Content-Length: 116512 | pFad | http://ha.wikipedia.org/wiki/Frederick_Lugard

Frederick Lugard - Wikipedia Jump to content

Frederick Lugard

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Frederick Lugard
Governor-General of Nigeria (en) Fassara

1 ga Janairu, 1914 - 8 ga Augusta, 1919
← no value - Hugh Clifford (en) Fassara
Gwamnan Arewacin Najeriya

Satumba 1912 - 1 ga Janairu, 1914
Charles Lindsay (dan siyasar Birtaniya) - Charles Lindsay Temple
14. Governor of Hong Kong (en) Fassara

29 ga Yuli, 1907 - 16 ga Maris, 1912
Matthew Nathan (en) Fassara - Francis Henry May (mul) Fassara
Gwamnan Arewacin Najeriya

1900 - 1906
← no value - Percy Girouard (en) Fassara
Member of the Privy Council of the United Kingdom (en) Fassara


member of the House of Lords (en) Fassara

unknown value
Rayuwa
Haihuwa Chennai, 22 ga Janairu, 1858
ƙasa Birtaniya
United Kingdom of Great Britain and Ireland
Mutuwa Dorking (en) Fassara, 11 ga Afirilu, 1945
Ƴan uwa
Mahaifi Frederick Grueber Lugard
Mahaifiya Mary Jane Howard
Abokiyar zama Flora Shaw, Lady Lugard  (11 ga Yuni, 1902 -
Ahali Edward James Lugard (en) Fassara
Karatu
Makaranta Royal Military College, Sandhurst (en) Fassara
Rossall School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a mabudi, hafsa da ɗan siyasa
Wurin aiki Landan
Kyaututtuka
Aikin soja
Fannin soja British Army (en) Fassara
Digiri Janar
Ya faɗaci Mahdist War (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Conservative Party (en) Fassara

Frederick John Dealtry Lugard, 1st Baron Lugard (Yarayu daga 22 Janairun shekarar alif 1858 zuwa 11 Afrilu 1945), Anfi saninsa da Sir Frederick Lugard daga tsakanin shekara ta alif 1901 da 1928, yakasance sojan British ne, Dan'sonkai, Mabincikin Afirka kuma Mai'aiwatar da harkokin mulkin mallaka. Yayi Gwamnan Hong Kong a (1907–1912), Gwamnan ƙarshe na Southern Najeriya Protectorate a (1912–1914), Kwamishinan Birtaniya na farko a Nijeriya, daga (1900–1906) kuma shine Gwamnan karshe daga (1912–1914) na gabashin najireya Protectorate sannan kuma ba Governor-General na najireya daga shekarar (1914 zuwa 1919).

Farkon Rayuwarsa da Karatunsa

[gyara sashe | gyara masomin]
Wata Gada da ya gina

An kuma haife Lugard a Madras (now Chennai) dake Indiya, Amma ya girma ne a Worcester, kasar Ingila. Mahaifinsa shine Rev'd Frederick Grueber Lugard, Malamin dake was sojojin Biritaniya wa'azi a Madras, Mahaifiyarsa itace ta uku a wurin mahaifinsa, uwargida Mary Howard (1819–1865), yar'autar Rev'd John Garton Howard (1786–1862), wanda shine karamin yaron landed gentry daga Thorne da Melbourne kusa da York. Lugard yayi Karatunsa ne a Rossall School da kuma Royal Military College, Sandhurst. Sunan 'Dealtry' da ake masa, girmamawa ce ga Thomas Dealtry, abokin mahaifinsa ne.[1]

Lugard yafara aikin soja a karkashin 9th Foot (East Norfolk Regiment) a shekara ta 1878, inda yashiga bataliya ta biyu, a kasar Indiya kuma yana cikin wadanda suka jagoranci kaddamar da yaki daban-daban, kamar:

Yayi aikin soja

Anzabi Lugard dan kasancewa cikin Distinguished Service Order a 1887.[2]

Yakin Karonga

[gyara sashe | gyara masomin]

Tsakanin shekarar 1880, wasu ƙungiyar yankasuwan Swahili karkashin Mlozi bin Kazbadema, sun samar da wuraren kasuwanci a shiyar arewa maso yammaci na tabkin Malawi, wanda yahada da wani kurkuku a Chilumba a tabkin daga inda ake dibar ivory da bayi dan tafiya dasu. A shekarar 1883 kamfanin tabkokin Afirka suka Samar da wurin a Karonga domin chanja ivory da kayayyakin kasuwanci a wurin yan'kasuwan Swahili.[3][4]

Hulda yayi tsami tsakanin bangarorin biyu, saboda tsaiko da ake samu a kamfanin wurin Samar da bindigu, alburusai, da sauran kayan kasuwanci, da kuma saboda yan kasuwan Swahili sunfi komawa ga kama bayi, da kai farmaki a wuraren da kamfanin yayi alkawarin basu kariya, daga nan aka fara samun kiyayya har zuwa shekara ta 1887. Jerin kaikawon da aka rika samu a wannan lokacin har zuwa tsakiyar shekara ta 1889, shi akekira da Yakin Karonga, ko kuma a wani lokacinYakin larabawa.[5]

Kamfanin Tabkunan Afirka an kawar da ita a karshen shekara amma saidai a watan Mayun shekarar 1888, Captain Lugard, ya tunzuru daga British Consul dake Mozambique, sai yadawo ya jagoranci yaki da Mlozi, wanda kamfanin Tabkunan Afirka ta dauka nauyi, batare da taimakon Gwamnatin Biritaniya ba.[6]

Frederick Lugard

A watan Mayu zuwa Yulin shekarar 1888 Lugard ya kaddamar da farmaki na farko akan Swahili, a wannan farmakin ne, akayi wa Lugard rauni sannan aka maida shi kudanci.[7][8] Lugard yakai hari na biyu a watan December 1888 zuwa March 1889 itace babba kuma harda 7-pounder gun, wanda yakasa rusa ganuwar, bayan kuma rashin nasaran nan na biyu ne, Lugard yabar yankin Tabkin Malawi yakoma Biritaniya a April 1889.[9][10]

  1. cite web|url=https://www.findagrave.com/memorial/126290001/frederick-john_dealtry-lugard%7Ctitle=Sir Frederick John Dealtry Lugard (1858-1945) - Find A Grave Memorial|date=13 June 2018
  2. London Gazette |issue=25761 |date=25 November 1887 |page=6374
  3. O. J. M. Kalinga, (1980), The Karonga War: Commercial Rivalry and Politics of Survival, Journal of African History, Vol. 21, p. 209
  4. J. McCracken, (2012), A History of Malawi, 1859–1966, Woodbridge, James Currey pp. 27, 49. ISBN|978-0-521-21444-5
  5. J. McCracken (2012), A History of Malawi, 1859–1966, Woodbridge, James Currey pp. 51-2. ISBN|978-0-521-21444-5
  6. F. G. Lugard (1893). The Rise of Our East African Empire, Vol 1: Early Efforts in Nyasaland and Uganda, (1968 reprint), Abingdon, Routledge pp. 48-9. ISBN|0-415-41063-0
  7. F. G. Lugard (1893). The Rise of Our East African Empire, Vol 1: Early Efforts in Nyasaland and Uganda, (1968 reprint), Abingdon, Routledge, pp. 66-7. 08033994793.ABA
  8. P. T. Terry, (1965). The Arab War on Lake Nyasa 1887-1895, The Nyasaland Journal, Vol. 18, No. 1 pp. 74-5(Part I)
  9. F. G. Lugard (1893). The Rise of Our East African Empire, Vol 1: Early Efforts in Nyasaland and Uganda, (1968 reprint), Abingdon, Routledge, pp. 135-6. 08033994793.ABA
  10. P. T. Terry, (1965). The Arab War on Lake Nyasa 1887-1895 P. T. Terry, (1965). The Arab War on Lake Nyasa 1887-1895 Part II, The Nyasaland Journal, Vol. 18, No. 2, pp. 31–33








ApplySandwichStrip

pFad - (p)hone/(F)rame/(a)nonymizer/(d)eclutterfier!      Saves Data!


--- a PPN by Garber Painting Akron. With Image Size Reduction included!

Fetched URL: http://ha.wikipedia.org/wiki/Frederick_Lugard

Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy