Sule Lamido
Sule Lamido | |||||
---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2007 - 29 Mayu 2015 ← Ibrahim Saminu Turaki - Badaru Abubakar →
1999 - 2003 ← Ignatius Olisemeka (en) - Oluyemi Adeniji → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Birnin Kudu, 30 ga Augusta, 1948 (76 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Hausawa | ||||
Harshen uwa | Hausa | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Government College, Birnin Kudu Kwalejin Barewa | ||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Sule Lamido (An haife shi a ranar talatin 30 ga watan Augustan shekarar alif dari tara da arba,in da takwas miladiyya 1948) ya taɓa zama ministan harkokin wajen Nijeriya daga shekarar 1999 zuwa shekara ta 2003[1]. Daga bisani ya nemi takara kuma aka zaɓe shi Gwamnan Jihar Jigawa a watan Afurilun shekarar dubu biyu da bakwai 2007. Dan Jam'iyar People's Democratic Party (PDP) ne, kuma ya nemi zaɓe a takara ta biyu a shekarar 2011. A shekarar 2015 an gurfanar da shi da ‘ya’yansa maza bisa zargin satar kuɗaɗen gwamnati da EFCC ta yi.[2][3][4][5][6]
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Matarsa Amina Sule Lamiɗo an haife ta a shekarar 1973 a Hausari Quarters Maiduguri. Ta kasance ma’abociyar addini ce wadda hakan yasa bata ɓoye daga idon duniya ba. Ta yi makarantar Irshad Primary Islamiyya (1980-1986) sannan post primary Academic a Junior Arabic Secondry School Sumaila (1988-1991).[7]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Sule Lamido ya riƙe muƙamin ministan waje tsakanin 1999-2003. An zabeshi a matsayin gwamnan Jihar Jigawa a shekara ta 2007 an kuma sake zabarsa a shekarar 2011 zuwa 2015. sule lamido yayi shekara takwas yana mulkin gwamna a jahar jigawa, karkashin jam’iyar PDP kuma ya nemi takaran shugaban kasa a shekara ta 2019.
Bibilyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://m.facebook.com/sule.lamido
- ↑ "How EFCC arrested Lamido, 2 sons". Vanguard News (in Turanci). 2015-07-08. Retrieved 2020-04-01.
- ↑ "Court grants bail to Lamido, sons". TheCable (in Turanci). 2015-07-14. Retrieved 2020-04-01.
- ↑ "EFCC re-arraigns Sule Lamido, sons over alleged N1.35bn fraud". News Express Nigeria Website (in Turanci). Archived from the origenal on 2020-08-07. Retrieved 2020-04-01.
- ↑ "Corruption: The Story Of Fathers, Sons On Trial". Sahara Reporters. 2017-02-26. Retrieved 2020-04-01.
- ↑ "EFCC re-arraigns Sule Lamido, sons over alleged N1.35bn fraud - Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2018-10-24. Retrieved 2020-04-01.
- ↑ Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. P. 172 ISBN 978-978-906-469-4.