana karka kara barina nikadai wallahi inajin tsoro sai
intajin wasu abubuwan tsoro dayawa"
Tadanzame
"tomiye nasauri jaana,nifa takace"
Misalin karfe uku da rabi,suna rungume da juna yana shafa sumar kanta
"chuchu allah yayimiki albarka hakika ke tadabance kinsanyani farinciki mara
misaltuwa"
ya girgiza kai
"bakisan irin son danakemiki ba chuchu,zan iyayin komai akanki kuma babu wacce ta
isa takwace soyayyata agareki
Riga doguwa tadauko tasa,sannan tasauko daga saman dantasan yana kasan
"ina yaje"
Tayi wa kanta tambayar
"wayace miki haka ake tarban miji?kintsaya daga nesa kina wani cewa ina kwana"
Umar yamike
"kinga jera abincinnan akan dining bari in watso ruwa"
Tadauki kwandon ta kai kan dining din ta jejjera komai,tazauna tana jiransa.
Yazauna a kujerar dake fuskantarta suka fara karyawa yana janta da fira
Ya gyada kai
"ook ai bawan allahnnan ya jigata dayawa motarsa karkashin traler fa tashige da
kyar muka iya ceto ransa danni banyi zaton ma zeyi rai ba"
Tadakata daga kurban tea din datakeyi tana kallonsa dan bata fahimci abunda yike
nufi ba
Ta jinjina kai
"to gani nayi ba kai kayi aikinnan ba,doctor zubairu ne yayi amma kana cewa da kyar
kuka ceto rayuwarsa
Takauda idanuwanta akansa,tamaida kan wayar ta, tana duba sakon da aka turo mata
"to nidai bansani ba,kaida bakinka jiya kace doctor zubairu yace kadawo gida
bekamata kafita aiki a daren jiya ba"
"nace bandawo jiya bani,tunda mukai natafi asibiti bandawo gidannan ba sai a
safiyarnan"
"wai meyasa kaketa wasu maganganu da bangane bane,jiya bakadawo ba,misalin shabiyu
da rabi?
Ta girgiza kai
"saidai in mafarki kikayi danni lokacin ma ina emergency room"
Ta gyada kai
"dan allah kabar wasannan haka"
Hannunta yakama
"kedai zancema wa kibar wasan haka,nida na kwana asibiti zaki wani ce wai nadawo
gida...........
Takatse shi
"jaana please wasan ya isa haka"
"chuchu i'm serious saidai in mafarki kikayi amma ni wallahi bandawo gidannan ba"
Ya jinjina kai
"to nafadamiki mafarki kikayi baki yarda ba.......
"kwana kuma?banganeba"
"jaana wallahi jiya kadawo kacemin doctor zubairu ya amsheka,kuma tare dakai muka
kwana."
Yarfillo.
[20/10, 8:35 pm] Sumiee B.: 🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Wannan page din nakine anty nabila ina godiya da kokarinki gareni allah yabar
zumunci
AGE📕 4⃣
Dire kofin tayi,ranta yadan soma baci,akanmene yikeso yayi mata wasa da hankali?
"wai meke damunka ne? Indawo hankalina kamar yaya?tayaya munkwana dakai zaka cemin
kai ba a gidannan kakwana ba........
"jaana kasan bama irin wasannan ko?dan allah kafadamin dagaske ne baka kwana
agidana?
Idan kiga yananan akalarsa to tabbas munyi nasara a wannan aikin da mukayi na
karshe
Idan kuma kiga yacanza kala zuwa ja,to tabbas akwai matsala
Wannan lemun tsamin yana dauke da magunguna masu karfin gaske kitabbata kinshiga
dashi"
Tanajin umar yana kiranta bata tsaya ba,harsaida tashiga bedroom dinta
Gabanta nafaduwa
Saidai me,tana gama kwance kullin taga lemun tsamin yayi jawur
"Aasim!Aasim!"
Yadagota dasauri
"Aasim kuma?
Kamata yayi suka zauna akan gadon yakura mata ido yana karantar yanayinta
Yazaro wayarsa daga aljihu yadanna numban malan saidai kira biyu yana masa bedauka
ba
Yakuma danna kiran a karo na uku,saida takusan tsinkewa sannan aka daga
"Rauda.....
Sanin kankine kukannan ba bu maganin da zemana face yajanyo miki ciwon kai,
"mafita?a ina zamu samo mafitar jaana?gurin malan isah ne kadai muka sa ran zamu
sami mafita,
Amma gashi,sanadiyyar taimakona har ya rasa ransa nasan.......
Ya girgiza kai
"malan kwanan sa ne yakare,kuma na tabbata zamu samu waraka awani gurin.
Ta jinjina mai kai kawai amma ita kadai tasan tashin hankalin datake ciki.
Shima din dauriya yayi kawai amma zuciyar sa cike taf da da damuwa.
Itako Rauda mafarki takeyi cikin barcinta,malan isa tagani zaune yana lazumi
Saiga hayaki yafara shigowa dakin dayike,kan kace kwabo jijiyoyin wuyansa sun
mummurde,idanuwansa sun kakkafe
Dariya taji anfara yi me tsoratarwa daga bisani taga wani farin saurayi yabayanna
Dariyar ya cigaba dayi,lokaci daya kuma ya murtuke fuska kamar bashi yagama yin
dariyar ba.
Na gargadeka tun farko amma kayi taurin kai kana ganin kaman zaka iya ja
dani......"
Ya mike tsaye yana cigaba da yin dariyar sannan ya dubeta da razanannun idanunsa
"kinsa nayi abunda ban taba yi ba,tunda nike aduniya bantaba kisa ba
"Kiyi babban kuskure a rayuwanki,da kika karya sharuddan dana gindaya akanki
Mafi girman kuskuren da kikayi kuwa,shine dakika bari na kusanceki azahiri..."
"kisani daga yanzu kinrabu da farin ciki,kwanciyar hankali sannan abunda zance miki
na karshe shine
Idan har kinason rayuwar mijinki to tabbas kada ki kuskura ya kusanceki dan duk
ranar daya yi hakan to tabbas ze mutu kamar yadda wannan ya mutu!!!!!
Yakara sa fada yana nuna malan isa sannan yakuma fashewa da dariya
Ya jinjina kai
"zan kasance tare dake,akodayaushe,babu abunda zesameki da izinin allah"
Yarfillo.
[20/10, 8:36 pm] Sumiee B.: 🌹JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU(yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*_A kullum forum dinmu Kara bunk'asa yakeyi,mutanen cikinsa Kara basira da fasaha
sukeyi,ina jinjina ma golden writters Allah yabar zumunci a tsakaninmu_*
_GAISUWA Ga *MATAN K'WARAI* group *yar fillo* na godiya da addu'o inku gareta,ina
Kuma Jin dadin yadda kuke yaba labarina,ina godiya sosai_
AGE📕 5⃣
"Jaana,kayi min alkawarin duk rintsi bazaka taba rabuwa Dani ba,nasan matsala yanzu
muka fara ganinta......
"Chuchu kina tunanin akwai abunda ze bani tsoro har yasa nai tunanin rabuwa dake?”
"Nasan zaka iya jure komai,Amma ina Jin tsoro,nafi kowa sanin waye Aasim,abunda ze
iya?da abunda baze iya ba.
Nasan ze iyayin komai domin yaga yarabani da kowa,baze cutar Dani ba,ina da
tabbacin hakan Amma........
"Kai ze iya cutar da Kai,banason wani Abu yasameka abunda Nike tsoro kenan"
"Kinmanta da cewa Allah Yana tare damu?idan har muka rike addu'a,to tabbas muna
tare da kariyar Allah a kodayaushe.
Dan Haka kikwantar da hankalinki,zankira zayyad akwai wani malami dayace yasani a
k'auyensu,sai muji yadda za'ayi"
"Hmmmmmmmmm!!
Yakuma sauke numfashi
"To Rauda zamu zauna hakane?dole mukuma neman mafita,tun abun beyi k'arfi ba"
Abincin Rana Dana dare duk anty kaltum ce ta aikomusu,Dan Basu da nisa sosai
Bawani cin abincin sukayi dayawa ba,Dan hankalinsu ba a kwance yike ba.
Suna zaune a kan kujera,da daddare,bayan sun kammala cin abinci,yamike Yana maida
sauran kula
Karar da TV d'in falon yikeyi ne yafara damunta,ganin hankalinta bama akan TV d'in
yike ba,yasa tadauki remote d'in dake dake gefen kujerar takashe
Gajeren tsaki taja tamik'e ta zare socket din,tajuyo zata dawo kan kujerar
Takalli socket d'in da ta zare Yana nan akasa Amma Kuma TV Yana aiki
Ta kalli cikin TVn,wasu mutane tagani a zazzaune sanye da bak'ak'en Kaya sunyi
kasa da kansu suna karatu da wani yare
Zuwa can suka d'ago suka kalleta da manyan idanuwansu da yike bak'kk'irin babu wani
alamar fari acikinsa.
Zuciyarta tafara bugawa da k'arfi kaman zata fito waje saboda tsananin razana
"Suwaye?”
Yatambayeta dasauri
Addu'o I yadinga tofa Mata,zuwa can tadena sambatun datakeyi, Takoma sauke ajiyar
zuciya
Ya dauko wani tawul din yafara gogemata gashin kanta daya jike yayinda tashiga
bayin
"Aduk sanda kika ga wani Abu na tsoratarwa,ki rinka ambaton sunan Allah kikuma
dungayin addu'a,
"Bazan iya zama agidannan ba,bazan iya ba,ka maidani gida Dan Allah"
"Ko zaki iya gaya min yanayin da mama take ciki a halin yanzu?
Nasan tana cikin farin ciki,da jin dadin kinyi aure,abunda tadade tanason tagani,
Me kike tunanin zataji idan har ta fuskanci kina cikin matsala a halin yanzu?
"Nasan zata shiga damuwa,da tashin hankali,wanda ze iya tado mata da ciwonta,sam
komawarki gida ba mafita bane
Ta yayama daga yin auranki kwananki daya da tarewa ace kinkoma gida,me kike tunanin
mutane zasu ce?
To bazan kara zuwa ko nan da can batare dake ba,ba abunda ze koma tsorataki ina
tare dake"
Yak'arasa fada yana share mata hawayen dake gangarowa daga idanuwanta
Amsa tayi tana dubansa,shid'inma ita yike kallo ganin nawin cire kayan takeyi
agabansa yasa yace
Ya jinjina Kai
"Eh,Amma ai naga nawin cire kayan kikeji agabana,shiyasa zanfita"
"To canza"
Ta marai-raice fuska
"Kayi hakuri"
Cikin sanyin jiki ta war-ware k'aramin gyalen da ke kanta tadan daura a k'irjinta
Sannan tafara yaye doguwar rigar dake jikinta,cikin sauri tacire rigar tasa hannu
zata d'auki rigar baccin
Dakatar da ita yayi tahanyar rik'emata hannu
"Menene kuma?
Ya girgiza Kai
"Ina sane banmanta ba"
"Amma......
Yakuma katseta
"Chuchu duk wad'annan abubuwan dakika ga anayi,anayine dan ahanamu samun cikar
burinmu,shiyasa aka biyo ta wannan hanyar dan aga ankauda tunaninmu akan abunda
mukadad'e muna muradi"
Ta girgiza kai
"Amma ai ba ayau ba,kabari sai mundawo cikin natsuwar mu tukunna.......
"Kada kibawa azzalumai damar cin galaba akan rayuwar auranmu,nasan da zarar mun
cika burinmu to tabbas wannan tsoratakin da akeyi za Adena,Dan dama anayine Dan aga
ancanza mana tunani
"Idan har kanason rayuwar mijinki to tabbas kada ki kuskura ya kusanceki Dan duk
ranar da yayi hakan to tabbas ze mutu Kamar yadda wannan ya mutu"
Aduniya babu abunda ta tsana irin taga b'acin ran Umar,Amma yaza ayi ya fahimci
irin abubuwan datake gani na razanarwa??
Juyowa yayi ahankali yana kallonta,ya sakar mata murmushin karfin Hali
"Kada kidamu kanki,ki hawo kikwanta,nima nasan ba dai-dai bane inbukaci hakan
agareki awannan yanayin danike ciki
Amma idan muka ce zamu biyema wannan al'amarin haka zamuyita zama,kuma kimin uzuri
kinfi kowa sanin hak'urin dana dad'e inayi"
Ta jinjina Kai
"Nasani,amma ka gafarceni tukunna Dan Allah"
Sai dai babu amai babu labarinsa sai uban kakarin datakeyi
Sai dai me? A memakon taga ruwa saitaga jini nata bul-bulowa
Baya tayi dasauri tana murza idanuwanta Dan tabbatar da jinin datagani
NA
HARIRA ALIYU (yarfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
AGE📕 6⃣
Bacci yikeyi sosai,tafashe da kuka tana dafa kanta datakeji yanayimata wani irin
ciwo Kamar ze rabe biyu
Washegari
Anty kaltum da yaranta anan suka wuni,hakan yasa tad'an saki sai yamma suka tafi
"Yanzu,ko anjima?
"Yanzu mana,"
Ya bata amsa
Ta gyad'a kai
"To muje karakani d'akin"
Bedroom d'inta suka shiga tasauya kayan dake jikinta zuwa ga bak'ar jallabiya
"Muje nagama"
"Chuchu!
"Chuchu,zuciyata tana bugawa da k'aunarki ne,a duk sanda nakalleki inajin k'aunarki
na k'ara bin jinina da dukkanin jijiyoyina......
Tayi guntun murmushi tare da kama nasa hannun tad'aura akan nata k'irjin tace
"Nima haka, kodayaushe zuciyata bata wani abun da take ambato face sunanka,ina
sonka fiye da yadda Nike son kaina,fiye da yadda nike son rayuwata,bazan iya rayuwa
idan babu Kai na"
"Ina alfahari da samunki danayi amatsayin Mata,zankasance tare dake har k'arshen
rayuwata"
Har lokacin murmushi be bar fuskarta ba
Saida suka shiga motar me gadi yabud'e suka hau Kan titi sannan yace
"Uhm muje.......
Ya ketseta
"Wajen shan ice cream ko?
Ta jinjina Kai
"Hakane,kumafa na kwana biyu bansha ba,tun zuwan dakayi kaduna wancan karen dakazo
mindashi"
Ya gyad'a Kai
Wuri me kyau suka zauna aka kawo musu ice cream d'in,suna sha suna fira cikin
nishad'i
Suna shiga falo ko zama basuyi ba,ya fizgota jikinsa yana shisshin shina wuyanta
cikin wani irin yanayi
"Jaana please"
Yayi nasan cafkar labb'anta masu ban Sha'awa aduk sanda take motsasu gurin yin
magana
Kissing d'inta yafarayi azafafe,yana shasshafata
K'arfinta tasa gabad'aya,ta turesa tare da janye jikinta tana maida numfashi
"Chuchu idan kika hanani yin abunda zuciyata take muradi ahalin yanzu,wallahi
zanshiga wani Hali,kitausayamin please......
Zuciyarta tafara karyewa,hak'ik'a tana tsananin k'aunarsa tana son tafaranta Masa,
Amma yazatayi?idan wani abu yasamesa fa?
Yak'arasa fad'a Yana sakinta yakoma kan kujera yazauna,ya lumshe manyan idanuwansa
shikad'ai yasan halin dayike ciki
Sun d'auki lokaci ahaka,daga bisani yataso yadawo inda take durk'ushe
Kafin tafito haryaciro mata kayan bacci,hakan yak'ara mata tausayinsa sosai
Bayan tasa kayan tazauna kusa da shi tare da kama hannunsa ta matse cikin nata
Amma.......
"Nacemiki nafahimceki meyasa kikeson nanata abu d'ayane,alfarma d'aya kawai Nike so
kimin"
Yacigaba dacewa
"Inaso muraba d'aki wajen kwanciya,kikwana a naki in kwana anawa,saboda aduk sanda
nike tare dake hankalina tashi yikeyi.........
Ta katseshi
Ya jinjina kai
"Nasani amma hak'uri zakiyi, Kamar yadda kika rok'i alfarmar in k'yaleki nakuma
k'yaleki
Nima kimin wannan alfarmar dan Allah ta wannan hanyarce kad'ai zansamu sa'ida"
Yace
Ya durk'uso yanayimata murmushin k'arfin Hali tare da manna mata kiss a goshinta
"Good night''
Yafad'a yana ficewa daga d'akin tare da rufomata k'ofa
Shiko Umar bedroom d'insa yashiga,yashiga toilet tare da sakar ma kansa ruwan sanyi
Yafurta ahankali
Janyo tawul yayi yad'aura ya janyo wani yana goge gashin kansa
Itako tana zaune gefen gadon tana rarraba idanu,dan gani takeyi kamar zataga wani
abun tsoro
Sama-sama taji andafa mata kafad'a,tabud'e ido cikin yanayin bacci tana kallon
kafad'ar,wasu dogayen yatsu tagani bak'ak'e sid'ik tare da zak'o-zak'on k'umbuna
Motsi tafara ji ak'asan gadon, hakan yatabbatar mata abunda yatab'atan yana
k'ark'ashin gadon
Hanyar fita d'akin tayi,ta murd'a hannun k'ofar amma gam tak'i bud'ewa,
Wayam babu kowa,bubbuga k'ofar tayi tana kiran sunan Umar,amma shuru
Wani kalan gurnani tafaraji me tsoratarwa yana fitowo daga cikin bayi
Bam!
Aka banko k'ofar bayin,runtse idanuwanta tayi dasauri tana ambaton sunan Allah Dan
tasan shikad'ai ze kawomata agaji
"Habibty!
Yanayimata wani irin kallo da idanuwansa masu d'auke da k'wayar ido kalar golden
Yacigaba da cewa
"Barka dai habibty,barka da dare"
"Dan.....Dan.....Allah...kayi.... hak'uri'
Girgiza kai tayi jikinta na kyar-kyarwa kamar wacce akaciro daga cikin k'ank'ara
"Kinfi kowa sanin bana nanata magana sau biyu,idan bazaki taso ba to akwai wad'anda
zasu taso dake
Yana gama fad'a kuwa taji anciccib'eta and'agata sama amma kuma bata ganin wad'anda
suka d'agatan
Tana ihu kuma amma ihun baya fita
Kan gadon aka direta, gabad'aya jikinta ya mutu bata da kuzarin dazata iya guduwa
"Tun kan asan za a haifeki nike karanta al'qur ani,yanzuma zanso ace ni nike
karantamiki tunda naga arud'e kike wasu ayoyinma ba dede kike karantasu ba"
"Sabida ba'ayiki dan kowa ba,anyiki ne danni kad'ai,kuma dani kad'ai zaki rayu,ina
sonki habibty bazan tab'a iya rayuwa babu keba.........
Runtse idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi suna gangaro gefen kuncinta
"Rauda!!!!!!
Yakira sunanta
"Kicire tunanin cewa zanrabu dake arayuwa,Dan wallahi babu wani malamin da ya Isa
yarabani dake"
Y'arfillo.
[20/10, 8:37 pm] Sumiee B.: 🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
_Kuna a raina yan uwana yan *Golden Pen* hadin kanku na burgeni hakika kun cika
Zinarai, kuma yan Amana, inama yan k'ungiyoyi zasuyi kuyi daku yan uwana, da tabbas
zasu samu ci gaba, wlh *Golden Pen* kun hadu dari bisa milyoyi, bani da abunda zan
baku shiyasa na baku wannan page kuyi yan da kukeso dashi na bakushi kyau ta,👌_
AGE📕 7⃣
"Rauda!!!!!!
Yakira sunanta
"Kicire tunanin cewa zanrabu dake a rayuwa,Dan wallahi babu wani malamin da ya Isa
yarabani dake"
Tanaso tayi magana amma taji bakinta yayi mata nawi takasa motsashi,kamar yadda
takasa motsa koda d'an ya tsanta
Bakisan cewa wa'annan kyawawan labb'an suna d'aya daga cikin manyan dalilan dana
kasa rabuwa dake ba??
Ya matso da fuskarta kusa da tasa,dan har lokacin gashin kanta na damk'e a hannunsa
Kallon lips d'inta yikeyi
Bata da ikon hanasa dan bata da yadda zatayi, in Banda rad'ad'i babu abunda lips
d'in kemata
Wani kalan yanayi taji tafara shiga, ahankali tunaninta yafata tsayawa taji kanta
yanayimata waiwayi take wani kalan bacci me cike da wahala ya d'auketa.
Washegari,ana kiran assalatu tafarka, tabud'e idanuwanta dasukayi mata nawi tana
kallon cikin d'akin
Ajiyar zuciya tasauke tatashi daga kwanciyar datake ta jingina da jikin gadon
Nannauyar ajiyar zuciya tasauke tana tunanin yadda zata cigaba da rayuwa da aljani
amatsayin mijinta bayan kuma ga nata mijin yanaso yarabata dashi
Sannan tafito falon lokacin gari yafara haske, bedroom d'insa ta nufa dan bataji
fitowarsa sallah ba
Sassanyar ajiyar zuciya tasauke tasa hannu a gefen fuskarsa tana shafawa ahankali
Dasauri yakoma yazauna yana d'an runtse idonsa alamar ciwon na damunsa
Rauda tace
"Lafiya jaana?
"Cikin dare amma nasha magani nasan zebari nan bada jimawa ba"
Itama tazauna suna fuskantar juna tafara tsiyaya ruwan zafi a Kofi
"Babu komai"
Dasauri ya dafa cikinsa,tasowa tayi dasauri ta dawo inda yike tana tambayar
"Jaana cikinne?
Hankalinta yatashi
"Fad'amin inda maganin yike in d'auko maka"
Ya girgiza Kai
"Aa,d'auko min wayata kawai inkira doctor zainab nasan yanzu bata wuce asibiti ba
sai ta biyo takawomin allura"
Tad'auko mai wayar tamik'amai har lokacin yana dafe cikinsa
Tace aa
Yafad'a mata
Tace
"To shikenan ganinan zuwa yanzu insha Allah"
"Chuchu bafa wani abu bane,inayin alluran zedena dama nasaba irin ciwon kada
kid'aga hankalinki please"
Doctor zainab ta fahimci abunda yike damunsa tsaf hakan yasa data mai allura zata
wuce tacema Rauda tana son magana da ita
A falo suka zauna,Rauda zata had'amata tee tacemata tabarshi ta k'oshi tazauna suyi
maganar kawai
Kuma dama tsoro wajibine ga duk macen da takai budurcinta gidan mijinta
Amma yanzu kai ya waye andaina wannan k'in amincewar,kuma miyema abun gudu ga wanda
yazama muharraminka?
Bakisan idan Sha'awa tayiwa namiji yawa tana iya halaka saba?
Wannan ciwon cikin dakikaga yanayi somin tab'i ne inhar bazaki yadda da mijinki ba
"Dan allah ki ajiye wani tsoro da fargaba agefe ki bawa mijinki kulawa kinji?
"Nizan wuce nasan yanzu yasamu bacci dan allurar tanasa bacci sai anjima"
Rauda tamik'e tayimata rakiya zuwa k'ofar falo sannan takoma d'akinsa
Ganin yasamu bacci yasa ta janyo mai k'ofar tadawo falo tana nazarin abunyi
Gabad'aya tarasa yadda zatayi,wayarta tad'auko tadanna numban aminiyarta Salma bugu
d'aya salma ta d'auka tanacewa
"Kenan Aasim kwantan b'auna yayi,yayi kaman yarabu dake ashe azzalumin
yananan......
"Ni yanzu damuwata d'aya cewa dayayi Umar ze mutu idan har ya kusanceni,gashi umar
yana matuk'ar buk'atata, kifad'a min yadda zanyi please Salma,ke kad'aice wacce
nike iya gayama damuwata"
"Ina ganin kaman yafad'a miki hakane dan ya tsorataki, Amma baze iya kashesa ba,
Dan ina tunanin umar yafi k'arfinsa tunda har yabari kika auresa"
Ta girgiza Kai
"Bana tunanin hakan"
Salma tace
"To yakamata munemi wani malamin Rauda,zan k'ara yin tunani anjima inga yadda
za'ayi amma kafinnan kinsan y'ar dabaran dazakiyima umar d'in dan ki rage masa
feeling d'in"
Fitowa daga d'akin tayi tashiga kicin tabud'e kular data zuba ferfesun kifin tare
da d'auko plate zata zuba?
Saidai me a memakon taga kifin saitaga manyan b'eraye kwance acikin kular da alamu
sun dahu sosai sai uban turiri sukeyi"
Mamakine ya kamata kodayike ba abun mamaki bane dantasan zata iya ganin abunda yafi
hakama ayanzu
Ruwan indomie ta maida tana tsaye har indomin ta nuna tajuye a plate
"Madam yadai?
"Dede"
Tafad'a tana ajiye plate d'in agabansa
Yayi murmushi tare da kamo hannunta yazaunar da ita a k'asa inda yike zaune
Tagyad'a kai
"To allah yasa mudace"
Ya amsa da amin
"Naka"
Tafad'a
Yace
"Ok tashi muje"
Yakauda kansa yayinda takesa rigar dan bayaso yaga abunda zetada mai hankali
Shiko canza kayan yikeyi yana kallonta,wani irin feeling d'inta na taso Masa
"Lafiya jaana?
"Jaana cikinne?
"Jaana!
"Jaana please kabari sai munje gun malamin tukunna banaso wani abu yasameka.....
Aasim tagani tsaye idanuwansa sunyi jawur yana nuna wani abu da hannunsa
Dasauri takalli abunda yike nunawan, Umar ta hango can saman d'akin jijiyoyin
wuyansa sun mummurd'e idanuwansa sun firfito waje
Wata iskace tad'auketa tahad'a da bango wanda kanta yayi mugun buguwa
"Wallahi bazan k'ara sab'a ma umarninka ba,duk abunda kace inyi zanyi amma dan
allah kada karabasa da rayuwarsa
"Kina ganin kamar bazan iya abunda nace ba ne ko,to yau zanbaki mamaki!!!!
Hannunsa yaja baya, umar yafad'o daga saman yazube a k'asa yana maida numfashi
sama-sama dan ya wahala matuk'a
Dagudu tatashi ta isa gun Umar tana jijjigasa tana kiran sunansa
"Kisani ayanzu dama biyu zanbaki,ko kisa yasakeki ko kuma ki rasasa gabad'aya"
"Ayanzu dama biyu tarage miki, ko kisa shi yasakeki kokuma kirasasa gaba d'aya"
Zayyad naganin kiran yasan ba lafiya ba,ya d'auka Jin muryar Rauda yasa yace
Mik'ewa zayyad ya yi daga kujerar da yike na office dan ranar Yana asibiti duty
d'in dare yikeyi
"What?meyasamesa
Gudu yike yi sosai har ya kawo gidan,saidayayita horn sannan me gadi yabud'e dan
shi baccinsa yikeyi besanma wainar da ake toyawa ba
A tsakar gidan yayi parking yafito dasauri yana bubbuga k'ofar falon
Tasan zayyad ne ta tashi har lokacin jikinta narawa taje tabud'e k'ofar
Hijabin datake sallah dashi dake gefen kujera tad'auko tazura,yashimfid'eshi abayan
motar
Yatada,zata shiga baya yace aa tashiga gaba dan ba inda zata zauna abayan
"Aasim...Aasim....
"Aasim?
Ta jinjina mai kai
"Shikenan idan munje asibiti koda za atambayeki ace meyasamesa kice accident yayi
kinji?
"Kikwantar da hankalinki yadawo cikin hayyacinsa yanzu amma yasamu bacci kina iya
shiga"
Lokaci d'aya harya fad'a,tana zaune tana kallonsa har asuba inbanda kuka ba abunda
takeyi
"Saiyanzu nafahimceki chuchu, saiyanzu na fahimci abundance yasa kika k'i yarda
Dani, Amma inaso kisani babu abunda zesa inrabu dake
Inatare dake duk runtsi duk wuya"
Y'arfillo.
[20/10, 8:37 pm] Sumiee B.: 🌹 *_JINNUL_*
*_AASHIQUE_*🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
AGE📕 8⃣
_Wannan page d'in nakune masoya jinnul aashique,na sadaukar dashi gareku,saboda
k'aunarku ga littafin,ina godiya ga yadda kuke son wannan labari allah yabar
zumunci,sannan ina baku hak'uri akan dad'ewa danikeyi bana typing insha allahu
zanyi k'ok'ori inga ina yin yadda yadace nagode._
Ajiyar zuciya yasauke dan babu inda bayamasa ciwo ajikinsa amma dan kada yak'ara
tada mata hankali yasa yace
"Chuchu nifa naji sauk'i yanzu,wuyanane kawai ked'an yimin zafi,kuma shima nasan
zuwa anjima zedaina insha allahu"
Numfashi yasauke me nawi zuciyarsa cike da tarin damuwa dan shima tunanin nasa ya
tsaya yarasa ta inda ze b'ulloma al'amarin,ada yayi tunanin al'amarin mesauk'i ne
amma daren jiya yatabbatar mai da al'amarin Aasim ba k'aramin babban al'amari bane
Ahankali
K'arfe takwas doctor zayyad yashigo d'akin yana sallama
Umar ne ya amsa mai,dan ita Rauda baccine yad'auketa me tattare da ciwon kai me
tsanani
"Yajikinnaka?
"Dasauk'i"
Ya amsa mai
Zayyad yace
"Jiya cikin dare Rauda takirani tace inje kana cikin wani Hali dana tambayeta meke
faruwa sai tace min Aasim,wai meke faruwane Umar?
"Zayyad yanzu ba lokacin dazanyima bayani bane amma aikasan bana b'oyemaka komai"
Zayyad yamik'e yafice daga office d'in batare da yakuma cewa komai ba amma zahiri
yana cikin damuwa da ganin halin da abokinsa keciki
Umar yace
"To amma da na tashi Rauda ka ajiyeta itama inzaka dawo sai kabiya kad'aukota"
"Jikinne?
Ya girgiza Kai
"Aa ni naji sauk'i kitashi zayyad ze wuce ya ajeki agida inze dawo sai ya biya
yad'auko ki"
Hmmmmm chuchu kinmanta da night gawn ne ajikinki kiyi hak'uri kije kicanza kaya ai
ba dad'ewa zaki yi ba"
Umar yafad'a,shuru tayi Tana nazari dan gani takeyi kamar idan tatafi wani abunne
zekuma samunsa
Tunda suka shiga motar babu wanda yayi magana harsuka iso gidan
Tagyad'a mai kai kawai tare da ficewa daga motar yaja yawuce.
Tatsaya a bakin k'ofar tanajin kamar kartashiga amma babu yadda ta iya yazamarmata
dole
Saida tatsaya tana k'arema falon kallo kamar yaune tafara ganinsa sannan tashiga
tamaida k'ofar tarufe
Ahankali tafara takawa zuwa step tafara hawa step d'in ahankali
Tana tunanin abunda zata farayi,tana tsoron yin wanka gashi Kuma yazama dole
Bata tsaya sa ruwan zafi ba,nasanyi ta tatara cikin k'an k'anin lokaci tayi
wankan daba ta da tabbacin tafita.
Ko mai bata tsaya shafawa ba ta sanya atamfa riga da skirt d'akinsa ta nufa dan
d'auko masa kayan
Sautin shesshekar kukanne yacigaba da k'aruwa kuma da dukkanin alamu daga bayi
shesshekar yike futowa
Ajiyar zuciya tasauke mai nawi tana hamdala da bataga abunda ke kukanba dan tabbata
ba alkhairi bane
Fargaba da tsoro suka k'ara kamata, ahankali tafara saukowa daga step k'irjinta na
dukan uku-uku
Harta gama saukowa can gefe tahango wata tsohuwa kwance tana d'ago mata hannu tana
cigaba da kukan
Wani irin lugude k'irjinta yacigaba dayi tana jin zuciyarta na rawa kamar zata fito
waje saboda tsananin tsoro
Tama rasa inda zatayi dan dole saitabi gaban tsohuwar kafin tafita waje ita kuma ba
abun takoma sama ba taga abinda yafi wanda takegani ayanzu
Dukda akwai tazara atsakaninsu sosai amma hannu kawai tsohuwar tasa tajanyo wuyanta
Runtse ido Rauda tayi dan kallon fuskar tsohuwar na k'ara razanata
Jin shuru yasa tabud'e idanuwan a tsorace saidai wayam bataga kowa ba babu tsohuwar
Abun mamaki kuma ganinta tayi a d'akin umar gaban wardrobe d'insa
Ita da har tad'auki kayan tafita falo ya akayi kuma taganta a d'aki
Jikinta narawa tabaro d'akin tana k'ara kallon inda taga tsohuwar
Ficewa tayi dasauri tamaida k'ofar tarufe sannan ta jingina da k'ofar tana maida
numfashi
Ahaka zayyad yadawo yatadda ta
Tana ganinsa ta taso tashiga motar dan jinta takeyi kamar akan k'aya take
Kallon ta zayyad yayi sosai take yafahimci firgici atare da ita hakan yasa shi
tambayarta yace
"Lafiya madam?
Ta fad'a Masa,yayi ajiyar zuciya yana nazarin abunda tafad'a mai sannan yace
"Inaganin gobe idan allah yakaimu mutafi katsinan kawai gurin malamin da zayyad
yace"
Daddare tana zaune kusa dashi yafarayin bacci, itama gyan-gyad'i ne yafara
d'aukanta
Yagyad'a kai
"Dama akwai allurar daban masa bane saiyanzu na tuna shine nazo inmasa"
Ya girgiza Kai
"Aa basai kintashesa ba,ai allurar bata baya bace ahannu za aimasa"
Still banza yayi da ita,cikin idanuwansa takalla taga k'wayar idonsa golden
Azabure tamik'e lokacin yagama allurar yazare yana wani mugun murmushi
Kasa k'arasawa tayi yayinda ya kauda fuskar zayyad dayayi amfani da ita fuskarsa ta
bayyana
"A..asim"
Tafad'a cikin rawar murya
To allura ce wacce ruwan dake cikinta yike d'auke da abubuwa da dama,zanfad'a miki
kad'an daga ciki
Dafarko dai tana d'auke da guba wacce bata kisa amma tana shiga cikin k'ashi da
b'argo da kuma jijiyoyin mutum,ta rink'a rugurguza k'ashi tana tsittsinka
jijiyoyi,abu nabiyu shine takan saka mutum ya cutar da kanshi yanaji yanagani
batare da ya iya hana kansa ba,
Umar yatashi daga kwanciyar dayayi daky'ar yana dubansa cikin dakewar zuciya yace
"Duk wad'annan abubuwan kanayine dan karabani da matata,to kasani inason matata
fiye da yadda nike son kaina,kuma babu wata barazanarka da zata sani naji Tsoro
Sannan inaso kasani kalmar saki bazata tab'a fitowa daga bakina ba
"Rauda kisani inasonki babu abunda zesani fargaba akanki,ko kad'an kalamansa basu
dameni ba Dan nasan be isa yamin abunda allah be minba,ki kwantar da hankalinki
babu abunda zesameni kinji?
Ta jinjina Kai kawai tanacigaba dayin kukan tarasa wannan wace irin Jarabawa ce
take bibiyarta takuma kasa rabuwa da ita
Ya d'aga ta suka kwanta akan gadon asibitin yana cigaba da kwantar mata da hankali
Zayyad yad'auko su, yadawo dasu,suna shigowa motar anty kaltum nashigowa
Zayyad yace
"Habadai anty idonki ne amma babu ramar dayayi"
Jinjina kai tayi amma bata yarda ba dan tafi kowa sanin k'anin nata
"Aa, office zani dama nabiyo ne inga lafiyarku tunda kuma kuna lafiya shikenan"
Umar yace
"To sister gobe zamuzo amana girki medad'i"
Zayyad yace
"Ni zan tafi daddare zanbiyo in k'ara duba jikinnaka mukuma k'ara tattaunawa akan
zuwa katsinan"
Shiko kwantawa yayi yanajin jikinsa nayimasa wani iri, ya lumshe idanunsa cike da
damuwa da fargaba
Ahaka ta gama had'a abun karin tasamesa,tadad'e tsaye akansa tana magana amma
bejiba dan yalula cikin tunani
Tatambayesa
Yakakaro murmushi yana tashi daga kwanciyar dayayi
Jikinsa yafara rawa,yanajin cikin naman jikinsa kamar ana huramai wuta
Aje kofin hannunta tayi dasauri tana dubansa tare da amsar kofin hannunsa
"Jaana,meke faruwa?
Kasa bata amsa yayi dan zafin cikin jikinsa dad'a k'aruwa yikeyi
Dasauri tamik'e tabud'e fridge tad'auko goran ruwan tafara shafamai ajiki
Jiyayi hannunsa yafara wani irin ciwo yarike hannun dasauri yana ambaton sunan
Allah
Saida yakusan awa d'aya ahaka sannan hannun yalafa,amma still zafin jikin yananan
Y'arfillo.
[20/10, 8:37 pm] Sumiee B.: 🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Dedicated to Little hajjo and my elder sister Hafsat Aliyu
AGE📕 9⃣
Ina bawa masoyana hak'uri abisa ga jimawa dani keyi ban yi posting ba,nima ba da
son raina bane,bank'i ace kullum naturo muku ba amma uzururruka sunyi min yawa
inafatan zaku amshi uzurina,kuma zanyi k'ok'ari insha allahu inga ina yin posting
akan lokaci nagode da k'aunarku gareni da kuma jinnul aashique.
GAISUWA
Ga y'an uwana y'an Golden pen writters allah yak'ara mana dank'on zumunci
FATAN ALKHAIRI
Ga aminiyata AISHA A IBRAHIM allah yazab'a miki abinda yafi alkhairi a rayuwarki
Amin.
Wannan page d'in sadaukarwa ne gareka jarumi sadauki,AASIM na sadaukar dashi gareka
ranka shi dad'e allah yak'ara girma👍🏻
Duk iya k'ok'orin da umar yayi,wajen ganin ya b'oye yadda yikeji ajikinsa dan gudun
kada hankalinta ya tashi,kasawa yayi saboda tunda yike a duniya betab'a jin irin
yadda yike ji ahalin yanzu ba,iya kuma karatunsa na likita da yayi betab'a karo da
wannan irin ciwon da yikeji ajikinsa ba bare yasan wani magani ko allura ze ma
kansa yaji sassauci.
Yasa ta k'ure AC d'in falon,takuma kawo mai fankar k'asa,badda wacce take sama
tanata nata aikin
Amma a banza,a memakon yaji sanyi-sanyi sai ma yikejin zafin nakuma k'aruwa.
"Chuchu"
Ya kira sunanta ahankali ganin yadda tashiga damuwa sosai
"Na'am"
Jaana ina jin tsoro,jikina na bani wani babban al'amari yana shirin faruwa
damu,bana so wani abu yasameka"
Yafad'a
Ba a jima ba kuwa zayyad yadawo gidan,gwaje-gwaje yayi masa amma bega komai ba
"A bayanin dakamin nayimaka gwaji akan abunda nike tunani yana damunka amma banga
komai ba"
Sai kuma ya dakata yana duban Rauda dan ba ya so yayi maganar agabanta
Ta mik'e ta hau sama,ya maida kallonsa kan zayyad Yana cigaba da cewa
"Zayyad,zafin dani keji a jikina yawuce yadda zan kwatanta maka,jini keyi kamar ana
huramin wuta acikin jikina"
Umar ya zayyana mishi abunda yafaru daren jiya a asibiti,da allurar da Aasim yayi
masa
Zayyad ya jinjina kai cike da tsananin mamaki danshi tunda yike aduniya betab'a jin
makamancin al'amari irin wannan ba Koda kuwa a littafi ballan tana a zahiri
"Babban malami ne gaskiya,kuma koda yaushe gidan shi cike yike taf da jama'a bana
tunanin ze iya barinsu yazo,amma bari na kirasa naji"
Ya danna numban malamin bugu biyu ya d'auka suka gaisa,zayyad yasanar dashi
buk'tarsu akan yazo tare da rok'onsa daya taimaka
Zayyad yayi mai godiya sannan ya kashe wayar yana kallon Umar yace
Ta waiga da sauri tana kallon cikin bayin,ruwan data had'a acikin kwamin wanka ne
taga yana ta zakud'owa kamar dakwai wani abu aciki
Ta rufe idanuwanta da sauri jin tsigar jikinta na tashi bakinta na ambaton sunan
Allah
"RAUDA!
Tabud'e idanuwanta da sauri tana kallon cikin ruwan inda taji ankira sunannata
Wani mutumi tagani d'an k'arami shi ba wada ba shi ba yayan wada ba,d'an
siriri,fatar jikinsa wata kala kamar gansa kuka,koriya shataf,idanuwansa wasu kala
kamar na mage
Jikinta na rawa ta murd'a k'ofar bayin zata fita amma gam k'ofar ta rufe
Ta runtse idanuwanta kawai,jitayi an damk'i hannunta ta ware idanun tana k'wala ihu
Taji yafad'a
Tare da kecewa da wata kalar dariya
"Rauda!Rauda!
"Subhanallah me yasameta?
Ya amsa ruwan ya yayyaffa Mata,ko minti biyu beyi da yayyafa mata ruwan
ba,tafarfad'o tana sauke ajiyar zuciya me nawi
"So sukeyi su kasheni,sunce bazasu tab'a rabuwa dani ba wayyoh allahna na shiga
uku!
Zayyad yayi jugum Yana kallonsu gabad'aya tausayinsu yikeji,lokaci d'aya yanayinsu
ya sauya daga farin ciki zuwa tashin hankali
Suko suna falon har lokacin,ba maganar neman abinci dan babu me jin yunwa acikinsu
Zuwa can dai ya dubeta tana kwance akan k'afafunsa yayinda yike zaune kan doguwar
kujera yace
"Nasan bakyaji ai,nima baji nike yi ba amma yazama dole munemi wani abu musa acikin
mu dan zama da yunwar itama babbar matsalar ce"
Ta jinjina Kai
"Shikenan kasa yakawo koma miye"
Koda me gadin yasiyo kuwa,kad'an suka tsakura, suka gabatar da sallar magriba da
issha,sannan suka kunna karatun qur'ani acikin a falon
A haka bacci ya d'auke Rauda,shiko umar ko kad'an be runtsa ba dan jikeyi kamar ana
d'add'aure jijiyoyin jikinsa,ga zafin da yike ji Yana dad'a k'aruwa.
"Lafiya?
"Tabbas samunka matsayin miji agareni,wani babban rabo ne daga ubangiji,na tabbata
da bakai na aura ba da yanzu wanda na aura ya maidani gidanmu danna tabbata babu me
iya zama dani da wannan lalurar atare Dani"
Ajiyar zuciya yasauke tare da kama hannayenta yana kallon cikin idonta
"Zan rink'a b'oye wa dan kawai hankalin naka ya kwanta amma kasan damuwata bazata
tab'a ciruwa ba face na rabu da matsalar dake tattare Dani"
Ta gyad'a kai kawai dan ita tasan yanzu ma suka fara shiga cikin matsala
Shiya jasu sallar, Allah-allah yikeyi ya idar sabida zugin da k'afarsa keyi masa
Jikinta yayi sanyi dan ta fahimci ba kwanan dayayi azaune bane yasa k'afar tasa
haka,k'ila abunda ke shiga cikin jikinsa ne
Ajiyar zuciya tayi tana girgiza Kai,batasan me yasa yike son b'oye mata halin da
yike ciki ba
"Jaana dan allah kadena min irin haka, at least in kanajin abu kafad'a min ko kana
da wacce tafi nine?
Nida bani da wanda yafika ai komai naji saina sanar dakai amma Kai......
Ya katseta
"Chuchu kinsani babu abunda zan b'oye Miki,k'afar ta Dena tund'azu"
Ta kauda kanta gefe gudun kada yaga hawayen da ke Shirin zubo Mata
"Chuchu"
"Na'am"
"Zonan"
Ta bud'e jik'akk'un idanunta tana kallon yadda ya runtse idonsa alamar yana jin
rad'ad'i
K'arfe tara tayima zayyad a Tasha,Dan malam aminu ya sanar dashi sunkusa isowa
Dattijone kamilalle me cike da natsuwa,ya mik'ama zayyad hannu sukai musa baha suka
gaisa,sannan suka shiga motar zayyad d'in
Malan yace
"Ai da wuri nafito ina idar da sallah danma motar tad'an tsaya mana amma da mun iso
tund'azu"
Tunda suka iso get d'in gidan malan aminu ya fahimci akwai gagarumar matsala acikin
gidan
Zayyad ya shiga yayi parking,sannan suka fito zayyad yafara knocking d'in falon
Har lokacin suna rungume da juna, bakinta kuma bedena karanto addu'o in ba
Dede lokacin wayar Umar tafara k'ara ganin numban zayyad yasa yace
Suka mik'e sukayo falon yana d'an ciccije bakinsa dan ciwon dad'a k'aruwa yikeyi
Ta gaishe da su tana kallon malan aminu Wanda shima ita yazuba ma ido
Ta basu hanya suka shiga sannan ta maida k'ofar tarufe,takoma kusa da Umar tazauna
Malan aminu yatashi ya dafa kan umar yana nazartar abunda ke damunsa
Ya girgiza kai fuskarsa d'auke da damuwa yana duban Rauda sannan itama ya dafa nata
kan
Janye hannunsa yayi dasauri yana kallonta fuskarsa d'auke da tsantsar mamaki
A fili yace
"Aasim bin ramzad?
Yasauke numfashi Yana kuma girgiza kai cike da tarin fargaba
Gabad'aya sun zuba mai ido suna jiran suji abunda zece
"Zahiri kuna cikin babbar matsala,domin kuna tare da rauhanin da ba kowani malami
bane ze iya ja dashi"
"Amma nayi mamaki,Aasim bin ramzad rauhanine,kuma a iya sanina rauhanai basa
cutarwa,wani laifi kuka masa haka da ya tunzurasa yike azabtar daku?
"Tabbas akwai laifin dakuka masa mai girma wanda ya tunzurasa ya canza daga
ainihinsa,kuma ni tabbas bazan iya ja dashi ba amma zan iya nemansa inji dalili
inkuma jaraba rok'onsa ko ze iya hak'ura"
Har lokacin babu wanda yayi magana kallonsa kawai sukeyi,umar ne yakatse shurun ta
hanyar cewa
"Malan dan Allah kataimaka kayi iya abunda zaka iya, wallahi muna cikin damuwar da
bazamu iya kwatanta maka ba"
Malan aminu yagyad'a kai yaciro wani turare a aljihunsa ya fesa sannan yafara
karanto addu'o I da basajin me yake fad'a illa bakinsa da suke gani yana motsawa
Ahankali d'akin yafara duhu,saiga shi ya bayyana cikin ainihin suffarsa ta yarima
Fuskarnar tasa a tamke ya watsawa malan aminu razanannun idanunsa cikin b'acin rai
yace
"Fad'i kiran me kakemini,meke tafe dakai,me Kuma yashigo dakai matsalar da babu
ruwanka,shin kanaso rayuwarka ta salwanta ne?
"Tuba nike ranka shidad'e,amsa Kira na dakayi kad'ai ya isheni,bakuma nanemeka bane
dan na Isa,illa Dan na rok'eka da ka sassauta ma wad'annan bayin allahn.....
Aasim ya kalli Rauda da umar yana yimusu wani kallo da shi kad'ai yasan ma anarsa
"Nafad'a kuma zansake fad'a muku,ko ku rabu da juna kokuma daga yanzu kicigaba da
fuskantar barazana,kuma gubata akullum k'ara ratsaka zatayi wallahi sai ka gwammace
mutuwarka da halin da zaka shiga
Gabad'aya malan aminu ya jik'e sharkaf da zufa,shiko zayyad harda fitsari ya saki
saboda tsananin tsorata
"Agaskiya bazan iya ba,ku gafarceni amma ya wuce k'arfin da kuke tunani,bazan iya
ba dan allah karku sake nemana dan rayuwata zata iya shiga cikin hatsari"
Zayyad na kiransa amma be tsaya sauraronsa ba ya k'arasa ficewa daga falon dan
gabad'aya ya firgita
Rauda ta runtse idanuwanta cikin tashin hankali maganganun malan aminu nayimata
yawo acikin kunnuwanta
"Aasim bin ramzad rauhanine kuma rauhanai basa cutarwa tabbas kunyi masa laifin
dakuka tunzurasa wanda yasa ya canza daga ainihinsa"
"Tabbas ban kyauta ba maka ba,amma ban cancanci wannan hukuncin daga gareka ba"
Wanene Aasim? Menene had'insa da Rauda? Me suka masa da ya canza sa daga ainihinsa?
Muhad'u a page 🔟 dan jin yadda zata cigaba da kasancewa taku a kullum
Y'arfillo.
[20/10, 8:38 pm] Sumiee B.: 🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo) 🧕🏻
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
🅿AGE📕 🔟
_Wannan Page naki ne anty Nabeelt Allah nike rok'o ya baki lafiya, yasa kaffara ne
ya kuma k'ara dank'on zumunci a tsakaninmu Amiiiin_
Maman ummi kema ina Allah yak'ara lafiya yasa kaffarane yakuma nuna mana auran ummi
lafiya😅
_GAISUWA DA JINJINA_
*_Ga ya ommer allah yak'ara k'warin ido muna godiya da zak'ulo mana kura-kuran mu
daka keyi, da kuma gyara dakake mana, bazamu iya biyanka ba ya Ommer wlh muna jin
dad'in shugabancin ka sosai Allah ya bar mana kai da rai da lafiya mai anfani, ya
kawo bata tagari kuje har katsina musha ringen-rigegen_*💃🏻💃🏻💃🏻
FARKON LABARI
Cikin katafariyar jami'ar dake cikin katsina
D'alubai ne sukayi dandazo a wani wuri da alama sakamon jarabawarsu da sukayi suke
dubawa
Tafiya Rauda Take yi cikin sauri har da gudu-gudu yayinda ta hango dandazon
d'aluban
Ganin yadda maza da mata suka cakud'e yasa tasamu gefe ta tsaya,dan bazata iya
shiga cikin maza ba
Bata ma fara duba sunan ta daga sama ba,daga tsakiya tafara tanayin k'asa
Cikin haibaci d'ayar me suna laurat wacce itace take fitowa da first class a
department d'insu,takalli d'ayar me suna farida tace
"Farida waike wace irin k'wa-k'walwa kike da itane,ace kowani semester bakya iya
fitowa da ko third class sai dai probation"
Farida taga ne nufin laurat sarai hakan yasa ta fashe da dariya tace
"Kannawa ne a toshe yike, kwata-kwata baya iya d'aukar komai,saboda dattin talauci
da kuma miyar kuka sun toshesa"
Rauda tasan da ita suke,hakan yasa tabar gurin jikinta a sanyaye ba tare da ta
tanka mu su ba
Can baya taje tazauna k'asan wata bishiya, gabad'aya tarasa me ke mata dad'i dan
ta tabbata idan tacigaba da kasancewa tanafitowa da wannan sakamakon to tabbas
watarana koranta za ayi
Wasu hawaye ne masu zafi sukafara biyo kuncinta yayinda ta tuno mahaifinta dakuma
yadda yike so tayi karatu
Shin ya zatayi?
Wata tattausar murya taji tayi mata sallama,tad'ago da idanuwanta da sukayi sharkaf
tana kallon me yin sallamar
Amma nanma kasa amsawa tayi dan ji tayi jikinta yayi mata wani iri tsigar jikinta
tafara tashi
Murmushi saurayin yayi yana durk'usawa daga tsayen dayike,tazarar dake tsananin su
bazata wuce kamu hud'u ba
"Be kamata ace kink'i amsamin sallama ba,domin ko nasan ke musulma ce yakamata ace
kin amsamin"
"Kwata-kwata hawaye beyi kyau a wannan kyakkyawar fuskar ba,kamata yayi ace
murmushi ne akanta ba hawaye ba"
Mamakine ya kamata ganin yanayinsa da Kuma tsadaddun kayan dake jikinsa amma kuma
ya zauna a k'asa
Amsa tayi idanuwanta a kansa,tana tambayar zuciyarta, shi kuma wannan wanene?
Bayan ta gama goge hawayen ta mik'a mai handkerchief d'in tana mamakin kafeta da
idanu dayi
Takasa k'arasawa samakon lura da saurayin dake zaune dirshan gaban Raudan
Cikin daburcewa salma ta d'aga mata kai tana kallon saurayin wanda shima ya mik'e
Ganin yadda salmar ta saki baki tana kallon sa yasa Rauda ta galla mata harara tana
matsowa kusa da ita
"Am....nace...dama...
Harara Rauda takuma galla mata ganin yadda duk tawani daburce daga ganin mutum
"Amma dan Allah inaso ind'an yi magana dake,na y'an mintoci idan bazaki damu ba"
"Wannan ai zubar da ajine,ki wani saki baki kina kallon mutum salon ya
rainaki,inbanda shashanci miye zaki wani kafe mutum da ido kamar kinga wani sabon
halitta "
Rauda wurgar da k'aramar jakar dake hannunta tayi tafad'a kan k'aramin gadon k'asa
tana lumshe idanuwanta dasuka k'an-k'ance saboda b'acin rai da kuma damuwar da take
ciki
Salma ta zauna kan kujerar dake tsakar d'akin,
Tace
"K'awa waye wannan dana gani,a ina kika samosa?
Kamata yayi kidamu da jarabawar Dana fad'i ba ki tsaya kina tambaya akan wani can
da k'ila ma ba k'ara ganinsa zaki yi ba"
Salma ta sauke numfashi tana tasowa daga kan kujerar tada wo gefen raudar ta zauna
"K'awata kema kinsani nafi kowa damuwa da damuwarki,kawai dai na tambaya waye shine
ganin bantab'a ganinki tare da shi ba,amma kiyi hak'uri"
"Bansan ya zanyi da raina ba,kiduba fa kiga tunda jarabawar nan ta matso na dena
bacci,kwana nikeyi ina karatu,amma abun haushi sai naje rubuta jarabawar sai inji
namanta komai,
Haka b'angaren lissafi kwata-kwata bana ganewa, nasan nan gaba korata za'ayi"
"Dan Allah karkiyi kukannan,addu'a zamu cigaba da yi,sannan kuma kik'ara dagewa
insha'allah za'a wuce wurin"
Daddare tana zaune bacci yakasa d'aukar ta, tunanin sakamakon jarabawar ta kawai
takeyi
Taja guntun tsaki tare da mik'ewa tasha ruwa sannan ta dawo zata kwanta
Ta durk'usa ta d'auka sannan takoma bakin gadonta,tana jin k'amshin dake fita
ajikin handkerchief d'in sama-sama
Zaunawa tayi tana k'arema handkerchief d'in kallo,farine k'ar sai wani zanen fulawa
golden a jiki,ta kara kusa da hancinta
"Waye shi?
Ko karyawa bata tsaya tayi ba,kasancewar tasan halin lecture ran bayi da kirki ko
kad'an gashi yayi mugun samata ido
Gabad'aya ajin yayi tsit, yayinda yashigo ya gabatar da bayani me tsawo sannan
sannan ya rubuta wani word ajikin allo
Ya juyo yana kallon d'aluban yana duba wanda ze zak'ulo ya maka mai tambaya
"Rauda"
"Radi..cals"
Shuru tayi dan batasan miye ma'anarsa ba,bugun zuciyarta nadad'a k'aruwa
"Radicals is a........
Lecturer mamman ya dafa kansa na y'an mintuna sannan ya ware jajayen idanuwansa
yana kallonta
"Yauma baki sani ba ko?duk wata tambayar da za'ayima d'an secondary idan akayimiki
Baki sani ba,wai shin a wace makaranta kikayi karatu kafin kizo jami'a?
Shin lefin daga malamankine wad'anda suka koyar dake?kokuma daga k'wa-k'walwarki
ne?
Yad'an numfasa tare da jan dogon tsaki sannan ya d'auke kallon sa daga kanta
yamaida kan sauran d'aluban
Cikin yauk'i da yanga laurat ta mik'e tafara bayani cikin wani salo na turanci me
burgewa
Tunda Rauda tafito da ga ajin zuciyarta ke suya, gabad'aya taji rayuwar tafitan
mata arai,
Gabad'aya d'aluban dake tsakar makarantar sauri sukeyi saboda hadarin da yayi
bak'ink'irin yanata cida alamar yana gab da fara ruwa
"Hostel zankoma"
Wani irin yarr taji ajikinta, dasauri takallesa suka had'a ido
Ta d'auke idanuwanta akansa Tana mik'ewa da niyyar cigaba da tafiya zuwa hostel
d'in
"Tafiya cikin ruwannan ze iya haifar miki da zazzab'i ki fake ruwan ya tsaya dan
Allah"
Ya maida handkerchief d'in aljihu yana kallon yadda ruwan ke sauka da k'arfi
"Dama ance mata ba sa tsoron ruwa, amma kuma hakan kuskure ne,saboda ze iya shafar
lafiyar mutum"
"Yau kuma meyafaru naga damuwa a fuskarki, ko tun da muwar jiya ce?
Itama kallonnasa takeyi gani takeyi kamar ta sanshi,kamar ta tab'a ganinshi,to amma
a ina?
"Wanene Kai?
"Aasim?
Ta mai-maita sunan tanaso ta tuna inda ta tab'a jinsa
Ya d'aga kai
"Eh Aasim,kinji sunan wani iri ko?
Dariya ya Kuma yi
"To ni d'an Nigeria ne"
Tak'ara kallonsa
"Amma iyayenka su ba y'an nigeria bane"
"Um to,yanzu dai abar maganar Nigeria ko wata k'asa,da y'an wata k'asa nayi miki
Kama?
"Sunana Rauda"
Yafad'a fuskarsa na nuna tsantsar farinciki data rasa gan me ko farincikin menene
"Nagode"
Ya sauke numfashi,yace
"Zanso muk'ulla alak'a ta abota,ma'ana muzama kaman y'an uwa ni dake,tunda nafara
ganinki naji na natsu dake,bansani ba ko zaki bani damar hakan"
"Bangane ba"
"Ni ina alak'a ne da wad'anda suke Dede Dani,amma kai kafi k'arfina kayi hak'uri"
"Wannan ba magana bace,dani dake duk d'aya ne,kuma duk allah ne yayimu danhaka kada
kisake fad'in haka"
Ta jinjina Kai
"Shikenan"
Kodayaushe idan batada lecture suna tare Yana koya mata karatu wanda take fahimta
sosai
Wanda hakan yafara ba wa mutane mamaki,ita kanta tana mamakin kanta,da ta karanta
abu sau d'aya sai taji ya zauna mata
Kamar kullum tagama d'aukar darasi,tafito daga lecture room fuskarta d'auke da
nishad'i daga nesa ta hango motarsa,inda yayi mata horn
Tak'arasa suna ma juna murmushi,sallama ta mai ya amsa yana K'ara rage glass d'in
motar
"Yau kindad'e"
Yace
"Hakane shigo to yau yawo zamuje"
Bata musa ba,ta zagaya ta bud'e marfin motar tashiga, Saida tazauna ya tada motar
sannan tace
Ta girgiza Kai
"Aa ni bansan ko inafa,danni ko a kaduna ba yawo nike yi ba ballantana a garin da
ba nawa ba"
ya juyo suka had'a ido,tayi saurin lumshe nata tana cewa cikin wata kalar murya me
sanyi
"Wai meyasa idan muka had'a ido sai inji tsigar jikina na tashi ne?
"Nima bansani ba, hala nawa idanun sunfi naki k'arfi ne shiyasa"
Ta bud'e idanun ta sauke su akansa,tana jin jikinta nayi mata wani iri
"Kace dai kai d'an baiwa ne kawai,dan komai naka ya bam-banta dana sauran mutane"
"Ze iya kasancewa,kinsan aljanu duk inda kike tunaninsu sun wuce Nan"
Dariyar ta kuma yi
"Eh lallai Kam,ai duk k'arfin aljani baze iya yin siffar mutum kaman naka ba,sufa
ance ko sunyi suffar mutum to basa iya yin k'afar mutum saidai kaga kofato"
"Ashe?tofa
Ta jinjina kai
"Eh Mana,ai ta k'afafunsu ake gane su,kuma ance muryarsu ma basa iya yin ta mutane"
Yafad'a
"Kaga,mu bar maganar aljanun nan kar su jimu,dan wallahi ni tsoronsu nike ji,wai
shin ma ina zaka kaini ne,naga kana ta luluk'awa?
"Nufina inda zankai ki,da kinsan inda zan kaiki da baki ce inata luluk'awa ba"
Ta gyad'a Kai
"To ina zaka kaini?
"Gidan aljanu"
Ta d'aga Kai
"Eh bari kaji inbaka wani labari,akwai wata rana ina kwance bayan sallar
magriba,d'akin babu haske sosai najuya zan gyara kwanciya sai naga jariri akwance
kusa Dani,amma banga fuskarsa ba,mace ne ko na miji bansani ba,nak'ara kallo a karo
na biyu still nagani,amma kafin in k'yafta idona sai naga babu komai,
Washegari nike ba y'an gidanmu labari har Nike ce musu,da ace zankuma ganin jaririn
dana d'auka shine suka dinga min dariya wai inje ind'auka ma aljanu d'ansu zan
gane kurena"
"Cap kuma da kikagani baki ji tsoro ba?ai ni innine bazan iya bacci ba?
Wani madai-dai cin gidane me kyan gaske wanda tsayawa fasalta shima b'ata lokacine
Gabad'aya jikinta yayi sanyi kallon gidan kawai takeyi gabanta na fad'uwa
"Muje ko?
Kallonsa tayi
"Ina ka kawoni?
Ta girgiza Kai
"Aa bazan shigaba kafad'a min inane Nan?
Shuru tayi tana k'ara kallon gidan jinsa da tayi tsit da alamun babu kowa aciki
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)
✍✍✍✍✍✍✍
*GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*
✍✍✍✍✍✍✍
❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo
magical Our creative golden pen Be hold our words A product of our pen Savour our
words, for it will cause you no pain_❄
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
1⃣ 1⃣ 1⃣1⃣
1⃣1⃣
AGE
Wannan Page d'in nakune jinnul aashique group,ina me k'ara baku hak'uri akan rashin
typing d'in da banayi dawuri.
Wata kyakkyawar budurwa ta taso daga cikin falon dasauri tana fad'in
"Dagaske?tare kuke?
"Oyoyo sister"
Itadai Rauda butun butumi tazama,dan takasa cewa komai kallonsu kawai takeyi,ga
kuma tambayar dake zuciyarta
Jin Aasim yakirata da matarshi,shida ko maganar soyayya bata tab'a shiga tsakanin
su ba,miye na kiranta da matarshi?
"Kinga fad'ama ammi tafito su gaisa sannan kizo kiyi shirmen naki"
Rauda da batace komai ba har lokacin,ganin nazman ta wuce yasa takalli Aasim da
sauri tace
"Ina Nan?
"Gidan mu Mana"
Yad'aga gira
"To ba gashi yanzu nafad'a Miki ba"
"Ai sai ka fad'amin tun a makaranta nan zamuzo inje incanza Kaya Amma......
Takoma ta zauna tana duban Aasim daya tashi daga kujerar ya koma wacce mahaifiyar
sa take yazauna yana kama hannunta
Ya girgiza kai
"Aa ammi"
Nan da nan ko yana yinta yasauya zuwa damuwa tafara tattab'a jikinsa alamun tana so
ta ji zafin jikinsa
Rauda ko Sha'awa suka bata,dan dukkanin alamu akwai soyayya da shak'uwa me k'arfi a
tsakaninsu
Wata yarinya da bazata wuce shekaru biyu da rabi ba,ta tashigo falon rik'e da
k'atuwar y'ar baby
Tafad'a jikin Aasim cike da jin dad'in ganinsa
"Miye sunanki?
"Tatida"
"Shahida ta ke so tace"
"Shekararki uku?
Ammi tace
"Kinga y'ata karki biye ma shirmen shahida,tashi kuje kisa wani abu acikinki"
Aasim yayi gaba tana binsa a baya,wani madai-dai cin falo suka shiga
Komai na falon kalar golden ne,kama daga kan kujeru,kafet,labulaye kai komai na
d'akin kalar golden akayi ado dashi
"Bissmillah,zauna"
Ta zauna hankalinta na kan shahida gabad'aya k'aunar yarinyar ya shiga zuciyarta
Aasim ya matso da zagayayyen tebur d'in da nazma ta d'aura tiren akansa gabanta
yana cewa
"Kedai kice ganin shahida ya k'osar dake,da alamu tashiga ranki ko?
Ajiyar zuciya Rauda tasauke,azuciyarta tana addu'ar allah yabata irin shahida
Takuma sauke ajiyar zuciya tana tambayar zuciyarta,haryaushe daga zuwanta aka
shirya mata wad'annan abubuwan?
Ya tambaya yana zama a gefenta dayike kujerar da take kai three seeter ce
Bata ce mai komai ba,ya d'auko wani juice ya tsiyaya mata kofi yana mik'a Mata
Sannan tace
"Kadube kanka da kyau,kaduba irin baiwar kyau da allah yayi maka,sannan ka kalli
gidan ku
"Ina sonki"
"Ina sonki"
Ya kuma fad'a
"Kana Sona?
Ya cigaba da cewa
"Meyasa baki fahimci cewa ina sonki ba tuntuni?
"Dan allah kabar maganar Nan, kaima kasan ba abu me yuwuwa bane"
"Shikenan Amma zan tattara miki su kitafi dasu,kuma dan Allah karkice aa"
"Shahida"
"Tafiya da tiyi?
Rauda tayi shuru tana kallon ta sosai hakanan take jin zuciyarta wani iri,dan ita
kanta bata son rabuwa da yarinyar
Aasim dake tsaye yana kallonsu ya mik'oma shahida hannu alamar tazo
"Shahida zo inkai ki gurin ammi kinji,nan da kwana biyu zanzo inkaiki gurinta
kinji?
Basu dena kallon juna ba ita da shahida har saida matar ta sha kwanar falon
"Saboda kawai inaso inganta,dan ta iya haihuwa data haifo kyakkyawar yarinya irin
haka,allah zuciyata ta kamu da son yarinyar"
Ya jinjina kai
Takallesa tace
"Kai kuma me?
"Miye?
Tatambaya tana d'an zaro ido
Yace
"To kince maganar soyayya wasace,aure kuma ai shi gaske ne ko?shine nace zaki
aureni?
"Nidai nace ina sonki,kisoni ko karki soni wannan matsalar ki,danni soyayya dake ba
gudu ba ja da baya"
Dariya ta kuma yi
"Allah Aasim bazan iya soyayya dakai ba,kafi k'arfina Allah"
Ya tab'e baki
"Nagaya miki wannan matsalar kice,amma ni inkinga na ja da baya to nadena numfashi
ne Allah"
"Masoyiya gashi"
Harararsa tayi
"Wacece masoyiyar taka?
"Ke Mana,kodayike matata yakamata ince tunda baki san kalmar wasa"
Wai gowa tayi dasauri tana kallon mutanen dake kai da komowa
Ze kuma magana tayi mai nuni da yayi hak'uri dan tasan ba k'aramin aikin d'alubai
bane su taru suna kallonsu
Murmushi yayi yana kuma fad'a k'asa-k'asa yadda motsin bakinsa kawai ta hango
Tana shiga d'akinsu ta tadda salma na ta patrol a d'akin da alamu hankalinta atashe
yike
"Sakeni ni,kinsa hankalina yatashi yadda y'an kidnapping d'innan sukayi yawa gabana
nata fad'uwa,ina fargaban ko su sukayi awon gaba dake.....
Dariya Rauda tayi sosai,ta zauna gefen gado tana kallon salmar
"Amma ai idonki ze yi ko,dannasan idan kika dunga rusa kuka sai hawayenki sun
k'are"
Tsaki salma taja, tabud'e tukunyar girkin da take yi batare da ta sake kula ta ba
"Kinga k'awata,kiyi hak'uri,wallahi ina fitowa daga lectures Aasim yajani wai muje
yawo"
"Yawo Kuma?kuma kika bishi,allah Rauda kiyi hankali da Aasim d'innan,dan wallahi
y'ay'an masu kud'i ba kirki garesu ba"
"Aa shi ba haka yike ba,ba yadda kike tunani bane,gidan su yakaini,gidan iyayenshi
kinga ma abunda mahaifiyar sa tabani"
"Wallahi k'awa bakiga kirkin mutanen ba,yadda suke da kud'i da kyau,saiki rantse
zasuyi wulak'anci
Amma sam abunda suke dashi be rufe musu ido ba,baki ga yadda suka tarbeni ba,kuma
ma kinsan me?
Rauda tafad'a
"Gaskiya Kam,amma kuma da baki cemai haka ba k'ila rabon jindad'i ne ke kiranmu"
Girgiza Kai Rauda tayi tana dariya tashige toilet dan d'auro alwala
Da daddare,tana kwance bacci yakasa d'aukar ta,hakanan take jin zuciyarta cikin
farinciki mussaman idan ta tuno maganganun sa
"Please zuciya ta kada kifara son Aasim, Aasim yafi k'arfinki ta ko ina ba sa'an ki
bane please"
Ganin numban Aasim yasa tayi saurin bud'e wa k'irjinta na d'an bugawa
Naji kaman na sauke wani nawi da ya rataya a kaina,bazan iya kwatanta miki irin
k'aunar da nikeyi miki ba
Murmushi tayi tana jin wani farinciki na ratsa zuciyarta ajiye wayar tayi tana
lumshe idanuwanta
Washegari bata da lectures,hakan yasa suka kwashi kayan su dayayi datti suka fara
wanki
Suna cikin wankin kira yashigo wayarta,salma dake kusa da wayar tad'auka zata mik'o
mata
"Aasim ne fa"
Salma ta ce
"Allah bawai yau kad'ai ba,tun farkon had'uwarmu,indai kiransa zeshigo wayata to
sai naji gabana yafad'i
Duk yadda tayi da karta sa soyayyar sa aranta kasawa tayi dan shi d'in na dabanne
Arana sai yakirata fin sau goma,kuma duk sanda yakira da irin zafafan kalaman da
yike fad'a Mata masu matuk'ar rikita mata zuciya
Tace
"Ni fa yunwa nike ji kuma yau batajin cin abinci wallahi"
"To mekike son ci habibty, fad'a min ko menene shi zan nemomiki shi"
Yace
"Kifito ina wajen hostel"
Kasancewar ana sanyi a lokacin rigar sanyi kawai tad'aura akan doguwar rigar dake
jikinta
Tayi mai sallama ya amsa yana sakar mata murmushi me cike da so da k'auna
"Menene aciki?
"Habadai?
Ya jinjina kai
Mamakine ya kamata
Yayi murmushi
"Kedai ba cine naki ba?dan haka kije kici"
"Aa saikafad'amin inda kasamo shi,dan a iya sanina ba inda ake saida dambu anan
kusa-kusa kai ko da ranane
Hak'ik'a naji dad'in comments d'inku,ina kuma k'ara godiya a gareku yawan comments
d'in ku shike k'ara k'arfafamin gwiwa Page 12 yana zuwa insha Allah,taku akullum
Yarfillo.
[20/10, 8:39 pm] Sumiee B.: 🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
1⃣ 2⃣ 1⃣2⃣
1⃣2⃣
AGE
Wannan Page d'in nakine mamana,allah ya k'ara miki lafiya yasa kaffarane, ina
k'aunarki araina domin kin kasance uwa tagari me share min kuka na a kodayaushe.🥰
"Akwai wani sabon restaurant da aka bud'e babu kalar abincin gargajiyan da basa
saidawa,kuma har dare suna kaiwa,anan na siyo"
Ta jinjina Kai
Ya cigaba da cewa
"Sannan dakike cewe a iya sanin ki babu inda ake saidawa a kusa -kusannan yawo kike
yi? Keda sai kiyi sati ma wani zubin baki lek'a ko wajen makaranta ba"
Ya amsa da Amin
Taja iska alamar sanyi na ratsa jikinta sosai tana tana mammatse jikinta da yike
rawa kad'an saboda sanyin dake kad'ata
"Wai shin kai baka jin sanyi ne?
Ya bata amsa
"Me kikagani?
Rauda tace
"Gani nayi bakasa rigan sanyi ba,kuma ko rawar sanyi bakayi"
"Ni me nayi?
"Allah har fargaban ayi hutu nikeyi,saboda zanyi missing d'inka,da dariyar da kake
sani,tunda nahad'u dakai ka kawarda duk wata damuwata kasanya ma zuciyata farin
ciki ina godiya sosai"
"Kin can-canci komai habibty,zan iya yimiki komai,sannan zan iya yin komai akanki"
Ya jinjina kai
"Dagaske habibty,zan iya bada rayuwata akanki"
Wata sassanyar ajiyar zuciya tasauke,tana jin wani farinciki na ratsa illahirin
zuciyarta
Ta d'aga kai tana kallon saman bishiyar wacce iska ke kad'a ganyayyakinta,suna
kad'awa ahankali
"Bansan meyasa kake sona ba,duk da nasan matsayina be kai ace ka soni ba"
Yace
"Nima kaina bansan meyasa ba,abu d'aya ne nasani na kuma yarda dashi,shine allah ne
ya jarabceni da k'aunarki,habibty bazan iya rayuwa idan babu keba,kuma kada kiyi
tunanin nafad'a mikine dan kawai soyayya
Ta kuma sauke ajiyar zuciya da yin shuru na y'an sakwanni sannan tace
"Nima ina sonka Aasim,kuma insha allahu zan rayu tare da Kai,dannasan zan rayu
cikin farin ciki idan na kasance tare da Kai"
Aasim yayi murmushi da alamu maganar da ta fad'a tayi masa dad'i sosai
"Nagode habibty,bari nabarki kikoma ciki,tunda sanyin na damunki"
Tace
"Yadai da magana ne indawo?
"Rauda!
"Ina sonki"
Koda ta koma d'aki, murmushi be bar fuskarta ba,taci dambun sosai tasha Lipton
sannan ta kwanta zuciyarta cike da tunaninsa
Washe gariDa wuri ta shirya zuwa lectures,tana tafiya tana tunanin meyasa be kirata
ba yau,dan kullum da asuba sai ya kirata,shike tashin su sallah,
Haka ma idan gari yayi haske sai ya kirata yace ta tashi ta shirya
Wunin ranar wayar sa bata shiga ba,data kira sai taji a kashe
"Yau tun safe Nike kiran wayar Aasim a kashe,shine duk hankalina ya tashi
wallahi,dan bantab'a kiransa naji irin haka ba"
"Nima nayi tunanin hakan,amma kuma da fad'uwa wayar tayi,da yazo yafad'a min kuma
da na gansa acikin makaranta,amma fa banga alamunsa ba,har inda yasaba tsayawa naje
bangansa ba, shiyasa nike tunanin ba lafiya ba"
Rauda tayi shuru kawai dan ita zuciyarta tafi bata ba lafiya ba
Daren ranar batayi wani baccin kirki ba,washegari ma haka takira wayar yafi sau
d'ari amma abu d'aya ake gaya mata,akashe
Hankalinta ya tashi sosai,ko abinci takasa ci,bata tab'a sanin tana k'aunar sa ba
sai a lokacin
Hakan yasa bayan tafito daga lectures tayanke shawarar zuwa department d'insu ta
tambaya
Salma ta tambaya,
"Zan lek'a b'angaren su Aasim ne intambaya nagaji da zama cikin rashin sanin wani
Hali yike ciki"
Suka jera suka tafi,da isarsu suka tadda d'alubai na zaune suyi group-group sunata
fira da shewa da alamu sunfito daga lectures ne,wasu kuma suna ta bitar karatu
"Dan allah ina tambayar Aasim ne,kwana biyu bana ganinsa bansani ba ko lafiya?
"Aasim?
Yace
"Gaskiya bangane shi ba saidai ku tambayi wancan shine yike da list sunayen
gabad'aya kuma shi ze iya saninshi,amma ni ba lallai insanshi ba saboda muna da
yawa"
Tafad'a sannan suka k'arasa gurin wanda ya nuna musu suka mai sallama
"To gaskiya bamu san wani me suna haka ba,sai dai inba a department d'inmu yike ba"
Salma tace
"To ya akayi haka Rauda?ni al'amarinnan yafara d'aure min kai fa,ace a department
d'insu babu wanda yasansa?
Rauda ta sauke numfashi me nawi batare da ta ce komai ba, Dan gabad'aya jikinta
yayi sanyi
"Habibty...
Ji tayi k'afafunta suna neman kasa d'aukarta,hakan yasa ta durk'usa tana cigaba da
yin kukan
"Habibty please kiyi hak'uri,tashi kishiga mota, banaso hankalin mutane ya dawo
kanki"
Salma tawuce tabarsu,itako Rauda kifa kanta tayi agaban motar tana cigaba da yin
kukan da ta rasa ko na menene
"Dan girman Allah habibty,ki wa girman allah kiyi shuru,wallahi kukanki sosamin
zuciya yike yi"
"Please kiyi hak'uri nasan nayi kuskure, Amma ba wai da niyya nai hakan ba,tafiya
ce takamani kuma cikin gaggawa......
"Okay idan tafiya takamaka baka iya sanar min kafin katafi?
"Naso insanar dake kafin intafi amma saboda yadda tafiyar tazo min bansamu daman
kiranki ba"
Jingina tayi da kujerar motar batare da ta k'ara cewa komai baYa matso kusa da ita
yana cigaba da cewa
"Abunda natsana a duniya shine inga hawaye a fuskarki, narok'eki habibty, ki tsayar
da hawayennan haka"
"Dan Allah karka k'ara yimin irin haka,bakasan halin da na shigaba wallahi nikad'ai
nasan tashin hankalin dana shiga"
Ya jinjina kai
"Shikenan, insha'allah bazan sake ba,kin hak'ura yanzu?
Yayi murmushi
"Yauwa tawan Allah yabar minke,yanzu fad'amin ina kikeso muje,gurin shan ice
cream,gurin cin tantabara ko gurin saida dambu?
Ita ko Rauda zuba mai fararen idanuwanta tayi tana sauke ajiyar zuciya
"Zahiri tana sonsa acikin zuciyarta, Wanda bata tab'a tunanin zata k'ara sa wani
d'a namiji a cikin zuciyarta ba
Sai gashi Aasim ya canza mata tunani yasa ta k'ara komawa soyayya
"Aasim kasa na karya alk'awarin dana d'aukar ma kaina,na bazan sake yin soyayya
ba,gashi yanzu zuciyata tagama amincewa dakai
Inada wata kalar zuciya da bata iya yin soyayya ba,idan harna fara son mutum to
gabad'aya hankalina gushewa yikeyi
Dan allah kada kayi amfani da son danike maka,ka wahalar min da zuciyata,nasha wuya
a baya banaso nasake mai-maita wa"
Yavcigaba da cewa
"Inaso kiyimin alk'awarin ko da nan gaba kin gano wani abu da baki san da shi ba a
tare Dani,to kiyi min alk'awari bazaki rabu dani ba,ba kuma zaki dena sona ba,
sannan kuma zaki gafarceni abisa b'oye mikin da nayi"
Kallonsa takeyi cikin rashin fahimta dan gabad'aya bata fahimci inda maganarsa ta
dosa ba
"Bangane ba,dama kana b'oye min wani abu ne?to meyasa?kuma menene shi?
"Lokaci na zuwa,da nasan dole zaki gane gaskiya,aduk lokacin dana tuna hakan sai
inji hankalina ya tashi dan bansan wani hukunci zaki d'auka a lokacin ba"
"Owo nafahimta,kana da aure ne ko?kana da mata shine ka b'oye kak'i fad'amin ko?
"Kai, lokacin ma ko haihuwata anyi?ohhh na tuna anhaifeni lokacin kenan tun ina
jaririya ko?
Dariya yayi Yana paka motar a harabar gurin saida Ice cream
"Kinga habibty muje musiyo muyi mu koma,yanzu aka kirani akafad'a min muna da
meeting"
"Kace yanzu aka kiraka?da wace wayar to ince ga wayarnan a ajiye,kuma ni tunda
nashigo motarnan banji ankirata ba?
"Ook muje"
Basu wani b'ata lokaci ba,suna shiga tazab'i kalar ice cream d'in datake so suka
fito
Yana ajiyeta ya juyaDa daddare bayan tayi shirin kwanciya,ta kira wayarsa,tagama
ringing be d'auka ba
"Habibty bamu gama meeting d'inba haryanzu,ki kwanta kiyi bacci ina sonki"
Murmushi tayi tare da rungume wayar a k'irjinta baccin da batayi kwana biyu ba kuwa
yad'auketa
Bayan sati d'aya, hankalinta ya kwanta,dan suna tare soyayyar su nadad'a yin k'arfi
Ranar wata laraba,tashirya dan zuwa gurin saloon,dama sunyi dashi intaje shi zeje
yad'aukota
"Rauda ko?
"Eh itace"
Rauda tak'ara kallonta, bata tab'a ganinta ba,to a ina tasan ta?har tasan sunanta?
Baki san akwai wasu jinsi dazasu iya biyowa ta suffar mutane su cutar dake ba?
Cikin raahin fahimta Rauda ke kallonta amma takasa K'ara cewa komai
"Ya kamata dai kirink'a ban-bance jinsin mutum da kuma na aljani,domin yana tare
dake akodayaushe
Nabarki lafiya"
Tana gama fad'ar haka ta dire ko cewa me napep d'in ya tsaya batayi ba
Taciro kud'insa tabasa, dasauri tashiga shagon tazauna tana maida numfashi
"Aa bakomai"
Amma cikin zuciyarta mamaki da kuma al'ajabin saima ne,me take nufi da yakamata ta
rink'a ban-bance jinsin mutum da na aljani?
"Steaming"
Har aka kammala mata bata dawo cikin natsuwarta ba,juyayin abunda yafaru kawai
takeyi
Tana zaune ana taje mata kai, Aasim yayi sallama dayike yasan wurin ya tab'a kawota
Yashiga shagon da murmushi a fuskarsa yana kallon gashin kanta da yayi bak'i sid'ik
yana ta shek'i
Ta jinjina Kai tana janyo d'an kwalinta zata d'aura gaban makeken madubin da ke
manne a bango
Gabanta ne yafad'i Ras, yayinda ta ga Aasim sanye da wasu kaya irin na sarakai ta
cikin madubin kuma yayi wani bau farinsa da kyansa ya ninka wanda tasani
Tayi saurin kauda kanta a madubin ganin madubin yafara yimata dishi-dishi
Amira tace
"Nima dai yau tunda tashigo haka naganta"
"Shikenan muje"
Yad'an waigo yana dubanta ganin tana tsaye bata da niyyar tafiya
Yana cewa
"Kifad'a min meke faruwa,ni nasan akwai wani abu hakanan dai bazan ganki a daburce
ba"
Ya kalleta
"Eyeh,mene?mekika ce?
"Akwai abunda nagani da nakasa fahimta, please k'afad'a min gaskiya kai mutum ne?
"Banyadda ba,idan kai mutum ne ya akayi siffarka,da kayan jikinka suka sauya acikin
madubi?
Ta gyad'a kai tana zage jakar ta ta ciro reza ta bud'e tare da sawa akan
yatsanta ta danna
"Ko na yarda dakai inaso inga jini a jikinka,idan har kasan abunda kafad'a min
gaskiya ne to ka amsa kayi abunda nace"
"Habibty..,.
A memakon taga jini,wani kalar abu taga yana fitowa kore shataf
Ganin k'ofar bata da alamun bud'ewa yasa ta juyo tana kallonsa tare da had'e hannun
ta guri d'aya cikin kuka da tsananin firgici tace
"Nidai kabud'emin infita,karabu dani kayi hak'uri,kar ka cutar Dani wallahi banyi
ma komai ba......
Shurun ko tayi dan tsawar ta k'ara razana ta, kyar-kyarwa kawai takeyi kamar anciro
ta da ga cikin k'an-k'ara
"Inda zan cutar dake da tuni na cutar dake,kinsan adadin shekarun da nayi ina tare
ke ne?
Da zan cutar dake da tuni ban cutar dake ba,ko kinga al'amarin cutarwa a tare Dani?
Ta jinjina Kai tana kallonsa,ayanzu tsoron yafara raguwa dan ko tafahimci ba cutar
da ita d'in zeyi ba
Yacigaba da cewa
Kuma ni mijinki ne,inada aure dake tun shekaru hud'u da suka wuce,sannan har da y'a
a tsakanina dake"
Ya jinjina Kai
Yacigaba dacewa
"Zanyi miki bayanin ko ni waye,da kuma yadda akai na aure ki har kika haihu batare
da kinsani ba"
🙎🏻
Typing dakwai wahala Allah, muhad'u a Page 13
Yarfillo.🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)
1⃣ 2⃣ 1⃣2⃣
1⃣2⃣
AGE
Wannan Page d'in nakine mamana,allah ya k'ara miki lafiya yasa kaffarane, ina
k'aunarki araina domin kin kasance uwa tagari me share min kuka na a kodayaushe.🥰
NA KASA MANTAWA DAKE😭
Dede da rana d'aya, kodayaushe cikin tuna ki nikeyi, hak'ik'a nayi babban rashi da
na rasaki,y'ar uwata hajara aliyu allah Nike rok'o ya jik'anki da rahama,ya gafarta
Miki,yasa aljannah ce makomarki Amin😭😭😭
"Akwai wani sabon restaurant da aka bud'e babu kalar abincin gargajiyan da basa
saidawa,kuma har dare suna kaiwa,anan na siyo"
Ta jinjina Kai
Ya cigaba da cewa
"Sannan dakike cewe a iya sanin ki babu inda ake saidawa a kusa -kusannan yawo kike
yi? Keda sai kiyi sati ma wani zubin baki lek'a ko wajen makaranta ba"
Ya amsa da Amin
Taja iska alamar sanyi na ratsa jikinta sosai tana tana mammatse jikinta da yike
rawa kad'an saboda sanyin dake kad'ata
Ya bata amsa
"Me kikagani?
Rauda tace
"Gani nayi bakasa rigan sanyi ba,kuma ko rawar sanyi bakayi"
"Ni me nayi?
"Allah har fargaban ayi hutu nikeyi,saboda zanyi missing d'inka,da dariyar da kake
sani,tunda nahad'u dakai ka kawarda duk wata damuwata kasanya ma zuciyata farin
ciki ina godiya sosai"
"Kin can-canci komai habibty,zan iya yimiki komai,sannan zan iya yin komai akanki"
Ya jinjina kai
"Dagaske habibty,zan iya bada rayuwata akanki"
Wata sassanyar ajiyar zuciya tasauke,tana jin wani farinciki na ratsa illahirin
zuciyarta
Ta d'aga kai tana kallon saman bishiyar wacce iska ke kad'a ganyayyakinta,suna
kad'awa ahankali
"Bansan meyasa kake sona ba,duk da nasan matsayina be kai ace ka soni ba"
Yace
"Nima kaina bansan meyasa ba,abu d'aya ne nasani na kuma yarda dashi,shine allah ne
ya jarabceni da k'aunarki,habibty bazan iya rayuwa idan babu keba,kuma kada kiyi
tunanin nafad'a mikine dan kawai soyayya
Ta kuma sauke ajiyar zuciya da yin shuru na y'an sakwanni sannan tace
"Nima ina sonka Aasim,kuma insha allahu zan rayu tare da Kai,dannasan zan rayu
cikin farin ciki idan na kasance tare da Kai"
Aasim yayi murmushi da alamu maganar da ta fad'a tayi masa dad'i sosai
Tace
"Yadai da magana ne indawo?
"Rauda!
"Ina sonki"
Yafad'a,takuma yin murmushi tare da juyawa dasauri,tashige ciki
Koda ta koma d'aki, murmushi be bar fuskarta ba,taci dambun sosai tasha Lipton
sannan ta kwanta zuciyarta cike da tunaninsa
Washe gariDa wuri ta shirya zuwa lectures,tana tafiya tana tunanin meyasa be kirata
ba yau,dan kullum da asuba sai ya kirata,shike tashin su sallah,
Haka ma idan gari yayi haske sai ya kirata yace ta tashi ta shirya
Wunin ranar wayar sa bata shiga ba,data kira sai taji a kashe
Salma tace
"Damuwa Kuma? Tamece?
"Yau tun safe Nike kiran wayar Aasim a kashe,shine duk hankalina ya tashi
wallahi,dan bantab'a kiransa naji irin haka ba"
"Nima nayi tunanin hakan,amma kuma da fad'uwa wayar tayi,da yazo yafad'a min kuma
da na gansa acikin makaranta,amma fa banga alamunsa ba,har inda yasaba tsayawa naje
bangansa ba, shiyasa nike tunanin ba lafiya ba"
Rauda tayi shuru kawai dan ita zuciyarta tafi bata ba lafiya ba
Daren ranar batayi wani baccin kirki ba,washegari ma haka takira wayar yafi sau
d'ari amma abu d'aya ake gaya mata,akashe
Hankalinta ya tashi sosai,ko abinci takasa ci,bata tab'a sanin tana k'aunar sa ba
sai a lokacin
Salma ta tambaya,
"Zan lek'a b'angaren su Aasim ne intambaya nagaji da zama cikin rashin sanin wani
Hali yike ciki"
Suka jera suka tafi,da isarsu suka tadda d'alubai na zaune suyi group-group sunata
fira da shewa da alamu sunfito daga lectures ne,wasu kuma suna ta bitar karatu
"Dan allah ina tambayar Aasim ne,kwana biyu bana ganinsa bansani ba ko lafiya?
"Aasim?
"Eh "
Yace
"Gaskiya bangane shi ba saidai ku tambayi wancan shine yike da list sunayen
gabad'aya kuma shi ze iya saninshi,amma ni ba lallai insanshi ba saboda muna da
yawa"
Tafad'a sannan suka k'arasa gurin wanda ya nuna musu suka mai sallama
"To gaskiya bamu san wani me suna haka ba,sai dai inba a department d'inmu yike ba"
Salma tace
"To ya akayi haka Rauda?ni al'amarinnan yafara d'aure min kai fa,ace a department
d'insu babu wanda yasansa?
Rauda ta sauke numfashi me nawi batare da ta ce komai ba, Dan gabad'aya jikinta
yayi sanyi
Rauda ko kanta na k'asa ko kallon motar batayi ba dan damuwar dake zuciyarta nema
takeyi tafi k'arfinta
"Habibty...
Ji tayi k'afafunta suna neman kasa d'aukarta,hakan yasa ta durk'usa tana cigaba da
yin kukan
"Habibty please kiyi hak'uri,tashi kishiga mota, banaso hankalin mutane ya dawo
kanki"
Salma tawuce tabarsu,itako Rauda kifa kanta tayi agaban motar tana cigaba da yin
kukan da ta rasa ko na menene
"Dan girman Allah habibty,ki wa girman allah kiyi shuru,wallahi kukanki sosamin
zuciya yike yi"
"Please kiyi hak'uri nasan nayi kuskure, Amma ba wai da niyya nai hakan ba,tafiya
ce takamani kuma cikin gaggawa......
"Okay idan tafiya takamaka baka iya sanar min kafin katafi?
"Naso insanar dake kafin intafi amma saboda yadda tafiyar tazo min bansamu daman
kiranki ba"
Jingina tayi da kujerar motar batare da ta k'ara cewa komai baYa matso kusa da ita
yana cigaba da cewa
"Abunda natsana a duniya shine inga hawaye a fuskarki, narok'eki habibty, ki tsayar
da hawayennan haka"
"Dan Allah karka k'ara yimin irin haka,bakasan halin da na shigaba wallahi nikad'ai
nasan tashin hankalin dana shiga"
Ya jinjina kai
"Shikenan, insha'allah bazan sake ba,kin hak'ura yanzu?
Ta d'aga kai alamar eh
Yayi murmushi
"Yauwa tawan Allah yabar minke,yanzu fad'amin ina kikeso muje,gurin shan ice
cream,gurin cin tantabara ko gurin saida dambu?
Ita ko Rauda zuba mai fararen idanuwanta tayi tana sauke ajiyar zuciya
"Zahiri tana sonsa acikin zuciyarta, Wanda bata tab'a tunanin zata k'ara sa wani
d'a namiji a cikin zuciyarta ba
Sai gashi Aasim ya canza mata tunani yasa ta k'ara komawa soyayya
"Aasim kasa na karya alk'awarin dana d'aukar ma kaina,na bazan sake yin soyayya
ba,gashi yanzu zuciyata tagama amincewa dakai
Inada wata kalar zuciya da bata iya yin soyayya ba,idan harna fara son mutum to
gabad'aya hankalina gushewa yikeyi
Dan allah kada kayi amfani da son danike maka,ka wahalar min da zuciyata,nasha wuya
a baya banaso nasake mai-maita wa"
Yavcigaba da cewa
"Inaso kiyimin alk'awarin ko da nan gaba kin gano wani abu da baki san da shi ba a
tare Dani,to kiyi min alk'awari bazaki rabu dani ba,ba kuma zaki dena sona ba,
sannan kuma zaki gafarceni abisa b'oye mikin da nayi"
Kallonsa takeyi cikin rashin fahimta dan gabad'aya bata fahimci inda maganarsa ta
dosa ba
"Bangane ba,dama kana b'oye min wani abu ne?to meyasa?kuma menene shi?
Yayi murmushin da ya tsaya masa iya labb'a kawai
"Lokaci na zuwa,da nasan dole zaki gane gaskiya,aduk lokacin dana tuna hakan sai
inji hankalina ya tashi dan bansan wani hukunci zaki d'auka a lokacin ba"
"Owo nafahimta,kana da aure ne ko?kana da mata shine ka b'oye kak'i fad'amin ko?
"Agurinki kenan amma ni agurina had'uwarmu tun bayan shekara ashirin ne?
"Kai, lokacin ma ko haihuwata anyi?ohhh na tuna anhaifeni lokacin kenan tun ina
jaririya ko?
Dariya yayi Yana paka motar a harabar gurin saida Ice cream
"Kinga habibty muje musiyo muyi mu koma,yanzu aka kirani akafad'a min muna da
meeting"
"Kace yanzu aka kiraka?da wace wayar to ince ga wayarnan a ajiye,kuma ni tunda
nashigo motarnan banji ankirata ba?
"Ook muje"
Basu wani b'ata lokaci ba,suna shiga tazab'i kalar ice cream d'in datake so suka
fito
Bayan yatada motar sunfara tafiya tace
Yana ajiyeta ya juyaDa daddare bayan tayi shirin kwanciya,ta kira wayarsa,tagama
ringing be d'auka ba
"Habibty bamu gama meeting d'inba haryanzu,ki kwanta kiyi bacci ina sonki"
Murmushi tayi tare da rungume wayar a k'irjinta baccin da batayi kwana biyu ba kuwa
yad'auketa
Bayan sati d'aya, hankalinta ya kwanta,dan suna tare soyayyar su nadad'a yin k'arfi
Ranar wata laraba,tashirya dan zuwa gurin saloon,dama sunyi dashi intaje shi zeje
yad'aukota
Sun d'an yi nisa kad'an wata kyakkyawar budurwa ta tsaida a dai-daitan da Rauda ke
ciki
"Rauda ko?
"Eh itace"
Rauda tak'ara kallonta, bata tab'a ganinta ba,to a ina tasan ta?har tasan sunanta?
Baki san akwai wasu jinsi dazasu iya biyowa ta suffar mutane su cutar dake ba?
Cikin raahin fahimta Rauda ke kallonta amma takasa K'ara cewa komai
"Ya kamata dai kirink'a ban-bance jinsin mutum da kuma na aljani,domin yana tare
dake akodayaushe
Nabarki lafiya"
Tana gama fad'ar haka ta dire ko cewa me napep d'in ya tsaya batayi ba
Taciro kud'insa tabasa, dasauri tashiga shagon tazauna tana maida numfashi
"Aa bakomai"
Amma cikin zuciyarta mamaki da kuma al'ajabin saima ne,me take nufi da yakamata ta
rink'a ban-bance jinsin mutum da na aljani?
"Steaming"
Tana zaune ana taje mata kai, Aasim yayi sallama dayike yasan wurin ya tab'a kawota
Yashiga shagon da murmushi a fuskarsa yana kallon gashin kanta da yayi bak'i sid'ik
yana ta shek'i
Ta jinjina Kai tana janyo d'an kwalinta zata d'aura gaban makeken madubin da ke
manne a bango
Gabanta ne yafad'i Ras, yayinda ta ga Aasim sanye da wasu kaya irin na sarakai ta
cikin madubin kuma yayi wani bau farinsa da kyansa ya ninka wanda tasani
Tayi saurin kauda kanta a madubin ganin madubin yafara yimata dishi-dishi
Amira tace
"Nima dai yau tunda tashigo haka naganta"
"Shikenan muje"
Yad'an waigo yana dubanta ganin tana tsaye bata da niyyar tafiya
Yana cewa
"Kifad'a min meke faruwa,ni nasan akwai wani abu hakanan dai bazan ganki a daburce
ba"
Ya kalleta
"Eyeh,mene?mekika ce?
"Akwai abunda nagani da nakasa fahimta, please k'afad'a min gaskiya kai mutum ne?
"Banyadda ba,idan kai mutum ne ya akayi siffarka,da kayan jikinka suka sauya acikin
madubi?
Ta gyad'a kai tana zage jakar ta ta ciro reza ta bud'e tare da sawa akan
yatsanta ta danna
"Ko na yarda dakai inaso inga jini a jikinka,idan har kasan abunda kafad'a min
gaskiya ne to ka amsa kayi abunda nace"
"Habibty..,.
A memakon taga jini,wani kalar abu taga yana fitowa kore shataf
Ganin k'ofar bata da alamun bud'ewa yasa ta juyo tana kallonsa tare da had'e hannun
ta guri d'aya cikin kuka da tsananin firgici tace
Shurun ko tayi dan tsawar ta k'ara razana ta, kyar-kyarwa kawai takeyi kamar anciro
ta da ga cikin k'an-k'ara
"Inda zan cutar dake da tuni na cutar dake,kinsan adadin shekarun da nayi ina tare
ke ne?
Da zan cutar dake da tuni ban cutar dake ba,ko kinga al'amarin cutarwa a tare Dani?
Ta jinjina Kai tana kallonsa,ayanzu tsoron yafara raguwa dan ko tafahimci ba cutar
da ita d'in zeyi ba
Yacigaba da cewa
Kuma ni mijinki ne,inada aure dake tun shekaru hud'u da suka wuce,sannan har da y'a
a tsakanina dake"
Ya jinjina Kai
"Zanyi miki bayanin ko ni waye,da kuma yadda akai na aure ki har kika haihu batare
da kinsani ba"
🙎🏻
Typing dakwai wahala Allah, muhad'u a Page 13
Yarfillo.
[20/10, 8:39 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)🧕🏻
1⃣ 3⃣ 1⃣3⃣
1⃣3⃣
AGE
Wannan Page d'innaki ne besty hajiyayye, Allah ya kaimu December musha biki,mu
rak'ashe mu kwaso shoki😁😁
Fatan alkhairi ga golden pen writters gabad'aya,ina jinjina muku da kuma fatan
Allah yak'ara mana basira.
3:28🕒pm.
WED,APR 24✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
"Duk da banso ace zansanar dake a wannan lokacin ba,amma ya zamar min dole,
Amma ina rok'onki da kisa ma zuciyarki natsuwa, kicire duk wani tsoro dake cikinta
wallahi ina yimiki so me tsanani bazan iya rayuwa idan babu ke ba,dan allah ki
fahimceni ki kuma amshi uzurina"
Yafad'a cikin wani irin yanayi wanda yak'ara sa jikinta yayi sanyi
Ganin abun takeyi kamar a mafarki,ga jikinta yayi wani mugun mutuwa
Daky'ar take iya motsa jikinta, hak'ik'a zuciyarta na cike da tarin tsoro amma
maganganun sa sun d'an rage tsoron
Kallonsa kawai takeyi takasa gasgata al'amarin,wai Aasim ba mutum bane,kenan shine
JINNUL AASHIQUE d'in da malamai ke fad'a Mata,yana hana ta aure.
"Rauda!
"Nagode"
"Sunana Aasim,d'a agurin sarki Ramzad, mahaifina shike mulkar masarautar rauhanai.
Mahaifina na sona sosai dan yana fifitani a kan yarima sarman agaban kowa, Wanda
hakan ke bak'anta ran sarauniya jalila(kishiyar mahaifiyarsa)
Masarautar mu babban masarauta ce dake can wata duniya,muna rayuwa kamar yadda ku
mutane kukeyi
Kuma muna saukowa zuwa wannan duniyar duk k'arshen sati sau d'aya domin muga abunda
yike tafiya
Mukuma shak'ata,mahifina yana da zafi sosai dan idan yayi magana d'aya to baya
canza ta
Amma kuma duk yadda yakai ga zafi,idan narok'e sa akan abu yana yi yakuma hak'ura
Hakan yasa ko samran da mahaifiyar sa idan suna so suyi wani abun sai sunbiyo ta
hanyata.
Muntaso cikin rayuwar jindad'i bamu tab'a neman wani abu mun rasa baMuna da k'arfin
iko da kuma k'arfin mulki,tayadda ake tsoron mu a ko'ina,duk wani aljani fargaban
ya had'u damu yikeyi
Akwai wata rana munsauko wannan duniyar,nida fada wa na,muna tafiya cikin nishad'i
da kwanciyar hankali
Kwatsam sai muka fara jin k'amshin salbaan, salbaan wani abune da ake haihuwar
rauhanai dashi kuma kowani rauhani da kalar nasa salvaan d'in
Amma abun mamaki sai naji k'amshin shi a duniyar mutane,na lula cikin tunanin ya
akayi haka?meke faruwa?
Maganar d'aya daga cikin fadawa nane ya katsemin tunanin dana tafi inda yace
"Naji,amma ya akayi haka?tunda muke zuwa wannan duniyar bantab'a jin irin haka ba
sai yau"
Ba faden me suna iliyas,wanda shine babba kuma shugaba agaba d'aya fada wana yace
"Ranka shidad'e idan kabani dama zanje naduba inda k'amshin ke futowa"
"Ranka shidad'e haihuwa ce akayi,kuma k'amshin daga jikin jaririyar yike fitowa,ina
ganin kaman a jikinta salbaan d'in yake"
Natambayesa da mamaki
Ya jinjina kai
"Eh ranka shidad'e"
Nayi miki addu'o i nakuma sa wata rauhaniya da tadinga kula dake da kuma
al'amuranki"
Daganan kuma nayi tafiya nisa wacce bandawo ba sai da nayi shekaru goma Sha biyar
Bayan dawowa na,nazo wannan duniyar domin naga abubuwan da suka canza bayan tafiya
ta
Munzo wucewa ta wuraren gidanku sai k'amshin salbaa nanki ya bugi hancina
Nayimata umarnin data fita,sannan nazauna gefen gadon ina k'are miki kallo
Wanda narasa dalilin hakan,wani dare ina kwance d'akina naji babu abunda nike so
illa naganki
Hakan yasa naciro wani madubi narik'e a hannuna tare da ambaton sunanki
Bayyanar da kikayi acikin madubin itace mafarin komai,domin babu kaya ajikinki da
alamu wanka kikeyi
Nayi saurin kauda madubin domin a k'a'idar mu bama kallon mutane a wannan yanayin
Alokacin dakika cika shekaru sha shida, alokacin nagama afkawa cikin kogin
k'aunarki
Ban b'oye wa ammi komai ba,nasanar da ita dakuma auranki da nikeso inyi
Ammi tayi k'ok'orin fahimtar dani akan yaza'ayi ina jinsin rauhan in auri
bil'adama?
Na nuna mata cewa nidai ina k'aunar ki kuma inason in aureki idan har tanason
farincikina to ta amince min
Tace min to yazanyi da gimbiya saima y'ar k'anin mahaifina wacce tun muna yara take
Sona?
Na sanar da ita cewa,ban tab'a son saima ba,ni ke nikeso kuma dake kad'ai zan iya
zaman aure
Na ko yi hakan,dan inbaki manta ba akwai wata rana dakikayi mafarkin wasu fararen
mutane sunzo d'aura auranki
To alokacinne aka d'aura aure na dake,na kuma dunga rayuwar aure dake batare da
kinsani ba
Wanda zuciya ta ta K'ara zafafa a k'aunar ki,tayadda bana iyayin kwana biyu banzo
naganki ba.
Alokacin manema suka fara b'ullo Miki,naso nad'auki mataki domin ina tsananin
kishinki sai ammi ta hanani tanuna min ba dai-dai bane
Alokacin da kikai sha bakwai,alokacinne me martaba yagano auren dake tsakanina dake
Wanda yashiga b'acin ran da duk wani wanda yike cikin masarautar sai da hankalinsa
ya tashi
Ya umarci da a hukuntani ni da ke
Be k'ara cemin komai ba,yasa aka hukuntani abisa laifin b'oye masa danayi
Amma kuma be zartar da hukunci atsakanina dake ba wanda bansan abunda yasa sa yin
hakan ba.
Duk da me martaba baya son auren,kuma be amince da shi ba,yayi matuk'ar farin ciki
domin wannan karonne karo nafarko da aka sami jika a masarautar
Nayi farin ciki sosai haka ma ammi,ke gabad'aya masarautar sunyi farin ciki da
haihuwar shahida
Hakan yasa taga gata,da riritawa,kuma tana tare da me martaba a kodayaushe domin
yana sonta sosai
Maganar hana auranki kuma,ina kishinki bazan tab'a barin wani d'a namiji ya rab'e
ki ba,duk ko ranar da hakan ta kasance to sai dai ranar da numfashina ze tsaya
Dan allah ki amince mucigaba da rayuwa ahakan,babu abunda bazan iyayimiki ba indai
zesaki farinci kuma inaso yazama sirri atsakaninmu..........
Ahankali tabud'e idanuwanta da sukayi mata nawi,dan tunda yayi nisa a labarinsa
taji kanta kaman and'aura mata dutse
Sai taganta kwance kan gadonta,ga salma gefenta tana ta sharar bacci
Ta tambayi kanta tana k'ara yin mamaki,agogo ta kalla k'arfe Sha d'aya nadare
Tabbas mafarki tayi dan alokacin dasuna magana dashi ko magriba ba tayi ba yanzu
kuma shad'aya na dare
Ta janyo wayarta dake gefe ta danna numbansa bugu d'aya yad'auka yana ambaton
sunanta
"Habibty.....
"Wai ni ba mutum bane ko?kuma inada aure dake harda y'a ko?
Ya katseta
"Ba mafarki kikayi ba habibty zahirine,ganin halin dakika shigane yasa na maidaki
d'aki"
"Aasim! Dan Allah kacemin mafarki nikeyi,taya zaka kasance ba jinsin mutum
ba,wallahi ina sonka,idan wasa kakeyi kadena..........
"Kak'yaleni nace!!!!
"Salma,inaso inje gida,inason inga mamana,bazan iya cigaba da zama a makarantar nan
ba"
Salma tace
Salma tace
"Kinsan k'arfe nawane yanzu da zaki doshi kaduna??
Salma hankalinta yak'ara tashi dan bata tab'a ganinta cikin wannan yanayin ba
"Ba mutum bane,ze iya zuwa Nan,kar ya cutar Dani,salma ki taimakeni,wallahi tsoro
nikeji"
Salma tayi jugum tana kallon ta,da kuma tunanin abunda yasameta.
Salma tadad'e da gama abun Kari,tana zaune gefenta tana jiran farka warta
"Yajikinnaki?
Salma ta kuma tambayar ta,
"Dasauk'i"
Bata ce mata komai ba tabi bayanta da kallo,sannan ta mai da idanuwanta kan wayar
ta da salma ta had'a mata wacce ta ragar-gaje sakamakon bugata datayi a k'asa jiya
Gyad'a mata kai kawai Rauda tayi,tana bin bayanta da kallo harta fice
"Habibty"
"Dakata banason jin komai daga bakinka,mekayi kenan?kana ganin kayi dai-dai?kasan
bak'in cikin da zuciya ta shiga alokacin da aka fasa aurena har sau biyu?
Naji alokacin kamar bak'in ciki ze kasheni,haka b'angaren samarina da mutum yafara
zuwa sai ya dena ashe kaine kake hanasu, kenan ahaka kakeso ink'ara ci rayuwa ta
batare da nayi aure ba ko?
Ya girgiza kai
"Ina tare dake,duk abunda d'an adam zeyi miki zan iya yimiki ninkin baninkin
shi,amma tabbas maganar aure ki cireta a zuciyarki"
Dafa kanta tayi dayike Sara mata tana ambaton sunan allah
Bayan sati biyu,bata k'ara ganinsa ba,bata kuma k'ara jin d'uriyarsa ba
Har suka kammala jaraba wa, suka fara Shirin tafiya gida
Tana cikin had'a kayanta taga wata farar takadda
Tafara karantawa
Tasan takaddar Aasim ce,ta ninketa tana sauke ajiyar zuciya sannan tacigaba da
had'a kayan
Tare suka fito da Salma,dan yayan salman dake gombe yazo zed'auketa
Suka gaisa da shi, sannan sukayi sallama,ita kuma Rauda tafito bakin titi tana
jiran adai-deta sahu wacce zata Kai ta Tasha
Ya Salam, tafad'a afili dan yayi kyau nafitar hankali, azuciyarta tace dama ashe
wannan kyan da walaki,dan yayi yawa
"Habibty Bismillah"
Ajiyar zuciya tasauke tana jingina da kujerar motar,ko minti biyu cikakku ba ayi ba
taga motar ta tsaya acikin wani gida me shegen kyau
"Gidanki Mana"
Ta girgiza Kai
"Nariga nakira mama nafad'a mata nataho,idan taga nadad'e fa?nide kabarni intafi"
Ta girgiza kai,
Yacigaba da cewa
"Idan a mota zakije tafiyar awa arba'in da hud'uce,dan haka ki kwantar da
hankalinki acikin minti d'aya zan iya kaiki har cikin gidanku"
"Muje madam"
Kamar bazata fito ba,sai kuma tafito tana k'are ma gidan kallo,wanda yasha ado da
furanni masu shegen kyau
"Zauna"
Yak'arasa fad'a yana janyo wani k'aramin tebur ya ajiye aganta tare da
ambaton,tea,aarish
"Oya Bismillah"
Abun al'ajabi gani tayi wayam,babu komai akan tiren sannan taji cikinta yayi dam
"Rauda!!!
"Dan allah ki yafemin,nasan nayi kuskure kuma ban kyauta miki ba,amma ki gafarceni
wallahi ina k'aunar ki,son da nikeyi miki ne yasa na aikata duk abunda nayi
Bakisan yadda naji ba,dakike jin wani iri akaina,zan iya yimiki komai dan insaki
farinciki, nayi miki alk'awari amma inaso ki yafemin, bazan iya zama cikin
kwanciyar hankali ba muddin kina fushi Dani"
"Na yafema,amma kaima kayi min alk'awarin bazaka cutar dani ba"
"Shikenan"
"Mik'e habibty"
"Nasan dama zaki fahimceni,abu d'aya nikeso kiyimin,shine kiyarda ina k'aunarki"
Ji tayi gabad'aya tsoronsa da takeji ya yaye,ta Lumshe idanuwanta tana jin wani abu
na ratsa zuciyarta
"Aasim!
Ya amsa
"Na'am habibty"
"Habibty, kifad'a min duk abunda kikeso zanyi miki shi da izinin Allah"
"Shikenan nagode"
"Babu y'ar godiya,muje kizagaya gidan kigani komai natsara shine dan idan kika gani
ya burgeki"
"To muje"
Kama hannunta yayi suka fara zagaye gidan,sannan suka dawo bedroom
Shima antsara shi komai na d'akin kalar pink,sannan ya bud'e mata toilet d'in dake
ciki
"Wayace Miki,aduk sanda kikaga dama zakizo,kuma nima aduk sanda naga dama
zankawoki"
Hannunsa yasa yana shafa dokin wuyanta ahankali yakai kan zip d'in doguwar rigar
dake jikinta
Ta kallesa tace
"Yadai?
Ta girgiza kai aa
Kafin ta k'ara magana sai ganinta tayi cikin kwamin wanka shak'e da ruwa yasha wasu
k'ana-nun fulawowi jajaye wanda suka lullub'e saman ruwan
"Please kabani"
"Allah bazan baki ba sai kinyi wankan,idan kuma bazakiyi ba to taso ki amsa"
Ta jinjina kai
"Naji"
Ajiye kayan yayi akan abun wanke hannu,yafita ya kullo mata k'ofar
Tafito daga cikin kwamin zata d'auki,samtsin tiles ya kwasheta zata fad'i
Ta tambayesa da mamaki
Ya jinjina kai
"Eh dawowa nayi"
"Mutum ne inze shiga wuri sai ansani amma mu sai munga dama za'asani"
Baya tayi dasauri dan tama manta bata maida kayan jikinta ba
"Habibty I'm sorry bazan sake ba,amma miye laifina danna kalli matata??
"Bahaka bane"
"Aa kifad'a min gaskiya,yanzu danni ba mutum bane kin rage son dakikeyi min ko?
Gyad'a kai kawai yayi amma yanayin fuskarsa yanuna Babu dad'i
"Amma yanzu innakai ki,za'a ga kin kai dawuri, kibari nan da minti arba'in sai
inkai ki"
"Shikenan"
Sis nabila ina missing d'inki Allah ubangiji yabaki lafiya yasa kaffarene
Y'arfillo.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)🧕🏻
1⃣ 4⃣ 1⃣4⃣
1⃣4⃣
AGE
Wannan page d'innaki ne sis maman haidar,allah yak'ara mana k'arfin zumunci
atsakaninmu💛💛
Fatan alkhairi ga kowa,allah ya bamu ikon ganin wannan azumi dake gabato mu,ya kuma
bamu ikon aikata ayyuka acikinsa,masu ulcer allah yabamu lafiya👏🏻
Sis nabila allah yak'ara lafiya,naji dad'i dakika fara warwarewa allah kawo sauk'i
gabad'aya kiyi gyam dan bazamu barki kisha azumi ba ehe🤪🤪🤪
11:09🕒pm
SUN,APR 28✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
Gefen had'add'en gadon ya zauna,yana kallon kafet d'in dake malale gaban gadon.
Ita ko tana tsaye,tana kallonsa,sai kuma taji babu dad'i ganin yadda yana yinsa ya
sauya zuwa damuwa
"Aasim"
"Habibty bakiyi min komai ba,kawai dai inajin zuciyata babu dad'i ne,nasan bazaki
tab'a min kwatan son danike yimiki ba
Koda na kasance a jinsin d'an adam,bare kuma jinsin rauhan,shiyasa nike jin babu
dad'i danna tabbata da ace nakasance a cikin jinsin ki,da zanji dad'i domin ko
bakomai zuciyarki zata natsu dani koda baki soni kamar yadda Nike son kiba
Amma yanzu zuciyarki ba a natse take dani ba,ina tsoron wata rana ragowar sona daya
rage a zuciyarki shima yatafi kamar yadda natsuwar tatafi"
Tausayinsa taji ya mamaye zuciyarta,shin wani irin so yike mata ne har haka?
Ta tambayi zuciyarta
"Nima kaina bansan dalilin dayasa nike miki irin wannan son me tsanani ba,
Wani zubin har mamakin kaina nikeyi,amma abu d'aya nasani nakuma yarda dashi Allah
ne ya jarabceni da k'aunarki,
Rauda dan Allah kitaimakeni koda kwatan son da nike yimiki ne kiyimin,wallahi ina
sonki bansan tayaya zan fahimtar dake irin son da nikeyi miki ba"
Zuciyar tace ta k'ara yin rauni, cikin kwantar mai da hankali tace
Saboda bantab'a tunin al'amarin ka haka yike ba,amma nasan nan da wani d'an
lokaci,komai zeyi dede insha'allahu"
"Buk'ata??? Kamarya"
Tatambaya cikin rashin fahimta
Ya mik'e ya bud'e wata durowa yad'auko kwalin waya,sannan yadawo yazauna yana
mik'amata
"Nasan kina buk'atar waya,tundaKinfasa taki,ga wannan kiduba idan tayi miki to,idan
kuma batayi ba sai a canzo ta yanzu"
"Bawai batamin bane,tayi danyi saidai idan aka ganni da ita a gida fa,wa zance
yabani?
"Hakane,to fad'i wacce kike ganin babu matsala idan anganki da ita"
"Infinix note"
Ya gyad'a kai
"Babu komai"
"To"
Ta kallesa tace
"Babu abunda zanbaka?to mekakeso"
Matsowa yayi gab da ita,yana kallon cikin idonta
Tayi k'asa da kanta dan bata iya jure kallon cikin idanunsa
"To shikenan,kibani wad'annan labb'an kawai,masu kama da jar tufa,na minti uku
kawai"
"Labb'a?kayi me dasu??
Ta gane abunda yike Shirin yi, dasauri tak'ara sun kuyar da kanta tana k'ok'orin ja
baya
"To ai banace kin iya bane dama,kuma bance kiyi min ba,nida kaina zanyi"
"Nidai...nidai........
Wani irin yarrrrr taji jikinta nayi,ta lumshe idanuwanta a hankali tanajin
gab'ob'inta nafara sarewa
"Habibty!"
Tasauke ajiyar zuciya me nawi,tana jingina da jikin katangar zauren dan har lokacin
bata koma dede ba
Hanif yace
"D'azu nida mummyna"
Ta dire shi k'asa tana jan akwatinta,d'ayan hannunta kuma takama hannunsa suka nufi
cikin gida
"Dagaske?ina hanifa?
Dede lokacin suka shiga cikin gidan,da umma tafara cin karo,tana zaune kan tabarma
tana gyara wake
"Lafiya"
Har zata shiga d'akinsu ta hango inna a kicin, gudun kartayi laifi yasa takoma baya
ta tsaya daga bakin k'ofar tana gaisheta
"Ita d'inma a dak'ilen ta amsa,juyawa Rauda tayi ta shiga d'akinsu tana sallama
"Dallah jibeki k'atuwa dake kin wani shige jikinta ko kunya bakyaji"
"Kedai kice kawai kinji haushi ne,baki zo a auta ba,kuma mama tafi sona a kanki"
Anty ummi takuma harararta
"Kinga ummi zubo mata abinci,kibar min auta ta huta daga isowarta har kinfara
damunta?
Wacece Rauda?
Sannan Maryam (mama),allah ya azurtashi da yara dan umma yaranta takwas uku maza
biyar Mata
Sai mama,wacce take da uku,dan tayi haihuwa takwas amma uku ne kawai suka tsaya
Umma da inna kansu ahad'e yike dan komai tare sukeyi sun had'e ma mama kai babu
abunda ke shiga tsakaninsu face kyara da hantara
Mussaman da suka ga tana da hak'uri dan duk abunda zasuyi mata bata tab'a d'aga ido
ta kallesu bare tamaida musu martani
Haka suma y'ay'an sun tsani yaran d'akin mama,domin sun fisu kyau nesa ba kusa ba
Hakan yasa sauran y'ammatan suke tsananin jin haushin ummi da rauda dan duk inda
suka shiga sai an kallesu
Haka aka dinga aurar dasu duk wad'anda aka ga girmansu yazo d'aya kuma sunsami masu
neman auransu
Sai ahad'a su a aurar dasu,sau biyu ana fasa auran Rauda,kuma duka biyun sai ranar
d'aurin ake fasawa
Hakan yasa yazama abun Gori,dansu gabad'aya babu wata y'a data rage a
gabansu,kullum cikin yada habaici sukeyi
Rauda ganin yadda al'amarin aure yike kasancewa agareta yasa taciresa aranta, ta
k'udiri niyyar yin karatu
Mahafinta be hanata ba yabata goyon baya d'ari bisa d'ari dan yana matuk'ar ji da
ita acikin y'ay'ansa
Hakanko ba k'aramin k'ara basu haushi yayi ba dan su yaransu babu wanda yawuce
secondary.
Cigaban labari
Sai yamma anty ummi tafara Shirin tafiya,suna zaune a falon rauda tashiga da
akwatinta d'aki dan ta canza kayan jikinta da hanifa tab'ata da tumbud'i
Ta ajiye akwatin tana zaunawa a k'asa ta zage,bandir d'in kud'i tagani rafa na y'an
dubu-dubu
Gabanta ne yafad'i,tad'auki kud'in tana juyawa da kuma mamakinsu dan tasan bata
ajiye ko biyar acikin akwatin ba
Lokaci d'aya Zuciyarta ta tuno mata da Aasim,takuma fara jin maganar sa acikin
zuciyarta
"Am,am waya...
Wani tsallen murna anty ummi tayi tare da k'arasawa kusa da Rauda ta tsugunna
(Dayike tun bayan fasa auranta,duk saurayin dayazo baya yin sati biyu yike
tafiya,daganan bazata sake ganinsa bama bare wata maganar aure tashiga tsakaninsu)
Rauda tasauke ajiyar zuciya tana jin tausayin y'ar uwar tata ganin yadda lokaci
d'aya tashiga farin ciki dagajin tasamu saurayin da ya dad'e,bata san cewa shine
jinnul aashiquen ba
Rauda ta kuma sauke numfashi tana bata amsa cikin sanyin jiki
"Aasim"
"Mene?
"Aasim,sunan sa Aasim"
"Aasim?
Anty ummi ta ce
"Anty ummi please yanzu kaina ciwo yikeyi,zanzo har gida inbaki labari"
"D'azu baba"
Ta d'aga kai
"Eh baba"
Baba yace
Washegari tana gyara falo,mama na zaune tana karatu,ta kwashi kayan da ta wanke
tashiga d'aki dan sawa a drower
Ta fad'a
"To nidai kadena zuwa please,banaso a fahimci wani Abu,kabari har inkoma makaranta
sai mucigaba da had'uwa"
Zaro ido yayi tare da cewa
"Mene?kema kinsan bazan iya ba,bazan iya ko kwana d'aya batare dake ba"
"Hmmmmm bazaka gane ba,idan kai ba'a ganinka,aini wani zubin za'aga ina magana
nikad'ai idan inayi dakai,basai ayi tunanin k'wa-k'walwata tafara samun matsala
ba?
Ya jinjina kai
"Hakane,amma kema kinsan baze yuwu indena zuwa gurinki ba,sai dai inkin yadda
murink'a had'uwa a gida"
"Gida?
Dafe k'irjinta tayi dayike dukan uku-uku tana sauke ajiyar zuciya
Fulo ta janyo ta d'aura kanta tana rufe ido,jitayi iska na kad'a ta ahankali
Ta bud'e ido sai dai a me makon taganta a gadon mama,awannan k'aya taccen gadon
taganta
Tashi tayi dasauri tazauna,dede lokacin Aasim yafito daga bayin yana goge ruwan
jikinsa daga shi sai k'aramin towel
K'irjinta ne ya buga dam, Dan karo nafarko kenan da tab'a ganin na miji ahaka,gashi
babu inda babu gashi ajikinsa yana kwance kan farar fatar dake jikinsa
"Habibty"
"Nidai gaskiya tsoro Nike ji kamaidani dan Allah,sai muyi maganar da zamuyi acan
tunda tayi bacci"
"Nidai kamaidani"
Jitayi tafara shiga wani yanayi,kamar na bacci kamar na suma,daga nan bata k'ara
sanin inda kanta yike ba sai wajen k'arfe uku nadare tafarka
"Rauda!"
Ya kira sunanta,ta bud'e idon ahankali amma bata bari tak'ara kallon cikin idonsa
ba
"Rauda ina sonki,rauda ina k'aunar ki,zan iya yin komai akanki"
Tasauke ajiyar zuciya tana mamakin yadda baya gajiya wajen fad'an wad'annan
kalmomin
Sai lokacin ta lura da kayan ta dake gefe, tad'an zaro ido gabanta na fad'uwa tace
"Amma badai-dai bane hakan,nidakai ba jinsi d'aya bane,kuma allah be halatta aure a
tsakaninmu ba.......
Juya mata baya yi,dan baya buk'atar jin wad'annan kalaman nata,sosa masa zuciya
suke yi
Ita d'inma juya mai bayan tayi,tana mamakin irin wannan al'amari
"Rauda kitaimaki rayuwata kidaina fad'a min irin wad'annan maganganun,nidai ina
sonki koma me zakice bazan iya rabuwa dake ba"
"Ya Salam"
"Zuwa ya zama dole Rauda,dan ko ki yarda,ko kar ki yarda ya zamar miki dole
kije,babu abunda ze sameki ina tare dake"
Ajiyar zuciya yasauke yana k'ara kama wata fulawar da ta sauko daga saman d'akin
yakuma runtsewa a hannunsa
Maman isqah ina godiya,harda k'arfafa gwiwarki yike sawa nike daurewa Allah,amma
typing akwai wuya😒
Y'arfillo
🌹 JINNUL
AASHIQUE🌹
NA
HARIRA ALIYU (y'arfillo)🧕🏻
1⃣ 5⃣ 1⃣5⃣
1⃣5⃣
AGE
Wannan page d'in nakune y'an golden forum,na sadaukar dashi gareku kuyi yadda
kukeso da shi🧡🧡
8:00🕒 Am
FRI,MAY 3
Mama bata k'ara tambayar ta ba,dan tafi kowa sanin matsalar y'arta
Addu'a taci gaba da tofa Mata,bata bari ba harsai da tadawo cikin natsuwata
"Aa kina wasa dashi banace miki duk sanda zakiyi bacci kiyi alwala ba, sannan
kitofa ma jikinki addu'o i?yaushe rabon da kiyi hakan?
Rauda ta yi shuru tana tunani,dan ita rabonta da tayi alwala ko azkar d'in bacci
har ta manta
Shuru Rauda tayi nanma mik'ewa mama tayi tafice daga d'akin dan d'auro alwala
Rauda ta jingina da jikin gado kanta nawani irin sarawa, gabad'aya yanzu tunanin ta
nema yikeyi ya tsaya jitayi kamar ba ita ba
Kallo d'aya yamata yagano tashin hankali da tsananin damuwa a tare da ita
"Akan tarayyarka da Rauda ne,kasan tun bayan haihuwar shahida be kuma cewa komai
ba,to jiya abu saima yaje fada
Yike cewa abunda kakeyi sam be dace ba,saboda da wanine yike aikata hakan da tuni
an d'auki mataki akansa
Amma saboda kai d'an sarki ne,sai azuba maka ido ak'i cemaka uffan
Shine sarki yaturama sak'on Kira,kafin na turama nawa sak'on sai da naje na sami me
martaban akan wani mataki yike shirin d'auka
Shine yace bega laifin abu saima ba,dan tabbas ba adalci bane,kana d'an da ya
haifa kana aikata laifuka wanda kaine jigon masarautar,kuma ya zamar maka dole ka
rabu da ita,domin auran jinsin d'an adam baya daga cikin tsarin masarauta"
"Inbanda munafurci meya ruwan abu saima da rayuwata,nafahimcesa tunda nak'i auran
y'arsa na nuna banason ta yashiga bak'in ciki Dani"
"Nidai duk wannan bashi bane,abunda nikeso da Kai dan Allah ka amince ka rabu da
ita, banaso ka bijirewa umarnin da mahaifinka ze baka,nayi maka alk'awarin tara
maka kyawawan mata a jinsinka kazab'i wacce tafi maka........
"Bazan iya ba ammi,wallahi bazan iya ba,bazan iya rabuwa da ita ba"
Ammi tayi shuru tana kallonsa,durk'usawa yayi agabanta yana kama hannayenta
"Ammi kitaimaki rayuwata dan Allah,ammi bazan iya rayuwa inba tare da ita ba,idan
da abunda zaki iya yi kiyi dan Allah"
"Aasim babu abunda zan iyayi,kasani kai kad'ai gareni bayan kai banida wani d'a
aduniya, narok'eka kada ka fusata mahaifinka dan nasan ze iya d'aukar ko wani
hukunci akanka,bar ganin yana sonka amma yafi son kimarsa da darajarsa fiye dakai
kuma zeyi komai ne abisa adalci"
"Kaga dai nice na haifeka amma narok'eka daka bi umarnin da ze baka,banaso wani abu
ya sameka kai kad'ai nike dashi aduniya"
Ita ko Rauda kasa komawa ta kwanta tayi,tunda tayi sallar asuba tana kan darduman
Mik'ewa tayi jikinta babu k'wari,ta ninke dar duman tana yin hanyar waje
"Rauda"
"Meke damunki?
"To tashi kije ki karya kisha magani,idan bedena ba anjima idan nadawo kasuwa sai
inkaiki chemist"
"To"
Shuru tayi tana lumshe idanuwanta,mama tadawo d'akin hannunta rik'e da kofin tea da
paracetamol
Da yamma, tana bayi zatayi wanka ta tasa ruwan agaba tana kallo
Wani haske tagani ya b'ullo cikin bayin,sai ga Aasim ya bayyanaKallo d'aya suka ma
juna suka gano damuwar da kowanensu yike ciki
Shiko wani kalar abune ya k'ara sukar sa,Wanda yasan tsan-tsar k'aunar tane
Yasan akwai kyawawan mata a duniya amma bega tamkar ta ba, tabbas baze iya rabuwa
da ita ba
"Rauda"
Shima shuru yayi suka kalli juna na y'an wasu sakwanni sannan yace
"Meyasa kika tada hankalinki?ba wani abun tsoro zaki gani ba idan munje,zaki ga
kowane a suffar mutane kamar yadda kike ganina,kuma sannan ina tare dake,babu wani
abun da zesa meki"
"Aasim,dan allah ka rabu Dani, kabarni inji da abunda yike damuna please"
Jitayi ya rungumo ta tabaya,tayi saurin runtse idonta danji tayi illahirin jikinta
ya amsa
"Rauda,ina sonki,nasan kema kina sona dan allah kada kik'ara ambaton in rabu da ke"
"Aasim ina sonka,dan girman allah idan mafarki nikeyi cewa kai ba mutum bane ka
tasheni,nayi alk'awarin bazan sake yin baccin ba bare inkuma yin makamancin irinsa"
Sai da suka kwashi minti biyar ahaka,sannan ya d'agota yana kallon kyakkyawar
fuskarta data jik'e sharkaf da hawaye
"Rauda,nayi alk'awarin zan rayu dake ako wani irin yanayi, zanyi miki komai kamar
yadda jinsin ki zeyi Miki,dan allah ki kwantar da hankalinki kinji?
Ta bud'e jik'akk'un idanunta tana kallonsa kawai batare da ta ka'ra cewa wani abu
ba
Ta tsaresa da kyawawan idanuwanta tana kallon yadda yike ya mutsa fuskarsa alamar
haka tata fuskar take komawa idan tana kuka
Gyad'a masa kai kawai tayi,yayi murmushi tare da manna mata kiss a goshi
Ta sauke doguwar ajiyar zuciya bayan b'ace warsa sannan tayi wankan a sanyaye
"Kisamin sakata a k'ofa,kada kibar min k'ofa ta kwana a bud'e sannan kiyi addu'a
kafin ki kwanta"
"To"
Rauda tace,mama ta fice daga d'akin tana janyo mata k'ofa
Rauda tamik'e ta sa sakata a k'ofar falon sannan ta dawo ta zauna tana d'aukar
wayarta dake k'ara
"Habibty"
A cikin y'an sakwanni taganta acikin sahara,babu gida gaba babu gida baya
Begama rufe baki ba saiga wasu dokuna guda biyu,d'aure da wata kujera ta zaman
mutum biyu da rumfa a samanta
Saurin rik'esa tayi,dan girman dokunan ya wuce misali,wani irin tsoro yafara
d'arsuwa acikin zuciyarta
Yak'arasa fad'a yana kama hannunta,babu yadda ta iya suka shiga suka zauna,dokunan
suka juya inda suka fito a guje
Gabad'aya gurin Sahara ne,amma kuma ga wasu bishiyoyi masu shegen kyau dasukayi ma
wurin ado
Ahankali taji tsigar jikin ta dena tashi,suka kalli juna yayi mata murmushin
k'arfin Hali dan gabad'aya hankalinsa a tashe yike
Wasu zabga-zabgan mutane Rauda tagani masu matuk'ar girma sanye da bak'ak'en kaya
da wasu manyan takobi ahannayensu
Idanuwannasu jawur kamar gauta,tayi saurin rufe idanuwanta k'irjinta nawani mugun
bugawa
Rauda sakin baki tayi tana kallon cikin masarautar,da tsayawa fasalta ta b'ata
lokacine
Ga mutane kala-kala iri-iri kuma duk inda suka gifta sai sun zube suna kwasar
gaisuwa
Kallonsa tayi taga kayan jikinsa sun sauya zuwa kayan sarauta,idanuwansa ma k'wayar
ciki sun tashi daga bak'in dasuke sun koma wani kala
Shima d'in tsoro yabata,ta k'an-k'anme jikinta tana ambaton sunan allah
Bata yadda tak'ara bud'e idanuwanta ba harsaida taji dokunan sun tsaya
Wani k'ayataccen wurine me shegen kyau daga can gabansa kuma wata k'atuwar fada ce
"Habibty babu abunda zesameki,mutafi fada,kuma idan munje duk abunda kiga nayi kiyi
irinsa kinji?
Aasim yace
Mik'ewa Aasim yayi suka d'anyo baya sannan ya zauna,itama ta zauna kamar yadda yayi
"Yarinya!
Nayi miki uzuri,awancan lokacin domin ko kina cikin rashin sani,amma ayanzu zan
yanke hukunci a bisa saninki"
"Kayi min afuwa,abi bazan iya furta kalmar saki a gareta ba"
"Abi kataimaki rayuwata, wallahi ita kad'ai nikeso bazan iya rayuwa idan babu ita
ba"
"Abune da baze tab'a yuwuwa ba kana d'an dana haifa inbarka ka sab'awa shari'ar
masarauta,dan haka ka furta saki agareta"
Ammi dake gefe ta taso cikin tashin hankali ta wanka masa mari
Komawa tayi inda take,tanayi ma Aasim wani kallo me cike da bada umarnin ya aikata
abunda akace Masa
"Miye hukuncin duk wanda ya karya dokar masarauta?kuma akace ya bari ya yak'i bari"
Me fad'an hukunci yayi shuru,yana tunanin abunda zece ganin d'an sarki ne dakansa
"Kaji hukuncin da ya rataya akan duk wanda ya aikata laifi irinnaka,dan haka sai ka
zab'a cikin biyu,
"Tunda ni amatsayina na mahaifinka ban isa inbaka umarni kabi ba,yazamar min dole
ind'auki hukunci akanka,dan haka fad'i ina jiranka,wane kazab'a"
"Zan irga uku,idan har na irga uku baka saketa ka rabu da ita ba,to tabbas zaka
bar min masarauta"
"D'aya.....
Biyu........
Amma kuma sai yayi shuru,yana cize leb'ansa da k'arfi tare da runtse idanuwansa
"Uku"
Abu saima ne ya mik'e shima cikin tashin hankali dan betab'a zaton Aasim ze zab'i
barin masarautar akan Rauda ba,ga saima can tana kukan inda babu shi bazata iya
rayuwa ba,kuma shi yayi hakanne dan sama ma y'arshi farin ciki dan yasan idan Aasim
yarabu da Rauda dole ze auri saima
"Yarima kasan hukuncin duk wanda ya zab'i barin masarauta kuwa? Dole fa sai ka bi
ta tauran
(Tauran wani wurine zagayayye,da yike da k'unci da zafi, Wanda duk bayan minti biyu
yike fitar da wani k'ara me kama da sautin tsawa,wanda duk wanda yike ciki sai
hucin k'arannan ya tsattsaga jikinsa)
"Wanda sanin kankane sai rauhan yatsaya acikin tauran har sai ya tsallake k'arar
tauran guda arba'in da tara,shin kamanta da azabar dake cikin tauran ne?
Aasim yayi masa wani kallo me cike da tsana dan inba da din munafuncinsa ba da
yanzu wannan abubuwan basu faru ba
Rauda da jikinta ya gama mutuwa hawaye suka gama wanke mata fuska saboda tsananin
tausayin Aasim,shin wani irin so yike mata da ze zab'i rabuwa da ahalinsa saboda
ita?
"Rauda ina k'aunar ki,zan iya hak'ura da komai inhar zan rayu dake"
Sarki Ramzad da jikinsa yagama yin sanyi duk da b'acin ran dayike ciki kukan
d'annasa na tab'a masa zuciya
"Na baka daganan zuwa gobe,kaje kanatsu kayanke wa kanka abunda yafi maka,wannan ne
adalci na k'arshe da zan maka
Idan har ka amince da rabuwa da ita,to kazab'i ko y'ar sarkin wace k'asa ce zan
aura ma ita
Idan kuma har kakai goben kana kan bakanka na k'in rabuwa da ita to tabbas zaka bar
min masarauta
Sannan kuma zaka tsallake tauran ninki biyu, d'aya na barin masarauta d'aya kuma na
jayayya dani"
Bubbuga k'ofar da akayine ya sa Rauda ta tashi,akan gadon mama ta ganta
Dafa kanta tayi da yike sarawa kamar ze rabe biyu tana girgiza shi
Y'arfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE*🌹
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_🧕🏻
1⃣ 6⃣ 1⃣6⃣
1⃣6⃣
AGE
Ina yima ɗaukancin masoyana barka da sallah, dafatan anyi sallah lafiya, wannan
Page na baku shi amatsayin barka da sallah, sannan ina me baku haƙuri akan jina
shuru da kuka yi bani da lafiya ne ina buƙatar addu'arku
_7:32_🕒 PM
FRI, JUN 7
Cikin rashin k'warin jiki ta mik'e jiri na d'ibarta,ga kanta da yayi mata mugun
nawi tana jin kamar an d'aura mata gingimemen dutse
Ta zare sakatar falon tana jingina da bango da sauri,dan ji tayi tana neman fad'uwa
"Sannu,ina ganin idan gari yayi haske kawai zamu je k'aramin asibiti adubaki,
k'ilan harda typhoid,kidaure kiyi sallan"
A gaggauce tayi sallar saboda sanyin datake ji sosai,tana idar da sallar ta koma
kan gado ta lullub'e
B'angaren Aasim kuwa,tunda taron fada ya tashi,yashige d'akinsa tare da kullewa dan
gabad'aya baya son a damesa
Yana jiyo muryar ammi daga bakin k'ofar tana fad'in ya bud'e
Amma yak'i saboda baya son yaga tashin hankalin dake tare da ita,harta gaji ta wuce
K'wan-k'wasa k'ofar aka kuma yi,yaja gajeren tsaki tare da kifa kansa
Daga can k'ofar d'akin muryar mus'ab yaji Wanda ya kasance babban amininsa
Dan nasan jiya kana cikin rud'ani ne,shiyasa kak'i yin abunda me martaba ya umarce
ka"
Aasim Ya sauke gauron numfashi tare da lumshe idanuwansa wad'anda suka kad'a
sukayi ja
"Ni wallahi banga abunda kagani agurin waccan bil'adamar ba,da yasa gabad'aya ka
rikita tunaninka,
"Dan allah kada ka k'ara b'ata min Rai,ni ita nike so kuma ita na zab'a zanyi
rayuwa da ita,abunda nagani da ya rikita min tunani akanta kuma
"To mekake so ince maka? A matsayinka na aminina kamata yayi kabani shawarar yadda
zanyi insamu mafita amma kazo kana fad'a min abunda kasan ze k'ara min b'acin ran
danike ciki"
Sannan yace
"Bazan takuraka ba,akan fasa abunda kayi niyya,amma ina me baka shawara da kada ka
bijirewa umarnin mahaifinka,katuna da haihuwar ka da yayi,da kuma rainonka har
izuwa girmanka ko ba komai yaci wannan arzik'in "
Tabbas yasan abunda yike shirin yi ba dai-dai bane,to amma ya zeyi? Ya zeyi da
muradin zuciyarshi?
"Nasan zaka fahimceni abi,idan nak'ara yimaka bayanin yadda nike jinta a cikin
zuciyata"
B'acewa yayi,be bayyana a ko ina ba sai abakin falon sarki inda yike hutawa
Kallo d'aya yayima kuyangin dake tsattsaye bakin k'ofar ya kauda kai tare da cewa
Gabanshi na fad'uwa ya shiga k'asaitaccen falon da akayi masa ado da zinarai kala-
kala
Sarki Ramzad na zaune kan wata kujera me d'an fad'i ya jingina idanuwansa a lumshe
Sarki Ramzad ya ce
Aasim yace
Jinjina kai sarki Ramzad yayi yana yima wazirin sa nuni da hannu alamar yafita ya
basu guri
Tabbas babu abunda yi keso sama da Aasim, yana matuƙar jinsa acikin zuciyarsa
Kuma babu abunda yafiso irin yaga Aasim cikin farin ciki
"Aasim, ka sani bawai na hanaka abunda kake so bane, dan jin daɗina
A'a, saboda adalci ne, domin babu wani rauhani daya isa yayi haka a ƙyalesa, Kaga
ko bekamata na ƙyaleka ba dan kana ɗan dana haifa
Kasani da zarar akace babu ni, to kaine mai mulkin wannan masarautar
Ya kamata ka fahimce ni, nayi maka alƙawarin ko ƴar gidan wacece idan Kaga tayi
maka zan auramaka in har a jinsin ka ce
Amma baze yuwu in barka ka cigaba da rayuwa da bil adama ba bazeyu ba"
"Abi,dan Allah kabarni nayi rayuwa tare da ita,ita kaɗai nike so banajin zan iya
rayuwa da wata mace a duniya in ba ita ba........
" dakata!
To kasani bazan takura ka ba, tunda har ban isa dakai ba, nan da awa ɗaya zamu je
fada, duk abunda kayanke kafaɗa acan"
"bana son na kuma jin komai daga gareka, tashi ka bani wuri"
"Abi.....
Ƙarfe takwas suka isa ƙaramin asibitin gwamnatin, sun tadda mutane da yawa akan
Layin ganin likita
Kallon jama'ar dake wurin kawai take yi amma zahiri hankalinta baya gurin
Damuwarta ta kuma ƙaruwa yayin da taga har zuwa lokacin bata ji wani alamun Aasim
ba,
_"Rauda ina ƙaunarki, zan iya haƙura da komai inhar zan rayu dake"_
Mama dake zaune kusa da ita ta kalleta cikin rashin fahimta tace
"mene?
Daburcewa Rauda tayi, dan ita bata san maganar da tayi a zuciya ta fito fili ba, ta
rasa me zata ce
Numfashi mama ta sauke tana kaɗa kai, lokacin layi yazo kansu tamiƙe tayi gaba
batare da ta kuma cewa komai ba
Rauda tabi bayan ta, gwajin farko da likita yayi ya gano BP ɗinta yayi ƙasa sosai
" BP ɗinki yayi ƙasa sosai, shi yasa kike jin ciwon kai da kuma jiri, zan rubuta
miki magunguna Asiya kisha, sannan kidena barin kina shiga cikin tunani Allah ya
ƙara lafiya"
Mama ta amshi takaddar maganin suka, fito kowanne zuciyarsa babu daɗi
Napep suka hau ta kawo su gida suna gab da tsayawa taji maganar Aasim
"wani irin ganganci ne wannan? miye kikema sauri da ba zaki tsaya yagama tsayawa
ba?
guntun tsaki mama ta ja,tana zage Jakarta zata ba mai Napep ɗin kuɗi
A tsaye tagansa,rufe ƙofar bayin tayi da sauri tare da ƙarasawa inda yike
"Aasim, kana lafiya? Me ya faru na jika shuru? Ince dai ba wani abu a kayi maka ba?
Be bata amsa ba, illa rungumeta da yayi,yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya
Ita ɗinma ajiyar zuciyar ta sauke, tana jin sonsa na bin duk wani sassa na jikin ta
Ɗagota yayi ya zuba ma fuskar ta ido amma kuma har lokacin beyi magana ba
"miye baze yuwu ba, kayi min magana yadda zan fahimta dan Allah"
Kuma Ɗagota yayi yasa hannayensa duka biyu ya tallabo fuskarta yace
"Rauda inaso kiyimin alƙawarin cewa ba zaki taɓa rabuwa dani ba,har ƙarshen
rayuwarki"
"nasani a yanzu, amma bansan meze iya faruwa nan gaba ba, shi yasa nikeso kiɗaukar
min alƙawari da kanki da kuma bakinki"
Katseta yayi
" kinga Rauda kada kice komai,na san watarana zamu dai-daita dasu, amma ke bazan
iya jurar rashinki dai-dai da rana ɗaya ba"
Ajiyar zuciya ta sauke me nawi, tare da fitowa daga bayin, ɗaki ta shiga ta zauna
akan gado
Maganar daya faɗa ce kawai take yi mata yawo a kunne
_"kinga Rauda kada kice komai nasan wata rana zamu dai-daita dasu amma ke bazan iya
jurar rashinki dai dai da rana ɗaya ba"_
Lumshe idanuwan ta tayi, tana fatan ace har yanzu Mafarki take yi
Ɓangaren Aasim kuwa, lokacin da ya koma masarauta saura ƴan mintoci a tafi fada
Ammi tayi ma jakadiyarta nuni data fita sannan ta dawo da kallon ta kansa
"Aasim ni kake wulaƙantawa ko? Ace tun jiya nikeson yin magana da kai amma ka sawa
Ɓangaren ka takun kumi ko?
"ammi ki gafarceni, amma banajin zan iya haƙura da duka zaɓi biyu"
Wai shin Aasim lafiyar ka ƙalau kuwa? Ko ko taɓin hankali ne yasa meka?
" shin kana tunanin bil adama zata sama ma dauwamamman farin ciki ne?
Kayi babban kuskure Aasim, ko da yike laifi na ne da na goyama baya tun farko
Amma ina so ka sani nadama da danasani zasu biyo bayan ka inhar kazaɓi rayuwa da
ita sannan........
"lokaci yayi, zaɓi ya rage gareka, abu na ƙarshe da nike so kasani shine. Idan har
kazaɓi rayuwa da ita to kada ka ƙara zuwa inda nike,kaje inayi maka fatan alheri"
Aasim numfashi ya sauke Yana Miƙewa cike da tsananin ruɗani tabbas ya san ze
aikata babban kuskure amma yana da yaƙinin iyayen sa ba zasu iya jurar rashin sa
ba, nan da wani ɗan lokaci zasu nemesa kuma ma ya san da wuya Abi ya zartar da
hukuncin kora a kansa ƙilan yafaɗi Hakan ne dan ya tsorata sa ya rabu da rauda
Ɓacewa yayi ya bayyana a fada, kamar kullum fadar cike take da manyan rauhanai
Shuru ya biyo baya na wasu mintoci, sannan sarki ramzad yayi gyaran murya
"Aasim, kafaɗa ma fada abunda ka yanke, shin ka haƙura zaka rabu da itanne? Ko ko
kana kan bakanka na rayuwa da ita?
" bana buƙatar jin shurun ka, rayuwa da mu kazaɓa ko rayuwa da ita?
" Abi dan Allah, kayi haƙuri kabarni na cigaba da rayuwa da ita, nayi maka alƙawari
bazan sake aikata kuskure ba.......
" ya isa, ka riga da ka bani amsar tambaya ta, dan haka kada ka ƙara cewa komai"
Sarki ramzad ya maida kallon sa ga rauhanan da suka yi jugum jugum saboda mamakin
kafiyar da Aasim yayi
Yace
"tunda abunda ya zaɓa kenan, to bazan fasa hukuncin dana yanke ba, dan haka aje a
shirya tauran zuwa jibi za a zartar da hukuncin"
Ɗaya daga cikin manyan fadawanne ya durƙusa cike da tashin hankali yace
"mai martaba, Aasim ɗan kane, be kamata ayi masa hukuncin kora ba, a sassauta masa
ranka shidaɗe"
Gabaɗaya jikin Aasim ya gama mutuwa, amma ya kasa ƙara furta komai
Hawaye kawai yikeyi, a haka aka watse daga fadar cike da juyayin al'amarin
ƴarfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_ 🧕🏻
1⃣
1⃣7⃣
AGE 7⃣ 1⃣7⃣
_9:15_🕒 PM
SAT, JUN 8
"dan kinga ina kuka, shi ya sa kika yi wani iri? Ba kyaso kiga ina kuka ne?
"shi kenan farin ciki na, daga yau bazan sake yin kuka ba, kinsan Abi ɗinki na
sonki da yawa baya so ya ganki cikin damuwa"
" shi kenan, ki ƙara haƙuri kinji? Zaki ganta har sai kin gaji, yanzu faɗamin me
kikaci yau?
Ya tsura mata ido yana jin tausayinta, kullum bata da maganar da ta wuce ina
amminta?
Gashi da wuya ta rayu da ita yadda take so numfashi ya sauke tare da nuni da hannun
sa
Sai ga Rauda ta bayyana a ciki, har lokacin tana kwance akan gado tana rawar sanyi
Ta duƙunƙune da bargo
"Rauda!
Ya kira sunan ta, ta buɗe idanuwan ta a hankali tana duba inda ta jiyo muryarsa
amma bata ga kowa ba
" ina masarauta, nima banajin daɗine bazan iya zuwa ba, kinsan duk abunda kikeji
ajikinki inaji ajikina,ga kuma damuwar da nike ci"
Ta rufe kamar yadda yace, amma ba ta ganshi ba har zata buɗe, sai taga duhun dake
cikin idanuwan ta ya fara yayewa
"habibty"
Ya jinjina kai
" ba zaki gane yadda nike jinki a nan ɗina ba, wallahi Rauda bansan dalilin da yasa
nike miki irin wannan son me zafi ba, jini keyi kamar idan na rasa ki zan iya rasa
rayuwa ta, nima ba da son raina na bijire wa umarnin su ba, amma nasan ba zamu jima
ba zamu dai-daita dasu"
"Aasim dan Allah inda hanyar da zaka bi kabi, bana so kasha wahala"
Yayi murmushi yana sa hannu ta cikin madubin ya kama hannun ta tare da matsewa
cikin nasa
"kar ki damu habibty, tabbas nasan tsallake tauran akwai wahala kuma nima hankalina
na tashi idan na tuna azabar dake ciki
Amma kuma hankalina ya kan kwanta idan na tuna cewa zan samu ƴancin yin rayuwa dake
bayan wannan wahalar, fatana dai kiriƙe min alƙawarin da kika ɗaukar min"
Haƙiƙa ta ƙara jin ya shiga zuciyar ta to me ma zesa ta karya alƙawarin data ɗaukar
mai?
Ta tambayi zuciyar ta tana ganin babu, Guntun murmushi yayi tare da katse mata
gajeren tunanin da ta tafi
"ki tuna ke mutum ce, kuma halin mutanen yanzu sai Allah, zasu ɗaukar ma alƙawari
amma daga baya su nuna su basu ma san da maganar wani alƙawari ba, amma dai ke na
yarda dake na kuma san ba zaki taɓa juyamin baya ba"
"Meyasa?
Ya tambaya
"wa yace miki muma rauhanai irin ku ne mutane ragwaye,babu abunda kanta zeyi"
Haka suka cigaba da fira har saida barci ya fara ɗaukar Rauda sannan ya kaudar da
madubin
Yana jin kamar bashi da wata damuwa, dan firar da yayi da ita yasa hankalinsa ya
ɗan kwanta
Miƙewa yayi ya isa sashen ammi, sai dai kuyangin ƙin buɗe masa ƙofa suka yi dan
sunce tace bata buƙatar ganawa da kowa
*Ranar tsallake tauran*
Duk wani masoyin Aasim da ke cikin masarauta hankalinsa a tashe yike, musamman ammi
da gaba ɗaya ta fita hayyacinta
Haka Shima sarki ramzad dauriya kawai yikeyi yana nuna kamar abun Be dame shi ba,
amma zahiri ƙasan zuciyarsa cike take da tashin hankali
Ammi kasa haƙuri tayi saura minti goma sha biyar ta shiga Ɓangaren sarki ramzad
"na roƙeka ka janye wannan hukuncin akan ɗana, shi kaɗai gareni"
"in janye hukunci fa kika ce? Kema kinsan abunda baze taɓa yuwu wa ba kenan,akwai
sauran minti sha biyar, kina iya zuwa kisa ɗanki ya bi abunda nace mai, dan shine
kika isa dashi.
Yadda bawa zeyi laifi in hukunta sa, haka zan hukunta abunda na haifa dan haka babu
maganar janyewa"
Gyara zama yayi cike da ƙaguwa da kukannata dan tashin hankalin da yike ciki kaɗai
ya ishesa
"kinga Samira,bana buƙatar jin wannan kukan naki, ki tashi ki ɓace min da gani"
"na fahimci ni kaɗai nike son Aasim, kai wahalar da ze shiga ko ajikinka, to shi
kenan zan tafi amma ka sani duk abunda ya sami ɗana da kai zanyi kuka"
"ki dakata min da waɗannan kalaman naki, duk ba laifinki bane da Ace tun farko baki
basa goyon baya ba da munkawo wannan matakin?
Juya wa ammi tayi ta fice tana kuka bata zame a ko ina ba sai Ɓangaren Aasim
"ammi me yafaru?
" idan kai baka son rayuwar ka ni ina so, ka duba wahalar da za kasha idan ka shiga
tauran"
Ammi tafaɗa
"ammi indai tsallake tauran ne,ki kwantar da hankalinki zan tsallake lafiya insha
Allahu Babu abunda ze same ni"
"Aasim......
" ammi dan Allah kada ki ƙara cewa komai, ammi Rauda itace farin ciki na na kuma
son kina son duk wani abu da ze faranta min
Kinsan kema bazan taɓa yin nisa dake ba, dan haka ki kwantar da hankalinki dan
Allah, kada ki karya min gwiwa"
*filin tauran*
Wurin ya cika sosai da rauhanai, Aasim na tsaye daga gefe inda babban ba fade yike
" ka tabbata?
Runtse idanuwan sa yayi yayin da ya isa ƙofar, ya ɗan tsaya ya karanto wasu abubuwa
sannan ya kutsa kai
Wani baƙin hayaƙi ne ya dunƙule yayi tsawo baka iya ganin ƙarshensa a saman tauran
ɗin
Zuwa can hayaƙin ya fitar da wata ƙara me razanar wa wanda ta sauka a jikin Aasim
Faɗuwa yayi a ƙasa saboda tsananin azaba,gashi ba a so a kwanta dan danne mutum
take yi
Yun ƙurawa yayi ya tashi da ƙyar yana duban jikinsa daya fara huhhujewa
Mus'ab ne ya ruga da gudu ya taro sa yana Kiran sunansa cikin kaɗuwa da halin da ya
shiga
Aasim be kuma sanin inda kansa yike ba, har saida yayi kwana biyu
Mus'ab na ganin ya buɗe ido ya matso kusa dashi sosai yana faɗin
"sannu, ga magani ammi ta aiko maka, tace da ka farka kasha ze taimaka gurin
komawar jikin ka dai-dai"
Aasim yayi murmushin ƙarfin hali yana sake girgiza mai kai
Mus'ab ya jinjina kai,yana miƙa mai maganin da ke cikin wani kofin silver
Sai da ya sha rabin maganin sannan ya ajiye yana kallon yana yin garin
"kwana biyu??
Mus'ab ya kauda kansa da ga kan Aasim yana mamakin irin ƙaunar da yike wa wannan
bil'adamar
"to Meyasa zata damu, bayan ta juya ma tunani, ta san yanzu ka zama nata ita kaɗai"
"Kaga mus'ab bana so kana faɗan magan ganu marasa daɗi a kanta"
Mus'ab yace
Aasim banza yayi dashi, sai da ya fice sannan yaja gajeren tsaki
" *habibty!*
Ta tambaya a ƙagare
"amma Meyasa? Ka san damuwar da na shiga kuwa? A sanadin na Dena jinka, na Dena
ganin ka"
" da gaske Mana, nidai Ina son inganka yanzu dan allah"
"habibty bana so kiganni a yana yin da nike ciki ne, kiyi haƙuri a kwana biyu
tukunna"
Ya faɗa
"to bazan iya zuwa ba, sai dai in janyo ki ta cikin inda nike kallon ki, amma
kafinnan ina mama?
Ya jinjina kai
"shi kenan"
A tsorace
"A...a..sim"
Miƙewa yayi daƙyar ya ƙara sa inda take, dan har lokacin yana jin jiki
Murmushi ya kuma yi
"dan Allah kada kiyi kukannan, kinsan dai abunda bana so na gani a fuskar ki kenan
ko?
" duk a sanadina Aasim? Yanzu ahaka zaka cigaba da zama kenan?
Ajiyar zuciya ya sauke me nawi yana jin guguwar ƙaunarta na daɗa lulluɓesa
"a'a habibty, nan da wani ɗan lokaci zan koma yadda nike, ki kwantar da hankalinki
kinji?
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
1⃣ 8⃣ 1⃣8⃣
1⃣8⃣
AGE
_wannan Page nakune ƴan golden forum, haƙiƙa bana gajiya da yabonku domin kun can-
canta Allah nike roƙo ya ƙara mana basira da fasaha ya kuma ƙara mana danƙon
zumunci a wannan gida na mu me albarka amin_
_8:52_🕒 AM
SUN, JUN 9
Ya kuma yin murmushi ya na kama hannun ta zuwa bakin gadon suka zauna suna
fuskantar juna
"to shi kenan ya isa haka,Nasha faɗa miki cewa idan kina kuka bakya yin kyau amma
kinƙi yarda"
Ƙarasa goge ragowan hawayen tayi tana zuba masa fararen idanuwan ta
"inji wa ya faɗa miki? Ai ke idan akwai abunda ya wuce kyakkyawa dashi ya kamata a
kira ki, domin kyawun ki na daban ne"
"zan iya yadda da Hakan amma a gurinka, dan nasan son da kake min ze iya sawa Kaga
kyau na fiye da kima, amma ni nasan ni ba kyakkyawa bace"
Ya kama hannun ta yana matsewa cikin nasa
"da gaske habibty kina da kyau, bawai idona rufe wa yayi ba"
"to shi kenan Naji, amma ya kake ji ajikinka nasan ko ina yima ciwo yike yi ko?
" ya ilah, habibty baki ji abunda nace miki ba ko? Kina so raina ya ɓaci ko?
Girgiza kai
Yace
"oook idan bakya so raina ya ɓaci ki maida hawayen nan kada ki bari su zubo"
Tayi ƙoƙorin maida hawayen amma ina kafin tayi wani yunƙuri su biyo kumatun ta
"bazan taɓa bari hawayenki su zuba a ƙasa ba, indai ina tare da ke Rauda, dan Allah
ki bari"
Kwantawa tayi a jikinsa tana haɗiye wani ƙullutun damuwa da ya dunƙule mata
maƙogoro
"ka barni inyi kukan dan Allah,in banyi ba ina jinsa yana dunƙule min a ƙirji"
"to wai kukan me kike yi ne? Faɗa min,indai kukan halin da nike ciki ne kibari, nan
da wasu kwanaki zaki ga na koma dai-dai"
Cike da takaicin ganin ta da yayi, dan shi gaba ɗaya haushinta yike ji
Dama ya san ze ganta Aida da ainihin suffarsa ze shiga ɗakin dan ya razana ta
Ita ko Rauda bayan fitar mus'ab ɗago wa tayi tana duban Aasim dan a kallon da
mus'ab ya yi mata ta hango tsanarta ƙarara a tare dashi
"abokina ne"
Ya bata amsa
"mama ta dawo"
A gaggauce tace
"to gaskiya zanje adubamin hawan jinana ƙila ya hau da yawa da ni banga kowa ba a
ɗaki wallahi"
Mama tace
"gidan ku, dudu nawa nike? Bari kiga kiyi aure kibani wuri yadda zan koma yarinya
shataf, dan gayu zan dinga ci"
Bayan sati biyu,hankalin Rauda ya kwanta sosai bata da wata damuwa musamman data ga
Aasim ya warware ya koma yadda yike
Uwa uba ga soyayyar da suke yi me zafi, wacce tasa ko da yaushe bata rabo da
tunanin sa
Maganar sa taji
Kafin ta Ƙarasa maganar taji wata iska me daɗi ta lulluɓeta tana janta
Jin iskar ta lafa yasa ta buɗe idon, a kwance tagansa gefen gado
"miye na wani zare idanu, abunda yafi haka ma zaki gani, zaki wani ce in bari ki
gama guga, kinsan yadda na matsu in ganki kuwa?
Ta faɗa a shagwaɓe
Ji tayi wani abu ya fara taso mata ta Lumshe idanuwan ta daga kallon sa da take yi
Shiko sun kuyowa yayi daf da fuskarta yana kallon ɗan ƙaramin bakin ta
Yatsan sa ya dawo dashi yana zagaye tausasan lips ɗinta wanda Hakan ke ƙara sa tana
shiga wani yanayi
Kissing ɗinta ya fara Ahankali yana bin duk wani sassan jikin ta
Gaba ɗaya jin ta take yi a wata duniya da bazata iya fasalta irin ta ba
Sai wuraren ƙarfe uku ta farka, yana kwance kusa da ita ya zuba mata ido
"habibty!
"ki faɗi,duk abunda kike so, nayi miki alƙawarin zanyi miki shi a take batare da
ɓata loka ci ba"
Murmushi ta kuma yi
"babu"
"shi kenan"
Washegari
Bayan tagama ta ɗauko doguwar riga ta saka tana zage zip ɗin
"wallahi kin gansa nan, nazo wucewa ta wata kasuwa nagansa naga ze yi miki kyau a
hannun ki shine na siyo miki"
"wow gaskiya yayi kyau kamar kasan kuwa ina son siririn zobe"
"shhhhh"
"kar in ƙara jin kalmar godiya abakinki, dan babu ita a tsakanin mu"
Anty ummi ce
"zama tayi kan kujera cike da nisha ɗi tana duban Anty ummin
"bangane ba"
"to babu abunda ya faru kinsan wata ran zakiji ki cikin annashuwa"
" a'a ba zinari bane, ɓarawon zinari ne, a makarantar mu wata take saida wa dubu
ɗaya to tunda na siya ma ban taɓa sawa ba sai yau"
"dama hanif zanɗauko a makaranta nace bari in biyo, kince zakizo har yanzu baki zo
ba"
"kinsan banji daɗi ba kwana biyu amma zan zo jibi in Allah ya kai mu"
Washe gari suna zaune a tsakar gida gabaɗayan su suna gyara masarar da baba ya kawo
Suna cikin gyaran aisha ta shigo yarinyar umma da ƙaramin akwati a hannun ta
idanuwan nan nata sun yi jawur da alamu kuka taci
"ubanki kenan, nace ubanki kenan Aisha, dan yayi waya da ƴammata shine abun yaji?
Mazan yanzu ba haƙuri ake yi da su ba, ina farin ciki hankalina ya kwanta na gama
aurar da ku shine kike kike so ki tattago naki auran?
Ga wasu nan auran ma ya gagare su suna neman mazan ruwa a jallo basu samu ba"
Umma tace
"faɗa mata dai, wata ma sau biyu ana fasa auran ta kuma babu wanda ya ƙara
shinshinar ta, sai ke da Allah ya tarfa ma garin ki nono ya rufa miki asiri kikayi
auran zaki rinƙayin yaji
Maza tashi ki ɓace min da gani in ba kinaso in rufe ki da duka ba, sakarya kawai"
Mama Miƙewa tayi ta shige ɗaki dan tasan da ita suke yada haibaicin
"mama dan Allah kada abunda suka faɗa ya ɓata miki rai"
Jikin Rauda yayi sanyi sosai, tausayin mama take ji, anya wannan rayuwar da tekeyi
a ɓoye da Aasim tayi wa kanta da mama adalci kuwa?
"komai lokaci ne mama, kuma komai yayi farko yana da ƙarshe ki kwantar da
hankalinki ai da banyi auran ba ba a zaune nike ba, karatu nikeyi"
A gaggauce tagama ayyukan da zata taya mama dan ranar itace da girki
Ƙarfe goma mama tayi mata sallama taja mata ƙofar da yike hadari ya taso sosai
Ta dakatar dashi
" ina so muyi wata muhimmi yar magana, kuma dan Allah inaso ka fahimce ni, ka kuma
yarda da abunda zan faɗa ma"
Ya kaɗa kai
"to insha Allah ina jinki"
Katseta yayi
" sannan me? Faɗamin kawai me kike so kice"
"na sani Aasim, kuma kai ma ka san baze yuwu In cigaba da zama a haka ba, idan ni
nasan ina tare da kai ai mutane basu sani ba.......
"eh shirmammu ne mana, ina so ki sani bazan taɓa barin wani ɗa namiji ya raɓeki ba,
dan haka ki ma cire maganar aure a rayuwarki duk wani abun da ɗan adam zeyi miki
nayi alƙawarin zanyi miki ninkin shi"
"Aasim dan Allah na roƙeka,Hakan shine kwanciyar hankalin mama, ka riga da ka san
a yanzu babu wanda nike so sama da kai, kuma bawai ina nufin kabar ni in yi aure
dan inyi nisa da kai bane, a'a...
"kinga Rauda idan kinji abunda nafaɗamiki to, idan kuma baki ji ba bari in sake
nanata miki
Sai da suka yi kwana biyu be kuma zuwa inda take ba,bata damu ba dan haushin sa
take ji sosai dan ta fahimci ba zasu daidaita dashi ba dan baze yuwu ta cigaba da
rayuwa mutane suna yada Mata habai ci ba
Rana na ukun tana tsaye a ɗaki tana ninke kayan da ta kwaso akan igiya
Maida kanta tayi kamar Bata gansa ba cigaba dayin abunda take yi
Hakan ya sosa masa rai amma sai ya danne ya ƙara so tare da rungume ta ta baya
"nayi"
Tafaɗa tana cigaba da ninke kayan
"to inkaine sai mene Aasim? Me kake so ince maka? Tunda ka kasa fahimtata"
"ba haka bane, dan Allah ki saurareni, ranar ma raina ne ya ɓaci, kinsan ina ƙaunar
ki, kishin ki da sonki ne suka hanani fahimtar ki a ranar"
"to dan Allah ki saki ranki kinji? Ba na son ganin ki a yana yin ɓacin rai"
Ta kallesa sosai
"kinga ƙarfin da nike dashi idan na bayyana ga mutane da yawa ba zasu iya ganina ba
To akwai wani kogo da ake zuwa a ƙasar Iraq inda wani tsohon rauhani yike
Idan rauhan yayi training awurinsa na tsawon watanni ƙarfin sa ze ƙaru ta yadda ze
iya bayyana a bainar mutane da yawa
Kinga idan nayi sai inbayyana a gidan ku a matsayin mutum in kuma auranki kinga shi
kenan baki da wata damuwa"
Jinjina kai tayi da sauri dan dama burinta be wuce ta rayu dashi ba, kuma tunda ga
hanyar da babu wanda ze gane ai shi kenan
Ya faɗa
"dan Allah ka tafi yanzu, wallahi ina son ka da kai kaɗai nike so nayi rayuwa a
yanzu"
Murmushi yayi
"kwantar da hankalinki, jibi in Allah ya kai mu zan tafi,sai dai innata fi babu
wata hanya da zata sa damu har sai na gama watannin da zanyi"
Ya jinjina kai
Bayan kwana biyu suna tsaye suna sallama dan ranar ze tafi
" habibty dan Allah ki kula da kanki,na ajiye miki kuɗi a cikin akwatinki duk
abunda zaki buƙata kiyi dasu,inda zan shiga bani da damar koda ganin ki ta madubi
dan haka ki kula min da kanki"
"baka da matsala, zan kiyaye insha Allah, kaima ka kula da kanka sosai"
Ya sumbace ta a goshi
Ita ko Rauda kallon gefen hanya take tayi zuciyar ta cike da tunanin Aasim
Tana ganin ta suka rungume juna cike da kewar juna, salmar ce ta ɗauki akwatinta
tana tambayar ya hanya
"lafiya lau"
Faɗuwa tayi tana ambaton sunan Allah tare da tashi da sauri tana kallon motar
Ganin motar ta tsaya yasa ta duba ƙafarta inda take jin zafi da alamu anan ne taji
ciwon
Ganin ta durƙusa tana duba ƙafarta yasa shima ya durƙusa yana faɗin
"sannu baiwar Allah, kinji ciwo haka? Tashi mu tafi asibiti wallahi bada niyya ta
na buge ki ba, saurin da nike yi ne"
Gabanta ne ya sake faɗuwa,ƙarfin hali ɗagowa tayi ta kallesa suka haɗa ido
*"Rauda"*
_"kada ki ƙara kirana ko nemana, kisa a ranki cewa baki taɓa sanina ba a duniya, ki
gogeni daga rayuwarki"_
Nan da nan ɓacin ran shekarun da suka wuce ya dawo mata sabo fil
Miƙewa tayi tana jin raɗaɗin dake ƙafarta ya tafi sakamakon tuno wa da maganar sa
da tayi
Ƴarfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(y'arfillo)_ 🧕🏻
1⃣ 9⃣ 1⃣9⃣
1⃣9⃣
AGE
_Wannan Page nakune masoya ƴarfillo, haƙiƙa ina jin daɗin yadda kuke yaba labarina
a koda yaushe, nayi kuma matuƙar mamakin yadda labarina ya samu karɓuwa a gurinku,
babu abunda zance muku face godiya Allah ya bar zumunci_
*_Aishatu babayo_*
_ina jinjina miki a koda yaushe,ina kuma godiya da kulawar ki gareni_
*_fatan alkhairi_*
_ga babbar aminiyata da babu kamar ta, *Aisha a Ibrahim* marubuci yar hilwana_
_11:34_🕒AM
TUE,JUN 11
"malan ka bani hanya in wuce? Taimakon kai ni asibiti ne bana so ko ana yima mutum
dole ne?
"Umar?
Binta yayi da kallo yana tambayar kansa to wai ko ba ita bace ne? Ko gizo idanuwan
sa suke masa
Ya zaro ta daga aljihu, ganin me kiran yasa yayi saurin ɗagawa tare da karawa a
kunnen sa
"doctor Umar mutanen nanfa suna cikin wani hali suna gab da rasa rayukansu dan
Allah ka hanzarta"
Be ce komai ba ya kashe wayar yana ƙara kallon get ɗin makarantar ganin sun shige
yasa ya koma motar sa
Ita ko Rauda ba ta tsaya ba har sai da ta isa ɗakin su tana shiga ta wurgar da
ƙaramar jakar dake hannun ta tare da zubewa a ƙasa tana mai da numfashi sama-sama
Salma ta durƙusa tana duba ƙafar Raudan da har lokacin take zubar da jini
"bangane a'a ba, kina ganin yadda jini ke zuba, ga kuma numfashin da kike yi sama-
sama"
"aiko bazan ƙyale ki ba, tunda ba zaki tashi mutafi asibitin ba bari na kira sadiya
ƴar medicine tazo ta dubaki"
Basu ɓata lokaci ba suka emergency room inda Majin yatan suke
Washegari
Rauda na zaune riƙe da plate ɗin abinci tana jujjuya cokalin dake hannun ta
Dan gaba ɗaya ba ta jin cin abincin hakanan take tsintar kanta da faɗuwar gaba a
duk sanda ta tuna sa
_"kada ki ƙara kirana ko nemana, kisa a ranki cewa baki taɓa sanina ba a duniya, ki
goge ni daga rayuwarki"_
Ta kuma sauke numfashi a karo na biyu tana kallon salma da idanuwan ta da suka
canza launi
"babu komai"
Ada nayi tunanin ciwon da kika jini, sai da Naga ana wanke miki ciwon naga ko a
jikin ki hankalinki da tunanin ki ma basa gurin gabaɗaya
Ta buɗe idanuwan ta da suka kaɗa suka yi ja saboda ɓacin ran da ta shiga sakamakon
zafafan magan ganunsa da suka kasa dena yi mata yawo a kunne
"shikenan"
Shi ma Umar haka ta kasance gareshi ko abincin kirki ya kasa ci Allah Allah yike
gari ya waye ya tafi Katsina
Washegari da wuri ya tashi ya shirya ya ɗauki jakar sa wacce ya sa kaya kala biyu a
ciki ya fito falo
"Katsina kuma? Ince shekaran jiya ka dawo daga katsinar? Me zaka je kayi kuma?
" wani abu ne ze kaini, amma bazan wuce kwana biyu ba zan dawo insha allah"
"amin"
Ya faɗa tare da juyawa ya nufi hanyar fita
Ɓangaren Rauda kuwa ta samu ɗan sassauci dan har ta shirya dan zuwa duba sakamakon
jarabawar su da ya fito a ranar
Tare da Salma suka fito suna tafiya suna fira jefi-jefi har suka isa wurin
Kamar yadda wurin ya saba da cika maƙil da ɗalubai a duk sanda sakamakon ya fito
Rauda tsayawa tayi daga baya kaɗan tana na zartar yana yin wurin yayin da Salma ta
kutsa cikin ɗaluban
Rauda na tsaye har Salma ta dubo nata ta fito tana mai da numfashi
Salma tace
"ba laifi, bari na dubo miki"
Sai dai ba ta gani ba, Hakan yasa taɗaga kai sama tana dubawa
Numban jarabawar Rauda ta fara gani a farko ta ɗan ware idanu tana sake dubawa
Numban raudan ce kuwa, wani irin farin ciki ne ya lulluɓeta ta daka tsalle tana
ihun murna
Salma tace
Fitowa tayi fuskarta ɗauke da tsantsar farin ciki, dan har wasu siraran hawaye ne
suka biyo kuncin ta
" kinga zauna a wurin bishiyar can ki jirani inje in haɗo mana drinks dan munana
farin cikin mu"
Tana gama faɗa ta juya a guje ta nufi wurin da ake sai da drinks
Tare da maganar da ya faɗa mata a rana ta farko da ya fara koya mata karatu
_"Rauda ina tabbatar miki da cewa zaki iya, kuma jarabawa me zuwa da first class
Zaki fito Abu ɗaya nike so dake ki mai da hankali akan abunda zan rinƙa koya miki"_
"Aasim nayi rashin ka sosai,zan so ace kana tare dani ayau nasan sai ka fini farin
ciki"
Dai-dai lokacin Umar ya shigo cikin makarantar wuri ya samu yayi parking yana
kallon ɗaluban da ke kai da komowa
Tunda ya zuro da ƙafafunsa ƴammatan dake zaune suna tattauna wa akan saka makon
jarabawar su suke kallon sa
Sai da yaɗan ɗauki wasu sakwanni yana nazarin wurin dan ta cikin glass ɗin motar
yana hango yadda ƴammatan suka zuba masa ido suna jiran suga fitowarsa
"wow"
Wasu daga cikin ƴammatan suka faɗa ya yinda wasu daga cikin su suka saki baki suna
kallon sa
Ya ja Guntun tsaki
"to wai ta ina zan fara ne manta ne?
Wata daga cikin ƴammatan ta taso ta ƙaraso inda yike tana yauƙi wai dan ko zata ja
hankalin sa
" idan da akwai wanda nike nema miye ya shafe ki? Miye ya ruwan ki? Ko akwai abunda
ya dameki dani ne"
Tsaye kawai budurwar tayi dan gaba ɗaya kunya ta gama lulluɓeta ganin yadda ya
yarfa ta cikin jama'a
"fushi ba naka bane, kai da kake so ka nemo ta, kuma ai dole sai da tambaya zaka
gano inda take"
Numfashi ya sauke ya juya sosai yana fuskantar budurwar tare da zare glass ɗin
idanun sa
Ƙarfin hali budurwar tayi dan ganin kyawawan idanuwan sa sun ƙara rikita ta
Budurwar tace
"masu suna Rauda suna da yawa a makarantar nan, gano ta batare da sanin department
ɗinta ba, zeyi wuya gaskiya amma miye sunan mahaifin ta?
Kuma ya kamannin ta suke? Dan akwai wata dana sani a department ɗin mu"
"gaskiya ba ita bace dan wannan sunan ta Rauda mannir kuma ita tana da jiki"
Ya tambaya a ƙagarance
Haka yayi ta tambayar mutane amma duk wanda ya tambaya sai yace be san ta ba
Tayi saurin ɗauke kanta tana dafa ƙirjinta dake bugawa da sauri
Shi ko Umar juyawa yayi da niyyar komawa mota dan ya fara gajiya
Dayike ita take fuskantar inda take yayin da Umar ya juya mata baya
Salma ta kalli Rauda ta dan bata gane abunda take nufi ba amma sai ta mai da kallon
ta ga Umar tana cewa
" dan Allah ki nuna min inda Rauda take, ina son in yi magana da ita ne please "
Ƙara kallon Rauda tayi har lokacin girgiza mata kai take yi
Cikin sauri ya Ƙarasa gurin bishiyar yana yi mata sallama dan kafin Salma ta Ƙarasa
tuni ya riga ta Ƙarasa wa
"ok wa alaikumussalam"
"nafi awa ɗaya ina neman ki, duk wanda na tambaya sai su ce basu sanki ba....
" kinga Rauda dan Allah kiyi haƙuri, ki tsaya ki saurare ni ki sauko daga fushinnan
please"
" ohh na tuna wai na bugeni da kayi? Ai babu komai nasan tsau tsayi ne, sai anjima"
"da alamu dai kayi ma kuwa ne, dan ni Banta taɓa ganin ka ba face ranar da ka
bugeni"
zuciyarsa na cigaba da harbawa, wata kalar sabuwar ƙaunar tace ta fara bi masa
jinin jikinsa
"Rauda nasan nayi kuskure a baya amma dan Allah kada kiyi min irin wannan hukuncin
na nuna baki sanni ba..........
" daka ta bawan Allah, na gaya maka bansan ka, ban san ka ba, kaje Kane mi Raudar
da ka sani dan Allah ka ƙyaleni"
Tana gama faɗar haka tabar wurin dan ji tayi zuciyar ta ta fara karye wa
" gani zanje Katsina, mama ta aikeni kai kana ina ne?
Zayyad yace
"ook ok ganinan zuwa, amma ka kwantar da hankalinka dan Allah, a Ina zan same ka?
Sunan hotel ɗin da ya sauka ya faɗa mishi, sannan ya kashe wayar ya koma motar sa
Tunda ta koma ɗaki take kuka wanda bata san taka mai-mai na menene ba, tana yi ne
kawai dan ta samu sassauci a cikin zuciyar ta wacce take yi mata suya
Ƙarfe biyar zayyad ya isa hotel ɗin Numban ɗakin ya tambaya a ka nuna masa
Ya ƙwan-ƙwansa ƙofar
Umar na kwance kan gado ya Lumshe idanuwan sa jin ana ƙwan-ƙwansa ƙofar yasa ya
miƙe
Ji yayi kansa ya sara, ya dafa kan yana cigaba da tafiya ya buɗe ƙofar
Zayyad kallon sa yayi sosai ganin yana yin sa ya tabbatar mai da yana cikin damuwan
"to miye na damuwa anan? ince Rauda ce yarinyar da baka so Meyasa zaka dami kanka
dan kawai tace bata sanka ba?
" zayyad bazaka gane ba, wallahi a yanzu zuciya ta ta kamu da tsananin ƙaunar ta,
tun ranar dana haɗu da ita Naji naka sa sukuni"
"aini wallahi Rauda tayi min dai-dai da ta nuna bata ma taɓa sanin ka ba
Yarin yar nan tasha wulaƙanci a wurin ka, dan kawai Kaga Tana mutuwar sonka kai ta
wulaƙantata ni kaina ta sha kirana tana kuka akan abubuwan da kake mata
Har ta gaji, sai yanzu ne zaka zo kace wai kana son ta?
Ni wallahi dama nasan wannan ce damuwar taka dan ban tada hankali na nayi ta gudu
akan hanya ba"
"zayyad tabbas nasan nayi kuskure a baya amma yanzu wallahi ina son ta, ka taimake
ni muje tare da kai ka bata ha ƙuri nasan tana ganin girman ka"
Ƴarfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION💫💫💫~*
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
*_fatan alkhairi_*
_Gareka yayana Abdullahi ɗan Fulani nagode da kulawar ka gareni da Allah ya ƙara
dan ƙon zumunci a tsakanin mu_
_12:00_🕒AM
Wed, JUN 19
"wa? rufamin asiri inje inbata haƙuri ta saurare ka ka kuma wulaƙan tata? Ai
wallahi babu ruwana"
"Zayyad wallahi ina son ta,ka taimaka muje dan Allah wallahi tun safe ba abunda
nasa ma cikina.....
"to Naji zan yi tunani kafin goben, dan nasan ka nasan wannan shegen miskilancin
halin naka"
Umar be ƙara cewa komai ba, har Zayyad ya tashi ya je ya siyo abinci ya ajiye ledar
a gaban sa
"ka san Allah Umar bana wani jin tausayin ka, wallahi dariya ma kake bani,dubi
yadda ka wani marai-raice akan yarinyar da ka furta da bakinka baka son ta, baka
ra'ayinta"
"wallahi Rauda kinyi dai-dai Allah ya sa ma gobe ko mun je ta kuma nuna bata san ka
ba"
"yanzu Zayyad dan kaganni cikin damuwa shine kake wannan dariyar har kana faɗin
baka jin tausayi na?
OK yi haƙuri, gaskiya kabani tausayi sosai jima nike yi kamar inyi ma kuka"
"wai ni Rauda na kasa gane miki wallahi, kin zauna kina ta kuka daga ganin mutumi,
Na tambaye ki waye shi kince baki san shi ba yakike so inyi da raina ne? Wallahi
kukan nan naki ɗaga min hankali yike yi"
Rauda tayi ƙoƙorin tsai da kukan ta amma ta kasa dan da ta tuno sa sai taji wani
dunƙulen abu ya to kare mata ƙirji
"Salma kiyi haƙuri, baki san abunda nike ji bane, nayi alƙawarin zan faɗa miki amma
ba a yanzu ba, dan yanzu ina buƙatar natsuwa ne"
"shikenan ubangiji ya yaye miki, amma ki rage sa kanki cikin wannan muguwar
damuwar"
Kaɗa Mata kai kawai tayi alamar taji, amma Saman zuciyar ta ji take yi kamar an
ɗaura mata wani abu me nawi
"me yasa dan nagansa hankalina ze tashi haka? Shin ko har yanzu ƙaunar sa bata fita
acikin zuciya ta bane?
Girgiza kai tayi da sauri tana sa hannu ta bubbuga kanta
"Rauda ki natsu, kin riga da kin cire sa aranki,tsayin lokaci,ki cigaba da man tawa
da shi kamar yadda ya umarce ki a baya
Kada ki manta da alƙawarin da kika ɗaukar ma kanki na ko zaki mutu baza ki ƙara ne
mansa ba"
Tausayin ta Salma taji sosai, dan sai lokacin ta gane abunda take nufi
*Kogon iraq*
(bari mu wai-wayi Aasim)
Kallo ɗaya zaka ma sauran rauhanan ka gano tsantsar gajiya da damuwa a tare da su
Banda Aasim da shi sam babu wannan alamar gajiyar a tare da shi
Tsohone tukuf fari sol me dogon gemu, dan gemun sa har jan ƙasa yike yi
"yaro wani abu ne ya tsaya min a rai ya sa na kira ka, gani nayi gaba ɗaya rauhanan
da suke training sun nuna gajiya warsu da ƙosawar su
Amma kai Kwata-kwata banga Hakan a tare da kai ba, dan wani zubin ma hango ka nike
yi kana murmushi"
"tabbas abunda kafaɗa gaskiya ne, Sam ajikina bana jin gajiya wa,ƙosawa ta ɗaya ce
ingama inje inyi abunda nazo domin sa"
"tabbas ba ƙaramar ƙauna kake yi wa bil'adamar can ba, tunda har ka iya rabuwa da
ahalinka da matsayin ka na ɗan babban sarki, ka kuma zo kana shan wahala dan kawai
ka cigaba da rayuwa da ita
Amma kana ganin ba kayi kuskure ba kuwa? Da ka bata yarda ɗari bisa ɗari?
Murmushi Aasim ya kuma yi yana girgiza kai
"ko kaɗan banjin nayi kuskure, domin yadda nike son ta, haka ita ma take sona"
"to shikenan Allah yasa Hakan, amma nasan halin mutane lokaci ɗaya zasu nuna son
abu lokaci ɗaya kuma zasu nuna ba sa so, ina yi maka fatan nasara a rayuwar ka"
Miƙewa yayi ya koma cikin ƙan-ƙarar yana jujjuya maganar abu simnan
"nasan ba zaki taɓa juya min baya ba Rauda, ina tsananin rashin ki Allah yasa kina
kula min da kanki"
Da sassafe Umar ya tashi ya shirya cikin manyan kaya, wani ya din malesia ne me
silɓi kalar navy blue
_"Jaana idan kasa manyan kaya kana yin kyau, ganin ka nike yi kamar ango"_
Ya faɗa yana komawa bakin gadon yana tashin Zayyad dake ta sharar baccin sa
Umar yace
"me zamuje muyi da sassafe haka? Kabari gari ya waye sosai mana"
Umar ya ce
"ai dama ba yanzu zamu tafi ba, kata shi dai ka shirya dan nasan wannan daɗewar da
kake yi a wanka kamar me canza fata"
"Allah ka cika ta kura umar, sai kaje ka haɗo mana abin kari ai kafin in fito"
_Umar dan Kaga ina son ka shiya sa kake wulaƙan Tani ko? Ka sani cewa bani na ɗaura
wa kaina ba, Allah ne ya ɗaura min"_
Tun daga nesa suka hango juna wanda sai da ƙirjinsu ya amsa su duka biyun
Kamar ta juya ta koma sai kuma wata zuciyar tace ta cigaba da tafiya kawai
Tunda ga nesa yike kallon ta,tafiya take yi a natse kamar tana jin tsoron taka ƙasa
Komai nata daban ne, wani numfashi ya sauke tare da ajiyar zuciya
Zayyad ko burgesa tayi ganin yadda ta ɗauke kanta kamar Bata gansu ba
Ta kuma haɗe fuskarta, har ta iso inda suke tana niyyar wucewa
"Rauda dan Allah ki tsaya ki saurare mu, mun san munyi kuskure amma kiyi wa girman
Allah da soyayyar da kike yi wa annabi Muhammadu(s.a.w)"
"to bawan Allah ina jin ka na tsaya ne ba dan niyya ba sai dan kira fiyayyen
halitta da kayi"
"nagode sosai, amma me ze hana muɗan sami wuri mu zauna, saboda mu tattauna abunda
ya kawo mu a tsana ke?
Zayyad yace
"ok to shikenan,dama akan maganar Umar ne, ya ce min kin ƙi kula sa kina ce mai
baki san shi ba, Rauda nasan Umar me laifi ne a wurin ki amma dan Allah kiyi
haƙuri....
Dafa kanta tayi cikin damuwa tana kallon Umar da ya zuba mata ido
" oh Allah na,bawan Allah wai ba kaji abunda nafaɗa ma jiya bane? Nace ma ban san
ka ba"
"bawan Allah idan baya jin hausa sosai ne kafaɗa masa yadda ze Fahimta bansan sa
ba"
"Rauda nasan zafin zuciya ne yasa kike faɗan haka, yanzu Nima zaki ce baki sanni
ba?
Ta ɗaga kai
" eh kaima ban san ka ba, ina ga dai me kama da ni kuka sani amma bani bace
gaskiya"
Gaba ɗaya kan shi ya ɗaure ganin irin kallon da take masa
"gashi sunan mu yazo ɗaya, amma shin ka taɓa haɗuwa da ita ne a baya?
" to a ina ka Santa kenan? Tunda baka taɓa haɗuwa da ita ba?
"Rauda sau nawa zan baki haƙuri ne? Idan ma haƙurin da na baki beyi miki bari
indurƙusa in baki amma kidena nuna min bake bace please"
"Ashe?
" kenan hotuna ta tura maka, ta kuma faɗa maka sunan ta Rauda isma'il
Shin baka tunanin tayi amfani da hotunan da ba nata ba, ta kuma yi maka ƙaryar
suna?
" idan tayi min ƙaryar suna da kuma hotuna ai bazata aro fuskar ki tasa ba, kinga
Rauda kidena wani kwana-kwana ke ce domin har video call mun sha yi dake"
"to ni dai ban san ka ba, nafaɗa kuma zan sake faɗa, dan Allah kada ka sake biyo ni
inda nike, kaje ka nemi wacce ka sani amma bani Raudan ba Dan ni ko me kama da kai
ban sani ba bare kuma kai"
Zayyad yace
"Rauda ko Allah muna yi masa laifi ya yafe mana bare tsakanin mu ƴan adam........
"Umar shiga mota mu tafi ko kabita bazata saurare ka ba, kuma Kaga hankalin mutane
ya fara dawowa kanmu"
Be ce komai ba ya buɗe motar ya shiga, zayyad ya mara masa baya yana tada motar
"zayyad kafaɗamin yadda zanyi in shawo kanta, wallahi ina jin zuciya ta tana min
nawi, ina sonta zayyad"
Tabbas a yanzu ya yadda Umar da gaske yi ke yi yana sonta, ganin duk irin zafin sa
amma yana niyyar durƙusa mata
Amma Sam shi bega laifin ta ba, dan Umar ya cancan ci hukuncin da ya wuce haka ma a
wurin ta
"kai ma Umar ka san ba ka kyauta mata ba,abunda da yawa maza ba su gane ba shine
Idan taji baka da lafiya nikaina sai tamin kira fin goma tana tambayar ya jikin ka
Amma kai sau nawa tana faɗa ma tana gadon asibiti amma ka iya kira ko sau ɗaya ne
kace mata ya jiki ba kayi
"zayyad dan Allah ka dena tuna min abunda ya wuce nasan ni me kuskure ne ka faɗa
min yadda zanyi kawai"
"ka cigaba da zuwa kana bata haƙuri insha Allah zata sauko"
Rauda na shiga ɗaki tafaɗa kan katifa tana maida numfashi dan zahiri ba ƙaramar
dauriya tayi ba
Tabbas ta san yadda taso Umar, babu wani mahaluki a duniya da za taso kamar yadda
ta sosa
Tasha yin kuka,kasa barci akan ƙaunar sa kai har rashin lafiya
Wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncin ta yayin da ta tuno wahalar da tasha a kan
ƙaunar sa
"me yasa Umar? Me yasa kamin haka? Me yasa baka zo a sanda nike buƙatar ka ba sai
bayan na cire ka a zuciyata?
"dan Allah zuciya ta kada ki dawo min da ƙaunar shi,ki ci gaba da manta wa da shi"
Amma still nuna take yi bata Sansa ba, wani zubin ma ko saurarar sa bata tsaya wa
yi
"Rauda!
" Rauda ya kamata ki tausaya min, ki sassauta min haka, wallahi ko barci bana iya
yi,Rauda ina ƙaunar ki a yanzu fiye da yadda kike tunani........
"na roƙeka ka fita da ga rayuwa ta kadena zuwa inda nike, dan Allah"
"ina sonki Rauda bazan iya rayuwa babu ke ba, dan girman Allah ki yafemin abunda
nayi miki"
Ji tayi kuka na so ya ci ƙarfin ta,da sauri tabar wurin tana dafa ƙirjinta da yike
yi mata suya
"Rauda dan Allah ki sassauta masa haka, wallahi ya galabaita kuma kema fa har yanzu
kina son sa"
Rauda ta ɗago jiƙaƙƙun idanun ta tana kallon salma
_kada ki ƙara kirana ko nemana kisa aranki cewa baki taɓa sanina ba ki gogeni daga
rayuwar ki_
Girgiza kai tayi da sauri yayin da zafafan kalaman sa suka sake yi mata yawo a
kunne
"bazan iya ba Salma, bazan iya ba idan nayi haka ban kyauta wa kaina ba, shi da
bakin sa yace in goge sa daga rayuwa ta, nayi kuma abunda yace Meyasa yanzu ze dawo
gareni Meyasa?
Tunda ya koma mota yike jin zuciyar sa na ƙuna tuƙi kawai yike yi batare da yana
kallon hanya sosai ba
Sai dai duk da haka Be tsira ba dan wata ƙatuwar bishiya ya daka
"kamar yadda muka gama da horon ƙan-ƙara yanzu zamu shiga kogon marzaj
Kogone dake ɗauke da tsumi wanda dashi ne zan haɗa muku bayyana acikin jama'a
Sai dai kusani kafin kuje inda tsumin yike akwai wasu baƙaƙen ifiritai wanda suke
da sarauniyar su guda
Sanin kanku ne kamar yadda muke da ƙarfi haka suma ifiritai suke da shi
Dan haka sai kun dage dan idan ba kuyi da gaske ba, za ku iya rasa rayukan ku
Da zarar kun isa wurin wannan tsumin kuyi gaggawar ɗiba sannan kuyi gaggawar fitowa
Amsawa suka yi da to
Wasu daga ciki farga ba ne maƙil acikin ransu, yayin da shi Aasim Sam baya jin wata
fargaba
"anan zan dakata inbarku ina yi muku fatan nasara, sannan kusani shan wannan tsumi
agareku bawai bayyana acikin jama'a kaɗai ze muku ba
Aasim ne a gaba, tafiya suka ƙara yi me nisa sannan suka isa ƙofar wurin
Sai da suka tsaya sukai nazarin wurin sannan suka doshi ƙofar
Wasu manyan ifiritai ne suka bayyana wanda girman su ya wuce na misali sanye da
wasu baƙaƙen kaya da manyan wuƙaƙe
Suka zaga ye su
Sunyi kusan awa ɗaya suna gabzawa yayin da su Aasim suka jigata sosai
Tunawa da Rauda da yayi da irin ƙaunar da yike mata yasa yaji wani sabon ƙarfi yazo
mishi
Nan da nan ya miƙe daga zubewar da yayi ya shiga tsakiyar su yana kai musu sara ta
ko ina
Ta ɗauro alwala ta gaba tar da sallah sannan ta ɗaga hannu tana kai kukan ta ga
ubangiji
Salma tace
Tunda ga nesa take kallon inda yike tsayawa duk safiya amma bata ga motar sa ba
Ƙirjinta ne yayi wani mugun bugawa ta juyo a razane tana duban Zayyad
"Rauda Umar ya na cikin wani ma wuya cin hali bani da tabbacin ze rayu ko baze rayu
ba"
Ƴarfillo.
[20/10, 8:40 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
2⃣ 1⃣ 2⃣1⃣
2⃣1⃣
AGE
~_Ina da wata buƙata kutayani da addu'a Allah ya biya min,ya cika min burina
please_~
_8:50_🕒PM
THU, JUN 20
Zayyad yace
"baki ji me nace bane? Accident yayi kuma duk kece sanadi, dan da kin saurare sa da
Be shiga damuwar da ze fita hayya cin sa ba"
"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, ka kai ni asibitin da yike ka kaini in gansa
dan Allah"
Ta faɗa tana runtse idanuwan ta da suka cicciko da hawaye masu zafin gaske
Sanin kanki ne Umar ɗin da kika sani da, ba shi bane yanzu
Wani irin roƙo ne be yi miki ba? Wani irin haƙuri ne be baki ba? Amma duk kika nuna
baki san yanayi ba?
Dafa kanta kawai tayi da yike cigaba da sarawa batare da ta ƙara tanka masa ba
Kwance ta hango Jikinsa duk bandeji, jikin ta na rawa ta Ƙarasa gaban gadon
zuciyar ta na wani irin rawa
"Umar!
Ta Kira sunan sa,ko motsi Be yi ba ballantana ya amsa mata, idanuwan sa na rufe ruf
Ta kuma faɗa
Kafin ya ganta sosai,ita ko ganin ya buɗe idon yasa ta sauke wani nannauyan
numfashi
"Rauda"
"Rauda ina son ki, dan Allah ki ce min kin haƙura da abunda nayi miki, ki amsa kin
yafe mini"
"nagode"
"a'a Rauda, sam kada ki bani haƙuri na cancan ci fiye da abunda ma kikai min"
Kaɗa kai tayi tana kuma share fuskarta gaba ɗaya jikin ta ya mutu.
Ya girgiza kai
"a'a ki tsaya Zayyad ya duba ki, ki tsaya tare dani please"
Bata jira jin me ze ƙara cewa ba tayi gaba,tana tafiya jiri na kwasar ta
"bafa ze yuwu ki tafi cikin wannan halin ba, tunda dai har kinzo asibiti muje
induba ki"
Numfashi ta sauke tana kaɗa kai dan ta ƙagara ta zauna ji take yi kamar zata faɗi
Da daddare,tana zaune kan gadon asibitin ta tsura ma drip ɗin ido, gani take yi
baya sauri dan kaɗan-kaɗan yike ɗiga, Allah Allah take yi ya ƙare su tafi
Sannan ta ce
"kaɗan ƙara gudun ruwan bana so dare yayi sosai ba mu tafi ba"
Zayyad yace
"ai bayan wannan ma akwai wasu,dole tafiyar ki sai ta kai gobe da yamma saboda da
alamu kinyi ta ciwon a tsattsaye"
Salma tace
"gaskiya gwara kitsaya ki samu sauƙi Ƙawa,kiyi haƙuri zuwa goben"
"Hakan ya kamata,Shima Umar yanzu muka dawo dashi ɗakin dake jikin wannan"
Lokacin Salma ta daɗe da yin bacci,zare abun ruwan tayi ta sauko ta fito
Gabanta na faɗuwa ta dafa ƙirjinsa jin yana numfashi yasa ta sauke doguwar ajiyar
zuciya tare zauna wa a kujerar dake gaban gadon
Ta tsura mai ido,kyakkyawar fuskar nan nasa tayi fayau, sai dogon hanci
"Umar!
Tabbas ta san har yanzu tana ƙaunar sa, dan sonsa da banne acikin zuciyarta
Shine wanda ta fara so, kuma shi kaɗai ne wanda tayi ma so me tsanani
Gashi lokacin ta daɗe tana fatan zuwan sa na ranar da Umar ze ƙauna ce ta yazo,
amma sai dai kash
Aasim,ya riga da ya danne komai, dan Shima tana sonsa amma bazata taɓa haɗa son da
take yima Umar da wanda take yi masa ba
"Meyasa sai yanzu Umar? Me yasa kabari lokacin Dana daɗe ina jira ya wuce?
Meyasa?
"kai ne burina, kai ne zaɓi na, kai ne wanda nayi fatan rayuwa dashi a matsayin
miji na har abada, amma kabari lokaci ya wuce dan bazan iya janye alƙawarin da nayi
wa Aasim ba, bazan iya ba!
Kuka me ƙarfi ne yaci ƙarfin ta, ta kifa kanta jikin gadon tana kuka me tsuma
zuciya
Umar duk abunda ta faɗa yana ji, da fari farin ciki ne da jin daɗi ya mamaye
zuciyar sa amma Aasim da ta ambata yasa jikin sa yayi sanyi
Waye shi? Wani irin alƙawari ta ɗaukar masa da take faɗin bazata iya karyawa ba?
"dan Allah kada ki bari ƙaunar Umar ta kuma tasiri a zuciyar ki, Aasim shine wanda
ya cancan ce ki, shi ne ya sadaukar da rayuwar sa da komai nasa akan ki, Umar ko
shine ya wulaƙanta ki a lokacin da kike neman kulawar sa"
Sarauniyar ifiritai tana zaune kan kujerar ta tana kallon abunda yike faruwa
Dakatawar suka yi kuwa, yayin da Aasim da sauran suka tsaya suna mai da numfashi
"nadaɗe banga jarumi irin ka ba,sannan kuma na daɗe banga sakarai irin ka ba wanda
yike sadaukar da rayuwar shi dan kawai ya rayu da bil'adama wannan babban kuskure
ne"
"a gareni Sam ba kuskure bane,kuma a shirye nike da inshiga kasadar da tafi wannan
in har yin Hakan ze ƙara min kusanci da ita"
"kun aikata laifi dan kawai ku sami bayyana acikin mutane kuka shigo mana kogo kuka
karya mana doka,amma duk da Hakan jarumtar da ka nuna zata sa inyi abunda bantaɓa
yi ba
Wato inbada gudunmuwa wajen karya dokar da kakannina suka kafa, tabbas wannan tsumi
dokace bama bari a ɗiba amma kuje na baku dama ku ɗiba iya wanda ze muku"
"godiya muke sarauniya, Allah ya ƙara girma, haƙiƙa kina da taushin zuciya me cike
da tausayi ubangiji ya shiga cikin lamarinki"
Suka wuce zuwa inda tsumin yike, tun da suka isa wurin Aasim ke murmushi
Sai da suka gama ɗiba sannan suka juyo suka yi ma sarauniyar godiya
"aduk lokacin da danasani ya riske ka,ka kuma yi niyyar ɗaukar fansa kada ka manta
wajen neman agajina"
Meyasa ake yi masa zancen yayi kuskure, shi dai yasan Rauda bazata juya mai baya
ba, to shi ko wani danasani zeyi?
Washegari da sassafe Salma ta koma makaranta dan akwai test ɗin da zata yi
Rauda na kwance ita kaɗai, Umar kasa haƙuri yayi ya taso ya shigo ɗakin
Ya jinjina kai
Ya tambaya
Dai-dai lokacin Zayyad ya shigo ɗakin ganin Umar yasa yayi sororo yace
Umar yace
Rauda tace
"dan Allah kabarni in tafi yanzu tunda Naji sauƙi abar ragowar alluran haka"
" wallahi Rauda na taho babu hanya, baki ga yadda matasa suke ta zanga-zanga ba da
Manyan makamai "
Rauda tace
" subhanallah zanga-zanga kuma? Na mene?
"Nima bansani ba amma nasan baze wuce na siyasa ba, bari in koma dan Naga faɗa yana
so ya kaure a wurin"
Da yamma tana tsaye tana kallon tvn dake manne jikin bango
Nurse ce ta shigo
Rauda tace
"wai yanzu ko kaɗan babu hanyar da mutum ze bi ya koma inda yike"
"wallahi babu, dan muma tun rana aikin mu ya ƙare amma waɗanda zasu amshemu basu
zoba ga kuma Waɗan da aka ji ma ciwo ana ta kawo su"
Hakan yasa dole makaranta ta bada hutun gaggawa dan abun harya fara shafan ɗalubai
Dan bata son suna kasancewa tare a yanzu so take yi ta nisance sa ko dan ta hani
zuciyar ta
Bayan kwana uku da dawowarta,suna zaune tsakar gida ita da mama suna girkin dare
"baƙo?
Ta tambaya a zuciyar ta amma a fili shuru tayi tana mamakin wani baƙo ne zezo wurin
ta
Mama tace
"baƙo kuma? Wanene?
Rauda tace
" Nima bansani ba mama, dan bamuyi da wani zezo ba, amma bari naje nagani "
Ko da mamakin ta, Umar ta gani tsaye ya sha wata maroon ɗin Shadda
"ki dena mamaki dan kinganni a ƙofar a gidan ku, nabi kwatancan da kikamin ne na
shekarun da suka wuce"
Gyara tsayuwarta tayi tana yi masa wani irin Kanno masu fassarori da yawa
"to ka kyauta, amma me ya kawo ka gidan mu? Kuma Ƙarasa wanda zaka aika ya kirani
sai mahaifi na?
"adoka ta musulunci idan zaka nemi yarinya ai sai ka fara tambayar izinin iyayen
ta, kuma na tambayi baba ya bani izini innemeki"
Gajeren murmushi tayi wanda ya tsaya mata iya baki kawai wanda ya rasa gane ma'anar
sa
"izinin nemana fa kace Umar? To wai ma in tambaye ka, wani neman da ga ciki?
" Umar ke nan, akan mene zaka nemi izinin aurena batare da ka nemi soyayya ta ba?
"Rauda, ina ce waɗannan abubuwan sun wuce, nasan fa kina sona har yanzu Meyasa zaki
ta maida hannun agogo baya....
Katsesa tayi
"ki faɗa sau biyu, da rana ta farko da kika je asibiti, da kuma rana ta biyu da
kika shigo ɗakin da daddare
"yayi kyau da kaji Hakan, amma ka sani faɗin ina son ka bashi zesa na saurare ka
har na kuma yin wata soyayyar da kai ba, Umar dan Allah ka nisanci rayuwa ta ka
gogeni daga rayuwar ka na roƙeka kamar yadda ka roƙeni a baya"
"Rauda wallahi ina ƙaunar ki,idan kika amince min a gobe zan iya turo iyayena ayi
maganar aure dan ki tabbatar da da gaske nike, wallahi a yanzu banajin zan iya
rayuwa babu ke kuma nasan kema kanki a yanzu kin fahimci Hakan"
"babu abunda na fahimta, kaje kanemi wata, dan yanzu ina da wanda nike so dan Allah
karka ƙara zuwa inda nike"
Ze kuma yin magana ta shigo gida da sauri
Ɗaki ta shiga ta zauna kan kujera tare da kifa kanta wasu hawaye masu ciwo suna
biyo kuncin ta
Mama ta ce
"wani Umar?
"wannan na wayar me kama da Larabawa? To ya aka yi kuka haɗu har yazo nan ba
kundena waya ba tun tuni?
" to miye abun damuwa har da kuka? Ince Umar shine wanda kike so,ban manta ba fa
duk mazajen da kika tsaida da Allah beyi auran ba kin tsaida su ne kawai dan baki
samesa ba, Nasha ganin ki kina kuka kuma nasan duk a kansa ne, to tunda yanzu Allah
ya kawo sa ba sai ki ma Allah godiya ƙila shine alkhairin kuma mijin shiyasa duk
Waɗan can da akasa ranar da su aka fasa kuma yanzu kin tabbata da gaske yike yi?
"cewa yayi wai a gobe ze iya turo iyayen sa dan intabbatar da gaske yike yi"
"to ba shikenan ba, ai kin rama abunda ya miki kuma ya gane kuskurensa kawai ki
kula sa ki kuma amince dan nasan maƙiya sai sun kusan mutuwa saboda baƙin ciki"
Kallon mama kawai take yi yadda lokaci ɗaya ta shiga farin ciki tabbas mama tayi
gaskiya ƙila shine alkhairin shiyasa aka fasa da waɗancan amma Aasim fa?
~ƴarfillo~.
[20/10, 8:41 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽
✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽
✍🏽~*
2⃣
2⃣2⃣
AGE 2⃣ 2⃣2⃣
_Wannan Page nakane *ASLAM* _haƙiƙa ka kasance ɗan albarka wanda aduk sanda na tuna
nike jin sanyi ko da ko ina cikin damuwa ne, ina son ka sosai yarona Allah ya
albarkaci rayuwar ka_
*(nasan bestie zata ce yaro ko zuwa duniya beyi ba kin damemu da aslam aslam, to ki
kwantar da hankalin ki duk da ban riga na haife sa ba amma ƙaunar sa na zuciya ta)*
_Ako da yaushe bana gajiya da yi muku fatan alkhairi masoyana Allah ya bar zumunci_
*_Sannan ina me baku haƙuri sakamakon daɗewa da nike yi banyi typing ba saboda
ƙarancin lokaci, na yanke shawarar ringa yi akai-akai amma sai dai zaku rinƙa gani
ba yawa nagode_*
_8:32_🕒AM
WED,JUL 3
Haka ya cigaba da kasancewa Umar kullum sai yazo gidan su Rauda, gaba ɗaya ya ajiye
aikin sa dan ya tattaro ya dawo Kaduna kuma yayi ɗamarar baze koma Abuja ba har sai
ya shawo kanta
Kamar kullum yana tsaye jikin motar sa yana jiran yaga wuce war yaro ya aika ya
kira ta dan yayi ta kiran wayar a kashe
Sam bata lura da shi ba dan wurin yayi duhu babu haske
Shiko Umar ji yayi kamar shi yayi tuntuɓen ƙarasowa yayi da sauri
Yayi mata tambayar, ɗago wa tayi dan sai lokacin ta lura dashi
Duk da duhun dake wurin be hana ta ganin kyakkyawar fuskar sa ba ma'abociyar haske
da kwarjini
Amma takasa ce mai komai dan duk sanda ta gansa jikin ta mutuwa yike yi
Yayi shuru yana kallon ta yana jin ƙaunar ta na wani irin fizgar sa
"Rauda!
Tsayawa tayi tare da zuba masa fararen idanunta masu ƙara masa ƙaunar ta
" Rauda Allah ma da halicce mu muna yi Masa laifi mun roƙesa gafara ya kuma yafe
mana, ballan tana imu-imu ƴan Adam
Kisani ko Abaya wallahi ina sonki, amma bansan me ya hanani zuwa wurin ki ba, wani
zubin sai na ɗauki waya zan kira ki sai inji nakasa, kuma ko wulaƙancin da nayi
miki Abaya ba da son raina bane
Da kin kirani zanji babu wacce nike jin haushi a duniya sai ke shiyasa nike gaya
miki magan ganu marasa daɗi
_"Kisani ƙaunar da nike miki bazata taɓa bari inbar wani ya raɓeki ba,ke tawa ce ni
kaɗai"_
Ji tayi kanta yayi mata nawi, ta Lumshe idon ta tana ambaton sunan Allah
Tafi minti biyu a haka daga bisani ta buɗe su ta kuma ɗaura su a kanta
Ya Rame sosai,kallo ɗaya zaka masa ka gano baya cikin kwanciyar hankali
"hankalina baze taɓa kwantawa ba har sai kin amince dani,na kuma gode, sannan zuwa
yaushe ne zaki gama tunanin?
Ta faɗa
Ya jinjina kai
Bata ƙara cewa komai ba, ta juya zata koma gida dan bazata iya Ƙarasa wa shagon ba
Dole tana buƙatar wanda ze bata shawara amma wa zata gaya mawa sirrinta?
Ita ce ƴar uwar ta, wacce zasu kashe su rufe batare da wani ya sani ba
Da sallama ta shiga gidan, mijin ta ne ya amsa yana yaye labulen falon dan ya gama
shiri ze tafi kasuwa
Shiga tayi ta zauna kan kujera tana kallon Anty ummi dake sanyawa hanif jakar
makaranta
"yaro na yakake?
" a'a my hanif ina sauri ne shiyasa amma zan kawo maka next time kaji?
"ya mama? Ince dai lafiya dannasan bakya fita da sassafe haka"
Rauda tace
"lafiya lau"
"kinga inni zaki zuba mawa karma ki zuba dan bana jin yunwa, magana nazo muyi"
"magana kuma?
"a'a Sam ba maganar kuɗi bace, ina cikin damuwa ne kawai na kuma rasa yadda zanyi"
Jin kalmar damuwa yasa Anty ummi ta gyara zama tare da tattara hankalin ta guri
ɗaya
Rauda bata ɓoye mata komai ba tun daga ranar da ta fara ganin Aasim har zuwa
tafiyar sa
Wani irin kallo Anty ummi take yi mata na wacce ta fara taɓuwa
"ki dena min kallon wacce ta fara taɓuwa Anty ummi, wallahi da gaske ne, kiyarda da
abunda na faɗa miki"
"bawai banyadda da abunda kika faɗa bane, a'a na yarda dan jinnul aashique mun san
kina dashi amma tabbas baki da hankali
Dan Inba marar hankali ba babu wacce zata yi abunda kika yi, ace kiyar da kirinƙa
rayuwa da jinnu har ki amsa mai zaki rayu dashi har abada kuma ki ɓoye mana"
"nidai Anty ummi kiga ya min yadda zanyi bagashi yanzu na faɗa miki ba, ki gaya min
ya zanyi da Umar,ina tsananin ƙaunar sa har yanzu amma idan natuna wulaƙancin da
Yamin Abaya sai inji duk ya fita a raina"
"ke yanzu har ma kya ga laifin Umar,ai wallahi kidena ganin laifin sa dan bayi da
laifi kwata-kwata bayin kansa bane"
Rauda tace
"to yanzu yakike ganin zanyi?
"aganina tunda shi Aasim ɗin bada mugunta yazo miki ba ki kula Umar ɗin kucigaba da
soyayya
Idan ya dawo sai ki basa haƙuri kice ya bar ki auri Umar, shi kuma ya cigaba da
rayuwa dake a ɓoye, ina ganin Hakan itace hanya me sauƙi tunda Shima yana sonki"
"da wuya ya yadda, dan yana sona fiye da yadda kike tunani"
"dolen shi ma ya yarda dan babu inda aka ce aljan da mutum suyi rayuwa, kina ganin
Gorin da ake yi miki akan rashin aurannan dan haka kada ki bari Umar ya kubce miki
Idan ma be yadda ta sauƙi ba ai sai aje gurin malamai ya rabu dake ta tsiya
Ta kaɗa kai kawai amma ita ta san akwai babbar ƙura a gaba
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
2⃣ 3⃣ 2⃣3⃣
2⃣3⃣
AGE
_12:15_ AM
SUN,JUL 7
"chuchu!
Daga can Ɓangaren Umar tashi yayi daga kwancen da yike yana bata amsa
"na tabbata mana chuchu,wallahi a shirye nike da in aure ki koda kuwa anan da sati
ɗaya ne"
"shikenan idan da gaske kake yi inaso inga alama idan kuma bada gaske kake yi ba
dan Allah kada ka kuma cutar da zuciya ta"
Sai kuma ta kasa Ƙarasa wa dan bata san sanda sunan Jaana ya fito daga bakin ta ba
"dan Allah me Rauda? Ki faɗi kome kike so wallahi zanyi miki shi a yanzu Ba tare da
na ɓata lokaci ba"
"dan Allah kada ka kuma cutar da zuciya ta, idan ka kuma yi min abunda kayi Abaya
ina tabbatar maka da zan iya rasa raina......
"ba sai kin roƙe ni ba Rauda a yanzu bani da wacce nike so sama dake acikin zuciya
ta,kuma ina me tabbatar miki da ba zaki sameni me kuma sanya ki damuwa ba, a yanzu
buri na inga nasa ki farin ciki"
"Umar kasan Kaine wanda nike so kai ne zaɓin zuciya ta, me yasa kayi min abunda
kayi Abaya me yasa?
"dan Allah ki dena tuna baya Rauda, na tabbata a yanzu son da nike miki ya ninka
wanda kike min sau dubu"
"anya kin kyauta wa kanki kuwa Rauda? Ki tuna Aasim da ya bar ahalinsa matsayin sa
da komai nasa akan ki, shin kina ganin kinyi masa dai-dai? Ya tafi yana fafutukar
yadda ze rayu dake amma ke zaki ci amanar sa?
"to idan baki amince kin auri jinsin ki ba, haka zaki ƙare rayuwar da jinsin da ba
naki ba? Kuma Umar shine wanda kike so"
"idan Aasim ya samo abunda yaje nema fa, na bayyana acikin jama'a, baki da hujjar
da zaki ce ya barki kiyi aure tunda dai Shima ze iya rayuwa dake a matsayin mutum
batare da kowa ya sani ba"
Shiko Umar suna gama waya alwala ya ɗauro ya gabatar da nafiloli sannan ya ɗaga
hannayen sa yana godiya ga ubangiji,yana kuma roƙon Allah da ya kaɗe duk wani
sharri da ze sa ya ƙuntata mata
Zaune suke cikin Sahara suna tattauna yadda suka yi gwaji akan bayyana cikin jama'a
"ni fa a suffar mace na bayyana, na yi shigar kaya masu kyau na bayyana a wata
kasuwa
Idan Kaga yadda mazen bil'adama suke kallo na kai kace haɗiye ni zasu yi
"amma kai ko ka iya iskanci wallahi, ni a suffar almajiri na bayyana a wurin wani
cin a binci kuma a suffar yaro
Wata mata da ta ganni sai da ta kusan yin kuka
Wai ji ɗan ƙaramin yaro amma yana neman abunda zeci bata san ƙila tun kan a haifi
iyayen ta nike duniya ba"
"Aasim kai kowa yana bada labari amma ka zauna kayi shuru, lafiya dai ko?
Ya faɗa
"a'a akwai komai mana, nasan baze wuce tunanin bil'damar ka kake yi ba, to ka
kwantar da hankalinka mana saura wata ɗaya fa mu koma, musha biki"
"abokina a wace ƙasa zaka ci amarcinne? Dan nasan yadda ka zaƙu muna komawa zaka yi
mata maganar aure"
"ni kunbi kun cika min kunne da surutu bari in baku wuri"
"afuwan fa mun manta da yarima ne a wurin, wanda baya son haya niya"
"habibty ina tsananin rashin ki,nasan kema kina can kina tunani na, ke ce rayuwa ta
habibty"
Macijiyar ta tsura mai ido amma ta kasa matsawa daga inda take
Ta wuce
"da gaske nikeyi kana da kyakkyawar zuciya shiyasa nike tausaya maka"
Da safe, tana zaune tana tsakurar abun kari dan Sam bata jin cin komai
Tana sallama
"lafiya lau"
Ta bashi amsa
"masha Allah Naji daɗi da Naji Hakan, tun ɗazu naso in kira ki sai nayi tunanin
baki tashi ba"
Tayi ɗan murmushi dan jin muryar sa damuwar da ta cunkushe zuciyar ta ta rage
_~Ƴarfillo~_.
[20/10, 8:42 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
✍✍✍✍✍✍✍
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
✍✍✍✍✍✍✍
2⃣ 4⃣ 2⃣4⃣
2⃣4⃣
AGE
_Wannan Page nakine *maman isqah* kin kasance me dogon sharhi a duk lokacin da nayi
posting ina matuƙar jin daɗin Hakan Allah ya bar zumunci_
*_Fatan alkhairi_*
_Ga *princess mazadu* ina miƙa gaisuwa_
_9:48_🕒 AM
MON, JUL 8
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
"yau na tashi cikin farin ciki sakamakon wani kyakkyawan mafarki da nayi"
Umar ya faɗa
Rauda tace
"mafarki? Mafarkin me?
Daga can Ɓangaren Umar gyara zama yayi yana ɗan jingina da kujerar da yike zaune
"mafarki nayi munyi aure,kin haifa min kyawawan yara ƴan uku, masu kama da ke"
Jin tana amsa mai faran-faran yasa yaji ya ƙara shiga cikin nishaɗi
"inma ba zaki iya ba, ranar haihuwar sai mu raba in haifi biyu ki haifi ɗaya"
"wa yaga Umar na naƙuda, ai inaga duk faɗin garin Abuja sai sun taru"
"ke haihuwa fa, cap ai kudai mata sai dai mu muku fatan shiga aljannah amma zahiri
kuna mugun ƙoƙari"
Ajiyar zuciya ta sauke, dan tunda ta fara jin muryar sa taji natsuwa na saukar mata
"Rauda!
"kin karya?
Ya tambaya
Umar yace
"na sani kawai ina buƙatar inganki ne"
Yace
"to shikenan Allah ya kai mu ki kula min da kanki"
"nagode"
Ta faɗa tana ajiye wayar
Ranar wuni tayi cikin farin ciki dan firar da suka yi ce kawai take mata yawo a
kunne
Dan duk wanda yaga Umar sai yayi mamaki ga kuɗi ka ga kyau ga kwarjini, duka Allah
ya haɗa masa
Yau Asabar, tun ƙarfe huɗu Umar ya taso kuma tunda ya taso suke waya
"wai ni Rauda yau wayar nan ba zata ƙare bane? Muna da aiki fa ga yamma nayi"
Murmushi Rauda tayi tana yin ƙasa da muryar ta tace
Tana gama faɗa ta kashe wayar tana duban mama dake ta zuba murmushin jin daɗi
Mama tace
"soyayya da mai da yaji"
"kai mama"
Ƙasa Rauda tayi da kanta cike da jin kunya tana tura mai saƙo
_amin chuchu, ki kula min da kanki, ki kuma sa girkin dani zanci, ina sonki_
Murmushin jin daɗi tayi bayan ta gama karantawa a zuciyar ta tana faɗin
"na yarda da ake cewa addu'a bata faɗuwa ƙasa, kuma duk daren daɗewa Allah ze amsa
ka"
Ta faɗa tana tuna lokacin da take tashi dare tayi ta addu'ar Allah ya ɗaura wa Umar
son ta
Ta kwashi minti 30 tana shiryawa, sai da ta gama sannan ta ɗauko doguwar riga ta
sanya
Ya faɗa
To tace tare da ajiye wayar ta ɗauko gyale ta yafa tare da fesa turare emergency
Cikin natsuwa ta fito yana tsaye yana waya cikin ƙana nan kaya
Yayi kyau sosai, yana wayar yana murmushi yana kuma shafa kwataccen sajen sa wanda
ya zagaye farar fuskar sa
Ƙarasa wa tayi tana zuba masa kyawawan idanuwan ta wanda suka narke da ƙaunar sa
Sai da ya gama wayar, sannan ya fuskance ta yana kallon fararen idanunta fuskar sa
ɗauke da murmushi
" lafiya lau,boo boo kinsan Allah kinyi kyau kamar wata balarabiya, ji nike yi
kamar in sace ki"
Ya jingina da jikin motar yana Lumshe shanyayyun idanun sa da suka jiƙe da tsananin
ƙaunar ta
"ba yanzu ba to sai yaushe? Kinsan Allah bazan iya ƙara wata uku ba tare da na
mallake ki ba"
" sai ayi transfer ki koma ta Abuja, amma Allah bazan iya ƙara wani lokaci me tsawo
ba tare dake ba"
"Allah bazan iya ba, ba zaki gane yadda nike jinki a raina bane, ki taimaka kiga ya
ma baba kafin in koma na turo plz"
"shikenan"
Gaba ɗaya ya ƙagara goben tayi jefi-jefi ya kan duba lokaci gani yike kamar lokacin
baya gudu
"banga laifin ka ba, dan kayi mamaki ni kaina abun ɗaure min kai yike yi,dan bazan
iya kwatanta adadin ƙaunar da nike mata ba"
Washe gari Rauda na zaune gaban Abba, dan tun a daren jiya ta gaya ma mama abunda
Umar yace ita kuma mama ta faɗa masa
"maman ki ta faɗa min abunda Yaron yace, gaskiya na yaba da hankalin sa da kuma
tarbiyyar sa, kuma nasa ya yanki amadu dake Abuja yayi min bincike a kansa bayi da
wata matsala
"ai ni dama gobe yace wallahi,amma Allah ya kai mu jibin ki tambaye sa da wani
lokaci zasu zo?
"shikenan amarya"
Tayi dariya tace
"amarya kuma?
Umar yace
" eh mana, dan zan faɗa ma uncle ɗina yace nan da wata uku suke so"
"to Aasim ina maka fatan alkhairi, amma kada ka manta da neman taimako na aduk
sanda ka shiga tsaka me wuya"
"Nima na gama shiryawa mu haɗa hanya, amma dan Allah ina neman wata alfarma a wurin
ka"
Jazmi yace
"inaso mu biya ta masarautar mu, nasan mahaifiyata zata ji daɗi idan ta
ganka,saboda sunan ka ya karaɗe duniya na ɗan babban sarki, kuma masarautar mu zata
ƙara matar ba da suna idan kaje"
"shikenan muje, amma fa muna zuwa zan wuce dan bazan daɗe ba"
"nayar da mu tafi"
Gefe kuma kyawawan kuyangi ne ke rawa cikin salon ƙwarewa da ɗaukar hankali
Kallon su kawai Aasim yike yi amma kwata-kwata hankalin sa baya kansu in banda
ƙosawa babu abunda ya cika zuciyar sa
*~Ƴarfillo~*.
[20/10, 8:42 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
2⃣
2⃣5⃣
AGE 5⃣ 2⃣5⃣
_11:59_🕒 PM
MON, JUL 8
Domin magiyar duniya babu wacce jazmi da mahaifiyar sa basu masa ba akan ya kwana
anan take suka bada kuɗin gaisuwa suna tambayar nawa aka yanke sadaki?
baba haƙuri ya basu akan ze neme su nan da wani ɗan lokaci amma dan ba Umar Rauda
anbashi
Tun bayan tafiyar su Rauda da Umar suke maƙale a waya,wata kalar soyayya ce me zafi
take ƙara shiga tsakanin su
Yana bin ƙamshin jikin ta wanda yasa dashi da ita har uwaɗɗakan da take
Ita ko tsayuwar mutum taji a bayan ta,kuma bata jiyo tafiya ba, Hakan ya sa gaban
ta yaɗan fara faɗuwa
Juyo wa tayi a hankali,wani mummunan faɗuwa Gabanta yayi zuciyar ta na wani irin
kaɗawa
Tsaye tayi tana kallon sa ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi,in banda fargaba da tunanin
abunda ze faru babu abunda ya cika zuciyar ta
Shiko mamaki ne ka masa, ganin ita da zata yi farin ciki da murnar dawowar
shi,shine zata tsaya tana kallon sa kamar ma bata so dawowar nasa ba
"habibty!
"habibty duk ɗoki da murnan da nike yi akan naganki ashe ke bakyayin Hakan, nayi
zaton zaki yi farin ciki da ganina amma sai Naga saɓanin Hakan, ki faɗa min me ke
faruwa, ko kin canza min matsayi a zuciyar ki ne?
Ta tambayesa tana fatan yace be samo ba dan ta samu hujjar kare kanta
"na samo habibty,yanzu baki da wata matsala ko nan da gobe kika ce na fito na
bayyana a gidan ku zan bayyana"
" to shikenan yanzu kaje ka huta, anjima sai ka dawo dannasan mama tana gab da
shigowa"
"a'a anjima kam sai dai Nazo mu tafi, dan wallahi ina buƙatar ki sosai"
" a'a bazan bari Hakan ta kasance ba,dole na nemi mafita nasan yadda zan ɓullo ma
al'amarin tun kafin Aasim ya gane"
Miƙewa tayi ta zura hijabi kai tsaye gidan Anty ummi taje ta gaya mata
"kisa Allah aranki babu abunda ze faru insha Allahu,ze ya fahimce ki da yardar
Allah"
Girgiza kai Rauda tayi dan ta san Aasim baze taɓa yarda ba
"Anty ummi nasan baze yarda ba, damuwa ta mani kada yayi ma Umar wani abu, ina
sonsa sosai bana so wani abu ya same sa"
Miƙewa Rauda tayi tana kaɗa kai bata ƙara cewa komai ba tafi to tana tafiya tana
harharɗewa
Ko bata duba ba ta san Umar ne, dan taken kiransa daban tasa masa
" a'a ba haka bane, na kira ka da rana wayar bata shiga ba, da yammannan kuma bana
cikin natsuwa ne shiya sa"
"subhanallah me ya faru?
Ya tambaya da sauri
"bazan iya rayuwa babu kai ba, ina fargaban ka kuma nisan tata"
"chuchu taya za'ayi na nisance ki? Kema kinsan bazan iya ba, a yanzu babu wani abun
da ze rabani dake sai dai mutuwa"
"Rauda, wai meke faruwa ne? Ki faɗamin dan Allah, dan wallahi hankalina ya fara
tashi"
"wannan ba maganar waya bace, kabari zan faɗa ma amma kafinnan inaso kamin wata
alfarma guda ɗaya"
"alfarma? Wace kalar alfarma kinsan kin wuce da matsayin alfarma a gurina kifaɗamin
kawai ko menene zan miki shi"
"zan kashe wayata na tsawon kwana uku,kuma bana so inkaji shuru kace zaka kira
wayar mama ko wata wayar da zaka sameni, sannan kada kayi yunƙurin zuwa har sai na
neme ka da kaina"
"what? Kinsan me kika ce kuwa Rauda? Inyi kwana uku batare da Naji muryar ki ba?
Kema kinsan bazan iya ba"
Ya faɗa
"kayi haƙuri, Nima ba da son raina bane,akwai matsalar da nike so inga yadda zata
kasance ne tukunna"
"Rauda kifaɗamin abunda ke faruwa, kinsan ba ƙaramin aiki na bane nabaro Abuja
yanzu ko?
"a'a, dan Allah kayi haƙuri,zan kashe wayar yanzu kuma dan Allah kayi abunda nace
ma please Jaana"
Ze kuma yin magana ta katse kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya
Wani kalan nawi taji ƙirjinta ya mata ta shiga gida lokacin mama ta dawo
Mama ta tambaya
Da daddare, saida mama ta ta tafi ɗakin baba sannan taji iska na ɗiban ta
" Aasim!
Ta Kira sunan sa, ya sassauta rungumar da yayi mata tare da ɗago kyakkyawar
fuskarta ya zuba mata ido
Shuru tayi tana kallon sa kawai, sun kuyo da fuskar sa yayi yana ƙoƙarin haɗa bakin
sa da nata
"please ka tsaya"
Zata miƙe yayi saurin danne hannayen ta dana sa, yana kissing ɗin wuyanta
*~Ƴarfillo~*.
[20/10, 8:42 pm] Sumiee B.: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
*🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
_Wannan Page nakine *oum deedad*, nakine ke kaɗai kiyi yadda kikeso dashi_
_11:22_🕒 AM
TUE, JUL 9
Hakan yasa ya dakata daga abunda yike yi ya tsura ma fuskar ta ido cike da mamakin
sabon al'amarin da ta zo masa dashi
Yafi minti uku yana kallon ta da karantar yana yin ta, daga bisani ya ɗaga ta ya
bar ɗakin
"Rauda be kamata ki canza masa lokaci ɗaya ba, idan Hakan ya ɓata masa rai fa? Har
ya gano kina ganin ze tsaya ya saurare ki?
Ta riƙe ƙofar tana kallon sa kawai dan tama rasa yadda zata yi
Haƙuri zata je ta basa kome? Dan zahiri ba taso ya ƙara wata mu'amala da ita
Dan ta san aduk sanda wani abu ya shiga tsakanin su ƙara ƙaunar ta yike yi
Tana tsaye tana saƙe-saƙe taji ya kira sunan ta kuma har lokacin idanuwan sa na
rufe
"Rauda! Zo nan"
"nace kizo ko? Bawani abu zan yi miki ba ai tunda bakya so"
Jin ya haƙura da abunda yike niyyar yi yasa ta ƙara so gaban kujerar ta durƙusa
Tashi yayi daga kishingiɗar da yayi yana kama hannun ta na dama gami da shafa
tafin hannun
Sai ga wani ganye ya fito, mamaki ne ya kamata ganin yadda ganye ya fito a hannun
ta
Shafa ganyen yayi sai ga tsakiyar ganyen ya zama kamar TV take ya fara nuna masa
Ita dai Rauda taga yana kallon ganyen amma bata san me yike gani ba dan yana zaune
ne akan kujeran yayin da take tsugunne a gaban sa
Hankalin sa ya tashi sosai take idanuwan sa suka sauya kala zuwa ja kamar garwashin
wuta
Nan da nan jikinsa ya fara fitar da wani turiri wanda yasa taja baya da sauri cike
da tsoro
Ja da baya ta fara yi cike da tsananin razana dan ya zamar mata kamar wani namijin
zaki
"nace ni zaki ci amana? Ina can ina shan baƙar wahala da saida rayuwa ta akanki,
ashe ke kina nan kina cin amana ta?
Dede lokacin ta kai jikin bango babu kuma inda zata ƙara matsawa
Damƙo gashin kanta yayi wanda yasa ta saki wata ƙara saboda tsananin zafin da taji
Ya matso da fuskar ta dede tasa dan tana jin yadda yike fitar da wani huci me zafin
gaske
"kiyi magana!!
Ya faɗa cikin tsawa wanda saida fitulun ɗakin wasu suka tarwatse
Babu inda baya kyarma a jikin ta cikin tashin hankali da tsananin tsorata tace
" ka.....yi...ha..ƙuri"
Cigaba da kallon ta yayi still hannun sa na damƙe da gashin ta amma ya kasa ƙara
furta komai in banda suya babu abunda zuciyar sa ke masa
Dan yanzu ma babu ƙwayar idon kwata-kwata, ƙara rinewa kawai suke yi
"ashe shiyasa baki yi farin cikin dawowa na ba,ashe shiyasa kika ƙi amince wa da
buƙata ta saboda kin canzani a zuciyar ki"
Aasim ya faɗa cike da tsananin takaici
"bazan taɓa amince wa da wannan butulcin ba, bazan taɓa amincewa ba!!!!
"zanje inga uban da ya tsaya masa,zan ɗanɗana masa kuɗar da bake kaɗai ba duk wata
mace idan tagansa bazata yi marmarin ƙara kallon sa ba"
"naroƙeƙa kada ka cutar da shi,duk abunda kace inyi zanyi amma kada kataɓa lafiyar
sa"
"wallahi zan rabu dashi amma kada ka cutar dashi dan Allah"
Juyowa yayi tare da sukuyowa yana yi mata wani kallo me cike da razanarwa
"na baki nan da kwana uku, ki yanke duk wata alaƙar dake tsakanin ki dashi idan
kuma kika ƙi........
Ya dakata da maganar yana yi mata gargaɗi da ya tsansa wanda saboda tsananin tashin
hankalin da ya shiga yike rawa
"wallahi zaki yi mamakina, dan ke tawa ce ni kaɗai babu wani mahalukin da ya isa ya
raɓeki, babu shi!!!!
"kada kiji tsorana Rauda, ni baiwar Allah ce me tsananin tsoron sa, bazan cutar
dake ba"
Rauda ta takure da bangon gadon har lokacin illahirin jikin ta rawa yike yi
"sunana ummu Salma,kuma ni aljana ce, abunda ya kawoni gurin ki kuma nazo in
taimake ki ne"
"taimako?
"na daɗe ina bibiyar rayuwarki, babu abunda bansani ba akan ki, tabbas rayuwar ki
tana cike da sarƙaƙiya da ruɗani,shiyasa nazo na taimaka miki
Duk da ni aljana ce bani da ƙarfin da zan iya karawa da rauhani, rauhanin ma kuma
Aasim bin ramzad wanda ya kasance ɗan sarkin rauhanai me ƙarfin gaske, nasan bani
da ƙarfin da zan iya karawa dashi amma ina da ɗan taimakon da zan iya baki da kuma
shawarwari waɗanda zasu amfane ki"
"a'a nagode da taimakon ki amma bana so wani abu ya same ki tunda kinyi niyyar
taimakona, Aasim yana da wani madubi da yike ganina dashi yanzu nasan yana ganki ya
na kuma jin duk abunda kike faɗa kiyi gaggawar barinnan dan Allah"
"kafinnazo nan saida nayi amfani da wannan turaren,a halin yanzu Aasim baya ganin
mu
Kuma wannan turaren shi nazo na baki, saboda nasan a duk sanda yanzu Aasim ya ganki
da Umar ze iyayi masa komai
Kuma ya kamata ki haɗu da Umar ki yi masa cikakken bayani, domin ya zauna da shiri
da kuma addu'o i
Sannan kusan mafitar da zaku ne ma,a duk sanda zaki haɗu da Umar Kisha fa wannan
turaren Aasim baze ganku ba, kuma inaso kuyi duk abunda zakuyi cikin gaggawa,
sannan kijuye turaren a man shafawanki da zarar zaki haɗu da Umar ki shafa"
"ni zan tafi, kiyi ƙoƙari ki haɗu da Umar a gobe tunda kinga kwana uku kaɗai Aasim
ya baki, sannan ki shafa idan zaki kira Umar ɗin, duk yadda kuka yi gobe zan dawo
inji, na barki lafiya"
Rauda tayi shuru bayan ummu Salma ta ɓace tana juya turaren a hannun ta
Tun bayan da suka yi waya yike kiran wayar ta yike jin a kashe
Ya shiga damuwa sosai,dan ko bacci ya kasa yi kuma har lokacin kuma trying ɗin
wayar yike yi amma still ba ta shiga
Ajiyar zuciya ya sauke, ya rasa ta yadda ze gane abunda take nufi, gashi tace kada
yake sai ta ne mesa, to me ke faruwa??
Miƙewa yayi ya ɗauro alwala, ya dinga nafiloli dan bayajin ze iya yin barci
*~Ƴarfillo~*.
[20/10, 8:43 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
2⃣ 7⃣ 2⃣7⃣
2⃣7⃣
AGE
*_Gaisuwa da jinjina ga umar ɗalha muna godiya da ƙoƙarin da kake yi a forum kai
da sis nabila allah ya bar zumunci_*
_8:09_🕒 PM
WED, JUL 10
Ya sani tun bayanzu ba tana tsananin ƙaunar Umar shiyasa ya sa ido sosai akan Umar
Me Umar yike dashi da yike ɗaukar hankalin ta? Ya zo mata asuffa me kyau dan yana
tunanin kyan da Umar yike dashi shine yasa ta ke sonsa
Amma sai gashi duk ƙoƙarin da yayi ganin karsu haɗu bayan tafiyar sa sun haɗu,
abunda dai yike gudu shiya faru
Washe gari,Anty ummi tazo Rauda ta sanar da ita duk abunda ya faru
"yanzu maza ki shafa turaren ki kira sa, dan abun bana zama bane karya je ya cutar
da ɗan mutane"
Rauda ta ɗauko turaren ta shafa sannan ta lalubo wayar ta, ta danna kiransa
Lokacin Umar yana zaune a office wata patient tana mai bayanin abunda ke damunta
Sam hankalin sa baya wurin, dan bejin abunda take cewa Sam
Zayyad da ke zaune ɗayan Ɓangaren Shima yana sauraren bayanin da patient ɗin dake
zaune gaban sa take masa
Ya lura da yanayin Umar Sam hankalin sa baya wurin da alamama ya Lula cikin tunani
ne
Ɗan buga tebur ɗin dake gaban sa yayi wanda ya dawo dashi daga duniyar da ya tafi
_chuchu_
"Rauda yanzu fisabilillahi abunda kika yi kin kyau ta kenan? Kin sa hankalina ya
tashi wallahi ko bacci ban iya yi ba"
" zan taho Kadunan, amma kafinnan faɗamin meke faruwa ne?
" to ya zanyi Anty ummi, ya zama dole infaɗa masa, idan yaji ze haƙura ba shikenan
ba,haka Allah ya ƙaddaromin"
Umar cikin sauri ya koma office, ko zama beyi ba ya fara tarkata takaddun dake
gaban sa
"train station kuma? Me zaka yi a can, kai da kake da patients ɗin da suke jiranka
a waje?
" zanje Kaduna ne, kuma banajin zan iya driving shiyasa zanbi train"
"Kaduna?
" wai ba shekaran jiya ka dawo daga kadunan ba, me kuma zaka je kayi?
"bangane me kuma zanje inyi ba, kasan dai hakanan bazan tsiri tafiya ba, batare da
dalili ba"
Zayyad ya ce
"Umar nifa kwata-kwata bangane maka ba, dan nasan ada sai kayi shekara ko watanni
batare da kaje Kaduna ba
Amma tunda kafara son Rauda shikenan kamai da Kaduna kamar nan da wuse
" to ba sai ka kaini asibitin mahaukata a duba ni ba, Kaga malan in zaka kaini ka
kaini, in kuma bazaka kaini ba nafita na tari taxi drop"
"a'a muje inkai ka,ƙila takai sunan ka gurin malamai ne shiyasa duk kabi ka susuce"
Ta zura hijabi, fuskar nan tata tayi fayau ga idanuwan ta da suka ƙanƙance saboda
kukan da tasha
Tana fitowa suka haɗa ido, gaban sa ne yafaɗi dan yana kallon ta ya gano tsantsar
damuwa atare da ita
Be ƙara cewa komai ba suka shiga ɗakin da ba komai a ciki sai kujeru guda biyu da
kafet
Ya tambaya
Ya girgiza kai
"a'a dan Allah ki zauna muyi magana, dan ganin ki a damuwa ya ƙara ɗaga min
hankali"
Ta zauna a kujerar dake kallon tasa,yayin da shi ya zuba mata ido yana sauraran
abunda zatace
"bansan ta inda zanfara faɗama bane Umar, ina tsoron yadda zaka fahimci abun, da
kuma hukuncin da zaka yanke idan na faɗama"
Daurewa tayi ta faɗa mai labarin Aasim da kuma halin da take ciki a halin yanzu
Doguwar ajiyar zuciya Umar yayi yana zame hannayen sa daga kan haɓarsa
"wallahi na zata wani babban al'amari ne, da nasan wannan maganar ce ma da ban tada
hankali na ba, duk ɗauka ta baba ne yace ya fasa bani ke"
Ki faɗa masa cewa neman ki yanzu nafara, alaƙa dake kuma yanzu nasa gaba"
"kinga Rauda, ki kwantar da hankalinki babu abunda ze faru,ni da zaki min wata
alfarma ma dakin amince munyi aurannan nan da wata ɗaya"
Zame hannun ta tayi tana jingina bayan ta da jikin kujerar dan ta san Be san waye
Aasim bane shiyasa yike faɗar haka
" Aasim ba kamar aljanun da ka sani bane, yana da matuƙar ƙarfi,kuma ze iya yin
komai akanmu"
"duk ƙarfin sa Allah ya fisa rauda, domin Allah shiya halicce mu ya kuma halicce
shi, ubangiji shike da iko akan duk kanmu, dan haka babu abunda ya isa ya mana
wanda Allah be yi mana ba, akwai wani babban malami da na sani zan faɗa masa nasan
ze iya ɗaukar mataki a kansa
Amma kicire fargaban cewa ze raba mu, dan wallahi babu wanda isa ya raba ni dake
sai Allah"
"ki yarda dani babu abunda ze faru da izinin Allah, abu ɗaya nike so dake kidage da
addu'a
Sannan ki kasance koda yaushe kina cikin alwala da kinji alamar sa kiyi addu'a
Kuma kada ki ƙara tanka masa, duk abunda ze ce miki kiyi banza dashi ya kasance
bakin ki ba abunda yike faɗi face ambaton Allah"
"yanzu zanje gida inyi wanka sai intafi zaria dan acan malamin yike,dama da mota
nazo da daganan na wuce, amma kinga sai naje gida na ɗauki mota"
"amma shekaran jiya ka koma, kuma yau na saka ka dawo, ka bar zuwa zarian sai gobe
kada ka gaji da yawa"
Ta faɗa
Ya amsa da amin yana yin gaba
"Umar!
*~Ƴarfillo~*
[20/10, 8:43 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
2⃣ 8⃣ 2⃣8⃣
2⃣8⃣
AGE
_7:38_🕒 PM
SUN,JUL 21
sai da ya watsa ruwa ya sauya kaya sannan ya fito hannun sa rik'e da makullin mota
"na hutar dake,nasan rakiyar bata tsakani da allah bace dan asaimiki waya ne"
"kai ya umar amma dai kasan ina raka ka ai ko ba maganar waya ko?
ya jinjina kai
"nadai hutar dake kibari anjima in na dawo sai muje in sai miki"
"kinsan bana son yawan magana ko?allah idan kika ban haushi zan fasa siyan wayar"
sai da suka idar sannan malan shitu ya tashi dasauri yana d'aukar darduman da yike
kai yace
"alhaji umar kaine da yamman nan tashi kan tabar man nan in shimfid'ama darduma"
"aa dan allah tashi alhaji umar tabarma ba wurin zaman ka bane,bare wannan tabarman
da ta yayyage"
"haba malan nida wataran cikin k'asa ma za a turbud'ani miye abun damuwa dan
nazauna kan wannan tabarman?
"shiyasa a kullum kake burgeni alhaji umar sam baka da girman kai irinna masu kud'i
ba ka nuna k'yamarka ga talakawa sam"
"gaskiya wannan al'amari akwai rikitarwa amma bari muyi isikhara mu gani"
"malan bazan iya hak'ura da ita ba,dan ina sonta fiye da yadda kake tunani idan da
mafita da kuma yadda za'ayi ayi kawai"
malan ya gyad'a kai yana kuma d'aukar carbin sannan yace
"dan mafita za asamu mafita da izinin allah amma fa za a sha gwagwarmaya sosai"
"malan ashirye nike da in fuskanci duk wata gwagwarmaya indai akanta ne,dan haka
karkaji komai indai akaina ne,kai dai kayi duk abunda kaga ya dace dan allah ga
wannan ayi duk sadakokin da za'ayi"
"insha allah zamuyi abunda zamu iya amma kaima fa sai kadage da addu'a
sosai,musamman inzaka kwanta allah ya shige mana gaba"
"amin"
"shikenan alhaji umar allah ya kiyaye hanya duk abunda ake ciki zankira ka in sanar
dakai insha allah"
bayan kwana uku,bata k'ara jin d'uriyar Aasim ba hakan yasa taji tad'an rage
fargaba dan umar be koma abuja ba kullum sai yazo ya kwantar mata da hankali
yauma suna tare ya d'auko wata leda ya bud'e wacce malan shitu ya aiko mai dashi
ya d'auko wasu turaruka da wani mai a wata kwalba ya mik'o mata yana fad'in
"d'azu malan shitu ya aiko dasu yace kifara amfani dasu a yau........
dagatawa yayi yana kallon yadda ta toshe hanci dan yana bud'e ledar taji wani mugun
wari ya bugi hancin ta
"wari kuma?
ta d'aga kai tana k'ara toshe hancin dan ji take warin na kuma k'aruwa
"eh mana,kinsani muna cikin matsala amma kuma na kawo magani kina toshe hanci"
"inshafa fa kace"
ya d'aga kai
"Rauda nasan bazaki ji dad'in amfani da magungunan nanba sam,amma ya zama dole ki
daure ki duba damuwar da nike ciki dan allah "
ta amsa
"kinga wannan idan zaki kwanta zaki shafa,wannan kuma da rana sai wannan hayak'i
ne.........
"lafiya chuchu?
ya tambaya,ta bud'e idanuwanta da suka fara yi mata nawi saboda sarawar da kanta ya
fara yi mata
"sannu ze dena kinji,kiyi hak'uri dama malan yace dole zakiji haka"
kad'a kai kawai tayi tana bud'e turaren ta shafa a goshinta kamar yadda yace
wani kalan nawi taji goshin ya mata kamar an d'aura mata dutse
"umar!
katse ta yayi
"kada ki k'ara fad'in haka,insha allahu zamu yi nasara"
"please rauda kiyimin alk'awarin duk rashin dad'in maganinnan zaki daure kiyi"
guntun murmushi yayi yana shafa sumar kansa had'i da kallon ummu salma wacce ya
d'aure da wasu mugayen igiyoyi
"tabbas kin tafka kuskure da kikai tunanin wani k'aramin alhakin turaren ki zeyi
tasiri akaina,kin manta waye Aasim ne amma zan tunatar dake yanzu"
"ka gafarceni ranka shidad'e kayi min afuwa nasan nayi kuskure ka yafeni dan allah"
hannunsa ya sa yayi nuni da ita sai ga wani haske ya fito ya caki k'irjinta
"zaki kasance a haka har tsawon kwana bakwai,kinga gobe bazaki sake tunanin shiga
gona ta ba"
gurin rauda ya nufa kai tsaye lokacin ta shiga gida dan umar aranar yike so ya koma
abuja
tana zaune tana k'ok'orin shafa turarukan da maganin taji tsayuwar sa agabanta
runtse idanuwanta tayi dasauri tana karanto duk wasu addu'o i da suka zo bakinta
zaunawa yayi kusa da ita yana amsar turaren hannunta yana juyawa
"kinyi shuru ko baki so intayaki ne?ba rabuwa kikeso kiyi dani ba ince wannan.shine
maganin da akace miki ze rabaki dani?
har lokacin addu a kawai take karantowa kamar yadda umar yace tarink'a yi aduk
sanda yazo
*~y'arfillo~*
[20/10, 8:44 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
2⃣ 9⃣ 2⃣9⃣
2⃣9⃣
AGE
_2:28_🕒 PM
MON,JUL 22
"wato da nabaki lokaci ki yanke duk alak'ar dake tsakaninku shine kike neman ma
rabuwa dani ko?
wallahi kinbani mamaki bantab'a tunanin haka daga gareki ba,na d'auki amana.da
yardata na baki amma a k'arshe ni zaki watsa wa wa k'asa a ido"
hmmmm ya k'arasa fad'a yana sauke numfashi sannan ya cigaba da cewa
"Rauda kisani bazan tab'a rabuwa dake ba,kuma bazan tab'a bari wani namiji ya
rab'eki ba,kada ma ki wahalar da kanki wajen yin maganin da ze wahalar dake domin
banga maganin da zeyi shamaki atsakanina dake ba,
sannan kisani kina d'auke da cikina a tare dake dan haka kibi ahankali wajen yin
amfani da wasu magungunan da zasu iya cutar min da yaro ina fatan kingane?
"nashiga uku!
ta fad'a tana duban cikin,wasu hawayen tashin hankali suka fara biyo kuncinta
washegari umar na zaune a office bayan yagama duba iya adadin patient d'in da yace
ze duba
kulle office d'in dan yana buk'atar ya huta sakamakon rashin baccin da bayayi kwana
biyu dan duk dare tashi yike yi yay ta kai kukansa ga ubangiji akan wannan matsalar
d'agowa yayi ze aje wayar karaf idonshi yayi gamo da Aasim wanda ke zaune a kujerar
dake gaban tasa
kallonsa umar yayi da mamaki dan shi sam beji shigowar mutum ba hasali ma k'ofar
office d'in a rufe take to ta ina ya shigo?
"kamata yayi kafara tambayar waye ni,kafin ka tambayi abunda nazo dashi"
umar ya kallesa da sauri mamaki k'arara a fuskar sa,amma ko kad'an beji wani tsoro
ba
"nazone inyi maka gargad'i cikin lalama,ka rabu da matata dan zan iyayin komai
akanta"
"naji dad'in zuwanka da kuma yadda kazomin cikin salama,hakan ya tabbatar min da
kana da sauk'in kai
amma ina so kasani bazan iya rabuwa da rauda ba domin inason ta fiye da yadda kake
tunani"
"ba damuwa ta bane yawan son da kake mata,dannasan babu wanda zeso rauda fiye
dani aduniya,inaso karabu da ita ayau ba sai gobe ba"
"shikenan ni zan rabaka da ita dole,kashirya ma shiga tashin hankali kasa aranka
cewa daga yau kun k'ulla abota da damuwa"
yasa handkerchif ya share gumin da yafara tsattsafo masa tabbas wannan abun bana
zama bane
"gaskiya al'amarinnan me girma ne,amma ina ganin zanje gurin wani kakana gobe dan
yana da lak'anin da yafi nawa inyaso sai muji abunda zece shi"
umar yace
"shikenan malan dan allah ka k'ok'arta"
haka suka cigaba da gwagwarmaya,har na tsawon wata d'aya amma babu canji
inbanda wahala ma babu abunda rauda kesha,dan arana sai tayi suma fin biyar
rauda ta rame sosai,dan ita kad'ai tasan azabar da take sha dan Aasim yace muddin
bata rabu da umar ba to bazata samu sassauci ba
b'angaren umar ma kullum cikin kawo masa farmaki akeyi,amma da yike jarumi ne shi
kuma yana tsaye da addu'o i shiyasa shi nashi ya zo dasauk'i
duk inda sukaji wani malami sai sunje amma a banza,dan babu abunda yike canzawa
ranar wata alhamis umar yazo,kai tsaye yayi sallama yashigo falon mama dan yanzu ba
maganar fita waje
da ta tashi zata fita zata zube,hakan yasa dole inyazo yike shigowa ciki
mama ta amsa da
"da dauk'i,d'azu dama nike niyyar nace a kira ka,wata k'anwar babansu tace akwai
wani malami acan k'auyen yola kuma yanayin irin wannan aikin ana dacewa"
umar yace
"to mama ai babu matsala,yaushe kike ganin ya kamata atafi"
"zuwa lahadi"
"amma saidai kabari muje ko,kai ka huta dan.zirga-zirgan da kakeyi tayi yawa"
mama tace
mama ta sauke numfashi,ta d'auko darduma ta shimfid'a mai a gefe sannan ta dawo
falon tace
amsawa yayi da to,ya mik'e cikin ladabi ya shiga uwadd'akan yana sallama
"da sauk'i"
ji tayi idanuwanta sun cicciko da hawaye tayi k'ok'arin shanye su amma takasa sai
da zubo
"ni banason ganin hawaye a fuskarki yana k'ara tada min da hankali,dan allah
kibari"
"tun safe nike fama da ita tak'i cin komai,k'ila kai idan ka tursasata zata ci"
*~y'arfillo~*.
[20/10, 8:44 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
3⃣ 0⃣ 3⃣0⃣
3⃣0⃣
AGE
_5:13_🕒 PM
MON,JUL 22
dan bazata iya yi mai musu bane kawai yasa ta amsa tafara ci amma zahiri ji take
kamar tana cin magani
kad'an taci ta ajiye plate d'in tare da komawa ta kwanta tana kuma jan bargon
yana yi ne kawai dan ta janye a kan k'udurinta amma gashi har lokacin bata da
alamar janyewa
a hanakali ya furta
ina sonki,ina k'aunar ki bazan iya jurar ganin ki cikin wannan halin ba,ba zan iya
ba habibty"
kwantawa yayi kusa da ita ya rungumeta ta baya tare da sauke wani numfashi me nawi
tabbas rauda itace farin cikin rayuwar sa,taya ze bari wani ya rab'e ta
lumshe idanuwansa yayi wad'anda suka rine saboda tsananin damuwar da yike ciki
"please Rauda kada ki gujeni,bazan iya rayuwa idan babu ke ba,ki.kasance tare dani
dan allah"
washegari umar ya shirya komai na tafiya yola driver ya samu wanda ze kaisu ya
dawo dasu
ranar asabar dawuri suka tafi dan tara dai-dai suka fita
tafiyar awa hud'u sukayi suka isa yola,wani restaurant suka fara tsayawa
mama can gefe suka zauna aka kawo musu abinci yayinda umar da rauda ma suka zauna
daga can gefe
duka su biyun tsakurar abincin suke yi dan sam basa jin wata yunwa
"wallahi nima haka,abincin ma babu dad'i ko na nemo mana abu me ruwa ne?
ta jinjina kai
"amma kafinnan inaso ind'an shiga bayi"
wata ma'ai kaciyar wurin ya kira yace ta nuna mata bayin shi kuma ya tafi inda ake
saida drinks
Rauda ta tura k'ofar bayin ta shiga cikin y'an mintoci tagama abunda zatayi
motsi taji a bayanta ta waiga da sauri amma bata iya ganin komai dan bayin yayi
duhu dund'um
umar tunda ya dawo wurin yike duba agogon wayar sa,ganin anfara kiran sallar
magriba gashi har lokacin bata fito ba
mama tace
"bari naje bayin nace mata tayi sauri,nima bana son tafiyar dare wallahi"
nuni tayi mata da hanyar bayin,mama ta k'arasa wurin bayuka uku ne,biyu a bud'e
alamar babu kowa aciki
babu kowa a cikin bayin,ta dawo baya kad'an tana nazarin ko akwai wani bayin awurin
amma da alamu bayukan kenan
mama tace
"yarinya ce tace zata zaga tund'azu to munji ta shuru shine nai tunanin ko banan ta
shiga ba,dan na duba bayukan banganta aciki ba"
"to saidai in wani wurin tayi,danni dakaina na rakata har k'ofar bayin amma muje
wurin bayin nagani"
d'ayar tafad'a,komawa ko sukayi sai dai babu alamunta,hankalin mama yafara tashi
mama tace
"to ai da tanan dai zata wuce tunda naga wurin sallar nasu a waje yike"
"bari naduba waje to ku k'ara duba cikin ko da tafito bamu lura bane"
babu inda ba a duba ba awurin ba alamar Rauda ba hankalin su mama kad'ai ba har na
ma'aikatan.wurin sai da ya tashi
A hankali tafara bud'e idanuwanta,harta bud'esu gabad'aya slip d'akin tafara kallo
daga bisani ta saukar dasu k'asa
kan wani k'asaitaccen gado ta ganta,mamakine ya kamata ita da take bayi ya akai
taganta a kan gado
wata k'ofa tagani,ta diro daga kan gadon dasauri ta nufi k'ofar
Aasim ta hango tsaye yana jera abinci kala-kala akan wani had'add'en dining table
"barka da tashi habibty"
kallonsa kawai take yi amma takasa furta komai,ya k'arasa inda take ya tsaya gab da
ita had'i da d'aura hannun sa akan wuyanta
"zazzab'in jikinki ya sauka ko? nasan kina jin yunwa me kikeso kifara ci"
"ina ne?tambaya kike yi?to gidana ne gidanki kuma inda zakiyi rayuwa ta har abada"
fizge hannun tayi tana durk'ushewa k'asa tare da had'e hannayenta wuri d'aya
"narok'eka ka maidani inda ka d'auko ni,kabar ni nayi rayuwa da wanda nike so"
murmushin takaici yayi yana cigaba da tafiya ya zauna kan wata kujera yana kallonta
kawai
"umar shine zab'ina kataimakeni ka rabu dani,kaje kasamu jinsinka dan allah"
tasowa yayi ya dawo gabanta ya durk'usa yana kallonta da idanuwansa da suka fara
rinewa
"Rauda!"
"to kisani wallahi tallahi babu abunda zesa inrabu dake,rayuwa dake yanzu nafara"
mik'ewa tayi ta nufi k'ofar da ya nuna mata,ta murd'a dajine sosai me dogayen
bishiyoyi
*~y'arfillo.~*
[20/10, 8:44 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
3⃣ 1⃣ 3⃣1⃣
3⃣1⃣
AGE
_wannan page nakine *karima keffi*,ina godiya da k'aunarki gareni allah ya bar
zumunci_💛💛
_3:07_🕒 PM
THU,AUG 1
dajine sosai me dogayen bishiyoyi inbanda kukan tsintsaye babu abunda take iya
juyowa
umar ko na can hankalinsa inyayi dubu ya tashi har jami'an tsaro aka kira aka had'u
dasu aka cigaba da nemanta amma shuru
yace su ma dena bawa kansu wahala dan ba mutum ne ya d'auke ta ba suk'arasa k'auyen
kawai
tafi k'arfin awa biyu durk'ushe awurin gabad'aya k'wa-k'walwarta nema takeyi ta
dena aiki,ganinta takeyi wani iri takasa gasgata cewa rayuwar da take yi da gaskene
ta sauke doguwar ajiyar zuciya tana kallon sararin samaniya da taurari sukamasa ado
a hankali ta furta
"ya allah ka taimakeni kafitar dani daga wannan rayuwar"
Aasim yana tsaye yana kallonta gabad'aya jin zuciyar sa yike yi babu dad'i sam baya
so ya ganta cikin damuwa
"ina k'aunarki kece farin ciki na,dan allah ki rayu dani ni kad'ai nayi miki
alk'awari zansaki farin cikin da babu wata mahalukiya da zata fiki jin dad'i a
duniya"
"miye umar yike dashi wanda bana dashi?ki fad'amin kisani ayanzu babu siffar bazan
iya yi ba,zan iya yin komai domin insaki farin ciki..........
"inbari inga kina rayuwa da wani a matsayin miji? bazan iya ba"
"kinsan zafin da nike ji a duk sanda naga umar tare dake? kisani zan iya mutuwa a
duk ranar da wani mahakuli ya kusance ki,dan haka ki ajiye maganar aure arayuwar ki
dan bazan tab'a amincewa ba"
jinjina kai tayi cikin tsananin damuwa,tasa hannu ta share fuskarta tana fad'in
"shikenan Aasim nasan bani da ikon saka ko hanaka,kayi duk abunda kayi niyya kada
kabari wani ya rab'eni
amma kasani gangar jikina ce kad'ai zaka cigaba da rayuwa da ita dan zuciyata tana
ga umar,ayanzu shine mallakinta.......
runtse idanuwansa yayi dasauri dan jin maganarta yayi kamar wani mashi ya cake sa
"duk abunda zaki ce sai dai kice,amma bazan tab'a lamuncewa da wani ya rab'eki ba"
ta janye jikinta kad'a kai
"shikenan,kayi yadda kake so dani,nasan allah yana tare dani kuma nasan wata rana
zeyi min maganin komai"
addu'o yike karantowa sosai,cikin ikon allah saiga Rauda ta bayyana aciki lokacin
tana zaune ta d'aura kanta bisa gwiwowinta
"tabbas inda take ba k'aramin wuri bane,kuma ba k'aramin nisa yike dashi ba,nasan
ayanzu idan ni na kirata zataji tsoro saboda bata san muryata ba,dan.haka kai umar
matso kusa da k'waryar ka kira sunanta da k'arfi"
"Rauda!!
d'ago kanta tayi da sauri jin ankirata da kuma muryar umar,sai kuma ta sauke ajiyar
zuciya tana maida kanta dan tasan ba dai-dai kunnenta yajiba
"bazaki iya ganinsa ba amma mu muna ganinki,muna so muyi komai cikin gaggawa kafin
Aasim ya dawo dan.haka ki natsu kiji abunda zan.fad'amiki"
jinjina kai tayi dasauri
"fad'i inaji"
"a yanzu rafanan da nike dasu bazasu iya shigowa inda kike ba,dan haka dole kifito
daga cikin wannan gidan kiyi tafiya zuwa inda wata bishiya take"
d'aga k'afar tayi dasauri jin ta taka wasu k'ayoyi masu zafin gaske tare da sakin
wata y'ar k'ara
takawar tafara yi tana runtse idanuwanta saboda tsananin azabar datake ji a tafun
k'afafun nata
ko rabin wurin bishiyar bata kaiba ta tsaya tana girgiza kai hawaye masu zafi na
biyo kumatunta
"Rauda ki daure dan allah,kinji malan yace wannan ce kad'ai damar da muke da ita"
umar ganin ya dena ganinta cikin k'waryar yasa hankalin sa ya k'ara tashi
"ya naga nadena ganintame ya faru kuma"
"malan umar bamu.da lokaci dan na tabbata Aasim na iya zuwa ayanzu,dan haka dole mu
shirya cikin gaggawa"
mama ta tallabota ta bata tatasha,aiko tana sha taji cikinta yafara wani irin
hautsinewa
Aasim yana tsaye cikin katafariyar kasuwar su,tunani yike me ze siya ya kaimata
wanda ze sa ta farin ciki
ya k'arasa fad'a idanuwansa na sauka akan wasu sari had'e da wasu gwala gwalai masu
masifar kyau
*~y'arfillo~*.
[20/10, 8:45 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
3⃣ 2⃣ 3⃣2⃣
3⃣2⃣
AGE
_wannan page nakine *fatima batula*,na sadaukar dashi gareki kiyi yadda kike so
dashi_
_12:04_🕒 PM
FRI,AUG 2
cikin tsananin b'acin rai da tashin hankali ya bayyana a gidan malan isa
kai tsaye ya danna kai ze shiga d'akin da suke amma wani turari me zafin gaske yasa
yayo baya da sauri
kallon d'akin yafara yi da wani irin mugun wari ke fitowa daga cikinsa
ya kutsa kai cikin d'akin yana runtse idanunsa dan ji yayi wani zafi ya ratsasa
kamar wuta
gabad'ayan su addu'a suke karantowa,banda Rauda da tayi lamo jikin mama tana jin
k'wak'walwar ta kamar zata juye
nafad'amiki cewa da akwai d'ana a jikin ki,meyasa zaki biye musu kisha wannan
bak'in rubutun?
ya tambaya cikin fusata,ta kasa bashi amsa inbanda lumshewa babu abunda idanuwanta
suke yi
maida idanunsa yayi kan malan isa da har lokacin yike ta kwararo addu'o
"narantse da allah idan har kayi sanadiyyar rasa d'ana sai ka d'an-d'ani kud'arka"
malan isa ya sauke numfashi dan sai lokacin hankalinsa ya kwanta da yaga yayi
nasarar kama sa
"duk zaune,ku kuma natsu,ina fatan yanzu zaka tsaya muyi magana ta fahimta"
Aasim kallon Rauda kawai yike yi,yana jin zuciyarsa nayi masa wani irin rawa
"kada ma ka b'ata bakinka gurin fad'in inrabu da ita dan bazan tab'a rabuwa da ita
ba har abada"
Aasim yace
"wannan ba damuwar ka bace,ita nagani na zab'a da kuma ita kad'ai zanyi rayuwa"
"to ina had'aka da allah,da ka furta ka rabu da ita ka kuma yi alk'awarin bazaka
sake rab'arta ba"
"shikenan idan ba zaka rabu da ita dan allah ba,zamu rabaka da ita da ikonsa insha
allahu"
ya k'arasa fad'a yana d'auko wata k'warya da ya cikata da rubutu da ruwan addu'a
wani irin k'ara Aasim yayi cikin gigita ya kallesa da mamakin wani irin abu ya sa
acikin k'waryar da har yayi tasiri ajikinsa
"kada kayi tunanin zaka tab'a jin kalamar rabuwa da ita a bakina,kasani duk abunda
zakayi sai dai kayi"
malan isa ya jinjina kai yana kuma d'ina ya k'ara watsa masa,ze kuma watsa mai
"kisani wannan zafin da nike ji be kai zafin da nike ji acikin zuciya ta ba,na cewa
kinzab'i rabuwa dani,ki barshi ya cigaba da aikinsa"
yasha matuk'ar wahala gabad'aya jikinsa ya wani irin kwakkwailewa kamar an watsa
masa ruwan zafi
saida ruwan addu'ar ya k'are gabad'aya sannan malan isa ya koma ya zauna yana
mamakin kafiya irin na Aasim
"kinyi farin ciki ko habibty?haka dama kike so ko,da kinsan bazakiyi rayuwa dani ba
da baki amince min ba tuntuni,ki kasa na k'ara shiga duniyar k'aunarki amma yanzu
zaki juya min baya ko?
tabbas mahaifina yayi gaskiya da yace nayi babban kuskure da na baki yardata,amma
ina so kisani bazan tab'a rabuwa dake ba duk da kin butulce min domin kece zab'in
zuciyata"
"kayi hak'uri Aasim,bada son raina bane amma umar shine farincikina kayi hak'uri
kabarni na rayu dashi amatsayin mijina,ka amsa ka rabu dani bazan iya jurar ganin
ka cikin wannan halin ba"
"nasan bazaki tab'a ganewa ba,bazaki tab'a gane irin k'aunar da nike miki ba,dan da
ace kinsan ko da rabin.k'aunar danike miki ne dake kanki baki zab'i ki rabu dani
ba,amma babu komai"
kuma fashewa tayi da kuka,tana jin zuciyar ta na yima ta wani irin ciwo
"idan har baka amince ka rabu da ita ba,zan saka.cikin kwalbar nan ka k'arake
rayuwar ka acikin ta,dan haka gaggauta yin abun da nace"
mama ta kama hannun ta,k'wace hannun tayi tana k'ara sawa gabansa
tana turjewa mama da goggo hanne suna janta ahaka suka fita da ita
ahankali tagama bud'e idanunta ta sauke su akan umar da ke zaune kan kujerar dake
gaban gadon
yunk'urawa tayi ta tashi,tana jin jikinta yayi mata sakayau kamar ancire.mata wani
abu me nawi
ta girgiza kai dan ji take kamar tafara wata sabuwar rayuwa,gaba d'aya jikinta babu
inda ke mata ciwo
"ba ko ina,yaushe aka kawoni.asibiti"
"kwana uku?
"me ya faru?
ji tayi zuciyarta tayi mata wani iri,gaba d'aya saitaji babu dad'i
*~y'arfillo~*.
[20/10, 8:45 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
3⃣ 3⃣ 3⃣3⃣
3⃣3⃣
AGE
_Ina bawa masoyana haƙuri abisa jina shuru da su kayi, na san wasu daga ciki sun
fara manta labarin amma na san akwai waɗanda har yanzu suke zaman jirana kamar_
*_Karima, fati s noma, ummu kaltum, safnah, aisha babayo_*
_Ina matuƙar jin daɗin yadda kuka dinga kirana musamman *Karima* , da bata cikakken
sati biyu sai ta kira tana faɗin a turo musu uncle *Aasim*_
_Dan haka wannan Page ɗin nakine *Karima* Allah yabar ƙauna_
_9:13_🕒PM
WED, SEP 25
Jingina tayi da filo tana lumshe idanuwan ta A hankali batare da ta bashi amsa ba
Ta buɗe idanuwan ta A hankali ta ɗaura su a kansa cikin wani irin yanayi na damuwa
"Sam ban kyauta masa ba, na zama me son kaina da kuma son zuciya ta, ya rabu da
komai nasa, ya sha baƙar wahala duk a kaina amma be damu ba kullum burinsa ya zeyi
ya rayu dani ya kuma sani farin ciki"
"dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki manta da komai kisa wa ranki kamar rayuwar
da kika yi da Aasim mafarki ce kinji farin cikina?
"abune da baze yuwu ba Jaana bazan taɓa iya manta wa da Aasim ba, bawan Allah ne me
haƙuri da tsananin ƙaunata"
Umar ne ya amsa
Bayan kwana biyu taji sauƙi sosai aka bata sallama suka dawo Kaduna
Ta zama shuru-shuru dan Sam bata son Magana dan koda suka koma gida ɗaki ta shiga
ta kwanta
Zuwan da Umar yike yi akai-akai shine yasa taɗan fara sake wa harta fara mantawa da
Abunda ya faru
_Idan masu karatu basu manta ba a baya mun tsaya ne a inda Rauda ta tafi dogon
tunani tunda kan haɗuwar ta da Aasim da rayuwar da tayi dashi bayan irin wahalar da
yike basu ita da Umar da kuma ruwan gubar da Aasim ya sa ma umar a asibiti a
lokacin da ya bayyana da fuskar zayyad,kuma yace ma karin wannan gubar shine idan
umar ya furta ya saki Rauda amma muddin yaƙi sakinta to duk kwanan duniya ruwan
gubar na ƙara shiga cikin jikin sa_
Umar ya tashi da ƙyar daga kujerar da yike ya dawo kusa da ita ya zauna tare da
kiran sunan ta
"Rauda"
"kisani ina sonki kuma a shirye nike dan in fuskanci ko wace irin ƙalubale akanki,
ki kwantar da hankalin ki kisawa ranki cewa duk runtsi duk wuya ina tare dake bazan
taɓa guje miki ba"
"ina zamu samu mafita, a ina zamu samu ma karin wannan gubar dake jikin ka? Lafiyar
ka tafi min komai Jaana bazan iya jurar ganin ka cikin wannan halin ba na san
kanajin jiki daurewa kawai kake yi dan kar hankalina ya ƙara tashi"
Umar ya sauke gauron numfashi, yana runtse idanuwan sa dan ji yike yi kamar ana
dafa naman jikin sa sabo da tsananin zafin da yike ji
Sai da yaɗanji jikin ya lafa masa sannan ya fara magana da muryar sa da tayi sanyi
ƙalau
"zamu samu makari chuchu, kisani babu abunda yafi ƙarfin Allah kuma yana sane damu
mu cigaba da kai kukan mu garesa na tabbata ze yi mana maganin komai"
Rauda ko ta kasa baccin kallon kyakkyawar fuskar sa kawai take yi da tayi mugun
faɗawa kamar wanda yayi wata yana jinya
Ta matso ta kama hannun sa, saurin sakin hannun tayi dan ji tayi zafi rau
Hankalin ta ya tashi sosai dan tana jin hucin da yike fitowa daga jikin sa
Waigawa tayi bata ga komai ba taci gaba da tafiya still tana jin sawun tafiyan a
bayan ta
Wani irin ihu ta ƙwala sakamakon ganin wani mutum zarƙameme me dogon ƙaho,baya ta
fara yi da sauri yayin da ya cigaba da tahowa yana dariya da wata kalar murya me
tsoratar wa
Ƙundun bala ta fara yi daga kan step ɗin har zuwa ƙasa
Goshinta ya bugu da bango, ta ƙara yin wata ƙara tare da dafa goshin wanda ya fara
zubar da jini
Ta ɗago kai tana kallon step ɗin amma wurin wayam babu kowa
Ƙarasawa wurin fridge ɗin tayi tana waige-waigen inda zata sake ganin abunda ta
gani
Ahaka ta buɗe fridge ɗin, tayi baya da sauri dan amemakon taga ruwa da drinks ɗin
dake ciki wasu kalar macizai ta gani sun dunƙule wuri ɗaya
Babu inda baya rawa a jikin ta, ƙarar sawun tafiya taji daga wurin kicin tayi
saurin juyawa
Zuwa can taji shuru, bakinta be dena furta addu'an ba ta buɗe idanun tana wawware
su
Amma babu kowa a wurin, ta kalli fridge ɗin Shima babu macizan
Da sauri ta ɗauki goron ruwa da ƙanƙara ta haye sama da sauri har tana cin tuntuɓe
Basai ya tambaye ta abunda ya faru ba, dan ya san wani abu me tsoratar wa ta gani
Ya kamo hannun ta ya zaunar da ita kusa dashi yana tsurawa kyakkyawar fuskar ta ido
Amsar ruwan yayi ya sha, sannan ya yunƙura da ƙyar ya ɗauko wani ƙaramin akwati
wanda kayan taimakon gaggawa suke ciki
Ya dawo ya zauna ya fara goge mata jinin, ya gyara mata wurin sannan ya rufe
akwatin ya aje a gefe
Hawaye ne kawai ke bin fuskar ta,a hankali yike jin ɗigar hawayen a jikin sa
" kukan ki ƙara tada min hankali yike yi, kidena kinji"
"dan Allah Jaana kada kace zaka hanani kuka, wannan kukan shine yike rage min ciwon
da nike ji acikin zuciya ta bazan iya dena yin shi ba"
Tashi tayi suka nufi ba yin, tsayawa tayi ya fara yi sannan itama tayi
Washegari da safe ita ta fara tashi,ta sauko ta shiga kicin ruwan zafi kawai ta
ɗaura, dan bata jin zata iya yin abun kari me wahala
Adurƙushe tagansa bakin gado yana ta kakari, jijiyoyin wuyan sa sun mummurɗe
idanuwansa sun canza launi zuwa jawur
Yafi minti goma a haka, da ƙyar ya samu ya amayo wani dunƙulen jini
Gyara wurin tayi, ta taimaka masa yayi wanka sannan ya koma ya kwanta
"ina zakije?
Ta faɗa
"a'a banajin zan iya cin wani abu, ki zauna tare dani kawai"
Ta sa hannu tana share fuskar ta dan har lokacin ta kasa tsaida hawayen dake ta
ambaliya a fuskar ta
"bazeyuwu ka zauna ba ka karya ba, kabari in kawo maka"
Ta sauke numfashi tana kaɗa kai, tare da fuskantar sa sosai tana matse hannun sa
dake cikin nata
"kayi haƙuri da abunda zan faɗa Jaana, nasani bazaka ji daɗin sa ba Sam, amma inaso
ka sani Nima ba dan inaso bane illah itace kaɗai mafitar mu a yanzu"
"dan Allah inaso ka sake ni, bazan iya jurar ganin ka cikin wannan halin ba......
"yanzu kenan da Ace nine Nike da matsalar ki, rabuwa dani zaki yi kenan ko"?
Ta girgiza kai
Umar yace
"eh mana, kisani babu abunda zesa inrabu dake wallahi ko da zan mutu ne kuwa"
"idan har akan wannan maganar ce, bana son in ƙara jin komai"
Jikinta a sanyaye ta baro ɗakin, kan kujera ta zauna tana jin zuciyar ta nayi mata
nawi
Wayar ta ta ɗauko ta kira anty ummi tabata labarin komai sannan ta ƙara da cewa
"anty ummi ina cikin tashin hankali idan na rasa umar ban san ya rayuwa zata
kasance ba, bansan ya zanyi ba"
Daga can ɓangaren anty ummi ta sauke gauron numfashi cike da al ajabi tace
"tabbas kina cikin tashin hankali Rauda, Allah ne kaɗai ze iya fitar daku, ina
ganin ki nemi Aasim ɗin ki roƙesa tunda yana sonki ƙilan y tausaya ya cire mai
gubar"
Kaɗa kai kawai tayi ta kashe wayar, ta san Aasim baze taɓa saurararta ba
Yayi kyau sosai, farin sa ya ƙara ƙaruwa dan har ɗaukar idanu yike
Da murmushi ya amsa sallamar yana shafa baƙin sajen da ya zagaye fuskar sa wanda ya
kwanta luf
Dan jin zuciyar sa yike cikin farin ciki ganin ta fara neman saki a gurin umar
*yarfillo.*
[20/10, 8:46 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
3⃣ 4⃣ 3⃣4⃣
3⃣4⃣
AGE
*YAN UWA MUNA KARA KIRA DA MABIYA LITTAFAN GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION DA SU
KIYAYE DA WANNAN MAI CUTAR TASU DA SUNAN YANA SAIDA LITTAFAN KUNGIYARMU,TO KARYA
YAKE MACUCI NE KAWAI LITTAFANMU IS FREE 1 NE KAWAI NA KUDI,KUMA DA YACE YANA BA
KUNGIYARMU KUDIN REGISTER DIN DA KUKE BIYA DOMIN MU TURA MASHI SABBIN LITTAFAN
MU,TO WALLAHI DUK KARYA YAKE MANA MU BAMU DA MASANIYA AKAN WANNAN B'ARNAR DA YAKE
MANA SAI DAGA BAYA MUKA JI,SANNAN KUMA INA SON KUSAN NUMBER DIN SHI SABODA YANA NAN
YANA SHIGA GROUPS NA MATA DA SUNAN MACE SABODA HAKA KU KIYAYE GA NUMBER DIN SHI NAN
(08107707692)*
_5:36_🕒 PM
SUN, SEP 29
"Ashe so kan juye ya koma ƙiyayya Aasim? yanzu farin ciki kake yi da wahalar da
nike sha ko?
Ta ɗan tsaya ta share hawayen da suka gangaro mata sannan ta ci gaba da cewa
"bantaɓa tunanin cewa zaka iya cutar dani ba, amma kaduba kagani...
" sanadin tsoratarwar dakasa ake mini, ka hana zuciya ta sukuni ka hanamin
kwanciyar hankali,shin kana ganin Hakan da kake yi dai-dai ne kenan?
Aasim yayi ɗan murmushi,a hankali ya taso daga kujerar da yike ya dawo gabanta ya
durƙusa
"habibty banzo nan dan inji waɗannan bayanan daga wurin ki ba, koma menene ai ke
kika jawo ma kanki, kifaɗamin abunda yasa kika kirani kai tsaye"
"dan Allah ba dan ni ba, katausaya mana ka cire gubar da kasa ma mijina ina
tsananin tausayin sa bazan iya jurar ganin sa cikin wannan halin ba"
Wani irin mugun kallo ya yi mata dan shi a duniya bashi da wanda ya tsana sama da
umar, take murmushin dake fuskar sa ya ɗauke
Ganin irin kallon da yike mata yasa ta ƙara durƙushewa tana haɗe hannayen ta guri
ɗaya
" kinga kada ma ki wahalar da kanki wurin roƙona dan bazan taɓa lamunce ma buƙatar
ki ba, nafaɗamiki ma karin gubar ai kije ki tirsasa shi ya sake ki shi kenan ze
warke ze samu lafiya"
Tayi shuru tana cigaba da kallon sa,wasu siraran hawaye na kuma biyo kuncin ta
Aasim ya sauke numfashi, dan yana tsananin jin zafi idan yaga tana zubar da hawaye
Ya rasa irin wannan ƙauna da yike mata, da ace ze iya da ya yi mata abunda take so,
amma baze iya ba
"ya isa haka to, akwai wata mafita guda ɗaya, kuma ita kaɗai ce alfarmar da zan iya
yi miki"
"na san ba lallai bane ki amince da wannan alfarmar da zan iya yi miki, duk da na
san kina son lafiyar mijin ki amma na san da wuya ta yi miki"
Rauda ta girgiza kai a hankali tace
Ya faɗa yana shafa gefen sa wata ƴar ƙaramar wuƙa ta bayyana, ya riƙe yana miƙa
mata
"idan har kika caki saitin zuciyar sa da wannan wuƙar to ya riga da ya warke ya
gama"
"kana nufin inkashe sa kenan?to bazan iya ba, idan har Hakan shine burinka Kaga
bayan sa a doron ƙasa to burinka baze taɓa cika ba Insha Allahu"
"kinji nace miki ki kashe sa ne? Sam ni faɗa miki haka ba, wannan wuƙar ba abunda
zata masa face fitar da gubar dake jikin sa kuma daga lokacin ze dawo lafiya kamar
be taɓa yin wani ciwo ba a rayuwar sa, dan bana ce ki zurma mai wuƙar bane a'a ko
yaya idan taɗan huda jikin sa jini ya fita shi kenan "
Shuru tayi tana cigaba da yi masa wani irin kallo me cike da rashin yadda
" sanin kanki ne ban taɓa yi miki ƙarya ba, kuma ni rauhani ne ba mutum ba, bana
saɓa alƙawari kamar yadda ku mutane ku keyi"
Tabbas ta san be taɓa mata ƙarya ba, amma ta san a yanzu ze iya yin komai, amma
abunda take tantama a ranta Shine meyasa ze bata ma karin gubar cikin sauƙi anya ba
wani abu ne yike shiryawa ba kuwa?
Ya ƙara matsowa kusa da ita yana shafa wuƙar a hannun ta sai ga wuƙar ta ɓace
"aduk sanda ki ka amince zaki yi amfani da ita ki shafa hannun ki kawai zata fito,
sai dai wannan wuƙar tana da sharaɗi"
Ya ɗan tsaya yana kallon yana yin fuskar ta sannan ya cigaba da cewa
"a yayin da ta coki jikin sa zata fitar da duk wata cuta ta jikin sa a take, sai
dai zata mantar dashi rayuwar da yayi na shekaru shida da suka wuce"
"zata mantar da shi rayuwar sa ta shekaru shida? ban gane abunda kake nufi ba"
"kije kiyi nazarin abunda na faɗa zaki gane abunda nike nufi, na barki lafiya"
Me yike nufi?
Ɗakin ta shiga yana durƙushe kusa da bayi da alamu bayin yaso ya shiga ya kasa
Kakari yike yi kamar ransa ze fita,Idanuwansa sun yi jawur saboda tsananin wahala,
hawaye kawai Rauda keyi
Yafi minti goma a haka, da ƙyar ya samu ya amayo wani dunƙulen jini
Jikinsa yayi mugun sanyi dan ya sha wahala sosai, ja baya yayi da ƙyar ya jingina
da jikin gadon yana maida numfashi a wahalce
Tashi tayi ta gyara wurin har lokacin idanuwanta basu dena zubar da hawaye ba
Sai da tagama sannan ta dawo kusa dashi ta zauna ta zuba mai ido cike da tsananin
tausayin sa
Ba tace komai ba ta fara mammatsa mai ƙafafun, zuwa can ta ɗago ta kalle sa tace
"Jaana yanzu a haka zamu cigaba da zama, kana cikin wannan halin?
"dan Allah ba Danni ba ka yi abunda yace, lafiyar ka tafi min komai, ko da bana
tare da kai idan nasan kana cikin ƙoshin lafiya zanji daɗi amma bazan iya jurar
ganin ka a wannan halin ba, bazan iya ba"
Umar ya sauke doguwar ajiyar zuciya tare da sa hannu ya janyo ta jikin sa ya matse
ta tsam yana sauke numfashi
"Rauda ina miki so me tsanani wanda duk runtsi duk wuya bazan taɓa rabuwa dake
ba,dan Allah kada ki ƙara ambaton rabuwa a tsakanin mu"
"tunda mukai aure baka samu farin ciki daga wurina ba, inbanda fargaba da tashin
hankali umar dan Allah.......
"na faɗamiki duk runtsi ina tare da ke, wallahi koda mutuwa zanyi bazan taɓa cikama
wancan azzalumin burin sa ba"
*~ƴarfillo.~*
[20/10, 8:47 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
3⃣ 5⃣ 3⃣5⃣
3⃣5⃣
AGE
_10:23_🕒 AM
MON, OCT 14
Yana rungume da ita bacci ya ɗauke shi,tashi tayi ta janye jikin ta zauna
Maganar da suka yi da Aasim ce ta dawo mata, me yike nufi da idan wuƙar ta caki
Jikinsa zata mantar dashi rayuwar da yayi na shekaru shida?
Ta ɗan yi shuru tana nazari, kenan yana nufin har da ita umar ze manta a rayuwar
shi dan shekarunsu biyar da sanin juna
Ta ya ya Hakan ze yuwu?
Tashi tayi jikinta babu ƙwari ta sauko ƙasa dan dole ta sake neman Aasim
Kallon juna suka yi na ƴan sakwanni sannan ta ɗauke kanta ta maida kallon ta gefe
"inaso ka ƙara yimin bayani akan abunda kace ɗazu, dan ni ban gane ba"
"kace ze warke amma ze manta da rayuwar da yayi abaya har ta tsawon shekaru shida,
kenan kana nufin har dani ze manta?
" eh har dake ze manta,dan idan har kika Coke sa da ita ze suma baze farfaɗo ba har
sai yayi minti talatin, a lokacin da ze farka ze manta dake ze manta wacece ke da
kuma matsayin da kike dashi a wurin sa, kinga shi kenan burina ya cika dole zaki
nisance sa kikasan ce tare dani ni kaɗai"
Takasa ƙara furta komai kallon sa kawai take yi, ya matso kusa da ita yasa hannu
yana shafa gefen wuyan ta
"dani kaɗai zaki rayu Rauda, har ƙarshen rayuwar ki kuma kisani da zarar yayi
wannan Suman ya farfaɗo kada ki sake ki nuna masa ke matar sa ce ke duk wani abu ma
da kika san idan ya gani ze tuna dole ki fara kauda sa tun yanzu"
"ya kake so inyi da iyayena ƴan uwa na da kuma ƴan uwan shi da basu san matsalar da
muke ciki ba? Aasim wannan ba adalci bane kar kamanta fa nidashi ma'aurata ne ta
yaya zaka sanya wannan shamakin a tsakanin mu?
Guntun murmushi yayi yana taɓe baki cikin yana yin ko in kula
"wannan matsalar ki ce ba tawa ba, nadai gaya miki wannan ce kaɗai damar da kike da
ita idan kinga dama kiyi amfani da ita idan kuma bakiga dama ba ki barta"
"kinga ni daga yanzu ma ba zaki ƙara nemana kiganni ba, dan haka zaɓi ya rage
gareki abu ɗaya dai nike so ki ƙara sani ke Rauda tawa ce ni kaɗai
Na barki lafiya"
Kanta ta kifa kan gwiwowin ta, wasu hawaye masu ciwo suna gangaro mata
Bayan sati ɗaya, umar ya jigata iya jigatuwa dan ya fita daga hayyacin sa ma tuƙa
Duk wanda ya gan sa sai ya tausaya masa dan ya koma kamar bashi ba
Hankalin ƴan uwa ya tashi sosai, musamman anty kaltum da kullum a gidan take wuni
Rauda ko ta rame sosai dan rabon da ta sama cikin ta wani abu har ta manta
Ranar wata Asabar Jikinsa yayi tsanani sosai dan be taɓa shan wahalar da ya sha a
ranar ba
Anty kaltum ta fito daga ɗakin tana share hawaye dan gani take tana gab da rasa ɗan
uwan ta
"Rauda ba nace kidena zurfafa tunani bane? So kike yi kema wani abu ya same ki?
" gaskiya kin bani mamaki bantaɓa tunanin jin haka daga gareki ba"
"anty Sam ba wai dan lalurar da Allah ya ɗaura masa bane nace Hakan, a'a saboda
nice sanadiyyar shigar sa cikin halin da yike ciki"
"bangane ba"
Kwashe komai Rauda tayi ta faɗa mata sannan ta fashe da kuka tana cigaba da cewa
"anty inason umar bazan iya jurar ganin sa cikin wannan halin ba, kisa baki dan
Allah ya sake ni ko ya samu sassauci"
Anty kaltum zufa ce kawai ke karyo mata gabaɗaya tausayin Rauda ya kamata
"kunsan kuna cikin wannan matsalar me yasa baku sanar mana ba tun tuni?
" dole zamu nemi mafita baze yuwu ayi masa yadda yike so ba, bari na kira hajiya
(kakar su)
" hajiya yanzu ba lokacin wasa bane a kan maganar rashin lafiyar umar ne"
" yanzu yaki ke ganin za ayi? Akwai wani malamin da kike ganin ze iya?
Hajiya tace
"akwai shi nan kusa damu ma kuwa"
*~ƴarfillo~*
[20/10, 8:47 pm] Sumiee B.: *🌹JINNUL*
*AASHIQUE🌹*
NA
HARIRA ALIYU _(ƴarfillo)_🧕🏻
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
3⃣ 6⃣ 3⃣6⃣
3⃣6⃣
AGE
*_Wannan page naki ne mariam Nijer ina godiya da ƙaunarki ga wannan littafi Allah
ya bar zumunci_*
_9:22_🕒 PM
SUN, OCT 20
_Bissmillahir rahmanin rahim_✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
"shi kenan kije kisamesa yanzu gobe sai ku biyo jirgin yamma dan allah hajiya"
"Insha Allahu"
Sallama suka yi anty kaltum ta ajiye wayar tana duban Rauda wacce ta zabga tagumi
"ki kwantar da hankalin ki Rauda Insha Allah zamu sami mafita kinji"
Rawar sanyi yike yi sosai dan haƙorarsa har wasu ƙarar karawa da juna suke yi
Ya rame ya ɗashe jikin sa kamar babu jini abunka ga farin mutum sai yayi kamar
takadda
"ina tare dake masoyiyata duk runtsi duk wuya bazan taɓa guje miki ba"
Ya faɗa a cikin zuciyar sa yana maida idanuwansa ya rufe saboda azabar da yike ji
na nuƙurƙusar cikin ƙasusuwan jikin sa
Hajiya kam kuka take yi sosai ganin yadda umar ya koma cikin ƙanƙanin lokaci
Malan Audu ya ɗauko wata ƙaramar jarka wacce take cike da ruwan rubutu
Umar ya amsa ya kafa kai sai dai yana sha yaji cikin sa yayi wani irin ƙullewa
Gaf-gaf-gaf jikin sa ya fara rawa kan kace kwabo kujerar da yike ta fara jijjiga da
ƙarfin gaske
Wata kalar iska ce zagaye kujerar da yike kai ta fara ɗaga sa ta maka sa da bango
Sannan ta maida sa ɗaya bangon ta kuma makawa kafin wani ɗan lokaci tuni yayi jina-
jina
Da taimakon addu'ar da malan Audu yayi tayi ne iskar ta lafa, lakwaf ya faɗo kan
kujerar
"a gaskiya hajiya iyakar abunda zan iya kenan domin idan aka ce za a cigaba wahalar
da tafi ta yanzu ze kuma sha saboda wannan gubar dake jikin sa"
Umar be bata amsa ba dan be ma san abunda take cewa ba har lokacin kallon Rauda
kawai yike yi
Hajiya ta taso tana gallawa Rauda harara dan gabaɗaya haushin ta take ji saboda
dalilin ta ji kanta ya shiga cikin wahala
"magana nike yi ko baka Jina ne? Nace ka sake ta yanzu yanzunnan tunda ba ƴar gwal
bace, kai ko ƴar gwal ɗince ma rabuwa zaka yi da ita dole!
A galabaice yike kallon hajiya cikin muryar sa da tayi sanyi sosai yace
"ya zamar maka dole umar, wallahi sai ka sake ta ba zamu zuba ma ido ka mutu akan
mace ba, kayi abunda nace!
"umar baze taɓa iya Sakina ba hajiya, kiyi haƙuri nikaina bazan iya cigaba da ganin
sa acikin wannan halin ba ina da wata mafita guda ɗaya"
"ya bani zaɓi amma Hakan baze yuwu ba har sai kun bani goyon baya da haɗin kai"
"yace dole ne inkauda duk abunda ze tuna ma umar dani matar sace dan duk ranar da
ya tuna to ciwon da yafi nada ze dawo masa kuma bayi da makari, ina roƙon ku da ku
taimake ni wajen cika sharuɗɗan wannan mafitar"
"yanzu ashe zaki iya bin umarnin azzaluminnan wurin rabuwa dani? Kenan kin zaɓi
rayuwa dashi dani kenan? Ashe ƙaunar da kike masa tafi wacce kike min?
" ba haka bane umar kasani rayuwa ta ragaggiya ce idan har zanyi ta babu kai, amma
kasani son da nike yi maka ne yasa na amince da buƙatar sa dan bazan iya ganin ka a
wahala ba"
"ina baki umarni a matsayi na na mijin ki da kada ki sake ki aikata haka agareni,
dan idan kika yi sanadiyyar da zan manta dake wallahi bazan taɓa yafe miki ba
Rauda"
Tashi tayi dag wurin ta haye sama tana kuka kan gado ta faɗa tana jin numfashin ta
nayi mata sama-sama to wai ita ya zata yi da rayuwar ta ne?
Zama tayi gefen gadon tana kallon ta gabaɗaya ma ta rasa me zata ce mata
"ya zanyi da raina, anty wallahi dama mutuwa nayi da ganin wannan rayuwar me cike
da ruɗani"
Anty kaltum da sauke numfashi tana girgiza kai cikin damuwa tace
"kada ki ce haka Rauda ko wani ɗan adam yana tare da jarbawar sa kiyi haƙuri ki
cinye nasan Allah yana tare dake"
"shi kenan anty, dan Allah ki taimakamin gurin aiwatar da wannan abun, acikin kwana
biyu kaɗai"
Anty kaltum gabaɗaya tausayin ta ya dabai bayeta cikin sanyin jiki tace
"Insha Allahu zan taimaka miki Rauda kuma wannan soyayyar da kuke wa juna nasan
Allah baze barku a haka ba duk daren daɗe wa ze yassare muku Insha Allahu
Da daddare kowa ya kwanta dan hajiya da anty kaltum ma a gidan zasu kwana zayyad ne
kaɗai ya tafi
Rauda bayan ta idar da sallah ta shiga kicin ta haɗa mai lipton dan shi kaɗai yike
iya sha
Ɗakin sa ta nufa ta tura ƙofar
Yana jingine da gado ya Lula cikin tunani murɗa ƙofar da tayi ne yasa ya dawo daga
dogon tunanin da ya tafi
"kada ki sake ki shigo min ɗaki, ki koma bana buƙatar ganin ki"
Ya jinjina kai
Zumbur ya miƙe yana ɗan ja da baya dan gani yike yi kamar zata caka mai wuƙar da
Aasim yace, bawai tsoron wuƙar yike ji ba a'a yana tsoron ya manta da ita ne
Jiri yaji yana neman ya kwashe sa yayi ƙoƙarin dafa bango amma kafin ya kai ga dafa
bangon tuni ya zube a ƙasa
*~ƴarfillo~*.