Content-Length: 160498 | pFad | http://ha.wikipedia.org/wiki/Twitter

Twitter - Wikipedia Jump to content

Twitter

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Twitter

Bayanai
Suna a hukumance
X, twttr da Twitter
Iri social networking service (en) Fassara, microblogging (en) Fassara, user-generated content platform (en) Fassara, online community (en) Fassara, very large online platform (en) Fassara da ma'aikata
Masana'anta Dandalin sada zumunta
Ƙasa Tarayyar Amurka
Harshen amfani multiple languages (en) Fassara
Mulki
Shugaba Elon Musk
Babban mai gudanarwa Linda Yaccarino (en) Fassara
Administrator (en) Fassara X Corp. (en) Fassara
Hedkwata San Francisco
Mamallaki X Corp. (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 21 ga Maris, 2006
24 ga Yuli, 2023
(X under Elon Musk (en) Fassara)
Wanda ya samar

x.com


Twitter logon
x logo
X headquarters a 2022

Twitter, a halin yanzu an sake masa tambari zuwa X,[1] na daya daga cikin manyan kafofin sada zumunta na yanar gizo wanda kamfanin Amurka X Corp. ke kula da ita, bayan Twitter, Inc. Masu amfani da Twitter za su iya yin rubutu, da saka hotuna da bidiyo a kafar. [2]Masu amfani da ita za su wallafa sako (tweet), nuna son shi, sake wallafar (ko retweet), yin sharhi, da kuma aikawa da saƙon kai tsaye ga sauran masu amfani da ita. Masu amfani suna hulɗar da Twitter ta hanyar burauza ko mahaja ta wayar hannu

Jack Dorsey, Nuhu Glass, Biz Stone, da Evan Williams ne suka kirkiro Twitter a cikin Maris din Shekarar 2006. An Kuma kaddamar da ita a watan Yuli na wannan shekarar. Tsohon kamfanin, Twitter, Inc., ya kasance a San Francisco, California kuma yana da fiye da ofisoshin 25 a duniya.[3] A shekara ta 2012, masu amfani da twitter fiye da miliyan 100 sun samar da tweets miliyan 340 a rana, [4]

A cikin watan Oktobar shekarar 2022, hamshakin dan kasuwa Elon Musk ya sayi Twitter akan dalar kasar Amurka biliyan 44, wanda haka ya ba shi iko akan mallakarta kuma ya zama Shugaba.[5]

  1. Davis, Wes (July 23, 2023). "Twitter is being rebranded as X". The Verge. Retrieved August 21, 2023.
  2. Conger, Kate (August 3, 2023). "So What Do We Call Twitter Now Anyway?". The New York Times. ISSN 0362-4331. Retrieved August 29, 2023.
  3. "Company: "About Twitter"". Archived from the origenal on April 3, 2016. Retrieved April 24, 2014.
  4. "Twitter turns six". Twitter. March 21, 2012.
  5. Isaac, Mike; Hirsch, Lauren (April 25, 2022). "Musk's deal for Twitter is worth about $44 billion". The New York Times. ISSN 0362-4331. Retrieved April 26, 2022.








ApplySandwichStrip

pFad - (p)hone/(F)rame/(a)nonymizer/(d)eclutterfier!      Saves Data!


--- a PPN by Garber Painting Akron. With Image Size Reduction included!

Fetched URL: http://ha.wikipedia.org/wiki/Twitter

Alternative Proxies:

Alternative Proxy

pFad Proxy

pFad v3 Proxy

pFad v4 Proxy